Showing 6001 words to 9000 words out of 17653 words
Chapter 3 - GUDUN TSIRA LITTAFIN YAKI BY ABDULAZIZ SANI MADAKIN GINI.txt
da
mutuwar Siyama ba da jama'arta saboda in dai
wannan lokaci yazo to duk wani Boka dayake
wannan nahiyar ma sai sun kashe shi sun shafe
harkar tsafi gaba daya tamkar ba a taba yinta ba
a
wannan nahiyar,duk cikin bincikena na ga wannan
al'amari.Sa'adda sarki Darwaz yaji wanann batu
sai
ya gyada kai yace ai kuwa indai muka hada karfi
da
karfe mu ta kai dole ne muga bayan wadannan
makiyan namu.Yanzu zan shiga cikin gida nayi
shiri
in yaso ka samemu a can kofar fada inda zamuyi
zuga mu tafi gaba daya.Lokacin da boka Hurgas
yaji
wannan batu saiya bushe da dariya sannan yace
aini
bana bin zugar mutane saidai ku riskeni a can
gaba
ko hanya ina jiranku.Nine zan zamo mai yi muku
jagora har mu riski abokan gaba tunda nine zanfi
kowa saurin gano inda abokan gabar suke.Koda
gama fadin sai boka Hurgas ya bace bat daga
cikin
fadar tamkar bai taba wanzuwa ba a wajen.Koda
ganin hakan sai sarki Darwaz ya ruga izuwa cikin
gidan sarautar ya iso cikin ainihin turakarsa ya
shiga
kimtsa kansa yana sanya kayan yaki.Yana cikin
wannan haline matarsa Larisa tare da 'yarsa
gimbiya
Husaira suka shigo cikin turakar da sauri cikin
tsananin tashin hankali.Husaira ta kasance
kyakkyawar budurwa abar kwatance domin da
kadan
Siyama zata fita kyau.Ga wanda ma bai iya
tantance
kyawu ba cewa zaiyi sunyi kunnen doki.Lasira da
Husaira suka sha gaban Sarki Darwaz idanunua
cike
da kwalla suna shirin fashewa da kuka.Kawai sai
Lasira ta kama kafadun Darwaz ta rike a lokacin
da
hawaye ya zubo mata ta dubeshi tace,haba yakai
mijina saboda me zaka bar karagar mulkinka ka
tafi
farautar kabilar Banu Hanzar alhalin baka da
tabbacin
ganinsu tunda sunyi hijira sun gudu.Kayi sani
cewa
zata iya yiyuwar cewa tuni ma sun fice daga cikin
nahiyar nan gaba daya.Ka tuna cewa fa
kwananka
uku kacal akan karagar mulkin nan,Idan har wani
tsautsayi ya sameka a cikin wannan tafiya shike
nan
fa ka rasa karagarka nida 'yarka kuma
rayuwarmu
ta
shiga cikin hadari kenan tunda ka san cewa kana
da
makiya da yawa a cikin majalisar garin nan da
cikin
jama'ar gari.Lokacin da Lasira tazo nan a
zancenta
sai Sarki Darwaz ya bushe da dariya,al'amarin
dayai
matukar baiwa Larisa mamaki da haushi kenan,ta
kura masa idanu,ita kuwa Husaira sai ta sunkui
da
kanta kas tana zubar da hawaye kawai.Daga can
sai
Darwaz ya tsuke bakinsa kuma ya hade fuska ya
dubi Lasira yace,yake matata yanzu ke ashe har
kina
tunanin cewa wani abu zai iya taba lafiyata a
wannan
fita da zanyi?Ashe kin manta da cewa ni mutum
ne
mai tsananin sa'a da rabo bisa dukkan abinda na
sa
agabana?A iya saninki dani tun muna matasa
wane
abune kika taba ganin ya gagareni?Larisa ta
girgiza
kai tace duk abinda kasa agabanka sai kaga
bayansa
amma wannan karon naji a jikina cewa lallai zaka
riski matsala kasancewar mai Laya ya kiyayi
zamani.Darwaz ya gyada kai cikin murmushi
yace,ai
ko Giwa ta fadi tafi karfin karnuka su dasa mata
wawa sai a sannu.Kada ki manta cewar 'yarki
Husaira ta gadoni a jarumtaka gani da taurin
zuciya,don haka ko babu ni dole ne ayi shakkarki
saboda ita kuma itace zata gaji karagata.Ke
Husaira
mene dalilin da yasa kike zubar da wannan
