Showing 3001 words to 6000 words out of 14906 words

Chapter 2 - THE WIFE'S SECRET (Macen Sirri) free pages By Mom Islam.txt

06 Dec 2025

1698

da za'a mance da lokacin ibada?
A gurguje ya shirya ya fice kai tsaye mota ya shiga, bai zarce ko ina ba sai Company tunda ya shigo ciki, yai parking ƴan mata da ma'aikatan suke gaishe sa, wani yayi musu alama da hannu wasu kuma ya gyaɗa kai, inda kasan mai ciwon baki, cikin takunsa na ƙasaita ya ƙarasa inda mahaifin nasa yake, akwai wasu mutane su biyar a ciki, kuma duk sa'annin Dadyn ne, ga dukkan alamu da akwai abinda suke tattaunawa akai, yace musu "good morning" bayan sun amsa ya nemi guri kusa da Dadyn ya zauna a wata kujera mai kyau, kana ya Ciro wayarsa yana daddanawa, bayan wasu lokuta Dady ya sallamesu suka wuce, ya zare farin gilashin dake manne a idanunsa kana yace "mai yasa baka wuce office ɗinka ba?" ɗan sunkuyar da kai yayi tare da cewa "Dady ai nayi tunanin kana kirana ne?"
"Eh ina nemanka kuwa, saboda gobe insha Allah zamuje ƙauye nida yayuna guda biyu, ina fatan kana shirye-shirye saboda kar bikin yazo baka shirya komai ba"
"Eh Dady"
Yai maganar yana sunkuyar da kansa ƙasa,
Dady yace "jeka Allah yayi maka albarka"
Ya amsa da Amin sannan ya fice, kai tsaye ya wuce hadaɗɗen office ɗinsa, tare da zama yana tsaka da tunani aka fara nocking, "yes come in" ya faɗa idanunsa a lumshe, "Sadiq ne ya shigo, fuskarsa cike da fara'a, cikin zolaya yace "ango ansha ƙamshi"
AB ya wani murtuke fuska tare da cewa "Sadiq ina ganin girman ka fa, wlhi zamu ɓata, haba ka barni inji da abinda ya dameni mana" Sadiq yace seriously Dady ya kirani musamman a waya yace min wai inzo gobe zamuje ƙauye, ashe inada rabon zuwan ƙauye?"
AB yace shege tunda aljanna ne ai sai kayita shela wa jama'a su sani, kuma ka sani babu inda zani ko gobenne ma, ai bance musu ina sonta ba, sune suke neman ƙaƙaba min ita.."
Sadiq yace "wlhi gata zasuyi maka, da ƴan matan garinnan da bazasu so Mutun saboda Allah ba sai dan kuɗinsa ai gara ka auri wacce bata ma san daɗin kuɗin ba, ta inda zaku gina soyayyarku cikin aminci"
"AB ya saka masa tsawa tare da cewa "kai Sadiq na baka ita halak malak kaje ka aureta, ni bana sonta, me zanyi da ita, ka gayamin ai an haɗani da masifa, ƴar ƙauye da?"
Sadiq ya girgiza kai tare da cewa "dan Allah karka ɓatawa su momy rai, nafi son ku rabu lafiya" shiru yayi masa ba tare da ya sake bi ta kansa ba.
A ranar dai ba wani aikin kirki yayi ba, ƙarfe 4:pm ko sallama beyiwa Dady ba ya fice a Company ɗin, kai tsaye gida ya wuce, yana isa ya shiga parlorn momy, dan sai da ya karyo kwanar gidansu sannan ya fara jin yunwa, ba kuma zai koma da baya ba, a parlor ya samu momyn bayan yayi mata Barka da yamma ta amsa, yace "momy kin gama abinci ne?"
