Showing 6001 words to 9000 words out of 44270 words
inason naji kanun labaran" dariya ta yi ta ce"mai zafi ma kuwa, yanzu dai kaje General na
kiranka" okay ya ce sannan ya fita tana biye dashi.
Da sallama bakinsa ya turo ƙofar ɗakin, zaune ya tadda Mami tana bawa Ma'eesha abinci sai
General dake tsaye gefenta sauke idanunsa ƙasa ya yi sannan ya ƙaraso parlon Mommy na
biye dashi, cikeda ladabi ya ce"Father gani" saida wasu ƴan daƙiƙu suka shige sannan ya
kallesa fuskarsa babu alamun rahama ya ce"Farooq mene dalilin barin yarinyar nan tafi tafiya
da ƙafarta bayan kasan meke damunta?, sannan idan kasan bazaka iya fita da ita ka kulamin
da ita ba mene naka amsawa?, zan iya barin duk wani abu da nake na kaita inda zata sannan
na dawo da ita domin duk duniya babu wacce nakeso sama da yarinyar nan, baka saba yimin
haka ba tausayi da jiƙai ne tsakaninka da ita saboda haka ka tabbata ka cigaba da tafiya a haka
idan ba haka ba zaka fuskanci zallar ɓacin raina get out of my side!" kansa a ƙasa ya miƙe yana
kallonsa ya ce"sorry Father Allah ya wuci zuciyarka" sannan ya fice daga parlon, rai ɓace
Mommy ta miƙe tana kallon General batace komai ba itama ta juya ta fita. Kallonsa Mami tayi ta
ce"yallaɓai wannan abun bai dace ba koba komai kasan Farooq ba daga nan ba wajen kulawa
da Ma'eesha yana iya bakin ƙoƙarinsa meyasa zaka yi masa haka?, ai sai ka saka yi dinga
tunanin kodan bakai ka haifeshi ba yasa kayi masa haka" wani kallo General ya watsa mata
sannan ya ce"ai daman ba nine na haifeshi ba bare ya yi tunani akan haka, lemme tell you
something wlh indai akan Ma'eesha ne zan iya faɗa da kowa koda kuwa ace kece da kika
haifeta hope you get me right?" ya fice daga parlon a fusace, tagumi Mommy ta zuba tama rasa
me zatayi tabbas ba ƙaramin so General Kewa Ma'eesha ba kasancewar ita kaɗai ya haifa
itama ɗin bayan shekaru masu ɗinbun yawa, bayan ya cire rai da sabon ƴaƴa kuma tun daga
kanta bai ƙara ba wannan ne dalilin daya sanya yake mata wani irin so bashida burin daya
shige yaga tana farin ciki haka duk lokacin da ciwonta ya tashi yafi kowa shiga tashin hankali
domin kasancewarta AS kuma tana ɗauke da Asthma hakan yasa lokaci zuwa lokaci ciwon
yakan tayar mata.
*FAROOQ POV*
"Kin gani ko Mommy, General ya fara gasamin magana akan ƴarsa kuma duk laifinki ne above
one year Ina cewa ayi auren nan amma kin ƙi yarda dani, yanzu me kike tunani nan gaba kaɗan
zai iya korata cikin gidan nan indai akan wannan shegiyar ƴar tasa ce sbd haka ni gaskiya
bazan iya cigaba da lamuntar wulaƙanci ba gwara kawai ayi auren yanzu sai yanda nayi da
Ma'eesha kafin nadawo kansa kuma!" ya ƙare maganar yana wani wuci kamar zaki, ita kanta
Mommy ranta a ɓace yake dan General ya bata mamaki amma idan tayi duba da irin halinsa da
kuma kasancewarsa soja sai gane zai yi abinda yafi haka ma dole ne su nemi mafita tun kafin
ya juyo kansu, shiru sukai na wani lokaci sai kuma ta ce"shikenan Farooq ka shirya zuwa
anjima zamu wajen Malam nan da 1months Ma'eesha zata dawo ƙarƙashinka sai yanda kaso
zaka yi da ita" kallonta kawai ya yi sannan ya juya ya shige toilet dan idan ba shower ya
sakarwa kansa ba bazai taɓa jin daɗin duniyar ba, kwafa Mommy ta yi sannan ta juya ta fita.
