Showing 69001 words to 72000 words out of 322641 words

Chapter 24 - DEEN Complete Hausa Novels By Arewa Novels.txt

27 Nov 2025

7961

daga duniyar kallonshi

Dariya matar tayi tace
"haba madam? Daga ganin marar lafiya saikuma a bige da kuka?"

Sai a sannan tasan ashe kuka takeyi

Hanki din hannunta tasa tana tsane fuskarta tana murmushin jin kunya

"to ai kiganshi yanzu, 5 seconds na neman zama 5 minutes, allah yabashi lfy insha allah very soon za'a barku kushiga wajenshi kiyita ganinshi babu mai takura maki" tafada tana Dariya

Dan murmushin kunya tayi tana tashi
"thank you very much" tafada tana murmushi

"Don't mention.. Amm, nace dan uwanki ne?" tafada tana qumshe Dariya

Kada kai kawai zee tayi sannan ta nufi hanyar fita tana mata sai anjima

Cikin Dariya matar tace
"to allah yaqara donqon zuminci, allah kuma yaqaro afuwa"

Itadai zee fitowa tayi murmushi a fuskarta

Tana fitowa daidai su mummy ma na fitowa da niyyar tafiya gida Hakan yasa suka wuce bayan itama zee din tayimasu kaka sallama suka shige mota harda daddy suka wuce gida



*BAYAN KWANA UKU*


Cikin kwanakin nan abubbuwa da dama sunfaru ciki harda nasarar damqe su master da akayi a gidan wani abokin huldar kayan mayensu inda wani dan leqen asiri yakawoma yan sandan rahoto sukuma basuyi wata wata ba suka yiwa wajen tsinke inda sukayi ramm da dukkansu aka kwashesu sai magarqama

Ciki kuma harda sauqin da Deen yasamu dukda ba farfadowa yayi ba Amma an chanza mashi daki inda ana iya shiga aganoshi Saidai kwata2 ba'ason ayi hayaniya


Tsakanin zee da kaka saina rasa wanda yafi farinciki da wannan cigaban dukda ita zee nata farincikin be bayyana ba kamar na kaka amma a badini tafi kaka murna da Hakan

Kullum sai sunje asibitin Sau biyu, dasafe da kuma bayan isha'i

Sosai su daddy ke hidimtamasu kaka wajen abin da yashafi lafiyar Deen don haryanzu ko sisin kaka beyi ciwon kai ba da sunan maganin Deen

Hakan yasa kaka ke ganin girmansu sosai don ita kaka dama batada babban masoyin da yawuce mai nunawa dan jikallenta qauna

A bangaren zee kau duk lokacin dasuka zo daga gaisuwa da tambayar mai jiki bata qara cewa komai sai kallon Deen da zata cigaba da yi

Su kaka da mummy sunsha kamata ta kafeshi da ido dukda yadda take kallon a fakaice

Izuwa yanzu babu wannan abin oxygen din a hancinshi Hakan yasa fuskar shi ke afili Saidai tayi fayau taqara haske lips dinshi kuma sunqara pink sosai

Yau sunyi baqi yan dubiya sosai ciki harda yan makarantarsu dama mallamai, Cikin mallaman harda mr ibrahim


Rasa inda zata sa kanta tayi don kunya lokacin da mr ibrahim ya yimata jaje da fatan Allah ya tsare gaba

Haka dai ta amsa da amin batareda ta iya hada idanu da ko daya daga cikin su ba

Haka akaita zuwa ganinshi, a yan kwanakin nan tasan Deen mutumin mutane ne don sai zuwa dubanshi ake takoina kuma duk wanda yazo da kalar yabon da zaimashi na kyawawan hallayenshi Hakan yasa taji ya qara burgeta akan nada kuma take kwadayin itama watarana tasamu mutane masu yaba hallayenta, wadanda zasu nuna damuwarsu sosai idan wani abu ya sameta

Ahmad mai adaidaita ma yazo dashi da matarshi ganin din, Saidai lokacin dasukazo su zee basukai ga zuwa ba saida sukazo sannan aka gayamasu


Zaune suke suna dan fira jefi jefi

Kaka ce da baaba abu sai mummy da zee a dakin

Can su ukun ke firarsu yayinda zee ke gefe tana yan danne dannenta a sabuwar wayar da daddy ya siyamata tanayi tana dagowa tana kallon Deen lokaci bayan lokaci


