Showing 3001 words to 6000 words out of 15272 words
Chapter 2 - YASMEEN COMPLETE HAUSA NOVELS BY MAMAN YUSRA.txt
daya bamu.
Kana iya k'ok'arinka wajen ba y'ay'anka tarbiya wasu b'ata gari suna warwarema.
Allah kar kabarmu da iyawarmu kamana jagora wajen ba y'ay'ayenmu tarbiya.
Fitowa kawai nayi daga cikin hall d'in don idona bazai iya jurar kallon wannan iya shegenba.
Nafi awa tsaye awaje ina tunani yadda zan koma gida ga wajen da d'an karan nisa.
Jinayi an rik'emin k'ugu tare da fad'in
"fine baby ke bazaki shiga ayi rawar dake bane?"
Juyowa naye da sauri na tureshi tare da kwad'a mashi mari cikin b'acin rai.
โ๐ป *~UMMYN YSRH~*
[02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: ๐๐๐๐๐๐๐
๐๐๐๐๐
๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
*YESMEEN*
๐๐๐๐๐๐๐
*STORY & WRITEN BY:*
*UMMYN YSRH*
*ยฎPURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
_KINCHANCHANCI YABO TA KO'INA DOLE IN YABA KUMA IN GODIYA DA FATAN ALKHAIRI AGAREKI_
*SIST HALIEYMERH AMEEN*
_ALLAH JA KWANA DA LFY MAI AMFANI ALLAH K'ARA D'AUKAKA YABAR ZUMUNCI_๐๐
*inaba masoya wanna novel hak'uri na rashin jina da sukayi na kwana da yawa amin afwa kunsan jiki da jini๐ฅ*
*35~40*
Fitowa tayi da sauri da nufin shiga kitchen don taji kamar miyarta na kamawa,bata kulaba ji tayi ta buge mutum,juyowa tayi don bata hak'uri,saidai kafintayi magana Hajiya Talatu ta rigata,
cikin masifa tace
"Tooow! Muguwa,y'ar bak'in ciki.shine kika taho aguje don ki bangajeni?
Kina bak'in cikin cikin jikina ko? Burinki ya zube muzama d'aya ,toh ta Allah ba takiba,keda haihuwa saidai kiga munayi,mun ajiye biyar gana shida yana hanya."
Ummah Habiba tace
"don Allah ki hak'uri bada niyya na buge kiba,miyace naji tana kamawa na shiga sallah shine na fito da sauri,amma ki hak'uri."
Sallama sukaji daga k'ofar falon da sauri Hajiya Talatu ta durk'ushe gurin tana rik'e ciki,tare da bubbuga y'ar yatsarta kamar mai nak'uda,lokaci guda ta fita hayyacinta.
Umma Habiba ta amsa sallamar tareda yima mai sallamar barka da zuwa saidai ko kad'an batabi ta kantaba,
"Subhanallah! Talatu meke faruwane?"
Cikin muryar wahala tace
"ina d'aki naji miya na kamawa a kitchen shine na duba na fito zan koma d'aki, shine Habiba ta fito ta nufoni gadan _gadan ya gulleni a cikina."
"ita Habiban!!?"
"eh,wai don meyasa zan tab'amata girki alhalin nasan baran girkina bane."
"toh!muguwa mai bak'in hali,y'ar bak'in ciki,duk tsiyarki sai jikana na fito duniya,idanma burinki cikin ya zube toh k'aryarki munafuka,duk abunda yasami cikinnan k'arshen zamanki kenan agidannan wallahi."
"wallahi bada sani na bugetaba Haj......."
"rufemun baki,tunda tasamu cikinnan kike bak'in ciki,zamuje asibiti yanzu adubata kuma Wallahi ina k'ara gaya miki akasami wani abu ya tab'ata abakin aurenki."
