Showing 1 words to 3000 words out of 17653 words
Chapter 1 - GUDUN TSIRA LITTAFIN YAKI BY ABDULAZIZ SANI MADAKIN GINI.txt
Kundin Masoya
GUDUN TSIRA
Littafi na daya(1)
Part A
AYARI NE NA WATA KABILA wacce ake kira da
BANU
HANZAR.Shugaban wannan kabilar ya kasance
Gwarzon Jarumi kuma sadauki na gaske wanda
ake
kira da SHARWAN IBN KILYIN.Itadai wannan
kabilar
asalinsu sun fito ne daga yammacin birnin Kisra
ya
zamana cewa rayuwarsu taci gaba a cikin zagaya
duniya saboda neman inda tsuro da ruwa
yake,domin kiwon dabbobinsu da kuma
farauta.Masu
bincike da hasashe na wannan zamani sun
tabbatar
da cewa a duniya kaf babu wadansu mutane
wadanda suka lakanci iya kiwo da farauta sama
da
mutanen kabilar Banu Hanzar kuma su dama can
tun farkon rayuwarsu a jeji suke rayuwarsu tun
kafin
ma birnin Kisra ta kafu don haka kabilar Banu
Hanzar suna habaka a yawa kuma gashi suna da
zaratan jarumai gwanayen yaki don haka yan
fashi
ko yan hari suna matukar shayinsu.Lokacin da
kasar
Kisra ta kafu kuma ta gawurta a zamanin wani
azzalumin sarki wanda ake kira da suna
RUGUZAN
IBN MAULAS sai ya fara matsawa kabilar banu
hanzar da biyan haraji mai yawa akan zaman da
sukeyi a cikin yankin kasarsa.Ba komai ne yasa
Sarki Ruguzan yayi haka ba saboda ganin kabilar
ta
banu hanzar take da yawa da kuma zaratan
jarumai,yana tsoron kada wata rana suyi tunanin
yi
masa juyin mulki su karbe masa KARAGAR
MULKINsa.A wannan lokaci Shugaba Sharwan ya
fara
manyanta shekarunsa sun haura sittin kuma Allah
ya
albarkaceshi da 'ya guda daya wata kyakkywar
budurwa ta gaba kwatance mai suna
SIYAMA.Siyama
batafi shekara goma sha takwas ba a duniya
kuma
Allah ya hore mata tsananin jarumtaka da rashin
tsoro fiye da mahaifinta sannan tana da matukar
tausayi gami da jin kan makaskanci.A rayuwar
Siyama babu abinda tafi tsana sama da zalunci
da
azzalumi.Tun da Siyama ta cika budurwa samarin
kabilar sukayi caa?akan neman aurenta amma sai
tayi watsi da kowa tace ita kam bataga gwani
ba.Al'amarin daya dugunzuma hankalin
mahaifinta
shugaba Sharwan kenan ya kirata suka kadaita a
cikin tantinsa da yake su basa gina gida saidai
suka
kafa tantuna a cikin daji saboda basa zama a
waje
daya.Idan sun gama cin gajiyar wannan dajin sai
su
matsa izuwa na gaba dashi.Lokacin da shugaba
Sharwan ya kadaita da Siyama sai ya dubeta
cikin
tsananin damuwa kamar zai fashe da kuka
sannan
yace,yake 'yata inaso kiyi sani cewa ni dake ne
kadai
muka rage a cikin dangin zuri'armu kuma tunda
aka
kafa kabilarmu muke sarauta.Shin ba kya tunanin
cewa idan kika mutu ba kiyi aure ba shike nan
sarautar nan ta bar gidanmu?Koda jin wannan
batu
sai Siyama tayi murmushi sannan ta dubi
Sharwan
cikin nutsuwa tace,Ya kai Abbana inason ka
fahimci
dalilin da yasa bani da gwani a cikin dukkan
samarin kabilar nan tamu.Su duka suna so nane
saboda abu guda biyu,Abu na farko shine saboda
kyawuna.Abu na biyu kuma shine saboda
matsayina
na 'yarka.Duk wanda ya aureno yana ganin cewa
ya
sami damar da zai sami mulkin kabilar Banu
Hanzar
a sama.Na daukarwa kaina alkawarin cewa ba
zan
taba aurar wani 'da namiji ba sai wanda na
tabbatar
