Showing 3001 words to 6000 words out of 18571 words
Chapter 2 - Shimfidar Mijina Hausa Novel By Princess Eshat Aysm.txt
gatan auren ki, idan har baki kula da shimfid'ar sa ba zaki wayi gari kiga ya daina b'are2 akanki, a sannu zaki nemi soyayyar ma ki rasa, kada kiga kina amarya yanzune yakamata ki gyara SHIMFID'AR ki basai lokaci ya k'ure ba, ki jure duk zafin da zaki sha na kwana biyu ne kawai.....
Murmushi tayi ta bank'aro k'irji, nanfa ya dad'a rikicewa, ta zura bakin ta a nashi ta fara jujjuya shi, tuni ya manta da maryam na jiran su, saida suka nutsu ya tuna, tare sukaje sukayi wanka sai shagwab'e masa takeyi yana lallab'a ta.
"muje muyi brkfst Maryam na jiranmu".
Ta ce "Ba yanzu ba bacci nakeji".
ya tsareta da ido ya ce "kinsan k'arfe nawa kuwa, idan kinci sai kiyi baccin".
"To amma bazan iya futa ba kad'auko mun sai
muci anan".
tsintar kanshi yayi da cemata "to".
yana barin d'akin tayi sauri ta saka key ta koma ta kwanta, wayar ta ne ya fara ruri ta tashi ta d'auko, ganin Sakina yasa ta saki dariya ta d'auka.
"Amarya Amarya".
"ke ina wani amarya nasha azaba, wlh dak'yar nake tafiya".
Sakina ta kwashe da dariya ta ce "Kice kin more, kinga yanzu ne ma yakamata ki kula da kanki kada kwana biyu aji kin buga, ki tashi yanzu ki da'au gyanyen magaryan nan ki dafa ki shiga ciki, 30mnt ki fito ki goga man zaitun zakiji kin warware, idan kin gama ki k'irani".
"to k'awata".
kettle ta kunna cikin hanzari ta dafa ta juye a baf, yana d'an hucewa ta shiga ciki harda 'yar k'ararta daga baya kuma tafarajin dad'i yana shigar ta.
.
.
Azaune ya sameta ta rafka tagumi.
"kinsan Allah yarinyar nan bata tashi ba".
binshi tayi da kallo kafin tace "shine ka shanyani kaje kayi zamanka"?
ya lakuce mata hanci ya ce "fanfon toilet d'in tane naji ruwa yanata zuba ashe b'aci yayi da k'yar nasamu na gyara".
Ta sauk'e ajiyan zuciya, ta fara zubawa yace
"ki zuba naki yanzu banajin yunwa sai anjuma zanci".
mamaki ya kamata, ta fara ganin canji har acikin k'wayar idon shi, ta basar ta zuba nata taci ta k'oshi ta wuce d'aki ta barshi, mamakin ta ya k'aru ganin bai biyota ba, ta lek'o shi taga waya yakeyi don haka ta masa uzuri.
ππππππππππ
*SHIMFID'AR MIJINA*
ππππππππππ
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
PML
_We dont just entertain and educate we also touch the hearts of the readers_
.
Writen By Princess Eshat Aysm
.
.
Page 6
.
_K'irk'irarren labarine banyi don cin zarafin wani ko wata ba_
.
.
.
*Nayi mstk naturo page 5 a matsayin 4, yanzu page 6 zan tashi*
.
.
.
.
ya dad'e yana zaune a wajen duk hankalin shi yana kan Fateema, yana so yakai mata abincin kuma baya so Maryam ta d'ago shi.
saida ya shafe awa d'aya kafin ya d'au abincin yayi d'akin Fateema, tana ganin shi ta taso da sauri ta rungumo shi tana dariya, bayan sunci ta d'au dogon hijabin ta tanufi d'akin maryam, a kwance ta tarar da ita da alama tayi zurfi a tunani.
Ta zauna daga d'an nesa da ita ta ce "Aunty ina kwana".
sai a lokacin tasan da shigowar ta, ta amsa fuska a sake ta ce "kinci abincin kuwa"?