*YOBE STATE*
*Sabon fegi*
*6:30am*
*MUHAIRA POV*
Yanayin lokacin sanyi ne sbd haka kowa yana cikin ɗaki shida ƴaƴansa, zaune take kan wata
tsohuwar kujerar katako gabanta wani tulin wanke-wanke ne, yinsa take yayinda duk jikinta
yake kakkarwa sanyin numfashi yana kai kawo wanke kayan take amma tuni hankalinta yabar
wajen, dubban tunanunnuka ne ke yawo cikin kwanyar kanta, bakinsa ɗauke da sallama ya
shigo cikin gidan cikin rawar murya ta ce
"Sann..sannu da shigowa Baba"
Sai a sannan nasamu sukunin ganin fuskarta tsarki ya tabbata ga ubangijin halitta wanda ya
halicci wannan kyakkyawar budurwar tsayawa fasalta kyawu irin na Muhaira ɓata lokacine dan
indai magana kake ta kyau to dazarar kayi ido biyu da ita magana ta ƙare tamkar ba mutum ba
haka take da kyau saima ka saka idanunka cikin nata nan zaka gane Ubangiji ya yi baiwa. Kallo
ya bita irin kallon tausayin nan duk ƴaƴan gidan sai ita kaɗai za'a saka aiki haka ma kuma cikin
wannan sanyin ga yanayi na lalurarta, jiki a sanyaye ya ƙarasa gabanta cikin sanyin murya ya
ce"Aishatu tashi kinji" batasan mene yiwa babba musu ba domin bata taɓa yi ba ta taso ne inda
ko tanason abu ko bata so dole sai ta aikatashi, sosai ransa ya ɓaci hakan yasa ya fara kiran
matan nasa
"Falmata!! Falmata!! Ya'acca!! Ya'acca!!"
Da sauri suka fito suna kallonsa da alama ma bacci suke ya ce"wai yaushe zaku fara imantawa
wannan yarinyar ne?, me tayi muku haka da zafi?, kodan maraicinta ya kamata ace kuna
tausaya mata sannan kuma ga yanayi na lalurarta wannan rashin imani ne kuke gwada mata
kuma baku tunanin wata rana ayiwa naku haka" rai ɓace Falmata ta ce"haba mai gida idan
bamu sata aiki ba kallonta zamu yi?, gaskiya ka wani daina nuna ka fifita yarinyar nan akan
ƴaƴanka wannan ba daidai bane" baki buɗe yake kallonta sai kuma ya yi kwafa ya ce"A'isha
tashi daga nan" dakyar ta iya yinƙurawa ta miƙe daga wajen jirin yana shirin ɗibanta da sauri
Bani kura ya kamata ya ce"sannu kinji" tsaki Ya'acca tayi dan ita daman tun yarinyar na ƙarama
ta tsaneta ashe zasu zauna tare da ita ga yarinya ce kyau kamar wata aljana. Bani kura bai
sake bi ta kansu ba ya shige da ita ɗakin da take kwana.
Ɗan ƙaramin ɗaki ne babu komai cikinsa sai wata tsohuwar tabarma da wani bargon mai
kamada tsumma sai kuma Ghana most go ɗin da kayanta ke ciki, zaunar da ita ya yi sannan ya
ce"sannu bari na samo miki ko kunu ne sai kisha muje asibiti" gyaɗa masa kai kawai tayi
sannan ya juya ya fita, jingina tayi da garun ɗakin wasu irin zafafan hawaye suka shiga sakko
mata ita ɗaya tasan irin zallar azabar da take ciki ga kuma yunwa da take ji dan rabonta da
abinci tun jiya da rana tuwon daren da suka girka basu bata ba saboda Bani kura ya yi musu
faɗa akanta haka ta kwana da yunwa yanzu kuma tana tashi da safe aka sanyata gyaran gidan
gaba ɗaya. Kusan 10mins sannan ya shigo hannunsa riƙe da wani kofi sai leda zama ya yi
gabanta ya miƙa mata kofin karɓa ta yi sannan ya buɗe mata ledar, ƙosai ne aciki da alama siyo
mata shi ya yi, dakyar takai bakinta kan kofin kunun ta fara sha ko sugar babu ciki amma haka
take sha daman inda sabo ta saba saida ta gama ci sannan ya ce ta shirya shima kuma ya fita
dan shiryawar.
