[4/5, 3:04 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=gi_t *UWAR AGOLA* NA MAMAN AFRAH Labarin mai cike da abin dariya *Daga marubuciyar* *Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.* 09025576222 🅿️1️⃣ Malam Nura ne tsaye a tsakar gidansa ya sha babbar riga yana baza ƙamshin turarensa da ya bankaɗa, sai wani ɗaɗɗaga kai yake tamkar ƙadangare, taku biyu ya yi ya ja ya tsaya yana hura hanci ya shiga kwaɗawa matarsa uwar gidan kira. "Haule" Kira ɗaya ya yi a na biyu ta amsa ta fito daga ɗaki ta zo ganinsa yana cika yana batsewa ta nemi kujera ƴar tsugunno ta zauna ta zubawa sarautar Allah ido. Ko kallo bata ishe shi ba ya shiga kiran ɗaya matar tasa. "Kuluwa, Kuluwa, Kuluwa" Shiru kake ji wai malam ya ci shirwa tamkar ma bata gidan, kallon Haule ya yi ya ce "Kuluwa ta fita ne?" Wani takaici ne ya turnuƙe ta amma ta danne abin da ta ji ta ce "Haba Malam ka tambayi agwagwa hanyar rafi, ai kaza za ka tambaya kansha labari" Tamkar ta watsa masa garwashin wuta haka ya zaburo ta da masifa yana faɗin "Dakata Haule ni fa Kuluwa kawai na tambaye ki ba wai baƙar magana ba, ke ga mai bakin aku daga an tambaye ki abu sai ki tsiri karin magana ke ga wacce ta yankewa ƙasar Hausa cibiya" Banza ta masa kamar bata ji ba, ganin haka ya ƙara cewa "Wai ba magana nake miki ba Haule? Wai ku mata mai ya sa bakwa kiyaye aljannarku da za ku samu a ƙarƙashin ƙafar mijinku ne? Yanzu ya kyautu ki wofantar da ni?" Haule a ƙufule ta ce "Ka tambayeni na baka amsa ka ce baƙar magana na faɗa maka, kai ba kuturu ba ba kuma makaho ba, ba gaka ga ɗakin Kuluwar ba baka zuwa ka duba ko tana nan, a ce kana mijinta amma kana tamabayata ko ta fita, idan fitar ta yi ma ai kai ba za ka kasa sani ba, dole za ta sanar maka... Tun kafin ta kai aya ya tari numfashin ta da faɗin ",Ai ka ji, to ni bani da lokacin ɓatawa taɗi zanje wajen amarya dan haka idan neman magana kike sai ki yi ke kaɗai tun da kare ma ba ya haushi shi kaɗai" Ya faɗa yana juyawa ya shiga baza babbar rigarsa ya nufi ɗakin Kuluwa tun kan ya ƙarasa yake ci gaba da kiranta tun yana faɗin Kuluwa, har yake kiran ta da sunan ta na gaskiya wato Hauwa amma shiru. Kuluwa kuwa duk abin da ake tana jin su kawai niyya ce bata yi ba shi ya sa bata amsa ba, yana zuwa ya ɗaga labulen ɗakin idanunsa suka sauka a kanta tana zaune a tsakar ɗakin da kwanon silba a gabanta hasken fitilar ta ya gauraye ɗakin. Kallo ɗaya ta masa shi ma na raini ta sauke idanunta a kan kwanon gabanta, garri ne take sha da gyaɗa a ciki dan haka sai da ta ciko luday ta kai baki ta sha, kafin ta haɗiye ya ce "Kuluwa yaushe na zama sa,an ki ne?" Bata ce ƙala ba sai da ta haɗiye ta saka ludan a kwanon ta miƙe tsaye ta ce "Wallahi idan ka sa na ƙwaru sai na kai ƙaranka wajen mai gari ka biya ni diyya?" Saroro yake kallon ta ya ce "Kashe ki na yi da zan biya diyya" Tana muzurai ta ce "Ni dai na faɗa maka hawainiyarka ta kiyayi ramata wallahi, dan ... Hanzari ya katse mata da faɗin "To uwar ƴan kishi ki fito ina da magana da ku, ita ta fito amma ke da bakya iya danne baƙin kishi shi ne za kike ɗaga jijiyar wuya, to dan ki sani aure babu fashi, da ba a aure ba zan aure ki ba" Yana faɗar hakan ya juya fuuuu ta biyo bayansa ranta in ya yi dubu ya ɓaci, daman ya san a rina wai an saci zanen mahaukaciya!. A daidai inda Haule take zaune ya ja tunga ya tsaya ita ma tana ziwa ta kama tsantsa da hannu biyu ta tsaya tana wani karkaɗa kai, irin na mai jiran kule ta ce casss. Malam Nura bai yi wata-wata ba ya ja wata doguwar gyaran murya ya ce "Ba tare da ɓata lokaci ba dan ina da wajen zuwa, domin wajen amarya mai jiran gado zan je, yauwa na tara ku ne a kan na faɗa muku sati mai zuwa ranar asabar za a ɗaura mini aure, kuma ina ƙara jaddada muku duk mai son zaman ta ya ci gaba da wanzuwa a cikin gidan nan to ta tabbatar ta yi biyayya ga maganata sannan ta shirya tarɓar sabuwar amaryata" Ya faɗa yana washe baki a daidai inda ya ambaci amayarsa tamkar an masa bushara da gidan aljanna. Haule ta yi wata ƴar dariyar rainin hankali ta ce "Ubangiji Allah ya sanya alkairi, ya bada zaman lafiya, ya kawo ta lafiya" Tana kai wa nan ta miƙe abin ta hankali kwance za ta bar wajen, Malam kamar an warto maganar daga bakinsa ya ce "Haba Haule kamar wani wanda bakya sona, ina faɗa muku batun ƙarin aurena zan muku kishiya amma ke hankalin ki kwance, kamar an tsoma tsumma a randa?" Wata ƴar shewa ta yi ta ce "Wallahi har ka bani wata ƴar bazawarar dariya, haba Malam in da sabo ai na saba, wane dare ne jemage bai gani ba ai sai dai daren mutuwarsa, ni kishiyata ai in ban manta ba ina ga goma sha takwas kenan" Da sauri Malam ya ce "Goma sha takwas fa kika ce?" Tana gyaɗa kai ta ce "Ƙwarai ma kuwa" Ya ɗan yi shiru sai kuma ya ce "Tabbas na tuna haka lissafinki yake, wallahi na ɗauka goma sha bakwai ne, ashe fa sai da na auri Ladiyo sannan na auro Kuluwa, da yake Ladiyo kwanan ta uku a gidan nan muka rabu shi ya sa nake mantawa da ita a lissafin matan nawa... Haule ta tari numfashin sa da faɗin "To ka ga kuwa wacce aka yi wa kishiyoyi goma sha takwas mai zai ɗaɗa ta da ƙasa? Ai ni ƙarin aurenka shan ruwa ma ya fi shi wahala" Wani murmushi ya yi sai dai Kuluwa da ta hayyyaƙo masa ya sa maganar da ya yi niyyar yi ta maƙale, tana huci kamar wacce ta yi tseren gudu ta ce "Daman ya za a yi ta damu, ai kishiya ko sau dubu aka taɓa maka sunan ta kishiya, kuma dole za ka ji ciwo, ai ta san cewa ba ita za a yi wa kishiya ba ni za a yi wa shi ya sa bata damu ba" Haule ta haɗe rai ta nuna Kuluwa da yatsa ta ce "Ahir ɗinki ki fita idona in rufe kuma hawainiyarki ta kiyayi rama ta, domin wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa ni ba kanwar lasa ba ce, sannan bakin rijiya makaho ba ya yin wasa a wajen!" Tana kai wa nan ta juya tana kallon Malam Nura ta miƙa masa tafin hannu ta tana faɗin "Bani sallama, wato kuɗin toshiyar baki na faɗar kishiya" Kamar wanda yake jira ta tambaye shi da sauri ya saka hannu a aljihun babbar rigarsa ya ciro dubu ɗaya ƴan ɗari biyar-biyar guda biyu ya miƙa mata guda ɗaya ta karɓa ta juya, ta nufi ɗakinta, Kuluwa yana miƙa mata ta ce "Dan tsiya naira ɗari biyar ce kuɗin faɗar kishiyar?" Yana mata kallon kin rainawa kanki hankali ya ce "In za ki karɓa ki karɓa ki rage zafi, saboda wannan ma na bada mai yawa ki tambaye ta ki ji wataran idan zan ƙara aure klin nake bata ƙanana ƴan naira hamsin guda biyu kuma ta gode mini" Ya faɗa cike da ƙafafa. Haule wacce take dab da shiga ɗakin ta juyowa ta yi ta ce "Ai idan ana cin ɓaure ba a tona cikinsa, kai kake batun klin ai wannan an bani da daraja, ai in ban manta ba akwai lokacin da ya bani ƙuli-ƙulin naira hamsin lokacin zan yi kwaɗon yakuwa na tambaye shi kuɗin ƙuli-ƙuli ya ce bashi da kuɗi da ya fita ya siyo ƙuli-ƙulin hamsin ya kawo min ya ce in karɓa a matsayin abin faɗar kishiya, lokacin da zai auri Hafiza ƴar gidan ƙanin mai gari, haka na karɓa na masa fatan alkairi, ni da kike ji da gani na ga jiya na ga yau kuma zan ga gobe a cikin gidan nan, ba a banza ba kowace mace take zuwa ta tafi ta barni" Tana kaiwa nan ta bankaɗa labulen ɗakin ta ta shige. Malam Nura ya dawo da kallonsa kan Kuluwa ya ce "Idan kin ji ana damo sarkin haƙuri to Haule ce shi ya sa duk auri sakin da nake yi saki ba ya biyowa ta kanta saboda ba ta ɗaga mini hankali idan zan sake aure... Kuluwa wacce tun lokacin da ya ce zai je wajen amarya mai jiran gado ranta ya ƙara ɓaci, tana ganin wato ita yanzu ta zama amarya mai murabus sabuwar amaryarsa ce mai jiran gado, kamar ta kai masa duka ta ce "Wato shi ya sa ka ce za ta je wajen amarya mai jiran gado, wato an samu sabuwa ni yanzu na zama tsohon hannu, ka gama shanye mangwaro ka yi jifa da shi ƙudaje su baibaye shi ko?" Yana wani ƙanƙance idanu irin na ɗan duniya ya ce "Ƙarya na yi?" Baki ta saki ya layar mai tafiya, kafin ta samu zarafin bashi amsa ya miƙa mata ɗari biyar ɗin, da sauri ta warta tana warta ta yayyaga ɗari biyar ɗin wajen gida takwas ta yaga, da sakakken baki ya bi ta cike da mamaki ya ce "Kin yi wa kanki amma dai ki sake tabbatarwa aure babu fashi" Cike da masifa ta ce "To ni ka sake ni, ba zan iya zama ba" Yana mata dariyar kin rainawa kanki hankali ya ce "Haramun ne dai mace ta nemi saki, sannan ki sani babu saki tsakanina da ke har sai kin zauna na tsawon lokaci a gidan nan, in kin manta in tuna miki, auren biyan bashi aka mini da ke, ina bin mahaifin ki dubu takwas ya hanani ya bani auren ki, aka ranta masa dubu takwas na cika dubu biyu aka biya sadaki dubu goma dan haka ba zan yi asarar dubu goma ba duka watan ki biyu fa a gidan nan" Ya faɗa yana mai juyawa ya kama hanya zai fita domin zuwa hira wajen annurin zuciyarsa amaryarsa wacce yake kan ganiyar soyayyarta da kwaɗayin auren ta. Yana dab da shiga zauren gidan, Kuluwa wacce ya bari da ƙamshin turarensa ta ɗaga murya cike da takaici ta ce "A haka za a ƙare dai!. Da wani turare mai warin gawa, ai wallahi amaryar ma bata da aji tun da ba a shafa turare ɗan fesawa sai madarar turare" Har zai tafi, sai kuma ya juyo yana nuno ta da yatsa ya ce ,"Ki taka a sannu bar ganin kin tara ki kiyayi mai nema, kuma ba don biyan bashi aka mini da auren ki da tuni na sake ki wallahi dan ni sakin mace tamkar in je jigon dabobi ne in since rago daga ɗaurin da aka masa" Yana faɗa ya fice . Kuluwa wani takaici ne ya mata dirar mikiya, kallon ɗari biyar ɗin da ta yaga ta watsar ta yi haushi ya sa ta juya da gudu gudu ta shige ɗakin ta taje take kuka dan hatta garin kwakin da take sha ji ta yi duk ya fita daga ranta, ƙafa ta saka ta yi ball da kwanon garin, tamkar dai shi ya mata laifin sai da kwanon ya kife garin ya malale a ƙasa ta yi zaman ƴan bori a tsakiyar ɗakin tana tunanin mafitar hana auren Malam Nura dan tana ƙaunarsa kuma ba ta so ya auro wata ta hana ta rawar gaban hantsi, daman ta daɗe tana jin raɗe raɗin yana neman aure duk da shi daman auri saki shi ne sana,arsa. Malam yana fitowa ya nufi, wajen Idi mai gashin tsire sai da aka cika masa ƙatuwar takarda da tsiren ya cake kuɗin ya bayar, ya ratsa shagon Abbati mai kayan sanyi ya sayi lemon kwalba guda biyu masu sanyi. Yana ta jin daɗin zuwa ya ga masoyiyarsa ya kama hanyar yana hango irin cin tsiren soyayyar da za su yi da bazawarar tashi, domin shi ya sa ma ko tuwon gidansa bai ci ba. Sallama ya sa aka yi da ita dan yana ta kiran wayar ba a ɗauka ba, gabaɗaya sai haɗiyar yawu yake kasancewar ƙamshin tsiren da cika masa hanci alla-alla yake ta fito. Jim kaɗan babu ɓata lokaci kuwa sai gata ta bayyana. Tun da ta fito ya mata ƙuri da ido har ta ƙaraso, irin takun da take yi shi ne yake ƙara narkar masa da zuciyarsa a kanta yana son ganin mace cikakkiya, ɗaurin ɗankwalin ta turo ka ga tsiya shi ne ya fi tafiya da Malam Nura bai san ya washe haƙora ba sai da ya ji muryarta ta karaɗe kunnuwansa da faɗin "Kallon fa?" Da sauri ya dawo hayyacinsa yana faɗin "Ai ke ɗin ce kullum kamar sake miki halitta ake yi" Ya faɗa yana kafe ta da kallon ƙurilla. Dariya kawai ta masa ba tare da ta ce komai ba, shi ya gaishe da ita ta amsa a maimakon ta fara gaishe da shi, kujerar da ta fito da ita a hannunta ta zauna a ka shi kuma yana rakaɓe a jikin katangar, har ya saba idan dai zai zo zance ba ta bashi abun zama. Ledar hannunsa ya ajiye ya ɗakko wani dutse a can gefe mai ɗan girma wanda zai isa ya zauna a ka ya zauna, har lokacin yana ta washe baki. Sun ɗan fara taɓa hira kenan ya janyo ledojin ya fito da lemukan tare da takardar yana kallon ta ya ce "Wannan tsaraba ce siyowa na yi dan na birge ki... Tun kafin ya ƙarasa maganar Hadiza ta saka hannu ta dafe takardar ta saka a leda bai ankara ba ta saka lemukan a leda tana faɗin "Ina godiya sosai, shi ya sa na fitar da kai tilo a cikin zawarawana, saboda kai na fasa komawa gidan tsohon mijina dan na san zan huta za ka gwada mini gata" Dariyar yaƙe ya yi ya ma kasa furta komai dan ya ga ƙarfin halin nata shi da ya siyo su ci tare shi ma ya mayar da mugun yawu amma ta tattare, a zuciyarsa ya ce 'Aikin uban me kika mini da zan ciko miki takarda da tsire haka, to wallahi ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa' Ganin yanayinsa ya sauya ta ce "Ka yi shiru" Da ɗan sauri ya ce "Daman siyowa na yi mu ci tare muna hirar soyayya" A zuciyarta ta ce 'Tashin balagar tsintsaye, idan ka ci nama da lemon nan ka ce ba sunana Hadiza ba' A fili ta ce "Ka ji ɗan aljanna bari na buɗe mu ci, ai ina ta jin labarin yadda kake farantawa iyalinka ma" Ya washe baki yana tuna yadda ya biya wanda suka shirya mata ƙaryar nan tun da asali ba a garin suke ba dawowa suka yi. Yana gyara zaman hular kansa wanda duka haya ya karɓo a wajen Iliya me wanki da guga ya ce "Duk sati sai an yanka ɗan akuya, kullum kuma ana yanka kaji biyar" Ta lunshe ido ta ce "Babu mai raba ni da kai sai mutuwa ina son namiji mai kyautatawa iyali" Ya kalle ta yadda take farrr da ido ya ce "Ai ni in dai wannan fagen ne bani da matsala ko kayan faɗar kishiya kowacce akwati guda na mata, yanzun nan sai da na musu kyautar dubu biyar biyar" Ya faɗa yana tuno kuɗin faɗar kishiyar da ta basu ɗari biyar biyar da yadda suka sha daru da Kuluwa wacce takaici da baƙin kishi ya sa ta yaga tata ɗari biyar ɗin. Tana buɗe takardar ta ce "To ai hakan da daɗi za su ji sauƙin kishin" Ya kyalkyale da wata dariya ya ce "Ai basu da matsala yanzu ma sai da suka bani saƙon gaisuwa, dan Kuluwa amarya tana ta nannaga cewa kar na manta saƙon gais... Zuwan Zainaba ƴar kimanin shekaru goma sha uku wajen, shi ya katse masa hanzarin maganar da ya guntso zai fesar, tamkar an jefo ta haka ta musu dirar mikiya, sanye take da atamfa riga da zani, ta ɗaure wani mayafi ƙarami a ƙugunta tamkar wacce aka sakawa wasan dambe. Zainaba ƴar Hadiza ce yaranta biyu zainaba mai shekara goma sha uku sai kuma Shafi,i mai shekara uku, ita kuma Hadiza tana da shekaru talatin cif. Kamar ya kwaɗawa Zainaba mari haka ya ji, ya lura yarinya bata da kunya ko kaɗan shi kuma son uwarta ya rufe masa ido yana tsoron ya tsawatar mata a samu matsala, hakan ya sa ya miƙa hannu ya ɗakko naman yanka ɗaya dan ya fara jin haushin kar Hadizar ta ɗaukawa Zainabar naman da yawa. Zainaba wacce babu wanda ta tsana sama da Malam Nura dan ta fi so mahaifiyarta ta koma gidan mahaifinta, gata da shegen kishi kamar ba yarinya ba tsananin kishi take wa ubanta, shi ya sa duk ta tsani zawarawan Hadizar musamman Malam Nura da yanzu shi za ta aura. Da gangan ta je kamar za ta durƙusa ta buge hannunsa naman da yake miƙo mata tsoka guda ya suɓuce ya faɗi, ita kuma Zainaba da sauri ta ce "Ban gani ba" Ta faɗa kamar za ta yi kuka, murmushi Hadizar ta yi ta ce "Ba komai kin san shi babu ruwanshi" Wani abu da ya tsaye masa ya haɗiye muduk ya ƙirƙiri dariyar yake ya ce "To waye bai san yaro ba, bare ma bata gani ba" Zainaba ta faki idon mahaifiyarta ta wurga masa wata muguwar harara tare da murguɗa masa baki ta sunkuya ta ce "Innata ashe za ki iya cin daɗi ban da mu?" Hadiza wacce take baƙincikin su ci naman tare da Malam Nura ta ce "Haba Zainaba daman za mu rage muku ke da ɗan uwanki, amma tun da kin zo ɗauki kawai mu sai mu ci girma" Baki sake Malam Nura yake ganin ikon Allah, domin kaf Zainaba ta naɗe takardar ta haɗa da lemukan ta kama hanyar shiga gidan, Hadiza ta ɗan ɗaga murya ta ce "Kar fa ki hana Shafi'i" Da to ta amsa mata ta shige gidan, Malam Nura da ƙwallar baƙinciki ta kawo a idanunsa da sauri ya yi hanzarin mayar da ita yana washe bakin ƙarfin hali ba ya so ta gane halin da yake ciki, ga yunwa da take ƙwaƙular hanjinsa. A zuciyarsa yana faɗin 'Wayyo dubu huɗu ta da ɗari biyar' Tana ƙara turo ɗaurin ɗankwalinta gaban goshi ta ce "Tun da an yanka kaji ai sai ka ci idan ka koma gidan ko masoyi" Kamar zai yi kuka ya danne ya ce "Ai kuwa naman kaza yana can don kwanon samira aka cika mini, idan na koma na ci" Ya faɗa yana sauke idanunsa a kan hannunsa ta cikin farin wata sai sheƙin man jikin naman da kuma ɗan burbuɗin ƙuli-ƙulin da ya maƙale a hannun. Idanunsa ya sauke a kan yankan ɗayan da ya faɗi daga hannunsa wanda Zainaba ta bige masa, kuma shi dai iya saninsa ya san da gangan ta yi don ba sa ga miciji da ita, ido ya ƙurawa yankan naman ya ga ashe har ƙafa ta saka ta murtsuke yadda ba zai amfanu ba, da a nufinsa idan sun yi sallama da Hadiza ta shige gida ya dawo ya ɗauka a ƙalla dai ya rage asara!. Muryar ta ce ta katse masa tunani da faɗin "Bari na shiga gidan ina son shiga banɗaki" Wani irin washe baki ya yi ta tashi shi ma tashin ya yi ta ɗauki kujerar ta, sallama suka yi ta tsaya masa ƙememe me ta ce "Au baka bani kuɗin karin safe ba, ko goben da tuwo kake so na karya" Yana kallon yadda ta masa wani farfari da idanun ya saka hannu a aljihu, dubu biyu ya ɗakko ya bata ko godiya babu ta karɓe, juyawa ta yi ta fara takun nan nata da yake so ya saki baki kamar dolo yana kallon ta tana dab da shigewa ta jiyo tare da masa bye-bye, shi ma hannun ya ɗaga mata ta shige ya juya ya fara tafiya ransa a matuƙar ɓace, don ko hirar kirki basu yi ba ga asarar nama da lemon kwalba. Tun da ya kama hanyar gida ya tsinewa Zainaba ya fi cikin carbi, ya ƙosa asabar ta yi a ɗaura auren Hadiza ta koma gidansa ko ya huta da ganin wannan fitsararriyar yarinyar. Kayan jikinsa ya duba ko zai ga datti a jiki domin so yake ya je ya cire ya haɗa da na jiya ya mayar inda ya karɓo, saboda tsabar maƙo ba ya iya ɗinka sutura ta kirki amma yanzu da yake neman auren Hadiza shi ne yake arowa yana sakawa dan gudun kar a raina shi. Da sallama ya shiga gidan babu kowa a tsakar gidan sai Kuluwa, ita Haule tana ɗaki ita da yara tana musu tatsuniya, Kuluwa jin muryarsa sai ta ji tamkar ya caka mata mashi a maƙoshi, ta yi banza da shi ta buɗe randa ta ɗakko ruwa a kofi, tahowa ta yi lokacin ya zo daidai saitin ta zai tafi ɗakinsa, buguzum-buguzum ta zo wucewa kaɗan ya rage ta bangaje shi. Tana shiga ɗaki ya tsaya gyaran murya ya yi a saita bakinsa yadda amon muryar zai isa ga kunnen ta ya ce "Kai gaskiya mace ƴar duma-duma mai diri ta yi, ko tafiya take sai ka ga ɗagwas-ɗagwas, ,gwanin sha,awa na yarda mata suna suka tara, amma wata macen idan ta taho yadda aka san motar tantan za ta wuce... Kuluwa wacce tun da ya fara magana ta tsaya tana huci kamar zakanya domin a take zuciyarta ta raya mata cewa da ita yake wato amaryarsa wacce ya kira da suna mai jiran gado ita ce ta iya tafiya, tun da dai ta san duk wanda ya yi zagi a kasuwa ya san da wanda yake, rai a ɓace ta dangwarar da kofin hannunta wanda ta ɗauki ruwa, ta taho a sukwane don zuwa a yi wacce za a yi ita da Malam Nura don ba za ta bar wannan maganar ba, ta sanya a ranta ita da amaryarsa shege ka fasa domin za a yi zaman doya da manja!. MAMAN AFRA 09025576222 [4/6, 5:18 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=gi_t *UWAR AGOLA* NA MAMAN AFRAH *Daga marubuciyar* *Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.* 09025576222 🅿️2️⃣ Malam yana tsaye sai ganinta ya yi kamar an jefo ta, ta fito ta tsaya tana huci kamar zakanya, da kallo ya bita yana aro jarumta ya tsuke fuska amma alamu sun nuna Kuluwa bata lura da tamke fuskar da Malam Nura ya yi ba don idanunta sun rufe da kishi hakan ya sanya ya zuba mata na mujiya. Sai da ta tsare shi da ido tq ce "Nura wace ce take tafiya kamar motar tantan ɗin? "Ta faɗa yana kallon yanayin ta ya gama gane ta haɗa kanta da baƙar wahala don baƙin kishi mugun ciwo ne musamman na mijin da bai damu da kai ba, kuma ba ya ɗaukar duka ɗawainiyarka. Sai da ya danne dariyar da ta so ƙwace masa ya sassauta murya ya ce "Haba Kuluwata, ni a wa zan kira ki da motar tantan ki duba kanki da kyau ai idan diri ake nema da iya tafiya sai dai mata su take miki baya, amma ai ke tafiyarki kamar ƙirga sawun ki kike" ,Shiru ta yi tana binsa da kallo amma ƙwaƙwalwarta tana raya mata avubuwa da dama ciki kuwa har da nuna mata raina mata hankali ya yi hakan ya sa ta ce "Ka ji da shi ciwon ajali a ɗan yatsa, ai ni na san ba a sakewa tuwo suna, mai hali ba ya canjawa, ai duk wannan maganganun naka ba ganewa zan yi ba wai an yi yamma da kare, tun ba yau ba na san cewa kai munafukin mata ne k... Hannu ya ɗaga mata a ƙufule cike da faɗa ya ce "Dakata! Kuluwa, ni nan da kike ganina na fiki hawa tamfar ɓacin rai don haka ki taka a sannu ko na shuka miki rashin mutunci, ni yanzu hankalina a kan sabuwar amaryata yake dan haka a halin da ake ciki yanzu ina kan bakana na cewa mata suna suka tara! Kuma Hadiza ita ce zara a cikin matan" Yana faɗar hakan ya juya ya yi hanyar ɗakinsa ya barta a tsaye tana jin tamkar ya watsa mata wuta da ya ce Hadiza amaryarsa ce Zara kenan su duk suna suka tara wato ba mata ba ne su. Har ta kama hanyar ɗakinsa ta fasa ta juya ta shige ɗakinta tana jin tamkar ana hura wuta a zuciyarta, tana shiga ta kwanta tana saƙa da warwarar yadda za ta ɓullowa lamarin ta yadda za a fasa wannan auren domin ita bata fatan Malam Nura ya ƙara auro kowace mace har duniya ta naɗe!. Yana shiga ɗakinsa ya cire kayan jikinsa ya mayar da linkin ya ajiye ya saka wasu kayan, cikinsa ne yake ƙugi yunwa yake ji tamkar ƴaƴan hanjin cikinsa za su fito su nemi abinci da kansu haka yake ji. Tunanin inda zai samu abin da zai saka a cikinsa ya yi jim kaɗan ya fito ya je ya rufe ƙofar gidan, ɗakin Haule ya nufa yana shiga ya same ta a zaune tana lissafa ƴan kuɗaɗen ta lokacin duk yaran sun yi bacci, daman yaran uku ne nata biyu ɗayan kuma wata mai rabon haihuwar ce a cikin matan da ya aura ta haifa ta kawo masa ita ta karɓa take riƙewa. Kasancewar basu samu haihuwa da wuri ba tun da babbar ƴarsa Alawiyya tana da shekara tara, sai Kabiru mai shekara shida, su ne ƴaƴan Haule, da kuma Lauwali mai shekara huɗu shi ne ba ɗan Haule ba. Allah da ya taimake shi duk yawan aure-auren sa matan ba sa samun ciki da yanzu ƴaƴan sun kusa ashirin. Yanzu yana da shekara talatin da bakwai a duniya, inda Haule take da shekara talatin da ɗaya, Kuluwa kuwa ashirin da tara. Haule mace ce mai haƙuri da kawaici abin duniya da duniyar ma basu dame ta ba, inda Kuluwa take masifaffiya da baƙin kishi tana da masifa sannan bata barin ta kwana. Shi kuma Malam Nura mutum ne mai son mata sannan yana da maƙo ba ya ɓanɓaruwa ta daɗin rai kuma mutum ne shi da ba ya sauke haƙƙin iyalansa bayan yana da hali tun da manomi ne sannan yana neman kuɗi amma kulluɓ cikin tarawa da kuma ambaton babu yake. Yana shiga ta yi saurin ɓoye kuɗin nata duk da bata san cewa ya gani ba, tun da ya san halinsa mutum ne mai son abin wani yanzu yana iya cewa ta ara masa kuɗin. Yana washe baki ya samu bakin gadon ya zauna ya ce "Haulatuwa uwar gidan ran gida, uwar gida sarautar mata, ke ce ta farko kuma kowacce bayanki take bi" Ɗan kauda kai gefe ta yi tana rayawa a ranta cewa sai yaushe zai daina zambaɗa ƙarya da kuma daɗin baki, ta ɗan saki murmushin irin ta ji daɗin nan a fili ta ce "Wannan haka yake, kana fasa min kai fa amma" A zuciyarta kuma ta ce 'A haka za ka ƙare kullum cikin daɗin baki abin da za ka faɗawa wannan daban wanda za ka faɗawa wacccan ma daban shi ya sa duk lokacin da gidanka aka ce akwai mace fiye da ɗaya kai kake haddasa fitina amma a guji zuwa rafi wata rana tulu zai fashe!' Yana ɗan washe bakin samun nasara ya ce "Kin cancanta ne" Dariya kawai ta yi ya ɗan sauke numfashi ya ce "Za a samu wani abu a nan ne?" Tana kallon sa ta ce "Kamar me?" Ya ce "Abin da zan saka a bakin salati yunwa nake ji" Sai da ta karkata kai gefe ta ce "Ayya daman gayan tuwon da Kuluwa ta bamu na yi miya su kansu yaran bai ishe su ba sai da na siya musu awara suka ƙara" Shiru ya yi yana nazari ya san shi ya bada hatsi kaɗan wanda ba zai isa a ci a ƙoshi ba sannan bai bada kuɗin kayan miya ba ya san kuwa Kuluwa ko da danginsa zai zo bai isa ta bashi miya ba. Ya ɗan yi jim ya ce "Kuma babu sauran miyar?" Ta ce "Wallahi babu" Miƙewa tsaye ya yi ya fito ta taɓe baki ta bi bayansa da kallo. Yana fitowa ya nufi ɗakin Kuluwa ya shiga tana zaune ta doka uban tagumi ita kaɗai ta san tunanin da take kusa da ita ya je yw zauna sai da ya zauna ma ta lura ya shigo ɗakin. Wata harara take zabga masa kamar idanunta za su faɗo ya rausayar da kai irin nn ƴan duniya ya ce "Kuluwa tawa, ni kuwa na Allah" Wani gajeran tsaki ta ja ta ce "Kanka ake ji mahaukaci ya faɗa rijiya" Basarwa ya yi ya ce "Ki bani tuwo ina jin yunwa" Tana masa kallon tsaf ta ce "Inda ka je ba a baka ba?" Yana kawar da maganar ya ce "Bani da inda ya fi nan, wallahi yunwa nake ji kamar in ci babu" Dariya ta yi mai haɗe da shewa ta ce "Da za ka ci babun ma da ya fi" Ganin abin nata ba na ƙare ba ne ya ce "Ke Kuluwa abin naki ya isa ba fa tsoronki ake ba, ki ɗakko tuwo ki bani tun da ba ke kika noma mini hatsin ba" Kamar jira take ta tashi da sauri ta janyo wata roba da tuwon yake ciki ta turo gabansa ta ce "Inda wannan gayan tuwon ne gashi nan" Yana kallon tuwon ya ce "Ina miyar?" Ta ce "Wacce ka bani kuɗin cefanen na yi?" Yana zare ido ya ce "Idan ma ban baki ba ke ba a cin arziƙin ki ne, wata shegiya miya ba za ki nema ki yi ba a miki ciki a miki goyo, wato na nemi hatsin tuwo na baki na miyar ma ni kike so na nemo" Hannu ta saka da buga ƙasa ta ce "Wannan ne baka isa ba wallahi, ni ba wahalalliyar mace ba ce, idan kanka zafi yake to ni nawa hayaƙi yake, masifa wane shege ta kashe, miya ce baka bada kayan yi ba ni kuma wacce na yo billahillazi ba zan bada ba, ɗumamen tuwo zan yi da ita gobe, nima gari na siya nasha da daren dan haka ka ɗauki tuwon ka fita min a ɗaki" Ganin ba zai iya masifarta ba ya miƙe tsaye ya saka ƙafa ya buge robar tuwon ya ce ",Aikin banza gayyar na ayya gayyar tsiya, ɗanyen tuwon, abin da har yau baki iya tuwo ba sia ɗanye, kana ci yana maka dariya, ai an kusa yin ta ta ƙare wato zan auro galleliyar amarya Hadiza mai iya girki da iya tafiya ta zo ta kawo sauyi a gidan nan" Yana kaiwa nan ya juya ya fita daga ɗakin. Cikin ɗaga murya take faɗin "Idan har tusa tana hura wuta za mu gani, lokaci zai nuna ai daman duk wanda ya ce bai iya kuka ba uwarsa ce bata mutu ba za mu jira zuwan amarya mu ga yadda za ku ƙare! Daman yanzu za a yi amarya mu za a shuka mu kamar dusa" Yana jin ta ya yi dogon tsaki har zai shige ɗakinsa ya dawo da baya ya zo ya ɗaya labulen ya ce "Kin ba kanki amsa" Yana faɗar hakan tafi ya shige ɗakinsa. Tun da ya kwanta yake juyi yunwa ta hana shi ya runtsa ya ɗakko waya ya kira Hadiza suka yi hira suka yi sallama yana jin suna hira tana tauna, alamar tana cin abu kuma yana jiyo muryar Zainaba tana batun akwai daɗi ya san kuwa nama da lemon da ya saya ne suke ci, shi an bar shi da ciki yana masa ƙugi. Bayan sun gama wayar ya buɗe wani jug, gayan fura ne a ciki haka ya ɗakko ya ci ya sha ruwa ya kwanta bacci ya yi awon gaba da shi da mafarkin an kawo amarya Hadiza gidansa. Washe gari da safe yana fitowa ya ga yaran suna shan koko da waina, gaban Kabiru ya je yana faɗin "Kabiru ina kuka samu waina?" Yaran suka haɗa baki wajen cewa "Iyarmu ce ta saya mana" Baki ya washe ya kalli Haule da take gyaran wake ya ce "Ku dai