Showing 9001 words to 12000 words out of 31629 words

Chapter 4 - KISHIN BALBAL BOOK 2 HAUSA READ NOVELS BY JAMILA UMAR TANKO.doc

matarsa a cikin wani hali ba komai ba ne dan na taimake ta."
Dadi ya kama ni dan na rasa yadda zan yi daman, kudin cefanen nawa dubu daya da dari biyar ne kuma kamata yayi in bashi kamar dubu uku. Sai na yi godiya na shiga cikin get da sauri shi kuma ya ja motarsa ya tafi.
Tanimu bai gane ni ba ya taso a fusace yana yi min tsawa.
"Ke! ke! Daga ina ? Ina za ki je?"
Bana son bata lokaci na sanar masa ni ce. Sai ya bude baki sororo, ya ce " Ah Hajiya daman kin fita ne? Anan muka sha wasan keke da yaranki dazu da yamma."
Na yi ajiyar zuciyar jin dadi na ce " su na ina yanzu?"
Da alama ya yi mamakin tambayar, sai ya ce " ah sun shiga ciki ai."
Na tambaya ko Usman ya dawo?
Ya ce "ai oga Usman tunda asuba ya fice."
Daman sanda na wuce Tanimu yana bandaki bai ga fita ta ba dan haka bai san bana nan ba.
Na rasa in da zan fara nufa shin sama zan hau ko gidan Safiyya da Umma zan fara shiga? In tambayi inda yarana suke. Amma kuma bana so su ganni a haka dan haka na haura sama da sauri.
Kash! Mufidah na ci karo da ita tana sharar matattakala, tunda haka Allah Ya halicce ta, tana da iskar yin shara dare da rana.
Da alama ta razana da ta ganni yanzu a cikin wannan shigar, ni kuwa a duniya ita ce ma bana so ta gani a cikin wannan hali.
Aka hau kallon-kallo, ta qurawa qafafuwana ido. Na bata fuska, raina ya baci, na zo na wuce ta. Ta sake bin qaurina da kallo dan daurin kirji na yi zanin bai sauka ba.
Ina murda qofar falona sai ta budu, na shiga da sauri na kalli falon komai yana nan a yadda na bari, na runtuma cikin dakunana na lelleqa babu kowa.
Na saka wata rigata abaya na jawo hijabi na saka na fito a gigice. Na iske ta, ta gama sharar amma tana tsaye a bakin qofarta tana kallona bata ce min komai ba ban ce mata ba sai harara na sauka qasa. Gidan Umma na so in hau, sai na jiyo muryar yarana a gidan Safiya a dakin Mus'ab su na wasa.
Dadi ya kama ni na nufi bakin qofar da sauri, bugu daya na yi, Safiya ta bude na shiga na iske ita kadai ce a falon. Mu ka hau kallon-kallo fuskarta cike da mamaki. Na tambaya su Ahmad su na nan? Ta gyada kai gami da jero min tambayoyin da ban san amsarsu ba.
Ta ce "ashe bakya gida tunda safe, ni ban ma sani ba, sai da yamma Umma ta ce ga yaran nan zata fita unguwa. Kin yi tafiya ne? Ko wajen Boka kika koma?"
Na wuce cikin dakin da sauri, su na ganina sai suka kwashi tsalle da ihu suka rungume ni. Kukan dadi ya balle min wanda na kasa tsayar da shi.
Na dubi Safiya na yi mata godiya na kwashe su muka fito. An yi musu wanka tsaf da kayansu wakakku. Abin tambayar shine gidana aka shiga aka bincike aka dauko musu wadannan kayan? Dan wadannan kayan sababbi ne a dakina suke a cikin durowata. Shin Safiya ce ko Umma.? Amma na sha kunya dan zasu ga gidan qayau a bushe, falo babu kujeru sannan ko ina a hargitse babu gyara. Me zasu dauke ni? Qazama, ballagaza? Ai da sauqi tunda su ne suka shiga gidan kowa ya san kowa, tunda ba Mufidah ba ce ta shiga ai da sauqi. Ko ma dai me zasu dauke ni sai dai su dauka tunda na dawo na sami yarana lafiya kalau Alhamdulillahi..