da cewat zai so ni SO na gaskiya ba don
kyawuna
ba ko don matsayina ba.Abu na biyu shine bazan
taba yarda nayi aure ba har saina tabbatar
dacewar
kabilarmu tana zaune a cikin kwanciyar hankali
wanda bama tunanin fuskantar wata barazana
daga
sarkin Birnin nan.Sharwan ya dubi Siyama
yace,abinda kika fada gaskiya ne,amma ai bamu
isa
muyi Yaki da sarki Ruguzan ba.Saboda yawan
mayakansa kuma gashi ya kasance Azzamuli
mara
tausayi.Mu kuwa a matsayinmu na kabila kawai
ba
kasa guda ba,babu wanda zai bamu gudunmawar
dakarun yaki saidai ma a kuramu da matsayin
'yan
tawaye ayi mana taron dangi a shafemu gaba
daya.Yanzu dai abinda ya kamata ayi shine,mu
zauna tare da yan majalisata da kuma tsofaffun
kabilartamu domin ayi shawara bisa abinda muke
ganin zai fishshemu.Koda jin wannan batu sai
Jikin
Siyama yayi sanyi tayi shiru batace komai
ba.Kamar
yadda shugaba Sharwan ya fada hala al'amarin
ya
kasance,wato saida aka zauana taron yin
shawara
aka shafe sama da sa'a bakwai ana kace nace
kowa
na fadin albarkacin bakinsa,sai daga karshe wani
tsoho wanda yafi kowa yawan shekaru a kabilar
wanda yaga zamani da yawa ana kiransa da suna
Wamhas ya daga hannu alamar yana son yace
wani
abu,dama shi kadaine baice komai ba tunda aka
fara
taron.Koda shugaba Sharwan ya hango tsoho
Wamhas ya daga hannu sai yayi tsawa akayi tsit
sannan ya baiwa Wamhas umarnin yayi
magana.Wamhasa ya yunkura da kyar saboda
tsufa
yana mai dogara sandarsa ya mike tsaye sannan
ya
fuskanci shugaba sharwan yace ya shugabana
ina
son ka sani cewar Yaki ko Hijira duk bazasu
kubutar
damu ba saboda duk sarakuna na wannan
zamani
basu da wani adalci,azzalumai ne duk inda muka
je
zamu tarar da abinda muke gujewa.Bamu da
wata
mafita face mu nemi sulhu da sarki Ruguzan.Dole
ne mu tashi wakilinmu guda daya wanda zaije
har
fadar Sarki Ruguzan ya kaskantar da kansa ya
nemi
alfarmar ya sassauta mana wannan haraji izuwa
yadda ba zamu rinka takura ba,sannan kuma idan
za'aje gareshi aje masa da kyautar shanu da
tumaki
kamar guda dari dari,manya manya kuma
kosassu.Tabbas idan aka je masa ta wannan siga
a
gaban fadawansa zaiji nauyin yaki amincewa da
bukatarmu musamman daya kasance mutum mai
son abin duniya.Ya shugaba na kai da kanka ya
kamata kaje ka gana da sarki Ruguzan amma
tunda
yanzu bakada cikakkiyar lafiya kamata yayi ka
tura
'yarka Siyama ta wakilceka yin hakan zaisa Sarki
Ruguzan ya dauki abin da muhimmanci.Koda jin
wannan batu sai Majalisar ta rude da kace
nace,wasu suna goyan bayan shawarar da tsoho
Wamhas ya kawo wasu kuma basa goyon
baya.Kawai sai Siyama ta mike tsaye ta tako
kafafunta ta
zo gaban Sharwan ta risina cikin girmamawa tace
Ya
shugabana,Wamhasa ya gama magana,shawarar
sa
itace kadai mafita a garemu tunda idan baka
manta
ba kasha gaya min cewa abinda na gaba ya
hango
na baya ko ya hau kan tsaunin dayafi kowanne
girma da tsayi a duniya bazai hangoshi
ba.Sannan
kuma ance Durkusawa wadai ba gajiya
bane.Sa'adda
Shugaba Sharwan yaji bayanin Siyama sai
hankalinsa ya dugunzuma har ya budi baki zaice
wani abu sai gaba dayan 'yan majalisar suka
rude
da cewa sun amince da shawarar tsoho
Wamhas.Don haka sai ya kasa cewa komai.Nan
