Showing 36001 words to 39000 words out of 44270 words

Chapter 13 - BA ITA BA CE! Free Books by Nanameera.pdf

11 May 2025

4071

ta fice
daga ɗakin babu kowa a parlon sai kawai tayi waje wata ƙofa ta gani tana facing tata da sauri
taje ta buɗeta dan ita tsoron gidan take ji, babu kowa a parlon sai ƙamshi da dake tashi ko'ina
tsaf yake bedroom ɗin ta shige da sauri taja wani irin numfashi saboda wani irin ƙamshi dake
tashi a ɗakin ga wani irin sanyin AC wanda ya gama ratsa ɗakin a hankali ta cigaba da taka
ƙafafunta har taje bakin gadon ta zauna tana bin ɗakin da kallo komai na ɗakin fari ne ta haka
tagane yana matuƙar son kala fara dan duk inda zai zauna zagaka farin abu ko coffee wani
ƙaton Enlargement tagani a kafe a ɗakin da sauri ta tashi taje wajen ta zuba masa ido tana
kallonsa haka kawai kuma ta yi murmushi ta ɗauki lokaci mai ɗan tsayi kafin ta koma ta zauna
kallon gefenta tayi taga wata ƙofa aikuwa da sauri ta tashi taje ta buɗe ƙofar, ƙofar ta glasses ce

daga ciki kuma wani wajene wanda aka ƙawata shi da kayan kiɗa masu matuƙar kyau da tsada
sai wasu kifaye da aka zuba cikin wani glass suna motsi gwanin ban sha'awa da gudu ta ƙarasa
wajen ta tsuguna tana zuba musu idanu hakan ba ƙaramin faranta mata rai ya yi ba. Wata
drawer tagani daga gefenta haka kawai taji tanason ta buɗe taga mene ne aciki ƙarasawa
wajen tayi ta buɗeta wani ƙaton Enlargement ne amma an rufeshi da wata ledar raping da
alama ana matuƙar ji da hoton turo baki tayi ta ce"to ya kuma a rufe ni so nake nagani" ajiye tayi
ta sake ɗauko wani shima dai kamar wancan ɗin an rufeshi ba'a ganin fƙarfe sake kwaɓe fuska
tayi kamar tayi kuka ita kaɗai ta ce"nidai wlh sai nagani meyasa za'a rufesu to?" gyara zamanta
tayi a nutse tashiga ɓare hoton kamar an sakata tana gamawa ta juyo dashi tana kalla wowww
hotonsa ne cikin wasu riga ɗinkin jamfa da babbar riga sai alkyabba irinta sarakai akansa
hannunsa riƙe da wata ƙaramar yarinya kallon yarinyar tayi sai kuma ta ce"kaiiiii wlh sunyi kyau
dama ni ce" ita kadai take murmushi dan ba ƙaramin kyau hoton ya yi mata ba ajiyeshi tayi a
gefe ta ce"yawwa sauran ɗayan" daga haka ta shiga ɓare wancan shima kamar ɗayan shi ne
dai a jikin hoton amma wannan karon shida wani babban mutum ne anyi masa naɗi irin na
sarakai fari ne shima kuma kyakkyawa ajin farko dukda ya fara manyanta amma hakan bai
hana kyansa fitowa ba wannan karon ɗin ma da wannan yarinyar tsaye a gabansu tana
murmushi kana ganinta kaga kyau da kuma zallar hutu tana sanye cikin wata doguwar riga iya
gwuiwarta an raba mata gashin kanta gida biyu anyi mata kalba dashi kowanne ɗaya ya zubo
kan kafaɗarta sannan an jera stones jajaye akai shafa hoton tayi sannan ta lumshe idanunta
batasan ko suwane waɗannan ɗin ba amma duk inda suke sun kasance jininsa ne domin duk
kama suke yi dashi abu ɗaya takeson yanzu ta sani shine wane shi???.


Haka ta ƙarasa yininta a ɗakin har akayi kiran sallar magrib sannan ta mayar da komai inda ta
ganshi ta fice daga wajen anan toilet ɗinsa tayi alwala tayi sallah sannan ta fito parlon ta zauna
tayi shiru tana tunane-tunane, har tayi sallar isha'i Zaki bai dawo gidan ba zuwa sannan kuma ta
fara tsorata da zaman nata ita kaɗai ganin har 9pm tayi yasa ta fashe da kuka ta takure kanta
jikin kujera tana kallon ƙofa tana cigaba da kuka.



