Showing 33001 words to 36000 words out of 44178 words
haka bata ganshi ba. Hudun yana mata magana amma ta kauda kai gefe sai su Bintu ne suka amsa sallamar, yana dariya ya ce
"Ni da ba ni na kai zomon ba rataya aka bani" Cike da masifa ta ce
"Malam Hudu to na ga dai aure ne an ɗaura, to yanzun mai zan muku da kuka zo kuka tsaya mini, baka ga ina tare da mutane ba? Idan ma batun jere kuka zo ku koma ku faɗawa Malam Nuran ni Hadiza gayu na ce tariya ba yau ba, sai nan da sati biyu zan tare!!!" Malam Nura da yake bayan ta tsaye bai san lokacin da ya gyara tsayuwar nigogin da ya yi ba, gabansa yana faɗuwa ya haɗiye wani yawu muƙut, ba komai ne ya sanya shi wannan fargabar ba sai tunawa da ya yi da cewar ya shanye maganinsa da zai fito wanda aka ce kuma sai ranar da amarya za ta tare zai sha, daɗin daɗawa ma maganin kaf cikin magungunan Hudu ya ce masa ya fi kowanne tsada ya fi kowanne aiki.
Su Bintu da suke kusa da ita su biyu ɗaya tana bata baki, da yake sauran matan da suke wajen ganin zuwan mazan sai suka ɗan basu waje, amma Bintu da yake tafiyarsu ɗaya daman kamar yadda hausawa suke cewa sai hali ya zo ɗaya ake abota, Bintu ta ce
"Ina bayan ki ƙawata, ai kina da ƴancin ki yi yadda kike so, auren zawarci ne fa ba wai na budurci ba, kin ga kenan ko wata biyu kika ɗauka ba sati biyu ba kin da fiye da wannan damar...
Kafin wani ya sake furta komai Malam Nura ya yi taku ɗaya biyu sai gashi a gaban amarya, yana zuwa ya ja ya tsaya hannuwan nan biyu a aljihu yana kashe ta da wani murmushi, don ba zai tsaya a masa sakiyar da ba ruwa ba, yana kallon ruwa kwaɗo ya masa ƙafa gwara dai ya yi duk yadda zai yi ganin bai yi asarar wannan ranar ba, bai yi asarar kuɗin maganinsa da ya bankamawa cikinsa ɗazu ba.
Tsayuwarsa ta dakatar da su Hadiza da maganar ka ce na ce idanu ta zaro baki sake ita kanta ganin irin kan da ya mata bata san bakin ta ya furta
"Angina malam Nura?" Kansa ne ya ji ya masa gingirim daman kuma ya san a rina wai an saci zanen mahaukaciya, ya san in har ta ga wankan nan nasa ƙarya take ta ce bai yi mata kyau ba, shi ya san wanka iya wanka.
Yana murmushi ya ce
"Na,am amaryata Hadiza" Daɗi ne ya baibaye mata zuciya musamman da ya zo a wannan daidai gaɓar da wurin yake a cike, kowa dai zai ganshi ya san ba ƙarya ta yi ba.
Tana kallonsa ta ce
"Wannan kyau haka" Ya gyara tsayuwa ya ce
"Ai daman na faɗa miki zan baki mamaki"
Bakin ta har kunne ta ce
"Ai kuwa ka bani ina sonka Malam Nura"
Allah ne kaɗai ya san daɗin da Malam Nura ya ji musamman da ya ga ta mayar masa lulluɓin da ta cire masa ɗazu a gaban ƙawayenta da abokansa, amma yanzu gashi ta sake rufa masa bargon mutunci.