take
aka yanke hukuncin kashe gari da safe Siyama
tare
da dakaru arba'in zasu tafi izuwa fadar saki
Ruguzan
dauke da shanu da tumaki dari dari.Kashe gari
kuwa
da sassafe Siyama da dakaru arba'in suka hau
dawakai kuma suka tusa dabbobin a gaba suka
nufi
cikin birnin Kisra.Bayan tafiyar rabin sa'a kacal
suka
iso fada.A wannan lokaci Siyama da dakarunta
duk
sunyi shiga ne da fatun dabbobi.Siyama tana
sanye
da riga da wando na fatar damisa wadanda suka
kasance matsattsu don haka duk suka fito da
kyawun surar jikinta.Babu wani 'da namuji dazai
ga
Siyama a wannan yanayi bai kidime ba saboda
tsananin kyawun kirar da Allah ya bata.Siyama ta
kasance doguwar mace mai madaidaicin kaurin
jiki,wato ita ba siririya bace kuma ba mai kauri
bace.Tana dogon hanci da kuma dan karamin
baki
tamkar da wuka aka yanka mata shi.Kirjinta a
cike
yake kuma kugunta a bude yake,cikinta a shamule
kamar bata ciin abinci.Gashin kanta dogo ne
kuma
baki sidik yana haske da walwali tamkar
madubi.Siyama bata kasance Farar fatar jiki
ba,kuma
bata kasancewa baka ba,ita dai madaidaiciya ce a
haske,.Wani irin launin fata gareta na musamman
mai tsananin ban sha'awa wanda irinsu a duniya
ma
kaf basufi a kirga ba.A wannan lokaci Siyama na
rike
da wani dogon mashi a hannuta,a kuibin cinyarta
ta
hagu kuwa ta daure wata zabgegiyar takobi.Su
kuwa
gaba dayan Dakarun dake take mata baya su
arba'in
sunyi shigar yaki ne suna rataye da Takubba da
Garkuwoyi.Da isowarsu Siyama kofar gidan
sarautar
birnin kisra tare da wadannan dabbobi sai dakaru
suka taresu suka hanasu wucewa akaje aka
gayawa
sarki Ruguzan zuwansu.Jim kadan sai ka manzon
ya dawo,da zuwansa sai ya dubi Siyama
yace,Sarki
yace na kaiku gareshi amma dole ne ku ajiye
dukkan makaman dake jikinku anan sai kum fito
da
kayanku.Koda jin wannan batu sai jikin dakarun
Siyama yayi sanyi kuma hankalinsu ya
dugunzuma
suka rasa abinda zasuyi.Ita kuwa Siyama sai ta
dubesu tayi murmushi batace komai ba,kawai sai
ta
fara mika mashinta sannan ta cire takobinta ta
bayar.Bisa dole suma dakarun suka bayar da
dukkan
makamanus sannan akayi musu jagora izuwa
gidan
sarautar har aka iso cikin fadar Sarki
Ruguzan.Fadar
ta cika makil da mutane duk inda mutum ya duba
saidai yaga kawunan bil'adama fululu,babu
masakar
tsinke.Sarki Ruguzan na zaune akan Karagar
Mulkinsa yana ta nishadi bisa kallon wadansu
'yan
mata dake faman tika rawa,makidansu suna gefe
daya suna ta buga ganguna.Sarki Ruguzan sai
kyalkyala dariyar farin ciki yake domin shi a
rayuwarsa babu abinda yake so sama da
mata.Saboda tsananin son matansa nema ya
kasa
zama da matar aure daya,a shekara daya yakan
auri
mata kala ashirin.Da zarar mace tayi sati biyu ko
uku sai yaji ta isheshi don haka sai ya saketa ya
auro wata saboda da ruwan idonsa.Koda Siyama
da
dakarunta suka shigo cin wannan fadar kowa yayi
arba da ita akaga tsananin kyawunta sai kowa ya
kame.'Yan matan da suke rawa ma sai suka
daina,masu kida suka kasa ci gaba da
kidansu.Shi
kuwa Sarki Ruguzan dimaucewa yayi bai san
sa'adda ya mike tsauye ba ya kurawa Siyama
idanu
jikinsa na Tsuma ko kifta ido ba yayi sai kace
Gunki.