hawaye
daga idanunki?Shin kina tsoron kada na fita ne
wani
tsautsayi ya sameni?Koda jin wannan tambaya
sai
Husaira ta dago kai ta dubi sarki Darwaz cikin
murmushi tana mai share hawayenta tace,ko
kadan
ni bana tunanin akwai wani mahaluki ko wani
tsautsayi da zai sameka.Ina zubar da wannan
hawaye ne saboda kawai takaicin kace bazaka
tafi
tare dani ba.Ka sani cewa a rayuwata ban taba
fita
yaki ba na daukar rayukan bil'adama da
yawa.Wannan ce kadai damar da nake da ita
wacce
zan gwada tsantsar iyakar jarumtakata kuma a
yanzu
ne takobina za ta sami damar shan jini mai yawa
ta
more,amma gashi ka hana.Ina mai rokonka don
darajar iyayenka da kakanninka wadanda suka
shude kayi mini izini yanzun nan naje na kimtsa
cikin gaggawa ayi wannan tafiya dani.Ka tuna
cewa
ni kaina jarumtakata ta ninka ta marigayi sarki
Ruguzan sau uku,bare kai kanka.Ai abin kunya ne
ma ace kaine da kanka zaka tari Siyama ka
yaketa,ni
ya kamata ka barni da ita a matsayina na 'ya
mace
kamarta nayi mata kisan gilla na ciro kanta nazo
maka dashi.Lokacin da Husaira tazo nan a
zancenta
sai mahaifiyarta ta shara mata mari ta dubeta a
fusace tace,yanzu ke dama manufarki kenan,ashe
ban sani ba?Wato zuciyarki ta kekashe ta zama
irin
ta ubanki kin gadoshi da rashin imani da tausayi
alhalin kina matsayin 'ya mace wacce nake son
tayi
aure ta bar mini zuri'ar dazanyi alfahari da ita
mai
farin jini a cikin al'umma?Koda Larisa tazo nan a
zancenta sai Husaira da Sarki Darwaz suka duni
junansu suka bushe da dariya.Husaira ta hade rai
ta
dubi Larisa tace yake ummina ki sani cewa kyan
'da
ya gaji ubansa,idan mai mulki yana son ya sami
karfi da biyayyar talakawansa dole ne ya kasance
mara tausayinsu.Ni SARAUNIYAR GOBE ce wadda
take da burin dama yafi na mahaifinta don ni so
nake na mallaki duk kasashen dake nahiyar nan
gaba daya su zamo a karkashin mulkina.Koda jin
wannan batu sai Sarki Darwaz da Larisa suka
kurawa
Husaira idanun cikin tsananin kaduwa da
mamaki,daga can sai Sarki Darwaz ya bushe da
dariyar farinciki yace,tabbas yaune na san cewa
banyi haihuwar banza ba tabbas na sami irin 'yar
dana dade ina mafarkin samu.Koda gama fadin
hakan sai Sarki Darwaz ya rungume Husaira cikin
murna yana
A*H PHYSICIST
maicewa,jeki ki shirya yake 'yata
lallai tare dake zamu tafu wannan gagarumin
yaki.Kafin Sarki Darwaz ya gama rufe bakinsa
tuni
gimbiya Husaira ta ruga izuwa cikin turarkata.Ita
kuwa Larisa saita durkushe a kasa ta fashe da
kukan
bakinciki.Ko kallonta Sarki Darwaz baiyi ba ya
gama
shirinsa ya zuba dukkanin makamansa na yaki a
jikinsa sannan ya fice daga cikin turakar ya bar
Larisa a zaune a kasa dirshen tana rusa
kuka.Wannan shine abinda ya faru a cikin birnin
Kisra bayan Siyama ta sami nasarar kashe Sarki
Ruguzan da kyar da sidin goshi domin ta kawo
karshen mulkin zaluncin da yakeyi a nahiyar
harma
jama'arsu su sami damar gudanar da rayuwarsu
a
cikin daji a kwanciyar hankali.Abinda bata sani
bashine ALLURA TA TONO GARMA,domin babu
wani
sauki talakawa zasu samu face karin
matsawa,talauci
da fatara wacce sai sun gwammace mutuwarsu
akan
rayuwars a doron kasa.Kuma ta tsokano tsuliyar
dodon daya shafe shekara da shekaru a kwance
yana faman shara barci kuma ta kulla gabar da
ba
a
san ranar karshenta ba.
