Showing 1 words to 3000 words out of 153597 words
Chapter 1 - A DUNIYATA 2 Complete Writing By Safiyya Huguma .pdf

í µí°ƒ í µí°ˆ í µí°˜ í µí°€ í µí°€
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
í µí¹‹í µí¸¼í µí¹‚ 1
í µí¸¼ &
í µí¹ˆ '
"Hustle until you no longer need to introduce yourself,push your self because no one else is
going to do it for you". Kalamansa na qarshe kenan da tarin mayan attajiran da sukayi meeting
na qarshe dasu wanda keson saka share dinsu cikin sabon kamfanin da kwanaki bakwai suka
rage masa ya budeshi. Kalamai ne da suka dauki hankulan mutanen dake wajen,wanda dasu
aka kammala zaman.
Sanda yake sallama dash fiye da rabin hankalinsa yana kan wayarsa da tun dazun ya
lura tana haske. Sai da gurin ya rage saura shi daya da hudu daga cikin guard dinsa da wannan
karon dasu yayi tafiyar wadanda ke nesa da inda yake,ya miqa hannu a nutse yana jawo wayar
gami da fesar da iska me dumi daga bakinsa. Cikin kowanne motsi yana jin farinciki na yadda
al'amuran bude kamfanin ke gudana da dukkan wani haske qyalli da kuma alamu na nasara,bai
taba qwallafa rai akan wani abu kaman haka ba,baisan me yasa dukka tunaninsa da hankalinsa
suka raja'a wajen son ganin cikar wannan mafarkin nasa ba. Tunda yazo samu cikakken zama
na awa biyu cur ba,saidai idan dare yayi ya wafci wasu awanni ya tilastawa kansa kwanciya ya
huta. Kowanne minti idan ya shude da amfaninsa a wajensa,ko baya din dama shi mutum ne
me girmama lokaci tare da bashi muhimmanci qwarai.
Sunan farouq kawai daya gani ya sakashi gyara zama yana furta
"Ya salam" Qasa qasa fuskarsa nason fidda wannan sihirtaccen murmushin nasa da ba kasafai
ake samun dacen ganinsa ba. Wani sirri ne kwance cikin murmushinsa dake qara masa haiba
da kwarjini da fitar asalin kyan da ubangiji ya huwace masa. Yasan zayasha qorafi ne kawai
wajen farouq din......don yace masa zai kirashi har baisan adadi ba......hakanan bazai ma iya
tuna awar qarshe da sukayi waya ba.
"Hala baka da wani abu me muhimmanci cikin rayuwarka sama da business dinka?" Kalmar da
farouq ya fara jera masa kenan. Boyayyen murmushi ya saki yana daga dogayen qafafunsa ya
aza saman dunqulallen table din gabansa me azabar kyau. Wani irin shaquwa da fahimtar juna
ce tsakaninsu dake sanyasu iya fahimtar mode din juna koda basa kallon fuskokin juna. Yasan
zaiji fiye da haka ma a bakin farouq din,don muryarsa a dake take da alama har kan fuskarsa
akwai alamu na qosawa
"Idan ka cire ku family na.......tabbas ba abinda ya fishi muhimmanci cikin duka kaf rayuwata".
"Aurenka da yarinyar su a wanne muhalli ka sakasu?....." Ya sake masa tambayar kansa tsaye
cikin salo na kaiwa maqura da son masa titsiye.
"Aure?....yarinya?" Ya maimaita maganar har ga Allah cikin son neman qarin haske.
"Eheeennn" Farouq ya fada a taqaice,cikin ransa yana jin rainin hankalin jadda yana neman fin
qarfin tunaninsa muddin ya gaya masa ya manta da lamarin auren dake gabansa.
"Mmtsewww......au" Fuad ya furta wani siririn murmushi yana sake qwace masa. Sai a yanzun
kwanyar tayo masa tariyar karatun baya na abinda ya baro a nigeria. Kusan gaba daya sabgar
ta shafe daga tunaninsa,abinda ya sanya a gaba ya mamaye tunanin komai daga kansa.
