[11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LrTZNGwF35IKXX4sLRvFug *GABAR CIKIN GIDA* *ƊANƊANO ƊANƊANO* Mama Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Numfashinta ne yake barazanar ɗauke wa, tana ta fafutuka da rayuwarta yayin da ƙafarta ɗaya ke duniya ɗaya ke lahira. Maganinta take nema ba ta ganshi a cikin ɗakin ba, drawar da ta san tana zuba magungunan a ciki ba. Ta duba ba komai a ciki, dakyar ta iya miƙewa ta ƙarasa bakin ƙofar ta buɗe ƙofar,tana buɗe wa ta ji numfashinta ya ɗauke ta zube a wajen. Numfashinta ta janyo da ƙarfi tana kwance wajen ta sauke idanunta akan wan mahaifinta wanda suke kira da Abba da ƙanwar mahaifinta da ƙasar mahaifinta wacce suke kira da Aunty Lailai. Da 'ya'yansu suna kallonta suna murmushi. Can ta hangi maganinta a saman Centre carpet, da rarrafe tana jan jiki ta ƙarasa wurin maganin, ta miƙa hannu za ta ɗauka sai ƙanwar mahaifinta ta take hannun tare da cilla maganin ƙasar kujera. Hawaye ne ke zuba daga idanunta ta kalli ƙanwar mahaifinta da ta take mata hannu ta yi mata alamar da ta yi haƙuri ta bari ta ɗauki maganin. Ba tare da tausaya wa ta cilla maganin ƙarƙashin kujera. Sanin cewa za ta iya dauko maganin ne ya saka ta tura hannu ta fito da maganin tare da watsa mata kallon tsana, tana bin ta da ido har ta haura upstair hannunta rike da maganin, yaranta biyu Kausar da Nabeela suka mara mata baya. Zafafan hawaye ne suka fito mata da idanunta ta mayar da kallonta ga wan mahaifinta kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kai ya nufi part ɗin sa. Numfashinta ke sama da ƙasa sai ya yi kamar zai dauke sai ya dawo kamar tana janyo shi suna kokawa da shi. Ga ƙirjinta dake sama da ƙasa. Kwanciya ta yi sa saman tiyel ɗin falon duk da ciwon baya son sanyi a haka tana jan jiki ta ƙarasa ƙodar ɗakinta ta na shiga ta tuna wayarta na falo tare da maganinta ta barshi, a haka ta koma tana jin numfashinta kamar zai bar gangar jiminta gabaɗaya. Tana zuwa ta ga Yaa Mansur yana shigowa falon, kallonsa ta yi da idanunta da suka zubar da hawaye tana mika masa hannu alamar taimako take nema, kau da kansa ya yi tare da cewa. "Shegiya dama ki mutu kowa ya huta, ko za mu yi farin ciki a gidan." Sanin cewa ciwon baya son sanyi amma sai ya ƙure gudun A.C dake falon wanda hakan ya sa ciwon mata ƙara tsananta. Haurawa ya yi sama yana cewa. "Ina jiran jin daddaɗan labarin mutuwarki, duk wanda ya far sanar da mu sai na masa kyauta mai tsoka." Wayarta ta hango a ƙasan center tables inda ta ajiye tare da maganin. Tana jan jiki ta ƙarasa wajen tare da ɗaukar wayar. Lambar ƙawarta A'isha ta lalubo daƙyau ta danna kira har ta yi mata 3 missed calls ba ta ɗaga ba daga nan daga nan ta ajiye wayar tana kwance tana kallon wayar ƙirjinta na sama ƙasa numfashin na yi kamar zai dauke gaba ɗaya saboda sanyin A.C ya yi yawa. Wayar ce ta kawo haske alamar kira ya shigo, duk da ba ta duba ko waye ba ta danna ɗaukar kiran, ta kasa magana sai sautin numfashinta. Cikin wayar ta ji muryarsa yana cewa. "Assalamu alaikum, Fatima Zahrah kin manta yau muna da lecture ƙarfe tara ba ki zo ba ga shi har loka..." Ƙasa ƙarasa wa ya yi da maganar sakamakon jim sautin numfashinta tare da ajiyar zuciya. "Subhanallah ciwon ne ya tashi?" Ba ta iya magana ballantana ta masa masa. "Ya Salam kuma na san Umminki ba ta dawo ba ko, kin ga ina zuwa." Katse kiran wayar ya yi yayin da numfashinta ya tsaya cak, ba ta motsi kwata-kwata. Wani babban Mention mai matukar girma da tsaruwa, girmansa ya kai unguwa guda. Tun kafin ki ƙarasa Mention din za ki ga symbol inda aka rubuta *ASADULLAH MENTION* zagaye yake da security dake kula da wajen. Mai daidaita sahu ne ya ƙara so mention tun daga nesa take ce masa ya tsaya amma bai saurare ta ba yake ƙoƙarin ƙarasawa bakin gate ɗin. Hannu da ya ga wani security ya ɗaga masa alamar ya dakata daga can ne ya sa ya dakata. "Haba Mallam ina ce maka ka dakata ina za ka ke haka, ka san ba'a bari a ƙarasa wajen ko?" "Yarinya meye alaƙar ki za Mention ɗin?" "Aikatau nake yi." Ta bashi amsa a takaice, ya sake ce mata "Ina son shiga cikin wajen nan ne ko Allah zai sa na yi ido hudu da ɗan albarka, duk da na ji an ce baya ƙasar. "Wa kake nema." "Sir Asadullah nake so na gani ido da ido ko..." Tsawa suka ji an daka masu wani security dake ƙarasowa wajen yana cewa. "Who is there!?" Da sauri ta mika masa kudin tana cewa. "Baba ka tafi." Ta fito daga cikin napep ɗin yayin da mai napep ɗin ya juya, ganin ta ya sa security ɗin komawa. Gaishe su ta yi ba wanda ya amsa mata kamar dai kullum, gate suka bude mata ta shige. Gidajen dake cikin Mention ɗin suna da yawa kuma kowanne ya hadu iya haduwa, kana ganin wajen ka san an narka dukiya a wajen. Wanda ya fi kowanne tsaruwa ta nufa, ɗaga kai ta yi tana kallon upstair na gidan tun kafin ta shiga. Alhaji Ahmad ta hanga yana sanye da medical glass, hannunsa rike da jarida yana karantawa. Sauke kanta ta yi ya nufi main falo, kasancewar safiya ne masu gidan ba su tashi da wuri don haka ba ta yi mamakin ganin ba kowa a falon ba. Sai sanyin A.C da ƙamshi dake tashi a falon. Kai tsaye ta nufi sashen da take aiki, kamar an ce ta juya sai ta hangi Doctor da wanda yana yawan ganinsa ya zo ɓangaren Sir Asadullah. Sai dai yau ta ga ya nufi wani ɓangare wanda tunda ta zo gidan ba ta taɓa zuwa wajen ba, don ba ta ma ganin ko masu gidan na zuwa ɓangaren. Ganin da ta yi Doctor ɗin na waige-waige alamar rashin gaskiya ne ya sa ta yi tunanin bin bayansa. A hankali take sanɗa tana bin bayansa har ya ɓacewa ganinta, ko da ta ƙarasa wajen ta kasa gane wane ƙofar ya shiga. Sai ta lura da ƙofa ɗaya dake buɗe. Don haka ta ƙarasa a hankali jikin ƙofar tana leƙe. Gabanta ne ya yi mummunar faɗuwa sakamakon ganin Sir Asadullah a cikin ɗakin an ɗaure masa hannaye da ƙafarsa da wata doguwar sarƙa. Toshe bakinta ta yi da hannayenta biyu tana kallonsa. Da ba don ƙwayar idanunsa da suka kasance ruwan ash kamar na mage ba da ba za ta yi saurin gane shi ba, don ganin yadda ya canza mutum mai tsantsar kyau, kwarjini da cikar haiba.Yadda ya dawo. Wayar Doctor ɗin ne ya yi ruri, ya ciro daga Aljihun suit na rigarsa, ƙara wayar ya yi a kunne. *Prison/Gidan yari* Zaune yake a saman gadonsa kasancewar a gidan yarin ma shi yana V.I.P ne komai nasa shi kaɗai aka ware masa, ƙaramin falon da wasu kujeru ga bedroom a ciki. Sabanin sauran wadanda ba vip suke ba da suke ɗaki ɗaya a cakuɗe da juna. Don shi hatta abincinsa ma siyo masa ake yi baya cin abincin da sauran prisoners ke ci. Zaune yake a bakin gadon kare da waya a kunnensa ya danna kira. Ana ɗagawa ya fara magana cikin fusata yana cewa. "Wai Doctor meye amfanin aikinka, kullun sai na sa an kawo mani jarida ina jiran na ci karo da labarin wanann matashin ɗan kasuwa Asadullah ya mutu amma shiru nake ji me ye haka!?" Doctor dake kallon Sir Asadullah ya ce. "Wai gaggawan mene ne kake yi?" Jidderh dake laɓe jikin ƙofar tana kallon Dr amma ba ta jin maganar da na cikin wayar ke faɗa. "Ka ga ka kwantar da hankalinka ba kai kaɗai ke son ganin bayan Asadullah ba a cikin gidan nan ma maƙiyansa ne zagaye da shi. Kuma sun yi mani tayin makudan kuɗaɗe idan na kashe shi, so ka bi komai a hankali, yanzu haka allurai da magungunan da nake bashi a hankali suke raunana jinsa da ganinsa za su yi masa illar da zai yi rayuwar da gwamna mutuwaraa ma akan rayuwarsa domin rayuwa ce mara amfani. Ka jira lokaci." A fusace ya ce. "Ba zan iya ba! Ka san cewa Asadullah shine mutumin da ya saka aka kama ni ƙarshe gani a gidan yari duk sanadinsa. Ya yi fatali da dangantaka dake tsakani na da shi, ina kiransa da sunan Yayana shi ma ƙaninsa yake kira na ko sunana baya kira amma dan na aikata wani laifi wanda zai iya yafe mani amma ya haɗa ni da hukuma ya mance dangantaka dama ɗan uwa zai iya tura ɗan uwansa prison? Wallahi sai na ɗauka fansa kuma rayuwarsa ce fansa a gare ni." "Ka kwantar da hankalinka yallaɓai." "Wane kwantar da hankalin zan yi ka san yadda rayuwar gidan yari yake rayuwar ƙaskanci da rashin 'yamcin da ya saka ni abu ne mai sauki? Idan har ba ka yi masa alluran guba ya mutu nan da kwana biyu ba to za ka ga abinda zan aikata maka duk da ina rufe kuwa." "Na sani in sha Allah za ka ji kyakkyawar labari, ka san sai mun iya takun mu, kasancewarsa babban mutum sananne kuma idan ba ku da kuka saka ni aikin ba babu wanda ya san yana ƙasar nan, kowa ya ɗauka yana waya ƙasar wajen harkokinsa. Hatta bodyguards ɗin sa na ji suna magana kan cewa wai Sir Asadullah bai taba tafiya shi kadai ba sai ya je da na hannun damansa, kuma sauran guard ɗin ma sai ya samary da su zai yi tafiya. Amma wannan karon ace ya yi tafiya shi kadai kuka ba wanda ya ga fitansa su ba su yarda ba. Ka ga dole mu bi a sannu , na fada wa Hajiya haka ita ma ta damu akan kashe shi." "To ni dai ina jiran jin labari mai daɗi ne kawai." Yana gama fadar haka ya katse kiran wayar tare da shafa gemunsa yana dariya. Bayan Dr ya mayar da wayarsa a Aljihu ne ya kalli Asadullah ya ce "Ka yi mani alkhairi da dama a rayuwata kai mutumin kirki ne matashin da al'umma ke bukatar irin ka, amma ke bukatarka, ama dole na aiwatar da aikin da aka saka ni don tseratar da rayuwata da iyalina." Sir Asadullah kallon Dr yake yi kuma yana kallon Jidderh dake laɓe, kasancewar Dr ya bawa ƙofar baya ya sa baya ganinsa, sai dai da alama baya fahimtar komai baya cikin hayyacinsa sai lumshe idanu yake yi kamar mai maye. Wani allura ta ga Dr ya ciro sirinjin da ruwan alluran a ciki ya ciro. Yana soka masa a jijiyar hannu sai ya wani zabura ya miƙar da jikinsa sai jikin ya fara rawa kamarazari kafin kuka ya saki jiki ya kumshe idanu. Ganin Dr yana hada kaya alamar zai tafi ya sa Jidderh ta yi saurin barin wajen a guje ta nufi ɓangaren da take aiki. Hawaye ne kawai ke bin fuskarta na tausayin wannan bawan Allah. Mansur tunda ya katse kiran wayar ya tabbatar ciwon Fatima Zahrah ne ya tashi. Don haka hankalinsa ba ƙaramin tashi ya yi ba don yana tausayin yarinyar. Department ɗin ƙasar Fatima Zahrah ya nufa. Wato A'isha, daidai lokacin take ƙarasowa da motar ta a wajen. Bayan ta yi parking ne ta fito daga cikin motar yayin da Mansur ya fito daga cikin motar. Ganin yanayinsa ya sa ta ce. "Lafiya ya na ganka a firgice?" "Ba lafiya na kira wayar Fatima Zahrah ta daga amma ta kasa magana da alama ciwonta ne ya tashi don dai..." "Ba lokacin dogon bayani zo mu tafi gidan nasu." Shiga suka yi cikin motar da sauri ta ja motar suka bar jami'ar. Dama ke nake so na gani saboda na san baki da shamaki da gidan,don dai idan ni ne ba bari za'ayi na shiga cikin gidan ba. Musamman idan wannan Yayan nata sojan yana gari sai ki ga gidan zagaye da sojojinsa. "Okay Yaa Hilal kake nufi ko?" "Eh shi nake nufi ko ba Yayanta ba ne?" "Eh cousin brother nata ne, mahaifinsa shi ne wan mahaifinta ne." Gudu take yi akan titi har suka iso katafaren gidan . Kasancewar security sun santa sosai kuma Alhaji Babba ya basu damar indai ta zo a barta ta shigo kai tsaye babu shamaki ya sa suka bude mata gate ta shigar da motarta ciki. Ko parking space ba ga nufa ba saboda ta san halin da aminiyarta ke ciki. Har can wajen main door ta yi parking, a tare da Mansur suka fito. Knocking take yi ta ji shiru, zuwa lokacin ma Fatima Zahrah ma ta suma ita kadai ce yashe falon kamar gawa. A'isha ta bude kofar sannan ta leƙa ganin ganin ba kowa sai Zahrah dake kwance ba ga motsi ne ya saka ta juya cikin tashin hankali ta kira sunan Mansur tare da masa alamar ya ƙaraso. Da hanzari ya ƙaraso wajen suka shiga taimaka mata ya yi suka dauke ta suka sanya ta a bayan motar. Key A'isha ta yi wa motar suka bar gidan a guje. Cikin damuwa Mansur ya ce. "To ina mahaifiyarta take ne?" "Ka mance ta fada mana sun tafi Saudiya aikin umara ita da mahaifinta." "Okay na mance sai yanzu na tuna fa, amma yadda Zahrah take ba isashshiyar lafiya ba ai bai dace ta zauna a wannan gidan ba. Gidan da suka kamar maƙiyan juna suyi ta gaba da juna ko wani na bukatar taimako sai dai ya mutu ba wanda zai kalle shi. Kuma babu bare a gidan duk ƴan uwan juna ne dangin juna jini ɗaya. Wanan al'amarin wannan ahalin yana ɗaure mani kai." Haka dai suke ta jimama lamarin har suka ƙarasa wani asibitin kudi dake kusa da su. Taimakon gaggawa aka fara ba ta bayan sun yi nasarar farfaɗo da ita ne aka sanya mata oxygen. Mansur ma da A'isha suna asibitin sun manta da wani school ma saboda hankalinsu na ga ƙawarsu. Har yamma suna tare da ita ba tare da sun leƙa school ba. A'isha ce ta kwana da a asibitin bayan ta kira iyayenta ta sanar da su. Washegari aka sallame su tare da ba ta magunguna bayan an yi mata allurai. A'isha ta yi driving ɗin ta har gidansu ta yi horn. Ganin sojoji da yawa ne ya sa suka gane cewa. Yaa Hilal ne ya dawo. Parking ta yi a parking lot tare da kallon Fatima Zahrah ta ce. "Besty zan barki a nan don wadannan murɗa-murɗan sojojin ba na son ganinsu, na San yanzu ma ogan na su na ciki." Godiya ta yi mata sannan ya fice daga motar, ita kuma ta motar ta tafi. Cikin yanayin sanyin jiki irin nata take tafiya. Ta nufi main door. Tana rike handle ɗin ƙofar ta ji hayaniya na tashi daga falon, Hango su ta yi sun hallara a babban dinning area, Yaa Hilal ne suka zagaye ƴan matan kowacce na cewa ita ta girka masa na ta zai ci. Har suna kokawa kowacce so take ya karbi plate da ya zuba masa abincin da ta girka masa. Musamman Aunty Nabeela wacce kowa ya san irin son da yake masa, shi ne bai bayar da fuska ba amma soyayyar ta gare shi ya kasa ɓoyuwa, duk da cewar A Kausar ma tana son sa amma ta iya ɓoye nata. Da sallama ɗauke a bakinta ta shigo falon, dukkansu suka juya suna kallonta ba wanda ya amsa mata sallamar sai Yaa Hilal. Sauran kallon tsana ne suke jifanta da shi tare da mamakin yadda aka yi t warware Haka alhalin ba ta iya fita. Jin muryar Yaa Hilal ya amsa mata sallamar ne ya saka ta kalle shi tare da cewa. "Yaa Hilal ina wuni ka dawo lafiya?" Bai amsa mata ba ballantana ya kalle ta. Ba ta yi mamaki ba don ba yau ya fara ba, kuma halinsa ne. Tafiya take a hankali ta nufi part ɗin mahaifiyarta hannunta rike da jakar magungunan da aka bata. Da _Jidderh_ Yau daƙayar ta iya aikinta tun da ta ji ana shirin kashe Sir Asadullah. Ko da ta kammala aikinta ba ta tsaya ɓata lokaci ba ta fice daga gidan. Tafiya take yi tana saƙe-sake hawaye ne cikin idanunta. Yau kam ba ta tsaya tare mai adaidata sahu na ta tafi da ƙafa duk da nisan wajen da unguwarsu. Daga ganin unguwar ta masu matsakaicin ƙarfi ne, dan duk gidajen dake layin na talakawa ne. Wani karamin gida ta shiga bakinta dauke da sallama. Wata dattijuwar mata mai kimanin shekaru arba'in da biyar tana zaune a kujerar tsuguno tana tankaɗe garin tuwo ta amsa tare da cewa. "Hauwa kuluwa har kin dawo?" Murmushi Jidderh ta yi tare da cewa. "Eh Ummata." Kallo ɗaya Umman ta yi mata ta gane cewa tana cikin damuwa. "Jidderh akwai abinda aka maki a can ne?" Kuka ta fashe da shi tana cewa. "Ummata kashe shi suke son yi." "Waye za su kashe kuma me ya yi masu su waye za su kashe sh?" "Umma mutumin da ya zama bango ga al'umma suke son ganin bayansa. Bai da wata illa a rayuwarsa yana da kirki da son taimakawa marasa ƙarfi, Allah na kawai ya san yawan adadin mutanen da suka yi arziki ta sanadiyyarsa Umma ki duba yawan mutanen da yake taimaka wa, hatta su ɗin na jikinsa da suke ƙoƙarin ganin bayansa a gidansa suke zaune cikin rufin asirinsa suke ci suka sha suke komI na rayuwa. Amma. Suke neman ganin bayansa. Wallahi zan taimaka masa ba za su taba nasara ba sai na binciko su na tona asirinsu." "Kun ji shashasha wawiya an fada maki karo da masu kuɗi wasa ne? To maza-maza ki bar zancen nan kafin su farga dake su saka ki a dogon barci" Wani matashin saurayi mai kimanin shekaru ashirin da biyar yake da lokacin da ya shigo gidan. "Yaya wallahi ba ka ga yadda ya koma ba ne." "Jidderh abinda ya kai ki shi za ki bana son shiga abinda ba ruwan ki." "Yaya da ruwana kuma sai inda ƙarfina ya ƙare." *CIGABAN WANNAN LITTAFIN ZAI ZO MAKU A RANAR BIYAR GA WATAN DA ZA MU SHIGA IN SHA ALLAH. 7/5/2025 BA ZAN CE NA FI KOWACE MARUBUCIYA IYA RUBUTU B,AMMA TABBAS ALƘALAMINA NA DA KAIFI KUMA NA MUSAMMAN NE. KUN GWADA KARANTA LITTAFAI NA KUN GA SALON RUBUTUNA KUN GANI KUN YABA MANI, NI KUMA IN SHA ALLAH NA ZA KU YI NADAMAR BIBIYATA BA. NA GODE DA YABO DA KUMA ADDU'AN KU A GARE NI, ALLAH YA BAR ƘAUNA.* [11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LrTZNGwF35IKXX4sLRvFug *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) .*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page2️⃣ "Yaya da ruwana kuma sai inda ƙarfjna ya ƙare." "Au haka kika ce?" "Ko na rasa rayuwata akansa ban damu ba in dai shi zai rayu. Saboda shi bango ne da al'umma da yawa suka jingina da shi, rashin rayuwarsa zai zama sanadiyar shigar wasu cikin wani hali, ceton rayuwarsa tamkar ceton al'umma ne. Wannan ma kaɗai ya ishe ni abun alfahari." Ajiyar zuciya Umma ta sauke tare da kallon Isah ta ce. "Ka rabu da ita kawai je ka shirya ka tafi wajen aikinka." Ba musu ya bar wajen ya nufi ɗakinsa. _Fatima Zahrah_ Tana shiga ɗakinta ta gan shi a yamutse alamar an yi mata bincike. Drawar da take zuba magungunanta ta bude ta zuba su sannan ta fara gyara ɗakin da aka hargitsa mata. Bayan ta gama ta karkaɗe gadon ta kwanta bakinta ɗauke da addu'a. Wayarta da ta ajiye gefen filo ta soma ruri. Ganin lambar ya saka ta ɗaga tare da cewa. "Ummina barka da warhaka." "Barka dai Zahrah tawa ya kike?" "Ina lafiya Ummina." Ta yi maganar cikin raunin murya. "Na san ba za ki taba jin dadin zaman gidan nan ke kadai ba, kuyi haƙuri in sha Allah next week za mu dawo?" "To Allah ya dawo da ku lafiya ya karɓi ibada." "Amin ya Allah, kin ci abinci Kuwa?" "A'a." "Ki je ki ɗebi abinci ki ci na San yanzu masu girkin sun gama ." "To Ummi ina su Abi da su granny?" "Suna can suna ibada, na ji hankalina bai kwanta da har mafarkinki na yi shi ne n kira na ji lafiyarki." Mumrmushi ta yi tare da cewa "Ina lafiya Ummina." Sallama suka yi sai ta ajiye wayar tare da miƙewa tsaye ta nufi ƙofar fita. Tana zuwa babban falon gidan ta nufi hanyar kitchen kai tsaye. Tsawar da aka daka mata ne ya sa ta juyo tana kallon Hajiya Maimuna matar wan Babanta. "Gidan uban waye za ki je a wajen?" "Dama yunwa nake ji shi ne zan ke na ɗebi abunci na ci." "To yau dai ba za ki samu cin abinci a gidan ba. Domin masu aikin da ke girka abincin kina ci yau mun hutar da su. Saboda zuwan Babban yaronmu, kasancewar Hilal baya son abincin masu aiki. Don haka wannan abincin haramiyarki tunda ba da uwarki aka shiga kitchen ɗin ba." Cikin sanyi jiki ta juyo ta kalle kowa da ke wajen, duk suna nan sai dai wannan karon ba ta ga Yaa Hilal ɗin ba. Cikin sanyin jiki ta koma part ɗin Umminta. Hijabinta ta saka har ƙasa kamar yadda shine shigar da take yi idan za ta fita. Ta ɗauki handbag ɗin ta da makullin motarta. Fitowa ta yi sanye da hijabi a hankali take tafiya zuwa lokacin kowa ya watse a babban falon gidan. Taku ta ji daga upstair ɗin tana juya wa idanunta suka sauka akan Yaa Hilal yana sanye cikin wando na uniform ɗin su sau sai farar T-shirt mai dogon hannu. Cikin takunsa na isa da ƙasaita da kaga idanunsa ka ga zarra ƙirar jikinsa irin na jarumam mazan nan ƙarfafa saboda yawan motsa jiki da yake yi . Cigaba ta yi da tafiya yayin da yake bayanta. Tunawa ta yi da wata rana ƙanwarsa Maryan ta shiga gabansa tana tafiya kawai sai ya janyo ta tare da hankaɗa ta ta fadi a saman tiyel ta fasa goshi. Tunawa da hakan Fatima Zahrah ta yi ƙanwarsa da suka fito ciki ɗaya ya ji mata haka ballantana ita da ta zamo kamar mujiya a wajensu. Da sauri ta matsa jikin bango don bashi hanya. Ko kallonta bai yi ba ya wuce abinda ya barta da ƙamshin turarensa. Bayan ta fito ne ta hangi ficewarsa gidan shi da sojojinsa. Parking lot ta nufa ta shiga motarta har ta yi mata key kenan sai ga kira ya shigo wayarta . A'isha ce ƙawarta ke kira bayan ta isa gida. "Assalamu alaikum." Daga can ɓangaren A'isha dake zaune a falon mahaifiyarta ce ta ce. "Wa'alaiki salam, ya jikin naki?" "Alhamdulillah." "Kin ci abinci kin sha magana kamar yadda Dr ya faɗa?" "No yanzu dai zan je restaurant na siyo." "Akan me ba kuna da masu girki har mutane uku ba?" Mumrmushin takaici ta yi tare da cewa. "Kin san ɗan gatan gidan ya dawo, kuma baya son girkin masu aiki aiki, shine suka ce masu aikin su bari su ne za su girka. Na je zan ɗebi abinci shi ne mahaifiyarsa ta hana ni saboda ɗanta aka girka." Cikin fusata A'isha ta ce. "Ji wani maganar banza, yadda fa suka takama da gidan kema dole ki yi, shi ɗangatan na su ai gidan kakansa da ya haifi ubansa ne kema haka gidan kakanki da ya haifi Babanki matsayinku ɗaya akan me za su nuna maki wariya?" "Kada ki damu da Ummina na nan da dole za ta bani abincin da zan ci." 'kin ga ki koma gida kawai bari yanzu zan kawo maki abinci, kin ga ba ki da lafiya Please kada kuyi driving a cikin wanna hali ." Godiya ta yi mata sannan ta fice daga motar ta kashe ta cire key. _Jidderh_ Gabaɗaya ranar ba ta yi barcin kirki ba saboda halin da ta ga Sir Asadullah a ciki. Kamar kullum bayan ta yi sallar asuba ba ta koma barci ba, ayyukan gidan ta yi kamar yadda ta saba yi. Bayan ta kammala ta yi wa Mahifiyarta sallama ta nufi hanyar titi don yau da ƙafa za ta tafi saboda ba ta da kudin abun hawa. Hakan ya sa ta bar gidan da wuri yau. Tana tafiya hankalinta na ga wajen uban gidanta, sai jinjina lamarin take yi a zuciyarta. *SHEKARU BIYU DA SUKA WUCE* Da misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe motocin sir Asadullah suka shigo harabar kamfaninsa. Kai tsaye motocin suka nufi parking space, motoci ne guda biyar biyu a gabansa biyu a bayansa sai wata hadaddiyar mota dake tsakiya, ita ce wacce Sir Asadullah ke ciki. Security ne tsaye ƙikam a parking space ɗin. Bude masa murfin bayan motar direbansa ya yi ya fito yana gyara zaman rigar suit ɗin da ke jikinsa. Ya wuce ciki yayin da amintaccen bodyguard ɗin sa wato Sulaiman ya take masa baya har zuwa hanyar da za ta sada shi da office ɗinsa. Secretary ɗin sa ta miƙe ta ce. "Good morning welcome sir, your friend is here to see you ilet him in as per your request anytime your friend are around I should always let them in." "Okay." Ya faɗa yayin da ya shiga office dinsa bayan bodyguard ɗinsa Sulaiman ya bude masa ƙofar office ɗin ya shiga. In da ya samu abokinsa Sagir zaune a office ɗin yana jiransa. Bayan sun shiga ne Sulaiman ya tura ƙofar office ɗin. Sir Asadullah ya wuce wajen hanger ya cire jacket ɗin dake jikinsa ya yi hanging ɗin jacket ya bar shert dake jikinsa. Zama ya yi a mazauninsa ya zauna yana kallon Abokin nasa ya ce "Sagir ya aka yi ne daga ina haka da safe? Okay sorry ba mu gaisa ba ko?" Ya yi maganar yana murmushi , shi ma Sagir ɗin murmushi ya yi tare da cewa. "Ban sani ba." _Fatima Zahrah_ Fitowar ta kenan daga cikin ɗakinta tana sanye da hijabi hannunta rike da waya ta kara a kunne tana cewa. "Okay ga ni nan fitowa ba bari na zo na shigo da ke." Ko da ta ƙaraso falon gidan gaba ɗaya ilahirin jama'ar gidan suna falo, sai dai kowa ya yi shiri kamar ruwa ya ci su. Hajiya Dada ce ta kalli Fatima Zahrah ta ce. "Ina za ki je hak cikin ranar nan?" Mumrmushi ta yi tare da cewa. "Kakus kin manta na faɗa maki cewa tun da muka shiga s.s ce ɗin nan an kawo sabuwar student tana so na?" Kai Dada ta jinjina alamar gamsuwa sannan ta ce. " Eh na tuna har kika ce A'isha sunan ta ko?" "Yauwa to ita ce ta ce na yi mata kwatancen gidanmu ta zo tana waje." Bayan kamar mintinan bakwai suka shigo rike da hannun juna murmushi bakinsu dauke da sallama. A'isha ta durkusa ta gaida jama'ar gidan suka amsa gabaɗaya sakamakon tsofaffin gidan na falon. Har Fatima Zahrah ta ja hannunta suka wuce cikin part ɗin su. Suna zuwa falon A'isha ta kalle ta tare da cewa. "Zahrah duk wadannan nan ahalin gidan nan ne?" "Eh me kika gani?" "Kun yi yawa na gani." Zahrah ta yi murmushi ta ce . Shi Wannan tsohon da kika gani wanda yake sanye da medical glass yana karanta jarida , shi ne Kakanmu wato Alhaji Muhammad Tafarki kenan, amma muna kiransa da Papa. Sai matarsa wacce ke zaune a gefensa wato Hajiya Jummai muna kiranta da Dada. Ƴaƴa guda hudu suka haifa cikinsu har da Abbi na. Babban ɗan su shi ne Alhaji Abubakar Tafarki, muna kiransa da Abba nan gidan yake zaune tare da matarsa Hajiya Maimuna muna kiranta da Umma. Suna da yara uku Yaya Hilal da Yaa Aminu sai Aunty Maryam. Bayan Abba sai ƙanin Abba wato Alhaji Adam Tafarki muna kiransa da Dady, shi ma nan yake zaune tare da matarsa Hajiya Amina muna kiranta da Mummy suna da yara biyu mace da namiji Yaa Mansur sai Aunty Nadiya. Daga Dady sai mahaifina wato Alhaji Salis Tafarki muna kiransa da Abbi sai matarsa Hajiya Zainab muna kiranta da Ummi ina da yayyu maza biyu wato Yaa Mahmud da Yaa Sadik sai ni auta. Daga Abbina sai autarsu wato Hajiya Laila muna kiranta da Aunty aurenta ya mutu nan take zaune da yaranta mata biyu wato Aunty Nabila da Aunty Kausar." "Ma sha Allah shi ya sa na ga kuna da yawa." Ai idan kin kira Babban gida ne, don Papa ya ce ba wanda zai tashi ya koma wani gida cikin ƴaƴansu, kowa ya zauna a family house, sai dai Aunty dake mace ce ta yi aure a wani gidan, Kafin auren ya mutu ta dawo ya yaranta." "To me ya saka Papa ya hana sosai tashi sai dai su zauna family house?" "Ba jituwa ne a tsakanin alhakin namu, tamkar maƙiyan juna haka muke." "Ta yi maganar cikin takaici." Ganin ranta ya ɓaci ya sa A'isha kawar da zancen, don da alama abun na ƙona mata zuciya. Fatima Zahrah ta tashi ta je ta kawo wa A'isha ruwa da lemu. Daga nan suka fara firan school ka asancewar suna shekaran ƙarshe a a secondry school, suna shirin zana waec da neco. _Asadullah_ Kwance yake yana saman tangamemen gadonsa yana barci, da misalin ƙarfe goma sha biyu na rana. Kiran wayarsa ce ta farkar da shi daga barcin da yake yi. My Mom shi ne sunan da ya bayyana a kan fuskar wayarsa. Cikin Muryar wanda ke barci ya ce "Mom." "Wai har yanzu barci kake yi ne, bayan na fada maka yau za'a kawo maka matar da za ka aura ko ka mance?" "Mom don Allah ki daina wahalar da kanka wajen nema mani matar aure, shi aure lokaci ne da shi idan lokacin ya zo zan yi." "Ba na son gardama, ga ta nan tana jiranka ka shirya ka fito." Ba ta jira cewarsa ba ta katse kiran wayar . "Oh Mom ke baki gajiya kin kawo mani ƴan mata sama da sau biyar na ce ba su yi mani ba, amma ba ki gaji da aikin nemo matan ba. Wannan ma haka za ta koma don ba wata ƴa mace a gabana." Tashi ya yi ya shiga bathroom ya sakarwa kansa 🚿 shower kusan mintuna talatin yana wanka, fitowa ya yi sanye da white bathrobe a jikinsa sai ƙamshin turaren wanka da sabulunsa yake yi. Hand dryer ya sa busar da gashin kansa. Man shafawarsa mai tsada ya shafa a jikinsa. Ya shirya cikin ƙananan kaya riga J.C na kamfanin ƙwallon ƙafan Manchester united. Sai baƙin wando 3quater da ya sanya. Ya fesa turarensa mai daɗin ƙamshi da tsada. Tsadadden agogonsa na kamfanin GUCCI ya ɗaura a tsinysiyar hannunsa. Sai takalmi shi ma na kamfanin GUCCI ya saka a ƙafarsa. Wayoyi guda biyu ya ɗauka ya fice daga ɗakin. Downstairs ya nufa inda ƙamshin turarensa ya riga shi isa gare su. Suna zaune a main falon gidan. Alhaji Ahmad da matansa biyu Hajiya Hajiya Zubaida da Hajiya Zulaihat suna zaune samun kujera. Yayin da Kamal da Fauziyya da Suhaila na ke zaune a ƙasan carpert. Can gefe kuwa budurwar da aka kawo masa ya gani ko ta yi masa ne. Tunda budurwar ta ji ƙamshin turarensa ta juya zuwa in da ƙamshim ke fitowa . Idani ta zubawa Asadullah tana ganin tsantsar kyau da Allah ya masa. Kallo ɗaya za ki masa kin san ya haɗa jinsi da Fulani. Dogo fari ne yana da kayan siffa da nagarta kyakkyawa ne yana da zagayayyen fuska mai ɗauke da manyan idanu ƙwayar cikin idanun ba baki ba ne Ash color ne ruwan toka kamar dai idanun mage.hancinsa dogo wanda ya dace da fuksar sai ƙaramin bakinsa wanda ya yi kasance pink color. 'Wow' Ta furta tana kallonsa wanda shi ko kollonta bai yi ba idanunsa na kan Mom da take masa kallon sai yanzu ka ga damar fitowa. Murmushi ya sakarwa Mom tare da mata alamar ta yi haƙuri. Bayan ya ƙaraso ne ya ya kalli Mahaifinsa tare da cewa. "Barka da safiya Dad." "Barka dai Son ka fito, ya aiki?' "Alhamdulillah." Kallon Mom ya yi tare da cewa. "Barka da safiya my Mom." "Barka my son ya kake?" "Alhamdulillah." Kallon Hajiya Zulaihat ya ce. "Barka da safiya Aunty." "Barkanka." Ta fada a takaice. Taɓe baki Mom ta yi tare da kau da mai daga kallon kishiyar ta ta. "Barka da safiya Babban Yaya.?" Cewar Kamal yana murmushi, shima mumrmushin ya mayar masa da martanin tare da cewa ƙanina ya kake?" Fauziyya ta ce. "Morning big bros." "Morning my dear ya kike?" "Am fine." Suhaila dake maƙale jikin Hajiya Zulaihat ta kalle shi ta ce. "Ina kwana Yaya." "Ƙanwata ya kike?" "Lafiya lau." "Ma sha Allah." Mom ta yi gyaran murya ya kalle ta sai ta yi masa nuni da budurwar da aka kawo masa. Bai kalle ta ba ya ce. "Ita ma wannan kamar sauran dai a sallame ta kawai, idan na tashi zan nema da kaina ." Ɓata fuska Mom ta yi tana kallonsa. Kamal ya ce . "Babban Yaya wannan fa tafi sauran wadanda aka kawo maka a baya. Ba ka kalle ta ba ne ta hadu." Suhailat dake jikin Hajiya Zulaihat ta ce "Yaya kam wannan kyakkya..." Hajiya Zulaihat ta kai mata duka a baki, cikin ɓacin rai ta ce "Ina ruwanki ban fada maki ki daina shiga sabgar mutanen nan ba, Ina ruwanki?" Dad ne ya kalle ta yace. "Haba mana Zulaihat me ya sa kike haka, ko da ba kece kika haifi Asadullah ai ɗan ki ne, tunda ɗana ne, kamar yadda Suhaila take ƴata, ki daina raba Mani kan yara ba na so." Ba ta ce komai ba ta ja hannun Suhailat suka wuce cikin. Asadullah ya ce. "Na rasa me na yi wa Aunty." "Kada ka damu wani shawara ka yanke akan yarinyar nan, tana da tarbiyya ƴar ƙawata ce." Shiru ya yi yana kallon budurwar da ta sunkuyar da kai kafin ta ɗago ta kalle shi suka haɗa idanu. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LrTZNGwF35IKXX4sLRvFug *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page0️⃣3️⃣ Shiru ya yi yana kallon budurwar da ta sunkuyar da kai kafin ta ɗago ta kalle shi suka haɗa ido. Ɗauke kansa ya yi daga kallonta yayin da ita kuma sai kallonsa take yi. Yamutse fuska ya yi tare da kallon Mom ya ce. "Mom ba ta da wani banbanci da sauran matan da kika kawo mun fa, kuma duk na ce ba su yi ba kika hakura wannan karon ma ina so ki hakura Mom zan nemo mace da nake gani ta dace da rayuwata." "Son wannan karon fa ba zan saurara maka ba, don haka ko me za ka ce sai ka auri Fadeela." Kallon Dad ya yi zai yi magana Dad ya ce. "Ba ruwana tsakanin ku da Mom ɗin ka ce, duk abinda ta fada ya zauna, idan aka biye maka a tuzuru za ka yi ta zama. Shekarunka talatin amma a ce ba ka da budurwa, sai ka ce wacce aljani ta aura?" Bai ce komai ba ya nufi upstair a abin sa, don ya lura yau kam Mom ta gama da shi ba za ta saurare shi ba . Ita kam Fadeela duk da ta lura ko kallon arziki bai yi mata ba, kuma da alama baya son ta amma hakan bai son ta amma hakan bai sa ta ji za ta iya haƙura da shi ba. Mom ta kalle ta tare da cewa. "Kada fa wannan ya dame ki, ki kwantar da hankulinki ki faɗa wa Mamanki ina na nan zuwa za mu tsara komai." Cike da farin ciki ta yi godiya ta fice daga gidan. "Oh Allah zamani ne ya kawo mu da mata ke tallan kansu a wajen namiji haka, ni kam Mom Wallahi ba'ayi namijin da zan je tallan kaina har gidansu ba. Ko da ya fi Yaa Asad kyawu da kuɗi kuwa." Cewar Fauziyya tana tashi wajen. Kamal ya bi ta da kallo tare da cewa. "To ke meye naki a ciki, da ba don yayanki ba ne zan iya cewa kishi kike yi yi. " "Yaa Kamal kenan." Ta fada tana barin wajen. _Fatima Zahrah_ Gajiya ta yi da zaman ɗakin nata, don haka sai ta yanke shawarar zuwa part ɗin Kakanninta. Don idan kewar ta ishe ta an nan take zuwa ta ɗebe kewa. Ko da ta ido main falo Aunty Laila ce da ƴaƴanta, Kausar da Nabeela. Tun kafin da ta ƙara so ta ji Muryar Nabeela na cewa. "Wallahi ba zan yarda ba sai dai ita ta hakura ta bar mani Yaa Hilal ɗin don ba zan iya haƙura da sonsa ba." Kausar ma ta ce. "Kamar yadda ni ma ba zan iya haƙura da sonsa ba, ai na girme...." Sallamar Zahrah ya sa ta yi shiru kuma ba wacce ta amsa sallamar daga uwar har ƴaƴanta. Sai na tsuki da suka ja. Dama ba ta saka ran cewa za su amsa ba. Don idan da sabo sun saba. Kai tsaye ta nufi part ɗin Kakanninta. Bakinta ɗauke da sallama ta shiga falon. Dada ce ta amsa yayin da take ajiye wani bowl a saman Centre table. Amsa mata sallamar ta yi tare da cewa. "Duk wayewar garin yau sai yanzu kika shigo." "Ba haka ba ne Dada kin san next month zan yi walima ina karatu ne." "Haka fa ƴar albarka duk kin fi sauran yaran ke da yayunki, amma sauran ba abunda iyayensu suka koya masu sai gaba da baƙar zuciya." Mumrmushin kawai Zahrah ta yi ba tare da ta ce komai ba. Sai ta kawar da zancen ta hanyar cewa. "Dada me kika dafa ne?" "Yayanki da ya dawo ne yake son kwaɗon zogale shi ne na masa." Kallon rashin fahimta ta yi mata tare da cewa. "Wani Yayana kuma?" "Wanann mara imanin mana, ai na gayawa kowa na gidan ya shiga hankalinsa kafin ya illata su, ke na san baki da tsokana ballantana ki shiga gonarsa ya illata ki a banza, ga shi ke ba isashshiyar lafiya ba. Ya zo ya dukanki ya illata ki a banza wai shi soja ." Zama Fatima Zahrah ke ƙoƙarin yi Dada ta ce. "Na ji har yanzu bai zo ba, ki je ki kira mani shi ko ki tambaye shi a kawo masa nan ne a ɗakinsa? Da sauri ta kalli Dada tana cewa. "Ni kuma?" "Ko kema baƙin halin kika fara koya ne da kuma gaba? Kafa ku biye masu kin ji shi wanda na ce ki kira a matsayin Yayanki ne kamar yadda na haifi ubansa haka na haifi ubanki, kuma Hilal bai ɗauko baƙar zuciyar uwarsa ba, yana da kirki gara yanzu da ya zama soja ya fara canza halaye, na rashin imani da tausayi irin ta su ta sojoji Ko kema an koya maki gabar ne?" Da sauri ta girgiza kai tare da cewa. 'A'a" "To kira shi." Cikin sanyi. Jiki ta tashi ta nufi ɗakinsa duk da cewar lokacin ƙarfe tara na dare ne. Ba kowa a main falo dama idan dare ya yi ba su cika zama ba kowa na part ɗin sa. Upstair ta haura don a can part ɗin sa yake, duk da cewar tunda ya gama karatu ya dawo ƙasar ba ta taɓa zuwa ɗakinsa ba. _Hilal_ Fitowarsa daga wanka kenan ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa. Sai wani da yake goge ruwan dake kansa. Gashin ƙirjinsa ya kwanta luf a fafdaɗen ƙirjinsa. Kallo ɗaya za ka masa ka san cewa ƙakkarfa ne don surar jikinsa a murɗe take ga ƙwanjin dake hannunsa wanda kallo ɗaya za ka masa kasan cewa yana yawan motsa jiki da exercise. Ba fari ba ne kuma ba za ka kira shi da baƙi ba za ka iya kiransa da wankan tawaɗa. Dogo ne sosai yana da ƙira da cikar halitta irin na lafiyayen ɗa namiji ga kyau ga cikar zati Allah ya bashi. Sannan yana da ƙira irin na ƙakkarfan namiji jarumi na azo a gani Bayan ya gama tsanar ruwan jinkinsa ne ya ajiye ƙaramin towel ɗin. Sallama Fatima Zahrah ta yi a falon ta ji shiru don sai ta yi tunanin baya nan, har za ta juya sai ta yanke shawarar duba shi a bedroom ɗin sa. Sallama ta yi kai tsaye ta tura ƙofar falon. Ƙamshi ne ya ziyarce ta ta tsaya tana ƙarewwa falon kallo. Ya burge ta komai fari ne a cikin dakin kama daga fentin da labulaye da kujeru komai fari ne, hatta Centre carpet da Centre table komai fari ne sai ɗaukar ido suke yi kamar ba'a taɓa amfani da su ba. Hatta tiyel ɗin ma fari ne. Ƙofar bedroom ɗin da ya kasance shi ma fari ne ta yi knocking. Yana tsaye gaban dressing mirror 🪞 ya juya ya kalli ƙofar ba tare da ya yi magana ba. Sai da aka sake knocking sau uku kafin ya ce. "Come in." Da sallama a bakinta ta shiga ɗakin, kallo ɗaya ya yi mata ta cikin dressing mirror ya ɗauke kansa. Haka bedroom ɗin ma ya tafi da ita don shi ma komai nasa farin ne. Idanunta ne ya sauka akan wani butterfly 🦋 da aka yi ƙaton elergment aka zana butterfly din shima fari dai ɗaukar idanu yake yi, don har shinning yake yi. Ba ta san lokacin da ta saki murmushi ba har sai dai dimpul ɗinta suka lots. Jin shiru ta shigo ɗakin ba ta ce komai ba ne ya saka ya kalle ta ta cikin mirror ya ga murmushi ma take yi. Gyaran murya ya yi wanda ya sa ta dawo nutsuwarta. Kallo ɗaya ta yi masa ta ganshi ɗaure da towel iya ƙugu. Kau da kanta daga kallonsa ta yi tare da cewa. "Ina wuni?" Banzan ya yi da ita kamar bai ji me yake cewa ba. Sanin cewa ya ji ta kuma ba ta saka ran zai amsa mata ba, don bai taba amsa mata gaisuwa ba ko ta gaishe shi. Idan ya amsa sallamarta shi ne nan. "Dama Dada ce ta aiko ni wai a kawo maka zogalen anan ne ko za ka zo can ka ci?" Nan ma banza ya yi mata kamar ba da shi take yi ba. Don har sake maimaitawa ta yi nan ma ya share ta kamar bai ji ta ba. Closet din kayansa ya shiga ya bar ta nan tsaye. Tana ganin haka ta juya ta fita tana magana ƙasa-ƙasa. "Mutum sai jin kai da nuna isa. Idan ba don Dada ba mai zai shigo da ni ɗakinka ballantana ka nuna ni banza ce a wajenka, idan ba don naka-naka ne ba da ko kallonka zan yi." Haka ta dinga gunguni ita kaɗai har ya karasa ɓangaren Dada. Dada na kallonta ta ce. "Me ya ce a kai masa ne, ko zai zo nan ya ci?" Tura baki ta yi tare cewa "Bai ce mani komai ba kuma ya ji ni." Shiru Dada ta yi kafin ta ce. "Kada wannan ya dame ki, kin san yana da mishkilanci haka yake ba kowane lokaci yake magana ba yin ta yake ba sai ya zama dole." "Ina nawa zogalen na ci? "Ga naki a kitchen ki je ki ɗauk." Ta dauko nata zogalen da ya ji yajin ƙuli da yanke-yanke ta yi bisimillah ta fara ci. Har ta gama Hilal bai zo ba, hakan ya saka Dada ta ce ta ɗauka ta kaiasa kafin ta wuce part ɗin su. "Da ko na je wulakanta ni zai yi, zan ke na kwanta gobe ina da jarabawa." "To idan ba ke ba waye a nan da zan aika, dare ya yi ni ba lafiyar ƙafa ba ballantana na haye upstair." Haka ba don ranta ya so ba ta ɗauki bowl ɗin ta nufi kofar fita, ta ji Dada na cewa . "Nan za ki dawo mu kwana ko ɓangarenku za ki koma ? " Ba ta ce komai ba ta fita don ranta ya ɓaci da komawa part ɗin sa. _Jidderh_ Tafe take sanye Da Kayan makarantan secondry school, makarantar Gwamnati ce take zuwa mai suna Government Day secondry school. Tafiya take yi ga rana ana ƙwalawa tun karfe biyu aka tashi amma kasancewar unguwarsu da nisa da makarantar yake daukarta karfe uku da rabi kafin ta isa gida. Sanye take ta riga fari wanda ya sauko har guiwarta sai farin hijabi da dogon wando wanda ya kasance blue. Sanye take da farin socks socks da takalmin sandal baƙi na roba, duk ya yi ƙura sakamakon tafiyar ƙasa da ta sha. Madaidaicin gidansu ta shiga gida ne mai ɗauke da ɗakuna huɗu Isah yayanta yana zaune a ɗaki biyu ciki da falo, sai ɗakuna biyu wanda Innarsu Jidderh ke amfani da shi Jidderh kuma tana amfani da ɗaki ɗaya. Sai ƙaramin kitchen a tsakar gida da kuma banɗaki shi ma a tsakar gidan. Da sallama Jidderh ta dawo sai dai ba ta ji an amsa ba, amma hakan bai bata mamaki ba saboda ta san Innarsu ba ta nan, sai matar Yayanta Isah wacce kwana biyu take naƙuda a tsaitsaye. Tana shiga tsakar gidan ta nufi randar ƙasa da suke zuba ruwa. Ta bude ta ɗebi ruwa ta sha saboda ƙishirwa ga rana da ta kwaso. Bayan ta sha ruwan ne ta je za ta shiga ɗakinta don ɗakin Inna a rufe Sa'adatu matar Isah kullum cikin barcin rana take, hakan ya sa kai tsaye za ta shiga ɗalibta sai ta ga jini a ƙofar ɗakin Sa'adatu. Ta bi jinin da kallo har jikin labulen, cikin tashin hankali ta nufi ɗakin ta fad'a ciki. _Fatima Zahrah_ Knocking ta yi a bakin kofar falon Hilal, jin shiru sai ta tuna cewa ta barshi a bedroom ne da ta shigo isar masa da saƙon Dada. Don haka ta nufi bedroom ɗin nasa sanin cewa ko ta yi magana ba zai amsa ba ya sa ta yanke shawarar shiga ta ajiye masa. Tura ƙofaf ta yi tare da sallama. Ba ta ga kowa a ɗakin ba, da alama ya fita. Don haka ne ma ya ajiye masa bowl ɗin zogalen a table da ta gani a gaban kujera. Har za ta fita sai ta tuna fa butterfly da ta gani a ɗakin da sauri ta juya ta nufi wajen, sai dai tsayinta bai kai ta taɓa shi ba, kuka tana son ta shafa photon. Don haka ta juya in da ta ga wani kujera da yake zama. Janyo kujerar ta yi ta ajiye a wajen, sai ta hau kujerar ta taka ta. Hakan ya saka ta miƙa hannu ta ciro glass din photon Tana shafar photon tana murmushi cike da shauki. Tsawon mintuna goma ta dauka a haka, kafin ta kai hannu da niyyar mayar da photon bisa tsautsayi dai ya faɗo ya tarwatse. Hilal dake cikin closet yana shiryawa ya ji wannan karar, da sauri ya fito in da ya yi tozali da ɓarnar da ta yi masa. Ganin ɓacin ran dake kan fuskarsa ya wanda babu sassauci a tattare da shi ne ya saka jikinta ya fara rawa. Nufo ta ya yi wanda ganin haka ya sa ta fara neman hanyar tsira don ta san mai ƙwatarta a wajensa sai dai Allah. Tsalle ta yi ta diro daga kan kujerar a guje ta nufi hanyar fita za ta fice. Cikin zafin nama ya zare takalmin dake ƙafarsa ya jefi ƙafarta ta dama daidai saitin guiwarta, kasancewar ta baya ya jefe ta hakan ya sa ƙafarta ta lanƙwashe ta faɗi a wajen. Ƙara ta saki saboda ta ji zafi kuma ga buhuwar da ta yi. Tsawon mintuna biyar tana kwance a ƙasan kafin ta yunƙura idanunta na zubar da ba hawaye ta juyo ta kalle shi ta ga ya wurga mata harara tare da yi mata alama da hannu na ta zo. Tana ɗingisa ƙafa ta karasa gabansa, tsawon mintuna uku bai yi magana ba kafin ya fara magana cikin fusata. "Kin yi mun ɓarna za ki gudu uban waye zai kwashe tarkacen da kika tarwatsa!?" Waige-waige ta fara yi can hanyar bathroom a cikin wani corridor ta hangi kwandon zuba shara da da abin kwashewa. Ɗauka ta yi ta zo ta tattara Wajen ta share tas. Sai da ta gama ta mayar ta ajiye, kallonsa ta yi ta ga ya zuba mata rikitattun idanunsa ba tare da ya yi magana ba. "Na rasa wani rin hukunci zan maki ma, ke ba abar a daka ba, idan na ce zan dake ki sai kin kusa mutuwa a hannunsa." Ƙofar fita ya nufa kafin ya fice ya juyo ya kalle ta ya ce. "Ki fada tsallen kwaɗo ba tare da kin tsaya ba, idan kuma kika tsaya na lahira sai ya fi ki jin daɗi. Kuma ki sani duk abinda za ki yi a cikin ɗakin nan akan idanuna kike yinsa, don ina kallonki." Yana gama fadar haka ya fice yayin da ta fara tsallen kwaɗo tana kuka. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page0️⃣4️⃣ Yana gama fadar haka ya fice yayin da ta fara tsallen kwaɗo tana kuka. Ummin Zahrah kuwa tana ganin karfe goma ta yi Zahrah ba t dawo ba ta yi tunanin kila a ɗakin Dada za ta kwana. Don dama wani lokacin tana kwana a wajen kakarta. Sai da asuba take dawowa part ɗin su. Don haka Ummi na leka ɗakin Zahrah ta ga ba ta nan ta san tana wajen Dada don ba ta fita. Yayin da ita kuma Dada ganin Zahrah ta jima ba ta dawo ba ne ya sa ya yi tunanin bayan ta sanar wa Hilal ɗin saƙonta ta koma wajen Umminta ne. Don dama daga kaka har Papa cikin jikokin su sun fi son Hilal da Zahrah. Duk da cewar iyayensu ba sa ko ko ga maciji da juna. _Hilal_ Yana fitowa daga part ɗin sa downstairs ya nufi ɓangaren Kakanninsa. A can ƙasar maƙoshi ya yi sallama, don ko Dada ba ta ji shi ba, ganinsa kawai ta yi ya shigo. Kallonsa ta yi daga sama har ƙasa don ta ga alamar shirin fita yake yi. Don haka ta ce. "Kai kuka ina zuwa cikin daren nan, sannan k shigo Mani ko sallama babu kamar gidan kafirai ko, to ai ko kafirai ne ka ƙwankwasa ƙofa, saboda an kai ka cikin nasara asarar duniya ka je can ka koyo mugun hali." Bai ce mata komai ba ya miƙe ya nufi hanyar fita ya fice. Taɓe baki Dada ta yi tare da cewa. "Wannan kam matarka na da aiki wallahi, a ce ma magana sai ka ga dama kake yinsa, idan. Ka ga dama ba ka yi kamar kurma, dubi yadda ya shigo ya zauna mani ko magana babu, ai ko kurma ne ya ɗaga mani hannu zan san ya gaishe ni. To Allah ya kyauta."da _Jidderh_ Tana shiga cikin ɗakin ta dade kai tare da furta kalmar. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Jakar makarantarta ta saki ganin matar Yayanta kwance a cikin jini da alama naƙuda take yi. "Aunty Sa'adatu garin ya kika zauna har hakan ta faru?" Sa'adatu wacce ta gama galabaita na naƙudar da take yi ta saka magana. A guje Jidderh ta fito daga ɗakin ta nufi hanyar fita, kai tsaye ta nufi titi duk da sam ta mance wata gajiya da yunwa da ta kwaso. Sai da ta kai bakin titi sannan ta tsaya daga gudun da take yi. Wani mai keke napep (adaidata sahu) ta tare ta shiga. "Mallama don Allah ka yi sauri mu tafi nan za ka bi matar Yayata ce ba lafiya." Ta karasa maganar tana nuna masa layin da ta fito, don haka ya bi in da ta nuna masa. kai tsaye har kofar gidan suka sauka. A guje ta fita ta shiga gidan ta same ta har lokacin a kwance. Wani zani ta ɗauko ta ɗora mata ta cire mata wannan da ya ɓaci. Dakyar ta iya taimaka mata ta tashi tare da jingina a jikin bango. Hijabinta ta saka mata shi a jiki ta taimaka mata duk da ba wani iya tafiya take yi ba, amma Jidderh ta taimaka ta rike ta har suka fito ƙofar gida. A cikin napep ɗin ta saka ta ita ma ta shiga suka bar ƙofar gidan. General hospital ta nemi ya kai su, don can ne take da yakinin sauƙin kashe kuɗi. Suna shiga harabar asibitin wasu ma'aikata suka hange su shi ne suka ɗauko keken da aka ɗaukar marasa lafiya suka saka ta a ciki. Mai keken na ganin Jidderh za ta wuce ya ce . "Kud'ina da?" Sai a lokacin ne ta tuna cewa ai ba ta ko sisi. "Mallama don Allah ka yi hakuri Wallahi ban da kuɗi." "Fitowa ya yi daga cikin napep ɗin ya lalle ta ya ce. "Amma ke ba karamar ƴar rainin hankali ba ce, ta ya ya za ki kira ni ki ce baki da kuɗi, wanann I zancen banza ne, fitsari na zuba a cikin keken ne ba fetur ba, wallahi ko ki bani kud'ina ko na tafka maki rashin mutumci a a wajen nan." "Ka ga Mallam meye na rashin mutunc, ba na cikin nutsuwata ce, duk na bi na rikice ba ka ga a halin da muka kawo ta ba ne, kai ba ka da tausayi ne idan ƴar uwarka ce ya za ka ji?" Wata ma'ikaciyar asibitin ce ta zo ta ce. "Ke koyi sauri ana jiranki." "Ba in da za ta je sai ta biya ni kuɗina." "Nawa ne kudin naka?" Matar da ta zo kiran Jidderh ta tambaya. "Naira ɗari biyar ne." Ta mika masa kudinsa yayin da Jidderh ke mata godiya. Da sauri suka karasa ciki inda ya hangi Aunty Sa'adatu zaune a keken da aka ɗauko ta kuma ko numfashi ba ta yi. "Nurse a kai ta kan gado a ajiye a duba ta mana, dubi yadda kuka barta cikin wannan halin." "To ai sai ki ɗauke ta ki kai ta a gadon ki yi mata abinda ya dace." Ɗaya daga cikin nurse ɗin ce ta faɗa. Jidderh ta kalle ta da mamaki za ta yi magana sai ta ji Muryar nurse ɗin da ta bayar da kuɗin napep ɗin su ta ce. "Ki kawo takardar awonta da kayan da ake rubuta masu idan za su zo haihuwa su kawo." Shiru Jidderh ta yi kafin ta ce. "Ba ta zuwa awo ai." Gabaɗaya suka kalle ta tare da kallon Sa'adatu da ba ta san ma me suke cewa ba. Wata ce . "To sai ki kwashe ta ku tafi ku bamu waje, duk wayar da kai da ake yi wa mata akan mahimmancin zuwa awo ga masu ciki a banza ne wajenku. Ya ya ya mace da ciki za ta zauna ba ta zuwa asibiti ana yi mata awo a duba lafiyar Babyn a bata magunguna, sannan kun bar ta ta gama galabaita kun kawo ta idan ta mutu ku ɗora mana laifi ko?" "Duk abinda za ku faɗa ku faɗa amma daga baya na yanzu ba, saboda tana cikin wani hali ku taimaka yi abinda ya dace don Allah." Haka Jidderh ta dinga roƙonsu tana magiya da taimakon wanan nurse da ya biya masu kudin nape suka ta saka baki suka karɓe su. Bayan an shigar da ita ɗakin haihuwar ne aka lissafa wa Jidderh kayayyakin da za su yi amfani da su wajen karbar haihuwar da bayan ta haihuwar. Lissafin dubu goma suka yi mata na abubuwan da za su bukata. A guje Jidderh ta sake fita duk da ba ta san ya za ta yi ba. Yanke shawarar komawa gida ta yi ko Inna ta dawo, haka kuwa aka yi ya tare da nape ta ce sai ya kai ta gidan za ta amsa masa kudin. Har ƙofar gidan ya sauke ta, ta na sauka Inna na dawowa. Don haka a wajen Inna ta karbi ɗari biyu ta nawa mai nape ya tafi. "Lafiya na gan ki a firgice Jidderh?" "Inna Aunty Sa'adatu ce na dawo na tarar da ita cikin jini, ta fita igayyacinta. To asibitin Gwamnati na kai ta suna ta fada kin san ba ta zuwa awo, dakyar suka amshe ta, yanzu kayan da zasu yi mata amfani suka ce sai na siyo wai dubu goma. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, duba goma ina za mu dame shi yanzu, daga ni sai Naira ɗari biyar. Ko shi Yayan naki bana tunanin yana da kuɗin, don ko da zai fita hannu na ya karbi ɗari biyun da zai yi bayan baro da zai dinga ɗaukar kaya." "Umma bari na je kasuwar na same shi ko za'a samu wani abu wajensa, ko wajen abokansa ya nemi aron kudin, Inna ke ki tafi asibitin ni kuma zan ke kasuwar da yake aiki na nemo shi. Tana gama fadar haka ta juya ta tafi don ba su da nisa da kasuwar. Inna ta shiga cikin gidan ta dauki zannuwa tsofaffi da flask na ruwan zafi ta rufe gidan ta wuce asibiti. _Asadullah mansion_ Dad ne ya fito da shirinsa na fita, bayan ya leƙa ya yi sallama da babban ɗansa Asadullah. Har zai nufi wajen motarsa in da direba ke jiransa, juyawa ya yi ya kalli part ɗin ƙaninsa Uncle Adam. Har yamma ta yi ba su ga juna ba. Don haka ya ciro wayarsa ya danna masa kira. Uncle Adam dake zaune tare da matarsa Hajiya Mami, sai yaransu uku Nasir, Maryam, da Abida. Wayarsa ce ta soma ringing, ganin Yayansa ke kira ya sa ya kau da kai tare da cewa. "To me kuma zai sanar mani?" "Mamy da ke kallon wayar ta ce. "Ai ba laifin kowa ba ne sai laifin wannan munafukar matarsa, idan ba munafurci ba ta san cewa ƴaƴanmu na son Asad sannan za ga je ta kwaso wata bare ta kawo a cikin gidan nan, wallahi ba zai yiwu ba, sai dai hankalin kowa ya tashi a cikin familyn nan." Har sau uku Dad na kiran wayar Uncle Adam bai ɗaga ba, sanin cewa ba lafiya ba don kullum dai ya zo gai da Dad amma yau bai zo ba, ya kira shi ba'a ɗaga ba, hakan ya saka nufi ɓangaren Uncle Adam. Knocking ya yi Nasir ya je ya buɗe ƙofar, ganin Wan mahaifinsa ya sa ya gaida shi cikin girmamawa. "Abbanku na nan?" ",Eh yana ciki." "Ka ce masa ina jiransa." Ciki ya shiga ya sanar da Uncle Adam sakon Dad, don haka Mami ta taɓe baki tana cewa. "Wallahi kada ka yarda da wannan zancen, dama kai ne mai ɗaurawa Asad aure gida bai ƙoshi ba ai ba za'a kai dawa ba. Ta ya ya zamu bari damar da muke hange ya wuce mu, idan Asad bai auri ɗaya daga cikin ƴaƴanka ba wasu banza ne za su ci daga waje. Sai dai mu kare a cin arziki muna zaune a gidan da ya gina muna cin abincin da yake siya muna sha daga gare shi muna sutura daga gare shi a haka za mu kare ba za mu mallaki dukiyarsa ba sai dai wasu banzaye ina da sake wallahi. Ka je ka same shi duk abinda za'ayi ayi don na dan Asad bai da zaɓi." Uncle Adam bayan ya gama sauraren Mami kuma ya hau kan maganarta ya zauna, ya fice don zuwa amsa kiran Dad. _Isah_ Tsaye yake rike da baro ana loda masa buhuhunan suga yana kai wa wani shago. Duk da rabin hankalinsa na gida wajen Sa'adatu don ya san tana naƙuda. Ganin lokacin sallar la'asar ta yi ne ya saka shi bayar da ajiyar baron ya nufi masallaci don yin sallar la'asar. _Jidderh_ A guje ta shigo kasuwar tana mayar da numfashi, don ba ta ma san ta in da za ta fara neman Isah ba, tunda yawo yake yi ba zama wake guda yake yi ba. Waige-waige ta fara yi ta in da za ta gan shi. Ga shi zuwa lokacin yunwa ya ci ƙarfinta, don tun koko da ta sha da safe ba ta sake saka komai a cikinta ba. Yawo kawai take yi a cikin kasuwar ba tare da ta san in da za ta gan shi ba. Gajiya ta yi da yawo ta jingina da jikin wani shago ta kumshe dara-daran idanunta. Halin da Aunty Sa'adatu take ciki kawai take tunawa, tausayin ta ya saka ƙwalla suka fara bin fuskarta. Ga shi Isah bai da waya ya siyar da ita ya siya masu abinci. Ji ta yi an goge mata hawayen dake kan fuskarta, ta bude idanunta da sauri ta sauke su akan Isah. _Fatima Zahrah_ Tana cikin yin tsalle kwaɗon da ya saka ta duk ta gaji, ga sanyin dake ɗakin ya mata yawa, kasancewar ba ta son sanyi. Don shi kuma ɗakinsa kullum cikin sanyi yake don sai ya ƙure gudun A.C ga shi yanayin damuna ake ciki harin ya yi sanyi. Numfashinta ne yake barazanar ɗauke wa, hakan ya sa ka ta kasa cigaba da tsallen kwaɗo, don duk jin jikin da ta yi ta kasa tsayawa saboda ya ce yana ganinta. Zubewa ta yi a saman tiyel ɗin dake ɗakin. Nan ta dinga fafuka da numfashinta dake barazanar ɗauke wa. Tsawon lokaci tana cikin wannan halin har ta kai ta daina gane komai ta sume a wajen. _Hilal_ Da misalin ƙarfe ɗaya na dare motarsa ta da danno kai a cikin gidan. Wani soja ne ya ke driving ɗinsa, ya bude masa murfin bayan motar ya fito kai tsaye ya nufi cikin gidan. Bayan ya shiga babban falon gidan ne ya lashe wutar falon, cikin duhu ya cigaba da tafiya har ya haura upstair. Kai tsaye ya nufi part ɗin sa. Nan ma ya rage hasken falon sannan ya wuce bedroom ɗinsa. Sam bai lura da Fatima Zahrah dake kwance a can ƙarshen ɗakin ba. Kayan jikinsa ya rage ya shiga bathroom ya yi wanka. Fitowa ya yi sanye da white bathrobe a jikinsa. Shiryawa ya yi cikin riga da wando na barci farare, don shi komai nasa fari ne . Haurawa gadonsa ya yi da niyyar da niyyar yin barci, kashe hasken ɗakin ya yi ya kwanta bayan ya yi addu'ar kwanciya barci. Tunawa ya yi da wani aikin da zai yi a aka. System ɗinsa, tashi ya yi ya kunna hasken ɗakin, idanunsa suka sauka akan Fatima Zahrah dake sume. Dafe goshi ya yi don shi sam ya mance da ita. "Wanan wace irin sakarya ce, tun da ta san tana da lalura why not idan ta ga zai tashi ta je ta nemi maganinta ta sha. Mtssssw." Ƙara sawa ya yi gabanta yana kallonta ya ma rasa abun yi. Fita ya yi daga ɗakin kai tsaye ya nufi part ɗin su Fatima Zahrah, karon farko kenan da ya shiga part ɗin tun bayan da aka ƙara wa gidan girma aka gyara aka bawa Kowa part dinsa. Ko da ya zo kasar bai taba zuwa ba sai yau Kasancewar duhu ne ya sa ya kunna hasken wayarsa. Bayan ya shiga falon wanda ya ke tashin ƙamshi ya tsaya yana nazari ina ne ɗakinta, don ya san can ne zai samu maganin da zai bata. Kuma bai dace ya kawo ta ya ajiye cikin halin da take ciki ba don iyayenta ba su sani ba ballantana su yi mata wani taimakon. "Ina ne ɗakinta? Kada na shiga ɗakin mahaifiyarta ko mahaifinta a samu matsala." Rintse idanunsa ya yi ya bude kai tsaye ya nufi wani ɗakin ya shige. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *SADAUKARWA* wannan shafin sadaukarwa ne a gare ki masoyiyata.AMMEY LAYLERH ki yadda kike so da shi Allah ya bar ƙauna. Page0️⃣5️⃣ Rintse idanunsa ya yi ya bude kai tsaye ya nufi wani ɗakin ya shige. Yana shiga ba kowa a ɗakin, ɗakin ya sha gyara tsaf sai ƙamshi kawai ke tashi a ɗakin. Kallo ɗaya ya ji wa ɗakin ya gane ɗakinta ne don ga photon ta manne a ɗakinn. Da kuma takardun da ya gani kan gado wanda alama ya nuna karatunsu take yi. Dube-dube ya fara yi a cikin ɗakin ko zai ga magani babu a fili, don haka sai ya fara bude drawers har ya gani a side drawer ɗint. Ledar ya ɗauko ya bude ya ga inhelar da magungunan ta na sha da kuma allurai. Ganin cewa har ya kai matakin da ta suma ba zai fi dacewa ya yi mata al ki Alluran, don haka ta ya ɗauko alluran da sirinjin ya saka a cikin Aljihu rigar barcin dake jikinta. Mayar da sauran magungunan ya yi ya fito yana zuwa falo sai ya ga an kunnah hasken falon. Ido huɗu suka yi da mahaifiyarta wanda ta ji motsin rufe ƙofar lokacin da ya shiga ɗakin, ta yi tunanin Fatima Zahrah ce sai dai sanin ba ta dawowa cikin dare idan ta kwana ɓangaren Dada ya sa ta fito ta ji lafiya me ya dawo da it a tsakiyar dare. Kallo ɗaya Hilal ya yi wa Ummin Zahrah ya ɗauke kai ya nufi hanyar fita, jin muryarta ya yi tana cewa. "Me kake yi a nan a cikin daren nan?" Bai ba ta amsa ba ya yi ficewarsa. Abbi ne ya biyo bayan Ummi ya ce. "Lafiya?" "Ba lafiya?" "Subhanallah me ya faru?" "Wannan yaron Hilal ne ya shigo part ɗin nan." Kallon mamaki ya mata tare da cewa. "Hilal kuma, to me ya zo yi?" "Tambayar da nake masa kenan amma kai ma ka san ba zai taɓa bani amsa ba." Shiru Abbi ya yi kafin ya ce. "Ba damuwa je ki kwanta kawai." "Ba damuwa fa ka ce, akan me zan iya kwanciya ka san mutanen gidan nan ba ƙaunarmu suke yi ba, ba su ƙi wuta ta cinye mu ba su huta. Musamman mahifiyar Hilal ta tsani ganin mu a rayuwarta ita da Laila, ba sa ƙaunarmu ba sa ƙaunar ƴaƴanmu musamman Zahrah sun tsane ta sannan na ga ɗan su mafi soyuwa a gare su ya shigo part ɗin nan wanda na san ba alkhairi ya kawo shi ba ɗakin ƴata budurwa a cikin wannan daren ka ce ba damuwa?" Hannunta ya rike suka shiga cikin ɗakin Hilal na koma wa ɗakinsa har lokacin tana sume, allura ya ciro da sirinji ya ɗebi ruwan alluran ya yi mata a jijiyar hannunta. Ba jimawa ta ja numfashi tare da sauke ajiyar zuciya. Tashi ya yi ya jefa alluran a kwandon shara. Ta kasa tashi kasala ce kawai take ɗawainiya da ita, ga ƙafafunta sun gaza ɗaukar ta sakamakon tsamin da ƙafar suka yi mata na tsallen kwaɗo da ta yi. Yunƙurawa ta yi da niyyar tashi tsaye ta kasa, komawa ta yi ta zauna idanunta na ciko wa da ƙwalla. "Ke dalla tashi ki fitar mani a ɗaki!" Ya faɗa yana galla mata harara. Sake yunkurin tashi ta yi a karo na biyu amma ta kasa. Kukan shagwaɓa ta saka masa tare da cewa. "Wallahi ba zan iya tashi ba ƙafa ta ciwo take yi." "Idan ba ki tashi kin fice ba sai na sake saka ki punishment ɗin." Kallonsa ta yi cike da tsanarsa wanda ta ji ya yi ɗarsu a cikin zuciyarta. "Dama ba ƙauna ta kuke yi ba, idan son damunku ne na mutu ku huta da gani na a duniyar nan." Ƙasa-ƙasa ta yi maganar yadda ba zai ji ta ba. Ganin bakinta na motsi ya sa shi cewa. "Me kike cewa?" Shiru ta yi don ba za ta iya maimaita abinda ta fada ba. "I Sa'id out!" Ya faɗa cikin tsawa. Kallonsa ta yi cike da jin tsoronsa ta mike da ƙyar tana kuka mai sauti. Sautin kukan ne ya ji ya dame shi, don haka ya furta kalmar " shhhp." Haɗiye kukan ta yi tana miƙewa ta zube kada don ƙafarta ba ta iya tafiya. Tana zube wa ƙasan wajen saman tile sai ta ga duhu ya mamaye ɗakin. "Wayyo Ummina ki zo ki taimaka Mani." Sai jin muryarsa ta yi yana cewa . "Idan na sake jin muryar sai na sauya maki kamanni, ƙarfe biyun dare za ki dame ni da hayaniya, to ki shiga hankalinki. Duk lokacin da ƙafarki ta sake ki to ki fita ki bar mani ɗaki." Shiru ta yi kamar ruwa ci ta sai hawaye da ke bin fuskarta. Daga nan ya juya ya kwanta tare da addu'ar kwanciya barci, ba jimawa barci ya yi awon gaba da shi . _Jidderh_ Murmushi ta sake lokacin da idanunta suka sauka akan Isah. Yaya Aunty Sa'adatu ce ba lafiya tana naƙuda na kai ta asibiti ana bukatar kuɗi kimanin dubu goma." "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un." "Yaya meye abun yi tana cikin mawuyacin hali ." Aljihunsa ya lalubo kudin da ya samu na yau. Naira dubu biyu da ɗari biyar ce. "Kin ga abinda nake da shi." "Yaya ko aro ne ka nema." "Mu je wajen abokin aikina." Suna zuwa ya ya yi wa abokin aikin bayanin halin da matar ke ciki, dubu takwas ya bashi , godiya suka masu suka tafi. Daga nan suka nufi asibitin a cikin keke nape, bayan sun sauka suka nufi in da ɓangaren masu haihuwa . Nan suka tarar da malaman asibiti na ta yi wa Inna faɗa, sakan Sa'adatu ta dade tana naƙuda ba'a kawo ta ba, a halin da ake ciki ma yanzu ba za ta iya haihuwa da kanta ba sai an yi mata tiyata. Kudin da aka fada ne ya saka hankalin su tashi, ba Inna hatta Isah da Jidderh da ksarasowarsu kenan sai da hankalinsu ya tashi, sakamakon jin wai ana neman Naira dubu ɗari daga hannunsu. Ɗaya daga cikin nurse ɗin ce ya ta kalli Isah ta ce masa. "Ka je Doctor ya yana son ganinka." "Ina Ofishin Doctor?" Da hannun ta yi masa nuni, cikin sanyin jiki ya karasa kofar tare da yin knocking, izinin shigowa Doctor ya bashi ya shiga . Hai da Doctor ɗin ya yi ya amsa masa tare da tambayar sa "Kai ne aka kawo matarka za ta haihu ko?' "Eh nine." "Garin ya ka yi sakaci har haka nan, dai da ta galabaita ƙarfin ta ya kare har ta fara fita hayyacinta ne za ku kawo ta, ga shi yaron bai zauna da kyau ba a cikin mahaifa ba ku sani ba saboda sakaci irin na ku. To yanzu dai dole sai an yi mata aiki ana bukatar kudi kimanin Naira dubu ɗari, na sanar da nurses su fada maka. "Doctor to yanzu dan Allah ba hanya?" "Babu in dai kana son ceton rayuwar matarka." "Doctor ba na da kuɗin za'a iya fara mata aikin kafin na dawo zan je neman kudin ne." "Ba zai yiwu na taɓa ta ba, dole sai ka nemo kudin nan." Da sauri ya tashi har ya nufi hanyar fita, wajen su Inna da Jidderh ya nufa. Bayanin komai ya masu in da hankalinsu ya tashi . "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Isah ina za ka samo wadannan makudan kuɗaɗen?" "Wallahi Inna ban sani ba ba na da shi ban da hanyar samun da, yanzu haka dubu goma ne a hannuna, da Jidderh ta sanar da ni halin da ake ciki ne na nemi barin dubu takwas." "Kuma ga shi mu ba wata ƙaddara muke da ita ba ballantana mu ce mu ɗaga mu siyar don biyan buƙata" Inna ta fadi haka cikin tsananin damuwa. "To Inna ku yi Mani addu'a zan je na nemi bashi ko na samu." Addu'a suka yi masa daga ita har Jidderh sannan ya wuce Masallaci ya fara zuwa kasancewar ana kiraye-kirayen sallar magrib Su Inna ma masallacin suka nufa ɓangaren mata. Sai da ya yi sallar magrib sannan ya wuce wajen wani uban gidansa da yake ɗaukar wa kaya. Cikin ikon Allah suka hadu kofar gidan ya dawo sallah. "A wa nake gani kamar Isah?" "Ni ne Alhaji." "Allah ya sa dai lafiya?' "Alhaji matata ce za'ayi wa aiki ana neman dubu ɗari , shi ne na zo ko aro ne ka taimake ni ka bani zan dinga maka aiki kana tara wa a lissa..." "Dakata Isah aiki da kake samun dubu biyu uku ne za ka biya ni?" "In sha Allah Alhaji." "Bani da shi sai da safe." Ya shige ya barshi nan tsaye Haka ya dinga yawo bai samu ba duk inda ya ke tuninin samun kuɗi ya gagara har karfe goma sha ɗaya na dare ƙarshe ya hakura ya koma asibiti. Hankalin Inna da Jidderh ya tashi sosai a ranar dai ba wanda ya rintsa cikinsu sun yi zaman tashin hankali. Bayan sun idar da sallar asuba jidderh ta kalli Inna ta ce. "Inna zan je gida na canza kayan makarantar da ke jikina." Kasancewar tun jiya da yake yawo da kayan makarantar ba ta koma gida ba, awara suka siya a bakin asibitin suka ci. Ko da Uncle Adam ya fita zaune ya samu Dad a sama wani kujera da aka tana da don shaƙatawa. Zama ya yi shi ma daya daga cikin kujerar sannan ya kalli Dad ya ce. "Barka Yaya." Kallon mamaki Dad ya masa kafin ya ce. "Meke faruwa ?" "Meye bai faru ba.? Dama wata shawara na yanke, na bawa Asadullah auren ƴata Abida." Mumrmushi Dad ya yi tare da cewa. "Ma sha Allah. Yanzu dai bari na dawo Sauri nake yi zuwa gobe za mu tattauna akai." Daga nan da y mike ya nufi wajen da motarsa take direbansa na jiransa. _Jidderh_ Ko da ta koma gida murhun ita ce ta nufa don ɗora masu abun da za su saka wa cikinsu. Bayan ta hura wutan ne ta ɗora ruwa ta dama koko ta juya a cikin jug, ta duba ta ga akwai sauran tuwo da Inna ta yi da rana sai ta ɗauko ta ɗumama, tuwon masara ne da miyar kuka. Bayan ta ɗumama ta zuba a cikin kula, wanka ta yi ta shirya cikin riga da zani na atamfar roba. Hijabi ta saka ta kullo ɗakin sannan ta ɗauki jug ɗin da kulan ɗumamen tuwon, da ta saka a cikin leda gari ya yi zafi. Fitowa ta yi tana tafiya akan hanya, tana tunanin halin da Aunty Sa'adatu ke ciki. Ga Isah bai samu kudin ba. A ƙafa take tafiya ta yi tafiya kamar kimanin mintuna talatin, a babban tita ta ta tare abun hawa. Ya tsaya tare da cewa. "Ina za ki je Hajiya.?" "Asibiti za ka kai ni, sai dai ba kudi a hannuna sai na shiga ciki zan karbo maka wajen Yayana." Na "Amma gaskiya za ki kara Mani kuɗi." "Ka taimaka mani dan Allah." "Shiga muje." Sun fara tafiya ta jikin mirror ya hango Jidderh na goge ƙwalla. "Hajiya ki yi hakuri sauki na zuwa in sha Allah, waye na ki ne a asibitin?" "Matar Yayana ce za'ayi wa aiki za ta haihu." "Ayyah to Allah ya sa ayi a sa'a ki daina mata kuka yau za'ayi aikin ne?" "Ban sani ba saboda sai an bayar da kuɗin aiki." "Amma Kada ki ce na cika tambaya, na ga kina cikin damuwa ne kudin aikin ne babu?" Kai kawai ta ɗaya masa ba tare da ta ce komai ba. "Amma ina ganin me zai hana ku nemi taimakon Sir Asadullah, saboda mutum ne mai taimakon al'umma musamman marasa ƙarfi, kuma mutane na zuwa wajensa idan suna da matsala, kuma ban taɓa jin wanda ya je bai samu abinda yake so a wajensa ba. Kema ina da yaƙinin za ki samu, in dai kin je duk da ganin sa ba abu mai sauki ba ne." "Tunda na gaggawa ne ki je kamfaninsa kawai." "Ban san in da kamfanin yake ba." "Bari na kai ki. Amma fa security ba za su bari ki shiga ba sai kin samu hanya da taimakon wani." Godiya ta yi masa kai tsaye ya kai ta har kofar tangamemen kamfaninsa, wanda yake saka ran za ta same shi a wajen. _Sir Asadullah_ Zaune yake a bayan motarsa motoci biyar ne yau suka fito da su. Biyu gabansa sai biyu a bayan wacce yake ciki. Lafiyayyun motoci ne na alfarma sai ƙyalli suke suna ɗaukar ido. Jidderh dake can tsaye bayan mai napep ya tafi ta saki baki tana kallon motocin. Ɗaya bayan ɗaya suke cinna hancisu s cikin katafaren kamfanin. Ganin motar ƙarshe ta shiga ne ana shirin rufe gate ɗin ta ruga a guje za ta shige. Security ne ke ƙoƙarin hana ta shiga yayin da ya dage akan shiga ciki. "Ke kuma daga ina haka har kike dagewa sai kin shiga ko kamfanin na ubanki ne?" Wani security dake tsaye yana kallon yadda take artabu da abokin aikinsa ne ya yi maganar. Wanda ya tare kofar gete ɗin ne ya ce bar ta kawai ko an fada mata yanzu ne lokacin da yake sauraren ƴan maula irin ta, ko tsabar talauci ne ke neman haukata ki kina yarinya da ke?" Bayan motocin sun tsaya ne ɗaya daga cikin masu tsaronsa ya yi saurin buɗe wa Sir Asadullah murfin motar. Fararen ƙafarsa ɗaya ya fara zirowa waje, kafin ya fito da ɗayan sai da ya ɗauki sakanni sannan ya fito. Sanye yake da Suit a jikinsa rigar ciki fara wanda ake hango kwalar rigar sai rigar Suit blue da ya dora sa saman na cikin da wando shi ma blue na Suit ɗin rigar.wuyarsa ɗaure da necktie faru yana da layin blue a jiki. Takalmin ƙafarsa sau ciki baki sai ɗaukar ido suke yi, agogon Diamond dake ɗaure a tsinysiyar hannunsa ya kalla, fuskarsa sanye da farin glass a idanunsa. Har ya fara taku zai shiga ciki sai ya ji sautin ƙara na mace. Juyowa ya yi yayin da idanunsa suka yi tozali da jidderh dake kokawa tura gate security ya riƙe. Yana juyowa ta ce . "Yallaɓai!" Daidai sanda ta fadi ledar hannunta ma ya bugu a ƙasa, kokon ya malale a wajen. Kuka ta sake tana cewa. "Yallaɓai ka taimake ni!" Glass din idanunsa ya cire tare da zuba mata blue eyes ɗinsa. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page0️⃣6️⃣ Glass ɗin idanunsa ya cire tare da zuba mata blue eyes ɗinsa. Kuka ne kawai take yi idanunta a kansa, mai da dubansa ya yi a wajen security da ya ture ta ta faɗi, kallon garhaɗi da ya masa ne ya saka ya rusunar da kai alamar ban haƙuri kafin ya ce. "Sir ita ce ta janyo na hana ta shiga na sanar da ita cewa ba yanzu ne lokacin da kake bayar da taimako ba, amma ta kafe sai ta shiga tana ƙoƙarin nuna mani ƙarfi a bakin aikina." Kallon Jidderh ya yi tare da yi mata alamar ta taso da hannunsa mai rike da glass. Da sauri ta tashi ko ta kan ledar da kokon da ya zube ba ta bi ba. Ƙarasawa ta yi gabansa sannan ta zube akan guiwarta. Kallont ya yi ga ta dai kyakkyawar yarinya doguwa fara fuskarta mai ɗauke da dara-daran idanunta da zankaɗeden hanci da ƙaramin bakinta. A daidai wannan lokaci kamata ya yi a ce tana makaranta ba nan ba. "Me ke tafe da ke?" Ta tsinkayi muryarsa ya jefa mata tambaya. "Taimako muke nema yallaɓai ka taimake mu ka rufa man asiri kamar yadda Allah ya rufa maka." "Me kike so?" "Yallaɓai matar Yayana ce take kwance s asibiti ana bukatar kudi kimanin Naira dubu ɗari ga shi ba mu da..." Kafin ta karasa maganar sai ta ji takun takalmin ƙafarsa ya fara tafiya. " Yallaɓai ka saurare ni don..." Kafin ta karasa maganar da za ta yi ta ga ɗaya daga cikin mutane da yake tare da su ya ciro bandir na 1k guda biyu, wato dubu ɗari biyu kenan ya ce mata. "Ga wannan ya ce a baki." Tsabar ruɗewa da ganin kudin da ba ta taɓa rike irinsu ba ko da ba nata ba sai yau. Ta ɗauka Sir Asadullah share ta ya yi ba ta san ya yi wa ɗaya daga cikin mutanensa alamar ya bata dubu ɗari biyu ba. Tashi ta yi a guje cikin farin ciki nufi inda ta ga ya bi don ta yi masa godiya, sai wasu dake ciki da alama security ne suka yi mata alamar ta koma . Dube-dube ta fara ko za ta gan shi ba ta gan shi ba kuma ba ta san wace kofar ya shiga ba. "Allah ya saka masa da alkahiri ya baka a inda kake nema duniya da lahira ya jikan Magabata." Da sauri ta fice ta kwashi kayan da ta zubar ɗumamen tuwon na nan amma koko ne ya zube. Ta dauka jug da ledar ta zuba cikin ledar kudin ta dukunkune su a hijabi. Fita ta yi in da ta samu mai nepe ta shige tare da sanar da shi inda zai kai ta. _Asadullah mansion_ Mom ce ta nufi part ɗin Asadullah don ta lura wasan ɓuya yake son yi da ita, tun lokacin da ta ce dole sai ya auri Fadeela ƴar ƙawarta Duba wa ta ji gabaɗaya ba ya ɗakin don haka ta fito tana tamabayar ma'aikatan da suke falo. "Kun ga fitar Asad ne?" "Eh Hajiya ya yi mintuna talatin da fita." Jinjina kai ta yi tana shirin komawa part ɗinta sai ta ga an banko ƙofar an shigo. Mami ce fuskanta ba walwala. "Dama wajenki na zo." Mumrmushi Mom ta yi tare da cewa "Sannu da zuwa, ga wuri ki zauna." Kallon ma'aikatan dake ta gyaran falon ta yi tare da cewa. "Ku ba mu wuri." Kowace ta ajiye aikin da take yi ta basu waje." Dubanta ta mai da ga Mami dake cika tana batsewa ta yi tare da cewa "Ki zauna mana Hajjaju." "Ba zama ya kawo ni ba." "To meke tafe da ke?" "Na ji an ce kin samar wa Asad matar aure ko?" "Eh haka ne, ƴar gidan ƙawata Hajiya Lubna ba zaɓa masa." "Saboda me ye kika zaba masa?" Murmushi Mom ta yi tare da cewa. "Saboda duk macce da na kawo masa baya so yake cewa, na kawo masa ƴan mata sama da guda biyar yana bijire wa zancen." "Amma gida bai ƙoshi ba ai ba za'a kai dawa ba, ga ƙanninsa nan Abida da Maryam duk suna masifar son sa, amma kika tsallake su saboda son zuciya irin ta ki." "Ba son zuciya anan saboda bai ce yana son su na hana shi ba." "Kenan shi ya ce yana son matan da kike kswo masa su suka ce suna son sa?" "Ni ce na ga dacewarsu tare." "Okay su bawa ƴaƴan da kika tsallake su me suka rasa kyau ne ba su da shi ko ilimi.?" "Kin ga mu bar zancen nan kawai tunda na riga na zaba masa kuma wannan karon bai Mani gardama ba. Ina ga ki yi hakuri kawai." "Hakuri fa kika ce, ai ke ce zan ba hakuri don wallahi sai na ɓallo maki ruwa, idan har baki janye zancen auren Asad da wata mace ba ɗaya daga cikin ƴaƴana ba to ki na mai tabbatar maki da lokacin nadamarki ya kusa zuwa. Kallon mamaki Mom ke bin Mami da shi. _Fatima Zahrah_ Gabaɗaya ta kasa barci sai hawaye dake tsiyaya daga idanunta. Ga shi ba saman carpet take ba saman tiles ga ƙarfi da ya mata ga sanyi dake ratsa ta banda sanyin AC da ya mata yawa, ba komai da za ta iya lulluɓa da shi, hijabi da ta sanya lokacin da ya saka ta tsallen kwaɗo ba ta san in da ta jefar ba yanzu. Takure wa ta ji waje ɗaya wanda da ba don alluran da ya yi mata ba da ba abinda zai hana ciwonta tashi. Shi kam hankalin sa kwance yake barcinsa cikin lallausan bargonsa. Da zarar ta bude baki za ta yi kuka sai ya tuna da gargadi da ya mata sai ta haɗe baki. Dare mahutar bawa in ji masu iya magana, lokacin da kowa ke barcinsa a gidan cikin kwanciyar hankali amma ita ya sam ba haka ba don kasa barci ta yi. Har karfe hudu na asuba ba ta yi barci ba. Misali karfe hudu da rabi ya farka. Sakamakon haka ya saba dama. Hasken ɗakin ya kunna yayin da haske ya gauraye ɗakin. Can ya hango ta kudundune ta juya baya. A tunaninsa barci take yi don haka tashi ya yi ya shiga bathroom. Wanka ya yi tare da ɗaro alwala. Cikin closet din kayansa ya shiga ya shirya cikin jallabiyarsa blue mai gajeren hannu. Zuwa lokacin ƙarfe biyar ta yi don haka ya ɗauki sallaya don zuwa sallar asuba a masallaci. Ƙarasa wa ya yi kusa da in da take kwance a ƙasa ya ce "Ke!" A hankali ta mike zaune don dana idanunta biyu. "Tashi ki tafi." "Miƙewa ta yi a hankali ta fara tafiya, ƙarasa wa ta ji wajen in da hijabinta ke ajiye a ƙasa ta ɗauka ya rike a hannu. Ya riga ta isa bakin ƙofar ya bude ƙofar ya fita tana bayansa suka fito. Jinkinta da sauƙi sai zai tsamin da jikinta ke mata. Suna saukowa Downstairs suka ji ana tafka salati da tafa hannu. Tsabar tsoron da Zahrah ta ji ba ta san lokacin da ta ƙanƙame Hilal ba. _Jidderh_ Cikin farin ciki ta shiga asibitin fuskarta ɗauke da jin dad'i. Daga nesa ta hango Inna da Isah fuskarsu dauke da damuwa Isah har da ƙwalla yake goge wa Tana ƙarassa gabansu ta ciro Naira dubu ɗari ta mikawa Isha tana cewa. "Yaya ga kuɗin na samo." Ta fada tana saka ɗaukan kudin cikin leda a ta cikin hijabi. Cikin mamaki suke kallonta suka hada baki wajen cewa. "Jidderh ina kika samo wadannan kuɗaɗen?" "Yaya zan maku bayani ka je ka biya a fara shirin yi mata aiki." Da sauri ya nufi kofar ofishin Dr. Kallont Inna ta yi tare da cewa. "Jidderh ki faɗa in da kila samo maƙudan kuɗaɗe masu yawa?" "Ba ni aka ba iyakar su kenan ba rabi ne." Wani kallo Inna ta mata tare da cewa "Jidderh kada ki sa zuciyata ta tarwatse mi fada gidan uban da kika samu wadan nan zunzurutun kuɗi haka?" *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z .*GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page0️⃣7️⃣ Jidderh kibsa zuciyarta ta tarwatse ki faɗa mani gidan uban da kika samu waɗannan zunzurutun kuɗi haka " Shiru ta yi ta ma rasa ga in da za ta fara yi wa Innarsu bayani. Sai da Inna ta daka mata tsawa cikin fusata ta ce. "Ba tambayarki nake yi ba?" Wata nurse ce ta zo ta ce. "Don Allah nan asibiti ne akwai makiyayata ba mu bukatar hayaniya." Inna ta fita ranta a ɓace Jidderh ta bi bayanta har waje in da Inna ta zauna akan baranda. Durƙusawa Jidderh ta yi a gabanta tana cewa. "Mama ashe akwai ranar da za ki iya zargi na, akan zan aikata wani abun da ba daidai ba. Ke fa kika bani tarbiyya kuma...." Dakatar da ita ta yi ta hanyar ɗaga mata hannu. "Ba abinda nake son ji daga gare ki ba kenan, wa ya baki baki kuɗi?" "Wani mutum ne." Da sauri Inna ta kalle ta tare da cewa. "Wani mutum ne a zamanin nan zai ɗauki kudi kimanin Naira dubu ɗari biyu ya baki?" "Inna na san kin san shi ko ba ki san shi ba na san kina jin labarin da a gari, ba kowa ba ne illa Sir Asadullah ." Kasancewar ba ɓoyayyen mutum ba ne ya saka Inna ta gane shi, don ko a gidan rediyo da gidan TV da jaridu tana jin labarinsa sosai. Da kuma yayyukan alkhairi da yake yi wa al'umma. "Ina kika gan shi?" Nan ta bawa Inna labarin komai tun shigarta nape da yadda ya kI ta kamfanin komai ta faɗa mata. Shiru Inna ta yi tare da cewa. "Allah ya saka masa da alkhairi." Da Amin ta amsa daidai lokacin da Isah ya dawo. Shi ma tambaya ya yi daga in da kuɗin suka fito, nan ta bashi labari kamar yadda ta bawa Inna, shi ma addu'a ya yi masa Sannan y yi Jidderh godiya bisa jajircewarta wajen samo kudin, sannan ya ɗaura da cewa. "Na na biya kudin komai, shi ainihin tiyata da za'ayi mata dubu arba'in da biyar ne, sai kuɗin gadon jariri kowane rana dubu goma sai kuɗin magunguna shi ne ya saka suka ce mu nemo dubu ɗari. "To Allah ya sa ayi a sa'a ai ta sha wahala sosai ." Cewar Inna cikin tausayi take maganar. Sauran dubu ɗarin da ya rage Jidderh ta miƙawa Isah. "Ya ga sauran kudin na ga ko rigar jarirai ba ku siya ba, ka siyo kayan baby da pampers da man shafawarsa, powder da flask na zuba ruwan zafi, abinda ya rage sai a siya kayan abinci a ajiye tunda ga mai jirgo bai kamata a cigaba da manejin abinci ba." Karba ya yi yana farin ciki tare da godiya . _Fatima Zahrah_ Tana ƙankame da rigar Hilal ta rike jallabiyar jikinsa ƙam tana kallon Aunty Laila da ke zare idanu akansu. Don tana tsoron ƙanwar mahaifin nata sosai, saboda ba ta raga mata, ko kaɗan, tun tana yarinya abu kadan za ta kai mata duka tun tana yarinya har yanzu kuwa da ta balaga ta zama cikakkiyar budurwa kuwa. "Me nake gani haka, karuwancin naki ya bar waje har cikin gida za ki fara bin maza ɗaki kina lalata da su?" A lokacin ne Hilal ne ya kalli ƙanwar mahaifin nasa ya ce. "Take your correction Anty, ni ba fasiƙi ba ne ban aikata komai da ita ba." "Hilal rashin kunya za ka yi Mani?" "Ba haka ba ne Aunty na ga kina zargin na aikata wani abu ne kina son ɓata Mani suna a cikin family." "Ai ba da kai make ba wanan ƙaruwar da ta biyo ka har ɗaki nake tuhuma, je ka sallah kada ka rasa jami'i" "Aunty ki bar yarinyar nan ta tafi duk yadda kike tunani ba haka ba ne." 'To jeka ɗan albarka." Ganin zai iya rasa jami'i ya sa ya wuce da sauri, fitarsa ke da wuya Zahara har ta kai bakin part ɗin su ta ji an finciko ta tare da sauke mata tagwayen maruka wanda ya sa ta sakin ƙarar azaba." Ummu dake shirin tayar da Sallah ta ji ihun ƴar ta , da sauri ta fito ta ƙaraso bakin part ɗin. Daidai lokacin da Aunty Laila ke shirin ƙara saukewa Zahrah mari Ummi ta riƙe mata hannu tare da cewa. "Kul!" Da mamaki Aunty Laila ke kallon ta tana mamakin matar da a baya ba ta iya tanka mata ko me za ta yi wa ƴarta kuwa, ta sha dukan Zahrah ba ta hana ta ba amma yanzu har tana mata tsawa. "Okay ni kike dakatarwa akan na daki Zahrah, to wannan kuma kin yi kaɗan, baki isa ki hana ni na daki Zahrah ba matukar ta yi ba daidai ba sai na ɗora ta a hanya na ba ta tarbiyyar da ta dace." "Ƴata a tarbiyyancen ta take, 'ya'yanki ke bukatar tarbiyya, kin kasa basu tarbiyya sannan ki ce za ki bawa ƴaƴan wasu? Wanda take da shi ya ishe ta." Wani kallo mai cike da tsana da ƙiyayya, kafin ta ce. "Ai duk cikin tarbiyyar ne yasa kike tura ta karuwanci ba ta kwana gida, yanzu tarbiyyar ce ta saka kika tura ta ɗakin Hilal ta je ta kwana yanzu za ta dawo maki ko?" "Oh ta nan kika ɓullo to ba abinda zai kai ƴata part ɗin Hilal ballantana ta shiga ɗakinsa. Kada ki sake danganta Fatima Zahrah da wannan ƙazamin kalma na karuwanci." Dariya Sunyi Laila ta yi tare da cewa. Yadda na ga na gansu sun fito yanzu a jere daga part ɗin sa hijabinta a hannu tana tafiyar tana cije baki idan karya ne kada Allah ya barni na bar wajen nan lafiya." Kallon mamaki Ummi ke yi wa Fatima Zahrah kafin ta ce. "Zaharata ki ƙaryata abinda na ji yanzu, a ina kika kwana ba tare da Dada kika kwana ba?" Kuka ne ya suɓuce wa Zahrah kasa magana sai kuka. "Zahrahta ina kika kwana?" Ba ta ce komai ba sai kukan da take yi "Da gaske ɗakin Hilal kika kwana?" Kai ta ɗaga alamar eh. Kasake Ummi ta yi tana kallonta galala ta kasa magana. Juya wa ta yi ta koma ɗakinta. Tana jin Aunty Laila na cewa "Ba bakin magana ne?" Fatima Zahrah ma ɗakin Ummanta ta shiga tana kuka. Umma wacce dama Sallah za ta yi don haka ta juya gabanta gabas ta tayar da Sallah. Zahrah ta kasa tashi tana nan durƙushe sai risgar kuka take yi ganin yadda aka mata sharri tana ji tana gani. Har Ummi ta idar da Sallah daidai lokacin da Yayyun Fatima Zahrah Mahmud da Sadik suka dawo daga masallaci. Sun shigo gaida Umminsu. Ganin autarsu na kuka ya sa duk hankalinsu ya tashi. Musamman Mahmud da ya fi Sadik sauƙin kai. "Lafiya Auta?" Ba ta tanka ba sai kuka, kallon Ummin ya yi wace ta shafa addu'a ya fara gaishe ta, Sadik ma ya gashe ta. Suka haɗa baki wajen tambayar abinda ya faru da Zahrah. "Ku tambaye ta da kanku, na dai ji ƙanwar mahaifinku na cewa wai a ɗalin Hilal ta kwana, ta gansu suna fitowa a tare." "What!?" Sadik ya faɗa yana cewa sharrin har ya kai haka, wallahi matar nan da ..." "Ba sharri ta yi ba tunda ba tambaye ta da kaina ta kasa ƙaryatawa." "Ke!." Ta san halin Sadik da zafin zuciya yanzu zai iya kai mata duka, don haka ta miƙa da sauri ta koma jikin Mahmud. "Dakata Sadik akwai wani abu dai, amma ba yadda kake tunani ba, na san ba komai wallahi." Sadik ya kalli Mahmud ya ce. "Yaa Mahmud meye hujjar ka?" "Na sani ka sani tarbiyyar da Ummi ta bamu tarbiyya ce da ba za mu iya aikata wani abun da ba daidai ba. Musamman tarbiyyar da ta yi wa Zahrah da ƙoƙarin da take wajan kula da tarbiyyar ta kasancewar ta ƴa mace ba za ta aikata abinda ba daidai ba." Kallon Fatima Zahrah ya ji tare da cewa. "Sanar da ni abinda ya faru bar kika kwana a ɗakin wanda ba muharramin ki ba." Nan ta kwashe komai da ya faru ta sanar da su. Tun da Dada ta aike ta har ɓarna da ta masa zuwa punishment ɗin da ya bata. Haƙiƙa ransu ya ɓaci da abinda Hilal ɗin ya yi wa Zahrah, wani irin zalunci ne zai saka ta tsallan kwaɗon na tsawon lokaci ya fita har ya dawo. Cikin zafin zuciya Sadik ya mike zai fice. Jin muryar Umminsa ya ji tana cewa. "Dawo Sadik!" Dawowa ya ji zuciyarrsa na tafarfasa ya ce. "Ummina abinda ake mana a gidan nan ya fara isa ta, wannan ai zalunci ne. Ta ya ya zai azabtar da yarinya don ta yi masa ɓarna. Ai da ya fadi ko nawa a ne ɓarnar da ta masa sai mu biya. Amma ka yi wa ɗan Adam horo da har ya kasa tafiya, don shi soja ne sai ya gwada ikonsa akanta. Gabaɗaya an tsane mu a gidan nan kamar ba jininsu ba." Zahrah dai ɗakinta ta nufa tare da faɗawa toilet, gasa jikina ta yi da ruwa mai zafi sanna ta ɗauro alwala ta zo ta saka doguwar riga ta gabatar da sallah. Ba laifi ta ji dadin jikinta. _Aunty Laila_ Tana zuwa ta part nata ta nufi ɗakin yaranta mata biyu duk suna barci ba sallar asuba. Duk ta kai wa Nabeela da Kausar ta ce. "Ku tashi banzaye kun kasa karkato hankalin Hilal zuwa gare ku, to ki tsaya kowacce cikinku ta rasa ga waccen mai kama da aljanar tana neman yi masu sakiyar da ba ruwa." "Wace ce wanan ?" Nabeela ta tambaya." Kausar ta bata amsa da wace ce mai siffar aljanna a gidan nan?" "Uban me zai yi da wannan figaggiyar yarinyar , ai babban goro sai magogin karfe." Nabeela ta ce. "Kema ki hakuri ki bar Mani shi." "Wallahi ba zan hakura ba kowa ta iya allonta ta wanke. Kuma na san ko Mahifiyarsa da mahaifinsa ba za su bari ya kula yarinyar nan ba, na rasa abinda ya kai ta part ɗin sa amma zan yi maganinta." _Jidderh_ Washe baki take yi tana dariya har dimple ɗin ta na lotsawa, Inna da isah fuksar kowa da farin ciki anyi nasarar ciro baby boy dake cikin Sa'adatu. Sa'adatu da baby suna barci suna hutawa, babyn ma sha Allah sai barcinsa yake kan gadon baby yana sanye da Kayan sanyi a jikinsa. _Fatima Zahrah_ Kasancewar ba ta samu barci a daren jiya ba ya saka tana isar da salla ta kwanta tana barci. Can cikin barcinta sai ta ji ana kiran sunanta a hankali ta bude idanunta ta sauke su akan na Umminta. Da sauri ta tashi zaune ganin idanun Umminta ya naɗa ya yi ja. "Ummina lafiya ?" Ba ta ba ta amsa ba ta ce. "Ki zo falo ana son ganinki." Daga nan Ummin ta fice, gaban Zahrah ya fadi, don kamar kuka ta ga Umminta na yi . Da sauri ta tashi ko sanye da hijabi da ta yi sallah ta fito babban falon gidan. Gabaɗaya ahalin gidan ne suka hadu, tana fitowa kowa ya zuba mata idanu. Kallon yayyunta ta yi Mahmud da Sadik ta ga ransu a ɓace ga Umminta ido ya yi ja. Kallon kakanninsu ta yi ta ga ita suke kallo, cikin sanyi jiki ta karasa tare da zubewar akan guiwarta. 09065327995 [11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z Ba *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *SADAUKARWA* _Wannan shafin sadaukarwa ne ga ƙungiyar Jajirtattu writers association Alla ya ƙara mana ƙwarin guiwa fa haɗin kai_🥰🤝 Page0️⃣8️⃣ Kallon Kakanninsu ta yi ta ga ita suke kallo, cikin sanyin jiki ta ƙarasa tare da zubewar akan guiwarta. Ta kalli Kakannin nata ta ce. "Barka da safiya kun tashi lafiya?" Suka amsa mata ba yabo ba fallasa. Daga nan ta kalli iyayen nata maza ta haɗa jam'i wajen gaishe su ta ce. "Ina kwana?" Mahaifinta ya amsa amma sauran ƴan uwansa ba wanda ya amsa, ta saba da haka don kullum ba su amsa gaisuwarta sai dai idan sun ga idon Papa da Dada. Wanan karon ma Papa ya kalle su ya ce. "Ba ku ji tana gaishe ku ba ne, kullum abu ɗaya ya ƙi wucewa wa, yaushe za su haɗa kai ku so juna sai bayan mutuwsata?" Jin haka ya saka suka amsa mata da lafiya lau daga nan ta juya kallonta ga iyaye mata wanda suka share ta ba su amsa ba har sai da suka ga ɓaci ran Papa sannan suka amsa iya surukan ne suka amsa amma ita kam Aunty Laila ba ta amsa ba. Zahrah ba ta damu ba ta juya wajen Yayyun su maza da suke zaune gefe ɗaya. Bilal, Mansur, Faisal, Mahmud da Sadik. Gaishe su ta yi wanda ba su so amsawa ba idan aka cire Mahmud da Sadik. Hilal kam dama ba ita ba kowa sauran yaran gidan suka gaishe su kallo ba su ishe shi ba ko da kuwa Faisal da Maryam ne wadanda suka fito ciki ɗaya , duka yaran Abba da Umma ne to ba amsa gaisuwar su yake yi ba Sannan ta kalli gefen ƴan matan gidan Maryam, Nadiya, Nabeela da Kausar. kasancewar duk sun girme ta nan ma ta gaishe su Maryam kawai ta amsa tare da. "Lafiya lau sister." Umma kam harara ya ta gallawa ƴarta, don ta tsani halayyar ta. Gyaran Murya Papa ya yi wanda hakan ya saka kowa ya dube shi tare da kallonsa, idan aka cire Hilal wanda shi tun da ya shigo wajen bai yi wa kowa magana ba, tunda ya tsarin ya ɗora ƙafarsa ɗaya kan daya yana danne-,danne a wayarsa. Duban Aunty Laila Papa ya yi tare da cewa. "Auta faɗa abinda kika faɗa mani gaban kowa." Ba tare da tuninin komai ba ta fara magana. "Dama wancan banzar yarinyar da nake faɗa maku cewa tana bin maza kuka ƙi yarda da zance na yau za ku yarda. Don na dade da sanin wannan yarinyar yawon banza kawai take zuwa da sunan makaranta." "Ki faɗi a abinda kika faɗa mana kai tsaye." "Wannan yarinyar tana zuwa ɗakin Hilal idan ga tara mazajen waje, hakan ya saka na ga ya kamata a taka mata burki na san bayan Hilal za ta iya bin wasu mazan na gidan nan don ga wasu samarin nan a gidan." Fatima Zahrah ta fashe da wani kuka mai cin rai da ƙunar zuci. Jin sharrin da ake mata . Papa ya kalle ta tare da cewa. "Kina da tabbacin cewa maza take bi a waje za ki iya rantsuwa akan haka?" "Papa me ya kawo zancen rantsuwa fa, na rassa waye zan yi wa sharri sai wannan ƴar yarinyar duk cikin yaran gidan nan." "Me zai hana idan ita kaɗai kika tsana." Dada ta yi magana tana kallon ƴarta wacce ta tsani halinta, shi ya saka ba sa shiri sai ta ce sai ba ta son ta. Kallonta mahaifinta ya ji tare da cewa. "Kina da tabbacin akan abinda kika faɗa?" "Ƙwarai kuwa da asuba kafin ayi sallar asuba na ganta tana fitowa daga ɗakin Hilal da alama nan ta kwana, sun fito tare da shi hijabinta a hannu Sautin kukan Fatima Zahrah kawai ke tashi a falon, shi kuwa gogan Hilal har yanzu yana yadda yake sai sarrafa wayar hannunsa yake yi cike da ƙwarewa. Ko a jikinsa bai nuna alamar cewa yana jin me suke faɗa ba, ko a jikinsa. "Za ki iya rantsuwa akan zargin da kike masu cewa sun yi lalata a ɗakin Hilal?" "Ba zan rantse ba amma na san tabbas wani al'amari y faru a tsakaninsu." Kallon Hilal Papa ya yi tare da cewa. 'Hilal ka sanar da mu abinda ya faru." Tsawon minti ɗaya kafin ya bude baki ya ce "Dad ku tambayi yarinyar mana,." Ya yi magana har lokacin idanunsa kan wayarsa, kamar ba shi ne ya yi yi maganar ba. Daga karshe ya ce "Ku faɗa wa ƴar ku shaidar zina wuya ne da shi ta kiyayi hakan matukar ba tana da juriyar da za ta iya jure bulala tamanin ba." Yana gama fadar haka ya tashi ya nufi upstairs ɗin. Binsa da kallo suka yi Aunty Laila ta fara masifa tana cewa "Hilal rashin mutumcin naka har ya kai haka, to ka zo ka ka yi mani bulala tamanin ɗin mara kunya." Dada ce ta janyo Zahrah ta zaunar a gabanta tana goge mata hawaye ta ce "Ki yi shiru Shalelen Dada, ki wanke ka ki ta hanayar fada mana gaskiya abinda ya faru na yarda da ke." Nan ta goge hawayenta sannan ta basu labarin komai da ya faru tun daga kan aiken da Dada ta yi mata har zuwa ɓarnar da ta masa da punishment da ya saka ta duk ta sanar har ya zuwa kasa tafiya wanda hakan ya saka ba ta da zaɓi ta kamata a wajen. Shiru falon ya ɗauka ba abinda ke tashi sai sautin kukan Zahrah. Dada ce ta janyo ta a jinkinta ta rungume ta tana rarrashinta. "Ki yi hakuri shalele na san dama sharri ne kawai aka maki." ",Ke Laila ki kiyaye ni ba za ki kaso aurenki ki dawo mani gida kina wargaza mani zuri'a ba. Akan me za ki bayar da shaidar da ba ki ta tabbacin faruwarsa, za ki bi ki tayar wa mutane da hankali ki ƙuntata rayuwar baiwar Allah Saliha na rasa me yarinyar nan ta yi maku da kuka bi kuka ɗora mata karan tsana. Kun tsane ta daga ita har sauran ƴan uwan ta da iyayenta. Na ji kokarin ganin na gyara komI amma hakan ya ci tura so kuke bakin ciki ya kashe ni?" Papa ya yi maganar idanunsa sun canza launi saboda ɓacin rai da yake fama da shi na tsawon shekaru. Ganin lokaci na tafiya ne ga yaran gidan akwai masu zuwa aiki da masu zuwa school ne ya saka Papa cewa . "Ya kamata kowa ya tashi ayi breakfast lokaci na tafiya kada su makara." Gabaɗaya kowa ya mike maza da mata zuwa wajen yin breakfast. Babban dinning table ne wanda ke zagaye da kujeru guda ashirin. Ma'aikatan gidan ne tsaye sun kai su huɗu suna jiran a basu umarnin abincin da za su zuba wa kowa." Nan kowa ya fadi abin da ransa yake so a zuba masa. Umma ce kaɗai ta kasa cin komai, don ta lura Sam huɗubar da take yi wa yaranta da alama Hilal baya ɗauka. Maganar zuci take yi tana cewa. 'Anya ba yaron nan ba ne ya ceci rayuwar yarinyar nan, duba da yadda yarinyar nan ke bayar da labarin cewa ciwonta ya tashi da alama har suma ta yi, to idan ba shi ne ya yi mata magani ba babu yadda za'ayi har ta wanke ta iya tashi har ta fita daga ɗakin sa ƙafafunta, shin ina ma ya samu maganin da ya mata amfani da shi! ? Ta sha fada masu ba ta yafe ba duk wanda ya taimaka wa Zahrah akan ciwonta, idan ya tashi sai dai su barta har numfashinta na karshe ya iso gare ta. Amma Hilal baya jin maganar ta shi ne har da yi mata magani ko, wanda nake tunanin zai iya ƙarasa ta lahira ne ya ceci rayuwarta. Dole na tashi tsaye akansa.' Jin Abba ya taba ƙafarta ne ya saka ta lalle shi tare da fara cin a abinci. Hilal ne ya fito sanye da shigar kananan kaya sa sai zuba ƙamashin turarensa mai daɗin ƙamshi yake yi . Zama ya yi tare da kallon mug ɗin da ruwan shayi ke ciki, wanda hakan ya tabbatar wa da mai aikin ruwan shayi zai sha. Zuba masa ta yi ya ɗauka ya fara sha ba tare da ya haɗa da komai ba. Suna bama cin abinci ne Papa ya lalle su ya ce. "In sha Allah ranar Asabar Fatima Zahrah za ta yi walimar saukar alƙu'ani mai girma. Don haka ranar ba aiki ba zan karbi uzuri daga wajan kowa ba dole kowa ya je wannan walimar in sha Allah." Ba wanda ya tanka a wajen ballantana su ce Allah ya sa Albarka ko su yi mata murna. Don bakin ciki ne ya bayyana a kan fuskarta . Kallon sauran ƴan matan Dada ta yi tare da cewa Nabeela da Kausar Allah ya sa ma kun iya karatun sallah, ga ƙanwar bayanku nan ta sauke kuma nan kuma sakarci uwarku ta daure maku gindi." kallon Maryam da Nadeey ta ji tare da cewa . ",Ku kuna zuwa amma kun kasa hada ko da izu goma Allah ya shirye ku." Zahara ta mike tare da cewa. "Bari na je Dada na shirya zan makara fa." "To Shalele a dawo lafiya Allah ya maki albarka." Da amin ta masa ta tashi ta nufi part ɗin su. Dada ta kalli Ummi ganin duk jinkinta a sanyaye yake ta ce "A'isha kada fa wannan abun ya dame ki." Murmushi ta aro ta yafa a fuskarta sannan ta fara kokarin yin breakfast. A can ɓangaren su Jidderh kuwa yanzu damuwarsu ta kau, ba abinda ke damunsu yanzu, tunda an yi nasarar ciro yaro a cikin Sa'adatu kuma duk suna cikin ƙoshin lafiya. Tana samun kulawa sosai daga wajan likitoci da kuma dangi. Don iyayenta ma suna zuwa asibitin sai yamma suke komawa gidan. Inna a asibitin take kwana Jidderh ke tashi da asuba ta girka masu abincin breakfast. Don kudin da Asadullah ya ba ta da shi duka siyen kayan abinci, idan ta yi shirin zuwa school sai ta dauki abincin idan ta kai asibiti daga na za ta nufi school. _Asadullah_ Saukowa yake yi daga upstair ɗin Zuwa downstairs. Da sallamarsa ciki wanda ba wanda shi kaɗai ya ji sallamar da ya yi ya ƙaraso dinning area. Gabaɗaya sun dinning table suna yin breakfast. Dady da Mom, sai Hajiya Zulaihat, Kamal Fauziyya da Suhailat. Kasancewar ba wanda ya ji sallamarsa ballantana ya amsa masa. Sanye yake cikin Suit blue black with white inner sai necktie blue white ƙamshin turarensa ne ya tabbatar masu da isowarsa. Kallon Dadynsa ya yi tare da cewa. "Gud morning Dad " "Morning my Son ka tashi lafiya?" "Alhamdulillah." Ya amsa yana mai da dubansa ga Mom ɗinsa wacce ke masa kallon kake ya yawo da hankali ko. "Mom Barka da safiya sai yanzu na ga kiranki." Taɓe baki ta yi tare da cewa . "Ka gama duk abinda za ka yi aure ba fashi sai ka yi shi anan kusa kuwa." Kallon matar mahaifinsa ya yi wacce ko kallonsu ba ta yi ba ya ce. "Hajiya ina kwana?" Hajiya Zulaihat ta kalle shi kamar ba za ta amsa ba sannan ta ce. "Lafiya." Idan ba wa da ya kalli bakinta ba ma ba za su gane Hajiya Zulaihat ta amsa gaisuwar ba. Ƴarta Suhailat ce ta gaishe shi cikin farin ciki ya amsa mata cikin kulawa tare da tamabayar ta ya school. Kamal ne ya mike tare da rike hannun Asadullah ya ce. "Big bros ƙafata ƙafarka." Nasir wanda shigowar sa kenan part ɗin ya rike ɗaya hannun Asadullah shi ma yana cewa. "Big bross ni ma ƙafata ƙafarka." Dariya suka yi in banda Hajiya Zulaihat da ta tsuke fuska. Mansur ya gaida su Dady da Mom da Hajiya Zulaihat wacce ta masa kamar dole. Asadullah ya lalle Mansur ya ce "Uncle ya tashi kuwa?" "Eh na barshi yana breakfast." Sallama suka yi duk da Mom ta so Asadullah ya yi breakfast amma ya ce zai yi a kamfani. Ɓangaren ƙanin mahaifinsa ya nufa wato Uncle Adam mahaifin Mansur ɗin. Nasir ne ya masu jagora zuwa ciki. Da sallama a bakinsu suka shiga. Duk suna zane a dinning table Uncle Adam Mami da kuma Maryam da Abida. Gaida Uncle Adam ya yi sannan ya gaida Mami, ta amsa masa cikin sakin fuska tana tamabayar sa aiki. Ya amsa da Alhamdulillah. Abida da Maryam suka taso zuwa gabansa suna gaishe shi, ya amsa cikin sakin fuska da walwala. Kowacce na na ƙoƙarin jan hankalinsa cikin salo Abida ta ce. "Mu da Yayanmu amma ganinsa na mana wahala sai dai a jaridu da gidan T.V ko?" Murmushi ya yi ya ce "Abida aiki suna Mani yawa ba na da lokaci sai dare wani lokacin nake dawowa kuma a gajiya." Maryam ta yi saurin cewa . "Ya ya a bamu lokaci mana a cikin satin nan mu yi fira sosai." "Ba damuwa zan duba na gani ko zuwa Friday da yamma ." Cikin jin dadi suka ce "Promise" Jinjina kai ya yi tare da yi masu sallama suka fice Kamal da Nasir suka yake masa baya. Body guard ɗin sa na tsaye ƙikam suna jiran fitowarsa, yana fitowa hana ɗaya suka karasa in da motocinsa suke. Uncle Adam ya kalli Mami ya ce . "Wai cikin yaran nan wace ce za'a bawa Asadullah??" "Maryam mana ita ce babba " "To ai ni kam Abida na ce masa amma ba matsala sai a canza da ita." Abida ta mike tsaye tana cewa. "Wallahi ban yarda ba akan meye za ku ce haka bayan kun san za'a bashi auren ne saboda kwadayin dukiyarsa, kuma Maryam ba ta da wayon da za ta kwashi dukiyarsa. Don na fi ta gohewa da wayewa da zan san banyar da zan kwaso maku dukiyarsa. Kar ku manta Yaa Asad fa ba karamin attajiri ba ne yaro ne da kuɗi. An ce fa shi kansa bai san iya adadin dukiyar da ya mallaka ba. Kamfanoni gidajen man fetur hannayen jari duk banda sauran kadarorinsa sai na mallake, kuma duk shekara sai na haihu." "Na ji ke mai wayo ko to ba zan hakura ba kuma idan kika nuna Mani bakin ciki da hassada to kin san dai wannan gidan da muke ciki gabaɗaya wanann Mansion ɗin mallakinsa ne, abaunda ake ci da sha da sutura da karatu da motoci da muke hawa duka daga cikin dukiyarsa ne ko? To wallahi kika yi wasa idan na sure shi sai na sa an kore ki daga cikin Asadullah Mansion." A fusace Abida ta yi cikinta suka kacame da dambe. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page0️⃣9️⃣ A fusace Abida ta yi cikinta suka kacame da dambe. Uncle Adam mamaki ya kama yaran nasa, daga magana har da dambe akan mutumin da bai ma san suna yi ba. Mami ce ta daka masu tasowa wanda ya saka suka saki juna kowace na maida numfashi. "Wani irin hakka ne wannan shi da kuke yi akansa ya san ma kuna yi ba. Kowace ta ɓace mani da gani sai mun yi shawara da mahaifinku akan wacce za'a bashi. Don ko ma wace ce cikinku ai duk ɗaya ne idan ɗaya ta samu arziki ai tamkar ita ce ta samu, saboda kowa ce za ta mori arzikin ƴar uwarta." A'a Mamy tun da ni ce babba dole ne na fara yin aure kafin ita ta yi, kuma ni nafi dacewa da shi ba ita ba, ki daina cewa ai duk ɗaya ne domin duk shan inuwar gemu bai kai ya maƙogoro ba. Dan sai ta fara gina kanta kafin sai abin da ta ba mu sannan ki ce duk ɗaya?" Maryam ce ta cigaba da yin magana ran ta a ɓace. Nan suka fara sa'insa dakyar Uncle Adam ya shawo kan yaran nasa suka watse kowacce ta nufi ɗakinta. _Fatima Zahrah_ Fitowa ta yi sanye da riga da wando hadi da hijabi har ƙasa, hijabin fari ne yayin da riga da wando na uniform ɗin ruwan toka. Sanye da niƙab da ta ɗaura a fuskarta wanda idanunta kawai ake gani. Ko k'afarta ta saka Safa. Sanyayyen ƙamshin turaren ta ke tashi daga jikinta. Ƙarasowa ta yi tana kallonsu ta ce. "Zan tafi islamiyya sai na dawo." Ba wanda ya amsa sai Dada da Papa sai kuma yayyun Zahrah. Jin ba wanda ya amsa ne ya saka Papa ya kalle tare da cewa. "Ba ku ji ana sallamar ku ba ne?" Ya yi maganar ransa a ɓacewanda hakan ya saka dole suka amsa mata da a dawo lafiya. Girgiza kansa ya yi cikin damuwa ya bar wajen. Dada ta kalle ta tare da cewa. "Me ya saka baki son shafa kwalli, sai ki bar fuska haka nan ba kwalliya sannan saka kuwalli ma ya zama Maki wahala.? Ga idanun ki masu matukar kyau da jan hakali sai ki bar su a koɗe ba kwalli." Kallon ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan ta jyi tare da cewa. "Ke Tani je ki ɗakina ki ɗauko Mani kwalli a gaban dressing mirror." Cikin girmamawa matar da aka kira da Tani ta amsa wa Dada tare da nufar ɓangaren Dada. Minti ɗaya ta dawo ɗauke da Kwalli ta zo ta kawo wa Dada . Durkusa wa Zahrah ta yi a gaban Dada, nan Dada ta zizara mata kwalli a idanunta. Sai yaba kyawun idanun take yi kafin Zahrah mike ta nufi hanyar fita don zuwa makaranta. Tana zuwa parking lot sai ɗaya daga cikin direbobin ya taso, don dama akasari shi ne yake kai ta makarantar. Har zai buɗe mata bayan motar sai ga Yaa Mansur ya fito. Wani mugun kallo ya yi wa Zahrah kafin ya kalli direban da ya bude mata bayan motar ya ce. "Kai Falalu zo ka ka kai ni wajen aiki na makara." Kallonsa Zahrah ta yi don ta san da gangan yake yi, duka mazan gidan nan suna da motoci su suke driving da kansu. Yana ji tana faɗa ta yi letti amma yana cewa a kai shi. Waige-waige ta fara yi don dama direbobin gidan su biyu ne ɗayan ya tafi garinsu ganin gida. Cikin damuwa ta kalli Ya Munsur ta ce. "Ya dan Allah ka yi hakuri tun da ga motarka nan sai ka hau, ka taimaka ka bar shi ya kai ni na makara." Wani banzan kallo ya mata kamar ba zai yi magana ba sannan ya ce. "Kin fi ni sanin da motar ne, ko ubanki Salisu ne ya siya mani motar.?" Daidai lokacin da Hilal ya fito daga ciki ya nufi motarsa, kallo ɗaya ya yi masu ya kau da kai ya shige motarsa tare da yi mata key. Maigadi ya bude buɗe massa gate ya shige ya fice. "Yaa Mansur don na roke ka akan uzurin da nake da shi kake zagin Abbi, amma kai ma ai ɗa ne a wajen sa kamar..." "Dalla rufe mani baki kafin yanzu na sauya maki kamanni, Salisu Uban Mahmud da Sadik sai ke amma ban da Ni." Da sauri ta kalle shi tana mamaki ko ba komai ai mahaifinta ƙanin mahaifinsa ne bai isa ya canza shi a matsayin kawunsa ba amma yake kiransa sunansa gatsai ba. Juyawa ta yi ta nufi bakin gate don zuwa neman abin hawa. Shi kansa Falalu direba bai so haka ba, saboda mazan gidan kowa motarsa yake hawa. Neman ya ƙuntata rayuwar ta yake so. Wani tunanin Zahrah ta yi ta dawo don ta roki ɗaya daga cikin Yayyunta su kai ta, don kafin ta karasa ta nemi abun hawa za ta ƙara makara. Da sallama ta koma cikin falon, zuwa lokacin duk sun watse Yaa Sadik ne yana kokarin komawa ciki ya ji sallamarta. Amsawa ya yi tare da cewa "Shalelen Dada lafiya ko mantuwa kika yi ?" "A'a Yaa Sadik ban yi mantuwa ba, dan Allah ka taso ka kai ni na makara." "Ina Falalu yake?" "Yana nan." "To me yasa ba ki je ya kai ki ba?" "Na je har ya bude mani motar zan shiga shi ne Yaa Mansur ya ce wai ya kai shi wajan aiki." "What, aiki fa kika ce, ina motarsa take ?" Ba ta bashi amsa ba hakan ya saka ya kalle ta tare da cewa. "Mu je." Fita ta yi daga falon ya mara mata baya, suka nufi parking space, daidai lokacin da direban ke ƙoƙarin barin wajen. Da sauri Sadik ya tari gabansa tare da yi wa Falalu alamar tsaya. Bayan Falalu ya tsayar da motar ne sai ya fito tare da cewa Sadik. "Barka da safiya yallaɓai." "Yauwa barka, ya aka yi Zahrah da ta riga fitowa daga gidan amma ba ka ɗauke ta ba, bayan ka san kowace safiya kake kai ta makaranta." "Eh ina shirin kai ta ne har na bude mata marfin motar sai ga Mansur ya fito ya ce sai na fara kai shi wajen aiki." Sadik ya karasa tare da bude murfin motar na baya in da Mansur yake zaune ya ce. "Shiga ki zauna." Wani kallo Mansur ya yi wa Sadik Sannan ya ce. "Ba ka isa ba wallahi." Ganin haka ya saka Zahrah cewa. "Yaa Sadik ka bari kawai na je na nemi abun hawa idan ba za ka kai ni ba." Ta yi maganar kamar wacce za ta yi kuka. Ba in da za ki je don neman abin hawa, kamar yadda kika ya saba kai ki zai dauke ki ya kai ki idan ya fara ajiye ki sai ya kai mo ma waye in da zai je." Mansur ya fito ransa a ɓace yana yi wa Sadik wani kallo kafin ya ce. "Ba ka isa ba wallahi me kake takama da shi ne da har za ka nemi rai na Mani wayo ko Mahmud zai yi Mani wannan iskancin ne ballantana kai?" " Yaa Mahmud ka ce idan shi zai iya ɗaukar wulakancin da kuke yi ni ba zan iya ba. Akan me za'a kai yarinya makaranta za ka hana sai ka ce kai ne ka siya motar ko kake zuba man da ake amfani da ita, Papa ne ya siya ya ke zuba mai kuma ya ɗauki direban da zai dinga kai yara makaranta wanda saboda su ne aka siya motar. Don kai yara ba saboda mu dinga zuwa aiki da ita ba. Ba ka da hujjar hana ta a kai ta makaranta sai dai ka fito ka shiga taka motar ka je aiki?" "Saboda ubanka Salisu ya siye motar?" "Ba shi ya siya ba kamar yadda kai ma ba ubanka Adamu ya siya ba?" Cikin ɓacin rai Mansur ya ce. "Mahaifin nawa kake kira gatsai haka?" "Oh ashe ba dad'i kake kiran nawa maihaifin kai tsaye, ai uba bai fi uba ba." A zafafe Mansur ya fito daga cikin motar tare da cakumar Sadik shi ma Sadik kamar jiransa yake ya kai masa naushi a baki nan da nan bakinsa ya fashe.Mansur ma ya kai masa naushi ya fasa masa baki. Suka fara dukan juna suna dambe sosai. Cikin tashin hankali Fatima Zahrah ta nufi cikin gidan aguje tana kuka. _Asadullah_ Yana cikin kamfaninsa mai suna ASADULLAH VENTURES. Yana tsaye a ofishin sa yana kai da kawo wa. Staff dake aiki a kamfanin suka ji ƙarar ringing bell. Ƙarar karaarrwar ne ya saka kowa ne ma'ikaci tunanin ko kiran me yau ake masu. Don da sun ji karar ƙararrawa sun san abu mai mahimmanci ne ya saka ake neman su. Sai suka ji magana daga cikin kowace na'ura dake cikin ko'ina na kamfanin na cewa. "The C.E.O of Asadullah ventures wants see us at the staffs comperene now." Nan fa kowa ya mike suka tsaye tsaye daidai saitin wani glaass. Chief of staff meeting ya danna wani remote, bangon glass dake gabansu ya zama lifter haka kowa ya dinga shiga sai suka tsinci kansu a wani waje a ƙafarsa an yi rubutu ta cikin glass din sai shinning yake yi an rubuta . CONFERENCE ROOM. Komai na wajen abun sha'awa ne. Ciki suka shiga su hamsin ne maza da mata, kowa yana sanye cikin shigar suits baƙi. "ASADULLAH AHMAD THE CEO ASADULLAH VENTURES is coming closer to the comperene room." Nan da nan dukkansu suka mike tsaye kafin ya ƙaraso wasu na gyara zaman Suit ɗin su wasu na gyara zaman necktie ɗin su . Ƙamshin daddaɗen turarensa ne ya riga shi isowa gare su. Zama ya yi ya yi sannan ya basu izinin zama. Ko gaisuwa da suka yi bai amsa masu ba Sakatarensa ya yi wa alama da hannu wanda hakan ya saka ya fita. Ba jimawa ya dawo tare da security dake kula da gate. Kallonsa ya yi tare da cewa. "Kai ne ka ture yarinyar da ta zo neman taimako har ta faɗi ƙasa abincin ta ya zube kasa tana kuka ko?" Wani wahalallen yawu securitn ya haɗiye tare da bude baki da niyyar yin magana Sir Asadullah ya ɗaga masa hannu alamar dakatarwa. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *SADAUKARWA* Wannan shafin sadaukarwa ne ga JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION. Haƙiƙa ku Jajirtattun ne kuma haziƙai, marubuta ƴan baiwa Allah ya ƙara mana ƙwarin guiwa. Page1️⃣0️⃣ Wani wahalallen yawu securitn ya haɗiye tare da buɗe baki da niyyar yin magana. Sir Asadullah ya ɗaga masa hannu alamar dakatarwa. "Babu wani uzuri da za ka bani wannan ne karo na ƙarshe da za ka sake wulaƙanta mutane da suka zo neman taimako. Ka sanar da su lokacin da nake sauran mabuƙata." Risinar da kansa ƙasa ya yi alamar ban haƙuri tare da cewa. "An gama sir." Kusan mintuna ashirin ya ɗauka yana masu magana sannan ya ba wa kowa damar fadar wani ƙorafin idan suna da shi. Daga bisani ya sallami kowa ya koma bakin aikinsa. _Fatima Zahra_ Sautin ihun da take yi ne ta nufi part ɗin Papa ya saka hankalin mafi yawan jama'ar gidan hankalinsu ya ɗan tashi. Don sun san akwai wata matsala. Papa dake zaune a falo yana karanta jarida ya jefar da jaridar take da miƙewa cikin tashin hankali yake kallonta. Dada na dake bedroom da sauri ta fito ta tarar da Papa rike da hannun Zahrah yana tamabayar ta abinda ke faruwa. Ta kasa sanar da su saboda tsabar kuka hannun Papa ta janyo yana bin ta da sauri yayin da Dada ta take masu baya. A babban falon duka suka hadu da sauran mutanen gidan. Gabaɗaya suka nufi harabar gidan. Tun daga nesa Yaa Mahmud da ya hangi cewa da Sadik ne ake dambe sai ya ya ruga wajen a guje kafin su isa, ya shiga tsakaninsu ya raba daidai lokacin da sauran mutanen gidan suka ƙaraso. Ganin yadda lokacin guda suka ji ma junar su ciwo jina-jina. Cikin ɓacin rai Papa ya fara magana. Wani wani irin rayuwa ne kuke yi a cikin gidan nan, kuna ƴan uwan juna amma kuke yi kamar za ku kashe juna? To wannan abun ya ishe ni, ku zo ina son ganin kowa a falo yanzu ba sai an jima ba. Ina nufin kowa dake cikin zuri'ar nan. Har wanda baya gidan a kira shi ya zo ina son ganinsa." Daga nan ya yi shigewarsa ciki, Mahmud ya ja hannun Sadik suna shiga su ma suka shiga ciki. _Jidderh_ Tattara kaya take yi cikin wata jaka, Inna na zaune akan kujera rike da baby. Aunty Sa'adatu tana zaune kan gado sanye da hijabi. Yaa Isah ne ya shigo ɗakin tana cewa. "Inna kun gama shiryawa ga shi nan n tsayar da mai abun hawa ku zo mu tafi." Inna ta kalli Jidderh wacce ta gama shirya kayan a jaka ta ce. "Kin gama Jidderh?" "Eh Inna na gama." Ta fada daidai lokacin da take ɗaukar jakar. Isah ma ya shigo ya dauki wasu kayan ya fice . Inna ta kama hannun Sa'adatu ta tashi yayin da Jidderh ke daidaita mata takalminta. Bayan ta saka takalmin ne suka nufi hanyar fita. A bakin asibitin suka tarar da Isah da mai napep din suna jiransu. Shiga ciki suka yi Inna da Jidderh da Sa'adatu suna baya, yayin da isah ke gaba gefen mai napep din. Har ƙofar gida ya kai su, in da Isah ya biya shi kudinsa sannan suka fito da kayan suka shiga cikin gidan. *Waye Alhaji Muhammad Tafarki?* Muhammad Salisu shi ne cikakken sunan Papa, mahaifinsa mau suna Salisu mutumin jihar Katsina ne. Shi kaɗai ne a wajen iyayensa. Wato Salisu da Hauwa'u. Bayan auren Salisu da Hauwa'u sai da suka shekara goma ba su samu haihuwa ba. Wanda har zuwa lokacin Hauwa'u ta fara shiga cikin damuwa, musamman ganin waɗanda suka yi aure lokaci guda da wadanda suka yi aure bayanta daga mai yara uku sai mai huɗu. Shi dai Salisu sai ya yi ta ba ta hakuri tare da tunatar da ita cewa Allah ne ke bayar da haihuwa kuma lokaci ne in sha Allah wata rana za ta samu. A haka har wata rana Hauwa'u ta samu ciki farin ciki a wajen Salisu da Hauwa ba'a magana da ma duk wani makusantarsu. Bayan watanni tara Allah ya sauke ta lafiya in da ta haifo ɗanta namiji tabarakallah. Ranar suna yaro ya ci suna Muhammad. Ya taso cikin so da ƙaunar iyaye, suna yi masa duk abin da yake so. Ya yi karatun boko da islamiyya. Bayan ya samu karatunsa daidai gwargwado don ya sauke al-ƙur'ani ya yi karatu har matakin digiri. Daga nan sai ya fara kasuwanci daga Kano zuwa Katsina. Shaguna biyu ya haɗe waje guda ya fara sana'ar atamfofi. Cikin ƙankanin lokaci arziki ya ƙara bunƙasa. Dan shaguna biyu da ya bude sai kara haɓaka suke yi. Ana cikin wannan yanayin ne Allah ya yi wa Mallam Salisu rasuwa. Wato mahaifin Muhammad. Ya yi kuka sosai wanda har saboda mutuwar ta shiga jikinsa ko fita baya yi sai da ya kwashe wata ɗaya. Yaron shgonsa ke kula da komai kafin ya fara zuwa. Haka suka cigaba da zama da shi da mahaifiyarsa a cikin gidan. Wanda daga baya ne ya siye babban gida wanda ya fi wanda suke ciki. Yayin da wanan da suka ciki kuma suka zuba ƴan haya a ciki. Daidai wannan gaɓar ne kuma Hauwa'u wanda Muhammad ke kiranta da Ummina ta matsa masa akan yi yi aure. Tun da Allah ya rufa masa asiri yana da arzikin da zai iya rike mata biyu ma ba ɗaya ba. Wata rana yana zaune a shagonsa yana lissafin kuɗi. Wata matashiyar budurwar kyakkyawa da kin gan ta kun ga cikakkiyar bafulatana. Dukkanin Yola ce ita mahaifinta ya bar ƙauyen bayan ya siyar da shanunsa ya dawo nan garin Katsina . Ta zo siyen zannuwa a kasuwar ne Allah ya jefo ta shagon Muhammad. Tun da ya kalle ta ya ji ta kwanta masa a rai. Kudin siyayyan da ta yi ya sanar da yayansa kada su karbi kuɗinta. Haka kuwa aka yi ta ƙarasa wajen shugaban tana masa godiya sai ya nemi ta yi masa kwatancen gidansu. Ba tare da ɓata lokaci ba ta sanar da shi, wanda a washegarin ranar ne ya zo gidansu. Bayan sun gaisa ya bayyana mata kudirin sa akanta, don zancen aure ne ya kawo shi ba wani abu ba. Ta amince da zancen suka fahimci juna. Daga nan soyayya ta ƙullu tsakanin Muhammad Tafarki da kuma Amina wacce ake kira da suna Dada. Kasancewar sunan mahaifiyarta ta ci ya sa iyayenta basa kiran sunanta sai dai a kira ta da Dada. Cikin ƙaƙanin lokaci manya suka shiga in da Muhammad ya tura abokin mahaifinsa da abokinsa aka nema masa auren Dada. Wanda aka saka rana biyu masu zuwa. Ummi kuwa sai shirye-shirye, take yi sosai don dama burinta ta ga auren Muhammad. Nan gidan da ya suye wanda suke zaune tare da Ummin ya siya. Rana ba ta ƙarya sai dai uwar ɗa ta ji kunya. An ɗaura auren Muhammad da Dada in da ta tare da gidansa ɓangarensa daban na Dada ma daban. Zama suke na amana da juna don wata matsala ba ya taɓa shiga tsakaninsu ba. Haka ma da Ummi. Don Dada tana shiga cikin ɓangaren Ummi ta yi mata aiyuka, sannan ita take dafa abinci kowane lokaci ta kai ma Ummi. Ana nan har Dada ta samu ciki wanda ya sa familyn suka kasance cikin farin ciki. Dada tana samun kulawa sosai daga wajan uwar mijinta. Bayan wata tara ta haifi ɗa namiji, nan ma zo ku ga farin ciki a wajen wannan family. Ranar suka aka sakawa yaro suna. Abubakar. Ya taso cikin kulawar uwa da uba da kuka Kaka. Bayan shekaru biyu Dada ta dake samun wani cikin. bayan watanni tara ta sake haihuwar ɗa namiji ranar suna yaro ya ci suna Adam. Umma ke kula da jikokinta nsosai take nuna masu ƙauna dujansu. Shekaru uku ne ke tsakanin Abubakar da Adam. Lokacin da aka yaye Adam a lokacin ne aka saka Abubakar Makarantar boko da ta islamiyya. Kuka a wannan tsakanin ne Dada ta dake samun wani cikin in da bayan watanni tara ta sake haihuwar ɗa namiji ranar suna yaro ya ci suna Salisu. Wato sunan mahaifin Muhammad da ya ya rasu ya saka masa. Yaron da aka nunawa gata da so da kulawa fiye da sauran yaran. Kasancewar sunan mahaifinsa ne d shi wato mijin Ummi. Daga Muhammad har Dada ba mai kiran sunan Salisu sau suna kiransa da suna Abbi. Umma kuma mijina take kiransa. So da ƙauna da suke yi wa Abbi ya kasa ɓoyuwa. Dan duk wanda ya so gidan nan dai ya fahimci sun fita soyayyar Abbi fiye da sauran yaran. Ko kukansa suka ji sai hankalin su ya tashi sosai. Yaran sai suna kiran Muhammad da suna Papa. A ƙa'idar Papa ko ya dawo kasuwa sai ya fara zuwa ɓangaren mahaifiyarsa ya gaishe ta, ya ba ta nata tsarabar sannan ya wuce da nasu ɓangaren su. 'Ya'yan nasa ma anan yake ganinsu ya barshi tare da Kakarsu. Sai dai tun da aka haifi Salis wanda suke wa laƙani da Abbi Dada da Papa suka kasa kawaici akan sa kamar yadda suke yi akan sauran yaran biyu. Don Papa ko ya dawo kasuwa ba ya ɗaukar yaro daga ɓangaren Dada ya tafi da shi nasu bangaren nan ya ke barinsa. Amma tunda aka haifi Salis ya kasa yi mata kawaicin da yake yi akan Abubakar da Adam. Don sai ya ɗauke da ya jI shi can ɓangaren tare da su, sauran ƴan uwan kuma sai su natsu tare da kakan. Ita kanta Dada lokacin da take goyon sauran yaran ko ta ji suna kuka a ɓangaren Ummi ba ta zuwa sai ta yi kawaici har sai Ummi ta kira ta ko da kawo yaran . Amma ta ɓangaren Salisu wanda suke kira Abbi ba wannan kawaicin, tana jin kukansa zata nufi ɓangaren Ummi cikin hanzari. Ta ɗauke sa ta ta je da shi part ɗin sa bashi mama ya sha . Kuma wani abu da yake ɗaurewa Umma kai sauran yaran ba sai ta je ta ɗauko su ko ta ce a kawo su ba, Dada da kanta za ta kai su ko Papa zai kai su amma shi wannan Salis da ake goyo ba'a kai shi dai dai idan ita ce da kanta ta je ta ɗauko shi. Umma ta so ta yi magana amma sai ta bar abun a cewar kika saboda shi ne ƙarami shi ya saka suke nuna masa irin wannan soyayya. Duk da cewa sauran ma ko da suke ƙanana ba'a nuna masa haka ba, ko shi Abubakar da suke ƙarami kuma a kansa aka fara haihuwa ba'a nuna masa wannan soyayyar ba, haka ma Adam. Ana cikin wannan haka nan ne aka saka Adam makaranta ɗaya da Yayansa Abubakar. Lokacin ne Kum aka yaye Salis wanda ake kira da Abbi. Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya har aka yaye Salis. Lokacin da aka yaye shi Ummi ba ƙaramin mamaki ta yi ba, ganin uban jibgin kayan wasa da aka siyo masa, ɗaki guda aka cika da kaya. Wasa. Ga kuma kayan yaye da aka siyo masa sakamakon yaye shi aka yi. Kama daga kan kwalim biscuits, kwalim chocolate da Sweet da wasu snack da lemun roba da na kwali duk an siya masa. Ga motar wasan yara jirgi da keke da jita da kayan wasan yara kala-kala. Umma ta kira Papa ta ce masa "An ya kuna adalci a tsakanin ƴaƴanku kuwa ? Me ya saka kuka fifita soyayyar Salisu fiye da sauran ƴan uwansa?" Kallonta Papa ya yi tare da cewa "Ba fifita shi muka yi ba Ummi, duk da cewa idan n kalle shi sai na ji dadi saboda Sunan Mahaifins ne da shi." Wannan ba dalili ba ne sai dai zan fada maka ku ji tsoron Allah ku yi adalci a tsakanin ƴaƴanku. Ba ni ce na fada ba fadar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ne. Za ka iya tafiya." Tashi ya yi har ya kai bakin ƙafa ya juyo jin tana cewa. "Kada ku janyo ƙiyayya a tsakanin ƴaƴanku matukar kuka cigaba a haka. Idan ka fita ka siyo Mani maganin zazzaɓi kai na ciwo yake yi." Jinjina kai ya yi sannan ya fita don zuwa siyo mata magani. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page1️⃣1️⃣ Jinjina kai ya yi sannan ya fita don zuwa siyo mata magani. Bayan kamar mintuna ashirin ya dawo hannunsa rike da ledar magungunan da ya siyo mata . Tana kwance a saman doguwar kujera ya shigo da sallama a bakinsa kallo ɗaya ya yi mata gabansa ya faɗin, a guje ya ƙara da gabanta tare da kiran sunanta. Shiru ba ta amsa har sau uku yana kiran ta shiru ba amsa, hakan ya saka ya fito a gigice ya koma ɓangarensu. Wayarsa ya ɗauka ya kira wani abokinsa mai suna Dr Ibrahim ya sanar da shi halin da ya zo ya samu mahaifiyarsa. Dada ma ta nufi ɓangaren Umma cikin tashin hankali. Ganin ta ta yi kwance rai ya yi halinsa. Durƙusawa ta yi tana kuka a wajen. Har Dr Ibrahim ya zo da kayan gwaje-gwaje ya karasa gaban kujerar da Umma ke kwance. Bayan ya yi gwaje-gwaje ne ya girgiza kai tare da abokin nasa wanda Papan ma shi yake kallo. "Abokina sai dai da mu yi hakuri Inna ta riga mu gidan gaskiya." Wani jiri ne ya so ɗibar Papa wanda hakan ya saka shi zubewar bisa guiwoyinsa. Sai nanata kalmar Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un yake ta nanata wa. Kafin zuwa can hawaye suka fara bin fuskarsa. Zani ya dauko a bedroom ɗin ta ya zo ya lallube ta har fuska. Dada ma sai kuka ta ke yi sosai don ta ji mutuwar Umman . Dr Ibrahim ya fita tare da sanar da su yana zuwa Nan fa labarin ya fara karade unguwar mutune suka fara shigowa. *Bayan shekaru biyu* Haka rayuwa ta cigaba da tafiya a wajen wannan iyalan na Papa. Yana kyautatawa iyalansa sai dai ya fifita soyayyar Salis a cikin ƴaƴansa uku. Don komai na Salis na musamman ne iyayen su ke masa . Kullun Papa idan zai dawo kasuwa sai ya yi wa Salis tsaraba wanda ba ya yi sa sauran yaran. Kama daga kayan sawa har kayan maƙulashe. Don har yanzu ya kai Abubakar wanda a yanzu yake da shekaru takwas a duniya ya fara fahimtar cewa iyayen nasa na nuna masu wariya a tsakanin yaransu. Ko Adam da yake da shekaru biyar ya fara gane cewa an fi son Salis fiye da su. Saboda ƙiri-kiri suna kallo za'a siyo masa kofin gwangwani da yawa a jera wa Salis a ɗaki bayan ƙwai da ake tar masa a ɗaki din zuwa lokacin bai wuce shekaru biyu ba ko daa ka siyo masa tsire da nama ba iya ci su yake ba . Haka za'a loda masa a gabansa sauran yi sauran ƴan uwansa na kallo ba'a ajiye masu ba kuka ba'a tsammu su ba. Suna kallo da halin su ci Lokacin ne kuma aka yaye shi. Bayan yaye shi ne Dada ta sake samun wani cikin, bayan watanni tara ta haifi ƴa mace. Sun yi farin ciki da samun ƴa mace sosai. Ranar suna yarinya ta ci suna Laila. Zuwa lokacin an saka Salis makaranta, sai dai ko a makaranta ma an fifita shi za sauran ƴan uwansa. Don makaranta da aka saki shi ya fi wanda aka saka sauran ƴan uwansa kudi, don makaranta ce ta kuɗi sosai tana da tsada. Kullun da safe idan Suka shirya zuwa makarnata za'a girka wa Abubakar da Adam abinci su je da shi makaranta yayin da shi kuma Salis za'a soya masa ƙwai da dankalin turwa wata rana ya kai ƙwai da indomie da lemun kwali ko na gora da sauransu. Ko da sun ce wa Papa ya siya masu abinda ya yake siya wa Salis ba ya siya. Makarantar su Abubakar da Adam ya fi nisa, makarantar Salis a kusa yake amma kullun safiya sai Papa ya kai Salisu makaranta a motarsa sannan ya wuce kasuwa. Su kuma sauran ƴan uwansa sai su tafi makarantarsu a ƙasa. A haka rayuwa ta yi ta tafiya ana nuna masu banbanci da fifiko wanda har hakan ya kunna wa Ababakar da Adam wutar ƙiyayyar ɗan uwansu. Don haushinsa suke ji a cikin zuciyarsu. Don ko Laila dake ƙanwa ce a wajen Salisu ba'a nuna mata soyayyar da ke ji nunawa Salis . Ko da ta cika s shekaru uzu makarantar da suke aka haɗa ta a cikinsa. Kuma sai a siya wa Salis abu amma ita a barta haka nan ba komai. ko Makaranta ce tana gani za'a kai Salisu da mota yayin da ita kuma ba ta damuwa ba saboda karancin shekarunta a lokacin. Yau da gobe har ita ma ta yi wayo ƴan uwan suka fara cusa mata tsanar Salis, don ida za su je makaranta a hanya suke zancen yadda iyayen suke nuna banbanci a tsakanin yaran ta hanyar bata labarin abubuwan da ke masa wanda su ba'ayi masu da yadda kullun Papa ya dawo kasuwa sai dawo masa da tsaraba. *Bayan shekaru goma* Abubakar ya gama karatun secondry school yayin da Abba ya nema masa girbi a jami'ar Bayero in da y fara karatunsa na digiri . A lokacin kuma Adam na s.s. 2 a secondry school yayin da Salis yake j.ss 2 ita kuma tana primary 5 ne a lokacin. Bayan Abubakar ya fara karatun jami'a ne sai ya zama Adam ne ke zuwa tare da Laila makaranta, har lokacin Papa bai daina kai Salisu makaranta a motarsa ba, kuma har lokacin bai daina siyo masa kaysyyskin da yake siyo masa ba, kama daga na ci da na sha har zuwa na sakaws. Don a ɗinkin Dada an yi masa jere da kifin gwangwani da sauran kayan maƙulashe da su lemukan kwali. Dan ko girki idan aka gama sai a saka masa naman da ya fi na ƴan uwansa. Ranar da ba makaranta Papa ya kan ɗauke shi ya tafi da shi kasuwa wurin kasuwancinsa. Har ya kai Dr Ibrahim abokin Papa ya yi wa Papa magana akan yadda yake fifita son ɗan sa Salisu fiye da sauran wanda har Dada ma ta fifita soyayyar Salisu fiye da sauran duk da kasancewar Laila ƴa mace ƙarama a cikinsu kuwa. Don dukkansu uku a jami'ar Bayero university suka yi karatun digi yayin da Salisu aka tura shi ƙasar Ingila ya ƙarasa karatunsa har matakin masters ɗin sa. Papa ya sour babban fili wanda ya yi gini ɓangare ɓangare a cikin gidan. Bayan ya san cewa ƴaƴansa Abubakar da Adam suna neman aure. Don ya ce baya son yaransa su yi nisa da su. Don zuwa lokacin arzikinsa ya ƙara bunƙasa sosai. Abubakar yana aiki a jami'ar Bayero University ne yayin da Adam ke aiki a kamfanin Papa dake nan garin Kano. Duk da cewar Salisu baya ƙasar sai dai idan ya dawo yake zuwa amma sam ƴan uwansa nasa mu'amala da shi. Ko fira suke yi da zaran ya zo cikinsu ya zauna za su watse su bar wajen. Wannan ƙiyayyar ta yarinta sun gina ta a cikin zuciyarsu. Sam ba sa ƙaunarsa a cikin zuciyarsu. Don ko motoci da Papa ya siyaasu na sa ya ninka kudin ta su motar sau uku. A hankali bikin Abubakar da Adam ya ƙarato don rana ɗaya za su yi auren. Ana saura sati ɗaya bikin Salis ya diro a ƙasar don sauran masa shekara ɗaya ya kammala haɗa masters ɗin sa. An saka ranar auren Laila ita ma nan da wata ɗaya mai zuwa. Bayan kammala bikin su Abubakar. Ko da Salisu ya dawo garin ana ta a hidimar biki in da ya cire kuɗaɗe masu yawa ya bawa ƴan uwansa do su ƙara wajen hidimar biki amma tsabar tsanar da suka masa ko abin hannunsu ba sa son karɓa. Da ya same su duka su uku Abubakar da Adam da Laila ya masu magana akan abinda ya masu da suka tsane shi basa son ya rabe su sai suka nuna masa cewa ai shi dama daban yake ba a cikinsu yake ba. Shi ai daban ne su uku suke abu ɗaya shi dama an nuna masa ba ɗaya suke ba. Wata ranar juma'a jama'a suka shaida ɗaurin auren Abubakar Muhammad Tafarki tare da amaryasa Maimuna Ibrahim, sai kuka aka ɗaura auren Adam Muhammad Tafarki tare da amaryarsa Amina Abdullahi. Bayan an gama shagulgulan biki aka kawo amare a ɓangarensu da ke nan c cikin gidan Papa kowacce ɓangareta daban. Suna zaune lafiya ba wata matsala a tsakaninsu. Har aka yi bikin Laila in da aka ɗaura auren ta da angonta Aminu in da aka kai ta gidansa dake garin Zaria. Ba dade wa Maimuna matar Abubakar ta haifi ɗanta namiji ranar suka yaro aka sakawa yaro suna Hilal. Lokacin cikin Amina wata biyar, kuma a wannan lokacin. Daidai wannan gaɓar ne Salisu ya dawo daga ƙasar waje. Ya so ya yi aiki a can saboda wani kamfani sun ɗauke shi aiki, amma. Papa ya hana don ba zai iya nisa da ɗansa mafi soyuwa a gare shi ba. Bayan dawowarsa Papa ya ce shi ma ya yi aure, ya ce baya da wacce yake so hakan ya saka Papa ya nema masa auren ƴar abokin kasuwancinsa, Alhaji Garba. Abokin Papa ne shi ma kuma mutum ne kamili ganin tarbiyyar yarinyar ya sa Papa sha'awar aura wa Salis ita. Ko da Papa ya dawo ya tura Salisu ya je ya gana da ƴar abokinsa, bayan ya ke kuka suka fahimci juna aka tsaida rana nan da wata ɗaya mai zuwa. Papa ya saka aka gyara masa ɓangaren dake kusa da nasa. Komai na ɓangaren na musamman ne don ya fi sauran duka ɓangarorin gidan kyau. Hatta Maimuna da Amina sun san cewa an fifita soyayyar Salis fiye da na mazajensu. Don haka suka suka biyewa mazajensu. Anyi bikin Salis da Amaryarsa Aisha lafiya in da ga tare a ɓangaren da aka tanadar mata A'isha ba ta da matsala mace ce mai tsananin kyau da sura idan ka ganta za ka rantse daga jinsin Larabawa ta fito. Ha tsabta da son kwalliya. Mace ce mai son zaman lafiya ba ta da hayaniya. Tun da aka yi auren Dada ce ke aika mata da abinci daga ɓangarenta. Har sai da ta cewa Dada ta huta haka nan za ta dinga girkawa da kanta. Tana girkawa kullun ta aikawa Dada da Papa na su, har ta fara kai wa Maimuna da Amina suka ce ba za su ci ba kada ta sake kawo masu abun ci. Don ta lura ba da sonta ita da mijin don ko gaishe su ta je yi da ƙurar suke amsawa amma ba ta fasa ba. Har ta yi wa Salis magana ya nuna mata kada ta damu haka suke ya saba da hainsu daga su har mazajensu. Papa da Dada sun zaunar da su don sasanta su amma ba abinda ya canza. Har Amina aka samu jikoki biyu in da Maimauna ta haifi Hilal yayin da Amina ta haifi Y Mansur, ko da Aisha ta shiga yin barkar haihuwa ba'a bari ta dauki yaron jariri ba ko sakar mata fuska ba su yi ba don dama ba a gidan ba ne kasancewar haihuwar fari ne sai bayan kwana arba'in ne aka dawo da su ɗalibai Hakan ya da ta yi zamanta ba ta sake zuwa ba . Don lokacin ma tana da ciki Dada ce kawai ta sani. Kwanci tashi cikinta ya kai wata tara in da ta hafi ɗa namiji sai dai Dada ta hana ta koma gidan ta ce ai duk ɗaya ne, iyayen suke bar ta wajen Dada. Ranar suna yaro ya ci suna Mahmud. A haka rayuwa ke tafiya daga sakanni zuwa mintuna daga mintuna zuwa awanni da awanni zuwa kwanaki daga kwanaki zuwa satittika daga satittika zuwa watanni har zuwa shekaru. Yanzu haka Maimuna na da yara uku. Hilal, Faisal, da Maryam. Amina kuma yara biyu take da su Mansur da Nadiya. Yayin da kuma A'isha ke da yara Uku Mahmud, Sadik da Fatima Zahrah. A can ɓangaren Laila tana da yara biyu mata kasancewar ta dade ba ta samu haihuwa ba, Nadiya da Kausar. Har lokacin ba jituwa don ƙiyayyar ta shafi jikokinsu nasa shiga sabgar yaran Salisu. Musamman Hilal da yake da wani bakin hali da mishkilanci don ko kakannin ba su ishe shi kallo ba tun yana yaro. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page1️⃣2️⃣ Har lokacin ba jituwa don ƙiyayyar ta shafi jikokinsu nasu ba su shiga sabgar yaran Salisu. Musamman Hilal da yake da wani baƙin hali da mishkilanci don ko kakanninsu ba su ishe shi kallo ba tun yana yaro. Ko sauran ƴan uwansa nasa ma baya cika kula su, ko da irin yara suna zaune suma wasa ya baya shiga cikinsu. Duk da kasancewar Faisal ƙaninsa ne uwa ɗaya uba ɗaya amma baya wasa da shi ko Maryam ma fa take mace kuka ƙaramar ƙanwarsa baya shiga sabgarsu. Ko yana zaune a wajen suka je wajen kusa da shi sai dai suyi ta wasansu iya su ƙaɗai. Idan ma ya ji sun dame shi da hayaniya tun da baya son hayaniya zai tashi ya bar masu wajen ne ya koma wani wajan ya killace kansa. Mansur da Nadiya sukan shigo domin wasa da su duk da haka shi baya shiga kum Mansur ne sa'an Hilal don ko watanni biyar ne a tsakanin Hilal da Mansur. Yaran Salisu kuwa Mahmud da Sadik ba da zuwa ko ina daga part ɗin su sai kuma na kakanninsu don ko sun je sai an koro su wata rana ma s haɗa masu da duka don Maimuna matar Abubakar ba ta da mutumci ko kaɗan. Da Mahmud suka fahimci tsanar da aka masu sai suka daina shiga wajan su sai dai wakan kakanninsu. Ita fama ƙanwarsu Fatima Zahrah ba ta zuwa ko ina kullun tana maƙale da Dada ballantana ba isashshiyar lafiya ce da ita ba tana da ciwon athma kuma mai tsanani da tari ya fara mata daga nan idan tana tari sai ta ce wa Ummi tana jin numfadhinta sama-sama ita Umminta ta ɗauka mura da tarin da take yi ne ya sa take numfashi sama-sama don haka dai ta faɗa wa Abbi ya siyo mata maganin tari suka fara ba ta amma bai daina ba. Don haka suka yanke shawarar kai ta asibiti. A ranar da suke da niyyar kai ta asibiti ne Ummi ta shirya ta tana kirasa girki kafin su tafi. Ta ɗora manja a tukunya ta ɗora a wuta sai ta ji ƙarar kiran wayarta, fita ta yi daga kitchen ɗin ta nufi falo don ta san Abbi ne ke kiran wayarta. Tana falo tana amsa wayar da Abba ya kira ta sai Fatima Zahrah ta nufi kitchen lokacin manja da Ummin ya ɗora a wuta ya ƙone yana hayaƙi. Fatima Zahrah na shiga ta shaƙi wannan hayaƙin sai ta fara tari numfashinta ya fara fita sama-sama ta fadi a wajen daidai lokacin da Ummin ta dawo kitchen da sauri ta lashe wutar tare da ɗaukar Zahrah ta nufi Falo don ba kowa Mahmud da Sadik suna school ita ma saboda asibitin da za su ne ya sa ta zauna gida Abbi na office. Ɗaukarta ta yi ta nufi harabar gidan tana ƙwalawa direba kira. Dada ce ta fito don ɓangaren su yana kusa da nata. Ganin Ummin rike da Zahra hankalin Dada ya tashi da sauri ya ƙaraso tana tambayar abinda ya same ta. Shiga motar tayi bayan Ummin ta saka Zahrah a bayan motar sannan ta koma sauri-sauri ta dauko Hijabinta. Koda suka karasa asibitin ganin halin da Zahrah ke ciki aka amshe su cikin gaggawa. Bayan wani lokaci tana kwance tana barci Dr ya fito ya basu izinin su zo yana son ganinsu s office dinsa. Nan yake sanar da su cewa Fatima Zahrah na ɗauke da cutar Athma. Cikin tashin hankali Dada ke mamakin wai ƙaramar yarinya mai shekaru goma ce ke da wannan cuta. Nan ya sanar da su cewa ciwon baya son sanyi zai iya tashi idan sanyi ya shiga jinkinta Kum ta kiyayi wanka da ruwan shayi da shiga cikin ƙura ko hayaƙi ya dai kafa masu dokokin da za su kiyaye tare da magunguna da kuma Inhelar da za ta dinga shaƙa. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya a cikin gidan ba abinda ya sauya akan zaman da suke yi, ana cikin wannan halin Laila ta dawo da yaranta wai mijinta ya sake ta. Ta kwaso yaran wai ba za ta bar su a wajen kishiya ba. Tun da Laila ta dawo ta fahimci soyayyar da Dada da Papa ke yi wa yaran Abbi musamman Fatima Zahrah ya sa ita ma ta fara jin haushin hakan. Don ba su ma damu da yaranta yadda suka damu da Zahrah ba da yadda suke kula da ita ya ƙaru saboda laruran da take da shi . Ta so ace Dada za ta fifits Nabeela da Kausar me amma ta ga ba haka ba. Don haka sai ga haɗa kai da sauran matan gidan suna ƙuntatawa Ummi. Papa ya samu buɗi sosai ya canza masu gidan wani ƙaton gida na Alfarma ya siya mai part da yawa sama da ƙasa. An gyara gidan sosai ba kowane iyali part nasu. Iyaye mata part ɗin su hudu har da Aunty Laila kenan kowacce part ɗin ta da ɗakunan hudu da falo bayan babban falon na kowa a gidan dai samarin gidan kowanne part ɗin sa na upstair. Zuwa lokacin Hilal mahaifinsa ya kai shi karatu ƙasan waje. Sai da ya yi shekaru biyar bai dawo ƙasar ba, sai dai su dinga waya da iyayensa. Yana can zaune a ƙasar America yana gudanar da aikinsa a can. A yanzu yana da matsayin Chief of staff of the army Tamim Walton. Yana gudanar da aikinsa a can ƙasar America saida mahaifinsa Dady ya matsa masa Sannan akan ya dawo, baya haka ma mahifiyarsa Mummy ma ta damu da dawowarsa. Yaa Mahmud kuma aikin banki yake yi, yayin da Yaa Sadik kuma lauya ne, sai Yaa Mansur kuma ɗan jarida ne, sai Yaa Faisal dake shaƙar ƙarshe a jami'a. Hakan ya saka shi ya dawo ƙasar in da suka shirya liyafa ana shagailin dawowarsa. Bayan kwana biyu da dawowarsa ne Dada ta dafa masa zogale wanda ta aika Fatima Zahrah ta kai masa har ta yi masa ɓarna ya saka ta punishment ciwonta ya tashi ta kwana a ɗakinsa wanda ya kawo hargitsi a cikin gidan. Har sandiyar fitar Zahara zuwa makaranta da Mansur ya ce a kai shi Wajan aiki har aka yi dambe da Yaa Sadik da Yaa Mansur har Papa ya kira kowa ya zo. *Cigaban labari* Gabaɗaya ilahirin jama'ar gidan kowa ya hallara a falo. Ga fuskar Sadik da Mansur duk sun ji wa juna rauni. Kallo ɗaya za ka yi wa Papa ka gani ɓacin ran da yake ciki. "Ban san ya kuke so na yi ba, so kuke ku kashe ni da baƙin cikinku ko? Yaushe za ku so juna? Yaushe za ku saka ni farin ciki kuma ku zauna cikin farin ciki?" Kallon Munsur ya yi tare da cewa. "Kai a matsayinka na Yaya a wajen Zahra don ko kana so ko ba ka so ita ɗin jininka ce ba ka isa ka canza ta ba. Shin akwai wanda baya da motar kansa ne a cikin samarin gidan nan? Sauran motocin gidan na tanade su ne saboda ƴan mata idan za su je makaranta da iyayenku mata idan za su fita unguwa. Amma saboda neman fitina da tashin hankali ya sa ka hana ya kai ta bayan ta makara da zuwa makaranta ko?" Kallo sa ya mai da kan Nabeela ya ce. "Kema ranar har ta shiga Mota kika ce sai dai ta fito akai ki a dawo da ke kafin a kai ta ko? Shin motar mutum ɗaya yake zama a ciki ne ba na za ku iya zama a tare a kai kowacce makarantarta ba?" Budar bakin Nabeela ta ce. "To Papa ta yaya zan shiga motar da ita ta saka mani cutar da take da ita, ai ana ɗaukar cuta ta shaƙar numfashi." Kausar ta yi saurin cewa. "Wallahi ni ma ba zan iya zama waje daya da ita ba." Sadik ya yunƙura zai yi magana Abbi ya ɗaga masa hannu. Hakan ya saka ya danne zuciyarsa. Zahra kan hawaye ne ke fita daga idanunta ganin yadda ƴan uwanta ke gudun ta saboda wata larura da Allah ya jarabe ta da shi. A fusace Papa ya ce daka masu tasowa tare da cewa. "Kuna da hankali kuwa? Me take da shi da kuma gudunta? Ko cutar ƙanjamau da hanta da suke da illa ana ɗaukarsu ta hanayar shaƙar iska ne? Ballantana ciwon asma meye illarsa?" Kallon Aunty Laila ya yi tare da cewa. "A gabanki yaran nan suke fadin irin wannan magana kina kallonsu ko?" "Papa ka yi hakuri yara ne ba su san komai ba." "Irin tarbiyyar da kike yi wa yaranki kenan ko? To na gaji haka nan, dama ina fama da iyalan gidan nan amma tunda kika rabu da mijinki kika dawo da yaranki komai ya ƙara lalacewa. Ki kwashe su ki mayar da su gidan uban su ba. Zan iya ba." "Papa don Allah ka yi hakuri Wallahi mahaifinsu baya ƙaunarsu yanzu haka ma baya ƙasar amma da zaran ya dawo zan mayar da su." Wayarsa ce ta soma ruri ya duba ya ga abokinsa ne Dr Ibrahim. Hakan ya saka ya ɗaga. Bayan ya saurare maganar ne ya katse kiran wayar tare da ɗaukar sandarsa ya fara tafiya yana cewa. "Fita na gaggawa ta kama ni, za ku iya tafiya sai na dawo." Daga nan ya fice daga gidan kowa ya watse Mahmud ya kai Sadik asibiti yayin da shi ma Mansur Faisal ya ɗauke shi don kai shi a yi masa diresin Wajen. Daga nan kowa ya watse washegari tafiyar gaggawa ya kama Hilal ya koma America. Papa da kansa ya saka aka kawo masa sabuwar mota ya mallaka wa Zahrah, ya ce duk in da za ta ke ta tafi da ita ta bar masu wadancan motocin. Ta yi farin ciki da godiya ta ce ba ta son direba za ta dinga driving da kanta. Don haka Yaa Mahmud ne idan yana free yake koya mata. Sai da Hilal ya dauki lokaci bai dawo ƙasar ba don har sai da Mom ta matsa masa akan rashin dawowarsa. Hakan ya saka rana ya dawo kasar tare da yaransa sojoji, wanda saboda murnar dawowarsa ne Mummy da Umma da Aunty Laila suka ce da masu girkin gidan kowacce kada ta shiga kitchen su za su shiga su girka masa girki na musamman. Ranar da ya dawo ne Zahrah tana kwance a asibiti da ciwonta ya tashi ta zo ɗaukar magani Aunty Laila ta cilla maganin ƙasan kujera har ƙawarta da abokinta suka ɗauke ta zuwa asibiti. *Cigaban labarin* Bayan Fatima Zahrah ta gama waya da ƙawarta akan cewa akan za ta kawo mata abincin da za ta ci ne ya sa koma cikin ɗakinta tana zaman jiran zuwan A'isha. Bayan kamar mintuna talatin aka tura kofar dakin aka shigo da sallama. Tashi zaune ta yi tana amsa sallama tana kallon A'isha. "Sannu ya jikin?" "Da sauki na gode." Miƙa mata abincin ta yi ta cire cokali ta bude ta fara ci. Aisha ta tashi ta karasa ta dauki mata ruwa a fridge. Bayan ta gama cin abincin ne A'isha ta kalle ta ta ce. "Don Allah ki daina sakaci har ciwon ya yi tsanani. Ba ki da magani ne?" "Ina da magani na je zan ɗauki maganin shi ne a falo shi ne Aunty Laila ta jefa su ƙasan kujera suna kallona suka tafi suka bar ni. Sai ga Yaa Mansur ya sake buɗe gudun A.C hakan ya saka ciwon nawa ya yi tsanani. Sai ga kiran wayar abokin kwara ya kira ni a waya ya ji halin da nake ciki maybe shi ya saka ya kira ki, farka wa na ji na ganni tare da ku a asibitin. Bare sun Y Mani abin da jini na suka kasa yi mani. Kun cece rayuwata yayin da dangina suka nemi kashe ni." *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page1️⃣3️⃣ Bare sun yi mani abun da jinina suka kasa yi mani. Kun ceci rayuwarta yayin da dangina suka nemi kashe ni." Ta yi maganar tana goge ƙwallar da ya gangaro daga Idanunta. "Gaskiya zamanki ke kaɗai a cikin wannan gidan ba zai yiwu ba, saboda ba ki da isashshiyar lafiya ga Umminki da Abbinki ba sa gari, dama a ce ko su Papa da Dada suna nan ne da sauƙi. To dukkansu huɗu tare da tafi Saudiya aikin umara to ya za ki yi?" "Ba yadda zan yi A'isha." "Ko za mu je ki cigaba da zama a gidanmu kafin su Umminki su dawo?" "Rufa mani asiri kafin a ƙalla mani wani sharrin, a haka ma kwana ɗaya da muka yi asibiti sai da suka ce wai yawon karuwanci na tafi." "Subhanallah!, To Allah ya kyauta." Da amin Zahrah ta amsa yayin da wayarta ke ruri. "Wai ina Yaa Mahmud da Yaa Sadik ne?" "Sun bi su Abbi Ni ma saboda exams na ce ba zan je ba." "Okay Allah ya dawo da su lafiya." Bayan sun taɓa fira A'isha ta yi mata sallama, miƙewa ta yi suka nufi ƙofar fita. A ƙofar falon suka hadu da Yaa Hilal yana ƙoƙarin shigowa falon, tsaya wa suka yi ya fara shigowa A'isha ta kalle shi ta ce. "Sannu ina wuni?" Ko kallonsu bai yi ba ballantana ta saka zan zai amsa mata, da kallo ta bishi ya haura upstairs har yana tsallake steps. Sai da ya ɓacewa ganinta sannan ta mai da dubanta ga Zahra ta ce. "Shi wannan guy ɗin kullum idan aka gaishe shi baya amsawa mutane gaisuwa, dai ya yi kamar kurma don ko kallon mutum baya yi ballantana a san cewa yana ji baya amsawa ne." "Hmm to dole ne sai kin gaishe shi ballantana idan bai amsa ba ki yi ta damuwa da mita?" "Ke ma kin san ban cika gaida mutane ba, ban san me ya saka ba shi duk na hadu da shi ba na iya haƙura sai na yi masa magana ba, so nake ko sau ɗaya ya kalle ni ya amsa mani" "Saboda me?" "Kawai dai ban taɓa ganin namijin da ya cika duk wasu qualities da ake buƙata a wajen ɗa namiji ba sai shi." Taɓe baki Zahrah ta yi tare da cewa. "A ganinki kenan, shi ɗin wasali ne da shi da za ku ce baki taba ganin ɗa namijin da ya kai shi ko yafi shi ba?" Murmushi A'isha ta yi tare da cewa. "Zahra kenan, ke ai baki san komai ba akan nagarta ɗa namiji, amma bari na fada maki duk in da ake neman cikakken ɗa namiji aka zo kan wannan guy ɗin an gama. Yana da ƙira da ƙira da da cikar halitta da zati irin na cikakken ɗa namiji. Yana da wani irin kwarjini da zarra wan da ba kowane irin mutum zai iya tunkararsa ba, ni kai na nikan so na yi masa magana wanda zai sa ya kalle ni amma sai na ji na kasa saboda kwarjinin dake cikin idanunsa, wallahi yana da jini mai gudu a jikinsa." Cikin takaici Zahra ta ce. "Kema sai ki shiga sahu tun da kin zama ƴar wahala." Cikin rashin gane in da zancen ta ya dosa ta ce "Sahun me zan shiga?" "Sahun masu sonsa mana, ga Aunty Nabeela nan da Aunty Kausar. Bayan su ma wasu ƴan matan ni kan ga sun biyo shi har gida. Kada ki ga haushinsa da nake ji wallahi namiji ya yi ta masu wulakanci amma suna bin sa don rashin zuciya. Kada ki ga wata fa ranar na dawo daga Islamiyya har tana kuka akan ya ƙi sauraron ta ta biyo shi tana masa magiya tare da roƙonsa, kamar shi kadai ne ɗa namiji a duniyar nan." Ganin A'isha na kokarin cigaba da na ƙoƙari na cigaba da zancen sa ne ya saka ta ce mata. "Ke Mallama zanensa ya ishe ni haka nan, ba ki san mugun hali da muguntarsa ba ne shi ya saka kike yabonsa wallahi bai da imani." "Ya taba maki abu na rashin imani ne?' "Zan baki labarin amma ba yau ba, kin san ba na da lafiya ." Sallama suka yi A'isha ta ja motarta ta fice yayin da Zahra ta koma cikin gidan. _Sir Asadullah_ Kwance yake a ƙasar ɗakin an rufe masa baki da salatef, ƙafarsa ƙafarsa ma an ɗaure ta da da wani sarƙa an ɗaure masa sarkaa sarƙa a ƙafarsa. Juyi kawai yake yi a ƙasan ɗakin sam tiyes ɗin ga kansa dake sara masa. Hatta hannayensa ɗauke suke waje guda an haɗe su waje guda. Kwance yake .yana fuskarsa na fuskantar ƙofar amma da alama baya cikin hayyacinsa. Manyan idanunsa sun yi jajir kamar wanda ya yi shaye-shaye. Cije baki kawai yake yi don cikinsa da kansa ba karamin ciwo suke yi masa ba. Ga zazzaɓi ga yunwa rabin da aba shi abunci tun juya da safe ga shi yanzu yammaci ne. Yana cikin wannan halin sai aka turo ƙofar ɗakin yake ciki aka yi, wata mace ce sanye da da hijabi da kuka niƙab wanda ya rufe mata fuskarta ko ƙwayar idanunta ba'a gani, bayanta wani namiji ne yana sanye da facemask da baƙin glass a fuskarsa. Daga ganin yanayin shigar da suka yi ka san sun yi shi ne saboda ɓadda kama, ta yadda ba wanda zai gane ko su waye su. Suna shiga suka same shi a halin da yake ciki. Bayan sun kalle shi ne sai suka kalli junansu. Body language suke yi daga gani ba sa so su yi magana ne don kada a ce yana cikin hayyacinsa ya gane ko su waye ta hanyar muryoyinsu. _Jidderh_ Tun da ta ido Asadullah Mantson ɗin hankalinta na wajen Asadullah. Ta so ta duba yau ma ta ga halin da yake ciki don tana son sanin waye ke son ganin bayansa. Mutumin kirki mai nagarta da taimakon al'umma. Kitchen ta fara shiga ta gaida ma'aikatan gidan dake ta aikace-aikace. Ta gushe su don masu gidan suna ciki. Haɗa idanu suka yi da wata budurwa wacce za su iya zamowa sa'annan juna. Kallonta ta yi tare da mata alama ta zo da hannu. Ganin haka Bahijja ta fito tana cewa Mama shugaban masu aikin gidan cewa. "Mana ina zuwa yanzu." Ba ta jira cewarta ba ta fito ta samu Jidderh a corridor da zai sada ka da kitchen ɗin. "Ke lafiya kika kira ni?" "Tambayarki zan yi don Allah." "Ina jin ki Allah ya sa na sani." "Ina Sir Asadullah yake ne kwana nan ba na ganinsa." 'Eh to na ji an ce wai baya ƙasar wai ya tafi wata ƙasar, sai dai ban san wace kasa ba ce ya tafi. Sai dai abin da yake bawa mutane mamaki bai taɓa tafiya shi kadai ba tare da amintaccen bodyguard ɗinsa Sulaiman ba. Don shi ma Sulaiman ɗin yana maganar hankalinsa bai kwanta ba, don duk ƙasar da Sir Asadullah yake tafiya a fadin duniyar nan yana da lambarsa na ƙasar amma abin da ya bashi Imamaki wai wannan karon lambarsa ta kowace ƙasa ba ta tafiya." Jinjina kai Jidderh ta yi tare da cewa. Wa ke sanar da ke haka?" "Muna jera masu abinci a dinning table ne sai Sulaiam din ya shigo ya sanar wa Dadyn sir Asadullah." Jinjina kai Jidderh ta yi tare da cewa. "Na gode sosai na tsayar da ke ki koma wajen aikinki ni ma yanzu zan fara nawa aikin. "Amma me ya saka kika tamabaya?" Murmushi ta yi tare da cewa. "Ba komai na dai tambaya ne." Daga nan Bahijja ta koma wajen aikinta. Ita kuma Jidderh madadin ta mayar da hankali wajen aikinta kawai sai ta tsinci kanta da son zuwa ɓangaren da ta je ta ga an rufe Sir Asadullah ana masa allurai ana son kashe shi. Dafe kirji ta yi tare da cewa. "Kar dai a ce har sun ida nufi su akan sa." Aikin dake gabanta ma ba ta tsaya yinsa ba, ta nufi part ɗin da ta ga wannan Doctor dake don kashe shi ranar ta ga ya je. Mutane biyu mace da namiji. Da suka je dubansa suna kallonsa sai da sautin murmushinsu ya fito. Maccen ta kalli namijin tare da mika masa wata allura da sirinji da kwalbar ruwan alluran. Daidai lokacin Jidderh ta tura ƙofar a hankali kasancewar sun juyawa wa kofar baya ya sa ba bayansu take gani, suka ba su san an turo kofar ba kasancewar ƙofar baya ƙara . Tana kallo ya yi masa alluran a damtsen hannunsa. Ana masa alluran take ƙofofin gashin jikinsa suka miƙe jijiyar kansa ta yi ruɗu-ruɗu ta fito idanunsa suka rikeɗe zuwa ja. Hannayensa biyu dake ɗauke da sarƙar ya ɗaya tare da ɗora su a saman kansa yana wani ihu mai haɗe da gurnani. Take Jidderh hawaye suka wanke mata fuska. Mace ta yi namijin almar jinjina da hannunta . Kuka ne ya ci karfin Jidderh ta sake kofar ta rufe. Wanda ƙarar rufe ƙofar ya saka suka juyi da sauri. Ita ma sai ta fara waige-waige don ta san idan ta kama hanya za su gane ta. Wani kontena ta gani sai ta durƙusa tare da kwantawa dab kada su hanahe ta. Don yana da girma. Suna fitowa suka fara waige-waige ba su ga alamar wani ya zo wajen ba, don haka suka juya suka bar Wajen. Tana. Kallonsu sai dai ba su ganinta tasowa ta yi a hankali don ta tabbatar da su waye sai ta ga sun nufi cikin gidan. Hakan ya tabbatar mata da cewa ƴan cikin gidan ne suke neman kashe Sir Asadullah. Da sauri ta bi bayansu don ta gano ko su waye amma sai dai ba ta ga kowa ba sun ɓacewa ganinta. Fridge ta nufa dake fakon ta ɗauko youghurt da cake ta tura cikin hijabi. Cikin sanɗa ta fita ta koma part ɗin da ta fito. Tura ƙofar ɗakin ta yi yana zaune jingine da jikin bango ya ɗaga kai ya lalle ta. Ƙarasa wa ta gabansa ta zube tare da cewa. "Yallaɓai barka da safiya?" Kallonta kawai yake yi kamar wanda ya ga sabon halitta. "Yallaɓai dan Allah me ka yi masu kuma su waye ke son ganin bayanka?" Nan ma shiru ya kasa magana. "Yallaɓai zan so fitar da kai sai dai na san ba abu ba ne mai yiwuwa, don matukar suka gane na san in da kake ba za su barni ba, ga shi Dad ɗinka baya gari ballantana na sanar da shi, amma zan yi shawara ko zan sanar wa Mom ɗin ka." Kallonta kawai yake yi ko motsin kirki ya kasa yi. Cake ɗin da youghurt ɗin ta ciro daga cikin hijabi. Ganin hannunsa ɗaure da sarƙa ya sa ta bude cake ɗin a cikin ledar da yake ta kai masa bakinsa. Nan da nan ya gutsiri cake ɗin, ganin haka ya sa ta dinga gutsura tana bashi a baki yana ci. Tana kuka bashi youghurt , sai da ya cinye tas ya kuma shanye robar youghurt ɗin sannan ta kalle shi ganin yadda ya rame. Ƙwallar tausayin sa ne ya zubo mata, ta mike ta bar wajen da sauri don kada wani ya zo ya tarar da ita wajensa. Ta tafi ta ƙudiri niyyar sai ta yi wa Mama magana, duk da cewar Mama ƴar aiki ce a gidan amma ta dade don ta ji labarin cewa Mama ta reni Asadullah yana yaro ita ke kula da shi. Za ta yi shawara ta sanar mata halin da ake ciki. Don tana tsoron tunkarar ƴan gidan da zancen ya kasance ta saka kanta a cikin hatsari. _Hilal_ Zaune yake a bayan motarsa yayin da ke gaba yana driving. Wayarsa ce ta yi ruri ya duba. Ganin Papa ne ya ɗaga tare da yin sallama. "Assalamu alaikum" Daga can ɓangaren Papa ya amsa tare da cewa. "Sojana ya kake?" "Am fine." "Yauwa dama ƙanwarku ce za su yi gasar karatun Al-ƙur'ani a garin Kaduna. Shi ne nake so a ce ka kai ta." A tunaninsa Maryam ce da suka fito ciki ɗaya ko Nadiya ƴar wajen Uncle Adam ko ɗaya daga cikin yaran Aunty Laila, sai dai ya san cewa ba damuwa suka yi da karatun Alqur'ani ba ballantana su je wani gasa. Gara ma Maryam duk da ita ba ta sauke ba ya san daƙyar idan ita ce. "Papa wacce kake nufi? Don na ga dukkansu ba wani nisa suka yi a cikin karatun Alqur'ani ba." "Ka mance Zahra ta sauke har walima ta yi, to ita ce nake nufi ai." Haɗe fuska ya yi tare da cewa. "Kuma ba wanda zai kai ta sai ni?" "Yayanninta ba sa nan kai ba Yayanta ba ne idan aka cire Mahmud da Sadik. " "Papa a gaskiya ni ba zan...." Katse shi ya yi ta hanyar cewa "Ba na bukatar wani uzuri daga wajenka. Ba wanda zan iya sawa ya kai ta bayan kai, don mahaifinta da mahaifiyar ba sa nan, ko na da ina nan zan bi ta ji tafi duka gidan nan na san ba wanda zai kai ta, don haka ka koma gidan yanzu ka same ta ku tafi can Makarantar ka yi magana da Mallamansu. Don ban yarda ta tafi tare da kowa a makarantar ba ƴa mace ce ita sai da saka idanu da kula. Na san ban isa da mahaifiyaeka ba amma idan ba za ka je ba zan kira ubanka na bashi umarnin da dole sai ya bi. Don haka yanzu na gama magana da Mallamansu suna jiranku kai da ita." Yana gama maganar ya kashe kiran wayar, ransa a ɓace, wai shi ne zai dauki yarinyar can ya kai ta wani gari Umarni ya bawa direban ya juya akalar motar zuwa gidan. A parking space ya tsaya, tsawon mintuna biyu da bude basa motar bai fito ba, kafin ya fara fito da ɗayar ƙafarsa waje, sannan ya fito da ɗayan ya fito gabadaya. A falon ta samu ƴan matan gidan duka suna kallon T.V suna fira. "Sannu da zuwa Yaya." "Kausar ta fada tana miƙewa don ta ɗauka saboda messages nata ya dawo da ta sanar da shi ya dawo gidan ta masa girki kuma akwai maganar da za ta masa. Bai amsa gaisuwar ba ya kalli Maryam ya ce. "Je ki kira mani yarinyar can?" Wace yarinya Yaya?" Harara ya banka mata tare da sauke kai " "To Yaya ba kowa a nan iyakar mu kenan sai dai idan Zahra kake nufi." "Eh ita." Da mamaki suka kalle shi Nabeela ta zaro idanu tana cewa. "Lafiya?" Bai tanka mata ba, ba jimawa Maryam ta dawo tare da Zahra Sanye da Hijabi kamar kullum. "Mugun kallo ya mata sannan ya ce. "Idan kin shirya ki same ni a mota." Yana gama fadar haka ya fice ya barsu da ƙamshin turarensa. Fatima Zahrah ta koma ta dauko wayarta a ɗaki, tana fito Kusar ta ce. "Uban meye za ki masa meye tsakaninku?" Ba ta tanka mata ba ta nufi hanyar kofar fita. Ƙasancewar akwai matattakala kin fita wanda sai kin sauka ta nan. Tana fita Kausar ta bi bayanta ta hankaɗa ta da ƙarfi ta tafi luu idsnunta a rintse ta sadakar dole sai ta illata. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page1️⃣4️⃣ Kasancewar akwai matattakala ƙoagar fita wanda sai kin sauka ta nan. Tana fita Khausar ta bi bayanta ta hankaɗa ta da ƙarfi ta tafi luu idanunta a rintse ta sadakar dole sai ta illata. Bayan ta sadakar tana jiran ta ji yadda Allah zai yi da ita Idanunta a rintse ta ji sauka a jikin mutum, don tabbas hannun mutum ne, tabbatar da cewa ba faduwa ta yi ba ne ya sa ya ƙanƙame shi a jikinta. Jin daddaɗan ƙamshin turarensa ne ya sa gabanta ya faɗi, saboda tsoronsa da take ji. Tana buɗe Idanunta ta sauke akan idanunsa masu rikita mai kallonsu. Harara ya watsa mata tare da sakinta ta faɗi ƙasa, ƙara ta saki ta ɗan ji zafin faɗuwar sai dai duk da haka ya gode masa ya ceci rayuwarta. Don da daga can saman matattakalar ne ta faɗo tabbas sai sai ta karye. Tashi tsaye ta yi tana tura baki tare da goge ƙwalla a zuciyarta tana cewa. 'Ya san dama zai yarda ni na fadi me yasa ya tare ni, ai da ya barni kawai na fado na ji ciwo, bayan na sakankance da cewa ya taimake ni ashe wani sabon muguntarsa zai mani. Sai sai na shi da sauki tun da daga jikinsa ne ya yarda ni da daga matattakalar na fado ba. ' Ɗaga kai ta yi ta kalli ƙofar ta ga Kausar, Nabeela, Nadeeya da Maryam sai kuma su Mama da Aunty Laila. Mugun kallo suke mata sai Maryam ce kaɗai ke mata kallon tausaya wa. Ko da ta juya ta ga baya wajen har ya karasa parking space, da sauri ta karasa wajen tana ɗan ɗingisa ƙafa. Yana zaune a bayan motarsa direbansa na gaba. Tana tsoron ta zauna kusa da shi sai ta tsaya. Don sanin halin mutanen gidan sai su ce ba zasu shiga mota tare da ita ba, mazansu da matan.Cikin takaici ya fara magana. "Tsayuwar me kike yi a wajen da ba za ki shigo ba." Da sauri ta bude bayan motar ta shiga. Ba abinda kake ji a motar sai sanyi da kuma daddaɗan ƙamshi wanda ya sa sai da ta yi ajiyar zuciya. Direban ya ja motar suka fice daga gidan. Tana mamakin yadda wani lokacin Yaa Hilal ya ɗan banbanta da sauran mutanen gidan. Don shi baya hantararta ko kyararta ballantana ya nuna ƙyamarta kamar yadda sauran suke yi. Shi dai idan sun haɗa idanu ya harare ta ko ya mata mugun kallo, amma ko gaishe shi ta yi baya amsawa, sallama dai yana amsawa kamar yadda ya zama wajibi a Addinin Musulunci. Amma sauran mutanen gidan ba sa amsawa ko sallmarta ce. Direban ya ɗan juyo ya kalli Hilal ya ce. "Sir ina za ku je?" "Ka tambayi yarinyar nan ina ne makarantar islamiyyarsu." Jin haka ya sa Fatima Zahrah ta sanar da shi wajen. Wayarsa ta kawo haske alamar kira ya shigo. Ɗaga wa ya yi kafin ya yi magana ya ji Muryar Mama na fada tana cewa. "Ina za ka je da wannan banzar yarinyar ?" "Mama Papa ne ya aike ni makarantarsu." Tsuki ta ji tare da cewa. "Akan me za ka yarda?" "Mama cewa ya yi idan ban yi ba ai sai ya kira Abba ya bashi umarni." Tsuki Mama ta ja tare da katse kiran wayar. Kallon Aunty Laila da Mummy ta yi tare da cewa. "Kin ji wai mahaifinki ne ya tura su wani wajen." Aunty Laila ta ce. "Gaskiya ba na son kusancin wannan yarinyar mai ƙirar aljanna kusa da Ajmal, ga Nabeela da Kausar suna mutuwar sonsa." "Kwantar da hankalinki matar Yaya matuƙar ina raye ai ko da wasa n hakan ba zai taba yiwuwa ba kar ki saka Ni ma na shata masa dogon layi akanta " *Prison Gidan yari* Sanye yake da kaya irin nasu na ƴan gidan yarin, sai faman Safa da marwa yake yi a cikin falon. Ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan yarin ya shigo tare da sallama. Bai amsa masa sallamar bs sai da ya karaso ya ce. "Yallaɓai wadannan jaridun da n kawo maka iya su ne waɗanda aka fitar yau.da sauri y kalli ma'ikacin ya ce. "Ka tabbatar ba wani jaridar bayan wandada aka kawo mani da za'a iya rubuta abun da nake bukatar ji?" Cikin tabbatarwa ya amsa masa da "Ƙwarai kuwa." Dunkule hannu ya yi ya naushi iska yayin ma'aikacin ya ce. "Yallaɓai zan tafi bakin aiki na." Kuɗi dake kan kujerar ya yissa nuni da hannu, ɗauka ya yi yana yin godiya ya fice. Dunƙule hannu ya yi ya dakin bangon ɗakin yana cewa. "Dole ka mutu Asadullah ba zan taba samun kwanciyar hankali ba sai na ji labarin mutuwarka zan samu nutsuwata. Tura ni gidan yarin da ka yi shi ne kuskure mafi munin da ka tafka a rayuwarka. Tunda likitan ya gagara kashe ka to ni zan ɗauki mataki da kaina. Don a duk lokacin da na ganni a cikin gidan yarin nan na tuna kudanci da dangantakar mu amma ka iya aikata Mani haka sai zuciyata ta yi ya tafarfasa. Me ya da ka kasa yafe mani kana da iko da alfarma na fitar da ni ka kasa. To an zo wajen da na ƙasa jurewa da gatana ka kawo ni nan." Haka ya dinga surutu shi kadai karshe ya fice daga ɓangaren ya nufi wani ɓangaren na gidan yarin. Wasu maza hudu ne suke shan sigari dai busa hayaƙi suke yi. A hankali ya karaso wajen, kallo ɗaya suka masa suka ɗauke kai. Shi ma shiru ya yi bai yi magana ba, don tsabar jin kai irin nasa yafi karfin ya masu sallama ko ya gaishe su. Ɗaya daga cikin su ne ya kalle su ya ce. "Mallam lafiya ka zo ka wani tsaya wa mutune akai?" "Kai ka damu da shi ni dama ban cika shiga sabgar ƴaƴan manyan nan ba." Wani ya faɗa aji bayan ta yi gama busa hayaƙin sigari. Kallon banza ya yi masu tare da cewa. "Waye madurguji?" Da sauri suka kalle shi tare da cewa. "Me yasa kake nemansa mutum ne shi mai hatsari." "Sanin haka ya sa nake nemansa don zai mani amfani." "Ka zagaya bayan dutsen nan za ka same shi da shi da muƙarrabansa." Suna fada masa haka ya juya ya bar su ya nufi bayan dutsen da suka kwatanta masa. Tafiya yake yi yana murmushi tare da girgiza kai. Wasu mutane ne kimanin du biyar a bayan dutsen, ɗaya daga cikinsu wanda alama ya nuna shi ne oga yana shan sigari, zaune yake akan dutsen yayin da sauran mutane huɗu suke zaune a ƙasa. Yana zuwa wajensu ya tsaya akansu yana cewa "Waye madurguji a cikinku?" Kallo ɗaya madurguji ya masa ya zuƙi hayaƙi tare da kallon ɗaya daga cikinsu ya ce. Wanda aka kalla ne ya tashi ya kwashe ƙafar mai tambayar tare da cewa. "Ka rage tsawonka sannan ka san waye a gabanka ko kai waye." Murmushin takaici ya yi tare da kallon jikinsa yadda aka kwashe masa ƙafa har sai da ƙura ya ɓata masa jiki, yana duƙe akan guiwarsa ya ce. "Da kun san waye da matakin da na taka a rayuwa da za ku san cewa na fi ƙarfin wulakancin tantirai irinku." Dariya Madurguji ya kece da shi sannan ya bushi hayaƙin ya hura a fuskarsa sannan ya ce . "Mu tantirai ne kuma na sani amma duk tsiya ba na butulu ba ne, ka koyi halarci a Rayuwarka, ina da tarihinka da butulcin da ka yi wa ɗan uwanka uban gidansa wanda ya zama garkuwa a gare ka lallai kai babban maci amana ne." Tsuke fuska ya yi tare da cewa . "Wannan bai shafe ka ba aiki na kawo maka kuma zan maki biya mai tsoka idan za ka yi." _Jidderh_ Bayan ta kammala aikinta ta nufi ɓangaren ma'aikatan gidan, kai tsaye ta nufi ɗakin Mama. Da sallama ta shiga, Mama ta amsa tare da ba ya izinin shigowa. Shigo wa ta yi t tarar da Mama na ninke kayan z ta wanke. "Jidderh ke ce?" "Eh Mama ni ce." "Na ɗauka kin tafi gida lokacin tashin ki ya yi." *Ban tafi ba Mama dama ina son magana da ke." "To ki zauna mana Jidderh." Ta yi maganar tana nuna mata kujera mai zaman mutane uku. Zama ta yi tare da cewa. "Barka da warhaka Mama." "Barka dai Jidderh ina fatan dai lafiya." "Lafiya lau dama ina son na sani yaushe Dad zai dawo?" Kallon ta Mama ta yi tare da yin ɗan jim sannan ta ce. "Ni ina zan sani ai wannan ba hurumina ba ne." "Haka ne amma dan Allah ina son na tamabaye ki ko ka kin san in da Sir Asadullah ya tafi?" Kallon mamaki ta yi mata tarar da cewa. "Jidderh wannan amsar ban san amsar da zan ba ki ba." "Am dama na gan shi a cikin gidan nan ne?" Da mamaki ta kalle ta tare da cewa. "Ban gane yana gidan nan ba, bayan kowa na gidan nan ya tabbatar da cewa baya nan, a ina kika gan shi ?" "Shiru ta yi tana nazari don da alama masu neman kashe shi suna cikin gidan da alama ma na kusa da shi ne, kada yanzu magana ta fita ga shi baya cikin hayyacinsa kada ta ɗaure kanta. Don haka ta canza zancen da cewa. "Shekara nawa kika dauka Mama kina masu aiki a gidan nan?" "Zan kai shekaru talatin ina aiki a gidan nan, akan idanuna aka haifi Asadullah da sauran yaran." "Mama idan ba damuwa zan so ki bani tarihin wannan gidan." Murmushi Mama ta yi tare da cewa "Ba damuwa yanzu ina da aiki idan ki ka sake zuwa zan baki tarihin wannan bahagon gidan." Kallon mamaki ta yi mata tare da cewa. "Bahagon gidan kuma Mama." Murmushi irin ta su manya sannan ta ce. "Ba za ki gane ba, wannan gidan ya wuce sanin tunaninki , Allah ya kyauta." Ta so jin wani magana daga bakin Mama amma ba yadda ta iya haka ta yi wa Mama sallama ta bar gidan zuciysrta cike da saƙe-sake. *Kuyi hakuri da wannan* Maman Ihsan ce✍️ 09065327995 [11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page1️⃣5️⃣ Ta so jin wani magana daga bakin Mama amma ba yadda ta iya, haka ta yi wa Mama sallama ta bar gidan zuciysrta cike da saƙe-sake. Ko da ta koma gidan sallama ta yi ta shiga, Inna na zaune bisa tabarma a tsakar gidan tana yi wa yaron Sa'adatu. Sa'adatu na tuƙa tuwo a saman murhun gawayi. Amsa mata sallamar suka yi tare da mata sannu da zuwa. Amsawa ta yi sama-sama ta ta shiga ɗakinta. Halin da ta bar Asadullah kawai ke damunta. Tana tuna tarin alkhairi da ya yi mata a rayuwa. A hankali ta fara tuna ranar da ta je kamfanin a karo na biyu da neman aiki. Wata ranar talata da misalin karfe goma na safe, mai keke napep ya sauke Jidderh a bakin kamfanin Asadullah. Bayan ta biya mai napep kuɗinsa ne ta karasa bakin kofar kamfanin. Cikin ikon Allah sai ta samu wancan security ne a bakin gate. Kallo ɗaya ta yi masa ta gane cewa shi ne mutumin da ranar da ta zo neman taimako za'ayi wa Sa'adatu tiyata ya hana ta shiga. Wanda wurin dagewarta na son shiga ne ta faɗi har kokon da A ta kai asibiti ya zube. Yana ganinta shi ma ya gane ta, da sallama a bakinta ta karasa wajensa. Ya amsa mata tare da sauraren me za ta ce. "Don Allah ina son ka taimake ni na hadu da Sir Asadullah ne." "Ke baiwar Allah ganin Sir Asadullah ba abu ba ne mai sauƙi, bar ganin wancan ranar kin gan shi cikin sauki sa'a kika ci yana isowa kika zo shi ya sa kika gan shi kafin ya karasa ciki, amma da zaran ya shiga ganinsa zai maki wuya. Ko nan bakin gate mutum baya shiga ba tare da an bada izinin shigarsa ba." Marairaice fuska ta yi tare da cewa. "Ka taimaka ka barni na shiga." Ko na barki kin shiga daga gate to idan kin shiga ciki ba barin ki za'ayi ki shiga ba. Don ma'aikatan ma hana ki za su yi ki shiga dole sai sun sanar da shi har sai ya bada izinin shigarki ciki." "To ai shi ne ya ce duk lokacin da nake bukatar ganin shi na zo kai tsaye." Ta faɗa tana addu'a Allah ya sa kada ya gane karya take masa. "Ina shaidar yake dole zai baki katinsa mai ɗauke da saka hannunsa ." "Eh ya bani ɓacewa katin ya yi, kuma yau in sha Allah sai na shiga nan, ka je ka tamabaye shi mana." Kallon ta kawai ya yi sannan ya bude mata gate yana cewa "Ai su ba za su bari ki shiga ba kya dawo." Tana shiga wajen ta saki baki tana kallon yadda aka narka dukiya wajen ƙera Kamfanin. A zuciyarta ta ce. 