Showing 48001 words to 48253 words out of 48253 words
miƙa hannunsa waje ya wanke ya ajiye butar. Zama ya yi ya fara cin tuwon yana santi Salma na yi masa dariya. Bayan ya kammala ya yi mata sallama tare da bata nera ɗari biyu ko da za ta sayi wani abun. Godiya ta yi masa ta karɓa ta ajiye a inda ta saba ajiye wa. Wani irin sauyi ya ke ji a jikinsa wanda bai taɓa jin irinsa ba a kaf rayuwarsa. A haka ya daure ya fita waje yana jiran Yayansa. Ko da Malam Jamilu ya riski ɗan'uwansa a zaure sai ya ce.
"Lafiya kake kuwa yau Rabi'u?"
Murmushi ya yi kawai ya gyaɗa kai alamar lafiya yake. Ba tare da sun sake yin magana ba suka hau samam babur ɗaya Malam Rabi'u na tuƙawa suka wuce kasuwa.
Tinda suka tafi kasuwa Mairo ta zo gidan suka ƙule da Samira a ɗaki,sun jima sosai a ciki kafin Samira ta fito cikin shirin fita. Ko sallama basu yi wa Salma ba dake ta shaƙar ɓaccin gajiya a zaune. Bayan awa biyu da fitar Samira Malam Rabi'u wanda ya kasa zama a kasuwa ya dawo gida. Hankalinsa a tashe ya nufi ɗakin Salma. A kishingiɗe ya ganta tana baccin gajiya. Bai ɓata lokaci ba ya tura ƙofar ɗakin ya saka sakata sannan ya nufi Salma gadan-gadan...........
*Wacece Aabida da Innaji?*
*Ta yaya Aabida ke shiga rayuwar Aabid har su zamo ma'aurata?*
*Wacece Dijahn Aabid?*
*A tsakanin Aabida,Innaji,Hasiye da Samira wacece asalin MUGUWAR MACE?*
*Ya ƙarshen waɗannan mutane zai kare?*
*A cikin MUGUWAR MACE PART 2 ne kawai za ku samu amsar tambayoyinku.*