Showing 36001 words to 39000 words out of 48692 words
Chapter 13 - KAWAR ZUCIYA 2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf
yasan yadda ya wayi
gari jiya da Sophie ta juya masa baya taki
tallafarsa. Sophie taki ta gane shi mai
tsananin son kasancewa da mace ne, haka
halittarsa take, son samu matarsa
Safiyyah ta daina saka kunya irin wadda
ita Safiyyah ke sakawa a tsakaninsu, tayi
kokarin gyara (sexual life) dinsu, ta maida
hankali a kanta fiye da komai ta hakura
da batun haihuwa tunda Allah bai ga
214
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
damar basu ba, amma a’ah ita Sophie
yanzu ba soyayyarsa ce a gabanta ba,
kullum hankalinta naga kulafucin son
samun Da tareda shi, ita dai ta samu
haihuwa ta kowacce hanya, hankalinta ya
tashi daga kan wajibinta (kula da
aurenta) zuwa abinda ba wajibi ba
(neman haihuwa).
Haihuwa idan Allah bai ga damar
bata ba wa ya isa ya bata? Yayi duk iya
kokarinsa akan Sophie ta yarda da hakan
abu ya faskara. A wannan lokacin Arch.
Zayyan Bello, ya tabbatarwa kansa cewa
yanada bukatar kara aure, musamman da
yake da tabbacin kowa zai aura zata bi
bayan son da yake yiwa uwargidansa
Safiyyah ne.
A duk yadda nature din Safiyyah
yake yana son abarsa a haka, yana
darajjata, yana daukaka martabar
al’amarinta a duniyarsa da cikin
rayuwarsa fiyeda na kowacce mace,
bayan wadda ta kawo shi duniya (Mama),
215
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
amma yau ya tsinci kansa dumu-dumu da
son kara aure bayan Safiyyah, amma ga
wani hanzari; macen duk da zai aura,
zata zamo masa matar biyan bukatar
gangar jikinsa ne kawai, sabida ta
wannan fannin Safiyyah ta gaza, amma
soyayyarsa da kaunarsa har abada suna
ga “stammerer Hijabhie dinsa ta
gargajiya wato Arch. Safiyyah Usman
Dandume”.
Sannan kowacece Allah ya rubuta
zai aura, ko da kuwa Azeezah dince ko
watanta, idan ta haihu Safiyyah zai
kyautarwa abinda ta haifa, in sha Allahu.
Wannan wani alkawari ne da
Zayyan yayi da zuciyarsa yau, bayan
samun kansa da sha’awar kara aure, zai
haifi Da da matar ya mallakawa Sophie,
in dai Dansa ne halalinsa to zai kyautar
dashi ga Safiyyah. In fact, sai sun yi da
wajewa/yarjejeniyar nan da kowacece
Allah ya rubuta masa zai aura, kafin ya
yarda ya aureta.
216
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Zai fito fili ya gaya mata shi ba don
rashin haihuwar matarshi ko rashin sonta
ne yasa zai kara aure ba, kawai dai….
Kawai abar kaza cikin gashinta inji
Zayyan, amma ‘infatuation’ na son kara
aure ya sameshi, irin wanda ka iya faruwa
da kowanne lafiyayyen Da namiji, mai
cikkar lafiya da cikkar kurucciya
kamarsa, ga wadatar arziki da yalwar jin
dadin duniya da yake ciki a wannan
lokacin, yana da damar auren mace fiye
da daya, da addini ya riga ya bashi, duk
son da yake yiwa Safiyyah bazai hana shi
cika sunnah ba yanzu, watakila yawan
son da yake mata shi yake sawa Safiyyah
ke ganin yana matsa mata, soyayyarsa ta
yi mata yawa, shi kuma ke sakawa take
garashi yadda takeso in yazo da
bukatarsa gareta kamar ta samu
gare-gare abin wasan yara.
Ya tuna rabon da ya gaisa da Mama
Fatu yau kwana biyu kenan, don haka ya
kunna daya daga wayoyinsa da ba’a
217
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
sanshi sosai da layin ba, don ya kira
Mama su gaisa, Safiyyah kam ya riga ya
bata hutu bazai ko kirata ba.Amma yana
kunnawa sakonta na shigowa har guda
uku a jere. A cikin sakonta na farko afujajan
take tambayarsa saukarsa lafiya a jihar
Ikko, da yanda ta damu da ya bude waya
taji lafiyarsa suyi magana ko yaya ne.
