Showing 9001 words to 12000 words out of 17653 words
Chapter 4 - GUDUN TSIRA LITTAFIN YAKI BY ABDULAZIZ SANI MADAKIN GINI.txt
tayi arba da yar uwarta Ilela
sai
ta cika da tsananin mamaki gami da
farinciki.Lokaci
guda suka ruga suka rungume juna suna masu
fashewa da kukan murna suna kankame jikinsu
tamkar kara aka tsaga,kuma a danginsu su kadai
ne
suka rage.Bisa dole aure ya rabasu suna kuka
kuma
tin daga ranar da Sultan ya auri Shamirat ya
dawo da ita birnin Madinatul Sultan ita da Ilela
basu
sake
ganin juna ba,kuma basu taba zaton zasu sake
saduwa ba,domin a ka'idar dokar Birnin Kisra duk
mutumin da aka bashi mukamin shugabanci na
wani Birni to shida Iyalansa shiga cikin Birnin
Kisra da
dukkan dazuzzukan da suke kewayenta sun
haramta
gareshi.Saida Ilela da Shamirat suka dade a
kankame da juna suna kukan murna sannan
Shamirat ta farga da Siyama ta hangota a tsaye
a can gabansu.Da yake Siyama tana kama da
mahaifiyarta,Shamirat na ganinta ta gane cewa
'yar
suce,don haka sai ta cire jikinta daga cikin na
Ilela
ta
bude hannayenta a lokacin da hawaye ya zubo
mata tana kallon Siyama tace,taho gareni yake
'yata naji
dumin jikinki kafin mu sake rabuwar karshe.Nice
kadai 'yar iwar mahaifiyarki wacce tayi saura a
doron
kasa.Koda jin wannan batu sai Zuciyar Siyama ta
karaya,nan take itama idanunta suka ciko da
kwalla
ta fara zubar da hawaye bata san sa'adda ta
ruga
izuwa ga Shamirat ba suka rungume juna suka
suna
kuka.A'amarin daya baiwa su Sharwan matukar
tausayi kenan suma suka ci gaba da
kukan.Kamar yadda Sultan ya tsara haka duk
al'amarin ya kasance wato saida Kabilar su
Siyama
suka kwana biyu a cikin Birnin Madinatul Sultan
ba
tare da wani dan garin ya fahimci hakan
ba,sannan
Sultan yasa aka shirya musu guzuri mai yawan
gaske,kuma aka nuna musu hanya mafi sirri
wacce zasu fice daga cikin nahiyar gaba
daya.Lokacin da
Sharwan yazo suyi bankwana da Sarki Sultan sai
duk su biyun suka kasa cewa komai suka fashe
da
kuka suka rungume juna.Tsawon 'yan dakiku
suna
kankame sannan Sultan ya janye jikinsa daga
cikin na Sharwan ya dubeshi a lokacin da hawaye
ya
zubo masa yace,yakai abokina kayi sani cewa
wannan rabuwa da zamuyi yanzu ina ganin cewa
itace rabuwarmu ta karshe wadda har abada
baza
mu sake saduwa ba tunda zaku bar wannan
nahiyar tamu ne gaba daya,bansan ranar da zaku
sake
dawowa ba.Wata kila kafin ku sake dawowa bana
raye,wannan hawaye nawa da kaga ya zubo bisa
dalili biyu ne.Dalili na farko shine na SO da
KAUNAr
dake tsakanina dakai.Dalili na biyu kuma hawaye
ne
na takaici bisa zamu rabu alhalin har yanzu ban
sami damar dazan iya saka maka bisa abinda
kayi
mini a baya ba.Koda Sharwan yaji wannan batu
sai
nan take shima hawaye ya zubo masa yace,yakai
Abokina kayi sani cewa bana fatan naga ranar
dazaka saka mini bisa abinda nayi maka a
baya.Kuma ko a yanzu ka gama saka mini tunda
harka bamu mafaka a cikin birninka a irin wannan
lokaci wanda babu wani shugaban birnin dake
karkashin masarautar Kisra yayi kundunbalar
dakayi domin ka siyar da rayuwarka ne Domin
tamu.