Safiya ta rako ni har bakin qofa tana so ta ji amsa amma na kasa magana, na ce ta bani aron wayarta in kira mijina. Babu musu ta miqo min, daman lambarsa ce kadai na haddace a duniya, ina kira wayar ta shiga da alama bai san lambar ba ya dauka. Bayan mun gaisa ya tamabaya wacece? kafin in gama bashi amsa ya gane ni sai ya katse. Na yi ta kira ba amsa daga qarshe ma ya kashe wayarsa gaba daya. Babban tashin hankalina muryar wata mace na ji a gefensa tana ce masa Usman kalli.
Kuma duk gidansu babu mai kiransa da wannan sunan Usman, ko ace Malam babba ko ace masa Baban gida.
Toh, wannan wacece? A ina yake yanzu? Gashi bani da lamar kowa a 'yan gidansu akaina balle in kira a fada min inda ya tafi.
Raina ya baci hankali idan yayi dubu ya taci.
Safiya ta kula da hakan sai ta tabe baki ta ce "tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka. Na baki shawar kin qi ji sai da kika je kika karya mana sirrinmu, mun koma ma dan a Mayar gyara ya kore mu, ya ce baya gaba ya koma baya. Ai gashinan ba mu kadai kika cuta ba har da kanki. Yanzu haka auren stephanie yana daf da mutuwa danginsa da shi kansa mijin sun tisa ta a gaba. Ki duba agogo, qarfe tara ta wuce amma babu Dr.isa babu alamarsa baya dawowa gida sai qarfe sha biyu na dare sannan ya zauna a mota yayi ta wayar soyayyarsa sannan in ya gama ya shigo gida, in na yi magana ya ce mararsa lafiya ne suka kiran shi. Ai ga irinta nan ke ma har kin fi mu shiga masifa tunda 'yan matan sun fara zuwa har gida su na neman mijinki."
Na zazzare ido na tamabaya " mijina kuma?"
Ta harare ni ta ce "Hmmm da yamman nan wata mai.kyau ta shigo nan, ta ajiye tsaleliyar motar ta a wajen get ta ce sunanta Jalilah tana neman Usman ne an ce nan ne gidansa."
Ban san sanda na dire Haidar a qasa ba na zaunar yana ta ihu ban kula shi ba saboda wani gumi ne da kartawar ciki suka hadar min, sai kuma na fara ganin duhu-duhu.
Na laluba hannun Safiya na riqe gamm na ce "Safiya yaya zan yi? Kamar baba gani sosai."
Takaici ya sa ta fusge hannunta ta ce " ki tambayi kanki, kin dauka mu kadai kika yiwa mugunta? Wallahi ba mu ga komai ba ma kamar ma wani kurtun farin jini ne ya fashe musu, mata masu aji daga ko ina sai bayyana suke suna ta binsu. Kin san kuwa Murjanatu Bibi su na waya da mijjna? Hmmm soyayya ma ta qullu saura ke, ke ma na san za ki ji wani labari daga baya."
Na fashe da kuka na ce "Safiya ki fada min gaskiya in kin san wani abu da yake faruwa tsakanin Usman da Mufidah?"
Safiya ta ce " Ah Mufidah ai ta fara daukar ragamar aikin matar gida Usman ma da dadewa. Umma ta ce min yaranki ma a wajenta su ka wuni sai da yamma ta sauko da su."
'Dararam dam' haka na ji wani abu ya tsargo min. Zan sake yin magana motar Dr.Isa ce ta danno kai.
Safiya ta ce "bari in shiga ciki, kada ma ya ganni anan dan gaba muke yi kwana da kwanaki ba ma magana."
Ta tafi ta bar ni a tsaye yara kuwa tuni sun watse su na ta wasa da guje-guje. Na surfa musu zagi na ce su taho mu tafi. Haidar na wawura a fusace na hau sama dan bana so ma Dr.Isa ya fito daga mota ya ishe ni da tambaya. Haushinsa na ke ji , manyan munafukan dinkin duniya wato ya hade da Murjanatu Bibi na san shine ma zai cusawa Usman raayin son Mufidah nan gaba.
