Showing 12001 words to 14906 words out of 14906 words
Chapter 5 - THE WIFE'S SECRET (Macen Sirri) free pages By Mom Islam.txt
kowane uba bane yake nunawa ɗansa ko ince ba kowane iyaye bane suke bawa yaransu irin shi, ya kamo hannunta suka wuce bedroom ɗinsa, ya dinga rarrashinta yana yi mata nasiha, sannan yace "koda ya shigo karki sake ki nunar masa da ke kika ɗauka, ki barmin komai a hannuna Insha Allah zan yi maganin komai.
Sai 11:an ya kama hanyar komawa gida, yau haushin kowa ma yake ji, kai tsaye part ɗinsa ya wuce, dama momy tasa a jiye mata motsinsa, mai gadi ne ya kira momy a waya yake gaya mata Abu-Basir ya shigo"
Godiya tayi masa kana ta katse kiran.
ƘAUYE
Yau biki ya rage saura sati ɗaya, kasancewarsu mutanen ƙauye ba wani gyaran jiki da wasu abubuwa akayi mata ba, iya kacin tattabara da wani magani nasu na gargajiya shikenen, Habiba dai har yanzu rawar kan na nan,
Habiba baƙa ce, ɓakinta mai kyau zamu iya kiranta da Black beauty, gata da dogon hanci, bakinta ɗan ƙarami yayinda idajuwanta suka kasance madai-daita,
Tunda taji Inna da Malam Habu suna hirar bikinta saura mako ɗaya, ta dinga yiwa ƙawayenta da yaran anguwarsu alƙawari, tace musu kowa sai yaje binni, aikuwa suka dinga murna, ƴan uwa da abokan arziki sun fara taruwa, ana ta kawo gudunmawa daga danginsu na can ƙyauen dake gabansu, tun safe Inna ta zuba mata kayanta a bako, saboda zataje ƙauyen kakannninta tayi musu sallama, aiko Habiba sai murna take, kasancewar ba a cika samun mashin anan ƙauyen basu ba, yasa Malam Habu ya goyata a kan keke da buhun kayanta a hannu ta rungumeshi, suna tafe tana damunsa da surutu, tsayawa da keken yayi tare da juyowa yana kallonta yace "Habiba wato duk faɗan ki dinga kintsuwa da nake yi miki bakyaji ko?"
Habiba ta kwashe da dariya kafin tace "Baba ni babbar damuwata idan nayi aure na gama abincin ƴan gayu wa zai dinga kawo muku kai da Inna?"
Girgiza kai Malam Habu yayi, kawai yaci gaba da tafiya tana ci gaba da tsuba masa surutu iri-iri,
Suna isowa ƙauyen ta diro akan keke, ta ruga idan da zasu je da gudu, ta ɗora buhun kayan a kanta, ta samu mutane a tsakar gidan, shiyasa ta tsaya tana ce musu Hannunku" su kuma suna ce mata amarya ansha ƙamshi, sai dariya take tana cewa "sai ma kun ga garin da za'a kaini yasin aljanna ta farko ce"
Suka hangame baki suna kallonta, malam Habu ya shigo tare da sallama, suka amsa masa, yana haɗa idanu da Habiba ya zabga mata harara
Tuni ta shige ɗakin mahaifiyar Malam Habu da gudu, tana shiga ta haye saman gadonta mai rumfa, Kaka dake zaune a ƙasa tana gyara kabewa tace "Habiba yaushe kika shigo?"
Kafin ta bawa Kaka amsa Malam Habu ya shigo aiko tayi tsit da bakinta, tare da juyawa kamar mai barci, Malam Habu ya gaishe da Mahaifiyarsa cike da girmamawa, suka ɗan taɓa hirar ɗa da uwa, har take ce masa ya shirye-shiryen bikin?" Yace mata alhmdulilah tazo yi muku kwana biyar sai ta dawo gida"
Kaka tace "babu laifi ai an gode naji daɗi sosai, Malam Habu yace daga nan sai taje gidan saƙo dangin mamanta suma ta gaishe su"
Kaka tace "Insha Allah duk zata je"
Malam Habu ya miƙa mata ɗaurin Suga da sabulun wanka wanda ya Ciro a aljihunsa, sannan ya ce mata zai wuce, kaka tace masa ya ɗibi kabewa ya tafi dashi a fara rage hanya, malam Habu yace "ai akwai acan gidan nasu koba zai ɗiba babu yawa zai ɗauka" guda uku ya ɗiba a buhu manya-manya sannan yai mata sallama ya wuce.