★GÛDÛÑ TSÎRA★
Littafi Nà uku ( 3 )
Part C
★A-Haleefah Physicist★
Domin ka siyar rayuwar ka ne domin tamu.Koda
jin wannan batu sai Sultan yayi
murmushi yace ai taku rayuwar itace mafi amfani
akan tawa domin kune kadai zaku iya kawo
sauyin
rayuwa a wannan Nahiya gaba daya,ku kawar da
zalunci ku shimfida adalci.Abokina idan har
hakan
zata tabbata raina fansa ne akan naku.Inason ka
saurara da kyau kaji shawarar dazan baku yanzu
wacce idan karkuyi amfani da ita sai mafarkinku
ya
tabbata gaskiya a wannan Nahiya.Abinda nake
nufi
shine sai sauyi yazi mana an kawar sa zalunci
irin
nasu Sarki Darwaz.A duk sa'adda kuka hadu da
wadansu mutane wadanda suka zo muku da wani
sabon addini to ku yarda dasu kuma ku karbi
addinin nasu.Sa'adda Sharwan yaji wannan batu
shida Siyama da Ilela sai suka cika da tsananin
mamaki.Sharwan ya dubi Sarki Sultan yace,yakai
abokina yanzu kana nufin kenan akwai wani
addini
wanda shine na gaskiya wanda yafi duk Allolin da
ake bautawa a wannan Nahiya,kuma yafi tsafi da
dukkan Aljanun da akayi imani dasu?Sarki Sultan
ya
gyada kai yace kwarai kuwa kuma saduwa da
ma'abota wannan addini shine burina na
karshe.Tuni
na dade da samun labarin wannan addini a wajen
iyayena kuma suma tun suna yara suka sami
labarinsa a wajen nasu iyayen.Da zarar na sadu
da
wadannan mutane zan ajiye tsafi na
rungumesu.Lokacin da Sultan yazo nan a
zancensa
sai Sharwan ya kawo gwauron numfashi ya ajiye
sannan ya dubi Sultan yace,yakai abokina yanzu
yaza ayi na shaida wadannan mutane a duk
sa'adda
na sadu dasu?Sultan yayi gyaran murya sannan
yace zaka iya shaida wadanan mutane ta hanyoyi
guda biyu,hanya ta farko itace yanayin
shigarsu.Ko
yaushe zaka gansu a cikin sutura ta kamala
mazansu da matansu,basu barin tsiraicinsu ya
bayyana ba.Abu na biyu kuma shine sun kasance
mutane masu gaskiya,amana gami da rikon
alkawari.Basu dauki duniya a bakin komai
ba.Babu
abinda suke gudu sama da dukiya da mulki.Koda
jin
wannan batu Sai Sharwan ya girgiza kai yace,ni
kuwa zan sa ido sosai duk ranar dana sadu da
wadannan mutane zan karbi addininsu hanni
bibbiyu
domin kana fadin halayensu yanzu naji na kamu
da
tsananin kaunarsu bisa kyakkyawar
mu'amalarsu,wanda duk wani mahaluki daya
dauki
irinta zai gudanar da rayuwarsa cikin kwanciyar
hankali dajin dadi na har abada.Koda jin wannan
batu sai farin ciki ya lullube Sultan ya rungume
Sharwan yana mai masa godiya sannan ya sake
janye jikinsa daga cikin nasa suka fuskanci juna
ya
ce,yakai abokina kayi sani cewa tafiyar dake
gabanku da kuma hadarin dake cikinta ba kadan
bane domin kafin ku sami damar fita daga cikin
Nahiyar nan sai kunyi tafiya ta a kalla wata
bakwai
da rabi,kuma akwai manyan kasashe guda uku a
gabanku.Wannan birni nawa na Madinatul Sultan
yayi iyaka da wata babbar lasa da ake kira
DARUL
HUNAN.Kafin ku isa iyakar sai kunyi tafiya ta
kwana
arba'in da daya.Indai kuka ketare wannan iyaka
lafiya ba tare dasu Sarki Darwaz sun riskeku ba
kun
tsallake dukkan hadari.Ina ji a jikina cewa abune
mayuwaci ku isa har can su Sarki Darwaz basu
cimmuku ba domin nasan cewa sai sunyi amfani
da
kowacce hanya don ganin sun riskeku saboda da
zaarar sun iso nan Birnina sunga bakwa nan zasu
tabbatar da cewa kun wuce gaba.Tunda bani da
tabbacin zan tsira da rayuwata,ina son ku tafi da
matata Shamirat tunda kune kadai kuka rage
mata
a
doron Kasa.Idan kuka barta anan tare dani Sarki
