Showing 66001 words to 69000 words out of 322641 words

Chapter 23 - DEEN Complete Hausa Novels By Arewa Novels.txt

27 Nov 2025

7958



Zokaga kuka a wajen wadannan ahali musanmman na master, uwar tayi kuka kamar zata shide, fadi take allah ya isa tsakaninta da murtala, bazata ta6a yafemashi ba kuma tayi danasanin haihuwarshi datayi

Abu dai ba dadi, sai bayan an kukkulesu ne sannan aka samu wani yazo yafadama yan sandan gidan da su mastern suke kwana amma koda sukaje babu su babu alamunsu donma ga yadda suka iske dakin a hargitse wardrobe dinsu babu komai ya tabbatar musu sun gudu.

Hakan yasa aka baza matakan tsaro akoina harda tashoshin motoci da airport don kama wadannan shaidanun



*KAKA*


Kamar yadda mutanen unguwa sukayi alqawari saigashi suna gama sallar asuba suka sake taruwa don fita nemanshi

Kasa kansu sukayi kashi2 inda kowa da inda ya nufa yadda abin zaifi zuwa da sauqi sannan suka bazama


Kaka kau kallo daya zakamata tabaka tausayi saboda har ramar dare daya saida tayi

Kan kace me? Gida yafara cika da mata yan jaje, a unguwa duk inda ka wuce sai kaji ana labarin 6acewar Deen din Kaka mai koko.


Wajajen qarfe tara saura yansanda suka dira kofar gidansu Deen.

Nan suka nemi iso cikin gidan sannan suka shiga

Haka aka rakasu dakin Kaka inda take zaune ba uhm ba uhm uhm sai yar charbinta datake ja

Ganin yansandan hankalinta yaqara tashi jin maganar Deen ce takawosu

Saida suka kwantar mata da hankali sosai sannan suka sanar daita Deen na asibiti dukda basu fadamata halin dayake ciki ba

Nan take gida ya kaure da koke koke, Kaka nayi mutane nayi, yan kadan ne masu rarrashi

Haka Kaka tafito tana shar6ar kuka da ita da matar mallam Nasiru da Baaba Abu aminiyarta suka bi yansandan bayan kowacce mace tafito an rufe gidan

A motar ne matar mallam Nasiru ta bugawa mallam Nasirun waya akan anga Deen yana asibiti takuma fadamashi sunan asibitin


Su zee na zaune a waiting room tareda daddy su Kaka suka iso


Sosai Kaka ke kuka akan abari ta ganshi

Haquri akaita bata akan tayi Haquri likitoci ke ciki tabari sugama aikinsu

Dukda Hakan batayi Shiru ba sai kuka take tana su taimaka mata shi kadai gareta

Haquri duk akaita bata akan ta kwantar da hankalinta insha allah komai zaizo da sauki

Dakyar aka samu ta zaune tayi shiru Saidai kwata2 hawayenta sunqi tsayawa


Zuwansu Kaka ba qaramin sake dagulama zee lissafi yayi ba don itama kukan nata da akasamu yayi sauqi ta cigaba dayi, tanajin cewa duk itace silar komai, idan wani abu yafaru da Deen tasan bazata ta6a yafewa kanta ba


Ana haka su mallam Nasiru da kingin yan tawagar neman Deen din suka qaraso, nan aka hadu aka tsaya jiran tsanmmani... ✍️



Manage 👏 babu dai editing, mugun wuya yake mun aradu☹️


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀?
8/2/21, 9:34 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?*









*025*





Sun jima anan sosai sannan likitocin suka fito daga dakin da aka kwantar da Deen din


Mutanen na kyalla ido suka ga fitowarsu duk sai suka tashi kowa cikin jiran jin abinda likitocin zasu ce

Matsowa kaka tayi gabansu likitocin cikin hawaye tace
"Likita ya ake ciki? Ina jikana? Meya sameshi?"