"Am sorry......kasan halin......"
"......halin mijin aljana.......zata sakashi ya aikata fiye da haka ma,saidai alhmdlh.....duk abinta a
wannan karon munci qarfinta,kuma in sha Allah dan uwana bazai mutu babu aure ba". Dariya
sosai ta qwace ma fu'ad din ganin yadda farouq din ke maganar very serious,abinda ya jima
baiyi ba,ya rasa abinda yasa suka damu da auren nan......ya fuskanci gaba dayansu murna
suke dashi.....ya karanci dukkaninsu sun daukeshi serious kuma da gaske suke lamuran baki
daya.....ciki harda MAAMAH duk da akwai qatotuwar ayar tambaya a kanta......don ya sani,koda
yaushe ita ungulu bata jewar banza.
"Ka duba email dinka na sauke maka saqo......ka duba urgently"
"Alright" Ya amsa masa suna katse wayar dukansu.
Yasan tsaf xaya iya mancewa idan bai duba saqon yanzu ba kaman yadda farouq ya
buqata. Don haka kanshi tsaye ya bude email dinsa. Baibi takan sabbin saqonni da ya fahimta
kaman akwaisu ba,kanshi tsaye ya bude saqon farouq din.
Daya bayan daya yake bin hotunan daya turo da kallo ba don yana fahimta can can ba.
Hotuna ne na style readymade na kayan maza masu azabar kyau da aji da wani fitaccen
kamfanin fidda readymade suturu ke samarwa. Company ne da sanya suturar data fits daga
cikinsa sai wane da wane......sai mutanen da suka amsa sunan shegu ne su ta fannin kudi da
dukiya.
A idanu kayan sunyi kyau,saidai shi baisan me zaiyi dasu ba,don haka ya jawo daya
wayar tashi ba tare daya dauke dubansa daga kan hotunan kayan ba ya dannawa farouq din
kira.
"Am coming" Abinda yaji farouq din ya fara fadi kenan da alama yana magana da wasu ne daga
gefe
"Have you seen it?" Idanunsa ya lumshe kadan sannan ya budesu
"Yes I have.....but bansan me zanyi dasu ba......hala ka fara preparation na bude garment
company ne?". Wani qululun takaici ya tsayewa farouq a wuya,seriously mutumin nan da
gasken gaske yake ya fara mantawa da cewa aure zaiyi. Duka ya sakar masa ragamar komai a
hannunsa ba tare da damuwa ko tambayar ya ake ciki ba ko meke faruwa ba.
"Na rantse da Allah sa'arka daya baka kusa dani......shin wai ka manta yarinyar mutane da zaka
aura wadda ka kaiwa sadaki?,in all likelihood ka samu memory formation right?" . Wannan
karon ma saida sautin dariyarsa ya isa har kunnen farouq
''Calmdown mana dude......abun yayi zafi ne har haka?"
"Yama fi haka zafi" Ya fada yana jin ya tuqewa halin fu'ad din.
"To am sorry......amma dai ka sani......ina da abubuwa masu muhimmanci da yawa a
gabana.....kai din kuma wakili nane a ko ina......duk abinda ya dace ka zartar ka zartar....na
baka wuqa da nama" Ya fada calmly,don bayason ya sake tunzura farouq din,tunda yana ganin
yana iya bakin qoqarinsa a abinda shi a nasa ganin baikai muhimmanci da suke bashi ba. Dan
shurun da farouq din yayi da yadda ya sauke numfashi ya tabbatar masa fushinsa ya
sauka,dama ko can basa wani dogon fushi da juna,da farouq ya zazzage abinda ke cikinsa
shikenan,shine dama me yawan kauda kai.....zaka jima kana masa abu amma miskilancinsa bai
bari ya nuna maka har kasan kana masa ba daidai ba,har sai sanda ya gama taraka tukunna.
"Kayi magana dasu abdulghafar......for now ya kamata su sassauta tsaronsu akan yarinyar"
"For what reason?" Fu'ad ya maida masa kanshi tsaye yana gyara zamansa sosai saman
lallausar kujerar da yake zaune akai.