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
AL'AMARIN JARUMA SIYAMA KUWA,lokacin da ta
samu ta fice daga cikin gidan sarautar sarki
Ruguzan
tayi ta gudu a cikin daji har ta isa inda ta bacewa
dakarun birnin Kisra,ashe cikin wata korama ta
shige
tayi nutso izuwa karshenta ashe akwai wata
barauniyar hanya a kasan koramar nan wacce ta
bulle har izuwa cikin wani kogon dutse wanda
yake
a cikin wani daji daban dake nesa sosai.Koda tayi
doguwar ninkaya a kasan koramar ta tabbatar da
cewar ta iso cikin wannan kogo sai ta taso izuwa
saman ruwan ta shaki numfashi kuma ta tsaya ta
dan huta sannan ta cigaba da tafiya a cikin
ruwan
har saida ta iso karshen katon kogon dutsen ta
cikin
wani dan karamin rami wanda mutum bazai taba
tsammanin cewar za'a iya ficewa ta cikinsa ba.
Tana fita daga cikin kogon ta tsinci kanta a cikin
wannan katon daji wanda tace jama'arta su
jirata.Nan take ta kama waige waige da kalle
kalle
cikin tashin hankali tana zargin ko wani abu ya
sami
jama'arta ne?Nan take tayi wani irin fito na
inkiyar
da sukeyi a daji a duk sa'adda suka shiga daji
farauta a yayin da suka hango dabbar da suke
son
kamawa.Bisa mamaki sai taji an amsa mata da
irin
fion nata sai ga wani babban hadimi na
mahaifinta
ya fito daga cikin wanu surkuki daya buya ya
dubeta
cikin murna ya yafito ta da hannu.Cikin farin ciki
ta
ruga izuwa wannan hadimi shima ya juya ya ruga
izuwa wani bangare dabam na dajin.Saida sukayi
tafiya mai tsawo tana biye dashi taga an shiga
wani
sakon daban wanda ma bata taba shigarsa ba sai
taga dajin ya zamo sabo a wajenta.Kwatsam sai
ta
an shigo da ita wani sabon tafkeken kogon dutse
wanda ya akai girman gari guda wanda bata taba
sanin wanzuwarsa ba a cikin dajin.Shidai wannan
kogon dutse a karkashin wadansu dogayen
bishiyoyi
yake masu manya manyan ganyaye wadanda
suka
lillubeshi babu yadda za ayi mutum yaga wannan
kogon dutse face ya ture ganyayyaki da
bishiyoyi.Suna shiga cikin kogon sai Siyama tayi
arba da gaba dayan mutanen kabilarsu mazansu
da
matansu,yaransu da manyansu.Shugaba Sharwan
ne
kadai a tsaye,amma kowa a zaune yake a kas sun
jeru sahu sahu kuma duk sunyi shiru tsit tamkar
babu mai rai a cikinsu.Koda aka ga shigowar
Siyama
cikin kogon dutsen sai kowa ya kamu da tsananin
farinciki.Nan take Sharwan ya ruga gareta suka
rungume juna yana mai cewa ni san cewar sai kin
dawo a raye gareni.Jikina ya bani cewar bazaki
mutu ba yake 'yata abar alfaharina.Cikin tsananin
farin ciki Siyama ta janye jikinta daga cikin na
Sharwan ta dubeshi cikin mamaki tace,yakai
Abba
yaya akayi ka amince da duk abinda na umarceka
da ayi a cikin wasikata.Kuma yaya akayi kuka
gano
wannan boyayyan kogo inda Dakarun Kisra
bazasu
taba ganowa ba?.Koda jin wadannan tambayoyi
sai
Shugaba Sharwan ya bushe da dariya sannan
yace
yake 'yata kiyi sani cewa ba wani abu bane yasa
na
bi duk umarnin da kika bani ba acikin wasikar taki
ba face na yarda da kwakwalwarki gami da
tunaninki
da hankalinki baki taba shirya wani abu ba wanda
aka kasa samun nasara ba.Dalilina na biyu
wanda
shine ne mafi muhimmanci shine bamu da wani
zabi na samu tsira daga sharrin Sarki Ruguzan
face
mu yanke hukuncin kashe shi kuma muyi hijira ta
