Showing 60001 words to 62407 words out of 62407 words

Chapter 21 - SAKATA COMPLETED BOOK BY SAYYID (LEGENDS PEN).txt

23 Nov 2025

2558

babu abinda zan masa wallahi, ina son sa sosai, dan Allah ya yi hakuri.



 Shikenan Salma, ki ta shi ki shirya ki gyara jikin da gidan ga shinan zai so.



 Toh Mama na gode. Na fada zan kashe wayar.  Kina ji Salma?.



 Ina ji Ummah.



 Duk wani abu da kika san ya ta ba baki kyauta ki yi amfani da shi, ki yi amfani da kayan lefen ku, ya ce dani babu wani abu na shi da kika ta ba amfani da shi.



 Shikenan Mamah zan yi, har girki zan masa.



 Allah ya yi miki albarka.



 Amin. Na fada tare da sauke wayar a kunne, na san na cancanci hukunci kishiya a gurin Mus ab, sabida na nuna mummunar tsanar. Yanzu abunda nake fata shine, samun soyyayarsa a karo na biyu.



Ta shi na yi na shiga gyara gidan, cikin sauri da nutsuwa na ke kowanne aiki gaba daya gidan, cikin kankanin lokaci na gama gyaran gidan. Shinkafa da miya na dora, bayan na soya doya da kwai, na yi farfesun naman rago, na kuma yi papped chicekn na kaza, na hada masa lafiyayyane drinki, na jere komai kan dining na je na shirya. Wata doguwar rigar abaya mai kyau wacce ba a cikin lefe ya ban ita ba, lokacin biki ya bani da hannunsa, ban ma san ya a ka yi ta zo nan ba, shiri na yo tsaf gwanin ban sha awa na sha light make up abuna, sai dai ganin awanni babu Mus ab ya sa jikina ya mutu, ina cikin wanan tunanin ne wayata ta suma ringing dauka na yi tare da sawa a kunne.  Hello Salma fito bakin gate yanzu. Bangane wanda ya yi magana kamar dai Mus ab kuma kamar ba shi ba, mayafi na na dauka na fita compound, Abdul ne mijin Walida da mamaki matuka nake kallonshi har naje inda yake.  Lafiya, ina Yaya Mus ab din.



 Shi ya ba ni umarnin dakko ki, muje zaki gani.



Legends pen.



Page 46.



Shiga cikin motar na yi hankalina a tashe, ina ta faman tunani ko dai bai hakura ba, ko kuma a gida za ayimun fada oho, har mu ka shigo cikin unguwarmu, unguwar da na yi natukar kewarta kamar ba zan sake shi ga ba, kowacce na shekara dari banzo ba, taron mutane na gani a kofar gidanmu da yawa, nan da nan na bude baki cike da tsoro na ce.  Abdul mai ya faru?.