"Ina ganin kaman ya kamata ta sake.....duk da dama dole ka bata security da guard,ko don
yanayin halin tsaro da qasar ke ciki,sannan zuwa yanzu ta zama part of us......wanda duk xai
d'amfara da sunanmu dole a bashi tsaro"
"Forget about it farouq......she's gonna be able to do what you....." Sai kuma ya fasa qarasawa
yana jan siririn tsaki. Shi sam sam koda sau daya bai taba jin wani abu da yayi kama da yarda
ko gasgata yarinyar ba.....akwai abubuwa da yawa da uake suspecting a kanta,wanda ya sake
qaruwa tun daga lokacin data bayyanar masa a mazaunin ZABIN MAAMAH.
"Do you have concern about her actions?" Farouq ya tambayeshi yana tattara masa hankalinsa.
"Manta kawai......mu ajiye wannan,baka tambayeni akan komai ba dude?". Yayi maganar calmly
kaman zancan business din yafi bashi peace akan batun auren.
"Akan komai?,akan business dinka?,wannan shine kadai damuwarka?"
"Wani abu daban daya kamata na damu dashi sama da haka?". Numfashi sosai farouq
yaja,yana tsoron yadda fu'ad gaba daya baya bawa harkar nan muhimmanci,yana tsoron
faruwar wani abu......careless din yayi yawa har haka,yana jin kamar ya kashe wayar kawai,to
amma ya sani wannan shine abu na qarshe da zaiwa fu'ad ya bata masa rai,ya tsani a kashe
masa waya sam sam.
Yadda yake masa bayanin nasarorin da sauran abinda ya rage ya sake bashi tabbacin
business dinsa shine gaba da komai. Sunyi magana har ta kusan awa guda kafin su yanke
sadarwar dake tsakaninsu.
Sanda yake qoqarin minimizing email din idanunsa suka sauka kan wani sabon adreshin
email din dake dauke da sabbin saqonni guda uku,kamar zai share ya wuce sai baiyi hakan
ba,ya danna ya budeshi ya fara bin saqonni da kallo.
í µí°ƒ í µí°ˆ í µí°˜ í µí°€ í µí°€
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
í µí¹‹í µí¸¼í µí¹‚ 2
Kallon farko zaka fahimci ya bada dukka hankalinsa akan abinda yake ganin gilmawarsa
cikin wayar tasa. Saqonni ne kusan guda uku,kala daban daban,saidai kuma kowanne saqo
daya yakeson isar masa.
_mr muhammad jadda,You hereby warned to stop all activities related to lunching your
company_ saqon farko kenan.
A nutse ya sauke idonsa zuwa ga email na biyu
_Not heeding this warning may put your personal and professional assets at risk_ . Sake
matsawa yayi zuwa saqo na uku shima still dai kakkaifan jan kunne ne zalla a cikinsa.
_Ignoring this warning may lead to financial losses and reputational damage_ still dai qasansa
shima wani saqonne
_Proceed with caution,as this may have unintended consequences_.
Tsam yayi da ransa,yana sake bin saqonnin daki daki yana bitarsu. Wannan wanne irin
barazana ce haka me girma?,daga wanne sashe ta bullo?,su waye keda alhakin aiwatar da
hakan?.
Ya jima da sani......ba sanin jiya ko kuma yau ba.....sana'arshi sana'a ce dake dauke da
tarin hamayya gogayya da kuma abokan adawa na sarari dana boye,wani irin matsayi ne da
Allah ya bashi wanda bai taba tunanin samuwarsa a qananun shekaru irin nashi ba. Akwai tarin
mutanen da suka fishi jimawa cikin harkar.....saidai har yanzu basu samu irin nasibin daya samu
ba.
Gyara zamansa ya sakeyi da kyau yana furzar da iska daga bakinsa. Ya sani,zai iya
bincike akan ainihin adreshin,saidai kuma yasan zai wahala ya iya reaching komai akai koda
yaso samun haka. Beside ma,isn't the first time daya fara samun ire iren wadannan
saqonnin,wanda daga qarshe yake cimma daga wanne waje suke?. Ba abinda ya taba
girgizashi ko ya daga masa hankali kwata kwata,amma kuma hakanan yaji wannan saqon ya
tsaye masa a rai. Bai sani ba.....ko don saqon yazo masa ne a daidai sanda yake da burin
aiwatar da abinda ya qwallafawa ransa na cikar burinsa?.
