Showing 18001 words to 20000 words out of 20000 words

Chapter 7 - MACE GUDA DAYA TILO HAUSA NOVELS WRITING BY SAKINAT.txt

Sakinat   

23 Nov 2025

1332

yanayin daya ganta
gaba daya ta jigata marabar ta da matacce
numfashi, sai alokacin yaji tausayinta ya darsu
azuciyarsa shi kansa yasan baiyi mata ta dadin
rai ba saboda lokacin ransa yagama baci
afusace yake alhalin kuma bai kamata yabi da
ita ta haka ba sam bai tausaya mata ba yanda
yasaba bida yan matansa haka yabida ita alhalin
kuma yasan akwai banbanci su da ita, ahankali
ya rungumeta yafara hawaye acikin zuciyar sa
yace Allah nagode maka da kabani kamilalliyar
mace hakika nasan wannan rahama ce babba
kayi min batare da ka duba halayyata ba, duk
yadda na kasance ina saba maka amma sai ka
dauko kamilalliyar mace kabani,baka bani
mazinaciya Irina ba ya Allah nayi maka alkawari
daga yau bazan kara aikata zina ba har nadawo
gareka, zan tsaya a iya gonata daka albarkaceni
da ita.
MACE GUDA DAYA TILO....
Na
UMMI A'ISHA
7⃣2⃣
Hawaye ne yaci gaba da gudana akan
kumatunsa na tausayin matarsa, shi kansa
yasan ta wahala dayawa awa 4 ana abu 1
ummm tom ummi A'isha dai bata da ta cewa,
ganin bacci ya dauketa yasa yatashi yashiga
toilet dinta yayi wanka ya fito haka kawai ya
samu kansa cikin wani nishadi ai rayuwar aure
tayi yafada acikin ransa domin tunda yake
yawon bin mata bai taba tsintar kansa acikin
yanayin da ya samu kansa yau ba, dakinsa yaje
ya saka jallabiya yayi sallar magrib da isha
sannan yafito afalo ya tsinkayo wayoyinsa yana
dubawa yaga miss called din daddy wurin 5
murmushi yayi yasan dan bai ganshi a masallaci
bane shiyasa yakira yaji dalili to amma idan ya
tambayeshi me zaice? Ai gaskiya da kunya dan
haka sai kawai ya tura masa txt da cewa kanshi
ne yake ciwo kuma shine da yasha magani
bacci ya dauke shi sai yanzu ya tashi, dakin
junada ya nufa lokacin ta farka tana tuno abinda
ya faru tsakaninta da lamin dazu bude kofar ta
ga anyi shine ya shigo daga shi sai gajeren
wando runtse idonta tayi tafara fadin dan Allah
yaya lamin kayi hakuri ka kyaleni wlh zan mutu
ahankali yazo gefen gadon ya zauna yakamo
hannunta ya rike cikin nashi yafara kama yan
yatsunta daya bayan daya yana murzawa,
junada! Taji ya ambaci sunanta saura kiris ta
sume domin ji tayi duk duniya babu wanda ya
iya fadar sunanta kamar shi, yaci gaba da cewa
ki yafe min abinda nayi miki nasan na wahalar
dake ban biki asannu ba amma dan Allah kiyi
hakuri kinji hawaye taga yafara bin kumatunsa
ahankali ta girgiza kanta alamun ya daina kuka
hannunta ya saki ya tashi yashiga toilet ya
hada mata ruwan wanka yadawo dakin yace
tashi kije kiyi wanka, bazan iya tashi ba caraf ya
dauketa ya kaita toilet din wanka yayi mata ya
gyarata tsaf sannan yadawo da ita dakin ya
saka mata doguwar riga sannan ya shimfida
mata sallaya daga zaune tayi sallolin shi kuma
ya cire bedsheet din ya shimfida mata wani tana
idarwa ya cire mata doguwar rigar ya saka mata
rigar bacci ya dauketa ya dora akan gado yazo
kusa da ita ya zauna me zan dafa miki nasan
kina jin yunwa ahankali tace tea kawai zansha
ka duba kitchen akwai ruwan zafi acikin flask da
sauri ya mike ya Shiga kitchen din ya hado
mata tea mai kaurin gaske kamar koko ya kawo
mata dakyar ta tashi zaune ya fara bata har ta