mata sai kuke kukan babu kuɗi alhalin kuɗi suna wajenku a nannage, ban san mai ya sa kuka fi kula da ƴaƴanku sama da mazan ku ba, yanzu maimakon ki cika kwanon samira da wainar nan ki cika dogon kofi(Jug) Da koko ki kai mini ɗaki in saka miki albarka amma kika yi mirsisi tusar ango" Kallo ɗaya ta masa ta ɗauke kai ta mayar da hankali wajen yin abin da take yi. Yana tsaye ya ce "Haule ba magana nake miki ba?" Kuluwa wacce take wajen murhu tana iza wuta ta ce "Shiru ma ai amsa ce ga mai hankali" Cike da jin haushin ta ya ce "Ni dai Kuluwa kin zame mini ƙarfen ƙafa wallahi, ina dalili ana magana da kishiyarki amma kina tare mata faɗa" Banza ta masa ta fara waƙa tana faɗin "Wani mijin namiji ne wani kuma sauna ne" Kasaƙe ya yi yana cika yana batsewa ya ce "Da wa kike?" Tana ɗan ɗaga kai alamar mai jiran faɗa ta ce "Wanda yake tsoron ta mutu... Kafin ta ƙarasa maganar fuuuu ya yi hanyar ɗakinsa ya fito da ledar kayan aron da ya je hira da su jiya ya zo a fita daga gidan. Bayan ya mayar da kayan ya wuce wajen mai shayi ya sha shayi da biredi ya ƙoshi. Yana shigowa gida ya ce kira su ya ce "Yau saura kwana shida ɗaurin auren nan, ina so in faɗa muku bakin ku ya ƙare" Haule ta kalle shi da mamaki ta ce "Ban gane ba?" Ita daman Kuluwa kai ta ɗauke gefe bata ce komai ba. Ƴar dariya ya yi ya ce "Ina nufin na sallame ku zuwa turaka!. Wato duk wani tanadi da zan yi nan gaba na amarya Hadiza ne" Su duka cike da rashin fahimta suke kallonsa yana tsaye hannayensa a cikin aljihunsa yana murmushin jin daɗi shi kaɗai ya san irin amarcin da zai kwasa. Kuluwa a harzuƙe ta ce "Kamar ya wai?" Ya nuna ɗakinsa da hannunsa ya ce "Ina nufin daga yau duk wacce take da girki to iya girki za ta yi babu ruwanta da zuwa turakar miji da daddare, yanzu lokacin amarya ne!" Haule ta ce "Sabon salo kiran sallah da usur, wannan amaryar da abin da za ta zo kenan?" Yana kaɗa kai ya ce , "Eh akwai wasu ƴan magungunan gyara da zan fara sha to bana so maganin ya salwanta" Kallon -kallo aka shiga yi tsakanin Kuluwa da Haule Haule tana ƴar dariya ta ce "Toh Malam ai abin wannan ba komai ba ne, idan ka ce a baka wata biyu ma sai mu baka ka gama cin amarcin... Kuluwa ta bugi ƙirji ta ce ",Sannu Haule dami sarkin haƙuri, wallahi ba zan yarda ba, idan na yarda Allah ya tsine mini, wato ke saboda baki san ƴancin ki na mace ba za ki bar kwananki tun amarya bata tare ba namiji yake mata tanadin jikinsa, to ni dai ba zan yarda ba, tun da yau ma baki kwanana ne kuma bani da wani wajen kwana da ya wuce turakar Malam a yau, haka idan kwanan ya zagayo ma sai na je... Wani haushi da tsanar Kuluwa ce ya cika Malam daman ita take kawo masa cikas a kowane abu shi ya rasa wannan jaraba da ya je ya kwasowa kansa biyan bashin auren ta gashi ta addabe shi. Ganin tana masifa shi ma ya ce "Haule Allah miki albarka ai shi ya sa kika daɗe a gidan nan kika yi ƙarko" Kuluwa ta yi karaf ta ce "Ai ciwon kanta ne bata sani ba shi ya s... Haule ta haɗe rai ta ce "Kuluwa ki taka a sannu fa, shiru -shiru ba yana nufin gudun magana ba, kawai kyalewa ce da son zaman lafiya, kuma na san ciwon kaina kawai biyayyar aure ce da bin maganar miji, ni nan da kika ganni ina iya sadaukar da duk wani abu don farincikin mijina, ina iya haƙura da jin daɗina don in faranta masa" Baki sake Kuluwa take kallonta ba tare da ta ce komai ba ta ɗauke idanunta daga kallon ta ta mayar kan Malam, don ita idan ta tsaya maimaita magana da Haule hawan ruwa ne zai kamata. Tana kallon Malam ta ce "Na faɗa maka ba zan yarda ba, kuma da ka saka mata albarka nima ai ba tsine mini aka yi ba" Da yatsa ya nuna ta ya ce "Ai duk ƙwawarki kwanan turakar miji ya barki Kuluwa ki ɗauki na annabawa... Tana tafa hannuwa ta ce "Wallahi yau ma kwanana ne a ɗakinka zan kwan... Ya katse ta da faɗin "Ga fili ga mai doki, in dai za ki je ɗakin ki kwanta ga wurin nan, ni dai sunna ce ba zan aikata ba tun da na faɗa miki tanadin amarya Hadiza ne, ban da neman jaraba ma ke da kika kwana jiya a ɗakin ki amma yau shi ne don na nemi ku bani lokaci shi ne kika hau dokin zuciya kike sukuwa" Banza ta masa ta juya ta ci gaba da aikin ta. Hannu ya saka a aljihu ya ciro naira ɗari ya miƙawa Haule ya ce "Ungo nan Haule, ai ke kam kina cin ribar zaman aure daman mai haƙuri shi yake cin ribar zaman duniya, kin ga jiya ga ɗari biyar ɗinki ta faɗar kishiya, yanzu ga naira ɗari ta haƙurin bin maganar miji ɗari shida me kika manta" Tana dariya ta ce "Allah amfana, Allah barka da Hadiza amarya" Ya washe baki kamar gonar auduga ya ce "Amiiiiiin Haulen arziƙi" Kuluwa ta ɗago daga sharar da take ta ce "Ina tsiya ina wata ɗari shida, kamar wata matar kyankyaso zan ke karɓar wannan kuɗin ai wallahi sa,a ka yi da sai na ɓare maka kai a biyu" Tsaki ya yi ya ce "Ai duk namijin da ya auri mace mai baƙin kishi bai yi dace ba, gashi nan bakya cin ribar zaman auren kina zaune miji yana yi wa kishiya kyautar kuɗi" Ta ce "Ai ko ni zan iya kyautar sama da naira dubu ba wai naira ɗari ba" Ita dai Haule bata tanka musu ba, haka ya shige ɗaki ya bar ta tana ta kumfar baki, sai ta yi shiru kamar an tsikare ta sai ta ci gaba da masifa ita kaɗai. Da yamma Kuluwa ta shirya ta nufi gidan Baba Ramma mahaifiyar Malam Nura da sallama ta shiga bayan an amsa ta same ta tana tuƙa tuwo, tabarma ta shimfiɗa mata suka gaisa Baba Ramma ganin ran Kuluwa a ɓace ta ce "Kuluwa ina fatan dai kuna lafiya kuma kuna zaune lafiya" Kamar mai jira ta ce "Ina fa zaman lafiya gidan kamar filin yaƙi" Baba Ramma ta ce "Ya subhanallahi mai ya yi zafi shi ba wuta ba?" Kuluwa ta ce "A kan wannan neman auren da yake yj ne sai tauro da abubuwa yake yana kafa mana dokoki a gidan duk sai kambama amarya yake yana nuna ta fimu matsayi" Baki sake Baba Ramma take kallon Kuluwa cike da kasa ɓoye mamakin ta ta ce "Ke yanzu Kuluwa a kan ƙarin auren ne kika kawo ƙaran mijinki?In ce dai ba ke kaɗai ba ce ita Haulen fa?" Kuluwa ta ce "Ita bata san inda yake mata ciwo ba" Baba Ramma ta ce "Ni dai tun da Nura yake aure-aurensa Haule bata taɓa kawo ƙaransa ba amma ke kin zo kina ba kanki wahala, shin baki san cewa shi namiji idan zai ƙara aure sai mace ta kawar da kai ba, sannan duk wani rawar kai da wulaƙancinsa sai a lokacin yake tsurowa, duk da ba kowane namiji bane yake haka amma yawanci mazan duk haka suke" Kuluwa takaici ne ya cika ta hakan ya sa ta ce "Ni dai Baba dan Allah ki bashi umarni ya fasa auren nan ji nake kamar zuciyata ,a ta buga... Baba Ramma ta ce "Inyeee lallai fa, sannu Kuluwa, wato in hana shi rawar gaban hantsi bayan da ransa da lafiyarsa da ƙarfinsa a jikinsa ai daga nan in aure hamsin zai ƙara ba zan hana shi ba, komai lokaci ne wataran ko an ce ya yi ma ba zai yi ba" Kuluwa ji ta yi tamkar ta shaƙe Baba Ramma har sai ta bar numfashi, duk da ba wannan ne auren ta na fari ba amma bata san mai ya sa ko mijinta na fari bata son sa kamar yadda take son Malam Nura ga wani kishi da ta ɗorawa ka ta yake ɗawainiya da ita. Tana so ta faɗa mata har ƙairace musu ya ce zai yi wai tanadin amarya zai yj amma kunya ta hana ta magana haka ta taso ta baro gidan tana da na sanin zuwa tun da babu biyan buƙata!. Yau wani yadinsa da yake ganin ya fi kowane yadi kyan gani a cikin kayansa duk da shekara ta uku kenan da ɗinkawa ya gyara tass ya saka saboda ya gaji ya biyan kuɗin aro kaya. Hadiza ko da ya zo yau ta ga hannunsa babu komai hakan ya sa ta ƙi sakin jiki take wani kumbure-kumbure shi ma yana ganin yanayin ta ya san dalilin fushin amma haka ya basar don shi a nashi ganin ya gaji da nomawa jaki ciyawa yana kawo kayan daɗi don su ji daɗin hirar soyayya amma tana ba ƴaƴanta ita cw kaza uwar son ƴaƴa a zuciyarsa ya ce 'Idan aka ɗaura auren ai na huta sai su koma gidan ubansu, ko ki bar su a gidan kakannin nasu ina dalili' Hira yake jan ta da ita tana basarwa ya gaji ya ce "Hadiza yau ko bakya jin daɗi ne?" Ta yatsina fuska ta ce "Ƙalau" Fitowar Zainaba daga gidan tana riƙe da hannun Shafi,i shi ya katse musu maganar. Zainaba ce ta tsaya shi ma ya tsaya kasancewar hannunsa cikin nata, ta sunkuyo ta masa raɗa a kunne. Kai ya gyaɗa ta saki hannunsa ya taho da gudu yana cewa "Oyoyo baba" Yana zuwa ya haye cinyar Malam Nura ya ƙanƙame shi, kasancewar yana cin tuwo Zainaba ta je ta kamo shi suka fito. Dariyarta ta shiga dannewa ganin haƙarta ta cim ma ruwa, daman tun da ta ga Innarsu ta fito, ta saka a ranta yau ma sai ta masa abun da zai masa ciwo, hakan ya sa ta saka luda ta kwalfo miyar kuka ta ƙara a kwanon da Shafi,i yake in tuwo da yake miyar ta huce, ta ringa ɗaukan miyar da ludan ta zuba masa a jikin kayansa da duka hannuwansa har bayan hannun. Shi ne da suka fito ta raɗa masa cewar ya je ya haye cinyar Malam Nura duk ya ƙanƙame shi. Malam Nura gabaɗaya ya rasa ma ya zai yi, jikinsa jaga-jaga da miya gashi kuma miyar manja ce yadda fari yadin ya sha miyar tamkar ya saki kuka. Cikin yaƙe don kar ta ga kamar ba ya son ɗanta ya ce "Oyoyo Shafi,i ɗana na kaina" Ya faɗa yana ƙoƙarin ɓanɓare yaron don ya maƙalƙale shi, hannuwansa suna maƙale a wuyansa hatta wuyansa da gefen fuskarsa sun san Shafi,i ya ci tuwo. Dakyae ya ciro shi yana faɗin "Duk ka ɓata ni da miya" Ya faɗa yana kallon jikinsa. Hadiza ta haɗe rai ta ce "Haba Malam Nura to mene ne don ya goga maka miya kai baka san yaro ba" Gudun ɓacin ranta ya sa ya washe baki ya ce "Haba Hadiza amaryata ai da kai da kaya duk mallakar wuya ne, ina ni ina masa faɗa ai ba miya ba ko kashi ne ya goga mini ba zan ji komai ba ai ɗana ne" Dariya ta yi tana faɗin "Shafi,i jeka gida ka wanke hannunka" Don ita ba ta san duk shirin Zainaba ba ne, Zainaba kuma ta ce "Kake kamshin miya a maimakon ƙamshin turare " Ta faɗa tana dariya, don ita Hadiza ba ta son a kwaɓi ƴaƴanta bata ganin laifinsu. Ta kalle su ta ce "Innata yau ba a kawo nama ba?" Malam Nura a fili ya ce "Yau ba a kawo ba a yj haƙuri ƴar baba" A zuciyarsa ya ce 'Aikin banza shafa lalle a mazaunai kamar ubanki ne yake nema mini kuɗin' Idanun uwar ta faka ta galla masa harara tare da yatsina fuska ta juya ta nufi cikon gidan Shafi,i kuwa ya ja tunga ya tsaya ya ce "Alewa" Babu yadda Malam Nura ya iya haka ya ciro 200 ya bashi ya ce ya saya. Bai wani jima ba ya bata dubu biyun ta ta karyawa a zuciyarsa yana faɗin 'An kusa ɗaura aure ki tare in huta da wannan jigilar bada dubu biyu ki je can ki haɗu da su Kuluwa, ba kina kyashin cin tuwo a gidanku ba, idan kika je gidana tuwon ma gaya za ki samu sai kin nemawa kanki miya, kafin na gama cin moriyar ganga na hankaɗa ƙeyarki' Sun yi sallama ya kamo hanya ya tafi gida yana ta jera tsakin wankan miyar da Shafi,i ya masa. A can gida kuwa Kuluwa ta samu maganin matan ta bita zai-zai ta sha don ita tun da ya ce su bar kwanan turaka ta saka a ranta yanzu ta fara kwanan turaka. Ko da ya zo wanka ya yi ya cire wannan kayan. Tana sane da shi, don biredi da lemo ya siyo ya ci iyalinsa kuwa ko oho. Sai da ta daidaici ya gama komai ta nufi ɗakin tana zuwa ta ji ƙofa a rufe ta tura amma ƙofa bata buɗu ba. Daga waje ta bubbuga tana faɗin "Ka buɗe mini in shigo" Haule tana jinta a zuciyarta ta ce 'Kin haɗu da wahala' Daga cikin ɗaki ya ce "Wallahi sai dai ki kwana a waje amma na haramtw muku kwanan turaka" Tun tana magiya har ta lura abin ba na wasa ba ne. Haka ta raba dare tana zaune a ƙofar ɗakin da ta gaji ta ringa masifa ta koma ɗakinta. Washe gari ta yi ta masifa amma ko kallo bata ishe shi ba. Zaune suke a kan benci shi da abokinsa Malam Hudu, Malam Nura ya ce "Wannan dubu ashirin ɗon ka siyo mini shadda yadi huɗu yar dubu biyar biyar, wannan dubu biyar ɗin ka haɗo mini magani" Ya kalle shi da mamaki ya ce "Maganin mai?" Yana masa hararar wasa ya ce "Haba kai ma, maganin maza mana, gyara zan yi fa, ai shi ya sa ma na dakatar da su Haule daga zuwa turaka, saboda gyaran tarɓar amarya zan yi, ka ga kuwa tun da ba su na yi wa gyaran ba babu dalilin da zai sa suke zuwa mini turaka,sai dai wacce aka yi gyaran dan ita idan ta zo ta mora" Da dariya ya fashe ya ce "Wallahi kaima abokina da wani abu to ina kai ina wani gyara" Yana masa wani kallo ya ce ",Naka wasa ne, ka san dai mata suna gyara to mu maza mai yasa ba za mu yi gyara ba? Gwara ka siyo mini ka ga ai ba raini" Karɓa ya yi yana faɗin "Gaskiya na yarda amaryar nan ta musamman ce kana son ta, wato shadda ma sabuwa gal aleda mai kyau za ka yi ga magani," ,Shi ma dariya ya yi yana tuna irin son kuɗinsa sai dai ya samu yadika masu araha amma wannan karon dai ya yi ƙuri zai yi mai tsada. Malam Hudu yana irga kuɗin ya ce ",Gobe ai da sassafe zan tafi kanon saboda na kammala abun da zan yi in gama, ni anya wannan Hadizar za ka iya sakin ta kuwa kamar yadda kake sakin sauran matan? Na ga fa ka kamu da sonta" Ya yi tsaki ya ce ",Ita wa ta fi, ka san ai mace kamar riga na ɗauke ta in saka wannan in cire wannan" Haka suka yi ta tattaunawa abin su suna tsara yadda abubuwa za su kasance, daman ita Hadiza ya sallame ta kuɗin da ta yanka masa yanzu kawai ɗaurin aure ne za a yi da tarewa Mu je zuwa ba a fara wasan ba akwai ƙura mai tsakuwa ma kuwa🤔😹 MAMAN AFRAH 09025576222 [4/7, 5:00 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/Bu295Z6iGnL3SoKYtgqnbZ?mode=gi_t *UWAR AGOLA* 🅿️3️⃣ *Bojuwa herbs* *By* *Surayya Dee.* *08032773332.* *Sanyi flusher!* *Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.* *Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya Slsai ta dawo ko ta turo wasu*. *Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.* *Tightening set na hade mace ta dawo Zamzam tamkar yar budurwa.* *Tasirin magani Idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.* *Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.* *Akwia packages na mussaman ga Amare, uwargida ,zawarawa da masu jego.* *Tuntubeta a wannan lambar* *08032773332* *Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.* *UWAR AGOLA* NA MAMAN AFRAH Labarin mai cike da abin dariya *Daga marubuciyar* *Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.* 09025576222 🅿️3️⃣ Tun da ya kama hanyar zuwa gidansa yake jin farinciki don yana son ba marar ɗa kunya a wannan ƙarin auren da zai yi, musamman da Kuluwa take son hana shi rawar gaban hantsi tana son shige masa hanci da ƙudundune. Shi kuma bata san hakan ƙara rura masa wuta take ba tana ƙara zuga shi domin ya saka a ransa cewar zai yi abin da zai shallake mata tunani abib da bata zata ba, sai ya cusa mata takaici tun da shi bai saba idan zai yi ƙarin aure mace ta takura masa ba ko ta nuna rashin amincewar ko ta ɗaga masa hankali sai a kanta, don ita Haule in don ta ita ne duniya ta zauna lafiya. Ko da ya ƙarasa gidan tsaye ya tarar da ita tamkar tana jiran dawowarsa. Yana sallama amma bata amsa ba sai Haule ce ta amsa masa daga cikin ɗaki. Zai wuce ta sha gabansa ya ƙara ratsewa ta sake shan gabansa a ƙufule ya ce "Mene ne kuma?" Tana masa kallon raini ta ce "Duk abin da ka zata shi ne, ko in ce duk abin da kake ji da shi ni ɗin ma shi nake ji" Kallon ta ya yi ya a ransa ya fara tunanin anya wannan za ta bari ya ci amarcin nan a kwanciyar hankali kuwa? Zuciyarsa ta fara raya masa cewa ko dai ya aikata gidansu amma ba da zummar saki ba, tun da ya saka a ransa ba zai sake ta ba sai ya gama amfanar kuɗinsa amma dai yanzu tun da tana son kawo masa cikas gwara ya ce ta tafi gidan, sai dai ya ƙudiri cewa ba zai dawo da ita ba sai bayan wata biyu wataƙila ma lokacin ya saki Hadiza ya fara neman wani auren. Gyaran murya ya yi ya ce "Kuluwa abin naki ya fara yawa, ke baki san mace mai kishi fita take daga zuciyar miji ba?" Ta kama ƙugu da hannu ɗaya tana jijjiga jiki ta ce "To na nawa kuma? Ai na san wannan bazawarar da kake kira mai jiran gado ta daɗe da yin fatali da ƙaunata daga zuciyarka, shi ya sa baka ganin kaina da gashi" Haule da ta fito daga ɗaki ta mata kallon ɗaya saura kwata ta ce "Kuluwa ya kamata ki wa kanki faɗa, ki yi karatun ta nutsu, shi mijin da ya damu da kai shi kake kishi a kanka, kuma wa ya ce miki akwai ɓurɓushin ƙaunarki a zuciyar Malam da har kike ikirarin wata ta tunkuɗe son naki, idan baki sani ba in faɗaa miki, daga lokacin da mace ta sako ƙafarta a cikin gidan Malam Nura daga ranar duk wata ƙaunarta take bankwana daga zuciyarsa shi ya sa zaman ba ya iya zuwa ko ina ake rabuwa domin daga ya hango wata zancen ta cikin gida ya ƙare amma kin ɗauki kishi kin hana rai da zuciyarki sakat ki kafa faɗin wai mai jiran gado shin ke idan ta jira gadon sai me? Kafin ta jira gadon mata nawa ne suka jira dan Allah ki sauƙaƙawa kan ki amma shawara.... Cike da masifa da kallon raini ta ce "Haule ki kama girmanki idan ke bakya son Malam ni ina son shi, dan haka babu ruwanki da ni ki riƙe shawarar ki" Haule tana kwashe kayan shanya ta ce "Allah baki haƙuri" Daga haka ta kama kanta bata ƙara cewa komai ba ta ci gaba da sabgar gabanta. Malam Nura ya ce "Matsa in wuce" Ta yi ƙememe ko gizau bata yi ba. Hannu ya sanya ƙiii ya yi gefe da ita, da fisge ta sake shan gabansa cike da ƙosawa ya ce "Mai kike so ne wai?" A zuciyarta tunaninta masifar da ta addabe shi da ita ce ta yi tasiri dan haka ta sake tamke rai ta ce "So nake ka fasa auren wannan amaryar taka" Baki sake yake kallonta sai kuma ya fashe da dariya ya ce "Tambaya ɗaya zan miki idan bar kin amsa to" Ta ce "Ina jinka" Ya ce "Kin taɓa ganin wanda ya mutu ya dawo?" Tana masa kallon rashin fahimta ta ce "Ban gane ba" Ya ce "Idan har wanda ya mutu yana dawowa to haka za a fasa auren" Kallon ƙurilla ta masa don ta san kawai raina mata wayo ya yi hakan ya sa ta ce "Mai kake nufi?" Ya ce "Ba zai taɓa iyuwa ba ke ni da a ce auren nan an fasa to gwara aurenki da ni ya mutu" Yana faɗar haka ya juya zai tafi ta kamo rigarsa daga baya ta janyo shi ƙiiii tamkar wanda daman tigar tasa take jiran a ja haka ta shiga yagewa domin daman kayan sun ga yau sun ga jiya sun gaji fa shiga ruwa. A ƙufule ya juyo ya kai mata mari ta sunkuye ya mari iska yana zare ido ya ce "Kama hanya ki tafi gidanku" Gabanta yana bugun uku-uku ta zaro ido don tunanin ta sakin ta ya yi hakan ya sa ta ce "Ban gane in tafi gidanmu ba" Cike da ɗaga murya ya ce "Eh ki tafi sai na neme ki" Ɗan sanyi ta ji a ranta a ƙalla ba sakin ta ya yi ba. Cike da cika baki ta ce "Ai da ba a kawo ni gidanka ba sai da aka ɗaura mana igiyoyi uku dan haka yanzu idan baka warware ba babu inda zan je" Faɗa aka shiga zabgawa ita da shi amma ta ƙi tafi shi kuma so yake ta tafi ko ya sake idan amarya ta zo don ya lura lamarin Kuluwa babu sauƙi wai ciwon arne. Kiran Hadiza ya yi a waya ya ce yau ba zai samu zuwa ba, dan haka ta ce ya aiko a kawo mata kuɗin kari, haka ya ba wani dubu biyu ya kai mata, shi kuma ya ƙuduri aniyar kai Kuluwa gidansu tun da ita ta ƙi tafiya, ya kore ta amma ta ƙi saboda naci. Tana banɗaki ya je ɗakinta ya ɗakko kaya kala goma ya kai ɗakinsa ya zuba a zani ɗaya ya ƙulle, ya fita ya ba wani saurayi yw ce ya ajiye masa zai kira shi, haka ya karɓi kayan shi kuma ya dawo gida. Ɗakinsa ya shiga sai da ya ji fitowar ta daga banɗakin ya fito, yana fitowa ya washe baki ya ce "Ina gwanar wani ga tawa, Kuluwa ta Malam Nura bada kanki a sarw ki je gida ki ce ya faɗi, ni da ke amana ce babu rabuwa kowace mace sawu take, take miki" Kuluwa tana dab da shiga ɗakinta ta fara jin wannan batu hakan ya sa ta dakata tare da saurin jiyowa don ganewa idanunta. Rass idanunta suka yi tozali da Malam Nura har ta shuga ƙarewa tsakar gidan kallo tunanin ta ko da wata yake, sai dai ambaton sunanta da ya yi a maganar hakan ya bata tabbacin da ita yake. Wani irin washe baki ta yi tana tunano cewar ɗazu da ta yi salaar magriba ta yi ta addu,ar Allah sa ya fasa auren Hadiza Allah sa ya daina ganin kowace mace sai ita, hakan ya sa ta fara tunanin tabbas addu,ar da ta yi ce ta karɓu. Haule tana jin su a ɗaki ita da su Kabiru duk da yaran suna hayaniya amma hakan bai hana ta jin abin da Malam ya faɗa ba, sai dai hausawa suka ce sanin hali ya fi sanin kama, shi ya sa aka ce duk daren daɗewa idan ka daɗe baka tare da mutum to ka tambayi komai nasa amma ban da hali domin halinsa yana nan shi hali zanen dutse ne!. Ta san halinsa kamar yunwar cikin ta, kuma ta san ruwa ba ya tsami banza, dole akwai wata maƙarƙashiyar da yake shiryawa Kuluwar amma da yake idanunta a rufe suke ba za ta gane waye Malam Nura ba, shi ya sa har yau tana fata da kuma jiran ranar da Allah zai fitar da haƙƙin matan da yake kansa wanda ya ɗauka tun da ta san matuƙar ana kwana ana tashi zai auro daidai da shi wacce za ta zame masa ƙarfen ƙafa ta ganar da shi shayi ruwa ne!. Kuluwa ta wani gyara tsayuwa haɗe da gyara ɗaurin ƙirjin da yake jikinta, daman ruwa ta watsa tana ƴar dariya ta zumbura baki ta ce "Kamar gaske" Danne dariyarsa yake don ya lura har ta bada kai bori zai hau, hakan ya sa ya ce "To da wasa ne?" Tana kallonsa don yanzu ta fara takowa zuwa gare ta ta.ce "Ai ka ce babu kowace mace a gabana amaryar taka mai jiran gado fa?" Ya ƙyalƙyale da dariya irin ta ƴan duniya ya ce "Rabu da ita ai da tsohuwar zuma ake magani, ai ni yau babu abin da zai sa ma in je wajenta hira, kin san dai tun da na fara neman auren na kullum sai na je hira ko? To yau ba zan je ba yau ranar ki ce, kuma ina miki albishir da cewa maganar auren ma janyewa zan yi" Ta masa tsuru da ido sai dai da ta tuna cewa addu,a ta yi kuma babu abin da ya gagari ubangiji sai ta yarda da maganarsa. Ganin hakan ya ɗora da faɗin "Yau gidanku za mu je mu gaishe da babanku sannan mu je duk inda kike so a tare daga haka mu dawo gida" Kanta ne ta ji ya yi wani gingirim ta fara tuno irin tsiyar da za ta shuka hakan ya sa ta ce "Yau fa bakin girkin Haule ne" Sai da ya ɗan kalli ɗakin Haulen ya yatsina fuska lokacin Haulen ta taso ta leƙo ta window inda ta ɗaga labule ya taɓe baki ya ce "Rabu da ita, kin manta daman na ce bakin girki kawai za kuke yi sannan ma ita fa babu ruwanta, to ma ya za a yi ta haɗa kanta da ke, ai ke ce ta gaban goshi" Bakin ta har kunne ta washe, Haule ta saki labulen tana danne dariyarta don ta san wata tsiyar zai shuka amma da yake ita Kuluwa dukan iska ce har yau bata gane inda ya saka gaba ba, bata taɓa tantance waye namiji sai ya shuka mata tsiyar ta zo tana tagumi da balbalin bala,i. Ɗaki ta shiga ya bi bayanta, rigarta da zani na kan gado da ta ajiye ta ɗauka ta saka, yana zaune a bakin gadon yana mata daɗin baki, ta ɗauki mayafi ta yafa kasancewar ko drower kayanta bata buɗe ba shi ya sa bata san ya kwashi kayan ta ba. Sai washe baki take suka fito ta rufe ɗakinta, shi ma ya rufe nashi ɗakin suka fita ko sallama ba su yi wa Haule ba, Kuluwa jin ta take a sama don miji yana yayin ta. A jere suke suna tafiya sun kama hanyar gidansu Kuluwar, suna tafiya suna hira Kuluwa ta ce "Nurana na kaina" A fili ya ce "Ke kaɗai kuwa" A zuciya ya ce 'Sakarya za ki gani shayi ruwa ne, banbancin suga ne kawai da lipton' Tana washe baki haɗe da kafe shi da ido ta ce "Haulen fa?" Hararar wasa ya mata ya ce "Ke wai sai kike maganar gawa shin gawa tana da amfani bayan san cire mata rai?" Ta yi shiru don bata gane ba ta ce "Gawa dai kake nufi" Haushi ya kama shi don Haule ta fita saurin gane zance ita kamar kidahuma sai an mata ɓaro -ɓaro. Cike da ƙosawa ya ce "Ina nufin ita bata da amfani ne a gidan" Ta ƙyalƙyale da dariya har wasu ƴanmata guda uku da za su wuce ta kusa da su suka bita da kallo. A sake kallonsa ta ce "Hadizar fa?" Ya yi tsaki irin na gajiyawa da maganr wasu matan da take masa ya ce "Na ce Haule ma bata da amfani bare wata Hadiza da bata zama matata ba" Allah ne kaɗai ya san daɗin da take ji a ranta ta washe baki ta ce "Zan iya zaginta baka ji komai ba?" Kafin ta yi zagin shi ya fara kama sunan Hadizar ya zaga yana faɗin "Ƙarewa ma ai kin ji na zage ta da kaina, ni fa bana ganin kowa sai ke" A zuciya ya ce 'In dai zan ci amarci bakya gidan nan gwara ko me zan yi in faɗa ' Ƙaran wayarsa ce ta katse musu maganar ya dakata da tafiya bayan ya fito da wayar daga aljihu ya ga sunan Hadizar ya ce "Hudu ne yake kirana" Ya faɗa yana ja gefe ya ɗaga wayar haɗe da ƙasa da murya ya ce "Amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida, amarya mai maganar zuma" Bata amsa masa ba ta ce "Maganar kayan da zan yj fitar biki ne, na ga yau baka zo ba yau na so mu yi maganar, ka ga lokaci yana wucewa saboda ɗinki ga kuma su Zainaba ba kai kuma uban nasu baka ce komai ba kan kayan namu" Shiru ya yi kansa yana juyawa shi ya ma rasa abin faɗa, abu na farko yana tunanin shi da ya cake kuɗi ya bata dubu ɗari biyu bayan kaf kauyen nasu dubu ɗari biyu da hamsin ne kuɗin budurwa ma bazawara dubu ɗari amma ta matsa masa ya bata dubu ɗari biyu kuma yanzu take masa maganar kayan fitar biki? Har tana ambaton wasu agololi shi ina ruwansa da kayan da ƴaƴanta za su saka shi da burinsa bai wuce a ɗaura aure ya ɗauke ta ta koma gidansa ya daina ganin ƴaƴan nata ba don ko gidansa ba zai ke basu fuskar suke masa difdiftu ba. Sai da ta sake magana ya dawo hankalinsa ya ce "Yanzu ina gidan Baba Ramma muna magana zan kira ki in na koma gida" Ta amsa masa tana yanke kiran, ya kara wayar ya taho yana ɗaga murya yana cewa "Haba kaima Hudu na faɗa maka ni da rabin raina ne Kuluwa za mu je gidansu mu gaishe da su, to sai na dawo ma ƙarasa" Kuluwa sai wani washe baki take, haka ya ƙaraso suka ci gaba da tafiya tana masa magana ta ji ya ce "To kayan uban me zan saya kuma" Kuluwa ta tambaye shi sai lokacin ya gane ɓaranɓaramar da ya yi, don ya gane maganar zuci ce ta fito fili ya ce "A,a daman Hudu ne yake cewa na fasa sayan kayan amaryar na ce kayan uban me zan saya ni da na fasa auren" Dariya ta yi ta ce "Ai ni so nake idan muka dawo daga gidanmu mu biya gidansu Hadizar nan a kira ta ta fito in zage ta tassss in faɗa mata daman bakin rijiya ba wajen wasa makaho ba ne, in ce a bi wani sarkin amma ba wannan ba" Gabansa ne ya faɗi amma da ya tuna cewa a gidansu zai barta shi kaɗai zai dawo sai ya yi dariya ya ce "Nima zan taya ki" Dariya suka yi su duka, lokacin sun ƙaraso gidansu Kuluwar. Dakatar da ita ya yi ya ce "Na saya klin da sabulai na wanka da wanki da za ki kai musu, bari na kira a kawo mana sai mu shiga da ƙwarin gwiwa" Sosai ta ji daɗi, wayarsa ya ɗauka ya kira wanda ya ba ƙullin kayan Kuluwa, ya ce ya kawo masa gidansu Kuluwa yana ƙofar gidan. Amsa masa ya yi da to gashi na zuwa. Saboda ya san halinta matuƙar ta ga kayan ba lallai ta shiga gidan ba, hakan ya sa ya ce ta shiga gidan ta faɗa musu zai shigo, da murna ta shige gidan shi kuma a take ya kira Hudu abokinsa yana labarta masa maganar da Hadiza ta faɗa masa yana ta kumfar bakin cewa son samun ta ya yi yawa kar fa ta fara tunanin za ta wanki aljihunsa ne, Hudu yana ta bashi haƙuri domin ya bi komai a sannu haka ya kashe wayar ransa yana ƙuna ya tsani duk wani batu da za a yi na taɓa kuɗi amma ya ga Hadiza idanunta idon kuɗi. Kashe wayar ya yi daidai da zuwan mai kawo kayan haka ya karɓa ya kutsa kai cikin gidan ya tsaya a zaure wani ƙaninta ya zo ya ce an ce ya shigo. Kuluwa tana zaune a kan tabarma kusa da mahaifiyarta mahaifinta yana kan tashi tabarmar yana sauraren rediyo sai ƙannenta mata guda biyu suna cin tuwo. Da sallama ta shigo aka amsa masa ana masa faram-faram mahaifinta zai iya cewa tun da aka ɗaura auren bai sake ido huɗu da Malam Nura a gidansa ba, sai dai su haɗu a hanya haka ma mahaifiyarta sai dai idan ta je gidansa amma yau gashi dan badangarci har cikin gida ya zo, kuma tare da ƴarsu wannan abin farinciki ne musamman da Kuluwar ta ƙyanƙyasa musu cewar klin da sabulai ya tsaya a wajen za a kawo masa wanda za a basu tsaraba, ta faɗawa mahaifiyarta hatta auren ma ya fasa, daɗi sosai uwar ta ji domin a tarihin aure-auren Nura kowa ya sani a ƙauyen Shabaru bai taɓa nemab aure ya fasa ba!. Maimakon su ganshi da leda riƙi-riƙe sai suka ganshi da ƙullin kaya, ita dai mahaifiyar Kuluwa saboda son samu tunaninta ɗinkuna ne ya musu aka ɗauro a zani, amma Kuluwa da ta yi wa zanin da aka ɗaure kayan ƙuru tabbas ta gane kamar dai atamfarta!. Malam Nura ya zauna a kan tabarmar da aka shimfiɗa masa daga gefe kusa da ta mahaifin Kuluwa duk da daman babu wani ganin girman juna tsakaninsu tun da akan biyan bashi suka yi ta ɗauki babu daɗi har dai ya bashi auren ƴarsa a kan hakan. Ƙullin ya ajiye a gabansa ya shiga gaishe da su suna amsawa, amma Kuluwa ta yi mutuwar tsaye sai dai hasashenta bai kai kan gaɓa ba, domin iya tunaninta bata taɓa kawo cewa zai ɗakko kayanta ya kawo ta gida ba, da a ce ta yi wannan tunanin da ta tabbatar cewa Malam Nura ba ƙaramin ɗan duniya ba ne, sannan da hankalin ta ya fahimtar da ita cewar maganganun da Haule take faɗa masa gaskiya ne sun ishe ta ɗaukan darasi sai dai ba haka ba ne, ranta ya kissima mata cewar ko dai ɗakkowa ya yi ya kawo a bayar zai ɗinka mata wasu, amma mai ya sa bata ga kayan ba sai yanzu, sannan ina ledar sabulan, wannan tambayoyin take ta yi a zuciyarta. Mahaifin Kuluwa ne ya ja shi da zance yana tambayar Baba Ramma inda mahaifiyarta ta yi ƙasa da murya ta ce "Kuluwa ko dai ɗinkuna mijin naki ya iyo mana? Gaskiya yarinyar nan kin samu mazaunan zama a gidan miji" Daɗi ne ya kashe Kuluwa ta murmusa bata ce komai ba. Sai da ya gama gaisawa ya kira ɗaya daga cikin ƙanen Kuluwar, tasowa ta yi ta zo wajensa su Kuluwa sai washe baki ake, ya ɗago ƙullin ya ce "Mariya ungo wannan kayan yayarku ne ki kai mata ɗaki" ,Daga mahaifin Kuluwa har mahaifiyarta mutuwar zaune suka yi, Kuluwa kuwa zigidim ta tashi tsaye tana zaro ido bata san lokacin da magana ta suɓuce ta fito ba ta ce "Kayana kuma? A kai min wane ɗaki, mai zan yi a gida?" Ta shiga jero masa tambayoyin domin abin ya razana ta da yawa. MAMAN AFRAH😍 09025576222 [4/8, 6:27 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/Bu295Z6iGnL3SoKYtgqnbZ?mode=gi_t *UWAR AGOLA* 🅿️4️⃣ *Bojuwa herbs* *By* *Surayya Dee.