Habiba na jin fitarsa ta duro daga gadon, cikin rawar kai take cewa kaka "wlhi kaka gidan da za'a kaini gidan ƴan gayu ne.." kaka tace "ahe kin dangwalo mana arziƙi ƴar nan?"
Habiba tace "amma zakije ko?"
Kaka tace "ko saboda wannan albishir ɗin da kikayimin ai ya zama dole inje, ƙafata, ƙafarki, Habiba ta washe haƙora tana ce wa "kaka kawai kiyimin zaman ɗaki tunda kinga babu wanda na sani, kaka nifa ko mijin nawa banma sani ba"
Kaka ta riƙe baki kana tace "ai zaki sanhi,
Habiba ta dinga zuba mata surutu, can anjima da misalin sha biyu, yaran gidan suka fita dibar ruwa a tuƙa-tuƙa, Habiba na zuwa ta ture bokitin wata yarinya tasa nata a layi, nanfa rikici ya kaure yarinyar da bata wuce sa'arta ba, ta shaƙo wuyan rigarta, Habiba ta wanka mata mari tare da cewa "hegiya tsinanniya, akwai wata rana da nazo gidan kaka nazo wucewa ta hanya naga babanki yana shan taba" nan fa yaran sukayi chaaaa akan Habiba, kowa sai dukanta yake, da ta zage ta dinga kai musu duka da naushi da yaƙushi har ta ƙwaci kanta, dukkansu sai wani uban sauke numfashi sukeyi, a taƙaice dai ruwan bokiti ɗaya ta ɗiba ta koma gida bata ƙara fitowa ba, Kaka na ganinta da wuyan riga a yage, tace "oh Habiba duk inda kika shiga sai anyi faɗa dake?, nidai bansan halin wanda kika gado ba"
Habiba na ƙoƙarin cire riga ta ɗauki zanin kaka dake rataye a jikin ƙofa tace "akwai wanda nai gado sama dake, kowa ya ganki ai yasan halinmu ɗaya"
Kaka ta girgiza kai tana cewa "Allah ya sauwaƙe wlhi"
Da ɗaurin ƙirji ta fito tsakar gidan nasu, babu kowa duk sun ɗora tukwanen abinci sun shige ɗaki, ƙananun tukunya ta fara leƙawa, a hankali take saka bakin zaninta tana buɗewa, tasa ludayi ta jujjuya, cikin sa'a ta samu nama zuƙu-Zuƙu a cikin tukunyar, ta dinga lodasu a zaninta suna ƙonata, befi guda uku ta bari ba, ta mayar da Murfin ta rufe, bata tunkari ɗakin kaka ba, kai tsaye banɗaki ta shiga, ta nemi guri akan dutsen da ake zama idan za'ayi wanda ta buɗe naman sai turiri yake yi, wajen guda takwas ta kwaso, ta dinga ci da zafi-zafi duk wanda zo shiga sai tace "umm...ummm"
Taimakonta ɗaya banɗakin yana lungu, bayan ta gama ta fito sai zare idanun take, da sauri ta shige ɗakin kaka tana mayar da numfashi, kaka tace "lafiya Habiba, tace "kahi nakeyi, kinsan bana rabuwa da gudawa, Kaka tace Allah ya sauwaƙe, ta miƙo mata wata ledar magani, Habiba ta karɓa ta duba tace "ai ararraɓi ne, yasin bazan hyaba" tana maganar tana turo baki,
Kaka tace "au hikenan Kahinne bai iheki ba"
Can a tsakar gida suna daga ɗaki sukaji kururuwa, ana cewa an sace nama...!
