Showing 15001 words to 18000 words out of 44178 words

Chapter 6 - UWAR AGOLA COMPLETE HAUSA NOVELS COMPLETE.txt

21 Apr 2026

240

ta linke ta je ta mayar mazauninaa ta fito daga ɗakin ta shiga ɗakinta ta garƙama sakata!.

MAMAN AFRAH
09025576222
[4/9, 6:17 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/DDmSp3AUB7gJnJQLnau59V?mode=gi_t

*UWAR AGOLA*

🅿️5️⃣



*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
*08032773332.*

*Sanyi flusher!*
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya Slsai ta dawo ko ta turo wasu*.
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*

*Tightening set na hade mace ta dawo Zamzam tamkar yar budurwa.*

*Tasirin magani Idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*

*Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga Amare, uwargida ,zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*08032773332*
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*


*UWAR AGOLA*


NA

MAMAN AFRAH

*Daga marubuciyar*
*Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.*
09025576222



🅿5⃣


*KULUWA*

Tana shiga ɗakin ta fara tunanin makomar ta a gidan Malam Nura, domin sai yanzu ne zuciyarta ta shiga zulumi da abin da ta aikata na ƙona masa wandon amarci!. Duk da ta san shigowarta ɗakin ba mafita ba ce amma dai ya zama wajibi ta tanadi wani abu da za ta tsira, tun kafin ya fito ya mata tijara.

A can cikin banɗaki kuwa Malam Nura sai da ya saɓa jikinsa sau takwas, yana wankan yana ta ƙiyasta irin kyan da zai yi yau, ya san lallai zai tashi kan mutanen ƙauyen Shabaru, duk da ya gama tsara nawa zai siyar da shaddar idan an kammala biji, don hatta kuɗin ɗinki sai ya fitar har da riba zai ɗora!.

Yana gama wanka ya mayar da riga ya fara shirin buɗe ƙofar banɗakin. Kuluwa tana ta tunanin abin da za ta aikata, wata dabara ce ta faɗo mata a rai, da sauri ta leƙo tsakar gidan daga jikin wata ƴar tula da take jikin ƙofar ɗakin, Haule ta hango tana duba ƙaramin mudubi a hannunta ta nufi ɗaki.

Da sauri ta zare sakatar ɗakin ta da ta saka, ta ɗan buɗe ƙofae kaɗan yadda ba za a ce rufewa ta yi ba, baki Kuluwa ta buɗe da ƙarfi ta shiga yin jiniya irin wacce ake yi wa sarki ko gwamna da sauransu. Malam Nura yana shirin fitowa sautin jiniya ya sauka a kunnuwansa, ɗif ya yi ya saurara don gabaɗaya ya rasa ta ce a zuciyarsa ya ce

'Ikon Allah, lallai wannan ɗaurin auren nawa zai tara mutane, to ko dai a dangin su Hadiza suna da alaƙa da sarauta ne, Allah ya taimakeni da na cire son kuɗi na yi ɗinkin na kirki, da kunyata zan yi, lallai yau akwai shagali' Ya faɗa baki washe yana buɗe ƙofar ya fito. Sai da ya fito tsakar gidan ya ji sautin jiniyar kamar ma ya ƙaru tamkar a cikin gidan ake yi.

Haule da ta shiga ɗaki ta jiyo ana

"Wooooo,waw,waw,waw,waw, waw" Dakatawa ta yi daba ajiye madubin ta saurara, amma sai ta ji ƙaran kamar daj da baki ake yi hakan ya sa ta ɗaura yara ne suke wasa.

Fitowarta ya sa ta ji ƙaran a ɗakin Kuluwa yake fitowa, mamaki al,ajabi ne suka mata dirar mikiya, hakan ya sa ta nufi ɗakin da ɗan sauri, domin sautin ya banbanta da muryar yara, tana leƙawa ta hangi Kuluwa tana ɗan zagaya ɗaki tana jiniya idanunta a rufe, gaban Haule ne ya faɗi domin tana ganin hakan ta san ba lafiya ba, salati ta kwasa lokacin Malam ya ƙaraso yana sauri domin lokaci ya ƙure.

