Showing 6001 words to 9000 words out of 31629 words

Chapter 3 - KISHIN BALBAL BOOK 2 HAUSA READ NOVELS BY JAMILA UMAR TANKO.doc

Cikin dare Usman ya ce da ni zai tafi Kano da safe, hankalina ya kasa kwanciya musamman ma da bai fada min maqasudin tafiyar ba dan haka na kwana ban rintsa ba.
Da asuba ya tashi ya fara shiri, bayan ya dauki wanka ya caba ado gami da fesa turare mai matuqar qamshi. Zuciyata tana raya min ko dai daurin aurensa zaa yi a boye?
Kudin cefanen da ya miqo min ma ban karba ba sai akan mudubi ya ajiye. Ya kada kai ya yi tafiyarsa abinsa, ya bar ni da takaici a cikin zuciya mai quna.
Bai damu da fushin da nake yi ba, ya tayar da motarsa ya fice. Na zabura na tashi na leqa ta wundo don in tabbatar, idan ya bi hannun dama cikin garin Bauchi zai shiga amma idan ya bi hagu hanyar Kano ne. Cikin rashin saa hannun dama ya bi anan na tabbatar da zargina gaskiya ne.
Na fallo da gudu na sauko qasa na fito bakin titi ina neman dan acabar da zai dauke ni in bi bayansa, kasancewar sassafe ne sai na rasa. Na dinga safa da Marwa a tsakiyar titi tamkar mahaukaciya.
Kwatsam sai ga Usman ya taho motarsa cike da wasu mata. Wata tsaleliyar budurwa ce ke zaune a gefensa babu dankwali balle mayafi.
A guje na tunkari motar saura kiris ta buge ni sai da yayi da gaske ya iya taka burki ya tsaya. Ya na kuwa tsayawa na yi wuf na bude gaban motar na zauna kusa da wannan tsaleliyar budurwa, muka cunkusu. Tana harara ta ina hararrar ta.
Gogan naka bai ce da ni komai ba ya ja mota muka fara tafiya. Hanyar Kano dodar mu ka kama.
Zuciyata tana tsananin quna tamkar wuta ake rura min ci take bal-bal. Babu abinda yake tashi a cikin motar daga ajiyar zuciya sai qwafa, harara da girgiza kai .
Ina juya baya na kalli matan dake zaune su uku, sai na ga ashe ta gaba ma bata da kyau kyawawan na baya har da wata mai zubin larabawa.
Na sake hargitsa na harari Usman, ya harare ni. Da gangan na dinga murtsikewa ta kusa da ni qafa amma sai ta yi sauri ta janye bata tanka min ba. Na saka a raina yau sai na ga qarshen gudun ruwansu, ko lahira zasu je sai na bi su.
Yadda Usman yake fincikar motar yana gudu ka san ransa a bace yake kai ka ce sama za mu tashi, ni kuwa banqi ace motar ta yi quli-qulin kubura da mu ba kowa ma ya huta.
Ba a magana balle a tsaya sallah ko rage mara, tafiya kawai yake yi ba tare da yana kaucewa rami ba.
Wata zazzaqar murya ce ta daki kunnuwana daga gidan baya "direba akwai na wudil kafin ka tsallaka gada, ka ajiye ni.'
Na ji kaina ya cushe tunanina ya wargaje gaba daya, na rasa me take nufi da hakan. Mu na isa wudil ya tsaya a inda ta umarce shi. Kudi ta zaro ta bashi ya bata canji. Sai na ji zuciyata ta yi tsalle sama ta dire .
Nan da nan qirjina ya fara bugawa. Zuciyata ke tambaya "kada fa a ce ba 'yan matansa ba ne, fasinjoji ya dauko."
Mu ka ci gaba da tafi kaina a qasa na kasa hada ido da shi.Daidai wata unguwa da ake kira mariri, ta kusa da ni ta ce "direba akwai na nan."
Ta zaro kudin mutum biyu ta bashi nata da na daya daga cikin 'yan baya.
Ya na tsayawa ta harare ni ta ce " ke dogari zan fita ."