Page 15-16
Kaka tai maza ta fito tsakar gidan domin ta jajanta musu, aiko taga matan gidan da yaran duk sun yi cirko-cirko ana jimami, matar da take girkin ta wuce kai tsaye ɗakin kaka, a gado ta samu Habiba tana ta tsalle, ta janyota ta sauko ƙasa, murya a hankali tace "Habiba ki faɗamin tsakaninki da Allah wa kika gani ya satar min nama, Habiba na sanki akwai riƙon alƙawari,
Nanfa mutanen gidan suka dawo ƙofar ɗakin Kaka suka tsaya, kai tsaye ba tare da jin tsoro ba, Habiba tace "ba mijinki bane na ganhi ya zuba su a baƙar leda ya fice da gudu... mancewa nayi ai banzo na gaya miki ba"
Matar tace "haba hiyasa ahe nayi aikan duniyar nan amma bawan Allah yaƙi zuwa ashe nama ya ɗiba, wlhi Innata ce ta kawomin badan haka ba, ai sai in hekara banci koda ƙahi ba"
Matan gida suka hau salati suna tafa hannu,
Tunda tasan abinda tayi, tai saurin zuwa ta sauya kaya sannan, sai da ta bari mutanen gidan sun shiga Sallah sannan ta ɗauki buhun kayanta a kai tace "kaka gidan saƙo zani, tunda nazo babu abinda kika bani, Alkur'an bayan iya zama da yunwa ba, niba dutse ba"
Kaka tace "haba Habiba ina jira matan gidan su gama ai zasu zubo miki"
Habiba ta gallawa kaka harara tare da cewa "aikuwa bari in zauna sai sun bayar sannan zanci, ai hikenan kinga ni na tafi"
Ta fito tsakar gida, tace "jama'a sai anjima bazan iya zama a gidan kaka ba, yunwa zata kaheni"
Tai maganar tana ƙarawa gaba,
Tsakaninsu da gidan saƙo idan a tafiyar titi ne yakai ɗari uku, haka ta dinga tafiya tana ambulawa ƙafafunta ƙasa, gonakin kan hanya kuwa sunci ubansu, gonar farko ta yalo ta shiga, ta tsinki guda goma, ta zuba a buhun kayanta, taci gaba da tafiya, can ta hango gonar gwaiba, gashi babu hanyar wucewa duk anyi shuke-shuke a gurin, da gudu ta tattake shukokin ta shiga, kai tsaye ta haye bishiyar tare da ajiye buhun kayanta a ƙasa, da sauri-da sauri ta dinga jefo da gwaibar, ta tsinki yakai ashirin gashi gwaibar irin manya-manya ne, tana shirin saukowa, sukayi ido biyu da 🐍, zaro idanu tayi saboda a duniya ta tsani snake da lizard bata ƙaunarsu ko kaɗan, ihu take iya ƙarfinta gashi ya kusa zuwa gurin ƙafafuwanta, yanke shawarar yin shahada, aiko ta faɗo ƙasa Timmm ta buga ɗuwawu akan dutse, da sauri ta tattara gwaibar a hijabinta, ganin snake ɗin yana saukowa yasa ta arce da gudu, mai gonar da yazo yanzu ya hangota cikin ɗaga murya yake cewa "ku kamo min ita, dan Allah karku bari ta bar gurinnan"
Haba 🤣 Habiba ta dinga gudu da buhun kayanta akai tana gudu tana riƙe da gwaiba a gaban hijabi, har ta wuce gidan da zataje sosai, sai lokacin ta tsaya a gindin bishiyar kanya tana fara mayar da numfashi, gashi duk gurin babu gidaje duk gonaki ne, bayan ta gama mayar da numfashi ta ɗaga kanta sama ta kalli bishiyar kanya, a fili tace "wannan dai dahen Allah ce, banga wani hege da zai ce tasa bace"
Ta ajiye kayan ta juye gwaibar a buhun, ta haye bishiyar kanya, ta dinga tsinko jajaye tana tarasu a ƙasa, har ta gama ta sauko babu wanda ya wuce a gurin, ta kwashe ta ɗibi na sha ta zuba ragowar a cikin buhun sannan ta ɗora kanta, taci gaba da tafiya, ga wata uwar yunwa dake addabarta, haka dai ta dawo da baya har ta iso gidan saƙo, cikin ɗaga murya tai sallama da buhun kayanta akai, ilahirin mutanen gidan suka amsa, wanda a ƙalla zasu kai su ashirin, suna tsakar gida, "ina wuninku dukkanku dan bazan iya gaisheku ɗaya-bayan ɗaya ba"
Tai maganar tana wucewa ciki ɗakin Goggo, girgiza kai sukayi suna mamakin har yanzu ita bata girma, sannan suka fara tsegumi, ɗaya daga cikinsu tace "gashi Allah ya haɗata da miji shugaban ƙasa ai kuwa ta warke, ɗayar tace "aiko beyi sa'ar mata ba, saboda wannan ba matar a aura ta nutsu yanzu bace"
Suka dinga surutansu, itakam ta wuce abinta.
