Showing 3001 words to 6000 words out of 44178 words

Chapter 2 - UWAR AGOLA COMPLETE HAUSA NOVELS COMPLETE.txt

21 Apr 2026

241

ta ce


"Ban gani ba" Ta faɗa kamar za ta yi kuka, murmushi Hadizar ta yi ta ce


"Ba komai kin san shi babu ruwanshi" Wani abu da ya tsaye masa ya haɗiye muduk ya ƙirƙiri dariyar yake ya ce


"To waye bai san yaro ba, bare ma bata gani ba" Zainaba ta faki idon mahaifiyarta ta wurga masa wata muguwar harara tare da murguɗa masa baki ta sunkuya ta ce


"Innata ashe za ki iya cin daɗi ban da mu?" Hadiza wacce take baƙincikin su ci naman tare da Malam Nura ta ce

"Haba Zainaba daman za mu rage muku ke da ɗan uwanki, amma tun da kin zo ɗauki kawai mu sai mu ci girma" Baki sake Malam Nura yake ganin ikon Allah, domin kaf Zainaba ta naɗe takardar ta haɗa da lemukan ta kama hanyar shiga gidan, Hadiza ta ɗan ɗaga murya ta ce

"Kar fa ki hana Shafi'i" Da to ta amsa mata ta shige gidan, Malam Nura da ƙwallar baƙinciki ta kawo a idanunsa da sauri ya yi hanzarin mayar da ita yana washe bakin ƙarfin hali ba ya so ta gane halin da yake ciki, ga yunwa da take ƙwaƙular hanjinsa.
A zuciyarsa yana faɗin


'Wayyo dubu huɗu ta da ɗari biyar'


Tana ƙara turo ɗaurin ɗankwalinta gaban goshi ta ce


"Tun da an yanka kaji ai sai ka ci idan ka koma gidan ko masoyi" Kamar zai yi kuka ya danne ya ce

"Ai kuwa naman kaza yana can don kwanon samira aka cika mini, idan na koma na ci" Ya faɗa yana sauke idanunsa a kan hannunsa ta cikin farin wata sai sheƙin man jikin naman da kuma ɗan burbuɗin ƙuli-ƙulin da ya maƙale a hannun.


Idanunsa ya sauke a kan yankan ɗayan da ya faɗi daga hannunsa wanda Zainaba ta bige masa, kuma shi dai iya saninsa ya san da gangan ta yi don ba sa ga miciji da ita, ido ya ƙurawa yankan naman ya ga ashe har ƙafa ta saka ta murtsuke yadda ba zai amfanu ba, da a nufinsa idan sun yi sallama da Hadiza ta shige gida ya dawo ya ɗauka a ƙalla dai ya rage asara!. Muryar ta ce ta katse masa tunani da faɗin


"Bari na shiga gidan ina son shiga banɗaki" Wani irin washe baki ya yi ta tashi shi ma tashin ya yi ta ɗauki kujerar ta, sallama suka yi ta tsaya masa ƙememe me ta ce


"Au baka bani kuɗin karin safe ba, ko goben da tuwo kake so na karya" Yana kallon yadda ta masa wani farfari da idanun ya saka hannu a aljihu, dubu biyu ya ɗakko ya bata ko godiya babu ta karɓe, juyawa ta yi ta fara takun nan nata da yake so ya saki baki kamar dolo yana kallon ta tana dab da shigewa ta jiyo tare da masa bye-bye, shi ma hannun ya ɗaga mata ta shige ya juya ya fara tafiya ransa a matuƙar ɓace, don ko hirar kirki basu yi ba ga asarar nama da lemon kwalba.

Tun da ya kama hanyar gida ya tsinewa Zainaba ya fi cikin carbi, ya ƙosa asabar ta yi a ɗaura auren Hadiza ta koma gidansa ko ya huta da ganin wannan fitsararriyar yarinyar. Kayan jikinsa ya duba ko zai ga datti a jiki domin so yake ya je ya cire ya haɗa da na jiya ya mayar inda ya karɓo, saboda tsabar maƙo ba ya iya ɗinka sutura ta kirki amma yanzu da yake neman auren Hadiza shi ne yake arowa yana sakawa dan gudun kar a raina shi.