Numfasawa likitan ta yi tana sake ƙare mata kallo sai kuma ta kalleshi ta ce"Baba yarinyar nan
tanada buƙatar kulawa ta musamman dan a halin da ake cikin ciwon zuciyarta yana gab da
shiga matakin ƙarshe gefe guda kuma Asthma bata samun kulawar taga dace da mai irin
ciwonta yanada kyau ace an kula da rayuwarta yanda ya kamata idan ba haka ba nan gaba
kaɗan labarin zai canza" sosai hankalinsa ya tashi cikin rawar murya ya ce"yanzu likita me
zamuyi?, yarinyar nan marainiyace nikuma banida ƙarfi bansan ya zanyi da ita ba" kallonta
doctorn ta yi ganin yanda ta matse jikinta guri ɗaya ga yarinya har yarinya amma babu
kyakkyawar rayuwa Allah mai iko aranta tayi maganar sai kuma a fili ta ce"Allah ya rufa asiri
yanzu zan rubuta mata magunguna ka tabbata ka siya mata dan tanada buƙatarsu" gyaɗa
kansa ya yi yana kallon Muhaira shima.
"Ke Muhaira!! Muhaira!!"
Dakyar take buɗe idanunta wanda suka sauya kala wani irin ruwa kwance akansu, tsaki kulu ta
yi sannan ta ce"kizo inji Umma" kallonta Muhaira ta sakeyi sai kuma ta fashe da kuka tana
cewa"Papii! Papinaaa!!, wajen Papi zani banson nan gidan A'aaaaaa!!" da sauri Kulu tayi waje
daidai lokacin da Bani kura ya shigo gidan hannunsa riƙe da magungunan Muhaira tana ganin
ta ce"Baba Muhaira! Muhaira jikinta ya tashi" da sauri yabi bayanta suka koma ɗakin lokacin
suma matan gidan suka fito. Kwance ya sameta tana birgima tana kiran iyayen nata harma da
wasu sunaye da sauri ya ƙarasa gabanta hankali tashe ya ce"Aishatu ya isa haka za'a kirasu
kinji ki daina dan Allah" ko saurarensa bata yiba ta cigaba da kukanta tana zallewa, rungumeta
ya yi ajikinsa yana tofa mata duk addu'ar da tazo bakinsa duk mutanen gidan sunyi tsuru tsuru
suna kallonta dan daman idan ciwon ya tashi haka ta keyi, sosai Bani yasha baƙar wahala kafin
ya samu aljanun subar kanta wani nannauyan bacci ya ɗauketa.
"Gaskiya mai gida a nemi mafita ya zamu dinga zama da mai lalurar aljanu acikin gida
yarinya sai ciwoka kala kala gaskiya bazata saɓu ba" caraf Falmata ta karɓe tana faɗin"kema
dai kin faɗa wlh wannan bazai taba yiwuwa ba haka kawai watarana ta shafawa ƴaƴanmu
jaraba"
Ko kallonsu Bani kura bai yiba ya girgiza kansa ya yi waje, suma suka fito suna maida zance.
*ABUJA*.
*MALAM DUDU POV*
A matuƙar fusace Farooq ya miƙe tsaye yana yiwa malamin wani irin shegen kallo ya
ce"bangane mai kake nufi ba?, Kai malam fito kayi mani bayani yadda zamu fahimta ka tsaya
kana yiwa mutane wani zancen banza!" kallonsu Malamin ya yi sai kuma ya fashe da dariya
lokaci ɗaya kuma ya haɗe rai ya ce"kai yaro ni ba abokin wasanka bane na baku aiki kuma
baku yisa yanda ya kamata ba sannan kuma baku taɓa bibiyar maganar ba shiyasa nima nayi
muku shiru kuma a halin yanzu banida wani abu da zanyi akai kamar yanda na faɗa muku
wannan yarinyar *BA ITA BA CE!"*
# *BA ITA BA CE!*
# *Human trafficking*
# *Destiny*
# *Affection*
# *SQUAD 2024*
# *Nanameera ce!.*
[8/2, 9:17 PM] Nanameera✌: *BA ITA BA CE!..*
*MIKIYA WRITERS ASSO...*
*@Nanameera08* _wattpad_
*nanameera08* _arewabooks_.
*Nanameera ce!*
*Daga marubuciyar*
*NAANAH*
*TSAKANINMU*
*SHEIKH HEESHAM*
*FATTOMAH*
*nd now*
*BA ITA BA CE!*
# *SQUAD 2024*
```Page 04```
Kallonsa Mommy take da tsananin tashin hankali kwata-kwata ta kasa fahimtar abinda yake
faɗa kwakwalwarta ta tsaya cak!, Miƙewa tayi dan fita daga gidan saidai kafin takai kofar zauren
tayi baya luuu zata waɗi da sauri Farooq ya tare ta hankali tashe kuma yake furta "Mommy!!
