Showing 12001 words to 15000 words out of 17653 words
Chapter 5 - GUDUN TSIRA LITTAFIN YAKI BY ABDULAZIZ SANI MADAKIN GINI.txt
sare na abokin mahaifinta wato
Sulta.Nan
take Sarki Darwaz ya kudurce a ransa cewar
bazai
sawa wannan rauni masa magani ba,kum bazai
yarda a dinke shi ba saidai yayi ta ciwon da zaiyi
har ya daina son kansa yayi warkewar
dole,sannan
kuma ya kudirci niyar cewa babu wanda zai sake
ganin fuskarsa saidai idan ya zama gawa hatta
matarsa da 'yarsa kuwa.Koda ya gama aiyana
hakan,sai Sarki Darwaz ya sake rufe fuskar tasa
da
rawani sannan yaje kan wata doguwar kujera ya
kishingida yana kwanciya barci ya saceshi saboda
tsananin gajiya gami da tsamin jiki bisa
gumurzun
da yayi da shugaba Sultan.
¤¤¤ ¤¤¤ ¤¤¤
Al'amarin su shugaba Sharwan kuwa suna cikin
tafiya a daji a cikin ayarin nasu gaba daya sai
kawai
suka ga Shamirat matar Shugaba Sultan taja
linzamin dokinta ta tsaya cak a lokacin da jikinta
gaba daya ya kama tsuma kuma kirjinta ya kama
daka kamar zuciyarta zata faso kirjin ta
fado.Koda
ganin haka Sai hankalin Shugaba Sharwan,Ilela
dana
Siyama ya dugunzuma suka rugo gareta aka
sauko
da ita daga kan dokinta akayi mata shimfida a
kasa
saboda tsammanin ko kamuwa tayi da wata
rashin
lafiya.Nan fa suka shiga tambayarta inda uakeyi
mata ciwo a jikinta.Koda jin wannan tambaya sai
hawaye ya zubowa Shamirat ta dubi Sharwan
tace,sun kashe mijina,naji a jikina baya numfashi
a
doron kasa.Koda jin wannan batu sai Sharwan ya
takarkare ya kurma uban ihu wanda ya tsorata
kowa
a wajen sannan ya fashe da matsanancin kuka
kamar bazai daina ba.Al'amarin daya karya
zuciyar
Ilele da Siyama Kenan suma suka rungume
Shamirat
suka taya ta kukan.Saida shugaba Sharwan ya
jima
a tsugunne bisa gwiwoyinsa yana kuka sannan ya
dago kai ya dubi Shamirat,bisa mamaki sai taga
yayi
mata murmushi yace,mijinki bai mutu rago ba.Na
tabbatar da cewar kafin su Sarki Darwaz su
kashe
shi saida yayi musu mummanar barna saboda
nasan
irin jarumtakar abokina gami da taurin
ransa.Bana
raba daya biyu,sai ya bar shaida a jikin Sarki
Darwaz.Ina son ku sani cewa zamanmu a waje
daya
yana da matukar hadari,don haka zaifi kyau mu
tashi
muci gaba da tafiya.Ba tare da gardamar komai
ba
kuwa aka kimtsa aka cigaba da tafiya ana keta
dazuzzuka masu sarkakiya,kwazazzabai,koramai
da
fadamomi iri iri suna masu tunkarar hanyar da
zata
kaisu Birinin Darul Hunam.Saida suka shafe
kwanaki
arba'in suna tafiya sannan suka iso wani daji mai
tsananin fadi mai cike da sahara.Iya hangen
mutum
a cikin dajin babu bishiyu ko daya,babu duwatsu
ko
alamar wani danshi na ruwa sai rairayi tsabarsa
tsubi-tsubi,wani rairayin ma tudunsa yakai na
tsauni.Da isowars wannan wuri sai Shugaba
Sharwan ya bada umarni aka tsaya aka yada
zango.Bayan an kafa tantuna anci abinci kuma
an
huta,sai Siyama ta dubi Sharwan tace,yakai
Abbana
menene dalilin da yasa ka bada izinin mu yada
zango a nan wajen?Lokacin da Sharwan yaji
wannan
tambaya sai yayi ajiyar zuciya sannan ya dubeta
cikin alamun takaici yace,yake 'yata idan baki
manta
ba abokina Sultan ya gaya mama cewa tsakanin
birninsa da birnin na gaba wanda ake kira Darul
Hunam tafiya ce ta kwana arba'in da daya,yau
kuma
kwananmu arba'in cif muna tafiya.Kinga kenan
saura
tafiyar kwana daya jal mu riski birnin Darul
Hunam.Dole ne mu tsaya daga nan mu tura
dakarun
leken asiri domin su gano mana halin da garin ke
ciki.Idan an dana mana wani tako ne mu san
yadda
zamu tsallakeshi.Idan kuma garin bazai shigu ba
mu
nemi hanyar dazamu kewaye shi.Sa'adda
shugaba
Sharwan yazo nan a zancensa sai gaba dayan
jama'ar banu Hanzar suka aminta da shawarar
tasa.Nan yake aka tashi wadansu kwararrun
dakarun
sumame guda uku wadanda akeji dasu aka turasu
izuwa cikin birnin Darul Hunam.