Hmm Nima danake typing ganinta yasa na kame
kam na zuba mata ido,sannan na kasa ci gaba da
rubutun danake.
★GUDUN TSIRA ★
Littafi Na Daya(1)
Part B
★A-H Physicist★
Ko kifta ido bayayi sai kace gunki.har Siyama da
dakarunta suka iso daf da karagar mulkin tasa
suka zube kasa gabansa suka kwashi gaisuwa
bai
iya cewa komai ba.Siyama ta mike tsaye ta dago
kanta sukayi arba ita da Sarki Ruguzan a lokacin
da da fuskarta ya cika da annuri gami da
murmushi mai taushi tace ya kai wannan sarki
mai
daraja gami da cikar mulki kayi sani cewa mu
kabilar Banu Hanzar mun kasance talakawanka
masu rauni da kaskanci don haka mun zone
neman alfarama a wajenka bisa harajin da muke
biya a duk wata guda.
Muna son Sarki yayi mana adalci ya rage mana
kaso biyu daga cikin kaso ukun abinda muke biya
saboda tattalin arzikinmu ya fara lalacewa.Koda
Siyama tazo nan a jawabinta sai Sarki Ruguzan
ya
bushe da dariyar farin ciki a lokacin da yaji wani
irin girman kai ya shigeshi.Lokaci guda kuma ya
hade fuskarsa ya dubi Siyama cikin nutsuwa
yace,yake wannan budurwa ma'abociyar
kyawu.Ke
kuma wacece a cikin mutanen Banu Hanzar kuma
me kuka zo mini dashi wanda zai sa na amince
da
bukatarku?Siyama ta dukar da kanta kasa tace
Sunana SIYAMA BIN SHARWAN 'ya ga shugaban
kabilar Banu Hanzar.Nazo ne bisa wakilcin
mahaifina.Ya shugabana ba komai muka kawo
maka ba face Shanu da Tumaki guda dari dari
kacal don amfanin miyar gidanka.
Bamu da wani abu wanda zamu iya baka amma
muna neman aldalcinka da jin kanka.Koda Sarki
Ruguzan yaji wannan batu sai ya bsue da dariya
a
karo na biyu sannan ya dubi wani babban
hadiminsa yace dashi a kai Siyama da jama'arta
izuwa masauki inda zasu huta kafin ya zauna da
'yan majalisarsa su tattauna dangane da bukatar
datazo masa da ita.Koda jin wannan batu sai
hankalin Siyama dana dakarunta ya tashi suka
fara
tunanin cewa lallai akwai wani abu wanda Sarki
Ruguzan yake so yayi na yaudara a garesu.
Nan take Siyama tayi dan guntun tunani sannan
ta
dubi dakarun nata tayi musu inkiya dasu kwantar
da hankalinsu babu abinda zai faru.Nan take aka
tafi dasu Siyama izuwa wani gida na musamman
inda ba a saukar kowa sai manyan sarakuna da
manyan attajirai.Shi dai wannan gida an kawata
shi ainun ya cika aljannar duniya babu abinda
babu a cikinsa na jin dadi.Da shigarsu suka iske
an kawo masu abinci na alfarma irin wadanda ma
basu taba ci ba sama da kala ashirin an shirya
shi
akan tebur sannan ga kayan shaye shaye ma iri
iri
cikin tambulan- tambulan wanda akayi shi daga
'ya'yan itatuwa nau'i nau'i.Koda ganin wanna
daula
sai dakarun Siyama suka dimauce basu san
sa'adda suka hau kan teburin ba suka dasawa
abincin wawa.Kawai sai sukaji Siyama ta daka
mus
tsawa.