"Aunty naci, ba wani aikin da zan miki ne"?
Maryam tayi dariya ta ce "Babu".
shiru sukayi na tsawon mintina kafin Fateema ta ce "zanje na kwanta".
Maryam murmushi kawai tayi ta bita da kallo harta b'ace, ta sauk'e ajiyan zuciya ta koma tayi kwanciyar ta.
.
.
.
Haka zaman nasu yayita tafiya, tare suke aiki Fateema tana girmama ta sosai amma Anwar ya canza mata kwata2, yanzu k'iri2 yake wasu abun wa fateema a gaban ta idan ta gudu d'aki yabita bazata sake ganinshi ba har sai gari ya waye, ranar da yadawo
D'akinta kuwa ko kallo bata isheshi ba, motsi kad'an yace bari na duba Fateema, ganin abun nashi ya fara yawa yazo zai sake futa ta taroshi da sauri, "Anwar meyasa ka canzamun, me kake zuwa yi d'akin fateema a darennan, kai kacemun ba don ka wulak'an tani zakayi aure ba yanzu menene sunan abunda kakeyi"?
Tak'arasa kamar zatayi kuka.
"yanzu idan banda fitina me nake miki, zuwa nake naga ko tayi bacci, wani lokacin bata bacci da wuri".
murmushi tayi ta koma ta kwanta, zuciyar ta kamar zata fashe don bak'in ciki, ahankali ta fara salati aran ta.
jikinshi ne yad'an yi sanyi ya koma kusa da ita ya kwanta, ya jata jikin sa ya ce "kiyi hak'uri".
Hanun ta tasaka a bakin shi ta ce "bakamun komai ba".
Tausayin ta ya kamashi, shi kanshi baisan yana mata wani abun ba.
D'an wasannin daya saba mata yayi bawai yanajin dad'in abun ba, lokacin da ya kusance ta ji yayi kamar ya kurma ihu, (babu magi babu gishiri balle su kananfari da masoro hhhhh lolx).
.
Da wuri ya koma falo yana sallar asuba ya gwammace ya kunna Tv,
bai tab'a sanin kyawun mace ba'a fuska yake ba sai yanzu, shi yanzu ko muryar Fateema yaji yakanji sanyi a ranshi, yana jin yafi sonta fiye da kowacce mace, ashe sha'awa yakan zama so...
Motsi yaji a bayan shi yasashi juya wa, fateema ya gani sanye da kayan baccin ta, tashin ta kenan tayi sallah ta fito, ganin Maryam da wuri take aikin gidan yasa itama ta fito taga oga yau yana d'akin ta, kallon mamaki ta mishi ta ce "meya fito dakai a yanzu"?
Ya mik'a mata hanu alamar taje, ba musu ta k'arasa kusa dashi, wani mayen kallo ya bita dashi yana had'iye yawu, hanun nata ya rik'o ya d'aura a bakin shi, ya saka yatsan ta d'aya aciki yana tsotsa, itadai batayi yunk'urin hanashi ba har ya gaji ya sake hanun ya d'aura ta a cinyar sa yana shak'an k'amshin ta.
"Ina Auntyn na ganka anan"?
.
a kasalance yace "tana bacci".
zamewa tayi ajikin sa ta ce "zanyi aiki, ka koma Ιaki".
Sauk'owa yayi shima yace "tare zamuyi".
Itadai duk mamaki ya hanata magana, gashi tana tsoron maryam tafito tagansu tare tasan ranta bazai mata daΙi ba, gashi bata son tashin hankali ko kaΙan ba'a koya mata ba, tare sukayi aikin sai mammane mata yakeyi.
.
maryam data tashi bata ganshi ba da sauri ta nufo falon taga ko Ιakinsa ya koma, tsorone ya kamata Ζlokacin datayi arba dasu, kukane ya kufce mata ta koma Ιaki da gudu ta faΙa gado ta saki wani kuka me tsuma zuciya.
"me nayi wa Anwar?