Dafatan zakuy commenting da liking sosai dan
karin karfin gwiwa
Daga:
GUDUN TSIRA
Littafi na hudu(4)
Part B
Nan take aka tashi wadansu kwararrun dakarun
sumame wanda ake ji dasu aka tura su izuwa
cikin birnin Darul
Hunam.
¤¤¤ ¤¤¤ ¤¤¤
A can birnin marigayi Shugaba Sultan kuwa tunda
Sarki Darwaz da gimbiya Huraisa suka kama
barci
basu farka ba har saida gari ya waye rana ta
take.Huraisa ce ta fara farkawa tana bude
idanunta
sai ta yunkura da nufin ta mike tsaye,amma sai
wata
kuyangarta mai suna Badura tayi sauri ta dannan
kafadunta kasa ta dubeta tace,yi hakuri ya
shugabata,kiyi sani cewa likita yace kada mu bari
kiyi kyakkyawan motsi,domin yin hakan zai iya
janyi
farkewar dinkin da aka yiwa rauninki.Koda jin
wannan batu sai bakin ciki ya turnuke Gimbiya
Huraisa ta koma ta kwanta,sannan ta dubi
Badura
cikin tsananin takaici tace yanzu ina mahaifina
yake?
Badura tace yana falo yana ta fama shara bacci
tun
jiya bai farka ba.Huraisa tace maza ki koma
wajensa
yanzku ki gani,idan har ya tashi daga wannan
barcin
kice dashi inason na gana dashi yanzu yanzu
cikin
gaggawa.Badura ta risina tace an gama ya
shugabata.Nan take Badura ta mike tsaye ta fice
daga cikin dakin ta nufi babban falon na marigayi
Sultan.Fitarta ke da wuya sai idanun Huraisa
suka
kai kan wata babbar akwatin karfe dake jikin
bangon
arewa na dakin,wacce aka kulleta da wani katon
kwadon madubi.Huraisa ta dubi wata kuyanga
dabam tace,maza kije ki nemo mini makeri ina
son
na cire wannan makulli domin naga abinda ke
cikin
wannan akwati,domin koma meye a ciki yana da
matukar muhimmanci ga shugaba Sultan,amma
kuma menene dalilin da yasa ya barshi anan bai
kaiwa matarsa Shamirat ta tafi dashi ba?
