Showing 15001 words to 18000 words out of 48253 words
na sa aljanu su shanye min ƙafafuwanku."
Cikin sauri Innaji ta saɓi jakarta sannan ta ɗauki jakar Aabidah ta riƙe a hannunta. Mayafinta na zamewa kamar zai faɗi amma ko ta kansa bata bi ba ta kama Aabidah da gefen kanta ya kurje yayi fari tas ko ɗigon jini babu a wajen. A dudduƙe suka fita suna bawa Boka haƙuri. Cikin tsawa ya ce.
"Ku tafi ku jira har sai na neme ku da kai na. Ku da kanku kun sani da ni da ku duk akan ɓata muke,idan Allah Ya hukunta faruwar abu to fa dole sai ya faru. Dama ce kawai yake ara mana muke yin abinda muke so,dan haka ku tafi ku bani lokaci na yi bincike na samo mafita."
Da jin haka sai hankalin Aabidah ya kwanta. Godiya suka dinga yi wa bokan sannan suka tafi cike da tarin damuwa da tsamin jiki. Sun jima a cikin mota Aabidah na saka tissue ta na goge ciwonta da ya fara tsattsafo da wani ruwan azaba. Da ƙyar ta iya tada motarta suka bar gidan Bokan suka nufi cikin gari. Suna tafiya Boka ya hau bincike akan Aabid,nan ya gano yana daf da isa gidan Maheer,cikin sauri ya hau yin wani irin tsafi akan Aabid. Ya na gamawa ya shafe ruwan hoton Aabid ya ɓace.
*Aabid.*
Tinda ya baro gidansa yake tuna duk wata rayuwarsa da ta gabata kamar wanda aka kai cinema aka kunna wa video yake kallo. Wasu irin zafafan hawaye ke sauka daga kwarmin idanuwansa wanda suka sa har baya iya ganin gabansa. Bugun zuciyarsa da ya tsananta ne ya sanya shi samun waje a bakin titi ya tsayar da motarsa tare da kifa kansa a jikin sitiyarin motar. Hannu ɗaya ya saka a ƙirjinsa ya dafe saitin zuciyarsa dake barazanar tarwatse masa. Ya jima a haka kafin ya samu nutsuwa ta fara ziyartarsa. Cike da matsananciyar kewa tare da kawa zucin ganin mahaifiyarsa da mace mafi soyuwa a ransa ya tayar da motar ya nufi gidan Maheer,domin kuwa shi kaɗai ne wanda zai yi masa jagora domin dawo da faricikin rayuwarsa da ya rasa na tsawon shekaru. Yana isa ƙofar gidan Aabid ya tsayar da motarsa a bakin gate ɗin gidan ya taka ya hau ƙwanƙwasa ƙofar gidan. Yana nan tsaye ya ji wani irin faɗuwar gaba ta kama shi har sai da ya ji kamar jiri na ɗibansa,babu jimawa kansa ya sara masa da ƙarfi, kamar ɗaukewar wutar nepa haka ya nemi tunaninsa na baya ya rasa,nan take ya hau duba kayan jikinsa da wajen da yake tsaye. Cike da matsanancin mamaki ya juya da sauri ya shige motarsa,yana jin muryar Maheer na faɗin.
"Waye?"
Cikin sauri ya tada motarsa ya bar ƙofar gidan da mugun gudu. Ko da Maheer ya fito ya buɗe ƙofar gidan sai bai ga kowa ba,cike da mamakin wanda ya zo yana yi musu bugu kamar zai ɓalle gate ɗin gidan ya koma ciki. Kai tsaye sashen su Hajiya ya nufa ya tarar da Salimah na shanya zannuwan Hajiya a igiya. Murmushi ya sakar mata ya ce.
"Sannu Auta,Allah Ya yi miki albarka."
"Amin Yah Maheer;barka da safiya."
"Barka dai Auta,Ya jikin Hajiya? Ina fatan yau kun samu bacci sosai ko?"
"Eh Alhamdulillah tinda ta sha maganin nan jiya take bacci bata farka ba sai da asuba,ta na idar da sallah ko azkar bata ƙarasa ba bacci ya ɗauke ta."
"Masha Allah. Allah Ya ƙara mata lafiya,ke kuma Allah Ya ƙara baki juriyar ci gaba da kulawa da ita ba tare da gajiyawa ba."