Kama Talatun tayi ta zaunarta kan kujera taje ta d'auko mata hijabi a d'aki sukayi gaba,juyawar da Umma Habiba tayi zatayi kitchen wani jiri ya d'ebeta ta zube k'asa.
Tana kaiwa k'asa YESMEEN na shigowa hannunta rik'e da ledar aikar aikan a k'asa da gudu ta k'arasa gareta tana fad'in
"UMMAH lafiya?
meke faruwa.?
"bakomai jirine ya d'ebeni,taimakamin intashi."
Kamata tayi don ta mik'e saidai ina ta mata nauyi bazata iyaba,gashi gidan ba kowa koda akwima ba kulasu zasuyiba.
Dagudu ta fita tayi gidansu Hanifa,rabondasu had'u tunranda abunnan ya faru.
Har k'asa ta d'urk'usa tagaida Mommy tace
"Mommy Hany tanan kuwa?"
"tana ciki,ya jikinnaki tace bakiji dad'iba,bansami zamaba shiyasa banshigo na dubakiba."
"jiki yayi sauk'i sosai."
"Toh Allah k'ara afwa."
"Ameen."
D'akin k'awar tata ta nufa Hanifa na ganinta taji wani dad'i da farin ciki.
"Don Allah idan bakya komai zo ki tayani wani abu."
"lahh! bana komai dama kwanciya zanyi muje."
Gidan suka nufa da sauri,inda ta barta nan ta sameta,gasu RUKY da k'annenta biyu zaune a falon ba wanda ya kulata.
Suna k'ok'arin d'agata saiga Zarah ta fito hannunta d'auke da ruwa ta nufo gurinsu YESMEEN tace
"Aunty YESMEEN ga ruwan Auntyce tace in d'ebo mata zata sha,nace ta tashi wai bazata iyaba."
"eh,ZAHRA jiri takeji."
Ruwan ta bata tasha sannan suka kamata su ukun da kyar don UMMAH HABIBA akwai k'iba kamar k'awata (HAMEBRAH MAI BABBAN DUWAIS๐)
Gado suka kwantar da ita ko zuwa anjima zataji tare.
Sai wajen biyar Y'an asibiti suka dawo,Hajiya Talatu ras da ita kamar ba ita ake rik'ewa d'azunba.
Su RUKY suka tarar zauna ana kallo ba batun sallar azahar balle la'asar,sun tasa T.V agaba kamar ibada.
Hajiyace tace
"Ina Bibanne taji mundawo don bak'in hali bazata fito ta duba muba?"
Zahra data fito daga d'aki tace
"sannunku da dawowa.Aunty na d'aki kwance batajin dad'ine."
"k'arya take ba wani rashin lafiya muna furcine kawai,don nace idan wani abu yasami surukata da jikana abakin aurenta shine bari ta kwanta ciwon k'arya."
"Hajiya rabu da ita wani salon muna furcinne."
"koma me ita ta sani Allah ya taimaketa ba abunda ya sameku ai."
โ๐ป *~UMMYN YSRH~*
[02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: ๐๐๐๐๐๐๐
๐๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
*~YESMEEN~*
๐๐๐๐๐๐๐
*STORY & WRITEN BY:*
*~UMMYN YSRH~*
*ยฎPURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
*Dis page is 4 u my sist Luv*
*YESMEEN TAFEESU*
*Allah yabar zumunci yy rabaki da iyaye lfy ya miki zabi da miji na gari da zuri'a masu albarka* ๐๐ป
*41~45*
Har wajen magrib Ummah na kwance gawani matsanancin ciwon kai dake addabarta,gashi tak'i yarda inma Alhaji waya in sanarmai kasancewar baya gari.
Har wajen k'arfe takwas na dare ba wanda ya lek'o duba Ummah y'an cikin gida,sai Zahra itama saita faki idonsun take shigowa gudu_gudu ta dubata ta fice,Mommyn Hanifa ma tazo ta duba Umman,Hanifa kuwa tunda suka shigo d'aga Umma bata komaba,jitake kamar tacire ciwon tamaida jikinta don harda kukanta.
