Showing 36001 words to 39000 words out of 48253 words
kada ki siya,domin idan kin siya kin yaɗa kin kashe min kasuwa. Don Allah mu so juna domin Allah kada mu dinga zalintar junanmu.*✨✍️
PAGE 17.
A na kiran sallar asr su Malam Bala suka isa gida. Da sauri Salma ta yar da jakarta a tsakiyar ɗakin Kande ta isa wajenta ta na dariyar farincikin ganinta. Sai dai yanayin da ta gani a tattare da mariƙiyar tata ne ya sanyaya mata jiki har bata san sanda ta zube a saman guiwowinta ba ta ɗora hannuwanta a saman na Kande ta ce.
"Gwaggona da gaske kewa ta kika yi sosai shi yasa baki da lafiya? Bamu fa jima da rabuwa ba Gwaggo,don Allah ki dena damuwa gani na dawo wajenki ba zan sake yin nisa da ke ba har abada."
Hawayen da Salma ta ga Kande na share wa ne ya sake rikita ta ta kifa kanta a saman cinyar Kande ta na kukan da bata san dalilin yinsa ba. Bayanta Kande ta ke shafawa a hankali ta na shan majina tare da lumshe idanuwanta da suka gaji da zubar da ruwan hawaye. Wani irin zafi take ji a cikin ranta. Murya na rawa ta ce.
"Ba ina kuka saboda kewar ki bane Salma. Ina kuka ne saboda bani da hanyar da zan aika wa Abdulwahab saƙon ya nesanta ki da garin Kura nisa na har abada. Ina kuka ne saboda fin ƙarfin da aka nuna mana da ni da ke marainiyar Allah. A yau na tabbatar da cewa wasu dangin suna suka tara kawai,domin da namu dangin aka haɗa kai aka nuna min iyakata,Kawunanki sun nuna min cewa ni ba kowa bace a wajensu face ƙanwar ubansu dan haka bani da hurumi a yanke hukunci a rayuwarki. Dangin mahaifinku kuwa sam basu san me ya faru ba har sai da mai afkuwa ta afku. Salma ina mai neman gafarar ki ki yafe min saboda gazawa da na yi a wajen rikon amanar ki har ki girma a aura miki kalar mijin da kike so."
Gaba ɗaya Gwaggo Kande ta gama rikita ƴar ƙaramar ƙwaƙwalwar Salma. Cikin rashin fahimtar inda maganganun Kande suka dosa Salma ta ce.
"Don Allah Gwaggo ki yi min bayani dalla-dalla yanda zan fahimci abinda kike son sanar da ni."
Zama Gwaggo Kande ta gyara ta zaunar da Salma a gefenta ta hau zayyano mata duk abinda yake faruwa,daga ƙarshe ta ce.
"Ɗazun nan Baffanninku suka bar nan ransu a matuƙar ɓace,domin a zaton su da sahhalewa ta aka ɗaura miki aure da Rabi'u. Sai da na yi musu bayani sosai,sannan na tabbatar musu da cewa Malam ya ce da amincewarsu da Kawunnanku aka ɗaura miki aure,sannan suka sassauta suka ce za su dawo idan Malam ya dawo daga ɗakko ki;dan ba za su amince da wannan ƙaddararran auren ba."
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Salma ta sauke a cikin kukan da take ta sharɓa tinda Gwaggo ta bayyana mata abinda ke faruwa. Kasa cewa komai ta yi sai ta miƙe ta ja jakarta zuwa ƙuryar ɗakin ta koma gefen katifarta dake ɗakin ta zauna ta na ci gaba da kukanta. Gwaggo Kande na ganin haka sai ta dinga bata baki ta na nuna mata cewar dole ne a warware wannan auren,dan haka kada ma ta sa wa kanta damuwa ballantana wani ciwon ya kama ta. Jiki babu ƙwari Salma ta fita tsakar gida ta na sharar hawaye ta ɗauki buta ta nufi bayi domin kama ruwa. Ta na shiga banɗakin ta rushe da wani sabon kukan mara sauti. Da ƙyar ta iya danne matsananciyar damuwar da ta rikito mata a lokacin da Gwaggo na bata labari mafi muni a rayuwarta. Sosai tausayin kanta ya lulluɓe ta sai ta rakuɓe a jikin gini tare da ƙanƙanme jikinta ta na ci gaba da kukanta. Ganin za ta makara sallar asr da bata yi bane ya sanya ta wanke fuskarta ta fito daga bayin ta ɗaura alwala ta wuce Hasiye da ke zabga guɗa ta na faɗin.