Shima daddy ya taso ya matso wajensu, zee a gefenshi itama cikin zaquwar tasan halin da Deen din ke ciki

"Dr how is he now?" inji daddyn

Family Dr dinsu dake kan gaba a kula da Deen din yace
"Alhamdulillah, ku kwantar da hankalinku. Insha allah zaiji sauqi kai yama ji sauqi insha allah, yanzu dai Alhaji muje office akwai bayyanan da zan maku gamedashi acan"

Caraff kaka tace
"harda ni za'aiwa bayanin, ni kakarsa ce bayada kowa saini nima banida kowa saishi ku taimaka ku fadamin wani hali yake ciki, ku kaini wajenshi don Allah" ta qarashe tana rufe fuska da gefen zani

Dafa kafadarta Baaba Abu tayi cikin sigar rarrashi itama tana matsar kwalla

"eh, ita grandma dinshi ce, i think itama tanada ikon jin abinda ke faruwa tunda itama makusanciyarshi ce" inji daddy

"ba damuwa, muje office din" inji Dr din yana yin gaba

Juyawa daddy yayi ga zee datake tsane idanunta da farin hankin hannunta yayi cupping din fuskarta
"dear, bari muje uhm? Kijiramu anan ok?" yafada a tausashe

Ahankali ta Kada kai, kiss ya mannamata a goshi sannan ya nemi wani acikin maxan yazo shima, nan mallam Nasiru yazo suka wuce tare, ita kau kaka tuni tayi gaba


Binsu da kallo zee tayi har suka shige sannan ta maida kallonta kan kofar dakin da Deen din yake ta kafeta da ido, jitake kamar taje ta bude tashige ta ganshi ko zataji sanyi sanyi a ranta

Komawa tayi ta zauna ta jingina da jikin kujerar tareda lumshe gajiyayun idanunta tana jiran fitowarsu daddy



*OFFICE*


Tunda Dr yafara bayyani kaka keta kuka harya kai aya

"innalillahi waina ilaihi rajiun, innalillahi waina ilaihi rajiun. Dama haka wancan Likitan na Janaral (General) yace, sosai ya gargademu akan kar ya shiga ruwa, ko iska ake sosai yace karya sake yafita babu kayan sanyi, yanzu idan Kamal yatafi yabarni ya zanyi? Ya zanyi da rayuwata ni Ma'u?" taqara Fashewa da kuka tana rufe fuska da gefen zane

"Hajiya kiyi hqr, insha Allah Allah zai tashi kafadunshi, insha allah zai samu lafiya" inji Daddy cikin sigar rarrashi


Dan kallonshi tayi ta gefen ido ta kauda kai tana cewa
"ai dama haka za'ace, dama ai wanda aka cuta ake ba haquri, yaro besan hawaba besan sauka ba anjamashi jinya, yaron daba ruwanshi da kowa, harkar gabanshi kawai yake yanzu gashi anjamashi shiga halin rai ko mutuwa, wannan abu da me yayi kama?" saikuma taqara Fashewa da wani kukan

Kasa cewa komai daddy yayi sai mallam Nasiru dayayi saurin cewa
"haba kaka? Komai fa muqaddarine daga allah, Duk abinda kike ganin yafaru da mutum to allah yariga da ya qaddara Hakan zai faru dashi don Allah kiyi hqr insha allah Deen dinmu zai tashi akan kafafunshi nan kusa"

Bata sake cewa komai ba sai kukan data cigaba dayi

"yanzu Dr zamu iya ganinshi?" inji mallam Nasiru

"A'a Gaskiya don a halin Yanzu baya buqatar hayaniya ko kadan.."

"Dan Allah likita kubari naganshi, wlh bazanyi hayaniya ba, yadda na shiga haka zan fito ko kwakwarar motsi bazanyi ba, Don Allah" inji kaka cikin muryar kuka

"kaka bawai hanaki nayi ganinshi ba, wlh dokace idan mutum na a wannan condition din ba'a barin ashiga dakin, kiyi hqr" inji Dr

"Nidai Don Allah kayi hqr inganshi, bakasan yadda nakeji a zuciyata bane da kasani daka bari na ganshi, don Allah Alhaji kacemashi yabarni na ganshi, shine kadai sanyin idanuna, sanin halin dayake ciki zaisani jin sauqin abinda nakeji a raina, don Allah" tafada tana kallon daddy pleadingly

Kallon Dr daddy yayi yace
"Dr please do something, abarta ta ganshi ko daga nesa ne"

Shiru Dr din yayi na wani lokaci cikin nazari sannan yace
"ok, Gaskiya Saidai ta cctv don it's a strict law patients dake cikin irin wannan condition din babu mai shiga wajensu sai likitoci, wannan dokace akowanne hospital ba a wannan kadai ba

Amma tunda ta nace zamu kaita recording room saita ganshi ta cctv, wannan shine iya taimakon dazamu iya yimata Gaskiya"