Abin takaici muna hawa sama sai yara suka nufi qofar falon Mufida zasu kwankwasa, da na yi kukan kura na cakumo su sai na dura su a cikin baqin falona marar haske.
Budar bakin Ahmad ke da wuya sai cewa 'yan uwan dama mama bata dawo ba, da a gidan Anti Mufida zamu kwana. Gidan ta mai kyau ya fi namu kyau ga haske ga Ac, ga kayan dadi."
Sauran suka "Eh wallahi daman acan ta kwana."
Kash! Sun ci saa bani da kuzari, yunwa ta gama cinye ni da yau sai na yi lugude a kan ruwan cikinsu, amma fa ya sha zagi na ce toh ko zai canza uwa ne ya kaura can.
Da gudu suka watse suka shige daki. Haidar dai nono yake nema, bai san babu komai ba ma saboda ban ci komai ba.
Na laluba na shiga kicin, na kunna kyandir na dafa indomie guda daya da shayi, amma tsabar tashin hankali da gajiya da wahala na kasa cinyewa da kyar na tura na dora da ruwan shayi.
Wannan ita ce baqar rana da na taba haduwa da irinta a rayuwata. Tun daga safe har dare babu alkhairi, sai baqin labari nake ta haduwa da su.
Bayan yara sun yi bacci na shiga na yi alwallah Ina ta jero salloli azhar, la'asar, magruba da Isha'i dan dukka ban yi ba sai yanzu. kuka na ke ta yi wiwi ina fadawa Allah. Shine Ya kaddara min shine Zai yaye min. Amma ina addu'a har bayan raina kada Usman ya qara marmarin auren wata mata ko ya ji yana son wata. Kada Allah Ya nuna min wannan ranar da Usman zai auro wata.
Ban sani ba bacci nake ko suma na yi, ko kuwa a ido biyu ne, ko dai a mafarki ne? Na ga mata kala-kala sun zagaye Usman kowacce tana cewa mijinta ne ni kuma sun tunkude ni a gefe guda. Daga kan gado na rintimo qasa, na tashi firgigit na ji ana kiran sallar assalamu.
"Auzubillahi da wannan mummunan mafarki."
Na fada a bayyane.
Na tashi a gajiye zuciyata baqiqirin na yi sallar assalamu da kyar, na rasa ma abinda zan dafawa yara. Can na hango wasu sauran indomie guda 2 haka na dafa musu suka ci hade da baqin ruwan shayi ni ban samu na ci ba ma. Na yi wanka, na yi musu wanka na ci gaba da safa da marwa a cikin gidan 'kwalam' babu komai.
Na tuna irin rayuwar qasqancin da na shiga jiya har da bara, na tuna yadda na yi sakaci har mata suka fara sinturi neman Usman har gida, abin ya kai har haka mace ta tako gidan aurena tana neman mijina ba zai yiwu ba. Allah Ya yayyafawa abin ruwan sanyi da ta zo bana nan, na tabbatar sai an dauki gawar daya daga cikinmu.
Na tuna yadda Mufidah har ta sami dama daukar yarana ta kai gidanta, ina kyautata zaton ma ita ce ta shigo har cikin dakina ta zabarwa yara kayan da suka saka, ta qarewa gidana kallo ta zuba asirin da zata zuba.
Cabdijam tabbas da sake, lallai ba zan dauka ba, ga kuma Usman din can a Kano tare da wasu matan ma dan na ji muryar wata a kusa da shi. Wallahi ba zaa kashe ni ba, babu sani babu sabo, babu boka babu Malam daga 'yan matan har Usman din na daina ragawa kowa."
Wata baqar kalma ce ta daki kunnuwana daga bakin Nazifi ya ce su zo su je gidan Anti Mufidah su ci kaji kuma ta kunna musu cartoon saboda nan gidan babu dadi.
Sauran suka ce "eh wallahi mu je kawai in mama ta shiga daki."
Na juyo na dube su cikin fushi, da har zan dake su sai na fasa, na san ba yin kansu ba ne yaudararsu aka yi da kayan dadi.
Na shiga daki a fusace na dauko mayafina na yafa na dauki Haidar na ce sauran su biyo ni. Na kulle gidana muka sauka qasa, akan hayar mu ma ta sauka su na hira su na cewa mun zaci ma gidan Anti Mufidah zaa kai mu.