Cikin razana suka mike tsaitsaye suka sunkui da
kawunansu kas.A sannan ne Siyama ta dubesu a
fusace tace shin a tunaninku Sarki Ruguzan zai yi
mana wannan kyau tane a banza?Ku tuna cewa
iyayenmu da kakanninmu basu taba shigowa
gidan
sarautar nan ba fiye da shekaru dari da suka
gabata.Basu taba dandanar abinci mai dadi ba
irin
wannan kuma sunyi zamaninsu tafiya sun tafi.Mu
hakura da irin yanayin rayuwarmu da muka saba
da ita kada a rudemu da dadin duniya a cutar
damu.Na lura da wani irin kallo wanda Sarki
Ruguzan ya dinga yi mini,kallo ne na sha'awa
don
haka idan harma zai biya mana bukatarmu bada
zuciya daya zai taimakemu ba.Lokacin da Siyama
tazo nan a zancenta sai dakarun nata suka shiga
taitayinsu sosai.Babban cikinsu wanda ake kira
da
Ilmar ya dubeta yace,ya shugabata yanzu mene
ne
abinyi kenan?Siyama ta numfasa tace zamu jira
daga nan zuwa yamma muji irin shawarar da
sarki
Ruguzan yayi da jama'arsa.
Idan ban gamsu da ita ba nasan abinda
zanyi.Amma abinda nake so daku shine dayanku
ya zauna a cikin shirin komawa can daji
sansaninmu nan da cikar dakiku kadan bayan na
gama rubuta wasikar dazan bayar a kaiwa
mahaifina.Koda jin wannan batu sai su Ilmar
suka
cika da tsananin mamaki kuma suka kasa gane
abinda Siyama ke kokarin shiryawa.Har Ilmar ya
budi baki zaiyi mata tambaya sai ta daka masa
harara tace kada kuyi mini tambayar komai kawai
ku zamo masu bin umarnina.Tana gama fadin
hakan ta bude jakarta ta fata ta fiddo alkalami da
tauwada gami da takarda ta koma nesa kadan
dasu
Ilmar ta zauna ta rubuta wasika.
Bayan ta gama rubuta wasikar sai ta nannadeta
ta
mikawa daya daga cikin dakarun ya karba sannan
ta dubeshi tace Ya kai Muzaru ka boye wannan
wasikar a jikinka yadda duk duban da za ayi baza
a ganta ba a lokacin da zaka fice daga cikin garin
nan.Lallai ka ruga izuwa sansaninmu ka kaiwa
mahaifina ita a cikin kankanin lokaci kuma ka
bashi wannan wasikar a sirrance ba tare da kowa
ya sani ba.Koda jin wannan batu sai Muzaru ya
risina yace An gama.Nan take Muzaru ya shiga
cikin bandaki ya kimtsa kansa sanna ya fito da
sauri yana fitowa sai Siyama ta dubeshi tace duk
wanda ya tuhumeka dalilin tafiyarka yanzu ka
gaya
masa cewar nice na aikeka wajen mahaifina
domin
ka gaya nasa halin da ake ciki don kar yaga mun
dade bamu dawo ba ya zata ba lafiya.
Muzaru ya sake risina yace An gama.Kawai sai
ya
juya ya fice daga gidan gaba daya da sauri.Kafin
Muzaru ya fice daga cikin gidan sarautar saida ya
ratsa ta cikin kofofi tara,kuma duk inda ya iso sai
an caje ko ina a jikinsa ba aga wannan wasika ba
da Siyama ta bashi,kuma sai an tuhumeshi dalilin
dayasa ya fito shi kadai ba tare da sauran
abokan
tafiyarsa ba,daya basu amsar kamar yadda
Siyama
ta umarceshi sai a bude masa kofar ya
wuce.Yana
fita daga cikin gidan sarautar ya zaburi dokinsa
da
gudun tsiya ya nausa izuwa cikin daji,bai tsaye a
ko ina ba saida ya iso sansaninsu inda suka kafa
tantuna.Tun daga nesa aka hango Muzaru shi
kadai ya dawo daga cikin Birnin Kisra,sai hankalin
kowa ya dugunzuma aka fara tunanin ko wani
abu
ya sami siyama da sauran mukarrabanta.Koda
isowar Muzaru sai ya tsaida dokinsa a daidai
kofar
tantin shugaba Sharwan ya sauka,wani badakare
ya
kama dokin nasa yaje ya daureshi.