"Eh tace masa tana yi masa murmishi, kitchen taje ta zubo masa da zoɓo mai sanyi ga daɗi da ƙamshi ta kawo masa, jollof ɗin shinkafa ne wanda taji kifi da carrot da latas da tumatur da Cucumber, cikin nutsuwa ya fara ci, itako tanayi masa kallon ya kusa zama ango sannan tana ganin auren yarinyar nan shine dai-dai saboda babbar damuwarta, ƴan matan da suke yawan shigowa gidanta nemansa, bayan kuɗin kawai suke bi ba komai ba, Shiyasa suka yanke shawarar haɗasa da yarinyar ƙauyen nan, sannu a hankali yake cin abincin har ya gama, ya buɗe murfin gorar ya tsiyaya zoɓon a cup ya fara sha, wani sanyin daɗi yaji, bai san lokacin da ya shanye duka ba, ya kishingiɗa a jikin kujerar, tunani iri-iri suna kwance a saman zuciyarsa, duk wata mafita da zai kamo sai ta suɓuce masa, gashi dai har tafiyar ta matso gobe zasu tafi ƙauye wanda bai isa yaja da maganar mahaifin nasa ba duk iya tantirancinsa, kiran sallahar magriba da akayi ne yasa shi miƙewa ya fita zuwa Masallaci, yayi mugun shagala da duniya, sai a lokacin yayi azhar da la'asar.
Ya daɗe a masallacin a zaune, shi kansa besan Me ya zaunar dashi ba, can anjima dai da ya gama tunaninsa ya dawo gida, jiki babu ƙwari, koda ya shiga parlonsa bai tsaya a nan ba ya wuce bedroom, babbar damuwarsa kwanan da Dady yace zasu yi acan...!


Page 5-6

Washe gari tun bayan da Dady ya dawo masallaci bai koma barci ba, yanata shirye-shiryen tafiyarsu ƙauye, momy ma tun asuba suke kitchen ita da Indo sunata hidimar girki, kasancewar zasu tafi da abinci a kula, ƙarfe 9:am Dady da momy sun shirya cikin shiga ta alfarma suna zauna a saman kujera mai zaman mutum biyu, dady ya ɗauki wayarsa ya danna number AB, bayan ya ɗaga yace "kai fa muke jira, ɗazu Sadiq ya kirani gashi nan zuwa wai ya kusa isowa"
AB kam barcinsa yake kwasa hankali kwance, kiran Dady nema ya tashesa, a barci,
Wayar AB na maƙale a kunnensa yace "Dady nifa barci ma nakeyi"
Murmishin yaƙe Dady yayi kafin yace "ka gaggauta tashi ka shirya wlhi idan baka shirya nan da 9:30am ba, zan shigo har part ɗin naka in fito da kai" Dady na gama magana ya katse kiran, da sauri ya miƙe ya faɗa toilet yayi brush sannan yai wanka, ya fito yana ɗaure da towel, wani irin feeling yake ji sosai har cikin gaɓoɓin jikinsa, "kenan yau bazai gana da Sara ba zai tafi wani gari har ya kwana, gaskiya akwai matsala, idan har bai samu ya kwantar da wannan matsananciyar sha'awar da take addabarsa ba, da sauri ya sanya hannunsa ya riƙe penis ɗinsa yana wani lumshe idanu, tunowa da maganar Dady yasa shi shiryawa da sauri, bai cika mu'amala da manyan kaya ba, amma yau su yasa, shadda ce mai ruwan sararin samaniya sai sheƙi take, tasha aiki mai kyau marar hayaniya, agogonsa mai kyau da tsada ya ɗaura a tsintsiyar hannunsa, kana ya ɗauki hula itama yasa shigen aikin gaban rigarsa, sannan ya sanya cover shoe fari sol, sai Hankey ɗinsa shima fari yasa a cikin aljihu, sannan ya ɗauki ATM da duk wani abu da yasan zeyi masa amfani kana ya fice,
Kai tsaye part ɗin momy ya wuce, a harabar gidan ya samu Dady da momy da Sadiq duka suna tsaye a gurin mota an loda kaya a boot ga dukkan alamu shi suke jira, Sadiq na ganinsa yace "mutumina kayi kyau fa.." AB ya watsa masa harara yana jifansa da wani irin kallo, babu wanda ya kula suma iyayen nasa basu kulasa ba, kasancewar momy yanzu ta koma ciki yabi bayanta da sauri, "momy yunwa nakeji" yai maganar a shogoɓe,
"Akwai ragowar abinci barin zubo maka" momy ta bashi amsa tana shiga kitchen ta ɗibo masa shinkafa da miya da naman rago soyayye, acan compound Dady sai faɗa yakeyi, momy na jinsa tayi masa shiru dan yanzu AB ma ya fara cin abincin,
