Showing 6001 words to 9000 words out of 20000 words
Chapter 3 - MACE GUDA DAYA TILO HAUSA NOVELS WRITING BY SAKINAT.txt
zauna
wurin lamin tanata yabon junada kafin kace me
tuni junada tagama girkin ta yi farfesun hanta
sannan ta hada salad ta zuzzuba su a flasks ta
zo ta jera akan dining farin ciki ne ya mamaye
zuciyar mummy, dakin su husna takoma ta
zauna suka ci gaba da caftarsu ba ita ta tafiba
sai dare tana zuwa dakinta ta sawa kofarta key
ta kwanta nan da nan taji bakin ciki ya
mamayeta sakamakon tunowa da abinda tagani
adakin lamin wata zuciyar tace yanzu har ya isa
neman mata? Eh ya isa mana tunda rayuwar
waje yayi wata zuciyar ta bata amsa dakyar ta
samu bacci ya dauketa. Ahaka suka zauna har
ya gama weekend dinsa ya koma kano, kullum
dakin su husna take wuni idan lokacin girki yayi
ita zata shiga ta girka musu, suna jin dadin
zama da ita sosai itama tana jin dadin zama
dasu mutuka gashi kuma shi kanshi dadyn nasu
yana ji da ita dan yauma foam ya kawo musu
na federal university Yola yace su cike su ukun
zasu fara zuwa makaranta tare. Su hasna
psychology suka cike ita kuma micro Biology
zata karanta,shi kuwa lamin yana can kano yana
shagalinsa yama manta da wata junada tunda
yatafi bai dawo ba saida yayi 2 weeks sannan
yazo amma duk da haka junada bataji zafinsa
ba asalima Allah Allah take yazo ta ganshi tana
cikin dakinsa tana goge masa takalmansa ya
shigo ko kallonta baiyi ba ya ajiye jakarsa ya
shiga bathroom, murmushi tayi ta tashi tafita
domin ta hada masa abinda zai ci.
MACE GUDA DAYA TILO
3⃣2⃣
Na
UMMI A'ISHA
Taliya da macaroni ta dafa masa da miyar
kwai ta kawo masa kan dining sannan ta fita
zuwa bangaren mummy, yana fitowa daga
wanka ya shirya cikin jar riga da wando baki
yafesa turaren volish mai sanyin kamshi ya fito
falo abincin data ajiye masa yaje ya buda
kamshi ne ya bugeshi domin miyar tun a ido ta
burgeshi tayi yellow tasha curry zama yayi ya
zuba yaci ya koshi sannan ya fita wurin mummy
acan ya samesu sunata zuba a babban falo
amma suna ganinsa suka yi shiru bai kulasu ba
ya shigewarsa dakin mummy. Sai dare yauma
takoma side din ta lokacin data shiga yana
zaune a babban falo yana daddana laptop
dagowa yayi ya kalleta yace ke kawo min tea to
ta amsa ta shiga kitchen ta hado masa tazo ta
ajiye akan dan teburin dake gabansa ta wuce
dakinta. Dasafe ta tashi ta gyara ko ina tsaf ta
shiya breakfast sannan ta wuce dakinsa baya
ciki da alama ya fita gyara dakin tayi sannan ta
debo kayansa data wanke masa tun jiya tafara
gogewa tana cikin gugar yashigo ya wuceta
yashiga wanka bai dade sosai ba ya fito daga
shi sai gajeren wando kallo daya tayi masa ta
sunkuyar da kanta kasa ke ina kika ajiye min
pants dina da kika wanke min? Mikewa tayi
cikeda jin kunya ta dauko masa ta bashi warta
yayi sannan ya wuce gaban drawer yafara
shiryawa.
[3/23, 9:31 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA
DAYA TILO
3⃣3⃣
Na
UMMI A'ISHA
Kanta yana sunkuye har yagama shiryawa
yafita daga cikin dakin gugar taci gaba dayi har
ta goge kayan tas gaba daya ta fito ta shiga
dakinta tayi wanka tana fitowa ta jiyo hayaniyar
su hasna acikin falonta ta shirya ta fito wurinsu.