Saurarawa ya yi ya ji ƙaran jiniyar daga ɗakin Kuluwar sannan ya tabbatar da baki ake yi. Haule cike da tashin hankali ta ce

"Innalillahi Malam akwai matsala zo ka ga abin da Kuluwa take yi" ,Wani kallo ya mata cikin halin ko in kula ya ce

"To daɗi ne ya mata yawa shi ya sa take jiniya wataƙila ta tuno da lokacin yarinta ne"

Cike da damuwa ta ce

"Ba lafiya ba fa, leƙa ka ga abin da take yi" Tsaki ya doka ya ce

"Kina jin dai yadda dandazon mutane suke jirana a waje da makaɗa, yau fa za a ɗaura aurena da Hadiza kuma a yanzu, ni har ina da wani lokaci ne bayan na ɗaurin aurena"

Yana faɗar hakan ya nufi ɗaki da sauri har yana neman faɗuwa, a kiɗime ta tura ƙofar ta shiga a take Kuluwa ta ƙara ƙaimi wajen jiniyar tun da duk tana jin abin da ake yi ta san yanzu zai je ya ga wandonsa amma tun da dai ita ta nuna babu lafiya a tare da ita babu mai tuhumar ta.

Ganin halin da take ciki Kuluwa ta fito da sauri tana faɗin

"Malam jikin na nata fa kamar tsamari yake, wallahi kamar fa aljannu ne... Yana dab da shiga ɗakin ya juyo tun kan ta dire maganar ta ya ce

"Haule ya kamata ki san wanda ya yi nisa ba ya jin kira, yanzu duk abin da za a faɗa ba ganewa zan yi ba wallahi, gabaɗaya hankalina ya karkata ga ɗaurin zuren nan, kuma ba kallon aljannu ba ko kukar bulukiya ce ta bayyana a jikin Kuluwa ba zan fasa tafiya ba" Yana kaiwa nan ya bankaɗa labulen ɗakinsa ya shige ya barta a tsaye da sauri ta juya zuwa ɗakin Kuluwar.

Yana shiga ya samu wayarsa tana ƙara alamar ana kiransa, kafin ya ɗauka ta katse nan ya hangi miss call rututu yana dubawa ya ga sunan Hudu da Hadiza su biyu da ransu suka tara masa wannan uban kiran. Yana shirin kiran ɗaya daga cikinsu kiran Hudu ya shigo ya ɗauka Hudu ya ce

"Haba Nura ya za a yi ka bar mutane tsaye ana jiranka, ka san kowa kai yake jira a tafi wajen ɗaurin auren nan, ga makaɗa ka bari suna ta faman kiɗa kuma ka san dai duk kiɗan nan da suke a kuɗi yake, daga wanka kamar wanda kake canja fata" Ya faɗa a faɗa ce.

Malam Nura ya sheƙe da dariya ya ce

"Wallahi ina can ina ta sheƙe wanka, gani nan fitowa" Maimakon ya bashi amsa ya ce

"Wai ihun jiniyar me nake jiyowa ne?" Hudub ya tambaya, Malam Nura ya doka tsaki ya ce..

"Kuluwa ce da neman jafa,i ta tada aljannu bata san ba ni ko bataliyar aljannun ne za su sauka a gidan nan sai na tafi ɗaurin auren nan" Shiru ya yi kafin ya ce wani abu Malam Nura ya kashe wayar domin ya ga ana ɓata masa lokaci, yana shirin ɗora wayar a kan katifar kiran Hadiza ya shigo,.ɗauka ya yi cike da rawar jiki ya ce

"Amarya bakya laifi, amarya mai magana suga... Kafin ya ƙarasa a gadarance ta ce

"Wai ina kuka tsaya ne gabaɗaya dangin amarya sun hallara babu dangin ango, ana jiranku, kamar za ku zo daga waji gari?"