Nan take muryar Salimah ta hau rawa,cike da matsananciyar damuwa ta ce.
"Kula da Hajiya ya zame mini dole Yah Maheer,kada ka manta bani da kowa bani da komai,ku ne gata na,kuma ku ne ahali na da nake gani na ji daɗi a raina."
Jinjina kai kawai Yah Maheer yayi ya wuce cikin sashen su cike da tausayin Salimah a cikin ransa.
*Aabidah.*
Kai tsaye gidan Innaji suka yi wa tsinke. Cike da damuwa Innaji ta ɗakko zuma ta shafa wa Aabidah a ciwonta da ke yi mata zogin azaba. Cikin tsananin damuwa Aabidah ta kau da kanta daga hannun Innaji dake lallaɓata tana bata haƙuri.
"Innaji kada ki damu da ciwon dake kai na,ina so ki mayar da hankali akan warkar min da ciwon dake cikin zuciyata. Innaji bana son Aabii ya rabu da ni,ina son sa ba zan iya ci gaba da rayuwa ba tare da shi ba a duniyar nan."
"Haba Aabidah ya kike magana irin wannan kamar an ce miki ko da Khadijatou ta dawo cikin rayuwar Aabid zai iya rayuwa babu ke? Ina son ki dinga tunawa da mun riga da mun kama Aabid kamu na har abada. Aabid ba zai taɓa ganin Khadijatou ba ballantana tarin sihirin da muka yi musu ya warware. Ke ina mai tabbatar maki da cewa ko da sun tuna da juna ba zamu taɓa yarda su haɗu ba;domin haɗuwarsu tafi tunawa da junansu hatsari a wajen mu."
Wani sabon kuka Aabidah ta rushe da shi sannan ta ce.
"Why me? Why meeee? Me yasa sai da nutsuwa da kwanciyar hankali ta same ni;ariziƙi na ya nunku,ina zaune da mijina lafiya wannan matsalolin za su kunno min kai? Ya Allah ka sake ara min dama ka nesanta Khadijatou da Mijina,Ya Allah ka sake raba tsakaninsu rabuwa ta har abada......
MUGUWAR MACE.
NA: HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️
*Za ku iya fara payment ɗin littafin MUGUWAR MACE da yake akan farashin 1k ta 9031416423,ku tura shaidar biya ta 09031416423.*
PAGE 9.
Sai da Innaji ta nisa sannan ta miƙe tsaye ta mayar da zumar da ta ɗakko mazauninta. Cike da mutuwar jiki ta kalli Aabidah dake gunjin kuka ta ce.
"To yanzu ya za ki yi da maganar Boka da ya ce ki janyo wannan yaron Maheer jikinki?"
A hasale Aabidah ta ce.
"Wai ke Innaji me yasa wani lokacin sai ki dinga yin magana ba kya tunani ne? Ni yanzu ina ruwana da wani Maheer? Ai sawun giwa ya take na raƙumi Innaji, yanzu babbar damuwa ta a duniya bata wuce na san inda Khadijatou take ba,ina so na nemo ta da kaina kafin Aabii ya ganta. Ina so na kashe ta har lahira kowa ma ya huta. Wannan karon ba zan yi kuskure ba wajen aikata inda ba za ta dawo cikin rayuwarmu ba har abada."
Labule Jauharah ta buɗe ta na kallon su Aabidah. A razane Aabidah ta kai dubanta wajen da ta ji motsi,ido huɗu suka yi da Jauharah da ke a buge sai lumshe idanuwa take yi kamar mai jin bacci. Tsaki Aabidah ta ja mai ƙarfi ta kalli Innaji ta ce.
"Yaushe wannan yarinyar ta dawo gida daga yawon dandin da ta tafi?"
Hannu Innaji ta ware tana kyaɓe baki ta ce.
"Yanda kika ganta haka na ganta,dan ba a gidan nan ta kwana ba. Ai ita da wancan da'un ba za ki taɓa sanin lokacin shigarsu ba ballantana fitar su. Ke! yaushe kika dawo gidan?"
Cikin tafiyar ƴan maye Jauharah ta isa kujera mafi kusa da ita ta zauna tana lumshe idanuwa. Cikin muryarta mai kama da ta matan da suka tsufa suna busa sigari ta ce.