Haka maza sukeyi idan sun k'ara aure?
ko kuma asiri ta mishi daga shigiwar shi? Na shiga uku"!
Kuka takeyi sosai tanaso tasan amsar tambayar ta.
.
.
.
To readers wazai amsa mataπ
ππππππππππ
*SHIMFID'AR MIJINA*
ππππππππππ
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
PML
_We dont just entertain and educate we also touch the hearts of the readers_
.
Writen By Princess Eshat Aysm
.
.
Page 7
.
_K'irk'irarren labarine banyi don cin zarafin wani ko wata ba_
.
.
.
*BARKA DA SALLAH GA DUKKANIN D'AUKACIN MUSULMAI TA DUNIYA BAKI D'AYA*
.
.
_JINJINA GA TASHAN FARIN WATA SHA KALLO HAJIYA AISHA INA GODIYA DA IRIN ADDUAN A KIKAMUN KEMA ALLAH YABAKI IKON BUD'E TAKI TASHAR MUSHA KALLO_
.
.
*NIFA BURINA KU GANE SAK'ON DANAKE SO NA ISAR, DUK WACCE BATA GYARABA TA TSAYA LALACI KO KUNYA YA HANATA GYARA SHIMFID'AR TA, NIKUWA NA AURE MIJINTAπ€£π€£π€£π€£*
.
..
..
.
.
.
.
.
Amsa d'aya tabaiwa kanta lokacin data gama kukan ta, watau asiri ta masa, take taji ta tsani Fateema tace shegiya ga ladabin k'arya, (matsalar mu kenan abu ba abuba ace asiri bazakiyi tunanin menene matsalar ki ba, to nidai ku gyara ycn).
.
.
Anwar Kam hankalin shi kwance sukayi aikin su da fateema, dak'yar ta hanashi shiga d'akin ta, shi kanshi bai san dalilin dayasa yake manne mata ba.
k'arfe 9am suka hallara wajen brkfst, fuskar maryam a d'aure kamar zata fashe, dak'yar ta amsa gaisuwan da Fateema take mata, ita kuwa fateema jikin ta ne yayi sanyi ta kasa cin abincin, Anwar yana lura da ita ta kasa cin komai, ya kalle ta ya ce "me yake damunki"?
ta ce "babu komai".
amma kamar zatayi kuka, nanfa ya rud'e, ya matsa da abincin dayake ci ya ce "babu komai a wannan fuskar"?
Ta mik'e zata bar wajen yayi saurin janyo ta, ta fad'o jikin sa, Maryam fashewa ne kawai batayi ba, da k'yar ta mik'e ta fizgo fateema ta sharara mata mari har 2, cikin zafi Anwar ya d'aga hanu zai kai mata marin itama wayarshi tayi
ruri, ya d'aga yaga BILAL ne sannan ya kara a kunne, "Matata na kawo taga amarya kuma naga kaman baku tashi ba".
"Ganinan zuwa". ya fad'a kai tsaye, yayi k'wafa yaja Fateema yakai ta d'akin ta yana bata hak'uri. (ko bkm tasha mari, hahahaha).
.
.
Awajen da yabar maryam a wajen ya tarar da ita sai rusan kuka takeyi, ko ta kanta baibi ba, wani haushin ta yaji yanayi ta dakar mishi mata.
.
BILAL yana ganin shi ya kwashe da dariya ya ce "mijin mace 2".
harara ya watsa mishi ya ce "kafara ko? nafi mijin hajiya tunda nasamu daman k'arawa".
Bilal zaiyi magana ya d'aga masa hanu ya ce "Bari na shigar da ita kafin kafara".
Dariya sukayi kafin yayi gaba Ummulkhairi tabi shi a baya.
.
Still tana wajen bata daina kukan ba, kallo d'aya ya mata ya ce "Ga Maman Fahat".
D'akin Fateema ya nufa, a kwance ya sameta tana waya kamar ba ita ke kuka d'azu saboda zafin mari ba, ya rufa a bayan ta yayi mata rumfa, zare wayar tayi ta kashe tana ajiyan zuciya, "kiyi hak'uri". ya rad'a mata a kunne, "Hak'uri kuma"?
ta tambaya.