"Ka ga amarya a gidan Malam Rabi'u Mai Shinkafa,babban manomin da ya ke ji da noman rani da ta damina,dattijo mai kamar yaro ga kuɗi ga tashen gayu. Yo kukan me kike yi kuma? Yarinya ki saki ranki ki je ki ci arziƙi ki bar arziƙi a mazauninsa. Yo ke in banda ma aljana ta aure shi ai ba sa'an aurenki bane,da sai dai ki zamo sa'ar jikarsa ta biyu ko ta uku."
Kallon Hasiye Salma ta yi a karo na farko a rayuwarta da ta ji ba za ta iya ƙyale ta ba ba tare da ta bata amsa ba ta ce.
"Alhamdulillah mu a kowanne hali gode wa Allah muke yi,dan haka na tabbata godiyar Allah ce ta kai ni ga matakin auren mijin da ban zaɓa wa kaina ba,da izinin Allah ba zan wulaƙanta ba idan ma kin zuga an aura min tsoho saboda mugunta ne."
Salati Hasiye ta saki ta na tafa hannaye tare da kama haɓa ta ce.
"Inyeeee! Ehh lallai ne yarinya wuyanki ya isa yanka. To Kande ga shi nan a gabanki yarinyar da kike ta kukan ta yi ƙarama da auren tsoho ta tsaya tana zaro kalaman da ko wata babbar albarka. Za kuma ki san kin kira ni da muguwa yarinya,baki ga komai ba a rayuwarki."
Labule Salma ta ɗaga ta leƙa kanta ta ce.
"Sai dai na ga alkhairi da yardar Allah."
A zuciye Hasiye ta ɗauki plate ɗin tasar da ke kusa da ita ta jefi Salma da shi ta na zagin ta. Salma kuwa ɗaki ta koma ta na jin faɗan da Gwaggo Kande ke yi mata akan ta dena biye wa Hasiye kafin ta sake ƙulla mata wani sharrin. Hijabinta ta ɗauka ta sa ta tada sallah,ta na idarwa ta yi wurgi da hijabin ta kwanta tare da juya wa Gwaggo Kande baya ta na tunanin makomarta. Gwaggo Kande kuwa sai ta zuba wa bayan nata ido kamar mai karantar wani abun a tattare da yarinyar.
Su na nan zaune shiru Malam Bala ya shiga gidan hannunsa riƙe da wata leda sai nason maiƙo take yi. Kai tsaye ɗakin Gwaggo Kande ya shiga ya samu gefen gado ya zaune ya na washe baki ya ce.
"Ohh Kande ashe haka yaron nan Abdulwahabu ya bunƙasa ya tunbatsa a Kanon? Ai ni yau na ga abun arziƙi Kande,yaron nan haka ya sa aka kawo mana abinci da nama zuƙu-zuƙu a ciki. Da zan tafi ya jimƙo kuɗi a aljihunsa ya yi min hasafi,a ciki na yi na motar dawowa na kuma siyo miki wannan kilishin ki ɗan taɓa.
A sheƙe Kande ta kalli mijin nata da take mugun ganin baƙinsa a yanzu ta ce.
"Idan ka gama cinyewa sai ka ƙara gaba,in kuma a can ɗakinka ko na makwaɗaiciyar da ɗoraka a keken ɓera za ka ci ka tashi tun yanzu ka ƙara gaba bana buƙatar komai daga wajenka."
Cike da takaici Malam Bala ya kalli Kande ya miƙe tsaye ya ce.
"Ke fa na ga alama a ƴan kwanakin nan ba a abun arziƙi da ke,amma wannan bai dame ni ba,taimakon da na sa a gaba ba zan fasa ba,zan ci gaba da yi na ceto bawan Allah'n da bai taɓa aure ba a rayuwarsa."
Ledar hannunsa ya ɗauka ya nufi inda Salma ke kwance ta na binsa da kallo idanuwanta na zubar da hawaye. Baki ya washe ya ce mata.
