Showing 21001 words to 24000 words out of 48692 words
Chapter 8 - KAWAR ZUCIYA 2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf
sauran fannoni na cigaban
rayuwarsu data ‘ya’yansu masu tasowa.
Baba Murtala wanda shine
makwafin Ubansu a halin yanzu, duk
meetings din da suke yi a karshen
kowanne wata in dai yana gari da shi a
ciki, akan rayuwarsu data ‘ya’yansu data
Estate din ‘ya’yan Mama ake meeting din,
a kowacce asabar din karshen wata, inda
126
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Baba Murtala yake shige musu gaba a
komai, don kula da habakar dukiyarsu da
cigaban rayuwarsu.
Duk da Mama ta amsa gaisuwarta,
ta kuma ganta da tirtsetsen ciki ta kasa
cewa a ranta “Alhamdulillah Baffa zai
haihu”, haka ta kasa cewa “Allah ya raba
lafiya” saboda can a kasan ranta tana jin
wani iri babu dadi, saboda tuntuni ta riga
ta sakawa kanta wani negative thought
haka (gurbataccen tunani) akan ‘In-vitro
Fertilization’.
Mama in ta tuna dan Zayyan dinta
na farko a duniya, haihuwar Baffanta na
fari dan dashe ne (IVF Baby) ne sai taji
gara ma bai haifa ba.
Yawan korafin Mama akan rashin
halaccin IVF yasa Zayyan ya sake bazama
neman fatawar Malamai mabambanta,
amma kamar can baya, har yau bai ji
fatawa sahihiyar da ta haramtashi ba.
Saidai malamai suce surrogacy shine
haramun (wata ta daukar ma mace cikin
127
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
da sperm din mijinta ta haifar mata dan
saboda ita bazata iya haihuwa ba).
Amma a duka binciken da yayi na
addini akan In-Vitro Fertilization, amsar
da yake samu shine;
“IVF is permissible in ISLAM with
the condition that it involves the gametes of
the married couple and adheres to the
sanctity of the marital union, aligning with
Islamic principles of lineage preservation”. Ma’ana; Dashen haihuwa ya halatta a
muulunci bisa sharadin cewa kwayayen
haihuwar da za’ayi amfani dasu su
kasance na ma’auratan ne, don a kare
martabar aure da samar da zuri’a
tsarkakakkiya kamar yadda dokokin
musulunci suka tanada”.
***** ****
****
“The IVF Mother”
128
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
A wannan lokacin da cikin ta ya
shiga watanni na takwas Zayyan baya
nisa da gidansa. Haka duk inda yaje
Safiyyah na ransa, baya awa biyu bai
kirata a waya don tabbatar da lafiyarta
ba. Tun cikin nada wata bakwai Zayyan
da Safiyyah da taimakon Yayarsa
Zubaina sun gama tanadar duk wani
abinda jaririn zai bukata, shi da Yaya
Zubaina suke shirye-shiryensu ba tareda
sun saka Zubaidah ba, har feeder da
gadon baccin jariri yana nan sun ajiye a
cikin dakin sa. Kuma komai suka tashi
saya sai sun zabo ajin farko na ‘yan gatan
jarirai.
A ranar da cikin Safiyya ya shiga
watan haihuwa ba yadda Safiyyyah bata
yi da Zayyan ya maidata Dandume ta
haihu a can ba, ya kafe yaki amincewa.
Yace “kina wasa ne kema yarinya.
129
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Ya kamata ki san cewa we have to
take extra care of this Baby, tunda dai kin
ga da yadda Allah yasa aka sameshi.
Bazan barki ki koma Dandume haka
kawai inje kiyi haihuwar gida ba, lallai sai
a asibitin da ake kula daku anan tun
farko zan bari ki haihu, in yaso Ammi ta
kawo wadda zata kula da ke gidannan, to
wannan kuwa, bazan ki amincewa ba,
hankalina ma zai fi kwanciya in ya
kasance muna tare koyaushe, fiyeda ina
nan nesa, ku kuna can Dandume”.
A can gidan su Safiyyah Ammi tuni
ta soma hada kayan haihuwa, su yajin
jego, garin yin kunun kanwa da kanwar
kanta duk ta tanada da sauransu, haka ta
hada su rankatakaf ta daure jiran
haihuwa kawai ake. Da EDD dinta ya rage saura sati
biyu shida kansa ya roko Ammi ta basu
mai zaman jego. Sai Ammi tace Sabah da
Rayyah su shirya su koma Abuja su
taimakawa Yayarsu, don masha Allah
130
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
‘yan matan Ammi sun horu, ba abunda
basu iya ba na manya kasancewar su
rainon Tsoffi.
