Showing 48001 words to 51000 words out of 65323 words
da ta fito zata fita jitai wani irin
fitinannen tashin hankali yakawo mata farmaki da k'arfi tace "ke gidan uwar wa zakije ne" ta
fad'a tana kafe Maryam da wani irin kallo.
Ba Maryam ba hatta MD da Nassar sai da suka zabura suka zuba mata ido, ita ko Maryam
babu wani shakka ko tsoro tace "haba Mama wallahi har kin bani tsoro irin wannan ihun haka
kamar aradu?"
Wani irin tuk'uk'i ne ya tokare haj. Sailuba ta kafe Maryam da wani shegen kallo zuciyar ta yana
suya yaushe Maryam ta sami damar fad'a mata magana haka lallai in batayi wasa ba wata rana
sai Maryam ta zageta anata haukan tunanin kenan.
Amma azahir cewa tayi "ni nake ihun bab? wai ma tukun me zakiyo ad'akin matar nan bana
hanaki mu a'mala dasuba?"
"Hummm mama kenan ai duk randa babu ke dole itace uwata, ko baki tab'a tunanin hakan
bane? kuma kadafa ki manta mama ba a raba hanta da jini mun riga mun had'u babu yadda
zakiyi tunda ta haifa kin haifa dole ne itama ta sarara agidanna dan Allah mama ki daina irin
wannan abun bashi da amfani ko kad'an haba"
Fashewa kawai haj. Sailuba tayi da kuka saboda tsabar tashin hankali da bak'in ciki kasa yi
mata magana tayi har ta shige d'akin Ammey tana kallon ta.
MD kuwa wani irin annushuwane ya kamashi sanda Maryam ke fad'awa haj. Sailuba magana
wani arnen murmushi kawai yake saki, yana ganin Maryam ta shige d'akin Ammey ya k'arasa
kusa da haj. Sailuba yace "hajajju makkatu me kike tunanin zai faru duk ranar da wannan
yarinyar tagane cewa ke ba uwarta bace uwar rik'o ce? Ya zakiji lokacin da tasan cewa mahaifiyar ta kike sawa tanawa cin mutunci da wulak'anci
Me zai faru idan tasan cewa ba dan Allah kike rok'on taba kina rik'on tane saboda wani banzan
dalili naki mara amfani?
Hhhhhhhhhhhh kad'an kika gani Sailuba domin Allah baya bacci"
Babu kunya haj. Sailuba ta kuma fashewa da kuka tana kallon MD kafin tace "hummmm
Muhammad kenan na maka alk'awarin bazan bar hakan yafaruba sannan kuma ina Mai farin
cikin sanar dakai cewa komai ya kusa zuwa k'arshe rayuwar Maryam zaiyi wulakantar da babu
wani rayuwa da zata kai tata lalacewa zata bi maza zata yi shaye shaye zata yi sata zata zama
abin kwatance da misali na miyagu da munanan halayya"
Sosai gabansa ya fad'i da jin furucin ta domin yasan zata aikata fiye da hakama jiyai hankalinsa
yai masifar tashi ya dubeta da tsantsar b'acin rai yace "Allah ya fiki yafi waninki Sailuba kuma
duk abinda kike tak'ama dashi insha Allah hakan ki bazai cimma ruwaba"
Wata shegiyar dariya ta saki tace "zaka gani zaka kuma tabbatar muzuba nidakai shege ka
fasa" daga haka tayi waje hankali a tashe.
Sosai maganganun ta suka tsaye masa rai sai dai kamar yadda yake tsaye wajen yiwa Maryam
Adda a ya zama dole ya k'ara zage damtse.
Maryam kuwa tana shiga d'akin Ammey ta rufeta da fad'a akan maganganun da taji tana
sakarwa haj. Sailuba tace mata koba komai matsayin uwa take awajen ta dan haka ta rik'a
sanin irin maganan da zata fad'a Mata.