Da sallama ya shiga gidan babu kowa a tsakar gidan sai Kuluwa, ita Haule tana ɗaki ita da yara tana musu tatsuniya, Kuluwa jin muryarsa sai ta ji tamkar ya caka mata mashi a maƙoshi, ta yi banza da shi ta buɗe randa ta ɗakko ruwa a kofi, tahowa ta yi lokacin ya zo daidai saitin ta zai tafi ɗakinsa, buguzum-buguzum ta zo wucewa kaɗan ya rage ta bangaje shi. Tana shiga ɗaki ya tsaya gyaran murya ya yi a saita bakinsa yadda amon muryar zai isa ga kunnen ta ya ce

"Kai gaskiya mace ƴar duma-duma mai diri ta yi, ko tafiya take sai ka ga ɗagwas-ɗagwas, ,gwanin sha,awa na yarda mata suna suka tara, amma wata macen idan ta taho yadda aka san motar tantan za ta wuce... Kuluwa wacce tun da ya fara magana ta tsaya tana huci kamar zakanya domin a take zuciyarta ta raya mata cewa da ita yake wato amaryarsa wacce ya kira da suna mai jiran gado ita ce ta iya tafiya, tun da dai ta san duk wanda ya yi zagi a kasuwa ya san da wanda yake, rai a ɓace ta dangwarar da kofin hannunta wanda ta ɗauki ruwa, ta taho a sukwane don zuwa a yi wacce za a yi ita da Malam Nura don ba za ta bar wannan maganar ba, ta sanya a ranta ita da amaryarsa shege ka fasa domin za a yi zaman doya da manja!.



MAMAN AFRA
09025576222
[4/6, 5:18 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=gi_t



*UWAR AGOLA*


NA

MAMAN AFRAH


*Daga marubuciyar*
*Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.*
09025576222


🅿️2️⃣


Malam yana tsaye sai ganinta ya yi kamar an jefo ta, ta fito ta tsaya tana huci kamar zakanya, da kallo ya bita yana aro jarumta ya tsuke fuska amma alamu sun nuna Kuluwa bata lura da tamke fuskar da Malam Nura ya yi ba don idanunta sun rufe da kishi hakan ya sanya ya zuba mata na mujiya. Sai da ta tsare shi da ido tq ce

"Nura wace ce take tafiya kamar motar tantan ɗin? "Ta faɗa yana kallon yanayin ta ya gama gane ta haɗa kanta da baƙar wahala don baƙin kishi mugun ciwo ne musamman na mijin da bai damu da kai ba, kuma ba ya ɗaukar duka ɗawainiyarka.

Sai da ya danne dariyar da ta so ƙwace masa ya sassauta murya ya ce

"Haba Kuluwata, ni a wa zan kira ki da motar tantan ki duba kanki da kyau ai idan diri ake nema da iya tafiya sai dai mata su take miki baya, amma ai ke tafiyarki kamar ƙirga sawun ki kike" ,Shiru ta yi tana binsa da kallo amma ƙwaƙwalwarta tana raya mata avubuwa da dama ciki kuwa har da nuna mata raina mata hankali ya yi hakan ya sa ta ce


"Ka ji da shi ciwon ajali a ɗan yatsa, ai ni na san ba a sakewa tuwo suna, mai hali ba ya canjawa, ai duk wannan maganganun naka ba ganewa zan yi ba wai an yi yamma da kare, tun ba yau ba na san cewa kai munafukin mata ne k... Hannu ya ɗaga mata a ƙufule cike da faɗa ya ce

"Dakata! Kuluwa, ni nan da kike ganina na fiki hawa tamfar ɓacin rai don haka ki taka a sannu ko na shuka miki rashin mutunci, ni yanzu hankalina a kan sabuwar amaryata yake dan haka a halin da ake ciki yanzu ina kan bakana na cewa mata suna suka tara! Kuma Hadiza ita ce zara a cikin matan" Yana faɗar hakan ya juya ya yi hanyar ɗakinsa ya barta a tsaye tana jin tamkar ya watsa mata wuta da ya ce Hadiza amaryarsa ce Zara kenan su duk suna suka tara wato ba mata ba ne su.