"eh". yafad'a yana shafa kanta.
ta ce "Nice nayi laifi, matsalan bata fad'amun laifina ba, kai kuma baka kyauta ba, yakamata ka tambaye ta ko akwai laifin danayi...
hanu yasa ya rufe bakin ta.
.
.
Ummulkairi mamaki ya hanata zama tabi Maryam da kallo, da k'yar tayi shiru saboda abun ya k'ona mata rai sosai, dak'yar ta bud'e baki tana murmushi ta ce "sannu da zuwa momyn Fahat".
"Bazan amsaba Maryam, da girman ki kizauna kina ta kuka"?
"kamawa tayi wlh nima bansan zanyi ba, muje ciki dama inason ganin ki".
.
Ba inda batayi da ita taci abinci ba tak'i, dole ta hak'ura ta d'au fahat ta fara masa wasa, ummulkairi duk tabi ta damu musamman irin kallon dataga Anwar ya mata ta tabbatar ba
lafiya suke ba, gyara zama tayi ta dubeta tace "maryam me yasame ki kike kuka"?
Ta ajiye fahat ta saita nutsuwar ta tace "Ina cikin matsala ummu, kwanan Anwar 8 kenan da aure amma gaba d'aya ya canza mun, abun yakai jiya yadawo d'akina amma wlh gaba d'aya hankalin shi yana can, asuban fari yabar d'akina duk tunani na d'akin shi ya nufa ashe suna nan tare a falonnan".
Wani nauyayyen nufashi ummu tayi ta ce "shine kike kuka a gaban shi"?
"ji nake kamar na mutu na huta, wlh asiri ta mishi ummu, bansan yaya zanyi ba".
Ummulkairi ta dube ta cikin nutsuwa ta ce "Anya kina kula da gidan ki a matsayin abu mafi matuk'ar muhimman ci a gareki"?
"sosaima ummu, banida lokacin kowa sai na gidana dana mijina, burina kullum na faranta wa Anwar, kuma kinsan bana wasa da tsafta".
Ummu ta ce "Ba wannan nake nufi ba, ina nufin ya kike sarrafa rayuwar auranki? ya kike sarrafa soyayyar dake tsak'anin ki da mijin ki, abu na farko me muhimman ci shine mijin ki ya samu nutsuwa dake, saboda samun nutsuwar sa shine naki, duk namijin
da bai samu nutsuwa da matar sa ba, a duk yadda yakai da sonki sai an samu matsala babba da rashin kwanciyar hankali, nutsuwa shine ki kyautata shimfid'ar sa ako yaushe ya kwanta dake ya samu wannan jin dad'in wanda shi zai bashi dukkan wata nutsuwa da kwanciyar hankali, lokuta da dama mu muke cutar da kanmu kuma muzo mufara kuka an asirce mana miji, shikenan mu fad'a neman taimako daga k'arshe mu fad'a hanun bokaye, bawai asirin ne bazata iya miki ba amma nafi so ki gyara abunda kika gaza idan babu canji sai mu koma yi masa addu'a kawai".
Maryam ta cire tagumin da tayi ta ce "na fahimce ki, shi yasa bana b'oye miki matsala ta ummu, sai dai ta yaya zanyi naga ya samu nutsuwar nan, nifa ban tab'a hana mishi kaina ba ko bana so nakan kwanta yayi abunda yaga dama dani".
ππππππππππ
*SHIMFID'AR MIJINA*
ππππππππππ
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
PML
_We dont just entertain and educate we also touch the hearts of the readers_
.
Writen By Princess Eshat Aysm
.
.
Page 8
.
_K'irk'irarren labarine banyi don cin zarafin wani ko wata ba_
.
.
.
.
.
.
.
.