Kuyanga ta
risina tace an gama ya shugabata.Itama sai ta
mike
tsaye ta fice daga cikin dakin.Jim kadan da fitar
wannan kuyanga saiga Sarki Darwaz yashigo
cikin
dakin kuyanga Badura na biye dashi kuma
fuskarsa
na rufe cikin rawani idanunsa kadai ake
gani.Koda
Huraisa taga Sarki Darwaz a cikin wannan yanayi
sai
ta yunkura ta mike zaune,sannan ta dubi gaba
dayan
kuyangin dake dakin tace,ku bamu wuri.Take
kuwa
kuyangin suka fice suka janyo kofa suka
rufe.Sarki
Darwaz ya zauna a kan gefen gadon data ke
kwance,ya dubeta yace,ki gafarceni yake
'yata,daya
yau kema bazaki saki ganin fuskata ba,domin
bana
son kowa yaga wannan shaida da Sultan yayi
min.Koda jin wannan batu sai Hankalin Gimbiya
Huraisa ya dugunzuma ainun ta dubeshi cikin
alamun tsananin damuwa da takaici a lokacin da
idanunta suka ciko da kwalla,tace haba yakai
Abbana ai idan har zaka boyewa kowa fuskarka
bai
kamata ace ni da mahaifiyata ka biye mana
ba,saboda zamu iya zama da kai a cikin kowacce
siffa ko da kuwa fuskarka tafi komai muni a cikin
wannan duniya,tunda ba fuskar taka muke so
ba,ruhinka muke bukata ya kasance tare damu
dimun da'iman.Lokacin da Gimbiya Huraisa tazo
nan
a zancenta sai Sarki Darwaz yayi murmushin farin
ciki,yace,yake 'yata na sani cewa kuna kaunata
kamar yadda kuke son kanku.Ina so ki sani cewa
abin kunya ne kuma abin kaskanci a cikin tarihin
jarumtakata duniya ta san cewa gwamnan da
yake
karkashina shine yayi mini rauni a fuskata.Idan
kika
ga wannan fuskatawa a fili to gawata ce a
kwance.Mene ne dalilin da yasa kika aika kina
son
yin magana da ni yanzu?Koda jin wannan
tambaya
sai Huraisa tayi ajiyar numfashi sannan tace, ba
wani abu bane yasa na aika kazo ba,sai domin
na
nemi gafararka bisa sakacin danayi har Sultan ya
sami nasarar yi min rauni a kafata gashi hakan
ya
haddasa matsala a cikin tafiyarmu.Kamata yayi
ace
munci gaba da tafiya yanzu don karfa abokan
gaba
su kara bamu tazara sosai.Na kirawo kane yanzu
domin na baka shawara,shawarar kuwa itace ku
kara
gaba kada ku tsaya jirana har izuwa gobe don ci
gaba da wannan tafiya.Ka tuna cewa idan har
wadannan abokan gaba namu suka sami nasarar
fita
daga cikin nahiyarmu shikkenan sun tsira.Lallai
ya
kamata mu kure musu wannan GUDUN TSIRA da
sukeyi mu kawo karshensu.Yayin da Gimbiya
Huraisa tazo nan a zancenta sai hankalin Sarki
Darwaz ya rabu gida biyu,ya rasa hukuncin daya
kamata ya yanke..Kwatsam sai suka ji ana
kwankwasa kofar dakin.Cikin fushi sarki Darwaz
ya
daka tsawa yace wane ne nan yake kwankwasa
mini
kofa?Kawai sai sukaji muryar Boka Hurgas yana
mai
cewa nine ya shugabana.Cikin hanzari Sarki
Darwaz
ya mike yaje ya bude masa kofar ya shigo.Hurgas
ya
risuna sannan ya dubi sarki cikin biyayya yace ya
shugabana zamanmu a wannan gari har izuwa
gobe
zai iya janyo mana dalilin dazamu kasa cimma
abokan gaba da tazarar kwana daya rak.Abinda
za'ayi shine,a dauki Gimbiya a sanyata cikin
keken
doki a cigaba a tafiyar a haka.Koda jin wannan
batu
sai farin ciki ya lullube gimbiya Huraisa,ba tare da
sarki Darwaz yayi wata gardama ba sai ya bada
umarni nan take aka fara shirye shiryen
tafiya.Kafin
abar garin saida Sarki Darwaz ya dora wani
babban
hadiminsa mai suna Zukairu akan kujerar
marigayi
Sultan,sannan akayi hawa aka fice daga cikin
birnin
gaba daya aka durfafi hanyar da zata kaisu birnin
darul Hunam.