Yadda yake a tsaye a siffa da zati me taba zuciya,haka zuciyarsa take a tsaye. Ba komai
ke bashi tsoro ko firgitashi ko sanyashi yaja baya akan abinda ya fuskanta ya kuma qudira zai
aiwatar ba.....don haka wannan saqon ma sai ya sanyashi cikin sahun sauran saqonni marasa
muhimmanci,wadanda ba komai bane a ciki face zallar barazana maras muhimmanci a
wajensa.
"Hasbiyallahu wa ni'imal wakil,hasbiyallahu la'ilaha illahuwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul
arshil azeem" Ya furta a nutse,take taji zuciyarsa tana sake samun nutsuwa da aminci.
Komai ya tattare yana duba lokaci,cikin jikinsa yake jin ya gaji,yana buqatar cikakken
hutu kafin gobe,so samu yabar qasar nan da kwanaki biyar,to amma ya fahimci zai wahala
dama ta bashi hakan.
Sanda suke takawa da guard dinsa zuwa mazaunin motocinsa guda biyu kira ya shigo
wayarsa. A gajiye ya zura hannunsa a side pocket dinsa ya zaluqota. Taku biyu baya sukayi
dukkaninsu,wanda wannan kuma sabonsu ne,don basu tsaiwa a waje muddin zai amsa
waya,saidai idan shine ya buqaci hakan.
Sosai ya zubawa sunan ido yana kallonsa,yayin da zuciyarsa ta cika da wasi wasi da
saqe saqen abinda kunnuwansa zasu iya jiye masa daga bakinta. Yaci gaba da irga bugawar da
wayar keyi,wanda yake jinsa kamar daidai da bugawar numfashinsa. Ko a tarihi,ko kuma a
labari yana kyautata zaton shi din yana cikin mutane sahun farko da idan labarinsu zai fita a
kundin littafin al'ajabi zai ja hankalin mutane da dama. Kiran uwa na daya daga cikin kiran dake
sanya dukkanin yaro alfahari.......kiran uwa na daga cikin kiran da kowanne yaro ke fatan gani a
kowacce rana.....kiran uwa kira ne dake iya juya zuciyar kowanne yaro daga baqinciki zuwa
farinciki.....amma banda su......banda tasu mahaifiyar......banda kuma nasu kiran wanda ba
komai a cikinsa face zallar ko kwanto da didibniya tsakanin lalubo alkhairi ko sharrinsa.
Yana daga cikin motor qafafunsa suna waje ya zauna,yana qoqarin lalubo nutsuwarsa da
yakan rasa a duk sanda kiranta ya riskeshi ya daga wayar.
Alamun daga kiran ya sanyata sake hada nutsuwarta waje daya,gami da dagawa hajja
furaira hannu wadda ke lissafo mata tsare tsare na abubuwan da suka shirya gudanarwa a wata
shimfidaddiyar farar takarda.
Tsit wajen yayi,bakajin motsin komai da kowa,abinda zai sanya wanda ke nesa irin
fu'ad din xaya dauka ita kadai ce wanze a dakin.
"Barka da warhaka" Ya furta da muryar nan tasa dake da tasirin kwarjini me yawa da haiba a
ciki.
"Barka kade.....ina fata kana lafiya?" Ta masa tambayar data zamo abu mafi dadewa baiji ba
daga bakinta. Duk da zuciyarsa ta kasa yarda haka siddan tayi kiransa amma ya hadiye
wannan.....ko yaya yaji dadin tambayar cikin ransa koda kuwa da manufa aka yita
"Alhamdulillah.....Allah yasa kuma hakan" Dan murmushi ta saki,zuciyarta tana ayyano nesanta
zuwa kusa da ita.