Darwaz zai iya kashemu tare.Koda jin wannan
batu
sai Shamirat dasu Ilela suka fashe da kuka,shi
kansa
Sharwan bai san sa'adda ya kama kukan
ba.Sultan
ya dubi Siyama yace,yake 'yata kiyi sani cewa sai
kin gaji da wannnan GUDUN TSIRA da kukeyi kinji
kamar ki tsaya a kasheki ki huta,amma inason ki
kasance mai juriya bisa duk irin tsananin da zaki
fuskanta,kisa a ranki cewar dukkan tsanani yana
tare
da sauki.Idan gaba dayan Kabilar Banu Hanzar
zasu
kare ya zamana cewa ke kadai kada ki sare kuma
kada ki cire babban burin dake ranki nason
dawowa
wanna kasa tamu domin kawar da zalunci.Koda
gama fadin hakan sai Sultan yayiwa Sharwan
bankwana na karshe inda matarsa Shamirat ta
rungumeshi suka fashe da matsanancin kuka na
bakin cikin rabuwa.Da kyar yar uwarta Ilela ta
janyeta daga cikinsa,ai kuwa sai Sharwan ma ya
sake rungumeshi ya fashe da kuka yana mai cewa
Abokina bazan yarda na tafi na barka basaidai na
zauna azo a kashemu gaba daya tare ko kuma
mu
tafi tare mu mutu a cikin wannan GUDUN TSIRA
da
mukeyi.Sa'adda Sultan yaji wannan batu na
abokinsa Sharwan sai yakamu da tsananin
tausayinsa ya dubeshi yace,na sani cewa babu
ranar
bakin ciki sama da ranar rabuwa da masoyi,to
amma babu yadda zamuyi da kaddara,haka tamu
kaddarar tazo,babu abinda zamuyi face mu
kasance
masu tunawa da junanmu tare da yiwa junanmu
fatan alkhairi har sa'adda mutuwarmu zata riske
mu,zanji dadi mutukar ka rike wannan a
ranka.Haka
dai Su Sharwan suka yiwa Sultan Sallama suka
tafi
matarsa Shamirat tana waigensa tana faman rusa
kuma ana janye da ita.A lokacin Sharwan da
Siyama
ma suka yi ta waigen Sultan Suna zubar da
hawaye
zuciyarsu na kuna kamar zasu fasa yin tafiyar.A
cikin daren ne su Sharwan suka sake sulalewa
daga
cikin Birnin Madinatul Sultan suka fice suka sake
nausa cikin daji suna tafiya cikin sauri sauri gudu
gudu kamar yadda suka saba ba dare ba rana har
tsawon kwana bakwai.Duk sa'adda suka hadu da
gungun yanfashi ko wadansu mugayen dabbobin
daji sai kaga sun tarwatsasu farat daya sunci
gaba
da tafiyarsu.
¤¤¤¤¤¤¤¤¤
A DAREN KWANA NA BAKWANI NE DA tafiyarsu
Sharwan,Sarki Darwaz ya iso cikin Birnin
Madinatul
Sultan tare da rundunarsa ta yaki,'yarsa Husaira
na
daf dashi bisa kan doki sun jera.Suna isowa kofar
Birnin saiga Boka Hurgas ya baiyana tsulum a
gaban
Sarki Darwaz yana mai kyakyacewa da
dariya.Cikin
fishi Sarki Darwaz ya dubeshi yace da kana ina
muka shafe wannan doguwar tafiyar baka
bayyana
ba sai yanzu alhalin kace kaine zaka yi mana
jagora
a cikin tafiyar?Yayin da Boka Hurgas yaji wannan
tambaya sai yayi murmushi yace ya shugabana ai
tunda aka fara wannan tafiya ina biye daku kuma
ina
muku jagora saidai na baku tazara mai
yawa,domin
na iso nan Birnin tun a kwanaki shida da suka
wuce.Tabbas zuwana da wuri yayi amfani domin
na
samo mana wani labari mai muhimmanci
dangane
da abinda muke zargi.Ko shakka babu shugaba
Sultan yayi wadansu baki daga birnin Kisra a
matsayin yan kasuwa,wato fatake,amma a cikin
kwanaki biyu aka nemesu aka rasa acikin birnin
nan.Bisa bincikena danayi na tura wadansu
zakwakuran hadimaina na aljanu sun bi bayan
wadannan fatake basu gansu ba kuma basu ji
duriyarsu ba.Ya shugaba kasani cewa Sultan
gawurtaccen matsafi ne don sihirin tsafinsa yafi
nawa karfi,Ni abinda nake zargi shine wadannan
fatake da akace sunzo fatauci kabilar banu
Hanzar
ne,kuma Sultan ne ya basu mafaka suka sauka
har