*FCT, ABUJA*
*MAITAMA DISTRICT*

Da gudu suka shigo parlon suna zuwa suka rungumeta murmushi Mami ta yi tana kallonta ta
ce"ke daɗina dake Aleema wauta" turo bakinta tayi ta ce"kai Mami dan Allah to menayi kuma?"
dungure mata kai ta yi ta ce"bansani ba" kallon bayanta tayi sai kuma ta ce"A'a inasu
jakadiyar?" taɓe baki Aleema ta yi ta ce"wai Granny ce ta ce su fasa zuwa nazo ni kaɗai ina
maee?" girgiza kai Mami ta yi ta kalleta ganin tayi upstairs da gudu, tana shiga ɗakin ta
rungumeta cikin jin daɗi ta ce"naji daɗi ganinki sister" shiru Ma'eesha tayi mata tana murmushi
tunawa da abinda Granny ta faɗa mata yasa ta fashe da kuka daidai nan Mami ta shigo kallonta
ta yi ta ce"Aleema mene yasa kike kuka?" kallon Mami tayi cikin kuka ta ce"Mami da gaske
Ma'eesha batajin abinda ake faɗa kuma bazata iya bani amsa ba?" gyada mata kai Mami ta yi

ta ɗora hannu aka ta ce" mun shiga uku wlh Mami duk wanda ya yi mata wannan abun Allah ya
isa bamu yafe ba kuma wlh sai naje har wajen boka ya tona masa asiri shima kuma ya
kurumce" girgiza kai Mami ta yi sannan halin Aleema da shirme ta ce"Aleema ki dinga yin abu
irin na mutune kinji" turo baki tayi ta ce cikin shashshekar kuka"haba Mami ya za'a yi a cucemu
kuma ace bazamu rama ba wlh duk inda ake nemo boka sai naje na nemoshi ya yi mana
maganin duk wanda ya cutar da ita sai inda ƙarfina ya ƙare har mai martaba ma nafaɗawa"
girgiza kai kawai Mami ta yi ta ce"yanzu dai ba wannan ba ki tashi kiyi wanka sai ku sakko da
ita kuci abinci" okay ta ce sannan ta tashi ta shige toilet ita kuma Mami ta dawo kusada
Ma'eesha ta riƙe hannunta ta ce"zaki ci abinci?" gyaɗa mata kai ta yi sai kuma ta ce mata"Khalil
zai zo ki shirya" kallon bakinta Ma'eesha ta yi sai kuma ta yi mata alama da hannu tana
tambayar wa? "Khalil" Mami ta sake faɗa gyaɗa mata kai tayi sannan ta tashi ta fita.



Zaune suke a parlon ya zuba mata idanu yana kallonta ita kuwa ta sunkuyar da kanta kullum
son Ma'eesha sake shiga zuciyarsa yake musamman yanzu da son ya haɗa da tausayi yana
matukar tausayinta ko kaɗan baya jin daɗi rashin maganarta da kuma jinta amma ya yi
alkawarin da zarar an ɗaura musu aure to duk inda magani yake sai yaje ya nemowa Ma'eesha
har zuwa sanda ubangiji zai yaye mata bazai gajiya ba. Dukansa ta yi wanda yasa ya dawo
daga duniyar tunanin daya tafi da hannu ta tambayeshi mene girgiza mata kai ya yi ta haɗe
ranta tana dungure masa kai murmushi ya yi ya kamo hannunta ya riƙe cikin nasa ya ce a
hankali"sauran 1week a ɗaura mana aure" tagane abinda ya faɗa hakan yasa tayi dariya har
Saida beauty point dinta ya loma sosai yaji daɗin ganin tayi farin ciki ya ce"ki rubuto mana
ƙasashen da zamuje" kasancewar a hankali yake maganar yasa take fahimtar abinda ya faɗa
gyaɗa masa kai ta yi daidai lokacin Aleema ta shigo parlon zama tayi kujerar dake facing tasu ta
ce"wato shine aka tawo ake cin soyayya ko a kirani mu gaisa ko?" murmushi Khalil ya yi ya
ce"haba wa ya isa kawai daman jira nake nagama da ita sai na kira ki" harararsa ta yi ta
ce"haka fa" murmushi duka suka yi sannan suka cigaba da hirarsu gwanin ban sha'awa wani
abun Ma'eesha tana tayasu da sabon yarenta.