Dagowa tasakeyi ta dan kalleshi saitaga kamar yatsun hannunshi sun dan motsa

Qara dan waro idanunta tayi tana kallon hannun sannan ta maida kallon ga fuskarshi amma bataga yakuma motsin ba

Bata Janye idanun ba akanshi ta cigaba da kallonshi babu ko blinking don idan idonta ba qarya sukayi mata ba tabbas taga yatsunshi sun motsa


Qara girma idanunta sukayi ganin idanunshi sunfara motsi a runtsen dasuke

Cigaba da kallonshi tayi idanu a ware bata ko kyaftawa don gani take idan ta kyaftasu zataga akasin abinda take gani yanzu

Cigaba na motsi idanun sukayi da alama soyake ya budesu

Can eyelids din suka fara rabawa idanun suka shiga budewa ahankali

Biji2 yafara gani Hakan yasa yashiga kyafkyafta idanun

Ahankali ganin nashi yafara clearing tun yana ganin abubbuwa blurring har ganin nashi yadawo clearly

Be sauke idanunshi koina sai cikin nata large pure white eyes din... âœï¸


Ummin fasihu 🧚ðŸ»â€â™€ï¸?
8/2/21, 9:35 PM - BuhainatðŸ˜: *ðŸ™ðŸ»â€â™‚ï¸DEEN ðŸ™ðŸ»â€â™‚ï¸?*







*026*







Cak komai nata ya tsaya ta kafeshi da idanu kamar yadda shima nashi ke kafe da ita


Sotake ta tashi tayi ihun murna ta nufeshi ta kamo hannunshi tayi mashi magana amma duk ta kasa, ko kyafta idanu batasonyi don gani take data kyafta ta bude zataga idanunshi a rufe kamar kullum

Mummy ce kema Zainab magana akan ta miqo ledar kusada ita amma shiru ko motsawa batayi ba

"bakiji ba?" inji mummy tana kallonta bama ita kadai ba harda su kaka

Still bata motsaba ko ta nuna alamun taji don bama lallai ne intaji dinba

Ganin ta zaune ta kafe wuri guda da ido yasa suma bin inda take kallo da ido


Atare duk suka miqe kowa bakinshi bude

"Deen!!" Duk suka fada atare

Kaka ce farkon qarasowa gabanshi tana riqo hannunshi cikin tsananin farinciki

Sai a lokacin ya janye idanunshi da basu ida washewa ba daga kan zee ya maidasu kan kaka dake kuka da Dariya lokaci guda

"kyakyawa na, katashi? Alhamdullilah! Alhamdullilah! Allah mun gode maka, allah mun gode maka" tafada tana Rungumeshi qamm

Lumshe oily idanunshi dasuka dan dishe yayi ya bude yana qara narkewa a wuyan kaka

Dago idanunshi yayi a hankali ya saukesu akan zee da yanzu take tsaye tana kallonshi itama idanun na kyallin hawayen dasuka taru aciki


"wai bazaki tafi ki kira Dr din bane?" inji mummy ganin tayi tsaye taqi gaba taqi baya

Magana mummy ya dawo da zee daga duniyar kallon Deen tayi saurin Juyawa ta nufi kofa

Binta da kallo Deen dake rungume still ajikin kaka yayi kamar yau yafara ganinta

Harta dora hannu a handle din kofar saikuma taqara juyowa ta kalleshi

Lumshe idanu yayi ya qara budesu akanta wani slight murmushi wanda yayi mugun tsayawa aran zee ya su6ucemashi

Saurin bude kofar tayi tafita ta rufo

Saidai maimakon tayi gaba saita koma ta jingina da kofar ta Lumshe idanu wanda Hakan yaba hawayen dasuka taru a idanunta damar gangarowa


Ahankali ta silale awajen tana dafa saitin zuciyarta datakeji tana kumbura da sacewa

Hawaye sosai take wanda ita kanta batasan na meye ba yayinda murmushin Deen na yanzu yaqi 6acemata a idanu



Rabashi kaka tayi da jikinta ta dago fuskarshi tana shafawa tana murmushi da hawaye a lokaci guda

Shima mayar mata da martanin murmushin yayi yana Lumshe idanu tareda budewa

Suma su mummy qarasowa sukayi cikin farinciki suna miqa godiya ga Allah (s.w.t) daya tasheshi

"sannu son, ya jikin?" inji mummy tana kallonshi tana kuma qara hango zallar qaunar da kaka kemashi


Dan kafeta da idanu yayi saikuma ya Lumshe idanu ya bude alamun da sauqi

Itakau baaba abu cewa tayi
"Allah mun godemaka, raggon maza an leqo lahira an dawo, to ya hanya?" tafada cikin sigar tsokana don dama haka takemashi