"Nifa Ammey indai akan kune babu abinda zaki fad'a min na fahimta matar da bata da lokacina
sai na gantali kullum tana tafe a hanya ita ba kasuwanci ba ba komaiba, ai wallahi duk laifin
Baffa ne da yasake mata haka dayawa shiyasa take iskancin ta son Rai"
"Ungo nan Ammey ta yiwa Maryam tace "idan har da gaske kina ganin mutunci na kamar yadda
kika fad'a to kada ki sake kinji ko?"
"Naji Ammey, ina Baffa shi nazo nema"
"Lafiya kike neman Baffa?"
Bata b'oyewa Ammeyn komai ba ta fad'a mata tana son bawa baban k'awarta jarine ya fara
sana a, sosai hakan yayiwa Ammeyn dad'i arai taji dad'i ya kasance yarta tana da zuciyar
tausayi dan haka Ammeyn ce da kanta ta bawa Maryam dubu d'ari tace "gashi idan Kuma bai
isaba kimin magana sai na k'ara miki?"
Rungumeta maryam tayi tace "na gode Sosai Ammey na Allah yaja da rai ta sumbaci Ammeyn
tayi waje da sauri tana fad'in saina dawo"
Sosai Ammey ke jin dad'in yadda yarinyar ta soma sakewa da ita ta rage wannan d'an banzan
yawon dayake sanyata fargaba da damuwa musamman idan haj. Sailuba ta dawo taga bata
nan ko zata kwana basata tuhumeta taji inda taje ba.
Tana fita suka gabza wani uban karo da MD ai kuwa taji zafi sosai shima haka duk suka dafe
wajen suna kallon juna kafin Maryam ta galla masa harara ta wuce tana sosa goshinta.
Da sauri yasha gabanta ya tsaya yana d'an diddira k'afa irin na shagwab'a yace"ni Allah Allah
Allah sai ki bigeni kuma ki wuce babu hak'uri ni sai na rama" yadda yayi maganar dole abin
yabata dariya batasan sanda ta saki murmushi ba tace "sorry"
Daga haka ta wuce kuma shan gabanta yayi yace "ina kuma zaki?"
"Gidan su Maryam ta bashi amsa dan har ga Allah sauri take ta tsai da baban Maryam yau
baifita nema ba dan haka yakamata taje akan kari
"Wanda kike siyayyar nan awajensa?"
Ta tsinci muryarsa tana shirin fita "Eh shi"
Ta bashi amsa tana ficewa da sauri ya bita ya rik'o hannunta yana kallon ta tace "dan Allah yaya
sauri nake sai batamin lokaci kake"
"Muje mana naganshi idan ya cancanta da amanar da kika bashi saiya cigaba da kula da su
idan Kuma ba haka ba sai na amso ko?"
Sanin cewa sunyi maganar da Ammey yasa bata musa masa ba suka jera suka shiga motar
yaja suka bar gidan.
Maman Islam ce
مسب الله Ù†Ù…ØØ±Ù„ا رلا ميØ
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*________________________
í ½í´¥ BA JININA BACEí ½í´¥
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 35
Saida tasa kashi suka biya wani spermaket ta d'an musu siyayya, dan Allah yasani hakanan
Allah yasaka mata tausayin iyayen Maryam, saboda yak'i nin su da kamewar su hakanan sun
iya babun su, dan malam Abdullah mutum ne jajir tacce tsayayye, akan iyakansa bai yarda da
zubar da daraja da kimar gidansa ba, haka kuma baya daukar raini ko kad'an dan haka hatta
iyalinsa suna shakkar sa saboda sam bai yarda da wulakanta kai ko zubda mutunci ba.
Yadda suke shiga cikin lungunan unguwar yasha mamakin yadda Maryam tasan wajen dan
koshi dayake namiji bai tab'a yowa ta area dinba sosai ya rink'a binta da kallo yana mamakin ta.
