Showing 9001 words to 10790 words out of 10790 words
Chapter 4 - Allon sihiri Par 2 By Abdul'aziz Sani Madakin Gini.txt
bishiyar ta
bace
musu da gani.A wannan lokaci ne Sarki Darmanu
ya
dubi Lubainu cikin murmushi yace,na fuskanci
cewar
Akisatul Sauwara ta kamu da matukar
sonka.Koda
jin haka sai mamaki ya kama Lubainu ya dubeshi
yace,wacce irin magana kake yi haka?Ai wannan
bayani naka daidai yake da tatsuniya a cikin
kunne
na,domin babu yadda za'a yi sarauniya Akisatul
Sauwara ta so ni saboda kwararan dalilai guda
uku.Dalili na farko shine a rayuwarta bata tabayin
soyayya ba don babu wani 'da namiji daya taba
burgeta.Dalili na biyu shine ta san cewa ni ba
cikakken namiji bane,kaga kuwa bazata so ta
auri
wanda baya haihuwa ba tazo ta rasa magaji.Dalili
na
uku shine ta fini kyau,ta fini mulki,kuma kasan su
mata sun fi son su auri wanda yafi su
komai.Koda
Yarima yazo nan a zancensa sai Sarki Darmanu
ya
bushe da dariya sannan dubi Lubainu cikin
nustuwa
yace,Lubainu kai saurayi ne matashi wanda har
yanzu yake daukar darasi a cikin karatun
duniya,sabanin magidancin mutum kamata wanda
yake da matan aure ashirin da hudu.Babu irin
soyayyar daban yi ba a rayuwata,dukkanin
alamomin
SO da KAUNA sun bayyana akan fuskar
Sarauniya
Akisatul Sauwara a gareka da kuma alamomin
kauna
a zahiri.Idan ma baka yarda da abinda nake gaya
maka ba yanzu nan gaba zaka gani a lokacin da
Kura takai bango.Ka bar ganin cewar tasan kana
da
mata a gida mai jiran ka koma gareta.Hakan ba
zai
hana taso ka ba saboda shi SO bashi da hijabi
kuma babu abinda yake iya tareshi idan har ya
yunkuro.Har Lubainu ya bude baki zaice wani
abu
sai ga Sarauniya Akisatul Sauwara ta dawo,don
haka
sai yai shiru baice komai ba yana ta nazarin
abinda
Sarki Darmanu ya gaya masa.Haka dai Akisatul
Sauwara tazo ta zauna tare dasu aka ci gaba da
hira,inda Akisatul Sauwara ta dubi Sarki Darmanu
tace,yanzu kai a ganinka ta yaya zamu jewa
boka
Darbusa?Shin zamuje masa ne cikin lumana da
nasiha ko kuwa zamuje masa ne ta tsiya tsiya?
Koda
jin wannan tambaya sai Sarki Darmanu yayi
murmushi cikin ajiyar zuciya sannan yace,ni ta
yaya
kuka zo mini keda Lubainu?Sarauniya Akisatul
Sauwara tace ai kai baka bari mun iso fadarka ba
tun a daji ka taremu kana mai badda kama kazo
mana a siffar tsoho don ka yaudaremu ka cutar
damu.Dajin haka sai Sarki Darmanu yayi dariya
kuma ya hade fuska yace,to kiyi zaton yaudara
da
tarkon tuggu ninki wanda nayi muku daga Boka
Darbusa tunda kin san cewa ya ninka ni sau dari
A
komai.Koda jin wannan batu sai hankalin
Sarauniya
Akisatul Sauwara dana Yarima Lubainu ya tashi
domin sun fuskanci cewar hadarin dake gabansu
na
fuskantar Boka Darbusa ba kadan bane.Kodai su
sha
wahala ko kuma su rasa rayuwarsu gaba
daya.Haka
dai suka ci gaba da hira har lokaci ya cika sai ga
wadannan manyan tsuntsaye guda uku na Sarki
Darmanu sun dawo suna masu saukowa kasa
daga
can kololuwar sama.Cikin gaggawa su ukun suka
mike tsaye suka hada nasu i nasu
su,kowannensu
ya hau kan tsuntsu guda.Sarki Darmanu ne akan
gaba,Sarauniya Akisatul Sauwara a tsakiya
sannan
Yarima Lubainu.Lokaci guda tsuntsayen uku suka
bude fuka fukansu suka tashi sama suka luluka
izuwa can sama suna masu giftwa ta gaban
Rana
wacce ke shirin faduwa ta zama ja jawur.Abin
gwanin ban sha'awa ga dukkan halittar da take
kallo