* *08032773332.* *Sanyi flusher!* *Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.* *Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya Slsai ta dawo ko ta turo wasu*. *Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.* *Tightening set na hade mace ta dawo Zamzam tamkar yar budurwa.* *Tasirin magani Idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.* *Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.* *Akwia packages na mussaman ga Amare, uwargida ,zawarawa da masu jego.* *Tuntubeta a wannan lambar* *08032773332* *Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.* *UWAR AGOLA* NA MAMAN AFRAH *Daga marubuciyar* *Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.* 09025576222 🅿️4️⃣ Malam Nura ya kalli Kuluwa sheƙeƙe ganin ta hayayyaƙo masa ya ce "Zama za ki yi a gidan mana" Hankalin iyayenta ya tashi Babanta cike da hasala ya ce "Nura saboda wulaƙanci ka sako min ƴar shi ne ba za ka barta ta taho ita kaɗai ba sai ka kawo min ita saboda rashin ta ido" Kuluwa har hawayen baƙincikin kishi ya silalo mata domin ta fara tunanin saboda amaryarsa ya dawo da ita gida, ba komai ne ya sanya ta zubar da ƙwallar ba sai tunowa da ta yi da irin barikin da Malam ya nuna mata ta yadda ya yudare ta ya kawo ta gida. Cikin muryar kuka ta.ce "Wallahi baka isa ba" Mahaifin ta ne ya tsawatar mata, ta ja bakinta ta yi shiru ba tare da son ranta ba, Malam ya ce "Ya kamata a barni in mutu kafin a binne ni, ni dai babu wanda ya ji na ambaci kalmar saki don haka bam saki Kuluwa ba" Wata nannuyae ajiyar zuciya Kuluwa ta sauke, saboda kalmar nan ta mata mugun daɗi, don ta fahimci cewar har yanzu tana da sauran damar da za ta hana shi rawar gaban hantsi dangane da wannan la,anannan auren da ta tsana, saboda ta san tun da har ya kawo ta gida a kan maganar auren ne. Mahaifiyarta cike sa takaicin cin fuskar da aka yi wa ƴarta ta ce "To a kan me za ka kwaso kaya ka kawo ta gida?" Kafin ya furta wata kalma ta juya wata tambayar ga Kuluwa tana faɗin "Ke Kuluwa ba cewa kika yi gaishemu kuka zo ba? Har kina faɗin yana wajen zai taho da sabulai, amma yanzu muke jin wani sabon al,amari?" Kuluwa ta ce "Wallahi ba ƙarya na yi ba haka ya faɗa ... Babanta ne ya ɗaga mata hannu ta yi shiru tana goge guntun hawayen da ya zubo ya mayar da kallonsa ga Malam Nura cikin kakkausar murya ya ce "Nura wane dalili ne ya sa ka dawo da ita gida tun da babu saki tsakaninku?" Gyaran murya ya yi tamkar wanda zai yi kiran sallah, har sake nannagawa yake sannan ya ce "Na dawo da ita gida ne ta zauna tsawon watanni uku ko huɗu" Gabaɗaya kowa idanu ya zuba masa, mahaifinta ya ce "To ina ga ko sakin ta ka yi idan ta yi wata uku ai ta yi idda, wane dalili ne zai sa ka kawo ta gida ta zauna har tsawon wata uku ko huɗu?" Kuluwa ta yi karaf ta ce "Wallahi ba zan zauna ba ƙafata ƙafarka" Babanta ne ya nuna ta da yatsa ta koma ta zauna tana jin kamar ta shaƙo Malam ta masa shegen dukan da ko cewa aka yi ga mace ba zai yi sha,awar kallon ta ba ma bare har ya ce zai aure ta. Mahaifiyarta ta ce "Banda sakarci namiji yana yakice ki, ke kina manne masa, shi kaɗai ne autan maza? Wallahi albasa dai bata yi halin ruwa ba, ni namiji yana cewa kama gabanki nale nufae gidan iyayena don gidansa bai fi na iyayena ba... Babansu Kuluwar ne ya dakatar da ita. Malam Nura ya ce "Daman rawar kanta ne ya yi yawa, tana ƙetara maganata a cikim gidan, kuma ita Haule ba haka take yi ba, na basu kuɗin faɗar kishiya ɗari biyar biyar amma Kuluwa tana karɓar kuɗin nan yadda ka san ta samu tsohon tsumma haka ta yayyaga ɗari biyar ɗin wai ta raina"Babanta ya ɗauki salati sai da ya salance kowa yana jiran dalilin salatin nasa ya ce "Amma Kuluwa an yi ƴar banza, yanzu kuɗin kika yaga naira ɗaiɗai har ɗari biyar?" Ran mahaifiyarta ne ya ɓaci ta ce "Haba mai gida ina tsiya ina wata ɗari biyar a faɗar kishiya, maganar kishiya ake yi fa wallahi ta min daidai ai ko dubu biyar ce gwara ta yaga" Baban Kuluwa ya ce "Ai ka ji ku mata daman ku kuke ɗaurewa ƴaƴanku tsantsa, ina laifin ɗari biyar gado ba na uwarka ba aka baka ƙyallan zani ai an mutuntaka, idan bai bata ɗari biyar ɗin ba ma ba wai ƙwata za ta yi ba" Malam Nura ya murmusa alamar jin daɗi ya ce "Wallahi tana neman takura min ne, kishin ta ya yi yawa, to babban dalilin da ya sa na kawo ta ma, na basu hutun zuwa turaka, ka san abu in ya shafi gidan aure to babu waji ɓoye-ɓoye ko jin kunya, to na ce su haƙura da zuwa taraka har sai amarya ta tare ita ma, to Haule ta yarda don wallahi har naira ɗari na ƙara mata... Baban Kuluwa ya katse shi da faɗin "Allahu akbar ka ga mai rabo, wata bayan ɗari biyar ɗin ka ga ai ta tashi da ɗari shida" Ran Kuluwa ya kai ƙololuwa wajen tashi, daman ta san babanta yana ja mata raini. Malam Nura ya ɗora da faɗin ",To ita tana da taurin kai jiya ma a ƙofar ɗakina ta kwana wai sai na buɗe" Mariya da Hinde jin maganar ta fi ƙarfin su cike da kunya suka tashi suka shige ɗakinsu. Mahaifiyarta kuwa sai saƙon harara take aika mata jin zubar da ajin da take yi a kan mijin da ko damuwa da ita bai yi ba Mahaifinta ya ce "Wannan kam bai kyauta ba, ke da kika je zaman aure ina ruwanki da aurensa, kuma duk dokar da ya shimfiɗa ai sai ki ce to" Ya juya ya kalli Malam Nura ya ce "Amma sai ka ce a mata faɗa ba wai zaman gida har watanni ba" Malam Nura ya ce "To a mata faɗan don aurena da Hadiza babu fashi" Baki sake take kallonsa tana tuna magangnun da ya faɗa a hanya amma yanzu har ya sauya ashe rami ya mata ta faɗa ba wai fasa auren ya yi ba, ita har da cewa daga gidansu su je gidan su Hadizar a zuciyarta ta ce 'Lallai namiji munafuki ne' Mahaifiyarta takaici ne ya hana ta sake furta komai Babanta ne ya ringa faɗa ta inda yake shiga ba ta nan yake shiga ba, sai da aka kammala amma Malam Nura da ƙarfin hali sai ya ce "To amma ta zauna ko sati ɗaya ne ta yi ta koma daga baya" Babanta ganin abun ba na ƙare ba ne sai ya amince Kuluwa tana ji tana gani Malam Nura ya musu sallama ya fita ranta in ya yi dubu ya ɓaci don ta lura kawai so yake sai ya gama ɓarzar amarci sannan ta koma amma duk da haka ya yi gudun gara ne ya tare a gidan zago don ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa, don ko a su ko a ita wanna amarci babu wanda zai ci shi ta daɗi!. Malam Nuwa kuwa yana fitowa waje ya yi wata miƙa haɗe da yin hamdala a fili ya furta ",Na jefar da ƙwallon mangwaro na huta da ƙuda, ina dalili mace kamar cingam, ai wallahi ba don kar na sake ta na yi asarar dubu goma ta ba da sakin ta zan yi, ko kuma in sake ta idan na gama amarcin na dawo da ita?" Ya sake jefawa kansa tambayar, sai kuma ya kaɗa kansa ya kama hanyar zuwa gida. Yana dab da zuwa gidan kiran Hadiza ya shigo, ya ɗaga ta balbale shi da masifa a kan cewar idan har basu yi maganar kayan da za ta saka a fitar biki ba to wallahi tana iya fasa aurensa, babu yadda ya iya ya shiga bata haƙuri yana faɗin yanzu zai je gidan ya fita wani abu ne. Ta saki gajeran tsaki irin na kai ya dama ɗin nan ta ce "Ka turo min kuɗin katin wayar da na kira ka, don ni ba a yi kuɗin katin wayata don kiran namiji ba, shi namiji shi ya dace ya bautawa mace" Shiru ya yi yana nazarin maganar ta, wato shi namiji shi ne wahalalle, bayan ya san kuɗin da take saka katin daga jikinsa take ɓanɓara. A zuciyarsa ya ce "Anya wannan za a yi abin arziƙi da ita kuwa in ta shigo gidana, tana titi ma katin waya ma ba za a mora ba to ina ga in ta shigo gidan za take siyan kayan miya idan na bada hatsin tuwo kuwa?' Kansa ya tamabaya yana ta wasi-wasi duk da bai gama yanke hukunci ba amma dai ya san cewar dole a more ta saboda yana ganin duk burga ce ganin tana gidansu amma in ra shiga gidansa sai yadda ya yi da ita. Haƙuri ya bata ya fasa shiga gidan ya nufi wajen mai siyar da kati ya saya ya tura mata, maimakon ya dawo gidan sai ya nemi waje ya zauna a majalissa ake ta hira. Kuluwa kuwa haka ta kinkimi ƙullin kayan nata ta nufi ɗakin su Mariya, ranta duk a ɓace sai dai ta yi alƙawarin ko ana mutuwa ana falkowa yau a gidan mijinta za ta kwana!. Babansu yana jin rediyo yana hamma, can da ya gaji ya kwashi rediyon ya shige ɗakinsa, haka ma mahaifiyarta tun da ta ce ta zubo mata tuwo ta ƙi sai ta watsa yinta, don ta lura Kuluwa ta yi nisa a rakiyar ɗa namiji ba za ta ji kira ba, hakan ya sa ta shiga ɗaki ta hau gadonta ta miƙe ta shiga sakin munshari. Baba ya taso ya saka sakata a gidan ya koma ɗakinsa, su Mariya ma tun suna hira suna zagin Malam Nura Kuluwa tana kare shi, har kowacce bacci ɓarawo ya yi awon gaba da ita. Kiran sunansu ta shiga yi amma ɗif, tasowa ta yi ta fito ta nufi ɗakin Baba tun kafin ta ƙarasa take jiyo tashin munsharinsa, ta leƙe ɗakin mahaifiyarta nan ma baccin take, saɗaf-saɗaf ta koma ɗakin su Mariya ta sungumo ƙullin kayanta ta ɗauki takalmi a hannu ta nufi hanyar ficewa, a hankali ta zare sakatar ta ja musu ƙofar ta saka takalmin ta yi fiyarta. Ko da ta je gidan ta shige abin ta ko sallama bata yi ba ta ajiye ƙullin kayana tana mamakin kayan da suke ciki domin ta ji da ɗan nauyi, tana cikin buɗe ƙofa Malam Nura da ya dawo daga majalisa ya shigo ya rufe ƙofar gidan, baki ya buɗe zai kwaɗa sallama, domin ransa fari ƙal Kuluwa tana gida, duk da ransa da sauran ɓurɓushin ɓacin ran kayan da Hadiza ta ambata zai yi mata. Sallamar ce ta maƙale, baki sake yake kallon ta ita da ƙullin kayan ta, Kuluwa kuwa ko kallo bai ishe ta ba ta buɗe ɗakinta ta kinkimi kayanta ta shige. Har ya ƙaraso ɗakin ƙofar ɗakin bakinsa a buɗe shi ya rasa tsakanin Hadiza da Kuluwa waye yake addabar rayuwarsa. Labulen ya bankaɗa lokacin ta kunna fitila tana since ƙullin za ta mayar da kayan mazauninsu. Yana bin ta da kallo ya ce "Waye ya je bikon ki?" Ƙugu ta riƙe da hannu biyu ta ce "Ni ce nan na bikato kaina, kuma wallahi idan ka ce kule casss zan ce, in banda ma maza baku da kunya kai kana da idon da za ka kalleni, ka zauna ka sharara mini ƙarya da daɗin baki ashe dai duk bula ce" Da yatsa ya nuna ta ya ce "Wallahi kika ƙara ambata cewar ina ƙarya sai ranki ya ɓaci" Ƙaramin tsaki ta je ta ce "Ya daɗe bai ɓaci ba" Fuuu ya fice daga ɗakin, sai kuma ya dawo ya ce "Ki shirya ƙunsar takaici idan amaryata ta tare domin da ƙafafun ki za ki fice ki yi yaji" Baki ta taɓe ta ce "Ɗan halak ka fasa!. Yana saka ƙafarsa a ɗakin tamkar da kiran Hadiza ya shiga, sai dai filashin ne ta masa, hakan ya sanya ya doka tsaki yana faɗin "Uwar son kuɗi ai wallahi kin gamu da gamon ki domin zani ce ta tarar da mu je mu" Ya faɗa yana doka mata kira ya zauna a bakin katifarsa, tana ɗauka ta ce "Nura wai mai ya sa kake so ka nuna gazawarka ne?" Harara ya galla mata ta wayar ya ce "Shigowa ta gidan kenan, ina jinki gimbiyar mata, autar mata" Bata tanka masa ba ta ce "Maganar kayan da na maka, nawa da na ƴaƴanka" Gabansa ne ya faɗi ya fara tunanin ita kuwa mai haɗa ta da sabgar cikin gidansa da har za ta ce ya yi wa yaransa wani kayan fitar bikin ta. Yana ɗan gyara murya ya ce "Haba Hadiza su Kabiru duk suna da kaya fa, wallahi ba za su rasa yadin da za a saka musu ba kin ga ba auren fari ba ne bare na ce zan yi ta wadaƙa da kuɗi, wannan aurena na ashirin ne, kin ga Haule ce matata ta farko, kuma na mata kishiyoyi goma sha takwas kin ga idan aka haɗa da ita goma sha tara ke ce ta ashiri... Bai ƙarasa ba ta ce "Malam Nura ban tambaye ka wannn dogon bayanin ba, ni kaina na sani wannan ne karon farko da zan aure ka, sannan da kake maganar su Kabiru ni ina ruwana da wasu su Kabiru? Ni fa ban san ma ƴaƴanka mata ne ko maza ne ko kuwa maza da mata ba ne, da har zan ce ka musu ɗinki" Yana sauke ajiyar zuciyar jin daɗin ashe shi ne bai fahimta ba ya ce "Allahu akbar wallahi zatona su Kabirun kike nufi da kika ce ƴaƴana" Tsaki ta doka ta ce "Ni da su Zainaba nake ita da Shafi,i" Dakyar ya samu zarafin amsa mata ya ce "Mai za a musu Hadiza???" Jin tambayar tashi kamar da gayya ta ce "Bari na maka gwari gwari, kayan fitar biki nawa da nasu za ka mana, ai su ma ƴaƴanka ne ko kuwa ƴaƴana ne ni kaɗai?" Wani ƙululun baƙinciki ya haɗiye ya ce "Wane mutum in ji mutuwa, ya za a yi in ce ba ƴaƴana ba ne, ai da an mutu har liman, ai ƴaƴanki ƴaƴana ne" Ta ce So nake ka mana ɗinki iri ɗaya mu saka ranar ɗaurin aure har kai da kuma su" Karaf ya yi ya ce "Ki muku a wanann kuɗin dana baki, ni daman na ba Hudu saƙon shadda kano zan ɗinka" Ta ce "Wato ma ka bashi to wallahi ka bashi namu ya siyo iri ɗaya idan ba haka ba ka zo ka karɓi kuɗinka na fasa auren" Tana kaiwa nan ta kashe wayar. Zamewa ya yi daga kan katifar ya yi zaman ƴan bori yana jin ɓacin rai, ba komai ne damuwarsa ba yadda ya bada kuɗin shaddar dubu ashirin amma yanzu ana cewa ya ƙara, duk wayar da yake Kuluwa tana laɓe, sai da ya gama ta juya ta koma ɗakinta tana jijjiga kai tana mamakin wannan wace irin amarya ce tana saƙawa a ranta dole ta yi fito na fito da wannan amarya domin ta lura za ta sha gabanta a wajen miji. Katifarsa ya janye bayan ya rufe ƙofar, ya tashi ya leƙo window ganin babu kowa ya koma ya shiga tona tsakiyar inda ya ajiye katifar, yayi tono sosai sannan kuɗi suka bayyana yan fito da su yana kuka mai cin rai, a fili ya ce "Ni dai wannan so ya zame mini jaraba ma ba jarabawa ba, ta yaya a ce ƴaƴan bazawara ma sai ka musu ɗinkin fitar biki" Dubu talatin ya lissafo ya ce ita dubu sha biyar yadi uku su ma ƴaƴan yadi uku, ya mayar da ramin ya rufe ya mayar da katifar yana kallon kuɗin gabansa yana faɗuwa yana tunanin da wannan kuɗin sai ya auri kusan mata uku amma wai iya hidimar amarya da ƴaƴanta ne. Haka ya kwanta da kuɗin a aljihu yana saƙa da warwara. Ko da ya fita da safe zai kai wa Hudu har ya tafi Kanon sai wurin mai pos ya kai aka tura masa ya masa bayanin cewar iri ɗaya zai siyo shaddar, sannan ya kira Hadizar ya ce ya bayar sai dai abin mamaki ko godiya bata masa ba lamarin da ya sanya cikinsa kaɗawa. Da dare Hudu ya dawo sai dai basu haɗu ba sai da safe, ya basho shaddar blue ta yi kyau sai ƙamshi take, haka ya ɗauki tashi ya kai ɗinki ya kai mata tasu, a haka ma sai da ta karɓa musu kuɗin ɗinki a wajensa, shi ya rasa wane dalili ne ya sa ya zama kamar wani sauna a wajen Hadiza. Kwana biyu aka ɗinka masa shaddar ta sha aiki ya kai aka goge, sai dai ya saka a ransa idan ya saka ranar ɗaurin aure cirewa zai yi ya samu ya fansar ya karɓi kuɗinsa domin ba zai saka shadda mai tsada haka ba. Tun daga zauren gidan yake karaɗi yana faɗin "Ga angon Hadiza nan, lallai Hadiza ta ciri tuta, wannan shaddar ko a aurena na farko nan saka ba, amma sai gashi a aurena na ashirin zan saka, Allahu akbar kabiran" Ya faɗa yana kara shaddar a jikinsa, Kuluwa tana kallonsa ta windown ɗakin ta amma bata fito ba, baƙinciki kamar ya kashe ta tana cin alwashin da ita kaɗai ta sani. Haule ce ta fito tana ta zuga shi tana wasa shi, haka ya ringa mata ruwan sanya albarka. Tun da ya faɗi cewa ba za su sake shiga turaka ba, babu wacce ya bari ta shiga, magungunan da aka haɗo masa ne yake ta narkawa cikinsa shi ala dole mai amarya. Ranar asabar, wacce ta kasance ranar ɗaurin aure, ango kansa ba rawa yake ba gilgilwa yake domin a yau ne sabuwar amarya za ta tare da daddare. Ana shirin tafiya ɗaurin ya baro su Hudu da sauran abokansa, sai wasu makaɗa da duk suka karaɗe layin da kaɗe-kaɗe suna ta waƙe ango suna ambaton sunansa da sunan amarya!. Baki a washe ya cika roba fal da ruwa ya kai banɗaki, ya dawo ya cika bokiti ya nufi bayin Haule wacce take gyara ɗaurin ɗankwali ta ce "Ango yau ruwan wankan har makayi biyu" Bokitin ya ajiye ya washe baki ya ce "Allah ne kaɗai ya san daɗin da nake ji yau Haule, ji nake kamar na ɗaga ruwan gidan nan na sheƙe a jikina" Da dariya ta tuntsure tana faɗin "Idan ka sheƙe duka ruwan ina muka kama muka riƙe, da wanne za mu yi aikin gidan, gwara dai ka je da guda biyun" Shi ma dariyar ya yi yana ɗauka ya shige banɗaki ita kuma ta shige ɗakinta. Kuluwa da take leƙosu daga ɗaki tana banka musu harara ganin babu kowa a tsakar gidan ta fito riƙe da ashana a hannunta, da sauri ta nufi ɗakin Malam ta ga shadda a kan katifa tana ta sheƙi ga wayarsa da kwalbar turare a gefe da kuma hula, baki ta taɓe ta ɗaga rigar ta ɗauke wandon ta fito, bayan ɗakinsa ta nufa ta ƙyasta ashanar ta saka a jikin ƙafar wandon, saj da wutar ta cinye gabaɗaya ƙafafun wandon ya koma gajeran wando mai iya cinye sannan ta saka ƙafa ta take, wutar ta mutu ta ɗakko wandon ta linke ta je ta mayar mazauninaa ta fito daga ɗakin ta shiga ɗakinta ta garƙama sakata!. MAMAN AFRAH 09025576222 [4/9, 6:17 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/DDmSp3AUB7gJnJQLnau59V?mode=gi_t *UWAR AGOLA* 🅿️5️⃣ *Bojuwa herbs* *By* *Surayya Dee.* *08032773332.* *Sanyi flusher!* *Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.* *Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya Slsai ta dawo ko ta turo wasu*. *Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.* *Tightening set na hade mace ta dawo Zamzam tamkar yar budurwa.* *Tasirin magani Idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.* *Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.* *Akwia packages na mussaman ga Amare, uwargida ,zawarawa da masu jego.* *Tuntubeta a wannan lambar* *08032773332* *Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.* *UWAR AGOLA* NA MAMAN AFRAH *Daga marubuciyar* *Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.* 09025576222 🅿5⃣ *KULUWA* Tana shiga ɗakin ta fara tunanin makomar ta a gidan Malam Nura, domin sai yanzu ne zuciyarta ta shiga zulumi da abin da ta aikata na ƙona masa wandon amarci!. Duk da ta san shigowarta ɗakin ba mafita ba ce amma dai ya zama wajibi ta tanadi wani abu da za ta tsira, tun kafin ya fito ya mata tijara. A can cikin banɗaki kuwa Malam Nura sai da ya saɓa jikinsa sau takwas, yana wankan yana ta ƙiyasta irin kyan da zai yi yau, ya san lallai zai tashi kan mutanen ƙauyen Shabaru, duk da ya gama tsara nawa zai siyar da shaddar idan an kammala biji, don hatta kuɗin ɗinki sai ya fitar har da riba zai ɗora!. Yana gama wanka ya mayar da riga ya fara shirin buɗe ƙofar banɗakin. Kuluwa tana ta tunanin abin da za ta aikata, wata dabara ce ta faɗo mata a rai, da sauri ta leƙo tsakar gidan daga jikin wata ƴar tula da take jikin ƙofar ɗakin, Haule ta hango tana duba ƙaramin mudubi a hannunta ta nufi ɗaki. Da sauri ta zare sakatar ɗakin ta da ta saka, ta ɗan buɗe ƙofae kaɗan yadda ba za a ce rufewa ta yi ba, baki Kuluwa ta buɗe da ƙarfi ta shiga yin jiniya irin wacce ake yi wa sarki ko gwamna da sauransu. Malam Nura yana shirin fitowa sautin jiniya ya sauka a kunnuwansa, ɗif ya yi ya saurara don gabaɗaya ya rasa ta ce a zuciyarsa ya ce 'Ikon Allah, lallai wannan ɗaurin auren nawa zai tara mutane, to ko dai a dangin su Hadiza suna da alaƙa da sarauta ne, Allah ya taimakeni da na cire son kuɗi na yi ɗinkin na kirki, da kunyata zan yi, lallai yau akwai shagali' Ya faɗa baki washe yana buɗe ƙofar ya fito. Sai da ya fito tsakar gidan ya ji sautin jiniyar kamar ma ya ƙaru tamkar a cikin gidan ake yi. Haule da ta shiga ɗaki ta jiyo ana "Wooooo,waw,waw,waw,waw, waw" Dakatawa ta yi daba ajiye madubin ta saurara, amma sai ta ji ƙaran kamar daj da baki ake yi hakan ya sa ta ɗaura yara ne suke wasa. Fitowarta ya sa ta ji ƙaran a ɗakin Kuluwa yake fitowa, mamaki al,ajabi ne suka mata dirar mikiya, hakan ya sa ta nufi ɗakin da ɗan sauri, domin sautin ya banbanta da muryar yara, tana leƙawa ta hangi Kuluwa tana ɗan zagaya ɗaki tana jiniya idanunta a rufe, gaban Haule ne ya faɗi domin tana ganin hakan ta san ba lafiya ba, salati ta kwasa lokacin Malam ya ƙaraso yana sauri domin lokaci ya ƙure. Saurarawa ya yi ya ji ƙaran jiniyar daga ɗakin Kuluwar sannan ya tabbatar da baki ake yi. Haule cike da tashin hankali ta ce "Innalillahi Malam akwai matsala zo ka ga abin da Kuluwa take yi" ,Wani kallo ya mata cikin halin ko in kula ya ce "To daɗi ne ya mata yawa shi ya sa take jiniya wataƙila ta tuno da lokacin yarinta ne" Cike da damuwa ta ce "Ba lafiya ba fa, leƙa ka ga abin da take yi" Tsaki ya doka ya ce "Kina jin dai yadda dandazon mutane suke jirana a waje da makaɗa, yau fa za a ɗaura aurena da Hadiza kuma a yanzu, ni har ina da wani lokaci ne bayan na ɗaurin aurena" Yana faɗar hakan ya nufi ɗaki da sauri har yana neman faɗuwa, a kiɗime ta tura ƙofar ta shiga a take Kuluwa ta ƙara ƙaimi wajen jiniyar tun da duk tana jin abin da ake yi ta san yanzu zai je ya ga wandonsa amma tun da dai ita ta nuna babu lafiya a tare da ita babu mai tuhumar ta. Ganin halin da take ciki Kuluwa ta fito da sauri tana faɗin "Malam jikin na nata fa kamar tsamari yake, wallahi kamar fa aljannu ne... Yana dab da shiga ɗakin ya juyo tun kan ta dire maganar ta ya ce "Haule ya kamata ki san wanda ya yi nisa ba ya jin kira, yanzu duk abin da za a faɗa ba ganewa zan yi ba wallahi, gabaɗaya hankalina ya karkata ga ɗaurin zuren nan, kuma ba kallon aljannu ba ko kukar bulukiya ce ta bayyana a jikin Kuluwa ba zan fasa tafiya ba" Yana kaiwa nan ya bankaɗa labulen ɗakinsa ya shige ya barta a tsaye da sauri ta juya zuwa ɗakin Kuluwar. Yana shiga ya samu wayarsa tana ƙara alamar ana kiransa, kafin ya ɗauka ta katse nan ya hangi miss call rututu yana dubawa ya ga sunan Hudu da Hadiza su biyu da ransu suka tara masa wannan uban kiran. Yana shirin kiran ɗaya daga cikinsu kiran Hudu ya shigo ya ɗauka Hudu ya ce "Haba Nura ya za a yi ka bar mutane tsaye ana jiranka, ka san kowa kai yake jira a tafi wajen ɗaurin auren nan, ga makaɗa ka bari suna ta faman kiɗa kuma ka san dai duk kiɗan nan da suke a kuɗi yake, daga wanka kamar wanda kake canja fata" Ya faɗa a faɗa ce. Malam Nura ya sheƙe da dariya ya ce "Wallahi ina can ina ta sheƙe wanka, gani nan fitowa" Maimakon ya bashi amsa ya ce "Wai ihun jiniyar me nake jiyowa ne?" Hudub ya tambaya, Malam Nura ya doka tsaki ya ce.. "Kuluwa ce da neman jafa,i ta tada aljannu bata san ba ni ko bataliyar aljannun ne za su sauka a gidan nan sai na tafi ɗaurin auren nan" Shiru ya yi kafin ya ce wani abu Malam Nura ya kashe wayar domin ya ga ana ɓata masa lokaci, yana shirin ɗora wayar a kan katifar kiran Hadiza ya shigo,.