Goggo na jin muryarta ta washe haƙora tana murmishi, Goggo makauniya ce, ta tsufa sosai, bata iya ganin komai, sai dai tana iya zuwa banɗaki idan ta dafa bango,
Habiba ta gaisheta ta amsa,
Goggo tace "ina innarta da babanta?"
Habiba tace "suna nan lafiya, goggo, tace "akwai Makani (Gwabza)da aka kawo min ɗazu ko ɗauka kici"
Da sauri ta fara dube-dube, aiko ta ganshi ba wani mai yawa bane, aiko ta fara ci, zuciyarta na gaya mata, wancan kwanon da ta gani a rufe, taje ta buɗeshi, aiko ta matsa da sauri tare da zuwa gurin kwanon ta buɗe Murfin a hankali, Goggo tace "har kin cinye ne Habiba naji motsin Murfin kwano" Habiba na shaƙewa tace "Goggo inaci ina rufe wa ne, kinsan haka aka koya mana a islamiya" Goggo tace "to to haka akayi"
Goggo bata sami ba, Habiba ta ɗibi nama har guda biyar, a cikin kwanon, yana cikin kakide ya daskare, kasancewar ta ajiye shi ne tun na Babbar sallah, ta dawo da ja da ɗuwawu ta koma gefe taci gaba da cin makanin, bayan ta gama ci ta samu leda a tsakar ɗakin ta kulle naman, Goggo na tambayar me ta kawo mata?, Habiba tace Kanya da yalo da gwaiba, tana maganar tana gyatsina mata baki saboda haushin ta haɗata da gwaza gata da Nama a kwano,
Goggo tace "Habu ɗinne yayi nomarsu?"
Habiba da bata son doguwar tambaya tace "shafa kiji"
Goggo tace "mezan shafa?"
Habiba tace "yalo da gwaibar mana, kin wani damu mutane mtswww"
Goggo dai ta karɓa ta fara ci harda cewa akwai zaƙi, Habiba ta ƙara mata, kowane ɗaya ta bata tace itama babu yawa ta samo,
Acan gidan Kaka, zuwa dare mijin wacce aka satarwa nama ya shigo, tun a tsakar gida ta fara balbaleshi da masifa, yace "tsaya kiji, na rantse da tsarkin mulkin Allah ban shigo gidan nan ba, ina can gurin jana'izar yaron liman DA Allah yayi masa rasuwa"
Ya ƙara da cewa "uwani yanzu baki ji kunya ba, da kika ɗora min sharrin sata?"
Sai kuma ta hau susar kai,
Mutanen gidan sukayi caa suna cewa "wlhi karki yarda, alamomi sun nuna Habiba jikar kaka ce ta sace naman cikin miya" tunda kaka taji haka, tai saurin fitowa da uban gudu har tana shirin faɗuwa, tace "haba ku kuwa, yarinyar da bataji ba, bata gani ba, kuce ita tayi sata, nidai a jinina ban haifi munafiki ba, sai dai idan kune kuka haifi munafukai, Mai gidan yace "kedai kaka bakyason gaskiya, a zamanin yanzu wa yake hedar ɗansa, tunda ke kin hedeta ai hikenan"
Dukkansu suka koma ɗaki suka barta a gurin a tsaye,
Fashewa da kuka tayi tana share hawaye tace "yanzu dan Allah in banda ƙin jini wazai yiwa ɗan wani sharri, nidai nasan Habiba bata ɗaukar abinda ba nata ba, haba dan Allah, amma sai Allah ya saka mata"
Acan gidan Saƙo, bayan sun gama cin gwaiba da yalo da kanya, ta tura ɗaurin naman a ɗankwali, kasancewar babba ne, ta ɗauki buta ta yi hanyar banɗaki da gudu, tana cewa "gudawa ce ta matseni duk na hanya ya matsa billahillazi zan saki a wando kuma mutum shi zai wanke" babu wanda ya kulata har ta shige banɗakin, ta ajiye butar a gefe, ta nemi guri ta zauna, tana jiyo warin kashi tana cin nama, itakam babu ruwanta, a hankali take yagowa tana kaiwa baki, wata yarinya wacce bata wuce shekaru goma sha ɗaya ba, ta shigo banɗakin da sauri, da buta a hannunta, sukayi ido biyu da Habiba zata jefa nama a baki, cikin sauri ta tura ledar a kanta, sannan ta fito da gudu, ai yarinyar na ganinta ta ruga da gudu, matan gidan suna tambayarsu mai ya faru ina sai gudu sukeyi, sunƙi tsayawa, a wata gona yarinyar ta faɗi, Habiba tahau kanta, tace "dan ubanki gayamin me kikaga ina ci?"