'Wannan wani irin gini ne, gaskiya duk wanda ya tsara wannan ginin kamfanin ya iya tsara gini, sai ka ce a ƙasar Turai. Gaskiya duk yadda aka yi turawa suka tsara wajen nan.' Gabaɗaya jikin bango ginin mirror ne ajikinsa, sannan ga wani wuta ne golding ke fitowa daga jikin mirror ɗin. Da wutar solar yake amfani da shi wanda kudinsa zai iya kai billions naira. Tana kai wa bakin ƙofar ta ji an ce. "Hey!" Tana jin haka ta tsaya tana kallonsa, kallon sama da ƙasa ya mata sannan ta ɗaure fuska ya ce. "Daga ina kike ko an faɗa maki ana bari mabarata ne su shigo nan wajen?" "Ni ba mabaraciya ba ce, na zo wajen sir Asadullah ne." Kallon dyama da ƙasa ya yi mata tare da daka mata tsawa . Lokaci guda ya tuna ita ce wacce ta zo ranar da kuma gargadin da aka yi wa security. Don haka ya ce "Me kika zo yi?" "Shi ya ce na zo duk sanda na so." "Ina katin da ya baki?" "Yallaɓai na nema ban gani ba " Haka nan sai ya tsinci kansa da ba ta izinin wucewa. Da kansa ya ce ta biyo shi a baya. Suna nufar wani ƙafa sai ta ga glass din ƙofar ya zuge da kansa. Suka shiga ckki, taɓa kallo ya yadda komai yake cikin tsari da sha'awa. Ganin idan ta tsaya kallo mutumin zai iya wuce wa ya sa ta ɗauke idanunta daga kalle-kallen da take yi . Nuna mata wata ƙofa ya yi tare da cewa. " ki shiga za ki ga wata mata ita ce za ta maki izinin shiga wajensa." Daga nan ya juya yayin da Jidderh ta kutsa kai cikin office ɗin. Wata matashiyar budurwa ce sanye da Suit baƙi tana danne-danne a laptop. Kallo budurwar ta yi mata tare da cewa. "Ke mahaukaciyar ina ce za ki shigo wa mutane ba tare da an baki izinin shigowa ba?" Wayar dake gabanta ce ta yi ƙara. Tana dubawa ta ga yallaɓai ne da kansa, tana ɗagawa ta ji muryatsa ya ce . "Let her in." "Okay sir,." Ta fada sannan ya katse kiran wayar. Tun zuwan ta yake kallonta da yadda suka ji da security na ƙafa har yadda aka yi ta a shigo duk akan idanunsa ne, sai dai yana mamakin karfin hali ir Irin na yarinyar . Bayan an nuna mata ƙofar da za ta shiga ne ta mike da sauri ta nufi ƙofar . Tura ƙofar ta yi tare da yin sallama. Can kasan maƙoshi ya amsa sallamar don shi kadai ya ji kayansa. Tana shigowa ta saki ajiyar zuciya sakamakon wani sanyin AC da da da ƙamdhin da ya yi mata Barka da zuwa. Tsaya wa ta ji tana kallonsa shi ma ya zuba mata blue eyes ɗin sa yana jiran me za ta ce. "Dama na zo ne don na sake yi msla godiya da irin alkahiri da ka yi Mani a rayuwa ta. Ka ce rayuwar matar Yayana ." Ba tare da ya kalle ta ba ya na ta danne-danne s laptop. "Don Allah zab samu aiki?" Dakatar sda abinda yake yi ya yi tare da zuba mata idanu ya ce. "Wane irin aiki, ne ya matakin karatunki?" "Ban yi karatu ba aikin goge-goe nake bukatar yi." "A yanzu muna da isassun ma'aikata, a shekarun ki ya kamata ace kina makaranta ne." "Eh ina zuwa ina son na hada biyu ne." "Yanzu ba buƙatar mai'iakata, anan." "Yauwa to can gidan fa ba buƙatar mai aiki ne?" Wayarsa ya ɗauka ya kira lambar Mom, bayan ta ɗaga ne yake tambaya ko suna bukatar ƙarin mai aiki, Mom ta ce eh don ɗaya daga cikin masu aikin ta tafi gida wai aure za'a mata. Ya ce zai turo ta . Bayan sun gama wayar ne ya bata adireshin ya ce duk mau abun hawannfs ta tare ta bashi zai kai ta. Sannan ya bata wa i Katin ya ce ta bawa security dake kula da ƙofa idan suka gani za su bari ta shiga ciki. Godiya ta yi masa ya bata kudi masu yawa ta wuce zuciyarta fara tas. Ta samu aikin da za ta tallafawa iyayenta . Bayan ta je ne ta ba wa security katin sannan suka bari ta shiga bayan sun duba. Ta shiga ciki ta samu su Mom da Dady , sallama ta U in suka amsa ta gabatar da kants. Daga nan Mom ta kira Mama ta ce ya nuna mata aikin da alawiyya ke yi sai ta cigaba da yi. Bayan ta gama tunanin da take yi ne ya goge ƙwalla. Tana zancen zuci. 'To dai me yasa aka daure shi aka kulle ji kamar dabba, anya iyayensa na tare da shi kuwa? Ba uwar da za ta juri hakan akwai sake. Ta yaya za'a ɗaure mutum mai daraja kamar Asad ko haukacewa ya yi bai cacanci haka ba. Daga karshe ta yanke shawarar nemo hanyar da za ta taimaka masa. Daga karshe ta fita ta samu Inna da Aunty Sa'adatu. _Hilal_ Suna isa makarantar direbansa ya yi parking motarsa. Ya fito ya budewa Halal bayan motar ya fito. Zahrah ma ta fito ta ɗaya bangaren. Kusan rabin jama'ar dake harabar makarantar zuba masu idanu suka yi. Don motar ta burge mutane sai ɗaukar idanu take yi. Ga mamallakin motar ya haɗu duk wanda ya kalli Hial sau ɗaya sai ya ƙara kallonsa. Ballantana yau Fatima Zahrah ta zo babu niƙab a fuskarta, don duk zuwa islamiyarsu da take yi sai ya sanya niƙab. Idan ko ta fito haka nan to sai ta tsargu da irin kallon da ake yi mata, ba maza ba hatta mata ma shagala suke yi da kallonta. Dan tamkar ita ta halicci kanta haka take. Don duk yadda kuke ji ana faɗin tsantsar kyau da ta wuce haka nan, idanunta ma ɗaukar hankalin mutane suke yi ga ƙaramin pink lips ɗin ta dai shinning suke yi. Sai dai ba ta da ƙiba siririya ce sosai kamar za'a hure ta ta faɗi ƙasa. Wani Mallami ne wanda yake son Zahrah don shi ya san fuskarta wata rana da ciwonta ya tashi a abinsa. Da fara'arsa Mallam Usman ya karaso wajensu. Sai dai yana kallon idanun Hilal ya ji kwarjininsa ya masa yawa. Sai da ya daure ya yi masa sallama tare da mika masa hannu suka yi musabaha. Bayan sun gaisa ya zubawa Zahrah idanu ba ko ƙyaftawa, sai da Hilal ya ji gaba sannan Zahra ta take masa baya. Mallam Usman ya yi gaba tare da yi wa Hilal jagora zuwa office ɗin shugaban makarantar. Da sallama suka shiga bayan sun gaisa da Hilal ne Zahrah ta gaishe shi. Bai san Fuskarta ba, amma ganin kyawon idanunta ya sa ya gane ta, murmushi ya yi tare da cewa. "Fatima Zahrah Salis Tafarki ko?" Kai ta gyada masa tare da sunkuyar da kai ƙasa. Ya sake cewa. "Yau ba niƙab ne?" Murmushi ta yi wanda har sai da dimple ɗin ta suka lotsa. Hilal ne ya lalle shi tare da cewa. "Na ji an ce gobe ne za'ayi tafiyar ko?" "Eh haka ne." "To ya tsarin naku yake?" "Eh iyayen yaran sun ba da yaran da za'ayi da su akwai motar makaranta da za'a tafi da su, akwai masauki da abinci kyauta da za'a basu. Sai dai akwai wasu iyayen yaran da ba yarda su bayar da yaransu, kamar ku kenan to ba za mu ce dole sai kun bayar da yaranku ba sai dai za mu baku adireshin wajen da za'a gudanar da karatun sai ku kawo su akan lokaci." Takarda mai ɗauke da adireshin wajen ya ɗauko ya bawa Hilal sannan ya sanar da shi jibi da misalin karfe tara na safe za'a gudanar da karatun don haka idan son samu ne sai a kawo ta zuwa karfe takwas da rabi." Amsar adireshin ya yi tare da yi masa sallama ya mike ya fice. Da sauri Zahra ta bi bayansa yayin da Mallam Usman ya bi ta bayanta don yana son magana da ita. Ko da ta ƙarasa har ya shiga motar yana jiran fitowarta. Har ta kai hannu za ta bude murfin motar sai ga Mallam Usman ya zo yana kiranta, hakan ya saka ta karaso wajensa tana jiran me zai ce. "Mallama Zahrah bai dace na kebe ina magana dake a titi ba, amma zan zo neman izini wajen iyayenki, akan amincewar su na zo ko Allah zai sa mu fahimci juna don ina ƙaunarki fisabilillah." Hilal ganin ta tsaya tana magana da wani yana zaune a mota yana jiranta, sai ya bawa direban damar ya tayar da motar su wuce su barta wajen. Hakan ya saka direban ya figi motar suka bar wajen, don dama Hilal ya ga yadda Mallam Usman ke yi wa Zahrah kallon ƙurilla. Ganin sun tafi ya saka hankalinta ya tashi. "Ya Salam Ya tafi ya bar ni." "Na ɗauka Yayanki ne." "Eh Yayana ne." "Me ya saka zai tafi ya barki?" "Ban sani ba Akaramukallah." "To yanzu ki yi gaggawa ki koma kada na jawo maki wata matsala, tun da kin ga ya yi fushi ya tafi, dama ba wata dogon magana ba ce zan nemi izinin ki ne kawai . Amma ko za ki shiga motata na kai ki gidan.?" "Ka bari kawai zan samu abun hawa." Sanin hakan zai iya janyo mata matsala duba da yadda Yayanta ya tafi ya barta ne ya saka shi ƙyale ta. Karasawa ta yi zuwa bakin titin don neman abin hawa. Tana tsaye a bakin titi wata mota ta tsaya a gaban ta, mamallakin motar ya fito yana mata magana ko kallonsa ba ta yi ba , har ya gaji ya tafi. Wani m ya tsaya shima bai samu fuska ba ya tafi. Ganin yadda ake kallonta ne ya saka ta yi nadamar fitowarta ba niƙab, don ko a school ma sai ta saka hijabi da niƙab. Tana tsaya ne don ba ta san ma yadda za ta tsayar da abun hawa ba. Wata motar ce ta tsaya kallon motar ta yi sosai ta tabbatar motar Mansur ne cos mate ɗin ta ne da suka karatu a University tare, wanda ya suka zo suka kai ta asibiti shi da A'isha. Yana zuge Glass din motar suka hada idanu, sanyayyar murmushinsa ya sakar mata,ita ma murmushi ta yi tare da karasawa wajan motar, murfin motar ta bude ta shiga. "Aminiya ya na ganki akan titi ke ɗaya ina motarki take?" "Hmm ba komai Aminin ƙwarai." Kasancewar su uku haka suke kiran junansu, daga Zahra har A'isha Aminiya yake kiransu su ma suna kiransa da Amini." Haka ya dinga jan ta da fira ita dai ba ta iya amswa masa ba, daga uhm dai um um. A ƙofar katafaren gidan na su ya yi parking daidai lokacin da Hilal ke fitowa daga gidan waya na kare a kunnensa. Cire wayar ya yi daga kunnensa tare da ƙarasawa wurin motar kasancewar glas ɗin motar bakin Glass ne na waje baya hangen na ciki. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.NT (Maman Ihsan) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *Eid Mubarak to you my fans, Allah ya maimaita mana da alkhairi* Page1️⃣6️⃣ Cire wayar ya yi daga kunnensa tare da ƙarasawa wurin motar, kasancewar glass ɗin motar baƙin glass ne na waje baya hangen na ciki. Knocking ɗin glass ɗin motar ya yi. A hankali Zahra ta kalle shi tare da cewa. "Amini bari na fita ka bar wajen nan da sauri." Kallon ta ya yi tare da cewa. " To laifin me na yi da zan bar wajen da sauri?" A hankali ya zuge glass ɗin motar tare da kallon Hilal. Wani banzan kallo Hulal ya yi masa sannan ya maida kallonsa kan Fatima Zahrah wacce ta sunkuyar da kai. Ɗagowa ta yi ta kalle shi sai da gabanta ya faɗi, ganin irin kallon da yake jifanta da shi. Ya tabbata ba wancan malamin da ya bar su tare ba ne, wannan kuma daban ne, wato ita kowa take kulawa kenan. "Ke fito ki shiga gida!" Jinkinta na rawa ta fito daga motar ta tsaya tana kallon Amini. "Kai ja motarka ka tafi kada na sake ganinka a ƙofar gidan nan." Wani kallo Amini ya masa yana don ya tanka masa sai Zahra ta yi magana a hankali yadda Amini ne kawai zai ji. "Don Allah ka tafi mutumin nan fa ɗan yawa ne zai iya tarfa ka a wajen nan" Ta yi maganar cikin sigar rarrashi. Don haka ya ja motar ya bar Wajen. "Zo nan!" Ya faɗa ransa a ɓace yana kallon Zahrah, sanin abinda da abun da zai biyo baya ba zai masa dad'i ba ya sa ta ruga cikin gidan a guje. Rufa mata baya ya yi shi ma ya koma ciki. Kamar daga sama suka ha an jeho ta. Gabaɗaya suna zaune a falon iyaye da ƴaƴansu. Gabaɗaya suka juyo suna kallonta, sallama ta yi masu ba wanda ya amsa a cikinsu, sai Abba da Dady su ma ciki-ciki suka amsa mata sallamar. Jin yadda ya banko ƙofar ya shigo ne ya saka ta juyawa da sauri ta nufi part ɗin su. Rufa mata baya yayi da sauri abu ga dogon mutum tana ƙoƙarin rufe ƙofar ya banko ƙofar da ƙarfi wanda hakan ya saka ta yi baya ta faɗi. Wuyan hijabinta ya cakumo ta miƙar da ita tsaye. A fusace ya fara magana cikin kakkausar murya. "Gabaɗaya ke ce kika fita zakka a cikin gidan nan, na tsani macen da ke kuka kowane kare da jaki, kin taɓa ganin wani namiji ya zo ajiye wata a cikin gidan nan? Wato sai ke ko? To bari ki ji ba wai na damu da ke ba ne ko ina da matsala da ke ba, babu ruwana dake matsalata ɗaya shi ne zubar da kimar ahalinmu.Don da zaran kin aikata wani abun da zai zubar da Mutuncin zuri'armu. Dama Abin da Aunty Laila take faɗa aka ki gaskiya ne yau na gani da idona. Sai dai zan maki gargaɗi duk sakaran da kika gayyato zuwa gidan nan ni na san abin da zan masa. Duk shashancin da za ku yi ku yi shi a waje amma ba gidan nan ba. Idan kuma ba haka ba ko?" Kwafa ya yi tare da barin ɗakin bayan ya sakar mata wuyan hijabi. Yana komawa falo ya same su zaune kamar yadda ya bar su. Aunty Laila ce kawai a tsaye, tana ganinsa ta ce. "Son meye haɗinka da wanan yarinyar ne?" Ciwon kai ya fara ji saboda dogon maganar da ya yi saboda shi baya so ya yi magana mai tsayi. Don haka bai ce mata komai ba ya nufi upstairs. Jin mahaifinsa na magana yana sake tambayarsa ne ya sa ya ce. "Dama na ga da muka tafi can lokacin da za mu dawo ta tsaya da wani saurayi. Na taho na bar su a wajen. Yanzu kuma wani daban ne ya kawo ta ba wancan ba." "Dama na fada maka yarinyar nan bin maza take yi, ai yau ka gane wa idanunka ai, yarinyar nan har cikin shege ta yi ita da munafukar uwarta suka zubar." Umma mahaifiyarsa ce ta faɗi haka, Cikin takaici ya ce. "Dole na ɗauki mataki akanta kafin ta zubar mana ƙimar gidan nan, don koma mene ne sai dai a ce ɗaya daga cikin familyn Muhammad Tafarki." Yana gama fadar haka ya haura sama har yana tsallake steps. Ɓangaren Zahra kuwa tun da ya shaƙe wuyar hijabin dake jikinta ta fara jin numfashinta na barazanar ɗauke wa. Haka ta fara komawa da mumfanin nata wanda yake jin ba ta da wata hanyar shaƙar iska. Ko da ya gama faɗarsa ya fice duk ciwon nata ya fara tashi. Madadin ta tashi ta nemi maganinta sai ta zauna tana ta riskar kuka duk da yadda take numfashi daƙyar. Don kalaman sa sun yi mata ciwo. Tana tunanin me Aunty Laila ta fada masa akanta ne ya har yake cewa gaskiya Sunyi Laila take faɗa. Yana haurawa sama direct ɗakinsa ya nufa, yana shiga ya fara cire rigarsa, ya saura daga shi sai singileti da dogon wandon dake jikinsa . Wayarsa ta soma ruri ya duba ya gani Papa ya sa ya ɗaga tare da yi masa sallama. Muryar tsohon ya ji yana cewa ya sanar da Zahrah sammako za su yi sannan ya kira wayar Zahrah ya ji kamar ciwonta ya tashi. Bayan ya katse wayar gajeren tsaki ya yi cike da takaicin yarinyar ya sauko ƙasa. _Asadullah_ Kwance yake a saman katifar dake ɗakin, tun yana kan kafa har ya fado ƙasa, dafe kansa da yake jin kamar zai fashe. Wani sauti yake fitarwa mai kama da gurnani. Doctor dake tsaye a kansa ne ya ciro wayarsa a Aljihu tare da lalubo wata lamba. Kira ya dannawa lambar nan da nan aka ɗaga. Cikin wace irin murya mai kama da rauni ya fara magana. "Na gama maku aikinku don Allah ku sake mani ƴaƴanta." Ta cikin wayar ya ji Muryarta tana cewa . "Gaggawar ne kake yi ai aikinka bai ƙare ba." "B haka muka yi da ke ba kun saka ni aiki kuma na yi maku me kuke buƙata kuma, amma kin san ba haka muka yi da ku ba?....Wallahi ba za ku ga annabin rahama ba, mutumin da ya yarda da ni yake kyautata mani iyalai na, har yanzu wannan aikin da nake yi ina cin alfarmarsa, wanda bai cancanci haka daga gare ni ba, amma saboda son zuciya da kwaɗayin abun duniya kuna neman kashe shi. Sai dai shi idan ba ku sani ba kainuwa dashen Allah ne shi ba na mutum ba. Don da wani ne yadda kika dinga sakawa ana yi masa waɗan nan alluran da tuni ya bar duniya amma shi har yanzu yana a raye." Tsawar da ya ji wani ya daka masa ta cikin wayar ya saka shi yin shiru. "Za ka yi aikin da aka saka ne ko kuma sauratan banza? Kar ka manta ƴaƴanka suna hannunmu ba za mu sake su ba har sai ka kammala mana aikin mu. Idan kuma ka ɗauki lokaci mai tsayi to za mu tiro maka da gawar ɗaya daga cikinsu. Ya rage saura ɗaya wannan gargaɗi ne." Muryar macen ya ji tana cewa. "Kada ka bamu matsala fa ba wai mun ɗauke ka aiki ba ne saboda matsala, mun ɗauke ka ne saboda muna neman mafita. Don kai kaɗai ne likitan iyalin dake cikin Asadullah Mantson. Idan aka wani yana shige da fice waɗan nan security za su tsaurara bincike ne, amma kau ba wanda zai damu saboda sun san kai ne mai duba marasa lafiyar, za su yi zaton rashin lafiyar ɗaya daga cikin ahalin ne ya saka kake zuwa. Don haka ka iya takunka." Ana faɗin haka aka katse kira wayar, kallon Asadullah ya yi cikin rauni ya ce. "Ka gafarce ni yallaɓai, ƴaƴana guda biyu da Allah ya bani suka kama, saboda sun san cewa suke rauni na. Ba yadda zan yi ina son ƴaƴana." Yana gama faɗar haka ya harhaɗa kayansa ya fito daga ɓangaren idanunsa cike da ƙwalla. Kiciɓis suka ji da amintaccen bodyguard ɗin Asadullah wato Sulaiman, kallon Dr ɗin ya yi ganin daga in da ya fito ga shi yana zubar da ƙwalla. "Hey Doctor daga ina, me kake yi a wancan ɓangaren?" _Hilal_ Yana saukowa downstairs suka zuba masa idanu daga shi sai farar singileti da dogon wando baƙi. Singileti ya fitar da surar jikinsa na ƙaƙƙarfan namiji jarumi. Kallo ɗaya za ka masa ka san cewa yana yawan motsa jiki bisa la'akari da yadda ƙwanjinsa suka bayyana a fili. Kausar ta saki murmushi tare da maganar zuci . 'Allah ya nuna mani ranar da za ka zama mallakina ni ma na zama taka.' Nabeela kam cewa ta yi a zuciyarta ' Yaya Hilal har yanzu ba ka amince da bukatata ba, ko ba ka aure ni ba so nake mu ɗumin juna.' Kai tsaye part ɗin su Zahra ya nufa, bakinsa ɗauke da sallama. Gabaɗaya ahalin dake falon suka bishi da kallon mamaki ganin in da ya koma. Dady da Abba ne suka mara masa baya sannan su Aunty Laila da Mummy da Umma suka bi bayansu. Haka yaran ma suka tashi maza da mata. Yana shiga ɗakin ya tarar da tana kokawa da numfashinta. Kai tsaye ya nufi in da ya ɗauki maganin ranar da ya saka ta punishment ciwonta ya tashi. Yana duba wa ba komai a ciki haka ya hau duba maganin ko ina ya birkice ɗakin bai ga magungunan ta ba. Cikin kufula Umma ta ce. "Me kake ƙoƙarin yi ne?" "Maganinta nake nema baya nan." "Wai me ya sa duk cikin ƴaƴan da na haifa kai kaɗai ne ban isa da kai ba, ina ruwanka da maganinta ko halin da take cikin, shin kana da alaƙa da yarinyar nan ne ?" "Umma ba wata alaƙa ko wani abu a tsakanina da yarinyar nan, hasalima na tsane ta, wannan ƙoƙarin ceton rai ne. Wanda ko da ba ita ba ko wani ne na hadu da shi a hanya yana cikin halin da take ciki sai na taimaka masa ko da ban san shi ba zan ceci rayuwarsa wanann shi ne." Cikin takaici Aunty Laila ta kalli Abba ta ce. "Kana ganin yaronka na shirin ba mu matsala ko, ka faɗa masa ya fita daga harkar yarinyar nan idan ba haka wallahi sai ga abinda zai biyo baya." "Aunty ba na shiga harkarta yanzu ma Papa ya turo ni wajenta akan ciwonta ya tashi kuma na fada maki ba don ita ba ko maƙiyina ba na masa fatan ya tsinci kansa a cikin mawuyacin hali, aikin ceton rayuwaka da dukiyarsu nake yi rashin imanin nawa ba kai da zan iya ganin ɗan Adam w cikin mawuyacin hali na ciwo na yi fatali da shi ba saboda wata aƙida, ku saka wa ranku ba ita na ce ta ba rai na ceta ko na waye kuwa ." Abban ya ce. "Hilal mu ne marasa imani kake nufi ko meye?" "Ban faɗa ba Abba ka yi hakuri ba nufina kenan ba, ku saka a ranku ban ceci yarinyar nan ba rayuwa na ceta wacce ko a ina ne ko ban san mutum ba haka zan yi." Cikin ɓacin rai Umma ta ce. "Hilal ka fita ka bar ɗakin nan yanzun nan." "Zan fita Ummana amma sai na kammala abun da ya kawo ni, matukar na sa gaba a bi ba na dakata wa har sai na kai ga ci." Bai saurare su ba ya cigaba da neman maganin ba su yi mamaki ba don sun san halinsa in dai akan gaskiyarsa ne ba zai taɓa sauraren kowa." Kausar ce ta yi magana ƙasa-ƙasa tana cewa. "Ka gama wahalarka ba na kwashe magungunan na fita da su, kafin ka kai ta asibiti Allah ya sa ta mutu." Ba wanda ya ji ta sai shi a fusace ya kalle ta nada sai da hanjin cikinta ya ƙaɗa. Ya nufe ta tare da cewa. "Ki yi sauri ki kawo mani su duk in da kika kai su." "Yaa Hilal me zan baka ni fa ban san komai ba." Ganin za ta raina masa hankali ya sa shi cewa "Kada ki bari na sake maki tambaya a karo na biyu, ina suke na ce." Ganin ta masa banza ya saka ya shaƙo wuyarta tare da cewa . "Za ki fada ko sai na kashe ki kafin ita ta mutu ki riga ta mutuwa?" Idanunta suka firfito nan da na Yaa Mansur da Yaa Faisal suka fara ƙoƙarin kwatarta, amma ina sun kasa cire hannunsa daga wuyanta . Aunty Laila sai kuka take yi tana cewa zai kashe mata yarinya. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page1️⃣7️⃣ Idanuwanta suka firfito nan da nan Yaa Mansur da Yaa Faisal suka fara ƙoƙarin kwatarta, amma ina sun kasa cire hannunsa daga wuyanta. Aunty Laila sai kuka take yi tana cewa zai kashe mata yarinya. Nan da nan Abba ya ƙarasa yana kiran sunansa shi da Abba, su ma sun kasa cire hannunsa daga wuyanta. "Za ki faɗa ko ba za ki fada ba kin fi son mutuwa.?" Dukansa Aunty Laila take yi tana kuka amma kamar dutse take duka. Kausar jin ta kusa mutuwa ne kuka ba ta ga alamar zai sake ta ba ne ya sa ta ɗaga masa kai da muryarta da baya fita ta ce. "Zan faɗa" Jin haka ya sa ya sake ta tare da fuszar da iska mai zafi ta bakinsa. Aunty Laila ta rungume ta tana kuka yayin da Kausar ɗin ma ta kasa kuka. Don tashin hankali idan ya yi yawa ma ba ka samun damar yin kuka. Sai wuyar ta da ta rike take tari. "Ina suke!?" Ya faɗa a fusace yana kallonta. "Yana ɗakinmu a ƙarƙashin gado." Kallon Nabeela ya yi tare da cewa. "Ki yi sauri ki kawo Mani." Ba ta da wani zaɓi dole ta tafi duk da ba da son ranta ba ne, amma tun da tana son shige masa dole sai ta bi yadda yake so. Ba jimawa sai ga ta ta dawo da jakkar magungunan. Miƙa masa ta yi ya karba tare da juye su kan gadon. Kallon Zahra ya yi dake kwance kamar gawa, sannan ya mai da dubansa kan magungunan, sanin cewa alluran zai fi mata aiki a yanzu ne ya saka ya ɗauki alluran da sirinjin. Dubawa ya yi ya karanta sannan ya yi mata alluran. Bayan ruwan alluran sun bi jijiyoyin jikinta ne ta ja numfashi da karfi . A hankali ta buɗe Idanunta tare da sauke su akan fuskarsa dake ɗaure tamau. Sai ta fara bin su ɗaya bayan ɗaya da kallo, tana mamakin yadda gabaɗaya ilahirin gidan suka cika mata ɗaki. Ta dai san alkhairi ba zai kawo su wajenta ba. Tun da ba ƙaunarta suke yi ba. Hatta idanunsu duk ya nuna hakan bisa la'akari da irin kallon tsanar da suke jifanta da shi. Abba ne ya fara fita sai Dady, daga nan Umma da Mummy suka fita. Daga nan sai Yaa Mansur da Yaa Faisal, Nadiya da Maryam ma suka fita, ya saura sai Aunty Laila da yaranta. Aunty Laila kwafa ta yi tare da hannun Kausar suka fice. Nabeela ta rage ta tsaya ganin abinda zai tura wa buzu naɗi. Zuciyoyin kowa na gidan cike da takaicin Hilal, sai dai ba yadda suka iya da shi. Sun so a ce baya nan hakan ta kasance don damar da suka faɗe suna jira kenan. So suke ta bar duniyar gabaɗaya, don sun san hakan zai dasa baƙin ciki a zuciyar Salis da Matarsa. So suke ya ɗandani bakin cikin fiye da wanda ya yi sanadiyyar saka su a baya. Wanda tun tasowar ɗan uwan nasu ba su taba ganin ya kwashi bakin ciki ba a rayuwarsa sai farin ciki. Amma idan ya ji labarin mutuwar ƴarsa mace tilo da suka fi ƙauna shi da matarsa da iyayensu dole duk za su kwashi bakin ciki. A falo suka hadu dukkansu cikin takaici Aunty Laila ta ce. "Kan waccan banzar yarinyar ne yake kokarin kashe Mani ƴa ko?" Abba ya kalle ta tare da cewa. Kuyi hakuri Laila." "Haba Yaya wani haƙuri kawai abin da zai fi dauki ka yi gaggawar cewa ya koma can U.S a bakin aikinsa. Don wani sati mahajjata za su dawo, idan iyayen yarinyar nan fa su Papa suka dawo ba halin shirin mu ya tabbata." Umma ta cikin takaici ta ce. "Ba abinda ke ɓata mani rai da Hilal kamar taurin kansa sam baya tanƙwasuwa, idan ya kafe ya kafe kenan ba mai saka shi ba mai hana shi. Ina ga idan ya ƙure ni akan waɗan nan mutanen dai na gifta kalmar tsinuwa sannan zai dawo cikin hankalinsa." "Kul!" Abba ya dafa yana kallonta. "Abban Hilal ba ka ganin yadda muna hana shi abu baya hanuwa?" "Yana hanuwa mana, duk muka bashi umarni baya taba tsallake wa, sai dai na lura da shi in dai akan gaskiyarsa ne baya mana biyayya, matuƙar ya san cewa shi ne mai gaskiya to fa baya sauraren kowa." Cikin takaici Umma ta sake cewa "To zan nuna masa mu ne muka haife shi ba shi ya haife mu ba." Aunty Laila ta ce. "Ina ga ayi masa aure kawai shi ne mafita, ya ɗauki matarsa su tafi can U.S sai idan sun zo mana ziyara. Don haka ha ƴan uwansa nan ya zabi daya daga ciki, idan bai zaba na mu za mu zaba masa da kanmu." Jinjina kai Abba ya yi cike da gamsuwa. Dady ya ɗaura da cewa. "Ƙwarai kuwa a cikin Nadiya, Kausar da Nabeela cikin su uku ba zai rasa wacce yake so ba." Aunty Laila ba ta so ya hada da ƴarsa Nadiya a ciki ba, taso cikin ƴaƴanta biyu don haka ta ce. "Ai Kausar da Nabeela suna son sa ne ita Nadiya ta ce tana sonsa ne?" Kowa ya kalle ta dake ba kunya ce da ita ba ta ce. "To wace mace ne za ta kalli cikakken namiji irin ya Hilal ta ce ba ta so, wallahi ina son sa ." Maryam sai taka ƙafarta take don ta yi shiru amma ko a jinkinta . Abban Hilal ya ce . "Shi kenan, za mu bashi zaɓi cikin su uku , idan ya ki haƙiƙa za mu sura masa duk wacce muka ga dama." Daga haka suka watse kowa ya yi part ɗin ta sai Aunty Laila da ta zauna zaman jiran fitowar Hilal. A can cikin ɗakin kuwa bayan ta dawo daidai ne ta yunƙura da niyyar tashi amma ta kasa.koma ta yi ƙasa ta kwanta. Sanin sanyin tile zai iya kawo barazana ga lafiyarta ya saka shi ɗaukar ta cak ya ɗaura a saman gadon. Sannan ya kalli Nabeela ya ce. "Ke kuma fa akwai abinda kike jira ne?" Taɓe baki ta yi tare da cewa. Magana nake so mu yi da kai." Kallonta ya yi na sakan sakan uku ya ce. "Ina jin ki." "Sirri ne." Jin haka ya sa ya juya dan ficewa daga ɗakin. Cikin sanyin murya irin nata ta ce. "Na gode da ceton rayuwata da ka yi, Allah ya saka maka da gidan Aljanna." Bai amsa ba sai ce mara ya yi "Ki shirya ƙarfe bakwai na safe za mu tafi. Da mamaki Nabeela ta lalle shi tana cewa. "Ina za ku je tare?" Fita daga ɗakin ya yi ba tare da ya ce mata komai ba. Haka ta dinga binsa a baya har ya haura upstairs, ya shiga falonsa ta bishi, yana ƙoƙarin shiga bedroom tana ƙoƙarin binsa. Dakata wa ya yi ba tare da ya juyo ba ya ce. "Lafiya?" "Magana da nake so mu yi da kai." "Ina jinki." "Ina za ku tafi da waccan yarinyar ne?" "Wata yarinya?" Sai da ta yamutse fuska sannan ta ce. "Zahrah " "Kaduna" Ya bata amsa sannan ya saka hannu a handle ɗin ƙofar zai shiga. "Yaa Hilal me za ku je yi da ita?" Bai ba ta amsa ba ya yi shigewarsa ciki, kai tsaye ita ma ta kutsa kai ta shiga bedroom ɗin nasa. Singileti dake jikinsa yake ƙoƙarin cirewa ganinta ya saka shi dakata wa tare da ɗauke fuska tamau. "Ke meye kuma?" "Maganar da zan maka ne ai ban yi ba ka shigo ɗaki." "Ina jinki." Juya baya ta yi yadda ba za ta kalli idanunsa ba ta ce . "Ya Hilal ina son ka don Allah ka aure ni, na maka alkawarin kasancewa duk yadda kake so." Ransa a ɓace ya juyo yana kallonta. "Ke!" Sai da ta firgita da ganin yanayinsa. "Sa'anki ne ni?" Sunkuyar da kai ta yi ta kasa hada idanun da shi, saboda tsoron da idanusa suka bata. Cikin ɓacin rai ya sake cewa. "Duk san da kika dake tara ta wannan maganar sai na karairaya ki." Ƙofar fita ya nuna mata da fice a guje tana kuka. Washegari tun da Fatima Zahra ta yi sallar asuba ta yi azkar da karatun Alqur'ani, ta gyara gyara ko ina a ɗakin duk in da ya dace sannan ta yi wanka. Riga da siket ta saka na leshi, kalar purple an yi masa ado da kalar zare pich colar ɗinkin sun ɗan kama ta amma sun zauna mata ɗagwas a jiki. Ba ta yi wata kwallaiya ba powder kawai ta shafa. Kasancewar safiya ne ba ta yi tunanin ganin kowa a falon ba, don haka ta fito kanta a buɗe gashi kanta ta tufke shi ta sake shi a gadon bayanta. A hankali take tafiya kanta tsaye ta nufi hanayar kitchen, jin idanu na yawo a jinkinta ne ya saka ta juya nan ta gan su gaba daya s dinning table suna cin abinci. Mamaki ya kama ta ganin yau sune da sammako wajen breakfast, sai kuma ta tuna da cewar saboda Hilal zai yi tafiya ne, don haka suka fito don suna ji da shi, in dai zai yi sammako zasu tashi da wuri saboda shi. Ko da ba su ci abinci ba za su kasance da shi a dinning table. A hankali ta ƙara so don ta gaishe su. Cikin sanyi ta durkusa ta gaida Abba bai amsa mata ba, haka Dady shi ma shiru bai amsa ba. Ta gaida Umma da Mummy da Aunty Laila. Ba wacce ta yi mata kallon arziki. Ta kalli Yaa Hilal ta ce. "Ina kwana Yaa Hilal?" Bai amsa mata ba shi ma, ba ta hakura ba ta kalli Yaa Mansur ta ce. "Yaa Mansur ina kwana?" "Wallahi na sake jin sunana a bakinki sai na sauya maki kamanni mayya kawai." Murmushin takaici ta yi ta kalli Yaa Faisal ta kalle shi ta ce, "Yaa Faisal ina kwana?" Idanunsa akanta ya kada ko ƙyaftawa, sanyayyar murmushinsa ya sakar mata tare da jinjina mata kai alamar ya amsa. Duk da ta fito neman abin da za ta saka wa cikinta ne, kuma da alama an gama an jera a dinning table, sai dai tun da iyayenta suka tafi zaman cin abincin gidan ya gagare ta, don ƙiri-kiri za ta hana ta cin abinci sai dai ta shiga ta girka nata ita kaɗai. Kallon agogon hannunsa Hilal ya yi ya ga bakwai saura mintuna goma sha biyar. Tana shiga kitchen ta dafa ruwan zafi ta soya ƙwai ɗaya, ta haɗa tea ta ɗauki bread ta zauna a falon ta fara ci da sauri ganin lokaci ya kusa. Nan da nan ta gama ta je kitchen ta wanke kayan da ta ɓata. Ta koma ɗaki. Wayarta ta ɗauka tare da ƙaramar jakkar da ta zuba mata kala uku sai na barci. Wayarta ta saka a handbag ta ɗauki dogon hijabinta ta saka pich colour ta saka ta fito zuwa Babban falon gidan. Ba kowa a falon ta nufi parking space a can ta hango su duka. Tana ƙarasa wa ta kowa ya fara mata mugun kallo, bata ce komai tana ƙoƙarin shiga motar ashe ta taka ƙafar Kusar ba ta sani ba, don sun cika wurin da ƙyar ta kutsa ciki ba wanda ya bata hanya. A fusace Kausar ta janyo mata wuyan hijabi ta sauke mata lafiyayen mafi wanda ya saka ta saki ƙara tare da dage kumatu. "Ke mahaukaciyar ina ce za ki taka ni ki wuce, sa'arki ce ni?" Jinjina kai Umma tayi tare da cewa. "Kin yi daidai, uban me take taƙama da shi, ta zo za ta shiga mota tana taƙama to ba Salisu ya siya motar ba ɗana da guminsa ya siye motar." Kallonsu take yi ɗaya bayan ɗaya ba wanda ya yi magana ko ya tsawatar wa ko ya yi wa Kausar maganar marin da aka yi mata na cin zali. Ji ta yi kamar kada ta shiga motarsa abun gori ba wuya har mahaifiyarsa tana mata gorin motar ɗanta ne da ya siya da kudinsa, wato ba kudin ubanta ba ne." Zuciya ta kawo mata wuya ta ji ba za ta iya shiga motarsa ba, don haka ta juya ta koma gefe ta lalubo lambar wayar Papa akan ya haɗa ta da wani da zai kai ta. Duk da ba ta taɓa tafiya ita kadai ba. Sai dai daga wayar Papa har ma Abbi ba wanda ya shiga. Waige-waige ta fara yi tana neman Direban gidan amma ba ya kusa. Tana da sanyi amma da zaran an ƙure ta fushinta baya da kyau. Tsawa Hilal ya daka mata wanda sai da ta kowa ya tsorata. "Za ki shigo ne ko me kike jira!?" "Ba zan tafi da motarka ba, ina jiran Direba ya zo ya ɗauke ni ya kai ni." Fitowa ya yi yana kallon ta da mamaki bai san cewa zuciysrta ta kai haka ba. "Wuce ki shiga na ce." "Ba zan shiga ba sai dai na shiga motar da ubana ya siya da guminsa ba wani..." Saukar marin da ta ji ne ya saka ta kasa karasawa, don sai da ta daina ji da gani na wucin gadi. Jiri ne ta ji yana ƙoƙarin ɗaukarta ta yi luu za ta fadi, ya tare ta ta ai faɗa jikinsa. Ɗaukar ta ya yi cak ya saka a bayan motar, yazo ya dauki jakkarta da ta fadi ƙasa ya bude handbag ɗin ta, ganin ta ɗauko magungunanta ya saka ya koma cikin motar ya zauna gefenta. Umma ta ce. "Hilal dole sai ka kai ta ne?" "Alkawari na yi wa Papa da ya nemi na kai ta." Ɗaya masu hannu ya yi, suma suka masa fatan sauka lafiya. Zuwa lokacin Zahra ta sume, yaraf ta kwanta a jikinsa. Ganinta kwance a jikinsa ya saka Nadiya, Kausar, da Nabeela jin wani kishi da tsanar Zahrah a zuciyarsu. "Kun ga karuwanci ƙiri-kiri ji yadda ta kwanta a jikinsa." Aunty Laila ta faɗa tana kallonsu su Mummy. Umma ta ce. "Son na tsani yarinyar nan irin tsabar da ba na son ta tsaya ko inuwa ɗaya da tsatsona. Ka bari direba ya kai ta ko kuma ka raba mota kai ka shiga wata tunda ga sojojinku nan." "Umma kada ki damu ba na son na kwashi gayya ne." "To ka raba jikinka da na wannan yarinyar." Kai ya jinjina tare da cire ta ya jingine da kujerar motar. Zuge glass ɗin ya yi tare da bawa direban umarnin ya ya ja motar su tafi. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.NT (Maman Ihsan) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* Page1️⃣8️⃣ Kai ya jinjina tare da cire ta ya jingine da kujerar motar. Zuge glass ɗin motar ya yi tare da bawa direban umarnin ya ja motar su tafi. Sai da motar ta bar gidan sannan suka koma ciki suna ta zagin Zahrah. Juyawa ya yi ya kalle Zahrah wacce idanunta ke lumshe, ga zara-zaran eye lashes ɗinta a kwance. sai sheƙi suke yi girarta sun kusa haɗe wa da juna. Kau da kansa gefe ya yi tare da yin gajeren tsuki. Handbag ɗin ta ya duba daidai lokacin da ta ja wani ajiyar zuciya. Garin haka ya saka ya ɗauko Inhelar daga cikin jakkarta ya ya kai kai ta shaƙi iskarsa. A hankali numfashinta ya dawo daidai. Kallonsa ta yi ta kauda kai gefe. Ga fuskarta ya kumbura don sai da shatin yatsunsa biyar suka kwana a saman kumatunta. Ga ɗayan gefen kumatunta in da Kausar ta mare ta, sai dai bai fito sosai kamar wanda Hilal ya yi mata ba. Kau da kanta ta yi gefe tana tuna abun da aka yi mata a yau ya tsaya mata a rai sai ajiyar take saukewa akai-akai. Wayarsa ce ta soma ruri, ya duba ya ga abokinsa ne. Ɗagawa ya yi ba tare da ya yi magana ba. Daga can bangaren kamal ya yi sallama. Ya amsa masa kamar baya son magana. "Ina hanyar garinku." "Ma sha Allah, ka ce muna da babban baƙo mu shirya." "Kada ka wahalar da Amarya kai ma ka san a hotel nake sauka, ballantana yanzu da na zo da wata." "Wata wace ce ita?" Sai da ya ɗan yi jim kafin ya ce ƙanwata ce, za su yi gasar karatun Alkur'ani ne." "Ma sha Allah, gaskiya bai kamata ku sauka a hotel ba, sai dai ku zo gidana tun da akwai wadatattun ɗakuna. Ko ku nawa ne kowa zai samu ɗaki don Allah ka yi Mani wannan alfarmar." Shiru ya yi kafin ya ce. "Kada ka damu ni..." Katse shi ya yi ta hanyar cewa. "Idan ba ka sauka a gidana ba wallahi ni ma ba zana sake sauka a gidanku ba, tun da yadda na dauke ka ba haka ba ne a wajenka." "To na ji sai mun iso." "Hauwa ko kai fa." Sallama suka yi ya katse kiran wayar. Zahara Idanunta a lumshe tana jin sa. Kira ne ya sake shigowa wayar. Ya duba ya ga sunan da ya bayyana akan fuskar wayar ALEXANDRA shi ne sunan da ya yi seved number ta. Ɗauka ya yi bayan ya yi murmushi mai sauti wanda har sai da Zahra ta ji sautin murmushinsa. Bayan ya ɗaga ne sai ya fara magana cikin yaren ƙasar Spain. Tsawon mintina talatin suka ɗauka suna wayar kafin Zahra ta ji ya katse kiran wayar.ita dai ba ta jin me suke cewa. Take dai ga kiran video Call ya shigo wayar . Ɗaga wa ya yi sai ga fuskar wata Baturiya ya bayyana kan fuskar wayar. Matashiyar budurwa ce take masa magana kamar za ta yi kuka. Ba abinda take ji daga Yaren ƙasar Spain sai dai ta ji tana ambaton U.S da kuma Nigeria. Ba ta ji me yake cewa ba amma sai ta ji sautin kukan yarinyar na fitowa daga cikin wayar. Ɗan ɗaga kai ta yi ta saci kallon wayar sai ta ga kyakkyawar Baturiyar na masa. Taɓe baki ta yi tare da kau da kanta gefe. Sun mai mintuna talatin ko wajen video call sannan ya katse wayar. Daga nan ba ta san lokacin da barci ya ɗauke ta ba, kasancewar an kashe A.C saboda yanayin ciwonta. Ba ta san lokacin da suka isa garin Kaduna ba, don barci take yi. A ƙofar gidan Abokinsa Jamilu ya sa direba ya yi parking. Wayarsa ya ɗauka zai kira Jamilu kenan sai ga kiran Jamilu ya shigo wayar. Ɗaga wa ya yi ya ce. "Muna waje." Mai gadi ne ya wangale masu gate daidai lokacin da Jamilu ya iso harabar gidan. Motar na shigowa direban Hilal ya nufi parking space ya yi parking. Jamilu ne ya buɗe murfin motar ya sauke idanunsa akan fuskar Zahara dake barci. "Tabarakallah ma sha Allah, tsarki ya tabbata ga ubangijin halittar da ya halicci wannan kyakkyawar sura." Wani kallon Hilal ya masa sannan ya ɗauke kai ya mayar kan fatima Zahra, har lokacin barci take yi, tsawa ya daka mata wanda ya saka ta farka a firgice. Dara-daran idanunta ta hau raba wa sai ta tuna in da suke, don haka ta tsuke fuska tare da kau da kai daga kallonsa. "Haba meye haka ka yi haka ake tashin mutum daga barci?" Bai kalle shi ba ya fita bayan direbansa ya bude masa murfin motar. Jamilu ne ya kalli Zahra tare da sakar mata murmushi ya ce. "Ƙanwata zo mu shiga ciki ko?" Ba musu ta ɗauki jakkar kayanta ta ta fito. Jamilu ya masu jagora zuwa ciki, yana gaba shi da Hilal Zahrah na binsu a baya. A falon gidan suka tsinci kansu. Da sallama suka shiga a bakinsu. "Ku zauna bari na kira matar gidan." Yana gama fadar haka ya nufi wani corridor. Bayan mintuna biyu sai ga shi ya dawo tare da matarsa hannunsu sarƙe cikin na juna. Murmushi take sakarwa Zahra lokacin da suka ƙaraso falon. Ita ma Zahra murmushin ta sakar masa. "Sannunku da zuwa." Ta faɗa yayin da suke da zama akan kujera mai zaman mutum biyu. Kallon Hilal ta yi tare da cewa. "Barka da zuwa mazan fama ya aikin?" "Barkanki dai Alhamdulillah." Ya amsa ba tare da ya daga kai ya kalle ta ba. Kallon Zahra ta yi tare da cewa sannu da zuwa ƴar uwa." Murmushi Zahra ta saki tare da cewa. "Yauwa ina wuni?" "Lafiya lau kin zo lafiya ?" "Alhamdulillah." Jamilu ya kalli Hial ya ce. "Mr Man ya za ku yi wanka ne ko dai kun ci abinci?" Kamar bai ji me ya ce ba, ya cigaba da danne-danne a wayarsa. "Ka ce Mani tare da ƙanwarka kake to na ga dai wannan ba ta yi kama da Maryam ba, ina ka samo ta, ko ita ce mai shirin zama Amaryarmu?" Sai a lokacin ya ɗago ya yi masa wani bazan kallo mai nuna cewa na fi ƙarfin ajin yarinyar. "Me kake nufi ai wallahi wannan matar wuce sa'a ce, don Allah ina ka samo ta?" Sai da ya yi kamar ba zai amsa ba sannan ya ce. "Ƴar ƙanin mahaifina ne." "Wow gaskiya ban san ta ba " "Ai ba za ka sani ba." Ƴar uwa mu je na kai ki ɗaki ki yi wanka ki ci abinci ko?" Sumayya matar Jamilu ce ta faɗi haka tana jan hannun Zahrah, har masaukinta ta kai ta sannan ta janyo mata ƙofar. Zama ta yi tana kallon ɗakin sai ta miƙe da niyyar shiga wanka sai ta ji tana son jin muryar iyayenta. Don haka sai ta nufi Falo da niyyar ɗaukar wayarta ta manta ta barta a in da take zaune. A can falon kuwa Jamilu ya kalli Hilal ya ce. "Amma gaskiya da zan baka shawara ka ji da ka auri yarinyar nan Zahrah" Zahra dake shirin zuwa ɗaukar waya cak ta tsaya gabanta na faɗuwa. Don haka ta tsaya dafe da ƙirjinta. Wani kallo ba ka da hankali Hilal ya yi masa tare da cewa. "Allah ya kiyaye sa ai nafi ƙarfin ajin yarinyar nan, ko mata sun ƙare ba abinda zan yi da ita." "Ina ga dai ka makance ne yarinyar nan wallahi ko maƙiyina idan ya lalle ta ya san Allah ya yi halitta a wajen. Don wallahi ba za ka taɓa cewa ita ƴar Afrika ba ce. Ga ta nan kamar wacce ta fito daga jinsin Larabawa ko indiyawa." "Kai ka daina ƙoɗa yarinyar nan don ba ta gabana ko mata sun ƙare ba zan iya aurenta ba, don ba ta da banbanci da namiji a wajena." Rintse idanu Zahra ta yi don kalamansa sun taɓa mata zuciya . "Lallai ba ka da hankali Hilal ko ƴan matanka na can ba abinda suka fi Zahra da shi, sai dai wata ƙila su fita hasken fata, amma bayan haka ba kyau ko diri suka fita ba , idan dogon gashi ne na ga alamar ita za ta yi gashin. Ba za ka gane baiwar da Allah ya yi mata ba sai ka aure ta. "Na auri wa? Ai da na auri yarinyar nan gara na yi kiwon kare." "Subhanallah, wace irin ƙiyasta kake yi wa yarinyar nan har kake danganta ta da dabba? Dabbar ma karya?" Zahra dake tsaye ba ta san sanda kuka ya suɓuce mata ba, har dai da suka ji kukan nata suka juya suka kalle ta. Dafe goshi Jamilu ya yi cike ta jin haushin hakan, don bai so yarinyar ta ji wannan kalmar ba. Hilal kam ko a jikinsa. Wayar da ba ta iya ƙsrasowa ta ɗauka ba kenan . Ta juya ta koma ɗakin da ka sauke ta. Don ta muzanta yau, bs'a taba muzanta ta ko an ci zarafinta irin yau ba. Lallai family ɗin sun sun yi mata tsana mafi muni. Da ace tana da damar zaɓin yadda rayuwarta za ta kasance to da ba za ta taɓa zamowa a cikin wannan zuri'a ta su ba. Ba ta taɓa tsanar Hilal irin na yau ba . "Ka gani ko yarinyar nan fa ta ji ka, dole ranta ya ɓaci ." "Wannan ba matsala ta ba ce." Ya tashi yana cewa "ina bukatar yin wanka." Miƙewa ya yi ya masa jagora zuwa wani ɗaki dake jikin na ɗakin da aka sauke Zahrah. *Prison / Gidan yari* Wayarsa ya ɗauka tare da lalubo wata lamba wacce ya yi savin da LAUYANA. Ya yi ta kira har sau uku ba'a ɗaga ba, sai a na huɗu sannan ya ɗaga. "Barista lafiya ina ta kiran wayarka ba'a ɗagawa?" Daga ɗayan gefen ya ce. "Ina fa lafiya ni ma kai na a matsayina na lauyan dake kare ka dakyar na sha." Cikin nuna halin ko ina kula da lamarinsa ya ce. "Kuɗaɗen da suke hannuna ya ƙare, kuma ka san ba zan iya rayuwar da sauran prisoners suke yi ba, don ka san ba na iya cin abinci da abinda suke sha, duk siya nake yi kuma ga kuɗin hannuna sukan kare. Ko siyen abinci da abin sha ma kudi nake kashewa." Sai jin muryar lauyan ya yi yana cewa. "Ai ko ka fara koyon cin abincin da suke ci." "Ba gane ba me kake nufi, akwai abinda ya faru ne?" "Komai ma ya faru, domin sakamakon shari'ar da aka yi maku kai da Asadullah ka san cewa kotu ta binciko duk wasu ƙadarorin da ka tara na Asadullah ne, bayan gano komai kotu ta kwace duk wasu ƙadarorinka tun daga kan gidaje, filaye da gonaki da motocin da ka tara duk koto ta ƙwace yanzu haka an rufe asusun bakinka (Bank account) duk an rufe ba kudin da zai iya fita daga ciki. Wayarce ta suɓuce a hannunsa ta faɗi a wajen sumamme. *To na dan fans zuciyarku tana cike ta tarin tambayoyi, ku dai ku cigaba da bin alƙalanina da sannu zan warware maku wannan albarin mai cike da sarkakiya* *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page1️⃣9️⃣ Wayarsa ce ta suɓuce a hannunsa ta daɗi ƙasa , a wajen ya fadi sumamme. Bayan kamar mintuna talatin sai ga wani ma'ikatcin gidan yarin ya yi sallama ya shigo, hannunsa rike da jarida da ya kawo masa. Saboda kullun cikin neman jaridu yake ko zai yi tozali da ta mutuwar Asadullah. Sai dai ba haka ba bai taba katari da abin da yake son ji ba . Fridge ma'iakacin ya nufa tare da ɗauko ruwan sanyi ya yayyafa masa. Sai da ya yayyafa masa a karo na biyu sannan ya farfaɗo a firgice. _Fatima Zahrah_ Kuka take yi sosai kamar ranta zai fita, ta rasa wani irin tsana ne familyn su suke yi mata. Yanzu ƙiyayyar har ta kai a danganta ta da ƙasaitacciyar dabba kamar Karya. Kuka take mai cike ta ƙunar zuciya dake nuna tsantsar bakin cikin dake zuciyarta. Don Hilal ya ci zarafinta a gaban abokinsa. A can kuwa bayan Jamilu ya raka Hilal ɗaki ne ya wuce ɗakin Sumayya matarsa. Ganin yanayin kamar yana cikin damuwa ne ya saka ta ajiye wayar dake hannunta, tare da mai da hankali akan mijinta. Zama ya yi gefenta ta riko hannunsa cikin na ta. "Please ki ke ki rarrashi yarinyar nan." "Wace yarinyar kuma ?" "Baƙuwarmu." "Me ya same ta?" Nan ya sanar da ita yadda suka yi da Hilal, ita ma ranta ya ɓaci sosai. Cikin takaici take cewa. "Me ta yi masa ne haka?" "Ba abun da ta yi masa, kawai dai sun tsani yarinyar da ƴan uwanta da iyayenta ne." "Me ya saka haka suka zama kamar maƙiyan juna, alhalin jini ɗaya suke?" Na ya bata labarin komai da musabbabin tushen GABAR CIKIN GIDA da suke yi. Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa. "Wannan matsala tun farko kakanninsu ne suka haddasa ta, domin kuwa idan Allah ya baka ƴaƴa an sani dole akwai wanda kafi so a cikin ƴaƴanka amma kafa ja taɓa nuna wa ballantana sauran su fahimci kafi son ɗaya daga cikin yaran. Hakan na kawo matsala a tsakaninsu. Ballantana yadda ka sanar da ni sun fifita mahaifan Zahra da yawa. Kamar shi mahaifinta kaɗai suka haifa, ta yaya za ka banbance yaranka ta kowace fuska ka min yafi sauran ba kyau." 'Tashi ki je ki rarrashe ta Please." Tashi ta yi ta je ta yi knocking a ɗakin. Sai da Zahra ta yi sauri ta goge hawayenta hawayenta tare da daidaita nutsuwata sannan ta ba da izinin shigowa . Sumayya ce ta tashi tare shigo tsare da yin sallama. Zahra ta amsa mata tana ƙakalo mumrmushin wanda iya fatar bakinta kawai ta tsaya. "Yi hakuri har kin shigo ban shirya ba na fito ba ko?" 'lafiya kamar kin yi kuka meke faruwa?" A ganinta ba za ta iya fada mata ba, don haka sai ta ji murmushi tare da cewa. "Ba damuwa bari na yi wankan yanzu na fito Aunty." Kar ki kira ni da Aunty ina son mu zama ƙawaye ko bakya son mu kasance ƙawaye?" Mumrmushin ta yi tare da cewa. "To na daina in sha Allah." Tana fadar haka ta nufi hanayar toilet tana cewa. "Ina zuwa." Murmushi kawai Sumayya ta yi don yarinyar ta burge ta, da wata ce da tana tambayar ta za ta saki baki ta dinga bada labarin familyn da abinda ake mata, ko zancen abun da Hilal ya mata ba t dauka za ta iya fada mata ba." Wank ta yi tare da ɗauro alwala sannan ta fito, don lokacin sallar ta gabato Mumrmushi suka sakarwa juna yayin da Sumayya ta ce "Bari na zo Zahrah.' Kai ta jinjina tare da cewa to. Tana fita ta sanar wa mijinta yadda suka yi shima yarinyar ta burge shi. Zahara kuwa jakarta ta bude ta ciri man shafawarta da powder. Kaya ta ɗauko ta saka riga doguwar riga fitted grown na atamfar super england mai ruwan ƙasa da fari. Ɗan ƙaramin shafe ɗin ta ya fito ɗinkin ya karbe ta kuma ya zauna mata a jiki. Gashin kanta ta tufke ta nannaɗe sannan ta ɗaura ɗankwali ta saka hijabi, in da ta ga sallaya ta nufa ta gabatar da sallar azahar. Hilal wanka ya yi shi ma ya shirya cikin ƙananan kaya, yana shirin fitowa sai ga Jamilu ya shigo ɗakin tare da sallama. Ya amsa masa kamar baya son magana. "Zo ku ci abinci ko?" "Okay mu je masallaci mu dawo." Ya faɗa yana saka wayoyinsa a silent ya zuba a Aljihu suka fita zuwa Masallaci. _Asadullah Mansion_ Dad ya kasa barci har ƙarfe ɗayan dare, Mom ce ta farka ta ganshi tsaye yana zageye ɗakin. "Alhaji lafiya kuwa?" Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa. "Hajiya lafiya kau ki kwanta kawai." Tashi zaune ta yi tana kallonsa, ganin haka ya sa ya zauna bakin gadon tare da cewa. "Gabaɗaya hankali na ya kasa kwanciya ne dangane da tafiyar Asadullah. Dalili na farko bai taɓa tafiya ba tare da ya sanar da ni ba. Amma wannan karon sai na ga text message yana sanar da ni tafiyar. A lokacin na yi mamaki haka, da abinda ya hana ya same ni ya sanar da ni, sannan kuma har tsawon wata ɗaya kenan amma bai kira kowa a waya ba. Sannan suka layukansa na ƙasashen da yake zuwa na gwada kira ba sa tafiya. Ina ji a ajikina akwai wata matsala." "Gaskiya ne Alhaji ni ma kaina abun ya dame ni, jiya na gama wannan tuninin ina son da safe mu tattauna akan zancen. Kada ka yawaita saka damuwa kasan yanayin ciwonka baya son damuwa." Jinjina kai ya yi suka kwanta zuciyar kowa cike da saƙe-sake. Washegari gari da safe bayan yaran sun tafi school masu zuwa aikin sun tafi. Dad ne sai Mom da Aunty. Sun saka mijin nasu a tsakiya Dad ya kalli Aunty da Momya ce. "Ina son zan yi tafiya don nemo halin da ɗana yake ciki." "To Alhaji tun da ba ka san wace ƙasa ya ya tafi ba ta ina za ka fara?" "Ni ma ban sani ba daidai duk ƙasashen duniya da na san yana zuwa zan je na ji dalilin shirun nasa." Kallon Mom Aunty ta yi tare da cewa. "Allah ya kyauta ya wadaran naka ya lalace." Banzan kallo Mom ta yi mata tare da cewa. "Alhaji kana jin matarka ko, ka yi Mani iyaka da ita, ban san me yasa kake magana da ita akan matsalar da ta shafi Asadullah ba, ko ka manta irin ƙiyayyar da take masa ne, ko gaisuwarsa ba ta amsa wa da kyau. Ita da shi ba maganar arziki idan ya mata magana ba ta kula shi, sannan ta hana yaranta duk da ta san ƴan uwansa ne amma ta hana su magana da kowa, idan ta ga Suhaila na kiran Asad da Yaya ko tana masa magana sai ta yi mata duka. To wallahi ki zuba idanau idan wani abu ya samu ɗana sai na yi kuka dake." Dariya Aunty ta yi har da ƙyakyatawa ta ce "To makira ta nan za ki ɓullo to Ina jira daidai nake da zamaninki" Abba ne ya nuna wa Aunty ɓacin ransa wanda ya sa dole suka yi shiru Aunty ta tashi ta nufi ɗakinta Bayan ta tafi ne Kin ta kalli Dad ta ce . "Wallahi matar nan ba ƙaunarmu take yi ba daga ni har yara na, kuma duk abinda ya samu Asadullahi sai na yi Shari'a da ita." Dad ne ya kwantar mata da hankali sannan ya fita , kiran amintaccen bodyguard ɗin Asadullah ya yi wato Sulaiman. Bayan sun gaisa ne Dad ya masa tambayoyi dangane da wuraren da Asadullahi ke zuwa tare da shi. Da kuma wuraren da da yake zuwa shi kadai ba tare da kowane guard ɗin sa ba. Bayan sun tattauna Dad yana ƙoƙarin koma ciki sai ga Uncle Adam ya karaso wajen. Bayan sun gaisa ne y ce " Dama part ɗin ka zan tafi. Ya ake ciki ne har yanzu ba ka ji motsin Asadullah ko labarin ƙasar da ya tafi ba?" Girgiza kai Dad ya yi cikin damuwa ya kalli ƙanin nasa ya ce. "Adam har yanzu ba wani labari bai taba yin tafiya ba tare da ya sanar da Ni kasar da zai tafi ba, ko kuma ya tafiay bai yi Mani sallama ba sai dai wannan karon na ga sakon message da ya tura mani ta waya wai ya tafi wata ƙasar sai ɗauki lokaci kafin ya dawo." Jinjina kai Uncle Adam ya yi tare da kallon Sulaiman ya ce. "Har da kai bai sanar da kai ba?" "Bai sanar da ni ba, kuma abun da ya bani mamaki mun dawo daga kamfaninsa ASADULLAH GLOBAL RESOURCES." "To da kuka dawo sai aka yi yaya?" "Sai ya shiga gidan sauran guard ɗin suka tsaya a harabar gidan kamar yadda suka saba, ni kuma na ɗauki laptop da wasu file da ya dawo da su na taka shi har part ɗin sa, na ajiye masa a falonsa na fito. To tun daga ranar ban sake ganinsa ba har yau." Wani banzan kallo Uncle Adam ya masa tare da cewa. "Wannan ai zance banza ne , ta yaya kuka aikin kula da mutum ku ce b ku san lokacin da ya fito ba, barci kuke yi ko me?'" "Alhaji ba barci kuke yi ba, sanin kanka ne ko dare yayi akwai security da basa barci, sai dai su yi ta zagaye gidan nan har gari ya waye kafin wasu su karbi aiki. Amma wallahi ba wanda ya ga fitowarsa a cikin gid..." "Shut up! Me za ka ce kana nufin yana. Kwance a ɗakinsa ne ko me kake nufi? 6)To je ka kira shi." _Fatima Zahrah_ Fitowa ta yi zuwa dinning area kamar yadda Sumayya ta sanar da ita. Suna zaune su uku, Hilal, Jamilu da Sumayya. Bakinta ɗauke da sallama ta karasa wajen, tana sanye da hijabi wanda ya rufe mata jiki. Amsa mata sallamar suka yi ta karaso ta zauna. Abinci Sumayya ta zuba mata jallop ɗin cuscus da ya ji kayan lambu da kuma lemun ta zuba mata a kofi da ruwa. Sai farfesun kaza. Kaɗan ta ci ta kasa sake wa ganin irin kallon da Jamilu ke yi mata . Tashi ta yi bayan ta ɗan ci kaɗan ta sha ruwa, kallonta Jamilu ya yi tare da cewa. "Me kika ci?" "Alhamdulillah na ƙoshi." "Ban yarda ba, nan fa kamar gidanku ne, ina zuwa Katsina fa a gidanku nake sauka kuma ina sake jikina kamar gidanmu. Duk da ban taba haduwa da ke ba, sai dai ina tunanin ke ce mai fita kullum da niƙab ko?" Murmushi ta yi sannan ta sunkuyar da kai. "Okay na gane kullum idanunki kawai ake gani, nima yanzu na gane ki ne saboda wannan kyawawan idanun naki." Wani kallo Sumayya ta masa ya wayance ya cigaba da cin abincinsa. Wayar Hilal ce ta yi ƙara ya duba ALEXANDRA ce ke kiransa a waya. Ɗagawa ya yi suka fara magana cikin yaren ƙasar Spain. Tun da ya fara magana Jamil dake jin me yake cewa ne yake masa wani mugun kallo da harara. Su kam Sumayya da Zahra ba sa jin yaren sai dai idan ya ambaci Nigeria ko ya ambaci U.S ne suka san me ya kira. Bayan Hilal ya gama wayar ne Jamil ya kalle shi rai a ɓace ya ce. "Kana nufin goben nan za ta bar ƙasar U.S ta biyo ka Nigeria?" Kallonsa Hilal ya yi kamar baya jin me yake cewa, ya cigaba da danne-danne a wayarsa. "To ai sai ka bari idan ka koma can Katsina ta je ta same ka, amma ba gidana wacen shegiyar za ta zo ba." Sai a lokacin ya kalli Jamilu ya ce. "Gobe za ta zo kuma duk in da nake dole nan za ta zo, ba ka isa ka hana ta zuwa in da nake ba. Don da na yi niyyar kama hotel ai hana ni ka yi ka sa dole na sauka a gidanka. Don haka duk in da nake nan ALEXANDRA za ta kasance baƙuwata ce." "Baƙuwarka amma ba bakuwar arziki ba ne don haka ka je ka kama maku hotel kai da ita, Zahra za ta zauna a nan har ta kammala abinda ya kawo ta ." "Wallahi ba ka isa ba, yadda ka hana ni da farko na hanu yanzu ba ka isa ka saka ni ba." Yana gama fadar haka ya tashi cikin takunsa na ƙasaita ya nufi bedroom ɗin da ya sauka. Da kallon mamaki suka bishi wanda sam Jamilu bai yi mamaki ba don ya saba da halinsa. Zahara kam mamakin isa da gadara da yake da shi take yi. Washegari gari kasancewar da safe ne za'a gudanar da musabaƙar ya saka Zahra tun da ta yi sallar asuba ta yi azkar sai ta nufi kitchen. Don ba ta saba da barci safe ba. Ruwan tea ta dafa da ya ji kayan ƙamshi sananne ta yi farfesun kayan ciki ta soya dankalin turawa da plantain sai ta soya ƙwai . Lokacin da Sumayya ta fito har ta gama komai ƙamshin da ta ji ne ya bata mamaki Suka gaisa tana mata maganar ta wahalar da kanta tana girki, murmushi kawai ta yi tare da komawa ɗakinta. Kasancewar karfe takwas ta yi ne ya saka Zahra ta gama shirinta. Lokacin da Sumayya ta shigo kiranta har ta sanya hijabi. A tare suka fita in da suka tarar da Hilal da Jamilu suna cin abinci. Hilal kam ya shanye farfesun kayan ciki ya masa dad'i . Don bai ci komai a wajan ba tun da ya ji ƙamshin farfesun. Jamilu kowa har santi yake zubawa yana cewa. "Sweetheart wanan girkin na yau na musamman ne, gaskiya ya yi dadi." "Ba ni ba ce na yi Zahrah ce ta yi." Cak Hilal ya tsaya tare da ture bowl ɗin gabansa ya bar wajen. Da kallon mamaki Jamilu da Sumayya suna bishi, Zahra ko kallonsa ma ba ta yi ba, ba ta da riko amma abinda ya mata jiya ya tsaya mata a rai.zama ta yi inda Jamilu ya daga murya yake ce wa Hilal. "Ba ka birge ni ba har sai ka amayar da abun da ka ci sannan zan san ka yi abin kai." *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page2️⃣0️⃣ "Ba ka birge ni ba har sai ka amayar da abun da ka ci." Sunkuyar da kanta ƙasa ta yi ba tare da ta nuna ma ta san yana yi ba. Nan Jamilu da Sumayya suka dinga jan ta da fira da yaba irin daɗin da girkin nata, har ta saki ta fara dariya. Ganin saura mintuna arba'in a fara ne ya saka Zahra hankalinta ya fara tashi, musamman da ta ga Hilal baya da niyyar kai ta. Lura da yanayinta ne ya saka Jamilu cewa. "Ƙanwata lokacin ya kusa ko?" Murmushi kawai ta yi ba tare da ta yi magana. Don haka ya cigaba da cewa. "Bari na yi masa magana ya shirya, ai tare da ni za ku tafi. Don direban nasa na ce ba sai ya kira shi ba, ya bar shi s hotel ɗin za mu tafi da motata." Yana gama faɗar haka ne ya tashi tare da nufar ɗakin da Hilal yaƙew. Bayan kamar mintuna goma Jamilu ya fito ransa a ɓace. Da alama sun samu saɓani da Hilal ɗin. Jikinta ne ya yi sanyi ganin yadda ya fito, sai ya yi murnushi tare da cewa. "Ƙanwata muna ina zuwa please." Jinjina kai kawai Zahra ta yi ba tare da ta ce komai ba. Suna nan zaune ita da Sumayya sai ga Jamilu ya fito, sanye yake cikin wata yadi mai ruwan ƙasa, sai zuba ƙamshi yake zubawa. Kallon Zahra ya yi tare da cewa. "Fatima Zahrah ta shi mu tafi Yayanki baya da niyyar tashi kada ki makara." Kamar ba za ta je ba sai kuma ta yi wani tunani, saboda Ya Hilal na gidan ta san ko zuwa ya yi ya cutar da ita ko aka rasa ta dole shi za'a tuhuma tun da ya san shi. Don haka sai ta miƙe ta ce. "Yaa Jamil ina zuwa, ɗakinta ta koma ta ta ɗauko ƙaramin handbag ɗinta da niƙab, sai ta tuna a ce kada su saka saboda a san su. Don haka ta ajiye ta fito bayan ta rataye ƙaramin handbag ɗin ta. A tsaye ta same su shi da Sumayya suna rike da hannun juna. Don haka gaba suka yi tana biye da su a baya. Ɗaya daga cikin motocinsa dake parking space suka nufa. Ya shiga mazaunin Direba, Zahara ta kalli Sumayya ta ce "Auntu ke ba za ki je ba ne?" Murmushi ta sakar mata tare da cewa. "Sister ta ce ta haihu yau ake suna, can zan tafi ku yi haƙuri." Murmushi ta sakar mata tana cewa "Allah ya raya." Da Amin ta amsa mata yayin da ta buɗe mata murfin motar, ta shiga ta zauna gefen Jamilu. Ɗaga masu hannu ta ta yi yayin da ya yi wa motar key maigadi ya wangale masu gate suka bar gidan. Wajen harabar in da za'a gudanar da gasar karatun Al-ƙur'anin ya cika da mutane. Suna parking kiran waya ya shiga cikin wayarta. Ba kowa ba ne face Mallam Usman, Mallamin islamiyarsu da ke sonta. Ɗaga wa ta yi baya ta yi sallama take sanar da shi sun iso. Wajen da aka tanada saboda parking motoci ya nufa. Bayan ya yi parking suka fito. Mamakin cikar jama'a dake wajen ta yi, duk da an sanar da su da yadda komai zai gudana a wajen, amma ba ta yi tunanin yawan jama'ar sun kai haka nan ba. Taro da ya ƙunshi manyan mutane tun daga kan ƙusoshin gwamnatin zuwa hamshaƙan ƴan kasuwa da ƴan siyasa, sarakuna. Da masu matsayi a gwamnati. Jami'an tsaro kuwa ga su nan cike a wajen suna gudanar da aikinsu. Don an saka matakan tsaro sosai ba waje ne da za ka je kai tsaye a bar ka ka shiga ba, sai an bincike babu wani abu na cutarwa a tattare da kai. Cikin sanyin jiki ta ƙarasa in da ta hango tawagar ƴan jiharsu. Yayin da Jamilu ya zauna ɗaya daga cikin kujeru da aka tanada don baƙi su zauna. Tana ƙarasawa ƴan tawagar su da Mallamansu suka nuna jin daɗinsu da isowarsa. Nuna mata wajen zaman da aka tana da dan su aka yi. A hankali ta fara taku cikin nutsuwa ta nufi wajen zamansu , taka step ɗin take yi cin nutsuwa yayin da ta kasa ɗaga idanunta. Saboda idanun. Mutane da take ji yana mata yawo a jiki. Ɗaya daga cikin kujeru uku da suka rage ba mutane ta nufa. Kowane kujura an rubuta sunan state, kai tsaye ta nufi wanda ta ga an rubuta Katsina state. Saura na Adamawa da Niger state. Su ne da alama ba su ƙaraso ba. Zaman ta ba jimawa sai ga ƴar jihar Niger ta iso Salma Usman Isma'il. Daga kashe sai ga na jihar Adamawa namiji ne shi ma ya ka karaso wajen. Ƙamshin daddaɗen turarensa ne ya daki hancinta. Wanda ya haifar mata da faɗuwar gaba, kamar an ce ta ɗaga kai sai kuwa ta sauke su akansa lokacin da yake shigowa cikin taron. Da Sanye yake cikin wata ɗanyar shadda fara sa sai ɗaukar idanu yake yi, yana sanye da baƙar hula sai bakin takalimi hannunsa ɗauke da tsadden agogonsa. Duk da fuskar nan a tsuke take babu sassauci amma hakan bai hana kyawunsa da cikar haibarsa bayyana ba. Jamilu ne ya karaso wajensa yana masa nuni da in da za su zauna, kamar ba zai zauna ba sau ya bishi suka zauna. Nan Sheikh Muhammad bin Ali shahararren Mallamin da ake alfahari da shi ya yi sallama, tare da bude taro da addu'ar ya gabatar da abinda ya tara su . Tare da yi wa manyan baƙi da kowa barka da zuwa, in da ya gabatar da sunanyen wasu manyan baƙi da suka halarci taron. Governor bai samu zuwa ba amma ya turo Wakilinsa ya halarta. Cikin nutsuwa aka fara gabatar da komai, tamabayoyi ne ake masu na alƙu'arni. Maza da mata ana tambayarsa cikin sura kaza aya ta kaza ka karanto su. Ko kuma a yanko aya a tsakiyar surorin al-ƙur'ani a ce ka karanta , har sai ka kai yadda suke so sai a dakatar da kai a sake shiga cikin wata surar a ce a ce cikin sura kaza aya ta kaza ki karanto su. Kina gama kai in da ake so sai a dakatar da ke a sake tamabayarki wata aya cikin wata sura ki karanto su. Kuma an soma kowane harafin ki bashi hakkinsa don ko kaɗan kika yi kuskuren harshe sai na gyara maki. Tun ana yi wa ƴan wasu state har aka zo kan Katsina state in da Zahra ke wakiltar ɗaliban jiharsu. Kowace tamabaya aka yi mata cikin kowane sura aka fada mata lambar ayar kai tsaye za ta fara rero karatunra cikin zazzaƙar muryarta mai saka nutsuwa a cikin zuciyar ma'abota saurarenta. Ta burge mutane da yawa saboda karatun na ta ba'ayi mata gyara ko ɗaya ba, kowane harafin tana bashi hakkinsa. Kuma duk surar da aka yanko mata za ta fara babu tsayawa har sai an dakatar da ita. Ta burge mutane da yawa ga yan jarida da yan gidajen rediyo suna ɗauka, bayan masu ɗauka da wayoyinsu. Tsawon lokaci aka ɗauka ana gudanar da komai gwanin sha'awa, yayin da Zahra ta shiga ran mutane da yawa, yadda duk in da aka aka ce ta karanto za ta karanto take ba tare da sai ta tsaya nazari ko tinani ba. Hakan ya saka jaharta Katsina ta ci wannan gasar. Ita ce ta zo ta ɗaya a cikinsu. In da ta samu manyan kyaututtuka na ban mamaki. Don kujerar Hajji sai da ta samu guda biyar da mitoci biyu. Ga masu ba ta kyaututtukan kuɗaɗe. Tsabar farin ciki kuka ta yi sai hawaye ke bin fuskarta. Sauran ma sun samu kyautar amma ba ta kai ta Zahra ba, ta biyu zuwa na biyar ne suka samu kyautar kujerar Hajji. Farin ciki a wajan Mallaman makarantar ta su ba'a magana. Don sai washe baki suke yi. Haka aka tashi taron cikin farin ciki, yayin da ƴan jarida ke ta ƙoƙarin sun ji ta bakin Fatima Zahrah Salis Tafarki amma abun ya ci tura. Don ta kasa magana sai kuka take yi. Gashi sai hasken Camera ke ta haska ta ta ko ina, wasu saboda ƙwazonta yayin da wasu kuma saboda kyawun da Allah ya yi mata. Kamar yadda tsarin su yake sai an koma state ɗin ta kafin a damƙa wa iyayenta kyaututtukan da aka bata. Haka ma ta kasance. Sallama ta yi wa Mallamansu da niyyar idan ta koma za ta same su a makaranta ita da iyayenta. Tafiya take a hankali ta ji mutane na bin ta a baya za su yi photo. Ba musu ta bawa duk masu bukatar daukar photo da iya dama, wasu kuma ita kadai suke dauka saboda su yi posting a a social media. Jamilu ne ya karaso wajen da suke ya kira ta don ta zo su wuce. Da Ɗaga kai ta yi suka haɗa idanu da Nihal ya watsa mata mugun kallo. Ganin haka ya saka ta bar wajen da sauri don wuce wa. Tana tsaka da tafiya ta ji ana mata sallama. Juyawa ta yi ta kalli mai sallamar. Wani matashin saurayi ne kyakkyawa yana sanye cikin gezna ruwan sky blue ya guard ɗin sa na biye da shi a baya. Murmushi ya sakar mata tare da cewa. " Hafiza barka da wannan lokacin, don Allah ko za'a jiƙaina a bani lambar waya?" Shiru ta yi wanda ganin haka ya saka ya yi murmushi tare da miƙa mata wani kati. Karɓa ta yi ta yi gaba. Tana tafiya cikin sanyin jikinta, wanda har lokacin ba ta daina jin idanun mutane na yawo a jinkinta ba. Suna ƙarasowa wajen parking motocin sai wani mutum yana sanye cikin Suit ya karaso, tare da miƙawa Hilal da Jamilu hannu suka gaisa. Kallonsu ya yi tare da cewa "Na so na ji matakin Shari'a don Allah idan ba damuwa ina son na sani wannan sister naku an yi mata miji ne?" Da sauri Jamilu ya ce . "Ƙwarai kuwa nan ba da jimawa ba za'ayi mata aure sai ka yi hakuri." Cikin sanyin jiki ya masu godiya ya tafi. Ita dai Zahra mamakin Jamilu ne ya kama ta. Gefen motarsa wajen me zama banza ya bude mata. Shiga ta yi ta zauna wajen me zaman banza. Hilal ya zauna bayan motar kasancewar ya tura direbasa ya dauko massa ALEXANDRA a airport. "Mallam ina motarka da Direbanka, bai tanka masa ba ya dinga danne-danne a waya. Har suka karasa gidan bai yi magana ba, Sai Jamilu dake ta jan Zahra da fira yana yabawa baiwar ilimin da Allah ya yi mata.ita dai fage uhm sai umm." A parking space suka yi parking ta fito shima ya fito yayin da Hilal ya fito daga karshe. Key ya saka ya buɗe gidan suka shiga. Kai tsaye ta nufi ɗakin da aka sauke ta. Jamilu ya kalli Hilal ya ce. "Abokina gaskiya ina son wannn sister ta ka fatan za ku bani aurenta, hakan ya saka na cewa wancan gayen ta kusa yin aure ya haƙura." Ita ko wayarta ta ɗauka tana kiran Abbi da Umminta, ba su shiga ba don ta lura tun tuni ya dace su dawo amma ba su dawo ba, amma ta ji Yaa Sadik ya ce mata jikin Papa ne ya tsayar da su, amma nan da kwanaki uku za su dawo. Don Papa na asibiti likita na kula da lafiyarsa. Fitowa ta yi da niyyar ta duba ko akwai aikin da za ta taya matar gidan, fitowarta ya yi daidai da shigowar direban Hilal da wata baturiya a bayansa. Tana ganin Hilal ta ruga wajensa wanda ganinta ya sa ya miƙe tsaye ta rungume shi a jikinta tare da sumbatarsa a kumatu. Mumrmushi ya yi mata yayin da Jamilu ya tsuke fuska yana masu wani banzan kallo musamman ALEXANDRA. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page2️⃣1️⃣ Fitowa ta yi da niyyar ta duba ko akwai aikin da za ta taya matar gidan, fitowarta ya yi daidai da shigowar direban Hilal da wata baturiya a bayansa wanda ganinta ya sa ya miƙe tsaye ta rungume shi a goshinta tare de sumbatarsa a kumatu. Murmushi ya yi mata yayin da Jamilu ya tsuke fuska ya masu wani banzan kallo musamman ALEXANDRA. Kau da kai Zahra ta yi ya nufi kitchen ɗin, tsawon mintuna biyu suka ɗauka kafin ya zame ta daga jikinsa ya fara magana cikin yaren ƙasar Spain. "Dama da gaske za ki zo duk in da nake?" "Ina mai tabbatar maka ko a karkashin ƙasa kake zan bila?" "Anya za ki iya zaman Nigeria kuwa?" "Me zai hana idan ina tare da kai." "Amma da kin jira dai na dawo." "Gaskiya ba zan iya jira ba domin sanin kanka ne cewa ba zan iya hakuri rashinka har na sati ɗaya ba, ga shi kamar ba za ka dawo ba, don haka tare za mu koma ƙafata ƙafarka." Sai a lokacin da ta kalli Jamilu don ta san shi tare da Hilal tare da shi suka yi karatu a can ƙasar. Gaishe shi ta yi ya amsa mata ba wani sakin fuska, duk da cewar ta dade da gane cewa baya son tarayyarta da abokinsa amma ba ta damu ba, saboda shi Hilal yana sonta. Amma duk da ta ji wani irin yadda ya amsa mata sai ta ji wani iri, lakatar hancinta da Hilal ya yi ne ya sa ta lalle shi tan murmushi. Cikin yaren Hausa Jamilu ya fara magana yadda ya san cewa ba za ta ji shi ba. "Dalla Mallam ka ɗauke mani wannan abar a cikin gidana, duk da ba yau za ku koka Katsina ba sai gobe tabbas wannan ba za ta kwana a gidana ba, sai dai daga kai har ita ku je ku jama hotel ku kwana, washegari ka zo ka dauki Zahra ku tafi, ko ma da kaina zan iya mayar da ita gidan. Wani kallon baka isa Hilal ya yi masa ba, sannan ya ɗaura da cewa. "Tabbas nan gidanka ne amma ba ka isa ka kore mu ba, har sai gobe idan mun tashi tafiya. Da lokacin da na yi niyyar kama hotel me ya saka ka dame ni akan na sauka a gidanka, duk da ba da shawarar son raina na sauka ba saboda yanzu kana da mata, ni kuka nake ganin kamar zan takura har. Kana fushi da ikirarin ba za ka sauka a gidanmu idan ka sake zuwa garin ba. Dole ba da son raina na zo ba. Sannan yanzu ka kawo Mani wani zancen ba ka isa ba." Yana fadar haka ya ja hannun Alexandra suka nufi bedroom ɗin da y sauka. Muryar Jamilu ya ji yana ce masa. "Nan gidan Sunnah ne wallahi ko da wasa kuke aikata Mani ɓarna a cikin gidana sai na baku mamaki, tun da ta kasa hakuri ka koma can ku cigaba da iskancin da kuka saba." Kamar Hilal bai ji shi ba ya share shi suka shiga cikin bedroom ɗin. "Zahra tana kitchen tana mata goge goge, ta ji maganar Jamilu tana mamaki dama haka halin ya Hilal yake, take ta ji babu dad'i a ranta. _Asadullah Mantson_ Uncle Adam ya cigaba da yi wa Sulaiman faɗa akan me za' ce ba'a san in da Asadullahi yake ba. Bayan shi ne na hannun damansa. Ya kamata ace duk in da yake yana tare da shi. Ko da cikin falonsa ne. Jin faɗar ya ƙi karewa ne ya saka Dad yi masa magana akan ya bar shi don yana iyakar ƙoƙarinsa. Uncle Adam bai saurari Dad ba ya kira duka guard ɗin dake kasance tare da Asadullahi ya masu tambaya, sai dai kowa amsa iri ɗaya suke bashi. Dole ya ƙyale su don ba abinda zai ce masu kuma. _Jidderh_ Tun daga ranar kullun sai ta faki idanun mutane ta nufi ɓangaren da Asadullahi yake, ta je ta bashi abinci ya ci ta bashi ruwa. Sannan take samun nutsuwata a rayuwarta. Kuma kullum sai ta yi masa kuka, musamman ganin yadda ya rame duk da shi ba mai yawan cin abinci ba ne amma ta lura duk ta saci jiki ta kai masa abin da zai ci. Duk da shi ba mutum ba ne mai yawan cin abinci ba ne, amma ta lura kullum idan ta je kai masa abinci sai ya dinga rawar jiki wajen cin abincin. Da alama yunwa yake ji. Hawaye take yi idan tana kallonsa. Su kansu waɗan da suka tsare shi a wajen dau ɗaya sauke bashi abinci. Su kansu sun fara mamakin ganin kwana biyu baya galabaita da yunwa. Don haka suka fara tunanin saka ido a bangaren da kuma mutanen cikin gidan, don sun san tabbas akwai wani abu a ƙasa. Don haka yadda suke barin ɗakin da suka barin ɗakin Asadullah ba tare da sun saka key ba, saboda sun san cewa sun ɗaure shi da sarƙa, ba iya tashi zai yi ba, kuma bugu da ƙari ba wanda yake zuwa ɓangaren da aka aje shi. Don haka ya faɗa tunanin su rufe. Kamar kullum yau ma ko da ya shiga part ɗin bayan Doctor ya tafi ne, ta shigo ɗakin. Sanye take cikin wata doguwar riga baka, ta sanya p cap 🧢 a kanta, sannan ta saka facemask da ban n gallass. Ba wanda ya zai iya gane ko wace ce saboda ta yi shigar ɓadda kama. Tura ƙofar ta yi ta ji ta a buɗe. Jidderh wacce ta gana ba shi meet pie ta tashi da sauri jin motsi ta nufi toilet. Tana. Shiga ana gama shigowa ɗakin jin kamar motsi ya saka ta waige-waige ganin ba kowa ya saka ta nufi toilet ɗin ta tura ƙofar da sauri ta shiga ciki. _Zaharah_ Ganin har yamma ta fara gabatowa Sumayya ba ta dawo ba ne ya saka Zahra ta shiga kitchen bayan ta idar da sallar la'asar ta shiga kitchen Fried rice ta girka masu ta wanda ya ji kayan haɗi da hanta. A dinning table ta jera komai. Daidai lokacin da Jam'i da ya fita ya dawo, don haka nuna jin dadinsa ya yi mata godiya. Tuna cewa Alexandra na gidan ya saka Jamilu canza fuska, kallion Zahra ya yi tare da cewa. "Ƙanwata ki kai wa Yayanki da baƙuwarsa na su a daki, saboda ba na son ta fito, ɗin a zahirin gaskiya ba na ƙaunar ganinta." Ya ƙarasa faɗa yana yin tsuki Ba musu Zahra ta samu madaidaicin flask ta ta zuba masu na su, ta haɗa da soyayyar naman kaza. Sai Lemun kwakwa da ta haɗa duka ta jera su a tire. Ta saka plate da cokula. Kai tsaye ta nufi ɗakin da ta san ya sauka. Sallama ta yi ba'a amsa ba, har sau uku shiru. Hakan ya saka ta shiga kai tsaye tun da ta san ba ɗakin ma'aurata ba ne, kai tsaye ta shiga ciki. Kanta a ƙasa ta ajiye tire a saman table dake ɗakin. Ɗagowa ta yi ta sauke idanunta akan su. Zaune yake akan doguwar kujerar mai zaman mutum uku, yana sanye da wando dogo babu riga a jikinsa. Alexandra tana zaune a saman cinyarsa babu kaya a jinkinta daga ita sai pant ko bra babu a jikinta. Suna tsotson bakin junansu. Zaro idanu Zahra ta yi tare da furta kalmar. "A'uzu billahi minash shaiɗani raƙumi." Da sauri ta fito cikin yanayin firgici. Jamilu dake falon ya kalle ta . tafe da cewa. "Zahra lafiya?," Ba ta iya cewa koma ɗakin ta sauka Da hanzari ya nufi ɗakin ganin abin da koro Zahrah, shi ma ganinsu ya yi kamar yadda Zahrah ta gansu . Take ya tsuke fuska ya fito ransa a ɓace, zama ya yi a Wajan cike da takaicin Hilal. Bayan m Kamar muintuna ashirin sai ga kiran sallar magrib. Jamilu ya mike kenan sai ga Hilal ya fito sanye da farar jallabiyarsa da alama alwala ya zai je masallaci. Kallo ɗaya ya shi ma Hilal ya masa ya ɗauke kai . Masallaci ya nufa yayin da shi ma Jamilu ya ɗaura alwala ya nufiadallaci don gabatar da sallar magrib. _Zahrah_ Tun da ta shiga ɗaki ba abinda take dai sai aikin kuka, kuka ba take yi sosai don hankalinta ya tashi da abun da ta gani, mace kusan tsirara tana zaune a saman cinyar Yaa Hilal tana tsotson bakinsa. Dama haka halin Yaa Hilal yake ba ta sani ba. "Yaa Hilal me ya saka ka zaɓe wannan ƙazamar rayuwar ne? Dama da gaske ne da nake ji cewa wai sojoji suna da neman matan banza da shan giya? Shin kai ma kana shan giyar ne?" Haka ta dinga riskar kuka kamar ranta zai fita. Jin har an tayar da Sallah ya saka ta tashi da sauri ya nufi bathroom. Wanka ta yi sauri-sauri ta ɗauro alwala, rigar barci ta saka riga da dogon wando farare. Ta sanya Hijabi har ƙasa ta fara gabatar da sallar magrib. Tana nan zaune ha tana addu'o'i har aka kira sallar isha'i. Sai da ta yi sallar sannan ta hau kan gadon bayan ta naɗe sallayar da hijabi ta ajiye. Kwanciyar ta ke da wuya sai ga Sumayya ta turo ƙofar ɗakin bakinta ɗauke da sallama. Amsa mata Zahra ta yi tare da yi mata sannu da zuwa. Amsawa ta yi cike da jin dad'i tare da yi mata godiyar girki. Murmushi ta yi tare da cewa. "Ba komai kada ki damu." ""Na sha Allah Allah, ina ganin girki har yawu na tsinke wa Sai da oga ya ce kafin na ci sai na kira ki kema kin ci." Gaskiya na ƙoshi yanzu." "Me kika ci?" "Ba komai ba na jin cin komai ne." . "Akan me gaskiya ban yarda ba tashi mu tafi " Duk yadda ta so ƙin fita Sumayya dai da ta takura mata suka fito. Jamilu na zane a dinning table yana jiransu, daidai lokacin da Hilal ya dawo daga masallaci. Sallama ya yi wanda idan ba wanda ya kalli bakinsa ba zai san ya yi wata sallama ba. Kasancewar sun kalli kofar ya sa suka amsa. Sumayya ce ta gaishe shi cike da kulawa, ya masa mata a takaice ya nufi bedroom ɗin da yake ciki. Jamilu da Zahra ba wanda ya ce masa uffan. "Ka kira abokinka mana ya zo ya ci abinci. Ko ƙanwarsa ta kira shi ne?" "Kada ki damu an kai masa nasa a ɗaki kasancewar yana tare da baƙuwarsa." "Baƙuwa ya yi ?" "Eh" Ya bata amsa a takaice. "Okay ai da ta fito mun yi dinner tare." Tsuke fuska ya yi tare da cewa. "Ki bar su kawai." Ita ta yi sevin nasu suka fara cin abinci, Zahrah dai abin da ta gani ya tsaya mata a rai. Duk da yau ranar farin ciki ne amma abin da ta gani ya shafi farin ciki da walwalar da take ciki. Har Allah take gari ya waye su kama hanayar komawa gida. Nan suka dinga cin abinci suna jan ta da fira suna ta yaya ta murna na samun nasara tare da mata fatan alkhairi. Bayan sun kammala ne ta yi masu sallama ta shiga cikin, duk da sun so a ce ta tsaya sun yi fira da ita. Kwanciya ta yi ta bayan ta ɗauro alwala ta yi addu'ar kwanciya barci. Ƙarfe biyu na dare ta farka ta ɗauro alwala ta zo ta gabatar da sallar nafilfili. Sai asuba ta idar tare da yin addu'o'i. Har aka yi assalatu ta yi sallar asuba. Azkar ta yi sai da garin ya fara haske ta fito zuwa kitchen. _Hilal_ Akan hanyarsa ta dawowa daga masallaci suka jero tare da Jamilu. Bayan Jamilu ya bashi hannu sun yi musabaha ya kalle shi ya ce. "Hilal" Bai kalle shi ba amma ya san ya ji shi. Don haka ya cigaba da cewa "Nan fa Nigeria ne ba U.S ko London ba, irin rayuwar da kake yi a can kada ka ce za ka yi shi a nan. Domin Addininmu da Al'adar mu ya sha banban da ta su. A can don ka rungume mace ka sunmbace ta ko yi abinda ya fi haka ba wanda zai kalle ka. Amma anan ba haka ba ne. Yanzu har ya kai ka kira ɗaya daga cikin matan da kake harka da su don su zo su same ka a ƙasar ka?" Yau za ku tafi ina za ka kai ta?" "Gidanmu." Da mamaki ya kalle shi don ya san in dai ya fadi abu sai ya aikata. Don haka ya ce. "Allah ya kyauta. Amma da zan baka shawsra ka ɗauka ko da sai na ce . Ka auri yarinyar nan Fatima Zahrah." Wani banzan kallo ya yi masa tare da ɗauke kansa. "Na yi maka kwaɗayin samun nagartacciyar matar aure ne ya da na baka wanann shawara. Don idan ka aure ta to tabbas ka nema wa yaranka uwa ta gari abun alfahari ga...." Ɗaga masa hannu ya yi alamar baya son maganar, don haka ya yi mumrmushi tare da cewa. "To ni zan yi ta biyu da ita in sha Allah ba zan bari ta kufce mani ba." _Zahrah_ Tana shiga kitchen ɗin sai hayaƙi da ƙauri ya turnuke ta. Sakamakon manja da Sumayya ta bari a wuta ya ƙone ta fita zuwa ɗakinta don ɗauko green pepper da ta dawo da shi jiya daddare sai ta ajiye a bedroom ba ta kawo shi kitchen ba. Zahra na shiga ta shaƙi hayaƙin, da sauri ta kai hannu ta kashe gas ɗin cikin ƙarfin hali. Tana fita ƙofar kitchen ɗin numfashinta ya fara ɗauke wa. Kafin ka ce ne har ta zube a wajen. Ƙoƙarin tashi take yi don ta je ɗaki amma ta kasa. Cikin wannan halin Sumayya ta rugo da gudu sakamakon tuna Abinda ta bari a wuta. Ganin halin da Zahra ke ciki ya saka ta yi ihu daidai lokacin da Hilal da Jamilu suka iso . Wajen suka nufa in da suka yi kanta, cikin tashin hankali Jamilu ya ce. "Meke faruwa?" Cikin kuka Sumayya ta ce ba ta sani ba. Halal dake tsaye hannunsa a cikin aljihun wandonsa ya ce "Ina ga wanann hayaƙin ya saka ciwonta ya tashi." "Wane ciwo?" Jamilu ya tamabaya ciki n damuwa. "Athma" Ya faɗa yana kallonta. Juyawa ya yi ya nufi ya nufi bedroom ɗin da ta sauka. Handbag ɗin ta ya buɗe, ya duba Inhelar ya ciro daga cikin jakkar ya fito. Fitowa ya yi ya nufi in da take durƙusawa ya yi a gabanta ya shaƙa mata Inhelar ɗin. Zuba mata idanu suka yi suna kallonta. Numfashinta ya fara daidaita. "Ki yi hakuri don Allah ban sani ba " Sumayya ta faɗa cikin rauni. Sannan Jamilu ya kalle ta da cewa. "Gaskiya duk wanda zai suna da ke sai ya kiyeye abinda zai iya jefa rayuwrki cikin hatsari, shawarar da zan bashi kenan ko?" Ya faɗa yana kallon Hilal. "Ko ba haka ba abokina?" Taɓe baki Hilal ya yi tare da cewa. "Ko kuka ka bashi shawarar ya nemi gida kusa da asibiti ya tare saboda ko da ta ɓaci ba su da nisa da asibiti ba sai ya yi ta wahalar sintiri ko wace rana ba don zuwa asibiti ba, idan ma da gida a asibiti nan ta kamata ya tare da ita." Yana gama fadar haka ya wuce abinsa. Da kallon mamaki suka bishi, Zahra wacce numfashinta ya dawo daidai tsabar mugayen kalamansa ya sa ta ji shi kamar saukar aradu ƙirjinta kamar an ɗora mata dutse, zuciyarta kuwa kamar an watsa mata garwashin wuta. Su kansu ba su ƙi dadin kalamansa ba, don gara kalmar da ya yi mata shekaranjiya in da ya ce ba ya kallonta a matsayin mace. Ba ta da banbanci da namiji a idanunsa. Tsabar ɓacin rai ya saka ta fashe da kuka mai cike da ƙunar rai. Take kuma numfashinta ya ɗauke. 🤔 _Tofah ga Jidderh can ashirinta zai tonu a toilet garin taimakon Asadullah. Ga Zahra na cikin wani hali saboda mugayen kalaman Hilal, ko ya za ta kaya?_ *A gaskiya rashin comments naku ya saka bana yin typing kullun. Domin sai na yi zaman awanni biyu ko uku ina typing ne ya sa comments na minti biyu ba za ku iya ba? Idan har ba ku canza ba to ba za ku samu update kullum ba wata kila ma na ce na mayar da shi paid book. Don idan paid ne ba zan damu da rashin reactions ko comments ba*😒 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page2️⃣2️⃣ Tsabar ɓacin rai ya saka ta fashe da kuka mai cike da ƙunar rai. Sumayya ce ta taimaka mata ta tashi, har zuwa bedroom ta ta raka ta, a bakin gado ta zauna. Nuni ta yi wa Sumayya da handbag ɗin ta, ganin haka ya saka ƙarasa ta ɗauko mata. Cikin ƙarfin hali ta ɗauko magani a ciki, ganin haka ya saka Sumayya ta ɗauko mata robar ruwa a fridge ta buɗe sannan ta miƙa mata. Amsa ta yi bayan ta saka maganin a bakinta ta haɗiye. Karɓar sauran ruwan ta yi ta ajiye. Yayin da ita kuma ta koma ta kwanta. Zafi kawai kalamansa ke yi mata a zuciya, don Yaa Hilal ya ci mutumcinta ya mata tozarci da ba wanda ya taɓa yi mata ba. Duk da zafin da zuciyarta ke yi sai ta dinga karanto addu'o'i a bakinta, ba jimawa barci ya ɗauke ta. Ganin ta yi barci ya saka Sumayya fita daga cikin ɗakin. Tana fita kitchen ta koka don karasa sauran aiyukan nata. Cikin ɓacin rai Jamilu ya nufi bedroom da Hilal yake ciki. Ko sallama bai yi ba ya kutsa kai ciki. Hilal dake rike da waya a kunnensa ko kallon ƙafar bai yi ba ballantana ya kalli wanda ya shigo. Sai da ya gama wayarsa fuska a tsuke ya kalli Jamilu wanda shi kuma yake kallon Alexandra dake kwance saman gadon cikin bargo, barci take ji hankali kwance. "Yanzu abin da kake yi wa yarinyar nan ya dace?" "Ni ba abinda na mata kada ka ɓata Mani rai da safen nan." Cikin ɓacin rai Jamilu ya ce idan dai har ba za ka taba canza wa ba ko? To ko don ka saba take haddin mata ne ya saka ba ka ganin ƙimar mace. Ba tare da ya kalli Jamilu ba ya ce . "Ban taɓa keta haddin ko wace mace ba ka sani, kai kanka shaida ne. Ko da wasu sun fadi haka kai mai iya ƙaryata wa ne. Ban taɓa aikata fasikanci ba duk tsiya ta sai dai na ragewa kaina zafi amma ba na wuce gona da iri ba." Shiru Jamilu ya yi yana kallonsa, don ya san halin abokin nasa tun suna secondry school har suka tafi ƙasar waje karatu. Ko a zaman su a ƙasar ya dai san sauran abokansu na dake can suna sheƙe ayarsu da mata, suna lalata da mata. Sai dai shi Hilal bai taɓa aikata lalata da kowace mace ba, sai dai yana romancing da su ya rage zafi amma ko da wasa bai taɓa gigin aikata zina ba. Iyakarsa rungume-rungume da sumbace-sumbace har sai ya ji ya rage zafi. Duk da akwai baƙaken fata da suke sonsa a can sai dai iyakarsa da su ragewa juna zafi. Duk da wasu sukan na ce akan ya biya buƙatarsa da su baya yarda. Idan mace ma ta nace amsa akan haka to rabuwa yake yi da ita. Alexandra ita ce Baturiyar da ya daɗe yana mu'amala da ita ba tare da ya rabu da ita ba kamar sauran ba. Don sun kai shekara a tare, amma ganin irin son da take masa ne ya saka ya kasa rabuwa da ita. Don tana masa so ne sosai wanda ko wata mace ta gansu tare sai ta yi kamar za ta yi hauka take yi. Don ta kusa kashe wata baturiya mai suna Juliet akan Hilal. Mumrmushin takaici Jamilu ya yi tare da cewa. "Na sani wannan ɗin ma Allah ya yafe maka." Daga nan ya nufi ƙofar fita har ya rike handle ɗin ƙofar har zai fita ya tsaya ya ce. "Ina neman auren Zahra fatan dai za ka shige Mani gaba har burina ya cika." "Ka bar wannan zancen kawai matukar kana son abotarmu ta ɗore Gajeren murmushi Jamilu ya yi tare da cewa. "Shikenan idan na za ka taimaka Mani ba na san hanyar da zan bi." Yana gama fadar haka ya fice ba tare da ya sake yin wata magana ba. Ba jimawa dai ga shi ya sake shigowa ta tire a hannunsa. Breakfast ne aka jera a ciki. Kamar yadda Jamilu bai ce komai ba haka zalika shi ma bai ce masa komai ba ya tashi ya shiga bathroom don yin wanka. Tsawon mintuna talatin ya ɗauka kafin ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa. Sai wani karami dake hannunsa yana tsane gashin kansa . Ƙarasa wa ya yi zuwa bakin gadon yana tayar da Alexandra. A hankali ta bude idanunta tare da sauke su akan ƙyakyatawar fuskarsa. Allah ya jarabe ta da son Hilal a zuciyarta fiye da kowa da komai. Kuma ba ta da burin da ya wuce ta ga ya yi sex da ita amma hakan ya gagara. Don ya faɗa mata gaskiya ba zai taba iya yin sex da wata mace ba matukar ba matarsa ba ne, addininsu ya gane su da aikata hakan. Lokacin da ta ji ja sanar da ita haka sai ta nuna masa cewa ya aure ta mana, ya nuna mata hakan ba mau yiwuwa ba ne, familyn da ba za su yarda ba, musamman yadda ya san yanayin kakansa Baffa . Don haka ta hakura ta kyale shi amma ta sawa ranta dole wata rana sai ya yi sex da ita ba za ta iya haƙura ba kamar yadda sauran ƴan matan suka haƙura. Don duk iskancin da yake yi da mace sai dai ita ta yi tsirara a gabansa amma shi sai dai ya cire riga da wando amma bexer na jikinsa ba zai taba barin ya yi tsirara tare da mace ba. Akwai wata mace mai suna Rahama ƴar wani attajiri ne suka tsaka da iskancin su ta ha kamar hankalinsa baya jikinsa dai ya fara ƙoƙarin tura hannu cikin gajeren wandon dake jikinsa, rike mata hannu ya yi tare da girgiza mata kai. Ba ta hakura ba ganin kamar baya cikin hayyacinsa ta fara ƙoƙarin tura hannu a cikin wandon nasa hakan ya saka ya hankaɗe ta tare da yi mata gargaɗi. Kuma tun daga ranar bai dake kula ta ba ta yi bi ta nada hakuri bai saurare ta ba. Kallon Alexandra dake kwance ta zuba masa idanu kamar ta cinye shi yake yi, kafin daga bisani ta saki murmushi tare da yi masa alama ya zo gare ta . Juyawa ya yi yana magana. "Ki tashi ki yi wanka mu bar garin nan." "Kana nufin yanzu za mu je garinku?" Kai kawai ya ɗaga mata ba tare da ya yi wata magana ba. Ganin haka ta tashi da sauri don ta ga ko walwala babu a fuskarsa. Ko da ta fito wanka ya har ya shirye ya saka ƙananan kaya. Ba zai ci komai ba don haka ya duba iya abinda Alexandra za ta iya ci. Coffee ya haɗa mata ya bata biscuits yayin da ta gama shirya ta karaso wajen. Sanye take da riga mara hannu iya guiwarta ta tsaya. Direbansa dake hotel ya kira ya sanar da shi ya zo za su tafi. _Fatima Zahrah_ Har lokacin barci take yi hankali kwance . Tana lullube da bargon da Sumayya ta lulluɓa mata lokacin da ta dawo duba ta ne ya lulluɓa mata bargon da rage gudun AC . Kamilu da Hial na zaune a falon bayan sun gama yin breakfast sai ga Hilal ya fito hannunsa rike da janar kayansa da kuma Jakar Alexandra. Cikin fara'a Sumayya ta gaishe shi ya masa mata ba yabo ba fallasa. Fita ya yi direbansa dake wajen mota ya hange shi ya ƙaraso da sauri. karba ya yi ya ki bayan motar. Yana komawa ne Sumayya ta ce. "Ga Zahra na barci har yanzu." Bai ce mata komai ba ya ciro kudi masu yawa a ajiye mata a gabanta ba tare da ya yi magana ba ya nufi ɗakin. Godiya ta yi masa amma bai amsa ba ya shiga ɗakin da Zahra ke ciki. Kallon Jamilu Sumayya ta yi tare da cewa. "Wannan abokin naka halinsa sai shi, ina tausaya wa matar da zai aura." Mumrmushi kawai Jamilu ya yi ba tare da ya y magana. Yana shiga har lokacin tans barci.kallo ɗaya ya yi mata ya san cewa ta ji sauƙin ciwon da yake damunta. Pillow da take kwance ya daka, ta bude idanunsa tare da sauke shi a fuskarsa, shi ma ita yake kallo fuska a tsuke. "Kin san yau za mu tafi tsabar wulakanci ya da kuka kwanta kina barci ko? waye yaronki da zai zauna zaman jiranki?" "Ka yi haƙuri kai na ke ciwo ne shi ya sa na kwanta." Tsuki ya ja sannan ya ce. "Na baki mintuna biyar ki haɗa kayanki ki same ni. Mota." Yana gama fadar haka ya fice zuwa ɗakin da yake. Kiran Alexandra ya yi suka fito tare sallama suka yi wa masu gidan suka fita. Da kallo suka bi su Sumayyaa ce ta iya amsa masu. Ɗakin da Zahra take ta shiga, ta same ta tana hada kaya. Jamilu ya yi sallama suka amsa sai da aka bashi izinin shiga sannan ya shiga. Ganin tana hada kaya ya ce. ",Ai ba ki yi wanka kin shirya ba." Sumayya ta ɗora da cewa. "Ko breakfast ba ta yi ba." Jinjina kai ya yi ya ce. "Ki kwantar da hankali ki yi wanka ki ci abinci." "Mintuna biyar ya bani, kuka yanzu saura mintuna uku ." Ta fada tana saurin tattare komai nata. "Ba in da za ki tafi har sai kin yi wanka kin ci abinci." "Ku yi hakuri idan na ce gida zan yi." "Awa nawa za ku dauka a hanya, ba zai yiwu ba." Ƙwalla ta goge tana cewa "Kada ku damu ba na jin yunwa." Duk yadda suka yi sam ta ƙi ganin haka ya saka Sumayyaa ta yi saurin komawa kitchen. Abinci a flask ta kawo mata da karamin flask na ruwan zafi da bread ta haɗa a basket. Daidai suna fitowa Jamilu na rike da Jakkarta. Suka bita har wajen motar. Direba na gaba Hilal da Alexandra na baya, ta kwanta a ƙirjinsa. Bayan Jamilu ya daka kayanta a bayan motar. Ganin yadda suke manne da juna ya sa ta shiga gaban motar. Ba wanda ya hana ta don sun san gara ta zauna can ya fi mata. Sumayya ta miƙa mata breakfast nata a ta ce. "To idan na tafi da kayan waye zai kawo ki barshi kawai." "Na baki duka har da kayan." Godiya ta yi tare da yi masu sallama suka tafi. Jamilu ko kallon Hilal bai yi ba haka shima. Direba ya ja motar suka bar gidan suka ɗaya wa Zahra hannu. *Daga alƙalamin*✍️ Maman Ihsan ce *Yawan comments yawan typing* [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page2️⃣3️⃣ Direba ya ja motar suka bar gidan suna ɗaga wa Zahra hannu. _Jiddrrh_ Jin motsi kamar an nufo toilet ɗin ya saka ta tsaya jikin bango ta bayan ƙofar yadda ko da an buɗe ƙofar ba za'a ji ta ba. Ko da ya tura ƙofar ta shiga sai ta tsaya tana ta waige-waige, ganin ba kowa abun ya bata mamaki don ko tantama babu ƙarar ƙofar ne ta ji. Ganin ba kowa ya saka ta janyo ƙofar ta fito. Tsayawa ta yi tana ƙarewa ɗakin kallo Sosa ganin ba alamar kowa ne ya saka ta yi ajiyar zuciya. Message ne ta ji ƙarar ya shigo cikin wayarta. Don haka ta duba tare da kiran wata lambar. Bayan an ɗaga daga can Muryar namiji ne ya ce. "Wai meke faruwa ?" "Ina jin kamar akwai matsala, na ga ƙofar nan ta ɗan buɗe. Sannan ina shigowa na ji kamar ƙarar rufe ƙofar toilet. Amma na duba babu kowa." Ki tabbatar kin duba da kyau sosai don idan har asirinmu ya tono tun yanzu ba mu kai ga mallakar dukiyar ba akwai ƙura. Don ba ga shi har yanzu haƙarmu ta gaza cimma ruwa." "Wannan shi ne dalilin da ya saka ya kasance a raye ba mu kashe shi ba. Ga shi baya cikin hayyacinsa. Kafin akai wannan matakin wani irin barazana ne ba'a yi masa ba ga shegen taurin kai kamar na uwarsa." Ta fada tana jan tsuki. Fita ta yi daga ɗakin da alama ranta a ɓace yake. Tana fita Jidderh dake cikin toilet ta fito daga cikin toilet ɗin. Kallonsa ta yi na tsawon mintuna biyu hawaye na bin kumatunta. Ganin yadda kyakkyawan matashin saurayi mai ji da kyau ga Naira yadda rayuwarsa ta kasance a yanzu. Kukan tausayinta kawai yake ji. "In sha Allah sai na bi duk wata hanya da zan bi don ganin na kuɓutar da kai daga waɗan nan azzaluman mutanen. Sai dai hanyar da zan fitar da kai ne zai bani wahala dole na nemi taimakon Yaya Isah. Shi kadai zai iya taimaka Mani don kuɓutar kai ." Goge hawayenta ta yi ta fice da sauri don gudun kada wani yazo ya ganta. _Hilal_ Sun isa Katsina lafiya lau, sai dai bai sanar wa kowa na gidan cewa sun taso yau ba, saboda ya san cewa zasu iya zuwa tarbonsa su saka idanau da zarar sun ji ƙarar mota. Don haka ya ɓoye masu sannan ya saka direba ya bi ta bayan gidan ta can wajan garden ɗin gidan. Don akwai ƙofar da za ta sadaka da part ɗin Hilal. Ita dai Zahra kallon ikon Allah take yi dalilin da ya saka ya sa abi ta baya, madadin gaban gidan. Sai da aka ƙara da daidai wajen ƙofar Sannan ya bawa direba umarnin tsayawa. Bayan ya tsaya durban ya fito da sauri ya bude masa masa. Fitowa ya yi yayin da direban ya bude wa Alexandra. Don ya sant da Hilal tun a U.S. Jakar kayansu ya cewa Direban ya fito masu da shi. Kai tsaye ya nufi ƙofar sai a lokacin Fatima Zahrah ta gane dalilin da ya saka ya bi ta baya. Da alama baya son mutanen gidan su san cewa ya zo da Alexandra. Hakan ya saka ya bi don kada a ga shigarsa da ita . Kuma ya san cewa za ta iya rayuwa cikin part ɗin nasa, saboda babban daflo ne mai ɗauke da ɗakunan uku, kowane ɗaki da toilet ga kitchen da dinning area. Hatta sauran samaarin gidan su Yaa Mansur Yaa Faisal, Yaa Mahmud da Yaa Sadik sai dai su nasu ya banbanta da part ɗin Hial don su Falo ne mai ɗauke da bedroom guda biyu. Kowanensu fa toilet in ga kitchen da dinning area. Hial rike da hannun Alexandra suka shiga part ɗin. Direba ya bisu da kaya. Sai da ya kai kayan ta fito Zahrah duk ba ta sani ba ta yi nisa a zurfin tunanin da ta lula tana mamakin Hilal ɗin. Sai dai direban ya dawo ƙarar rufe motar ya saka ta dawo cinkin tunaninta. Tada motar ya yi ya koma gaban gidan a parking space ya yi parking. Don akwai ɗan tafiya da in da aka sauke Hilal. Kasancewar gidan babban gida ne. Yana tsayewa ta bude ta fito, tana rike da basket ɗin abincin da Sumayya ta bata, don a cikin mota ta ci jin yinwa ta addabe ta, ta fito fuskarta dauke da murmushi. Direban gidan kasancewar suna shiri yana washe baki ya ƙarasi wajen da take yana mata sannu da zuwa. Nuni ta masa da bayan motar daidai lokacin da direban Hilal ya bude don fito mata da Kayanta. Ɗaukar Kayan ya yi yana mata sannu da zuwa. Tare da murnar Allah ya sa albarka aka nasarorin da ta samu. Don ya ji a rediyo. Nan yake sanar mata da su Papa sun dawo da asuba. Tsakken farin ciki ta yi ta nufi cikin gidan. Ba kowa a falon sanyin A.C dake tashi. Ta nufi part ɗin su ta tana ƙealawa Umminta kira. Suna zaune a falo suna kallon T.V in da aka hasko Zahra tana karantu ta ha hanyar amsa duk in da aka ce ta karanta ba tare an yi mata gyara ba, daɓanin sauran an yi masu gyara. Abbi da Ummi sai Yaa Mahmud da Yaa Sadik kowannensu dau farin ciki yake da ganin shalelen nasu a wanan wajen. Jikin Ummu ta fada tana kukan shagwaɓa, dariya suka hau ya suna tsokanar ta. Ɗaya bayan ɗaya ta dinga rungume su tana masu sannan da zuwa. Daga kan Abbi ta fara sai Ummi, sai Yaa Mahmud da Yaa Sadik. Gaisawa suke cikin n so ƙauna. Direban gidan ya yi sallama ya shigo mata da kayan ta. Fita ta yi a guje ta nufi part ɗin Kakanninta tana ƙwala masu kira. "Papa! Papa!" Jin shiru ta fara kiran . "Dada! Dada!" Tana shiga ɗakin ta hango su zaune akan kujerar mai zaman mutum biyu, suna kallon T.V fuskarsu ɗauka da farin ciki sosai. Mummy da Umma da Aunty Laila suna zaune akan kujerar mai zaman mutum uku kowacce fuskarta kamar an aiko mata da saƙon mutuwa. Sai Dady da Abba suna zabe sun zauna akan kujerar mai zaman mutum ɗaya kowa nasa daban . A ƙasa kuma Yaran gidan ne idan aka cire Yaa Mahmud da Yaa Sadik wanda tare da su aka tafi Saudiyya sun bi iyayensu. Yaa Faisal ma yana zaune fuska a murtuƙe yana kallon T.V don ya yi takaicin rashin kashe Zahra da bai samu damar yi ba a lokuta mabanbanta, Yaa Faisal shi ma yana kallon T.V fuskarsa a tsuke. Ƴan matan gidan kuwa musamman Nabeela da Kausar kamar za su haɗiye zuciya su mutu. Yayin da Nadiya ke hararar TV Wanda ma tv bai san tana yi ba, aikin baza kenan sai harara a duhu. Maryan kam ba wanda ya isa ya gaje yanayin da take cikin farin ciki ne ko akasin haka don fuskarta ba yabo ba fallasa. Tana ƙarasa wa ta faɗa tsakiyarsa ta rungume su dukkansu tana dariya. Su ma dariyar suke yi suka rungume ta . Muryarta ta ji wanda hakan ya saka ta mayar da hankali ga TV da suke kallo. Ta sauke Idanunta akan fuskar tv in da ta yi tozali da kyakkyawar fuskarta tana cikin jama'a tana rera karatun Alqur'ani mai girma. Ga ƴan jarida da ƴan gidan rediyo kowa na ɗaukar ta. Ga masu ɗaukar ta da waya,. Ɗauke kanta ta yi ta mayar kan Yayyun Mahaifinta Abba da Dady. Ciki-ciki suka masa mata. Su ma don ganin idanun Papa da Dada ne. Daga nan ta gaida su Mummy da Umma da Aunty Laila. Ba su amsa ba sai da Dada ta yi fada suka ce ba su ji ba ne. Ta haifa samarin da ƴan matan gidan tun da duk sun girme ta ita ce ƙarama a gidan. Dada da Papa suka tamabaye ta Hilal, ta ce ya ce zai shigo. Lokacin da aka fara bata kyautar kujerar Hajji da motoci Dada har taka rawa ta yi Papa na dariya. Maryam ce kawai ta yi mumrmushi sauran baƙin cikinsu ƙaruwa ya yi . Suka kasa zama suka fara wucewa ɗaya bayan ɗaya. Dad ya nufi part ɗin su Mummy ta bishi. Sai Faisal da Maryam. Don Hilal bai shigo ba. Abba na tashi Umma ta bishi sai Mansur da Nadiya ma suka bi su . Aunty Laila tana tashi Nabeela da Kausar suka bita. Taɓe baki Dada ta yi Papa ya ce. "Allah ya nuna mani ranar da burina zai cika." _Mummy_ Mummy sai faman Safa da marwa take yi a falon ta, lokaci-lokaci tana kallon Dady da shi ma ya yi zaune ita yake kallo. Sai Yaa Faisal da Maryam suna zaune akan kujera. Maryam dai ko a jinkinta. Don a ƙasar ranta ma farin ciki yake da wanann nasara da Zahra ta samu. Ta ɓoye ne don gudun kada Mummy ta yi mata duka kamar yadda ta kan mata idan ta ganta tare da Zahrah. "Alhaji ka ga yadda yarinyar nan ta samu ɗaukaka kuwa?" "Na gani mana tun da tare muke." "Alhaji har BBC Hausa fa aka haska yarinyar nan tare da nasarorin da ta samu. A rayuwa ta na tsani na bude idnau na ga yarinyar nan ballantana nasarar da take da shi." "To yanzu ya za'ayi wannan dai ya wuce kuma." Mumrmushi ta yi tare da cewa. "Bai wuce ba don ba'a ma fara yanzu wasan zai soma." Kallon Maryam ta yi tare da cewa ta miko mata wayarta , bayan ta mika mata ta lalubo lamabar Hilal In da ba ta yi seved da My Son, har kiran ta katse bai ɗaga ba. "Ke Maryam je part ɗin yayanku ki kira Mani shi, akan me zai dawo ko shigowa ya kasa. Je ki duba idan bai da lafiya ne mu sani tun da ya yi fita da wannan yarinyar mai kama da aljanu." Har Maryam ta tashi sai kuma ta ce. "Dawo ki zauna bari na je na duba shi da kaina na ji dalilinsa na rashin zuwa in da muke." Tana fita ya nufi upstairs part ɗin sa ta nufa kanta tsaye, fuskar nan a tsuke. *Ku yi hakuri da wannan ba na da caji* [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page2️⃣4️⃣ Tana fita ta nufi upstairs part ɗin sa ta nufa kanta tsaye , fuskar nan a tsuke. _Umma_ Kamar yadda Mummy ta kasa tsaye ta kasa zaune ita ma haka ne a wajenta. Ta kasa zaune ta kasa tsaye. Ƴaƴanta Mansur da Nadiya suna bin ta da kallo Abba ya kalle ta ya ce. "Ki zauna mana Hajiya." "Alhaji Kullum sai Salis da iyalansa ke nasara ta kowace fuska a gidan nan. Tsawon shekaru muna ɗauke da dafin ya fesa mana a zuƙatanmu. Na tsane su wallahi ga shi wannan shegiyar yarinyar mai kama da ƴaƴan aljanu ta sanadiyar ta darajar wannan family ya ɗauke ɗaukaka." Mansur ya kalle ta ya ce "Umma tun da daɗewa da na jima da illata rayuwar yarinyar nan. Amma Abba ya dakatar da ni!" Kallon mamaki ta yi wa Abba ta ce . "Yanzu ɗanka yana ƙoƙarin aikata abin da kai ka kasa aikatawa shi ne za ka dakatar da shi?" Girgiza kansa ya yi tare da cewa. "A dai nemi wata hanyar ban da kisa. Kada a kashe ta ." "Wani tun kada a kashe ta kun taso cikin baƙin ciki da takaicin ubanta, yadda aka ɗauke ku boyi-boyi saboda shi, sannan yanzu ga shi yanzu tarihi yana neman maimaita kansa." "Kamar ya?" "Eh mana, saboda yadda aka fifita ubanta akan kowa haka yanzun ita ma ƴarsa aka fifita ta da sauran ƴaƴanku. Gara ma Hilal shi kadai suke nuna wa soyayyar kusan yadda suke mats." Shiru ya yi don tabbas maganarta gaskiya, amma ba zai iya ɗaukar hakkin ɗaukar rai ba." Duk yadda Mansur da Ummu ke zuga Abba bai yarda da zancen su ba, ya ce su dai nemi wata hanyar. Nadiya kam ita ma tsanar Zahra ce a zuciysryarta, sai dai tana da rauni ba ta goyi bayan shawarar Yaa Mansur ba, sai dai ta ce . "Gakskiya idan akwai hanyar da za'abi don a ruguza rayuwarta ina goyon baya, sai dsi zancen kisan ne ban amince ba." A fusace Mansur ya daka wa Nadiya tsawa ya ce. "Dalla rufe mana baki banza kawai, Allah ne bai bani iko ba, tun tana yarinya nake ƙoƙarin illata ta ban samu dama ba. Na aikata abubuwa da yawa don ciwonta ya tashi, musamman idan ba masu taimaka mata a gidan nan, sai ciwon ya tashi bayan tsawon lokaci na rasa mai taimaka mata amma dai na ji labarin cewa wai suma ce ta yi ta farfaɗo da bayan likita ya bata taimakon gaggawa." Ya karasa maganar cike da takaici. _Aunty Laila_ Kallon Nabeela da Kausar da suka tasa ta gaba suna kuka take yi. Don kowacce ta kasa danne baƙin cikinta. Ta tasa su a gaba bakin ciki ya hana ta yi magana, don ita ma kukan ne ba ta biye masa ba. Don duk wanda zai ji bakin ciki da haushin Zahra da iyayenta to a bayan Aunty Laila yake. Kamar ya hur wuta ta saka su haka take ji. Ga Kausar da Nabeela sun saka ta hana da ta yin tunani mai kyau, saboda kukan su ya dame ta. Rarrashinsu ta kasa yi don haka ta nufi bedroom ɗin ta zuciyarta na mata zafi. Kwance yake a saman makeken gadonsa,ya yi rigimgine da alama ya faɗa duniyar tinani ne. Alexandra da ta gama waya da ƙawarta ce ta nufo gadon da yake kwance singileti ne sai gajeren wando a jikinsa. Wanka ya yi yana so ya shiga cikin gidan, amma ya kwanta sakamakon wani babban al'amari da yake yi ji a jikinsa, don a duk lokacin da wani babban al'amari ke tunkaro rayuwarsa yakan ji a jikinsa. Sai dai wannan karon jikinsa ya yi sanyi. Tun da suka dawo ya ji a jikinsa don ko da Alexandra ta fara romancing ɗinsa ya dai biye mata ne. Amma sam hankalinsa na duniyar tunani. Ganin yadda ya kwanta rigingine ne tare da miƙar da hannunsa yana kallon sama ya sa ta ƙarara tare da yin pillow da damtsen hannunsa. Ta fara magana cikin yaren da suke magana wato yaren ƙasar Spain. "Keke damunka ne haka ba na jin dadi ko zuwan nawa ne ya saka ka cikin damuwa?" Girgiza mata kai kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba "Ka tabbatar?" "Eh na tabbatar." Kissing ɗin sa ta fara yi yayin da shi kuma ya zare bakinsa daga nata. "Ba ki ga yanzu na fito wanka na tsarkake jikina ba, so kike wani wankan ya sake hawa kaina?" Kasancewar ta ba musulma ba ba ta ma san da cewa wani wankan tsarki ba, sai dai ta lura da shi a duk lokacin da suka yi wasanni da shi matukar suka ɗauki lokaci suna wasa da junansu su duk da ba sex yake yi da ita ba amma sai ta ga ya tashi ya yi wanka ko da kuwa fitowarsa kenan wannan abun ya wakana. Sai dai idan iya kissing suka tsaya ne ta ga baya wanka. "To wai me ya saka kowane lokaci sai ka yi wankan." "Haka addini na ya koyar da ni." Ta dake kissing ɗin sa har ya fara mayar mata da martani, ɗan jan yaloluwar rigarta ya yi wanda gane abinda yake nufi ne ya saka ta yi saurin zare rigar daga jinkinta. Ya fara yawo da hannunsa a sassan jinkinta. Akwai wani abu ɗaya da yake damun Alexandra game da shi. Don tun da take da Hilal ko da wasa ba ya taɓa ganin tsiraicinsa ba, sai dai shi ya kalle jinkinta amma ba zai taba bari ta ga jikinsa ba ko a wajen wasannin su ko a wajen wanka. Haka dama shi yake zai yi wasa da mace ta cire komai na ta amma shi ba wata mace da ta ga jikinsa.wssu daga cikin matan da yake mu'amala da su ta yi masa wannan ƙorafin ya ce in dai ba za ta iya harka da shi a haka ba ta hakura, dole haka ta cigaba da zama da shi don Hilal ƙarshe ne wajen iya sarrafa mace da gamsar da ita. Don a haka ma idan ya yi wasa da su suna samun nutsuwa da gamsuwa fiye da idan wasu mazan sun yi sex da su. Wannan dalilin ya sa suka nace akansa don ya yi sex da su ko sau ɗaya ne, don a haka ma sun sami gamsuwa ina ga an ce ƙololuwa. Wata budurwarsa ce ma mai suna Mufy ƴar wani attajiri ne a nan garin London yake zaune da iyalansa. Mufy ta mutu akan soyayyar Hilal, ita ce ta gwada saka masa wata ƙwaya a cikin lemu don ya yi sex da ita, sai dai Allah ya tsallakar da shi daga tarkonta don ko da ya sha maganin bai yi tasirin saka shi fita daga hayyacinsa ba da ya fahimci munufarta ne ya mata maruka biyu tare da yanke mu'amala