ɗauka ya yi cike da rawar jiki ya ce "Amarya bakya laifi, amarya mai magana suga... Kafin ya ƙarasa a gadarance ta ce "Wai ina kuka tsaya ne gabaɗaya dangin amarya sun hallara babu dangin ango, ana jiranku, kamar za ku zo daga waji gari?" Cike da farincikin jin muryarta ya ce "Allah ja zamaninki ranki shi daɗe, gamu nan zuwa" Shiru ta ɗan yj ta ce "Gani nan na sha kwalliya da shaddata, ana gama ɗaurin aure nan za ka zo a mana hoto, ina son ganinmu da shadda iri ɗaya" Ya washe baki kamar ta masa busharar da kujerar makka ya ce "Ai ina nan ki jirayi fitowata nima, dan ba bari zan yi ki fini kyau ba atoh" Ya faɗa cike da wasa, dariya sosai ta yi ta ce "To sai kun ƙaraso" Ya amsa mata. Har zai kashe ta ce "Ai na bango za a mana hoton na rataye a ɗakina" Ya yi karaf ya ce "Ni guda huɗu xa a mini naki ke kaɗai guda uku na jera su, sai namu wanda za a mana tare in kafe a bango" Tana ƴar dariya ta ce "Ai ina so in ganmu da kaya iri ɗaya" Ya ce "Yau kwa za ki gani" Har za su yi sallama ta ce Wai ƙaran mene ne nake ji?" Da kamar ba zai faɗa mata ba don ya ga tana cinye mishi lokacin gashi ana jiransa, amma da yake so ya rufe masa ido ya ce "Kuluwa ce zazzaɓin kishi ya kama ta, take jiniya kamar wata motar ƴan sanda" Baki ta taɓe ta ce "Ta jirayi zuwana" Dariya ya yi suka yi sallama yana ta mamakin ta domin ya san ta da zafin kai bai sani ba ko don ranar ɗaurin auren ne shi ya sa take lallaɓa shi ko kuwa wani abu ne ita dai ta sani domin shi dai ya san ruwa ba ya tsami banza. Turare ya ɗauka ya shafa a jikinsa, ya ɗakko mai zai shafa ya lakuto kenan wayarsa ta sake ƙara, ganin sunan Hadiza ya ɗauka cike da masifa ta ce "Wallahi idan ka ƙara wasu daƙiƙai baka zo ba da wani za a ɗaura mini aure, ka san zan aikata ko?" Tana faɗa ƙit ta kashe wayar har lokacin yana iya jiyo jiniyar Kuluwa. Wannan man na hannunsa da ya lakuto ko murzawa bai yi ba tsabar kiɗimewa, bai san ya lakuta man a tsakiyar hancinsa ba. Da sauri ya ɗaga rigar ya ɓalle maɓallin ya saka da sauri, don gabaɗaya Hadiza ta faɗar masa da gaba, domin a maganar ta babu wasa kuma ya san matuƙar aka ɗaura auren ba za ta biya shi kaf kuɗaɗensa ba. Yana saka rigar ya ɗauki wandon amma saboda hankalinsa ba a jikinsa yake ba haka ya zura ƙafafunsa ya ji kowacce ta wuce ya ja mazugin ya ƙulle ba tare da ya lura da abin da yake faruwa da wandon nasa ba. Maɓallin rigar ya ɓalle ya ɗauki hula ya saka, turaren ma bai fesa a kayan ba ya ɗakko wayarsa ya fito a sukwane. Kusan karo suka yi da Haule da ta taho sanar da shi cewa ko malami za a nemo ya yi wa Kuluwa ruƙiyya. Ganinsa yana sauri ta ce "Malam na faɗa maka halin da Kuluwa take ciki" Malam Nura yana zare ido cike da masifa ya ce "Haule ki ƙyaleni, don a halin da ake ciki yanzu ko gawa ce a ajiye sai dai a jira idan na dawo daga ɗaurin aure a yi jana,izar" Baki sake take kallonsa don ya bata mamaki ta rasa wane irin so yake yi wa wannan auren, ita dai duk aure-aurensa bai taɓa ɗora rai a kan aure kamar wannan ba. Sai lokacin ma ta lura da wani lafcecen mai a saman hancinsa ta ce "Malam ka ga fuskar ka kuwa mai ne lafke a wuri guda ko shafawa baka yi ba, kuma fuskar gata nan firi-firi babu mai" Bai jira cewarta ba ya saka hannu ɗaya ya murje fuskar, kasancewar man da ɗan dama sai ya yi wani uban maiƙo yana sheƙi kamar ya shafa man ƙuli. Takalminsa ya saka ya fara tafiya, gaban Haule ne ya faɗi ganin ƙafafun Malam Nura a waje, duk da halin damuwar da take ciki na jinyar Kuluwa don gabaɗaya ma muryar Kuluwa ta shaƙe saboda jiniyar da take yi amma hakan bai hana dariya ƙwacewa Haule ba, don a tunaninta tsabar sauri ne ya sa Malam ya manta bai saka wandon shaddar ba. Sai da ta ɗan dakatar da dariyarta marar sauti lokacin har ya kusa da zaure ta ɗaga murya ta ce "Malam...Tun kan ta kai aya ya ɗago mata hannu ko juyowa bai yi ba, alamar ba zai samu damar tsayawa ba, cike da ɗaga murya ta ce "Duk saurin ne ya sa ka manta baka saka wandon shaddar ba?" Jin tambayar ya yi kamar ta rainin hankali shi gabaɗaya hankalinsa yana kan ɗaurin auren da Hadiza ta ce za ta fasa da shi idan bai yi sauri ba, ga wayarsa da Hudu yake kira. Kamar ba zai duba ba tun da dai ya san ya saka wandonsa, amma sai ya kalli ƙafar abin mamaki babu alamar wandon, da sauri ya janye rigar daga gaba, ƙwabrinsa ya gani zangar -zangar a waje, gabansa ne ya faɗi, domin abin da ya fara zuwa ƙwaƙwalwarsa shi ne aljannu ne suke son raba tsakaninsa da Hadiza in ba haka ba shi da ya san ya saka wandon ya za a yi ya ga babu. A kiɗime ya ɗage rigar har saman gwiwarsa amma sai fatar jikinsa yake gani bai ga shaddar ba. Haule tana dariya ta ce "Ka koma ka sako" Shi dai har lokacin yana cikin ruɗani, jin furucin ta ya yi saurin ɗage rigar gabaɗaya, gajeran wandonsa na shadda iya cinya ya bayyana ƙasan da alamar ƙonewa. Idanunsa ya zazzaro tamkar za su faɗo ƙasa, ya lailayo wani uban ashar mai maiƙo ya fara narkawa yana faɗin "Uban waye ya ƙona wandon shaddar nan?" Kuluwa wacce muryarta ta fara dishewa saboda jiniya, ta jiyo sautin maganarsa, gabanta ne ya bada sautin rass domin ta san mai rabata da Malam Nura yau sai Allah matsawar ya gano gaskiya. Haule salati ta hau yi tana kallon yadda aka yi wa wandon ƙunar wulakanci kamar ma ƙafa ɗaya ta fi ɗaya. Ba komai ne ya zo ƙwaƙwalwarsa ba sai tunowa da ya yi cewar kayan siyar da su zai yi idan aka gama sabgar biki, sannan ya tuno wayar da suka yi ɗazu da Hadiza a kan za a musu hoto a tare da shaddar nan iri ɗaya, hankalinsa bai kai ƙololuwar tashi ba, sai da ya tuna cewar ana can wajen ɗaurin aure ana jiransa, kuma kaf kayansa banu wani mai abin arziƙin da zai iya shiga taro, taron ma na ɗaurin aurensa!. Tunowa da magaar Hadiza na cewar idan ya ƙara daƙiƙu bai je ba za a ɗaura mata aure da wani, shi ne lamarin da ya saka shi cikin firgici. Haule da take kallonsa cike da mamaki ta rasa ma wane tunani za ta yi. Kamar wanda aka cakawa mashi ko kibiya hular ya wurgar wayarsa ma a wajen ya sake ta, Haule ta fara tunanin ko dai aljannu ne suka sauka a gidan ko kuma jifa ne aka yi wa Kuluwa da Malam ɗin, domin yanayinsa ya nuna ba a hayyacinsa yake ba, hankalin ta a tashe ta fara masa kallon ko dai hauka ya fara. Malam Nura kuwa, zuciyarsa ta gama faɗa masa wanda ya masa wannan aika-aikan, sannan a take ya gama gane dalilin jiniyar Kuluwa kenan. Haule sai ganin Malam ta yi ya falfala da gudu takalman nasa kowanne ya kama gabansa, saboda yana fara gudu ya cire su, Kuluwa kuwa gabanta yana faɗuwa tana jin tamkar ta fito da gudu ta bar gidan, amma tunowa da ta yi idan ta tafi za a kawo amarya bata nan sai ta fasa, don daman ƙannenta ma sun ce za su zo yau ɗin. Jin ƙaran gudun Malam ta yi saurin sauya akalar jiniyar tata zuwa carar zakara. Haule da take tsaye tana jin kamar na fita waje neman taimako, amma tana tsoron tijarar Malam jin Kuluwa ta daina jiniya ta tsiri carar zakara sai lamarin ya sake cunkushe mata. Ganin ya je tsakiyar gidan ya tsaya yan waige-waige, idanunsa suka sauka a inda aka ƙona wandon, yana dubawa ya ga sawun takalmin Kuluwa zarginsa ya zama gaskiya daman ya san babu mai wannan ɗanyen aikin sai ita, gaban Haule ya shiga faɗuwa, domin gabaɗaya gumi ya wake masa fuska ga sheƙin man fuskarsa ga tsantsar tashin hankali da ya bayyana, wata kaza da ta taho da ƴaƴanta za ta shiga ɗakin ta, ganin zai bige mata ƴaƴa ta kai masa cako, haushi ya sa ya shura ta da ƙafarsa, da gudu ta yi hanyar ɗakinta. Dubawa yake mai zai yi wa Kuluwa ya huce duk da ya san ko mai ya mata ba zai huce ba amma dai yana so ya mata abin da za ta san ta taɓo gidan rina!. Ɗakinsa ya juya da gudu sai gashi ya fito da adda, kiran sunansa Haule ta shiga yi tana tsoron tunkararsa don gani take kamar ya haukace, wajen murhu ya nufa inda Haule ta hura wuta, ya ɗakko wani ƙaton faskaran icce mai wuta a jiki, kafin ta ƙifta ido ya yi wa ɗakin Kuluwa tsinke, yana kwaɗa mata gigitaccen kira. Kuluwa ambaton sunan ta kaɗai ya isa ya sanar da ita ya gano tsiyar da ta shuka masa, bata san lokacin da carar zakaran da take ya tsaya cak ba, a sukwane ta nufi ƙofar ta saka sakata. Mutuwar tsaye Haule ta yi jin Kuluwa tana faɗin "Haule kira jama,a a waje, ki ce gida babu lafiya" Ta faɗa don ita a tunaninta madoki ya ɗakko zai mata dukan mutuwa bata ma san abin da ya ɗakko ba. Haule ta shiga ruɗu lallai wanda ya ƙona icce shi ya san yadda toka take tsada, in ba haka ba ashe dai duk abin da Kuluwa take ba aljannu ba ne iya shege ne kura a rumbu!. Da ƙafa ya buga ƙofar ta yi wani ƙara, Kuluwa ta koma ta manne da jikin drower ta tana ciccira ido, ya dawo ta windo ya leƙa idanunsa kamar garwashi ya ce "Wallahi wallahi karambanin akuya ya sa ta leƙe ɗakin kura, amma za ki gane shayi ruwa ne, ni kika ƙonawa shaddar kusan dubu talatin?" Kasancewar bata hango abin da yake hannunsa sai fuskarsa, ta ce "Ina sane wai karuwa ta taka matar aure! Ai a ganina ba raini ba ne don an ce wa karuwa hayo gado don abin da ta saba ne kuma sana,arta... Addae da ya ɗago da faskaran icce mai wuta a jiki shi ya sa jikin taƙaura ya yi la,asar wato bakin Kuluwa ne ya rufu ruffff Malam Nura ya ce "Yadda kika datse ƙafafun wandon shaddar ɗaurin auren Hadiza, haka zan datse ƙafafunki da wannan addar ki koma gurguwa, sannan na saka bakin wutar nan a dungulumin ƙafar taki yadda za ki ji a jikin ki, kin maida min wando gajere na maida ki gurguwa, ramuwar gayya ai ta fi ta gayya !" Haule sai yanzu gabaɗaya ta gane inda aka saka gaba da gudu ta tsallake wayarsa da take ƙara ta yi hanyar ƙofar gidan don a kawo ɗauki. Kuluwa ido ya raina fata a yadda yake magana rai ɓace ta san zai iya aikata komai ma, tun da ransa a ɓace yake ƙololuwa iya zamanta da shi bata taɓa ganin wannan ɓacin ran ba, kuma ta san duk a kan Hadiza ne yake wannan shi ya sa ita kuma ta riƙe ta abokiyar adawa ta har abada ba za ta daina kishi da ita ba. Hannu biyu ta ɗora a ka tana tunanin kar fa ya ɓalle ƙofar ya aiwatar da ƙudurinsa, kafin a zo a kawo ɗauki cike da magiya ta ce "Gida zan tafi" Yana mata kallon tsana ya ce "Sai dai a kai ki gida a baro, don sai na mayar da ke gurguwa!." Ƴar uwa ban hankalinki minti biyu,,, kina son sayen kayan kicin? Ko zannuwan gado kike so? Leshi,,, shadda atamfa kayan yara,,, takalmi da jaka,,, ko kina son siyan abaya,,, mayafai huluna da sauransu ki tuntuɓeni 09025576222 MAMAN AFRAH 09025576222 [4/11, 5:14 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/DDmSp3AUB7gJnJQLnau59V?mode=gi_t *UWAR AGOLA* 🅿️6️⃣ *Bojuwa herbs* *By* *Surayya Dee.* *08032773332.* *Sanyi flusher!* *Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.* *Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya Slsai ta dawo ko ta turo wasu*. *Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.* *Tightening set na hade mace ta dawo Zamzam tamkar yar budurwa.* *Tasirin magani Idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.* *Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.* *Akwia packages na mussaman ga Amare, uwargida ,zawarawa da masu jego.* *Tuntubeta a wannan lambar* *08032773332* *Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.* *UWAR AGOLA* NA MAMAN AFRAH *Daga marubuciyar* *Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.* 09025576222 🅿️6️⃣ Kuluwa jin furucinsa na cewa sai dai a kai ta gida a baro domin zai gurgunta ta ne, sai ta ji gabaɗaya hankalin ta ya tashi musamman da ta san daga ita sai shi ne yanzu a cikin gidan Kuluwa ta fita samo masu kawo ɗauki. Cike da yaudara ce "Na ji zan biya ka shaddar gabaɗaya... Ai furucin ta ƙara hasala shi ya yi hakan ya sa ya ajiye addar da faskaren iccen, saboda ya ga ita Kuluwa kamar ta ɗauki abin da wasa bata san irin baƙinciki da ƙunci haɗe da takaicin da ta ƙunsa masa ba, yana ajiyewa ya shiga buga ƙofar amma ta ƙi buɗuwa Kuluwa gabanta sai dukan tara tara yake tana jin tsantsar tashin hankali da fargaba domin da alama ƙaramar hauka ta samu Malam Nura. Jin ƙofar ba za ta buɗu ba ya yanke hukuncin ɓalle ƙofa, waige ya fara ya tafi a guje ya ɗakko taɓarya duk ya haɗa gumi wuyan rigarsa ya jiƙe. Yana ta saƙa da warwara a zuciyarsa domin yana tunanin idan ya gama nakasta Kuluwa wato ta mayar da ita marar ƙafa to zai haɗa mata da takardar saki, don ya hango wannan ce kawai mafita in ba haka ba idan amaryar ma ta zo babu alamar kwanciyar hankali. Yana fara buga ƙofar da ƙarfi Kuluwa ta shiga zabga ihu tana neman ɗauki. Haule tana fita ta ga mutane a tsaitsaye da yara a can ma ta ga yaran ta su Alawiyya suna tsaye suna kallon kiɗa. Kalle-kalle ta fara Hudu da ya hango fitowar ta ya taho da sassarfa ganin babu alamar nutsuwa a tare da shi, cike da damuwa da tashin hankali ta ce "Hudu akwai matsala fa a gidan" Ta faɗa tana nuna gidan da hannu. Hudu hankali tashe ya ce "Mene ne?" Haule ta ce "Kuluwa" Cike da fargaba ya ce "Allah sa ba wankan manja ta masa ba, hana shi fitowa ta yi?" Haule cike da ƙosawa da maganganub nashi duk da ya matso kusa da ita kuma ba kowa ne ya lura ba don kowa sabgar gabansa yake. Tana kallonsa ta ce "Idan manja ne ra watsa masa da sauƙi, wallahi wandon ɗaurin auren ta ƙone" Idanu ya zaro tamkar za su faɗo ya dafe ƙirji ya ce "Amma wannan mata an yi masifaffiya, ta san shaddar nawa ce wannan...Haule ta katse masa magana da faɗin "Wallahi yana can ya ɗakko adda zai sare mata ƙafafu" Da sauri Hudu ya shige gaba ta mara masa baua, don ya san a yadda abokib nasa yake da son samu son kuɗi kamar tsohon da ya shekara casa,in, ga uban buri da ya ɗora a kan shaddar har cigiyar dillalai ya bashi bayan auren ya samo masa masu saye amma ta aikata wannan ƙanƙancin. Da gudu gudu suka nufo cikin gidan gudun kar a yi aika-aika. A can cikin gidan kuwa Malam Nura ganin aikain ɓalle ƙofar babba ne sai ya cire rigar ya rataye, kasancewar lokacin da ya saka rigar yana sauri daman ko singlet bai saka ba, don kiran da Hadiza ta masa ta ce za a ɗaura auren da wani in bai zo a kan lokaci ba shi ya dagula masa gabaɗaya lissafin da bai shirya a tsanake ba, ko mai bai shafa ba haka ya fito jiki fari tas, taimakon da Allah ya masa guda ɗaya wannan man da ya lakuta a saman hanci ba tare da sanin ya lakuta ba, shi ne Haule da ta saka ya murje fuskar ta yi dama dama duk da man ya yi yawan da ban da sheƙi da gumi babu abin da yake kamar ba sabon ango mai shirin angwancewa ba. Ko da ya cire rigar ya rataye a kan igiya, ya ɗauki taɓarya ya shiga bugawa a jikin ƙofar tana ƙara duk ya loɓa ta, kasancewar akwai langa-langa a jikin ƙofar daga waje.. Hudu yana shigowa da ɗan gudu a kan hular Malam ta ɗaurin auren ya yi wa ƙafarsa masauƙi ba tare da ya sani ba, hular ta lotse, bai ƙaramin kai zuciya nesa ya yi ba da ya hangi Malam Nura ba sanye da wando gajere na shadda iya cinya duk ƙafar a ƙone baƙiƙƙirin tamkar wanda aka fito da wandon daga gidan da gobara ta kama. Ya daddage sai bugun ƙofar yake. Yana zuwa ya kama shi yana riƙe shi yana bashi baki, Malam Nura rai a ɓace ya ce "Hudu, Hudu, Hudu, sau nawa na kira ka?" Ya faɗa yana fisge riƙon da ya masa, Hudu ya ce "Sau uku" Malam Nura ya ce "To babu ruwanka a cikin wannan magana, abu ɗaya za ka mini shi ne, ka tafi wajen Hadiza kake ta bata haƙuri ta yi wa iyayenta ta jira in zo a ɗaura auren nan da ni, wallahi aka ɗaura da wani na shiga uku na kaɗe har ganyena" Dariyarsa ya danne ganin duk abokin nasa ya susuce a kan mace, duk ya karaya ya rasa wane irin tafiya da zuciyarsa Hadiza ta yi. Hudu ya ce "Ka kwantar da hankalin ka abokina, ai Hadiza bata da wani miji sai kai" Malam yana riƙe da taɓarya ya ce "Kai dai ka je ka yi abin da na ce maka Hudu, baka san wace ce Hadiza ba, ita ta kirani a waya ta ce in zo kafin wasu daƙiƙu duk da bata faɗi daƙiƙa nawa ba ne, amma ta ce idan na haura daƙiƙu ban je ba da wani za a ɗaura mata aure" Kuluwa wacce take cikin ɗaki kunnuwanta a buɗe tamkar kunnuwan maciji jin wannan batu ranta fari ƙal, tana fatan Allah kai damo ga harawa, don za ta fi kowa farinciki wataƙila har ruwa sai ta zuba a ƙasa ta sha idan aka fasa ɗaura auren nan da Malam Nura ta ga ƙarshen tsiya da kuma tijara. Hudu bai amsa masa waccan maganar ba ya ce "Yanzu dai garin neman gira za ka rasa idanu gabaɗaya, domin kana nan kana ɓata lokacin ka za ta samu wani bazawarin a yi wufff da lokacin ɗaurin auren ka a ɗaura, yanzu abu ɗaya ya dace ka yi mu tafi a ɗaura auren idan ya so muna dawowa ka yi wa Kuluwa huluncin ƙona wandon nan" Kamar zai yi kuka ya ɗaga ido ya sake kallon windon ɗakin inda yake iya hango Kuluwa tare sa tsantsar ƙarfin hali a tare da ita domin babu da na sani a fuskarta, don ta ji an zo ceton ta gabaɗaya sai ma ya ga rawar kanta ya dawo. Baki ya damƙe ya ce "Ka san dai babu wanda zai ɗauki maƙudan kuɗi ya sayi rigar shadda kaɗai ko? Ta cuceni ta taƙaitani ai dai ba zan je wajen ɗaurin aure da gajeran wandon ba, wallahi babu mai cewa ma gajeran wando ne tun da ba a iya hango wandon sai zallar ƙwanrin ƙafata, kalli yadda ta mayar da wandon nan iya cinyata dab da tsantsa ta fa yake, banbancinsa da ɗan kamfai(Pant) Kaɗan ne"Ya faɗa yana saka hannu ya kama wandon yana nunawa Hudu. Hudu ya danne dariyarsa saboda arziƙin da Malam Nuran yake da shi ya wuce ya yi wannan abun a kan shaddar da bata kai dubu talatin ba har kuɗin ɗinkin, amma duk ya saka damuwa a ransa. Hudu ya ce "Ka bar batun wanna shaddar tata ta ƙare, don ko a Kano shagon da na siyo ita kaɗai ta rage a bandir ɗin ni na saye gabaɗaya, ka ga kuwa ko da an sake kawowa ba lallai a samu mai zanenta sak ba da sai a yanko a yi wandon ka siyar da ita tun da asarar kake hangowa" Kasa magana ya yi harara kawai yake aikawa Kuluwa ji yake tamkar ya zama ƙuda ya shiga ɗakin ta windown ya aiwatar da nufinsa ko ya samu sauƙi. Maimakon ya yi wa Hudu magana sai ya juya wajen Kuluwa ya ce "Kuluwa baki da zanen shadda kalar wannan?" ,Da mamaki take kallonsa har dariya ta so kuɓuce mata amma gudun masifarsa ta danne, saboda ta san tana darawa zai ce bata damu da halin da yake ciki ba, muryarta da alamar dariya domin sai da ta danne, yau ne ta tabbatar da cewar idan mutum yana neman mafita komai ma gani yake zai dace tana karkata kai cike da nuna damuwar da yake ciki ta ce "Haba Malam ina ni ina shadda irin wannan mai tsada, kai ma ina jin a kaf rayuwarka wannan ne karon farko da ka ɗinka kuma kananganin siyar da ita za ka yi ba za ka ci gaba da sakawa ba bare ni... Kamar zai kai mata duka ya ce "To na ji abun da na tambaye ki da ban amsar da kike bani da ban... Hudu ya ce "Ba fa ita ta kai zomon ba rataya aka bata, ga wacce ta yi abun can tana ɗaki baka da damar hukuntata kawai don ita ce kuka mai daɗin hawa... Malam yana masifa ya ce "Ya isheka matarka ce ko tawa?" ,Hudu ya ce "Allah ya baka haƙuri, wai kana nufin zanin shaddar za ka ɗaura idan tana da akwai?" Ya faɗa yana haɗiye dariyarsa don har ya hango gogan nasa ɗauri da zani. Malam Nura ya yi shiru yana tuno da yanzu fa yana can a cikin jama,a ana masa Allah sanya alkairi, ana ta musu hoto shi da Hadiza wataƙila ma har hannunsa dai ta kama, tana masa murmushi, da yanzu ta zama mallakinsa amma Kuluwar nan ta kawo masa tsaiko a lamarin auren nan. Kamar ya kai wa Hudu duka ya ce ",Kamar wani bayerabe zan ɗaura zani, ka san dai na ɗaura zani na je wajen nan wallahi kwanan ɗaurin aurena da Hadiza ya ƙarw don ba za ta aureni ba, daman nufina a je a samu wani tela mai saurin ɗinki ya ɗinka mini wandon, ko zanin ba zai isa ba sai ya mini ƙafafun in ya so daga saman ko atamfa ce ya saka a mini kwanbileshin (Combination) ka ga idan na saka babu mai cewa zanin atamfa ne daga sama tun da rigar shaddar za ta rufe wajen. Idanun Hudu gabaɗaya sun kawo kwalla, amma ba ta kuka ba sai ta tsabar dariyar da take cinsa yake dannewa, ba komai yake bashi dariya ba illa idan ya kalli Malam Nura da wannan ƙonannan wandon, abu na biyu idan ya tuna yadda ido ya juye da mujiya, wato Malam Nura ya je wajen Hadiza ne da soyayyar ƙarya saboda an ce mijin ta da suka rabu mai kuɗi ne, kuma ita ma tana da kuɗi shi ne ya je da nufin ya aure ta ya wanki banza, ya tatiƙe kuɗaɗen ya sake ta, ya tsakuri wani abu daga abin da ya mora daga gare ta ya auro wata, amma da yake Allah ya ga mugun ƙudirinsa aai ya jarabce shi da son ta na gaskiya, sannan sai gashi shi take wanka a maimakon ya wanke ta, ita take cin kuɗinsa har yanzu yana ganin idan ya aure ta, zai ci kuɗin ta ne. Abu na uku yana mamakin yadda Kuluwa ta shammace shi ta ƙona wandon shaddar, ya san ba komai ba ne yake faruwa da abokinsa sai irin tijarar da yake yi wa mata, da ɗaukan haƙƙinsu ya aure ki ya wulakanta ki ya sake ki, shi a lamarinsa ma bai san mene ne so ba, don kowacce ba yana auren ta don so ba ne, kawai son zuciya ne. Hudu ya ce "Kawai ka haƙura da shaddar nan ka samu wani kayan ka saka" Yana masa kallon ka janyo ruwa ya ce "Haba Hudu ka hana ni sakat da maganganun da ka san amsar su, yanzu a kaf suturuna ina na ga wanda zan shiga taron jama,a, babu wani kayan kirki fa ka sani, a ce kamar aurena da Hadiza amma ban saka kaya na kirki ba, ni wallahi damuwata ma idan har ba da shaddar nan na je wajen Hadiza ba wallahi ba za ta ɗauki hoto da ni ba, har fa cewa ta yi za ta kafe hotonmu a ɗakin ta, wallahi Kuluwa idan muka yi gaba da gaba ni da ke ina ga ba wai ƙafafu kawai zan datse miki ba, gunduwa-gunduwa kawai zan yi da ke" ,Ya faɗa kamar an caka masa wani abu ya zabura ya koma ya buga taɓaryar hannunsa da ƙarfi a jikin ƙofar ɗakin nata, da yake ta san ƙofar tana da ƙwari ta ce "Lokacin da zan fito ma baka gidan nan, kuma dole ka aika mini takardar sakina... A masifance ya ce "Ƙarya kike mai mugun hali, ai wallahi ba zan yi asarar kuɗina ba da aka ɗaura mini aure da ke, ba yanzu zan sake ki, bare ma ke da kika mini aika-aika ai ko a gurguce kike sai na ci gaba da gana miki azaba a gidan nan, ke Hadiza ma a kan bayanji za take zaunawa tana tuƙa tuwo, kuma dole ki sunkuya ai sai kin karɓi ukuba... Saboda ta sake cusa masa haushi ta ce "Haule miƙe mini wannan rigar shaddar da ya cire, miƙo min ita ta window in ƙarasa babbake ta, in ya so sai ki ara masa riga da zani na atamfa tun da neman aron zani yake" Da sauri ya kalli igiya ya ga rigar tana nan a rataye. Bai ce komai ba domin shi kaɗai ya san irin haushin da yake ji a kan Kuluwa baki ba zai misalta ba. Wayarsa da take ta neman ɗauki Haule ta tafi ta ɗakko tare da hularsa da Hudu ya take ta lotse, ta haɗo kan takalmansa, wayar ta miƙo masa ya karɓa ya kalli sunan Hadiza ne ɓaro -ɓaro a jiki ya rasa ma ya zai yi Hudu ya ce "Ka ɗaga wayar mana, wai ni yaushe ka zama matsoraci ne wai? A ce kana tsoron mace haba abokina" Malam Nura kamar zai yi kuka ya ce "Baka san so ba ne Hudu, so ne ya mini raga-raga da zuciya ni ban san ma akwai so ba sai wannan karon, ni dai na san masoyina kuɗi amma ban san ana son ɗan adam ba... Hudu ya ce "Taɓɗi ai daman idan mutum ya ƙi sharar masallaci ta kasuwa yake yi, yanzu ai ga ta inda jarabawarka ta fito, idan ka saki mata ba har kuka suke ba ka mayar da su saboda suna sonka amma ka ce musu son banza... Kiran da ya shigo ne ya datse maganar haka ya yi ta maza ya ɗaga yana ɗauka ta balbale shi da masifa kamar uwarsa ta ce "Nura ni za ka wulaƙanta a idon duniya? Tun ɗazu lokacin ɗaura aurenmu ya cika, amma dai baka duba lokaci ko? Tun daɗewa sha ɗayan ta wuce yanzu Babana ne ya ƙara awa ɗaya ɗaya, idan har awa ɗaya ta cika akwai mazan da zan sa su hau layi duk wanda na ga wankansa ya mini shi zan zaɓa... Sai da ya gyara muryarsa ya ce "Haba masoyiyata gani nan fa ai kaf garin nan babu wanda zai kai ni ɗaukan wanka, in kin ga yadda shaddar nan ta karɓe ni zaki yi mamaki su Hudu ma sai yabawa suke, abin da ya tsayarmu abinci ne da naman da aka dafa na ɗaurin aure ake zubawa a kwanuka za a raba in mun dawo, shi ne ya tsayar da mu amma gamu nan" Hudu da yake jin ƙaryar da Malam Nura yake shararawa ya kalli kan murhu ya hangi wata tukunya ce da alama ma ruwa ne kawai yake dahuwa babu wata alamar za a yi girki barw har a samu nama, shi da ya tambaye shi mai za a ba abokai ma cewa ya yi daga wajen ɗaurin aure kowa ya kama gabansa shi babu kuɗin da zai kashe, ya maido da dubansa zuwa jikinsa da babu kaya sai ƙonan nan gajeran wando, shi da wandon ma babu wanda zai saka amma yana batun wai ya yi kyau. Hadiza daga ɗaya ɓangaren ta ce "Yawwa nawan, ai shi ya sa ina nan ina faɗawa ƙawaye da ƴan uwa cewar su jirayi zuwanka, domin kowa idan ya ce mini kin yi kyau sai na ce masa ai iri ɗaya muka ɗinka da angon shi har ya fini yin kyau ma" Hudu da Haule da Kuluwa duk sun jin abin da take cewa kasancewar a handsfree wayar take, kamar zai yi kuka ya juya ya kalli rigar shaddar ya daure ya ce "Abin ba a cewa komai sai ma kin ganni hula ta zauna daram" Haule ta yi saurin kallon hularsa da karin da aka mata ma ya ɓaci saboda taka hular da Hudu ya yi. Hadiza ta ce "Shi ya sa nake son miji kerewa sa,a shi ya sa ɗazu da aka ce baban su Zainaba ya zo ya ce in yarda a ɗaura da shi... Gaban Malam Nura ne ya buga da ƙarfi, inda Kuluwa ta carara guɗa. Malam Nura da sauri ya ce "Ki ce ba za a ɗaura da shi ba" Ta yi karaf ta ce "Ina ni ai sai sabon aure da Nurana, wai burgar kuɗi zai yi wa mutane bai san ba cewar kuɗi suna wajenka in na aureka ma babu abin da zan rasa gidanka ma sai ya fi nashi sau dubu" Yana gyaɗa kai kamar tana ganinsa ya ce "Shakka babu gamu na zuwa" Kafin ta amsa tashin hankali ya sa Malam Nura katse kiran da sauri ya juya yana kallon Haule ya ce "Haule dan Allah ki samo mini hayar zanin shadda ko nawa ne kuɗin hayar zan biya, ko siket ne ma, in dai za a samu kalar shadda ta wacce bata ji jiki ba, ko zanen ba ɗaya ba ne, ki samo mini, bari na saka wuƙa na yanka miki gefen wandon nan da Kuluwa ta yi wa lahani, ki tafi da shi ki nuna musu kalar shaddar ko Allah zai taimakeni a samu, a yadda nake jin Hadiza ta ɗauki lamarin saka shaddar nan ta kai shi ƙololuwa, ga hoton nan da take ta ambata idan har babu shaddar nan tana iya fasa auren, gwara ki samo zanin in tsargashi da reza ya yi kamar wando in ɗinke da zare da allura ya fiye mini" Haule da Hudu kawai dariya suka ƙyalƙyale da ita ganin yau ɗaya Malan ya zama kamar wani sauna a kan mace Malam Nura kuwa harara yake aika musu, a inda Haule ta yi ɗiff kawai sai ji suka yi Kuluwa ta carara guɗa ta ce "Duniya juyi -juyi kwaɗo ya faɗa ruwan zafi" Wannan kalaman ya yi wa Malam ciwo, hakan ya sa ya ƙara ƙudurtar duk lokacin da ya kama Kuluwa mai ƙwatar ta sai Allah. Hudu ne ya ce "Yanzu ka bar batub hayar zani ko siket, don ba samu za a yi ba, bari na je gida a cikin kayana na samo maka wanda za ka samu ka saka mu tafi ɗaurin auren nan" Buɗar bakin Malam Nura ya ce "Akwai sabbi dal wanda baka taɓa sakawa ba?" Yana masa wani kallo cike da gatse ya ce "A,a akwai sabbi wanda na kawo daga kasuwa yanzu" Malam Nura ya ce "Ka san dai ai ba zan saka tsoho na je wajen ɗaurin auren Hadiza ba" Hudu ya ce "Idan ka je da shi a koro ka" Malam Nura ya ce "Da in saka tsohon kaya gwara a samo mini aro a wajen wanki da guga" Hudu ya ce "Wallahi ka sake ka karɓi kayan wanjen ƴan wanki da guga, za a tsinka ka a wajen ɗaurin aure, wajen ɗaurin aure ai wajen taron jama,a ne ka sani ko mai kaya ya je wurin? Ai wanda kake ara ma saboda hira kake zuwa da daddare shi ya sa asirinka yake rufuwa" Hannu ya sa yana dafe fuska don takaicin Kuluwa ne kawai yake shaƙa. Haka Hudun ya lallaɓa shi ya tafi gida ya samo masa kayan, Hudun yana kuyawa Malam Nura ya bi bayansa da kallo yana ganin kayan jikinsa saboda kyaun da Hudun ya yi shi tsoronsa ma ɗaya kar abokin ango ya fi ango kyau. Hudu yana fita ran Malam ya ɓaci ganin ya kashe kuɗi amma zai ƙare a kayan aro, kuma tsohon kaya, a zuciye ya yi wurgi da taɓaryar hannunsa ya fara tafiya da baya-da baya sai kuma ya tafi da gudu ya yi tsalle ya doka ƙofar ɗakin Kuluwa cikin sa,a ƙofar ta ɓalle don ta ya bugu. Kuluwa da take cikin nishaɗi babu zato da tsammani ta ji ya bugo sai ta ga wayam ƙofa ta buɗe, idanu ta zaro domin har ta fara hango tsayawar alƙiyamarta. Malam Nura wanda ya buga ƙofar jirif ya faɗi a reran saboda tsallan da ya yi amma bai ji ciwon faɗuwar ba saboda ya ga kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Kuluwa ganin ya faɗi ta fara ƙoƙarin tserewa don ta tabbatar ya kamata kashin ta ya bushe sai dai idan tana da sauran kwana ne za ta kai labari, a kiɗime ta kai kallon ta kan ƙafafunta da ya ce zai sare, da gudu ta taho, bai ankara ba ya ji ta taka cinyarsa, ya ji saukar ƙafarta a ƙirjinsa yana ƙoƙari tashi daga kwancen ya ga wulgawarta ta samansa fittt kamar walƙiya. A sukwane ya muskuta, cikin sa,a ya cafko ƙafarta ɗaya, jan ciki ya yi ya janyo addarsa. Kuluwa wacce nufinta ta fice daga gidan amma a lokacin da take dab da cim ma nasara sai ji ta yi an riƙe mata ƙafa ɗaya da ƙarfi irin riƙon da ba za ta iya ƙwacewa ba. Fisgar ƙafar ta yi, amma ta kasa ƙwatar kanta, jan ƙafar ta yi da ƙarfi ta zube ta fara rarrafawa da ƙarfin ta na gaske, ƙiii ta fara janyo Malan da addarsa, ganin tana neman kufce masa ya yi ta maza ya miƙe zaune, har lokacin yana riƙe da ƙafarta, wani uban