*MOMMY FOV*

Murmushi ta yi tana kallon Farooq ta ce"ni banga abin ɗaga hankali ba bayan in Sha Allah
nasara na tare damu" girgiza kansa ya yi ya ce"Mommy u can't understand what I'm talking
about Mommy ina magana ne akan Ma'eesha fa, kina gani fa aure zatayi nan da one week
kuma kinfi kowa sanin ni ba ƙaunar wannan guy ɗin nake ba kamar yanda shima baya ƙaunata
ko kaɗan" tsaki Mommy ta yi ta ce"kai daɗina dakai shashasha ne wlh bakasan abinda kake
yiba ina ruwanka da wanda zata aura?, mene haɗinka dashi idan tayi aurenta tayi nesa damu ai
shikenan daman ita kaɗai ce matsalarmu kaga idan babu ita komai zai zo mana da sauƙi ita
wannan zamu iya sakawa a kaɗata kawai kaga idan muka kashe General duk abinda ya
mallaka zai dawo hannunmu mu kaɗai tunda danginsa ba anan garin suke ba kafin su yi
tunanin yin wani abu tuni mun bar ƙasar" miƙewa ya yi ya ce"Mommy naji duk wannan amma ni

abinda baki sani ba shine indai ina raye to Ma'eesha bazata auri Khalil ba yanda banida damar
aurenta haka shima zan haramta masa ita" sakar baki Mommy ta yi tana kallonsa sai kuma ta
ce"lahhh kaji shashashan yaro" ko saurarenta Farooq bai tsaya ya yi ba ya yi waje abinsa haɓa
Mommy ta kama tana jinjina hali irin na Farooq. Tun kafin ya sakko yake jin dariyarsu yana
zuwa ya kallesu ko inda yake Khalil bai kalla ba hakan kuma ba ƙaramin ƙona masa rai ya yi ba
dan yaso ya tanka masa ne suyi tashin hankali ganin sunyi kamar basu san da inuwarsa a
wajen ba yasa ya juya ya fice yana buga ƙofar da ƙarfi da sauri Ma'eesha ta kalli ƙofar dan ita
bata ma ganshi ba ganin babu kowa kuma yasa suka ci-gaba da hirarsu tana binsu da kallo.



Shafa kanta Mommy ta yi ta ce"ki daina wannan kukan ke wai wace irin shashasha ce nafada
miki shida zaman aure da ita saidai a lahira amma anan dai duniya ya yi kaɗan bai isa ba sbd
haka ki kwantar da hankalinki kamar tsumma a randa" cikin kuka ta ce"haba Mommy kullum
haka kike cewa amma gashi har yau sauran kwana 6 ɗaurin auren banga ana niyyar fasawa ba
ni wlh bazan iya sharing miji da wata ba watar ma kuma kurma wacce koda naci mutuncinta ba
jina zatayi ba dan Allah Mommy ki taimaka minnnn!" ɗago fuskarta Mommy tayi ta ce"kawo
kunnenki na faɗa miki wani abu" miƙa mata kunnen tayi ta raɗa mata da sauri ta kalli Mommy
tana murmushi ta ce"dan Allah Mommy da gaske kike?" gyaɗa mata kai Mommy tayi ta
rungumeta tana dariya ta ce"kaiiiii amma naji daɗi sosai Mommy" da sauri Khalil ya saki handle
ɗin ƙofar gaba ɗayansa ya jike da gumi kana kallon fuskarsa kasan hankalinsa a tashe yake

"Khalil lafiya?"

Da sauri suka kalli ƙofar sai kuma suka miƙe tsaye dafe ƙirjinta ta yi ta ce"mun shiga uku
Mommy badai sunji ba?" shiru Mommy tayi tana kallon bakin ƙofar murɗa handle ɗin akayi suka
shigo suna kallonsu duka His Excellency ne ya ce"


_Free pages sun kusa ƙarewa ƴar uwa only 4 pages remain isn't free it's 500# via 9086030007
Hauwa lawan adamu Opay digital service evidence via 08106608363 or 07041901078 ki biya ki
karanta cikin kwanciyar hankali akwai special group posting sau biyu a rana with is 1k only
karku manta zaku iya fara payment yanzu ƙofa a buɗe take_