"Lafiyarmu qalau,sai shirye shirye da muke yi gadan gadan". Bai wani fahimci shirye shiryen da
take magana a kansu tashin farko ba......har sai data dora da nata bayanin.
" Na kiraka ne don na shaida maka.....ina buqatar wasu kudade da zan qarasa duk hidimomin
da suka ragen.....ta bangaranka da kuma bangaren ita kanta amaryarka......don kasan hidimar
biki ba qaramin abu bane,......bare ni da zan aurar da dan fari......kuma ita kanta yarinyar ya
kamata ace ita,danginta da dukkan wani dage da jibi da ita yasan cewa tabbas da gaske
mamallakin diamond company zata aura.......banason harkar qaranta......ya kamata duniya
kanta ta shaida d'ana zaiyi auren fari".
Kusan koda yaushe fitar kalmomin bakinta suna zame masa tamkar makaranta ne......ya
jima da sanin maamah din macace me son izza da nuna isa.......ya dauka wani tsohuwar dabi'a
ce a tattare da ita.....amma xuwa yanzun ya sake amanna mutuwa ce kadai zata iya samun
nasarar rabata da wannan halin.
"Me ake buqata?" Ya tambayeta kai tsaye.....don shima da nashi plan din. Zuwa yanzu yana
kallon komai ne tamkar a tafin hannunsa ake shiryashi,abinda ya rage masa ya sani kuma
kadanne da bayajin zai zame masa me wahalar riska.
"Kudi nakeso ka sakamin......sannan ka sakawa amaryarka......kamar million......."
"Kiwa saddiq magana......zan gaya masa ya saka miki adadin abinda kike buqata" Ya yanke
bayanin da taso yi masa da adadin kudaden da duk da yasan ya jima da fin qarfinsu........amma
kuma ana nemansu ne a muhalli da gurbin da babu buqatar yawan wannan adadin.
Murmushi ta saki tana jin wani dadi yana ratsa zuciyarta,tun a yanzu tana sake samun
tabbacin nasarar dake bibiyarta,tana kuma fara jin qamshi da dadin da uwa keji a yayin da take
gwada girman izzarta akan yaranta suke kuma bibiyarta sau da qafa akan duk wani buri ko
quduri nata
"Allah yayi maka albarka" Ta fada tana murmushi. Kalmar ta dinga masa amsa kuwwa cikin
kunnuwansa,sai ya dinga jin kamar ba daga bakin maamah ta fito ba. Idan yace bazai iya tuna
ranar data fadi wannan kalmar a kansa baiyi qarya ba.
A hankali sai yaji kaman zuciyarsa tana rugujewa. Inama ace ta fadi kalmar ne domin
cancanta da kamatar ta fadeta a kansa?,bawai don duniya ko wani abu dake cikinta ba?,bawai
don son rai ko biyan buqatar rai ba.
Da wannan murmushin dake sake yalwata saman fuskarta a kowacce rana ta ajjiye
wayar saman table din gabanta. Qasaitaccen table ne da yazo cikin set na kayan furniture din
da aka qawata sabon gidan nata data riga kowa tarewa a ciki. Gida ne datake jin zata kece biki
na alfarma a ciki......zata daga sunanta da kuma martabarta a idanun qewaye dama duniya
gaba daya.
"Kowanne motsinsa sai ya dangantani da saddiq hamza kibiya" Ta fadi tana duban idanun
hajja,har cikin ranta tana jin wata wuta tana ruruwa tare dason gaggautowar ranar da zata saka
kakkaifar wuqarta ta yanke wannan alaqar da tafi mata kama da baqar alaqa.
"Hanzarin na mene mariya?,saurin me kikeyi ne?,saura kwanaki nawa duka duka?" Hajja ta
bata qwarin gwiwa tana cike da kwadayi da son jin abinda ya faru tsakaninta da fuad din.
Kai
28, August 2025
Aysha
Iam fine
28, August 2025
Aysha
Masha Allah
25, August 2025
Ladidi
Masha Allah, the book is so meaningful
12, August 2025
Aisha
Nice story
28, August 2025
Aysha
Fgghj