Yesmeen ce ta d'au wayar Ummah ta danna wayar k'awarta kuma kwararriyar likitanta, Hajiya Amira tana d'agawa Yesmeen cikin ladabi ta gaisheta sannan tamata bayanin abundake damun Umman nata,tace
"Gatanan zuwa yanzu ta fito daga asibiti zata gida kenan."
Sallama sukayi ta katse wayar.
Ba'ad'au wani lokaciba ta iso gidan,Sallama tayi k'ofar falon ba wanda ya amsa mata sai Zahra,shigowa tayi tama Hajiya Talatu barka da dare,dak'ar ta amsa mata tayi wucewarta.
Da sallama tashiga d'akin su Hanifa suka gaisheta,kan k'awar tata ta nufa tana fad'a
"Habba! Hajiya nace kidaina yawansa damuwa ma ranki,komaifa d'an hak'urine da juriya,lafiyarki ayanzu ya fiyemiki komai,kinsani sarai Zuciyarki daf take da tab'uwa amma kinasa damuwa ma ranki,barin gwada B.P naki meyuwa yasake hawane?"
"Subhanallahi!
Jininki ya hau sosai,garin yaya? Wani irin damuwane haka ya sa jininki ya hau har haka?
Ummah dake kwance hawaye kawai ke gangarowa daga idonta.
YESMEEN dake gefe tambayar kanta take
"dama Ummah nada hawan jinine? Koshiyasa take yawan zuwa asibiti? Allah sarki Ummahna."
"Allah ka azurtata itama da sanyin idaniyarta,Allah ka bata lafiya."
Da sauri ta shige bayan gida ta rufe kanta,tanaji Dr.Ameerah tagama yimata y'an nasihohi tare da bata magunguna da allurai,wasu Umman nadasu,wasu kuma sai zuwa gobe za'a siyo tunda dare yayi yanzun ba halin Yesmeen ta fita.
Sallama sukayi da likitan,da k'ar Ummah ta rarrashi Hanifa taje gida zuwa gobe saita dawo,badon ranta yasoba haka ta fito Yesmeen ta biyota domin rakiya,bayan ta rakata ta juyo zata tafi idonta ya mata mummunan gamo, Ruky ta hango chan gefe jikin wani lunge rungume da saurayinta,gaba d'ayan hannayenshi na cikin rigarta.
Wa'iyazu billahi hirar wasu samari da y'anmatan zamaninmu nayau kenana,Allah ka shiryamana zuri'a.
Da sauri tashige gidan tambayar kanta take ko lafiya harabar gidan ba wuta d'azu dazata wuce taga wuta, ko kwan ya mutune ohho.
Hannu takai jikin k'ofar da zai sadata da cikin gidan sai dai maimakon taji k'ofa sai taji kamar jikin mutum ta kama,da sauri taja baya cikin tsoro tana,
Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un
Ta juya zata sa gudu tayi waje taji charaf an chafketa,runtse ido kawai tayi tana jero addu'o'in dayazo bakinta don tasan yaukam tata ta k'are yaukam tayi gamo,don dagajin irin wannan damk'ar da akai mata bana bil'adama bane.
Cikin sanyin murya kamar mai rad'a taji yace
"Yesmeen!
Don Allah ki taimakeni ko leb'en bakinki in tsotsa ko zan samu sukuni,kullum da sha'awarki nake kwana nake tashi."
Dummmmmmm!!!!!! taji k'irjinta yabada sauti, ba kowa ya mata wannan aika aikanba face babban d'an Hajiya Talatu Sani.
Kokawar yadda zata kwaci kanta take shikuma k'ok'arin cika burinshi yake,cikin ikon Allah sukaji bud'e k'ofar Gate d'in alamun shigowa,da sauri ya saketa yana ciza yatsa yace
"Next time."