Ranar Monday da sassafe ya fice ya nufi kano
ita kuma ta tafi wurinsu mummy tana shiga
suka fara yi mata albashir da sun samu
admission har daddy yasa aje ayi musu
registration dadi taji domin ko ba komai karatun
zai dan debe mata kewa,aranar ummanta tazo
mata murna kamar zatayi ihu haka suka koma
side dinta ta cikata da kayan ciye ciye ita kuwa
mahaifiyar tata kallon yartata takeyi tare da son
jin irin zaman da sukeyi da mutanen gidan cikin
fara'a tace wlh umma zamanmu lafiya dasu
kowa yana kaffa kaffa dani harta shi kanshi
daddy bakiga yadda yake kaunata ba kuma shi
baima cika zama agida ba amma duk lokacin da
yayo waya sai ya tambayi lafiyata dadi umman
taji sannan tace to ya zamanku da mijin naki
kuma? Murmushi nanma tayi tace shima lafiya
lau muke zamanmu umma yau da sassafe ya
tafi kano cikin fara'a tace ai mijinki yaron kirki
ne last week ma yaje ya gaishe mu, amma ina
masu aikin naki naga kamar babu kowa? Kanta
ta daga eh wlh umma mummy ta samo min
guda 3 to gaskiya banida ra'ayi ne tunda aikin
nawa ba wani mai yawa bane kuma ni in banda
kwanciya babu abinda nakeyi shiyasa nace gara
kawai na rinka aikin mijina da kaina ko nafi
samun lada murmushi umman tata tayi tace
dakyau gaskiya kinyi kykkyawan tunani Allah
yavada lada haka suka ci gaba da hirarsu batare
da umman ta fahimci akwai matsala tsakaninta
da mijin nata ba, wuni guda umman tata tayi
amma ko kadan bata fahinci akwai matsala da
mijin nata ba sai la'asar sannan sukayi mata
rakiya zuwa airport ta hau jirgi ta tafi bauchi.
[3/23, 9:35 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA
DAYA TILO
3⃣4⃣
Na
UMMI A'ISHA
Acikin satin aka gama musu registration da
komai na makaranta dama tuni anfara lectures
dan haka daddy yace next week sai su fara
zuwa da kansa ya dauko key din mota sabuwa
Benz C230 ya bata yace saboda zuwa
makaranta murna wurinsu ba acewa komai ita
kanta junadan murna take domin ta daura
aniyar karatun dagaske bada wasa ba,shi kuwa
lamin ko weekend dinma bai zo ba saboda yana
can tareda Mary a kano haka yayi zamansa bai
waiwayi yola ba. Ranar Monday suka fara
halarta makarantar su uku husna da hasna
department dinsu daya ita kadai ce department
dinta daban haka suka rinka zuwa wani lokacin
har 2 suke kaiwa a makaranta babu laifi yanzu
tana dan samun saukin tunanin da yaje
addabarta. Sai karshen week din lamin yazo
yola lokacin tana side din mummy suna kallon
wani Indian film mai suna fashion kallo ya bisu
dashi yace kullum Ku kenan a kallo kun shiga
makarantar ma amma bazaku rage kallo ba
maza dai yarinya ta samo carry over wlh saina
tattakata sai a sannan junada ta daga kai ta
kalleshi yana sanye da brown din riga da bakin
wando fuskarsa sai sheki take tamkar wani
tauraro bataso ya daina yi musu fadanba domin
tana son amon muryarsa tana yimata dadi sosai
dakin mummy ya shigewarsa husna kuwa taba
baki tayi tace kaji shi ko ina ruwansa itama
hasna bakin ta taba tace bar masifaffe kawai ai
kuwa nan da nan junada ta bata fuska tace
bana son cin fuska gaskiya ya kuke zagin mijina
agabana? Murmushi sukayi sorry Anty harda
hada baki hakan da sukayine ya bata dariya
sosai. A haka sukaci gaba da zama har
karatunsu yayi nisa alokacin shi kuma lamin ya
gama service dinsa ya tafi Malaysia ya karbo
result dinsa yana dawowa ya samu aiki a state
university yola yafara lecturing tsakanunsa da
matarsa kuwa sai dai kallo domin har yanzu
yana nan akan bakansa neman mata kuwa
yanzu ma yasa kafa.