Mommy!! Mommy" tuni jikinta ya saki hakan yasa kawai ya yi waje da ita, kallonta ya yi
hannunsa riƙe da goran ruwan sai sauke numfashi take a hankali shi kansa dauriya kawai yake
amma tabbas abun ya tabashi sosai, riƙo hannunsa Mommy ta yi murya bata fita sosai ta
ce"Farooq ka fahimci abinda malamin nan ke faɗa kuwa? ni ban fahimta sosai ba, nufi yake duk
abinda mukayi ya tashi a banza kenan?, muna tareda silar rugujewar burikanmu, nashiga ukuna
Farooq idan General ya fahimta wlh mun kaɗe har ganyenmu ni wlh..."
"Mommy dan Allah ya isa haka kina neman fasamin kai kema, please abar wannan maganar
muje gida doctor ya dubaki maybe ma jininki ya hau baki sani ba, zamu yi maganar ko zuwa
gobe ne"
Batada wani zaɓin hakan yasa dole tayi shiru badan tagama faɗar abinda ke ranta ba sanin
kuma halin Farooq na fusata yasa tayi shirun, fita ya yi ya koma front sit ɗin ya tayar ya motar,
tafiya kawai sukai yana furzar da wani irin numfashi sai wuci yake haka har suka ƙarasa gida.
*MAI ZAMANI POV*
Kamar bazai magana sai kuma ya ce"meya sameta?" kansa ƙasa ya ce"wlh Father wai jininta
ne ya hau" miƙewa General ya yi ya ce"okay Allah ya bata lpy zuwa anjima kazo zamuyi
magana akan tafiyarka Paris" ya juya ya fita. Bin bayansa Mami tayi har bedroom ɗinsa, zaune
ta taddashi yana waya hakan yasa ta zauna kan bedside drawer tana kallonsa saidai ya
kammala sannan ya juyo yana kallonta yana murmushi ya ce"Madam ya dai?" shiru tayi bata
bashi amsa ba hakan yasa ya miƙe cikin takunsa na isa ya ƙaraso inda take hannunta ya kama
sannan ya koma ya zauna ya zaunar da ita bisa cinyarta yana kallon kyakkyawar fuskanta ya
ce"Gimbiyata yau gida aka tuna ne?, Sarautar ce ta tashi?" da sauri ta rufe fuskarta a ƙirjinsa
tana dariya ta ce"kai kam bakada dama wlh" dariya shima ya yi sannan ya ɗago fuskar tata
yana kallonta cikin ido ya ce"kema ai kin sani banda ma yanzu kina hanani" turo baki tayi kamar
wata ƙaramar yarinya ta ce"to ai kai bakasan ka girma ba" jan kumatunta ya yi ya ce" to kenan
dan mutum ya girma bazai enjoying lfy ɗinsa ba?" girgiza kai kawai tayi sanin halin mijin nata ta
ce"ai shikenan".