K'ofar falon ya bud'e tayi saurin shigewa,shikuma ya wayance kamar wanda ya fito daga ciki Ruky na ganinshi tace
"Ah! Yaya bakai baccibane?.
cikin k'uluwa dajin haushi yace
"banyiba y'ar iska jiranki nake,don kinga Alhaji baya gari shine bari kikai dare haka awajeko?"
harararshi take cikin duhu tace
"kaima yaud'in ai sa'a akaci kadawo gida da wuri."
"naji wuce ni kuban waje,wutannan nazo dubawa naga ya d'auke."
Wucewa tayi hannuta d'auke da ledodi guda biyu,tana wucewa yaje ya kunna wutan daya kashe dama yana ganin fitar Yesmeen ya fito daga d'akinshi da sauri ya kashe wutan domin cikar burinshi,saidai Allah bai bashi sa'a ba.
Ahankali ta shiga d'akin gabanta sai fad'i yake tana tunanin k'aryar dazatama Ummah idan ta tambayeta musabbabin dad'ewarta.
Hamdala tayi dataga tayi bacci,waje tasamu itama ta kwanta tare da addu'ar neman tsari dakuma fatan kar Allah yaba Yaya Sani galaba akanta.
โ๐ป *~UMMYN YSRH~*
[02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: ๐๐๐๐๐๐๐
๐๐๐๐๐
๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
*YESMEEN*
๐๐๐๐๐๐๐
*BY*
*UMMYN YSRH*
*ยฎPURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
*31~35*
Mutanen dake wajen duk suka juya don jin k'aran marin.
Wata daga gefe tace
"kai! yau JENTLE aka ma wanna marin? tashin hankali."
Da gudu ta garzaya cikin hall d'in don isarda abunda ya faru.
Cikin b'acin rai YESMEEN ta kalleshi rai b'ace take zazzagamai
"Don tsabar iskanci uban wa yabaka izinin tab'ani? Kai waye cikin muharramaina da har zaka kai hannunka jikina?
"ka dubeka,ka dubi shiganka ahakan idan an tambayeka zaka iya cewa kai musulmine."
"kun maida tab'a jikin junanaku tamkar wani sabon salon wayewa"
"ayau wai idan saurayi baitab'a jikinki ba sam baki wayeba."
"meye wayewar awanna d'abi'ar da rayuwar."
Waje yagama cikewa da mutane,
"Kudubeku amatsayinku na y'ay'a mata kuduba irin shigar dake jikinku na tabbata mafi yawanku bada wannan shigar kuka baro gidajen iyayenkuba."
"kunzo sai tabka zunubi da sab'ama ubangiji kuke."
"su mazan da kuka bari suke rungumeku suke shafe ko ina na jikinku kunada tabbacin aurenku zasuyine?"
"idan kunkai ga aure wani k'ima da daraja zakuyi a idonsu?"
"ko kuna tunanin zasu gama daku wani ya kwasane?"
"ko kad'an ba wanda zaiso zab'ama y'ay'a yenshi uwa ko ubanda bama gariba."
"wasu daga cikinmu bada sanin iyayenmu mukazonan ba idan Allah ya d'au rayuwarmu ahakan mezamucema Ubangijinmu."
"ga sab'ama ubangiji ga ha'intar iyayenmu dasuka d'au tsawon lokaci suna bamu tarbiya maikyau,mukuma muna ha'intasu."
"babu uwa ko uban da zaiso ganin y'ay'anshi cikin wannan shiga da mummunan yanayi da wasu daga cikinku suke."
"ayanzu mund'au rayuwar shaye_shaye wayewa da burgewa baga mazanba baga matanba."
"munsai cuta da hannunmu mun banka ma cikinmu,akwan kad'an kaga mutum nabun hanya yariga yamai illah,kekuma kinriga kin b'ata mahaifarki da kanki."
"wani riba akaci arayuwar shaye_shaye?"