Har Rayha autar su ta girma Ammi
bata san komai na hidimarta da rainonta
ba, Sabah da Rayyah ne suka yi raino da
hidimarta. Haka in Anti Dije ta haihu su
suke mata komai da babba ke yiwa
Maijego harda saka ruwan wanka. Haihuwar Safiyyah daban ce da
sauran haihuwa shiyasa iyayenta basu
takura ta dawo gida ta haihu a gabansu
ba.
Zayyan daga baya ya yiwa su
malam bayanin IVF na asibiti aka yi
mata, kuma malam a matsayin shi na
babban malami bai yi challenging IVF ba,
ya dubeshi ta kowacce fuska ta addini bai
ga inda ya zama haramtacce ba. Don haka ya bisu da addu’a da
fatan Allah ya sauki Safiyyah lafiya.
131
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Yanzunma Sabah da Rayyah data
turawa Safiyya tana da tabbacin zasu iya,
shiyasa ta turo su tunda Anti Dije bazata
bar gidanta taje jegonta ba, amma
hankalinta bakidaya yana kan babbar
‘yarta mafi soyuwa a ranta “Nana
Safiyyah”. Dare da rana tana yi mata
addu’ar sauka lafiya da samun saukin
nakuda a kowacce sallahr farillarta.
Da murna da doki sosai su Sabah
suke shirin tafiya Abuja, don kwatakwata
tun komawarsu Safiyyah can bai fi sau
biyu suka taba zuwa gidan Yayar tasu ba,
shima dubiyarta suka je da bata da lafiya,
na farkon kuma sun je ganin gidan ne
sanda zasu koma can da zama, malam
baya barinsu sam, don kowacce da
maganar aurenta a kanta in ka dauke
Rayha autar Ammi.
A motar haya su Rayyah suka tafi
Abuja su biyu. Tun kafin su iso Safiyyah
ta ware musu dakin da zasu sauka cike da
dokin ganin kannen nata, ta aje masu duk
132
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
abinda ta san zasu bukata, wannan shine
zuwansu Abuja karo na biyu tun
dawowarsu Safiyya nan daga Zaria.
Sabah dama tafi Rayyah baki,
kuma tafi duk sauran kannenta
faram-faram da jama’ah. Tunda Zayyan
ya je dauko su a tashar Jabi tana gidan
gaba Rayyah na baya, shida ita suke hirar
tsokanar juna a cikin motar. Zayyan yana
tsokanarta da amaryar robarshi, tazo
bikon shi, taga baya zuwa zance yanzu,
Sabah tace “haba dai inzo bikon ka, na
dai zo taron Da na wallahi, kaima kasan
kayi min tsufa Yaya Zayyan”, Zayyan yak
ama baki ciki dariya da mamaki yace
“really? Rayyah, yaushe ‘yar kauyen
matar nan ta kile haka?”
Rayyah dai dariya take tana jinsu.
Sabah ta kara cewa “Saboda Allah
Rayyah nida nake da sarbadeden saurayi
irin Jabir a gefe, yaro matashi me jini a
jika, dan late twenties, me zan yi da Yaya
133
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Zayyan? Wannan kayan tsufan ai sai
Nana Safiyyah”.
Zayyan ya tuntsure da dariya harda
bugun sityari yace “amma kin yankeni!
Saina gayawa Sophie, kina kira ma
darling dinta tsufa tun yanzu”.
Tunda su Sabah suka zo gidan suke
wani irin kula da Safiyyah da komai na
kulawar gidan ya koma wuyansu, ko
tsinke basa bari ta kawar, ko abinci taci
nan zasu kawo mata ruwa ta wanke
hannu daga zaune. Zayyan kuma ya
wadatasu da kayan dadi suke ta fama,
duk fitar da yayi ya dawo sai ya riko
musu abinmotsa baki, musamman
Rufaida Yughurt da Rufaidah Shawarma
da Pizza din Dominos da suke matukar so.
Yanzu kam kowa yaga Sophie ya
san dan cikin ta ya gama duk wani
shirye-shiryensa na isowa duniya. Tashi
sai da dabara kwanciya ma haka.
**** ***** ****
134
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Safiyyah ta fara wata irin naquda
mai matukar wahala ranar wata Litinin,
Zayyan baya gida yaje supervising ginin
wani sabon Estate da yake ginawa a
unguwar Jahi. Kasancewar tunda watan
haihuwar Sophie ya kama baya yarda
yayi nisa da tsakiyar Abuja.