tsawon kwana biyu sannna suka sulale suka bar
birnin nasa.Idan har Sultan yana son ya kubuta
daga
wannan laifi toya gaggauta fada mana inda
wadannan fatake suke ko kuma ya gaya mana
garin
da suka nufa tafi muje mu gansu da
idanunmu.Abu
na biyu shine a bisa binciken danayi kafin mu
baro
Birnin Kisra na gano cewa akwai wata tsohuwar
alaka ta zumunci mai karfi tsakanin Sultan da
shugaban Kabilar banu Hanzar tun suna yara
kanana,sa'adda suke haduwa a daji wajen farauta
Kaga kenan akwai yiyuwar shugaba Sultan zai
iya
taimakon Kabilar Banu Hanzar ta kowacce
Siga.Koda
Boka Hurgas yazo nan a zancensa Sai Sarki
Darwaz
ya fusata ainun har jikinsa ya kama
tsuma,zuciyarsa
kuma ta kama tafarfasa,kawai sai ya yunkura zai
sakarwa dokinsa limzani ya zabureshi da gudu
izuwa Birnin Madinatul Sultan,amma sai Boka
Hurgas ya daga masa hannu yana mai tsayar
dashi.Kawai sai Boka Hurgas ya tsugunna ya
debo
kasar kofar Birnin ya shinshinata kawai yayi
murmushi ya dubi Sarki Darwaz yace,ba shakka
babu mutanen kabilar Banu Hanzar sun shiga
cikin
wannan birnin gaba dayansu don haka duk inda
ma
suke shugaba Sultan ya sani domin naji kamshin
sawayensu a kan wannan kasa.Kafin Hurgas ya
gama rufe bakinsa tuni Husaira ta zare takobinta
ta
sakarwa dokinta limzami ta banke masu gadin
kofar
birnin da karfin tsiya ta kunna kao cikin birnin a
fusace.Ai kuwa sai Sarki Darwaz da sauran
Dakaru
suka rufa mata baya suka bar Boka Hurgas a
tsaye
anan yana ta kyalkyala dariyar mugunta da
farinciki.Kai tsaye Gimbiya Husaira suka durfafi
gidan
sarautar Sarki Sultan.Bisa mamaki suna isa gidan
sarautar sai suka iskeshi a bude wanwar ko masu
gadi babu.A cikin gidan sarautar kuwa gaba
dayan
dakarun suna zazzaune sun ajiye makamansu a
kas,kuma basa shirin tararsu.Koda suka iso
tsakiyar gidan sarautar inda wani badakare yake
sai
suka iske wani mutum guda daya jal a cikin
gagarumar shigar yaki.Koda suka matso daf
dashi
sai sukaga ashe ba wani bane face Shugaba
SultanKoda suka zo dab dashi sai suka ja
Linzamin
dawakansu suka yi tirjiya kuma suka yi masa
KAWANYA.Cikin tsananin fushi Sarki Darwaz ya
dakawa Sultan tsawa yace,yakai Sultan kayi sani
cewa kaci amanarmu ka hada kai da makiyanmu
da
basu mafaka,idan kana son ka tsira da rayuwarka
data iyalanka to ka hanzarta sanar damu inda
kabilar
Banu Hanzar Suke.Koda jin wannan tambaya sai
Sultan ya bushe da dariya,Al'amarin dayayi
mutukar
baiwa su Sarki Darwaz mamaki kenan.Daga can
sai
Sultan yayi shiru ga barin dariyar ya murtuke
fuskarsa ya dubi Sarki Darwaz yace,ko me zai
faru
bazan sanar daku inda Kabilar Banu Hanzar suke
ba
kuma matata tana tare dasu.Yakai wannan
azzalumin shugaba nawa kayi sani cewa ni bani
da
sauran buri a rayuwata face guda daya jal,wanda
ko
ban cika shi ba wadda ta kashe Dan'uwanka
Sarki
Ruguzan sai ta cika mini shi,wato Siyama 'yar
aminina shugaba Sharwan.Na sani cewa zan
mutu
a
hannunku amma ku sani kafin a kashe Gwaggon
Biri
sai yayi muguwar barna.Sultan na gama fadin
hakan
sai ya zare takobinsa ya daka tsalle sama kamar
tsuntsu ya hau dakarun Birnin Kisra da SARA DA
SUKA a saman yana fille musu kawuna tamkar ya
kasance mai fuka fukai,yana shawagi a kansu
saboda
karfin sihirinsa.Koda Sarki Darwaz da Husaira
suka
ga irin mummunar barnar da Sultan yake yi musu
sai suma suka zare takubbansu suka daka tsalle
sama suka tare shi aka ruguntsume da sabon
azababben yaki mai tsananin ban tsoro da ban
al'ajabi.