ihu ta saka tana faɗin "Jama,a ku taimakeni ƙafata, Haule kirawo jama,a a awaje su kawo ɗauki" Malam ya ce "Ai ba ƙafarki ba yau hatfa wuyanki yankan saniya zan miki kamar yadda kika raba wandon ɗaurin auren Hadiza da ƙafafunsa ta ƙarfi da yaji" Haule ta hau faɗin " "Innalillahi wa inna ilaihi raji,un Malam kar ka yi haka" Ta faɗa ba tare da jiran komai ba ta yi hanyar wajen, har lokacin mutane suna nan hango Hudu ta yi da ya kama hanyar gidansa ta tura wani yawo ya bi shi da gudu ya taɓo mata shi, ta ɗaga masa hannu, da ɗan gudu ya taho, tun kafin ya ƙaraso ta juya da sauri ta shige gidan, yana shigowa karaɗin Kuluwa ta fara masa sallama a kunne. Yana shigowa ya hau ƙoƙarin ceton ta don Malam ya fara saita ƙafar, a kwance suka same ta tana fisge-fisge ya haɗe ƙafafun ta waje guda da alama sare su zai yi da gaske. Hudu ya shigo da gudu yana faɗin "Kar ka yi haka Nura mene ne hakan" Yana zare ido yana faɗin "Ka barni na gurgunta ta, daga yau ba za ta sake wa wani haka ba" Hudu ya tafi bayansa ya shiga janshi, suka shiga kokawa, ai kuwa Kuluwa ta samu sa,ar ƙwace riƙon da ya mata, tana tashi ta zabga da gudu ta ƙanƙame Haule, Malam Nura ya fishe riƙon da Hudu ya masa, ya nufo wajen Kuluwa da Haule, Kuluwa da gudu ta saki Haule ta yi wajen Hudu, a rikice ta kai masa cafka za ta ƙanƙame shi. Haule ta dage ƙarfin ta faɗi take "Kuluwa Hudu ne ba ni ba ce, Kuluwa kar ki rungumi na miji ba muharraminki ba ne" Amma Kuluwa bata ma fahimtar abin da Haule take faɗa ta ga mutuwa muraran. Hudu ganin ta taho za ta cakume shi ya sunkuya, yana faɗin "Kuluwa alharam giya a gidan liman. Shigowar wasu mata kusan guda bakwai shi ya dakatar da kowa da abin da yake da wata maroƙiya tana faɗin "Gamu mun zo cin arziƙi, unguwa ta cika, ɓangaren mata ma yana can ya cika ana ta hidima ango kawai ake jira a ɗaura aure" Malam Nura da sauri ya warci rigarsa siyam siyam ya wuce ɗaki babu wanda ya lura da shi cikin mutanen da suka shigo. Wata nannauyar ajiyar zuciya Kuluwa ta sauke gani ta tsallake rijiya da baya. Haule ta hau yi wa matan sannu da zuwa. Kuluwa ta fara neman takalmin ta za ta tafi gida, amma shigowar ƙannenta su Mariya ya hana ta tafiya ta wayince tana musu yaƙe, nan ta shiga faɗa musu abin da yake faruwa bayan fitar Hudu. Suka shiga zuga ta a kan ta murje idanunta tw zauna duk kurin banza ne babu abin da zai iya mata kawai burga ce amma ba zai cire mata ƙafafu ba tun da ya san shi ma sai an ɗauki fansar abin da ya yi, da wannan ta ɗan saki ranta. Hudu ya dawo da wani yadi a goge tass a kawowa Malam ya ce ya saka don ya jima ma bai saka ba, ba lallai a gane cewar na Hudun ba ne amma dai ana iya ganin ba sabo ba ne. Haka ya saka ransa duk ba daɗi ya wanko ƙafafunsa da suka sha ƙasa ya shafa mai ya saka hula da turare suka fito da Hudu. Hudun ne yake raɗa masa a kan ya saki ransa saboda kar hankalin jama,a ya koma kansa. Haka ya shiga washe baki yana yaƙe duk da fargabarsa haɗuwarsa da Hadiza ne, yana tsoron ta gan shi da wannan kayana ta ce masa ta fasa, gashi ma ba ya jin ko ta yarda an ɗaura za ta amince a ta yi hoto da shi. Hadiza tun suka gama waya da Malam Nura take jin wani daɗi a ranta saboda ta san zai zo da kwalliyar kece rainin da kowa ya ganshi ya san bata yi zaɓen tumun dare ba, shi ya sa ma za ta saka su yi hoto ta kafe a ɗaki ta ko da baya nan ta yi baƙi za su ga miji na nunawa sa,a ta aura ɗan gayu mai saka kaya masu tsada.Shi ya sa ma ta yi gyara na musamman Hadiza ta yi amfani da Packages na bazawara wanda na musamman ne ƙawarta ta kawo aiko mata, da kuma cicciɓin garari, tightening set wanda yake haɗe mace, ga wani sanyi fllusher da yake wanko gabaɗaya sanyin mara, sanyin mahaifa, da sanyin jijiya, Hadiza gyaran da ta yi ita kaɗai ta san Malam Nura zai san ya yi sabon aure ba lallai ya bambance cewa ba bazawara ya aura ba saboda ta dawo tamkar sabuwar budurwa, duk abubuwan nan za a same su a wajen surayya halin yau ta wannan lambar 08032773332 [4/12, 7:04 PM] MOM MASHKR & AFRAH: *UWAR AGOLA* 🅿️7️⃣ *Bojuwa herbs* *By* *Surayya Dee.* *08032773332.* *Sanyi flusher!* *Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.* *Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya Slsai ta dawo ko ta turo wasu*. *Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.* *Tightening set na hade mace ta dawo Zamzam tamkar yar budurwa.* *Tasirin magani Idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.* *Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.* *Akwia packages na mussaman ga Amare, uwargida ,zawarawa da masu jego.* *Tuntubeta a wannan lambar* *08032773332* *Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.* *UWAR AGOLA* NA MAMAN AFRAH *Daga marubuciyar* *Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.* 09025576222 🅿️7️⃣ Hudu ne a gaba lokacin da za su fito daga cikin gidan Malam yana biye da shi, gabaɗaya idanunsa kafe a jikin kayan Hudu ba don kar Hudu ya ce bashi da godiyar Allah ba, kuma bai gode ƙoƙarinsa ba kawo masa yadin da ya yi ba da sai ya ce ya tuɓe kayan jikinsa ya bashi ya saka, don ya hango tsantsae tazara mai yawa tsakanin kyan da ya yi da kuma kyan da Hudun ya yi. A zahiri ma dai sai dai a ce kyan da Hudu ya yi amma Malam Nura ba za a ce ya yi kyau ba za dai a kira abin da ya yi da suna, ba yabo ba fallasa. Suna fitowa ƙofar gidan inda jama,a suke jiransu, saboda Malam ya yi gayya sosai, ga kuma wanda Hudu ma ya gayyato, tun da ya ga Malam yana ji da auren nan nasa da Hadiza. Kunya ce ta kama Malam Nura ganin duk kamar ma ido ba ya kansa, sai hannu ake ba Hudu ana gaisawa da shi, sai sun fara bashi hannu sannan ake ba Malam, wannan wai wanda ma suka san shi ne angon bare baƙi kamar makaɗa da maroƙa da suke ta wasa Malam Nura amma kuma Hudu suke kallo alamu sun nuna cewa sun ɗauka shi ne angon. Hudu ganin wannan kara da ake musu ya sanya hannu a aljihu ya ciro yan naira ashirin sabbi yake liƙawa maroƙan kamar wanda suke jira suka shiga ƙara ƙaimi wajen ƙarawa kiɗan nasu da wasawar armashi, shi kuma sai gyaɗa kai yake alamar yana taya Malam Nura farinciki. Malam Nura da bai fito da ko sisi ba, takaici ya hana shi magana sai hannu yake sakawa a kai- a kai yana gyara zaman hularsa, wacce tun lotsewar da ta yi lokacin da Hudu ya bi ta kanta bata dawo daidai ba sai yake jin kamar an kifa masa kwano a kan. Wato ta ƙi zama daidai. Kabiru da Lawwali ƴaƴan Malam Nura ne suke musu da wasu yara abokansu wanda musun ya sauka a kunnen Malam Nura inda abokin nasu yake cewa. "Ashe daman ƙarya kuke da kuka ce babanku ne ango, ashe bashi ba ne baban su Ya,u ne(Hudu) Kallu shi ne ya sanya sabon kaya amma babanku tsoho ya saka, ai ango ba ya saka tsohon kaya" Kabiru ne ya ce "Wallahi muna babanmu ranar nan ya siyo sabon kaya mai kyau aka masa ɗinki, kayan sun fi na baban su Ya,u kyau" Yaron ya ce "Ai dai tun da bai saka ba bashi ne ango ba" Malan da yake jin tamkar ya kwaɗawa yaron nan mari musamman da yake jaddada cewar Hudu ne ango sai tsumin Malam Nura na kishi ya motsa nan ya ci gaba da cika yana batsewa. Ayari suka yi don zuwa can gidan matan inda za a ɗaura auren, hakan ya sa aka fara tafiya masu kiɗa suna yi. Malam Nura ne ya ji duk hankalinsa ya tashi domin yana tsoron haɗuwarsa da Hadiza ba ya ma fatan ta gan shi da kayan jikinsa. Hadiza kuwa kamar ta san tunanin da yake ta doko masa waya, jin wayarsa tana ƙara ya ciro ta daga aljihu kamar ya san ita ce kuwa domin a ransa ita ya ƙiyasta za ta kira shi a daidai wannan lokacin. Wani gumi ne ya karyo masa amma ya yi ta maza ya maze ya ɗaga wayar suna tafiya, yana karawa a kunne ta ce "Ni fa na ƙosa in ganka wallahi, don tun da ka ambata min cewar ka yi kyau na ban mamaki, gabaɗaya sai na ji ka kwaɗaita min son ganinka, don na san yadda shaddar ta karɓe ni kai ɗin ma haka ne a naka ɓangaren" Hannu ya kai goshinsa ya sharce gumi, ya mayar da idonsa jikin kayan jikinsa ya haɗiye wani yawu muƙut ya ce "Yanzu dai gamu nan za mu je wajen ɗaurin auren" Sautin dariyarta ya ji har cikin kunnensa ta ce "Ka ce yau zan yi kwalli, don kafin ka ƙarasa wajen ɗaurin auren ka fara zuwa mu ga juna" Ƙulululuuuu cikinsa ya bada wani sauti don ya san tana son ɓallo masa ruwa ne, matuƙar ta ganshi da kayan nan ya san sai dai wani angon amma ba shi ba. Yana ƙirƙirar dariyar yake tamkar wani sabon mahaukaci ya ce "Haba Hadizatuwata, ni yanzu duk na matsu in ga an ɗaure mu da igiyoyin nan guda uku ki jira ni idan aka ɗaura sai in zo yau sai kin gaji da ganina don kanki" Ya faɗa yana aikawa Hudu harara wanda yake ƙunshe dariyarsa. Ta yi ɗan shiru, Malam Nura yana ta addu,ar ka ta ƙi amincewa ko kuma ya masa masifar nan tata, kamar daga sama ya ji ta ce "To shikenan sai an ɗaura ɗin ka zo, mai hoton ma yana nan yana yi a cikin gidan amma ni na ƙi yi na fi so sai mun yi tare kar kwalliyata ta ƙoƙe" Yana godewa Allah a zuciyarsa da cin nasarar da ya yi ya ce "Yawwa haka nake so, ai ana shafa fatiha zan garzayo nan" Ya faɗa yana sauke ajiyar zuciya ya san dai duk tsiya in aka ɗaura aure ba za ta ce a warware ba, ko ta ce sai ya sake ta ai dai ganin damarsa ne tun da sakin a hannunsa yake. Yana yin wannan tunanin ya ji ta ce "Ai ba zan jure ba, tahowa zan yi in tsaya ta windown gidanmu in hango ka, ka ga na yi kwalli kenan" Malam Nura wata wahalalliyar ajiyar zuciya ya sauke, jin wata lukutar masifar. Bai gama tunani ba da ya ji ta sake cewa "Dan Allah idan kun zo wucewa ka ɗago min hannu" Cike da ƙoƙarin danne damuwarsa ya amsa mata, amma a ransa yana raya cewa ba zai taɓa yin abin da ta ce ɗin ba saboda kar ta je ta ganshi komai ya caɓe. Yana shirin datse kiran ta ce "Ni yau duk kishin ka ma nake ba na so ake gani min kai, domin ko matanja ba don matanka ba ne da basu fara gane min kwalliyar ɗaurin aurena da kai ba" Dariya ya yi amma a zahiri ta ji sautin a baɗini kuwa dariyar yaƙe ce ya ce "Daman na yaga buhu na rufa a kaina yadda babu kowacce mace za ta gane miki ni, ko wajen ɗaurin auren sai na je da buhun rufe a kina" Dariya take sosai ta katse wayar bayan ta faɗa masa tana jiran wulgawarsa. Tana katse wayar ya kalli Hudu bayan ya sanya hannu ya goge gumi, ya ciro hularsa ya shiga fifitawa a kansa da shi ma tuni ya jiƙe da gumin yana ƙasa da murya ya ce "Hudu ina cikin talatainin masifa, Kuluwa ta cuceni, yanzu ga Hadiza can a windon gidansu in za mu wuce in ɗago mata hannu ta ga kwalliyata" Hudu ya bushe da dariya ganin gabaɗaya jama,ar fa suka taho tare kowa sabgar gabansa yake ya ce "To mene ne abin tashin hankalin sai ka ɗaga mata hannun ai" Harara ya aikawa Hudu bai sake cewa komai ba, har suka kusa shiga layin gidan su Hadiza gaban Malam Nura yana dakan lugude. Tun da aka shiga layin ya kutsa tsakiyar mutanen da suke tafiya, ya dunƙufar da kansa yake kallon ƙasa, Hudu ne yake faɗa masa cewar ya hango ta tana leƙowa daga windown, suna zuwa Malam Nura ya nannaɗe hannun rigar jikinsa sai da ya kai wajen kafaɗa yadda ba za a hango kalar yadin jikinsa ba, yana ɗan sunkuyawa kamar mai ƙusumbi ya shiga ɗaga hannu saitin ƙofar gidan nasu, don shi dai kawai ɗaga hannu yake yana bye-bye yi yake babu ƙaƙƙautawa. Hadiza wacce ta kira ƙawayenta guda biyu take shirga musu ƙaryar kuɗin shaddar da Malam Nura ya ɗinka musu ita da shi da yaranta, don dai da ta linka kuɗin ta faɗa musu, su kuma suka yarda suna fasa mata kai a kan cewar lallai ta tsinci dami a kala tun da dai gashi har ƴaƴanta ya yi ws kayan fitar biki ba su san cewar dai da aka kai ruwa rana ba ya ɗinka. Tsaye suke sun zubawa hanyar ido har dai suka fara jiyo tashin kiɗa, Hadiza ta ji kanta ya fashe, ƙawayenta suka ci gaba da wasa ta, musamman da suka ga mutane sun shawo kwanar sai kiɗa ake ana wasa ango, kowa ya gyara tsayuwa don ganin angon Hadiza don ta ce musu ya fi tsohon mijinta komai, gashi da kuɗi kuma ba ya jin ciwon fitar da kuɗi, hakan ya sa suka sake ganin girmanta. Tun da suka hango mazan suka zuba na mujiya, kasancewar ma su mazan da suka taho tawagar angon daga can tsallaken hanyar suke ba daga saitin inda gidan su Hadizar yake ba, wato daga tsallen dama suke tafiya, gidan su Hadiza daga ɓangaren hagun. Ɗaya daga cikinsu har ɗaɗɗage take tana son hango angon, Hadiza tana hararta tana cewa za ta gane mata ango. Amma maimakon ango ya fito fili a ganshi tamkar wata ɗan daren goma sha huɗu, sai ya ɓace a cikin mutane tamkar kifin da ya nutse a ruwa, hannunsa kawai ake hangowa, a haka yake tafiya a dudduƙe tsoronsa ɗaya ma kar ya yi tuntuɓe ya je ya faɗi a shiga uku don idan ya faɗi ya san dole Hadiza ta ganshi don daga ya faɗi za a fara cewa ango ya faɗi dole a ganshi kuwa. Hudu ztsabar dariya har da hawaye, mutane kuwa babu wanda ya lura da abin da yake faruwa. Ƙawayen Hadiza ne suka ce "Kin ce mu zo mu ga ango zai ɗago hannu, amma mu babu wani ango da muka gani bare mu ga kwalliyarsa, kawai iya wancan hannun da ake ɗago daga cikin jama,a tamkar shamuwa tana ɗaga fiffike shi kaɗai muke gani" Ɗayar ta ce "Ni hannun ma kamar wanda ya ji uwar wuya, duk kawai kamar dai ana rauda hannun ne ba wai ana ɗagoshi ba" Ɗayar ta ce "Ni fa yadda ta ce ya saka shadda irin tata kawai zatona zan hango haɗaɗɗan hannu ake hango shadda a jikin hannun, amma wannan babu abin da ake gani na shaddar fa, kawai sangalalin hannun ne ake gani tamkar wanda singileti ce sanye a jikin mai ɗago hannnun babu kaya" Ran Hadiza ne ya ɓaci da tsiyar da suke mata ta fara tunanin ko dai sun ɗauka ma ƙarya take bai ɗinka musu tare da ganin hakan ya sa a zuciye ta ce "Wallahi duk cikin ku kun san na fi ƙarfin in muku ƙarya, idan har ba shi ya saya mana ba babu dalilin da zan sa in ce shi ya saya, kuma har shi ya siyo ya ɗinka, amma tun da har kuka musa bari na kira shi ya fito gefe guda daga cikin ayar mutanen, ku hango shi" Ta faɗa tana doka masa waya. Malam Nura da ya kusa tsallake rijiya da baya wato gani yake an kusa wuce saitin gidan su Hadiza ya huta da wannan jarabar ta ɗaga hannu, ya san dai idan an je an ɗaura aure in ta ganshi kowacce jaraba za ta yi sai dai ta yi tun da an ɗaura. Amma me yana cikin wannan halin wayarsa ta fara neman ɗauki, saboda tsoron abin da zia biyo baya ƙin ɗagawa ya yi da ya ga sunan Hadiza hannunsa ne kawai yake karkarwa domin hatta hularsa da ya cire yakw riƙe da ita a ɗaya hannun neman suɓucewa take amma har lokacin bai daina ɗaga hannun ba. Hudu ne ya kalle shi ya ce "Dan Allah ka daina ɗaga hannun nan, kamar wani mai ɗaga tutar nigeri,a" Malam Nura ya ce "Wallahi wanda yake ɗaga tutar ma ya fini ƴanci nidai wanna aure na Hadiza ya wahalar da ni" Hudu ko tausaya masa bai yi ba ya shiga masa dariya don shi kaɗai ya san waye abokinsa da irin tsiyar da ya shuka, ya san yanzu kawai abin da ya shuka ne bai ma fara girba ba. Ran Hadiza ne ya ɓaci ganin ɗaga daga cikin ƙawayen nata ta yi tsaki ta ce "Ƙaryar banza" Tana faɗar hakan ta tafi, ɗagar ta tsaya tana mata dariya, Hadiza tana kallon aminiyar tata ta ce "Kema Bintu baki yarda da ni ba?" Bintu tana dariya ta ce. "Ina fa zan yarda sai na ganshi ido da ido, wannan mazan na yanzu masu shegen son kuɗin tsiya har zai tsaya kashe miki kuɗi a kayan fitar biki ke da shi da ƴaƴan da ba ma nashi ba, bayan kuɗin da kika ce ya baki" Ƙwafa Hadiza ta yi ta bar wajen cike da haushin Malam Nura da bai ɗauki waya ba, tana saƙawa a ranta cewar zai zo ya same ta. Sai da ya ga sun gota wajen yadda ba za a iya gane shi ba tun da sun ɗan yi nisa ya ɗago yana sauke nannauyar ajiyar zuciya ya ce ."Haba ina dalili gabaɗaya wuyana ya ƙage a sunkuyon nan, hannuna ma da nake ɗagawa haka" Ya faɗa yana mayar da hularsa ya ɗora a kansa ya danna ta sai kuwa ya zama kamar wani maroƙi!. A haka suka ƙarasa wajen da aka tanada don ɗaura auren, Malam Nura yana ta sauke ajiyar zuciya, ana ta kaɗe-kaɗe har dai aka saurara aka yi abin da aka taru dominsa, wato aka ƙulla aure tsakanin Hadiza da Malam Nura!. Maroƙa suna ta cewa ...."Aure ya ɗauru, Allah bada zaman lafiya" Malam Nura ya ce "Hudu babu pure water a nan wajen ne?" Ya faɗa yana waige-waige. Hudu ya ce "Mai za ka yi da pure water?" Malam ya ce "A ƙasa zan zuba in tsotse, wallahi ƙirjina tun da na fito daga gida kamar ana bubbuga kalangu, har sai yanzu da auren nan ya ɗauru duk da har yanzu ina jin tamkar mafarki ne" Tsaki Hudu ya yi ya shiga gaisawa da jama,ar da suke musu Allah sanya alkairi, bakin Malam Nura har kunne yana ta washe bakin murna. Ana ta raba alewa da goro, sai hotuna ake ɗauka tsakanin abokan ango da ango, Malam Nura duk lokacin da aka ƙyalla hoton sai yake tuno haɗuwarsa da Hadiza maganar hoton nan amma idan ya tuna cewa an ɗaura auren sai ya ji da dama-dama wai kibiya a ido!. Wani saurayi da yake maƙotan su Hadiza wanda ya ji Hadiza tana faɗawa mai hoton da ta kirawo cewar zai musu hoto na kata,i, wanda zai ɗauki hankali a wanko musu na bango za ta liƙa a ɗaki, shi ma angon hakan, har rana cewa ita da shi tamkar an biyun sarari suke kayan nasu iri ɗaya ne, ana ta fasa mata kai, ganin Malam Nura da wani shegen yadi wanda yake tsohon yayi ne an jima da gama yayinsa, ga wata uwar hula da ya kifa sai wani uban maiƙon mai yake ga wani gumi yana kwaranyo masa, da sauri ya saita wayarsa ya ƙyalla hoto guda biyu, wato ya ɗauki Malam Nura gabaɗaya biyun kuwa yana dariya haƙoran nan a waje tamkar an bashi kyautar kujerar makka, duk da shi a wajensa Hadiza babbar kyauta ce . Yana gama hoton ya saka wayar a aljihunsa ya hau mashin ɗinsa ya bar wajen taron ya nufi gidan su Hadiza. Yana zuwa ya faka mashin ɗina a waje har neman tuntuɓe yake saboda tsabar gulma. Yana shiga da ƙaran guɗar mata kunnuwansa suka fara cin karo, ana ta murnar an ɗaura aure. Kiran Hadiza ya yi gefe tana ta washe baki tana wani farfari da iyayi tana zuwa ya ce "Wai Hadiza ba Malam Nura ne kika aura ba, mijin Haule da Kuluwa?" Harara ta dalla masa ta ɓata rai ta ce "Ba na son gulma da rainin wayo, ni ina ruwana da matansa da zan ɓatawa kaina lokacin wajen sanin sunansa, na san dai Malam Nura sunansa, kuma mijin Hadiza don ni yanzu kaina kawai na sani, ba ruwana da kowacce shegiya ta yi ta kanta su shiryawa zuwana gidan!" Yana mata hararar wasa ya ce "Bakya cin ribar zance, ni fa kawai so nake na tabbatar don ni dai na ga shi ake ta tayawa murna a wajen ɗaurin auren, kuma na san shi kika ce za ki aura" Tana zare ido ta ce. ",To uban mai kake son sani, eyeh masu zuwa lahira da ƙoƙon masaki, ku fa ko kashi mutum yake idan ya ganku ya tashi" Ganin tana neman ja masa lokaci ya ciro wayarsa daga aljihu ya kamo hoton Malam Nura ya miƙa mata wayar, tana karɓa ta sauke idanunta a kan Malam Nura da ya hangame baki yana dariya, hular nan tasa da ta masa wani iri tamkar tashi da ƙwawa ta mayar da shi kamar wani tsoho, yadin jikinsa ta kalla gaba ɗaya a ɗaya hoton ma mazan da aka ɗauke su tare ne suka cinye hoton shi yadda idanunta suka nuna mata ma duk a firgice yake, can ta sauke idanunta a inda ya tattare hannunsa lokacin da zai ɗaga mata hannu, kasancewar a firgice take da ya gyara hannun ma bai gama gyaruwa ba ya bar shi a hakan, shi kuma Hudu bai lura ba bare ya sanar da shi. Wani uban ashar ta ɗura ta ce "Sallamanu kuma an ɗaura auren? Ka tabbatar an ɗaura mana auren da shi????" *A page 10 zan gama free pages, wanda yake so zai iya saya mu ƙarasa har ƙarshe, wanda bashi da ra,ayi babu dole kar ma ki zo ki min ƙananun maganganu ba ɗauka zan yi ba a toh* MAMAN AFRAH 09025576222 [4/13, 6:37 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/DDmSp3AUB7gJnJQLnau59V?mode=gi_t *UWAR AGOLA* 🅿️8️⃣ KINA BUKATAR INGANTATTUN SKIN CARE PRODUCTS TO KIZO SH SKIN COLLECTION DOMIN TA SHIRYA TSAF DAN MAGANCE MK MATSALAR FATARKI YAR UWA KURAJENE DAKE A A GLASS NE Y BATA MK FUSKA KIKA RASA YADDA ZAKIYI KO KUMA DAI TABO NE YAYI MK DANBARE DANBARE A FUSKA TO ZO NA BAKI SIRRIN MATSALARKI WANI ABUN SHA AWA MA ITA FA SH SKIN COLLECTION BATA DAUKAR MAI TA BAKI KAI TSAYE BA TARE D TAGA KALAR FATARKI BA SBD SANIN MAKAMAR AIKI ZAKU IYA TUNTUBAR CEO SH :08029156203 what up only 👆🏻 *UWAR AGOLA* NA MAMAN AFRAH *Daga marubuciyar* *Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.* 09025576222 🅿️8️⃣ Salmanu yana kallon ta ya ce "Ƙwarai kuwa an ɗaura aure" Tamkar ta rusa ihu haka ta ji, a take zuciyarta ta shiga mata zafi tana tuna irin kyau da iya gayu na tsohon mijin ta, duk da dai shi ma Malam Nura yana gayun idan zai zo zance, amma dai bai kyautu a ce yau ranar farinciki, ranar da dangi da abokai da ƙawaye za su yi tozali da shi a matsayin mijinta a ce ya saka wannan yadin tsoho hakan kamar rainin wayo ne. Tunani ta fara a ranta shin ina kayan da yake sakowa masu kyau idan zai zo hira? Mai ya sa duk bai saka su ba sai wannan tsohom yadin? Wata zuciyar ta shiga faɗa mata cewar ya yi hakan ne don ya tozata ta, in ba haka ba ya za a yi ya mata haka, cike da takaici ta ce "Salmanu mutumin nan fa cewa ya yi ya mini kwalliya ta ban mamaki, cewa ya yi ya yi matuƙar yin kyau, haka na shiga faɗawa ƙawaye in ta zuzuta shi, daga an ce in zo a yi hoto sai na hau faɗa musu cewar sai ya zo saboda mu yi hoton tare domin shaddar mu iri ɗaya ce, kenan yanzu ya mayar da ni maƙaryaciya a idon duniya ko mai yake nufi, yanzu kamar ni Hadiza gayu a ce mijin da zan aura ya je wajen ɗaurin aure da wannan matsiyacin yadin? Kamar ni a ce angona ya je wajen ɗaurin aure duk a firgice kamar wanda ƴan bindiga suka biyo ya tsere" Salmanu ya taɓe baki ya ce "Ai ko ni na yi mamaki, shi ya sa ban yi ƙasa a gwiwa ba na ce bari na ɗakko miki hotonsa ki ganshi muraran, wani dagaje-dagaje da shi wuyan riga duk gumi, ji wani hannun riga a tattare wallahi ko nutsuwa bashi da ita" Hadiza ji ta yi kamar ta rusa inu, a take ta fara saƙa da warwarar cewar wannan dalilin ne ya sa da ta ce tana window tana jiran wucewarsa ta ganshi, shi ya sa ya ɓoye kansa. Cike da baƙinciki ta ce "Ashe shi ya sa da za su wuce ban ganshi ba sai hannunsa da yake ɗagowa yana reto kamar kututturen icce, ni dai wallahi Malam Nura ya cuceni kuma a yau ba sai gobe ba zai warware auren da aka ɗaura" Baki Salmanu ya kama ya ce "To ke kuma haka ake, wannan ai sai ki sa mutane su ce na kashe miki aure, kawai na annabawa za ki ɗauka" Idanunta ne suka kaɗa suka yi jawur tana fata da addu,ar Allah dai ya sa wannan batun a mafarki ne, wayar ta sake ƙurawa ido tana kallon hoton sosai, zooming ɗinsa ta shiga yi tana jin kamar ta shaƙo Malam Nura daga wayar ta masa rashin arziƙi zuwan Bintu ƙawarta wajen ne ya dakatar da ita daga abin da take, ta yi saurin wayincewa tana miƙawa Salmanu wayarsa haɗe da sakin dariyar yaƙe ta ce "To shikenan Salmanu na gode ga wayar taka" Karɓa ya yi ya juya, Bintu ta ce "Ango da abokan nasa basu ƙaraso ba ne?" Wani farrr ta yi da ido don ta kawar da ƴar sauran ƙwallar takaicin da ta taru a cikin idanunta ta ce "Eh basu ƙaraso ba" Ta faɗa a fili a zuciyarta kuma ta ce 'Aikin banza shafa lalle a mazaunai, ai idan kin ga ango a wajen nan to sai dai in gawarsa ce za a kawo, domin ba karen mahaukata ne ya cije ni ba da zan bari ya zo wajen nan da wannan koɗaɗɗan yadin, haka kawai ya kunyata ni, a ɗaukeni maƙaryaciya' Gaba ta yi Bintu ta take mata baya, tana zuwa ta shiga ɗakin da take, waya ta shiga dokawa Malam Nura domin ta kora masa kashedin kar ya kuskura ya zo musu gida, sannan ta ƙara da faɗin ya kawo mata takardar sakin ta. Tana jin wayar tana shiga amma har ta tsinke ba a ɗaga ba, babu ƙaƙƙautawa ta ci gaba da kiran amma shiru kake ji wai malam ya ci shirwa domin ba a ɗaga ba. A ɓangaren Malam kuwa ana tsaka da ɗaukan wannan hoto wanda ya yi wa laƙabi da hoton masifa, ya ji wayarsa tana ƙara, yana dubawa ya ga sunan Hadiza ya shiga faɗawa Hudua bayan sun ware gefe guda Hudu ya ce "Malam Nura ka daina tsoron matar nan fa, kawai ka ɗaga wayar, daga nan mu wuce gidan nasu kamar yadda ta buƙata" Malam Nura ya ɗan zaro ido ya ce "Ai ba na so ta kunyata ni a cikin mutane fa, ka san dai mun yj maganar shadda na saka, to ya zan yi tunda wannan mai kunnen ƙashin ta ƙona shaddar, ko dai kana ganin in faɗawa Hadiza cewar Kuluwa ta ƙona wandon?" Hudu ya zaro ido ya ce "To wallahi idan ka kuskura ka faɗa mata ka sani yaƙin duniya ne na uku za a yi a gidanka, don gabaɗaya sai an ƙone gidan" Malam Nura ya ce "Mai ya sa ka ce haka?" Hudu ya ce "Kana ganin Hadiza za ta bar maganar nan ne, kana faɗa mata za ta tada zaune tsaye, ita ma Kuluwa ba ƙyaleta za ta yi ba, su je su ringa bala,i, gwara kake saran shuka kana kallin gatari!. Idan baka takatsantsan kishin Kuluwa da Hadiza mai zafi ne, a wannan kishin sai ka gwammace kiɗa da karatu" Shiru Malam Nura ya yi ya ce "Ka rabu da su kowacce ka san daidai da zamanin ta nake ita ma Hadiza dama ce na ara mata, sai ta shiga gidan zan nuna mata asalin waye malam waye Malam Nura don duk wannan iyayi da juyannin da take kamar waina a tanda ba ɗorewa zai yi ba, idan har na wawuri abin da zan wawura na daga dukiyarta to da wasu daga cikin kuɗin zan yi amfani in gallo wani sabon auren!" Hudu yana kallonsa yana jijjiga kai ya ce "Ka ƙaddara gidanka ya kama da wuta kenan, don ni yanzu haka ina hararo irin zaman da za a yi tsakanin Hadixa da Kuluwa" Tsaki ya ja ya ce "Rabu da su daidai da su nake, kowacce ta yi tsarara kamar shayi!" Ayarin jama,a suka biyo makaɗa suna aikin su na kaɗe kaɗe, ango sai wani jin kansa yake, yana tunano irin garar da zai kwasa idan an kai amarya ta tare, don yanzu yana tunano cewar la,asar sakaliya tana yi zai aarasa haɗe sauran magungunan da Hudu ya siyo masa a Kano ya shanye don ba zai tsaya kallon ruwa kwaɗo ya masa ƙafa ba!. Dole ya sha amarci don yana rayawa a ransa cewar Hadiza sai ta yi wata guda currr tana amarci kuma ita kaɗai ce za take zuwa turaka amma su Kuluwa sai dai suke tuƙa tuwo babu mai zuwa ɗakin miji, ya saka hakan a ransa sai dai a yi wacce za a yi duk nacin Kuluwa kuwa dole ta haƙura su barwa amarya Hadiza turaka daman ya san ita Haule baiwar Allah ba za ta ƙi amincewa ba, Kuluwa ce uwar ƴan taurin kai. Ana tafiya Hudu yana danne dariyarsa idan ya kalli Malam Nura ya san ƙarfin hali ne domin duk da yana cika baki amma ya lura yana tsoron Hadiza ta ce ba za ta yi hoto da shi ba. Gabaɗaya mutane kowa ya kama gabansa, daga Hudu da Malam Nura sai wasu abokansu guda huɗu ne suka nufi gidan su Hadiza, don masu kiɗan ma Hudu ya ce su je can gidan Malam Nura su jira su. Suna tsaye a ƙofar gidan abokansu suna ta zolayarsa, sai yaƙe yake musu don hankalinsa ba a kan su yake ba, yana fatan ya tsallake rijiya da baya. Wayar Hadiza ya shiga kira, Hadiza kuma ganin kiransa da sauri ta tashi daga cikin mutane don daman mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, damab kar jira take saboda ta yi ta kira bai ɗaga ba, yanzu kuma faɗuwa ta yj daidai da zama tun da gashi ya kira da kansa, har sauri take don ta shiga ɗaki ta kora masa kashedin kar ma ya dosk gidansu idan aka ɗaura auren nan, domin ta fasa hoton sannan ta ƙara faɗa masa cewar ya aiko da takardar saki ta fasa auren. Tana dab da shiga ɗakin Babanta wanda shigowarsa kenan sun dawo daga wajen ɗaurin auren ya hango ta ya ce "Ke Hadiza!" Da sauri ta juyo ta ce "Na,am Baba" Yana kallon ta ya ce "Malam Nura ba ke suke tsaye a waje suna jira ba, shi ne kika bar su a tsaye" Ranta ba don ya so ba ta ce "Yanzu zan fita daman" Ɗakin ta fasa shiga ta juyo ganin Baban ya ja ya tsaya, Bintu ma ta tashi, sauran ƙawayen ma duk suka fara miƙewa suna faɗin "Ah lallai ashe ango ya samu ƙarasowa bari mu je" Hadiza kamar ta yi inu haka ta ji, amma babu yadda za ta yi, haka ta biyo bayansu suka fito. Baban ma juyowa ya yi yana faɗin "Zainaba ɗakko mun kujera zan fita waje saboda masu zuwa, wanda suka rasa ɗaurin aure" Zainaba wacce take sanye da shaddar ta ta taso ta ɗakko kujerar ta biyo bayansa. A can ƙofar gida kuwa Malam Nura ya fara zargin ko dai wani ya ƙyanƙyasawa Hadiza cewar bai saka kaya ba, gani yana kiranta bata ɗauka va, wata zuciyar kuma tana faɗa masa ko dai kiran da ta yi ta masa ne bai ɗauka ba ya sa ta ƙi ɗauka. Kamar daga sama ya hango ta sun fito ita da ƙawayen ta, gabaɗaya tsabar kyan da ta yi ya sa kwata -kwata ya sha,afa da kayan jikinsa, kwalliya da ɗaurin ɗankwalin Hadiza sun tafi da hankali da tunaninsa, bai ma lura da yadda ƙawayenta suke rarraba idanun neman ango mai sanye da shadda kalar ta ƙawarsu amarya ba. Hadiza kuka ne kawai bata saki ba, gashi babu halin ta masa wani rashin mutunci tun da ga Baban ta can a waje a wajen inuwa shi da mutane, bata ma san haka yadin jikin nasa yake ba sai da ta gani ido da ido ta gane cewar ashe dai wayar da ta ganshi a hoto a wayar Salmanu hoto ya gyara yadin. Hudu kuma Malam Nura kawai yake bi da kallo ganin gabaɗaya ya raja,a da kallon amarya ya manta da laifin da ya mata. Malam Nura wani ɗan ƙaramin tari ne ya suɓuce masa, a take ya yi gyaran murya ya ce "Amarsu ta ango, aure ya ɗauru, mun zama tsintsiya maɗauri ɗaya, na zama naki kin zama tawa buri ya cika" Wannan kalaman da ya yi su ne suka ankarar da ƙawayen nata cewar angon nata ne wannan!. Hadiza rasa ma bakin magana ta yi ta ce "Uhm an ɗaura" Ya washe baki tamkar mai tallar makilin ya ce "Yau sai kwanan gidan Malam Nura" Kafin ta bashi amsa mai hoton da ta tsayar ya ƙaraso wajen domin daman yana cin abinci ne, kuma da ya ji Babanta ya ce ango da abokansa sun zo shi ne ya ƙarasa ci ya taso. Yana fitowa daga gidan camerarsa a hannunsa, Malam gani mai hoto ya ce "To ai sai mu fara abin da ya kawo mu" Ya faɗa yana jin wani daɗi, haɗe da saka hannunsa ya gyara zaman hularsa da ta ƙara kifuwa a kan tamkar ya saka hula dara. Irin hular nan da ba a mata kari. Abokai haka suka shiga yi wa Hadiza Allah sanya alkairi, tana amsawa kamar an mata dole!.