Da kanta ta matsa kusa da shi suka jeru, a take abokansa suke musu kirarin sun dace, ƙawayen nesa sukaa matso kusa ana ta sakin guda Malam Nura a zuciyarsa ya ce
'Ai Kuluwa ba ƙaramin cutata kika yi da kika ƙona wandon nan ba, Allah ma ya taimakaeni an mini dibara da yanzu kin jaza mini tsiya, to amarya tana ba za ta tare yau ba ai ɗan jijjiɓin bala,i kenan"
Hadiza ta fito da wayarta daga jaka ta shiga kiran mai hoto yana ɗauka Malam Nura ya ji tana faɗin
"Ka zo yanzu ango da abokansa sun ƙaraso za ka mana hoto" Malam Nura ya ciro hannayensa daga aljuhu ya shiga gyara hularsa, suka haɗa ido da Hudu da yake ta faman doka murmushi ganin sun samu karɓuwa.
Daga ɗaya ɓangaren mai hoto ya ce
"Ba kin ce shikenan ba?"
Kamar ta falla masa mari haka ta ji da ya yi wannan furucin ta ce
"Na faɗa maka ka zo yanzu" Da to ya amsa mata, nan ta kashe wayar tana aikawa Malam Nura kallon soyayya shi kuma gogan sai wani kashe mata ido yake ransa fari ƙal.
Shi Malam Nura yanzu maganar hoto ce a gabansa, shi dai a musu hoton nan da amarya wanda za su kafe a ɗakunan su. Yanzu babu batun ya yi maganar tariya a nasa ganin tun da daman fushin rashin saka kaya mai kyau ne ya janyi cecw ku ce ɗin da ta ce ba za ta tare ba yanzu kuwa ai babu wanna batun.
Mai hoto aka sauke a mashin nan ya shiga aikin sa babu ƙaƙɗautawa don su Hudu gefe suka koma suka zubawa sarautar Allah ido, mai hoto yana ta basu style ɗin yadda za su yi, yana ta walla musu hoto, ya musu ya fi kala goma sha biyar, nan suka nuna masa wanda za a musu na bango.
Malam Nura sai ya tsinkayi muryar amarya tana faɗin a kirawo Zainaba da Shafi,i nan fa aka kira su, amma Zainaba dakyar ta zo tana ta kumbure-kumbure don ta tsani Malam Nura babanta take tayawa kishi, shi ma Malam Nura a nasa ɓangaren haka ne, burinsa kawai ya ɗauke Hadizarsa a bar waɗannan ƴaƴan musamman ma Zainaba. Ko da aka jeru za a musu hoton da yaran kowa yana ta washe baki amma Zainaba ta cukule fuska ban da harara da take aika musu babu abin da take, sai za a ɗauki hoton ango da amarya suna kallon juna cike da soyayya shi kuma Shafi,i shi ma dariyarsa yake amma Zainaba sai ta shiga banka musu harara kamar idanunta za su faɗo!.
A hakan ne cike da rashin sa,a Malam Nura ya ji tazugen wandon jikinsa ya cire daga cikin wandon. A take ya ji tsantsar wandon ta masa yawa, daman ya san ya yi kaɗan tazugen dakyar ma ya ɗauru saboda ƙanƙantarsa, shi kuma garin sauri bai tsaya ya canza wani ba, idanu ya ɗan zaro a ɓoye yana ɗan yatsina fuska kamar mai jin kashi a zuciyarsa ya ce
"Innahu min sulaimana wa innahu bismillahir rahmanir rahima, li,ilafi ƙuraish, ilafihim rihlatash shita,i wassaif fal,ya,abudu rabba hazal bait allazi aɗ, amahum min ju,in wa aamanahum min kauf" Ya faɗa wani gumi yana karyo masa. Da sauri ya saka hannunsa a cikin aljihun rigarsa, ya riƙe saitin ƙugun nasa ta yadda wandon ba zai zame ya faɗi ba, tun da yanzu babu inda yake a riƙe sai hannunsa da ya riƙe shi.
A zuciyarsa ya ce
'Allah ka taimakeni kar wandon nan ya faɗi, kar ya tsinkani a idon jama,a, ya Allah yadda aka taru ake kallonmu ni da amaryata muna birge mutane Allah kar ka saka wandon nan ya rusa farincikin nanu, Allah kar ka ba wandon nan ikon ya kunyatani, yadda kowa yake kallona kamar wata ɗan daren goma sha uku ka sa abun nan ya ɗore' Ya faɗa yana sake bada ƙaimi wajen damƙe tsantsar wandon.
