Showing 90001 words to 93000 words out of 322641 words
Chapter 31 - DEEN Complete Hausa Novels By Arewa Novels.txt
ta nufi cikin gidan yayinda bala da maigadi da shima ya qaraso wajen ke qaqaniyar ciro kayanta dake booth
Knocking tayi a main door sannan ta murda handle din ta bude tashiga bakinta dauke da sallama
Da farko tayi tunanin babu kowa a falon Saida ta qarasa shigowa ciki sannan taga wata budurwa kwance cikin kujera waya kare a kunnenta tana kallon zee din data shigo
Murmushi zee tayi mata itama ta dan maida mata martani sannan tace
"I'll call you back" Daga nan ta katse kiran
Qara dagowa tayi ta kalli zee dake kallonta itama fuska dauke da murmushi
"mutanen katsina ne a wannan tsakar ranan?" tafada cikin maqaqqiyar murya datafi kama data mage
Qarasowa zee tayi ta zauna a kujerar dake facing dinta
"yeah, hope mun sameku lfy"
"lfy lau" inji budurwar sai kuma ta maida kanta kan wayar ta
Bata damu ba don tasan wacece Feenah da hallayenta kuma wai nan don ma suna d'asawa da zee saboda halinsu daya kusan zuwa daya yasa ta tsaya ta tankamata haka
Feenah itace autarsu mummy, mace mai shegen yanga da jin kai
Ga tsiwa don bata ragawa kowa, duk cikin 'ya'yan *Umma* wato kakar zee babu wanda ya kaita kyau
Tanada kyau irin na asalin rumawa ga jiki dan d'as daidai ita. Feenah irin classic ladies dinnan ne masu ji da wayewa don tama lunka zee ta shanye a wannan fannin.
Tanada fada sosai ga batason raini kwata2 shiyasa basa shiri da 'ya'yan yayyanta dasuke a matsayin 'ya'yanta itama sai zee da halinsu yakusan zuwa daya don dama kowa cewa yake ita ta gado a halin jin kai da yanga da gayu
Feenah yar gayu ce ta qarshe mai jida wayewa, yanzu haka ko sati batayiba da dawowa daga france inda take karatu wanda dawowar ta din din din ce don ta riga ta kammala karatun
"kunyi graduating, allah ya sanya alhairi"
Dagowa Feenah tayi ta watsamata wata harara tace
"Sai yanzu zaki yimin allah sanya alhairi? Kwana na nawa da dawowa amma ko kira bayan am very sure kinsan da dawowata"
"kai Aunty Feenah! Shiyasa fa na taso takanas nazo don nayimiki, ai kinfi qarfin nayimiki ta waya shiyasa na shiryo na taho"
Wata hararar Feenah taqara watsamata tace
"eh, maidani shashasha wacce batasan abinda take ba, yarinya gaba na aka haifeki tun kafin kisan kanki nasan basaja, ehe"
Dariya zee tadanyi tace
"haba uwas! Kar kisa ajimu aimana Dariya, ni da uwata haka muke🤞🏻babu mai jinmu"
Wani kallon sheqeqe tayi mata tace
"ku nawa kuke Hakan 🤞🏻? Keda waya ma Dakyar kike kirana sau daya a wata kuma ki kirani da uwa? Ina kika ta6ajin haka?"
"yanzu dai komai yawuce aunty Feenah, allah ya huci zuciyarki ai tsakanin uwa da diya sai allah, shiyasa ma nazo takanas don na goge laifina"
Harararta Feenah tayi ta kauda kai
Dariya zee tayi tace
"tuba nake ran uwata ya dade"
Dan ta6e baki tayi a yangace sannan tace
"ya wuce.. How's your studies?"
"Alhamdullilah aunty, hutu ma muke amma zamuyi resuming very soon"
"Ayyah, allah ya taimaka"
"amin... Ina hajiya granny?"
"hmm tana can dakinta yanzu ta koroni da chazbi"
Tashi zee tayi tana Dariya
"kin ta6ota kenan?"
"wai don nayiwa wannan qazamin yaron sultan tsawa shine ta koroni ita mai jika"
Dariya zee tayi ta nufi hanyar dazai sadata da cikin main gidan tana cewa
"Allah dai granny nayi missing dinta ai"
"ai gaki gata wannan karon ma da fada zaku rabu i bet you"
Dariya Kawai zee tayi ta shige itakuma Feenah ta maida hankalinta kan wayar ta
Direct part din Umma ta wuce cikeda dokin ganin ta
Da sallama tashiga falon umman tana cewa
"granny! Granny! Am back!"