Sabah ta kira shi a waya ta gaya
masa yazo su tafi asibiti Aunty Safiyyah
fa ta fara nakuda.
Nan da nan daa inda yake ya kira
asibitinta suka tura motarsu ta daukosu
daga gida, shikuma ya bar komai da yake
yi a Jahi, ya karya kan motarsa yayi
kwana zuwa asibitin. Suka iso kusan a
tare da motar asibitin data dauko su
Safiyyah.
Har da shi aka hadu aka gungura
gadon Safiyyah zuwa dakin haihuwa.
A cikin awannin da basu gaza uku
ba Safiyyah ta haifo santalelen yaron ta
135
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
namiji mai kama da shi sak. Akan
idanunsa, kanta bisa cinyoyinsa, yana mai
tayata nishin haihuwar cike da tausayi
kamar tare da shi suke labour, yana
karanto addu’a yana tofa mata. ganin
halin da Sophie ke ciki a wannan lokacin
ya kara masa son Mamansa Haj. Fatu,
yau ya yarda haihuwa ba karamin
al’amari bace ga mata, gashin kanta ya
wargaje akan cinyoyinsa yana supporting
dinta da kalamai na karfafawa, bai gushe
ba yana mata addu’a har ta haifo masa
Danliti, kuma photocopy dinsa, bulelen
yaro lafiyayye mai kama dashi sak.
Amma me? Likitoci sun yi sun yi
yaron yayi kuka bayan isowarsa abu ya
faskara, stillbirth!
***** ****
****
Zayyan sai ya rintse idanunsa a
hankali, daidai sanda tunaninsa ya zo
nan, yana mai tuno kyakkyawar fuskar
jaririn da ya gani a ranar, dan su shi da
136
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Sophie, sai ya ji komai na memories din
wancan lokacin ya dawo masa sabo. Wato
lokacin rayuwarsu daga shi sai Safiyyah a
gefensa. Amma a hakan ya daure ya
cigaba da tunano al’amuran da suka
gabata din, a kokarinsa na nemo maslaha
da warwara, wadanda duk ba masu dadin
tunawa bane a gareshi.
Abin kunya da bakin cikin da yafi
kowanne girma a gareshi shine, daga
Mama har yaranta duka aka rasa wanda
zai zo ya duba Safiyyah a asibiti, balle su
jajanta ko yi musu ta’aziyyah na yaron da
suka rasa, alhalin sunfi kowa sanin halin
da suka shiga da wahalar da suka sha
akan cikin wadda bazata lissafu ba kafin
samunsa, da wadda suka sha bayan
samuwarshi, in ka cire Yaya Zubaina da
ta kira su a waya, tayi ta lallashinsu, ta
kuma tunasar dasu muhimmancin yarda
da kaddara da tawakkali akan
jarrabawar Ubangiji kowacce iri ce.
137
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Saboda Baban Muntaqa baya
barinta tafiye-tafiye sosai, amma kwarai
taso zuwa har Abuja din, har lokacin
Zubaina a garin Kano take aure. Kullum
sai ta doko musu waya ta bata lokaci ta
lallashesu, tana tunatar da su
muhimmancin yin hakuri, da tagomashin
da Allah ya tanadarwa wadanda suka
rasa ‘ya’yansu suna kanana, tace kada
susa damuwar hakan a ransu. Allah da ya
basu wannan din, a lokacin da suka riga
suka fidda rai da samun haihuwa, shi zai
kuma basu wani kota IVF dinne cikin
kudura da buwayarsa.
Daga shi har Safiyyah a wannan
dan tsukun kusan zautuwa sukayi a zuci
da zahiri, saboda duk wata soyayyarsu da
burinsu da kawar zuciyoyinsu ya koma ga
zuwan Babyn nan duniya, sun gama
tanadin irin tattalinsa da zasuyi cike da
soyayya da kauna na iyaye, da kuma
tarbiyyar da zasu bashi duk sun gama
tsarawa. Kai har makarantar da zasu kai
138
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
yaron sun zaba tun bai zo duniya ba
saboda tsabar dokinsu ga isowarsa.
Kwarai su kadai suka san irin
wahalar da suka sha kafin Allah ya basu
shi ta hanyar ‘In-Vitro Fertilization’. Da
irin spending din da sukayi akan
samuwar cikin da rainonsa. Hakika
tattalin arzikinsa ya girgiza akan
haihuwar babyn nan da shirin tarbarsa.