Cike da farincikin jin muryarta ya ce

"Allah ja zamaninki ranki shi daɗe, gamu nan zuwa"

Shiru ta ɗan yj ta ce

"Gani nan na sha kwalliya da shaddata, ana gama ɗaurin aure nan za ka zo a mana hoto, ina son ganinmu da shadda iri ɗaya" Ya washe baki kamar ta masa busharar da kujerar makka ya ce

"Ai ina nan ki jirayi fitowata nima, dan ba bari zan yi ki fini kyau ba atoh" Ya faɗa cike da wasa, dariya sosai ta yi ta ce


"To sai kun ƙaraso" Ya amsa mata. Har zai kashe ta ce


"Ai na bango za a mana hoton na rataye a ɗakina" Ya yi karaf ya ce

"Ni guda huɗu xa a mini naki ke kaɗai guda uku na jera su, sai namu wanda za a mana tare in kafe a bango" Tana ƴar dariya ta ce


"Ai ina so in ganmu da kaya iri ɗaya"


Ya ce

"Yau kwa za ki gani" Har za su yi sallama ta ce

Wai ƙaran mene ne nake ji?" Da kamar ba zai faɗa mata ba don ya ga tana cinye mishi lokacin gashi ana jiransa, amma da yake so ya rufe masa ido ya ce

"Kuluwa ce zazzaɓin kishi ya kama ta, take jiniya kamar wata motar ƴan sanda" Baki ta taɓe ta ce

"Ta jirayi zuwana" Dariya ya yi suka yi sallama yana ta mamakin ta domin ya san ta da zafin kai bai sani ba ko don ranar ɗaurin auren ne shi ya sa take lallaɓa shi ko kuwa wani abu ne ita dai ta sani domin shi dai ya san ruwa ba ya tsami banza.

Turare ya ɗauka ya shafa a jikinsa, ya ɗakko mai zai shafa ya lakuto kenan wayarsa ta sake ƙara, ganin sunan Hadiza ya ɗauka cike da masifa ta ce


"Wallahi idan ka ƙara wasu daƙiƙai baka zo ba da wani za a ɗaura mini aure, ka san zan aikata ko?" Tana faɗa ƙit ta kashe wayar har lokacin yana iya jiyo jiniyar Kuluwa.

Wannan man na hannunsa da ya lakuto ko murzawa bai yi ba tsabar kiɗimewa, bai san ya lakuta man a tsakiyar hancinsa ba. Da sauri ya ɗaga rigar ya ɓalle maɓallin ya saka da sauri, don gabaɗaya Hadiza ta faɗar masa da gaba, domin a maganar ta babu wasa kuma ya san matuƙar aka ɗaura auren ba za ta biya shi kaf kuɗaɗensa ba.

Yana saka rigar ya ɗauki wandon amma saboda hankalinsa ba a jikinsa yake ba haka ya zura ƙafafunsa ya ji kowacce ta wuce ya ja mazugin ya ƙulle ba tare da ya lura da abin da yake faruwa da wandon nasa ba. Maɓallin rigar ya ɓalle ya ɗauki hula ya saka, turaren ma bai fesa a kayan ba ya ɗakko wayarsa ya fito a sukwane.

Kusan karo suka yi da Haule da ta taho sanar da shi cewa ko malami za a nemo ya yi wa Kuluwa ruƙiyya. Ganinsa yana sauri ta ce


"Malam na faɗa maka halin da Kuluwa take ciki" Malam Nura yana zare ido cike da masifa ya ce

"Haule ki ƙyaleni, don a halin da ake ciki yanzu ko gawa ce a ajiye sai dai a jira idan na dawo daga ɗaurin aure a yi jana,izar" Baki sake take kallonsa don ya bata mamaki ta rasa wane irin so yake yi wa wannan auren, ita dai duk aure-aurensa bai taɓa ɗora rai a kan aure kamar wannan ba.