Mai hoto cike da bada umarni ya ce
",Amarya kama hannun angon" Amarya tana murmushi ta miƙa hannu ta riƙo hannun Malam Nura da yake cikin aljihu yana riƙe da wandon, ta riƙe tana faɗin
"Cire hannun mana ya ka saka shi a aljihu?" Malam Nura idanu ya shiga rabawa a zuciyarsa yana faɗin
'Shikenan asirina a tonu, ya zan yi idan wandon nan ya zame Hadiza ta ga haɗe yake da tsohon wandona na yadi aka yi faci' A fili ya ce
"Ai na fi ganin kyauna idan hannuna yana cikin aljihu" Ya faɗa cike da ganin vata kunyata shi ba. Bata kawo komai a ranta ba ta riƙe hannun ana ta musu hoto shi kuma ya riƙe wajen gagam, don Hudu yana lura da shi ya ga hatta wajen da ya riƙe ƙafar wandon har tattarewa ta yi, shi kaɗai yake dariya a ransa duk da bai san mene ne ba amma banya raba ɗayan biyu matsala ce domin ya lura gabaɗaya abokin nasa ya fita hayyacinsa ba kamar lokacin da ake hoton ba duk ba a nutse yake ba.
Dabara ce ta faɗo masa yana cikin tunanin yadda zai yi ne wayarsa ta shiga ƙara, ya fito da ita ko gama ganin waye bai yi ba ya raɗawa amarya cewar Goggo Ramma ce take kiransa, haka ya ɗan ja gefe yana wayar ƙarya, da ta faki ido sai ya sha wata ƴar kwanar lungu, a kan wani dogon tsumma ya yi wa idanunsa masauki, da sauri bai yi ƙasa a gwiwa ba ya ɗauka ya ɗage rigar ya zare mazugin cikin, ya gyara wandon ya saka tsumman da ya tsinta ya ɗaurew wandon daga sama wato daga ƙugunsa wandon ya tsaya ya saki rigar yana sakin wani gauron numfashi. Fitowa ya yi daga lungun ya dawo yana ta jin daɗin ya tsira da mutuncinsa, amma dai alla-alla yake ya bar wajen tun kafin a yi abin da zai kunyata.
Haka dai aka sha hoto sai wajen ƙarfe shida saura ango za su tafi, abokan sun ɗan yi gaba sun tsaya shi zai yi sallama da amarya, yana tsaye yana washe baki ya ce
"To mu za mu tafi"
Amarya ta ce
"Tohm kuɗin karin nawa fa" Yawun bakinsa ne ya ƙafe ya ce
"Wane kuɗin kari kuma, ke da za ki kwana a gidana ai akwai su Haule a gida sai abin sa ranki yake so za a girka da safe" Ranta ne ya ɓaci ta ce
"Ai na faɗa maka ba yau zan tare ba ko?" Idanu Malam Nura ya zaro a zuciyarsa ya ce
'Ashe kuwa wanda ya mutu zai falko, duk wannan wankan da na yi don kin raina mini hankali, to ai kuwa ba zai taɓa yiwuwa ba mai kaza ya tashi da fifike' A fili kuma ya ce
"Amma dai wasa kike ko Hadiza?"
Farrrr ta yi da ido sai da bakin idon ya ɓace ɓat sai farin sannan ta dawo da idanunta daidai ya ce
"Wai wasa an faɗa maka a komai ake wasa ne, wallahi da gaske ba zan rare yau ba, kaima da wata magana yanzu fa batun ƙarfe shida na yamma ake yi ko jere ba a je an yi ba, kuma a yaushe zan tare?"