_Bamu fara komai ba cikin littafin BA ITA BA CE akwai abubuwan da karantawa kaɗai zai iya
fahimtar dakai karku bari a baku labari_


# *BA ITA BA CE*
# *Destiny*
# *Unconditional love*
# *Power*

# *SQUAD 2024*
# *Nanameera ce ✍️!*.
[8/12, 9:18 PM] Nanameera✌: *BA ITA BA CE!...*


*Nanameera ce ✍️*


*MIKIYA WRITERS ASSO...*


```Page 17&18```


"Lafiya na ganku tsaye?" wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya suka sauke sannan Mommy ta yi
murmushi ta ce"daman fita zanyi sai naji an turo ƙofar" kallonta Khalil ya yi sai kuma ya kalli
Ramlah wacce take ta binsu da ido ya ce"ki shirya zamuje asibiti" gyaɗa masa kai tayi sannan
ya juya ya fita his Excellency ma yabi bayansa dafe ƙirji Mommy ta yi ta ce"Allah nagode maka"
numfasawa Ramlah ta yi ta ce"bari naje Mommy" okay ta ce mata sannan ta buɗe ƙofar ta fita
ita kuma ta nemi waje nan ta zauna tana tunane-tunane. Kwance ta tarar dashi kan bed ya rufe
idanunsa ƙarasawa tayi ta zauna gefen gadon a hankali ta ce"doctor gani" shiru Khalil ya yi
mata kuma ba bacci yake ba saida ta maimaita sau uku sannan ya tashi zaune yana kallonta da
idanuwansa wanda sukayi ja da Mamaki ta ce"bakada lpy ne?" girgiza mata kai kawai ya yi
sannan ya tashi ya shige toilet taɓe baki ta yi sai kuma ta tashi ta fita dan daman bata gama
abinda take ba, fitowa ya yi cikin wani yadi maroon colour mai shara-shara ɗinkin jamfa da
wando ya ɗora hula zanna akansa fuskarsa maƙale cikin glasses kamar koda yaushe gaba ya
yi tana ganin haka tabi bayansa zaune ta sameshi a motar yana danna wayarsa gidan gaba ta
buɗe ta shiga sannan ya ajiye wayar yaja motar suka bar gidan. Murmushi Aleemah ta yi ta
ce"wlh kuwa Mami nifa na ƙagu ayi auren nan nasan ma gobe ko jibi su Fulani zasu zo" Mami
da take tajewa Ma'eesha kanta ta yi murmushi ta ce"ke kam Allah ya shiryaki Aleema in banda
abinki ai auren nufine na Allah kuma naga Zahrah ba wani shekaru ne da ita ba, abun da kamar
wuya Fulani tazo kinsan dai halinta" taɓe baki Aleemah ta yi ta ce"wlh Mami ita take jawowa
kanta bakiga yanda take wulaƙanta samari ba duk kuɗin mutum idan ya ce yana sonta sai ta
nemi ta ci masa mutunci kowa ya kasa gane kanta kuma taƙi ta faɗi wanda take so" girgiza kai
Mami ta yi ta ce"Allah sarki to Allah ya shiryata maybe Gani take basu yi mata ba ko kuma
akwai wanda takeso amma idan ba haka ba ai Zahrah tanada hankali kuma tasan me take"
murmushi Aleemah ta yi ta ce"ai ni wlh kullum addu'a nake mata insha Allah sai ta rasa wanda
zata aura tunda ita ruwan ido ta tsaya" girgiza mata kai Mami ta yi ta ce"ba'a faɗar haka ki dinga
yi mata addu'a tagari" turo baki gaba ta yi batace komai ba har Mami ta kammala abinda take
tashi tayi ta kalli Ma'eesha wacce tayi tsuru ta ce" taso muje kici abinci zamuje unguwa" maƙale
kafaɗa ta yi alamar bazata jeba tunda ta tashi daman babu wanda ta kula hatta General daya
shigo dubata bata kulasa ba, kamo hannunta Mami ta yi suka fice daga wajen sanin inda ta ita
ne bazata tashin ba. Kallon Aleemah ya yi wacce take sanye cikin wata doguwar riga ta atampa

me ɗan kama jiki kallo ɗaya ta yi masa ta ɗauke kai dan ita daman bata wani ƙaunarsa duk
sanda tazo gidan batason abinda zai haɗata dashi har tayi gaba taji ya ce"Aleemah" tsayawa