"eh babu komai, akaini rekodin din, naji akaini" tafada tana share hawayenta da ha6ar zane

Tashi Dr din yayi yace
"to bismillah"

Duk tashi suma sukayi Dr yayi gaba suka maramashi baya



Jin tafiyar su yasa zee bude idanunta ta dago tana kallonsu

Ganin zasu nufi wata hanyar yasata saurin tashi ta nufo daddy

Ba musu ya miqamata hannu ta kama suka cigaba da bin Dr

Recording room din suka shiga inda duk zirga zirgan da akeyi a hospital din ana ganinshi a wani qaton majigi

Dr din ne yayi ma mutumin dake in charge of wajen magana akan ayimasu zooming din room 12

Yadda yace din haka mutumin yayi, yayi zooming din abinda ke faruwa a dakin da Deen ke kwance

Gasping both kaka da zee sukayi suna rufe baki cikin tashin hankali

Deen ne kwance kan gado sanye da blue kayan asibiti da akewasa marassa lfy

Kanshi nannade da bandage, hancinshi sanye da abin oxygen dake taimakawa wajen jawo numfashi sai hannunshi dakeda cannula anamashi qarin ruwa

Zamewa kaka tayi zata fadi zaune mallam Nasiru yayi saurin kamata ya zaunar daita kan wata kujera

Kafe Deen din cikin majigin tayi da kallo idanunta na tsiyayar hawaye, ganinshi a wannan condition din ba qaramin ta6amata zuciya yayi ba hakan yasa tashiga yin kuka kamar zata shide

Zee kau Fadawa jikin daddy tayi ta rintse idanunta gamm

Bazata iya jurar kallon Deen a wannan halin ba hakan yasa taqara rintse idanunta gamm tana shesheka

Shafa bayanta daddy keyi cikin sigar rarrashi idanunshi na kan Deen din cikin majigi

Dole duk mai imani idan yaga Deen a halin dayake aciki ya tausayamashi

"Dr please do everything you can to save him, please" inji daddy

"insha allah sir, ku kwantar da hankalinku insha allah zai tashi zai koma kamar be ta6a kwanciyaba insha allah" inji Dr din cikin son qarfafa musu gwiwa


Dakyar aka samu aka rarrashi kaka tareda yimata nasihohi sannan suka fito

Alhaji ne yabiya duka bill din treatment din Deen din

Saida suka qara tattaunawa da Dr inda aka fadama kingin yan unguwansu Deen dake wajen halin da ake ciki, sosai kowa ya jajjanta tareda yimashi addu'ar samun sauqi

Nan mazan duk suka tafi da tabbacin zasu dawo anjima da marece aka bar kaka da matar Nasiru da baaba abu sai daddy da zee


Basu dade da tafiya ba motar gidansu zee tashigo hospital din

Wata dattijuwa cikin ma'aikatan gidansu zee ta tafito ita da bala driver daya kawota

Hannunta dauke da basket din abinci wanda mummy tasa akawo musu

Saida suka gagaisa da kowa sunamasu ya jiki sannan daddy da zee suka tashi akan zasubi bala ya ajiyesu gida, ita kuma dattijuwar mai aikin saita tsaya dasu

Godiya su matar mallam Nasiru da baaba abu suka shiga yimashi saboda sosai ya nuna hallaci duba da yadda ya tsaya akansu sosai batareda yayi la'akari da matsayinshi ba na babban mutum

Itakau kaka batama san da tafiyarsu ba don tunda tadawo ta zauna ta buga tagumi ba tace komaiba sai Kafe waje guda da ido datayi

Bayan tafiyarsu daddy ne dattijuwar yar aikin mai suna Inna Binta ta gabatar masu abincin datazo dashi, duk sunci sai kaka da sukayi juyin duniyar akan taci amma taqiya haka suka haqura suka kyaleta


A bangaren zee kau koda suka isa gida mummy ce ta tisata gaba tayi wanka da ruwan masu dumi sosai ta gaggasa jikinta sannan ta tilasta mata taci abinci dukda bada wani yawa taciba sannan tabata maggugunanta tasha tasata ta kwanta

Ko minti biyar ba'ayiba da kwanciyarta barcin gajiya ya saceta



Tasha barci sosai wanda ke cike da mafarkan Deen kala2 wanda tana tashi duk ta mance mafi yawa a cikinsu

Sosai taji dadin jikinta yanzu duk wata gajiya ta tafi sai dan abinda ba'a rasaba saikuma murar datake fama daita haryanzu