Sai lokacin ma ta lura da wani lafcecen mai a saman hancinsa ta ce

"Malam ka ga fuskar ka kuwa mai ne lafke a wuri guda ko shafawa baka yi ba, kuma fuskar gata nan firi-firi babu mai" Bai jira cewarta ba ya saka hannu ɗaya ya murje fuskar, kasancewar man da ɗan dama sai ya yi wani uban maiƙo yana sheƙi kamar ya shafa man ƙuli.

Takalminsa ya saka ya fara tafiya, gaban Haule ne ya faɗi ganin ƙafafun Malam Nura a waje, duk da halin damuwar da take ciki na jinyar Kuluwa don gabaɗaya ma muryar Kuluwa ta shaƙe saboda jiniyar da take yi amma hakan bai hana dariya ƙwacewa Haule ba, don a tunaninta tsabar sauri ne ya sa Malam ya manta bai saka wandon shaddar ba.


Sai da ta ɗan dakatar da dariyarta marar sauti lokacin har ya kusa da zaure ta ɗaga murya ta ce

"Malam...Tun kan ta kai aya ya ɗago mata hannu ko juyowa bai yi ba, alamar ba zai samu damar tsayawa ba, cike da ɗaga murya ta ce


"Duk saurin ne ya sa ka manta baka saka wandon shaddar ba?" Jin tambayar ya yi kamar ta rainin hankali shi gabaɗaya hankalinsa yana kan ɗaurin auren da Hadiza ta ce za ta fasa da shi idan bai yi sauri ba, ga wayarsa da Hudu yake kira. Kamar ba zai duba ba tun da dai ya san ya saka wandonsa, amma sai ya kalli ƙafar abin mamaki babu alamar wandon, da sauri ya janye rigar daga gaba, ƙwabrinsa ya gani zangar -zangar a waje, gabansa ne ya faɗi, domin abin da ya fara zuwa ƙwaƙwalwarsa shi ne aljannu ne suke son raba tsakaninsa da Hadiza in ba haka ba shi da ya san ya saka wandon ya za a yi ya ga babu.

A kiɗime ya ɗage rigar har saman gwiwarsa amma sai fatar jikinsa yake gani bai ga shaddar ba. Haule tana dariya ta ce

"Ka koma ka sako" Shi dai har lokacin yana cikin ruɗani, jin furucin ta ya yi saurin ɗage rigar gabaɗaya, gajeran wandonsa na shadda iya cinya ya bayyana ƙasan da alamar ƙonewa. Idanunsa ya zazzaro tamkar za su faɗo ƙasa, ya lailayo wani uban ashar mai maiƙo ya fara narkawa yana faɗin


"Uban waye ya ƙona wandon shaddar nan?" Kuluwa wacce muryarta ta fara dishewa saboda jiniya, ta jiyo sautin maganarsa, gabanta ne ya bada sautin rass domin ta san mai rabata da Malam Nura yau sai Allah matsawar ya gano gaskiya.


Haule salati ta hau yi tana kallon yadda aka yi wa wandon ƙunar wulakanci kamar ma ƙafa ɗaya ta fi ɗaya. Ba komai ne ya zo ƙwaƙwalwarsa ba sai tunowa da ya yi cewar kayan siyar da su zai yi idan aka gama sabgar biki, sannan ya tuno wayar da suka yi ɗazu da Hadiza a kan za a musu hoto a tare da shaddar nan iri ɗaya, hankalinsa bai kai ƙololuwar tashi ba, sai da ya tuna cewar ana can wajen ɗaurin aure ana jiransa, kuma kaf kayansa banu wani mai abin arziƙin da zai iya shiga taro, taron ma na ɗaurin aurensa!.


Tunowa da magaar Hadiza na cewar idan ya ƙara daƙiƙu bai je ba za a ɗaura mata aure da wani, shi ne lamarin da ya saka shi cikin firgici. Haule da take kallonsa cike da mamaki ta rasa ma wane tunani za ta yi. Kamar wanda aka cakawa mashi ko kibiya hular ya wurgar wayarsa ma a wajen ya sake ta, Haule ta fara tunanin ko dai aljannu ne suka sauka a gidan ko kuma jifa ne aka yi wa Kuluwa da Malam ɗin, domin yanayinsa ya nuna ba a hayyacinsa yake ba, hankalin ta a tashe ta fara masa kallon ko dai hauka ya fara.