A sakonta na biyu kuma tace “tayi
regretting laifinta, tana so ya bata dama
ko yaya ne in ya dawo tanaso suyi
magana, ya bata dama tayi repenting. A
cikin sakon ta gaya masa uzurinta na
ranar ‘mood swings’ ne irin na zuwan
al’ada (jinin haila) amma tayi nadamar
yadda ta kasa yi masa bayani ko biyar
dashi ta yadda zai fahimta!”
‘I’m so SORRY Habibiyyyy!”
Zayyan kasa bata amsa yayi, ya
kuma kasa kiranta, yana blaming dinta
da duk wani hali na sha’awar Azeezah
218
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
daya riga ya tsinci kansa a ciki yanzu
babu gaira babu dalili.
Ya share Safiyyah bai bata amsa ba,
domin hakika ta kai shi bango har fiyeda
zatonta, maza zasu iya jure kowanne irin
bahagon yaren matansu amma banda (sex
denial). Duk da haka shi Zayyan ya
tabbatarwa kansa a kowanne hali kuma
cikin kowanne yanayi sunansa Arch.
Zayyan Bello, mijin Safiyyah Usman
Dandume, babu abinda zai canza title
dinnan, balle har don tayi masa wani laifi
ya canza mata shi, ko ya canza matsayinta
a wurinsa….
Kullum yana gayawa kansa ya
dinga yiwa Sophie uzuri, uzuri sau
saba’in kafin yayi mata hukunci da tauye
hakkinshi a shimfida da take yi yanzu,
tunda a can baya ai ba haka take ba
(while she was in her twenties). Tsananin
son haihuwa data sakawa ranta a yanzu
da frustration na rashin samunta, shi yake
ta canza halayenta daga (normal
219
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
behaviors) dinta daya riga ya shaida zuwa
wasu halaye kala dabam, da sukasa ta
fidda ranta akan kowa da komai har
dashi kansa.
Domin a halin yanzu Safiyyah ta
kallafa ranta a kan son samun Da dashi ta
kuma baiwa son haihuwar muhimmanci
har fiye da soyayyarsu mai tarihi da
kuma rayuwar auratayyarsu. Ya kira Mama ne da niyyar su gaisa
kawai, don sun kwana biyu basu gaisa din
ba. Mama Fatu ta amsa da farin cikin jin
muryarsa, don sun kwana biyu basu yi
waya ko ganin juna ba, bai je Katsina ba,
Mama ta kira sunansa “Baffan Mama!”
tana cewa cikin tsokana.
“Ni Baffan Mama ina ka shiga ne
kwana biyu ko wayarka babu balle
kyallinka? Ko Hakimar taka diyar
Alaramma ta murza kambu, ta hanaka
zuwa Katsina wannan watan
kwata-kwata?”
220
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Yace “haba dai Mama, haba don
Allah, nifa dadina dake kenan, zargi da
zato mara tushe a kan Sophie.
To ni bama tare ma, ina Lagos
gidan Baba Murtala tana gida Abuja ita,
muna wannan project din dana gaya miki
zamu yi kwanaki nida Baba”.
Sai kuma ya sassauta murya ya ce
cikin lallashi.
“Don Allah don Annabi Mama ki
dinga kyautatama Sophie zato. Mama don
Allah. Ba wanda ya isa ya hanani zuwa
inda kike”.
Mama cikin gundura da zancen tace
“to naji, yaushe zaka dawo daga Lagos
din?” Zayyan yace “ganinan dai Mama,
amma Baba yace zan jima, akalla zamu
kai sati biyu anan kafin kammala project
dinnan”. Cikin subutar baki za’ace ko zarar
bunu, Zayyan ya nisa ya ce cikin rage
sauti kamar mai tsoron kada wani ya ji
221
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
shi ya furtama Mama abinda ke ta yawo a
ransa.
“Mama yau sai na ga yarinyar
gidannan, kanwata Azeezah, ta wajen
Haj. Nana Aisha, ta girma fiyeda zatona,
kawai naji ta kwanta min, har naketa
cewa a raina “ba don ba don ba….???” Zayyan ya hadiyi miyau da kyar, sai
yayi shiru kadan na wucin gadi, yua kasa
karasawa. Mama tayi gyaran murya tace,
“ehem, ina jinka Baffa, ba don ba
don ba me?”
Yayi ta maza yace “Na ce da sai na
yi wa Baba Murtala zancenta, in ji ko bai
yi mata miji ba?”.
Mama Fatu ta yi kabbara a ranta
har kabbarar tata fito fili bata sani ba,
cikin kokarin hadiye dokinta da
zumudinta ga zancen, kada ya gane
girman excitedness dinta, ta ce, “Ina zuwa Baffa”.
222
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Sai ta katse wayar tasu, ta fadi gaban
Ubangiji ta fuskanci gabas ta yi sujjadah
akan goshinta ta ce.