zuwa wani dan lokaci kafin a sami sauyin Sarki
mai
adalci...Saidai Kash!Mun saki reshe mun kama
ganye domin sarkin daya hau karagar mulkin
Birnin
Kisra a yanzu masifarsa da bala'insa sun ninka
na
Sarki Ruguzan sau goma.Samun azzalumin sarki
kamarsa a duniya sai an tona.Nidai a sanina
Sarki.Darwaz wanda ya kasance yaya ga Sarki
Ruguzan ya tafi wata nahiya dabam ya tare a
cikin
daji yana farauta kuma yace bazai dawo gida ba
sai
bayan shekara ashirin,ashe ya dawo birnin Kisra
babu shiri sakamakon wata rashin lafiya da
dan'uwan sa Sarki Ruguzan yayi bara.Ina mai
tabbatar miki da cewar a duniya babu abinda
Sarki
Darwaz yakeso sama da dan'uwansa Sarki
Ruguzan
don haka duk yadda zai yi yaga ya dauki fansar
ran
Ruguzan a kanmu sai yayi don haka nasan cewa
da
kansa zai jagoranci dakaru ya fito
farautarmu.Dole
ne yanzu muci gaba da tafiya dare da rana babu
sassauci,kuma dole ne mu kiyaye shiga cikin
biranen kasar nan face mun tura 'yan leken
asirinmu
sun gano halin da birnin yake ciki ta hanyar batar
da
kamanninsu izuwa matsayin 'yan gari.Ba zamu
taba
samun kwanciyar hankali ba face mun ga mun
fita
daga cikin wannan nahiya gaba daya.Yake 'yata
inason ki sani cewar muna cikin tsananin TSAKA
MAI WUYA dole ne muyi niyar yaki da dukkanin
karfinmu da ranmu kodai mu tsira ko kuma a
shafemu daga doron kasa gaba daya.Lokacin da
shugaba Sharwan yazo daidai nan a jawabinsa
sai
hankalin Siyama ya dugunzuma ainun fite da ko
yaushe.Nan take idanunta suka ciko da kwalla
tace,yakai Abbana ka yafeni kai da dukkan sauran
jama'armu hakika na jefamu a cikin masifa.Koda
jin
wannan batu sai Shugaba Sharwan yayi
murmushi
yace yake 'yata kiyi sani cewa baki da wani laifi a
wajenmu domin kokin yi abinda kikayi ko bakiyi
ba
sai mun shiga cikin wannan tashin hankali da
masifa
tunda tuni Sarki Ruguzan ya jefamu a cikin
wannan
tafarki.Inason ki kwantar da hankalinki kuma ki
tattauna da dukkan dakarunmu domin mu san
hanyar da zamubi mu kare kanmu harmu sami
nasarar fita daga cikin wannan nahiyar gaba
daya.Yanzu ba baku rabin sa'a kacal ku gama
dukkanin shirinku domin mu cigaba da
tafiya.Koda
jin wannan batu sai Siyama ta kirawo gaba dayan
dakarun nasu suka taru a gabanta,a sannan ne
taga
su Muzaru ashe tuni sunzo sun riski su Shugaba
Sharwan.Saida Siyama da dukkanin Dakarunta
suka
shafe rabin sa'a cif sannan suka kammala
dukkanin
shirye shiryensu,nan take akayi wata dabara aka
lullube jikin kowa da koren ganya,hatta dawakai
da
dabbobi saida aka lullubesu da ganyaye yanda ko
kada ba a ganin jikinsu sannan aka fito daga cikin
kogon dutsen aka ci gaba da tafiya,mata suka
goya
yara kanan,su kuma tsofaffi da miskinai matasa
suka
goyasu a bayansu akayi ta tafiya cikin sauri sauri
gudu gudu.A ko yauhse dakarun da suka kware a
iya leken asiri suna kan gaba sai sunyi tafiya mai
nisa sun tabbatar da cewar babu wani mugun
abu
a
gabansu sannan suke dawowa su bayar da
umarnin
a cigaba da tafiya.A bayan tawagar kuma a ko
yaushe wadansu dakarun leken asiri ne suna
bazuwa gaba da yamma,kudu da arewa don
tabbatar
da cewar ba wanda ya biyo sawunsu.Haka dai
aka
ci
gaba da wannan tafiya ba dare ba rana har
tsawon
kwana uku ba tare da an gamu da wani mugun
Abu bà.