Har ta kama hanyar ɗakinsa ta fasa ta juya ta shige ɗakinta tana jin tamkar ana hura wuta a zuciyarta, tana shiga ta kwanta tana saƙa da warwarar yadda za ta ɓullowa lamarin ta yadda za a fasa wannan auren domin ita bata fatan Malam Nura ya ƙara auro kowace mace har duniya ta naɗe!.


Yana shiga ɗakinsa ya cire kayan jikinsa ya mayar da linkin ya ajiye ya saka wasu kayan, cikinsa ne yake ƙugi yunwa yake ji tamkar ƴaƴan hanjin cikinsa za su fito su nemi abinci da kansu haka yake ji. Tunanin inda zai samu abin da zai saka a cikinsa ya yi jim kaɗan ya fito ya je ya rufe ƙofar gidan, ɗakin Haule ya nufa yana shiga ya same ta a zaune tana lissafa ƴan kuɗaɗen ta lokacin duk yaran sun yi bacci, daman yaran uku ne nata biyu ɗayan kuma wata mai rabon haihuwar ce a cikin matan da ya aura ta haifa ta kawo masa ita ta karɓa take riƙewa.

Kasancewar basu samu haihuwa da wuri ba tun da babbar ƴarsa Alawiyya tana da shekara tara, sai Kabiru mai shekara shida, su ne ƴaƴan Haule, da kuma Lauwali mai shekara huɗu shi ne ba ɗan Haule ba. Allah da ya taimake shi duk yawan aure-auren sa matan ba sa samun ciki da yanzu ƴaƴan sun kusa ashirin. Yanzu yana da shekara talatin da bakwai a duniya, inda Haule take da shekara talatin da ɗaya, Kuluwa kuwa ashirin da tara.

Haule mace ce mai haƙuri da kawaici abin duniya da duniyar ma basu dame ta ba, inda Kuluwa take masifaffiya da baƙin kishi tana da masifa sannan bata barin ta kwana. Shi kuma Malam Nura mutum ne mai son mata sannan yana da maƙo ba ya ɓanɓaruwa ta daɗin rai kuma mutum ne shi da ba ya sauke haƙƙin iyalansa bayan yana da hali tun da manomi ne sannan yana neman kuɗi amma kulluɓ cikin tarawa da kuma ambaton babu yake.

Yana shiga ta yi saurin ɓoye kuɗin nata duk da bata san cewa ya gani ba, tun da ya san halinsa mutum ne mai son abin wani yanzu yana iya cewa ta ara masa kuɗin. Yana washe baki ya samu bakin gadon ya zauna ya ce


"Haulatuwa uwar gidan ran gida, uwar gida sarautar mata, ke ce ta farko kuma kowacce bayanki take bi" Ɗan kauda kai gefe ta yi tana rayawa a ranta cewa sai yaushe zai daina zambaɗa ƙarya da kuma daɗin baki, ta ɗan saki murmushin irin ta ji daɗin nan a fili ta ce

"Wannan haka yake, kana fasa min kai fa amma" A zuciyarta kuma ta ce

'A haka za ka ƙare kullum cikin daɗin baki abin da za ka faɗawa wannan daban wanda za ka faɗawa wacccan ma daban shi ya sa duk lokacin da gidanka aka ce akwai mace fiye da ɗaya kai kake haddasa fitina amma a guji zuwa rafi wata rana tulu zai fashe!'

Yana ɗan washe bakin samun nasara ya ce

"Kin cancanta ne" Dariya kawai ta yi ya ɗan sauke numfashi ya ce

"Za a samu wani abu a nan ne?" Tana kallon sa ta ce

"Kamar me?"

