Showing 15001 words to 18000 words out of 25935 words

Chapter 6 - BA A BORAN NAMIJI HAUSA NOVELS BINTA UMAR ABBALE .txt

11 Nov 2025

2680

kan hanya nake gabad'aya na kasa iya danne lamarin a zuciyata ina ganin ko da Allah ya kaddara auren da wahala Yaya Rabi'u ya mutunta ni, duba da yadda ya kasa jure kutsen da akayi masa. Babanmu ya yi hakan ne da zuciya d'aya, Kuma a hasashen da yake a hannun Rabi'u kad'ai zan iya samun nutsuwa, sai dai har yanzu bai fahimci waye shi ba. Yaya Rabi'u bai ajiye kansa a kusa ba, yanda na fahimta duk tsokanar da yake mini ba ta da ala'ka da abinda Babanmu yake tunani. Ni kaina na jima ina rokon Ubangiji ya cire mini abinda nake ji a zuciyata dangane da shi. Amma duk kwanan duniya abin yana nan a mak'ale a zuciyata kamar ana tiri.

Na isa gidan Inna Hauwa a gajiye ga damuwa da ta yi mini dabaibayi. Zubewa na yi akan tabarmar dake shimfid'e a rumfarta na rufe fuskata da mayafina hawayen da nake dannewa suka fara zuba. Kukan kad'ai shi zan yi na ji sassaucin abinda yake damuna. Allah ne ya jarrabe ni da san Yaya Rabi'u duk da cewa; Akwai tarin maza masu nagarta da suke 'kaunata amma ba na Jin su a raina ko kad'an zuciyata ta fi karkarta a zuciyar da ba ni da gurbi. Da zan iya cire son Rabi'u da tuni na cire na jefar na huta da damuwa.
Inna Hauwa ta shigo rumfar tana fad'in." Kyauta daga zuwa kuma sai bacci, ko idonki biyu ne?"
Shiru na yi mata ina ta ko'karin danne mahaukacin kukan da yake ko'karin kufce mini. Hannu tasa za ta janye mayafin dana rufe fuskata. Na ri'ke da kyau ina girgiza mata kai.
Ta ce." Kuka ki ke yi Kyauta me akayi mini?" Zaune na tashi ina kare fuskata.
Ta ce." 'Karya ki ke yi da dalili wannan kukan na ki, ki fad'a mini abinda akayi mini."
Shiru na yi ban ce mata komai ba sai da ta sake magana tukkuna na yi mata bayani wai ko da shawarar da za ta ba ni. Kawai sai ta fara fad'a cewa; Yanzu an daina haka, auran na gani inaso ma ana samun tangard'a ballanatana na cushe! Idan tana raye ba zata bari ayi abinda za a yi kuka daga baya ba.
Na so nayi mata bayani amma ta'ki saurarata dama kuma macace mai fad'an tsiya da mita.
da zan tafi ta ba ni humra mai kamshi da dari biyu
Humrar kawai na kar'ba ta yi ta yi dani na 'ki kar'bar kudin. Na yi mata sallama tana jadadda mini cewa; Na fad'awa Nene gobe ta tsammaci zuwanta.
Na yi dakacen sanar da Inna Hauwa lamarin, domin na riga na san halinta 'yar tada zaune tsaye ce, duk da suna wasan 'kanwar mata da Babanmu hakan ba zai hana ya tsinkata ba muddin akan lamarin Rabi'u ne, ni kuma ba zan so hakan ba, wata'kila ita kanta Nene ta fuskanci 'bacin rai mai tsanani.
Dan haka ko da na koma gida ban tashi maganar ba, har dare dai ba ni da kuzarin kirki. Ina kwance a rumfa na ji shigowar Yaya Ibrahim gidan. Babanmu Yana tambayarsa Yaya Usman saboda ya kwana biyu bai zo ba, Yaya Ibrahim din ya ba shi amsa da cewa; Yanzu sukayi waya yana kan hanya.
minti goma sha biyar a tsakani Yaya Usman ya shigo gidan, ina jin suna gaisawa na yi shiru gabana na bugawa! kiran sunana da ya yi shi zaburar da ni, na tashi zaune ina amsawa.