"Yanzu Mine ta ajiye ni ta tafi. Babbar Yayaaa na ji kina wata magana akan waccan mujiyar, a ina take na aika yara a kawar miki da ita cikin sirri? Kin san yanda kike bani farinciki dole ne nima na rama wa kura a niyarta."
Tsaki Aabidah ta ja mai tsawo kafin ta ce.
"A hakan ne za ki yi min abinda zan mora Jauharah? Allah ya wadaran rayuwar da kika jefa kanki a ciki. Ke kan ki baki taimaki kanki ba ballantana ki taimake ni. Na kashe kuɗaɗena a banza akan ku,na ɓata lokaci na da energy na duk akan ku,daga ƙarshe kun zamo marasa amfani. Tashi ki bar nan kafin na huce takaicin dake cikin raina akan ki."
Tsuke baki Jauharah ta yi ta tashi tana tangaɗi ta shige ɗakinta ta rufe ƙofa. Tsaki Aabidah ta ja ta dafe kanta tana ci gaba da kukanta wanda take jin sanyi a ranta a duk saukar hawaye ɗaya daga idanuwanta. A wannan rana a gidansu ta kai azahar saboda tsoron kada ta koma gida Aabid ya sake bijiro da zancen Khadijatou ba ta jin zuciyarta za ta iya ɗaukan jin kalmar sunan babbar maƙiyyarta a bakin mutumin da ta fi so sama da kowa a rayuwarta. A duk bugawar sa'a ta agogo sai gaban Aabidah ya faɗi. Ta kasa ci ta kasa sha saboda damuwa da zullumi. Innaji kuwa Laure ta sa ta dafa mata abinci mai rai da lafiya da naman kaza ta ci ta ƙoshi ta kora da lemo. Ganin yanda Innaji ke warkajaminta ba tare da jimamin halin da Aabidah ke ciki bane ya sanya Aabidahn ɗaukan makullin motarta da mayafinta ta shuri takalmanta babu ko sallama ta bar gidan. Kai tsaye gidan ƙawarta kuma aminiyar cin mushenta ta nufa. Tin daga bakin gate mai gadi ya san yau Hajiya Aabidah bata cikin hayyacinta;duba da irin tuƙin da take yi. A gaggauce ta kashe motarta ta buɗe ta shiga gidan Hajiya Zaitunah. Zaune ta ga Hajiyan ita da yaranta suna kallo. Kallo ɗaya yaran suka yi wa Aabidah suka kawar da kawunansu suka ci gaba da kallon su, yara ne da aka sangarta suke jin kansu,dan haka ko gaisuwa bata haɗa su da kowa sai wanda suka ga dama. Ganin irin halin da Aabidah ke ciki ne ya sanya Hajiya Zaitunah wadda ta girmi Aabidah da shekaru takwas a duniya miƙe wa ta bi bayanta zuwa ɗakinta. Su na shiga Aabidah ta zauna a bakin gado ta rushe da kuka. Cike da matsananciyar damuwa Hajiya Zaitunah ta dafa bayan Aabidah ta ce.
"Ah ah Ƙawata lafiya kike irin wannan kukan? Me ya samu Aabii ɗin naki? Ina fatan dai ba sakin...."
"Allah Ya kiyaye Aabii ya sake ni. Ai ni da shi mutuwa ce za ta raba mu,walau ya binne ni ko kuma ni na binne shi. Ƙawata matsala ce mai girma ta taso min wadda muka jima da haƙa rami mai zurfi muka binne. Sai kuma gashi ta ɓullo a lokacin da bamu yi zato ko tsammani ba."
Waro ido Hajiya Zaitunah ta yi tare da dafe ƙirji ta ce.
"Kar dai ki ce min wannan mayyar ta dawo cikin rayuwarku?"
"Wai ke me yasa ba kya faɗan alkhairi ne? In dai boka na raye na yi imanin Khadijatou ba za ta taɓa dawowa cikin rayuwarmu ba."
"To meye zai ɗaga miki hankali haka bayan kin san ba dawowa za ta yi ba? Ko dai kema kin fara fuskantar irin matsalar da nake fuskanta ne?"
Ajiyar zuciya Aabidah ta sauke tare da goge majinar da ke shirin gangarowa a hancinta da tissue ɗin dake gefen gadon Hajiya Zaitunah. Cike da damuwa ta labarta wa ƙawar tata abinda ke faruwa. Salati Hajiya Zaitunah ta yi sannan ta ce.