da ita. Alexandra na da ta lura kamar ya fara fita hayyacinsa sun yi nisa a duniyar da suke ne ta kai hannunta da niyyar turawa cikin wandonsa ne ta ji ya rike mata hannun da ƙarfi yadda za ta ji zafi. Don har sai da ta daki ƴar ƙara. "Sauna nawa zan maki gargaɗi akan haka, ba na ce maku ba na so ba, duk wacce ba ta iya rayuwa da ni a yadda nake so ba to ƙofa a buɗe take za ki iya fita daga rayuwata." Ya ƙarasa magana yana mai matse hannunta wanda sai da ta yi ƴar ƙara. Daidai lokacin da Mummy ta ƙaraso part ɗin, sautin ƙarar Alexandra ce ta saka ta yi turus ƙirjinta na duka. Cikin sanyin jiki ta fara knocking jin ƙafar a datse. Kallon ƙofar ya yi tare da dubawa ta hanyar wata ƙaramar Camera da ya dasa wacce ba wanda ya san da zaman Cameran a gidan. Don idan CCTV Camera ya saka za'a sani ayi kuma taka tsan-tsan. Amma wanda ba wanda ya san da ita. Ta hanayar wayarsa ya duba ganin Mummy tsaye lokacin da ta sake knocking rai a ɓace ya saka ya kalli Alexandra dake kwaɓe fuska na zafin da ta ji ya ce ta mayar da kayan jinkinta. Da sauri ta mayar ya nuna mata wata ƙofa ta cikin wata durowa ya ce ta shiga, kada ta fito sai ya bata izinin. Mahaifiyarsa ce kuma matukar ta ganta akwai matsala. Tashi ya yi tare da ƙoƙarin daidaita kansa ya karasa bakin ƙofar daidai lokacin da Mommy ta sake knocking. Tana budewa ta turo kai ciki tana dube-dube. Kasancewar ya san ba z ta gane in da Alexandra take ba ya saka bai damu ba. "Na ji sautin ihu ne daga ina?" "Ihu kuma Mummy na waye kuma?" "Ai kai zan tambaya." "Okay Film ɗin da nake kallo ne knocking da na ji ya saka na kashe. Idan ba haka ba Mummy ina za ki ji ihu bayan ni kaɗai ne." Har ga Allah ya yarda da zancensa, don haka ta ce. "Ka dawo daga aikin wahalar da kake shi ne ko ka shigo ka ganni ko?" Sosai kai ya yi tare da cewa "Afuwa my Mummy Na gaji ne amma yanzu zan fito. Lafiya na ga kamar ranki a ɓace yake ." "Ba dole ba waccen ƴar banzar yarinyar na neman saka wa jini na ya hau?" "Wace ce Maryam?" "Wata Maryan waccen dai Aljanar yarinyar, me ya saka ma da za ku dawo ba ka ɗebi motar aguje ba ka nufi bishiya da ita sai ka yi tsalle ka fito ita ka barta a ciki ta mutu." Sai a lokacin ya gaje Zahra take nufi don haka ya yi shiru kawai. "Yanzu akan idanunanka ta samu wannan ɗaukar?" "Eh Mummy." "Kai kuma da nake kallonka jarumin da zai biya Mani buƙatata ta hanyar yarinyar na, ashe ma baka da amfani tun da kuma tare kwana biyu ka kasa yi mata komai ko dakatar da cigaban da ta samu." Ta yi maganar tana fita shi dai bin ta da ido kawai ya yi don bai san abinda zai ce mata ba. Yinin ranar Zahra ta yi shi cikin farin ciki da walwala har liyafa iyayenta suka haɗa mata a part ɗin su. Mutane biyu da tafi kusanci da su ta gayyata wayo Amininta da Aminiyarta, sune suka zo har part ɗin aka yi liyafar da su. Da Amini bai saki jiki ba amma da ya ga Yaa Mahmud da Yaa Sadik sun ja shi a jiki ya saki jiki aka yi liyafar cikin jin dad'i da walwala in da suka sha hotuna. Washegari ne Papa da Zahra suka shirya zuwa makarantar su Zahra, don dama an ce ta je da wani babba daga gidan. Yau Abbi ya tafi ƙasar Germany , Yaa Sadik da Yaa Mansur sun tafi wajen aiki. Don haka Papa ya ce su tafi tare. Tare suka tafi in da aka damƙa masu duk wasu abubuwa da Zahra ta samu a wajen gasar. Da kanta ta ce ta bawa shugaban makarantar kujerar Hajji daya cikin wadanda aka bata. Murna kuwa ba'a magana a wajen Mallaman makarantar. Papa ma ya yi farin ciki sosai da jin wannan kyautar da Zahra ta yi. Akan Hanyar dawowarsu Zahrah a ta ce. "Papa zan ba wa Yaa Hilal mota daya saboda ƙoƙarin da ya yi da ni wajen tafiyar nan zuwa gasar." Shiriu ya yi tare da cewa. "Hilal kuma?" "Eh Papa?" "To kina ganin zai karba?" "Zan dai bashi sakamakon abinda ya Mani saboda jin dadi zan bashi kuma na masa godiya." "Allah ya saka ya karba." "Amin." Kasancewar da sauran motocin suka dawo suna biye a bayansu . Bayan sun yi parking suka ba Zahra keys din in da Papa ya masu kyautar kudi. Daga nan suka nufi cikin gidan kai kai tsaye ta nufi upstairs ɓangaren Hilal. Daidai shi kuma yana saukowa gudu-gudu ba ta ankare da ba ta ji ta yi karo da abu kafin ta gama dawowa hayyacinta ta ji ta yi luu za ta faɗi. Kau da kai na na yi cikin tsoron abinda zai faru kafin na juyo na ji ƙarar da Zahra ta saki. *Cikin tsoro da firgici har alƙalamina ya faɗi, ko da na duka na ɗauko alƙamimin sai na ga ashe fanko ne ba komai a cikin alkalamin, ku jira na nemo wani alƙalamin don kawo maku rahoton abin da ya faru* *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page2️⃣5️⃣ Daidai shi kuma yana saukowa gudu-gudu ba ta ankare ba ta ji ta yi karo da abu, kafin ta gama dawowa hayyacinta ta ji ta yi luu za ya faɗi. Cikin zafin nama ya janyo ta ta dawo jikinsa. Jin yadda ya haɗa ta da jikinsa ne ya saka ta tura shi da hannayenta duka biyu. Amma madadin ta ji ya matsa sai ita ce ta sake yin baya za ta faɗi. Sai dai wannan karon bai janyo ta ba illa ƙafarsa ɗaya da ya saka ta bayanta, kafar daidai tsakiyar bayanta ya bata kariya bai yarda ya rike ta ba. Tsoro ne ƙarara ya bayyana akan fuskarta. Sai miƙa hannayenta biyu take yi tana ƙoƙarin riƙo rigarsa ta kasa kuma shi bai riko ta ba, ya zuba mata idanu ne yana kallon yadda tsoro ya bayyana a kan fuskarta . Ƙasa ya yi da ƙafarsa a hankali yayin da ita ma take sake yin baya sakamakon ta jingina ne ka ƙafarsa. Sai da ya tabbatar ta kusa kai wa ƙasa sannan ya cere ƙafarsa ya sake ta wanda hakan ya saka ta faɗi kwance tana mirginowa zuwa downstairs. Salati kawai take yi tana kiran sunan Allah idanunta a rintse. Har ta gangaro zuwa ƙasa bayan ta gama gangarowa daga downstairs ne ta saki wata kara tare da furta kalmar . "Wash bayana." Yana gama saukowa ya wuce ta kwance a ƙasa, a hankali ya juyo ya kalle ta tana yamutse fuska alamar ta ji zafi . "Uban me ya kai ki part ɗina?" Dakyar ta iya cewa. "Cikin kyautar motocin da na samu ne zan ce ka ɗauki ɗaya a ciki." Wani banzan kallo ya yi mata tare da cewa. "Da gaske?" Kai kawai ta gyaɗa masa . "Ke har kin yi arzikin da za ki bani mota, to na fi ƙarfin motocinki." "Na sani Ya Hilal, ba wai za ka duba wannan ba manufar dake cikin kyautar za ka du..." Kafin ta karasa zancenta har ya bar wajen ya nufi part ɗin su Papa. Duk yadda ta so tashi kasawa ta yi don bayanta ji take ya rike. Rintse idanu ta yi hawaye na bin gefen fuskarta. Tana cikin wannan yanayin ne sai Allah ya jeho Yaa Mahmud, ganinta ya sa ya karasa wajen yana tamabayar ta . "Subhanahi Zahra me ya faru da ke?" "Faɗowa na yi." Ɗaukar ta ya yi cak ya nufi part ɗin Umminsu da ita. Tana zaune a falo hannunta rike da littafin addini tana karantawa. "Lafiya me ya same ta?" Ta tambaya tana ajiye littafin kan Centre table dake gabanta. "Faɗowa ta yi daga upstair, a gasa mata jiki idan ya kama na asibiti ne sai ki kira ni." Daga nan ya nufi ɗakinta da ita a hannu, har cikin bathroom ya kai ta sannan ya fito. Ummi ce ta shiga don taimaka mata. Ita ta cire mata kaya ta gasa mata jiki da ruwa ɗumi. Sai da ta tabbatar ta gasa mata jiki musamman bayanta sannan ta bar ta ta ce ta yi wanka. Wanka ta yi ta fito ɗaure da towel. Sai dai ta ji dadin jinkinta sosai, Man zafi Ummi ta bata ta shafa a jinkinta kuma ta ji daɗin ruwan ɗumin. Magani ta bata ta sha sannan ta kwanta. Ba jimawa barci ya ɗauke ta. Ganin ta yi barci Ummi ta fita ta bar mata ɗakin. _Hilal_ Ko da ya nufi sahsen kakannin nasa sallama ya yi wanda shi kaɗai ya ji kayansa. Papa na waya yayin da kuma Dada ta ke yanka fruits a faranti. Kamar yadda ba su ji sallamarsa ba haka ba su san ya shigo ba. Ganinsa kawai Dada ta yi zaune bayan ta gama yankan fruits ɗin. Papa ko har lokacin bai san da zuwansa ba duk da yana waya idanunsa na kan T.V. Kallonsa Dada ta yi tare da cewa. "Kai yaushe ka shigo nan ne, mutum sai ka ce aljani. Ba wanda ya ga shigowar ka sai ganinka." Papa ya kalli gefen da Hilal yake zaune cikin soyayyar jikan nasa wanda yake jin son sa daban ne idan aka cire Zahrah cikin jikokin nasa ya ce. "Jarumin soja yaushe ka shigo, ina ta zuba idanu na ganka shiru, kadan ya rage ban bika ba har ɗakinka ba." "Barka da rana Papa." Ya faɗa kamar baya son magana. Cikin farin ciki ya amsa da . "Barka dai jarumina ya kake?" "Alhamdulillah" Ya faɗa a takaice. Sannan ya mai da dubansa ga Dada ya ce. "Ina wuni.?" Ita ma ta amsa masa cikin sakin fuska tana tsokanarta irin na kaka da jika. Shi dai bai tanka mata ba ya tashi ya bar wajen. Don idan ya yi gaisuwa ya gama kenan ba fira. Har ya kai ba bakin kofar ya murda handle ɗin kofar zai fita ya ji Papa na cewa. "Zahrah ta kawo maka makullin mota wai za ta baka ." "Ba na buƙata." "Ai ta sani kuma na san duk motocinka sun fi wacce za ta baka, amma kada ka ƙi karba ba'a mayar da hannun kyauta baya. Ta duba kirkin da ka ji mata ne na zuwa har Kaduna ka ajiye komai na ka ka tafi can saboda ita." "Ban tafi saboda ita ba, don da ace don ita ne ba zan tafi ba." ",Daga nan ya fice. Kallon juna Dada da Papa suka yi kafin Papa ya girgiza kai tare da cewa "Allah ya shirya ." Daga haka ya tafi zuwa part ɗin iyayensa, suka gaisa bayan haka ƙannensa Faisal da Maryam suka gaishe shi , ganin za su dame shi da surutu ya tashi ya bar falon Part ɗin Abba ya nufa nan ma ya same su duka , ya gaida Abba da Umma yayin ga Mansur da Nadiya suka gaishe shi. Bayan ya bar part ɗin ne ya nufi part ɗin Aunty Laila. Nabeela da Kausar kamar za su cinye shi. Ganin yadda suke kallonsa ne ya saka shi tsuke fuska. "Barka da warhaka Aunty." Cikin jin dadi ta ce. "Barka dai Son ka dawo?" "Eh" Ya amsa a takaice. Nabeela ta fara gaishe shi ya ce "Ina wuni Yaa Hilal?" "Lafiya lau." Ya amsa ya yin da Kausar ke ƙoƙarin gaishe shi ta ce. "Ya Hilal ina wuni ka dawo?" "Eh na dawo." "Alhamdulillah na ji dadi da ka dawo laflya." Bai ce komai ba sai tashi da ya yi ya ce. "Aunty zan tafi." "Ka zauna mu yi fira mana." "Aunty na gaji zan kwanta ne." Daga haka ya wuce, don yana son yin barci dan ya koma part ɗin sa Alexandra za ta dame shi. Don haka ya yi kwanciyar sa a babban falon gida, kasancewar ba kowa a falon." Bayan kamar awa ɗaya da kwanciyarsa sai ya ding jin hayaniyar ƴa matan gidan, sai dariya sha da shewa. A fusace ya tashi tare da daka masu wata irin tsawa wanda ya saka hanyar cikinsu kaɗawa. Nadiya da Maryam har z su gudu suka ji muryarsa yana cewa. "Kada wacce ta gudu, duk kuwa wacce ta gudu sai na yi mata ninkin wanda zan yi wa Sa'id." Sanin waye shi da abin da zai iya aikatawa in dai ya furta ya saka suka dawo. Belt ɗin wandonsa ya zare da ta kan Maryan ya fara, dukanta kawai yake yi, dai d ya tabbatar ta ji laushi kafin ya janyo Nadeey. Ita ma ya fara dukanta sosai kamar Allah ne ya aiko shi. Ganin Haka ya saka Nabeela gudu wa . Tsalle ɗaya ya yi ya isa gabanta. Finciko ta, ganin haka Kausar ta kara tsorata. A guje ta nufi ɗakin Mahaifiyarta. Sunyi Laila da ke kwance ta mike da sauri tana tamabayar Kausar abin da ya firgita. Nuni take yi da ƙofa ganin haka ya saka Aunty Laila rufe ƙofa ta murza key. Sai da ya gama dukan Maryam, Nadeeya, da Nabeela sannan ya lura da Kusar ba ta nan. Kuma duk dukan nan ba wanda ya ji ballantana ya fito cetonsu. Don ya hana su kuka wai baya don hayaniya. Kausar kuwa tana can wajen Aunty Laila tana rarrashinta duk da ba dukan nata ya yi ba. Ƙarin guiwa take bata akan ta daina wanann kukan tun da ta zo wajen ta ai ta tsira bai isa ya ce zai dakar mata 'ya a gabanta ba. "Wai me kuka yi masa?" "Wallahi ba abinda muka masa.' Girgiza kai ta yi tare da cewa. "Ƙarya ne haka kawai ba yadda zai iya cewa zai dake ku, sai dai da dalili." "Eh to yana barci a Falo mu kuma muna ta fira shi ne ya farka ya zare bellet daga wandonsa ya fara ta kan ƙanwarsa Maryam, daga ita dai Nadeeya yana zuwa kan Nabeela shi ne na gudu." "Kuma ai kun san halinsa baya son hayaniya da kuka kan shi kwance a wajen ai da sai ki tafi. Wani Wajan." "Mun ɗauka ba zai..." Dukan kofar da ake yi ne ya saka Kusar ƙankame Aunty Laila. "Ki fito kafin na ɓalle ƙofar nan na zo na same ki ." Rai a ɓace Aunty Laila ta ce . "Halal ka fita i idona ko mutuwa na kunyar idon mahaifi a ɗakina za ka zo ka ce zaka ɓalla?" "To idan ba haka kike so ba ki miƙo Mani yarinyar nan" "Wace yarinyar? Yarinyar da za'a aura makan ne za ka daka, so kake ta tsotsa da kai ta ce ta fasa?" Tsuki ya yi cikin takaici ya ce. "Kausar wallahi idan ba ki kawo mun kanki ba har kika bari na ɓalle ƙofar nan dukan ki sai ya ninka na su." "Ƙofar za ka ɓalle mun saboda ba ka ..." Kafin ta ƙarasa zancen nata ne ta ji wani ƙara take Kum ƙofar ta faɗi ƙasa, sakamakon duka ɗaya da ya yi wa ƙofar Bature sai ga ga ƙasa. Haka ya nufi Kausar da na ta ƙara tsorata don dama akwai ta da taron duka. Ƙanƙame Aunty Laila ta yi tana cewa . "Mum ki taimake ni." Yana zuwa ya finciko ta tare da hankaɗa ta ƙasa ya hau dukanta da belt ɗin hannunsa. Duk yadda Sunyi Laila ta yi kokarin ƙwatar ta amma ina ta kasa. Don wajen ƙwatar ta har ita ma ta samu rabonta ba shiri ta yi gefe tana duba hannunta da ya daka. Sai da ya tabbatar ya mata lilis sannan ya bar ɗakin yana huci. _Fatima Zahrah_ Bayan ta tashi daga barci ne sai ta ji dadin jinkinta sosai. Tashi ta yi ta nufi bathroom ta yi wanka da wani ruwan ɗumin. Sannan ta ɗauro alwala ta zo ya gabatar da sallah. Bayan ta yi addu'a ta fito ta samu kowa nata a falon. Abbi, Umma, Yaa Mahmud da Yaa Sadik. Yayyun nata ta bawa keys din motar, Mahmud ya ce. "Ta ya ya za ki bamu ai kece aka ba." "Yaya wallahi ba na so ɗaya ta ishe ni" Ba yadda suka iya dole suka karba suna mata godiya. Dubanta ta mayar kan Abbi ta ce. "Abbi sauran kujerar Hajji ka bawa wandanda ka ga sun dace, musamman masu bukata da ka san ba su taba zuwa ba sai ka basu, don ka ga mu kam Alhamdulillah Allah ya hore ana zuwa duk shekara." Sanya mata albarka kawai suke yi tare da yaba kyawun zuviyarta, don duniya ba ta dame ta ba. Washegari tun a school take jin Mararta na mata ciwo, dakyar ta iya fitowa daga lecture ko Amini da A'isha yau ba ta tsaya sun yi sallama ba ta nufi motarta. Gudu take yi wajen yin driving ɗin sauri take ta ganta a gida. Ikon Allah ne kawai ya kawo ta gida lafiya. Tana parking ta fito ko wayarta da jaka ba ta tsaya ɗauka ba ta fice daga motar. Tana shiga falon sai ta zube kan dogon kujerar ta kasa ƙarasa wa . Dama haka take fama a duk lokacin da za ta yi period, shi ya sa Ummi ke hana ta yawan shan zaƙi da take yi. Haka ta dinga murƙususu na azaba ga shi ta kasa, ga shi ta bar wayarta a mota. Tana cikin wannan yanayi sai ga Aunty Laila ta shigo ita da Mummy. Da alama daga unguwa suke. Kasancewar tana zubar da jini sosai ya saka Kayanta ya ɓaci don haka juyawa da ta yi kuma Abaya ruwan madara ta saka wanda jinin ya nuna a rigar sosai. Dama tana shan wahala sosai idan za ta yi baƙon wata. Daidai lokacin nan Hilal ya shigo falon, ganin yadda Zahra take ya saka ya kalli su Mummy da sauri ya ce. "Lafiya kuwa?" Buɗar bakin Aunty Laila ta ce "Ciki ta zubar shi ne ta zo ta kwanta wa mutane a nan." Da mamaki ya kalle ta tare da cewa. "Ciki kuma?" ", Kwarai kuwa ai wannan kana ganinta ne kawai baka san mugun abu da take aikatawa ba." "Waye ya faɗa maku ciki ne?" Mummy ta kalle shi a fusace ta ce "Ina ruwanka ne wai ma da kake tamabayar mutane, wannan jinin ya wuce jinin haila kam." Kallon mahaifiyar ta sa ya yi tare da kallon Aunty Laila daidai lokacin da Zahra ta saki jiki ta mirgino za ta faɗo ƙasa. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page2️⃣6️⃣ Kallon mahaifiyar ta sa ya yi tare da kallon Aunty Laila daidai Lokacin da Zahra ta saki jiki da ta faɗin. Cikin zafin nama ya nufi wajan da take kwance da niyyar ta tare ta kafin ta faɗo ƙasa. Tsawar da mahaifiyarsa ta daka masa bai saka ya fasa abinda yake yi ba. Tare ta ya yi ta fado akan hannunsa. Cikin fusata Mummy ta daka masa tsawa ta ce. "Hilal ba da kai nake magana ba ko?" "Ku yi hakuri Mummy kin ga yanayin da take ciki ga shi iyayen nata sun fita zuwa ta'aziyyar abokin Papa, Yayyun ma basa gidan idan wani abu ya faru da Ita ku da kuke gidan za'a tuhuma." A fusace Aunty Laila ta ce. "Uban waye zai tuhume mu ko akwai wanda ya sa ta yin cikin shege be ballantana ta zubar?" "Kuna da Hujja kan hakan?" Ba wacce ya bashi amsa, ɗaukar ta ya yi ya nufi kofar fita, Mummy za ta dakatar da shi Aunty Laila ta mata alama ta bar shi. Ta yi murmushi mai cike da ma'anoni. Yana fita harabar gidan sojojinsa suka taso alama ya masu da su koma, haka ya saka suka koma ya nufi daya daga cikin motocinsa. Direbansa ya bashi key ɗin motar ya karba sannan ya yi wa motar key a guje ya bar gidan. Asibiti ya kai ta in da ya yi parking ya fito ta ɗauke ta zuwa ciki. Aka karbe su cikin gaggawa kasancewar an san su a asibitin. Doctor ne tare da nurses suka rufa akan ta don zuwa lokacin a sume take. Jini ne ya ɓata masa amma bai damu da hakan ba. Yana nan zaune sai ga Dyoctor Ahmad ya fito ya ce masa ya biyo shi a office ɗin sa. Tashi ya yi ya bishi bayan sun gaisa yake cewa. "Amma na yi matukar mamaki da abin da idona ya gane Mani." Kallonsa Hilal ya yi ba tare da ya ce komai ba. Doctor Ahmad ya cigaba da cewa. "Maganin zubewar cikin da ta sha ne ya saka ta a cikin wanann halin." Wani kallo Hilal ya masa wanda har sai da Doctor ɗin ya tsorata. Don shi bai yarda ba. "Ka tabbatar da abun da ka faɗa?" "Ƙwarai kuwa ba abinda zai saka na fadi abin da ba haka ba, yaushe Zahra ta yi aure ne ban sani ba, kuma ban jima da zuwa gidan ba. Kai ne mijinta?" Banza ya yi masa zuciyarsa kawai yake jin yana masa zafi. Kai tsaye ya shiga ɗakin da aka kwantar da ita ya samu tana barci an saka mata ƙarin ruwa. Kallonta yake yake yi cike da ƙarin tsanarta a cikin zuciyarsa. Haka ya nufi motarsa ya nufi gida Tsuki yake ja lokaci zuwa lokaci . "To wai ma meye na wa na damuwa akan abun da ta aikata?" Wata zuciyar kuma ta ce masa, 'Ai dole ka damu don ko kana so ko ba ka so ita ɗin jininka ce, kuma idan ta zubar da mutuncinta tamkar ta zubar da Mutuncin ahalinku ne.' Yana shiga falon ya samu Mummy da Umma sai Aunty Laila suna zaune a Babban falon gidan a kan kujera. Suna jin karar ƙofar suka juya suna tambayarsa meke damunta. Yanayin ɓacin rai da yake ciki ne ba zai iya magana da kowa ba, don haka bai ce masu komai ba ya haura sama. Ko da ya shiga falon Alexandra ne zaune a falon. Don sai da ya saka key ya bude saboda baya son a san da zamanta ya saka yake rufe part ɗin da key. Tana ganin ya dawo rigarsa da jini ya tashi take tamabayarsa cikin tashin hankali. Ce mata ya yi ba komai mai ciwo ne ya ɗauka zuwa asibiti. Bedroom ya wuce har ya shiga ya dawo ya rufe kofar da key don gudun kada wata ta shigo ta ga Alexandra. Bayan awanni biyu Abbi da Ummi suka shigo falon bakinsu ɗauke da sallama. Daga Umma har Mummy da Aunty Laila ba wacce ta amsa. "Ummi ta ce barkanku da gida Ina wuninku?" Aunty Laila ce ta yi tsuki sauran ko ba su ma kalle ta ba ballantana su amsa. Don dama sun san ba amsawa za su yi ba Amma kullum sai sun yi masu sallama sun gaishe su duk da sanin ba amsa wa suke ba. Har yanzu Handbag ɗin Zahra na tsakiyar falon sai dai sun kira mai aikin ta goge hanci jinin. Ganin Handbag ɗin Zahra Ummi ta dauka ta shiga da shi tana cewa. "Zahra kenan ta ajiye jaka ta shige ciki ko?" "Abbi ne yake cewa. "Ta gaji ne shi ya sa ta ajiye anan." "Haba wani gajiya sai ka ce Jakar nauyi ne da ita?" Haka suke tafiya suna magana har suka karasa part ɗin su. Bedroom ɗin Zahra suka fara zuwa amma ba ta ciki. Ummi ta karasa jikin kofar bathrobe ta ji ba motsi, knocking ta yi shiru. Hakan ya saka tura ƙofar ba ta ciki. Abbi ya ce. "Ina ta shiga kuma mai baro Dada da Papa wajen ta'aziyya ballantana ace tana can." Kiran wayarta Abbi ya yi suka ji wayar a handbag ɗin ta. Mamaki suke ina ta shiga don ba ta fita sai ta nemi izinin iyayen ta. _Hilal_ Koda ya koma asibitn ya samu har ruwan da aka ƙara mata sun ƙare, Tana zaune ita kadai a ɗakin, tagaumi ta yi tana tunani waye ke tare da ita a nan. Ƙamshin turarensa da ta ji ne ya haifar mata da faɗuwar gaba. A hankali ta da ɗaga kai tana kallon ƙofar. Sakin kofar ya yi ya shiga fuskarsa a murtuƙe, ita kanta ta tsorata da ganin yanayinsa. "Ba za ki daina kallona ba da wannan shegun idnaun naki kamar na mujiya ba?" Da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa. Munafuka kawai Musa a baki Fir'auna a zuci ana maki kallon mutumiyar ƙwarai ashe ba haka ba kura ce ke lulluɓe da fatar akuya." "Ya Hilal me na..." Katse ta ya yi cewa. "Tun yaushe kika fara wannan harkar a ƙarancin shekarunki?" Kallon rashin fahimta ta yi masa ta ce. "Harka?" "Tambayarki nake yi waye abokin fasiƙancin na ki?" Shiru ta yi yayin da ƙwalla ke kwaranya a idnaunta. Ba ta yi aune ba ta gan shi a gabanta sai huci take. Shaƙo wuyanta ya yi ta fara zaro idanu tana kakari. "Na ce waye ya yi maki cik?" _Jidderh_ Ko da ta koma gida yau sam ta ƙi cin abinci kuma ta ƙi magana da kowa. Da Inna ta tamabaye ta sai ta ce mata ba komai. Tana cikin wannan yanayin ne sai ga Yaya isah ya dawo gidan. Kallo ɗaya ta mata ya gane tana cikin damuwa. Ƙarasa wa ya yi wajen yana cewa. "Subhanallah Autar Inna lafiya?" Kuka ne ya kufce mata ta ce. "Yaya tausayinsa nake ji." "Waye kike jin tausayinsa?" "Yaya wa ka sani bayan Asadullah da kullum nake maka zancensa." "Allah ya kawo masa ɗauki?" "Yaya ka taimake ni mu fitar da shi daga wannan halin da yake ciki." Kallon baki da hankali ya yi mata kafin ya ce. "Kin san me kike fada kuwa?" "Na sani Yaya." "Babban mutum ne fa ta Yaya kike tinanin fitar da shi, kada ki je ki saka rayuwarki a hatsari da." Mumrmushin takaici ta yi tare da cewa. "Matarka da ɗan ka suna raye a yau ne saboda Sir Asadullah, ko ka mance a halin da muka kai ta asibiti za'ayi mata aiki ba ka da kuɗi, na yi yawo ban samu ba, ka yi buga-buga ba ka samu ba na bika kasuwa ba ja da shi, ka nemi taimakon ubannin gidanka ba su taimake ka ba, sai da ja je kamfanin Asadullah ya taimaka mana da kuɗi wanda lokacin matarka tana gaɓar rayuwa da mutuwa . Don Allah ka taimaka masa ko don taimakawa da ya yi wa iayakinka duk d bai san waye ba " Ajiyar zuciya Isah ya sauke tare da cewa. "Kin saka jikina yin sanyi. Bari na shiga na fito sai mu san yadda zaj ɓullo wa lamarin." Murmushi ta yi tare da jinjina masa kai. *Waye Sir Asadullah?* Asadullah Ahmad Abubakar shine cikakken sunansa. Asalinsu mutanen jihar Yola ne a garin Adamawa, Asalinsu Fulani ne, makiyaya. Ahmad wato Mahaifin Asadullahi Ya taso shi kaɗai ne a wajen mahaifinsa Abubakar. Abubakar yana da ƙani mai suna Sale Ko da ya taso bai san Mahaifiyarsa ba. Don ta rasu yana da shekaru biyar a duniya. Sale lokacin da matar Yayarsa ta rasu bai yi aure ba saurayi ne shi. Mahaifinsa ke kula da shi su biyu ne suke rayuwa a cikin wannan gidan. Sai dai ƙanin mahaifinsa wato Sale shi yake masa komai na larura da ya shafi kuɗi. Saboda yana da rufin asiri da ƙoƙarin neman na kai. Ganin Yayan nasa ya daina fita ko ina saboda ɗawainiyar yaro ne ya saka yake masu komai na ci da sha har da sutura. Kullun idan Zai dawo sai ya siya masa ƙosai da biredi. Ana cikin wannan lokacin ne Saleh y yi aure, in da ya auro matarsa ƙyakyatawar Bafulatana mai suna Joɗa nan gidansa dake jikin gidan Yayansa ya ajiye ta . Shawara ya yanke tun da shi ya yi aure ga Yayansa tin mutuwar matarsa ya kasa ƙara aure. A wata ranar Juma'a ne y shiga gidan Yayansa bakinsa ɗauke da sallama. Hannunsa ɗauke da bakin leda. "Assalamu alaikum" Mallam Abubakar ya amsa yana sakin murmushi ya ce. "Saleh har ka dawo?" "Eh na dawo." Ya karaso ciki yana mikawa Ahmad ledar biredi da tsire da ya siyo masa . Karba ya yi cike da murna yana nuna wa mahaifinsa. Bayan sun gaisa ne Abubakar ke tamabaye shi kasuwa. Ya amsa masa da Alhamdulillah. Shiru ne ya biyo baya kafin Sale ya yi magana ya ce. "Yaya na ce me zai hana ka kawo Ahmad Gidana ya zauna, tun da ka gajara ƙara aure." Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "Ban hana ka ɗaukar Ahmad ba sobida kai ma uba ne a wajensa kamar yadda nake uba. Abu ɗaya ya yi mu da ni da kai uwa ɗaya uba ɗaya, to akan ne zan maka iko da shi. Cikin farin ciki duk suka yi sallama tare da cewa Gobe zai ya ɗauke shi. Washegari kuwa bayan ya sanar wa da Matarsa Joɗa ta yi farin ciki, don tana son Ahmad sosai. Da safe kafin ya fita ya shiga gidan Yayansa ya dauko Ahmad da Kayansa. Kafin ya yi tafiyarsa don yana zuwa Lagos kai shanu ne. Joɗa tana matukar don Ahmad sosai ba wanda zai ce ba ita ta haife shi ba. Duk da ba kowa yake kai yara ba Koda Joɗa ta sanar wa mijinta shawarar kai Ahmad makarantar boko. Bai yanke hukunci ba sai da ya sanarwa Mahaifin Ahmad, ya nuna duk masa duk hukuncin da ya yanke ka akan Ahmad daidai ne domin ɗan sa ne shi ma . *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page2️⃣7️⃣ Ko da Koda ta sanar wa mijinta shawarar kai kai Ahmad makarantar boko, bai yanke hukunci ba sai da ya sanarwa Mahaifin Ahmad, ya nuna masa duk hukuncin da ya yanke akan Ahmad daidai ne, domin ɗansa ne shi ma. Haka aka kammala masa komai ya fara karatu. Komai Sale ne ke yi masa. Don dama ya fi mahaifin Ahmad rufin asiri. A daidai wannan lokacin Joɗa ta fara laulayin ciki. Kuma cikin na wahalar da ita. Abubuwa suka yi wa Sale yawa, ya ɗan dakatar da wasu tafiye-tafiye da zai yi. Abubakar ne ya tashi da zazzaɓi mai zafi sosai hankalin Sale ya tashi sosai. Ya ɗauke shi zuwa asibiti. Shi ya dinga jinyarsa. Ahmad ya dinga kuka don ya yi wayau ya san abun da ke faruwa. Kwanansu biyu a asibiti Allah ya yi masa cikawa. Sale ya sha kuka Sosa don har sai da ya suma, Kasancewa Abubakar kadai ne ɗan uwansa Wanda ya rage masa. Ahmad ma ya sha kuka sosai da sosai don ya san mutuwa ya san mahaifinsa ya tafi kenan, ba uwa ba uba. Joɗa kuwa Ita ma sai da ta yi rashin lafiya don dama ga laulayin ciki da take yi. Bayan kwana arba'in suna zaune a tsakar gidan kan tabarma, Sale na shan fura da Joɗa ta dama masa. Ahmad ya yi sallama ya dawo daga makaranta. Gaishe su ya yi Joɗa ta masa alama da yazo gare ta. A hankali ya taka bayan ya cire Sandals din makarantarsa, kwantar da shi ta yi saman cinyar ta tana shafa kansa. Ganin kamar yana cikin damuwa ta ce. "Me yake damunka?" "Yanzu ni ma na zama Maraya ban da mama da Ba..." Hannu ta sa ta toshe masa baki ta ce. "Ka da ka sake kiran kanka maraya, domin kai ba Maraya ba ne tun da kana da mu ni ce mahaifiyarka ga kuma mahaifinka." Ta ƙarasa maganar tana nuna Sale dake kallonsu yana murmushi. Sannan ta ɗora da cewa. "Nan da watanni kadan zan haifa maka ƙani ko ƙanwa." Murmushi ya yi har sai da ƙananan haƙoransa suka bayyana. *Bayan watanni Bakwai* Wata ranar Litinin Joɗa ta tashi da naƙuda, wata maƙociyarsu ce Saleh ya kira. Dattijuwa ce da taimakon Allah da taimakon ta Joɗa ta haihu. Ta haifi ƴa mace fara kyakkyawar gaske, son kowa ƙin wanda ya rasa. Ranar suna aka saka wa yarinya suna Na'ima, murna da farin ciki a wajan su ba'a magana. Ahmad ya na matukar kaunar ƙanwar ta sa sosai. Ko kukanta ya ji ya yi yawa shi ma zai yi kamar zai yi kuka. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har aka yaye Na'ima. Shakuwa mai karfi ce ta shiga tsakanin Ahmad da Na'ima. Kullum yana ɗauke da ita inda sun rabu sai dai idan makaranta ce zai tafi, nan ma har kuka take yi za ta je. Idan ya tafi ya barta daƙyar take yin shiru sai Joɗa da Sale sun sha aikin rarrashi. Lokacin da ta cika shekaru uku aka saka ta makaranta ita ma, lokacin Ahmad na ajin karshe a primary school. Tare suke zuwa kamu na su gwanin sha'awa ba wanda zai ce ba su ne suka haifi Ahmad ba. Ɗan ƙaramin gidan da Mahaifin Ahmad ya rasu a ciki shi ne kawai mallakinsa, don dama shi ba mai shi ba ne, hakan ya saka Sale yake taimaka masa, har yakarbi Ahmad ya saka shi a makaranta. Zuwa lokacin kuwa dukiyar Sale sai bunƙasa take yi. Don shanu ne da shi sosai, ga filayen da ya siya ya ajiye a matsayin ƙadarori. Don ya tashi a gidan da yake ya siye babban gida ya koma, ga ɓangaren kiwo ta bayan gidan, sai dai akwai ƙofa daga cikin gidan da za ta sada ka da filin da ake kiwon. *Bayan shekaru goma sha biyar* Wata ƙyakyatawar yarinya ce tsaye a bakin titin a gaban wani makaranta, kallo ɗaya za ka yi wa makarnata ka san cewa makaranta ce ta ƴaƴan masu hannu da shuni. Sanye take da uniform ɗin makarantar riga da wando sai ƙaramin hijabi iya wuyanta. Wata lokaci-lokaci take kallon agogon hannunta yana ware Idanunta tare da tura baki gaba. Wata baƙar mota ce ta tsaya a gabanta tura baki ta yi tana kau da kai . Murmushi ya yi tare da cewa. "Tuba nake." Shiga ta yi tare da buga marfin motar da ƙarfi. "Ai sai ki ɓalla Mani marfin motar." "Wallahi Yaya Ahmad ka ɓata Mani lokaci ga shi na gaji." "Sorry ƙanwata ka da ki damu tun da yazu kin kammala zana waec da neco ai sintirin nan ya ƙare ko?" Banza ya masa kamar ba ta ji me yake cewa ba, don haka ya ce "Amaryar duk gajiyar ne?" "Wallahi na gaji ni kam Yaya kana damuna." "Kin ga ni kam ina cikin farin ciki, don daga yau ki fada ƙirga kwanakin aurenmu." Jin ta yi shiru ne ya saka shi cewa. "Na'ima." "Yaya." Ita ma ta kira shi. A hankali ta bude Idanunta ta sauke akansa . "Ina son fa na ci gaba da karatuna kafin na yi aure sai na shiga University." Dariya ya yi tare da cewa. "Ai kin san cewa ba za'a bari ba ko?" "To bayan mun yi aure za ka bar ni ko?" "Ban sani ba amma sai yadda ta kasance." A wani katafaren gida motarsa ta tsaya, horn suka danna aka buɗe masu gate. Shiga suka yi ya yi parking din motar, kusan a tare suka fito daga cikin motar. Hajiya Joɗa na zaune a kan kujera mai zaman mutum uku. Na'ima na shiga ta yi kira da jakarta ta karasa ta kwanta jikin Joɗa. "Wash na gaji." Ahmad ya gaida Joɗa ya shiga ɗakinsa. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har aka tsaida ranar auren Ahmad da Na'ima. Don saura sati biyu bikin ya rage, Ahmad yana koyarwa a wata makarantar secondry ta Gwamnati ce. Saleh wanda suke kira da Bappa ya siya wa Ahmad gidan da za su zauna. Joɗa wacce suke kira da Inna ta yi wa ƴarta kayan kitchen na gani na faɗa. Wata ranar Asabar ne aka daura auren Ahmad da Na'ima. In da suka tare da gilashi gidan da Bappa ya siya masa. Kuma an zuba masu komai a cikin gidan. Duk aikin Bappa ne ya yi wa Ɗan Yayansa. Kasancewar zuwa lokacin Bappa ya daina kiwo sai dai ya siye kadarori ya tara. Sannan kuma akwai manyan shagunansa da suke kasuwa ana siyar da kayayyaki a ciki. Zaman lafiya da kwanciyar hankali suke yi a cikin rayuwar aurensu. Tana samun kulawa sosai a wajen mijinta. Auren ba jimawa Allah ya nufe Na'ima da samun ciki. Sun yi farin ciki sosai da wannan kyautar da Allah ya basu. Bayan watanni tara ta haifi ɗa namiji santalele kyakkyawan gaske mai kama da mahaifiyarsa. Fari tas kamar yaron larabawa. Murna a wajen Bappa da Inna ba'a magana, sun samu jika, dama tun bayan haihuwar Na'ima Allah bai sake bata haihuwa ba. Gida aka dawo da ita tana samun gata da kulawa wajen iyayenta. Ranar suna aka sakawa yaro suna ASADULLAH. Ranar da suna cika sati biyu ne Bappa ya mallaka wa jikansa wato Asadullah manya-manyan kadarorinsa. Don sai da ya tara su Joɗa Ahmad da Na'ima. Sannan ya mallaka wa Asadullah takardun a ta hannun Na'ima. Takardar farko ta plaza ce da ya siya, ta biyu kuka na wani kamfani ne dake garin Kano. Takarda ta gaba kuma ta wani kamfanin ne dake garin Lagos. Ya mallaka masa su akan cewa da zaran ya kai shekaru ashirin da biyar za'a mallaka masa a hannunsa. Farin ciki mamaki ne duk suka mamaye Na'ima da Ahmad. Sai da ya ce Ahmad ya dakatar da koyarwa da yake yi ya koma ya fara juya kadarorin da aka mallaka wa jikansa kafin ya girma a mallaka masa. Haka suka cigaba da zama a gidan ana kula da ita da kuma yaronta Ahmad ma ya dawo gidan ya tare wai tare suka san a su zauna shi ma Wata rana an dukkansu suka shirya ɗin zuwa kasuwa. Bappa, Joɗa, Ahmad da Na'ima. Bayan sun gama siyayya Joɗa na rungume da jikanta Asadullahi dake cikib towel Bappa na gaba suka ji wata murya daga bayansu ta kira sunan Bappa . "Sale!" Dukkansu suka juya har da Na'ima da Ahmad suna kallon wannan mai kiran sunan. Baki duka saki da tsanin mamaki wanda har sai da firgici ya bayyana akan fuskarsu. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LrTZNGwF35IKXX4sLRvFug *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page2️⃣8️⃣ Dukkansu suka juya har da Na'ima da Ahmad suna kallon wannan mai kiran sunan. Baki suka saki da tsanin mamaki wanda har sai da firgici ya bayyana akan fuskarsu. "Inna wuro?" Mamaki ya kama su Na'ima ba na ganin tsohuwar ba sai na ganin saurayin da suke tare da shi mai tsananin kama da Ahmad. "Dama kina nan?" Abba ya mata tamabayar cike da mamaki. "Ina ƙasar Chadi garin dangin mahaifiyata" Jinjina kai ya yi tare da cewa. "Ikon Allah" Kallon Ahmad ta yi wanda ke tsananin kama da saurayin dake bayanta. "Wannan Amadu ne ko?" Abba ya yi murnushi tare da cewa. "Eh shi ne." Yana kallon Saurayin dake bayanta wanda ya zuba wa Ahmad idanu kamar ya ga sabon halitta. "Wannan fa wane ne?" "Ƙanin Ahmadu ne wanda na tafi ina dauke da cikinsa, wanda ni kaina ban san da shigar cikin ba sai bayan mun rabu da mahaifinsa." "Ikon Allah." Ya faɗa yana kallon Ahmad ya ce. "Ahmad wannan matar mahaifinka ce, a baya mata biyu yake da su duk da zaman nata da mahaifinka bai yi nisa zaman watanni uku suka yi, suka rabu lokacin ba za ka wuce shekaru uku ba. Ashe sun rabu tana da ciki. Lallai jini ba ƙarya ba, duk wanda ya kalle ka ta kalle shi ya san tsatso ɗaya kuka fito." Cikin so da ƙuna Ahmad yake kallon Adam, kafin ya bude masa hannunsa alamar ya zo gare shi. Shi ma cikin so da ya ji ya shige shi lokaci guda ya ƙara da gare shi suka rungume-rungume juna cikin so da ƙauna. "Ahmad ya ce Alhamdulillah ashe ina da ɗan uwa ban sani ba." Murmushi Adam ya yi tare da cewa. "Ni ma ban sani ba, ko da na girma mahaifiyata ba ta bani labarin mahaifina ba, ko da na yashi na ga mahaifiyata a gidan wani mutum matsayin matarsa, na ɗauka shi ne mahaifina. Sai da na ga ya rabuwa ƴaƴansa dukiyarsa kafin ya mutu ban da ni, da na tamabaye shi kai tsayeya faɗa Mani dukiyar ubansu ne ni ma na je ubana ya bani. Hankalinsa ya matukar tashi na tambaye mahaifiyata amma ba t sanar da ni komai ba. Dai bayan rasuwar mijinta na tashi hankali akan sai na ga ubana take sanar da ni ta yi aure ba ta wuce watanni uku na ta fito saboda ba sa jituwa da uwar gidan ta bukaci saki. Sai bayan ta koma ƙasar Chadi ta fahimci tana da ciki. Ba ta sanar da dangin mahaifina ba sai da lokacin da aka nuna Mani wariya na gane, sai kwanan nan take faɗa Mani ta ji labarin rasuwar mahaifina, da matarsa wacce ta riga shi rasuwa. A cikin kabarin take faɗa Mani ta bar su da yaro ɗan shekaru uku. Na damu shi ne ta kawo ni gidan mahaifina. Muka tarar wasu ne a ciki suka ce an basu aron gidan su zauna ne, daga nan suka Mana kwatancen gidan da kuke, kafin mu je shi ne muka biya kasuwa ashe da rabon nan za mu haɗu. Daga nan Abba ya ce su ɗinguma zuwa gida. Su ƙarasa tattaunawa a can. Haka kuwa aka yi bayan an loda siyayyar da suka yi a mota suka ɗunguma zuwa gida. Bayan na kai mahaifiyar Adam wato Inna wuro ɗaki, Joɗa ta kai ta nan ta ce ta yi wanka za'a kawo mata abincin. Ahmad ma ya kai Ɗan uwansa Adam ɗakin da ya zauna lokacin yana saurayi. Ya ce ya yi wanka kafin su ci abinci. Bayan awanni biyu suka hadu a falon suna tattaunawa, Abba yake sanar da su cewa "Gidan da wansa mahaifin Ahmad ya rasu ciki shi kadai ne ya bari gadonsa, don dama baya kiwo. Inna wuro dama ta san bai da komai don haka ba ta yi mamaki ba. Sau ya ɗuara da cewa . "Ahmad kuma kasancewar na saka shi a makaranta ya yi karatu har matakin digiri shi ya saka ya samu aikin Gwamnati. Amma yanzu dole aikin ya tsaya haka nan, saboda dukiyata da na mallaka da ya kamata a ce Na'ima ce ƴata za ta yi gadon komai na wa , amma kasancewar ta mace ya saka na mallaka komi na wa da sunan ɗanta Asadullah. A mallaka masa dukiyar idan ya mallaki hankalin kansa. Amma yanzu haka mahaifinsa zai cigaba da kula da kamfanonin kafin lokacin da Allah zai raya shi. Namiji ne shi kuma babba a cikin ƴaƴan ku ina fa yaƙinin cewa zai dauki nauyin ku da na ƙannensa. Kallon Adam ya yi tare da ya. "Zan baka ɗaya daga cikin gidaje na da kuma mota kamar yadda na bawa Yayanka." Daga shi har mahaifiyarsa farin ciki suka yi tare da mika godiya gare su. Kallon Adam ya yi tare da cewa. "Ka yi karatun boko ko?" Jinjina kai ya yi tare da cewa. "Na yi Abba har matakin diploma." "Alhamdulillah." Abba ya faɗa yana kallon Ahmad ya ce "Sai a samu wani gurbin a cikin kamfanin a bashi ya fara aiki." Jinjina kai ya yi cike da godiya ya ce "An gama Abba." Dubansa ya mayar kan Inna wuro ya ce. "Kin dawo Nigeria da zama kenan ko kin kawo sa ne ki koma?" "Na kawo sa ne na koma ." 'Umma ta yi saurin cewa. "Ai da kin zauna a gidansa tun da yanzu an bashi gida, ga mota kuma ga aiki ai ina ganin zamanki a nan zai fi." Cikin rauni ta fara magana ta ce "Zama na a can shi zai fi mani, domin kuwa ina son..." Sai kuma ta kasa ƙarasa wa. "Kina cikin wata matsala ne?' Girgiza kai ta yi alamar ba komai. Kallon Adam take yi alamar saboda shi ta kasa maganar, lura da haka ya saka Abba cewa. "Ahmad a kai shi wajan Alhaji Usman Isma'il ya zaɓi motar da yake so." Cikin girmamawa ya amsa tare suka mike suka fice. Abba ya kalli Na'ima ya ce ta karbi yaron hannun Inna wuro ta kwantar da shi tun da tana barci. Bayan tafiyarsu ne Inna wuro ta goge hawayenta ta ce. "Sale Ina ɗauke da muguwar cutar jeji a yanzu haka likitoci sun fada mani ba zan wuce Wata uku a raye ba." Daga Abba har Umma jikinsu ya yi sanyi tsananin tausayinta ya kama su . Sanin haka ya saka na yanke shawarar kawo Adam wajen dangin mahaifina, saboda anan ne kawai nake da tabbacin ko bayan raina ba zai rayuwar da yake yi a can ba, na san zai samu canjin rayuwa in sha Allah." Sun tausaya mata tare da yi mata addu'a. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Adam na aiki a ƙarƙashin Yayansa in da suke cigaba da kula kamfanin Asadullah. A wannan lokaci Allah ya yi wa Inna wuro rasuwa a can ƙasar Chadi. Mutuwar ta daki Adam sosai, don har ya kai ga suma. Abba, Ahmad, Adam sune suka je ƙasar Chadi a tare. Kwana biyu suka yi suka bar Adam a can, wanda shi sai da ya yi sati biyu ya dawo Nigeria. Na'ima na kula da Asadullah ɗanta ya yi kyau gwanin sha'awa. Duk wanda ya kalli yaron sai ya yi sha'awar ɗaukar sa. Tun yana watanni bakwai ya fara tafiyarsa ko ina. Wata rana sun je siyayya yayin da Na'ima ke goye da Asadullahi kasancewar yana barci. Tana zagayawa tana duba abin da take buƙata Ahmad na tsaye yana jiranta. Wata budurwar ta ƙaraso wajen yana kallonsa tana murmushi ga hawaye dake tsiyaya a fuskar ta. Kallo ɗaya ya yi mata ya gane ta ƙawar Na'ima ce ta school, yakan gan su lokuta da yawa a tare idan ya ya je ɗaukar Na'ima. Kallonta yake yi har ta karaso wajen da yake tsaye ta durkusa a gabansa tana kuka., Sautin kukan ne ya janyo hankalin Na'ima ta tsaya daga nesa tana kallonsu. "Don Allah Yayan Na'ima ka taimake ni wallahi son ka ya yi wa zuciyata illah. Tun da kake kawo ƙanwarka na kamu da mahaukacin soyayyarka. A yanzu na kasa auren kowa addu'a ta ita ce Allah ya haɗa ni da kai, ga shi ban san gidan Na'ima ba ballantana na bincike ta ko za ta taimake ni. Na yi jinyar zuciyata akan sonka ko ba za ka so ni ba ka aure ni zan kasance ne mai yi maka hidima. Tana juyawa ta ga Na'ima ta mike da sauri ta rike ƙafarta tana mata magiya . Ganin yadda take kuka akan son da take yi wa Ahmad ya sa ta yi kuka ita ma ta rungume ta. "Kin yi Mani alkawarin za ki taimaka Mani na aure shi?" Kai kawai ta gyada mata tare da share mata hawaye. "Wallahi tun da yake zuwa daularki da kawo ki na tamabaye ki kika ce Yayanki ne nake neman hanyar da zan sanar da ke. Ranar da muka bar makarantar ko da na fito ban hanku ba can ina nesa na hangi tafiyarku na yi kuka, amma ban fasa addu'a ba sai ga shi yau Allah ya amsa Mani." "Ki yi shiru zan baki adireshin gidana za mu tattauna kin ga yanzu ana Kallon mu ne." "Da gaske zai sure ni?" "In sha Allah zai aure ki. " "Kin yi aure ne ba ganki da goyo?" "Eh yarona ne sunansa Asadullahi." Addu'a ta yi mata tare da mata godiya bayan ta bata adireshin gidan nata ta tafi. Bayan tafiyarta ne Ahmad ya ce . "Ban san baki da hankali ba sai yau, anya kina so na kwai tun da baku kishi na?" Murmushi kawai ta yi aka ɗaukar masu kaya suka biya aka loda masa a bayan motar. A cikin mota ba wsnds ya iya magana a cikinsu har suka karasa gidan, nan ma sa ma'iaktan gidan ya yi suka shiga da kayan. Ko kallonta bai yi ba ya shige don ta ɓata masa rai. Zubaida kuwa komawa gida ta yi ba tare da ta siye komai ba, zuciyarta fara tas. Don ta san tun da Na'ima ta yi mata alkawarin aurensa ba makawa sai ta cika mata. Har dare Ahmad bai shiga ɗakin Na'ima ba, bayan ta kwantar da Asadullahi akan gadonsa ta shirya ta nufi ɗakin mijinta. Yana kwance ya yi rigimgine ta yi sallama, amsa wa ya yi ba tare da ya kalle ta ba. Ta karasa ta zauna bakin gadon. "Yaya Barka da dare." "Barka." Ya amsa a gajarce . "Fushi kake da ni?" Shiru ba amsa mata ba ta yi magana sau biyar kafin ya ce. "Anya kuwa Na'ima kina so na?" "Eh mana ko ka manta cewa ba haɗa mu aka yi ba mu muka hada kanmu kafin iyayenmu suka fahimci soyayya muke?" "Idan har kina so na dole ki yi kishi na." "Ina kishinka sosai saboda sai da so ake kishi, sai dai ban taɓa sakawa a raina cewa ni kadai zan rayu da kai ba, domin kai mijin mace huɗu ne, idan na yi jayayya da hakan tamkar ba bijire wa dokokin Allah ne. Tana matukar ƙaunarka kuma na tabbatar da ta san kai nake aure ba za ta roki Wannan alfarma a wajena ba. Ta ɗauka ciki ɗaya muka fito. Don Allah ka aure ta." Tashi zaune ya yi yana Kallon ta fuskarsa dauke da zallar takaici da mamaki. *Ba na da lafiya ina barar addu'arku my fans*😢 *Maman Ihsan ce*✍️ [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* *Maman Ihsan ce*✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page2️⃣9️⃣ Tashi zaune ya yi yana kallon ta fuskarsa dauke da takaici da zallar mamaki. Haka ta dinga roƙonsa da magiya akan ya amince da wannan aure. Wanda ƙarshe ma fada ya so ya zame masu. Washegari bayan ya fita zuwa office da rana sai ga Zubaida ta zo. Da fara'a Na'ima t karɓe ta hannu bibbiyu, bayan sun gaisa ta kawo mata ruwa da abinci, ta kasa ci cikin zaƙuwa ta ce. "Ya amince da ni kuwa?" Murmushin karfin hali ta yi tare da cewa. "Ki sha ko ruwa mana sai mu yi magana ." Ta dauki kofin da ta zuba mata ruwa ta kai baki ta fara sha, idanunta suka sauka akan babba frame na hoton Ahmad da Na'ima suna rungume-rungume da yarinsu Asadullahi. Kallo ɗaya za ka masu gane cewa. Ma'aurata ne . Ruwan da take sha ya sarƙe mata a wuya ta fara tari cikin firgici. Na'ima sai bubbuga bayanta take yi tana jera mata sannu Sai da ta tsagaita sannan ta ce. "Dama mijinki ne shi ba Yayanki ba?" "Yayana ne kuma mijina ne." "Na shiga uku." "Zubaida ta fada tana ɗora hannu akai." "Karki damu hakan ba zai hana ya aure ki ba, fatana da kyakkyawar zuciya kike son shigowa cikin rayuwarmu ba don wata manufa ba, idan Allah ya ƙaddara ke matarsa ce ban isa na yi jayayya da hukuncin Allah ba." Nan Zubaida ta dinga mata rantsuwa ba komai tsakanin ta Allah take sonsa. Ta yi mata alkawarin zai zo gidan su in sha Allah, kada ta sake zuwa nan gidan " Sallama ta yi mata suka fita ta raka ta har bakin gate. Tsawon kwanaki uku tana ta kokarin ta shawo kan Ahmad ya amince da zancen aurensa da Zubaida. Har fada suka yi magana ta yi nisa Ahmad ya kai karar ta wajen iyayensu. Faɗa sosai Mahaifiyarta ta yi masu, sannan ta nuna mata kuskure da take kokarin yi. Amma ta kasa fahimta karshe sai ta saka kuka wai ta yi alkawari kuma yarinyar ba ta da matsala za su zauna lafiya, za ta samu abokiyar fira . Ganin haka ya sa Abba ya ce a barta Allah ya tabbatar da alkahiri. Ba yadda Ahmad ya iya haka ya fara zuwa zance wajen Zubaida. Duk da ba wani sakar mata fuska ya yi ba. Aka saka ranar bikinsu rana ɗaya da na Adam ƙaninsa. Don shi ma ya samu wacce yake so. Kwanci tashi ba wuya Lokacin da aka saka na bikin ya zo. Wata ranar juma'a aka daura auren Ahmad da Zubaida sannan aka daura na Adam da Hauwa'u. Amare suka tare a gidajensu. Yayin da Zubaida suke zaune gida ɗaya da uwargidanta Na'ima. Sai Hauwa'u Amaryar Adam kuma suna zaune a gidan da Abba ya ba shi. Babu nisa a tsakanin gidajen na su. Ranar da aka kawo Amarya ranar Ahmad bai dawo ba sai ƙarfe goma na dare. Amarya na zaune a ɗakinta Na'ima na zaune a falo. Tana jiran dawowarsa. Tana ganinsa ta yi masa sannu da zuwa. Ya amsa mata fuskarsa babu walwala sosai. Cikin tsokana ta fara magana. "Ango ka sha ƙamshi, ina kazar amarcin da ka siyo?" "Ni na fada maki na siyo kaza?" "Na san kowane ango abun da yake tanada kenan." "To ban da wannan angon." Kai tsaye ya nufi ɗakinsa ta biahi cikin sanyin jiki. Kwanciya ya yi ba tare da ya rage kayan jikinsa ba. "Yaya." Ya ji muryarsa ta kira shi, a hankali ya bude idanunsa da ya lumshe su ya bude akan kyakkyawar fuskarta. "Ka sani fa yanzu ne lokacin da za ka fara gwada adalci a tsakanin matayenka, aure an riga an daura ba abinda ya rage illa mu yi fatan zaman lafiya a tsakanin mu da kuma fatan ka zama adalin miji a tsakaninmu." Haka ta dinga lallaɓa shi da maganganu masu dadi da kwantar da hankali har ya tashi. Da kanta ta taya shi rage kayan jinkinsa. Ya shiga don yin wanka . Da sauri ta fice ta nufi kitchen, kaza guda ɗaya ta fito daga cikin fridge, ta wanke ta ta shafa magi da kayan ƙamshi a jikin kazar, sai da ta tabbatar ko ina ya ji sannan ta bude Ovon ta kunna dan gasa kazar. Ko da ta koma ya fito daga wanka ƙaramin towel ta ta ɗauka ta taya shi goge jiki. Ta bashi kayan barci don ya saka. Ya muna mata cewa jallabiya zai saka. Fita ta yi zuwa lokacin kazar ta gasu sai ƙamshi take yi, leda mai kyau da tsafta ta saka kazar a ciki, sannan ta bude fridge da suke ajiye kayan sha, ta ciri fresh milk mai sanyi da hollandia youghurt ta saka a wata ledar ta fito daga kitchen ɗin. Yana tsaye ta shigo ɗakin. "Na ga ba ka shigo da komai ba ga shi mai yiwuwa yinwa take ji na san za ta ci." Kallonta kawai yake yi har Lokacin bai daina mamakin Na'ima ba. Ba yadda ya iya haka ya karɓa ta raka shi har kofar part ɗin Zubaida. Sau da ta ga ya shiga bedroom ɗin ta sannan ta bar wajen. Ɗakinta ta koma ta tura ƙofa ta shiga, jingina bayanta ta yi da bayan ƙofar tare da fashewa da kuka. Ba ta taɓa tunanin za ta ji haka a zuciyarta ba. Zuciyarta na mata zafi sai kuka take mai tsuma zuciyar mai saurare. Ganin kukan ba mafita ba ne ya saka ta tashi ta nufi toilet ta dauro alwala ta zo ta fara gabatar da sallolin nafila. Tare da addu'ar Allah ya sanyaya mata zuciya ya zaunar da su lafiya cikin aminci. Daga nan ta dauki alƙu'ani mai girma tana karantawa. Soi karfe biyu da rabi na dare ta kwanta. Ɓangaren Ahmad kuwa yana shiga dakin sallama ya yi mata. Tana zaune bakin gado, tana ganinsa ta saki ajiyar zuciya. Amsa sallamar ta yi tare da cewa. "Sannu da zuwa makararren ango." "Ayi Mani afuwa." Ya faɗa tare da ajiye ladar kazar ya zauna a bakin gadon. Kallonta ya yi tana sakar masa murmushi, ido ya zuba mata don bai san haka da kyau ba, don bai ma taɓa tsayawa ya yi mata kallon arziki ba. "Na san a gajiya kike bisimillah ki samu abinda kika ci." Taso wa ta yi ta nufi kitchen ta dauko faranti da kofuna ta ajiye. Duk yadda ta so ya ci abincin ba ci ba, ko dandana kazar ya kasa yi, da ya ga kamar ta damu ne ya saka ya ɗan sha fresh milk kaɗan. Ita ma ba ta wani ci ba ta bar shi. Ta kwashe sauran ta kai kitchen ɗin ta. Kwanciya ta yi bayan ta yi wanka ta sauya kaya. Shi kam ya dade a zaune kafin ya tashi ya zo ya yi sallar nafila ya kwanta. Haka zamansu ya kasance har ya gama kwanakin da zai yi ba abinda ya shiga tsakaninsu har ya koma ɗakin Na'ima. Da Na'ima ta fahimci haka sai da ta bata rai kafin Ahmad ya kusanci Zubaida. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har Allah ya azurta Zubaida da samun ciki. Suna zaman lafiya sosai komai tare suke yi. Hatta girki tare suke yi. Unguwa ma tare suke zuwa ko daga ɓangaren Na'ima ko Zubaida. Laulayin ta Zubaida ke yi kusan tare suke renon cikin ita da Na'ima, Asadullah na zuwa makaranta. Lokacin da Zubaida ta haifi yarinya namiji lokacin Asadullah na da shekaru biyar. Ranar suna yaro ya ci suna Kamal ansha Shagali sosai, kusan ma Na'ima ce ta dauki nauyin kayan sawarsu. Kowane kaya tare suka saka iri ɗaya hatta sarƙa da ɗan kunne. Haka suka cigaba da zama kusan raunon yaron Na'ima ke yi, wacce Asadullahi ke kiranta da Ammi, ita kuma Zubaida yana kiranta da Mom. Bayan shekaru biyu aka yaye Kamal wanda a watan da aka yaye shi a watan Zubaida ta sake samun ciki. Sai dai har wannan lokaci Na'ima ba ta samu ciki ba, tun bayan haihuwar Asadullah ba ta samu ciki ba. Sai dai a watan da aka yi auren Zubaida aka kawo ta gidan Na'ima ta riga ta samun ciki sai dai nan da nan ya ɓare. Daga nan ta samu sau biyu yana fita, har yau Allah bai sake ba ta ba. Ɓangaren Adam kuwa shi ma matarsa ta hafi ɗa namiji yaron ya ci suna Nasir. Tsakanin Nasir da Kamal watanni uku ne tsakaninsu. Kuma suna zunuban da juna kasancewar mazajensu wa da ƙani ne, sai sai a wajen Na'ima wuce haka saboda Adam din shi ma Yaya ne a wajenta tun da ɗan wan mahaifinta ne. Zubaida ma cikin ya zo mata da laulayi ne haka Na'ima ke ɗawainiya da ita har Allah ya sa sauke ta lafiya ta haifi ƴa mace. Ranar suna yarinya ta ci suna Fauziyya, anyi Shagali sosai. An ci an sha kowa sai farin ciki. Na'ima ma a wannan sunan ta yi rawar gani. Kuma yarinyar ta shiga ranta sosai don tana son ƴa mace. Ammi da Abba ma ba'a barsu a baya ba sun bada kyaututtuka wa mai jego da jaririyar. Ammi ma da ta tayar da hankali lokacin da za'ayi auren ganin ƴarta Na'ima ba ta taɓa ƙorafin zaman nasu ba hakan ya tabbatar mata da zaman jin dadi suke da juna. Matar Adam ma ta sake haihuwa in da ta haifi ƴa mace mai suna Abida. Asadullah ya yi wayau sosai don ko Kamal ya yi wayau sosai. Tun da ya ga Asad na kiran mahaifiyarsa da Ammi shima haka yake kiran Na'ima. Sai Zubaida wacce suke kira da Mom. Matar Adam kuwa Hauwa'u suna kiranta da Mamy kamar yadda suka ji yaransu na kiransu. Zama mai daɗi suke da ba tashin hankali a ciki. Matar Uncle Adam ma ta sake haihuwa ranar suka yarinya ta ci suna Maryam. Yaransu uku Nasir, Abida, da Maryam. Na'ima haihuwa dama tun da ta haifi Asadullah ba ta sake yi ba, sai bari. Sun yi yawon asibiti shiru. Daga karshe Dad sunan da yaran ke kiransa kenan ya ce su tafi ƙasar waje don a duba mahaifarta. Ita kam ta ce Allah ne bai kawo ba, tun da Nam kasar Nigeriya sun ce lafiya lau ba za ta je ko ina ba. Dole ya barta don har ga Allah ya so a ce sun tarar zuri'a shi da Ita. Mom ta nuna ita ma ya kai ta tun da ita ma haihuwar daga biyu shiru ya ce Allah ne bai kawo ba. Ta ji ba dad'i amma ta share. Lokacin da Asadullah ya kammala secondry school Dad ya kai shi ƙasar waje karatun digiri ɗinsa. Lokacin da Kamal ya kammala karatun secondry school ɗin Ne Mom ta yi tunanin shi ma zai kai shi ƙasar waje ne, sai ta ji yana zancen zai kai shi A.B.U Zaria Mom ta nemi da ya fita da shi shima ko da ƙasar Turkey ne ya kai shi mana, amma Dad ya ki amincewa. A nan kasar Nigeriya suka yi karantun su yayin da Asadullah ke can U.S yana karantunsa akan ilimin kasuwanci. Bayan tafiyarsa da kwana biyu Ammi ta shirya don zuwa gidan wata ƙawarta wacce ta samu accident. Duk da cewa a ƙauye take sai sai ba wani nisa duk da sai an bar gari. Tun da ta shirya don zuwa dubiya ƙauyaen jikinta ya yi matukar sanyi. Ji take kamar kada ta yi tafiyar. Ɓangaren Dad ma haka don sai da ya ce ta fasa tafiyar nan, ta ce ba damuwa ko ba yau ba dole za ta tafi, don haka ta fita yana biye da ita a baya. Don ya bari sai ta tafi sannan ya wuce kamfani. Ɗakin Mom ta shiga ta same ta kwance ba ta da lafiya. "Ya kamata ki je Asibiti Mom ɗin yara." "Eh yanzu zan lallaɓa na yi wanka sai mu tafi asibitin, Alhaji idan zai tafi office sai ya sauke ni." Sallama ta yi mata tare da addu'ar Allah ya ƙara Lafiya, ita ma addu'ar sauka lafiya ta yi mata suka ta fice. Har wajen Dad ya raka ta in da Direba ya ja motar suka tafi. Suna ɗagawa juna hannu ita da Dad. Daƙyar ya ja ƙafarsa ya koma cikin gidan cikin sanyin jiki wanda ya kasa gane me yake ji ne. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page3️⃣0️⃣ Daƙyar ya ja ƙafarsa ya koma cikin gidan cikin sanyin jiki wanda ya kasa gane me yake ji ne. Bayan kamar awanni biyu da tafiyarta har lokacin Dad bai fita ba, Mom kam har ta je ta ga likita ta dawo. Ganin Dad a gidan ne ya saka ta yi mamaki. Wayar Dad ce aka kira, jin ringing ɗin wayar ya saka shi faduwar gaba, don ya yi ta kiran wayar Ammi ba'a ɗaga ba. Cikin sanyin jiki ya ɗaga tare da yin sallama. Muryar da ya Abba ya ji ya yana tamabayarsa yana ina, bayan ya sanar da shi yana gida ne Abban ya ce ya zo ya same shi a wani wajen hanyar fita garin. Fita ya yi da sauri gabansa na faɗuwa ya kira direba ya ja su. Tun daga nesa suka ga jama'a an taru a gefen hanya, ga jami'an tsaro a wajen. Suna parking ya fito daga motar ya karasa wajen. Mota ce ta kone gabaɗaya ta ragargaje, komai ma motar ma ta ƙone san ƙwarangwal na mutane biyu. Ganin yadda Umma ke kuka ga Abba idanunsa sun rikiɗe zuwa ja ya sa ya karasa wajen yana cewa. "Umma Lafiya?" Dubansa ya maida zuwa ga Abba zai yi magana ya ji daga can gefe wani na cewa. "Allah Sarki Allah ya jikansu ga mijin matar nan ya iso?" Daidai lokacin idanunsa ya sauka akan zoben dake ƙasa wanda shi ne ya siya wa Ammi da kansa, ya zana dising din da yake so. Take ya zube wajen a sume. Kukan Umma ne ya tsananta. A can gidan kowa Mom ba ta san meke faruwa ba, ta gama shirya girki ta zuba a flask, tana ajiye wa a dinning table sai ga Kamal ya dawo gidan yana cewa. Yau bai fito lecture da wuri ba. Fauziyya tana school. Ganin yadda Ya shigo gidan yana kuka kamar karamin yaro ya saka Zubaida wato Mom ta ƙaraso wajen da yake, tana tamabayarsa. Kuka ne ya ci ƙarfinsaya kasa cewa komai. Daƙyar ya iya cewa. "Mun rasa Na'ima." Daidai lokacin da Fauziyya ke shigowa ta ji cewa ta rasa Ammi matar da ta rene ta kamar ita ta haife ta suka rasa. Zubewa wajen suka yi a sumammiya. Mom sai kuka take yi take yi. Dad ne y je ɗauki ruwan roba ya watsa mata daidai lokacin ta farfaɗo suka ga Abba da Umma sun shigo wanda suke cikin tashin hankali na fasa ƴarsu ɗaya tilo da suka yi. A ranar wannan ahalin sun ga tashin hankali sosai. Don tabbas rashin Ammi babban giɓi ne na rayawarsu. Kamar yadda Abba da Umma suka haife ta ita kadai haka ita ma Asadullah kadai ta haifa. An ɗauki tsawon kwanaki kafin Dad iya cin abinci, rashin Na'ima ba karamin girgiza shi ya yi ba. Ya rame ya yi baƙi. Mom ma ta shiga damuwa ko walwala da kuzari ta daina yi, gabaɗaya ta sauya ba ta da aiki sai kuka har dai idan ta kalli part ɗin Ammi. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har aka yi kwana arba'in da rasuwar Ammi. Har lokacin Asadullah na bai san da rasuwar mahaifiyarsa ba. Duk da ya so ya fahimci akwai matsala saboda ko suna waya da Dad ɗin sa ba walwala haka Mom ma ba yadda ya saba jin ta ba. Duk sanda ya tambayi ina mahaifiyarsa number ta ba ta shiga sai dai su sanaar da shi wani uzurin. Ko su ce mahaifiyarsa ba ta jin dadi ya kwanta. Da Kamal da Fauziyya kam sun daina ɗaukar wayarsa. Saboda sun san dalilin kiran nasa. Abba ma wanda yake kira da Grandpa da Umma da yake kiranta Grandma ko ya tambaye su za su ce tana lafiya Saura wata ɗaya ya kammala ya dawo Nigeria, don haka ya bar zancen kan cewa yadda Dad ɗin sa ya faɗa ne Amminsa ba lafiya tana asibiti ba ta iya magana. Ɓangaren Uncle Adam ma ƙanin Dad Asad ya yi kiransa ko ya ji daga bakinsa amma kamar hadin baki suka yi. Hatta ƴaƴansa Nasir, Maryam, da Abida sai da ya gargaɗe su akan kada wanda ya sanar wa Asad zancen rasuwar mahaifiyarsa. Kamfanin Asadullah da Dad ne ya kasance C.E.O na kamfanin baya zuwa don har yanzu bai dawo daidai ba. Ƙanimsa Uncle Adam ne kawai ke kula da kamfanin. Bayan wata ɗaya Asad bai sanar da kowa zai dawo ranar ba, don ko kiransu a waya bai yi ba ballantana ya sanar da su dawowarsa. Kasancewar rana ɗaya suka dawo shi da wani abokinsa mai suna Sagir . Da motar da aka ɗauko Sadik ɗin shima aka ɗauko su tare. Sai suka fara ɗaukar hanyar gidan Asad bayan sun ajiye shi a ƙofar gidan ne ya fito, Direban Sagir ya fito masa da trolling bag ɗin sa ya nufi gate ɗin gidan. Ƙaramar trolling bag ɗinsa ya ja ƙaramar door din gidan ya tura da niyyar shiga sai ya ji ta a rufe. Bubbuga ƙofar ya fara yi maigadi ya yana tambayar waye, jin shiru ya bude yayin da ya sauke idanunsa akan Asad dake tsaye yana rike da trolling bag, washe baki ya yi yana masa sannu da zuwa. Ya amsa masa ba yabo ba fallasa. Amsar trolling ɗin ya yi daga hannunsa yana binsa a baya. Da sallama ya tura ƙofar falon ya shiga, suna zaune a dinning table suna cin abinci. Jin muryarsa ya sa suka nufo falo don tabbatar wa. Maigadi ya ajiye masa trolling ya fita. Mamaki da farin ciki ya cika su gabadaya suka nufi wajensa Kamal da Fauziyya har suna rige-rige wajen fara rungumarsa. A tare ya rungume su yana raba idanu don ganin ta in da Amminsa za ta fito. Lura da haka ya saka Mom ta janye su Kamal daga jikinsa ta janyo hannunsa tana cewa. "Ku bar shi mana sai kun gajiyar da shi." Zaunar da shi take kokarin yi amma ya tsaya ƙikam yana cewa. "Inna Ammina?" Don wani kewarta da ƙawazucinta ya taso masa. Duk da cewar Mom na bashi kulawa tun Ammi na da dai don wanda bai sani ba zai ɗauka ita ta haife shi. Shiru suka yi ba wanda ya bashi amsa hakan ya saka ya nufi part ɗin Ammi yana ƙwala mata kira. "Ammina kina ina kin san yadda na yi kewarko kuwa?" Bata a falon don haka ya nufi bedroom ɗin ta nan ma ba ta nan. Dad ne ya janyo hannunsa yana cewa. "Muje na yi maka bayani." Ya yi maganar idanunsa cike da ƙwalla, ganin haka ya saka Asad ya juya ya kalli Mom da ita shigo ganin hawaye a idanunta ya saka ya ji wani jiri na ɗibarsa. Take ya yanke jiki ya fadi ƙasa sumamme. Mom ta saka kuka ta nufe shi tana kiran sunansa. Dad ya watsa masa ruwa amma ko motsi bai yi ba. Daidai lokacin Kamal da Fauziyya suka shigo hannun Kamal rike da robar ruwa mai sanyi. Shima ya bude bakin ruwan ya cika bakinsa ya farar da ruwan da ƙarfi akan fuskar Asad nan ma shiru bai motsa ba. Har aka yayyafa masa ruwa a karo na biyar shiru bai motsa ba. Kamal ya ɗauke shi tare da cewa "Dad mu tafi asibiti" Fita suka yi gabaɗaya, Kamal ya kwantar da shi a bayan mota Dad ya shiga ya zauna baya yayin da Kamal ya ja motar suka kama hanyar sibitin. Mom da Fauziyya suka fito ganin sun wuce ya daka Mom ta sa Direba ya bi bayansu. A hanya Dad ya kira Abba ya sanar da shi, hankalinsa ya tashi jin halin da jikan nasa ɗaya da yake tunawa da shi a matsayin bayan Na'ima. Shi da Umma suka zo asibitin inda isowarsa ya yi daidai da isowar su Mom. Uncle Adam ma ya iso a bayansa don shi ma Dad ya kira shi. Sai da aka ɗauki tsawon lokaci kafin likitoci suka samu ya farfaɗo. A ranar dai sai da rasuwar Ammi ya dawo masu sabo, don kuka suke yi sosai. Ɗaya bayan ɗaya Asadullah yake kallonsu kamar wani zautacce. "Don Allah kada ku ce Mani Ammina ta rasu, ta ce mani sai ta ga jikokinta na wa da na Kamal da Fauziyya. Kai na san ba za ta tafi ba ba mu gama rayuwa da ita ba, ba za ta bar ni ba.." Haka ya dinga surutu da sambatu kowa na ɗakin na kuka saboda yanzu aka yi masu matuwar. Bayan an sallame su har lokacin Asad na zubar da hawaye sai sai bai yi kuka ba a lokacin. Haka suka ɗunguma zuwa gida kowa rai a jagule. A part ɗin Asadullah suka nufa saboda bin sa kawai suke yi a baya. Kasancewar Mom ta kira mai aikin gidan a waya ya sa aka gyara masa part ɗin. A falonsa ya zauna har lokacin hawaye ke zuba daga idanunsa. Mamy matar Uncle Adam da yaranta Nasir, Maryam da Abida duk sun zo gidan. Mom ce ta kawo masa ruwan tea don ta san halin da yake ciki daƙyar zai iya cin abinci. Haka kuwa aka yi ruwan tea ɗin ma bai sha ba, sun yi fama da shi amma sam hakan bai saka ya sha ba. Nasiha sosai Kakanninsa suka yi masa shi kansa ya tausaya masu, sanin son da suke yi wa ƴarsu ɗaya tilo ga shi sun rasa ta. Umma ce ta dauki kofin shayin ta kai bakinsa da niyyar bashi a baki, kau da kai ya yi alamar ba zai sha ba, Abba ne ya shafa kansa yana bubbuga bayansa alamar rarrashi. Sai suka tuno masa da Amminsa don fuskar Umma da ta miko masa shayin sai ya ga Kamfanin ta da Amminsa bai san lokacin da ya sha ruwan tea ɗin ba. Sai dare sannan kowa ya koma gidansa in da aka bar shi da sauran mutanen gidan. Dad Mom Kamal da Fauziyya. Daren wannan ranar ya kasance dare mafi muni a rayuwarsa. Kamar yadda ake cewa dare mahutar bawa wannan daren kam bai masa rana. Duniyar ta yi masa zafi. Farin ciki ya ƙaurace a rayuwarsa damuwoyi sun mamaye masa zuciya kamar yadda duhu ke mamaye ɗaki bayan an kashe fitila. *Rashin comments rashin ganin typing akai-akai* *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page3️⃣1️⃣ Daren ranar ya kasance dare mafi muni a rayuwarsa. Kamar yadda ake cewa dare mahutar bawa wannan daren kam bai masa rana ba. Duniyar ta ya yi masa zafi farin ciki ya ƙaurace a rayuwarsa damuwoyi sun mamaye masa zuciya kamar yadda duhu ke mamaye ɗaki bayan an kashe fitila. A hankali ya yunƙura ya tashi, kai tsaye bathroom ya nufa don yin wanka. Bayan ya sakarwa jikinsa ruwa ne ya ɗauro alwala sannan ya fito. Farar jallabiya ya saka a jikinsa , ya dauki sallaya ya fara gabatar da salloli. Sai ƙarfe biyun dare ya isar sannan ya ɗauki alƙur'arni ya fara karantawa. A hankali ya ji ya fara samun sassauci. Addu'ar samun rahamar Allah ya yi Amminsa. Sannan ya tashi ya haura gadon ya kwanta. Har lokacin juyi kawai yake ji yana tuninin rayuwar da ya yi da Amminsa. Sai da ya dawo sallar asuba sannan barci ya yi awon gaba da shi. Mom da Dad tare suka shigo ɗakinsa ganin yana barci suka koma. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya yana samun kulawar Dad da Mom sosai, kuma ya kan ji dadin irin kulawar da suke nuna masa kamar ƙaramin yaro. Ɓangaren su Umma da Abba wandada yake kira da Grandpa da Grandma, suna bashi kulawa ganin Umma yake kamar Amminsa. Bayan ya tafi ƙasar Canada ya yi karatun masters ɗin sa ne ya dawo. Dad ya kira Abba da Umma sai Mom da kuma Uncle Adam. Akan idanunsu ya mallaka wa Asadullah na kamfanoninsa, da duk wace kadarorinsa Kasancewar Ammi kafin ta rasu ta yi masa bayanin komai da iyayenta suka mallaka masa. Ta kuma bashi ƙwarin guiwa akan cewa ya tsaya ya zama jajirtacce kada ya basu kunya. Cike da yakini iyayenta suka mallaka masa ƙasancewar ta mace ya saka ba su ba ta ba suka ce sai Allah ya raya shi za'a mallaka masa . Dan a matsayinsa na ɗa namiji babba a wajenta zai tsaya tsayin daka ya zame masu garkuwa har ita sai ya zama wani jigo ne na rayuwarta. Sannan ya tuna a ranar da Amminsa ke fada masa haka sai ya kalle ta ya ce "To Ammi da sun mallaka wa mijinki tun da shi namiji ne zai tsaya tsayin daka Kuma Yaya ne a wajenki." Mumrmushi ta masa tare da shafa lallausan gashin kansa irin na fulanin usuli ta ce. "Asad kenan, ni ma na yi masu maganar su bashi a lokacin, amma sai suka sanar da ni cewa, ba na da tabbacin cewa ni kadai ce macen da zai aura, zai iya kasancewa ya auri wata mace ko wasu matan bayan ni. Kuma haihuwa za su yi ba za su taɓa yarda cewa dukiyar mijinki ba ma su ba ne na matarsa ce da ƴaƴanta. Shi kansa bayan ran mutum ki ga ayi ta rigima akan gado ko da ya bar wasiyya da shedu ba za ki tsira ba hakan na iya janyo maki wata matsala daga kishiyarki. Wannan dalilin ya sa za mu mallaka wa ɗanki idan ya girma a mallaka masa ita, na sa me da sauran ƙanninsa da za ki haifa masa." Tunawa da Ammin ya saka shi zubar da hawaye, gogewa ya yi tare da addu'ar Allah ya shige masa gaba. "Ka adana su da kyau ka da ka yi sakaci da su." Ya ji muryar Abba na masa magana, sai a lokacin ya dawo daga duniyar tunanin da ya lula gyaɗa kai ya yi yana kallon Kakan nasa. Nan aka rufe taro da addu'a tare da masa fatan alheri. A washegarin ranar Dad ya tafi da shi ya nuna masa manyan filayen da ya mallaka masa takardunsu sannan ya nuna masa kamfanin da Dad ɗin ke jagoranta. Ya kuma yi masa bayanin wasu guda biyu ɗaya na garin Kano ne ɗaya kuma na garin Lagos. Kasancewar na garin Kano ne babba kuma yana da ilimin sanin abin ya saka ya yanke shawarar zama garin Kano. Duk wasu gyare-gyare da za'ayi ya saka an yi an farfaɗo da kamfanin. Hakan ya saka ya koma garin Kano da zama. Ya nemi lafiyayen gida ya siya. A cikin shekaru biyu kamfanin ya bunƙasa domin Allah ya saka wa ha hannunsa albarka. Kamfanin mai suna *ASADULLAH GLOBAL RESOURCES* Ya yi suna a garin Kano da kewayenta. Mom ganin Asadullah ya yi masu wuya ya saka ta tashi hankali wai yarinta ya yi nisar da ba za ta iya jurewa ba, sai sai ya dawo. Dad ya ce hakan ba mai yiwuwa ba ne. Da ta kira Asadullah ta yi masa magana ya ce yana shirin dawo da su nan garin ma, saboda shi ma baya jin daɗin rayuwar da yake yi ba tare da su a kusa da shi ba. Cikin ƙankanin lokaci ya saka aka samar wasa wani tangamemen fili mai matukar girma, ya kai wani ƙaramin unguwar. Aka yi gini ladiyayye na zamani irin babban gida wanda ya tara family haka aka tsara gidan. Tsaya wa fada maku tsaruwar gidan ɓata lokaci ne, don dai mu cika shafi biyu ina maku bayanin ginin da kayan more rayuwa da aka zuba. Wannan ginin shi ne *Asadullah mansion* Ya sanar da Dad du dawo, nan Dad da Mom suka dawo da Kamal sai Fauziyya. Ya so kakanninsa su ma su dawo kusa da shi, amma sun ƙi yarda sun ce za su dinga ziyartarsu lokaci zuwa lokaci. Ba yadda ya iya haka ya hakura ya bar su, sai dai ya nemi ƙanin mahaifinsa wato Uncle Adam ya ce su dawo kusa su zauna a nan cikin mansion ɗin. Haka kuwa aka yi bayan su Mom sun tare da a ɓangaren su da ya tanadar masu. Kowa da part ɗinsa a nan ɓangaren, part ɗin Dad daban na Mom daban haka na Kamal da Fauziyya. Sai shi uban gayyatar na shi ma daban ne a upstairs. Haka can ɓangaren da ya ware na Uncle Adam ma daban ne sai dai bai kai girman na su ba. Ga part ɗin ma'iaktan gidan ma daban, ga su gidaje can daban sun fi biyar kuma duka a cikin mansion ɗin. Don Dad ma ya masa maganar cewa cewa filin da ginin ya yi girma da yawa haka unguwa guda kuma iya su ƙaɗai. Harkokin Asad sai kara bunƙasa suke yi arziki na ta cigaba da haɓaka. Sunan Asadullah ya zagaye arewa saboda kasuwancinsa da kuma taimakon al'umma da yake da shi. Ga ƴan mata sai kawo masa hari suke yi, ƴaƴan manyan mutane, daga cikin gida kuma ga yaran Uncle ɗin sa Maryam da Abida. Sai dai ba wacce yake kulawa da sunan soyayya. Sai dai yana basu kulawa a matsayin Yaya a wajensa. Duk wani abu da ake kaiwa a cikin mansion ɗin nan daga aljihun Asadullah yake fitowa. Tun daga kan ɓangaren Dad har bangaren Uncle Adam. Kama daga abinci da abun sha har zuwa kan suturar sakawa duka shi yake yi masu da motocin da suke hawa da man fetur da suke zubawa a motocin duk daga wuyansa ne, don gidan man fetur ɗin sa suke zuwa a cika masu tankin motarsu. *Bayan shekaru biyu* A wannan lokacin Dad ya ƙara aure, in da y auri wata bazawara mai suna Zulaihat mijinta ya rasu tana da yarinya mace mai suna Suhaila, yarinyar ba za ta wuce sa'ar Fauziyya ba. Da farko Zulaihat wacce suke kira Aunty,da ta shigo cikin gidan suna zaune lafiya ita da Mom. Ba wata matsala a tsakaninsu, ta ɗauke su yan uwa Kamal da Fauziyya ma ta ɗauke su kamar ƴaƴanta, hatta Asadullah da bai cika Zama gidan ba ta na nuna masa kulawa. Sai dai daga baya lokaci guda ta ja jiki da kowa na gidan, ba ta shiga harkar kowa kuma ba ta bari wani ya shiga nata. Ƴarta Suhailat ma ta mata shamaki da kowa na gida. Ko da Dad ya tamabaye ta ko an mata wani laifi ne ya ce ba komai haka ta zaɓawa rayuwarta. Kamal da Nasir ɗan wajan uncle Adam duk a kamfanin Asadullah suke aiki. Yana sanye cikin Suit black with white inner sai necktie Black mai layin fari a jinkinsa. Ƙafarsa na sanyi cikin Black shoe ƙafa ciki sai ɗaukar idanu yake yi. Fuskarsa na sanye da farin glass. Sai agogon Diamond dake ɗaure a hannunsa. Ƙamshin turarensa na shumukh luxury scent ya ringa shi isowa falon, wanda gabaɗaya ilahirin jama'ar dake falon sai da kowa ya saki ajiyar zuciya. Dad, Mom, kamal da Fauziyya su ne zaune a falon. Sai Uncle Adam da ya shigo yanzu fuska ba walwala. Ko gaisuwar da su Kamal da Fauziyya ke masa bai masa ba. Su dai gabaɗaya hankalin su ya tafi kan Asadullah. Mom ta ce "My son har ka fito, ina fatan ka kira ta ka sanar da ita da zuwanka, ni ma na yi waya da mahifiyarta da safe na sanar da ita zuwanka. Don Allah wannan karon ma kar ka bani kunya kamar yadda ka saba. Ƴan mata hudu kana bijire mani, to wannan karo na hudu ba ja da baya, ko kana so ko ba ka so sai mun aura maka ita. Idan ba mu isa ba sai ka nuna mana iyakarmu." A fusace uncle Adam ya ce. "Ke Zubaida tsaya matsayinki. Ke kin isa ki ce za ki zaɓawa Asad matar da zai aura?" Mumrmushi ta yi tare da cewa. "Ga shi ko kana gani a matsayina na uwa a gare shi." "Ƙarya ne wallahi ai kama da wane ba ta wane." Dad ya kalli Uncle Adam ya ce. "Me kake yi haka ne?" "Ya me nake yi ko me matarka take yi, bayan na shaida maka cewa na bawa Asad auren ƴata, shi ne take shirin tura shi tura shi zance wajen ƴar ƙawarta ko ƙanwarta ce oho." "Ni ce dau uwarsa Ni nake da ikon zaɓa masa matar da ta dace da shi." Ƙarya ne, ƙarya ne wallahi. Ba ki haɗa komai da Asad ba face ki ce kina auren mahaifinsa ke matar ubansa ce bayan nan kuma fa? Yanzu idan ya sake ki wani iko kike da shi akan Asad.? Ni kuma nan ni ne maɗaurin auren Asad ko a lahira ni ne ubansa jini ɗaya Muke daga tsatsona Abubakar muka fito kin ga kuwa idan aka tsaga jinina za'a ga na Yaya." Kallomsa ya maida kan Asadullah ya ce. "Asad ɗana, ga ƴar uwarka can tana jiranka. Na baka ita a matsayin matar aurenka kuma uwar ƴaƴanka in sha Allah. Ko Na baka zaɓi ko Maryam ko Abida duk wacce kake so ka zaɓa a cikin su biyu." "Ba zai yiwu ba Adam ta yaya kake neman mayar da ni ƙaramar mutum ce. Tun yaushe nake kokarin ganin na zaba masa matar aure ta gari. Ƙawayena da dangi na bi na zakulo yana watsa Mani kasa idanu, sai yanzu da na shawo kansa kake so ya bijire Man? Shi su ƴaƴan naka ai bai ce yana son su ba ." "Ai ba zai taɓa kin nasa ya zaɓi bare ba." "Ai soyayyar ƴan uwantaka daban da..." "To ba ki isa ba na fi ki iko da Asad kuma idan na zartar da hukunci ya zauna ko Yaya ba zai yi jayayya da Magana ta ba." Sa'insa suka fara yi a tsakaninsu har ran Dad ya ɓaci ya daka masu tsawa. "Ya isa!" Sai da lokacin suka nutsu kowa ya yi shiru. Asadullah kallonsu yake yi da mamaki akan macen da zai aura suka wannan jijiyar wuya. Juyawa ya yi zai koma amma ganin kiran bodyguard ɗin sa Sulaiman ya saka ya nufi ƙofar fita . Jin muryar Mahaifinsa ya yi ya ce . "Asad." Juyowa ya yi sannan ya ce. "Na'am Dad." "Zo nan." Cikin sanyin jiki ya karaso bai kalli Mom ko Uncle Adam ba dan haushi suka bashi. "A cikin yaran kawunka da yarinyar da Mom ɗin ka ta zaɓa maka wacce kake so a cikinsu.?" Shiru ya yi ya ma rasa mai zai ce. "Dole za ka sanar da ni a gaban kowa kuma yanzu, saboda hakan ne mafita." Kowa ya zuba masa idanu suna jin faɗuwar gaba don tsoron abin da Asad zai ce. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page3️⃣2️⃣ Kowa ya zuba masa idanu sana jin jin faɗiwar gaba don tsoron abinda Asad zai ce. "Ba wacce nake so a cikinsu ko da na aure su sai dai idan biyayya zan yi. A zahirin gaskiya ba wata macen da na ji ta kwanta Mani a rai." Dam dam haka ƙirjin Uncle Adam da Mom yake bugawa, sakamakon jin zancen da Asad ɗin ke faɗa. "Ki yi haƙuri Mom wallahi biyayyar uwa ce kawai za ta ni zuwa wajen yarinyar da kika zaɓa mani, ga Uncle shi ma ya bijiro da zancen auren ƴarsa. Kin ga idan na bi ra'ayin ki na zaɓi yarinyar da kika zaɓa mani zai ji ba dad'i ganin ga ƴar uwata ƴarsa na ƙi ta. Kamar yadda idan na zaɓi ƴarsa na san ke ma za ki ji ba dad'i ne ki ce n watsa maki ƙasa a idanu. So ku yi hakuri Please." Ya karasa maganar yana haɗe hannayensa alamar roƙo. Dad ya kalle shi ya ce. "Ba zai yiwu ba dole ka zaɓi ɗaya daga cikinsu." Ɗan jim ya yi kafin ya ce. "To Dad ka bani lokaci kadan zan yi nazari kafin na zaɓi daya daga cikinsu." Mom ta yi saurin cewa "Ka je ka ga waccen saboda ka san ta don yaran kawun naka ba ɓoyayyu ba ne." Jinjina kai ya yi sannan ya fice daga falon. Sulaiman bodyguard ɗin sa ya tarar a ƙofar yana jiransa. Gaba yayin da s shik kuka take masa bayan fitarsa ne Uncle Adam kalli Mom ya ce. 'Yar bakin ciki hankalin ki ya kwanta burinki ya cika , hankali ki ya kwanta wato bai auri ɗaya daga ɗaya daga cikin ƴaƴana ba. To bari na fada maki kamar yadda bai sure ki ba Hakazalika ba zai auri kowace yarinya da kika kawo ba idan kuma kika matsa to mutuwar kasko zamu yi, dan Wallahi sai dai kowa ya rasa." Yana gama fadar haka ya fita fuu yana cika kar ɗanwaken da zai yi juyin farko a wuta. Dad kam gabaɗaya sun daure masa kai, yadda kowa ke nuna cewa sai ta hanyarsa Ajmal zai samu mata . Jidderh ce ta yi sallama ta shigo cikin falon, cikin girmamawa ta durkusa ta gaida Dad, ya amsa cikin sakin fuskar tare da tambayar ta mutanen gidan, ta amsa da Alhamdulillah. Nan ta gaida Mom ta amsa mata ba walwala, har ta mike ta nufi kitchen dai ta ji Mom ta ce " Jidder?" "Na'am gani nan zuwa." Ta fadada tana dawowa in ga Mom take. "Mom ga ni." "Ki fara shga cikin ɗakina ki ɗauko Maganin da zan sha." "To Hajiya." Ta fada tana tashi daga Wajen. _Asadullahi_ Yana zaune. Bayan motar yana kallon Togo da jama'ar sai dai hmhanafaya hankalinsa na wani wajen can daban, don a zahiri ba titin yake kallo ba ya lula can duniyar tunani. Al'amarin Uncle Adam da Mom. Fitowa ya yi daga cikin motar, ƙamshin tutarensa kawai ya tabbatar wa ma'aikatan kamfanin ya ya iso. Wunin ranar da na dai Asadullah ya yji shi gabaɗaya ya kada gane meke damuwa. Da wuri ranar ya dawo gida . Ƙofar Sualaima ne ya yi saurib fitowa daga motar ya zo ya buɗewa Asadullah . Yana fitowa ya nufi cikin gida. Ba kowa a falon ƙasa, don haka kai tsaye ya nufi upstairs. Direct ɗakinsa. Bayan ya shiga ne ya ji kamar motsi. Yana juyowa kafin ya samu damar ganin ko waye ya ji an fesa masa abu a fuska. Daga ranar bai sake gane komai ba, sai dai ya farka ya ga ne a in da yake. Sai dai an ɗaure shi da sarƙa. *Cigaban labari* _Hilal_ Shaƙo Idanunta ya yi ta fara zaro idsnu tana kakari. "Waye ya maki ciki?" Daidai lokacin ne Dr ya shigo yana ganin abunda an Hilal ke ƙoƙarin aikatawa. Da ƙurar ya kwace Zahra daga hannunsa. Take ta zube a wajen tana ta faman tari. "Za ki fara fadi ko sai na illata rayuwar ki?" Ita dai sam ta kasa gane me yake nufi da wai tun yaushe ta fara harka, sannan kuma wani ciki yake magana akai, sam ta kasa gane manufarsa. Doctor ne ya yi magana yana cewa Ka duba halin halin da take ciki mana, ka bari ta huta abi komai a sannu." Tashi ta yi ta zauna bakin gadon tana mayar da numfashi. Babu abinda Hilal ke aika mata da shi sai mugun kallo, bakin ciki ne a a cikin zuciyarsa. Zuwa ya yi ya samu Dr akan ya basu sallama. Tsoronsa da Doctor ya ji ne ya saka ya basu sallama. Yana shiga ɗakin ya tsuke fuska . "Tashi mu tafi kafin na ɓalla ki a wajen nan." Haka ta dinga rawar jiki tana ɗaukar dankwalinta da takalmi ta saka. A tare suka fice kowa zuciyarsa ba dad'i. Wajen parking motocin da aka tanada a asibitin suka nufa. Mazaunin direba ya shiga yayin da ya shiga ta zauna a gefensa. "Wa ya yi maki ciki? Kuma yaushe kika fara mu'amalar banza da maza?" Hawayen da take riƙrwa ne suka samu nasarar zubowa daga idanunta. Ita tun da take a rayuwarta babu wani ɗa namiji da ya taɓa rike ko da hannunta ballantana suka kai ga mu'amalar banza da shi. Amma wai yake mata zancen ciki har da ma tambaya wai yaushe ta fara Tsawar da ya daka mata ne ya saka ta sakin wani marayan kuka. Bai ce mata komai ba, ta cigaba da kukan nata, kasancewar baya son hayaniya da kuka ya saka shi yin parking a gefen hanya. Kallon gefen fuskanta ya yi ya ga shatin yatsunsa biyar a fuskarta sakamakon marin da ya yi mata a asibitin. Tsawa ya daka mata tare da cewa "Za ki rufe Mani baki ne ko dai na sauya maki kamanni a wajen nan, wallahi idan ba ki kiyaye ni ba sai na ɓallaki a wajen nan." Tana jin haka ta san muguntarsa don haka ta haɗiye kukan da take yi. Sai dai zuciyar ta mata zugi bisa kalamansa gare ta na cewa yaushe ta fara mu'amala da maza." A haka suka ƙarasa gidan ran kowa a jagule, bayan ya yi parking a parking space ne ta kai hannu dan buɗe murfin motar, amma sai ta ji ta a gam alamar ya yi lucking ɗin motar ta juyo ta lalle shi da niyyar yi masa magana ya bude mata sai ta kasa sakamakon zuba mata Mayun idanunsa da ya yi masu masu matukar kwarjini da ya yi. Sai ta sunkuyar da kanta tana Wasa da yatsun hannunta da suka sha jan lalle. Tsabar kwarjinin da ya yi mata ne ta kasa yi masa magana . "Tambaya ta ƙarshe zan yi maki kada ki ce mani baki sani ba. Waye ya yi maki ciki.?" Tura baki ta yi tare da cewa "Wai kai kana ta Mani maganar ciki ya za'ayi ma ace wai ina fa ci..." Kafin ta kai aya ta ji saukar yatsunsa biyar a gefen fuskarta wanda sai da ta ji wani shuu a kunnen nata, ga wani duhu da take ganin ya gifta, jin ta da ganin ta sau da suka ɗauke na wucen gadi, ba ta gama farfaɗo wa da azabtar marin da ya yi mata ba ta ji ya kai mata duka a baki, nan ma wani azaba ta ji wanda ya saka ta sakin ƙarar azabtar da ta sha har ta rintse Idanunta. Wani gishiri ta ji a cikin bakin nata, alamar jini ne bakinta ya fashe. "Get out in my car ƴar iska mai fuska biyu. Zan yi maganin ki ne." Tana buɗe kofar ta ji ya buɗu. Hakan ya saka ta fita a guje tana kuka. Lumshe idanu ya yi ransa na masa zafi. A hankali ya fito daga cikin motar cikin sanyin jiki kamar an jefi kaza da gishiri. Ba kowa a main falo, kai tsaye ta nufi part ɗin na su. Tana zuwa ta ga gabaɗaya suna falon. Abbi Ummi, Yaa Mahmud da Yaa Sadik. Cikin tashin hankali suke tambayar ta daga ina take suna ta kiran wayar ba ta shiga, sannan kuma wannan fuskar da ta kumbura da ga baki ya fashe. Ƙasa ba su amsa ta yi sai faɗa wa jikin Ummi ta yi tana sakin kuka mai cike da raɗaɗin zuciya da ƙunci. "Abbi me y saka ƴan uwanka suka tsane mu, me ka saka ba sa ƙaunar su ga nuna farin ciki da walwala. Dangin Ummi kawai suke ƙaunarmu ba sa son ganin kukan mu, amma danginka ba sa son su ga nuna farin ciki." Ummi ce ta ce . "Ya na ga fuskar ki a kumbura ga baki shi ma ya kumbura ya fashe, daga ina kika mun dawo ba ku nan ga wayarki a gida. Ballantana a kira . "Mom kin san lokacin period ɗina ne yanzu ko?" "Eh na sani me ya faru?" "Daga cikinsu da marata na ciwo na kwanta kin san wani lokacin ina zubar da jini sosai daga gani shi ne su Sunyi Laila da Mummy suka ce wai ciki ne da Ni na zubar..' Dukkansu salati duka hau yi. "Kada ki damu Allah yana tare da ke." Cewar Abbi yana mata kallon tausaya wa. "Me ya saka naga kamar kin sha duka ga fuska ta kumbura ga baki ya fashe?" "Yaa Hilal ne ya mare ni ya kuma duke ni a baki wai sai na fada masa wanda ya Mani ciki ." A fusace Yaa Sadik ya mike don zuwa ya samu Hilal. Yaa Mahmud ne ya rike shi tare da cewa. "Ka kiyaye Yaa Hilal domin ba Mansur ba ne ko Faisal da ka saba faɗa da su. Wannan Hilal ne karo da shi ba za ka ci riba ba, kai ma ka san waye shi ba sai na baka labari ba." Dawowa ya yi don shi ma ya san ba zai iya ja da shi ba. " A gaskiya wannan rayuwar cikin waɗan nan mutanen ba dad'i, gara mu bar masu gidan gabaɗaya mu koma wani wajen.," Sadik ta yi maganar cikin ɓacn rai, Ummi ne ya ce. Sai dai ku yi hakuri domin kuwa domin Kakanku haka ya tsara cewa ba wanda zai bar gidan nan." Hannun Zahrah Ummu ta kama suka shiga ciki n ɗakinta ganin yadda bakin ma ya kumbura. Wanka ta saka ga yi da ruwan ɗumi sannan ta fito ta sauya kaya ta sanya pad a jikin panta ta shafa miski a ƙasan wajen ta shirya cikin doguwar riga. Tea Ummi ta haɗa mata sannan ta ɗauko mata magani ta kawo mata. Amsa ta yi ta kafa kai bayan ta yi bisimillah ta sha, maganin ma ta sha sannan ta kwanta. _Hilal_ Yana shigo wa kai tsaye ya nufi upstairs. Jin Muryar Mummy ya yi tana cewa. "Yanzu da ka kai ta asibitin ka yarda ciki ne da ita ba sharri aka yi mata ba ko? Wai ina ruwanka ne ma da ka kai ta asibiti?" Na yi abinda zan yi wa kowa ne ko da a hanya na ga mutum haka zan taimaka masa ba wai don ita na yi ba ." "To Meye na ka na shiga damuwa ?' Daniwata ita ce yadda za ta zubar da kimar ahalinmu ta ɓata mana sunan family yadda aka san wannan family ya ji suna idan mutane suka ji daya daya cikin familyn ga abinda take aikatawa ai ta ɓata mana suna don. Sai ya shafi kowa da ke cikin gidan nan. Bayan haka Meye damuwata ita ta ne can ga ƙararta." Ya ji maganar yana haurawa upstair. *Kuyi hakuri na ji na shiru ina da uzuri ne don ba na ma gari na yi tafiya ne. Am very busy almost all the time* *Maman ihsan ce*✍️ 09065357995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page3️⃣3️⃣ "Damuwa ta ita ce yadda za ta zubar da kimar ahalinmu ta ɓata mana sunan family yadda aka san wannan family ya yi suna, idan mutane suka ji daya daga cikin familyn ga abinda take aikatawa ai ta ɓata masa suna don ya shafi kowa dake cikin nan. Bayan haka ta je can ta ƙarara." Ya yi maganar yana haurawa upstair . Ummi na fitowa daga cikin ɗakin Fatima Zahrah bayan ya ba ta magani ta yi barci ne sai ta nufi ɗakin Abbi. Zaune ta same shi akan gadonsa da alama tuninin yake yi. "Hannunsa ta rike a cikin nasa wanda hakan ya saka ya juyo ya kalle ta yana mata murmushin yaƙe . "Ya jikin Zahra?" "Ta yi barci." ",Allah ya sauwake." "Abban Mahmud." Juyowa ya yi ya kalle ta da alama yadda ta kira sunan maganar na da mahimmanci. "Yanzu haka za mu cigaba da rayuwa a cikin wannan gidan. Na gaji. Kusan shekaru talatin muna abu ɗaya. Na sha yi maka maganar mu tashi mu bar wannan gidan, ka ce Papa ya hana bayan ƙiyayyar da ake yi maka ya shafi matarka da ƴaƴanka, idan muka yi wasa sai ya shafi jikokinnu. To ba zan bari hakan ya faru ba, akan me za su saka mu a gaba. Musamman Fatima Zahrah tsanar da suke yi mata ya fi na kowa yawa a cikin gidan nan. Zan je na samu Papa idan har kai ba za ka bar gidan nan ba to ni zan bar gidan nan ni da yarana." Tana shirin tashi ta ji ya rike hannunta. "Kin ga don Allah ki sake hakuri in sha Allah wata rana komai zai dawo daidai. " Mumrmushin takaici ta yi tare da cewa. "Haƙuri na nawa kuma ai tun da ba yi haƙirin kusan shekaru talatin to wani hakuri ya rage kuma?" Da kike maganar tashi a cikin gidan nan kin san cewa ba na da in da yafi nan ko? Saboda nan gidan ubana ne kuma ya mallaka Mani wannan ɓangaren halak malak, ba wanda ya isa ya tashe ni a nan, kamar yadda suma suke takama gidan ubansu ne to haka ni ma, kamar yadda ya mallaka masu ɓangarorin da suke zaune haka ni ma ya mallaka mani na wa. Kuma sanin kanki ne cewa ya haramtawa ƴaƴansa barin gidan nan dole kowa ya zauna a cikinsa. So kike na saɓa umarnin mahaifina ne?" Tun da ya fara magana ba ta katse shi ba sai da ya kai aya ta ce . "Ba so nake ka tsallake umarnin mahaifin ka ba, ka zauna amma gaskiya ni da ƴaƴana abun ya ishe mu haka. Sun saka mu gaba musamman Zahra kullum cikin matsalarsu take. Har ya kai ga an yi mata ƙazafin ciki. Ba'a bar ta hakan ba sai da aka haɗa mata da suka akan laifin da ba ta aikata ba. Wallahi, summa tallahi ba zan bar maganar nan ba sai na sanar da Papa wannan zancen idan bai ɗauki mataki ba ni na san matakin da zan ɗauka akan hakan." Tana gama fadar haka ta nufi kofar fita duk yadda Abbi ke kiranta ba ta saurare shi ba ta fice abun ta, don ranta ya gama ɓaci akan zancen." _Asadullah_ Yana zaune a wata kujerar roba dake ɗakin da aka ajiye shi . Har lokacin hannunsa da ƙafarsa ɗaure suke da wani sarƙa. Sai dai wannan karon da alama yana cikin hayyacinsa. Wani mutum ne ya turo ƙofar ya shigo cikin ɗakin, sannan ya mayar da ƙofar ya rufe. Yana sanye da ƙananan kaya, sai dai ba za'a iya shaida kakanninsa ba, sakamakon ya sanya P. Cap 🧢 a kansa sannan ya sanya face mask 😷 a fuskarsa ga bakin gilashi a idanunsa. A hankali ya ƙara so gaban Asadullah ya janyo wata kujera ya zauna suna fuskantar juna. "Asad ya kake?" Kallo ɗaya Asad ya masa ya kauda kansa gefe . Dariya mai sauti mutumin ya yi sannan ya ce. Bari na baka wani labarin abun da ba ka sani ba, ko kuka na yi maka fashin baki akan a abinda ya shige maka duhu." Ajiyar zuciya ya sauke yana cewa na san ba za ka mance ranar 27 ga watan Oktoba ba na shekarar na shekarar dubu biya da sha huɗu. Ranar da ka kawo abokinka cikin mansion ɗin nan." A hankali Asadullah ya fara tuno abinda ya faru a wancan ranar. Tafiya suke yi cikin motocinsu yayin da motoci biyar ne suka suke a jere sai dai ta tsakiyar tafi kyau da tsaruwa. Don da alama ita ce wacce uban gidan na su ke ciki. Biyun da ke gabansa da biyun dake bayansa . Sanye take cikin Suit fara ta cikinsa ma fara sai bakin necktie da ya ɗaura a wuyansa . Takaliminsa ma baki sai sheƙi suke yi agogon hannunsa ya duba tare da kan gajeren tsuki. Daidai lokacin ya kalli gefensa idanunsa ya sauks akan abokinsa Sagir wanda suka yi secondry school tare. Alamar tsayar da motar ya yi wa Direba. Take duka motocin suka tsaya, ya yi wa ɗaya daga cikin guard ɗin alamar ya kira masa wancan mutumin. Take kuwa suka dawo tare ya yi masa alama da ya shigo cikin motar, kasancewar a ƙasa yake tafiya. Sam bai gane Asad ba. Guard ɗin ya ce masa "ka shiga daga ciki." "Na shiga ina a wannan zamanin na rashin tsaro na san ina za ku kai ni?" Mumrmushi Asad ya yi tare da cewa. "Sagir Ibrahim Sahabi." Wato idanu ya yi tare da cewa "Asadullah Ahmad Abubakar?" Jinjina masa kai ya yi tare da sake wani murmushi. Da sauri ya shiga ya zauna gefensa yana dariya. Suka cigaba da tafiya. "Sagir ya na ganka haka?" "Ai dole ka ganni haka domin mahaifiyata da mahaifina sun rasu, ga bashin da ake bin mahaifina da aka biya jama'a bashi har da na banki haka ban tsira da komai ba, hatta gidan da nake ciki sai da aka siyar da shi yanzu haka ɗakin wani abokina nake kwana shi da ƙaninsa yanzu haka a takure nake a cikin ɗakin. Jinjina kai Asad ya yi tare da yi masa addu'ar Allah ya ya jikin iyayen nashi. Ya amsa da Amin. "Ya zancen aiki fa ana zuwa aiki ne?" "Har yanzu ban samu aiki ba ka san yanayin ƙasar aiki sai mai hanya." "Kada ka damu lokacin samun aikinka ya yi, yanzu ka koma can in da kake ka ɗebo duk wani abun da ka san kana bukata ka zo zan baka wajan zama da aikin yi." Zaro ido Sagir ya yi tare da cewa. "Da gaske kake yi abokina?" Jinjina masa kai kawai ya yi alamar gamsarwa. Tasanar murna da farin ciki bai san lokacin da ya rungume Asadullah ba. Kai tsaye suka nufi *ASADULLAH GLOBAL RESOURCES* sai a lokacin Sagir ya lalle shi ya ce. "Dama kai ne kake da ASADULLAH GLOBAL RESOURCES da kuma ASADULLAH INVESTMENT NIGERIA LIMITED? kai ne me wannan hamshaƙin ɗan kasuwa da ake faɗa?" Murmushi ya sakar masa ba tare da ya ce komai ba. Kallon Sulaiman amintaccen bodyguard ɗinsa da ke gefen direba ya yi ya sanar da shi cewa ya sa ɗaya daga cikin direbobin su ya kai Sagir gidan da zai je ya kwaso kayansa. Haka kuwa aka yi Direban ya kai shi ya kwaso kayansa ya yi wa masu ɗakin sallama ya shiga mota suka bar layin Asadullahi na zuwa kamfanin bai wani jima ba ya bar komai a hannun ƙaninsa Kamal, yayin da ya koma gida tare da muƙarrabansa. Wani part ya bawa Sagir a cikin Asadullah mansion ya zauna a ciki. Sannan ya kira Jidderh ya saka y don ta gyara part ɗin. Bayan haka ya masa alƙawarin bashi aiki a kamfanin bayan ya karbi takardunsa. Haka kuwa aka yi washegari Asad ya ba shi gurbin aiki a kamfaninsa. Ya yi matukar farin ciki da wannan aiki. Wajen ɗaya suke da Kamal don shi ne mataimakin Kamal ɗin. Bayan wata ɗaya da faruwar haka sai kuɗaɗen suka dinga ɓacewa a cikin kamfanin. Dan miliyoyin kuɗaɗen ne ake sacewa. Lokacin da abun ya ishe shi bayan ya gano cewa ta hanyar Kamal da Sagir kudaden ke fita, don haka ya kira Abokin nasa Sagir da ƙanin nasa Kamal ya yi ya nuna ɓacin ransa akan abun da suke yi na almundahana da ku kudaden kamfani. Sannan ya yi masu maganar cewa idan albashi da ake biyansu ya masu kadan ne ko suna bukatar kudi su tambaye shi mana, zai iya kara masu ko ya basu. A lokacin sun bashi hakuri ne, sannan a wannan watannin kuɗaɗen suka ƙara ɓata kimanin Naira Miliyan Hamsin. A lokacin bai masu magana ba ya ƙale su bayan kwana biyu aka sake sanar da shi cewa miliyan ɗari aka rasa kuma an tabbatar ta hannunsu kai dai ne kudaden kamfani za su iya fita. Daga nan ya dakatar da su daga aiki har sai ya gama bincike. A binciken da ya yi ne ya gano ba iya kudaden da suka ɓata ba kenan, ransa ya ɓaci ƙarshe ya ce su rubuta takardar barin aiki su kawo masa. Kallomsu ɗaya bayan ɗaya ya yi tare da cewa. "Ƙanina da abokina sune suka yi Mani wannan aiki. Da ace wasu ne suka yi Mani ba zan yi mamaki ba, amma a ce ku makusanta na da na yarda da ku ne kuke Mani wannan ta'asar." Kallon Kamal ya yi da cewa. "Ina za ka kai waɗan nan kuɗaɗen haka, me za k yi da su, idan kana bukatar abu ka tambaye ni ba zan iya yi maka ba ne? Kana jinina ne ka yi mani wannan abun me ya saka ba za ka tambaye ni ba." Sunkuyar da kai ƙasa ya yi tare da cewa. "Yaya dan Allah ka yi haƙuri." Hakuri kam ya ƙare don dole za ku bar aiki a nan don ba zan sake yarda da ku ba, kun ci amanata yayin da na ɗauki yarda ba baku. Na baku damar canzawa ba ku canza ba yanzu kam bakin alkalami ya riga ya bushe." Zufa ce ta karyo masu suka fita jiki ba ƙwari. *Bayan awanni uku* Yana zaune a office ɗin sa ya sanya system a gaba yana duba wasu bayanai. Wayarsa ce ta yi ruri yana dubawa ya ga Sagir ne yake kiransa. Ya ɗaga take ya mike a firgice. Katse kiran wayar ya yi tare da fice wa a guje ko ta kan wayarsa bai yi ba ya fice. Yana fita ya samu Sagir a tsaye, cikin tashin hankali yake cewa . "Ina Ƙanina yake?!" "Mu je abokina, wallahi ƙaninka yana cikin mawuyacin hali." Ya faɗa yana bude masa murfin motarsa wanda Asad ya siya masa lokacin da ya bashi aiki." Shigewa ya yi bodyguard ɗin sa na kokarin yin magana Sagir ya ce. "Ku jira mu yanzu za mu dawo " Ya faɗa sannan ya figi motar a guje ya bar kamfanin. Slaiman ne ya bawa sauran bodyguard ɗin umarnin su bi bayansu. Take suka shiga motocinsu suka bi bayansu. Sai dai cikin rashin sa'a suka kasa gane in da motar Sagir ta bi. Don haka sai suka bi haryar da ta sha bamban da wanda suka bi. Gudu Sagir yake yi kamar zai tashi sama. Asadullah na tambayarsa wani asibiti Kamal yake ya ce masa bayan gari. Da mamaki yake kallonsa tare da tambayarsa. "Kamar ya bayan gari ba asibiti ne sai bayan gari?" "Abokina yanzu ba lokacin tambaya ba ne mu je kawai ka gan shi." Asadullah bai sake cewa komai ba fatansa Allah ya kai su ya ga ɗan uwansa. Sai da suka kai wajen da ba kowa sun sauka akan hanya tun daga nesa ya hangi Kamal a kwance. Suna karasawa ko parking din kirki bai bari Sagir ya yi ba ya fita ya nufa in da Kamal ke kwance. Ya "Ƙanina lafiya me ya same ka?" Kamal da idanunsa ke rufe ne ya buɗe idanunsa tare da watsawa Asad wani banzan kallo. "Meke damunka tashi mu je asibi..." Kafin ya ƙarasa magana Kamal ya fito da wuƙa daga ƙasansa ya soka wa Asadullah a ciki." Tsabar azabar da ya ji ne ya saka ya saki wani sautin azaba, bai gama dawowa daga duniyar azabar da ya ji ba ne ya ji an sake suka mashi wukar ta bayansa. Ya juyo don ganin wanda ya soke shi ta baya, amma bai samu ganin ko waye ba sakamakon duniyar da ya ji tana juya masa take ya zube a wajen jini na fita daga jikinsa. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page 3️⃣4️⃣ Yana juyawa dan ganin wanda ya soke shi ta baya, amma bai samu ganin ko waye ba sakamakon duniyar da ya ji tana juya masa take ya zube a wajen jini na zuba a jikinsa. Sagir ne ya saki wata dariya yana kallon Kamal tare da yi masa jinjina da hannu, shi ma alamar jinjinnar ya yi masa. Ya mike. "Ina fatan ya wulla lahira ko?" Kamal ya fadi maganar ya yin da ya mike yana kakkabe rigarsa. Sagir ne ya sunkuya ya kai hannunsa daidai saitin hancin Asadullah. Jin baya numfashi ne ya kalli Kamal tare da cewa. "Mun gama da shi, ka yi sauri mu bar wajen nan kada wani ya biyo ya tarar da mu." "To ya za mu yi da gawar?" Kamal ya tambaya cikin yanayin damuwa kamar zai yi kuka? "Ka yi hauka ne, ta ya ya zamu dauki gawar mu ce me?" Sagir ya bashi amsa yana hararar shi. "To ya za ka yi na san dole guard ɗin sa sun ga fitarku dole za'a tuhume ka." "Shi ya sa na ce maka kuɗaɗen nan za su ishe ni na bar ƙasar nan zuwa wata ƙasar na gina sabuwar rayuwa. Don haka za mu rabu a nan. Yanzu sauran aiki ya rage naka idan ka iya allonka ka wanke." Cikin damuwa Kamal ya ce yanzu wata ƙasar za ka tafi. Sai da ya bude murfin motarsa zai shiga sannan ya ce. "Ba zan iya fada maka in da zan tafi ba, domin hakan na iya zama hatsari a gare ni, na gode da taimakonka. Sai dai ka yi gaggawar barin wajen nan kada bincike ya biyo ta kanka. Hakan zai iya shafar siyasarka." Dawo wa ya yi ya ya ɗauke manya-manyan wuƙaken da suka soke su da shi yana cewa wannan ma hujja ce ba zan barta ba." Yana gama fadar haka ya shige motarsa ya bar wajen a guje. Cikin tashin hankali da Fargaba shi ma ya shiga motarsa ya bar wajen. Bayan mintuna biyar da barinsa wajen dai ga guard ɗin Asadullah sun ƙaraso wajen sakamakon hanyar da suka bi ba su ga alamar su hanyar ba. Burki suka ja da karfi suka fito a guje zuwa in da yake kwance. Baya motsi ga shi kwance cikin jini. Cikin tashin hankali suka ɗauke shi zuwa asibiti baya numfashi. Tsawon sati ɗaya bai farfaɗo ba, sai dai likitoci sun dukafa akansa. Sai dai sun tabbatar yana raye zai iya farfaɗo wa a kowane lokaci. Ga shi abokinsa da aka ce sun fita tare da Asad kafin aka tsince shi ba wanda ya san in da abokin yake ba. Ganin halin da yake ciki ne ya saka Dad da Uncle Adam suka matsa akan a fitar da shi ƙasar waje. Ba tare da ɓata lokaci ba aka shirya komai aka ɗauke shi zuwa ƙasar India. Dad, Mom, da uncle Adam suka tafi tare da shi. Cikin ikon Allah washegarin ranar da aka kai shi ya dawo cikin hayyacinsa. A ranar da ya dawo cikin hayyacinsa. A ranar Uncle Adam ya koma Nigeria. Mom da Dad suke tare da shi. Duk da ba zama wajensa suke yi ba kasancewar ma'aikatan asibitin ne ke kula da shi. Mom da Dad a hotel suke kwana washegari su dawo nan asibiti. Bayan sati biyu aka sallame su ya warware garau. Har lokacin ba wanda ya tambaye shi wanda ya yi masa wannan aika-aikar. Ganin yanayin da yake ciki kamar wanda ke cikin ruɗani. A ranar ne suka dawo ƙasar 9ja cikin farin ciki da annuri. Dad ya dinga kiran wayar Kamal don ya kira shi ya zo ya ɗauke su amma wayar a kashe take. Don haka ya kira Uncle Adam ya sanar da shi, Uncle Adam ba ya gari don haka ya kira ɗan sa Nasir ya sanar da shi. Take ya ɗauki key ɗin mota yana sanar da Mami in da zai je. Ganin haka ya saka Abida ta mike zurun za ta bishi. Maryam ma haka ta je za ta je ta tarbo masoyinta. Dakatar da su ya yi tare da cewa da mutum ɗaya zai tafi, sai ya yanke shawarar zuwa da Abida kasancewar ita ta fara yin magana. Maryam ya ce ta yi hakuri ta tarebe shi a gida. Ba da son ranta ba ta hakura Abida ta bishi cikin rawar jiki. Cike da farin ciki suka fita daga cikin ASADULLAH MANSION ɗin. Bayan sun ɗauko su akan hanyarsu ta dawowa ne Dad ke tambayar Nasir in da Kamal yake don wayarsa ba ta shiga. Ya ce juya dai sun ga juna da safe amma yau bai saka Kamal a idanunsa ba kenan. Mummy ta ce. "Ko yana kamfani ne tun da shi ke kula da kamfanonin ɗan uwansa." Ba mai Wannan amsar don haka suka yi shiru aka koma gida. Kowa ya ga Canji a wajen Asadullah don ko magana ba ya son yi. Wannan murmushi da ya saba yi a cikin ƴan uwansa duk babu ga kowa ya taru har da uncle Adam da iyalansa bangaren Dad ma kowa na nan hatta Hajiya Zulaihat wacce suke kira da Aunty ta zo duk da kasancewar ba ta shiga lamarin mutanen gidan musamman Asadullah. Har da ƴarta Suhailat sun zo. Wanka kawai Asadullah ya yi ya sanya riga JC da wando ya fito zuwa falon. Nan ya same su Dad ya tamabaye shi abinda ya faru da shi su waye suka so kashe shi. Nan ya basu labarin komai tun kiran da Sagir ya masa akan cewa Kamal na cikin mawuyacin hali har soka masa wukan da suka yi. Sai dai ya ce bayan Kamal ya soke shi ta gaba ya ji wani sukan ta baya ko da ya juyo bai iya gane ko waye ba, sai dai yana zargin Sagir ne, dan duk da yana kwance cikin jini yana jiyo maganganun da suke yi har sanda Sagir ya kai hannu sautin hancinsa don ya ji ko yana numfashi. Hakan ya saka ya ɗauke mumfanin na wasu daƙiƙu yadda za su yi zargin cewa Mutuwa ya yi. Har zuwa ɗaukar sa da guard ɗin sa suka yi ya sani akan hanyar zuwa asibiti ne bai sake sanin in da kansa yake ba sai da ya tsinci kansa a kasar India. Gabaɗaya firgici da tashin hankali ne ya ziyarci jama'ar wajen. Salati kawai suke yi yayin da ƴan matan ke kuka. Mum ce ta ɗauki wayarata ta kira jami'an tsaro akan su nemo Kamal duk in da yake a fadin garin nan. Kasancewar Kamla sanannen mutum ne kasancewarsa yana siyasa. Kuka Mom ke yi tana alwadai da halin ɗan nata. Tare da cewa sai ya girbi abun da ya shuka daga shi har abokin na sa. Uncle Adam ne ya tambaye Asad cewa wani abu ya taba shiga tsakaninsa da ɗan uwan nasa ne ko abokinsa. Nan ya sanar da su miliyoyin kuɗaɗen da suke diba daga kamfanin, wanda sanadiyar haka ya masu gargaɗi ba su daina ba ya dakatar da su. Nan aka dinga alwadai da halin na su musamman Kamal da suke uba ɗaya Asadullah a ce ya masa haka. A ranar aka kama Kama yana ƙoƙarin barin ƙasar a filin jirgin sama aka kama shi. Bayan jami'an tsaro sun tura su kotu an taru ana tuhumar Kamal akam laifin da ya aikata amma ya ce sam bai aikata abin da ake zargin sa da shi ba. An tambaye shi in da Sagir yake ya ce bai sani ba. alkali ya bayar da hutun Sa'a ɗaya kafin a cigaba da shari'ar. Nan ya nemi ganin Dad da iyalansa suka hadu a keɓance kasancewar Alkalin ma abokin Dad ne. Bayan sun haɗu Mom, Dad, uncle Adam, Aunty, Asadullah da Kamal. Kallonsu alkalin ya yi tare da yin gyara murya. "Hakika ban ji dadin yadda wannan lamarin ya kasance ba, Kamal ka amsa laifinka ba tare da ka wahalar da shari'a ba, yanayin da kake ciki ya isa ya tabbatar ba ka da gaskiya, an yi magana ka ce a kawo hujja saboda ka san kun binne duk wata hujja da za'a gane ku ko? To fa ka sani ina da hanyoyi da yawa da zan gane abun da kuke binnewa. Me ɗan uwanka ya yi maka haka?" Ya yi maganar yana kallon Asadullah wanda idanunsa suka yi jajir saboda tashin hankali. Kafin ya cigaba da cewa. "Ka masa laifinka zan maka sassauci a wurin Shari'a. Kasancewar wanda kuka yi yunkurin kashewa bai mutu ba yana nan da ransa. Ka ga ba hukuncin kisa zan yake maka ba ko?" Sai a lokacin Asadullah ya yi magana ya ce. "Ba zai taɓa fada ba yallaɓai, zaman gidan gyaran hali ne ya dace da shi kafin ya girbi abinda ya shuka. Butulu maci amana." Duk yadda aka kaɗa aka raya bai amsa laifinsa ba, kuma ya ki fadar in da Sagir yake. Tsabar ɓacin rai ya saka Mom ta shi ta wanke shi da mari tare da kai masa duka ta ko ina, sai da Uncle Adam ya ƙwace shi. Bayan awa ɗaya aka koma zaman Shari'a nan ma babu wani cigaba da aka samu. Daga nan Alkali ya bada umarnin akai Kamal gidan yari ajiyarsa za'ayi kafin a kamo Sagir a yanke masu hukunci daidai da abinda suka aikata. Daga nan ne Ka dauki Kamal aka kai shi gidan yari aka ajiye shi. Kallon Asadullah mutumin ya yi ba tare da ya cire facemask din ba ya kalli Asadullah dake cike da mamaki ya ce. "Duk da yana gidan yari amma ya fi ka rayuwar jin dad'i. Kalli yadda kake a kulle a daki kuma daure da sarƙa. Sai an baka abinci ko wane iri ne dole ka ci." Yana gama fadar haka ya fice ya bar Asadullah yana binsa da kallo. Har lokacin yana daure da sarƙa a hannunsa. Yana kai wa bakin ƙofa ya ya juyo yana cewa. "Ka san me ya janyo naka haka?" Murmushi ya yi sannan ya ce. "Yarda da mutane, da ba don lokaci ya kure maka ba da na baka shawarar cewa ka rage yarda da mutane, domin wani lokacin wadanda ka yarda da su sune za su iya cutar da kai." Yana gama fadar haka ya fice ya ja masa kofar ya rufe. _Ummi_ Tana fita daga part ɗin su ta nufo Babban falon gidan ta ga Hilal zaune yana danne-danne a system ɗinsa. Rai a ɓaci ta kalle shi ta tuna yadda Zahrah take kuka da kumburin da fuskarta ta yi sakamakon marukan da ya dinga sabga mata. Domin Ita uwa ce. "Hilal!" Ta kira sunansa rai a ɓace, ɗaga kai ya yi ya kalle ta ba tare da ya amsa ba. "Me Zahra ta yi maka da ka yi mata wannan dukar haka, to tura ta fara kai wa bango. Ba wannan ba ne karo na farko da ka fara dukan ta, ka sha azabtar mun ca yarinya da duka ko punishment har sumewa ta yi a dalilin ukubarka. Sannan duka da haka bai ishe ka ba saboda na kawar da kai ban taɓa nuna ɓacin rai akan abinda ake mata ba wai hakan na nufin ba na ƙaunar ƴata ba ne, kawaici nake yi maku amma tun da ba ku gane wa na gaji ya isa haka nan kada ka sake taɓa lafiyar Zahrah." Tana faɗin haka ya nufi part ɗin Papa bin ta ya yi da idanu, ita ma ba ta saka ran zai amsa mata ba duk da ta san ya ji ta sarai. Sai dai ya san cewa an ƙure ta ne don shi kansa shaida ne akan ƙiyayyar da ke yi wa Ummi da ƴaƴanta musamman Zahrah sun fi tsanar ta amma hakan bai saka Ummi ta nuna ɓacin rai ba sai yau. "Ni dai ba zan taɓa zuba idanu na bar ɗaya daga cikin ahalin gidan nan su yi duk abinda suka ga dama ba. Musamman Zahra dake da masoya ga shi yanzu har ta fara zubar da ciki, sannan a ce na ƙyale ta?" Ya faɗa yana girgiza kai tare da sarrafa na'urar dake gabansa. Wani tsanar Zahrah ne sabo ya dirar masa. "Zan yi maganin ƴar iskar yarinyar nan, ƙura ce ita lulluɓa da fatar akuya." *Maman Ihsan ce*✍️ da 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page3️⃣5️⃣ "Zan yi maganin ƴar iskar yarinyar nan, kura ce lulluɓe da fatar akuya. Da sallama Ummi ta ƙarasa part ɗin Papa. Dada ce a falo tana zuba kwadon zogale cikin bowl. Ta amsa sallamar tare da kallon Ummi ta ce. "Zahrah ne na ga kin zo da kanku?" Ta tambaye ne kasancewar ta san idan Ummi ta shigo da safe ta gaishe su ko wani abu ne sai dai ta aiko Zahra. Murmushi Ummi ta yi tare da cewa. "Wannan zuwan na wa ne Dada." Ajiye bowl ɗin da ta zuba zogale ta yi tare da cewa. "Tun da kin shigo shiga kitchen ki ɗauko plate ki zuba zogale, wancan mai murɗaɗɗen halin ke saka Ni yi masa zogalen nan, ga uwarsa ga masu aiki ya ce ba zai saka su ba na wa yake so." Gajeren murmushi Ummi ta yi don ta gane cewa Hilal Dada ke nufi tun da ta ce mai murɗaɗɗen halin. "Dada na gode ba zan ci zogale ba, wajen Papa na zo." Tana rufe baki sai ga Papa ya fito daga ɗakinsa. Ya kalli Ummi ya ce. "A'isha ke ce?" Ya yi magana yana gyara zaman medical glass dake saman karan hancinsa. "Eh ni ce." Ta fada kanta a sunkuye yayin da ta zube a saman guiwarta kamar mai rokon gafara. Zama Papa ya yi yana fuskantar ta ya ce. "A'isha lafiya dai ko?" Hawaye da ya taru a idanunta ta goge. "Papa wata alfarma nake nema a wajen ka, duk da na san abu ne mai matukar wahala a gare ka, amma dole na tamabaye ka shi don idan ba haka ba wata rana za'a wayi gari bakin ciki ya kashe ni." "Subhanallah me ya yi zafi haka?" Murmushin takaici ta yi tare da cewa. "Papa ina neman alfarma don Allah ka bar mu mu tashi daga gidan nan, mu nemi wani gidan mu zauna ni da yarana, ko ba komai za ku yi rayuwar farin ciki a cikin gidanmu." Shiru ya yi tare da yin nazarin kalamanta don tabbas ya san irin zaman da take yi a cikin gidan. Yadda ta zama sanayar ware a cikin matan gidan. Duk da ya so a ce ta ƙara hakuri na wani lokacin. "A'isha me kike son cewa ne?" "Sama da shekaru ashirin ina zaune a