Showing 75001 words to 78000 words out of 322641 words
Chapter 26 - DEEN Complete Hausa Novels By Arewa Novels.txt
Dan maqe kafada yayi yana qara Rungume hannuwa a qirji
Dariya yake bata sosai amma batasonyi Hakan yasa take dannewa, abin mammaki sai jitayi kamar sunawa juna magana da zuciya
Idan yana body language dinshi saitaji kamar tana jin muryarshi a zuciyarta
Sauke idanu tayi qasa tayi kalar tausayi 😔
Murmushi yadanyi yana kallonta yana jiran ta dago
Kamar ta sani saita dago tadan kalleshi
Dan huro hanci yayi sannan shima ya daga yatsarshi ta qarshe alamun 'to mu shirya'
Harararshi tayi tareda murguda mashi baki ta kauda kai acikin zuciyarta tana cewa _it's my turn nima , zakaga jan aji_
Dan wara idanu yayi ganin murguden datayi mashi saikuma yakai hannunshi yana dan yamutsa sumarshi
Tana jin idanunshi akanta amma taqi kallonshi tayi kamar su kaka take sauraro saida ta wajigashi sannan ta dago ta kalleshi
Kamar kau jira yake yayi saurin dago yatsarshi yana marairaice fuska
Duk yadda taso danne dariyarta saida ta murmusa Hakan yasa shima murmusawa yana qara dago yatsar
Saida tadan harareshi sannan tashiga dago yatsar nata kamar zatayi kamar kuma zata chanza shawara Hakan yasashi kafeta da idanu ba kyaftawa
Yamutsa fuska tayi ta kalleshi tadan turo baki sannan ta dago mashi
Cikin jindadi yaqara dago nashi sukayi kamar sun qulla Deen na raba tsakiya
Saikuma suka bawa kansu Dariya zee tashiga qumshe tata yayinda Deen yasaki murmushi mai sauti wanda yasa su kaka juyowa suna kallonshi
Saurin maida hankalinshi yayi ga abincin gaban shi da sai yanzu ya tuna dashi yashiga ci batareda murmushin yabar fuskarshi ba
Haka suka qare zamansu yayinda su kaka ke firarsu acan gefe kuma zee da Deen ke nasu firar ta kurame wanda idan ba sa ido kayi ba baka ta6a ganewa, fuskarsu sai tashin murmushi suke
Ahaka har lokacin komawansu gida yayi
Ba don sun so ba suka rabu dukda zee bata nuna a fuska ba kamar shi Saidai acan qasan zuciyarta jitake kamar su dawwama ahakan
Haka sukayi sallama dasu suka fito
Har suka kawo gida akwai kingin murmushi a fuskarta dakuma ta tuna wani abin saita rufe bakinta tana qumshe Dariya
Haka ta qarashe wannan yinin ashiririce ga yawan murmushin da takeyi every now and then
Shima Deen Hakan take a bangarenshi, kallo daya zaka mashi kasan yau he's very lively don fara'ar yau tasha banban data kullum, annurin dake fita a fuskarshi yau na dabanne
Saturday and sunday sunzo sun wuce lfy, Deen jiki sai qara kyau yake don masha allah yanzu sosai yake recovering speedly
A bangaren alaqarsu da zee kuwa sai abinda yaci gaba
Sosai suke jin dadin kasancewa tare don har aqage suke suga juna
Da lokacin Zuwansu yayi haka zakaga yana daga kai yana duban agogon dakin akai2, hankalinshi be kwanciya sai yaga shigowarsu
Itama a 6angarenta dataga lokaci yakusa zataita zumudi, bata qaunar abinda zai 6atamasu lokaci ko yaya ne
Saidai duk zumudin son ganin junan maganar dake shiga tsakaninsu idan suka hadun be wuce ta tambayeshi ya jikin ba shikuma ya amsa daga nan zasu ja bakinsu su tsuke sai body language ko kallon kallo
*MONDAY*
Yau ake fara zaman kotu akan case dinsu master da zee
Qarfe 10:00am ake fara zaman amma su zee suna wajen tun 9
Saida 10 takusan da yan mintuna sannan aka fara shiga kotun ana zazzaunawa