Kaina a duqe saboda kunya na fita sannan ta fice 'yar uwarta ma ta fito, sai suka gwaba min baqar magana kalmar dai ta "a koma makaranta jahilci na damuki."
Bani da bakin ramawa, saura mace daya a motar itama a hotoro ta sauka, da za ta fita sai ta ce "sannu da qoqari direba, ina baka shawara ka wuce da ita gidan mahaukata kawai."
Daga ni har shi babu wanda ya iya magana .
Ya ja mota ya ci gaba da tafiya.
Kamar daga sama na ji wata kakkausar murya mai firgitarwa "ke kuma a wacce unguwa za ki sauka?"
Na dago a firgice na dube shi, fuskarsa babu annuri, ainahin tsana ce ta bayyana.
Cikin rawar murya da in'ina na ce " dan Allah Usman ka yi hakuri na zaci..."
Tsawa ya daka min sannan ya bankada motar gefen hanya kamar zamu afka kwata, ya taka burki ya tsaya.
Ya tambaya " ina yarana?"
Sai a lokacin na tuna ashe na taba haifar yara guda hudu qanana har da me shan nono, su kadai na bari a gidan, qofa kuma a bude.
Na dora hannu akai na rusa kuka na ce " na Shiga uku Usman na manto su a gida su kadai kuma qofar ban rufe ba, dan Allah Usman ka yi hakuri mu juya Bauchi."
Ya sake fusata ya ce "fita daga cikin motata."
Kafin in sake cewa wani abu ya sa hannu ya bude qofar da nake jigine, ya saka qafa ya tunkudo ni waje. Ya ja motarsa ya tafi abinsa.
Ban taba zaton Usman zai iya daukar irin wannan mataki a kaina ba, yadda yake tsoron bacin raina.
Sai a lokacin na dubi shigar da na yi, bani da riga sai daurin qirji da hijab a baibai, takalman qafata kuwa daya kafar silifas ne, dayar kuwa takalmin Usman ne sau ciki.
Duk wanda ya tunkaro ni sai ya yi sauri ya kauce gudun kada in kai masa duka, tabbas su na da gaskiya dan babu maraba ta da mahaukaciy , na yi saranda kawai na yarda na sami tabin hankali.
Rigijigafji ta ina zan fara? Shin gidanmu zan tafi, ko gidan su Usman, ko kuwa gidan qawata, ko kuwa Bauchi zan juya? saboda yaran da na baro ban san ma halinda suke ciki ba.
Ga shi ba ni da waya balle in kira Umma ko Safiya in ce su dauki yaran su riqe min. Ga shi bani da kudin motar da zan koma Bauchin ma kuma ba zan iya shiga gari da wannan shigar ba.
Dan haka ba ni da zabi, kawai sai na fara bara ina cewa a taimaka min da kudin motar da zan koma Bauchi.
Gaskiya almajirai su na kallon ikon Allah, ga kudi nan cusu-cusu a aljihun bil-adama amma dakyar wani zai zaro naira biyar ya miqo ita din ma sai ya nemi kwarababbiya wacce ta kusa rabewa biyu sannan ya miqo. Mai imani kadan shi yake miqo goma mai babban imani shi yake bayar da naira ashirin. Wani kuwa hanci yake toshewa ya wuce. Allah dai Ya rufa mana asiri duniya da lahira, amma na ga wulaqanci.
Na fashe da kuka na yi kuka har na gaji ga yunwa ga qishirwa, babu wanka, babu sallah gashi an dade da yin azahar la'asar ta kusa ban tara naira dari ba.
Tunanin yarana kadai ya ishe ni ban sani ba ko sun bude get sun fita nemana ga babban titi, koma dai mota ta kade su ban sani ba.
Tamabaya nake yiwa kaina "ko me zasu ci? Ina zasu nufa? Wanne irin kuka yau zasu yi in sun tashi sun ga babu uwa babu uba? Haidar mai shan nono ga zazzabi yana yi da gudawa ban san halinda yake ciki ba.