Miqewa tayi tashiga toilet ta dauro alwalla sannan tazo ta gabatar da zuhr daya wuceta ta dora da asr da ake cikin lokacinta yanzu

Ta dade tana yima Deen addu'ar samun lafiya sannan ta nemi sakayyar allah akansu nurr dasuka ci amanarta da su master dasuka nufeta da sharri

Saida tagama sannan takoma kan gado ta zauna ta lula duniyar tunani

Ahaka wata maid tashigo kiranta inji mummy

Tashi tayi bayan ta yafa veil din gown dinta ta bita

Kamar yadda ta hasaso abinci mummy zata sata ci

Saida ta gaidata mummy ta amsa tana mata ya jiki ta amsa da da sauki sannan mummy ta zubamata farfesun kan rago wanda yaji kayan yaji sosai ta turamata a gabanta

Babu musu tashiga sha don itama tana buqatar abinda zai dan warware mata toshewar hanci datake fama dashi sai gashi kuma ya taimaka sosai don taji dadin jikinta bayan tasha


Haka taita kasa kunne taji ance ta taso su koma asibiti amma shiru

Gashi batada waya yanzu bare takira daddy ta narkemashi yasa akaita gakuma batason ta tambayi mummy, haka taita jira amma shiru

Daga baya ma saita daure taje tasamu mummyn da maganar sai cemata tayi ba yanzu ba

Abin ya 6ata mata rai sosai Hakan yasa takoma daki ta kulle taita kuka


Sai bayan isha'i mummy ta aika agayamata ta shirya suwuce hospital din

Tuni ta mance da zuciyar datake tayi saurin chanzawa tana addu'ar allah yasa su tararda ya farka

Da ita da mummy dawata maid dinsu suka tafi wannan karon ma da abinci a basket

A asibitin taga daddy Hakan yasa tawuce wajenshi da sauri ta Rungumeshi tana tura baki

Dagota dadi yayi yajamata hanci yana tsokanarta yana kiranta cry cry baby ita kuma sai qara zunbura baki take

Binsu mummy dasukayi gaba suma sukayi suka shiga dakin dasu kaka suke

Saida su mummy suka gama gaisawa dasu kaka sannan itama zee ta gaidata cikin jin kunya kuma ba kunyar komai bace saina tasan tanamata kallon itace silar rashin lfyar jikanta

Amsawa kaka da yanzu ta dan kwantar da hankalinta tayi tana tambayar ta ya jikinta, Amsawa tayi da dasauqi sannan itama ta tambayi lafiyar mai jiki itama ta amsa da dasauqi daga nan kowa yayi shiru

Mummy ce ta gabatar musu da abinci, amsa sukayi suna godiya suka ajiye ko don anjima don basu dade dacin abincin da matar mallam Nasiru takoma gida tayi musuba


Sosai mummy tasaki jiki dasu sukaita fira kamar dama sunsan juna, yadda mummy tasaki fuska tanata fara'a yasa suma suka saki jiki daita sunata hira harda kaka dake tofa nata akai akai


Zee kau tun bayan gaisuwarnan bata qara cewa komai ba saima sadda kai datayi tana wasa da zoben hannunta tana sauraronsu

Hankalinta gabadaya baya tareda su kawai dai tana wajen ne amma ko wuqa za'asa mata bazata iya recalling kalma daya a abinda suke cewa ba

Hankalinta gabadaya na kan Deen, idan akwai abinda tafiso yanzu to sanyashi a ido ne

Sun dan jima a Hakan sannan tadan dago taga haryanzu firarsu suke hankali kwanta

Dan Hadiye yawun bakinta tayi sannan tayi gyarar murya wanda Hakan yasa duk suka kallota, sai kuma taji ta takura da kallon amma saita basar tace
"zan dan je wajen daddy" tafada tana qirqirar wani busashen murmushi

Da to saita dawo su baaba abu suka amsamata suna kallonta yayinda mummy batace komai ba sai kauda kai datayi

Tashi tayi tana dan satar kallon mummy sannan tanufi hanyar fita ta fice

Duk binta da kallo sukayi harta fice sannan baaba abu tayi fuska kalar tausayi tace
"baiwar Allah, kai allah ka cigaba da karemu da zuri'armu wannan abu da me yayi kama? Yarinya nitsatsa amma anason wargazamata rayuwa, allah kacigaba dayimana katangar tsari da ire iren wadannan azzaluman bayin naka"