Tsakargidan na fita na raku'be a kusa da Nene cikin ranshin kuzari na gaishe su suka amsa Yaya Ibrahim Ya zuba mini Ido yana kallo kafin ya fara tambayata. Na ce." Lafiyata lau Yaya." Babanmu ya yi gyaran murya kafin ya fara magana akan abinda ya tarasu.
Ya numfasa ya cigaba da cewa" Ko bana raye a doran duniya ban amince ku aurar da Kyauta ga wani ba face Rabi'u shi na mallakawa ita a matsayina na Ubanta wanda shari'a ta ba ni damar za'ba mata miji nagartacce! wannan shine; dalilin tara ku anan."
Yaya Ibrahim shi ya fara sukar lamarin, Yana ta ko'karin nunawa Babanmu illar hakan da ya aikata, akan wane dalili zai yanke hukunci ba tare da ya saurari ra'ayin wanda akayiwa bajintar ba. Shi fa ya san waye Rabi'u tare da d'abi'unsa tunda tare suka taso, dalilin da yasa kenan kanwarsu bata ji'kuwa tunda an samu banbancin ra'ayi. Rabi'u Yana da 'kafafa da izzah uwa uba kuma rashin ha'kuri, gashi dai ubansa ba kowa bane amma bai ajiye kansa a kusa ba. Sannan duk lokacin da zaman majalisa zai had'a su yana jin irin zantunkan da yake yi akan irin macen da yake so ya aura wayaiyiya kuma 'yar manyan mutane, wannan shine kud'irin Rabi'u, Yana ganin idan a ba shi kyauta kamar an yi masa kutse ne, tunda ba shi ya ce yana sonta ba, zai ajiye a ransa ita din matar ladan noma ce. Kyauta macece mai ha'kuri da kawaici a ganinsa ba ta dace da zaman aure da Rabi'u azababbe ba wanda duk cikin abokanansu babu wanda bai san halinsa na musu da cacar baki ba, ga zahirin gaskiya Amma idan ana musu dai shi zai k'aryata mutum ya kawo k'auli da ba'adi, kuma ya tsaya kai da fata maganarsa itace daidai duk da ya san 'karya ya 'kir'kira, haka d'abi'arsa take yana da
baki sosai kuma ba a kada shi a magana. Yana zuwa majalisarsu ta samari take d'aukar zafi. wasu lokotan a tashi lafiya wani sa'in kuma a tashi da hayaniya!

Duk da Yaya Ibrahim ya bud'awa Babanmu asalin Rabi'u, amma sai ya take ya rufe shi da fad'a ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba. Yaya Ibrahim ya shiga ba shi ha'kuri ganin yanda ransa ya 'baci. Shi kuwa Yaya Usman fad'i yake Allah ya sanya alheri Ubangiji yasa da mu za a yi.
Nene dai tashi ta yi ta shiga d'aki uffan ba tace ba, ga dukkan alamu al'amarin bai kwanta mata ba, sai ya kasance ni da Babanmu ne kawai muke son Rabi'u, domin duk sukar da Yaya Ibrahim ya kawo a kansa bata samu gurbi a zuciyata ba, abinda nake ji dangane da shi yana nan a jibge ko 'kwarzane bai yi ba.

Washe gari da sassafe sai ga Inna Hauwa. Nene ta dinga tambayata lafiya domin zuwanta da safe ya bata tsoro! Ina d'aki a kwance na ji tana yi mata bayani abinda na je na fad'a mata kai tsaye kuma gurin Babanmu ta zo. Nene dai ba ta yi farinciki da zuwanta ba ko ga yanayin yanda take bata amsa.
Muryar Bababmu na ji a rumfar yana tsokanar Inna Hauwa kamar yanda ya saba.
Suka gaisa tana rama tsokanar da yake mata kafin ta kutso da ainihin abinda yake tafe da ita. Sai kawai na ji maganarsa a fusace ya juya lamarin kan Nene ya rufe ta da fad'a wai duk wanda zata je ta fad'awa lamarin nan bai isa ya hana shi iko da abinda ya haifa.
Inna Hauwa tana fad'a yana fad'a. Kawai sai na ji Nene ta fashe da kuka tana fad'in." Hauwa ta shi ki tafi dan girman Allah ki cire kanki daga lamarin nan babu ruwanki, ki kyale shi ya yi abinda ya ga dama."
Ganin tana kuka sai ya fita daga rumfar bai sake wata maganar ba. Ita kuma Inna Hauwa tana ta nanata maganar tare da fadin kuskuran da Babanmu yake ko'karin aikatawa.
Nene ta ce." Yanda na bi lamarin nan da addu'a Hauwa ke ma ki bi shi da addu'a. Bana san abinda zai daga mini hankali ko kad'an.
Wannan furucin shi ya sanyayyar da jikin Inna Hauwa ta bar maganar suka shiga yin wata da ta shafi zumuncinsu.