Ƙawayen ta kuwa kowacce ta shiga danne dariyarta ganin abin da yake faruwa, sai dai ta yi alƙawarin abin da ango ya mata ba zai tashi a banza ba sai ta rama. Umarnin mai hoto suka bi wajen layuwa aka shiga yin hotuna, sai dai tun da aka yi na jam,i sai mai hoto ya ce saura amarya da ango. Amarya daman bata tsaya a kusa da ango ba da aka yi wancan hotunan, kusa da Hudu ta tsaya, duk abin da take ango yana lura da ita kuma hakan ya ɓata masa rai, da Hudu ya ga amarya ta ƙi tsayawa a kusa da ango sai ya fita daga hoto ya koma gefe . Hadiza ta kalli inda su Baba suke ta ga hankakinsa ba ya wajen, ta ɗagawa mai hoto da yake kai camera idanunsa zai walla musu hoton ta ɗaga masa hannu ta ce "Dakata!" Daga mai hoto har malam da idanu suka bi ta, ta mayar da kallon ta kan Malam ta ce "Nura! Gaban Malam Nura ne ya faɗi amma ya yi kokarin dakewa ya zuba mata idanu ba tare da ya amsa ba, tana zaro idanu tare da kama ƙugu da hannu ɗaya tana wani karkaɗa jiki na rashin arziƙi ta ce "Nura ni ka sincewa zani a kasuwa ko? Ni ka sakawa wannan yadi ka je wajen ɗaurin aurena! Bayan ka ɗinka shadda saboda ban isa ba, kuma matsayina bai kai a saka babbar shadda a je ɗaurin aurena ba shi ne ka saka wannan yadin mai kama da likkafani don ka zubar mini da mutunci, ka sa na yi wa ƙawayena ƙarya, ashe wannan dalilin ne ya sa kake ta ɗago hannu kamar katako a wajen kafinta, to ina so ka sani darajar babana ka ci na fito don haka yanzu ba sai an jima ba ka bani takardata" Kamar mai raɗa haka take faɗar maganar, abokai da kawaye basu san mai take faɗa ba kuma ta yi hakan ne don kar hankalin su Babanta ya dawo kansu, amma da sai kowa ya ji abin da za ta masa. Yana kallon ta ya ce "Hadiza aure ya ɗauro, kuma ki sani tamkar auren zobe ne babu saki!." Kafin ta furta wani abu Babanta ya juyo inda yana magana da wasu mutane hakan ya sa ta kama bakinta duk da zugin da zuciyarta take mata. Malam Nura ya sake gyara zaman hularsa ya matsa kusa da ita ya ce mai hoto ya ɗauke su, ai kuwa da sauri ta matsa ta ce sai dai a masa shi kaɗai, mai hoto ya masa, Malam Nura ya waiwaya wajen Baba ya ga hankalinsu ba ya waje yanzu, da sauri ya matsa kusa da ita ya kamo hannunta tana fisgewa amma a haka aka ɗauke su tare, ƙawayenta da abokansa ganin ya kama hannunta suka shiga musu tsiya yana ɗauka ta fisge da ƙarfi ta kalli mai hoto ta ce ."Idan ka sake ka wanke wannan hoton sai ranka ya ɓaci" Malam Nura ya kalle shi ya ce "Idan ka wanke ka kawo zan biya ka da kuɗi mai tsoka" Hadiza rai ɓace ta matsa kusa da Hudu da bai ma san ta tsaya kusa da shi ba ta ce "Ɗaukemu da abokin ango" Kafin Malam ya juyo sai ganin hasken camera ya yi wal an ɗauki hoton, Hudu ma bai san da shi za a ɗauka ba sai bayan an ɗauka, ta yi haka ne domin ta turawa malam Nura haushi, ai kuwa ya shaƙa domin kawai ransa ne ya ɓaci, ƙololuwar ɓaci daman ya san a rina wai an saci zanen mahaukaciya, wato dai saboda bashi da kaya mai kyau shi ya sa ta yi hoto da Hudu saboda kayansa masu kyau ne. Wani haushin Kuluwa ne ya tokare masa maƙoshi, idan ya tuna cewar duk ita ce silar faruwar komai. Ta kalli Malam Nura ta taɓe baki ta cewa mai hoton ka wanke hotunan duka amma banda wanda ka mana ni da ango!" Tana faɗar hakan ta juya za ta shige cikin gidan, daman ƙawayen ta sun shige, suna son su ware kafin ta shiga gidan su yi gulmar kayan jikin mijin, tana dab da shigewa gidan ya ce "Hadiza ki jira fitowata da yamma sai kin kasa gane ni, ya maganar jere na ga baku kai kayan ba kin san dai yau za ki tare ko?" Yana faɗar hakan ko amsa masa bata yi ba ta ja ƙaramin tsaki ta shige gida, Hudu da sauran abokan suka fara takawa ana ta hira, Zainaba wacce take laɓe a wani waje ta fito, lokacin Malam Nura yana ƙoƙarin barin wajen tana zuwa ta ce "Ango bai sha ƙamshi ba, ango da kaya marar kyau, wallahi babana ya fika iya kwalliya gwara ma Innata ta koma gidansa" Tana faɗar hakan ta zuga da gudu cikin gidan, Malam Nura ya shaƙa, musamman da ya ga Zainaba sanye da shaddar da shi ya saya, amma shi ya ƙare a tsohon kaya. Su Hudu da suke tafiya suna hira ana dariya, fuuuuu suka ga Malam Nura ya zo ya wuce su, suna masa magana bai amsa ba, sai sauri yake kamar ya ci ƙafar kare. Haka suke tafiya yana gabansu suna bin sa a baya amma da tazara a tsakaninsu. Ko sallama bai yi wa su Hudu ba ya shige cikin gidan, makaɗan da suke ta kiɗa a ƙofar gidan ma bai bi ta kansu ba, Hudu ne suna zuwa ya sallame su, suka tafi shi ma gidansa ya wuce don lokacin rana ta yi kuma ya san abokinsa da maƙo babu abin da aka girka na auren. Don su ma abokan tafiya suka yi. Ko sallama bai yi ba ya shiga gidan kamar an koro shi, fuskarsa sam-sam babu fara,a, hayaniyar matan maƙota da suke ta magana ce ta masa dirar mikiya, yana shigowa gidan cike da mata suna cin tuwon masara da miyar ɗanyar kuɓewa sai hira ake yi, daman Haule ce ta yi don saboda da mutane masu shigowa. Ana ta gaishe da shi babu wanda ya kula, domin su ne da suka zo suka dakatar da shi daga ɗaukan mummunan mataki a kan Kuluwa. Kuluwa ya gani zaune a ƙofar ɗaki ita da su Mariya sun saka tiren funkaso da taushen da suka kawo mata, sai ci suka suna hira, daman bayan fitar Malam ta yi wanka ta saka kaya ta cokara ɗaurin ture ka ga tsiya, don yanzu ransa ya mata ɗan sanyi saboda ta ƙona shaddar ɗaurin aure. Yana shigowa kallo ɗaya ta masa dariya ta taho mata, hannu ta sanya ta toshe bakinta da yake cike da funkason da ta saka, fuuuuu ya zo ya wuce hula a hannu, don har lokacin yana hango kallon tsanar da Hadiza take masa a matsayinsa na sabon mijinta angon ta. Yana dab da shiga ɗaki, Haule wacce ta fito daga ɗakin ta ta hango shi ta kwashi guɗa, amma tsabar takaici ko waiwayowa bai yi ba, yana jin matan suna cewa ango ango amma babu wanda ya amsawa yanzu hankalinsa yana kan yadda zai birge Hadiza ya kankarowa kansa guntun mutunci a wajenta da kawayenta ma da ya ga suna masa kallon ɗaya saura kwata. Yana shiga ɗakinsa da wandon shaddar nan da Kuluwa ta ƙona ya yi tozali, ransa ya ƙara ɓaci yana tuno ranar da ya karɓo a wajan ɗinki amma yanzu ya zama gajere, gajeran ma iya cinya. Hular ya cillar a kan katifarsa. Yana rayawa a ransa cewar yau komin dare sai Kuluwa ta girbe shukar da ta yi domin ba za ta ci bulus ba. Rigar shaddar ya ɗauka, ya saka a leda, ya ɗauki gajeran wandon ya saka a ledar, wani tsohon wandonsa ya ɗauka na yadi ya saka a ciki, ya ɗakko kuɗi ya fito, fuuuuuuu yana tafiya kamar zai ci da ka, yana dab da shiga zauren Kuluwa da muryar dariya ta ce "Ango ka sha ƙamshi" Ta faɗa cike da sheƙiyanci, domin a tunanin ta fasa auren ma aka yi tun da ta ga sai muzurai yake yi. Tun da ya fito yake sauri, burinsa ɗaya ya ganshi a shagon ɗinki, yana zuwa ya samu mai ɗinki ya ce "Ibra wajenka na zo" Ibra da yake saka maɓalli a wata riga ya ce "Ango ango, ango ka sha ƙamshi, a mini afuwa ban samu zuwa ɗaurin aure ba, ina ta ɗinkin muta... Malam Nura ne ya katse shi da faɗin "Aure dai an ɗaura!" Sai ka bari ma haɗu a wani ɗaurin auren" Dariya sosai Ibra ya saki ya ce "Haka ne fa mutumina, kai ai baka wata uku cikakke ba ka yi sabon aure ba!" Malam Nura bai bashi amsa ba, domin yanzu hankalinsa ya karkata ga yadda za a yi masa wandon nan ya saka kayan da yamma ya je wajen Hadiza ko ta huce ya lura in bai yi kyan nan da take naci ba, wataƙila a samu matsala, shi ya ga ko tsinke ba a kawo gidan ba, kuma ya gama sakawa a ransa yau amarya za ta tare amma kuma ya ga babu niyya wai ango ya kwana da wando. Cike da jimantawa ya fito da kayan daga leda yana faɗin "Ka ga dai ɗinkin da ka mini, duba ka ga yadda Kuluwa ta mayar da wandon nan, don abin kunya da mazaunai suka mutu suka bar zani wai da wannan yadin na je ɗaurin aure!" Salati Ibra ya ɗauka yana riƙe da haɓa cike da zuga ya ce "Wannan shaddar mai tsada da kyau, shaddar da shugaban ƙasa yake saka irin ta, amma saboda kishin banza ta ƙona, amma dai ka hukunta ta ko?" Baki Malam ya dantse yana cewa "Barni da ita, wallahi ƙafafu na so datse mata kawai dai lokacin cirewar ƙafafun ne bai yi ba amma dai na san zan cire mata ƙafafu ta koma tuƙa keken guragu" Ya faɗa yana cika yana batsewa. Ibra ya ce "Yanzu ya za a yi da wannan?" Malam Nura ya ce "Faci za ka yi" Da mamaki yake kallonsa ya ce "Haba Malam Nura wane irin faci kuma, ai wannan ka haƙura da shi kawai, amma faci sai ka ce wata tayar keke" Malam Nura kamar zai kai masa duka ya ce "Ibra idan ba za ka yi ba ka faɗa mini na kai wani shagon, an ce maka sai keke ake yi wa faci" Ibra ya ce . "Ina jinka yi min bayani" , Malam Nura ya ce "Wannan wandon yadin nawa za ka datse shi daga gwiwa zuwa ƙasa, sai ka yanke ƙasan rigar shaddar ka haɗa ƙyallan da ka ciro a jikin riga, da wandon nan ƙonanne da wannan guntun ƙonannan wandon ka yanka mini ƙafar wandon zuwa gwiwa, idan ka yanka sai ka ɗora a kan wannan wandon yadin da ka yanke, sai ka ɗinka mini, ka ga idan na saka babu wanda zai ga saman tun da rigar ta rufe, iya ƙafafun ne za a hango, so nake in yi wankan kece raini na fita kunya da yamma, yadda zan gigitawa Hadiza tunani, don na ji hatta ƴarta Zainabar wannan da ba sona take ba tana cewa wai babanta ya fini iya wanka da gayu, gwara na nuna musu nima Kuluwa ce ta mini tsiya shi ya sa suka ganni da tsohon kaya!" MAMAN AFRAH 09025576222 [4/15, 3:33 PM] MOM MASHKR & AFRAH: *UWAR AGOLA* NA MAMAN AFRAH *Daga marubuciyar* *Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.* 09025576222 🅿️9️⃣ Tun da Malam Nura ya fara bayanin facin wando Ibra yake ta dariya, har ya gama faɗa masa amma bai tsagaita dariyar ba sai da abin ya ishi Malam Nura ya kalli Ibra cike da takaici ya ce "Dalla Malam ba kyauta za ka yi ba kuɗinka zan cake na baka" Dariyar ta tsagaita ya ce "Zan yi maka mana ai ka san ni da kai bata ɓaci, kawai dai lamarin ne ya bani dariya, yanzu duk kuɗinka abin ka sake ɗinka sabuwa ka zauna kana ta wannan lissafin, ka yarda mace ta maka aika-aika har burinta yake neman cika" Malam ya ce "Burin Kuluwa in tozarta ni kuma ba zan tozarta ba kuma sai na yi bikin nan yadda ba ta so, kai dai ka yi ƙoƙarin fito mini da shaddar nan kawai" Amsa masa ya yi ya ajiye aikin da yake ya shiga yi masa nasan kamar yadda ya buƙata. Malam yana zaune a gefe aka yanki ƙasan rigarsa aka yi ƙasan wandon aka yanke ƙasan wandon yadin aka jona na shaddar. Bakin Malam Nura har kunne ganin kwalliya ta biya kuɗin sabulu yana kallon Ibra cike da girmamawa ya ce "Ba gashi ba, ai wallahi da na san za a iya yin wannan dabarar da ko wajen ɗaurin auren ba zan je a haka ba" Ya faɗa yana karɓar wandon ya kara a jikinsa ganin ya masa yadda yake so ya biya Ibra kuɗin gyara har da ƙari. Ibra yana ta tsokanarsa ya ɗauki ledarsa ya nufi gida, lokacin gar an fara kiran sallar la,asar, Hadiza kuwa ya kira ta ya fi sau goma amma bata ɗauka ba, da ya gaji sai ya ƙyale ta. Babu abin da ya saka a cikinsa wuni guda, haka ya wuni a shagon ana masa gyaran sai da ya ga ya kammala sallah ce kawai take fito da shi daga shagon, ko da suka haɗu da Hudu a masallaci ma ya sanar da shi cewa yana can ana masa ƴan dabaru dariya ya masa saboda ya san kawai wandon nan ba zai saku ba. Lokacin da ya shigo gidan, matan nan duk sun watse sai kaɗan, bai ga Kuluwa ba, shi ma bai nemi inda take ba saboda daman ba nemanta yake ba, a cewarsa tauraruwa mai wutsiyaci ganin ta ma ba alkairi ba ne. Ɗakinsa ya nufa ya rufo ƙofar cike da hanzari ya cire kayan jikinsa ya saka wandon ya ɗora rigar ya kalli jikinsa ya fashe da dariya a fili ya furta "Hadiza daman rashin wando ne ya mini cikas yanzu za ki tabbatar da cewa wanka iya wanka Malam Nura ya iya" Ya faɗa yana sake kallon wandon tabbas ba a ganin saman yadin da aka haɗa daga sama, sannan waje da aka yi ɗinke-ɗinken ma ba a gani sai dai wanda ya yi kallon ƙurilla. Kayan ya cire ya linke, ya ɗakko wani kayansa ya saka don bai mayar da yadin Hudun ba saboda haushin yadin ma yake ji. Ya gama kenan, Haule ta zo ta buga ƙofar ya ce "Waye?" Ta ce "Ni ce fa ango na amarya Hadiza" Wani daɗi ne ya baibaye shi jin kiran da ta masa, duk da yana jin haushin yadda Hadiza ta masa a gaban mutane amma kuma da yake bahaushe ya ce, so hana ganin laifi, sai ya fara ganin laifinsa ne ba laifin Hadizar ba. Yana washe baki ya buɗe ƙofar yana faɗin ".Na baki ɗan mutum da uwarsa" Dariya ta saki tana faɗin "Ai ka cancanta ne ango, Allah dai ya sa an ɗaura a sa,a ya bada zaman lafiya" Da amin ya amsa har ya yi shiru ya ce "Haule anya kina sona?" ,Haule ta ce "Mai ya kawo wannan maganar?" , Malam ya ce "To ai ke ɗin ce sai kike ta nuna kamar dai bakya kishina, amma ko kaɗan ne ai kya ɗan gwada min kishi" A fili ta ce "Ai ka san ka so abin da mutum yake so ma yana cikin so" A zuciyarta ta ce 'Ku maza mace ma ta yi kishin ku ta haɗa kanta da wahala, yanzu ba ga Kuluwa nan daga yin kishi kake neman nakasta ta ba, haka kawai ai gwara ma mace kar ta ɗora namiji a ranta hakan zai sa ta zauna lafiya' Malam ya ɗan yi shiru ya ce "Kuma fa haka ne" Haule ta ce "Yawwa, daman na ce ko a kawo maka abinci na ga baka zauna ba ma bare ka saka wani abu a cikin ka, ni kuma duk na damu" Dariya ya yi ya ce a zuciyarsa 'Namiji ɗan gatan mata, wato dai kai idan matarka ɗaya ce shikenan ba kowacce mace ce take bada kulawa ba, amma idan sun haura ɗaya sai abin da ka gani kowacce sonka take' ,A fili ya ce "Barni Haule ai no yau ban ga ta zama ba an saci ɗan ɓarawo, babu batun cin abinci har sai na je na yi hoto da Hadiza kin san ranta ne ya ɓaci da bamu yi hoto tare ba da ta ganni da wannan yadin" Haule ta ce "Ba dole ya ɓaci ba wataƙila ta shiryawa ranar ne" Malam ya ce "Shiri ma ai in kin ji ɗaya kenan, in banda wannan Kuluwar ƴar wahala ta kawo mini cikas har akwai wanda zai kaini wanka" Shiru ta yi bata ce masa komai ba, saboda ba ɗabi,arta ba ne yi da kishiya a bayan idanunta. Sallama ta masa ta ce sai ya fito. Tana fita ya fito ya ga wani bokiti cike da ruwa, lokacin tsakar gidan ma babu kowa sai su Alawiyya suna cin abinci. Yana ɗaukan bokitin ya yo hanyar banɗaki, ya shiga ya rufo, Kuluwa tana kallonsa kuma ruwanta ne amma sanin akwai wata wutae tsakaninsu ya sa bata fito ba, domin ita hankalin ta kwance an yi ɗaurin aure ya je da tsohon kaya, kuma yanzu ma don zai je ya yi wanaka ta san sai dai ya saka wasu kayan aron. Yana shiga ya yi wanka ya fito, ya shiga ɗakinsa ya saka sakata, yana goge jikinsa ya saka singlet, ya ɗakko rigar shaddar nan ransa fari ƙal ya saka ta ya saka wandon da ya zo ɗauree mazugin sai ya ga ƙarami ne Ibra ya saka masa, ɗazu ma da ya gwada saboda a ruɗe yake shi ya sa bai lura ba, wata zuciyar tana faɗa masa ya cire ya saka wani wata tana faɗa masa kawai kar ya ɓatawa kansa lokaci ya bari. Maɓallin ya ɓalle ya ɗakko hularsa ya gyara karin ya goga mata turare ya saka, ya sanya turare a kayansa sosai ƙamshi ya cika ɗakin ya saka takalmansa ya je gaban madubi, ba ƙaramin kyau ya yi ba sosai ya yaba yana fatan Hadiza ta yaba fiye da shi a fili ya ce "Ashe dai ina da fasahar da zan saka shaddar nan a ranar nan amma na zauna na je ɗaurin aure da tsohon kaya" Ya faɗa yana ɗaukan wani tsumma ya sake goge takalmin sa. Ƙaramar ledar da magungunan mazan sa suke ciki ya ɗakko, wanda Hudu ya faɗa masa sai ranar da amarya za tare zai sha, sannan ya ce masa a huɗu zai raba maganin, wata ƙaramar kwalba ce kamar ta magani, a jikinta an sake laulaye ta da leda a cikin ledar kuma wata ƙwayar magani ce guda ɗaya, ita ƙwayar Hudu ya ce masa a biyu zai raba, ita kuma na kwalbar a huɗu. Yana ɗaga kwalbar bayan ya buɗe sai da ya sha ya fi rabi, wanda ya bari bai fi kwata ba, ya ɗauki ƙwayar da aka ce ya raba a biyu ya saka a baki ya tsotse ita ma ya tsotse ta duka, ya mayar da komai cikin ledar ya ɓoye. A fili ya ce "Ba a bori da sanyin jiki, ai tun da dai amarya yau za ta tare ina na ga ta zama, ai gwara na shanye duka, shi ma na kwalbar da na rage saura da daddare kafin a kawo ta zan shanye tasss, don ba zan zauna ta raina ni ba gwara ta san babu raini a lamarin" Ƙofar ya buɗe ya fito yana cikin kullewa Haule ya fito daga ɗaki, wata uwar guɗa ta carara tana faɗin "Kai ma sha Allah, kyau iya kyau ango, wanka iya wanka, na Hadiza jan gwarzo, na Hadiza mai kyan mamaki" Ɗari biyar ya ciro ya miƙa mata ya ce "Ki ba su Alawiyya hamsin-hamsin ki riƙe canjin" Karɓa ta yi tana masa godiya, sannan ta ce "Malam idan an yi sallar magriba zan je gida, baba zan dubo bai ji daɗi ba duk da dai an ce jikinsa da sauƙi amma dai zan dubo shi" Malam ya ce "Subhanallahi, a ki je kya masa sannu kafin in samu in ɓulla" Amsa masa ta yi ya yi gaba abin sa. Kuluwa wacce take ɗakinta jin guɗar da Haule ta yi ya sa gabanta faɗuwa, musamman kirarin da Haulen ta masa ya ƙonawa Kuluwa rai, amma haka ta taso domin ganewa idonta tun da dai bahaushe ya ce baba bori da sanyin jiki, tana leƙowa daga window abin da ya gani ne ya ɗaga mata hankali sa sauri ta dafe ƙirji tana zaro idanunta don su tabbayar mata da abin da ta gani zahiri ne ko kuwa gizo ne. Tabbas shaddar da ya ƙona wandon ta ce sanye a jikin Malam, kuma wandon ne take gani sannan shaddar sak ce a wandon daga gani ba haɗawa aka yi ba wato ba wata kalar shaddar ce aka samu wacce zanen ba ɗaya ba ne. Ranta ne ya ɓaci sai dai bata da damar amayar da abin da yake cikin ta, tun da ta san yanzu ma da sauran rina a kaba tun da ba yafe mata ya yi ba. Malam kuwa fita ya yi hannunsa ɗaya a aljuhu ɗaya yana riƙe da wayarsa da take ta ƙara. Yana fita Kuluwa ta fito tana huci kamar zakanya wani uban ƙamshin turare ne ta jo ya ziyarci hancin ta, ko ma ta ce ya buɗaɗe tsakar gidan, tsayawa ta yi ta kama ƙugu tana wani karkaɗa kai ta taɓe baki ta ce "Oh ni Kuluwa duniya sabuwa Malam Nura sanye da sabuwar shadda mai tsada yana ƙamshi tamkar an yi ɓarin turare" Haule ta yi dariya ta ce "Wallahi kuwa wai wajen amarya Hadiza zai je su yi hoto... Tun bata ƙarasa ba Kuluwa ta tari numfashin ta da faɗin "Ke kam Haule Allah yaye miki, yanzu a gabanki mijinki ya fita ya tafi wajen wata banza, amma har kike wasa shi kina ce masa wani na wata can banza, bayan kin san a cikin gidan gani ga kuma ke, ai ko da me -da me biyu ta fi ɗaya ko a rabon gado!" Haule ta tsura mata ido ta ce ..."To ina ruwana ita ma ta yi ta kanta, kuma ai na ga matarsa ce, to ya ma kike so na yi cakumarsa kike so in yi mu yi dambe saboda zai je wajen matarsa, to wallahi ni ko wajen bazawara zai je ba zan wahalar da kaina ba" Kuluwa ta ce "Ke dai na lura wannan ɗan kuɗin da yake baki ne suke rufe miki ido sho ya sa bakya samun damar nuna kishin naki" Haule ta yi wata ƴar bazawarar dariya ta ce "Ai ko da me da me kurna ta fi magarya zaƙi, inaso ki sani ba wai ba na son Malam ba ne kuma ba wai ba na kishin sa ba ne, a,a kaina dai na shafawa lafiya game da lamarin maza, sannan abu na gaa kin san da neman kuɗi nake kaina da ƙafata ina sana,a to kuɗin na nasho da bai taka kara ya karya ba maganin matsalata zai min? Kin ga kenan kawai dai a bar kaza a gashin ta, ke da kika ɗorawa kanki kishin da mai kika tsira, ba don Allah ya rufa asiri ba da yanzu ƙafafun ki biyu ba sa jikin ki" Tana faɗar haka ta juya ta bar wajen. Ran Kuluwa ya ɓaci jin Haule ta faɗa mata magana, tana yin ƙwafa ta ce "Hummm ba Hadiza ba ko Hadizo ce ta zo ina nan ina jiranta, tun da dole a ci kasuwa da maƙiyi, kuma hangen dala ba shiga birni ne ba, in da Malam Nura ne kaska ne raɓi mai jini ki bar shi da gashi, ai mai kashe miciji sai ya yi niyya zai ɗauji sanda, a yi dai mu gani idan tusa tana hura wuta, mu dai mazaunai ne ko dan zama za a neme mu, mu zuba mu gani, matuƙar ta shigo gidan na ƴar kallo za ta zama, don ni ce da ragamar mijina, an aure min miji maimakon ta koma gidan mijin ta shi ne aka ƙi cin biri aka ci dila" Duk wannan karin magaanar da take Haule tana jin ta bata taka mata ba. Malam Nura yana fita ya amsa kiran Hudu nan ya faɗa masa gasu nan zuwa, haka suka zo da wasu abokan nasa guda biyu suka ɗunguma zuwa gidan su Hadiza suna ta zuzuta irin kyan da ya yi. Malam Nura ya murmusa ya ce "Ni fa daman na faɗa maka Hudu sai na daka shaddar nan, amma dai har yanzu ina kan bakana idan ka samu mai saye ya zo na fansar masa" Hudu ya yi ƙasa da tashi muryar kamar yadda Malam ya yi lokacin da zai faɗa masa ya ce "Waye zai sayi wannan shaddar wando da ɗori ɗori" Shiru ya yi sai kuma ya ce "Ai idan aka samu mai son banza tsaf zai saya yake maleji, tun da nima ai sauƙi zan masa tun da na san wandon haɗi-haɗi ne wato yadi da shadda, wa ya ga haɗin gambiza" Ya ƙarasa faɗa yana dariya. A ɓangaren Hadiza ita kaɗai ta san irin ɓacin ran da ta ƙunsa, ranta ya sosu game da abin da Malam Nura ya mata abin ya fi mata ciwo ma da ya kunyatata a gaban ƙawayen ta bayan ta gama shirga musu ƙarya. Ta san ko ƙaramar hauka za ta yi Malam Nura ba zai sake ta ba amma dai ta ƙudurta a ranta cewar ba za ta tare yau ba ko ana muzuru ana shaho,a ƙalla sai ta shafa satika ba ta tare a gidansa ba sai ta gama bashi wuju-wuju sai ya san ita ya tozarta. Haka ta wuni suƙuƙu ranta a ɓace, don Zainaba ma sai da ta ce mata "Inna wai ya na ga angon bai saka sabon kaya ba, kika ce tare ya siyo mana shaddar, wallahi ko kaɗan bai yi kyau ba kamar dai ba ango ba, sauran abokan nasa duk sun fishi yin kyau, ai daman babana ya fishi iya gayu shi ya sa na ce ki koma amma kika ƙi" Harara ta zabgawa Zainaba kamar idanun ta za su faɗi, da sauri Zainabar ta bar wajen tana ƙunshe dariyar ta. Da yamma kasancewar ta yi gayyata hakan ya sa ta sake sabon ɗauri inda aka mata kwalliya da ɗaurin ɗankwali, haka suka fito ana ta gaisawa da muyane da suke Allah sanya alkairi. Kamar an ce ta waiwaya idanunta suka sauka a kan su Hudu da sukw tahowa, tabbas ta gane su Hudu domin Hudu bai sauya kayana jikinsa ba, sannan sauran abokan ma duk ta gane su tun da da su aka zo ɗazu, wato ta shaida kayan jikinsu duk da cewar daga ɗan nesa ne ta hango su. Na huɗun ne bata gane ba, mai kalar shaddar irin ta jikin ta, wani ɗan gayu ta gani amma da yake ta san Malam Nura bai zo ɗaurin aure da shadda ba ma, shi ya sa bata ma yi tunanin shi ba ne. Ranta ne ya ɓaci domin ta san abokansa ne ya aiko su zo su bata haƙuri a kan yana ya kiranta bata ɗauka, kuma ta san dai zancen gizo ba ya wuce na ƙoƙi, ma,ana duk a kan maganar tarewar ta ce yau, za a kafa mata ƙahon zuƙa, ita kuma ta saka a ranta daidai da zamanin su take, wato sai ta musu tatasss sannan ta faɗa musu ba za ta tare ba sai nan da sati biyu kuma sai idan ya cika sharuɗɗan da za ta gindaya masa, juyawa ma ta yi daga kallon nasu ta ci gaba da gaisawa da mutane don ma kar su ga fuska su yi zaton za su samu sassauci daga gare ta. Malam Nura ganin an kusa zuwa wajen da sahibar tasa take sai wani bubbuɗawa yake shi ala dole yana son kashe ta da mamakin wankan da ya yi. Sai da suka zo dab da su Hadizar ya mayar da wayarsa aljihu ya sanya hannayensa duka biyu a aljihun rigar ya tsaya daga gefe irin tsayuwar nigogin nan yana son ya mata ba zata don ya san ranta a ɓace yake tun daga batun shaddar nan. Shi kuma yanzu so yake a daidaita ta tare a yau domin ya gama shiryawa yau a matsayin ranar tariyar ta, kuma ranar amarci. Ko da suka zo su Hudu ne ya yi musu sallama, suka je gaban su Hadiza, shi kuma ta bashi baya don haka bata ganshi ba. Hudun yana mata magana amma ta kauda kai gefe sai su Bintu ne suka amsa sallamar, yana dariya ya ce "Ni da ba ni na kai zomon ba rataya aka bani" Cike da masifa ta ce "Malam Hudu to na ga dai aure ne an ɗaura, to yanzun mai zan muku da kuka zo kuka tsaya mini, baka ga ina tare da mutane ba? Idan ma batun jere kuka zo ku koma ku faɗawa Malam Nuran ni Hadiza gayu na ce tariya ba yau ba, sai nan da sati biyu zan tare!!!" Malam Nura da yake bayan ta tsaye bai san lokacin da ya gyara tsayuwar nigogin da ya yi ba, gabansa yana faɗuwa ya haɗiye wani yawu muƙut, ba komai ne ya sanya shi wannan fargabar ba sai tunawa da ya yi da cewar ya shanye maganinsa da zai fito wanda aka ce kuma sai ranar da amarya za ta tare zai sha, daɗin daɗawa ma maganin kaf cikin magungunan Hudu ya ce masa ya fi kowanne tsada ya fi kowanne aiki. Su Bintu da suke kusa da ita su biyu ɗaya tana bata baki, da yake sauran matan da suke wajen ganin zuwan mazan sai suka ɗan basu waje, amma Bintu da yake tafiyarsu ɗaya daman kamar yadda hausawa suke cewa sai hali ya zo ɗaya ake abota, Bintu