10am daidai alkali yashigo dakin shara'ar wanda ya dauki shiru tun bayan sanarwar isowarshi
Miqewa duk mutanen kotun sukayi bayan mai buga guduma ya buga
Saida alkali ya zauna sannan duk suka koma suka zauna
Mai gabatar da qara ya tashi ya gabatar da qarar daza'ayi a lokacin sannan ya miqa takardun ga mai girma mai shara'a
Shiru dakin yayi Saida alkalin yagama yan dube dubenshi sannan ya dago ga jama'ar wajen yace
"kotu zataso lauyoyin 6angarorin biyu su bayyana kansu"
Lauyan su zee ya tashi yafara gabatar dakanshi sannan mai kare su master shima ta gabatar dakanshi
Saida yaqara yan rubuce rubuce sannan ya dago yana bawa Lauyan su zee damar farawa
Lauyan ne ya buqaci su master da zee su fito
Daddy dake gefen zee ya dafa kafadarta cikin qarfafa gwiwa don ganin yadda tabi ta takura kanta, sannan yayi mata nuni da ta tafi
Tashi tayi jiki a sanyaye tanajin idanun mutane akanta ta nufi bayan dan akwatinan ta tsaya inda suma su master da sukayi wujiga wujiga dasu suka tsaya bayan dayan akwatin dake dayan gefen
Saida aka sasu gabatar da kansu suka kuma yi rantsuwa akan fadin Gaskiya sannan aka fara
Gyara zaman rigarshi ta lauyoyi Lauyan su zee yayi sannan ya kalli alkalin yana neman izinin abashi damar yiwa su master tambayoyi
Bashi daman alkalin yayi Hakan yasa ya wuce wajensu master daketa muzurai kamar zasu ci babu
Master yayi facing yace
"zaka iya fadamin yaya sunanka?"
Wani kallon sheqeqe yayi wa Lauyan sannan yace
"dazu toshe kunnuwanka kayi da auduga halan shiyasa bakajiba?"
Buga guduma alkali yayi sannan ya gargadeshi akan ya iya kallamanshi nan kotu ce ba wajen wasan yaraba
Kauda kai yayi yana Gyara tsayuwarshi irin ta tattatun yan tashan nan marassa tsoro, duk jikinsu tabon ciwone don ba qarya yan kwanakinnan dasukayi a cell sun jibgu don iskancinsu ya zarta tunani Hakan yasa duk sadda suka kawo masu iskanci jibgarsu ake kamar kayan wanki kuma Hakan be hanasu fasawa saima abinda yaci gaba shiyasa polisawan ma ke allah allah afara zaman kotun Ayi a yankemasu hukunci sutafi ko sa huta
Lauyan yasake cewa
"Ana tuhumarka kaida tawagarka akan neman yiwa Zainab Farouq Dan Faranshi fyade, meye zakace akan Hakan?"
Gyara tsayuwa yasake yi yana qara babbakewa harda pocketing din hannuwa a aljihu yace
"me fa?"
"ina nufin haka ne ko kanada ja?" inji Lauyan
Yanzun ma Saida yaqara Gyara tsayuwa sannan yace
"inada ja..."
Dagowa zee tayi tana kallonshi bama ita kadai ba harda kingin mahalarta kotun
"ba yunqurin yimata fyade ba kawai mukayi harda ma kisa don da munci nasara da bazamu barta da numfashi ba, kuma ko ayau muka qara samun dama saimun aiwata nufinmu don babu wanda ya isa ya jada master ya zauna lfy" yafada yana qara babbakewa yana muzurai
Qananu qananun magangganu suka shiga tashi a dakin har Saida alkali ya buga guduma sannan aka nutsu
Lauyan ne yaqara cewa
"kenan kun amsa laifinku akan Hakan?"
"da alamu dai kunnuwanka na buqatar likita" ya bashi amsa ataqaice
Qara buga guduma alkali yayi wannan karon a fusace yaqara bigemashi warning akan ya kiyayi harshenshi
Kauda kai kawai yayi bece komai ba
Dan murmushi Lauyan yayi sannan yaqara cewa
"zaka iya fadamana dasa hannun wa wajen taimaka muku don ganin kun cimma burinku?"
"eh zan iya" ya amsa a taqaice
"to muna jinka" inji Lauyan
"qawayenta ne"
"su wa kenan?"
Kamar bazaiyi magana ba saikuma yace "su sumee take ko wa?"
"sumee da wa da wa?"