shanye sannan ya kwantar da ita ya fita kafin
yadawo har bacci yayi awon gaba da ita.
MACE GUDA DAYA TILO..
Na
UMMI A'ISHA
7⃣3⃣
Yana shigowa yaga har bacci ya dauketa
dan haka kusa da ita ya je yakwanta yashiga
cikin jikinta, can cikin dare yaji zazzabi ya rufeta
jikinta yayi zafi zau kamar wuta cikeda
tausayawa yaja bargo ya rufesu sai dai shi baiyi
wani baccin kirki ba motsi kadan zai tashi ya
haskata yaga halin da take sannan zai kwanta
ana jimawa zai kara tashi da haka har gari ya
waye shi tun asuba yayi salla amma bai tasheta
ba gudun kar ya katse mata baccinta sai wurin
6 sannan ta tashi yana kwance agefenta ta dan
kalleshi sai taga idanuwansa arufe duk azatonta
bacci yake dakyar ta iya tashi kamar mai koyon
tafiya tafara takawa ahankali ya bude idonsa ya
bita da kallo cikeda tausayawa ahaka yaga ta
fito ta shimfida sallaya tasa dogon hijabinta har
kasa zama tayi saboda ba zata iya tsaiwar ba
kwalla ce yaji ta ciko masa ido yayi saurin
gogewa ahaka ta idar da sallar ta dawo gadon
ta kwanta, kanta ya dago ya kwantar akan
kirjinsa yace sannu junada yaya kike jin jikin
naki, zazzabi nakeji yana neman rufeni kuma
kaina sai ciwo yake sannan jijiyoyin jikina jinsu
nake kamar ana tsintsinka min su, cinyoyina
kuma kamar ana sassara min gashi sunyi tsami
kuma sunyi min nauyi,cikin tausayawa yace
sannu bari naje na nemo miki magani, yana
fitowa falo yaji ana kwankwasa kofar budewa
yaje yayi husna da hasna yagani a tsaye yaya
ina kwana lfy ya akayi? Gurin Anty mukazo, me
zakuyi mata? Mun jita shiru tun jiyane shiyasa,
lafiyar ta lau,Ku koma ku shirya mana breakfast
zan zo na karba yana gama fadin haka ya
maida kofar ya rufe yashiga dakinsa ya saka
jallabiya da dogon wando yafito saida yasa key
ya kulle kofar falon sannan yafita motarsa ya
dauka ya tafi wani chemist ya siyo mata
magunguna sannan ya dawo gidan, side din
mummy ya shiga ya dauko kayan breakfast din
yashiga side dinsu lokacin har ta tashi daga
bacci tayi wanka da ruwan dumi ta gaggasa
jikinta babu laifi ta danji dama dama tayi
kwalliyar ta cikin wani brown din leshi tana
zaune a falo ta kunna kallo, yana shigowa ta
sukwi da kanta kasa bata yarda sun hada ido ba
gabanta yazo ya ajiye abincin ya zuzzuba mata
soyayyiyar doya da kwai da farfesun hanta,
sauko da ita yayi ya dorata akan cinyarsa yafara
bata abaki gaba daya idonta sunyi jawur
fuskarta ta kumbura abinka da farar mace sai
kace sweet choco kawata, ahaka har ta koshi ya
bata maganin tasha sannan shima ya dan ci
abincin ya tashi ya shiga dakinta ya gyara mata
ya share ya kunna turaren wuta yadawo falonma
ya gyara ya shiga kitchen ya wanke mata
kwanuka ya share sannan ya dawo falon da
take,kallo kawai take binsa dashi daga shi sai
best da gajeren wando.
[3/24, 11:04 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA
DAYA TILO...
Na
UMMI A'ISHA
7⃣4⃣
Falon yadawo ya feffesa air freshener yasaka
turaren wuta bugun kofar da yaji ana yine
yasashi tashi ya leka su hasna ne cikin shirin
tafiya makaranta lekowa yayi yace ya akay?
Yaya dama mun shirya ne shine muka biyowa
Anty, kuyi tafiyarku ita yau bazata ba sai kun
dawo kofar ya mayar ya rufe, wunin ranar dai
bai huta ba dukkan ayyukan gidan shine yayi
mata har tausayi yabata saboda yanda yaketa
nan nan da ita gashi yanada lecture amma duk