★GUDÛN TSIRA★
Littafi Na uku (3)
Part B
★A-H Physicist★
Ba tare da an gamu da mugun abu ba kuma duk
sa'adda aka gaji ko lokacin barci yayi sai a nemi
wuri mai huduwar gaske mai
hadarin gaske inda baza a taba zaton cewa wani
abu
mai rai ba zai iya shiga wajen ba,sai a shiga a
kwakkwanta.A safiyar kwana na ukun ne suka
hangi wani babban Birni wanda ake kira
MADINATUL
SULTAN a can gaban dajin da suke,tazarar
dabata
wuce ziri'a dari da sittin ba.Koda hango wannan
birni na Madinatul Sultan sai kowa ya cika da
farin
ciki musamman Shugaba Sharwan.Nan take
Sharwan ya dubi Siyama cikin murmushi
yace,yake 'yata ki sani cewa mun iso birnin
Madinatul Sultan
inda zamu iya hutawa har tsawon kwana uku a
cikin
kwanciyar hankali kuma mu kara hada guzuri mai
kyau mu ci gaba da tafiyarmu.Koda jin haka sai
Siyama tayi ajiyar zuciya sannan tace,yakai
Abbana kayi sani cewa nikam bani da kwanciyar
hankali a
duk inda zamu shiga,ina mai shawartarmu damu
hakura da shiga cikin birnin Madinatul Sultan
kawai
mu kewaye ta bayan birnin mubi ta cikin daji mu
ci
gaba da tafiyarmu.Yayin da Sharwan yaji wannan
batu sai ya girgiza kai yayi murmushi sannan
yace,shin kin manta ne cewar shugaban da yake
mulkin birnin madinatul Sultan abokina ne kuma
aminina?Tun muna yara kanana muka saba a daji
wajen farauta saboda shakuwar da mukayi dashi
ne ma na bashi 'yar kabilarmu guda daya ya aura
a
sirrance ba tare da Sarkin Kisra ya sani ba.Akwai
amana da alkawari mai girma a tsakaninmu
dashi,ai
na tabbatar da cewa baza a hada baki dashi ba a
cutar damu ba,kuma ko me ake ciki ma ai yanzu
mun baro dakarun kisra a can bayanmu,koda an
aiko manzon sai mun rigashi isa birnin Madinatul
Sultan bare batun dakaru masu yawa wadanda
zasu
dana tarkon cutar damu.Siyama ta numfasa tace
na yarda da duk abinda ka fada ya Abbana.Bazan
hanamu shiga cikin wannan birni ba,amma kafin
mu
shiga din inason ka fara aikawa da manzo a
sirrance
yaje ya gana da Sultan ya sanar dashi duk halin
da muke ciki,idan har yace mu shigo cikin birnin
nasa
sai mu shiga tunda dai mun bashi amanar
kanmu.Koda jin wannan batu sai Shugaba
Sharwan
yayi murmushi yace,tabbas nima na gamsu da
wannan shawara.Nan take aka tashi wani
kwararran dan leken asiri wanda ake kira da
Jamar yayi shiga
irin ta fataken birnin Kisra aka bashi dukiya da
dakaru kimanin mutum arba'in bisa keken doki
suka
durfafi birnin Madinatul Sultan.Suma dakarun
nasa
gaba daya shigar irin dakarun Birnin Kisra
sukayi.Lokacin dasu Jamar suka iso kofar birnin
Madinatul Sultan basu fuskanci matsalar komai
ba
don ana ganinsu aka bude musu kofa ko cajesu
ba
ayi ba suka kunna kai cikin birnin,sukayi ta tafiya