Malam Nura kuwa, zuciyarsa ta gama faɗa masa wanda ya masa wannan aika-aikan, sannan a take ya gama gane dalilin jiniyar Kuluwa kenan.


Haule sai ganin Malam ta yi ya falfala da gudu takalman nasa kowanne ya kama gabansa, saboda yana fara gudu ya cire su, Kuluwa kuwa gabanta yana faɗuwa tana jin tamkar ta fito da gudu ta bar gidan, amma tunowa da ta yi idan ta tafi za a kawo amarya bata nan sai ta fasa, don daman ƙannenta ma sun ce za su zo yau ɗin.

Jin ƙaran gudun Malam ta yi saurin sauya akalar jiniyar tata zuwa carar zakara. Haule da take tsaye tana jin kamar na fita waje neman taimako, amma tana tsoron tijarar Malam jin Kuluwa ta daina jiniya ta tsiri carar zakara sai lamarin ya sake cunkushe mata.


Ganin ya je tsakiyar gidan ya tsaya yan waige-waige, idanunsa suka sauka a inda aka ƙona wandon, yana dubawa ya ga sawun takalmin Kuluwa zarginsa ya zama gaskiya daman ya san babu mai wannan ɗanyen aikin sai ita, gaban Haule ya shiga faɗuwa, domin gabaɗaya gumi ya wake masa fuska ga sheƙin man fuskarsa ga tsantsar tashin hankali da ya bayyana, wata kaza da ta taho da ƴaƴanta za ta shiga ɗakin ta, ganin zai bige mata ƴaƴa ta kai masa cako, haushi ya sa ya shura ta da ƙafarsa, da gudu ta yi hanyar ɗakinta.

Dubawa yake mai zai yi wa Kuluwa ya huce duk da ya san ko mai ya mata ba zai huce ba amma dai yana so ya mata abin da za ta san ta taɓo gidan rina!.


Ɗakinsa ya juya da gudu sai gashi ya fito da adda, kiran sunansa Haule ta shiga yi tana tsoron tunkararsa don gani take kamar ya haukace, wajen murhu ya nufa inda Haule ta hura wuta, ya ɗakko wani ƙaton faskaran icce mai wuta a jiki, kafin ta ƙifta ido ya yi wa ɗakin Kuluwa tsinke, yana kwaɗa mata gigitaccen kira.

Kuluwa ambaton sunan ta kaɗai ya isa ya sanar da ita ya gano tsiyar da ta shuka masa, bata san lokacin da carar zakaran da take ya tsaya cak ba, a sukwane ta nufi ƙofar ta saka sakata.


Mutuwar tsaye Haule ta yi jin Kuluwa tana faɗin

"Haule kira jama,a a waje, ki ce gida babu lafiya" Ta faɗa don ita a tunaninta madoki ya ɗakko zai mata dukan mutuwa bata ma san abin da ya ɗakko ba. Haule ta shiga ruɗu lallai wanda ya ƙona icce shi ya san yadda toka take tsada, in ba haka ba ashe dai duk abin da Kuluwa take ba aljannu ba ne iya shege ne kura a rumbu!.

Da ƙafa ya buga ƙofar ta yi wani ƙara, Kuluwa ta koma ta manne da jikin drower ta tana ciccira ido, ya dawo ta windo ya leƙa idanunsa kamar garwashi ya ce


"Wallahi wallahi karambanin akuya ya sa ta leƙe ɗakin kura, amma za ki gane shayi ruwa ne, ni kika ƙonawa shaddar kusan dubu talatin?"


Kasancewar bata hango abin da yake hannunsa sai fuskarsa, ta ce

"Ina sane wai karuwa ta taka matar aure! Ai a ganina ba raini ba ne don an ce wa karuwa hayo gado don abin da ta saba ne kuma sana,arta...

Addae da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login