Sai yanzu yake gane asalin halinta mai kyau ne irin na mahaifiyar ta wancen halin na aro ne
wanda aka d'ora ta akai bisa wani dalilin mara tushe da makama.
Ita duk wannan kallon dayake binta dashi sam bata kulaba dan hankalin ta yana kan wayar ta
suna chat da Halima sai yanzun ta d'ago dan taga ko sunkai inda ta kwantato masan ai batasan
sanda tasaki kara ba ta maida hankalin ta kanshi ganin suna shirin taka wani k'aton dutse,
shima da sauri ya taka burkin da sai daya janyo hankalin wasu daga cikin masu wucewa dake
cikin unguwa be.
Harara ta galla masa kamar idanunta zasu fad'o tace "to kasheni ka huta tunda ka gaji da ganin
rayuwata"
Murmushi ya d'an saki kafin ya d'an shafi fuskar ta yace "ina son ki princess dan Allah ki soni
my happiness" hararan ta kuma masa kafin ta d'auke kanta yasa hannu ya kuma juyo da fuskar
nata saitin sa ya kafeta da ido,
."dan Allah ki kalle ni nasan zaki yadda da abinda nake fad'a miki har zuciyana ne" bata musa
masan ba ta d'an kalleshi na kamar 1 mint take taji ta fara d'an tsuma tsuma tasoma k'ok'arin
kwace fuskar ta amma ya hanata damar hakan da sauri ta runtse idonta dan bazata juri kallon
wannan fitinannun idanun nasa ba.
Murya na rawa tace ni kaina ya k'age ka sakar min fuskana, kuma ka daina yimin wannan kallon
mayun" murmushi ya d'an saki kafin yace "indai akanki ne baby ki kirani lasan ma ba maye ba
da da yadda zanyi na tsaga jikina na sakaki da tuni na jima da yin hakan na huta' dan Allah
baby karki gujeni, idan kika gujemin hakan yana nufin abubuwa da yawa ciki harda rayuwana"
Yanayin da yayi maganar yasa dole ta kara bud'e idanunta akanshi yadda taga idanunsa sun
koma ba k'aramin tsoratata abin yayi ba sunyi wani irin mugun ja ga wani kyalli kyalli alamun
ruwan hawaye ne suka kwanta masa aciki, wani irin tausayin sa ne ya kamata tace
"Zaka iya aurata koda ace bana sonka?
Sosai maganar ta ya dakeshi, zaka iya aurata koda ace bana sonka?
ya sake maimata tambayar a zuciyar sa kenan akwai wanda take so Kennan tunda bata son
shi?
Wani irin ajiyar zuciya ya sauke kafin yace
"Baby wa kike so?
"Babu"
Ta bashi amsa atakaice sannan ta d'ora da fad'in ba kaine kakori muhseen ba yaron dayake
masifar Sona kamar zaiyi hauka tundaga ranan yake masifar tsorona bama kaiba ko a hanya ya
ganni wallahi canja hanya yake"
Sosai maganar ta ya masa zafi a zuciya amma sai ya daure tunda shine mai nema dole ya
sauke duk wani zafin ransa gefe ya nemi masalaha
"Kina son muhseen d'in?
Ta tambaye ta cikin tsantsar zafin rai dana zuciya.
"Ni babu wanda na tab'a jin ina so arayuwata shima muhseen d'in saboda nacinsa da rashin
zuciyar sa yasa na tausaya masa na fara kulashi" baisan sanda ya wani fisgeta ta fad'a jikinsa
ba ya wani k'ank'ame ta atare suka sauke wata irin ajiyar zuciya kafin yasoma magana cikin
sanyin da shi kansa baisan zai riskeshi a wannan lokacin ba yace
"Na amince baby zan aureki koda ace bakya sona nasan dole wata rana zanyi nasara zan
mallake ki KE DA ZUCIYAR KI"
"Ya jima yana zubar mata da sak'onnin da suka cunkushe masa zuciya suka hanashi sukuni,
bai tab'a sanin da akwai rayuwa irin wannan ba rayiwar da zaka kasa katab'us ka kasa sukuni
ba sai da ya had'u da jarrabar SO wanda ya hanashi sakat yake sanyashi kasa baci cikin dare
ya kasa runtsawa tsawon dare ya zubda hawaye ba adadi duk asanadin SO"
Tun bata fahimtar maganganun sa har ta fara fahimta sanadin da jikinta yayi sanyi bata san da
cewa akwai ranan da MD zai iya kallon idanunta ya furta mata tsadaddun kalamai irin wannan
ba musaman idan tayi tunanin yadda suke da shi.