¤¤¤ ¤¤¤ ¤¤¤
Lokacin da dakarun leken asiri na kabilar Banu
Hanzar suka tafi izuwa cikin birnin Darul Hunam
domin su gano halib da birnin ke ciki da kuma
sirrin
komai na birnin,Saida suka kwana suka yini basu
dawo ba.Al'amarin daya dugunzuma hankalin su
shugaba Sharwan kenan suka fara tunanin ko an
kama sune,don haka suma a koyaushe za'a iya
kawo musu harin sumame.Nan da nan shugaba
Sharwan ya hada taron gaggawa domin suyi
shawara bisa abinda ya kamata ayi.Nan fa
shawara
ta yawaita wasu suce kawai ayi shirin yaki a bi
sawun dakarun da aka aika guda uku.Wasu kuma
suce a sami wuri a buya a dan kara saurarawa a
gani.Saida kowa ya fadi albarkacin bakinsa san
nan Siyama ta daga hannu akayi tsit.Siyama ta
dubi
shugaba Sharwan tace,yakai Abbana inason ka
tuna
cewa dakarun sumamen da muka tura suyi mana
leken asiri a cikin wannan birni na darul Hunam
sune suka fi kowa kwarewa a aikin leken asiri a
can
birnin Kisra gaba daya,kuma sama da shekaru
goma
suke rike da wannan kambu ba'a taba turasu
aikin
dasu ka kasa ba.Haka kuma sun kasance dakaru
masu tsananin karfin damtse da tsananin karfin
gudu
da iya jure wahala ta tsawon kwana uku.Bisa
wannan dalili nake ganin cewa duk rintsi ko da
mutum daya ne daga cikinsu sai ya sami nasarar
dawowa nan garemu a raye ya bamu labarin
abinda
ke faruwa,saboda haka zaifi kyau mu dan kara
musu
lokaci daga nan zuwa tsakar date ko zuwa gobe
da
safe,saboda babu mamaki ma yanzu haka suna
kan
hanyarsu ta dawowa.Lokacin da Siyama tazo nan
a
zancenta sai jikin kowa yayi sanyi,aka sake yin
shiru
tsit aka rasa wanda zai soko shawarar data
kawo.Kawai Sai shugaba Sharwan yayi murmushi
ya
dubi Siyama yace,yake 'yata hakika kina da kaifin
tunani gami da hangen nesa,don haka na amince
da
wannan shawara taki.Lallai zamu ci gaba da
sauraron dawowar dakarunmu na leken asiri,daga
na har zuwa wayewar gari.Amma duk da haka
yanzu
zamu tura dakarun tsaro mutum bibbiyu izuwa
kowane bangare na wannan daji.Wato gabas da
yamma,kudu da arewam,nisan tafiyar zngo guda
domin su labe su zuba ido.Da zarar sunji wani
motsi wanda basu aminta dashi ba,ko sunga
wata
zuga ta dakaru su rugo su sanar damu.Koda jin
wannan batu sai gaba dayan yan majalisar suka
mince.Ai kuwa saida dare ya raba sannan akaji
dawowar dakarun sumamen da aka aika birnin
Darul
Hunam,sun taho a guje suna yin alamarsu ta
kukan
wani tsuntsu.Dama babu wanda yayi bari a cikin
ayarin,sai kuwa kowa ya mimmike aka tarye
su.Dakarun sumamen suka iso su uku suna ta
faman haki kamar ransu zai fita.Suka zube kasa
wanwar suna numfashi da karfi kamar ransu zai
fita.Saida suka bari suka huce sosai,suka dawo
cikin
hayyacinsu sannan aka basu ruwa suka
sha.Bayan
sun nutsu ne Siyama ta dubi babbansu mai suna
Hatmara tace ba mu labari yakai tauraruwa mai
wutsiya,mu kuka gano a cikin birnin Darul
Human?