"ban riqe sunan sauran ba" ya bada amsa a taqaice
Maida kallonshi Lauyan yayi ga alkali yace
"ya mai girma mai shara'a, zanso kotu tabani dama wajen gayyato qawayensu Zainab don amsa wasu yan tambayoyi" yafada yana dan russunawa
Dago kai alkalin yayi daga rubutun dayake yace
"kotu ta baka dama"
Nan kau aka kirasu gaban akwatin tambayar suka fito suka tsaya kusada su master kowacce na matsar qwallar danasani
Tunda suka fito zee ke binsu da kallo tana hawayen da batasan tanayi ba, zafi take ji sosai a rsnta don da ciwo wanda ka yarda dashi ya munafurceka
Suma Saida sukayi rantsuwa akan fadin Gaskiya sannan yafara masu tambayoyi
Suma b@su ba shara'a wahala ba suka shiga fadin Gaskiya suna fadin yadda suke zaune da zee a munafurce dakuma dalilin dayasa suka hada kai dasu master akan ganin bayanta
Sosai zee tashiga matsananciyar mammaki jin saboda Deen suka shiryamata wannan qullin, wai don tana sonshi, wai _*so*_
Jin ta bakin zee akayi itama inda itama ta warwaremasu yadda suke tareda su sumee, ta kuma nuna ita babu wata alaqa ta soyayya a tsakaninsu da Deen kawai abotace kuma ta karatu sannan kuma ta gayamasu abinda ke tsakaninta dasu master ta qarashe da gayamasu makircin da sumee tayi mata ranar da abin yafaru wanda Hakan yayi sanadiyar Fadawa tarkonsu
Saida aka maida akalar tambayar gasu sumee dasu master akan suna da ja akan abinda zee tafada suka nuna basuda ja duk abinda tafada haka yake
Kasancewar babu wanda yaba shara'a wahala a kowanne bangare yasa shara'ar tazo da sauki sosai inda Lauyan ya rufe jawabanshi da ambatar wanda ya taimaki zee wato Deen dakuma halin jinyar dayake ciki yanzu, sannan yayi Godiya yakoma mazauninshi ya zauna
Tsit dakin ya dauka kowa hankalinshi akan mai shara'ar daketa rubuce rubucenshi na fama ana jiran jin me zai yanke, a gefe guda kuma ahalin wadanda ake tuhuma wato su sumee dasu master harsun fara matsar kwalla ta baqinciki tunma kafin a zartar da hukunci
Saida yagama sannan ya dago ya kalli Lauya mai karesu sumee dayayi tsamo2 kamar zakaran da aka tsoma a ruwa yace
"Lauya mai kare wadanda ake da zargi, ko kanada abinda zaka dora dashi?"
Me zece? Bayan duk kowa ya amsa laifinshi, wannan ai tozarci ne agareshi.
Dama sunsan saurin miqa wuya zasuyi suka jajiboshi? Koda su keda laifi ai yakamata su dan ja bawai suyi saurin miqa wuya ba irin haka
Tashi yayi cikin jin haushi, yadan russuna yace
"banida tacewa ya mai shara'a"
Dan rubutu alkali yayi sannan yabashi izinin zama yadan qara rubutun sannan ya dago yana gyaran murya
Duk qara nutsuwa akayi don sauraron abinda zaya zartar
"Abisa hujjoji da aka gabatar dakuma miqa wuya da wadanda ake tuhuma sukayi batareda sunba shara'a wahala ba, zamu yanke hukunci kamar yadda constitution ta gindayar"
Shiru yayi Hakan yasa dakin yaqara daukar deadly silent
"abisa hujjoji dakuma amsa laifikansu dasu summaya Abdallah, nadeeya umar, nuratu shehu da ruqayya muhammad sukayi na munafurci da cin dunduniyar wacce ta yarda dasu dakuma hada kai da wasu don ganin bayanta an yankewa kowaccensu zama gidan yari na tsawon shekaru bibbiyu da tarar naira dubu dari biyar ga kowacce kamar yadda dokar constitution ta...... Da........ ta tanadar"
Dakin shara'ar ne ya dauki hayaniya yayinda su sumee suka fashe da kuka wiwi suna dora hannu akai
Yanzu ma Saida alkali yabuga guduma sannan dakin yadawo normal
Qara gyaran murya yayi don fara karanto hukuncinsu master Hakan yasa dakin qara daukar deadly silent
"A sakamakon hujjoji da kuma amsar laifin dasu Murtala lawal, Aliyu hassan, täjudeen garba, bashiru Ahmad da isma'il muntari sukayi na yunqurin yiwa Zainab Farouq Dan Faranshi fyade da kisa, Hakan yasa aka yankemasu hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru goma goma tareda aiki mai tsanani"
Dakin ne ya kaure da hayaniya wanda Saida alkalin yayi dagaske sannan yasamu akayi shiru
Ya cigaba dacewa
"abisa kuma kalaman barazana dayayi na ko yanzu suka samu dama saisun aikata abinda sukayi niyya an yankemasu zaman gidan yari na shekaru biyar tareda aiki mai tsanani dakuma yarjejeniyar duk abinda ya sameta na ta6a lafiyarta zamuyi holding dinsu responsible sannan suma kowanne zai biya tara na naira dubu dari biyar na tadowa bawan allah ciwon shi mai mugun hadari, idan aka hada da wancan yazama zama gidan yari na shekaru 15 tareda aiki mai tsanani sai tarar kudi naira dubu dari biyar biyar kowannensu, idan akwai wanda wannan hukuncin beyi mashi ba yana iya daukaka qara a supreme court"
Yana gama fadin Hakan ya bubbuga guduma Sau uku sannan ya miqe
Duk miqewa kowa yayi suna hada baki wajen cewa court!!!