“Allah na gode maKa da Ka nuna
min wannan ranar ina raye, ranar da
alkadarin diyar Alaramma ya karye a
zuciyar Baffa.
Yau Baffa da kansa ya ce min ya ga
wata mace daban yana so bayan diyar
Alaramma ba tareda na saka shi kona
tursasashi ba”. Mama har ta share
hawayen farin ciki da gyalenta. Ta rasa
ina zata tsoma ranta don dadi da farin
ciki.
Saida ta nutsu, sannan ta yi gyaran
murya ta sake kiransa, with so much
excitedness Mama ta ce,
“Baffa har yanzu kana kan layi?”
Ya ce, “Eh Mama”. Ta ce, “To ka
saurareni da kyau kaji abinda zan gaya
maka yanzu, maza kayi gaggawar sanar
223
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
da Baban naku, ina tabbatar maka yanzu
ne za ka yi aure mai suna aure idan aka
dace, aure na gata da mutunci, auren
babban gida daya dace da kai.
Sauran al’amuran ka bar komai a
hannuna, in dai ka gaya wa Alhajin naku
ka gama naka, ko lefe ni zan hada maka
komai kaji Baffa”.
Ya yi mamakin yadda daga ‘yar
magana ta subutar baki Mama ta dauki
zancen da matukar muhimmanci irin
haka.
A daren da kyar Zayyan ya iya yayi
barci saboda tunani, a karshe ya
tabbatarwa kansa ya kuma gayawa kansa
kara aure shi ne kadai solution na dukkan
matsalolinsu shida Safiyyah ta kowanne
bangare ya duba yaga hakan shine kadai
maslaha.
Amma daga bangaren ita Safiyyah
shin hakan zai zamo solution a gareta?
Kuma ta wace hanya zai bi ya gaya mata
224
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
yau shi Zayyan ya ga wata mace daban a
duniya bayan ita ya kalla sai biyu, kuma
yana so zai aura ya hada da ita? Duk da
cewa ba haramun zai aikata ba, kuma bai
taba yi wa Safiyyah alkawarin ba zai kara
aure ba, amma Hausawa suka ce, wai ido
da kunya!
Saboda nauyin idanun Safiyyah da
ya fara ji tun yanzu, tun ma kafin ya
sanar da Azeezah din ko mahaifinta, sai
yayi maza ya kara kashe wayarsa, gani
yake yana bude baki don yin magana da
Safiyyah za ta ji abinda ke binne a
zuciyarsa yau, wanda yake shirin aikata
mata, wato sha’awarsa ta kara aure. Don
haka kashe wayoyinsa shi yafi masa
komai sauki.
Washegari tunda sassafe wayar
Mama ce ta tashe shi daga baccin da ya
samu bayan ya yi sallar asubah.
225
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Kuma yana dagawa ko gama
gaisawa ba su yi ba, ta ce, “Baffa mu gode
wa Allah, mu kara gode maSa.
Yanzun nan na gama magana da
uwar gidan Alh. Murtala wato Hajiya
Nana Aisha, na tambaye ta ko an yi wa
Azeezah miji, ta ce tukunna, amma akwai
yaron da take tare da shi a Cyprus kafin
ta dawo. Saboda haka don Allah don Annabi
Baffa kada ka yi da wasa cikin maganar
nan, da zafi-zafi a kan bugi karfe”.
Shi dokin Mama a kan maganar ya
fara ba shi mamaki, kamar dama a jirace
ta ke da ya kyasa wata ya gaya mata?
Ya ce, “Mama ki bi a hankali, I haven’t
decided yet”.
Mama ta ce, “Zancen banza da wofi
kenan, ni har na saka Zubaida a fara
hada lefe na alfarma, don ni wurina yanzu
ne zaka yi aure na mutunci a inda ya dace
226
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Baffa, kuma aure daidai class dinka da
matsayinka”.
Bai ce komai ba har Mama ta kashe
wayarta. Ya ce, “Hummm! Mama kenan.
Kowa in bai da kudi da reputation to ba
mutum ba ne mai mutunci a idonta.
Ba wannan dalilin ne ya sa ya furta
abinda yake ransa a kan Azeezah kenan
ba, a'a shi ra’ayi ne da sha’awa suka
zarge wuyanshi.
Daidai lokacin Baba Murtala ya
kira shi a waya ya ce masa yana jiransa su
karya kumallo.
A gurguje ya yi wanka ya shirya
cikin ash colour yadin filtex mara kauri,
ya sanya hula kalar kayan jikinsa data
ciza sosai. Nan Zayyan ya fito a Zayyan
dinsa, tamkar saurayi dan ashirin da
bakwai ba mijin mace daya ba. Ya gama feshe illahirin jikinsa da
ultraviolet dinsa, sannan ya rufo dakinsa
ya karanta addu'ar fita gida da neman
sa’a sannan ya nufi cikin gidan.