*YOBE STATE*
*BANI KURA RESIDENCE*
Kallon Falmata ta yi da mugun mamaki ta ce"wai me kike nufi nifa bangane ba?" tsaki Falmata
ta yi ta ce"ke daɗina dake rashin fahimta wlh, yanda nace miki haka zamuyi idan dare ya yi yau
malam aikin dare zai yi kawai sai mu koreta ni a tunanina hakan shine kaɗai mafitarmu"
"Aikuwa bazaku taɓa samun nasara ba Allah yafi ƙarfin ku"
Da sauri suka juya suna kallon Bani kura wanda yake tsaye ya ɗage labule" a matukar razane
suka miƙe tsaye suna kallonsa duk idanunsu sun fito waje, ƙarasowa ya yi yana kallonsu
idanunsa sun rune na zallar ɓacin rai ya ce"kunji kunya wlh kuma kun bani mamaki, wace irin
tsana kuka yiwa wannan yarinyar ne?, me tayi muku da zafi haka da har kuke shirin rusa
rayuwarta?, idan tabar gidan nan ina take dashi inda zata zauna?, to wlh ku kuka da kanku ku
sani duk abinda kuke aikatawa Allah na kallonku kuma da sannu zai yi maganinku sannan
magana ta ƙarshe na yanke shawarar zan auri Aishatu saboda na inganta rayuwarta tunda
akwai aure tsakanin mu daga nan babu wanda ya isa ya ce zau takata a cikinku dan itama
sunan matata zata amsa". Da sauri Muhaira ta toshe bakinta tana girgiza kai inna'lil lahi wa ina
ilayhi raji'uun Baba ne zai ce zai aureta?, kenan saboda batada gata haka rayuwarta zata
kasance?, da sauri tayi ɗakinta saboda jin muryarsa yana ƙoƙarin fitowa daga ɗakin, tana zuwa
ta faɗa kan tabarmar tana rushewa da wani irin kuka mai taɓa zuciya tabbas rayuwarta batada
amfani kuma zuwa yanzu dole ta ɗauki matakin daya dace dan ko a mafarki bazata taɓa iya
auren Bani kura ba bare kuma a gaske dole ta samu wata mafitar wacce zata ɓulle mata saidai
batasan mene ne abinda zata yi ba!. Shi kuwa yana fitowa daga ɗakin ya yi waje dan zai je
wajen Mai unguwane ya shaida masa idan yaso zuwa gobe da safe sai a ɗaura auren kuma ya
yi hakan ne saboda ya samar mata da ƴanci cikin gidansa.
*11:30pm*
Wani irin baƙin hadari ne ya haɗo a sararin samaniya lokaci ɗaya garin yayi wani irin jaaa
kasancewar lokacin damuna ne ga kuma dare, a hankali kamar wata ɓarauniya haka ta fito
daga ɗakin tana sanɗa dan ko takalmi bata saka ba a hannunta ta riƙeshi babu kowa a tsakar
gidan sai kukan gyare da kakeji ga kuma kukan iska wanda yake haɗe da ƙura da sauri ta fice
daga gidan bayan ta zare sakatar ƙofar a hankali yanda wani bazai jiba, tana fita ta sanya
takalmanta ta kuma sake riƙe jakarta sannan ta fara wani irin gudu kamar wacce ake binta.
Gudun da take ya tsananta hakan yasa numfashinta ya fara janyewa saboda gudun da kuma
ƙurar iskar dake tashi ta ko'ina, ƙarfinta ne ya fara ƙarewa a hankali ta fara rage gudun nata
zuwa lokacin kuma an fara yayyafi, hakan yasa dole ta nemi waje ta tsaya sai a sannan ta
lurada a cikin kasuwa take amma duk shagunan mutane a rufe suke hakan yasa ta samu
rumfar wani shago ta shiga dan fakewa ruwan.
*MAITAMA DISTRICT*
*MA'EESHA POV*
Kallonta Mami tayi sai kuma ta ce"then yaushe zakuyi tafiyar?" cikeda fara'a ta ce"ranar Friday
Mami kuma kwana uku kawai zamuyi dan Allah ki bari naje" numfasawa ta yi ta ce"Ma'eesha
bawai hanaki nake ba saboda banason ki fita A'a ina gudun abinda zai je yadawo ne kawai" turo
baki gaba ta yi ta ce"Ayyah Mami wlh ba abinda zai faru kinga ai da ƴan department ɗinmu duka
zamu tafi nidai kawai ki yarda tunda Father ya yarda" harararta Mami tayi ta ce"oh sai kin tura
min baki gaba zan yarda?, ko shagwaɓar taki zaki min?" girgiza kai tayi tana murmushi ta
ce"sorry Mami nidai please ki ce Eh" ganin yanda ta marairaice fuska yasa ta ce"shikenan Allah
ya tsare hanya Amma ki kula sosai sannan banda shan ruwan sanyi Ma'eesha" rungume Mamin
tayi tana dariya ta ce"yawwa Mamina Allah ya bar min ke" taɓe baki Mami ta yi ta ce" wa Allah
ya bari da zai barni kedai ki yita shashancinki" dariya ta yi Mami ta ce" idan yaso bayan kin
dawo sai ki shirya dan mai martaba yanata tambayarki" da sauri ta miƙe tana tsalle ta ce"yeee
Mami zani masarauta?, harda ke Mami?" girgiza kai Mami ta yi ta ce" Allah ya baki nutsuwa,
Maybe hardani maybe kuma ke ɗaya zaki" da sauri tayi waje tana cewa"bari na faɗawa yaya
Farooq" murmushi Mami tayi