"Bross muje na tsaida bawan Allah yanata jira" tayi maganar cikin sanyin jiki dan kalaman sa
sun mugun kashe mata jiki sai da ya sumbaci goshin ta da idanunta da suka fi komai d'aukan
hankalin sa kafin ya saketa ya tada motar suka k'arasa gidan su Maryam d'in.
A mota ya tsaya ta shiga kamar yadda ta zata Abban yana nan yana jiranta kamar yadda ta
nema Umma ce tayi mata shimfid'a ta kawo mata ruwa da lemo, sai da ta gaida su sannan ta
sanar musu ai tare suke da yayanta Abba yace "kuma kika barshi awaje kai wannan yara Allah
ya shirye ku da rashin wayo"
Ya fita ya shigo da MD duk da kasancewar basu dashi amma yayin gidan kad'ai zai nuna maka
mutanen gidan suna da tsananin tsabta, sosai suka gaisa da su kafin Maryam tayiwa Abban
bayanin dalilin zuwansu, hakan ba k'aramin dad'i yayi wa Abban na ya zauna yayiwa MD
bayanin duk abinda aka sai mata da kud'ad'en da take kawowa harda shanu da yaje can
garinsu yasai mata da yake shi ba d'an garin bane.
Yanayin sa kawai yasa MD yaji hankalinsa ya kwanta da shi dan haka suka d'anyi shawarwari
akan abubuwan nata yace "tunda shanun sun kai har guda goma kuma duk Yan k'anana wanda
basu fara haihuwa ba kawai asai na mijin sa kamar guda biyar a had'a sai abada kiwo ga
wanda ya amincewa.sannan gidajen kuma anemi yan haya masu mutunci da amana asaka su
aciki"
"Nima tun farko shawaran da nayi da ita kenan tace in dakata tukun" murmushi MD yayi yace
"kasan yar k'auye ce babu abinda ta sani sai k'auyanci" shima Abban murmushin yayi yace "
banda abinka d'ana ai k'auye tushen kowa ne shima MD murmushin yayi suka ci gaba da
tattanawa, sun jima a gidan har sanda Maryam ta dawo suka suka shige d'aki dake sanda
sukazo bata nan Umma ta aike ta.
Umma ce ta lek'a tacewa Maryam ta fito zasu wuce sai da zasu tafi sannan Maryam ta kawo
k'udin da Ammey ta bata ta mik'ewa Abba tace
"Abba gashi nan ka nemi wata sana ar ka fara Allah ya taimaka.
Tsabar mamaki Abba kasa magana yayi gashi kuma ta toshe duk wata hanya da zai mata
godiya sai addu'ar da yay ta zuba Mata har suka bar gidan
MAMAN ISLAM CE
مسب الله Ù†Ù…ØØ±Ù„ا رلا ميØ
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*________________________
í ½í´¥ BA JININA BACEí ½í´¥
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 36
Suka shiga mota ya tada suka bar wajen saida suka d'an yi nisa da tafiya kafin ya d'an juyo ya
kalleta " enye enye ashe yarinyar tana da hankali, to nima aban jarin mana"
Murmushi kawai tayi tasan tsokanar ta yakeyi dan haka ta d'auke kanta suna cigaba da chat da
Halima wacce take zaman jiranta a gida.