Lamarin ya cigaba da tafiya cikin rashin da'di domin tunda lokacin da Babanmu ya furtawa Rabi'u abinda yake cikin ransa ya d'auke mini wuta, idan za mu had'u a hanya sai ya d'auke kansa. Hakan da yake mini ya fara sosa mini rai dan na tsani wula'kanci da a rayuwata! wasan da yake mini ya daina, ko siyan gawayi na je gurinsa sai da yasa yara su ba ni, kuma baya kar'bar kudin. Ganin abinda yake yi mini ya yi yawa yasa na kama kaina.
Gabad'aya ma na daina bi ta hanyar gidansu ko makaranta zan tafi sai da na yi zagaye ta bayan layi. Na daina zuwa siyan gawayi. Sai Yaya Ibrahim ya shiga sayo mana buhu guda Yana ajiyewa. Na ji dadin hakan sosai domin dama neman hanyar da zan nesanta kaina da Rabi'u nake yi.
Tunda maganar aure ya shiga tsakaninmu na daina zuwa gaisuwar Juma'a gidansu saboda ina jin tsoron na riske shi a gidan ya yi mini kallon banza. Bayan haka kuma ina jin kunyar Inno yanzu gabad'aya ba na so na had'u da 'yan gidansu ko a hanya ne saboda abinda yake shirin wanzuwa.

