Showing 18001 words to 18571 words out of 18571 words
Chapter 7 - Shimfidar Mijina Hausa Novel By Princess Eshat Aysm.txt
ɗaya hankalinsu ya tashi, da gudu Fateema tayi cikin gidan, batasan inda ta nufaba ma, kawai ganin ta tayi tashiga wani fankacecen falo, ashe sashin mahaifin Ahmad taje, da kuka tafara nuna mishi hanya tana cewa "Ahmad".
remot ɗin hanunshi ya ajiye ya ce "ina Ahmad ɗin, yanzu yabar nan".
dakyar ta iya cewa "ya faɗi, yana ɗakina".
Da sauri ya nufi ɗakin, Maryam sai safada marwa takeyi, tayi k'ololuwar ruɗewa, bata ɗauka zai ɗau abun da zafi hakaba, indai hakane Lallai shi yadace da Fateema ba Anwar ba, ɗagoshi yayi yafara hura masa iska a kunne, a hankali ya buɗe ido, ganin mahaifinshine yasa ya fashe da kuka, "Dad inason Fateema, ban taɓa so ba sai ita don Allah kafaɗa mata tadaina mun wannan wasan".
kanshi ya kulle ya dubi Fateema sai kuka takeyi, Maryam ne ta shaida masa abunda yake faruwa, murmushin manya yayi ya ce "haba Ahmad kamar ba namiji ba, ka godewa Allah da yasa angane kafin aure, yanzu dai maganar aure babu shi, kuma kada na sake jin ancemun kayi koda ciwon kai ne".
Kafin gari ya waye har itayen Fateema sunji wannan kwamacalan, 'yan biki kuwa da safe duk suka fara watsewa, kafin kace me zazzaɓi ya kama Fateema da Ahmad, ba k'aramin so Ahmad yakeyi wa Fateema, tanada shiga rai lokaci k'ank'ani, ta iya takunta sosai, abun duniya duk ya ishe gidan, Maryam dai ta kafe akan sai ta tafi da Fateema, Fateema ta kafe ita bazata komawa, ganin haka yasa ta shaidawa Anwar halin da ake ciki, shikam bai iya ɓacin rai ba, haushi ya kamashi, watau batason zama dashi, a tsawace yace abaiwa Fateema wayar, k'in karɓa tayi, ganin haka yasa Baba me yalo ya karɓi wayar akan zai bashi hak'uri, kafin yayi magana Anwar yafara zazzaga ɓacin ranshi, karshen furucin yace basai kin nunawa duniya sakinki nayiba saboda son zuciya, kiyi ta auren ki na SAKEKI saki UKU"....
Baba me yalo ya buga salati, yana faɗin assha, duk fa saida suka kaɗu harda Fateemar, Maryam ranta baisoba don tanason zama da Fateema sosai, tunanin ta ɗaya batasan wata irin kishiya za'a sake kawo mata ba, gashi taji ance maza idan suka ɗanɗani zama da mata biyu basu iya sake zama da ɗaya.
Aranar ta koma gida tabarsu da jimami.
Basai nabaku labarin irin murna da farincikin daya ziyarci Ahmad ba, duk da ance lokacin babu idda akan ta saida tasake sabon iddah.
watanni biyar tsak'ani aka ɗaura auren Fateema da Ahmad, tsantsan soyayya da k'warewa take nuna mishi a matsayin ta na bazawara, shikam ji yake kamar budurwa ya aura tunda dama baisan yaya budurwar takeba.
.
.
.
itakam Maryam tun daga lokacin ta rik'evmijin ta sosai, gyara kuwa tanayi ba kama k'afa, sai tazamto mace ɗaya tamkar dubu, tayi alk'awari bazata sake yin sake ayi mata kishiya ba, dak'yar suka shawo kan Alhaji ya yafewa Hajiya Jamila, yanzu nunawa Maryam so take sosai, kuma zumunci me k'arfi ya k'ullu tsakanin Maryam da Fateema.
.
.
Bayan shekara ɗaya Fateema ta haifo ɗanta na miji, Maryam kuma lokacin tanada ciki amma bansan wata nawa bane.
.
.
.
Wannan shine k'arshen *SHIMFID'AR MIJINA*
.
Wlh *SHIMFID'AR SA*
Yafi komai muhimmanci ki gyara kisha mamaki.
*DUK WANDA YAMUN EDITIN YA CIRE SUNANA ALLAH YA ISA WLH, KOWA YA IYA C&P SAI KUYITA AMFANI DA BASIRAR MUTANE, IDAN SO KAKE KA YAD'A ƁBAN YADDA A CIRE SUNANA BA, AKWAI NOVEL D'INA _SONE AJALINA_ WANDA NAYI AMFANI DA AISHATU SALIHU BICHIKI NAGA ANCIRE SUNANA ANA YAWO DASHI HAKA, TO WALLAHI DUK WANDA YASAKEMUN HAKA BAZAN YAFE BA*