Duniyar makaranta littattafan Hausa
Group Admin
MACE GUDA DAYA TILO
3⃣5⃣
Na
UMMI A'ISHA
Haka suka ci gaba da zaman doya da manja
tsakaninta dashi kullum side din mummy take
wuni idan babu makaranta idan da akwai kuwa
tana dawowa acan zasu yada zango ita dasu
hasna sai dai kullum tana gyara masa dakinsa
ta wanke masa toilet ta wanke masa kayansa ta
dafa masa abinci ta ajiye masa amma bata taba
burgeshi ba asalima shi a matsayin yar aikinsa
ya ajiyeta. Semester tayi nisa domin har sun kai
middle karatu sukeyi sosai kuma acikin wannan
yanayin ne daddy da mummy suka samu visa
zasu tafi kasar Spain inda daddy din zai halacci
wani workshop na tsawon sati biyu daga nan
kuma zasu wuce saudiyya domin gabatar da
umara dan haka tuni suka fara shirye shiryen
tafiya su kuma su husna sun gama hado
kayansu sun dawo sashen junada,washe gari
sukayi sallama dasu suka tafi suna tafiya suka
dawo falon junada suka zauna suna hangowa
yadda zasu kwashe da zaman gidan yaya lamin
ai kuwa basu dade da zama ba sai gashi fuska
babu annuri ya shigo ya ce ina take? Tana daki
husna ta bashi amsa to kice ta kawo min abinci
ya wuce dakinsa tashi husna tayi tashiga dakin
lokacin ita kuma junada tagama shiryawa cikin
wata atamfa yellow dinkin riga da skirt husna
tayi murmushi kin gama adai dai anty domin
yanzu yaya yadawo yace ki kai masa abinci to
ta amsa tafita da sauri tashiga kitchen dambun
shinkafa tayi da farfesun koda ta dauki juice mai
sanyi ta nufi dakin nasa yana zaune bakin gado
daga shi sai gajeren wando yana waya kanta a
kasa ta isa gabansa ta ajiye farantin ta juya ta
fice. Suna nan zaune a falon yafito cikin shiga
mai kyau blue din jeans da pink din riga yayi
kyau sosai sai kamshin turaren Phoenix ne ke
tashi ajikinsa ko inda suke bai kalla ba yafice.
[3/23, 9:51 AM] Ummi A'isha: [3/23, 9:41 AM]
Ummi A'isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO
3⃣6⃣
Na
UMMI A'ISHA
Husna ce ta kalli hasna tace tofa ai mun shiga
uku kuma tunda aka barmu awurin wannan
mugun hasna tace ai dama wlh da yaya Abdul
na nan agidansa zamu zauna harararsu junada
tayi tace ai kuwa da baku isaba wlh suna cikin
maganar sai gashi sun shigo shida wasu mata
guda 2 kyawawa dakinsa suka wuce bako sannu
dama yan matan ba musulmai bane Jim kadan
sai gashi ya fito ya kallesu daya bayan daya
yace wadannan abokan aiki nane zasu zauna
anan dan haka wlh koda wasa naji yarinya ta
fada idan su daddy suka dawo sai na illata ta
kuna jina kai suka daga dan duk cikinsu babu
wacce ta iya magana junada kuwa tafi kowa
bakin ciki ranta ya gama baci sosai juyawa yayi
ya koma dakin hasna ce ta mike ta shiga
dakinsu wanda yake opposite din dakin junada
husna itama tashi tayi tabi bayanta tana shiga
tasameta ta rafka tagumi kusa da ita taje ta
zauna tace hasna me kika fuskanta da wannan
lamari? Cikin takaici hasna tace ai husna yaya
lamin dan rainin wayone wai abokan aiki
wadannan sunyi kama da lecturers? Kawai yan
matansa ne wlh ni dama nadade da sanin yaya
lamin yana neman mata cikin bacin rai husna
tace ai shiyasa kullum nake tausayawa anty
junada tana mutukar hakuri dashi kuma bata
taba nuna mana laifinsa ba kullum cikin boye
sirrinsa takeyi bata taba fada mana tsakaninsu
ba Allah shiryeshi amin inji husna. Ita kuwa
junada dakyar ta iya tashi saboda jirin da yake
dibanta sai yau tasan tana tsananin kishin
mijinta akan gadonta ta kwanta tafara wani irin
kuka mai ban tausayi acikin zuciyarta kuwa
addu'a take masa Allah ya shiryar dashi haka ta
wuni tana kuka tuni kanta yafara ciwo amma
haka ta fito ta shiga kitchen ta dafa musu abinci
ta koma dakinta ranar haka dukansu su ukun
suka wuni cikin takaici shi kuwa yana can yana
holewarsa.