Jin shiru yasata ajiye jakkarta a sofa tana qara cewa
"granny! Wai ina kike..."
Bayyanar umman ya katseta saitayi wajenta aguje ta rungumeta tana Dariya
Qoqarin kwace kanta take daga riqon zee tana cewa
"wai wace yar malfar uba ce wannan?"
Dagowa zee tayi tana Dariya
"kai Umma, nice yar malfar uba?"
"yo banda shaqiyanci saiki shigo min gida ba sallama ba komai sai iface iface, shegiya mai kama da uwarta ta falo, dama yanzu itama nagama zaneta saura ke wlh"
"haba dai, ai muda duka sai ruwan sama kiji ingayamaki, don ma kinsamu anzo ana murnar ganinki? To nafasa murnar ma" tafada tana komawa kan kujera ta zauna ta rungume hannaye a qirji tana kumburi
"kanki akeji" inji Umma tana qarasowa itama ta zauna
"wai yama naga qaffafunki a gidan nan? Jinake ke da kanki kikace ke da nan har illa masha allahu"
"yo dama in don takece wazai zo? Ni wajensu kawu nazo da Aunty Feenah"
"haka fa, ai kin aikata, tunda ga uwarki dakikayo gadon komai nata ta dawo ai dole kema kizo yadda zaku taru ku samun ciwon kai, to wlh kubi a sannu, yanzu ba da bace yanzu kana yimin abinda bemun ba zan zane mutum radam da wannan charbin" tafada tana daga mata chazbahar hannunta
"inyee! Su granny an qaro wulaqanci, to bari na kama kaina, nama fasa zama dakinki dakin Aunty Feenah zan sauka, kar kin tashi cikin dare kin kasa barci ki juya kiga ina nawa cikin kwanciyar hankali kiji haushi kihau zugamun ita" tafada tana miqewa tsaye tana wucewa dakin Feenah dake kusada dakin Umma tana cewa
"mutum yayo tafiyayya yazo ganinka ko sannu da zuwa bare Ayi maganar ruwa saima maganar charbi da aka tareshi dashi, kai wannan grannyn her wahala is too much" tafada tana shigewa dakin
"eh zaggani dakyau kinji? Ja'ira mai zubin mami water idan abin Gaskiya ne Kiyi yaren dazan gane mana kuma anqi ayimiki sannu da zuwan, dake da sannu da zuwan na hada ku nayi muku qumuss, dama zuwa na kika yi da zan wani fara yimaki maraba, kijuya ki koma inda kika fitomana kiga wazai damu, aikin banja kawai" tafada tana tashi ta koma dakinta itama tana cigaba da surutai
Bata dade da shiga ba Feenah ta shigo ta tararda zee tafito daga toilet daure da alwala
Bata cemata komai ba sai wucewar datayi kan gado ta zauna
Qarasowa cikin dakin zee tayi tana gyara yafin gyalenta
"Aunty Feenah, ba'a shigo da kayana bane?"