ta ce "Ina bayan ki ƙawata, ai kina da ƴancin ki yi yadda kike so, auren zawarci ne fa ba wai na budurci ba, kin ga kenan ko wata biyu kika ɗauka ba sati biyu ba kin da fiye da wannan damar... Kafin wani ya sake furta komai Malam Nura ya yi taku ɗaya biyu sai gashi a gaban amarya, yana zuwa ya ja ya tsaya hannuwan nan biyu a aljihu yana kashe ta da wani murmushi, don ba zai tsaya a masa sakiyar da ba ruwa ba, yana kallon ruwa kwaɗo ya masa ƙafa gwara dai ya yi duk yadda zai yi ganin bai yi asarar wannan ranar ba, bai yi asarar kuɗin maganinsa da ya bankamawa cikinsa ɗazu ba. Tsayuwarsa ta dakatar da su Hadiza da maganar ka ce na ce idanu ta zaro baki sake ita kanta ganin irin kan da ya mata bata san bakin ta ya furta "Angina malam Nura?" Kansa ne ya ji ya masa gingirim daman kuma ya san a rina wai an saci zanen mahaukaciya, ya san in har ta ga wankan nan nasa ƙarya take ta ce bai yi mata kyau ba, shi ya san wanka iya wanka. Yana murmushi ya ce "Na,am amaryata Hadiza" Daɗi ne ya baibaye mata zuciya musamman da ya zo a wannan daidai gaɓar da wurin yake a cike, kowa dai zai ganshi ya san ba ƙarya ta yi ba. Tana kallonsa ta ce "Wannan kyau haka" Ya gyara tsayuwa ya ce "Ai daman na faɗa miki zan baki mamaki" Bakin ta har kunne ta ce "Ai kuwa ka bani ina sonka Malam Nura" Allah ne kaɗai ya san daɗin da Malam Nura ya ji musamman da ya ga ta mayar masa lulluɓin da ta cire masa ɗazu a gaban ƙawayenta da abokansa, amma yanzu gashi ta sake rufa masa bargon mutunci. Da kanta ta matsa kusa da shi suka jeru, a take abokansa suke musu kirarin sun dace, ƙawayen nesa sukaa matso kusa ana ta sakin guda Malam Nura a zuciyarsa ya ce 'Ai Kuluwa ba ƙaramin cutata kika yi da kika ƙona wandon nan ba, Allah ma ya taimakaeni an mini dibara da yanzu kin jaza mini tsiya, to amarya tana ba za ta tare yau ba ai ɗan jijjiɓin bala,i kenan" Hadiza ta fito da wayarta daga jaka ta shiga kiran mai hoto yana ɗauka Malam Nura ya ji tana faɗin "Ka zo yanzu ango da abokansa sun ƙaraso za ka mana hoto" Malam Nura ya ciro hannayensa daga aljuhu ya shiga gyara hularsa, suka haɗa ido da Hudu da yake ta faman doka murmushi ganin sun samu karɓuwa. Daga ɗaya ɓangaren mai hoto ya ce "Ba kin ce shikenan ba?" Kamar ta falla masa mari haka ta ji da ya yi wannan furucin ta ce "Na faɗa maka ka zo yanzu" Da to ya amsa mata, nan ta kashe wayar tana aikawa Malam Nura kallon soyayya shi kuma gogan sai wani kashe mata ido yake ransa fari ƙal. Shi Malam Nura yanzu maganar hoto ce a gabansa, shi dai a musu hoton nan da amarya wanda za su kafe a ɗakunan su. Yanzu babu batun ya yi maganar tariya a nasa ganin tun da daman fushin rashin saka kaya mai kyau ne ya janyi cecw ku ce ɗin da ta ce ba za ta tare ba yanzu kuwa ai babu wanna batun. Mai hoto aka sauke a mashin nan ya shiga aikin sa babu ƙaƙɗautawa don su Hudu gefe suka koma suka zubawa sarautar Allah ido, mai hoto yana ta basu style ɗin yadda za su yi, yana ta walla musu hoto, ya musu ya fi kala goma sha biyar, nan suka nuna masa wanda za a musu na bango. Malam Nura sai ya tsinkayi muryar amarya tana faɗin a kirawo Zainaba da Shafi,i nan fa aka kira su, amma Zainaba dakyar ta zo tana ta kumbure-kumbure don ta tsani Malam Nura babanta take tayawa kishi, shi ma Malam Nura a nasa ɓangaren haka ne, burinsa kawai ya ɗauke Hadizarsa a bar waɗannan ƴaƴan musamman ma Zainaba. Ko da aka jeru za a musu hoton da yaran kowa yana ta washe baki amma Zainaba ta cukule fuska ban da harara da take aika musu babu abin da take, sai za a ɗauki hoton ango da amarya suna kallon juna cike da soyayya shi kuma Shafi,i shi ma dariyarsa yake amma Zainaba sai ta shiga banka musu harara kamar idanunta za su faɗo!. A hakan ne cike da rashin sa,a Malam Nura ya ji tazugen wandon jikinsa ya cire daga cikin wandon. A take ya ji tsantsar wandon ta masa yawa, daman ya san ya yi kaɗan tazugen dakyar ma ya ɗauru saboda ƙanƙantarsa, shi kuma garin sauri bai tsaya ya canza wani ba, idanu ya ɗan zaro a ɓoye yana ɗan yatsina fuska kamar mai jin kashi a zuciyarsa ya ce "Innahu min sulaimana wa innahu bismillahir rahmanir rahima, li,ilafi ƙuraish, ilafihim rihlatash shita,i wassaif fal,ya,abudu rabba hazal bait allazi aɗ, amahum min ju,in wa aamanahum min kauf" Ya faɗa wani gumi yana karyo masa. Da sauri ya saka hannunsa a cikin aljihun rigarsa, ya riƙe saitin ƙugun nasa ta yadda wandon ba zai zame ya faɗi ba, tun da yanzu babu inda yake a riƙe sai hannunsa da ya riƙe shi. A zuciyarsa ya ce 'Allah ka taimakeni kar wandon nan ya faɗi, kar ya tsinkani a idon jama,a, ya Allah yadda aka taru ake kallonmu ni da amaryata muna birge mutane Allah kar ka saka wandon nan ya rusa farincikin nanu, Allah kar ka ba wandon nan ikon ya kunyatani, yadda kowa yake kallona kamar wata ɗan daren goma sha uku ka sa abun nan ya ɗore' Ya faɗa yana sake bada ƙaimi wajen damƙe tsantsar wandon. Mai hoto cike da bada umarni ya ce ",Amarya kama hannun angon" Amarya tana murmushi ta miƙa hannu ta riƙo hannun Malam Nura da yake cikin aljihu yana riƙe da wandon, ta riƙe tana faɗin "Cire hannun mana ya ka saka shi a aljihu?" Malam Nura idanu ya shiga rabawa a zuciyarsa yana faɗin 'Shikenan asirina a tonu, ya zan yi idan wandon nan ya zame Hadiza ta ga haɗe yake da tsohon wandona na yadi aka yi faci' A fili ya ce "Ai na fi ganin kyauna idan hannuna yana cikin aljihu" Ya faɗa cike da ganin vata kunyata shi ba. Bata kawo komai a ranta ba ta riƙe hannun ana ta musu hoto shi kuma ya riƙe wajen gagam, don Hudu yana lura da shi ya ga hatta wajen da ya riƙe ƙafar wandon har tattarewa ta yi, shi kaɗai yake dariya a ransa duk da bai san mene ne ba amma banya raba ɗayan biyu matsala ce domin ya lura gabaɗaya abokin nasa ya fita hayyacinsa ba kamar lokacin da ake hoton ba duk ba a nutse yake ba. Dabara ce ta faɗo masa yana cikin tunanin yadda zai yi ne wayarsa ta shiga ƙara, ya fito da ita ko gama ganin waye bai yi ba ya raɗawa amarya cewar Goggo Ramma ce take kiransa, haka ya ɗan ja gefe yana wayar ƙarya, da ta faki ido sai ya sha wata ƴar kwanar lungu, a kan wani dogon tsumma ya yi wa idanunsa masauki, da sauri bai yi ƙasa a gwiwa ba ya ɗauka ya ɗage rigar ya zare mazugin cikin, ya gyara wandon ya saka tsumman da ya tsinta ya ɗaurew wandon daga sama wato daga ƙugunsa wandon ya tsaya ya saki rigar yana sakin wani gauron numfashi. Fitowa ya yi daga lungun ya dawo yana ta jin daɗin ya tsira da mutuncinsa, amma dai alla-alla yake ya bar wajen tun kafin a yi abin da zai kunyata. Haka dai aka sha hoto sai wajen ƙarfe shida saura ango za su tafi, abokan sun ɗan yi gaba sun tsaya shi zai yi sallama da amarya, yana tsaye yana washe baki ya ce "To mu za mu tafi" Amarya ta ce "Tohm kuɗin karin nawa fa" Yawun bakinsa ne ya ƙafe ya ce "Wane kuɗin kari kuma, ke da za ki kwana a gidana ai akwai su Haule a gida sai abin sa ranki yake so za a girka da safe" Ranta ne ya ɓaci ta ce "Ai na faɗa maka ba yau zan tare ba ko?" Idanu Malam Nura ya zaro a zuciyarsa ya ce 'Ashe kuwa wanda ya mutu zai falko, duk wannan wankan da na yi don kin raina mini hankali, to ai kuwa ba zai taɓa yiwuwa ba mai kaza ya tashi da fifike' A fili kuma ya ce "Amma dai wasa kike ko Hadiza?" Farrrr ta yi da ido sai da bakin idon ya ɓace ɓat sai farin sannan ta dawo da idanunta daidai ya ce "Wai wasa an faɗa maka a komai ake wasa ne, wallahi da gaske ba zan rare yau ba, kaima da wata magana yanzu fa batun ƙarfe shida na yamma ake yi ko jere ba a je an yi ba, kuma a yaushe zan tare?" Malam Nura ya kalle ta ya ce "To mene ne abin wahala a wani jere, yanzu wasu ƴanmatan ma sai da isha,i ake tafiya da kayan a jera ai ba wahala ba ne gado ne fa kawai za a ajiye yanzu da gabaɗaya ma jeren maza ne suke yi" Hadiza ta ce "To bari ka ji ni wallahi kayana suna wajen kafinta da na saya daman sai za a jera za a ɗauke su daga can a wuce gidanka da su, ka ga a yanzu kuwa lokaci ya ƙure" Malam ya ce "Ni yanzu daga nan sai na je wajen kafinta a ɗoro kayan a baro wallahi ina iya jerasu duka ke kuma in aka yi isha,i sai a kai ki" Baki ta taɓe ta ɓata rai ta ce "Kamar wata amaryar kunkuru, to wallahi ba zai yiwu ba so kake ake gulmata ana faɗin ango ne ya mini jere, yadda kowace mace ake zuwa a jera mata kaya haka za a mini, kuma in tafi a tsanake, duk ka hana kanka sakat kamar dai baka da mata a gida, ni wanna auren jin sa nake kamar auren farko don haka a tsanake zan tafi" Malam ya tari numfashin ta da faɗin "To ko amaryar buzuzu ce ba dole a yi ɗokin ta ba, kuma da kike batun matana ai na san da zaman su, ke fa na ce miki wata guda za ki yi kina amarci, babu wacce za ta karɓi bakin kwananki" Fuska ta yatsina ta ce "Wllahi ko shekara za ka bani ba zan tare yau ba!" Su Hudu ne suka matso ganin abin yana neman wuce makaɗi da rawa, Bintu ma suka matso na aka shiga basu baki, a ƙarshe dai an shawo kan amarya ta ce za ta tare amma sai gobe, nan su Hudu suka shiga lallashin Malam a kan ya haƙura yau da goben ai duk ɗaya ne!. Ba dan ransa ya so ba sai don ba yadda zai yi haka ya haƙura, cikin ransa tsanar Kuluwa ce fal don ya san ita ta haddasa komai, da tun farko ya zo da shaddar a jikinsa daga wajen ɗaurin aure da tuni an jera kayan amarya ta tare a yau, amma da yake ta yi fushi tun da aka ɗaura auren shi ya sa ko shirin tarewa yau bata yi ba. Haka ya bata 5k don ta ce yau kuɗin ba iya na kari zai bata ba har da na abincin dare!. Ko da suka taho a hanya suna ta zolayarsa amma shi kaɗai ya san halin da yake ciki, banza ya musu kawai so yake ya samu abin da zai yi wa Kuluwa sanadiyyar daren amarcin da ta masa yau!. A can gida kuwa da magriba Haule ta fito da shirin fita tana faɗaw Kuluwa za ta je gidansu duba babanta, har tana cewa Kuluwar ko ita ma za ta je su fita tare. Buɗae bakin Kuluwa ta ce "Ni in fita yanzu haba Haule ai ban ga ta zama ba an saci ɗan ɓarawo, in ban da ma ke ina za ki samu damar fita ana jimawa fa ƴan kawo amarya za su yi wa gidan nan kutse" Baki ta taɓe ta ce "To wa ya aikeni bare ya ga na daɗe, ai dubiyar dai ta fiye mini, amarya kuma da ba a kaina za a ɗora ta ba ina ni ina su, kafin dai su kawo ta zan dawo don ba zama zan yi ba, kar a zo a ce kishi ne ya sa na ƙi zama a gidan basu san ni auren Malam Nura ko a gefen takalmina ba" Kuluwa ta ce "Ai ni ina nan na kasa na tsare, na je na yi wa baban naki sannu idan ƙura ta lafa don yanzu ba zan iya nisa da gidan nan a mini sakiya da ba ruwa" Da mamaki Haule take kallon ta ta ce "Ban gane ba, wace ƙura kuma sai ka ce wanda guguwa ta taso, wai ke Kuluwa ba za ki sauƙaƙawa kanki kishin wanda bai damu da ke ba, yanzu ban da Allah ya takaita da ba tuni ya lahanta ki va" Baki ta taɓe ta ce "Na ga alama idan ina biya ki hawan ruwa sai ya kama ni, ai ni da wuya ta karni ai gwara daɗi ya karni, ai abin alfahri ne ma a ce miji ya nakastaka a kan kishin sa soyayya kenan, kuma ni ina nan ko sama da ƙasa za ta haɗe yau kwanane idan amarya ta isa ta yi kwanan turaka yau Allah tsine mini don wallahi ko a ni ko a ita domin sai ta jira na famshe gabaɗaya kwanankin da Malam ya haramta mini shiga turaka, sannan zan bata dama ta yi kwana ukun da kowacce bazawara take yi" Baki sake Haule take kallon Kuluwa tana mamakin ƙarfin hali irin nata, ta san yau ko gawa za ta yi Malam ba zai bari ta kwana a turaka ba!. In ban da ma rashin zuciya mutumin da ya haramta mata shiga turaka kusan kwana shida yau, shi ne zai bari ta shigar masa turaka a ranar da yake jin sa zai ɓarji amarci da amaryar da ya gama yi wa tanadi a cewarsa. Fatan samun sa,a ta yi wa Kuluwar ta ja su Kabiru suka tafi. Suna fita Kuluwa ta rufe nata ɗakin ta tafi gidan mai maganin mata magunguna ta lodo ta biya kuɗin ta dawo gida. Tana zuwa ta kai ruwa banɗaki ta salsala wankanta, ɗaki ta dawo ta shafa wani turare mai suna MU JONE turare ne na jan hankalin mai gida da ta siyo an faɗa mata yana da kyau kuma matukar miji ya shaƙi ƙamshin shikenan sai yadda hali ya yi shiga motar mahaukaci!. Wando da riga ta saka domin mai maganin ta ce ta saka kaya na jan hankali, dan haka wani wandon Malam Nura da yake ajiye a ɗakin ta ta ɗauka ta saka sannan ta saka rigarta tshirt kasancewar bata da wanduna.Magani mai suna maƙale mata ta ɗauka ta zuba a nono ta dama ta shanye ta shafa humra. Wani kwalli idonka idona shi ma duk yana cikin kayan da ta siyo ta ɗauka ta rambaɗa a idanunta. Kanta da yake a tsefe ta shiga tajewa. A can kuwa su Malam Nura masallacin magriba suka wuce, bayan an yi sallah ya musu sallama duk ransa babu daɗi domin har ya hango zai kwashi amarci amma gashi an samu akasin lissafi. Hudu cikinsa har ciwo ya yi wajen tsokanar Malam Nura yana faɗin "Wai da gaske abokina duka ka shanye maganin nan kaɗan ka rage, gashi kuma mai maganin ya ce a ranar maganin yake barin amfani, to Allah ya sa ma kai ba gwauro ba ne, ga Haule nan ga kuma amarya Kuluwa sai wacce ka zaɓa" Ko amsa bai bashi ba saboda takaici. Shago ya wuce yana zuwa ya ce mai shagon ya bashi sufagilu guda huɗu, haka aka ɗakko masa ya bashi kuɗin ya saka a aljihu ya nufi gida. Kuluwa da ta gama shiryawa tsaf sai kuma ta ce "Ni da zan je turaka yau, gashi na gama haɗa bom wato na sha kayan gyara, gwara dai in shiga banɗaki in tsugunna don na ji taushen da ta sha ya saka mini ciki" Ta faɗa tana ɗaukan buta ta shige banɗaki ta rufo, a ranta tana ta saƙa yadda idonka idona kwallin da ta saka zai ruɗi Malam, da MU JONE da sauran abubuwan da ta yi amfani zai sanya idan har ta je turaka amarya za ta ƙufula ta ce an wulaƙantata a ranar amarci, in ya so da safe a yi badaƙala a sake ta shikenan ƙurunƙus. Malam Nura a hanya suka haɗu da Haule da za ta je gidan nasu, take faɗa masa sai Kuluwa kaɗai a gidan ita ma ba yanzu za ta dawo. Da sanɗa ya shigo zaure gidan, yana zuwa ya cire takalmansa ya shigo saɗaf-saɗaf motsin da ya ji a banɗaki ya tabbatar Kuluwa tana banɗaki bokiti ya ɗauka ya koma zaure da sauri. Yana zuwa zauren ya fito da gabaɗaya sufagilu yana buɗewa yna tatsewa a cikin bokitin wato can ƙasan bokitin amma daga cikin bokitin ba wai daga waje ba. Sai da ya gama tatsewa duka ya saka wani ƙaramin icce ya gyara shi ko ina. Kuluwa wacce fitowarta kenan daga banɗaki ta cika ruwa a buta za ta yi alwala, tana ƴar waƙarta. Alwala ta zauna a kan ɗan dutsi tana yi amma ta ba ƙofar gida baya. Da ta zo shafar kai ta cire hularta ta ɗora a cinya daman kan a taje yake bata ɗaure ba. Malam Nura ya taso da sanɗa yana zuwa ya kifa mata bokitin nan a kanta, a take kan ya shige cikin bokitin, ya saka hannu biyu ya danna saman kan ta cikin bokitin a take sufagilu da bokiti suka ce sun ga wurin zama a kan Kuluwa, domin babu ɓata lokacin gashin nan ya yi nutso a sufagilu. Kuluwa da bata ankara ba ta ji wani abu kamar roba a kanta, kafin ta ankara ta ga ya rufe mata har fuskarta, tana shirin yin magana ta ji an buga abun, abu na farko da ya fara zuwa ranta shi ne aljannu, don ta san dai gidan babu kowa, kuma daman wataran Haule tana cewa idan ta fito fitsari cikin dare tana ganin kamar gilmawar mutum, amma saboda ƙi faɗi irin na Kuluwa da ƙaryata mutum sai tw ce ita bata taɓa gani ba don haka ba za ta yar da ba. Baki yana rawa ta ce "Subhanallahi waye, mene ne haka, mai na yi muku? Ni ce fa Hauwa Kulu, da aka fi sani da Kuluwa don girman Allah ku yi haƙuri" Ta faɗa jikin ta yana karkarwa idan akwai abin da take tsoro shi ne aljannu. Shiru ta ji hakan ya sa ta saka hannu biyu domin ta cire abun ta cece ranta tun da bata gani bokitin ya rufe mata ido, am a tana ja ta ji gabaɗaya a manne yake da gashin ta, gabanta ne ya faɗi ta tabbatar da wannan aikin aljani ne. A take ta shiga lalume kwaraf ta buge butar alwalar ta, butar ta tuntsura ruwan ya zube, kasancewar wajen alwala ne duk a jiƙe yake kuma har ya yi laka a wajen irin tsantsin nan da ƙasa take idan ruwa yana jiƙa wuri. Da hannu biyu ta dafa ƙasa ta miƙe tana ta salatin da bata iya ƙarasawa take dawowa farko, a zuciyarta tana jin daman ta raka Haule dubiyar babanta. Malam Nura ransa fari rass cike da mugunta yana tuno irin ɗiban albarka da ta yi wa wandon sa ya kai wani ɗan icce ya ɗan soka mata a jikin hannunta, a take Kuluwa ta tabbatar da cewa ta faɗa hannun aljannu domin zaton ta farcen aljani ne aka caka mata a hannun. Salati take yi kafin ta ƙarasa sai ta kamo hailala, bata gama hailalar take kamo a,uziyya, a haka ta samu nasarar miƙewa tsaye tana baza hannu kamar makauniya ƙafafun ta ta yi wa masauki a wajen santsin lakar nan, a take santsin ya kwashe ta suuuuuu ƙafarta da babu takalmi ta tafi, domin gabaɗaya ta sille takalman wani ya yo kudancin Nigeri,a wani arewacin Nigeri,a ya nufa. Ji ta yi kamar an yi sama da ita sai gata ta faɗi jirif, duk da ta ji faɗuwar amma yanzu ba wai ta faɗuwar take yi ba batun ceton rai ake daga hannun mutanen da su suke ganinmu ba mu muke ganinsu ba. Da sauri ta tashi ta muskuta ta shiga rarrafe domin ta san matuƙar ta sake tashi to faɗuwa za ta yi tun da ba gani take yi ba bare ta taka inda babu laka. Wata zuciyar tana bata shawarar ta kama hanyar waje a nan ne za ta samu a rabata da abin da aljannu suka kifa mata ya manne mata a gashi, wata kuma tana faɗa mata ta koma ta shige ɗaki ta kulle duk da ta san aljannu har bango suna shiga. A zaton ta ko Haule ko ƴan kawo amarya sa kawo mata ɗauki. Tana sunkuye tana rarrafawa Malam Nura ya lallaɓa ya naɗe hannun rigarsa ya jimƙe ya sakar mata ƙulli a baya saboda bokitin iyakarsa wuya da kafaɗarta. Jin saukar ƙulli rididif har sau biyu ta ji dukan da bambanci da na mutane a take faɗuwar gabanta ta yawaita Malam kuma a zuciyarsa ya ce ',Yadda kika salwantar mini da daren amarcina da Hadiza, da yadda na yi asarar maganin da na ɗaɗɗaka yau, wallahi sai na baki wuju-wuju sai kin gwammace kiɗa da karatu, har da wani saka wandona ke kika san jarabar da kika taka, amma yau yadda zan tsurar da ke sai kin ji daman ƙafafun na guntule miki don har suma sai kin yi Kuluwa, za ki san ni kika yi wa rashin mutunci, kika barni ina yawo da wando kwambileshin (Combination)" Muryarsa ya shaƙe ta zama kamar ta yara kamar ta tsoho ya ce "Kuluwaaaaaa" Kuluwa da daman a tsorace take ga kuma bokitin da ya rufe mata kunne wani irin sauti ta ji da wata murya a take a tsure gudawar da take matsewa ta fara ƙoƙarin fitowa!!!. *Saura page 1 mu gama free pages daman na ce muku a 10 za mu gama masu son karantawa har ƙarshe za su biya 700 domin shiga group ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay shaidar biya ta 09025576222, *mutanena na Niger ga* *naku acc ɗin da za ku saka 88630104 nita ko* *amana* *Issaka issoufou.* MAMAN AFRAH 09025576222 [4/17, 12:47 PM] MOM MASHKR & AFRAH: *UWAR AGOLA* NA MAMAN AFRAH *Daga marubuciyar* *Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.* 09025576222 🅿️1️⃣0️⃣ Iya ƙarfin ta ta bada himma da ƙaimi wajen danne gudawar da take son ɓata mata wandon Malam Nura da ta saka wanda take ganin shi ne makamin da za ta ja hankalin sa har ya kai ga cikar burinta wato kwana a turaka, sannan ya zamana bata yi asarar kuɗin magungunan da ta saya ba. Fasa rarrafen ta yi ta koma daɓas ta zauna ta muskuta mazaunanta a ƙasa tare da sake murza su a ƙasan duk don ganin ta mayar da gudawar da take son ƙwace mata, domin iya tunanin ta ta fara hasashen ba za ta iya matsewa ba. Sau uku tana murza mazaunan duk da faɗuwar da gabanta ya yi musamman da ta ji aljani har ya san sunan ta, duk da tana tunanin ko dai ya haddace sunan nata ne lokacin da ta ce ita ce Hauwa Kulu da aka fi sani da Kuluwa. Duk da gudawar bata koma duka ba amma dai da dama dama wai kibiya a ido, domin kuwa ta daina matsar ta kamar ɗazu. Hannu ta kai jikin bokitin ta shiga kokawa ita da bokiti saboda tana so ta ɓanɓare shi ko ta samu damar gani da idon ta domin idan tana gani za ta fi samun hanyar tsira saɓanin idanun a rufe. Ta ja bokitin amma ta ji ya kama kan sosai, ta sake ja ta ji babu alamar zai fita a fili ta ce "Na shiga uku ni Kuluma(Ta ce Kuluma a maimakon Kuluwa) Ya na ji abu ya zama tif da taya da gashin kaina?" Malam Nura jin ta kira kanta da Kuluma a zuciyarsa ya ce 'Ai sai kin kira kanki da sunan maza yau, idan aka jima farkon sunan naki ma ba za ki tuna ba sakaryar banza da wofi mai almubazzaranci, haka kawai shaddar dubunnai kika ƙona' Daddagewa ta yi ta shiga ƙoƙarib miƙewa tun da ta ji ɗif babu motsin kowa, amma sai dai mai tana miƙewa ƙafafun ta hagu da dama santsi ya kwashe su ta koma ta yi zaman ƴan bori a cikin lakar a fili ta ce ",Na ga ta kaina yanzu kayan nan da na saka a raina zan wanki Malam da shi, zan ɗauke masa hankali daga sabuwar amaryar nan Hadiza shi ne nake faɗuwa a cikin laka ya zan yi da raina" Ta faɗa tana shafo jikin wandon domin jin inda lemar ta taɓa. Malam Nura ya shiga jijjiga kai yana bin ta da kallon tsana a ransa ya ce "Wato ni za a cuta da wannan wandon da ya miki kamar ƙafar tattabara, ai gashi nan kin zama kamar wacce ta yi nutso a ruwan kwata, amma za ki gane shayi ruwa ne' Yana faɗar hakan ya zo bayanta ya riƙo rigar daga baya ya shiga jan ta ƙiiiii amma ba wai gaba yake jan ta ko baya ba, kawai yana gewayawa da ita ne, wato round yake yi da ita, Kuliwa wacce ta fara saka rai a samu salama jin bata jin komai tunanin ta aljanin ta gama wadaƙar da zai yj da ita amma sai ta ji ana jan ta ana juya ta tamkar fanka, a gigice ta shiga faɗin "La haula wala quwwata" Ita kawai take maimaitawa a kiɗime domin zuciyar ta ta gama bata cewar ko dai wani jirgin aljannu ne zai tashi da ita zuwa garin aljannun shi ya sa ta ji yana juyawa hakan ya sa hanjin cikin ta ya karkaɗa da ƙarfi. Malam kuma ƙaimi ya bayar wajen juya ta a cikin lakar nan da cakwalin ruwan alwalar wajen. Tun tana la haula wala quwwata har ta dawo tana cewa "Wa qulna ya naru kuni bardan wa salaman ala ibrahim" Haka ta shiga maimaita samu fatiha. Sai da ya ga ta jigata sosai sannan ya sake ta, saka ta ɗin da zai yi tamkar ya tura ta suuuu ta bi caɓalin santsi ya kai ta dab da banɗakin ta rarrafo tana son guduwa ɗaki, jin ta samu bango ta dafa ta tashi tsaye ƙafafun karkarwa kawai suke kamar mazari, ganin hakan Malam ya juya ya ɗakko fanteka a ƙofar ɗakin Haule ya haɗo da wata bulallar maina. Yana zuwa lokacin ta ji tsoro da tsurewar da ta yi ba za su bar ta ta iya tafiya da ƙafafun ta ba, hakan ya sa ta durƙushe yana zuwa ya saka fantekar ya buga a saman bokitin, wani sauti ya bada wanda Kuluwa ta zaci aljanin yana adawa da kan ta ne, bayan abun da aka kifa mata hallaw ake son raba kanta da jikin ta. Hakan ya sa da sauri ta rarrafa kamar irin guragun nan masu laulayayyar ƙafa idan suna rarrafawa suna wani irin sauri, haka ta shiga sauri tamkar ana tura ta. Malam da sauri ya bi bayan ta ya ɗaga bulallae ya tsula mata, cike da yadda bulallar ta shige ta ta mata shigar sauri ta miƙe tsaye babu shiri, da ta tuno yadda lakar take taɗe ta da yadda ta ji an jujjuya ta ɗazu da sauri ta sake tsugunnawa sai kuma ta sunkuya kamar mai naƙuda tana jiran tsammani don ita gabaɗaya an dagula mata lissafi. Malam tuno da Hadiza ta ƙi tarewa ne saboda abin da Kuluwa ta masa ya sake ɗaga bulalar ya zabga mata. Cike da tsoro ta ce ",Ni dai Kuluwa alƙiyamata ta tsaya, ina zan ga Malam kafin in cika in nemi yafiyarsa a kan wandon angoncin sa da ƙona, Malam ka zo gida ka yafe mini ga aljannu za su yi ajalin Kuluwarka" Ta faɗa bakin ta yana karkarwa, wata harara ya aika mata tamkar tana ganinsa. Ƙafafun wandon jin ya mata jagafgaf ta shiga naɗewa domin gudu za ta yi ba na wasa ba, ko ɗakin Malam ne ta samu ta tsira da ranta saboda abin da yawa wai mutuwa ta shiga kasuwa. Tana tashi tsaye ya saka mata ƙafa cike da mugunta sai gata ta yi sama ta dawo ta rafku da ƙasa cike da ficewar hayyaci ta ce "Allah ya isa... Maganar ce ta maƙale kafin ta ƙarasa sakamakon tunowa da ta yi da cewar aljannu ne. Saɗaf saɗaf ta fara rarrafawa tana fatan ba su ji Allah ya isan da ta musu ba. Rabuwa ya yi da ita sai da ta kusa da ɗakin sa tana faɗin "Allah ya taimakeni gwara in je ɗakin Malam" Ta faɗa maganarta tana karkarwa, sai da ta kusa zuwa tana lalamawa ya saka ƙafarsa ya buga a ƙasa sau biyu, Kuluwa jin wani ƙara didif da ƙarfi sai ta ɗauka sakkowar wani aljanin ne, hakan ya sa babu shiri ba zato da tsammani ta miƙe tsaye ta falfala a guje duk da shamaki da bokitin ya mata da ganin gabanta, burin ta kawai ta shige ɗakin Malam gani take za ta tsira. Malam Nura a zuciyarsa ya ce 'Kaico Kuluwa ai tun da kika taɓa ni kin taɓowa kanki wallahi' Murya ya maƙe tamkar an shaƙewa biri wuya ya kasa magana haka ya mayar da muryarsa ya ce "Za ki faɗa wutar aljannu gata nanta cika ɗakin mijin naki sai ci take kamar an watsa fetur... A zuciyarta kuma ta ce 'Wuta? Innalillahi kar ta kwaile min mazaunai i rasa wanda zan ke juyawa in amarya ta zo' Ai ba ta jira ya ƙarasa maganar ba ta ja wani uban birki, ba ta san lokacin da ta yi wata kwana ta juyo ba. Malam a zuciyarsa ya ce 'Wato kwana ba sai mota ba, mutum ma yana ribas kuma ya yi kwana' , Kwanar da ta yi ne ta taho a kiɗime ya sake gyara murya ya ce "Kuluwa za ki faɗa ruwan maliya" Da kuka ta fashe bayan ta dakata da maganar don yanzu ta fara tunanin ko dai ba a duniyar mutane take ba a duniyar aljannu take. Zaunawa ta yi a ƙasa take mismis da baki tamkar mai zikiri amma ita kanta ko wuƙa za a daka mata a maƙoshi ba ta san abin da take faɗa ba. Amma dai da fargaba tana sanya ƙirji ya fashe da tuni nata ratattakewa zai yi domin a matuƙar tsorace take ita ba komai ne damuwar ta ba rashin sanin abin da yake a kanta. Ganin ta zauna ɗam ya taho ya saka bulallarsa ya zane ta tsaf duk ya burɗa mata jiki, idan ya tsula a nan ta saka can ta riƙw can har sai da ya tabbatar da ta jigatu kuma ya ji ɗan sanyi a zuciyarsa dangane da abin da ta masa sannan ya ƙyale ta. Sai faman basu haƙuri take har zai fice daga gidan ya fasa ya juyo dan ya ƙara tsorata ta cikin murya mai ban tsoro wannan karon ya yi magana ya ce "Yanzu za mu kyale ki, amma dai za mu cire miki mashayar ɗa (Breast) Guda ɗaya" Da sauri ta saki wajen ƙafafun ta da take murzawa ta riƙe mashayar da suka ambata tana zare ido daga cikin bokitin cike da murya kamar za ta yi kuka ta ce "Ku mini rai komai zan baku amma kar ku cire mini mashaya wallahi ban taɓa haihuwa ba ban shayar da ɗana ba, kuma mijina sabon aure zai yi, idan kuja cire mini kar a zo ake mini gori tun da gidan kishiyoyi ne" "Malam ya aikawa kirjin nata da ta damƙe gudun kar tsautsayi ya rutsa da mashayar kamar yadda aljanin ya faɗa mata a zaton ta, a zuciyarsa ya ce "Aikin banza abu ba abu ba, akwai ya babu kakar wajen uba, abu kamar ƙwallon goruba amma tana faman tada hankali' Jin haka ya ce "Za a guntule miki hanci da fatar baki" , A zuciyarta ta ce "Wannan aljanin maye ne, ta saka hannunta guda ɗaya cikin bokitin ta dafe hanci ɗaya hannun yana kan mashayar da ta dafe. Yana tunano wata sabuwar muguntar da zai mata sai ya ji alamun tahowa za a shigo cikin gidan, da sauri ya zo ya dilliƙa mata wani uban ƙulli har sai da ta gantsare, a zuciyarsa ya ce 'Ko