Itama murmushi yadanyi mata sannan ya maida kallonshi kan kaka da haryanzu ta tisashi gaba tana kallo kamar tasamu t.v

Murmushi yasake mata Hakan yasa takai hannunta a kumatun haggunshi tana shafawa, Lumshe idanu yayi ya sake budesu yana son dago hannu ya dora akan nata dake dafe da kumatunshi amma yakasa don kwata2 beda wani qarfi ajikinshi

"kyakyawa na, nayi zaton tafiya zatayi ka barni, nayi zaton barina zakayi ni kadai a duniyar nan, da katafi ka barni da bansan yadda zan kuma cigaba da rayuwa babu kai ba, rayuwa batareda kai ba rayuwar kunci ce Hade da dawwamammiyar kewa"

Girgiza mata kai yayi ahankali alamun ta daina kuka Hakan yasa taqara rungumeshi tanajin farinciki na huda zuciyarta takoina

Share qwalla mummy da baaba abu sukayi na tausayinsu, mummy na qara jingina soyayyar dake tsakanin wannan kakar da jikan

Jin shirun yafara yawa yasa mummy cewa
"bari naje na dubo likitan narasa abinda yasa basu qarasoba Tundazu"

Bata jira komai ba tanufi kofa

Murda handle din tayi ta tura sai taji abu ya tokare kofar cikin mammaki taqara turawa taji har lokacin atokare

Cikin mammaki tace
"ikon allah" taqara turawa wannan karon da qarfi


Firgigit zee ta dago daga hada kanta da gwiwa datayi

Jin ana turo kofa tabayanta yasata saurin miqewa tana ja baya

Gani tayi an bude kofar mummy ta leqo

Wara idanunta zee tayi don sai yanzu ta tuna abinda ya fiddota

Saurin yin u-turn tayi ta nufi hanyar dazata sadata da office din Dr din


Binta da kallo mummy tayi baki sake sannan ta ida fitowa itama ta nufi hanyar office din Dr din don bazata qara jiran gawon shanu ba


Tana shawo kwanar dazata sadata da office din Dr din sukayi kici6us da Drn da zee

Batabi takan zee ba tace ma Drn
"yauwa Dr, yafarka yanzu yanzunnan"

"ok muje mugani" inji Drn

Nan tajuya suka koma ta hanyar dasuka taho zee a bayansu


Shigowarsu yasasu duk dagowa suna kallonsu

Qarasowa Drn yayi ciki fuska a washe
"masha allah, alhamdullilah! You're back" yafada yana dan dafa goshinshi

Murmushi kawai Deen yayi kamar yadda yake tun lokacin daya tashi

Ciro abin wuyanshi Dr din yayi yasa a kunne sannan ya dora a qirjinshi yana feeling heartbeat dinshi

Duk tsit akayi a dakin ana kallonsu kowa fuska bayyane da farinciki

Saida likitan yagama duka gwaje gwajenshi sannan juyo gasu kaka, kaka bakinnan kamar gonar auduga


"to kaka ina tayamu murna, yatashi kuma alhamdullilah jiki da sauqi sosai sai dan abinda ba'a rasaba, yanzu ayimashi brush asamar mashi abu mai dan ruwa ruwa da zafi zafi yasama cikinshi

Ayanzu beda qwarin jiki sai ahankali qarfinshi zai dawo kuma don Allah banda hayaniya, please"

Duk amsa mashi sukayi da insha allah

Yan rubuce rubuce yayi a memo din hannunshi sannan yace
"abashi wani abin yasa a cikinshi kafin indawo mashi da maggungunan dazai dinga sha, Allah yaqaro afuwa"

Duk da amin suka sake amsawa sannan yafita


Waya mummy ta dauka bayan fitar Dr itama tafita don kiran daddy

Ita kuma kaka ta shige toilet don tarar ruwa itakuma baaba abu tafita sai dakin ya rage daga zee dai Deen

Kafe juna da ido sukayi expressionless

Ahankali Deen ya dago hannunshi ya miqomata yana dan murmushi

Hakan yaqara tsumata tayi saurin qarasawa wajenshi ta kama hannun ta damke gaam takifa fuskarta akai tana shesheka

Binta kawai yake da kallo not saying anything

Saida tayi mai isarta sannan ta dago da watery eyes dinta ta kalleshi taga shima ita yake kallo

"am so sorry.. Am sorry for everything, nina jawo komai, nakusan sanadin rayuwarka, daka tafi da bansan yadda zanyiba don bazan ta6a yafewa kaina ba, am sorry for causing you pain upon pain, forgive me.. Please" ta qarashe tana lumshe idanu hawayenta na gangarowa

Dora dayan hannun yayi akan nasu dake wuri guda sannan ya girgiza mata kai yana murmushi saikuma ya bude baki kamar zaiyi magana amma taqi fitowa

Ganin Hakan yasata cewa
"menene? Baka iya magana ne?"