Sa'adda Hatmara yaji wannan tambaya sai yayi
ajiyar
zuciya sannan yace ya shugabata kiyi sani cewa
an
sanya tsattsauran tsaro a cikin birnin darul
Hunam
da kewayensa.Babu ta inda mutum zai ratsa ba
tare
da ya fada hannun dakaru ba walau ta
gabas,yamma,kudu da arewa,amma duk da haka
saida mukayi amfani da kwarewarmu muka shiga
har cikin tsakiyar birnin ta cikin bututun ruwan
kwata dake karkashin kasa,amma da zamu dawo
sai
wannan hanya ta gagare mubi dole saida muka
rafke
dakarunsu guda uku a cikin daren yau mukayi
shigarsu mukayi kasadar biyo hanyar cikin gari,a
kyar da sidin goshi muka iso bakin kofar
birnin.Anan ne fa muka gane kuskurenmu saboda
saida asirinmu ya tonu aka kama mu aka kai mu
wajen shugaban masu gadin kofar.A nan ne akayi
kuskure aka shigar da mu cikin wani daki domin
gana mana azabar da zatasa mu fadi ko mu su
waye.Cikin sa'a muka bubbuge dakarun da suka
kamamu a cikin dakin,muka sumar dasu suma
mukayi shigarsu muka dawo baki kofa.Inda anan
ma
mukayi wani yakin na sumame muka bazar da
gaba
dayan masu gadin kofar kimanin mutum saba'in
sannan muka bude kofar garin muka fito muna
masu
falfala azababben gudu,har sai da muka iso nan
yanzu.Ya shugabata a cikin binciken da mukayi a
cikin birnin darul Hunam mun gano cewa aljanu
sun
kai labarin guduwar jama'armu daga can birnin
kisra,kuma gwamnan garin ya kafa doka cewa
duk
dan garin daya boye irin jama'armu a cikin
gidansa
hukucin kisa ne a kansa.Yanzu shawara ta rage
garemu mu san matakin dazamu dauka amma
komai zai iya faruwa domin gwamnan birnin
darul
Hunam zai iya turo dakarunsa su biyo sawunmu
su
iso har nan su riske mu gaba daya,kuma zau iya
tsayawa a bakin birninsa yayi mana mugun
tanadi
na yakarmu.Babban abinda ya tayar mana da
hankali
shin yawan dakarun birnin sun ninka namu sau
uku,inda mukace zamuyi fito na fito dasu zasu
iya
karar damu gaba dayanmu.Lokacin da badakare
Hatmara yazo nan a jawabinsa sai hankalin kowa
ua
dugunzuma ainun har da shugaba Sharwan aka
rasa
wanda zaice kala har izuwa tsawon yan dakiku
masu
yawa.Kwatsama sai Siyama ta dubi Sharwan
tace,zama bai kama mu ba yanzu,dole ne mu
tashi
yanzu muyi shirin yaki muje mu tari dakarun
birnin
darul Hunam a kan hanya tun kafin su iso
nan.Amma yakin sunkuru zamuyi musu,kuma dole
ne mu gaggauta gamawa dasu,sannan muyi
shigar
su su shiga izuwa cikin birnin muyiwa gwaman
garin juyin mulki,domin mu sami damar shiga
garin
har mu kwana,inyaso da safe mu kara guzuri mu
ci
gaba da tafiyarmu tunda bamu da wata hanya
dazamu bi face ta cikin birnin.Lallai bamu da
wani
zabi wanda yai muyi kamar yadda na shirya
yanzu
ni ba haka ba kuwa karshen mu ya yazo.Sa'adda
Siyama tazo nan a jawabinta sai wani babban
dan
majalisa mai suna Dairuf ya dubeta yace,ai juyin
mulkin da zamuyi bashi da wani amfani tunda dai
bazamu iya sani daga cikin jama'armu ya hau
karaga ba,kuma babu wani dan gari dazai yarda
ya
karbi karagar saboda tsoron Sarki Darwaz.Siyama
tace ai bukatarmu bata son karaga bane sai dan
kawai mu sami damar kwana a garin da samun
garin guzuri da ikon wuce gaba.Shugaba Sharwan
yayi ajiyar numfashi sannan ya dubi Siyama yace
na
yarda dake a kan cewa bamu da wani zabi wanda
yafi muje mu yaki wadannan mutane,amma fa
hadarin dake cikin yin hakan yana da yawan
gaske,kuma ban ga hanyoyin daza'abi a sami
nasara.Siyama tace nayi nazarin duk irin hadarin
da
kake tunani,kuma nayi tunani akan irin dabarun
da