MACE GUDA DAYA TILO
3⃣7⃣
Na
UMMIA'ISHA
Wasa wasa tun abin yana basu haushi har ya
dawo ya daina basu domin yan matan nan sai
da suka shafe kwana 9 acikin gidan sannan
suka tafi shi kuwa ko ajikinsa su husna kuwa
basu isa sun fadi laifinsa agaban junada ba dan
yanzu zata bata rai taji haushinsu sai dai idan
sun koma gefe suyita Allah wadai da halin yayan
nasu ita kuwa junada addu'a kawai take yi Allah
ya shirya mata shi ya karkato mata da
hankalinsa kanta. Ranar Monday tunda wuri ta
tashi ta shirya masa breakfast ta gyara masa
dakin ta koma ta tashi su husna suka shirya
suka tafi makaranta suna dawowa suka tarar
yana fitowa shida wata farar budurwa Christian
da sauri suka basu hanya suka fita sannan suka
shiga falon,junada cikin ranta taji kamar taje ta
shake wannan matar amma babu dama. Aranar
da daddare yazo da wata daban shi kuma
sassafe ya fice domin 8 to 10 yake yiwa wasu
daliban lecture wasu kuma 1 to 2 ita kuwa
junada saida tagama gyara ko ina sannan ta
nufi dakin nasa da nufin gyarawa tana shiga ta
ganta kwance kyakkyawa ce sosai ai nan da nan
kishi ya cikata duka ta daka mata firgigit ta
tashi tana mikewa ta kifa mata mari tace dan
ubanki me ya hadaki da mijina tsorone ya kama
arniyar tace kiyi hakuri bai cemin yana da mata
ba, ni nafada miki kuma yau sai na kasheki wata
kwalbar lemo ta dauka tace zaki kara kula
mijina? Cikin tsoro tace a'a hakuri ta fara bata
sosai saida ta Kara wanketa da mari sannan ta
hankadata waje ta cilla mata jakarta waje ai tuni
tafice daga gidan aguje ranta babu dadi tagama
gyara dakin tafice. Haka zaman nasu ya
kasance har sati 3 tuni an kafe musu time table
na exam anyi closing lectures din dan haka babu
inda suke zuwa karatu kawai sukeyi agida.
[3/23, 9:47 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA
DAYA TILO..
3⃣8⃣
Na
UMMI A'ISHA
Yauma kamar kullum da sassafe junada ta
tashi tagama gyare gyaren gidan su husna suna
can suna aikin nasu wato bacci idan suka
kwanta bacci daga asuba sai sun Kai 12 basu
farka ba itace take tashi da wuri take ayyukanta
duka. Wurin 11 tagama komai ta shiga dakinsa
baya ciki da alama ya fita kananan kayansa ta
tattara tashiga toilet ta wanwanke sannan ta
wanke toilet din, tana gamawa tadawo cikin
dakin tafara gyarashi tana gyaran gado suka
shigo shida wata arniya siririya baka kyakkyawa
ya dan saci kallon junadan yaga tayi kicicin
kunya ya dan ji don baisan tana cikin dakin ba
kallon yarinyar yayi yace Jen have a sit am
coming ficewa yayi daga dakin Jim kadan sukaji
karar tashin motar da alama fita yayi daga
gidan juyowa junada tayi taga karuwar tasa tana
gyara fuskarta ajikin mudubi fisgo ta tayi tafara
wanka mata mari tas! Tas! Tas tace dan ubanki
zaki kara biyo mijina? Cikin kuka tace no am
sorry pls tace ba wani hakuri dan ubanki yau
saina datse miki kafafu tuni Jen ta rude tafara
bata hakuri fincikarta tayi ta hada da bango ta
shaketa dai dai nan yashigo dasauri junada ta
saketa ita kuwa tace kafa me naci ban baki ba
sai gudu ko sauraronsa batayiba, cike da
mamaki ya kalli junada yace me kikayi mata?