Nan take akayi masa iso ya shiga cikin tantin.Da
shigarsa sai ya iske Sharwan tare da mahaifiyar
Siyama a zaune sunyi jugum fuskokinsu a cike da
alamomin matukar damuwa da tashin
hankali.Koda
ganin Muzaru sai mahaifiyar Siyama ta mike
zumbur ta tareshi tana mai rike kafadunsa a
lokacin da idanuta suka ciko da kwalla kamar
zatayi kuka tace,ya kai Muzaru ka gaya mini
iyakar
gaskiya,menene ya faru ga 'yata?Muzaru yayi
dan
guntun murmushi yace,Siyama tana nan lafiya
kalau kamar yadda kuka ganni,yanzu haka itace
ma
ta bani sako na kawowa shugaba,amma tace sai
na kadaita dashi.Koda jin wannan batu sai
shugaba Sharwan ya dubi Matarsa Ilela cikin
murmushi yace barkanmu.Yanzu hankalinmu ya
kwanta.Yake matata bamu wuri na gana da
babban
hadimi Muzaru.Ba tare da gardamar komai ba
kuwa Ilela ta mike tsaye ta fice daga cikin
tantin.Fitarta ke da wuya sai Muzaru ya kwance
kitson kansa guda ya fiddo wata takarda wadda
take a kanannade ya warwareta sannan ya
mikawa
Sharwan cikin sauri kuma hannunsa na
karkarwa.Shugaba Sharwan ya warware takardar
ya
karantata.Yana gama karanta wasikar sai ya
kurma
uban ihu ya durkushe kasa bisa guiwoyinsa.Koda
jin ihunsa sai Mahaifiyar Siyama ta shigo cikin
tantin a firgice,ta rungumeshi sannan ta fashe da
kuka tanace yakai mijina mene ya faru?Shugaba
Sharwan ya dubeta fuskarsa cike da damuwa
yace,yake matata kisani cewa damu da dukkan
'yan kabilarmu muna cikin babban tashin hakali.
A wasikar ta Siyama ta rubuto tace dukkanmu
mu
hada inamu inamu mu bar wannan daji mu kara
gaba,sannan tace mu hadu a wajen wannan
katon
dutsen,so take mu bar wannan nahiyar gaba
daya.Bansan abinda take shirin shiryawa
ba,amma
naji a jikina abin ba dadi,in bamuy da gaske ba
'yan kabilarmu guda daya bazata tsira da ranta
ba.Don haka yanzu mu fara shirye shiryen barin
wannan waje.Koda jin wannan batu sai Ilela ta
sake
kankame Sharwan tana mai fashewa da
matsanancin kuka.
WANE ABU SIYAMA TAKE SHIRIN AIKATA
WA?
ME ZAI FARU A ZAMAN DA SARKI RUGUZAN
ZAIYI
DA 'YAN MAJALISARSA AKAN YANKE WANNAN
HUKUNCI?
KABILAR SU SIYAMA ZASUYI HIJIRA KO ZASU
ZAUNA,IDAN SUNYI HIJIRAR MAI ZAI FARU DASU
A
GABA.
Muhadu a GUDUN TSIRA kashi na biyu don jin ci
gaban wannan kasaitaccen labari
★GUDUN TSIRA★
Littafi Na Biyu (2)
Part A
★A-H Physicist★
A CAN gidan sarautar sarki Ruguzan kuwa bayan
tafiyar Muzaru sai Siyama ta umarci sauran
dakarunta su talatin da tara dasu dauko abincin
guzurinsu dake cikin jakunkunansu su ci.Ba tare
da
gardamar komai ba kuwa suka cika umarnin suna
ji
suna gani suka hakura da wannan abinci mai
dadin
gaske na alfarma wanda aka shirya musu.Itama
Siyama nata abincin guzurin taci bayan sun gama
cin abincin kowa ya kimtsa sai Siyama ta dubesu
cikin nutsuwa tace,abinda nake so daku shine
lokacin da sarki ya turo a kirawoni ku biyoni a
baya
amma kafin mu iso inda zan gana da shi,ku
sulale
ku fice daga cikin gidan sarautar nan gaba daya
ku
nausa daji,zan hadu daku a can Dajin Zamhar
inda
kabilarmu gaba daya zasu yi zaman jiranmu na
tsawon rabin sa'a kacal.Idan har muka wuce
sa'a
daya bamu riskesu ba a can to abu ne mayuwaci
ni
daku ya kasance mun tsira da rayuwarmu.Koda
Siyama tazo nan a zancenta sai hankalin gaba
dayan
dakarun nata ya tashi ainun domin a sannan ne
suka gane abinda take shirin yi.Cikin alamun
firgici
daya daga cikinsu ya dubeta yace haba ya
shugabata saboda me zaki durfafi wuta alhalin
kinsan cewa baki sha maganin konewa ba?