Yarinyar tace "leda na gani a hannunki basan me kike ci ba"
Habiba ta ɗagata tare da kamo kunnenta tace "wannen hegen idanun naki kamar na kifi, Allah yasa inji wata magana ta ɓullo sai na zubar miki da haƙora"
Yarinyar tayi mata alƙawarin bazata faɗa ba, Habiba ta ruƙo mata hannu suka dawo gida,
Koda suka shigo tare sai tambayar yarinyar iyayen keyi akan ta gaya musu mai ya faru, tace "wai akan ta leƙata a banɗaki hine zata duketa, kuma tunda ta bata haƙuri ya wuce"
Habiba tayi musu murmishi ta wuce, tare da komawa ta ɗauko buta, tana gudun kar ta sake komawa wani ya ganta asirinta ya tonu, ko alwalar batayi ba ta dawo ɗakin Goggo, Goggo tace "ki tashi kije kiyi Sallah, Habiba ta miƙe cikin ɗaga murya take cewa "Goggo ta wani ishi mutane sai inje inyi Sallah kamar ance nata banayi, gahi dole sai na koma banɗaki"
Tana maganar ne, saboda asan ta shiga banɗakin kar wanda ya leƙota, yanzu kam hankali kwance ta cinye, sannan ta tauna ƙashi son ranta, a banɗakin tayi alwalah ta fito kai tsaye ta wuce ɗakin Goggo.
ABUJA
Duka wunin ranar bai san abinda momy tayi masa ba, yana zaune yana kallo wayarsa tayi ringing, dubawa yayi dan yaga mai kiran, tunda yaga Sadiq ne ya kawar da kai, tunowa da alwashin da ya ɗauka a kansa, yasa a kira na biyu ya ɗaga,
Muryar Sadiq wasai yace "Ya mutumina kana gidane, dama na gama raba invitation card ɗinne, yanzu Muna so mu shirya wasannin da za'ayi kafin ɗaurin aure dakuna wanda za'ayi bayan an ɗaura aure"
Kai tsaye AB yace "Abokina duk abinda ka tsara dai-dai ne, hakan ya bawa Sadiq damar sake sakin jiki, a take a gurin ya ɗauko pen da paper ya fara rubuta abubuwan da zasu gudanar tunda Dady yace idan ya gama list ɗin yayi masa magana ya tura masa da account sai yasa masa kuɗin,
Yasan dai koba komai zai samu wani abu ta wajen Dady,
Acan ɓangaren AB babban farincikinsa bai wuce kasar waje da dady yace zasu je ba, shi kansa ya gama tsarawa kansa irin rayuwar jin daɗin da zaiyi acan, shi kansa zai fi sakewa a acan.
Da wannan tunanin ya miƙe yayi shiga toilet yayi alwalah, yazo ya kabbara sallah, sallahar ma kamar zai tashi sama haka yake yinta, saboda bashi da sani akan addini kwata-kwata, saboda iyayensa sun tura shi karatu US harda Islamic, shi kuma iya boko da holewarsa da ƴan mata kawai yake yi,
Kasancewar yayi sallahar isha'i, ko addu'a bai tsaya yi ba, dan har yanzu a cikin ɓacin rai yake, kai tsaye ya haye bed yai rufda ciki, har yanzu ya kasa daina mamakin abinda Sadiq abokinsa yayi masa,
A hankali ya tashi tare da buɗe fridge yaga wayam babu komai, hankalinsa a tashe ya hau dube-dube tare da tunani iri-iri, daga ƙarshe dai yace "ko dai Dady ya shigo masa ɗaki ne?, sai kuma yace, koma meye duk laifinsa ne, da bazai kulle ɗakin da key ba yake fita haka, yana cikin tunani sai ga sallamar momy da Dady sun shigo har bedroom ɗin, yana tsaye a gaban fridge ɗin, hannunsa na kan murfin ya sunkuyar da kai, ɗago kan da zai yi sukayi ido biyu dasu...!
Complete book ɗinsa dubu ɗaya ne account number 3175689751 Name Zainab Habibu first Bank shaidar biya ta wannan number 08141799224
Mom Islam