banza kin ci uwar wuya' Yana faɗa ya yi saurin laɓewa yadda mai shigowar ba zai gan shi ba. Haule da ta dawo ta buɗe baki ta yi sallama, kasancewar ta baro su Alawiyya a gidansu sun ce a can za su kwana. Kuluwa jin sallamar Haule ta buɗe baki kamar ƙaramar yarinya tana faɗin "Taho Haule, taho ƴar uwata ta jini ba kishiyata ba, zo ki ga yadda na yi arangama da mutane ɓoye, wallahi na yi zaton alƙiyama ta ce ta tsaya ashe dai za ki zo ki same ni da rai" Ta faɗa tana sharɓar kuka tana miƙa hannayen daga zaunen da take ko sallamar bata amsa ba. Haule cike da tashin hankali ta ƙarasa shigowa da ɗan gudu ta nufi inda Kuluwar take, a daidai nan Malam da yake laɓe ganin ta bashi baya ya suɗaɗe ya saka takalmansa da abubuwan sufagilu ɗin ya bar gidan. Tana zuwa ta kwashi salati ta salance ya ce "Kuluwa aljannu kuma mun shige su, ai daman ina faɗa miki idan na fito fitsari da dare sai na ga kamar wulgawar mutum amma kika ce babu wasu aljannu a gidan nan,... Kafin ta rufe bakin ta Kuluwa ta ce "Kaico! Haule, taimaka ki gani abun da suka rufa mini yadda kika san an haɗa mayen ƙarfe da jikin ƙarfe haka ya haɗu da gashina ya ƙi ɓamɓaruwa, gashin nan da na tsefe zan ke yin kwalliyar da shi idan amarya ta tare amma kin ga sun maƙala shi a wani abu" Haule da ta ƙaraso cike da rikicewa ta ce "Kuluwa ai bokiti ne a kanki" Kuluwa ta ce "Haba Haule wane irin bokiti dan Allah ki taimaka a san yadda za a rabani da wannan abun na kaina, ni ba na ganin komai sai duhu, zatona ma ko matatar man aljannu ce" Haule ta ce "Ba waji matatar man fetur ɗin aljannu wannan bokitin naki ne baƙi" Shiru ta yi rana nazarin shin daman bokitin ta ne aljannun suka ɗauka kenan suka rufa mata amma ta kasa gane dalilin da ya sa abin ba ya ɓaaruwa. Haule ta ce "Ni na tasa garin yaya ta faɗa tana yaɓa bokitin amma sai ta ji shi ƙamƙa a kan Kuluwa, nan ta shiga ƙoƙarin ɓanɓarewa amma abin ya ci tura!.Tun tana ja abin yana bata mamaki har ya fara vata tsoro. Tana kallon Kuluwa cike da tausayawa ta ce "Kuluwa bokitin nan kamar dai tare da kanki aka yi su a mannr domin ya ƙi fita fa" Kuluwa kamar za ta yi kuka ta ce "Dan Allah ki cire mini, yanzu idan ƴan kawo amarya suka zo sai a mini dariya fuska a rufe," ,Amsa mata ta yi na Kuluwar ta ce "Bari in dafa ƙasa ki dage ƙarfin ki na bara ki cire mini amma kar ki bari daidai da ƙwayar gashina ɗaya ya tsige garin cirewa, kin san dai gashi shi ne adon mace" Banza Haule ta yi da ita ta shiga ƙoƙarin raba ta da bokitin amma ta ji shi gamgam idan ta ja da ƙarfi sai Kuluwa ta shiga zandama ihu tana faɗin wayyo gashin ta. Ta jima tana abu ɗaya amma ta kasa gane mene ne ya riƙe gashin daga cikin bokitin ganin abin ba na ƙare ba ne sai ta cewa Kuluwa bari ta je ta dubo Malam Nura a waje, har tana tambayar kuluwa daman bai dawo gidan ba ta ce ai ban da aljani babu wanda ya zo tun bayan fitar su, ba ta san cewa Malam ne aljanin nata ba. Haule hanyar waje ta kama da sauri tana jin Kuluwa tana rangaɗa mata kira amma ta yi banza da ita, don tana faɗar wai kar fa ta tafi ta bar ta aljanin ya dawo ya ida nufinsa na cire mata mashaya, wai ta kama hannun ta su tafi tun da ita ba gani take ba yanzu. Malam yana fitowa ya watsa gidan sufagilu ɗin a kwata, ya tafi wata majalisa wajen mai siyar da biredi ya zauna suna ta tsokanarsa mai zai kawo sabon ango majalisa shi da zai tarɓi amarya nan dai ya sanar da su cewar sai gobe ne tariyar. Haule tun da ta fito take ta duba shi bata gan shi ba. Tafiya ta shiga yi tana dubawa wani saurayi ɗan maƙotansu ta tambaya ya ce ya gan shi a wajen me shayi da biredi, nan ta ce ya kira mata shi. Tana nan tsaye sai ga Malam ya taho yana ta sauri tamkar bai san mai ya faru a gidan ba yana zuwa cike da nuna damuwa ya ce "Haule lafiya dai? Ko ƴan kawo amaryar ne suka zo?" Ya faɗa kafin ya ƙaraso, Haule ta ce "Malam mutanen ɓoye ne suka yi wa gidanka kutse wallahi suna can sun rufewa Kuluwa kai" Idanu ya zaro kamar dai ba shi ya aikata ba ya ce "Subhanallahi, subhanallahi mutanen ɓoye kuma? Ku kuke ganinmu ba mu muke ganinku ba, wane irin rufe kai, ya subhanallah wayyo Kuluwa" Ya faɗa don ba ya ma son ya nuna cewar yana jin haushin ta a kan abin da ta masa shi ya sa ya nuna tausayawa don idan ya sake Haule da shegen wayo za ta iya hango jirginsa. Haule ta ce "Wallahi nake faɗa maka bokiti ne suka rufa mata, kuma cikin ikon Allah bokitin ya manne da jikin kanta yadda ka san tare aka halicci bokitin da kanta ko alamar fita ba ya yi" Hannuwa ya tafa yana salallami ya nuna damuwa, a daidai na Hudu da ya zo zai je neman ɗansa da aka aika bao dawo ba ya gan su tsaye cike da zolaya ya ce "Sabon ango mai tariya gobe" Amma ganin Haule duk a ruɗe sai ya ce "Ya na ganku carko-carko lafiya dai?" ,Malam ya ce "Ina fa lafiya kukar bulukiya a gidana" Ya faɗa yana kwashe abin da Haule ta faɗa masa ya faɗa masa, sosai a jimanta abin suka ɗunguma zuwa gidan Haule ce a gaba kamar za ta ci da ka. Kuluwa da take zaune inda aka barta kamar an dasa ta bakin ta yana ta faman kai da komowa na addu,ar da duk ta ci nasarar cafkowa a bakin ta jin takunsu kafin su yi sallama ta sake rikicewa tunanin ta aljanin ne sallamar su ta sanya ta sauke ajiyar zuciya. Ko amsawa ba ta yi ba ta hau faɗin "A kawo ɗauki jama,a idan aka ce a haka zan rayu ni Kuluwa aljanin nn ya shiga haƙƙina" Harara Malam ya aika mata a ɓoye don har yanzu bai ji ya huce daga abin da ta masa ba. Hudu salati yake ba ƙaƙƙautawa shi ma Malam yana taya shi gudun a zarge shi. Hudu ya kama bokitin ya ja, amma gabaɗaya a manne yake Malam ma ya ja ya ji babu alamar zai fita, hakan ya sa cike da mugunta ya ja da ƙarfi ai kuwa Kuluwa ta zandama uban inu tana faɗin "Da ciwo waye wannan mai ɗanyen aikin?" Malam ya sanyaya murya cike da nuna damuwa ya ce "Waye kwa banda mijin ki Kuluwa ni ne nan damuwa na yi da wannan takunkumi da jinnu suka miki, Allah sa dai abin nan ba da shi za ki rayu b... Bai kai maganar ba Kuluwa cike da jin haushi ta ce "A bakin ka wallahi, wannan ai mugun fata ne, wato in zauna a haka ka ji daɗin rabuwa da ni ka ce na zama makauniya, ko idan baka rabu da ni ba ma " Haule ta ce "Haba Kuluwa kina kife kamar ƙwarya amma bakin ki ba zai mutu ba" Banza Kuluwa ta yi da ita Hudu ya ce "Wannan aikin fa ba ƙarami ba ne kawai a kira malam me ruƙiyya" Kuluwa ta ce "Haba Hudu ni ce fa ba aljannu ne a jikina ba, kawai ɗanyen aiki suka mini idan ka kira mai ruƙiyya zai dakeni a banza ne" Haule ta ce "Wannan bokitin babu mai raba ki da shi in ba malam me ruƙiyya ba, idan aka musu karatu dole su saki bokitin" Malam ya ce "Kawai a kira shi" Ya faɗa a zuciyarsa kuma yana ayyana Allah sa ya mata dukan kawo wuƙa ko banza ya sake rama masa. Fita suka yi suka je gidansa aka kirawo shi, tsoho ne don har ya fara ranƙwafawa ma, sai wani mayashi da yake riƙe da hiramin nasa, Hudu ya wuce neman yaron nasa don haka daga Malam Nura sai Malam mai ruƙiyya da wannan matashin. Ko da suka shigo Haule tana tsaye a gaban Kuluwa, Kuluwar ta saka hannu biyu ta riƙe ƙafafun Haule wai tsoro take ji kar fa a je aljannun suna jikin bokitin. Ko da Malam mai ruƙiyya ya zo hannunsa riƙe da carbi mai dubu, yana zuwa da ya gama zagaya Kuluwa buɗar bakinsa ya ce "Aljanin me a cikin bokitin shi ne ya zama tsani tsakanin kanta da bokitin idan ma ba a yi a hankali ba yana iya raba kanta da jikin wuyanta" Kuluwa fitsari ne ya ƙwace mata jin wai aljani a jikin bokitin da yake manne a kanta da kuka ta rushe tana faɗin " "Malam ka yi addu,a su fita daga jiki, wallahi ban san inda zan saka rayuwata ba in suka rabani da kaina ba na so in mutu in bar Malam Nura ya rayu da amarya su soye ni ina can kwance cikin ƙasa!" Malam Nura a zuciyarsa ya ce 'Ƴar baƙinciki sai mun yi soyayyar kuwa da zamanki da tafiyarki babu abin da za mu fasa' A fili ya ce "Kuluwa ko kina raye ko kina mace ai zaman Hadiza matsayin matata babu fashi tun da an ɗaura aure, ki ji da wannan abun na kanki don idan har aljannun nan basu yarda an ɓamɓare miki wannan bokitin ba, ni fa kaina zan sa a yi yekuwa a gari, jama,a su zo a kwashe ki a baro a kaiki can dokar daji bakin ruwa, ƴan ruwa su ɗauke ki don ba za mu rayu da rabi da rabi ba domin kin zama rabi aljan rabi mutum" Baki ta buɗe za ta yi masifa duk da maganarta idan ta yi amsa kuwwa take kasancewar kanta a cikin bokiti yake. Malam mai ruƙiyya ne ya kai hannu yana mai yin bismillah ya ranƙwashi saman bokiti sannan ya saka hannu ya ja amma ya ji babu alamar fita. Yana kallon Haule ya ce "Babu wani ɗan icce ƙarami haka?" Da sauri Malam Nura ya ce "Akwai wata ƙatuwar sanda ta dukan ɓarawo da na ajiye a ɗakina" Kuluwa wacce ta san girman sandar cike da ƙaraji ta ce "Mai za a yi da sanda? Ana batun icce kana batun sanda, kaima malam mai ruƙiyya ina laifin ma ka ce a baka tsinken kwakwa tun da yanzu dai ni ce ba aljani ba kuma duk abin da za a yi ni zan ji a jikina" Ɗan rakiyar malam ya ce "Ai dole sai an basu tsoro in ba haka ba ba za su fita ba" Wani yawu ta haɗiye tana jin babu daɗi Malam Nura wani daɗi yake ji a ransa ya ɗakko sandar ya kawo, Malamin ya ce tun da shi ya manyanta ba ƙarfi ne da shi ba, shi ɗan rakiyarsa ya karɓa ya buga a jikin bokitin, amma Malam Nura ya ce "Malam ita mace fa a ko ina mijinta ne a gaba ka bari na buga mata ina kishin wani ya mata ab... Kuluwa ta katse da faɗin ",Malam kar ka yarda babu wata soyayya da kishi tsabar haushina ne da yake ji wallahi kana bashi sandar nan ba iya bokiti zai rotsa ba har da kaina zai raba a biyu" Haule ta ce "Kuluwa mene ne haka ana son nema miki lafiya" Tsaki ta ja ta ce "Ai kin san akwai takun saƙa tsakanina da shi" Malam mai ruƙiyya ne ya karɓi sandar ya shiga karanta ayatul kursiyyu da falaƙi da nasi yana tofawa a jikin sandar sai da ya gama sannan ya nannaaɗe hannun rigarsa ya buga sandar Kuluwa ji ta yi kamar a kanta ne aka buga, Malam yana ci gaba da karanto addu,oi, yana tofawa yana buga sandar lokaci zuwa lokacj ganin yadda take zabura kamar mai farfaɗiya ya sa yake danne dariyar muguntar sa tun da shi ya san mene ne ba aljannu ba ne. Bokitin ya tsaye a biyu amma ƙasan yana manne da gashin, aka yi aka yi ya fita amma ya ƙi, sai da aka duba ta inda aka tsaga domin yanzu tana iya ganin mutane ma tun da an fasa bokiti daga saitin idanunta. Kuluwa jin Mama mai ruƙiyya yana jan bokitin tamkar wanda yake jan gashin ta ta ce ",Malam gashin nan fa ana gama cire mini bokitin nan zan yi fakin ɗinsa da ribbon ka ga kuwa ka bishi a hankali" Takaici ne ya ishi Haule na maganar da Kuluwar take ita ana so a ceto ta amma ita tana ta gashi duk don saboda ta birge mijin da ba ita ce a gabansa ba. Malam iya yinsa ya yi amma ya kasa fitarwa Kuluwa bata ankara ba ta ji ya ce "Kun ga dai duk na cire bokitin gefe da gefe kawai iya tsakiyar kanta ne bai fita ba, shi kuma kamar ma tare aka yi shi da gashin kanta don haka mafita da shawara ɗaya a kira Usaini wanzam mai aski... Tun kafin ya gama magana Kuluwa wacce gabanta ya bada sautin rassss jin an ambaci wanzam ta yi saurin faɗin "Malam mai ruƙiyya aska zai ara maka ka yanke bokitin?" Malam mai ruƙiyya ya ce "A,a ni da ba aikina ba ne riƙe aska, shi dai zai so ya saka askar ya askr gashin kanki shi ne mafitar...Tsaye Kuluwa ta miƙe tana faɗin babu wanda zai masa aski babu mai raba ta da gashin kanta ko ziri ɗaya!" Malam mai ruƙiyya da ɗan rakiyarsa suka fara yi wa Malam Nura sallama za su tafi, Kuluwa har ta kama hanyar ƙofar ɗaki ta shiga ta je gaban mudubin ta ta duba ta ga babu alamar zai fita sai gata ta fito da sauri ta ce "Haule na shiga uku za a mayar mini da kai babu maraba da na Malam Nura" Haule ta yi tsaki ta yatsina fuska ta ce . "To ai sai ki zauna a haka" Tana faɗa ta yi hanyar ɗakin ta, Malam Nura ya ce " ,Malam tun da fita za ku yi mu je fita zan yi nima na je masallacin isha,i daman amarya sai gobe za ta tare, Kuluwa ta ji daɗi da aka ce sai gobe amarya za ta tare, tana ganin za ta ci karenta babu babbaka tun da ta yi gyaran jiki, duk da tana jin haushi ta so a ce a gaban amarya za ta shige ɗaki da angon ta cusa mata haushi. Kuluwa ganin za a barta da rufaffan kai ba don ta so ba ta ce ta amince a kirawo shi. Tun da suka fita ta zauna tana garƙama kukan za a raba ta da gashin ta, gashi aljannu ne tana son zazzagin su da musu Allah ya isa tana tsoron sakamako ya biyo baya. Suna fita Huale da ta fito daga ɗaki ta shiga bata baki, har tana tambayarta mai ya sa ta saka wandon malam amma ta mata banza tana ta kuka, don ta so take taje gashin nan tana cusawa Hadiza haushi, duk da an ce Hadizar tana da gashi kasancewar mahaifiyarta buzuwa ce. Haule tana gefe zaune a kan kujera zuciyarta cike da jimami kawai sai ta ji Kuluwa tana faɗin "Wayyo gashina, wayyo zan zama warewa a cikin matan gidan nan, wata ma da gangan za take tamayar fita kitso don in ji haushi" ,Haule tsabar takaici banza ta mata saboda ita a ganinta ita da ta haɗu da iftila,in aljannu ai murna za ta yi da za a raba ta da bokitin. Zuwa jimawa Malam Nura ya dawo yana rafka sallama shi da Usaini wanzam, Kukuwa ta tashi tsaye hannuwanta biyu a saman guntun bokitin na kanta tana kuka shaɓe -shaɓe Malam Nura a zuciyarsa ya ce 'Ke da Allah ya taimake ki ma ba ƙafafu na cirw miki ba, ai gwara gashi sau dubu in kika ɗaura ɗankwali babu mai sani amma aka mayar da ke gurguwa ai kin tagayyara. Haule ce ta shinfiɗawa wanzam tabarma bayan ta amsa musu sallamar ta gaishe da shi, ya zauna da ƴar zabirarsa (Jaka) Mai ɗauke da kayan askinsa. Kuluwa tana ta ɓare baki ta zauna a gabansa ya cw Haule ta kawo kujera saboda ya ɗan yi sama, haka ya zauna a kujera yana faɗin "Sannu baiwar Allah,, Allah ya tsayar a haka, wataƙila ma tun askin suna ba a saki miki aski ba amma gashi yau larura za ta saka a yi, Allah sa haka ne alkairi... Kuluwa ta ɗago tana banka masa harara ta ce "Ina alheri a aske gashin matar da ba iya kaɗai ba ce a wajen mijin ta, wato tana da kishiyoyi, gashin nawa da nake ta cancanawa ina alkin ta shi, ni ko da aka haifeni ba a mini aski ba saboda gashina bashi da yawa mahaifiyata ta ce a bar min amma yanzu za a aske" Usaini wanzam yana fito da kayan aikin ya ce "Ƙaddarar kenan" Daga haka bai sake cewa komai ba, Malam Nura yana gefe zaune a kan wata kujerar yana danne dariyarsa ya san da a ce ta san shi ne ummul aba,isin wannan lamarin da mai raba ta da shi sai Allah, duk da yana gudun ɓacin rana watarana amma ya san dai ba za ta taɓa ganowa ba. Bokitin ya ɗan ɓaɓɓalle, ya ɗakko ruwa da sabulu ya ɗan goga a gaban inda bai riƙw ba da yake tsakiyar kan ya fi riƙewa. Babbar askarsa mai kaifi ya saka ya shiga ɗaiɗaye gashin Kuluwa yana zubowa ƙafa tana kallo sai da ya aske duka amma ban da gefe da gefen Kuluwa ta kai hannu ta ji an mata rantal (ƙwal kwabo) A tsakiyar kan ta taɓa inda bai aske ba duk bai fi faɗin yatsan hannun ba ta ce "Wannan ɗin fa" Wanzami ya ce "Wai idan kin yi ɗaurin ɗankwali sai kike fito da shi kin san gashi adon mace ne!" Kuluwa kamar ta yi kuka ta ce "Saimka ce wata ƴar bori, za ka bar mini wani gashi kawai ka ƙarasa cirewa" Haka ya cire Haule tana ta jera mata sannu, yana gamawa ya saki kan Kuluwa tana zaune ta shafa da hannu ta ji wayam ta ɗago ta kalli wanzami, ta kalli Haule ta ce "Haule ki riƙe sannunki tun da ba naƙuda nake yi ba!" Tana faɗar haka ta tashi fuuuuu ta yi hanyar ɗaki, dariyar da Malam Nura yake ta riƙewa ce ta ƙwace tun lokacin da ya yi ido huɗu d akan Kuluwa a hasken farin wata, har ƙyallin haskena farin watan ake gani a jikin kan, tana daidai shiga ɗakin nata ya tsagaita dariyar ya ce "Kuluwa mai ɗakin tsaka, ɗakko masa kuɗin askin sa" Harara ta juyo ta dallawa Malam ya ce "Ga ki da riga da wando da askekken kai sai kika yi kamar namiji" Banza t masa ya fita shi da mai askin yana ta dariyae mai askin yana nuna masa rashin dacewar hakan, a fili ya nuna yankarɓa a zuciyarsa ya ce " Ai baka san wace ce Kuluwa ba shi ya sa' Haule ma tsintsiya ta sanya ta share gashin ta kwashe ta naɗe tabarmar tana ɗan murmushi ta san da a ce yau ita ce tsautsayin nan ya faɗawa da Kuluwa sai ta yi ta ƙyalƙyalar dariya. Kuluwa tana shiga ɗaki ta cire kayan ta canja wasu zauna tana ta addu,ar Allah ya sa aljanin nan ya yi wa Haule da Hadiza abin da ya mata don a dawo ɗaya!. Haka ta kwanra cike da takaici haushin Malam Nura take ji can zuwa jimawa ta ɗauro ɗankwali ta fito ta sake alwala ta yi ta yi sallolin ta ta kwanta, don ko sha,awar zuwa turakar Malam ɗin ba ta yi tun da aka mata aski, haka ta ringa murƙususun ciwon marar magungunan da ta sha!. Malam Nura bayan ya gama komai ya dawo gida, yana ɗan duƙawa, saboda mararsa da take riƙewa cike yake da buƙata amma babu hali tun da amarya tana gidansu, shi kuma don ita ya yi gyara don haka ba zai je wajen sauran matan ba. Haka ya ringa safa da marwa yana neman ɗauki amma daga karshe ya jiƙa jar kanwa ya sha ya samu dama-dama ya kwanta bacci ya yi awon gaba da shi cike da mafaekin tarewar Hadiza. Washe gari da fara,a ya tashi kasancewar yau ce ranar da yake mafarkin zuwanta, sannan ya fara lissafin zuwa amarya ya samu yake ɓanɓarar kuɗi ko ya maida gurbin da ta masa na kuɗaɗen da ya kashe. Da ya yi wanla ma tazugen ya saka a wandon shaddar ya saka ta don ita ce rufin asirin sa a kaf kayansa, wajen sha ɗaya ya je gidan su amarya bayan sun yi waya, sun yi magana cewar da yamma masu jera kaya za su zo. Daɗi kamar ya kar Malam Nura tana tambayarsa mai ya sa ya saka kayan jiya ya ce ai saboda tare suka ɗinka shaddar shi ya sa yake son saka kayan, ba ta san cewar kayan ne babu na kirki ba wannan ne ɗaya-ɗaya. Sun yi sallama ya kamo hanya yana ta fainciki, don da zai tafi har da ba Zainaba da Shafi,i ɗari biyar ya ce su raba, har yana kama hannun Shafi,i yana faɗin su yi sallama, har da cewa Zainaba sai watarana, ita kuwa Hadiza da bata ma gane mai yake nufi ba ba ta kawo komai ba. Kuluwa haka ta tashi da baƙinciki da takaici musamman da ta ga gashin kanta a shara da Haule ta zuba, ta so ake mata kitso ɗan gaban goshi tana yarfo gashin domin ta nunaw amarya cewar ba fa dangin buzaye ne kawai masu gashi ba, duk da ta san ba za ta taɓa kamo ta a gashi ba amma dai ta kwatanta sai kuma gashi aljani ya yi mata tsiya. Da yamma ƴan jere suka zo, Haule ta musu abinci da Malam Nura ya bayar a dafa musu da kuma cingam da kuɗin tukuici na jere dubu biyu. Ƴan jere suna jeru suna waƙa suna shewa, duk Kuluwa tana jin su, tana tsegumin abin da aka kawo na jeren daga windon ɗakin ta. Suka gama jera kaya tsaf suka yi wa Haule da take musu faram,-faram magana, Kuluwa kuwa yadda ba ta musu magana ba haka babu wanda ya kula ta bare ma ita da ta so shuka musu tsiya da ture ka ga tsiya za ta yi ɗaurin ɗankwali amma kuma ganin babu komai kan a saisaye sai ta ɗauri tamtam kar ma ɗankwalin ya je ya faɗi ya kunyatata a gaban dangin kishiya. Tun da dai ba ta ɗauki Haule a matsayin kishiya ba yanxu hankalin ta yana kan Hadiza. Hadiza da za a kai kaya ta haɗa kayan sawarta karkaf da na Zainaba da jakar Shafi,i shi ma da aka kwashe masa kayansa duka, yaro yana ta murna za su koma wani gidan a inda Zainaba take ta ƙiyasta irin ɗaukan maganar da za ta yi da irin kunna wuyar da za ta yi a gidan sabon mijin innarta. Malam Nura bai sna wainar da ake toyawa ba ta tarewa da agololi har guda biyu, shi ya sa ma ya basu ɗari biyar don ya san shi da su sai dai idan sun je ganin mahaifiyarsu shi ma idan bai basu fuska ba daga zuwa ɗaya ba za su sake marmarin zuwa ba. Yana ta washe baki, kasancewar ranar da aka ɗaura auren ce ranar da mai gasa kaju yake gasa kaji da yawa to ranar kuma amarya bata tare ba, ranar lahdin kuma duk babu kaji a wajensa, hakan ya sa Malam Nura ya je kasuwa ya siyo danƙareriyar kaza, ta kai wa mai gashin ya ce ya masa gashi mai shegen daɗi!. Ya hana kansa sakar yana ta ɗokin zuwan amarya, Hudu ya tsokane shi ya fi cikin carbi ya ce "Gaskia abokina Hadiza ta ciri tuta har da wannan zabgegiyar kaza haka?" Malam Nura ya yi dariyar mugunta ya daɗe yana dariyar sannan ya ce "Ka saka a ranka Hudu wannan kaza a jakar Hadiza za a fanshe ta, don ba zan sarawa jaki ciyawa ba, dole duk zan fanshi kuɗina a hankali" Hudu ya ce "Ni kuma gani nake Hadizar nan ta sha bamban da sauran matan da kake aura fa, anya za ta yarda a ci tuwo a kanta da alama za ta kwatawa kanta ƴanci ba, kuma ta wani ɓangaren sai in ga kamar ta fi Kuluwa masifa, kar fa su mayar da kai ƙwallon ƙafa,, waccen ta garo nan waccan ta garo can" Tsaki ya yi yana jaddada ƙaryarsu dubu!. Suna can da shi da Hudu har aka yi isha,i sannan ya je ya karɓo kazarsa da take ta ƙamshi, Hadiza sau uku ta kira shi tana jaddada ya sayi kazar amarci, yana tabbatar mata da cewar danƙareriya ma kuwa, tana ta masa rantsuwar cewar matuƙar babu kaza wallahi ba zai kwana a ɗakin ta ba, ganin yana maƙale da kazarsa ya tabbatar masa cewar ga kaza nan ma a haƙarƙarinsa, sanin ta yi tanadin gyaransu na mata tun da ya san duk amare suna gyara na musamman idan xa a yi aure ya shanye sauran magungunan sa yana ta tanadin yau!. Ko da motoci biyu da aka aika ɗakko amarya suka tafi sho yana can yana ta zuba surutu shi da su Hudu a majalissa. Kuluwa wacce ta sheƙa wanka ta sha turare ta sake shan kayan mata don ta tabbatarwa kanta ko za a mutu yau ita ce amarya ba Hadiza ba wato ita ce da miji. Haule tana lura da ita amma bata ce mata komai ba. Ta gama shiryawa tsaf ta kame a kan gadon ta tana jiran a yi wacce za a yi. Tana na zaune ta ji dirar motoci ana ta zabga guɗa ta yi gajeran tsaki ta gyara zaman ta, tana ayyanawa a ranta rigima uban wa ta kashe!. An shigo da amarya Haule tana musu marhaba, aka tafi da ita ɗakin ta, bayan jimawa can ƴan kawo amarya suka farawa amarya sallama suka fito suka yi wa Haule sallama suka tafi. Hadiza ta ajiye mayafi ta turo ɗaurin ɗankwalin sabuwar atamfarta da ta saka, ta ɗakko jakar Zainaba da ta Shafi,i ta ajiye a gefe ta fito daga ɗakin tana ƙarewa tsakar gidan kallo tana taɓe baki. Gaban Haule ta je ta tsaya ta ce "Barkan ki da gidaa" Haule ta amsa tana mata barka da zuwa don ta gane ita ce dai Hadizar Malam Nura, Kuluwa da take zaune ta kasa kunne jin wata baƙuwar murya ta yi saurin leƙowa ta windon Hadiza ta bata baya don haka a kan gashin da Hadiza ta yarfo kitson har gadon bayan ta ta yi wa idanun ta masauki, gaban Kuluwa ne ya bada dididiffff ta zaro ido, da sauri ta janye ɗankwalin ta daga saman kanta ta shafo kan jin ƙwal uwar kwabon da wanzam ya mata ta ce "Allah tsinewa Usaini wanzam, yanzu daga gashi ma za a fara ci na wasa" Ta faɗa tana komawa ta zaune ta ɗaura ɗankwalin tana tunanin mafita. Hadiza ta gyara tsayuwa ta ce "Ina ne ɗakin da su Zainaba za su zauna" Cike da rashin fahimta Haule ta ce "Su wace Zainabar?" Hadiza ta yatsina fuska tana mata nuni da Zainaba da Shafi,i da suke tsaye ta ce "Ƴaƴan Malam Nura mana "Haule ta ɗan yi jimmm a ranta tana danne dariyar ta a zuciyarta ta ce "Bantan uban can kayyasa!!! Yau ake yin ta anya Malam ya san da yara nan za a tare kuwa? Taɓ akwai daru" A fili ta ce "Ni dai ban sani ba sai dai ki jira dawowar mai gidan" Ko amsawa ba ta yi ba ta juya tana wata tafiya, Haule ta shige ɗakin ta tana jijjiga kai alamar Malam ya ɗakko ruwan dafa kansa garin aure-aure. Yana can yana washe baki lokacin da direbobin kai amarya suka kira shi suka ce sun cika aiki. Waya ya ɗaga yana washe baki ana ta masa kirarin ango Hadiza ya kira lokacin ta fito daga ɗakin ta tana duba randunan ruwan da aka kawo mata ko an zuba ruwa, ɗagawa ta yi yake tambayar ta ta zo lafiya ta faɗa masa, na ya shiga tambayar ta tana ina ta faɗa masa tana ɗakin ta, ya ce ta koma ɗakinsa, Kuluwa da take tsaye ta kasa kunne tana jin wayar da suke ta ji tana cewa "Ai ni ban san turakar taka ba" Daga ɗaya ɓangaren ya faɗa mata inda ɗakin yake, ya ce mata ba a kulle yake ba a buɗe yake sannan ya ce gashi na zuwa ta jira shi. Kuluwa tana jin ta tana cewa to shikenan bari ta je turakar. Amma tana gama wayar a fili ta furta "Ai wallahi babu turakar da zan je sai dai idan ka zo ka nunawa ƴaƴana ɗaki sun kwanta " Ta faɗa tana ci gaba da abin da take, tasowa ya yi ya kamo hanya ya zo ƙofar gida kenan ta kira shi twke tambayarsa ya siyo ruwan roba mai sanyi tana jin ƙishirwa?Wannan karon ma a kan Kunne Kuluwa amsa mata ya yi da cewar ya manta lemo ya siyo, sai ta ce to ya taho da shi, har ya kashe wayar ya sake kira yake tamabayar ta tana turaka, a kan kunnen Kuluwa ta amsa masa tana turaka!. Tana gama wayar ta koma ɗakinta, Malam Nura gudun kar ya tafi da kaza na da lemo ganin taro ɗan maƙotansu ya ce "Hashimu ungo ledar nan ka je ɗakina amarya tana ciki ka bata!" Hashimu ya karɓa cike da ladabi. Kuluwa wacce tarar aradu da ka ta sanya ta fitowa ta lallaɓa ta tafi turaka ta zauna, don ta rantse yau ita za ta kwana da miji, duk bala,in da za a yi kuwa. Tana shiga ta zauna, Hashimu da ya shigo da sallama amma babu wanda ya amsa kasancewar Haule har ta kwanta bacci, Hadiza kuma tana ji amsawa ne ba za su yi ba ita da yaran ta, ganin hakan ya tafi ɗakin Malam Nura ya tsaya ya yi sallama, Kuluwa ta maƙe murya ta amsa yadda ba zai gane ta ba don ya san muryarta yana miƙa ledar ya ce "Amarya wai gashi in ji Malam" Hannu ta miƙo ta karɓa tana amsa masa yana bata ya juya ya fita daga gidan. Rashe-rashe ta zauna a tsakar ɗakin, ta buɗe lafiyayyar gasasshiyar kazar nan ta buɗe robar lemo ɗaya, ta shiga yi wa kazar cin ƙasƙanci tana korawa da lemo. Malam yana zuwa shagon ya siyo ruwan ya taho amma wasu abokansa da suka tare shi, su suka sanya ya ɗan jinkirta duk da hankalinsa yana gun amarya, har hannunsa yake shinshinawa a hanya yadda hannun ya riƙe ƙamshin kazar nan saboda tsabar riƙon da ya mata ta daɗe a wajensa. Yana shigowa zaure ya tsaya ya rufe ƙofar ya saka sakata sama da ƙasa, ledar ya ajiye a ƙasa ya ɗaga hannuwansa sama ya yi wata uwar miƙa ya ɗauki ledar yana murmusawa a zuciyarsa yana faɗin 'Hadiza ta yau ta dawo mallakina za ta kwana a gidana, an bar wannan shegun yaran fitsararriyar Zainabar wannan ai zan nuna musu yanzu uwar tasu a ƙarƙashin take fuskar zuwa gidan nan ma ba za su samu ba!" Wasa farin girki ya zaman zai kasance, Kuluwa ta tari aradu da ka ta cinye kazar amaryar da malam ya sha wahala ya siyo ta ɗanya ya bayar aka gasa ya biya kuɗi duk don a mori amarci, kar fa kuluwa ta sake laifi a karo na biyu, ga kuma agololi har biyu sun tarw a gidan malam nura da sai yanzu zai yi arangama da su, ga Hadiza ta shigo da zafin ta, shin tsakanin Malam da Hadiza waye zai ci moriyae auren da ya yi shin ita ce za ta samu kuɗin daga wajensa ko kuwa shi da ya ɗora rai, anya zaman zai je ko ina, ya batun zaman kuluwa a gidan, shin zai samu damar ci gaba da aure-auren sa? Amsar tana cikin ci gaban labarin domin mu yi tafiyar da ke ki tura 700 ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay don ki shiga grp mu gama har ƙarshe idan na kammala cmplt docment 1k ne. Mutanena na niger za ku tura 700 ta 88630104 issaka issofou nita ko amana shaidar biya ta 09025576222 MAMAN AFRAH