"Innalilahi wa inna ilaihi rajuun" na yi ta karantawa babu wanda ya zalumce ni nice na zalumci kaina na yarda na dauki laifin. Ina tsoron rasa Usman ma gaba daya dan da wuya ya ci gaba da zama da ni, na san mai haquri bai iya fushi ba. Duk duniya babu wanda zai bani gaskiya idan aka mayar da wannan zance. Iyayena sai sun fi kowa jin haushina da yin Allah wadai da ni, yadda suke qaunar Usman suke gode masa ba a taba yin siriki mai mutunci irinsa a gidanmu ba.
Na tashi da gudu na tare wani adaidaita sahu na ce ya kaini tashar mariri, dan babu yadda zai yi na riga na shiga na zauna ba zai iya kora ta ba amma na fuskanci kallon mahaukaciya yake yi min dan na jinm wasu tambayoyi na rainin hankali da yake ta jero min.
"Ke yanzu in an kai ki maririn kin san in da za ki je? Ke wai ma kina da kudin biyana?"
Na amsa masa da "eh ina da kudi kuma na san inda zan je."
Ya ja muka tafi amma fa kowa ya tsayar da mu sai ya fasa shiga, na san kuma qafata suke hangowa da qaurina a waje tabbas babu mai zama tare da mahaukaciya a bayan adaidaita kada tsautsayi ya sa tayi wurgi da shi waje.
Mu ka isa bakin tasha yana tunanin kudi mai yawa na miqa masa, naira casa'in da biyar kudina kenan na miqa masa su ma kuma a yagalgale.
Nan fa fada ya tashi ya dinga kwakwazo "ke kadai fa na dauko shata amma ki bani wannan kudin."
Wani mutum ya zo wucewa ya tsaya, don ya sasanta shine ya cika masa naira dari. Kalmar da ya fada ma kadai ta isa kowa ya waiwayo ya sake dubana.
Ya ce "baka ganin yadda take, kan fa ba daidai ba ne, ka yi mata uzuri mana daga gani ma bata dade da kamuwa da haukar ba, da alama iyayenta ko mijinta basu san ta fito ba ma. Allah Ya bata lafiya kawai."
Mai adaidaita ya ce "ko gidan radio zaa kai ta a yi cigiyar danganta amma gaskiya wannan sabon kamu ce bata yi datti da yawa ba."
Su na cikin wannan shawara na rantuma da gudu cikin tasha, ai shikenan ta tabbata aka dinga kaucea da gudu ana bi na da addu'a Allah Ya baki lafiya.
Fargaba ta guda daya ce ina tsoron kada wani ya dauke ni a hoto ya watsa a social media, ko in hadu da wadanda suka sanni. Ina tafe ina rufe fuskata har na je layin masu lodin Bauchi. Na ce a nuna min direba ina da magana da shi. kallon tara saura kwata suka yi min suka watsar, rashin sani ya fi dare duhu domin da sun gane ni ba zasu yi min haka ba, ni ce dai wannan hajiyar da suke gaisarwa har qasa, take yi musu rabon kudi su na daukar mata akwatuna da gudu. Dan shatar mota ma nake dauka ni kadai daga sai yarana har qofar gida. Yau sai gashi babu wanda ya kalle ni ina ta magana.
Daga baya wani ya daka min tsawa ya ce "ke wai me direba zai yi miki ne kike damun mu?"
Na langwabe kai na ce "kudin motata na baro a gida can Bauchi zai kai ni har qofar gida sai in shiga gida in dauko masa."
Qafata ya fara kallo ya kalli takalmi silifas da cover shoe na maza.
Sai yayi dariya ya ce "kwarai kuwa na ga alamar ya kamata a kaiki har qofar gida daga nan ma sai an hada miki da turu."
Wani daga cikin su ya ce wanne gidan wai take magana, ba Dawanau da take nufi? wannan daga gani ballowa ta yi baa sani ba."
Kamar daga sama na ji wasu mata na magana akaina.
Dayar ta zunguri dayar ta ce "lah kin ga matar direban nan ta dazu da muka zo tare da ita."