WAYE ZAI SAMU NASARA A WANNNAN
GAGARUMIN
GUMURZU TSAKANIN SU SARKI DARWAZ DA
SARKI
SULTAN?
SHIN SARKI SULTAN YANA FADUWA KASA
KUWA?
A WANE HALI KABILAR BANU HANZAR SUKE
CIKI?
SHIN ZASU SAMI NASARAR FITA DAGA NAHIYAR
NAN HAR SU HADU DA MA'ABOTA ADDININ
MUSULUNCI SU MUSULUNTA?
SIYAMA NA CIKA BURINTA NA DAWOWA
NAHIYAR
TA KAWAR DA MULKIN ZALUNCI?
YAUSHE ZA'A YI GABA DA GABA TSAKANIN
SIYAMA
DA GIMBIYA HUSAIRA 'YAR SARKI
DARWAZ,INDAN
SUN HADU ME ZAI AFKU A HADUWAR TASU?
WANE IRIN BURI BOKA HUGAS YAKE DASHI A
RAYUWARSA?
Mu hadu a GUDUN TSIRA kashi na hudu don jin
ci
gaban wannan kasaitaccen labari
Amsa:
Su Sarki Darwaz ne suke samun Nasara.
Eh Sarki Sultan yana faduwa kasa.
kwarai kuwa suna samun damar fita bayan sun
sha
wahala har su hadu da ma'abota addinin
musulunci.
Eh Siyama tana cika burinta,amma ba'azo gunba.
Idan Siyama da Husaira sun hadu ana tafka
azababben yaki mai tsoratarwa.
Burin Boka Hurgas ya mallaki Birnin Kisra da
Nahiyar tasu.
Sorry fah na barku kuna ta jira,ba nan ne shi
yasa.
Daga:
GUDUN TSIRA
Littafi na Hudu(4)
Part A
Lokacin da aka rungumtsume da masiffafen yaki
tsakanin shugaba Sultan dasu Sarki Darwas sai
ragowar dakarun nasu sarki Darwaz suka zama
yan
kallo,suka koma kwashe gawarwakin yan'uwansu
suna koma gefe daya.Dama wadannan dakaru
sun
firgita ainun da al'amarin shugaba Sultan saboda
a
cikin abinda bai wuce dakika dari biyu ba ya
kashe
sama da dakaru dari takwas da karfin sihirin tsafi
gami da karfin damtse da kwarewa a iya
yaki.Koda
aka fara wannan baki artabu sai Gimbiya Husaira
da
sarki Darwaz suka gane cewa lallai Sultan ba
karamin jan gwarzo bane,tunda gashi sunyi masa
rubdugu su biyun,amma tsawon dakika dari
dayansu
ya kasa koda lakutar jikinsa.Babban abinda ya
bata
musu rai mashi ne a hakan ma dada zullewa yake
yana ci gaba da saran dakarunsu yana mai ci
gaba
da yin mummunar barna.Koda ganin haka sai
Sarki
Darwaz da Huraisa suka kara fusata ainun suka
kara
kuntata shi.Lokaci guda sai Sarki Darwaz da
Huraisa
suka dubi junansu a sannan suka yi wata
alama,kawai sai suka doki kirjin Sultan da
kafafunsu
lokaci guda.Saboda karfin dukan sai da Sultan ya
fado kasa tim yana aman jini,amma saboda
tsananin
naci da tsananin juriya bai yarda takubban
hannunsa
ba.Cikin zafin nama ya mike tsaye zumbur a
daidai
lokacin da Sarki Darwaz da Huraisa suka duro
kasa
gabansa aka ci gaba da gumurzu.Wohoho,wanda
ya
iya ya huta.Hakika su Sarki Darwaz sun sha
matukar
mamaki,domin basu taba zaton cewa Sultan yana
da
jarumtaka da karfin sihiri a haka ba.Ba wai
tsagwaron karfin damtse ne da Sultan ba,amma
ya
sami tsananin horo na iya yaki gami da tsananin
zafin nama,tabbas ya cika tshoho mai dakawa
yara
gumba.Saida aka shafe sa'a guda da rabi cif ana
fafata kazamin yaki tsakanin Sultan dasu Sarki
Darwaz amma ya zame musu alakakai,kuma
saida
ya samin nasarar fitar da jini a jikin
kowannansu,duk