ya share yaki zuwa shi ta lafiyar matarsa yake.
Haka ya rinka bata kulawa har na tsawon sati
daya lokacin da ya fuskanci ta warware ne
yafara fita kuma aranar ya kawo mata yan aiki
guda 3 yace bai yadda tayi kowanne aiki ba in
banda girki da gyaran dakinsa,wata soyayya mai
wuyar fadi suke nunawa junansu, su husna kuwa
tuni sun koma sashen mummy domin abin yafi
karfinsu agabansu lamin yake kissing din junada
ko ya rungumeta,yauma suna zaune acikin falo
dukansu suna kallo ya dawo daga office ko
kunyar su baiji ba yaje yashige cikin jikin junada
ahankali ya lalubi bakinta yasaka cikin nashi
hasna ce tace kinga husna zo mu tafi duk
lokacin da suke da bukatarmu sa kiramu hakan
kuwa akayi suka tashi suka tafi wurin mummy,
ita kuwa junada dama tama manta da suna
wurin domin ta dade tana kaunar jajayen lips din
lamin dan suna mutukar burgeta. Ahaka
rayuwarsu tayi ta tafiya cikin farin ciki
alokacinne Kausar suka dawo daga kasar
Uganda ita da Abdulrahman cikinta ya tsufa
sosai, lokacin itama junada ta soma nata yan
jinyace jinyacen da zazzabi ganin abin yayi yawa
yasa lamin yakira mata likita har gida yana
dubata ya ta tabbatar musu tana dauke da juna
biyu na wata 2 tuni lamin yafara murna wai
shine zai haifi dan kanshi, murmushi ya saki mai
kayatarwa junada tace lfy? Kallonta yayi yace
abin ne ya burgeni dalibata zata haifa min yara,
murmushin itama tayi tace ai malamin ne akwai
iya daukar fansa dariya yayi yajawota jikinsa ya
rungumeta yace duk cikin friends dina fa ni kadai
ne nayi auri gashi har zan haihu dariya itama
tayi tace to ai kayi dabara nasan nice zan rigaka
tsufa tunda kai namiji ne murmushi yayi ya
kama hannunta yayi kissing dinsa sannan yace
no ni yanzu inada 27 ke kinada 21 tare zamu
tsufa, malami dai ya auri dalibarsa.
MACE GUDA DAYA TILO....
Na
UMMI A'ISHA
7⃣5⃣
Ahaka ya shagaltar da ita da soyayyarsa mai
wuyar fahimta. Washe gari kausar ta haifi
yaronta santalele mai kamada lamin sak dan
haka ranar suna ma sunan lamin din yayansa
yasakawa yaron, yanzu rayuwa tayiwa junada
dadi domin ta fahimci ita kadai ce MACE GUDA
DAYA TILO acikin zuciyar mijinta yana bata
dukkan kulawa kuma ahaka yayita tayata renon
cikinta har ya isa haihuwa ranar da zata haihu
lamin baya nan dan haka sai dawowa kawai
yayi yaga ta haifi jariranta masu kama dashi
sak, su husna kuwa tamkar zasu cinye su don
so shi kanshi lamin yaran sun shiga ranshi
dayawa haka akasha shagalin suna inda yaran
sukaci sunan mahaifinsa da mahaifin junada ana
kiransu sudais da shurem ansha buduri sosai
washe garin suna mami kanwar umman junada
ta tafi da ita bauchi tace sai bayan sunyi arba'in
zasu dawo lamin kuwa bai so ba dan babu
yadda zaiyi ne amma baiso sukayi nesa dashi
ba, ita kuwa Mami tayi hakane domin ta samu
damar gyara masa ita, duk karshen sati yake
zuwa bauchi wurinsu da haka har suka cika
arba'in saida suka dan zazzaga dangi sannan
suka dawo yola lamin ne yaje dakansa ya
daukosu yaci gayu cikin wani farin boyel mai
shegen kyau da tsada idan kaganshi bazaka
taba cewa yana da mata ba balle har kace ya
ajiye yara biyu.
[3/24, 11:08 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA
DAYA TILO.....
Na
UMMI A'ISHA
7⃣6⃣
Haka ya debo su yana cike da doki domin shi
kansa yasan yayi missing din junada, la'asar lis