Gidan Safiya na je na buga mata qofa, ta fito a gigice da alama tana cikin damuwa dan idanuwanta face-face da hawaye.
Ta kalle ni na kalle ta, na ce " Safiya ba zan iya daukar wulakanci ba, yau dai zaa yi ta ta qare. Yanzu dai ki ajiye min yaran nan ina zuwa."
Ta tsaya tana kallona cike da rashin fahimta, na dire Haidar a falonta na tura sauran cikin falon na jawo musu qofa na rufe. Wasu su na ta ihu su na kiran sunana na fice da sauri. Safiya dai ta sanqare a tsaye ta kasa fahimta ta.
Sama na koma gidan Mufidah na nufa kai tsaye, na yi mata bugu irin mai firgitarwa. Dan ta san ba alkhairi ba ne ya kawo ni.
A gigice ya fito da alama daga kicin take na ganta sanye da rigar girki (apron) da hular girki da wani takalmi marar nauyi, wai su 'yan gayu komai sai an bi qa'idarsa. Ta sake firgita da ta ga ni ce, musamman yadda nake a fusace. Bana buqatar sai an yi min iso kawai na yi ciki da ita na shiga falon.
Ta qi rufe qofa kuma ta qi shigowa ciki sosai ta na ta bi na da kallo, ina ta kai kawo a cikin falon da takalmi na shiga kuma na taka mata kafet da shi.Ta na ta kallona da alama ta tsorata sai da ta ji abinda take dafawa ya fara qonewa sai ta shiga kicin da sauri ta kashe wutar, ta sake fitowa ta rabe a jikin bango daf da qofar fita tana kallona.
Na tsaya a gaban mudubi da teburin da ke falon, ta jera hotunanta Dana 'yan gidansu, wasu ita da mahaifinta, wasu kuma ita da wannan mutumin da yake yi mata tsawa, da alama dai akwai kyakykywar alaqa a tsakaninsu dan na ga ko ina ita da shi ne.
Na isa zuwa jikin bango na ga wani qaton hoto an manna an rubuta Chief Judge Justis Hamza Dayyab.
Na san fuskar mutumin a talabijin da jaridu shine alqalilin alqalai na qasa gaba daya.
Na tabe baki na fada cikin gatsali na ce "Hmmm ashe shine babanki, Babba 'yar Babba, babba sai dan babba. Ke lauya, Mahaifinki alqalin alqalai na qasa gaba daya, shine kike tunanin za ki taka Fatima Aududu ki kwana lafiya, ko kwana lafiya ko? Qarya ne wallahi, duk da ina 'yar talaka amma na san 'yancin kaina."
Na juyo na sake dubanta duba na takaici na ce "ki na taqama da kudi, ilimi da martabar gidanku dan haka ki na ganin za ki iya siyan mijina da kudi kenan? Ki na ta bibiyarsa a boye, tun ba na yarda har na fara yarda, dan rannan na ga ya shigo gidanki ya zauna a falonki. Kada ki dauka Usman zai iya sonki ko aurenki, ba zai taba iya zama da ke ba dan ba kowacce mace ba ce take burge shi ba musamman ma ke. Baya sonki, baya son ganinki, kuma ya fada miki da bakinsa. Kada ki kuskure ki tafka wannan kuskuren."
Ajiyar zuciya ta yi sai ta saki wani murmushi wanda bai kai zuci ba, ta fara tafiyar taqama. Ta cire hular kanta ta yasar a qasa, ta cire rigar girkin (Apron) ta watsar a tsakar falon, ta girgiza kanta sai gashin kanta ya barbaje ya tashi qaho-qaho ya tsaya, da alama bata yin retouching, natural gashi ne.
Ta bayyana daga ita sai farar shima da wando Jeans iya cinyarta ko guiwarta bai rufe mata ba.
Ta saka qafa ta buga qofar falon ta rufe sai ta sa mukulli ta datse, ta zare mukullin ta bude gilashin windo ta wurga shi qasa.
Wannan karon ji nayi gabana ya fadi na tabbatar itama ta shirya yin fadan dan haka sai na cire mayafina na yi danmara da shi.
Maimakon ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login