"suna falo" inji Feenah
"kai Aunty Feenah, shine ko ki taimaka ki qarasomin dasu"
Wani kallon up and down tayi mata ta kamar dakai batareda tace komai ba
Wucewa zee tayi closet dinta ta zaro daya daga cikin hijjabin Feenah da sallaya tana cewa
"baqonka dai annabinka Aunty"
Ta6e baki Feenah tayi tace
"su ru6e a falon indai ni zan qaraso miki dasu ciki"
Zee bata qara cewa komai ba ta kabbara sallar zuhr daya riskesu kan hanya
Lokacin da tagama Feenah bata dakin Hakan yasa ta miqe ta cire hijab din ta linke ta maida da sallayar sannan ta yafa gyalenta ta zauna gefen gado ta dannama mummy kira don fadamata isarsu
Saida tagama wayar daita sannan ta bugama daddy shima ta fada mashi sun dan dade suna fira sannan sukayi sallama ta tashi ta fita
Falon farko tafara komawa ta dauko kayanta ta kawosu dakin Feenah sannan ta bude jakkar tsarabobin datayi ta warewa kowa nashi sannan ta tashi ta fita da nasu kawunnanta
Gidan dama part uku ne, na farko na kawu yusuf yayan mummy yanada mata daya da 'ya'ya hudu
Na biyu na kawu Umar qanin mummy mai bimata yanada mata shima da 'ya'ya biyu
Sai na ukun part din Umma wato mahaifiyarsu mummy inda take zaune da Feenah don dama' ya'yanta hudu rayyayu mijinta kuma tun Feenah na qarama allah yayi mashi rasuwa
Part din kawu yusuf tafara zuwa
Tun daga bakin qofa yaran suka tareta sunata tsallen murna
Itama zee rungume su tayi tana Dariya don Allah yayi ta da son 'ya'ya sa6anin Feenah da bata son 'ya'ya sam shiyasa yaran su kawun basa shigemata don sunsan sauran
Tare suka qarasa cikin falon sunata tsallen murna suna ina tsarabarsu
Zama tayi tana dora sultan akan cinyarta tana Dariyar musun da sukeyi akan wa za'a fara ba tsarabar
Ahaka mamansu tafito ta taddasu, riqe baki tayi cikin mammakin ganin ganin zee kamar daga sama
Qarasowa tayi tana tsawatarwa yaran akan su rufewa mutane baki sun bi sun cika mutane da surutu
Duk shiru sukayi kowanne na turo baki gaba
"A'a Aunty Raliya, kawai sai ki hana yara taryar yayarsu, kai kowa yazo, line up according to your age sai na baku"
Kamar jira suke sai suka taso cikin zumudi sukayi layi kowa fuska washe
Nan tashiga ciro tsarabar su tana basu daya bayan daya kowanne murna da Godiya
Sai da tagama basu sannan Aunty Raliya ta kada kansu ta korasu dakin su ko kunnensu zasu huta sannan ta juyo kan Zainab
"zee baby! Saukar yaushe? Har angama fushin? Ina alwashin kuma?"
Dariya tayi tace
"hmm kedai bari Aunty ai haryanzu alwashin na nan daram dam yanzu ma ai ba zuwanku nayi ba zuwan Aunty Feenah ce"
"to? Muma ai bamu gayya, can ku qarata daga ke har Feenar dama ina ciki daita dazu ta gigitomin auta to wlh ki gayamata ta kiyayi haduwarmu"
Tashi zee tayi tace
"A'a nan fa daya, gwara ki sameta da kanki don waqa a bakin me ita tafi dadi, ina uncle?"
"ana wajen aiki, yasu Aunty maimunar?"
"tana can lafiya lau tana gaidaku ga wannan bari nawuce part din kawu umar"
"to? Harda mu tsarabar? Gaskiya mun gode qwarai allah yasaka da alhairi"
Da amin ta amsa tana ficewa daga dakin tabar part din tawuce dayan part din na kawu umar
Suma a falo yaran suke suna homework
Jin sallamarta yasa duk suka dago
Kamar yaran kawu yusuf suma da gudu suka tashi suka taryeta cikin murna
Mamansu ma murmushi take na farincikin ganinta tana cewa
"yau agari inji maqi baqo?"
Qarasowa zee tayi ta zauna tana murmushi
Gaidata yaran suka shiga yi don sunfi yaran kawu yusuf nutsuwa ko hayaniya basu cika ba
Amsawa tayi tana shafa kansu tana tambayar su karatunsu duk suka amsa da alhamdullilah sannan suka koma suka dauki littafinsu dasuke homework suka shige ciki don dama mamansu ta saba musu da sunga baqi to su shige ciki bayan gaisuwa
Nan suka shiga gaisawa da mamansu da zee takira da Aunty maijidda
Kwata2 batada surutu kamar Aunty Raliya Hakan yasa bata jima ba sosai part din tafito bayan ta basu tsarabar su suma
Part din Umma takoma ta tarda tana sallar asr da aketa kira
Itama wucewa toilet tayi tai alwalla sannan tazo kusada ita ta gabatar da tata