tayi amma bata juyo ba takowa ya yi cikin tafiyarsa ta isa ya tsaya a gabanta haɗe hannayenta
tayi a ƙirji ta zuba masa idanu ɗan cute smile ya yi ya ce"ya kike?" "Lpy" cewar Aleemah
numfasawa ya yi ya ce"daman inason magana dake idan babu damuwa please" ta ce"ina jinka"
Farooq ya ce" mu ɗan zauna mana please" ɗaga kafaɗa tayi sannan ta zauna kan ɗaya daga
kujerun da akayi ado dasu a garden ɗin zama ya yi shima yana facing ɗin ta ya ce" na daɗe
inason na samu damar faɗa miki abinda ke cikin raina amma sai nake ganin kamar bazaki
aminta dani ba, wlh Aleema ina matukar sonki tun ba yau ba dan Allah kar kiyi rejecting
soyayya ta please leema" tunda ya fara magana Aleema take kallonsa with so much surprised
koda wasa bata taɓa tunanin haka daga gareshi ba duba da yanda yake maganar zaka fahimci
har cikin zuciyarsa haka yake nufi miƙewa ta yi ta ce"I'm so sorry amma ni ban taɓa soyayya ba
and kuma banajin zan iya farata yanzu coz karatu shine abinda nake focusing yanzu dan Allah
ka fahimceni" tana gama faɗin haka ta juya tabar wajen da kallo kawai Farooq ya bita sannan
ya girgiza kansa wani killer smile ya yi ya ce"karki damu yarinya da sannu zaki zo hannuna" ya
tashi ya yi waje dan daman fita zai yi


"Me kika tsaya yi?"

numfasawa ta yi ta ce"wlh Mami na ɗan tsaya magana da Farooq ne" "Farooq kuma mene ya
haɗaki da magana dashi?" murmushi ta yi ta ce"Mami karki damu" taɓe baki Mami ta yi ta
ce"kije ku ci abinci zuwa anjima Khalil zai zo ku fita nima yanzu fita zanyi" okay Aleema ta ce
sannan ta shige ciki, Da sallama ta shiga zaune ta tarar da Mommy tana danna wayarta da
alama magana mai muhimmanci take tana ganin Mami ta tashi tana murmushi ta ce"sannu da
zuwa" zama Mami ta yi ta ce"yawwa " "ya jikin Ma'eesha?" murmushi Mami ta yi ta ce"da sauƙi
Alhamdulillah yau ne dai ta tashi da abun dan taƙi kula kowa" girgiza kai Mommy ta yi ta
ce"Allah sarki ubangiji ya yaye mata cikin sauƙi" "Ameen" cewar Mami, Mommy ce ta ce"yawwa
daman munyi magana da talatu ta ce za'a samu kayan" "Nima daman abinda ya kawoni kenan
zuwa anjima idan kin shirya zamuje siyan ragowar wanda akayi order kuma sun zo to za'a je
jere in sha Allah" murmushi Mommy ta yi ta ce"Allah sarki Ma'eesha da yanzu tana ta surutu
kala-kala ta ce wannan ta ce wancen, to Allah ya kaimu anjiman daman babu abinda nake"
okay Mami ta ce Sannan ta tashi ta fita. Murmushi Mommy ta yi ta ce"dani kike zancen
Asma'u".



Ƙarfe 5pm Khalil ya iso gidan har parlon ya zo ya kama hannun Ma'eesha suka fita shida ita
suna gidan gaba Aleema kuma na gidan baya har suka isa mall ɗin babu wanda ya ce komai a
cikinsu kowanne da abinda ya dameshi. Siyayya sosai suka yo duk wani abu na nau'in kaya
babu wanda Khalil bai siyawa Ma'eesha ba wani abun ita take nunawa wani kuma shi yake
zaɓar mata hatta Aleema saida ya siya mata sai wajejen 6:30pm suka bar wajen kai tsaye kuma
wani park ya kai su wajene wanda aka ƙawatashi da kayan wasan yara irinsu lilo, swimming

pool da masu kayan wasan sannan akwai nau'i na abinci kala-kala a wajen zama sukayi kan
kujeru suna Kalle-Kalle ya yi hakane kuma sbd ya ɗauke hankalin Ma'eesha dan Mami ta faɗa
masa halin da take ciki dukansa ta yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login