"Ƴar salamemen Baba ga wannan ki motsa bakinki ko? Na kula a kwanakin nan kin saba da cin daɗi a gidan Yayanki."
Salma dai ido ta zuba masa bata motsa ba,kuma bata amsa ba. Ganin haka sai Malam Bala ya ajiye ledar zai fita. Har ya kama labule ya ɗaga ya tsaya ya kalli Gwaggo Kande ya ce.
"A shirya ta zuwa dare Rabi'u zai zo ya ga amaryarsa su ɗan tattauna ya ji ko akwai wani shagalin da take son ta gabatar,da yardar Allah gobe za a kai ta ɗakinta itama kamar yanda aka yi wa ƴar'uwarta Samira. Ai cewa ya yi ma kada mu damu da siyan kayan gado duk ya zuba mata ɗazu,shi dai matarsa kawai yake da buƙata ba komai ba."
Murmushin takaici ne ya ƙwacewa Kande ta ce.
"An zo wajen. Na tabbata siyawa Salma kayan ɗaki na daga cikin abinda ke damunka a kaf faɗin duniyar nan Malam. A al'dance idan mutum ya riƙe yarinya aka tashi aurenta shi ne zai yi mata kayan ɗaki,to kai gashi ba za ka iya cire kuɗi ka yi wa Salma kayan ɗaki ba. Da ka sani Malam da baka jefa rayuwar ta a cikin haɗari ba saboda kayan ɗaki. Ko ka manta har yanzu ɗan'uwanta na juya mata dukiyarta? Ka manta shi kanshi yana da arziƙin da ba zai bari ka sha wahala ba a duk lokacin da bikin Salma ya tashi? Malam...."
Cike da borin kunya Malam Bala ya ɗaga wa Kande hannu ya ce.
"Dakata Kande! Wai kina nufin ni Malam Bala Maji Daɗin Manoman garin Kura ni ne zan kasa yi wa Salma kayan ɗaki? To albishirinki,har kuɗin kayan gado na bada,da jin labarin zan kai na kujeru Rabi'un da kansa ya zo ya ce kada na yi ya riga ya yi. Yanzu gobe zan je na karɓi kuɗin gadona a yi wata hidimar da su. Wai me kika ɗauke ni ne Kande?"
"Marar riƙon amana da tausayin marainiya. Malam na tabbata da ka kai kuɗin gadon nan kamar yanda ka ce to da ka karɓo su yanzu,dan kai ba mutumin da yake wasa da dukiyarsa bace musamman idan ya ji banza ta faɗi."
Cike da borin kunya Malam Bala ya dinga faɗa,ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Sosai ran Kande ya ɓaci dan haka sai ta biye masa suka dinga musayar yawu har sai da Salma ta ƙwalla ƙara ta na kuka tana basu haƙuri. Cikin kuka ta durƙusa a gaban Kande da ke hawaye ta na masifa ta ce.
"Don Allah Gwaggo ki dena sa'insa da Baba domin ba halinki bane,tinda nake a gidan nan ban taɓa ji ya faɗa kin mayar masa ba. Idan har akai na ne kike faɗa da shi na yi alƙawarin yi wa Baba biyayya akan duk wanda ya aura min. Don Allah ku dena faɗa bana so,zuciyata zafi take yi min bana so."
Kuka sosai Salma take yi numfashinta na yankewa kamar mai cutar asma. Duk taurin rai irin na Malam Bala sai da jikinsa ya yi sanyi,da sauri ya ja labule ya bar ɗakin. A tsakar gida ya tarar da Hasiye ta na kaye-kayen kwanika,da dikkan alamu sana'ar tata ta laɓe ta yi musu,jin fitowarsa ne ya sa ta bar wajen ta hau kwashe kwanuka. Malam Bala na fita Kande ta rungume Salma a jikinta ta ce.
"In Sha Allahu ba za ki auri mutumin da ya isa yin jika da ke ba. Za ki girma ki auri saurayi kyakkyawa kamar yanda nake yi miki fata a koda yaushe. Baffanki Aƙilu zai je Kano gobe ya samu Yayanki ya sanar da shi duk abinda ke faruwa."
Girgiza kai Salma ta yi,dan jikinta na bata wannan auren fa ya gama ɗauruwa kenan sai ta je gidan Malam Rabi'u ko tana so ko bata so. Hana ta magana Kande ta yi ta ce ta je ta kwanta ta huta,dan ta ji jikinta ya ɗauki zafi,alamar zazzaɓi na sanɗarta.