Malam Nura ya kalle ta ya ce
"To mene ne abin wahala a wani jere, yanzu wasu ƴanmatan ma sai da isha,i ake tafiya da kayan a jera ai ba wahala ba ne gado ne fa kawai za a ajiye yanzu da gabaɗaya ma jeren maza ne suke yi"
Hadiza ta ce
"To bari ka ji ni wallahi kayana suna wajen kafinta da na saya daman sai za a jera za a ɗauke su daga can a wuce gidanka da su, ka ga a yanzu kuwa lokaci ya ƙure"
Malam ya ce
"Ni yanzu daga nan sai na je wajen kafinta a ɗoro kayan a baro wallahi ina iya jerasu duka ke kuma in aka yi isha,i sai a kai ki"
Baki ta taɓe ta ɓata rai ta ce
"Kamar wata amaryar kunkuru, to wallahi ba zai yiwu ba so kake ake gulmata ana faɗin ango ne ya mini jere, yadda kowace mace ake zuwa a jera mata kaya haka za a mini, kuma in tafi a tsanake, duk ka hana kanka sakat kamar dai baka da mata a gida, ni wanna auren jin sa nake kamar auren farko don haka a tsanake zan tafi"
Malam ya tari numfashin ta da faɗin
"To ko amaryar buzuzu ce ba dole a yi ɗokin ta ba, kuma da kike batun matana ai na san da zaman su, ke fa na ce miki wata guda za ki yi kina amarci, babu wacce za ta karɓi bakin kwananki" Fuska ta yatsina ta ce
"Wllahi ko shekara za ka bani ba zan tare yau ba!" Su Hudu ne suka matso ganin abin yana neman wuce makaɗi da rawa, Bintu ma suka matso na aka shiga basu baki, a ƙarshe dai an shawo kan amarya ta ce za ta tare amma sai gobe, nan su Hudu suka shiga lallashin Malam a kan ya haƙura yau da goben ai duk ɗaya ne!. Ba dan ransa ya so ba sai don ba yadda zai yi haka ya haƙura, cikin ransa tsanar Kuluwa ce fal don ya san ita ta haddasa komai, da tun farko ya zo da shaddar a jikinsa daga wajen ɗaurin aure da tuni an jera kayan amarya ta tare a yau, amma da yake ta yi fushi tun da aka ɗaura auren shi ya sa ko shirin tarewa yau bata yi ba.
Haka ya bata 5k don ta ce yau kuɗin ba iya na kari zai bata ba har da na abincin dare!.
Ko da suka taho a hanya suna ta zolayarsa amma shi kaɗai ya san halin da yake ciki, banza ya musu kawai so yake ya samu abin da zai yi wa Kuluwa sanadiyyar daren amarcin da ta masa yau!.
A can gida kuwa da magriba Haule ta fito da shirin fita tana faɗaw Kuluwa za ta je gidansu duba babanta, har tana cewa Kuluwar ko ita ma za ta je su fita tare. Buɗae bakin Kuluwa ta ce
"Ni in fita yanzu haba Haule ai ban ga ta zama ba an saci ɗan ɓarawo, in ban da ma ke ina za ki samu damar fita ana jimawa fa ƴan kawo amarya za su yi wa gidan nan kutse" Baki ta taɓe ta ce
"To wa ya aikeni bare ya ga na daɗe, ai dubiyar dai ta fiye mini, amarya kuma da ba a kaina za a ɗora ta ba ina ni ina su, kafin dai su kawo ta zan dawo don ba zama zan yi ba, kar a zo a ce kishi ne ya sa na ƙi zama a gidan basu san ni auren Malam Nura ko a gefen takalmina ba"
Kuluwa ta ce
"Ai ni ina nan na kasa na tsare, na je na yi wa baban naki sannu idan ƙura ta lafa don yanzu ba zan iya nisa da gidan nan a mini sakiya da ba ruwa" Da mamaki Haule take kallon ta ta ce
"Ban gane ba, wace ƙura kuma sai ka ce wanda guguwa ta taso, wai ke Kuluwa ba za ki sauƙaƙawa kanki kishin wanda bai damu da ke ba, yanzu ban da Allah ya takaita da ba tuni ya lahanta ki va" Baki ta taɓe ta ce
"Na ga alama idan ina biya ki hawan ruwa sai ya kama ni, ai ni da wuya ta karni ai gwara daɗi ya karni, ai abin alfahri ne ma a ce miji ya nakastaka a kan kishin sa soyayya kenan, kuma ni ina nan ko sama da ƙasa za ta haɗe yau kwanane idan amarya ta isa ta yi kwanan turaka yau Allah tsine mini don wallahi ko a ni ko a ita domin sai ta jira na famshe gabaɗaya kwanankin da Malam ya haramta mini shiga turaka, sannan zan bata dama ta yi kwana ukun da kowacce bazawara take yi" Baki sake Haule take kallon Kuluwa tana mamakin ƙarfin hali irin nata, ta san yau ko gawa za ta yi Malam ba zai bari ta kwana a turaka ba!. In ban da ma rashin zuciya mutumin da ya haramta mata shiga turaka kusan kwana shida yau, shi ne zai bari ta shigar masa turaka a ranar da yake jin sa zai ɓarji amarci da amaryar da ya gama yi wa tanadi a cewarsa.