ya kamata muyi
don ganin mun sami nasara.Abinda nake bukata
kawai shine ka bani dakaru guda dari biyi kacal
daga cikin dakarunka na musamamn masu tsaron
lafiyarka,zan jagorance sumu kai ga
nasara.Sa'adda
Siyama tazo nan a zancenta sai Shugaba
Sharwan
Sharwan yayi shiru yana mai sunkui da kansa
kasa
ya fada cikin kogon tunani ba tare daya nemi
shawarar yan majalisarsa ba.Daga can sai ya
dago
kai ya dubeta yace,yake 'yata kiyi sani cewa dalili
daya ne zaisa na yarda dake na baki dakaruna na
musamman don zuwa aiwatar da wannan aiki
mai
mugun hadari.Dalili kuwa shine tun kuruciyarki
kawo
iyanzu ban taba ganin wani abu ya gagareki ba
muddin kinyi niyyar aiwatar dashi,haka kuma ban
taba ganin kin shiga hadarin da kika kasa fita
ba.Zanyi kundubala a yanzu na baki dama,amma
ina
gargadinki daki sani cewa idan har kika kasa
samun
nasara kika janyo dalilin da kabilarmu ta tarwatse
ko
kuma mukayi asarar dumbin rayuka da dukiya
mai
yawa bazan taba yafe miki ba.Idan kin yarda da
wannan sharadi na baki izini ki debi dakarun
anwa
yanzu ki tafi.Koda jin wannan batu na shugaba
Sharwan Sai hankalin Siyama ya dugunzuma
ainun
saboda tasan abinda yake nufi bazai taba yafe
mata
ba,yana nufin cewa zai datse duk wata alaka
dake
tsakaninsa da ita tamkar ma bai taba sanin
taba,amma saboda ki fadi da tashin karayar zuci
irin
ta Siyama sai taki nuna tashin hankalinta a fili
kawai
ta dubi shugaba Sharwan cikin murmushi tace na
yarda da wannan sharadi naka ya
shugabana.Tana
gama fadin hakan sai ta waro wadannan dakaru
na
musamman guda dari biyu tayi musu umarnin
suje
su shirya cikin gaggawa.Nan take kuwa suka
sanya
bakaken tufafi suka rufe ko'ina na jikinsu
idanunsu,bakinsu da hancinsu kadai ake
gani.Wani
irin talakarma suka sa a kafafunsu masu taushin
gaske,gami da duhu yadda komai suka daka baza
aji
sautin sahunsu ba sannan a jikin kowanne daya
daga cikinsu akwai wadansu kananan wukake
masu
azabar kaifi da tsini sirara guda dari.Haka kuma
suna dauke da kwari boye a bayansu mai cin
kibiya
dubu da kuma karamar baka rataye a bayansu da
kuma sharbebiyar takobi.Sudai wadannan dakaru
an
basu horo na musamman wanda yasa suka kware
ainin a wajen iya kisan mummuke.Bayan
wadannan
dakaru sun gama shirinsu sun jera akan layi sahu
biyu,sai ga Siyama ta fito daga cikin tantinta
itama
tayi shiga iri daya da tasu.Al'amarin daya baiwa
kowa mamaki kenan a sansanin domin ba a taba
ganinta ba a cikin irin wannan shiga,kuma babu
wanda ya san cewa ita ma tana da horo irin na
wadannan dakaru.Nan take Siyama ta karaso
gaban
Shugaba Sharwan ta bukaci yasa nata
albarka,kuma
ya nema mata sa'a a wajen iyaye da kakanni
saboda
su dai wannan kabila ta Sharwan basu da wani
addini guda da sukyi imani dashi face iyayensu da
kakaninsu amma dai suna aiki da tsafi ko
sihiri.Nan
take Shugaba Sharwan ya dafa bayan Siyama
kuma
ya sumbaci goshinta yasa mata albarka,kuma
yayi
mata addua.Nan take Siyama taji wani irin
gagarumin karfin gwiwa ya shige ta.Kuma taji
dukkan tsoro ya kau daga cikin zuciyarta.Ba tare
da
bata wani lokaci ba sai Siyama taja wadannan
dakaru suka falfalwa da gudu izuwa cikin daji
suna
yin wani irin gudu na ban al'ajbi tamkar giftawar
tauraruwa mai wutsiya,kafin kace wani abu tuni
sun
kule uma sun bace a cikin duhun daren.Saida su
Siyama sukayi 'yar doguwar tafiya ta yan dakiku
masu yawa tana kan gaba sannan ta tsaya cak
suma
dakarun guda dari biyu sai sukayi cirko cirko a