To ina ruwan Allah! Kana naka
shima yana nashi. Kuma nasa shine
gaskiya. Duk jarrabawar da yayi nufi ga
bayinsa shi ya san ladan daya tanadar
musu akanta, zai kuma baiwa bayinsa
wannan ladan a duniya ko a kiyama, akan
hakurin da suka yi, in har sun yi hakurin
dominsa ne sun tsarkake shi.
In kaga wadannan ma’auratan a
wannan lokacin na makokin jaririnsu, sai
sun yi matukar baka tausayin da nan da
nan zai saka ka zubda musu hawaye.
139
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Domin sun rasa duk wani karsashi
na jikin dan adam, da kuzarin su na cikin
gida da waje. Can zaka hango su tsakiyar
makeken gadon su manne cikin jikin
juna, suna faman sauke ajiyar zuciya ba
mai iya baiwa dan uwansa baki. Ba mijin
ba, ba kuma matar ba, ba mai iya
lallashin dan uwansa koda da kalmar
“sannu” ta fatar baki ne. Wannan ya faru
bayan an sallami Safiyyah daga gadon
asibiti.
Babban bacin ransa yadda Mama
dasu Ya Zubaida duk suka yi shakulatin
bangaro dasu. Abun yayi matukar bashi
mamaki da tsoro, bai yi zaton kiyayyarsu
da Sophie ta kai haka ba, tunda in akan
haihuwa ne ai gashi ta haifa musu Allah
ne bai barshi ba. Tun daga lokacin ya
fahimci kiyayyarsu da Sophie maras dalili
ce, amma ya zaiyi?
Abun ya tsaye masa a rai kwarai.
Ya san tun fil azal jinin Mama bai hadu
dana Sophie ba, amma bai taba tunanin
140
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
abun ya rikide zuwa tsana tsagwaro irin
wannan ba har a gun kannensa da babbar
Yayarsa, da har zata dau ciki watanni
tara ta haife dan babu rai, amma su kasa
ko jajanta mata su kasa zuwa su kuma
kasa kiran waya wannan abun ya tsaye
masa a rai fiyeda zatonsu.
Abinda shi bai sani ba, tun daga
lokacin da Safiyyah ta yanke shawarar
yin Dashen haihuwa saboda gorinsu da
tsangwamarsu, daga lokacinne kuma ta
samu rashin son da suke yi mata ya rikide
ya kara matsayi zuwa tsagwaron tsana,
dama kuma sun sha alwashin koda ta
haifi dan da rai tunda ta hanyar IVF ne ta
samu cikinsa bazasu taba rika mata shi a
matsayin Da kamar sauran ‘ya’yansu
kuma jikokin Baba Bello ba. Saidai ta kai
Dandume su Alaramma su goya mata.
Bai manta da lokacin da ya kira
Mama ba, tun suna asibitin da Safiyyah ta
haihu kafin a sallameta, ya gaya mata
141
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Safiyyah ta sauka, amma yaron ko
shurawa bai yi ba.
Yasa hankaci ya tsane idanunsa ba
tareda Mama ta san idonsa ruwa yake
fiddawa ba, budar bakin Mama sai cewa
tayi, “yo daman wannan dan nata irin
sauran ‘ya’yan mutane ne da za’a zaci
dole zai rayu? Dasa mata shi fa akayi ta
karfi da yaji, to meye abun mamaki ko
damuwa don ya zo babu rai?
Shin in tambayeku; ku duka kaida
Safiyyahr, wai ana yiwa Ubangiji dole ne
akan abinda bai ga damar bayarwa ba?
Matarnan taka Safiyyah ‘juya’ ce Baffa,
na kara fadi gaskiya juya ce, ku yarda ko
kada ku yarda kuma ya rage naku. Da zata haihu da tuni ta haihu
kamar yadda kowacce mace ke haihuwa
naturally. Idan ka sake yarda aka yi
Dashen haihuwar Da da maniyyinka
Baffa Allah ya isa ban yafe maka ba! Tunda dai mata masu haihuwar nan
ta gaske ba karewa suka yi a duniya ba!”.
142
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Wannan maganar ba karamin
firgita shi da gigita shi ta yi ba, da sauri
ya cire wayar a kunnensa ya duba yana
tantamar anya Mamansa Haj. Fatu ce
wannan? Kodai wrong number ya kira? Sai a lokacin ma ya tuna cewa ai ko
sau daya Mama Fatu tun samun cikin
Safiyyah haka siddan bata taba kiransu
tace Allah ya