Ya ce

"Abin da zan saka a bakin salati yunwa nake ji" Sai da ta karkata kai gefe ta ce


"Ayya daman gayan tuwon da Kuluwa ta bamu na yi miya su kansu yaran bai ishe su ba sai da na siya musu awara suka ƙara" Shiru ya yi yana nazari ya san shi ya bada hatsi kaɗan wanda ba zai isa a ci a ƙoshi ba sannan bai bada kuɗin kayan miya ba ya san kuwa Kuluwa ko da danginsa zai zo bai isa ta bashi miya ba.

Ya ɗan yi jim ya ce

"Kuma babu sauran miyar?" Ta ce

"Wallahi babu" Miƙewa tsaye ya yi ya fito ta taɓe baki ta bi bayansa da kallo. Yana fitowa ya nufi ɗakin Kuluwa ya shiga tana zaune ta doka uban tagumi ita kaɗai ta san tunanin da take kusa da ita ya je yw zauna sai da ya zauna ma ta lura ya shigo ɗakin. Wata harara take zabga masa kamar idanunta za su faɗo ya rausayar da kai irin nn ƴan duniya ya ce


"Kuluwa tawa, ni kuwa na Allah" Wani gajeran tsaki ta ja ta ce


"Kanka ake ji mahaukaci ya faɗa rijiya" Basarwa ya yi ya ce

"Ki bani tuwo ina jin yunwa" Tana masa kallon tsaf ta ce


"Inda ka je ba a baka ba?"

Yana kawar da maganar ya ce


"Bani da inda ya fi nan, wallahi yunwa nake ji kamar in ci babu" Dariya ta yi mai haɗe da shewa ta ce


"Da za ka ci babun ma da ya fi" Ganin abin nata ba na ƙare ba ne ya ce


"Ke Kuluwa abin naki ya isa ba fa tsoronki ake ba, ki ɗakko tuwo ki bani tun da ba ke kika noma mini hatsin ba" Kamar jira take ta tashi da sauri ta janyo wata roba da tuwon yake ciki ta turo gabansa ta ce


"Inda wannan gayan tuwon ne gashi nan"

Yana kallon tuwon ya ce


"Ina miyar?"


Ta ce


"Wacce ka bani kuɗin cefanen na yi?" Yana zare ido ya ce


"Idan ma ban baki ba ke ba a cin arziƙin ki ne, wata shegiya miya ba za ki nema ki yi ba a miki ciki a miki goyo, wato na nemi hatsin tuwo na baki na miyar ma ni kike so na nemo" Hannu ta saka da buga ƙasa ta ce


"Wannan ne baka isa ba wallahi, ni ba wahalalliyar mace ba ce, idan kanka zafi yake to ni nawa hayaƙi yake, masifa wane shege ta kashe, miya ce baka bada kayan yi ba ni kuma wacce na yo billahillazi ba zan bada ba, ɗumamen tuwo zan yi da ita gobe, nima gari na siya nasha da daren dan haka ka ɗauki tuwon ka fita min a ɗaki" Ganin ba zai iya masifarta ba ya miƙe tsaye ya saka ƙafa ya buge robar tuwon ya ce


",Aikin banza gayyar na ayya gayyar tsiya, ɗanyen tuwon, abin da har yau baki iya tuwo ba sia ɗanye, kana ci yana maka dariya, ai an kusa yin ta ta ƙare wato zan auro galleliyar amarya Hadiza mai iya girki da iya tafiya ta zo ta kawo sauyi a gidan nan" Yana kaiwa nan ya juya ya fita daga ɗakin.


Cikin ɗaga murya take faɗin


"Idan har tusa tana hura wuta za mu gani, lokaci zai nuna ai daman duk wanda ya ce bai iya kuka ba uwarsa ce bata mutu ba za mu jira zuwan amarya mu ga yadda za ku ƙare! Daman yanzu za a yi amarya mu za a shuka mu kamar dusa" Yana jin ta ya yi dogon tsaki har zai shige ɗakinsa ya dawo da baya ya zo ya ɗaya labulen ya ce

"Kin ba kanki amsa" Yana faɗar hakan tafi ya shige ɗakinsa.