daga kasan Turba.Kamar yadda Sarki Darmanu
ya
fada haka al'amarin ya kasance wato saida suka
shafe kwana
hudu da yini daya suna tafiya a sararin samaniya
bisa
wadannan manyan tsuntsaye sannan suka hango
gidan boka
Darbusa a nesa kadan dasu.ALLON SIHIRI
Littafi na biyu(2)
Part F
Sannan suka hango Gidan Boka Darbusa a nesa
kadan dasu.Babban abinda ya baiwa Lubainu da
Sarauniya Akisatul Sauwara a cikin wannan tafiya
shine a tsawon duk kwanakin da akayi ko sau
daya
tsuntsayen dake dauke dasu basu gajiya ba,kuma
ba
a sauko kasa an yada zango ba.Haka kuma duk
su
ukun babu wanda wata bukata ta kamashi ta
bawali
ko bayan gari saidai kawai idan sun gaji da zama
akan tsuntsayen su kwanta suyita sharar barci
abinsu cikin kwanciyar hankali ba tare da
fargabar
komai ba.Da yammaci ne sakaliya suka hango
wannan gida na Boka Darbusa wanda saidai a
kirashi da aljannar duniya saboda ginuwarsa da
kawatuwarsa.Tunda Yarima Lubainu yazo duniya
ko
a bakin masana tarihi bai taba jin labarin gida
mai
kyan na Boka Darbusa ba.Saidai babban abin
takaice shine a tsakiyar dokar daji aka zo aka
gina
wannan gida wanda aka bata miliyoyin dinare
wajen
ginashi.Kai da gani kasan cewa in ba rikakken
Boka
ba wanda ya cika hatsabibin gaske babu wanda
zai
iya gina irin wannan gida a dokar daji haka ya
zauna
a cikinsa.Da saukar tsuntsayen uku kusa da kofar
gidan da tazarar kamar taku ashirin sai kawai
suka
ga an bude kofar gidan wacce ta kasance
katuwar
gaske.Kofar na budewa sai sukaga wadansu
kyawawan kuyangi su goma sha biyu sun fito
daga
cikin gidan a jere a layi.Shida a hannun dama
ragowar shidan a hannun hagu.Dukkaninsu suna
dauke da wani dan karamin kwando wanda akayi
shi
da karfen jauhar.Kowanne gwando an cikashi da
wani irin jan fure mai tsananin kamshi.Gaba
dayan
wadannan kuyangin suna sanye ne da dogayen
riguna masu launin kore wadanda akayi su da
Miski.Babbar cikin kuyangin ce kadai take da riga
kala dabam mai ruwan kwai wacce akayi mata
dinki
mai siffar dawisu.Tsananin kyawun wannan
kuyanga
gami da kyawun shigar datayi dole ne ya rudi
kowanne lafiyayyen 'da namiji.Cikin tafiyar
kasaita
da karairaya tamkar macijin gona haka wannan
kuyanga da sauran yan uwanta suka iso daf da
su
sarki Darmanu suka risina sukayi gaisuwa gami
da
yimusu barkda da zuwa.A sannan ne shugabar
kuyangin ta dago kai ta dubi su Lubainu tace lale
marhaban da manyan baki na musamma,lallai
mai
girma Darbusa yana farin ciki da zuwanku kuma
yace nayi muku jagora izuwa cikin fadarsa.Koda
jin
wannan batu sai Sarki Darmanu,Sarauniya
Akisatul
Sauwara da Yarima Lubainu suka sauki daha kan
wadannan tsuntsayen.Suna sauka sai tsuntsayen
suka sake bude fuka fukansu suka tashi
sama.Kafin
kiftwar ido sun kule a cikin sararin
samaniya.Koda
ganin haka sai mamaki ya kama Lubainu da
Akisatul
Sauwara suke a cikin zuciyarsu,Wai shin su
wadannan tsuntsaue wane iri nesu?Gashi sunyi
tafiyar kwanda hudu da yini daya basu yada
zango
ba,kuma da saukarsu yanzun nan sun sake tashi
sama ko hutawa basuyi ba bare su nemi ruwan
sha
ko abinci.Anya kuwa wadannan tsuntsaye ba
sihirtattu bane?.Amsar da suka kasa baiwa
kansu
kenan.Ba tare da fargabar komai ba kuwa su
Sarki
Darmanu suka bi wannan shugabar kuyangin a
baya
suka nufi cikin gidan.Su kuwa sauran kuyangin
tuni
suna kan gaba suna zubar da wannan Jan fure
mai
kamshi a kasa su Lubainu na bi ta kansa.Da