suka karaso gida cike da tsarabar bauchi su
husna sai murna akeyi shi kuwa lamin alla alla
yake su kebe shida matarsa domin ya tabbatar
mata da cewa yayi rashinta. Ahaka suka ci gaba
da rainon yaransu kuma alokacinne aka sanya
ranar bikinsu husna zasu auri wasu twins yayan
Governor din garin zamfara, dan haka suna
gama karatunsu aka fara bikin junada itace uwar
biki domin itace akan komai yan biyunta kuwa
har sunyi wayo sun girma ba adade da bikinsu
hasna ba ta yayesu lokacin sun cika 1 year.
Haka suka ci gaba da rayuwarsu cikin farantawa
juna tareda kyautatawa junansu ayanzu auren
ramuwar gayya yazama auren soyayya. Yau an
tashi da sanyi junada ta shirya cikin wani jeans
da riga body hug ta dora katuwar riga sanyi
asama ta nufi dakin lamin yana kwance yana
bacci shida yaransu murmushi tayi ta juya
tafice. Da yamma yafito cikin wata riga t. Shirt
green da bakin wando ya isketa afalo tayi kyau
tamkar wata budurwa ta bayanta yaje ya
rungemata tattausan hannunta tasa ta shafo
sumar kansa tace naga kayi kwalliya sai ina?
Neman aure ai tuni tafara kwalla aure ? Dariya
yayi yace dauko gyalenki ki rakani da gudunta ta
dauko ta fita ta sameshi a mota shida yan biyu
suna jiranta cikin garin yola suka shiga basu
zame ko ina ba sai state university yola suna
zuwa yafito yashiga cikin hall din inda dalibai
sukayi dafifi suna jiransa, test ya rubuta musu
yana cikin rubutunne yan biyu suka shigo cikin
hall din dagudu sudais ne agaba shurem ya
biyoshi cikin muryarsa ta yan yara yace daddy
help me pls dagudu yazo ya rungume lamin
cikin sauri lamin ya dagashi sama yana fadin
wooh! Bai kamaka ba gaba daya yan ajin suka
sa dariya wasu kuwa mamaki suke yanzu
wannan malamin dama yana da aure? Sun
ganshi dan yaro dashi ahaka yagama yi musu
test din suka nufo gida akan hanyarsu ta
dawowa ne yakalle junada yace yanzu idan
akace miki zanyi aure sai ki yarda? Kallonsa
tayi tace ehh mana murmushi yayi yace to ni
babu auren da nake nema domin ke kadai kin
isheni kuma ke kadaice MACE GUDA DAYA TILO
acikin zuciyata, kwantar da kanta tayi ajikin
kafadarsa tana cewa na gode mijina.
Alhamdulillah!
Anan nakawo karshen labarin MACE GUDA DAYA
TILO, barayin fasaha kuji tsoron Allah ku daina
yimana editing din littattafanmu batare da
izininmu ba, duk wanda ya canza min wannan
labarin ko ya cire sunana yasa nasa, ko yacire
number na,ko yayi min editing Allah ya isa ban
yafe ba.
Fatan Alkhairi gareki
Halamcy
Jinjina ga yan uwana marubuta
Fatima zarah ( d writer of xarah)
Kausar m Hassan ( d writer of tsaka mai wuya)
Serdeyeer ( d writer of miss Aysha)
Zainab Rogo ( d writer of auren gida)
Hafsat bounzer ( d writer of rabuwa da masoyi)
Aysha chuchu ( d writer of Duniyarmu)
Dorlin choco ( d writerof Aysha Noor)
Benaxir oumar ( d writer of kalma daya)
Hawwa jabo ( d writer of wacece ita)
Maman Khadija ( d writer of ni marainiya ce)
Maman Nana ( d writer of Mairo)
Cyama galadima ( d writer of Rayuwar rufaida)
Bebeelo ( d writer of kaddararmu)
Humaira ( d writer of samra)
Uhm! Yau fa abin na marubuta ne, yan uwa
makaranta kuyi hakuri sai mun hadu a labari
nagaba mai suna..... Nice taku akoda yaushe
sunan nawa bai canza ba UMMI AISHA

5
6
7

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login