Dole dai sai da ya gama sannan ya kora da moltina, kana ya fita, momy ma tabi bayansa bayan ta kulle ko ina, tayiwa Indo sallama sannan tace karta kashe waya ta barta a kunne, Allah ya kiyaye hanya Indo tayi musu dukkansu suka shiga mota, Sadiq da AB ne a backside momy da dady a gaba, Dady ne yake driving yayinda suke hurarsu jifa-jifa, duk inda Sadiq yaso yaja AB da hira abin yaƙi yiwuwa, saboda ya murtuke fuska kamar wanda aka aikowa da ranar mutuwarsa,
Sunyi nisa sosai da Abuja, su momy suna ta ɗan hirarsu, shiko chart yakeyi da Sara suna ta maganganun banza, da shi da ita,
Sunyi tafiya mai nisan gaske kana suka iso Kano, sannan suka ɗauki hanyar Malikawa dake ƙauyen Kano, ƙauyen fa ƙauye ne sosai, babu ginin siminti ko guda ɗaya, sannan titin nasu babu kwalta sai ƙasa, hakan yasa AB toshe hancinsa, yana wani yatsina fuska, har suka shigo cikin asalin ƙauyen, yara ƙanana suka hango wasu na tsalle wasu na ƴar gala-gala wani na carafke wasu kuma sunyi ƙungiya tare da ɗaurin ƙugu za'ayi dambe, haka dai suka dinga kallon yaran wani iri duk babu tsari a tare dasu saboda ƙauyanci ya ratsa jinin jikinsu,
A ƙofar gidan Malam motar Dady yayi parking, ƙofar gidan akwai jaki sannan an tara kashin saniya a gefe,
Irrrr haka ƴan matan ƙauyen da ƙananun yaran suka biyo motar sunata shafata, haka yaran sukeyi idan mota ta shigo kasancewar ba kasafai motar ma take shigo musu ƙauyen ba, Dady ne da momy suka fito suna yi musu murmishi, Dady kam sai ɗaga musu hannu yake yi, yayinda AB da Sadiq suka fito, shikam AB ya rufe fuskarsa da facemask blue, sannan yasa farin gilashi a idanunsa, nanfa ƴan matan ƙauyen wanda bazasu wuce shekaru 12-13yrs ba suka dinga kallon su, ɗaya daga cikin ƴan matan ne ta riƙe ƙugu tana ɗaure da wani ɗankwali a kwankwaso tace "kowa ya watse ƴan ƙauye kawai, ahe ma ƴan uwan babana ne, kun yarda da labarin da na baku ko? dama nace muku ƴan binni zasu zo, sannan harda mijin da zan aura hima zai zo" tai maganar tana yiwa yaran wani farrr da idanu, haka dai ta dinga korarsu tana ɗan matsawa gurin momy tana cewa "Hajiya hannu da zuwa, yauhe kuka taho?" Momy tace "kece habiba?"
Yarinyar tace "eh nice, Hajiya Amma ku ƴan gayu ne ko?"
AB dake biye da su momy shi da Sadiq sai wani girgiza kai yake yi, yana yamutsa fuska,
Har suka kai ga shiga cikin gidan,
Inna tana ganinsu ta washe haƙora tana yi musu lale marhabun, tayi musu masauki a ɗakinta da ya kasance babu ledar ƙasa sai daɓe wanda shima da ƙasar aka yishi, a taƙaice dai idan ka taka tsakar ɗakin duk ƙasa, ɗakin yanada girma harda gado mai rumfa da ranar ƙasa a gefe, cike da karrama wa ta ɗauko wasu sabbin kofunan silba a cikin kayan jerenta na tun tana amarya,taje ta wanke sannan tazo ta ɗibo musu ruwa mai sanyi a ranar ƙasa kana ta ajiyewa kowa a gabansa,
Dambu take dafawa, wanda yaji albasa mai ganye da zogale, koda ta fita duba abincin, AB ya ture ruwan gefe yana Ciro wayarsa da take cikin aljihu ya gyara zamansa ya cigaba danna wayarsa, hira Dady suka farayi da momy yana cewa "idan kikaga mahaifin Malam Habu da ƙanin mahaifinmu suna kama sosai, sannan shi malam Habu babu inda bamu dashi akan ya dawo kusa damu ba, yaƙi, shiyasa muka ga ya dace mu daɗa jansa a jiki" Momy tace "kuma a haka suke jin daɗin rayuwa?" Dady yace "waɗannan da kike gani sai su fimu kwanciyar hankali da zumunci" can suka jiyo muryar habiba nata tsalle tana cewa "dambu ya sauka alhmdulilah dambu ya dahu wlhi zamu ci daɗi, Inna ki zuba min nawa a faranti, inda zan baje inci in ƙohi"