bayanta.Siyama ta tsuguna kasa ta kara
kunnenta a
kasa tayi sauraro dan kadan sannan ta mike
tsaye
zumbur ta yafito dakarun su duka sukayi mata
kawanya,tayi musu radar wata magana.Nan take
dakarun sukayi wani sihiri su duka a lokaci
guda.Kawai sai kasa ta tsage suka shige cikinta
kuma kasar wajen ta koma ta hade kamar wani
abu
bai taba faruwa ba a wajen.Itama Siyama ta
shige
cikin kasar ta kule.Faruwar hakan keda wuya da
kimanin tsawon rabin sa'a saiga dakarun birnin
Darul Hunam su da yawa bisa dawakai dauke da
muggan makamai sun iso daidai wannan wuri.Da
isowarsu sai shugaban nasu ya daga hannu ya
tsaya.Take sauran yaran nasa ma suka ja
linzamin
dawakansu,dawakan sukayi turjiya da
haniniya.Shugaban dakarun ya shaki kamshi har
sau
uku yace,tabbas zuga ta bil'adama ta tsaya a
nan.Kafin ya gama rufe bakinsa sai sukaji kasar
wajen ta kama tsagewa,dawakansu na ruftawa
ciki.Kafin dayansu yayi wani yunkuri duk an
wurgo
musu wukake masu tsani sun caccake su a wuya
da
makogwaro.Nan fa suka rinka sulalewa kasa
daga
kan dawakansu suna bajewa kasa matattu,kafin
kiftawar ido su duka sun zama gawa,sauran
shugabansu shi kadai a tsaye jikinsa na karkarwa
yana waige waige da dube dube,amma baiga
wanda
yayi musu wannan barna ba.Bazato ba tsammani
kuma sai yaga kasar ta kara tsagewa,sai ga
dakaru
na fitowa sama daga cikin karkashin kasa su dari
biyu suna yi masa kawanya.Saida suka gama
fitowa
gaba dayansu sannan na cikon dari biyu da daya
ya
fito,kuma ba wani bane face Siyama.Kafafunta na
dira kan kasa saita durfafi shugaban wadannan
dakaru kai tsaye tana rike da sharbebiyar takobi,a
lokacin dashi kuma ya nutsu ya daina tsoron
komai
ya kura mata idanu kawai yana mai sadudar jin
kaifi
ya ratsa shi.Bisa mamaki sai yaji Siyama ta dora
fadin takobin akan kafadarsa sannan ta dubeshi
cikin
murmushin mugunta tace shin kana da iyali?
Mutumin yace kwarai kuwa inda da mace daya da
'ya daya.Siyama tayi murmushin murna tace
nasan
zaka so ka koma garesu a raye,don bazasu so su
rasaka ba,kaima bazaka so ka rasa su ba.Idan
kabi
umarnina da dokokina zaka koma garesu a raye
kuma cikin koshin lafiya,amma fa idan ka sabawa
umarnina da dokokina ko
gawarka ma iyalin naka bazasu shaidata ba.A
yanzu
inason ka yi mama jagowa mu koma har izuwa
cikin
birninku kuma har cikin gidan sarautarku gaban
sarkinku a matsayin mune jama'arka ba a kashe
maka ko yaro daya ba,ka bar sauran yaranka ne
a
baya.Kada ka kuskura kayi rawar baki ko ka
munafuncemu yadda asirinmu zai tonu.Idan kayi
haka tabbas a bakacin ranka.Koda gama fadin
hakan
sai Siyama ta dubi dakarun nata tayi musu
alama,nan take suka tube kayan matattun
dakarun
suka sanya,kuma suka dau makamansu suke
haye
kan dawakansu.Ita kuma Siyama sai tayi irin
shiga
irin wannan,sannan tasa wannan shugaban
dakarun
ya hau nasa dokin itama ta hau dokin suka jera
da
ita dashi.Sauran dakarun nata na biye dasu a
baya.Babu abinda zai baka mamaki a cikin
wannan
hikima da Siyama tayi face yadda ta shirya
dakarun
nata girman jikinsu yazo iri daya dana dakarun da
suka kashe masu bin wannan shugaba a baya.Ita
kanta sai gashi jikinta yazo iri daya dana
mataimakinsa kai kace wancan din ne wanda aka
kashe.Karkakara Kaka.Laifin dadi karewa.Muje ga
littafi na biyar don jin ci gaban wannan
kasaitaccen
labari.In kuna so to ku karamin karfin gwiwa.
Daga:
GUDUN TSIRA
Littafi na Biyar (5)
Part A
HAKA DAI SU SIYAMA suka ci gaba da