Fatan samun sa,a ta yi wa Kuluwar ta ja su Kabiru suka tafi. Suna fita Kuluwa ta rufe nata ɗakin ta tafi gidan mai maganin mata magunguna ta lodo ta biya kuɗin ta dawo gida. Tana zuwa ta kai ruwa banɗaki ta salsala wankanta, ɗaki ta dawo ta shafa wani turare mai suna MU JONE turare ne na jan hankalin mai gida da ta siyo an faɗa mata yana da kyau kuma matukar miji ya shaƙi ƙamshin shikenan sai yadda hali ya yi shiga motar mahaukaci!. Wando da riga ta saka domin mai maganin ta ce ta saka kaya na jan hankali, dan haka wani wandon Malam Nura da yake ajiye a ɗakin ta ta ɗauka ta saka sannan ta saka rigarta tshirt kasancewar bata da wanduna.Magani mai suna maƙale mata ta ɗauka ta zuba a nono ta dama ta shanye ta shafa humra.
Wani kwalli idonka idona shi ma duk yana cikin kayan da ta siyo ta ɗauka ta rambaɗa a idanunta. Kanta da yake a tsefe ta shiga tajewa.
A can kuwa su Malam Nura masallacin magriba suka wuce, bayan an yi sallah ya musu sallama duk ransa babu daɗi domin har ya hango zai kwashi amarci amma gashi an samu akasin lissafi. Hudu cikinsa har ciwo ya yi wajen tsokanar Malam Nura yana faɗin
"Wai da gaske abokina duka ka shanye maganin nan kaɗan ka rage, gashi kuma mai maganin ya ce a ranar maganin yake barin amfani, to Allah ya sa ma kai ba gwauro ba ne, ga Haule nan ga kuma amarya Kuluwa sai wacce ka zaɓa" Ko amsa bai bashi ba saboda takaici.
Shago ya wuce yana zuwa ya ce mai shagon ya bashi sufagilu guda huɗu, haka aka ɗakko masa ya bashi kuɗin ya saka a aljihu ya nufi gida.
Kuluwa da ta gama shiryawa tsaf sai kuma ta ce
"Ni da zan je turaka yau, gashi na gama haɗa bom wato na sha kayan gyara, gwara dai in shiga banɗaki in tsugunna don na ji taushen da ta sha ya saka mini ciki" Ta faɗa tana ɗaukan buta ta shige banɗaki ta rufo, a ranta tana ta saƙa yadda idonka idona kwallin da ta saka zai ruɗi Malam, da MU JONE da sauran abubuwan da ta yi amfani zai sanya idan har ta je turaka amarya za ta ƙufula ta ce an wulaƙantata a ranar amarci, in ya so da safe a yi badaƙala a sake ta shikenan ƙurunƙus.
Malam Nura a hanya suka haɗu da Haule da za ta je