"To ai wannan maganar taki daidai take da dawowar Khadijatou cikin rayuwarku Aabidah. Abu ne fa da muka riga muka sani amma muke take sanin,shi asiri lokaci ne da shi komai daɗewarsa a jikin bawa. Idan har kika ga bai karye ba to fa mutumin da aka yi wa asirin ya mutu,ballantana Khadijatoun da na sani mai taurin rai ce da kafiya,kada fa ki manta abubuwan da muka ƙulla mata a baya amma yarinyar nan sai da ta tsallake su. Dan haka ni dai shawarar da zan baki shine,ki koma wajen Boka ya sake maimaita sihirin da aka yi a can baya,ni kuma na yi miki alƙawarin yawata wa cikin garin kano da kewaye dan taya ki neman wajen binnewa kamar yanda muka yi a wancan lokacin."
Hawaye ne suka zubo wa Aabidah a karo na babu adadi. Muryarta na rawa ta ce.
"Wannan lissafin naki duk ba mai yuwa bane inji Boka. Domin kuwa da faɗa ma muka rabu,dubi nan ɗina,shi ne ya shaƙe ni ya buga da jikin gini har sai da wajen ya kwaile."
"Da dikkan alamu hannunsa ya fara yin sanyi gaskiya shi yasa lamuranmu ke ta taɓarɓarewa. Yanzu ina so ki shirya zuwa jibi zan kai ki wajen wani sabon boka da na ji labari wajen su Zinariya dan ni ma ina buƙatar a sabunta min aikina,gaba ɗaya cikin kwanakin nan bana gane kan Dad...."
Da ƙarfi aka buɗe murfin ƙofar ɗakin da su Aabidah ke ciki. Wani ƙaƙƙarfan mutum ne ya shiga ya tsaya a bakin ƙofa yana kallon su cikin tsananin ɓacin rai. Hannu ya ɗaga yana nuna Aabidah da ta yi sororo tana kallon yanda jikin Hajiya Zaitunah ke rawa. Kallon mutumin Aabida ta sake yi wanda a baya suke sakawa aiki har da ɗebo musu ruwan sha ta ga yanda yake huci kamar wani zaki,nan da nan jikinta yayi sanyi ta miƙe ta saɓa jakarta a kafaɗa ta bar ɗakin. Kai tsaye motarta ta nufa ta faɗa tana sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi kamar wadda ta yi tseren gudu. Tana tada motar ta mai gadi ya wangale mata gate ta bar gidan a guje. A hanya babu abinda take tunawa da ya wuce sauyin da ta gani a gidan Hajiya Zaitunah. Nan take tsoro da fargabar dake cikin ranta suka nunku. Murya na rawa ta ce.
"Shin me yake faruwa a rayuwarmu ne? Lallai dole ne na samarwa kaina mafita,domin kuwa ba zan taɓa yarda Aabii ya dawo cikin hayyacinsa ba kamar yanda mijin Hajiya Zee ya dawo cikin hayyacinsa."
Tana isa gida ta hau dannawa mai gadi horn,da gudu ya ajiye abincin da yake ci ya buɗe mata gate yana yi mata sannu da dawowa. Ko ta kansa Aabidah bata bi ba ta ajiye motarta ta kalli motar Aabid da ya yi mata wani irin mugun parking. Jiki a mace ta shige cikin gidan tana ɗari-ɗari dan bata san me za ta tarar a ciki ba. Ta na murɗa ƙofar shiga parlourn ƙasa ta ci karo da wajen kamar yanda ta barshi,sai ma takalmin Aabid da ke yashe a tsakiyar parlourn kamar wanda ya yadda shi da gayya. A hankali ta ci gaba da takawa har ta haura sama,kai tsaye ɗakinta ta nufa ta watsa ruwa kafin ta tsantsara kwalliya cikin ƙananan kayan da Aabid ke mutuwar so. Ɗakinsa ta shiga ta tarar da fitilar a kashe;sai dim light da ya kunna,karatun ƙur'anin da aka yi shekara da shekaru ba a saurara ko karanta ba a cikin gidan ke tashi a wayarsa. Kwance yake ya na kallon sama da idanuwansa da suka kaɗa suka yi jawur. Babban abinda ke damunsa shine cushewar tunani da rikicewar ƙwaƙwalwa,sai wani irin matsanancin ciwon kai da faɗuwar gaba da yake ji. Ƙamshin jikin Aabidah ne ya sanya shi lumshe idanuwansa hawayen dake kwance a cikinsu suka gangara gefen idonsa suka yi wa kansu masauki a kunnuwansa. Ba tare da ya damu da share wa ba ya sauke jajayen idanuwansa a saman fuskar Aabidah dake zaune a gefensa ta kasa furta komai saboda tsananin tsoron abinda zai je ya zo. Jin ta take yi kamar wata baƙuwa ko wata sabuwar halitta. Hannu Aabid ya miƙa mata cike da kulawa,ta na ganin haka ta isa gare shi da sauri ta kwanta a jikinsa tana mai rushewa da kuka. Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi ya hau shafa bayanta da sigar lallashi. Duk yanda ya so ya buɗe baki yayi mata magana ya kasa. A haka Aabidah ta samu baccin da bata yi ba ya ɗauke ta cike da mugayen mafarkan da ta dinga fatan ta farka ta buɗe ido dan ta dena ganinsu,amma inaaa gaba ɗaya duniyar mummunan mafarki ta yi mata dabaibayi.