Har su Kande suka yi sallar Isha'i basu yi wani shirin tarbar Malam Rabi'u ba. A ɓangaren Hasiye kuwa tini ta haɗa farau-farau a kwanon shanta sabo dal,sannan ta fito da tabarmarta sabuwa ta jingine ta na jiran zuwan baƙon nasu. Har ɗakin Kande ta shiga da sallama ta na washe baki kamar wawiya. Cike da mamaki Kande da Salma suka ɗaga kai suna kallon matar da ko ciwo Kande take yi bata shiga ta gaishe ta,ballantana ta yi mata sannu. Duk lokacin kuwa da ta ɗaga labulen ɗakin Kande to fa masifa da bala'i ne ya kai ta ba arziƙi ba.
Zama ta yi ta na dariya ta ce.
"Ah ah Ƴata salma har yanzu ki na nan kwance baki shirya ba bayan Babanku ya faɗa miki za ki yi baƙo anjima kaɗan?"
Ko motsi Salman bata yi ba ballantana ta tanka mata. Kande ce ta gaji da jin nacin da Hasiye take yi wa Salma ta ce.
"Kin ga kanwa uwar gami don Allah tashi ki bani waje,ki je can ki tarbi baƙon tinda dama ke kika haɗa duk wani tuggu da makircin da auren ya ƙullu. Ban san menene ribar ki ba na yin wannan zalunci,amma Allah Ya fiki,kuma a gobe ɗan'uwanta zai zo da jami'an tsaro dan a kama duk wani mai hannu a cikin wannan auren rashin ƴancin da kuka ƙulla."
Cikin Hasiye ne ya kaɗa har ƙarar ta ziyarci kunnuwansu Kande. Cike da tashin hankalin jin an ambaci hukuma a lamarin ta hau rantsuwa tana kumawa akan bata da hannu a haɗin auren Salma da Rabi'u. Kafaɗa Kande ta ɗaga ta ce.
"Jami'an tsaro ne kawai za su tabbatar da hakan idan sun zo."
Jiki na rawa Hasiye ta bar ɗakin ta wuce nata tana ta safa da marwa. Cike da tashin hankali take jiran Malam Bala ya dawo su san abinyi. Sai dai abun takaicin Malam Bala na zuwa Hasiye ta labarta masa duk abinda Kande ta ce,sai ya ja tsaki ya ce.
"Da yake an faɗa mata jami'an tsaron mahaukata ne ba sa bincike ko? Ai auren nan ya riga ya ɗauru kenan Hasiye,dan haka ki ma dena jin tsoron kowa da komai."
Kafin Hasiye ta buɗe baki ta ce wani abu,sallamar yaro ta karaɗe tsakar gidan. Mairo ce ta amsa tare da ce wa yaron.
"Kai Tsalha maye ka ishi mutane da sallama?"
Baki yaron ya murguɗa mata kafin ya ce.
"Malam Rabi'u ne ya ce na yi masa sallama da Babanku."
Da sauri Malam Bala ya fito ya na gyara rawaninsa ya ce.
"Ka ce masa ya shigo zauren gata nan fitowa."
Ɗakin Kande ya nufa ya ɗage labule ya ce.
"Salma ki na ina? Fito ga angonki ya iso."
Cikin sauri Kande ta ce.
"Malam na fa faɗa maka babu inda Salma za ta je."
Ganin za su fara faɗa sai salma ta bi ta bayan Malam ta fita sanye da hijabinta. Hasiye da ta ci burin shimfiɗawa Malam Rabi'u sabuwar tabarma sannan ta bashi farau-farau na jin fitar Salma ta lafe a ɗaki saboda tsoron jami'an tsaro. A zauren gidan Salma ta tarar da Malam Rabi'u ya sha sabuwar shaddar sa fara tas sai sheki take yi. Durƙusawa ta yi har ƙasa ta gaishe shi cikin ladabi da girmamawa. Murmushi Malam Rabi'u ya sakar mata wanda ya fitar da tsantsar kyawun fuskarsa. Sosai Malam Rabi'u yake da kyawun fasali,domin kuwa a zamanin samartakarsa ya na daga cikin kyawawan samarin garin Kura. Shi yasa ma jinkirin aurensa ya janyo raɗe-raɗin cewa aljana ce ta aure shi a lokacin da suke yawan shiga daji farauta da iyo.