Ummu sai da tayi dariya tace "shi namiji sarrafa shi akeyi kamar yadda yake Ιan miki wassannin nan yana motso sha'awar ki to kema haka zaki mishi, yakasan ce kina cin kayan itatuwa da ganyayyaki, kina yawan cin abinci me Ιan romo2, kidaina amfani da ruwan sanyi ta ko yaya, mace ba'aso tasha ruwan sanyi balle tsarki dashi, kizama kullum kina cikin Ιumi, ki yawaita shiga ruwan gabaruwa da kika dafa da garin lalle da magarya....
Shawarwari tayi ta bata harda irin shigar da zata rik'a yi idan ranar girkin ta yazo, d
sai a lokacin Maryam ta gane Babban sakacin da tayi, sai kiga kina ladabi iya ladabi wa mijinki, kina tsafta kin iya girki, kina kula dashi amma sam baya tausayin ki baya kula dake yanda ya kamata to wannan shine matsala mafi girma a gareki, wasu kuma sun sani amma sakaci da baiwa karatun novels muhimmanci yasa basu taΙuka komai.....
.
.
Saida sukayi sallahr azahar Maryam tana shirin tashi ta nemo musu abunda zasu ci, Fateema ta shigo,
cikin dogon hijabin ta kamar kullum nan kuwa kayan jikin ta tamkar da tsirara ne, Har k'asa ta tsuguna ta gaida Ummu sannan ta dubi Maryam ta ce "Aunty abinci is ready".
murmushi maryam r
tayi tace "ok sannu da aiki".
Mik'ewa tayi tabar Ιakin, Ummu tace "gaskiya kinsamu kishiya yaran yanzu ai sai sufara Ιaga maka kai, kinga ni wallahi tsoron kishiya nakeyi shi yasa bana wasa da *SHIMFID'AR MIJINA*
.
.
.
Sai dare Ummu tabar gidan, Anwar sai mamaki yakeyi ganin yanda Maryam take ta jan Fateema ajiki, ko kaΙan babu alamar Ιacin rai a fuskan ta kamar ba itace tayi ta narkan kuka ba, yadai zuba mata ido kawai yana mamaki, koda dare tayi fateema bata barshi ya shiga Ιakinta ba tasa key, itama Maryam kwanciyar ta tayi zuciyar ta fal da tunanin ta ina zata fara, tana jin shi yashigo tayi kamar tana bacci, wanka yashiga ya gama shirin kwanciya duk tana ganin shi har ya gama yazo ya kwanta a bayan ta, tsoron ta Ιaya kada ya nemi kusantar ta don tasha alwashi sai tagyara komai datayi loosing.
Shi kuwa so yake ya tambaye ta me yasa ta mari Fateema, kuma bayya son tashin ta a bacci, kamar tasan tunanin da yakeyi ta ce "kayi hak'uri da abunda nayi Ιazu".
sosai mamaki ya kamashi ya ce "Dama likimo kikayi? ni kaina kin bani mamaki saboda ganin mace me hankali nake miki ashe.... Juyowa ta tana fuskantar shi, hakan yasa yayi shiru yafara susa kai daya tuna shima ya Ιaga hanu zai mare ta, "sharrin shaiΙanne da zuciya da kuma sharrinka".
ta faΙa tana kallon shi, zaro ido yayi, ta ce "sharrin ka ma yafi yawa, tunda kayi aure ka canza kana wani Ιare2, ina kai zuciya ta nesa, abun yazama kadawo Ιakina ma bazaka barta ba, shiyasa nayi tunanin Bata barka hakaba".
Sosai yagane kuskuren sa, ya janyo ta jikinsa ya ce "kiyi hak'uri maryam, wlh tsintar kaina nake da hakan amma zan kiyaye ki yafemun".
wasanni ya fara mata ta hankaΙa shi ta koma nesa dashi ta ce "kayi bacci kawai".