"karfa kumanta duk abunda d'a namiji yayi adone,keko yananan yana bibiyarki har k'arashen rayuwarki."
"amatsayinmu na iyayen gobe idan mukaga iyayenmu cikin irin wannan yanayin ya zamuji azuciyarmu?"
"ku kwatanta hakan don suma iyayenmu haka zasuji idan sungamu ayanzu."
"muji tsoron Allah, muji tsoron randa zamu tsaya gaban ubangijinmu."
Tana kaiwanan tajuya tabar waje
Y'an isgili jikake
"Allahu akbar malama."
Suka juya sukayi ciki akacigaba da holewa
Way'anda abun ya shigesu suka shiga domin tattara kayansu suyi gaba.
Su malam JENTLE tunda yasha mari akabarshi tsaye sake da baki ranshi inyayi dubu ya b'aci yana tuna irin hukuncin dazai mata,kawai ganin bayanta yayi tayi gaba.
Adam ya kalli Hanifa yace
"Wai ina kika kwaso mana wannan y'ar k'auyen?"
"Y'ar k'auyefa kace?"
"YESMEEN d'ince baka saniba kome?"
"idan nasanta seme? Baki gayamata inda zakizo bane duk ta b'atamana show yadda mukaci burin chashewa da kwasar garar y'an mata."
"owwwohhhh!
Nufinku kenan akanmu?
Toh Allah bai baku nasaraba."
"kuma kasani zan iya jure cin mutuncinda za'amin, amma kar mutum yasake ya tab'a YESMEEN don akanta sai inda k'arfina ya k'are."
"kuma kasani duk bibiyar club danakeyi bantab'a saida mutuncina ga wani d'a namiji ba balle har kaci galaba akaina."
Ahaka suka rabu baram_baram,ta kwashi kayanta tayi gaba.
Lokacin data fito chan nesa ta hango YESMEEN tanata tafiya lokacin gari ya fara duhu,sauri sauri gudu gudu ta iskota tace
"Don Allah ki yi hak'uri y'ar'uwa danasan hakan zai faru kodawasa bazan fara gayyatokiba,Don Allah kimin afwa na tuba."
Juyowa tayi tamata wani irin kallo ta juya batace komaiba, adaidaita suka shiga, har suka iso gida ba wanda yakema kowa magana, suna sauka tashige gida,kafin Hanifa tasallami mai adaidaita harta shige.
Jitayi kamarta bita saikuma ta fasa zata bata lokaci harta huce.
Lokacin data dawo Umma Habiba taga duk yanayinta ya canza,tambayarta tayi
" meke faruwa?"
Taso ta b'oye mata tamata k'arya saikuma ta tuna idan tayi k'aryar ribarme zata samu,
Kaf ta kwashe abundaya faru ta fad'a mata har rabuwarsu.
Umma Habiba tace
"amma bai kamata kurabu da Hanifa hakaba,idan kinga mutum ya kauce hanya k'ok'ari kiga ya dawo kan hanya baki barshi yacigaba da gurb'atacciyar rayuwaba."
"hakane rainane kawai ya b'aci."
"karki manta Hanifa mai son muce batada wani mummunan hali,duk abunda take cikin gidannan tanayine don jin haushin abunda ake mana badon rashin tarbiyaba."
"yanayin shigarta kuma ahankali zata daina tunda cikin barikin sojoji ta taso cikin garin Lagos,dole yanayinta zai banbanta damu."
"karki manta da taimakon babanta nasami shiga Jos na d'aukoki tunda shid'in babban sojane."
"kiyi k'ok'arin daidaitawa da ita domin sata hanyardata dace."
"Insha Allah Ummanah."