da cewar suma sun yanke shi,domin a kalla sunyi
masa manyan raunika guda tara.Sakamakon jinin
dake zuba a jikinsa ne jiri ya fara dibarsa ya fara
gigta.Damar dasu Sarki Darwaz suka samu kenan
suka ci gaba da kai masa sara da suka gami da
naushi da bugu da dukkan karfinsu.Nan da nan
suka sami lagonsa ya zamana cewa tun yana
tsaye
saida ya durkushe kasa bisa gwiwoyinsa.Babban
abinda ya fusata Sarki Darwaz shine Sultan yayi
masa wani siririn yanka a kumatu,yayi masa
billen
dole,wanda har abada tabonsa bazai bata ba.Ita
kuwa Huraisa a kan cinyarta ta hagu ya yanketa
kuma wurin yayi dan zurfi dole ne tayi jinya ta
kamar
tsawon kwana uku,tsananin juriya ne da
jarumtaka
tasa taki sarewa.Sultan na tsugune a kasa sai
Sarki
Darwaz da Huraisa suka ci gaba da saran jikinsa
suna sukar cikinsa da takobi yana ihu,jini na
tsartuwa da fallatsi a jikinsa har saida sukayi
fata-
fata da sassan jikinsa.komai rashin imanin
mutum
idan yaga yadda aka daddatsa sultan sai tausayi
ya
kamashi,amma duk wannan abu da akayi masa
bai
mutu ba saboda taurin rai.Ana cikin haka ne Kan
Sultan ya lankwabe kasa ya daina motsi,Sarki
Darwaz da Gimbiya Huraisa suka dubi Junansu
sukayi murmushin murna bisa ganin sun sami
nasarar kashe shi.Kwatsam ba zato ba tsammani
sai
suka ga Sarki Sultan ya dago kansa sama ya
dubi
Sarki Darwaz yayi masa murmushin mugunta
sannan yace,ko ba komai harka mutu billen
danayi
maka bazai face ba daga kan fuskarka dashi a
za'a
binne ka a cikin kabarin ka.Kafin Sultan ya gama
rufe bakinsa tuni Sarki Darwaz yasa takobinsa ya
fille
masa kai.Take Kan yayi tsalle can gefe daya ya
rinka
mirginawa da gudu har saida bango ya tokare
shi,sannan gangar jikin nasa ma ta bingire
kasa.Cikin tsananin fushi Sarki Darwaz yaje inda
kan
Sultan yake ya sunkuya ya dauka sannan ya
mikawa
wani hadimi nasa yace,inason a tsire wannan kai
a
daidai kofar shiga fadata ya zamana cewa,kullum
sai
nayi arba dashi idan zan shiga,kuma ya zamo abu
na farko wanda baki zasu fara tozali dashi a duk
sa'adda suka zo.Hadimin ya risina yace an gama
ya
shugabana.Kawai sai hadimin ya jefa kan Sultan
a
cikin wata jakar fata ya kunshe.Adaidai wanann
lokaci ne Gimbiya Huraisa ta fara dingisa kafarta
ta
hagu wacce ke zubar da jini,kawai kuma sai ta
kasa
daukar nauyin jikinta ta fadi kasa,cikin dimauta
Sarki
Darwaz ya ruga izuwa kanta ya dauke ta ya ruga
izuwa cikin gidan Sarautar Sultan yana mai bada
umarnin a je a nemo babban likitan shugaba
Sultan.Bayan likitan ya gama sawa Gimbiya
Huraisa
magani kuma an dinke raunin saboda yayi
zurfi;sa'a
mata yi kaifin takobin Sultan bai taba kashin
cinyarta
ba.Nan take Huraisa ta kama barci akan gadon
shugaba Sultan dake tsakiyar turakarsa,sakam
akon
maganin barcin da likitan ya bata ta sha.A
wannan
lokaci ne likitan ya mike tsaye daga kan gefen
gadon ya dubi sarki Darwaz cikin alamun
damuwa
yace,Akwai bukatar gimbiya tayi kwana biyu a