Tun da ya kwanta yake juyi yunwa ta hana shi ya runtsa ya ɗakko waya ya kira Hadiza suka yi hira suka yi sallama yana jin suna hira tana tauna, alamar tana cin abu kuma yana jiyo muryar Zainaba tana batun akwai daɗi ya san kuwa nama da lemon da ya saya ne suke ci, shi an bar shi da ciki yana masa ƙugi.


Bayan sun gama wayar ya buɗe wani jug, gayan fura ne a ciki haka ya ɗakko ya ci ya sha ruwa ya kwanta bacci ya yi awon gaba da shi da mafarkin an kawo amarya Hadiza gidansa.


Washe gari da safe yana fitowa ya ga yaran suna shan koko da waina, gaban Kabiru ya je yana faɗin

"Kabiru ina kuka samu waina?" Yaran suka haɗa baki wajen cewa


"Iyarmu ce ta saya mana" Baki ya washe ya kalli Haule da take gyaran wake ya ce


"Ku dai mata sai kuke kukan babu kuɗi alhalin kuɗi suna wajenku a nannage, ban san mai ya sa kuka fi kula da ƴaƴanku sama da mazan ku ba, yanzu maimakon ki cika kwanon samira da wainar nan ki cika dogon kofi(Jug) Da koko ki kai mini ɗaki in saka miki albarka amma kika yi mirsisi tusar ango" Kallo ɗaya ta masa ta ɗauke kai ta mayar da hankali wajen yin abin da take yi.


Yana tsaye ya ce


"Haule ba magana nake miki ba?" Kuluwa wacce take wajen murhu tana iza wuta ta ce

"Shiru ma ai amsa ce ga mai hankali" Cike da jin haushin ta ya ce


"Ni dai Kuluwa kin zame mini ƙarfen ƙafa wallahi, ina dalili ana magana da kishiyarki amma kina tare mata faɗa" Banza ta masa ta fara waƙa tana faɗin


"Wani mijin namiji ne wani kuma sauna ne" Kasaƙe ya yi yana cika yana batsewa ya ce

"Da wa kike?"
Tana ɗan ɗaga kai alamar mai jiran faɗa ta ce


"Wanda yake tsoron ta mutu... Kafin ta ƙarasa maganar fuuuu ya yi hanyar ɗakinsa ya fito da ledar kayan aron da ya je hira da su jiya ya zo a fita daga gidan.


Bayan ya mayar da kayan ya wuce wajen mai shayi ya sha shayi da biredi ya ƙoshi. Yana shigowa gida ya ce kira su ya ce



"Yau saura kwana shida ɗaurin auren nan, ina so in faɗa muku bakin ku ya ƙare" Haule ta kalle shi da mamaki ta ce

"Ban gane ba?" Ita daman Kuluwa kai ta ɗauke gefe bata ce komai ba.


Ƴar dariya ya yi ya ce

"Ina nufin na sallame ku zuwa turaka!. Wato duk wani tanadi da zan yi nan gaba na amarya Hadiza ne" Su duka cike da rashin fahimta suke kallonsa yana tsaye hannayensa a cikin aljihunsa yana murmushin jin daɗi shi kaɗai ya san irin amarcin da zai kwasa.

Kuluwa a harzuƙe ta ce

"Kamar ya wai?"


Ya nuna ɗakinsa da hannunsa ya ce


"Ina nufin daga yau duk wacce take da girki to iya girki za ta yi babu ruwanta da zuwa turakar miji da daddare, yanzu lokacin amarya ne!"

Haule ta ce



"Sabon salo kiran sallah da usur, wannan amaryar da abin da za ta zo kenan?" Yana kaɗa kai ya ce

,
"Eh akwai wasu ƴan magungunan gyara da zan fara sha to bana so maganin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login