Sosai zee ke hawaye tana kallon su sumee daketa rusar kuka kamar zasu shide Saidai su master ko gezau saima muzuran dasuke kamar basu ji hukuncin da aka yankemasu Dakyau ba
Saida alkali yafita sannan duk aka fara fita bayan an tasa qeyar su sumee gaba su master kau polisawa na zagaye dasu don bayan mintuna 30 za'a qara gabatar da shara'arsu na kayan mayen dasuke huldarsu
Sosai wuri ya kaure da hayaniya, masu kuka nayi masu murna nayi haka dai daddy da mummy suka kama zee suka ficewarsu daga kotun gabadaya yayinda sukuma su sumee aka tusa qeyarsu cikin motar gidan yari suna kuka danginsu nayi aka fice dasu daga harabar kotun
Dayawa basu tafi ba saida aka gabatar da dayan shara'ar tasu master inda anan ma an yanke masu hukuncin zaman gidan yari na shekaru goma goma wanda idan aka hada da wadancan sun zama shekaru 25 kenan
Zokaga kuka ga ahalinsu Saidai su ko gezau don sun dake ko a fuska basu nuna wata dakuma ba dukda kowanne taciki na ciki
Haka aka tusa qeyarsu suma cikin motar gidan yari akayi gaba dasu akabar danginsu daketa faman ganin kuka... ✍️
😭wayyo ina team dinsu master dasu sumee? Kufito mutayasu kuka 😭 don yau baqar ranarsu ce
Allah sarki zamuyi missing dinku 😭😫
Ummin fasihu 🧚🏻♀?
8/2/21, 9:35 PM - Buhainat😝: *🙍🏻♂️DEEN 🙍🏻♂?*
*028*
Wunin ranar zee yinshi tayi a kasalance, she can't believe su sumee zasu zama prisioners na tsawon shekaru biyu
Dukda ita suka munafunta sai kuma taji tana tausayinsu, yanzu shikenan sun tafi prison suda fitowa sai nan da shekara biyu
Sunyi wasting din karatunsu sunyi tarnishing din mutuncin gidansu
Wannan tunanin yasa ta qarashe yininta a sanyaye tanajin komai baya mata dadi
Da daddare mummy tashigo dakinta ta zaunar daita tashiga yimata nasiha mai ratsa zuciya tana nunamata illar hulda da qawayen banza saboda gudun irin haka, yanzu da allah ya basu nasara akanta da yanzu wani zancen ake
Ta dade tana mata nasihohin kamar yadda tasaba yimata akai akai, abin mammaki sai ji taji nasihohin sun shigeta sosai sa6anin da datake ganin duk salon takura ce irin ta mummy
Saida tagama mata nasihohin sannan ta rufe da addu'a sannan ta umarceta ta tashi ta sauko suci abinci
Tashi tayi jiki a matuqar sanyaye don sosai nasihohin mummy suka qara saukarmata da kasala tabi bayanta suka fita
Koda ta kwanta ma barcin qin zuwa yayi dawuri, sosai nasihohin mummy suka qi barin brain dinta tanata jujjuyasu tana hango tsantsan gaskiyarta aciki
Ahaka barci ya dauketa can cikin dare batareda ta shirya ba.