sororo yayi yana kallon ta ta shige bargo ta barshi, ya lumshe ido yana tuno daΙin da yake sha a wajen Fateema, da haka shima bacci ya kwashe shi, zaman gidan ya gyaru sosai Maryam bata fushi saboda tasan matsalar ta, komai zata gani takan danne zuciyar ta, kuma duk nacin Anwar bata bari ya kusan ceta ranar girkin ta, abun yana taΙa masa zuciya yafara tunanin kodai ta fara k'yamar sa ne,
Tun yana share ta har yafara faΙa amma ko ajikin ta, ta dage da shan duk abun da ya kamata ta daina tsarki da ruwan sanyi, kullum da yamma kuwa sai ta tsiyayi miski da man tafarnuwa tayi matsi dashi, Ummu ta aiko mata abubuwa da dama kuma tana amfani dasu, ita kanta tanajin canji a jikin ta, wani lokacin taji sha'awa ta kamata amma sai ta daure, ita dai nufin ta tana so taji ta matse sosai sannan ta ciko tayi ruwa tayi Ιumi ta zamo cikakkiyar mace me iko.
.
.
.
Matsalar Anwar yanzu Ιaya shine haihuwa, abun ya fara damunshi yana so yaga jininsa, duk inda yaje yaga yara sai hankalin shi ya tashi,
Mahaifiyar shi kullum k'orafi a kan Maryam tak'i haihuwa aure shekara biyu (sai kace ita ke bayarwa kanta).
.
.
.
.
ππππππππππ
*SHIMFID'AR MIJINA*
ππππππππππ
.
.
.
*CLASSIC WRITERS ASSOCIATION*
C.W.A
.
*REALLY MISS YOU PURE MOMENT*
_ALLAH YASA HAKAN SHI YAFI ALKAIRI_
.
.
Writen By Princess Eshat Aysm
.
.
Page 9
.
_K'irk'irarren labarine banyi don cin zarafin wani ko wata ba_
.
.
.
.
.
Tana son Maryam sosai amma akan haihuwar nan duk tabi ta takura mishi akan a duba ta wai ko bata da k'wan haihuwa ne, shi dai bai taΙa nuna wa Maryam abunda yake faruwa ba, shi fatan sa Fateema ta samu ciki tunda Maryam har yanzu shiru.
.
.
Maryam ne da Fateema zaune suna kallo suna taΙa hira jefi2, Fateema tace "Baki zuwa ko inane, ban taΙa ganin kin fitaba".
"ina zanje Fateema, kiwane yake hanani futa".
Fateema ta ce "ko kasuwa baki zuwa, wlh ni nagaji da zama waje Ιaya, don Allah ki tambaya mana muje akwai abun da nake so na saya".
Shiru Fateema tayi kafin tace "duk abunda zaki saya kibaiwa Anwar zai siya miki".
Dariya ne ya kama Fateema ta ce "Akwai abunda zaka siya wanda bazaka so yasani ba".
Maryam tayi jum tana wani nazari can tace "Dama akwai gidan da nake son zuwa, idan munje sai a kaiki kasuwan".
Cikin murna Fateema ta ce "yauwa aunty".
Shiru sukayi na tsawon lokaci can Fateema tasake jefo mata wata tambayar "Aunty Yaushe zamuje gaishe da mahaifiyar Anwar, tunda nazo banga wani nasa yazoba".
Maryam k'osawa tayi da tambayar ta mik'e tace "idan mun futa sai mubiya can, bacci nakeji zan shiga ciki".
Kai kawai Fateema ta Ιaga mata taci gaba da kallon ta.
Ba'a jumaba Anwar ya dawo, da hanzari ta mik'e ta taroshi tana masa sannu da zuwa, hancin ta yaja yace "ina Maryam yau nagan ki ke kaΙa"?
Ta Ιanyi far da ido ta ce "yanzu ta shiga ciki".
yayi murmushi yace "bari na dubata".
Binshi tayi da kallo har ya wuce, taja dogon mumfashi ta zauna.
.
.
A zaune ya sameta tana waya da Ummu, tana ganin shi ta mata sallama ta ajiye wayar, pick Ζ΄ya mata a goshi yace "yunwa nakeji".
"Bakaso gaskiya ba, nasan ,Fateema tana kusa kaje ta zuba maka".
Shiru yayi naΙan lokaci kafin ya ce "Maryam meyasa kika canza ne, na lura kamar baki