Gaisuwarta Malam Rabi'u ya amsa sannan ya gyara tsayuwarsa ya na kallon yarinyar dake gabansa cike da ƙaunarta a ransa. Sai da ya yi gyaran murya sannan ya ce.
"Ina fatan magabatanki sun sanar da ke duk abinda ya kamata ki sani game da wannan auren? Don Allah ina so ki kwantar da hankalinki,dan ni da kika ganni mace bata gabana,surutu da zarge-zarge irin na mutane ne ya jawo ra'ayina har na ji na yarda na amince zan yi aure. Sai dai kuma na samu rashin sa'a a ranar da aka je ɗaura aure na a ranar matar da danginta suka ce sun fasa auren. Wannan dalilin ne ya sa Babanku tausaya min ya aura min ke. Ina fatan za ki zamo yarinya mai biyayya."
Kai kawai Salma ta ɗaga masa ta ci gaba da wasa da gefen hijabinta. Murmushi ya sake yi a karo na babu adadi,wanda hakan ya zamo ɗabi'arsa.
"To yanzu wanne irin taro ko shiri za ku yi ke da kwayenki?"
Shiru Salma ta yi bata ce komai ba. Kamar daga sama suka ga Mairo ta ci damara ta zo gaban Malam Rabi'u ta cake. Washe baki ta yi ta ce.
"Ai Salma ba za ta ce maka komai ba,mu dai kawayenta mu ne za mu yi party a ranar da za a kai ta da yamma."
Da jin haka sai Malam Rabi'u ya zira hannu a aljihu ya debo kudi ya ba wa Mairo ya ce.
"To gashi a sha party lafiya. Ni zan wuce sai da safe ko amarya?"
Kai Salma ta gyada masa ta juya za ta tafi. Kiranta ya yi sai ya ga Mairo ta ja ta tsaya. Hade fuska ya yi ya ce.
"Ki je ke na sallame ki ai ko?"
Washe baki ta yi tana sosa kai ta juya ta shige gida. Kai tsaye dakinsu ta shiga ta miƙawa Hasiye kudin da aka bata. Cikin sauri Hasiye ta karbe kudin har ta manta da abinda Kande ta fada mata na zuwan jami'an tsaro,sai da ta kirga su cas sannan ta zabga guda ta ce.
"Sufa dif za a kulla a yi fanke ba shikenan ba an sallami kowa?"
Dariya suka fashe da ita sannan suka ci gaba da tsara yanda komai zai kasance a washegarin.
A bangaren Salma kuwa;duk yanda Malam Rabi'u ya so ta karbi kudin da ya bata ki ta yi,daga karshe sai ta yi masa godiya ba tare da ta karbi komai daga gare shi ba ta shige cikin gida. Hakan da Salma ta yi sai ya sa Malam Rabi'u ganin mutuncinta,nan take ya tabbatar ba halinsu daya da iyayenta ba da ke ta nuna zalama da maitar abun hannunsa.
Washegari.......
MUGUWAR MACE.
NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️
PAGE 18.
Washegari da asuba har an shisshiga masallaci a wasu wuraren Salma ta tashi ta ɗauki wani abu a gefenta ta ƙudindine a rigarta,kallon Gwaggo Kande da bata rintsa ba ta yi tana saman sallaya ta na sallah,sai ta durƙusa inda suke ajiye butocinsu a bakin ƙofar ɗakin ta ɗauki butarta ta tafi banɗaki. Ta na shiga ta fito da hijabin Gwaggo Kande ƙato da ta ɓoyo a rigarta ta zumbula tare da tattare shi ya tsaya daidai tsawonta. Ƙaramar katangar banɗakin ta kama ta ɗale,ba tare da jinkiri ko tunanin komai ba ta dire ƙasa ta zura da gudu ta yi gaba abunta.
A can tsakar gida kuwa Hasiye ce zaune a saman bokitin ƙarfe sai zabga hamma take yi ta na jiran Salma ta fito daga banɗaki ta shiga. Jin shirun ya yi yawa ne ya sanya ta miƙe wa a hasale ta nufi bakin ƙofar shiga