Daga nan suka shiga fira inda yawanci fadan jika da kaka ne
Anan ta shiririce har magrib, dama bala tun bayan asr yayi sallama dasu ya juya
A dakin Feenah takoma tayi magrib Da isha'i sannan tafito riqeda tsarabar Umma takai mata nan ma da fada aka rabu sannan tafito daga part din ta shi shiga part din kawunanta don su gaisa kasancewar sun dawo
Anan duk ta shiririce sai can wajajen 9pm takoma part din Umma
Dakin Feenah takoma inda ta tarar daita lafe kan gado rungume da pillow tana waya cikin muryar da ba'aji bare ka tantance me take cewa
Kallonta tayi taga sai wani lumshe idanu take murmushi yaqi barin fuskarta
Tayi mammaki sosai da Hakan don Aunty Feenah ba ma'abociyar murmushi bace da wuya ka ganta tana fara'a don koda yaushe a wuya take jira take qiris ka ta6ota ta sauke maka kwandon bala'i batada haquri sam yadda kasan zawo
Qarasowa tayi ciki ta bude closet ta ciri towel ta rage kayan jikinta ta daura sannan tawuce toilet
Tadan jima sannan tafito tana makyarkyatar sanyi don garin yau da iska sosai gashi dama su cikin damuna ana yawan yimasu ruwa ba kamar cikin katsina ba shiyasa weather dinsu yafi nacan sanyi
Saida tagama shafe2nta sannan ta saka thick night gown ta hawo gadon ta kwanta
Har a lokacin waya Feenah keyi cikin qasa qasa da murya sai sakin siririyar Dariya take every now and then
Deen ne yafadomata arai, dama kuma yana ranta don yau ma wuni tayi dashi arai don ba taqi ba zuciyarta damar tsayawa tunaninshi shiyasa taqi zama bata nan bata can don da tadan nutsu zai fadomata arai
Qara qudundunewa tayi cikin bargon tanajin kewarshi na dawo mata sabuwa, babu abinda ya chanza a abinda take ji game dashi saima abinda ya qaru
Tana ahaka har Feenah tagama wayar ta ta gyara kwanciya ta kwanta
Shiru koina ya dauka don dare yayi sosai Saidai ko alamun barci babu a idanun zee, wannan dai tunanin nashi ya addabi kwalwarta kamar yadda yasabayi duk dare
Ta dade ahakan jin bazata iya jurewa ba yasata kiran sunan Feenah
Shiru, tasake kira hoping batayi barci ba
Juyowa Feenah tayi tana fuskantarta tana kallonta da idanunta dasuka fara jin barci
"ya akayi ne? Dama bakiyi barci ba?"
"eh Aunty, please magana zamuyi" tafada not sure idan ya kamata ta gayawa wani amma ai taji ana cewa problem shared is problem solved wata qila zata bata haske akan yadda zatayi ta rabu da abinda ke damunta
Kallonta Feenah ta tsaya yi na wani lokaci sannan ta muskuta ta tashi zaune ta jingina da jikin gado ta harde hannayenta a qirji tace
"yes? Inaji"
Itama tashi tayi ta zauna tana fuskantarta amma takasa cewa komai
"idan bazaki iya magana ba inkoma in kwanta banson wulaqanci" inji Feenah tana hade rai
Ajiyar zuciya zee ta sauke sannan tace
"dama Aunty, tambayarki zaniyi. Dan allah idan mutum ya kasance koda yaushe yana tunanin abu duk motsinshi saiya tuna da abin har ya hana shi barci wani sa'in, me Hakan ke nufi kuma tayaya mutum zai iya yakice tunanin a ranshi?"
Shiru Feenah dake sauraronta Tundazu tayi tana Kallonta irin kallon tuhuma sannan itama ta sauke Ajiyar zuciya itama tace
"Wani abu, shi abin menene? Mutum ne koko?"
Shiru zee tadanyi sannan tace
"eh asa mutum dinne"
Harararta Feenah tayi tace
"munafuka, gwara kifito kimin gwari2 yadda zan gane, mutum dan tatsitsi dashi sai gulma, mtcheew"
6ata fuska zee tayi tace
"kai Aunty, munafurcin me nayi?"
"kin fini sani ai, to bari kiji koma menene abin sonshi kikeyi, koma waye mutumin you're in love with him kuma babu yadda za'ayi ki yakiceshi a zuciyarki, the more kike qoqarin yakiceshi the more zai qara liqewa don haka the best solution is Kiyi accepting soyyayarshi"
Tunda Feenah tafara magana taja dabaya tana Kallonta baki bude
"w.. What?" tafada unbelievably
"yes, sonshi kike koma wanene, that's one of the symptoms of love, you're in love Zainab"
Qara jada baya tayi tana girgiza kai
"no.. No.. It can't be"... ✍️
Juma'at mubaraq in advance ? 🌜
Ummin fasihu 🧚🏻♀?