Momy tayi murmishi gami da cewa "oh habiba Sarkin rigima"
Shifa AB ya matsu su fita daga gidan, saboda wannan yarinyar gabaki ɗaya duk tabi ta cika masa kunne, yana tsaka da tunani ta shigo hannunta riƙe da kwano ɗan China mai murfi guda uku, ɗaya ta ajiye a gaban momy ɗaya a gaban dady ɗayan kuma a gabansu AB a cike yake dam sai zuba ƙamshi yake yi, ta kawo cokali da ƙuli-ƙuli, tana yi musu murmishi tace "wlhi kuci girkin Inna akwai daɗi" tayi maganar tana washe haƙora,
AB ya zabga mata harara wacce tasa ta ficewa daga ɗakin da sauri, batace wa Inna komai ba, sai ma jan abincinta da tayi ta fara ci, Inna tace ta tashi ta kai musu ruwa, tashi tayi ta ɗibi ruwan ta jera a faranti sannan ta kai musu, idanunta suka sarƙe ana AB da ya ɗago ya sake harararta, murguɗa masa baki tayi tare da ficewa da gudu, su kansu basu san meye ya faru ta fice da gudu,
Dady yace "bismillah muci abinci Wlhi mutanen ƙauye sun iya girki" momy tace "nifa yawuna har yana tsinkewa"
Dady ya buɗe kwanon yana bismillah ya fara ci, haka momy,
Sadiq yace "AB bismillah nifa zan fara ci" AB ya wani watsa masa mugun kallo kafin yace "akwai abinci a mota wannan ban taɓa cinsa ba, dan haka ba zanci ba, karya lalatamin ciki" yai maganar ba tare da jin tsoron komai ba, kakkaɓe jikinsa yayi ya fita, daga Dady har momy da Sadiq babu wanda ya tanka masa, har ya fice, a bakin ƙofa ya sameta a zaune tana suɗe hannu, tana ganinsa tayi wurgi da takalmin da taga yana ƙoƙarin sakawa, wani banzan kallo yayi mata wanda yasa ta tashi ta gudu tana cewa "duk naji abinda ka faɗa" ta murguɗa masa baki, waje ta fice da gudu, tana yi masa gwalo, sai da yasa takalmin Sadiq kana ya dauko ƙafar takalminsa guda ɗaya, sannan ya fita zuwa mota, yana fita ya sameta acan tana tsaye ta rungume motar, rai a ɓace yace "ke meye kikeyi a gurin motar nan?"
Sai da ta murguɗa masa baki kafin tace "abinda kazo yi" ya zaro idanu a cikin zuciyarsa yana cewa "babu wanda ya isa ya gaya masa baƙar magana sai wannan ƙwailar yarinyar, amma zai yi maganinta, ya tureta gefe tare da buɗe murfin motar ya shiga backside ba tare da ya rufe ba, a plate ya zuba abincin ya ɗauko cokali, tana laɓe tana kallonsa, ta lallaɓo ta ƙwace plate ɗin abincin ta ruga da uban gudu, bata zame ko ina ba sai bayan gari, ta nemi guri ta zauna ta fara ɗurawa cikinta shinkafa da miya, gani take yi zai iya zuwa ya sameta yasa ta ɗauke naman ta tura a baki tana zare idanunu,
Wani irin takaici da baƙinciki ne ya mamaye zuciyarsa, ji yake kamar ya kamota ya shaƙeta ko zai samu sassauci a zuciyarsa,
Dole ya sake zuba wani abincin gashi wancan nama har biyar ya loda, a halin yanzu naman bai wuce biyu ba ragowar haka ya zuba yaci, dan sai da ya rufe motar gudun kar ta sake zuwar masa, amma ya ɗau alwashin idan ya kamata sai yayi mata duka saboda a irin wannan rashin kunyar nata ta cancanci hukunci, domin bata san koshi waye ba,
Ya dade a mota bai koma ciki ba, har waya da Sara yayi, sannan sukayi video Call yace yana son ganinta haka babu komai a jikinta, hakan ko tayi video ɗin suka gama iskancinsu har yana wani lasar lips ɗinsa, sannan yace "gobe dai suna hanya,
Hango su dady shida Sadiq yayi suna tahowa da wani Dattijo suka iso gurin motar, lokacin ya gama cin abincin,
Dady ne ya Kwankwasa gilas ɗin motar, AB ya buɗe kana ya fito yana gaishe da malam Habu, cike da fara'a malam Habu ya amsa yana cewa "shine ɗan namu?"