basu tsaya a ko ina ba har saida suka iso kofar
fadar birnin.Suna zuwa aka yi musu iso suka
shiga cikin fadar suke zube a gaban Sultan suka
kwashi
gaisuwa.Sultan ya dubesu cikin alamun mamaki
yace yaku wadannan bakin fatake ku gabatar da
kanku domin ban sanku ba daga cikin fataken
dana
saba yin mu'amala dasu ba daga Birnin Kisra
ba.Koda jin wannan batu sai Jamar ya zura
hannunsa a cikin aljihu ya dauko wata wasika ya
bayar a mikawa Sarki Sultan.Koda Sarki Sultan
ya
warware wasikar ya karantata a gaban
fadawansa
sai
ya kamu da tsananin farinciki ya mike tsaye da
sauri
ya rungume Jamar yana mai yi musu lale
marhaban
tamkar yaga 'yan uwansa na jini.Al'amarin daya
daurewa 'yan majalisarsa kai kenan.Nan take
Sarki
Sultan yasa aka kai su Jamar masauki mai kyau
aka
kawo msu abinci da abin sha mai rai da
lafiya.Kafin
ma su fara cin abincin sai ga Sarki Sultan da
kansa
yazo har cikin turakar da suke,dakarunsa na take
masa baya.Nan take ya sallami dakarun nasa
yace
duk su kama gabansu su bashi wuri yana son ya
gana da bakinsa.Nan take kuwa dakarun suka
fice
daga cikin gidan suka barshi tare dasu
Jamar.Suna
gama fita Sultan yasa aka rufe kofar turakar da
tagoginta don kada ma iska ta dauki sautin
zancen da zasuyi takai izuwa kunnen dakarun
nasa.A
sannan ne Sarki Sultan ya dubi Jamar yace,Ya
kai
wakilin babban aminina,kayi sani cewa lallai
rayuwar
kabilar Banu Hanzar tana cikin tsananin hadarin
gaske domin tuni wani aljani yazo da sako daga
sabon sarki na Kisra cewar da zarar kun iso
Birnina
na sa a kamaku gaba dayanku a tsare a kurkuku
har
Sarkin yazo ya riskeku.Tuni na karbi wannan
sako
kuma na tabbatar da cewar zanbi umarni a
zahiri,amma a badini nayi watsi da umarnin Sarki
Darwaz domin irin amanar dake tsananina da
Shugaba Sharwan bazata barni na bari a cutar
daku
ba.Tuni wannan aljani ya juya da nufin ya koma
wajen Sarki Darwaz ya sanar dashi cewa ya isar
da sakonsa a gareni,amma sai na tura wani
babban
hadimina wanda yafi aljanin karfin damtse dana
sihiri
ya bishi a baya ya tsafanceshi ya kulleshi a cikin
wata kwalbar sihiri domin kada ya ganku akan
hanya yaje ya tona muku asiri a riskeku a kawar
daku.Yanzi ina son ku bari sai dare ya raba
sannan
kuje ku shigo da mutanenku izuwa cikin garin
nan.Hatta masu gadin kofar birnin nan zansa a
sauyasu a cikin daren nan na yau na zuba
yardaddu
a kan aikinsu.Idan ku ka shigo zan rana muku
dukkan kayayyakin daya kamata domin ku saje da
jama'ata domin ku sami damar tanadar da
guzurin
da kuke bukata ku kammala dukkan shirinku
sannan ki ci gaba da tafiyarku harku cimma
burinku na fita
daga wannan nahiyar gaba daya.