*โ๐ป ~UMMYN YSRH~*
[02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: ๐๐๐๐๐๐๐
๐๐๐๐๐
๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
*YESMEEN*
๐๐๐๐๐๐๐
*STORY & WRITEN BY:*
*UMMYN YSRH*
*ยฎPURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*(P.M.L)*
*51~55*
Wani sabon unguwa suka dosa,unguwar bai fiya yawan mutaneba,kowa damuwarshi yake bamai shiga sabgar wani,k'ofar wani d'an madaidaicin gida suka dosa,kafin YESMEEN su iso har sun shiga gidan.
Mai napep d'in ta sallama sannan ta nemi waje ta zauna,takai wajen awa d'aya da rabi tana zaman jiran fitowansu.
Fitowa sukaye,yanzu duk sun sauya shiga,budurwar sanye take da doguwar riga ta yane kanta da d'an k'aramin d'an kwalin,su Alhaji ansha jamfa da babbar riga.
K'ok'arin bud'e k'ofar moton suke zasu shiga,da sauri Yesmeen ta taso ta iso gabar budurwar,ganin Yesmeen datayi ba k'aramin razana tayiba.
Ahankali Yesmeen tace
"IHSAN kece kodai idonakemin gizo,meya kawoki nan? Yaushe kikayi aure?"
Kasa magana tayi,gyad'a kai kawai take.
Alhaji dake cikin moto yace
"shigomana kinsanfa Abuja zan wuce,waye wannan d'in."
Wani kallo Yesmeen ta watsamai,na takaici da bak'in ciki.
"kaje kawai Alhaji zamuyi waya, 'yar'uwatace."
kallon Yesmeen yake zuciyarshi na ayyanamai irin dad'in dazai kwasa wajenta inda zai sameta dun wasu tarkacen 'yan mata zai watsar dasu.
"Gawannan kuyi kud'in napep."
Karb'a Ihsan tayi ta duba dubu biyune,sallama sukayi ya k'ara gaba.
Tafiya sosai sukayi kafin su fito bakin hanya dak'ar suka sami abun hawa,ba wacce tama wani magana har suka isa wajen saida maganin,ta saya ta dawo suka d'au hanyar gida.
Ummah sai zurga_zurga take duk hankalinta atashe yake,tun k'arfe tara da rabi Yesmeen ta fita har yanzu sha biyu da wasu mintoci ba labarinta,Hanifa ta fita dubata har chemist d'in ba ita ba labarinta.
Sallamar Yesmeen taji daga falo wani dad'i taji,tare taga sun shigo da wata,sai kallonta take tarasa inda tasanta,tambayar Yesmeen tayi
"lafiya taje ta zauna haka?"
Kaf takwashe abunda yafaru ta sanar mata Ummah ajiyar zuciya tayi don ta fuskanci irin rayuwar da yarinyar take ciki,kowa hidimar gabansa yake basu buk'aci jin komai daga garetaba saida dare yayi kowa y rufe k'afa Ummah ta tarasu ta fara tambayarta
"Amatsayina na mahaifiya agareki koda banji labarinkiba tabbas na fuskanci irin rayuwar da kike ciki ayanzu,naji zafi da ciwon abun,garin yaya kika jefa rayuwarki haka? Meyasa kika zab'i kisaida mutuncinki ga mazanda mijin Aurenkiba?"
Kuka kawai take takasa furta komai
"ba kuka nakeso kiyiba tambayarki nayi idan baki buk'atar sanar dani shikenan kiyi hak'urin kukan dana saki,Yesmeen tashi kuje ku kwanta.
"kuyi hak'uri ba k'in sanar daku nayiba,tabbas Abunda kika fad'i hakane,
A dalilin maraici yasa namaida mutuncina tamkar haja,
A dalilin rashin mafad'i yasa nake komai ba tare da kwab'aba."
_Toh fah๐ค_
_kumin afwa zuwa gobe zanci gaba insha Allah_
โ๐ป *~UMMYN YSRH~*
[02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: ๐๐๐๐๐๐๐
๐๐๐๐๐
๐๐๐๐
๐๐๐