kwance tana jinyar wannan rauni nata kafin ta
fara
takawa saboda kyakkyawan motsi ma zai iya
sawa
dinkin ya farke.Koda jin wannan batu sai ran
sarki
Darwaz ya baci ainun,zuciyarsa ta kama tafarfasa
kamar zata kone saboda kin haushin cewar babu
dama a cigaba da wannnan tafiya a yau bare a
hanzarta cimma su Shugaba Sharwan.A daidai
wannan lokaci ne billen Sarki Darwaz ya dameshi
da
zogi har ma yana digar da jini.Koda likta ya lura
da
hakan sai ya shiga tsaida jinin sannan ya dubi
Sarki
Darwaz a tsorace yace ya shugabana akwai
bukatar
ayi masa dinki a kan wannan rauni naka.Cikin
matukar takaici Sarki Darwaz ya ce idan ka dinke
raunin zai fatar da tabonsa har abada?Jikin
likitan
na rawa yace,ai har abada tabon wannan yanka
bazai taba bacewa ba daga kan fuskarka.Kafin
likitan
ya gama rufe bakinsa tuni sarki Darwaz ya
11 hours ago
Abubakar Haleefah Physicist
zaro wata sharbebiyar wuka a kugunsa ya
kirbawa
likitan a cikinsa,kuma ya damki makoshinsa ya
daga
sama da hannu daya a lokacin da yake kakarin
mutuwa yace,kai ne mutum na karshe wanda zai
sake ganin wannan bille.Yana gama fadin hakan
yayi
wurgi da gawar likitan sannan ya bude kofar
dakin
ya kirawo dakaru suka dauke gawar likitan suka
fice
da ita kuma aka goge jinin daya fara zuba a
kasa.Tun a wannan Sarki ya ruge fuskarsa da
rawani,idanunsa kadai ake gani.Nan take yasa
aka
kawo kuyangi guda hudu wadanda zasu lura da
Gimbiya Huraisa,sannan ya fice daga cikin
daki.Yana
fita ya jagoranci wadansu dakarun nasa sukayi ta
yawo a cikin gidan suna bincika cikin
dakuna,lunguna da sako-sako ko zasu ga matar
Sultan,amma shiru ko alamarta babu.Saida suka
bincike ko'ina sannan sarki Darwaz ya hakura ya
koma can falon Sultan ya zauna don
hutawa.Bayan
an kawo masa abinci da abin sha yaci yayi
hani'an
sai ya kori kowa daga cikin falon hatta kuyangin
dake cikin dakin suna jinyar gimbiya Huraisa
kuwa
saida suka fice,sannan ya kullo kofa da kansa
yaje
gaban wani katon madubi ya tsaya.A sannan ne
ya
kwaye rawanin dake fuskarsa yaga billen da
Sultan
yayi masa.Bille ne mai tsawo da fadi,wanda yasa
masa muni,nan take zuciyar Sarki Darwaz ta
kama
tafarfasa kamar zata kone a karo na biyu har
saida
kwallar takaici ta cika amsa idanu.Ba komai ne
yasa
shi zubar da wannan kwalla ba face sani cewa
shugaba Sultan ya karya masa tarihin
jarumtakarsa,domin tunda yake yaki da gumurzu
a
rayuwarsa ba'a taba fitar da digin jini ba a
jikinsa,amma yau gashi ma anyi masa raunin da
indai zai bar fuskarsa a bude kowa sai ya
gani.Sarki
Darwaz ya tuna cewa duk wannan abu daya faru
Siyama ce silarsa tunda inda bata kashe
dan'uwansa
ba da ba zai fito farautarta ba har yayi yaki da
Sultan yayi masa wannan bille.Nan take Sarki
Darwaz yaji ya kara tsanar Siyama fiye da
koyaushe
kuma ya tabbatar da cewar ransa bazai taba yin
fari
ba face a ranar dayaga ya sare kan Siyama
kamar
yadda ya