Murmushi yayi ganin yadda take tambayar cikin damuwa saikuma ya nunamata cikinshi yana yamutsa fuska

Ganin Hakan yasata saurin tashi tana raba hannunsu tanufi wani flask dake kan wata locker wanda dama ana ajiyeta ne da ruwa ciki incase ya farfado don dama Dr yariga ya fadamasu zai iya farfadowa a kowanne lokaci

Tana cikin fiddo cups din kaka tafito hannunta riqeda bowl da dogon kofi dake dauke da ruwa

Daidai nan baaba abu tadawo ita da mummy dasuka Hade a waje

Maclean din da baaba tasiyo ta matsa a sabon brush data siyo ta miqama kaka da zatayi mashi brush

Daukan cups din zee tayi taje ta daurayo sannan ta dawo ta jawo flask din da kayan shayin dake cikin leda tashiga hadawa

Sosai tasa ginger powder aciki tayimashi hadin mai citta

Deen da kaka kema brush sai 6ata fuska yayi kaka nata qara lalla6ashi har aka samu aka gama brush din

Daidai nan zee tagama hada tea din taba kaka

Cikin jindadi tashiga sama zee albarka sannan tazo tafara ba Deen din shayin

Ana haka daddy yashigo tareda Dr

Tashi zee tayi tanufi daddy da sauri ta fada jikinshi cikin tsananin farinciki

Shima daddy riqeta yayi fuskarshi awashe suka ida qarasowa ciki

Deen tunda zee ta ruga wajen daddy yake binsu da kallo harsuka qaraso wajenshi, yama bar amsar shayin hankalin yakoma can

"masha allah, sannu kaji?" inji daddy cikin kulawa

Kada mashi kai Deen yayi yana dan murmushi sannan ya kalli zee da itama murmushi yaqi barin face dinta

"Allah ya sauwaqe ya qara lafiya, allah yakuma kiyaye gaba" inji daddyn

Duk da amin suka amsa banda Deen din dayayi murmushi kawai

"Gaskiya kayi mana hallacin dabazamu iya sakamaka da komai ba, ba don kai ba da yanzu wani zancen ake, babu abinda zamuce illah allah yasaka da alhairinsa" inji mummy tana murmushi

"hakane kam, babu abinda zamuce face allah ya sakamaka da alhairi, ka ceci rayuwarmu don rayuwar Zainab tamuce idan muka rasata komai na iya faruwa, words can't express how gratefull we are kuma insha allah saimun tabbatar an hukunta wadannan shaidanun daidai da abinda suka aikata don yanzu haka magana takai kotu on monday za'a fara zama" inji daddy


"Allah yakaimu, ai abinda yakamata kenan dama, yaran yanzu ka haifesu ne baka haifi halinsu ba, kuduba qannanun yara irin wadannan sun iya munafurci ni Zainabu, kuma wai qawayenta ne na qut da qut, duniya ina zaki damu? Idan wadanda ka yarda dasu suna maka zagon qasa ta bayan fage dawa zaka yarda ni Abu?" inji baaba Abu tana riqe ha6a

"shiyasa ai qawayen basuda wata amfani, ni dama basuyi minba tunda nafara ganinsu nakuma yimata magana amma taqi rabuwa dasu ai ga irin abubbuwan danake guje miki nan kinfara gani" inji mummy tana eyeing dinta

"wlh kam, qawayen yanzu ko bam (bomb)? Ke kina nan kin saki jiki dasu kina zama dasu da zuciya daya amma su basuda maqiyi daya wuce ke kuma basuda burin daya wuce suka bayan ki, ai da akayi abota ba wannan zamanin ba" inji kaka tana ajiye kofin shayin ganin besha

"To allah ya kyauta, yaranma naji ance cocaine dealers ne suna safarar miyyagun qwayoyi da hodar iblis yanzu haka da akaje gidan da aka kamasu akayi bincike saigasu nan birjik anata zaqulosu yanzu kunga abin yaqara tsawo ga wannan ga wancan" inji daddy