Hannu ya sa ya nuna mun Mus ab bayan ya yi parking sanan ya ce.  Zai miki bayani. Sauka na yi na nufi inda yake, idanun sa sun yi jazur kamar garwashi, da alama ya yi kuka, inda yake na nufa ina sauri kamar zan ta shi. Hannuna ya kama ya shiga jana zuwa cikin gida, ko ban da hankali na san mutuwa a ka yi a gidan Galadima, duba da irin mutane da kuma kukan da su ke, cikin gida mu ka shiga bangaren Hajja.  Ba dai Hajja ba ce ta mutu na shiga uku ina zan sa rai na da hakkin Hajja. Ganin Hajja da sauran  yan uwana gaba daya a bangaren Hajjan ya sa na ji wani sanyi, cika ni ya yi zai juya. Kallon mutanen dakin nake daya bayan daya, ko zanga wanda babu.  Ummanah! Ummanah. Na fada a rude, hannuna ya nuna mun dakin Hajja, alamun ta na ciki sosai, juyowa na yi na kalleshi a hanakali na matso inda yake.  Nifsil hayyat. Na kira shi, juyowa ya yi ya kalleni, ba na iya tantance yanayin da yake.  Mai ya faru?. Sautin muryar Ummanah na ji bayan ta sauke wata nannautar a zuciya sanan ta ce.  Kar ka ta fi ka bar ni, kar ka ta fi ka bar mu, Alhaji yaranka Salman ka, Asma unka da su Muhammadu, ka ce za ka rayu da mu, zaka zama bango a garemu, Alhaji idan ka ta fi ina zan sa rai na , ina  ya yanmu za su sa ransu. Suuuh na ta fi kasa jikake tim, da sauri Mus ab ya yo kai na tare da rungume ni cikin jikinsa kam, kamar wani zai kwace ni, cikin kuka na ke cewa.  Abbanah ne ya mutu!, Abbanah ya mutu, Abba mai yasa, Abba mai yasa zaka ta fi da huri, Abba mai mu ka yi maka zaka tafi kabarmu da huri, Abba dadin mai zamu ji a duniya idan babu kai, Abba dan Allah ka dawo, Abba kar ka tafi ka barmu, Abba kai ne gatan mu Abba kai ne jagoran mu Abba ba yanzu ba dan Allah, Abba ka yi alfahari da ni ko sau daya. Matseni Mus ab ya sake yi a jikinsa yana kuka sosai da sosai, kamar yadda kowa na bangaren Hajjan ke yi.  Salma Abba bai mutu ba fa, Abba zai dawo Abba ba zai ta fi yanzu ba, Abba shine bangon mu gaba daya, Abba shine karfin gidan Galadima, wallahi Abba bai mutu ba. Muryar Walida na ni da sauri na kwace jikina daga kan mus ab na yi inda take tare da rungume ta ina kuka, ina fadin.  Walida dan Allah kar Abba ya mutu. Muryar wani kawun su Abban mu ka ji ya ce.  Za a shigowa da gawar ku yi Sallama da shi. Ji na yi kamar ya bugamun guduma a kaina jin ya kira Abbanah da gawa. Amma ban iya magana ba aKa shigo da makara dauke da Abbanah a kwance daure da farin likafani, da sauri na yi wajen da su ka ajiye shi ina kuka ina fadin.  Abba yanzu kai ne ka tafi ka bar ni? Ka tafi ba tare da ka yi mun kallon ™arshe ba?, kallo a gidan mijina cike da soyayya, Abba har yanzu ina jin sautin muryarka yana kirana da  yar aljannata, yanzu fa shiru, shiru Abba ba zan ™ara ji k ce min komai ba?.



Wata Kwalla ta ci ka idona, Mus ab ya zo ya rungume ni. Kowa na zagaye da Abbanah yana masa addu a cikin hawaye, Yaya Asma u dai na dakin Hajja ta suma gaba daya, Sadiya ma ta fa di tun da ta ji ance wai Abba ne ya mutu, Abban ciki ku ance kwantawa ya yi a kasa yana kuka kamara karamin yaro, yanzu ma ana tunanin hawan jini shi ya tashi an kira masa likita, Mus ab ne ya kara rungume ni, ina kuka na ci gaba da cewa.



 Abba, ni ba zan iya ba, ban san rayuwa ba, ban san komai ba, ka yi mini komai. Kai ne jagora na, ka fi zama uwa fiye da uba. Kana tare da ni ko da yaushe. Abba, me ya sa za ka bar ni da huri haka? Me ya sa ba ka jira na dawo na rungume ka, na ce maka na gode ba, na gode da kyauta miji da kabani. Abba Na gode da ka bani rayuwa da tarbiya da soyayya.