Siyama
tayi ajiyar numfashi sannan tace,ai abinda ya
koro
bera ya fada cikin wuta yafi wutar zafi.Sau tari
sai
mutum yayi kundumbala ya tari fadan da yafi
karfinsa sannnan yake fita daga wata
masifar.Nasan
irin jarumtakarku kuma nasan iyakar irin abinda
zaku iyayi.Ku jajurce duk wuya duk rintsi ku fice
daga cikin garin nan a raye,kada ku damu dani
don
nasan duk yanda zanyi na kare kaina.Ku sani
cewa
daga yanzu mun daura damarar yakin ceto
rayuwarmu data jama'armu gaba daya da kuma
gyara rayuwar 'yan bayan mu don haka ranmu da
lafiyarmu ba a bakin komai suke ba.Siyama ba
gama fadin haka sai suka an kwankwasa musu
kofa.Take Siyama ta dubi daya daga cikin
dakarun
nata tayi masa inkiya yaje ya bude kofar saiga
hadimin Sarki Ruguzan wanda ya kawosu
masaukin
ya shigo da sauri fuskarsa cike da annuri.Koda
yaga
alamar su Siyama basu ci abincin da aka kawo
musu ba sai nan take fuskarsa ta sauya yanayi
ya
dubi Siyama cikin alamun tsananin damuwa yace
yake wannan ma'abociyar kyawu da kwarjini
mene
ne dalilin da yasa bakuci wannan abincin da aka
kawo muku ba alhalin sarki ya karbeku hannu
biyu
a matsayin manyan bakinsa ya karramaku kuma
ya
baku masaukin da yake baiwa sauran abokansa
sarakai.Koda Siyama taji wannan batu sai tayi
murmushi mai taushi ga hadimin wanda ya
kidimashi ya sukurkuce bisa ganin yadda
kyawunta
ya karu ainun tace,yakai wannan babban hadimi
na
sarki ka sani cewa mu mutanen daji ne wadanda
suka saba da abincin 'ya'yan itatuwa da naman
tsuntsaye da dabbobi,bamu saba da irin wannan
abincin naku ba don haka idan muka cishi da
yawa
zai iya lalata mana cikinmu.Yanzu menene ya
kawoka garemu?Hadimin ya maidawa Siyama
martanin murmushin yace,Sarki ne yace nazo na
tafi
dake izuwa inda zaku gana dashi,domin ya gama
zantawa da 'yan majalisarsa.Koda jin haka sai
Siyama
da dakarunta suka mike tsaye suka fito daga
cikin
dakin,amma sai wannan hadimi ya yasha
gabansu
ya dubi Siyama yace,ai ke kadai sarki yake son
gani
don haka dole ne masu tsaron lafiyarki su jiraki a
anan.Koda jin haka sai Siyama ta sake murmushi
tace,ai bazasu shiga cikin dakin da zan gana da
Sarki ba saidai su tsaye a waje.Koda jin haka sai
Hadimin ya juya ya wuce gaba yana mai yiwa su
Siyama jagora suka nausa izuwa wani bangaren
dabam na gidan sarautar,suka rinka shiga loko
loko,sako sako masu kwanoni da lunguna masu
zurfi
wanda komai kular mutum bazai iya dawowa
baya
yabi ainihin hanyar da aka biyi dashi ba,amma
Siyama tana haddace hanyoyin a cikin kanta
tamkar
akan takarda ake rubutasu da alkalami.Saida
sukayi
tafiya mai tsawo sannan suka iso kofar wani
katon
gida mai tsananin fadi da tsawo wanda indai
mutum
ya shiga cikinsa zaiji kamar an jefashi a RIJIYA
GABA DUBU ne.Siyama na ganin wannan gida ta
sake aiyana zargin abinda ta ayyana