*WASHEGARI*
Zaune yake a kan gadonshi na asibiti, ya jingina da pillow qaffafunshi a miqe hannunshi riqe da dan qaramin littafin hisnul muslim yana karantawa
A gefe daya kuma kaka ce zaune kan sallaya tana can charbi don gama sallar walha dinta kenan
Duk sunyi nisa a abubbuwan dasuke akayi knocking din kofa
Tare suka dago suka kalli kofa sannan suka kalli juna
Ganin kaka na niyyar tashi yasashi cewa
"bari naje kaka"
Yasan gardama zatayi mashi Hakan yasashi saurin saukowa kafin tayi magana ya nufi kofar
Daidai za'a murda handle din tawaje shima ya murda ya jawo kofar
Kasancewar na wajen be shiryama Hakan ba yasashi yowa gaba Hakan yasa Deen saurin tareshi
Gasping tayi cikin rintse ido cikeda tsoro
Jin an tarota yasa ta bude idanu ahankali nata yafada cikin nashi
Dan wara nata tayi cikin nashi tana saurin janyewa tanajin wani abu na tsirgamata a duk ilahirin jikinta
Shima dan jada baya yayi shima kamar a tsorace yana cewa
"oh... Sorry"
"wai ya naji shiru kamal?" sukaji muryar kaka daga ciki Hakan yasa Deen kallon ciki dukda ba hangen kakan zai iyayi ba
"A'a dama nabude ne saita fado..." qara yasaki sanadin take mashi qafa da zee tayi saurin yi ganin zai saki layi
"kyakyawana?!" inji kaka tana saurin miqewa tsaye jin qararshi
Saurin qarasowa wajen tayi taganshi duqe yana kama kafar da hannu guda yana yarfa hannu sai zee datake duqe itama tana jeramashi sannu a rude don ita batama san sadda ta tareshi da qarfi ba Haka
"subhanallilah! Lfy kuwa?" inji kaka tana duqawa itama tana taya Deen din kama kafar a rude Hakan yasa zee sake daburcewa
"eh... Dama... Kawai turo qofar nayi.. Ashe yana kusa sai ya buge kafar" tafada tana zazzare idanu irin na marassa Gaskiyarnan
6ata fuska yayi yace
"O'O! Ba Haka bane"
Dan waro idanu tayi kafin tayi magana yace
"ba kofa ta bugeni ba" yafada yana cije le6e alamun zafi
"h.. Hakane mana" inji zee tanajin zuciyarta na jumping tana tuna abinda yafaru ranar da ta tareshi daga su master
"A'a ba Haka bane" yafada yana qara tamke idanu alamun zafi
"to garin yaya? Kaida kasan ba cikakken lafiya ke gareka ba, tashi muje ka zauna tukunnan"
Zee data sure Tundazu tayi saurin cewa
"eh.. Eh, tashi muje ka zauna.. Sorry"
Taimaka mashi sukayi ya tashi yana dangyasawa kamar gaske Dariya na cinshi ganin yadda zee tabi ta rude
Har gadon suka kaishi ya zauna yana nishi yana sauraron zee daketa jeramashi sannu kamar ma ba a hayyacinta ba
Zee kau a bangarenta a rude take, tasan halin Deen yana iya cemata ita ta takashi idan ta tambayi dalili kuma yace don tayo gaba zata fadi ya tareta
Ina zata da wannan kunyar? Gashi ita yanzu tsoro ma takeji wani abu yasamu Deen ata dalilinta ganin yadda kaka bata wasa da abinda yashafeshi, afili take nuna qaunarshi tana nuna batason abinda zai ta6ashi Hakan yasa take tsoron wani abu yasake samun shi a sanadin ta gudun ata dalilin ma allura ta tono galma tasan itace wannan yarinyar data watsamashi abu mai sanyi, tasan idan tasan Hakan qila farfesunta zatayi
Kaka ce ke dan matsamashi kafar tana mitan ai dama kicihi yasashi tashi yaje bude kofar, banda gulma meye na zuwa bude kofa a matsayinshi na majinyaci? Ai ga irinta nan
Zee dai anyi tsuru2 tana ta zare idanu tama kasa zama
6ata fuska Deen yayi yace
"O'O! Nifa kaka ba koface ta bigeni ba"
Jin Hakan yasa zee wara idanu sai tayi saurin katsesu da
"kaka ina kwana ya mai jiki? Kinga mummy batazo ba ko? Wlh yau unguwa zataje shiyasa bata samu zuwa ba Amma tace in gaidaki" ta qarashe tana qaqalo murmushi
Jin Hakan yasa kaka sakin wancan zancen tayi murmushi tace
"Allah sarki, mummy ko mutumiyar kirki? Wlh babu komai, ai tana ma qoqari wlh, samun irinta acikin masu kudin yanzu sai an tona, wlh babu komai allah ya saka da alhairi yajiqan mahaifa"
Yaqe zee tayi tana cewa amin tana satar kallon Deen dake 6ata fuska haryanzu
Ganin zaiyi magana yasata qara saurin katseshi da cewa
"ga wannan kaka inji mummy, kuma tace a gaida mai jiki" tafada tana ajiyemata basket din abincin agabanta, da kaka ta lura daita sosai data gane a matuqar daburce take
"ohni ma'u🤔 wannan abu babu ko gajiya, kullum saikun