Watanni biyu kenan ban sa Rabi'u a idona ba. Na damu sosai, domin ni kad'ai na san ciwon da zuciyata take yi mini a kansa, ina ko'karin dannewa ne kada ya fuskanci yanda nake sonsa ya samu makamin da zai ya'ke ni, shiyasa na d'auki wannan matakin.
Ranar wata Alhamis misalin takawas da rabi na dare sai ga yaro ya shigo gidanmu wai Kyauta ta je Rabi'u yana kiranta.
Na ji gabana ya yanke fad'i! Ko sunansa aka ambata a gabana sai na ji wani iri. Ban ta'ba tsammanin zai zo zance gurina duba da yanda ya ke nuna halin ko'in kula akan lamarin.
Yaron ya kama hanya ya fita bayan Nene ta ba shi amsa kan cewa ya ce gani nan zuwa.
Na jima kafin na tashi da sanyi jiki na canza tufafi na fesa turare mai kamshi a jikina sannan na zurma hijabi har 'kasa na fito da dadduma a hannuna.
Nene dai ba ta ce komai ba har na fita daga gidan na same shi a tsaye a soro ya fesa kwaliyya da sabuwar shadda milk da dinkin 'yan birni hankalinsa gabad'aya yana kan wayar dake hannunsa.
A sanyaye na shimfid'a daddumar ina fad'in." Yaya Rabi'u ka zauna."
Gwasale ni ya yi ta hanyar fadin shi fa ba zance ya zo ba menene zan wani shimfid'a masa dadduma.
raina ya 'baci na murguda baki tare da d'auke daddumar na rungume a kirjina ban sake kallonsa ba. Sai na tsinkayi maganarsa yana fadin. To in banda abinki Kyauta ai da mayafi mai raga raga ya kamata ki fito domin na duba zahirinki meye zaki zurmo hijabi sai ka ce wadda za ta je gidan gaisuwa. Shi fa lamarin aure yana buk'atar nazari da tantancewa."
Na 'kulu sosai da maganarsa domin duk kawaicina kasa daurewa na yi na ce." Ai da yake bazawara ce ni. dole na fito da mayafi mai nuna tsaraici domin ka tantance ni."
Murmushi ya yi, ya shafa sajen fuskarsa Ya ce." Ni ban fad'a ba, amma dai kin san ba ni ke aka yi ba ni, na gani ina so ba, dole akwai nazarin da nake so na yi a kan ki."
Kasa daurewa na yi nasa masa kuka ina fad'in." To ni ma ai ba sonka nake yi ba. Nani'ka mini kai aka yi, kuma saboda farincikin mahaifina na kar'be ka."
Dariya ya kama yi yana kallona kamar wanda kukan nawa yake masa
d'adi!
Nasa gefen hijabina na goge fuskata na yi nufin shigewa cikin gidan sai ya tari gabana da sauran dariyar a tare da shi. Ya ce." Kyauta ni abinda yake ba ni haushi dake saurin kuka yanzu fisabillahi menene abin hawaye a cikin maganata idan ba shagwa'ba ba."
Hararasa na yi na murgud'a baki na ce." To ai kaine na ji kana wata magana ta daban. Shiyasa na fayyace maka abinda yake raina ni ma ba wani kwanta mini ka yi a rai ba."
Ya dinga kallon fuskata yana murmushi. Sai na kasa gane abinda yake kallo Na sake murgud'a bakina na juya masa 'keya. Ya sake fuskantata yana kallon bakina. Nan na fahimci abinda ya ke kallo tuntuni! a karo na uku na sake murgud'a bakin ina hararasa.
Ya dinga k'yalkyala dariya Yana fad'in." Lallai kin raina ni, yarinya daga harara sai murgud'a baki ashe haka za mu yi auran kina yi mini tsiwa!"
Uffan ban ce masa na kawar da kaina.
Ya cigaba da zantukansa idan na ga dama na ba shi amsa wani kuma idan na ji da rainin hankali na murgud'a masa baki! tun a nan na fahimci salon dana d'auka yana burge shi. haka mu ka yi zancen a tsaye kusan awa d'aya da rabi duk k'afafuna sun yi tsami.
Yaya Ibrahim ya shigo soron sai ya tsaya Yana kallonmu. Kafin daga bisani ya mika masa hannu suka gaisa kowanne fuskarsa a d'aure gaisuwar ma dai kamar ta dole sukayi. Ban ji dadin hakan ba a cikin raina, domin ina so tun kafin tafiya ta yi nisa a tsakaninmu su daidaita kansu komai ya wuce tunda surukantaka ta shiga tsakani.
Da zai tafi ya bani kyautar dari biyar sabuwar kar. 'Kin kar'ba na yi sai kawai ya lalubi hannuna ya saka mini ya fice daga soron ba tare da ya saurari maganar da nake yi masa ba.

Kwanan farinciki na yi a ranar ganin yanda na fara shawo kansa cikin 'kan'kanin lokaci. Kuma na fahimci akwai 'bur'bushin sona a tare da shi kawai dai ba zai nuna ba ne saboda 'ki fad'i da kuma wane k'udiri da yake cikin zuciyarsa.

Haka muka cigaba da soyayya mai tafe da rigima domin duk hak'urina a wasu lokotan idan ya kai ni bango tutsu nake masa, na daina kula shi ko ya zo zance bana fita. Dan akwai lokacin da mukayi fad'a ya zo yana fad'a mini irin kalar matar da yake so 'Yar duma-duma kuma wayaiyiya 'yar gayu mai zurfin karatun boko. raina ya soso sosai amma ban yarda na yi masa kuka ba saboda ba na so ya cigaba da ganin lagona sai dai ban kyale shi ba sai da na narka masa ba'kaken maganganu! masu zafi ban saurare shi ba kuma na buge zanina na shiga gida zuciyata kamar ta fashe saboda tsananin kishi.
Fushi ya yi mai tsanani! Sai na nuna masa na fi shi Koda wasa ban kira shi a wayar da ya siya mini ba, kuma ban yi masa text na kalaman soyayya ba irin wanda na ke yi masa kullum. wata hudu ba ma kula juna har Nene ta fahimci wani abu ta dinga yi mini fad'a akan dole na koyi ha'kuri da juri'a tunda na san halin wanda Allah zai hada ni zaman aure da shi. Jinta kawai na ke yi amma bana tsammanin zan neme shi domin ya kai ni ma'kura 'kaunar da nake masa ita ta haddasa tsananin kishinsa ba na so na ji yana ambatar wata mace a gabana balle ya yabi surar jikinta. shi kuma ya kasa fahimtar hakan. Na lura mutum ne shi mai zara da k'ulafucin 'ya'ya mata.