227
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Har addu'a Zayyan yake a ransa, Allah ya
sa Azeezah ba ta falon, ko bata tashi barci
ba, domin emotions dinsa a kanta suna
kasa boyuwa in ya ganta har gashi Baba
Murtala jiya ya kusa ramfo shi, watakila
shiyasa ya shiga ba shi labarin rayuwarta. Addu'arsa bata karbu ba, domin
kuwa yana shiga falon Baban da ita ya
fara yin tozali, tana zubawa Baba
Murtala tea mai ganyen na’a-na’a.
Azeezah ta sha kwalliyar safe har ta
gode Allah cikin wani ubansu
combination na swiss lace da atamfar
super orange and black.
Zuciyar Zayyan ta doka ta sake
dokawa da wani sabon infatuation da
sha’awar Azeezah, amma a hakan ya
daure yasa tsahonsa ya shiga cikin falon
da sallama dauke a bakinsa. Cikin
dakewa da karfin halin kauda idanunsa
daga gare ta.
Baba Murtala ya ce, “Zo daga nan
gefena Zayyan mu sha tea. Ke Azeezah
228
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
hada masa shayin na’a-na’a ya wartsake
makoshinsa”.
Ya durkusa gefen Baba ya zauna
yana gaisheshi da safiya.
Azeezah ta mike zata bar wajen,
Baba Murtala ya ce, “Shin ke wace irin
sakarya ce da kullum sai an ce ki gaida
mutane sannan zaki gaishe su? Kuma shin
baki ji nace ki hada masa tea irin nawa
ba?” A gaskiya Azeezah ta tsani yadda
Baba ke dizga ta a gaban yaron nan, don
ta lura wani matsayi yake da shi mai
girma a gun Babansu, tunda dan Arch.
Bello Rafindadi ne, wanda tun
haihuwarta ta ke jinsa bakin Baba da
girman abotarsu a bakin Babanta Arch.
Murtala Babangida.
To ya za ta yi? Haka ta juyo da
zummar gaishe shi, yayin da idanunta
suka fada a cikin nasa. Saura kadan
zuciyar Azeezah ta narke kamar yadda
kitse yake narkewa in ya shiga rana.
229
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Hatta kalmar gaisuwar makalewa
ta yi a makoshin Azeezah Murtala, domin
sai yau ne tayi ma Zayyan Bello kallo na
hakika don jiya ko kallon fuskarsa bata yi
ba. Duk wata jijiyar da ke cikin jikinta sai
da ta saki, ta karbi kwantaccen sakon da
ke cikin idanunsa zuwa gare ta, kafafunta
ma rawa suka hau yi, ta shiga gaishe shi
da shakakkiyar murya da dimaucewa.
Baba Murtala ya kara bada ita da
cewa,
“To shayin ma wato sai na sake
cewa ki hada masa karo na uku ko
Azeezah?”
Saura kadan Azeezah ta fashe da
kuka, sabida bazata iya hada wannan
shayin ba. Hannunta da jikinta duka
rawa suke. Zayyan ya cece ta da cewa.
“Kyaleta ta je Baba, ni ko Safiyyah
bata hada mun shayi, da kaina nake
hadawa, kyaleta zan hada da kaina
Baba”.
230
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Tsaki Baba Murtala ya yi, yana ta
korafi dai a kan halin sangartar diyar
tasa, har yana cewa, yana jin tausayin
duk mijin da zai kwashe ta. Domin kuwa
ba haka uwarta take ba. Murmushi Zayyan ya yi, beautiful
serene smiles dinsa, wani tsadadden
miskilin murmushi da ba koyaushe yake
yin irinsa ba, ya ce.
“To Baba ni in rage maka
dawainiya mana? Ni ina sonta a haka, ka
ba ni ina so”.
Sakatoto da baki Baba Murtala ya
yi yana kallon dan nasa, kafin ya ce,
“Tau? Ubanka nake dai ba Kakanka ba,
balle ka maida ni abokin wasan ka, ni ba
sa’an wasanka ba ne Zayyan da za ka
tsokane ni. Barni in sha ‘tea’ dina cikin dadin
rai, kada ka sa ya huce min da
shiriritarku”. Ya daga kofin shayinsa ya
kurba.
231
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Zayyan ya dinga murmushi yana
cewa, “In dai za ka ba ni Baba, ba zan yi
maka wasa ko shiririta ba nima, ai babu
irin wannan wasan