Ina mai tabbatar muku da cewar sai kun bar
birnina da kamar
kwana
bakwai sannan su Sarki Darwaz zasu iso kuma
duk irin binciken dasuyi bazasu taba gano cewar
na
baku mafaka a birnina.Lokacin da Sultan yazo
nan
a
zancensa Sai farinciki ya lullube su Jamar suka
zube kasa suna yi masa godiya.Kamar yadda
Sarki
Sultan ya shirya kuwa haka al'amarin suka
kasance
wato saida dare ya raba san
nan aka sauya nasu gadin birnin na Madinatul
Sultan sannan akaje aka shigo da kabilar Banu
Hanzar gaba dayansu izuwa cikin birnin a
sirrance
ba tare da kowa ya sani ba bayan an yi musu
shiga
irinta mutanen birnin.Siyama da mahaifiyarta da
shugaba Sharwan kuwa har cikin ainihin turakar
Sultan aka kaisu suna yin arba da juna sai Sultan
ya
ruga ga Sharwan suka rungume juna suna masu
fashewa da kukan farin cikin sake saduwa domin
rabonsu da ganin juna a kalla yakai shekara
goma
sha biyar.Sultan ya janye jikinsa daga cikin na
Sharwan a lokacin daya Hango Siyama da
mahaifarta
ya dubi Siyama cikin tsananin mamaki sannan ya
dubi Sharwan yace,yanzu wannan Siyama ce ta
girma haka?Sharwan ya gyada kai cikin
murmushi
yace,kwarai kuwa wanna Siyama ce rabonka da
ita
tun tana da shekara uku kacal a duniya,wata rana
sa'adda ka kawo mana ziyara a lokacin da ka
fito
farautarka ta karshe harka daura mata wata laya
a wuyanta kace mu adanata a jikinta har
abada.Yanzu
haka layar na jikinta tun wancan lokacin tana
bata
tsananin kulawa yadda ya kamata.Koda gama
fadin
hakan sai Sharwan ya taka yaje inda Siyama take
ya
zura hannunsa cikin wuyan Rigarta ya janyo wata
siririyar laya dake zagaye a wuyanta wacce
akayita
da hakorin zaki guda daya.koda Sultan yayi arba
da
wannan laya sai ya kamu da tsananin farinciki
sannan ya dubi Siyama yace yake 'yata kiyi sani
cewa asalin wannan laya ta kakana ce wanda ya
haifi
ubana nima gadonta nayi kuma ubana ya
tabbatar
mini da cewar duk wanda ya girma tare da layar
a
jikinsa babu makiyinsa dazai taba samun nasara
akansa.Kuma duk irin tsananin rintsin da mutum
zai
shiga sai dai kawai yasha wuya.Har yau har gobe
ban haihu ba kuma bisa binciken danayi a tsafi
da
wanda matsafa sukayi mini bazan taba haihuwa
ba
a takaice dai har na mutu bazan sami magaji
ba.Mahaifinki yayimini abinda har na mutu bazan
iya
saka masa da komai koda kuwa zan bada raina a
matsayin fansa ga nasa,bisa wannan dalili ne na
sallama wannan laya tawa a gareki tunda kina
yarinya karama,tunda shima bashi da wani 'da a
duniya saike kadai.Rayuwarki taci gabanki har
izuwa
lokacin da zaki gajeshi shine kadai babban
burinsa
a
doron kasa.Ina son mahaifinki yaga wannan rana
da
idanunsa kafin ajali ya riskeshi.Koda Sultan yazo
nan a zancensa sai na take Siyama taji ta kamu
da
tsananin kaunarsa don haka bata san sa'adda ta
ruga gareshi ba ta runguemshi tana mai fashewa
da kukan farin ciki domin ta tabbatar da cewa
basu da
wani masoyi a doron kasa wanda yafi
Sultan.Bayan
hake ne Sultan ya kirawo Matarsa wacce ta
kasance
'yar uwar Ilela mahaifiyar Siyama uwa daya uba
daya wacce ake kira da suna SHAMIRAT.Koda
Shamira
ta
shiga cikin turakar