Misalin karfe takwas da minti goma na ranar wata Juma'a muna zaune a tsakargida harda Babanmu da Yaya Ibrahim Muna hira yaro ya shigo Yana fad'in ana sallama da Kyauta inji Rabi'u.
Nene ta ba shi amsa ya fita.
Ta shi na yi na shiga d'aki na kwanta ba ni da niyyar fita minti goma a tsakani na fara jin hayaniya tana tashi a tsakargidan tsakanin Babanmu da Nene Yaya Ibrahim Yana sa baki.
Ina fitowa na fahimci akaina suke rigimar. Yaya Ibrahim ya kalle ni tare da ba ni umarnin tafiya gurin Rabi'u. Da sauri na sa hijabina na fito lokacin Nene ta d'auki zafi tana ta sakin maganganu masu kaushi! Babanmu ya yi mata shiru ya 'kyaleta! dama an ce mai ha'kuri bai iya fushi ba. Ni dai ganin yanda abin ya zama yasa da saurin gaske na fita hankalina ma duk baya jikina, ina Jin tsoro Rabi'u ya samu Babanmu ya fad'a masa rikicin da mu ke yi lamari ya 'kara dagulewa. Shiyasa koda na fita na sassauta fuskarta na gaishe shi. Aikuwa ya amshe da sauri yana ta jana da hira. Cikin raina na ce iskanci banza haka zan dinga yi maka a duk lokacin da kayi mini abinda ban gamsu da shi ba.
Mun jima muna hira kamar wani abu bai ta'ba giftawa ba a tsakaninmu.Ya d'auki dari biyar ya ba ni kamar koyaushe na yi masa godiya sosai kafin na koma cikin gidan da tunanin lamarina da shi.

***
Sannu a hankali na kammala sakandire lokacin na kuma yi haddar al'kur'ani mai girma tare da wasu littafan addinin musulunci. Lokacin auranmu Yana ta gabatowa daga 'bangaran mu komai an tanada lokaci kawai ake jira.
Yaya Rabi'u kuwa abubuwa sun kacud'e masa, babu gurin zama sannan bai gama had'a lefe ba. Akwatina biyu ya siya masu sau'kin kud'i amma turmin bakwai kawai ya zuba a ciki 'Yan uwansa mata suka zuba masa abinda ya yi saura. Sai aka fara fafutukar gurin zama domin ya dage shi ba zai zauna a cikin gidansu ba. Kuma gashi babu kud'in kama haya. Kuma shi a ra'ayinsa ya fi so ko hayar zai kama shi kad'ai ba ya son wanda zai yi tarayyya da wani.
Lokacin da Babanmu ya ji dambarwar da ake yi da shi sai ya dinga fad'a Yana cewa ai lefen ba dole ba ne. Tunda ba shi da kud'in kama hayar gurin zama sai ya rushe lefen ya je ya biya gidan da zai zauna turmi uku da takalmi da mayafi ya isa albarka ake nema a aure ba wani abu ba. saboda haka aure fa ba za a 'kara wasu wattanin ba, za a d'aura shi a lokacin da aka gindaya ba za a janye ba.

Babu wanda ya sani a cikin gidanmu Babanmu ya siyar da sabon kekensa da Yaya Usman ya siya masa dan ya dinga zuwa kasuwa. Ya kira Rabi'u ya bashi dubu hamsin kyan-kyan! a hannunsa yace ya je ya kama hayar dasu.
Sai da aka kwana biyu tukkuna da Yaya Ibrahim ya lura babu keke a gida ya tambayeshi bai 'boye ba ya fad'a masa abinda ya aikata.
Yaya Ibrahim ya ji ciwon lamarin sosai! amma sai ya danne bai ce masa komai ba ya 'kyaleshi duk domin a zauna lafiya.

Haka aka kawo lefena babu arziki sai kace na bazawara mara gata. Har kuka na yi da naga irin k'ananun atamfofi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login