Haka rayuwar gidan Aabid ta koma cike da shiru da tsoro tare da fargaba,ɗimuwa da kuma damuwa. Gaba ɗaya ya dena fara'a,ya dena duk wasu ayyukan da yake yi mata a baya,ko kamfaninsa ya dena fita,lokuta da dama yana ganin kira daga kamfanin zai ƙi ɗagawa har ya katse. Sanin cewa asirin da ta yi masa yana ta barin jikinsa a hankali shi yasa ko da wasa bata yi masa tsawa ko hantararsa ballanta ta saka shi yayi mata wani aiki,tana ji tana gani zai kunna karatun ƙur'ani bata da halin kashewa. A haka Aabidah ke lallaɓawa ta yi musu girkin da suke kasa ci daga ƙarshe sai dai ta kai wa mai gadi,shi kuwa mai gadi sai ya tsince naman ya cinye ya zuba wa karen maƙota abincin. Bayan kwana biyu Aabid ya tashi yana jinsa kamar sabon mutum,kewar Hajiyansa da ƴar'uwarsa ce ta mamaye zuciyarsa dan haka sai ya shirya tsaf cikin shaddarsa gezna ya saka hularsa sabuwa dal da takalmi mai tsada da ya dace da kayan jikinsa. Aabidah na ganinsa da irin wannan shigar hankalinta ya tashi,cikin kissa da kisisina ta dinga bugun cikinsa dan ta ji inda zai je,amma Aabid ya yi shiru bai bata amsa ba. Cike da shagwaɓa Aabidah ta kwantar da kanta a jikinsa ta ce.
"Wai ni Aabii laifin me na aikata maka ne a cikin gidan nan da ka dena yin hira dani,ka dena kula ni a matsayina na matarka ta sunna,kullum haka za mu kwanta mu tashi da kai ba tare da wani abu ya shiga tsakaninmu ba,idan na yi maka girki sai dai ka ce a zubar ka yi order a waje ka ci. Ko dai ka dena so na ne Aabii?"
Ta ƙarashe maganarta cike da zubar hawaye da ƙuncin zuciya. Numfashi mai tsawo Aabid ya ja kafin ya fesar ya samu waje ya zaunar da su a kujera. Fuskarta ya ɗaga yana share mata hawayenta kafin ya buɗe baki kamar mai jin tsoron yin magana ya ce.
"Ni kai na ban san me yake damu na ba a cikin kwanakin nan Baby....lokuta da dama sai in dinga jin ƙirjina,kai na da zuciyata suna yi min nauyi.... Aabidah ina ji a jikina akwai wani abu da na rasa mai muhimmanci a rayuwata. Jikina yana bani akwai wani abu da nake so ko yake jirana ko kuma...i just don't know what is happening to me. Ki yi haƙuri da duk wani sauyi da kike gani a waje na,da yardar Allah komai zai dawo kamar yanda yake tun fil azal."
"In Allah Ya yarda babu abinda zai dawo kamar yanda yake tun fil azal...."
Aabidah ta yi suɓucewar baki ta faɗa da ƙarfi. Cikin sauri Aabid ya kalle ta yana mamakin furucinta. Da sauri ta wayance ta hau ƙirƙirar abubuwan da take ganin za su ɗauke masa hankali,sai dai