Duk da amin aka amsa banda mummy da tadanyi murmushi kawai

Wai nitsatsa, Yarinyar da shegen rawar kai yayima yawa wataqila garin Hakan taje ta tsokano ma kanta su don ita haryanzu bata yarda haka kawai zasu nemi wargazamata rayuwa ba

Nan akalar hirar tasu takoma kansu, inda suketa addu'ar tonuwar asirin su master da kuma yin allah wadai dasu sumee dakuma fatan waraka wa Deen





*ZEE*



Ajiyar zuciya ta sauke bayan tafito tana dan juya manyan idanunta

Wawaigawa tayi don ganin inda zata hango su daddyn amma bata gansu ba

Har tayi hanyar office din Dr dinsu saikuma tafasa

Dawowa tayi ta nufi recording room dasuka shiga dazun dasafe

Saida tayi knocking sau hudu sannan aka bude kofar mutumin wata mata ta bayyana

Dan murmushi matar tayimata tace "hi"

Itama maida mata murmushin tayi tace
"hy"

"how may I help you miss?" inji matar tana kallonta

Rasa abinda zatace tayi Hakan yasata fara kame2

Ganin Hakan yasata cewa tashigo ciki sai suyi maganar

Shiga zee tayi tana wondering ina wancan mutumin yake na dazun?

Saida ta zauna sannan matar tace
"yes miss? How may I help you?" inji matar tana folding hannunta tana kallonta

Taking deep breath tayi sannan tace
"amm.. Dama sonake ayiman viewing wani dake kwance a room 12 ne please, patient ne amma anhana shiga ganinshi shine nakeso please kiyimin viewing dinshi"

Shiru matar tayi tana kallonta na dan wani lokaci sannan tace
"am sorry, amma ba'a zuwa ganin mutum anan, kiyi hqr kijira har abaku izinin shiga ku ganshi Hakan ma zaifi"

Shiru zee tadanyi tana kallon zoben hannunta sannan tasake dagowa ga matar

"please, kawai ganinshi zanyi koda flashing dinshi zakiyimin nadan ganshi ki kashe, I want to know how he is please" tafada pleadingly

"idan kinason sanin yadda yake likitanshi zakije ki nema ba nan ba, am sorry but it's strictly against the law, da ana yin haka da kowa ma nan zaizo don ganin nashi, kiyi hqr please ki jira har lokacin da za'a baku izinin shiga ganinshi, am sorry"

Kada kai zee tayi a sanyaye tana qoqarin maida hawayenta sannan ta miqe tsaye
"thank you" tafada ta nufi kofa

Binta da kallo matar tayi har Saida tadora hannu akan handle zata murda

"wane ward yake?" zee ta tsinkayi muryar matar

Juyowa zee tayi da sauri kamar dama jira take tace
"12... Ward 12"

Murmushi matar tayi tace
"ok zo kiganshi na seconds biyar kiwuce kafin azo akamamu anan babu ruwana" tafada tana operating din mouse din hannunta

Da sauri zee tadawo ta zauna tana murmushin jindadi dabatasan tanayiba

Kunnomata matar tayi tayi mata zooming dinshi sannan ta kaucemata don tagani

Tsayawa zee tayi tana kallonshi

Kwance yake kamar dazu haryanzu abin oxygen a hancinshi Saidai yanzu babu qarin ruwa a hannunshi da alamu an cire

"Don.. Allah ma, kidanyimin zooming face dinshi" tafada cikin sanyayar murya

Murmushi matar tayi tayi yadda tace, nan take fuskar Deen yafito daro2 a screen din majigin

Kafeshi tayi da idanu tanajin zuciyarta na kumbura don shauqi

Dukda abin oxygen din ya kare kaso mai yawa na fuskar Hakan be hanata ganin yanda fuskar tayi fayau ba

Idanunshi a lumshe sai lashes dinshi dasukayi zara zara suka hade dajuna sanadiyar lumshe idanun dayayi, ga girarenshi masu cika da baqi dasuka kusan hadewa

Maida kallonta tayi akan ciwon dake akanshi wanda aka nannade da banda sannan akan tulin lallausan sumarshi dake tuje as usual

Kafeshi da idanu tayi bako kyaftawa tanajin kamar zai bude idanu at any moment

Batasan iya lokacin data dauka a haka ba sai jitayi an dafa kafadarta hakan yadawo da ita


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login