shigarsu cikin gidan sai duk su ukun suka kama
kalle kalle da waige waige domin sun zama
cikakkun
yan kauye duk da cewar dukkaninsu sarakai ne
masu tarin abin duniya.Ba komai ne yasa suka
zama yan kauye ba face ganin kayan kawar da
idanunsu basu taba gani ba da abubuwan al'ajibi
wanda ko a mafarki da hasashe basu taba zaton
wanzuwarsu ba.A cikin wannan gida ne suka ga
wani katon Lambu wanda girmansa yafi na wani
dan
karamin garin kuma kyawawan bishiyoyin dake
cikinsa da furanni tamkar halittarsu akayi a ciki
ba
shukasu akayi ba sai kayi zaton idan kayi musu
magana zasu amsa.Barewa,tsuntsaye da kwaron
nan mai suna malan buda mana littafi kuwa gasu
nan birjik a cikin Lambun kala kala,launi launi
bazasu kirgu ba.Kai idan mutum yana kallon
wadannan Lambu da abubuwan dake cikinsa sai
ya
manta da duk wani bakin cikin duniya kuma sai
yaji
kamar shine sarkin duniyar gaba daya saboda
farin
ciki.Saida akayi tafiya dasu kusan ta rabin sa'a
sannan aka iso dasu fadar Boka
Darbusa.Wangamemiyar fada ce wadda girmanta
yakai a sanya gidan sarautar Sarauniya Akisatul
Sauwara guda uku a ciki.Wannan karon sai da su
Lubainu suka rinka yin tuntube suna faduwa kasa
saboda kalle kalle da waige waige bisa ganin
kayan
kawar da yafi wanda suka gani a baya,amma
kuma
duk wannan kawa sai ta zama ta banza domin
kuwa
ba karamar razana da firgita sukayi ba
sakamakon
ganin irin fadawan da suke cikin fadar.Babu
bil'adama ko guda daya a cikin dubbun fadawan
Boka Darbusa face wadansu irin halittu wadanda
mutum bazai iya tantancewa ba yace Aljanu ne
ko
Dodonni.Wasun su rabin jikinsu na mutum ne rabi
na Aljan,wasu rabi dabbobi,rabi dodanni,wasu
kuwa
rabinsu na Aljan ne da wuta.Sun ksance manya
manya,girda girda saidai a kwatanta girmansu da
siffofin maridai ko mutanen farko.Dukkaninsu
suna
da matukar muni,kwarjini da ban tsoro,kuma suna
dauke da mugayen makaman yaki iri iri
barkatai.Wani kalar makamin ma ko a tarihi
mutum
bai taba kin irinsa ba.Wadannan dakaru sun cika
fadar gaba dayanta sai yar siririyar hanua suka
bari
a tsakiyar fadar wacce fadinta bai wuce kamu
uku
ba,kuma itace hanyar dazata kai mutum har
izuwa
inda karagar mulkin Boka Darbusa take.Koda
Boka
Darbusa ya kyallara ido yaga kuyanginsa sun
shigo
cikin fadar tare dasu Sarki Darmanu sai ya mike
tsaye daga kan karagar cikin tsananin farin ciki
ya
bushe da mahaukaciyar dariya yayita dariyar
kamar
wanda aka bashi komai na duniya.Al'amarin daya
kara razana
su Yarima Lubainu kenan sukaji a jikinsu cewar
lallai
Boka Darbusa yaudarsu yayi daya turo aka
karbesu
hannu biyu,lallai yunkurin cutar dasu zaiyi
yanzu.Bayan Boka Darbusa yayi dariyar mugunta
har
ta ishe shi sai ya murtuke fuskarsa a lokacin da
wadannan kyawawan kuyangi goma sha biyu
suka
rikide suka zama aljanun haske rike da zabga
zabgan takubba kuma suka yiwa su Yarima
Lubainu
kawanya.Koda ganin haka sai Sarki
Darmanu,Sarauniya Akisatul Sauwara da Yarima
Lubainu ma suka zare takubbansu suka jingina
da
bayansu su ukun suna jiran suga ta inda za a
kawo
musu hari.Koda gani haka sai Boka Darbusa ya
sake
bushewa da dariyar mugunta karo na biyu sannan
ya dubi su Yarima Lubainu yace,kunyi hauka
kuma
kunyi babban kuskure harda kuke yin tunanin
cewa
zakuzi wajena neman Allon Sihiri na kuma na
baku
alhalin yau sama da shekara bakwai kenan ina
son