Shiru tayi masa taci gaba da aikinta ransa ya
baci sosai ficewa yayi daga dakin ya koma falon
ya zauna ita kuwa aikinta tayi tana gamawa ta
fito ta wuce dakinta.
MACE GUDA DAYA TILO...
3⃣9⃣
Na
UMMI A'ISHA
Mamaki ne ya kamashi to me yakori jen?
Wayarsa ya dauka yafara kiranta tana dauka
tafara zaginsa tana cewa banza mayaudari
dama ashe kanada mata shine ka daukeni ka
kaini gidanka dan matarka ta kasheni ko? To
daga yau babu ni babu kai macuci kawai ta
kashe wayarta mamaki ne ya cikashi to me
wannan yarinyar take nufi? Rannan ma da
yadawo bai samu Grace ba bayan kuma yatafi
ya barta adakin da yakirata awaya da kyar ta
dauka ta zazzageshi wai ba ita bashi domin
matarsa mahaukaciya ce kashe mutane take
wato itace take korarsu kenan kodai sonsa take?
Tashi yayi yabar falon ganin bashida amsar
tambayar da yayiwa kansa. Ita kuwa ta daina
ma saka abun aranta addu'a kawai takeyi Allah
ya shirya shi, yau saura kwana 3 su mummy su
dawo daga umara har sun fara shirye shiryen
taryarsu tana dakinta akwance su husna kuma
suna daya dakin ya shigo ki tashi ki dafa min
indomie guda 4 da soyayyen kwai ki kawo min
daki to tace ta mike ta shiga kitchen tana
mamakin kanta wai yau itace ake juyawa haka
duk irin gatan ta lallai ta yadda sarki agidan
wani sarkin bawa ne da wannan tunanin ta
gama dafawa ta soya kwai guda 6 ta dauki
cokala guda biyu dan tasan shi kadai indomie
Hudu tayi masa yawa dan bashida cin abincin
sosai dakin nasa ta nufa ta kwankwasa shiru
dan haka kawai sai ta tura kofar tana shiga ta
hangoshi daga shi sai gajeren wando ita kuwa
karuwar tasa zigidir take haihuwar uwarta sun
shagala sai romancing juna suke tuni jikinta ya
fara rawa ta saki farantin abincin ya zube filet
din tangaram din ya fashe karar ce tadawo dasu
cikin hankalinsu tuni ta ruga aguje tabar dakin
shi kuwa jikinsa yaji yayi masifar sanyi rana ta
farko da yaji kunyar junada ranar farko da yaji
ya tsani zina arayuwarsa kuma yaji ta fita acikin
ransa tashi yayi yace da Agnes ta shirya ta bar
gidan tambayarsa abinda ya faru tafara wata
tsawa ya daka mata yace ta fice kawai cikin
sauri ta shirya ta dauki jakarta ta fita shi kuwa
kamar wanda aka zarewa laka ajiki duk ya
sukurkurce.
Duniyar makaranta littattafan Hausa Group
Admin
Ummi A'isha
MACE GUDA DAYA TILO..