Ina juyawa muka hada ido da su sai na shaida su nima suna muka.ajiye a mariri, sai na fashe da kuka na tunkaro su.
Na ce" Bauchi za ku koma har kun gama abinda ku ke yi?"
Daya ta tabe baki ta ce "eh mun gama, kamar yadda ke ma kika gama abinda ya kawo ki."
Su ka wuce suka bar ni sai na biyo su a baya har sun shiga mota sun zauna sai na je jikin windon da suke ina yi musu magana cikin rada na ce "ku taimake ni da kudin mota ko da bashi ne in koma gida na baro yarana qanana babu kowa kuma a gidan."
Wannan karon fusata dayar ta yi ta harare ni ta ce "kuma ina ruwanmu wannan matsalarki ce. A qarshe dai kin ji kunya kuma kin bata alaqarki da mijin da kike yiwa kishi. Kin wulaqanta kanki kin wulaqanta 'yayanki shima kin kunyata shi. Wallahi da na san in da zan sake ganinsa sai na aure shi in ga yadda za ki yi."
Tabbas wannan kalma ta qarshe ta bata min rai, ta fusata ni sai ma na manta da hali da nake ciki gaba daya na rikice.
Na bata amsa na ce "ki auri mijina kamar yaya? Ai mai auren mijina sai ta shirya?"
Dayar ta ce min "ke ki yi shiru ana qoqarin a taimaka miki ki koma wajen 'yayanki har kina da bakin yin fada?"
Mafadaciyar ta ce " waye zai taimaka mata? sai dai ke amma ni ko sisi ba zan bawa wannan ba. "
Sai ga Danjuma direba ya iso yana niyyar kora ta.
Na dube shi a fusace na ce "ba ka gane ni ba ne Danjuma? Mamar Ahmad ce fa da ka saba kai ni Bauchi matar Usman banker."
Ya bude baki yana kallona kawai sai can ya ce "Ah hajiya me ya faru ne haka, lafiya? Innalilahi lafiya kuwa? Mota ce ta fadi da ku?"
Kowa ya bude kunnuwa yana so ya ji abinda zan ce sai na ce "ka kai ni Bauchi kawai har qofar gida zan baka kudin matarka, har ma in qara maka."
Nan da nan ya bude qofar baya kusa da masifaffiyar matar nan.
Ya ce "ki zauna da 'yan uwanki mata a baya shikenan ma motar ta cika a kwai wani a gaba daman."
Na girgiza kai na ce "gara in zagaya wancan gefen ba zan zauna da wacce take qoqarin aure min miji ba."
Na zagaya na zauna a kusa mai mutunci ta na mai yi min nasiha a nutse ta yadda zan dinga bawa zuciyata haquri da juriya in daina zargi da kishi babu kyau.
Ahlul kitabu ne su dukka amma na yarda da cewa ta fadi gaskiya, na yi mata godiya kawai.
Har zan karbi wayarta in kira gida in ji halinda yarana suke ciki amma sai na tuna da cewa ban san lambar kowa ba.
Har muka isa Bauchi masifaffiyar matar nan ban daina jin haushinta ba, daga ta daga ido sai ta ci karo da harara ta. Hannu take kewayawa a goshi da kafadunta tana kiran mai cetonta. Wato ga mayya tana neman tsari.
Mun isa Bauchi bayan sallar Isha'i takwas ya gota, direba ya sauke kowa a tasha ya wuce da ni gida. Ina ta salati ina fargaba abinda zan je in tarar. Ya na tsayawa a bankin get na fito da sauri na ce ya tsaya ya in dauko masa kudin motarsa. Abin mamaki sai ya ce in bari. Na tambaye shi dalili sai na ga idanuwansa ya cika da hawaye.
Ya ce "Usman mijinki mutumin kirki ne shine ya siya min tayoyin motar nan wani lokaci da ya je tasha ya tarar bana aiki, motata ta tsaya kuma ya biya min kudin gyare-gyare komai da komai har sai da motar nan ta tashi. Zaa kai shekara guda kenan yanzu, dan haka naga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login