Dady yayi dariya yace "shine ka ganshi nan kwanan nan zai dinga zuwar muku koda wane lokaci" malam Habu yace Allah ya tabbatar mana da alkairi, bari muyi Sallah sai mu gabatar da abinda ya kawo mu," cewar dady, kai tsaye dukkansu suka wuce masallaci bayan an idar da Sallah sunyi adu'oi sannan suka fito zuwa gida, dama malam Habu ya sanarwa ƴan uwansu na ƙauye da na nan kusa duka suka iso gidan aka taru, Dady ya bada dukiyar aure, a take a gurin suka gabatar da komai da komai, harda sa ranar 1month duka aka saka, kowa sai sanyawa dady albarka suke tayi, suna cewa zai ƙarfafa zumunci sosai,
Sadiq da AB a mota suka tsaya, sai yanzu ya sake tabbatar da gaskiyar maganar da Dady da momyn suke gaya masa, ace kamar shi namiji mai aji da Naira ya auri ƴar ƙauye wacce kanta ma bata sani ba bare tasan nasa, cije lips yayi da ƙarfi hawaye na fara wanke masa fuska...!
Page 7-8

Da sauri Sadiq ya jijjigashi, cikin tsoro yace "AB meke damunka, kana nufin bazaka yiwa iyayenka biyayya ba kenan, Wala Allah wannan auren da suke son yi maka ya kasance abin alfahari a gareka?"

AB na kuka yace "Sadiq bana sonta bana ƙaunarta wanda yake sonta ma zan iya tsanarsa" yai maganar idanunsa sunyi jajir damatsen hannunsa duk sun ƙara murɗewa,
Innalillahi wa inna ilahir raji'un Sadiq ya dina ambata yana kallon AB da ido cikin ido, tabbas ya gano asalin tsanar yarinyar a tare dashi, amma babu inda zaiyi tunda su Dady sun gama komai, yo shi waye ma, yaron abokin Dady ne, babu ruwansa dazai tsunduma kansa cikin wannan cakwakiyar, Gara dai ya yita bawa AB baki har zuwa lokacin da zai sakko daga wannan tsattsauran ra'ayin nasa,
Sun jima a mota har aka kira sallahar magriba suka fita Masallaci bayan an idar suka dawo,
Momy ko tana ɗakin Inna sunata Shan hira, kasancewarta bata da duhun kai, Habiba ko tunda akayi sallahar isha'i ta wuce inda suke kwana da yaran maƙotansu, Dady yana tare da Malam Habu sunata hirar zumunci, Malam Habu yace "ni banga yaranka sun shigo bane, ai ya kamata suzo suci tuwo"
Dady yace "ai kuwa inaga dai suna mota ne, amma bar in duba su"
Dady ya sa takalmi ya fita zuwa inda motarsu take a pake, AB na ganinsa yai saurin buɗe murfin motar, yana kallon Dady, "ku fito kuzo kuci abinci sannan an samar muku ɗakin da zaku kwana" Dady yai maganar yana kallon Sadiq, cike da girmamawa Sadiq yace "Insha Allah dady gamu nan zuwa"
Da ƙyar Sadiq ya dinga magiya akan AB ya fito sannan ya fito suka shiga cikin gidan, hannunsa na riƙe da nutrimlik, koda suka shiga, malam Habu ne ya rakasu ɗakin da zasu kwana, sannan ya nuna musu abincinsu anan ɗakin,
Godiya Sadiq yayi masa suka shiga, a saman katifar yayi Sadiq ya zauna tare da cewa "AB bismillah" shima zama yayi, kwata-kwata ɗakin beyi masa ba, saboda duk ƙasa, ga shi windunan a buɗe, duk sauro sai kuka sukeyi, wani almajiri ne yayi bara AB ya ƙwala masa kira, yazo da sauri, Sadiq yace ya shigo, bayan ya shigo suka tambayesa nan ba'a siyar da maganin sauro?"
Almajirin yace "taɓ babu hyago anan sai ka shiga can cikin kasuwa,
Sadiq yace "to mun gode, sannan ya sashi ya yanki tuwon, almajirin yayi godiya sannan ya wuce,
Haka dai suka kwana cikin rashin jin daɗin zaman ɗakin,
AB tun cikin dare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login