8/2/21, 9:35 PM - Buhainat😝: *🙍🏻♂️DEEN 🙍🏻♂?*
*033*
"No, it can't be. Haba Aunty ya zakice haka? So fa? This is totally impossible" tafada cikin qaryata zancen
Tayaya xa'ace tana son Deen? Deen fa, of all people ta rasa abin so sai Deen? Impossible!
Tsayawa Feenah tayi tana kallonta sannan tace
"bari kiji, nothing is impossible indai love is involve, shi so babu ruwanshi da wanda ya cancanta da wanda be cancanta ba kawai daya tashi kama mutum kama shi yake batareda duba cancanta ba, zee you're in love ko kinqi ko kinso don gayanan rubuce
vividly a idanunki so zaifi maki kidawo hayyacinki tunda wuri kibar yaudarar kanki"
"Aunty Feenah, baki san fa wa muke magana akai ba, da kinsani da kema kin qaryata Hakan da kanki, how on earth zan fada soyyayar Deen? Kinsan shi kuwa? Kwata2 beyi matching qualities danake nema a namijin da zanso qarasa rayuwata dashi ba, that annoying being? That timid mouse? How? When? Why?"
Dariya Feenah tayi tace
"kalli yadda kika firgice akan wannan yar maganar"
"har haukacewa ina iya yi akanta Aunty, kinsan ko dawa kike dangantani kuwa?"
"ban saniba kuma banson sani, abinda nasani shine you're in love with koma waye mutumin, gashinan rubuce 6aro2 a fuskarki kuma abubbuwan da kika fadamin early na daya daga cikin alamomin fadawa soyyaya, bari kiji kadan daga alamomin
Soyyaya tana zuwa ma mutum ta siga daban2
Na farko if you're in love with someone koda yaushe zai kasance maqale a cikin zuciyarki, idan wani abu kike zaki dinga wondering shi me yakeyi, kiji kamar a hasko maki shi ki ganshi, abin nufi anan koda yaushe yana maqale da zuciyarki dashi zaki dinga kwana kina tashi
Na biyu kunya, wasu yana zuwa masu da kunya, kiji bazaki iya hada idanu dashi ba and if you do bazaki iya jurar kallonshi eye-eye na tsawon lokaci ba
Zai kasance duk lokacin da kuke tare zakiji kamar ku kadai kuka rage a duniyar babu sauran wasu inma akwai kin manta da wanzuwarsu haka zalika idan bakwa tare zakijiki so empty kamar kin rasa wani muhinmmin abu na sashenki
Zakiji kina tausayamashi fiyeda qima, bakya qaunar wani abu ya sameshi idan kuma ya sameshi kiji kamar ke abin yasama koma kifishi jin radadin abin kiji kamar ki cire abin daga jikinshi ki maido naki
Akwai changing of heartbeat ma, idan akwai soyayya duk lokacin da kuka kusanci juna ko kuke tare sai bugun zuciyarki ta chanza
Duk damuwar da kike ciki arba dashi batareda ma kunyi magana ba zakiji kamar bakida sauran damuwa a duniyar nan
Komai nashi burgeki zaiyi koda ba abin burgewa bane
Shaquwa ta sosai da sosai zata shiga tsakaninku inda rabuwa a lokacin will hurt you both physically and emotionally...
Ke signs din soyayya are so much to be mention, so very much don idan natsaya lissafa miki sai mu kwana a zaune ni kuma barci nakeji'
Zee data maidata t.v Tundazu takasa magantuwa don kamar mai duba, maganganunta sunyi matching da abinda takeji sosai amma still this is impossible
Tayaya za'ayi ace tana son Deen? Classic girl kamar ta ta bige da son Deen
Deen beda qualities din datake bid'a tattare da namiji
Zata iya cewa daya kawai yake dashi cikin siffofin namijin datake fatan aura shine KYAU
Yes yanada kyau, a wannan ga6ar bazata ja ba don duk kushen mai kushe bazai iya kushe kyawunshi ba
Yana da kyau mai sanyi da tafiya da zuciya farat daya
Tana son namiji mai kyau amma ba kyawun kadai ba
Tana son namiji mai jida kyau da naira, jarumi mai jida kanshi, very Classic handsome guy abin nuni ga kowa
Yadda take Classic dinnan itama tana son Classic guy irin ta dan kwalisa mai ji da gayu da qasaita
Acikin abubbuwan data lissafo abu daya Deen ke dashi wato kyau amma duk kingin bedasu then how on earth