ku kawo kanku nan fadata kun ki.Ai abinda kuka
fada gaskiya ne cewar kowa a gidansa sarki
ne.Ina
mai tabbatar muku da cewa tunda har kuka shigo
nan cikin fadata to tabbas babu dayanku dazai
fita
daga nan a raye,kuma shi kun shigo dauke da
Allunan Sihiri guda biyu.Ku sani cewa tuni nayi
bincike na gano hanyar dazan iya cire Allunan
Sihirinku daga cikin kwalaben Sihirin da kuka
sasu.Ina cirosu zan hada su da nawa.Hakan na
faruwa shike na na zama SARKIN DUNIYAr nan
gaba
daya.Duk wata halitta dake bisa doron kasa
walau
mutum ko aljan,dabba,tsunstu ko kwaro sai ya
dawo
karkashin mulkina da ikona.Yanzu zan barku da
wadannan Aljanun haske da suka yi muku
kawanya
na ga iyakar shirin ku dakuke dashi don karbar
Allon Sihirina.Koda gama fadin haka sai Boka
Darbusa ya yiwa Aljanun izinin su hallaka su
Darmanu.Nan take kuwa Aljanun suka afka musu
aka ruguntsume da azababben yaki ya zamana
cewa
Aljanun suna kai musu sara da suka cikin
tsananin
zafin nama dabasu taba gani ba.Duk sa'adda
takobin Aljanun ta hadu da tasu saidai kaga
tarwatsin wuta na tashi kuma takobin Lubainu
data
Akisatul Sauwara suka rinka dakushewa,ta Sarki
Darmanu ce kawai batayi komai ba.Haka kuma
duk
sa'adda su Lubainu suka sami nasarar sara ko
sukar jikin Aljanun saidai suji kamar iska suka
soka.Bugu da kari da kyar su Lubainu suke iya
tare
harin Aljanun saboda karfin saransu,jinsa suke
kamar katon dutse ake bugawa a kan takubbansu
wanda sai kato arba"in sun tare zasu iya
daukarsa.A
duk sa'adda takobin Aljanun ta shafi jikinsu
Lubainu
koda kuwa dan lakatarsu tayi saidai kaji sun
kwalla
ihi saboda tsananin zafi da zogon da suka ji,a
lokacin da jini je tsartuwa gami da feshi daga
jikin
nasu.Koda Boka Darbusa yaga yana samun
wannan
gagarumar nasara saiya cigaba da kyalkyalewa
da
dariyar mugunta saboda ya tabbatar da cewar
hakansa ya kusa cimma ruwa.Al'amarin su
Yarima
Lubainu kuwa suna wannan yaki ne cikin nadama
da
takaici domin sun gane cewa lallau tsautsayi ne
yasa
suka biyo Boka Darbusa har gidansa domin
karbar
Allon Sihiri.Banda Tsautsayi kuma zasu iya cewa
Ajali ne ya kirasu,domin sun san cewa babu wata
dabara dazasu iya yi a yanzu su ceci rayuwarsu
daga hannun wadannan Aljanu na haske.
SHIN SU YARIMA LUBAINU ZASU KUBUTA DAGA
HANNUN WADANNAN MUGAYEN ALJANU NA
BOKA
DARBUSA HAR SU KARFI ALLON SIHIRIN
HANNUNSA?
IDAN HAR HAKAN TA KASANCE YAUSHE NE
ZASU
ISA KOGON BAHAR IMFAL YARIMA LUBAINU YA
SAMO MAGANIN DA YA FITO NEMA?
YAYA SOYAYYAR SARAUNIYA AKISATUL
SAUWARA
DA YARIMA LUBAINU ZATA KASANCE?SHIN
ZATA
BAYYANA MASA SIRRIN ZUCIYARTA NE KUMA
YAYA
ZAI KARBI TAYIN NATA?
A WANE HALI YAZARINA TAKE YANZU A CAN
BIRNIN
ZAMRAL BISA BAKIN CIKIN RABUWA DA
MASOYINTA
YARIMA LUBAINU?
INA LABARIN YARIMA MANGUL DA MAHAIFINSA
SARKI ALKAS WADANDA SUKA KOMA CAN
BIRNINSU A CIKIN BAKIN CIKI NA SABANI?
SHIN YARIMA MANGUL ZAI CIRE SON YAZARINA
DAGA CIKIN ZUCIYARSA GABA DAYA A
MATSAYINSA
NA WANDA YA ZAMO MASAKI MAI HANNU
DAYA?
WANE MATAKI ZAI DAUKA AKAN MAHAIFINSA
SARKI
ALKASA WANDA YACE YA CIRESHI DAGA
SAHUN
'YA'YANSA?SHIN YANA TUNANIN DAUKAR
FANSA NE
AKAN YARIMA LUBAINU KO KUWA YA RUNGUMI
KADDARA?
YAUSHE NE YARIMA LUBAINU ZAI DAWO
BIRNIN
ZAMRAL HAR YA SAKE SADUWA DA
MASOYIYARSA
YAZARINA 'YAR BABBAN ATTAJIRI NA
NAHIYAR?
Mu hadu a littafin ALLON SIHIRI 3(kashi Na Uku)
don
jin ci gaban wannan kayataccen Kasaitaccen
Labari.