"Ko bazaki baniba?" Ya sake tambaya, hararan wasa ta d'an yi masa ta dauke kanta tana d'an
murmushi.
Haka dai yai ta janta da hira har suka koma gida kai tsaye d'akin ta ta wuce shima fat d'in sa ya
nufa dan duk sun gaji.
Ita kam tana shiga falon ta tadda Halima tana zaman jiranta hararar wasa tayi mata tace " to
hajiyata shanyar taki ta bushe Allah badan gobe zan koma ba da tuni nayi tafiyata"
"Sorry dear gidan su name sake mukaje bamu tadda taba har sai da muka jira ta dawo"
"Naji kina jam u kedawa?"
"Tare da bross mana" wani irin waro ido Halima tayi tace "kedawa?"
Kunsan fa Halima bata da masaniyar shirin Maryam MD domin bata da yawan surutun mara
dalili.
"Ai kinji abinda nace kema neman zance ne kawai irin naki"
"Ai abunne dole yabani mamaki yadda baku shiri da bross kuma kice tare kuka fita ai kinsan
dole mamaki yamin illah"
"Humm wai kinsan ma wani abu kuwa?"
"A'a"
"Wai sona yake karkiga yadda yakemin naci kamar bashi ba duk ya wani susu ce"
"Ke dan Allah dena fadaymin dama ba babanku d'aya ba?"
Ta fad'a duk idanunta awaje tsabar mamaki
"To ni tsabar tsorata ranan da yace yana sona ihu na dinga zunduma masa nayi tunanin
kwakwalwan sa ne ya tab'u wallahi"
Jinjina kai Halima tayi tace "haba wallahi wani lokacin nakan zauna nayi tunanin yadda Ammey
take ba wata babba ace ta haifi kamar bross da ace kece akace yarta babu wanda zai yi
mamaki ammafa bross abin yana d'aure min kai, ke amma kinsami dami akala wallahi na miki
murna bross ai miji ne na yaw........ "Ke dalla rufewa mutane baki zaki fara halin naki babu fullstop ba qommer nace miki ina son
sane da zaki wani fara yyyyyyyy murya kamar ta yan China"
Harara Halima ta galla mata tace "ank'i a rufe banza mara mutunci ai dama inka shekara dubu
bakaga mutum ba tambaya halinsa ni zakiwa iskanci koda yake ni na kawo kaina bari nay
tafiyana"
"Jeki mana seme dama duk kin isheni kin saka min ciwon kai"
Sai da sukayi halin naau da suka saba duk had'uwa kafin su daidaita su hau zance na gaskiya
da gaskiya, wannan halin nasu tun suna yara suka taso fashi Halima surutu ratata Maryam
kuma fad'a.
Sun jima sosai Maryam ta fad'awa Halima gaskiya itafa bata son MD Halima tace "karki damu
yar uwa wata rana zakiso shi har kiyi kishin sa kawai dai mudage da addu'ar Allah ya zab'a
mana abinda yafi alkhairi amen"
Sosai Halima tabawa Maryam shawarwari masu kyau yayin da sukayi sallama dake hutunsu ya
kare zata koma schl itama Maryam d'in sati mai kamawa zata koma.
Tsakanins Maryam da Halima akwai so da k'auna akwai yarda da amana akwai shak'uwa mai
tsanani wanda yasamo asali tun suna yan yara alokacin basa rabuwa kullum suna tare ay fad'a
a shirya kullum basa gajiya da dambe da f basa b'oyewa junanau duk wani abu har kawo
wannan lokacin.
Name sake d'in ta kuwa k'awance ne irin na makaranta sannan babu abinda tasani akanta
banda mahaifinta da tasan mai k'udi ne dan har yanzuma bata bata damar zuwa gidansu ba
dan Maryam bata jan mutum ajiki sai ta gama karantar waye shi, itama dai bata da wani aibi
tana da kirki ga kamewa wanna neyasa Maryam k'ulla kanwace da