Riqe ha6a baaba abu tayi tace
"danqari! Ashe yan kwaya ne? Ca6 aikau sun aikata tunda dasun shawu suka bugu tafara gayamasu qarya kome yazo kansu yi zasuyi"

"To allah dai yashiryasu idan masu shiryuwa ne" inji kaka

"fatan kenan" inji mummy tana Kada kai

Dr ne yaqara duba Deen sannan yabasu maggungunan shi bayan ya gayamasu yadda qa'idar shan yake


Da zasu tafi zee jitayi kamar karta tafi kamar tayita zama anan

Don dole tabisu daddy tana waigen Deen dashima yake kallonta yanajin kamar karta tafi

Ranar nan zee ta dade batayi barci ba, duk motsin da zatayi saiya fado mata arai duk kuma lokacin daya fadomata a rai saita tsinci kanta da murmusawa

Barci 6arawo ne ya sadado batareda ta farga ba ya saceta


A bangaren Deen kuwa saida ya rama sallolin da ake binshi cikin daren nan sannan yasha maggungunanshi wanda Dakyar aka samu ya hadiyesu don dama shi kwata2 beson magani duk lokacin dazaisha magani sai kaka tata fama dashi don daya saka maganin abaki zaita kakari kamar zaiyi amai Dakyar ake samu ya hadiye

Yana gama sha ba dadewa barci ya daukeshi don dama cikin maggungunan harda na barci

Su kaka kau ranar sun dade kafin suyi barci, firarsu kawai sukesha cike da annushuwa kallo daya zaka masu kasan yau rana ta musanmman ce agaresu don farincikin dasuke aciki a bayyane yake a fuskokinsu

Suma sai can cikin dare barcin ya sacesu suka 6ingire




*WASHEGARI*


Tunda ta tashi bata komaba tana gama sallar asuba ta sauko tashige kitchen

Maid biyu ta iske cikin kitchen din suna hidimar dora breakfast

Sunyi mammakin ganinta by this time kuma a kitchen, shanye mammakinsu sukayi suka shiga gaidata

Amsawa tayi tana nufar abubbuwan dasuka dora tana bubbudewa

Saida tagama sannan ta rurrufe ta juyo garesu

"Akwai cow leg?" ta tambayi daya daga Maid din

"eh madam Akwai a Deep freezer, shi kikeson ci ne?" inji maid din cikin ladabi

"ciromin shi farfesu zanyi" tafada tana wucewa wajen tukwane ta dauki wata yar madaidaiciya

Yin yadda tace maid din tayi tana mammakin zee a zuciyarta don da wuya ka ganta kitchen da sunan girki sai idan mummy ta tilastata bakuma wai don bata iyaba ne kawai dai qiwuya ce da son jiki irin nata na yar hutu


Cikin qanqanin lokaci tafara hada farfesun qafar sa dinta wanda yaji citta sosai da kayan qamshi kamshi

Kan kace me? Har kitchen din dama gidan baki daya ya garame da qamshin girkinta

Koda tagama yar warmer tasamu tajuye aciki ta fita daga kitchen din tabar maids din da gulma ke cinsu a zuciya

Koda tashiga dakinta ajiyewa tayi kan mirror tayi tafada bathroom don freshen up


Kamar kullum yau ma qarfe 10 suka bar gidan don zuwa hospital din

Duk sammakon zee da zumudin dole saida tajira har lokacin da mummy tafito

Haka suka fito zuwa mota tanata cin magani don taso taje dawuri ya kasance farfesun da tayi mashi zai fara sha amma yanzu ai tasan ya riga ya karya

Haka tashiga front seat ta zauna ta dora yar warmer dinta a cinya tana cigaba da kumburi while itakuma mummy tashige baya ta zauna batama san wainar da zee ke toyawa ba


*HOSPITAL*



Mutane sosai suka tadda a dakin wadanda duk mazane yan unguwarsu


Da sallama suka shigo dakin amma kasancewar mutanen dakin nada yawa shiyasa ba duka suka lura da shigowarsu ba

Zaune taganshi bayanshi jingine da pillow hannunshi riqe da dan mug din shayi yana kur6a ahankali

Fuskarshi dauke da wannan murmushin mai karamashi kyau yana sauraron wani daga cikin matasan dasuka kewayeshi yana bashi labarin irin wahalar dasuka sha wajen nemanshi aranar da abin yafaru


Dauke idanunta tayi daga kanshi ta qarasa wajensu kaka dake masu sannu da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login