Dago idanuna na yi na kalleshi kwance cikin likkafanin.  Abba, ka tafi da damuwata, na yi maka laifi, Abba, na fusata ka, Abba ka yi fushi da ni, ji nake kamar har yanzu ban nemi gafarar ka ba Abba. Dan Allah Abba, ka yafe min, Idan ruhinka na jina, idan kana kusa dani, ka gafarce ni, na maka rashin biyayya a wasu lokuta, Ina sonka Abba, har abada, har abada zan ri™e sunanka, zan rike tarbiyar ka da Umarnin ka Abba, Ruhinka ya sami rahamar ubangiji Abba, na yi alkawari zan yi rayuwar da za ka yi alfahari da ita. Zan zama abin alfahari gare ka, domin kai ba kowane uba bane, kai uba ne na gaske& 



Legends pen.



Page 47



 Mus ab dauke yarinyar nan. Yaya iliyasu ya fada muryar shi na rawa, alamun kuka yake yi, kamani Mus ab ya yi zai dagani, ai kuwa ina mikewa na zube kasa tum.





Bayan su Hajja da kowa ya zo ya ci kuka a ka fita da Abbanah zuwa gidan na gaskiyya, kowa na gidan Galadima ya san ya yi baban rashi, kowa da kowa ya san Abba shine karfin gidan Galadima, Abban ciki likita ya duba shi ya tabbatar da cewa hawan jininsa ne ya tashi, sabida mutuwar ta yi matukar ta ba shi, sadiya kuma a wanan faduwar da tayi aka huce da ita asibiti, kuma wanan hucewar ta samu sauka, kyakyawan dan ta namiji, wanda ya zo duniya ranar da Abbanah ya bar duniyar.



Dama haka rayuwa take, lokacin da wani ya tafi kokacin wani ke zuwa, lokacin da wani farin ciki lokacin wani ke bakin ciki, Ummanah kam an samu ta yi shiru, amma gaba daya ba ta iya ko da magana, sai zubar hawaye ta ke. Yaya Asma u ta yi suman har ta gaji ita ma ta dawo kukan.



Tun faduwar da na yi ban bude idona ba sai can yamma, ban san a inda nake ba amma nasan ba asibiti ba ne, Abbanah ya mutu. Na fada tare da fashewa da kuka, ina cikin kukan ya shigo sai a lokacin na fahimci da kin shi ne na bangaren Hajja, ga hotonsa nan ga kuma wanu hoton nawa, ta shi nake kokarin yi na je na rungumeshi amma rashin kwarin jikina ya hanani ta shi, zama ya yi kusa da ni yana kallo na.  Salma kinga yadda Allah yake hukuncinsa ko?, ya dauke mana Abba lokacin da ba muyi tunani ba. Kuka na fashe da shi tare da fadin.  Ka yafemun dan Allah, na sani har da hakkin ka ke bibiyata a rayuwa, na yi furucin ko yau babu ran Abbanah ba zan kara zama a gidanka da matsayin matar aure ba, sai ga shi Allah ya dauke shi bayan ya jarabci ni da matsanancin son ka, dan Allah kar ka sake ni. Tasowa ya yi ya rungume ni tare da fadin.  Tun da ranan Abba ban sake ki ba Salma, sai yanzu bayan amanar ke da ta sake dawowa a hannu, Abba ya kira ni dazu bayan kin kira shi, ya kara bani amanarki Salma. Kuka na fashe da shi sosai ina rungume a jikinsa.  Sadiya ta sauka, ta samu namiji. Na ji dadi a rai na nasan ko ba komai sunan Abbanah za a mayar amma na yi danasin rashin biyayya ga iyaye na, da na yi biyayya da yanzu nima ina lokacin da zan haihu kuma zan mayarda sunan Abbanah, to yanzu ma ina cikin yake bare ya yi wata tara na haihu, idan ma na haihu ban lallai na farko ya kasance namiji ba.



Sai dare na fito daga dakin, zuwa lokacin na samu sauki sosai, na shigo cikin yan uwana kowa na jimamin mutuwar Abbanah. Ban sami zama tare da Ummanah ba sai dare, bayan na sha kuka na nemi ya fiyarta.