4⃣0⃣
Na
UMMI A'ISHA
Tana isa dakinta ta kwanta akan gado jikinta
sai faman rawa yake innalillahi kawai take
ambata, hayaniyar su husna ta jiyo a falo amma
bata fita ba tana nan kwance kamar marar
lafiya, shi kuwa lamin dakyar ya iya tashi yasa
kayansa ya fito daga falo tajiyo yana tambayar
su hasna ina take? Tana cikin daki inji su kai
tsaye dakin ya wuce ya ganta kwance ta
kudundune kanta ke ki tashi kije ki gyara min
dakina da kika bata ni fita zanyi yana fadin haka
ya fita ita kuma tashi tayi tana mamakin shi
kuwa lamin me yagani ajikin wannan arniyar? In
banda kashi ita bata ga komai ajikinta ba amma
dan jaraba irin ta maza shi burgeshi tayi ahaka
mikewa tayi taje ta gyara dakin ta kunna turaren
wuta sannan ta rufo kofar ta dawo wajen su
hasna. Washe gari da wuri ta fito saboda
yunwar da takeji kanta tsaye kitchen ta wuce ta
debo ruwan zafi tazo ta hada tea mai kauri ta
dawo falo tafara sha da niyyar idan ta gama
zata koma kitchen ta hadawa su hasna da lamin
nasu, kamshin turarensa tafara jiyowa tuni
kamshin nasa ya gama rudata ta ajiye kofin
sakamakon ganinsa da tayi ya fito yana sanye
cikin suit bakake yayi kyau sosai kallonta ya yi
sannan yace bani breakfast dina fita office zanyi
dasauri ta mike ta shiga kitchen ta soya masa
manyan kwai guda 4 ta debo ruwan zafi a kofi
sannan ta dauko masa bread ta dawo ta ajiye
masa ta koma ta dauko butter da yar wukar da
za ashafa butter din ta dawo ta ajiye ta nufi
kitchen ke ni zan shafa butter din? Taji yace
dawowa tayi tazo ta tsugunna ta dauka ta fara
shafa masa shi kuma ya dauki kwan ya fara ci,
yan yatsun hannunta ya zubawa ido farare sol
dasu dogaye miko masa tayi yasa hannu ya
karba yana mai ci gaba da kallon hannun nata
tana gamawa ta mike ta koma kitchen.
Ummi A'isha
[3/23, 11:54 AM] Ummi A'isha🏻: [3/23, 11:23
AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO.....
4⃣1⃣
Na
UMMI A'ISHA
Aiki tafara tanayi tana tunanin abin sonta
lamin ita dai Allah ya dora mata sonsa tun ranar
farko data fara ganinsa a makarantar su
shigowarsa taji cikin kitchen din kamshin
turarensa shine ya cika mata hanci tuni taji
jikinta yayi la'asar ta bayanta ya tsaya ya ajiye
kayan yabi bayanta da kallo sannan ya juya ya
fita ajiyar zuciya ta saki sannan taci gaba da
aikinta tana fadin Allah ya kara shirya min kai
lamin, sai data gama dukkan ayyukan sannan ta
nufi dakin sa domin gyarawa tana shiga taga
wata arniya zaune a bakin gadonsa nan da nan
kishi ya motsa saboda duk a tunaninta adakin ta
kwana kallonta tayi tana sanye da wata yar
ficiciyar riga iya cinya kanta taci gashin kanti fal
dubanta tayi tace sannu amma ya zaki zauna
tun safe acikin datti washe baki tayi tace no
zuwana kenan yanzu shima bai san da zuwana
ba nayi mishi surprise visit ne murmushin
takaici tayi ta jawo wani karfe tace yau zan
koya miki hankali jibga mata tayi zata kurma ihu
ta toshe bakinta ta yar da karfen ta soma gaura
mata mari tana cewa waya kawoki wurin mijina?
Yau saina kasheki idanuwan tane suka firfito ita
kuwa marinta taci gaba dayi saida ta kumbura
mata fuska sannan ta kaita waje ta cilla mata
handbag dinta ta dawo taci gaba da gyaran
dakin aranta tana raya cewa har yanxu ina son
mijina kuma zanci gaba da sonsa ya Allah ka
ganar dashi gaskiya tana gama gyaran dakin
yana dawowa alhalin kuma ba haka ya saba
yiba idan ya fice wani lokacin sai dare gabanta
taji yafara faduwa saboda ta tabbata karuwarsa
ce ta fada masa dukan da tayi