Haka rana daya ta zo ta huce, ya tabbata babu Abbanah a duniyar, rana ta biyu ta sake zuwa ta huce, babu Abbanah, rana ta uku ta huce. Ya zuwa yanzu kowa na gidan Galadima ya yarda babu Abbanah ya tafi, ya amsa kiran mahalincinsa, sai dai mutuwar ta bar mana abubuwa mai girma domin Hajja dai ciwon ta ya ta shi, ta shi mai tsananin na gaske, ya zamana mgana ba ta iyawa, Abban ciki ya daina walwala gaba daya, ko magana ba ya iya wa sosai, Ummanah ma hakan take, kowa na gidan Galadima ya samu sauyi. Haka a ka yi kwana bakwai, yaron wajen Sadiya mayar ma sa da sunan Abbanah, mun ji dadi sosai da sosai, washe gari kowa ya kama shirin tafiya gida, ciki kuwa har da ni Salma matar Mus ab.



Bayan mun yi Sallama da kowa mu ka koma gidanmu, duk da muna cikin jimamin rashin Abba hakan bai hana mun nuna kauna da kulawa ga junanmu ba. Na sake neman yafiyar Mus ab kuma ya yafemun, sanan ya roki ne alfarmar mayar da wanan abun tarihi, ko da wasa ba ya son sake tayar da maganar cewa a baya na taba kinsa.



Mun fara rayuwa cike da soyayya da kulawar juna, Mus ab ya zama bango na ya zama gata na, ya dauke ni a matsayin amanar da Abbanah ya ba shi, wata biyar da mutuwar Abbanah Allah ya yi wa Hajja rasuwa, wacce tun lokacin da Abbanah ya rasu ba ta sake jin dadi ba, mun yi kukan rashin ta sosai da sosai, tsakanina da yan uwana kowa ya karbe ni hannu biyu kamar wani abu bai ta ba faruwa ba, haka tsakanina sa Ummanah soyayya da kulawa ta ke nuna mun sosai da sosai, ta so komawa gidan su bayan rasuwar Hajja, amma su Abban ciki suka ce.  A a sam. Ta dole ta zauna gidan Galadima, ba tare da ta taba rasa komai na bukata ba. Mus ab ne baban jika na miji a gidan Galadima cikin kankanin lokaci ya maye gurbin Abbanah a gidan Galadima, ya zama shine bango gidan Galadima.



Ni kam tun rasuwar Abbanah na canja, daga asalin Salma da kuka sanni, na zama saliha mara yawan magana, mara yawan fada bare hayaniya, babu abinda na sa a gaba sai bautar sa yiwa mahaifiyata biyyaya da mijina, girmama iyaye da yan uwa, har gidan su Walida na je da sadiya mu ka yafe juna, su ka fadamun su ba su ta ba fushi da ni ba, ni ce dai na watsar da zumunci.





Watanni kadan da mutuwar Hajja, nasamu haihuwar  ya mace wacce a ka saka mata sunan Hajja, muna kiranta da little, soyayyarmu nida Mus ab ta zama abin kwantace a wajen kowa, domin ko ina ban iya boye son sa, haka shima ba iya yawa, naga amfani da ribar biyayya ga iyaye, kamar yadda shima ya ga amfanni da ribar kai kuka wajen ubangiji.







Tammata bi hamdillah.





Allah na gode maka da kabani damar kammala wanan labarin na Sakata cikin koshin lafiya, yadda na fara shi da bismillah, na karashi da Alhamdulillah. Kuskuren da ke ciki Allah kayafe mana, gyaran da ke ciki Allah ka bamu ikon amfani da shi.





Labarin Sakata; labari ne da kike nuna illar rashin biyayya ga iyayye da kuma ribar biyayaa ga iyayen, da amfani da girman Addu a.



Na gode sosai daga bibiyar ta tun farko har zuwa karshe.



Allah yasa mu dace, yayi mana kyakyawan karshe.



Legends pen



08129553971/ 08165383931





















Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login