cikin gidan nan, duk da wariya da ƙiyayyar da ake nuna mani haka na kawar da kai. Sakamakon hakuri da juriya da na ga mijina na yi na zama da ƴan uwansa. Ni ma na ɗora wannan aniyar. Zuwa gaba bayan ba fara haihuwa na fahimci tsanar da ake mana ya shafi yaran da muka haifa. A lokacin hankali na ya tashi amma ganin ba zaman kowa nake yi a cikinsu ba, kuma ina samun kulawa daga wajan mijina da iyayensa ya sa na watsar da lamarin kowa na cigaba da mu'amalantar kowa duk da ko na masu magana ba sa amsawa ƴaƴansu ba sa mu'amala da ƴaƴana ban nuna damuwa ba na mayar da hankali wajen tarbiyyar yarana da cusa masu aƙida mai kyau a cikin zuciyarsu, ban koya masu tsanar danginsu ko ƴaƴan cikin gidan ba. Amma na lura sun fi tsanar Zahrah fiye da tsanar da suke muna da sauran ƴan uwanta. Na rasa me ta yi masu a rayuwa sun cusawa ƴaƴansu tsanar ƴaƴana kamar ba jini ɗaya suke ba. To yanzu har ya kai a yi wa Zahra ƙazafin zubar da ciki sannan ayi mata duka har da kumbura mata jiki, gaskiya hakurina ya fara ƙarewa ba zan iya ba." Shiru Papa ya yi na wani lokacin daga shi har Dada kowa ya kasa magana. Don sun san tsananin hakuri da kawaici irin na Ammi tun fa ta fara kawo ƙorafi tura ce ta kai bango. "Aisha." Papa ya kira sunanta. A hankali ta ɗago kai ta kalle shi cikin sanyin murya ta ce. "Na'am Papa." "Mijinki ya dade yana burin barin gidan nan saboda halin da ƴan uwansa ke nuna masa. Ni ne na hana shi tashi sakamakon ina ganin ni ne Ummul aba'isin wadan nan abubuwa dake faruwa a cikin zuri'ta gabaɗaya. Yanzu dai don Allah ina rokonki wannan karon in sha Allah za ki ga abinda zan yi. Ki ƙara hakuri in sha Allah komai ya kusa zuwa ƙarshe." Ya faɗa yana jinjina mata kai alamar tabbatar wa. Godiya ta yi masa sannan ta yi masu sallama za ta bar part ɗin. Har ta dawo babban falon gidan Hilal na nan in da ta bar shi. Tana wuce wa ya tashi ya shiga ɓangaren su Papa. Ciki-ciki ya yi sallama wanda shi kaɗai ya ji kayansa, don su ba wanda ya ji sallamarsa ballantana su amsa masa. Kuma shi ma bai sake yin magana ba, ƙarasa wa ya yi gaban Centre table ya dauki bowl ɗin da Dada ya haɗa masa kwaɗon zogale. Bai yi magana ba saboda ya san shi ta haɗawa. Har ya kai bakin ƙaofa ya ji Muryar Dada tana cewa. "Kai kam matarka tana da aiki mutum sai bakin hali. To uwarka ce ta dafa maka zogalen da za ka ɗauka babu sannu da aiki ballantana ka yi Mani godiya ko? To ƙaniyar gobe, don ba za ka saka ni aiki na yi ba." Ya juyo ya kalle ta dai ya wuce ba tare da ya ce mata komai ba. Kallon Papa ta yi tare da cewa. "Kana ganin wannan yaron jikan naka abun da yake mani ko? Ba za'a taɓa yi masa abu ya nuna ya ji dadi ba, kuma an alhalin abin da yake so ne aka yi masa shi, amma jin kai da mishkilanci irin nasa ba zai nuna ba. Yo ba don shi ba kaf jikokin gidan nan idan aka cire Zahrah ai ba wanda zan yi wa bauta. Don ba zai yiwa na yi wa ubansa shi ma na masa ba, sai dai shi ba zan iya ba." Papa kallonta ya yi yana murmushi don ya san irin son da take yi wa Hilal da Zahrah na daban ne a zuciyarta. Kamar yadda shi ma haka yake jin su a ransa. Gara Zahrah tana yawan shigewa Kakannin nata har kwana ɓangaren su tana yi wasu Kayanta ma suna ɓangaren kamannin na su ne sai in da ta ga dama za ta ci ta sha ko ta kwana. Duk da akasari ta fi kwana a bangaren Umminta. *Bayan sati ɗaya* Zahra ta warke ta warware ta cigaba da sabgarta. Kuma har lokacin ba ta sake saka Hilal a Idanunta ba. Don ko zuwa part ɗin Dada ba ta yi ballantana ta hadu da shi. Ranar Ummi ta gama abincin rana ta aiki Zahra ta kai wa Dada. Duk da kasancewar suna da masu aikin girki a gidan da suke abinci gabaɗaya amma Ummi ta kan yi abin Marmari da ta san tana so kitchen ɗin ta da ke part ɗin ta. Ɗanwake ta yi ta san Dada na so ta zuba don a kai mata. Zahara ta ɗauki abincin ta nufi part ɗin Dada don kai mata. Bayan ta kai mata ne ta samu tana aiki a kitchen tana dafa zogale, ganin Zahra ta zo sai ta saka ta daka mata yajin ƙuli. Bayan ta gama daka mata ta zubawa Zahra na ta ta zuba wani a wani bowl ta zuba yajin ƙuli da yanka su tumatir da albasa. Ya Mika wa Zahrah ta yi tare da cewa. "Kar bi ki kai wa Yayanku wannan a ɓangarensa." Rass gabanta ya faɗi. Ƙasa amsa ta yi ta tsaya tana kallon bowl ɗin. "Karbi mana ki je ki dawo ga naki." Tura baki ta yi tare da cewa. "Da ban shigo ba waye zai kai masa?" "To kin san ina da ciwon ƙafa ba iya hawa bene nake yi ba, kuma sauran yaran ba sa shigowa saboda wai ke nake so ba na son su duk da na san hudubar iyayensu ne saboda sun san kina zama a nan wajena. Dama shi ne idan ya shigo ya dauka amma tun da ga ki ba wanda zan aika don ya hana masu aiki zuwa part ɗin sa ballantana na aika su kai masa." "To ki jira ya zo ya ɗauka, ba zan je ya ci zalina ba tunda shi mugu ne ba imani a zuciyarsa." Mumrmushi Dada ta yi tare da cewa. "Tun da ba mahaukaci ba ne shi ai ba zai dake ki haka kawai ba." "Ni fa ba zan je part ɗin nan ba." "Ku ji mani ja'irar yarinya ko ubanki Salisu na aika bai isa ya faɗa Mani haka ba, ballantana uwarki A'isha." Ganin ida idanunta ya ciko da ƙwalla ta ce. "Ki yi hakuri je ki dawo ƴar albarka kin ji, ba na son kina ɓata rai je ki dawo in ba ki labari mai daɗi tatsoniya zan maki." Sanin Zahrah na son tatsuniya idan tana ba ta ta yi ta dariya ya saka ta ce haka. Nan da nan ta amsa har tana murmushi. _Hilal_ Yana komawa part ɗin sa ya tarar Alexandra ta kammala haɗa kayanta a trolley bag ɗin ta. Don yau za ta koma ƙasar US. Duk da burinta bai cika akan Hilal ba, don har yanzu sai dai ya yi romancing ɗin ta bai taɓa gigin yin sex da ita ba. Duk iya hanyoyin da za ta bi don ta ja hankalinsa ya kai in da take so ya kai ta kasa. Da sun yi zurfi wajen wasannin su da juna ya fahimci yana neman wuce iyaka take zai raba ta da jikinsa ya je ya sakarwa kansa ruwa. Wata rana ma sai ya sha magani. Ita mamakinsa take yi yadda zai ce ba zai yi sex da ita ba amma zai yi wasa da ita son ransa ya kuma sarrafa ta yadda ransa yake so. Kamar dai yadda ta ji labarinsa a wajen wasu ƴan matan da suke cewa shi ne kaɗai namijin da suka ga zai yi wasa da mace son ransa duk yadda ta so ya yi sex da ita ba ya yi sabanin sauran mazajen da idan sun fara ba su dakatawa sai sun kai ga biyan buƙatarsu ta hanyar sex da su. A lokacin ta ƙalubalance su akan cewa su ne ba su iya janyo hankalinsa ba. Ta ce ita za ta gwada basirar ta sai dai ita ma kamar su ta kasa. Yana shigowa ya ajiye wayoyinsa saman wani table dake cikin bedroom ɗin sa. Ƙarasawa ta yi gabansa ta ɗora hannunta a daddaɗen ƙirjinsa. Cikin harshen ƙasar Spain ta fara magana. "Ni zan tafi na yi kokarin zama a wannan ƙasar ta ku, saboda soyayyar da nake maka na mallaka maka komai na wa dukkanin jikina da kuka zuciyata. Amma kai ka kasa yi Mani haka. Sanin abinda take nufi ne ya saka shi share ta a hankali ta matso da fuskanta saitin na sa ta tallabo fuskarsa ta fara kissing lips ɗin sa. Take shi ma ya mayar mata da martanin abin da take masa zazzafar kiss yake yi mata wanda ta fara zaucewa. Ganin yadda ƙafarta ke rawa ya sa ya dauke ta ya dora akan doguwar kujera dake kusa da su. Cikin kiɗima ta zame yololuwar rigar dake jikinta tana kara shige masa. Boturan gaban rigarsa ta fara ballewa bai hana ta ba, bayan ta balle rigar ne ta yi ƙasa da hannu wajen wandonsa. Rike mata hannu ya yi tare da zare bakinsa daga nata ya ce. "Na sha fada maki ba na bukatar haka daga wajan ko wata ƴa mace ko?" "Ni ina ne ba ka sani ba ko ba ka ƙalla a jikina ba? Sai sai ne za ka ce ba wacce za ta kalle ka?" "Tun farkon haduwa ta da ke na fada maki haka don haka ki tsaya iya matsayin duk ranar da kika sake ƙoƙarin aikata Mani abinda irin haka to hannun da kira kokarin kai wa wajen zan karya. Kuma zan rabu da ke har abada." Cikin kuka ta fara roƙonsa da magiya. "Don Allah ka taimake ni ko sau daya ne ka yi sex da burina kenan." "Ban taɓa sex da kowane mace ba kuma ba zan fara akanki." Kasancewar ba komai a cikinta ya sa ta kalli jikinta tun daga kirji har zuwa ƙasanta, ita da take ja wa maza rai saboda jikinta amma shi yana mata wulakanci ta bar ƙasar ta da kowa ta zo wajensa amma ya kasa yi mata abinda take so. Ganin ta bude baki za ta yi magana ya sake hada bakinsu tare da aika mata zazzafar sumbatar da ke mantar da ita kanta. Yana yawo da hannayensa a jikinta yana shafa duk in da hannunsa ya taɓa. Har lokacin bakinsu na cikin na juna. Zahra ta shigo part ɗin don kawo masa zogalen da Dada ta aiko ta kawo masa. Sallama ta yi ba kowa a falo, ajiye wa ta yi a saman Centre table dake falonsa. Har za ta juya za ta za ta koma sai ta ji wani sauti kamar Muryar mace kamar kuka haka take ji . Gabanta ya fadi ita a tunaninta ko cikin yan matan gidan ne suka masa mafi yake punishing din ta. Sai ta yanke shawarar ta fada masa abinda Dada ta aiko ta kawo masa. Tura ƙofar ta yi tare da yin sallama. Abinda ta gani ne ya girmi tunaninta. Ƙara ta saki tare da cewa. "A'uzubillahi minash shaiɗani raƙumi!" Sai ta saki ƙarar da ya ankarar da su da zuwanta. Kallonta suka yi Idanunta a rintse. Ita Alexandra ba ta damu ba yayin da Hilal ya dafe goshi tare da cije leɓensa na ƙasa. Zahra cikin tashin hankali ta ruga a guje ta fice, ganin haka ya saka shi ma ya tashi ya mara mata baya a guje. *Maman Ihsan ce*✍️ [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: G*GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *Sanarwa* Wannan ƙirƙirerren labari ne ban rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali ya zo ɗaya to arashi ne. Mai kashe auren wawa. *Sadaukarwa.* Wannan shafin sadaukarwa ne ga JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATIO Allah ya ƙara mana ƙwarin guiwa. *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page3️⃣6️⃣ Zahrah cikin tashin hankali ta ruga a guje ta fice, ganin haka ya saka shi ma ya tashi ya mata mata baya. Abu ga dogon mutum taku uku ya sha gabanta wanda hakan ya saka ta faɗa jikinsa, da sauri ta ja baya tare da furta kalmar. "A'uzubillahi minash shaiɗani rajim" "Ke wa kike yi wa ta'awizi, waye sheɗanin?" Ɗaga kai ta yi ta kalle shi da sauri ta kau da kanta haɗi da rintse idanu. Sakamakon arba da ta yi da faffaɗan ƙirjinsa mai ɗauke da kwantaccen gashi. Wani banzan kallo ya watsa mata ya ce. "Uban me ya kawo ki part ɗina?" Bakinta har rawa yake yi ta ce. "Dada ce ta aiko ni na kawo maka kwaɗon zogale." "Dan rashin hankaki shi ne kika shigo mani har cikin bedroom ɗina? Nan bai isa ki ajiye ki koma ba, wato ke ga munafuka shi ya sa kika shiga kiga abinda nake aikatawa ko?" "Wallahi ba haka ba ne, na ji kamar muryar mace na kuka ne a bedroom ɗin shi ne na duba." "Da kika leƙa uban me kika gani?" Tuna yadda ta ga suna yi da Alexandra ta yi. Wani yawu mai ɗaci ta haɗiye ta kasa faɗa masa abinda ta ga suna yi. Wani tsawa ya daka mata tare da cewa. "Me kika gani!" "Ban ga komai ba, ni ba abinda na gani." Jinjina kai ya yi tare da cewa ",Gud" Kunnenta ya rike da ƙarfi wanda ya saka ta saki wata ƴar ƙara. "Kin ceci kanki da kika ce ba ki ga komai ba, dan idan har na ji makamancin wannan zancen a gidan nan sai na sauya maki kamanni. Kina rufe idanu tare da firgita kamar kin ga wani bakon al'amari, ke da kika san maza kika wani firgita kamar wacce ba ta san namiji ba, munafuka mai fuska biyu." Kalmar da ta yi mata zafi kenan a kalamansa wai ta san namiji, tabbas Aunty Laila da Momy ba za ta yafe masu ba akan ƙazafin da suka mata. Ga shi an fara jifarta da kalmar da ta tsana. Alhalin ba namijin da ta ya taba rike ko da yatsarta ne. Hawaye ne suka cika mata idanu. "Bar nan wajen tun ban illata ki ba ƴar iskar yarinya kawai " A guje ta bar wajen tana kuka. Tana saukowa daga downstairs ta hadu da Yaa Mansur da Yaa Faisal, Mansur ya yi dariya tare da cewa. "Na gode Yaa Hilal da kake cin uban yarinyar nan, wallahi na tsani ganinta a cikin gidan nan." Shi dai Faisal bai ce komai ba ya nufi part ɗin sa. Tsuki Mansur ya ja sannan shi ma ya wuce part ɗin sa. Tsayawa ta yi a kofar part ɗin sannan ta daidaita nutsuwarta sannan ta shiga part ɗin Dada. Hilal na komawa ya cewa Alexandra ta tashi ta kimtsa ya kai ta airport. Kai tsaye ya nufi bathroom wanda ganin haka ya saka Alexandra nufar bathroom ɗin. Ganin haka ya saka ya fasa shiga ya ce ta shiga ta fara yin wanka ta zo ta shirya su tafi. Tambayarsa ta yi tare da cewa. "Me ya saka ba ka yarda mu yi wanka tare ne?" Madadin ya ba ta amsa sai cewa ya yi . "Lokaci na tafiua idan kika yi wasa za ki rasa jirgi don kin san ba ya jira." Shigewa ta yi shi kuma ya juya wajen wayararsa jin tana ruri Jamilu ne abokinsa wanda ke Kaduna da suka sauka a gidansa Lokacin da Zahrah za su yi gasar karatun Alkur'ani mai girma. Ɗaga wayar ya yi tare da yin sallama bayan sun gaisa Jamilu ya ce. "Ya Zahrah take?" "Abun da ya sa ka kira ni kenan don ka tamabaye ni?" "Kusan haka." Ya bashi amsa yana dariya. Tsabar takaici katse wayarsa ya yi tare da ajiye wa. Yana ji yana kiransa amma bai sake ɗagawa ba. Bayan Alexandra ta fito ne shi ma ya shiga ya yi wanka. Cikin closet ɗin sa ya shiga ya shigar cikin riga JC red colour da wando baƙi. Sai ƙamshin daddaɗen turarensa ke tashi daga jikinsa.ita ma ya sanya wata doguwar riga wadda ta tsaya mata iya guiwarta gashinta ta sake shi ya zubo gadon bayanta sai takalmi me tsini dake ƙafarta. Ta ƙofar baya suka fice ta yadda ba wanda zai gansu. Kamar yadda ya shigo da ita ba wanda ya sani sai Zahrah haka yanzu ma ya fita da ita ba wanda ya sani, don gilas din motar baki ne ba wanda zai ga na cikin motar. Ko sojojinsa bai fita da su ba. _Asadullah_ Tsawon sati ɗaya kenan ba'ayi masa allurar ko maganin da zai saka shi cikin wani hali ba. Wannan mutumin ne ya sake shigowa dakin, waya ne kare a kunnensa yana magana. "Eh ga ni nan na shigo ranki ya daɗe, na gane kada ki damu." Kallo ɗaya Asad ya yi masa ya ɗauke kai daga kallonsa. "Sir Asadullah ya kake?" Banza ya yi da shi bai yi magana ba, don lokacin bakinsa a buɗe yake ba su rufe masa baki ba. "Ina son na yi magana da kai idan har kana son fita daga cikin wannan ƙangin da kake ciki dole ka bi umarnin mu." Zama ya yi a akan kujerar dake fuskantar Asad. "Akwai wasu takardun kanfanoni da ƙadarorinka wanda kakanka ya mallaka maka suna ina?" Wani banzan kallo ya masa ya ɗauke kai ba tare da ya bashi amsa ba. Sake tambayar sa ya yi a karo na biyu, nan ma shiru bai ce komai ba. Murmushi mutumin ya yi tare da cewa. "Matukar kana son cigaba da numfashi a doron duniya dole sai ka sadakar da dukiyarka don ka ceci rayuwarka, matukar ka ce ba za ka sadaukar da dukiyar ka ga wadanda suka saka ka a cikin wanan halin ba to za su iya kashe ka." Mumrmushin gefen baki ya yi tare da cewa "Kai karen farauta ka fadawa iyayen gidanka ba za su taɓa samun abun da suke nema daga gare ni ba" "Za ka mutu fa?" "Ba na tsoron mutuwa. Ka fadawa iyayen gidanka idan har kwanakin da Allah ya ɗibar Mani a duniya suka cika dole zan koma gare shi ko sakan ɗaya ba zan kara a duniya ba. Don haka idan mai kisa ya yi hakuri wanda za'a kashe zai mutu. Idan za su taru don su cutar da ni kan wani to ba za su cutar da ni ba dai idan Allah ya rubuta shi a kaina. Ka faɗa masu haka." Shiru ya yi yana kallon Asadullah kafin ya yi ajiyar zuciya ya ce. "Gaskiya ka faɗa amma sun yi nisa ba sa jin kira, shi ya sa na hore ka da ka aikata abinda suke so." "Wai da wani yare nake magana ne da ka kasa fahimta ta, na rantse da wanda raina yake a zatinsa ba zan taɓa ba su abinda suke so ba. Kuma ka faɗa masu sun yi kuskure, domin na san duk wanda ya saka ka wannan aikin na jikina ne na kusa da ni. Don bayan iyalan gidan nan ba wanda ya san cewa Kakana ne ya mallaka Mani wannan dukiyar ba ballantana a nemi sanin inda takardun suke." "Oho wannan ba matsala ta ba ne, sai abu na karshe da zan ba ka." Ya yi magana yana ciro wata takarda a aljihunsa. Wani takarda ya ciro ya nuna masa. "Za ka saka hannu a wannan takarda." Kasancewar hannunsa a daure suke ya kalli takardar, takarda ce ake so ya saka hannu a ciki wanda dole sai da saka hannunsa makudan kudade za su fita daga Kamfanin, don miliyoyin kuɗaɗe suke son cirewa sai da ya kalli takardar sannan ya yi dariya ya ce. "Ba zan taba sanya hannu ba." Kallomsa mutumin ya yi don ya fahimci Asad na da taurin kai, wato dama da ya kasa magana yake kallinsu saboda allurai da magunguna da suke dankara masa na dicewar gayyaci ne. Duk yadda ya dinga magana da Asadullah akan ya saka hannu ko za su rabu da shi ta ki. Don ya rufe masa baki kamar yadda suke masa haka ya fice bayan ya rufe kofar ta waje. _Dad_ Gabaɗaya ya shiga damuwa saboda rashin sanin halin da ɗan sa yake ciki. Ya sanar da jami'an tsaro ya saka malamai su yi ta addu'a. Yanzu ta kai gabadaya ba ya fita. Yau ma kamar kullun, da misalin karfe biyu na dare sai Safa da marwa yake yi a cikin ɗakinsa. Kasancewar ranar girkin Mom ce ya saka ita ke tare da da shi a wannan daren. Farkawa ta yi ta bude idanunta. "Alhaji wai har yanzu ba ka kwanta ba, ka ragewa wa kanka damuwa haka nan, ka ajiye komai ka t rame kamar wanda ya yi doguwar jinya. Ajiyar zuciya ya sauke tare da zama a bakin gadon. "Ba dole na shiga damuwa ba Zubaida. Ki duba abun nan. Ba yadda za'ayi Asadullah ya yi tafiya wata ƙasa ba tare da ya sanar da ni ba. Ko da tafiyar gaggawa ce ta kama shi kowa sai ya sanar da ni. Amma lokaci daya a ce wai ya yi tafiya bai sanar da kowa cewa zai yi tafiya ba, sannan kuma ba'a samun wayoyinsa. Ga shi ko da bai fita da bodyguard ɗinsa ba sai ya tafi da Sulaiman. Amma wannan karon Sulaiman ma bai san in da yake ba. Duk da ta tabbatar mana da cewa wai Asad bai bar gidan ba, da ya bar gidan da ya sani." Tashi zaune t yi yana nazarin kalaman Dad kafin ta ce. "Alhaji bar zancen Suleiman don waɗan nan mutanen ba su san aikinsu ba, idan bai bar gidan ba ta sama ya tashi ya fire?" "Ni ma abun da ke ɗaure Mani kai kenan." "Alhaji ina da magana ." Mai da hankali ya yi a kanta yana cewa "In a Jinki?" Gyara zama ya yi tare da cewa. "In jinki . "Ka san dai matar ka Zulaihat ba ƙaunar yaran gidan nan take yi ba. Musamman Asadullah ta tsane shi. Gaskiya ban yarda da ita ba." Ɓata fuska ya yi sannan ya ce "Kina nufin ita kike zargi ko me?" "Eh ita nake zargi da batar Asad saboda hujjojin da zan sanar da kai." *Kuyi hakuri da wannan* *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *Sanarwa* Wannan ƙirƙirerren labari ne ban yi shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali ya zo ɗaya to arashi, mai kashe auren wawa. *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page3️⃣7️⃣ "Eh ita nake zargi da ɓatar Asad saboda hujjojin da zan zan sanar da kai?" "Wace hujjar ce da ke?" "Ko ka manta cewa a gidan nan Asadullah ba ya da wani babbar makiyiyar da ta wuce Zulaihat. Tun da ta zo gidan nan ja taɓa ganin ta kula shi a matsayinta Na matar ubansa? Ko gaisuwa idan ya yi mata ciki-ciki take amsa masa ko agolar yarinyata ba ta bari ta yi mu'amala da Asad, ba ma shi kadai ba dukkan yaran gidan nan ba ta bari ta yi mu'amala da kowa. Don duk ranar da ta ganta tana shigewa yaran gidan nan sai ta duke ta . Wani irin mugun zama ne wannan?" Shiru ya yi yana kallon Hajiya Zubaida, don tabbas abun da ta fada gaskiya ne, amma wannan ba shi ne hujjar da za'a zarge ta ba tun da ba'a kama ta da wata hujjar da zai saka a zarge ta ba. "Kin ga wannan ba hujjar da zai saka a zarge ta ba ne, na san cewa ba ta shiga harkar kowa a gidan nan ba Asad kadai ne, duk da na yi iya yi na amma hakan bai sa ta canza ba. " "Shikenan Alhaji Allah ya bayyanar da gaskiya." "Amin" Ya amsa mata cikin sanyin murya. _Jidderh_ A hankali take tafiya har ta ƙarasa cikin ɗan ƙaramin gidansu. Bakinta ɗauke da sallama ta shiga cikin gidan. "Inna, Yaa Isah, da Aunty Sa'adatu sai ɗansu dake rike a hannun Isah yana wasa. Gabaɗayansu suka amsa mata sallamar. Zama ta yi bayan ta gaishe su da gida. Aunty Sa'adatu ce ta kalle ta tare da cewa. "Jidderh lafiya kike kuwa?" "Lafiyata lau Aunty Sa'adatu me kika gani?" "Na ga duk kin rame kwana biyun nan ne." Marairaice fuska ta yi tare da cewa. "Yaya ya zancen da na yi maka na ji ka shiru wallahi Sir Asadullah na cikin wani hali sosai yake buƙatar taimako." "Wai ke Jidderh ba na fada maki cewa ki fita daga harkar gidan nan ba.?" "Haba Yaya kar ka mance da halaccin da bawan Allahn nan da ya yi mana a rayuwa. Saboda shi ne fa har yanzu matarka da ɗanka suke raye ko ka mance ne?" "Matata da ɗana suna raye ne saboda Allah ya yi kwanansu bai ƙare ba. Ki ce dai shi ne sanadin da suke raye." "To na ji, yanzu ta wata hanyar kake ganin za ki kuɓutar da shi daga cikin wannan halin da yake ciki, kin ga dai gidan nan masu kuɗi ne sosai kuma in fada maki gaskiya ina tsoron shiga sabgar masu kudin nan nake yi. Don za su iya sakawa a ɓatar da mu matukar asirin mu ya tonu. Sannan kin ce yana cikin gidan kin bani labarin matakan tsaron dake cikin gidan ta ya ya zamu fitar da shi ba tare da kowa ya sani ba?" Shiru ta yi tana nazari kafin ta ce. "Zan yi tunani akan hakan sai na sanar da Kai, fatan za ka bani hadin kai.Matukar na ga hanyar za ta iya ɓullewa ina goyon bayan ki ɗari bisa ɗari ma kuwa." Inna dai tana jin su ba ta ce komai baz duk da can ƙasar zuviyarta tana fargabr halin da Autarta take kokarin jefa kanta a ciki. *Bayan sati ɗaya* A hankali take tafiya cikin nutsuwa tana fitowa daga department din take. Sanye take da hijabi Union color, hijabin ya sauka mata har ƙasa takaliminta mai tsini kawai ake hangowa wanda shi ma ya kasance Union color ne. Fuskarta sanye da farin glass sai facemask da ta sanya. Hannunta rike da wasu takardu ta nufi wajen motarta. Ta kai hannu za ta buɗe murfin motar kenan sai ta ga an bude mata, juyawa ta yi ta sauke idanunta akan fuskarsa yana sakar mata murmushi. "Aminiyata yau shi ne za ki wuce ko ganin juna ba mu yi ba.?" Mumrmushi ta yi tare da cewa. "Wallahi na gaji ne Aminin ya kake?" "Alhamdulillah ina lafiya ?" Kafin ta yi magana sai ga A'isha ƙawarta ta karaso wajen tana cewa. "Zahrah har za ki tafi gida ne,?" "Eh zan tafi tun da mun gama me zan tsaya jira?" Wani saurayi sanye da ƙananan kaya ya zuba hannayensa a Aljihu ya yi sallama yana ƙarasowa wajen. Gabaɗaya suka amsa masa yayin da Zahrah ta shige motarta. "Zahrah magana nake son mu yi da ke." Ta san zancen akan soyayya ne dai wanda ya dade yana bin ta tana masa yawo da hankali. Yau ne ya tura mata sakon idan sun tashi yana son ganinta. Ba ta masa reply ba. "Am dan Allah Mustapha ka yi hakuri Wallahi na gaji ne za mu iya yin magana gobe?" Sanyayyaen murmushinsa ya sakar mata wanda ya zame masa ɗabi'a ya ce. "Ba damuwa Allah ya kai mu goben." "Amin na gode." Ya bar wajen suka bishi da kallo. Amininta ya ce. "Aminiya wannan gayen akwai hankali da nutsuwa ki bashi dama kawai na san zai kula mana dake sosai." Ba ta ce komai ba ta yi wa motar key suka yi mata sallama akan sai sun yi waya. A hankali take driving cikin nutsuwa tana rera karatun Alqur'ani mai girma cikin zazzaƙar muryarta. Har ta karasa gidan ta yi horn maigadi ya bude mata ta shiga cikin gidan. A parking space ta yi parking ta kashe motar ta fito. Wata baƙuwar mota ta gani a cikin jerin motocin dake wajen parking ɗin. Da sallama a bakinta ta shiga yayin da take cire facemask da ke fuskarta, Ba kowa a babban falon gidan, glass din ma ta cire tare da zare shi. Hijabin ma ta cire shi tare da ajiye kayan daje hannunta akan kujerar da ya zauna mai zaman mutum biyu. Riga da siket ne a jinkinta ɗinkin ya ɗan kama ta duk da ba ta da ƙiba shape ɗinta ya fito sosai kasancewar tana da cikar ƙirji ga hips ma tana da shi masu ɗaukar hankalin. Tashi ta yi don ɗauko remote control dake samann Centre table. Daidai lokacin da Hilal da wani abokinsa mai suna Ammar suna saukowa daga upstairs. "Wow" Ammar ya faɗa yana zare idanunsa akan Zahrah.Hilal da yake danne-danne a waya bai kalle shi ba ballantana ya san me yake nufi. "Man waccen lu'ulu'un fa?' Sai a lokacin ya ɗaga kai ya kalli Zahra dake shirin zama tare da remote control a hannunta. Tsuke fuska ya yi kamar bai ji me yake cewa ba. "Sister ɗin ka ce ita?" Banza ya masa kamar bai ji shi ba. Zahra ta kamo tashar Sunnah TV. In da suka saka wa'azin Sheikh Imam Abubakar Ghana in da yake wa'azi akan matan da suke ba sa kula daazajenu da yada wata macen take magana da mijinta. Har Zahrah ta yi dariya wanda sai da dimple ɗin ta ya lotsa. Ba ta san sun ƙara so wajen ba sai gani ta yi mutum ya zo ya tsaya gabanta fuskarsa ɗauke da Murmushi. Ɗaga kai ta yi ta kalle shi. Da sauri ta ta janyo hijabinta ta saka. Sai a lokacin ta lura da Hilal dake tsaye a bayansa fuska babu walwala kamar ko da yaushe. "Beauty ya kike?" Ba ta tanka masa ba ta yi kamar ba ta gan shi ba. Murmushi ya yi tare da cewa. "Assalamu alaikum warahmatullah" Sai a lokacin ta buɗe baki ta ce. "Wa'alaiki Salam warahmatullah" "Zan iya zama?" Ba ta ce masa komai ba don da alama wajen Hilal ya zo. "Da alama rowar Muryar ake yi mani ko?" A ƙufule Hilal ya ce. "Look Ammar kar ka ɓata mani lokcin idan ba za ka tafi ba zan tafi na bar ka." Ammar ya zauna gefen Zahrah ko kula Hilal bai yi ba ya cigaba da cewa. "Beauty ya sunanki?" "Fatima Zahrah." Ta faɗa a hankali. "Wow nice name." Wayarta dake ajiye a gefenta ya ɗauka, cikin Sa'a kuwa ba password don haka ba tare da ɓata lokaci ba ya saka lambar wayarsa ya danna kira. Take kuwa kira ya shigo wayarsa, murmushi ya yi tare da cewa. "Sunana Ammar Umar Galadima. Ni haifaffen garin nan ne, sai dai ban tashi a garin nan ba sakamakon iyayena sun koma ƙasar London da zama, a can muka hadu da Yayanki da yake a can ya yi karatu. Allah ya haɗa jinina da shi sosai mun zama aminan juna. Yanzu haka ni direba ne." Sai a lokacin ta ɗaga kai ta kalle shi jin ya ce wai direba ne shi. Dariya ya yi tare da cewa. "Kina mamaki ne? Ina nufi pilot me wato Direban jirgin sama." Nan ma kallonsa ta yi. "Okay ko aikin ba ya burge ki ne, haka ma ko iyayena ba sa son aikin sun fi son na zama injiniya. Sai dai wannan aikin shi ne burina tun ina yaro nake sha'awa na zama Pilot idan na girma, idan bakya ra'ayi sai na bari cox dama ba na samun zama cikin ahalina kamar yadda ya dace." "Ni kuma meye damuwata da aikinka?" "Bayan mun yi aure yadda zan zauna dake na baki cikakkiyar kulawar da ya dace na tarairaye ki." "Aure kuma? Da ni?" "Ai tun da na ganki na ga matar aure." Kallonsa ta yi tabbas Ammar ƙyakyatawar mutum ne, yana da hasken fata sai dai ba sosai ba. Matsakaicin tsayi ne da shi fuskarsa mai ɗauke da saje da gemu wanda ya ƙawata kyakkyawar fuskarsa. "Ban taɓa ganinki a nan ba duk ba nan cika zuwa ƙasar ba ni ma, ke ƴar waye a cikin gidan nan, don na san Hilal sister ɗin sa da suke ciki ɗaya Maryam ce." Kasancewar ba ta son abun da zai hada ta da kowa na gidan kamar yadda Ummi ke ja mata kunne akan shiga lamurran al'ummar gidan, gashi abokin Hilal hakan na iya ba ta matsala." Tashi ta yi ba tare da ta yi magana ba ta dauki jakarta ta nufi part ɗin su. Duk yadda Ammar kar kiranta ba ta tsaya ba ta wuce ciki. Ajiyar zuciya ya sauke sai a lokacin ya lura ashe Hilal ma ba ya wajen ya fice. Yana shirin barin wajen sai ga Mummy, Umma da Aunty Laila sun shigo da alama daga unguwa suke. "A'a'a yau Ammar kai ne a ƙasar ta mu?" "Eh wallahi Mummy na zo ina tambayarku ya ce kun je biki." Nan ya gaida su cikin girmamawa suka amsa cike da jin dad'i don sun san Ammar da hilal sosai. Don ko su idan sun tafi ƙasar London iyayen Ammar ba sa bari su sauka a hotel sai dai su sauka a gidansu. Kuma haka za su yi masu karamci har su kammala abun da za su yi su dawo . Kuma duk saboda amintar dake tsakanin Hilal da Ammar. Aunty Laila ta ce. "Ammar da alama ba ka ci abinci ba ko?" "Aunty na ci abinci na yi wanka dama za mu fita ne tare da Hilal." Mummy ce ya yi saurin cewa "Ina Hilal ɗin yake ne?" "Yanzu ya fira zan ce na same shi." Yana fadar haka ya fita da sauri yayin da su kuma kowa ya nufi part ɗin sa. " Ammar na fita ya tarar da wani soja ya nufo shi yana sanar shi shi sakin ogansa. Akan cewa idan ya fito sojan ya dauko shi ya kai shi inda zai tafi. Cikin takaicin halin Hilal ya sa Ammar ya koma ciki ya fasa fitar da za su yi. Addu'a yake a zuciyarsa Allah ya saka ya sake tozali da sanyin idanunsa. Ba kowa a Babban dakin gidan. Zama ya yi sannan ya lalubo lambar Zahra da y samu. Wayarsa ya lalubo ya dannawa Zahrah kira, har sau uku yana kira ba ta daga ba. Wayarsa ta soma ruri yana dubawa ya ga sweet Mom. Cikin farin ciki ya ce. " Mom albishirinki." Dariya ta yi tare da cewa. "Ko gaisawa ba mu yi ba kana Mani albishir, kalli wannan babban albishir ne. ina jin ka" "Mom Allah ya amshi addu'arjki yau na ga yarinyar da ta kwanta Mani." Cikin farin ciki ta yi kabbarta tare da cewa. "Alhamdulillah wata mai sa'ar ce haka?" "Mom ni na yi Sa'a sai jin gan ta." "Ƴar gidan waye?" "Mom familyn Tafarki ce" "Alhamdulillah ta zo gidan sauki ai." "Dad dinsa dake gefe sai farin ciki yake yi . Ƙannensa mata biyu da Fareeda da Fareesha sai murna suke har da tsalle. Farida ta karbi wayar tare da cewa "Yaya Please ka tura Mani pics din ta." Nan suka dinga murna kamar wacce an ce an bashi ita . Dad dinsa ya tabbatar masa zai zo ya samu Papa da kansa ya nema masa auren yarinyar. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *Sanarwa* Wannan ƙirƙirerren labari ne ban yi shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali ya zo ɗaya to arashi, mai kashe auren wawa. *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page3️⃣8️⃣ Dad ɗin sa ya tabbatar masa zai zo ya samu Papa da kansa ya nema masa auren yarinyar. *Washegari* Kasancewar weekend ne Zahrah na gidan ba ta je school ba. Kuma dama ba ta cika zama a babban dinning table na gidan da kowa ke zama don cin abinci ba. Don dama dokar Papa ne tare ake cin abinci a gidan gabaɗaya bayan masu aiki sun kammala yin girki. Zahrah kasancewar a ɓangaren Dada ta kwana don haka ta shiga kitchen don hada wa kanta breakfast. Don ta ce yau fankasau take son yi. Don haka tun da asuba bayan ta gama azkar ɗin safiya ta shiga ta gaida Papa da Dada. Kitchen ta nufa ta kwaɓa fulawa ta ɗan zuba gishiri da sugar da Baking powder ta rufe. Sannan ta fara shirin yin miyar taushe. _Hilal_ Yana tashi da safe ya nufi ɗakin motsa jikinsa. Kasancewar tare da Ammar suka kwana a ɗakinsa. Ammar kam yana tashi ya yi ya yi wanka bayan ya fito ne ya tsane jikinsa sannan ya shafa man shafawar Hilal ya kuma saka kayan Hilal ɗin. Turarensa ya shafa sannan ya saka takalmi ya ɗauki wayoyinsa ya sauka zuwa downstairs. Kamar yadda Papa ya wajabta wa kowa na gidan yin breakfast a tare da juna sai dai wanda baya nan ya fita. Duk da hakan bai saka an samu jituwa a tsakanin Abbi da mutanen gidan ba. Gabaɗaya jama'ar gidan sun taru a dinning area. Dada da Zahrah ce ba sa Wajen. Papa, Dady, Abba, Abbi, Mummy, Umma Ummi, Aunty Laila. Haka yara mazan gidan ma Hilal ne kawai ba ya wajen amma tun daga kan Mansur, Mahmud, Faisal, Sadik duk suna wajen. Haka ƴan matan gidan ma. Nabeela, Kausar, Nadiya da Maryam duk sun hallara kowa na cin abinda ransa ke so. Ammar ne ya karaso wajen yana tafiya cikin halittarsa ta nutsuwa da cikar kamala. "Assalamu alaikum warahmatullah" Ƙamshin turaren Hilal da suka ji ne sun ɗauka shi ne, amma sai suka ji saɓanin abinda suka yi zato wato sallamar da Ammar ya masu. Sabanin Hilal da idan ba wanda ya kalli fuskarsa ba ba zai san ya yi sallamar ba. Gabaɗaya ba wanda bai san Ammar ba a cikinsu, don haka Papa da bai san cewa ya iso kasar ba yake cewa. "A yau mutane Ingila ne a kasar ta mu?" Murmushi Ammar ya tare da sunkuyawa cikin girmamawa ya gaida Papa, ya amsa masa cikin jin dadi tare da tambayarsa iyayensa. Ya amsa da suna lafiya. Ya sake cewa yaushe ka ƙasar ne?" "Jiya mun shiga ɓangaren ka ba ka nan." "Eh to haka ne gaskiya juya sai dare na dawo." Nan ya gaida su Dady da Abba da Abbi. Suka masa masa. Sannan ya gaida su Mummy Umma da Aunty Laila. Lokacin da ya sauke idanunsa kan Ummi sai ya ga tsananin kamanninta da Zahrah kamar ta yi kaki ta ajiye. Sai ya gaishe ta cikin girmamawa ta amsa masa cikin sakin fuska da walwala duk da ba ta san shi ba. Don ita ba ta cika zama main falon gidan ba ballantana ta san masu shige da ficen da ke zuwa gidan. Ko fitowa cin abinci sai Papa na. nan take fitowa wani lokaci za ta yi girkin ta a kitchen dake part ɗin ta ne. Nan su Kausar suka shiga gaida shi cikin kauɗi. Ya amsa masu ba yabo ba fallasa. Shi dai bai ga Zahra ba kuma ba halin ya tambaya. Don haka ya kalli Papa ya ce. "Ina Dada take?" "Dada tana can ba ta fito ba ita da Zahrah wai can za su yi breakfast." Jin an ce ita da Zahra ya fara tunanin ganin Zahrah. "Son zo ka zauna mu yi breakfast tare mana. Duk da an kai maku a part ɗin abokinka, amma idan ka biye masa ba yanzu za ka ci abinci ba sai rana ta fito." Murmushi ya yi tare da cewa. "Bari na je na gaida Dada." Yana gama fadar haka ya nufi part ɗin Dada. Da sallama a bakinsa ya shiga falon, ta amsa tare da yi masa sannu da zuwa. Tana zaune a falo ita kaɗai ta kalle shi tare da washe baki ta ce "Ammar kai ne?" "Eh ni ne Dada?" Ya karasa ya gida ita cikin girmamawa. Ta amsa tare da cewa. "Ka ga mutanen Turai." Zama ya yi yana addu'a Allah ya sa Zahra ta fito ya ganta. Bai gama zancen zuci ba sai ga ta ta fito daga ɗakinta ta nufi kitchen. Tana tafiya a hankali ta nufi matattakalar stage ɗin tana sanye da wando pallazo purple colour sai shirt wanda shi ma purple ne. Wato up and down ne a jikinta. Kanta babu ɗankwali sai gashinta da ta yi parking a tsakiyar kanta ya sauka a gadon bayanta sai lilo yake yi. powder kawai ta shafa sai lips glow pink lips ɗin ta sai shinning yake yi. Flasks din da ta zuba fankasau ta jera a babban faranti da farfesun kayan cikin da ta yi ta jera komai ta sannan ta ɗauki don zuwa wajen Dada su yi breakfast tare. Sanyayyaen ƙamshin turerenta ke tashi daga jikinta. Tun fitowarta yake kallonta kamar zai cinye ta. Ita ko sam ba ta lura da shi ba, tafiyarta kawai take yi cikin nutsuwa. Ta ƙaraso ta ajiye darantin a gaban Dada, ta zauna suna fuskantar juna fuskarra ɗauke da Murmushi ta ce "Na san yawunki ta tsinke kin Kagara ki ci girkina ko?" Taɓe baki Dada ta yi tare da cewa. "Ai dole yarinya kin ɗauko hannun Umminki a wajen zaƙin girki." Mumrmushin jin dadi ta yi, jin Muryar Dada ta yi tana cewa. "Ga Yayanki nan ba ki gaishe shi ba " Sai da gabanta ya faɗi sakamakon ƙamshin turaren Hilal da ta ji yo, don ƙamshin girkinta ya hana ta ji ƙamshin sai yanzu. Tura baki ta yi don ko ta gaishe shi ta san ba amsawa yake yi ba. Don haka ta share kamar ba ta ji ba. Amma sai ta juya da sauri sakamakon jin wani muryar Ammar. Idanunta ta sauke cikin nasa yana sakar mata sanyayyar murmushinsa. Da hanzarin ta koma dakinta dake nan part ɗin. Ba jimawa ta fito sanye da hijabi iya guiwarta ya tsaya mata. Cikin sanyin murya ta ce. "Ina kwana?" "Lafiya lau ya kike?" "Alhamdulillah." Ta furta yayin da take bude flasks ɗin funkasau. Tare ta zuba masu ita da Dada kamar yadda suka saba ci . Ta zuba masu miyar taushe da ya ji naman kan rago. Kallonta Dada ta yi tare da cewa. "Ki zubawa Yayanki na shi mana." "Ba musu ta tashi ta koma kitchen ɗin ta ɗauko plate ta zo ta zuba masa. Ruwan shayin da ta dafa wanda ya ji kayan ƙamshi ta zuba na su shi ma ta zuba masa bayan ta haɗa madara da milo. Sai biredi ta jera masa a gabansa. A hankali ya furta . "Na gode Beauty." "Ko ba ka ra'ayin cin wannan akwai kaloli abinci a can babban falon ka fadi abinda kake so sai a kawo maka?" "Dada waɗan nan ma sun isa." Daga haka ta juya wajan Dada suna cigaba da yin kalaci yayin da Ammar ke ta santin girki. Bayan Dada ta ƙoshi ta tashi don zuwa ta yi wanka. Ya saura daga Ammar sai Zahrah. A falon. "Beauty." Ɗaga kai ta yi ta kalle shi "Me ya saka ba ki ɗauki wayata ba?" Shiru ba ta bashi amsa ba wanda hakan ya saka shi cewa. Ba na da lokaci gobe zan koma saboda ina da wasu zirga-zirga da zan yi. Don Allah kafin na wuce in son jin ra'ayin ki ina fatan zan samu girbi a cikin birnin zuciyarki ko tauraruwar mata." Shiru ba ta ce komai ba, ya cigaba da cewa. "Idan ba ki mani magana ba yanzun nan zan yi maki kuka a wajen nan." Jin haka ya saka ta ɗaga kai ta kalle shi wai zai yi kuka kamar wani ƙaramin yaro. Ba ta san lokacin da dariya ya suɓuce mata ba har sai da dimple ta suka motsa. Sanye yake cikin ƙananan kaya riga ja da wando ɓaki Kyakkyawar ƙiransa na mazantaka da ƙuruciya sun bayyana . Turo ƙofar ya yi tare da yin sallama can ƙasan maƙoshi wanda shi kaɗai ya ji kayansa. Idanunsa suka sauka akan Ammar da Zahrah da suke yi wa juna dariya. Wanda har sai da fararen haƙoranta suka bayyana, ga dimple ɗin ta ya lotsa sai dariya take masa. Shi ma kallonta yake yi ganin yadda take dariya daga cewa zai yi kuka. Wani kallo Hilal ke bin su da shi fuskarsa ba sassauci. Zahrah dake facing ƙofar ta ga shigowar Hilal ɗin. Gabanta ne ya fadi sakamakon ganin fuskarsa da ya ba ta tsoro kamar wanda zai yi aman wuta. *Ku yi hakuri da wannan*🙏🏻 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page3️⃣9️⃣ Wani kallo Hilal ke bin su da shi fuskarsa ba sassauci. Zahrah dake facing ƙofar ta ga shigowar Hilal ɗin . Gabanta ne ya fadi sakamakon ganin fuskarsa da ya ba ta tsoro kamar wanda zai yi aman wuta. Kasancewar Ammar yana kallonta ne ya sa ya mai da hankali ga in da yake kallo. Bai damu da yanayin fuskar Hilal ɗin ba don ya san dama shi ba mutum mai fara'a ba ne. Ƙarasowa ya yi ya zauna kan ɗaya daga cikin kujerun falon. "Man ka shigo?" Ya faɗa yana kallon Zahrah. Wacce ta sunkuyar da kanta tana juya zoben azurfan dake yatsarta. "Eh na fito ya gajiyan hanya?" Murmushi ya yi tare da cewa. "Ai ba gajiya ga mutum da ya saba zirga-zirga." Zahrah cikin sanyin muryarta ta gaida Hilal duk da ta san ba amsawa zai yi ba. Kuma bai amsar ba. Dada ce ta dawo falon Idanunta a kan Zahrah da ta ji tana dariya. "Ke kuma ina ta jin Muryar ki kina dariya keke baki dariya ne.' Kallon Ammar ta yi ta ga yana kallonta yana murmushi. "Ko ke da Ammar ne ya saka ki dariya haka, don idan ba shi ba kam ban ga abun da zai saka ki dariya." "Kai kuma yaushe ka shigo?" "Bai ba ta amsa ba ya ce. "Barka da safiya." "Yauwa barka dai ina fatan kana lafiya ya aiki?" Ita ma bai amsa mata ba. Zahrah ta kasa ɗaga kai saboda tasirin da kaifin idanunsa suke yi a jikinta. Tana jin tasirin Kaifin idanunsa a cikinta. Ɗagowa ta yi ta kalle shi sai ya galla mata harara . Sauke Idanunta ta yi sannan ta ɗauki kofin shayin dake gabanta ta fara sha. Dada ce ta kalli Ammar ta ce. "Wai kai yaushe za ka yi aure ne, kar dai ka biyewa wa wannan abokin na ka da ya kusa zama tuzuru." Dariya sosai Ammar ya yi tare da cewa. "Ba zan biye masa ba Dada, ni idan har kun amince mani ma a cikin satin nan zan angwance." Cikin rashin fahimta ta ce. "Ni kuma Ammar?" "Ƙwarari kuwa Kakus, idan za ki bani Wannan jikar taki." Zahrah dake shan shayi har sai da ta ƙwarewa ta yi, cikin tashin hankali Ammar ya mika mata ruwa shi da Dada sai jera mata sannu suke yi. Shi ko gogan yana hakimce kan kujera ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yana latsa wayansa. Dada ce take ɗan bubbuga bayanta tana shafawa alamar rarrashi. Bayan tarin ya lafa ne Dada ta ce "Ammar wannan ai ba hurumina ba ne, ka nemi soyayyar Zahrah idan ta amince ni ba ni da matsala sai ka nemi Papa. Duk da ba lallai ka samu hadin kansa ba don ban san me yake nufi da Zahrah ba. Lokacin da ta ci gasar karatun Kur'ani ta da ka gabatar na san kila ka sani ko?" "Na dai ji labarin ƴar gidan nan ce ban ma san ita ba ce." Murmushi ya yi tare da cewa. "Allah akbar ashe hafizan alƙur'arni ce, tabbas na san na zaɓawa ƴaƴana uwa ta gari." Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa. "Dada kina nufin Papa ba zai yarda ba ne?" "Ban san ya zai karbi zancen ka ba, amma a lokacin mutane manyan ƙasar nan sun zo nemam auren Zahrah wasu ƴaƴansu suka zo nema wa auren wasu kuma kansu suka zo nema wa. Kuma manyan mutane masu daraja da ba sa da aibu. Kai har ƴaƴan Gwamnoni da minister har kan manyan Mallamai amma Kakanta ya basu haƙuri don bai ma bari sun ga Zahrah ba. Sai ya ce tana da wanda za ta aura. Sai dai gaskiya ban sani ba ko a cikin samarin ta dake sonta ne. Don da wuya ta fita ba ta yi samu wanda ya nuna yana son ta ba. Hakan ya saka take fita da niƙab ko facemask." Jinjina kai Ammar ya yi tare da cewa. "Hakan ya mani." Dada ta ce. "Gaskiya sai dai ka nemi soyayyar Zahrah idan ta amince na tabbatar Papa ba zai yi mata dole ba zai bari ta zabi son ranta ne." Jinjina kai ya yi tare da cewa. "In sha Allah Dadarmu zan yi yadda kika ce." Kallon Zahrah ya yi tare da cewa. ",Yau nake son komawa dama kwana ɗaya na zo da niyyar yi. Ban san ina ne part ɗin na ku ba, ki zo ki yi Mani jagora ina son na gaida su..." Yadda ta zaro idanu ta rike baki ne ya saka bai karasa ba ya yi dariya. "Ina son gabatar masu da kaina ne kafin na wuce. Na san yanzu kowa ya bar dinning area . Kallonsa ta yi wato tun bai ji ra'ayinta ba har yana shirin gabatar da kansa ga su Abbi Shiru ta yi masa ba ta motsa ba, ya cigaba da cewa. "Please beauty ganin mu tare zai saka su san cewa saboda ke na je gaishe su " "Tura baki ta yi a hankali ta ce ka je saboda Allah mana." Hilal ne kawai ya ji me ta ce saboda yana da ƙarfin ji, duk yadda aka yi magana a hankali yana ji ko gulmarsa ba'ayi yana wajen. Duk da idanunsa na kan waya amma duk maganar da suke yi yana jin su. Ammar ya kalli Hilal ya ce. "Man kai ya kamata ma na kama ƙafa da kai babban Yaya, ka raka ni sai ka gabatar masu da kaina." Bai tanka ba ganin haka Ammar ya ce. "Wannan bahagon mutum ba in da zai je na ga alama tun da bai san ciwon so ba, sai dai ka ji na yi aure na barka a tuzuru don ko zancen ba ka yi." Ganin bai tanka shi ba ya kalli Zahra ya ce. "Beauty." Ita kunya ce ma ya bata tana don tashi ta bar wajen ta kasa. ",Bana da isasshen lokaci Please ko ba za ku shiga ba ki tsaya daga main falo ki nuna mani zan shiga ni kaɗai." Ganin ko motsi ba ta yi ba Dada ta ce. "Ba na son gulma ba tun ina ciki nake jiyo Muryarki kina ta masa dariya ba kuma Fira. Yanzu ki nuna masa waje ne kike wani ñoƙe-noƙe?" Tashi ya yi ya yi gaba ita ma ta mike za ta bi bayansa. Tana kawowa saitin kujerar da Hilal ke zaune ya sanya ƙafarsa ya harɗe mata ƙafa ta faɗi ƙasa. Ƙara ta saki ya sa yatsarsa ya ɗalle mata baki ta saka kuka." Dada ta ɗauka faɗuwa ce ta yi sai salati take yi tare da tambayarta garin ya ta fadi haka. Ammar ne ya yi wa Hilal wani kallon mamaki don ya ga sanda ya harɗe ta sannan ya bugar mata baki. Sai dai bai san me ya saka ya yi mata haka ba ko ta masa wani laifi ne. Duk da ko da laifin ta yi masa ya dace ya hukunta ta irin wannan faduwar idan ya zo da tsautsayi za ta iya karyewa. *Prison/Gidan yaro* Gabaɗaya ya kasa zaune ya kasa tsaye. Sai zirga-zirga yake yi a ɗakin. Ya rasa me yake masa daɗi. Ya so ya haɗa hannu da ɗan ta'addan dake cikin gidan yari. Sanin hakan ba zai amfane shi da komai ba ne ya saka ya fita harkarsa. Wayarsa dake kan gadon ya ɗauka, tare da lalubo wata lamba ya danna kira. Bugu ɗaya aka ɗaga. "Ka zo." Shi ne iya abinda ya ce sannan ya katse kiran wayar ya ajiye. Ba'a fi mintuna biyar ba sai ga wani ma'ikacin gidan yarin ya shigo. "Tura mani account number ka?" Take mutumin ya faɗa masa in da ta yi masa transfer na kuɗi. "Ina son a kawo mani katon ɗin ruwa don ruwan sha na sun ƙare. Ina son sabulu da omo da dai abubuwan da ka siyo Mani last time. Sauran canjin sai ka rike." Godiya mutumin ya yi masa tare da yi masa addu'a. _Jidderh_ Bayan ta shirya zuwa wajen aiki ta biya ta wajen Yayanta dan su karasa maganar da suka yi da shi. Bayan ta yi sallama a kofar ɗakin ya ba ta izinin shiga ne ta shiga. Yana zaune a bakin gado ta gaishe shi. Ya amsa tare da cewa. "Har kin fito za ki wuce aikin kenan?" "Eh Yaya dama ina son ne na ji ya ka ji shawara da na kawo?" "Ban ƙi ta ki ba Jidderh kamar yadda kika ce za ki Sanarwa amintaccen bodyguard ɗin sa in da aka tsare shi a cikin gidan kina ganin ba zai iya yiwuwa da shi aka haɗa baki ba?" Shiru ta yi tana nazari kafin ta ce "Na san zai ya aminta da shi kuma shi ne wanda kai tsaye yake iya shiga duk in da yake a cikin gidan." "Idan da hadin bakinsa a ciki kika tunkare sa da zancen fa za ki saka kanki a matsala ne?" "To sai dai idan jami'an tsaro zan fadawa zancen." "Tab kina ganin jami'an tsaro za su iya shiga cikin irin wannan gidan ne kai tsaye su fara bincike ba tare da sun nemi izinin mai gidan ba ko sun sanar da su shi abinda ke tafe da su?" Shiru ta yi cikin ɓacin rai ta ce. "To ya kake so na yi wallahi ba zan iya barinsa cikin wannan halin ba." "Kuma duk hanyar da kike ɗaukowa ba mai ɓullewa ba ce." Ganin duk sanda ta kawo shawara kowace iri ce baya bata goyon baya ya saka ta tashi tana tuninin hanyar da za ta bi." Rai a jagule ta nufi ƙofar fita ko sallama ba ta yi wa mutanen gidan ba. Keke napep ta tare ta shiga mutane biyu ne a ciki ita ce ta ukun su. Sai da aka sauke su ya kai ta har ƙofar gate ɗin *Asadullah mansion* ɗin tana sauka ta biya mai napep kuɗinsa ta nufi gate ɗin. Security na ganinta suka bude mata gate ta shiga. Kai tsaye main house din ta nufa. Mummy ta tarar a Falo, ta gaishe ta ta amsa mata ba yabo ba fallasa. Shiga ciki ta yi don gudanar da aikinta. Don sauran ma'aikatan gidan nan suke kwana ita kadai ce take zuwa daga waje. Da Mom ta nuna in dai zata dinga fita za'a sallame ta, Asadullah ne ya tsaya akan cewa a barta sannan Mom ta bar ta. Jidderh ta juya ta kallo Mom kamar ta sanar da ita cewa ga in da Asadullahi yake sai ta fasa sakamakon ta tuna Mama mai aiki ta taɓa sanar da ita cewar Mahaifiyar Asadullah ta rasu. Hakan ya durƙusar da yinƙirinta. Don a wannan gabar ba ta son ta aikata abinda zai iya janyo wa Asadullah ya shiga wani hali. Sai dai yadda gidan nan ke da matakan tsaro ta ya ya za ta iya fitar da shi ba tare de kowa ya ganta ba. Ga shi baya cikin hayyacinsa ballantana ta ji ta bakinsa ya bata mafita. Abun da Jidderh ba ta sani ba shi ne an daina yi wa Asadullah alluran gusar da hankali da magunguna da za su yi masa illah. Saboda yanzu an zo gabar da suke so. A hanzarce ta gama ayyukan da take yi sannan ta fara tunanin hanyar bi wajen da za ta je ɓangaren da aka ajiye Asadullah. Har za ta bi ta ƙofar kitchen ta fice sai ta ji Muryar Hajiya Zulaihat wacce suke kira Aunty ta ce. "Ke ina za ki je kike wani sanɗa?" A firgice ta juyo don ta tsorata jikinta har rawa yake yi . "Kallo ɗaya ta yi mata ta fahimci ba ta da gaskiya. Don haka ta sake tamabayarta a karo na biyu. "Amm uhm amm zan je wajen Mama ne na taya ta aiki?" "Wace Mama? Mama da ta gama aikinta ta fita kitchen." Dawowa ta yi tana sunkuyar da kai ta nufi ɗakin masu aikin gidan. Da kallo Aunty ta bita kafin ta ce . "Zan gano ki ne yarinya." Bayan kamar mintuna talatin ne ta sake fitowa cikin ikon Allah har ta bar sashen na wamdabya ganta. Ta baya ta zagaya har ta isa bangaren da aka ajiye Asadullah. Sai dai ƙofar a datse. Glass din window ta zuge sai suka hada idanu. Gabanta ta ji ya fadi rass. Ganin kallon da yake yi mata. Don duk ganin da take masa cikin wani yanayi yake amma yau ga shi zaune yana kallonta sai dai an daure masa hannaye da ƙafa suka an rufe masa baki da salatef. Ƙwalla ne suka cika Idanunta har suka gangaro. Ga mamakinta sai ta ga yana girgiza mata kai alamar ta daina kuka. "Yallaɓai kana ji na kana gani na?" Kai ya jinjina mata alamar eh. Farin ciki ya saka ta saki murmushi tana goge hawayen dake Idanunta. "Yallaɓai ta ya zan iya fitar da kai ko na je na sanar da Mom kana nan?" Kai ya girgiza mata alamar "Aunty fa na sanar da ita?" Nan ma kai ya girgiza mata alamar a'a. "Na sanar wa Dad?" Nan ma kai ya girgiza. "Na sanar da amintaccen bodyguard ɗin ka?" Sai a lokacin ya ɗaga mata kai alamar eh. A guje ta bar wajen tana murmushin jin dad'i. Tana tsaka da gudu ta ji an finciko mata hijabi ta baya wanda har ya shaƙe mata wuya. Kafin ta ankare sai ta ji ta faɗi ƙasa tim. Rai a ɓace Ammar ya kalli Hilal da ya tabbatar shi ya harɗe ƙafar Zahrah ta faɗi. Haba Man don Allah me ..." Ɗaga masa hannu ya yi alamar dakatarwa. Dada da a tunaninta Zahra Faɗuwa ta yi ne ta kama ta daƙyar, ta iya tashi ga ƙafarsa zafi ga kabbnta da ya ɗilla da yatsarsa sai zugi suke mata. Hawaye ne kawai take tsiyayarwa, don ita kanta ba ta san me ya yarda ita ba ta ɗauka ko da plate dake gabanta ta yi tuntuɓe. Sai dai lokacin da ta ji zafi a bakinta ta ga abinda Hilal ya mata sai ta danganta hakan da ihun da ta yi ne kasancewar baya son hayaniya. Kuma ya saba cin uban duk yaran gidan idan sun yi hayaniya a in da yake. Hakan ya saka in dai yana wuri kowa ke kama kansa ya shiga tausayinsa. Don haka Zahra ta ta ga ya dakar mata baki ta ɗauka karar ihun ne baya so ba ta san shi ya harɗe ta da ƙafarsa ya yarda ita ba, don Idanunta na kan Ammar. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page4️⃣0️⃣ Kuma ya saba cin uban duk yaran gidan idan sun yi hayaniya a in da yake. Hakan ya saka in dai yana wuri kowa ke kama kansa ya shiga taitayinsa. Don haka Zahrah da ta ga ya dakar mata baki ta ɗauka karar ihun ne baya so ba t san shi ya harɗe ta d ƙafarsa ya yarda ita ba, don Idanunta na kan Ammar. Hawaye ne ke bin fuskarta yana gangarawa wajen ƙunnenta. Taisayin ta ya saka Ammar ƙarasowa wajen ya kai hannu zai taimaka mata ya ji Muryar Hilal na cewa. "Kada ka taɓa ta tun da ba Muharramarka ba ce." Jin haka ya saka Ammar janye hannunsa rai a ɓace. Dada ce ta taimaka mata ta miƙe tana ɗingisa ƙafar suka shiga ciki. Dada sai jera mata sannu take ta yi. Ammar ya kalle shi fuska babu walwala ya ce. "Man me hakan ke nufi, idan ta karye ko ta yi targaɗe ko gocewar ƙashi fa? Ko da ta yi maka laifi ya kamata ka hukunta ta ne ta hanyar faɗa, ko duka ma yanzu ba kowane laifi ta yi za'a ce ayi mata duka ba, don ba yarinya ba ce ƙarama ta san me take yi." Ko kallonsa bai yi ba idanunsa akan wayarsa kamar bai yi komai ba. "Ga shi ina son na gabatar da kaina a wajan iyayenta kafin na koma London ga shi ka ɓata mani komai." Ganin bai yi magana ba ne ya saka shi sake cewa. "Yauwa sai ka raka ni mu je tare kai za ka yi mani jagora babban Yaya." Wani kallon ba ka da hankali ya yi masa sannan ya tashi ya bar part ɗin. Har ya kai bakin kofa ya ce. "Zan fita yin wani aiki me yiwuwa na kai yamma kafin na dawo." Bai tsaya jiran amsar sa ba ya fita, don shi ma Ammar ɗin baya da niyyar amsa masa. Don ya ji haushin abun da ya aikata. Dada ta gasa wa Zahra ƙafa sosai sannan suka fito. Mai aikin Dada Inna Ladi ce ta shigo da sallama. Tattare kayan da suka ji breakfast ta yi ta kai kitchen. Sai sannan Ammar ke jerawa Zahrah. Magani Dada ta bata ta sha sannan ta koma ɗakinta ta kwanta da taimakonka Dada. Hilal kuwa zuciyarsa wasai ya nufi harabar gidan. Fita suka yi shi da sojojinsa a tare. Mota uku suka fita da ita. _Mansur_ Bayan ya gana program din da zai gabatar ne kasancewarsa ɗan jarida ne. Yana zaune a office ɗin sa yana hutawa aka yi knocking. Izinin shigowa ya bayar yayin da abokin aikinsa mai suna Auwal ya shigo. Bayan sun gaisa ne ya ce. "Mansur Adam Tafarki." Kallonsa ya yi yadda ya kira cikakken sunansa sannan ya ce. "Me kake so?" "Fatima Zahrah Salis Tafarki." Wani banzan kallo ya masa tare da tsuke fuska ya ce. "Tashi ka fice mun daga nan." Murmushi ya yi tare da cewa. "Calm down my friend me ya yi zafi, walalhi ba da wasa nake ba Allah ya jarabe ni da son wannan sister ɗin taka ce." "Wace ce sister ɗin ta wa?" "Kamar yadda kowa ya san cewa daga familyn Muhammad Tafarki kuke wato kakanka, kowa ya san sunanka ne Mansur Adam Tafarki, kuma Zahra Salis Tafarki ƴar ƙanin mahaifinka ne ai ƴar uwarka ce ." "Ba na da alaƙa da ita don haka ka fice ka bani waje, kuma kada ka sake zuwa Mani da makamancin wannan zancen, idan ba haka ba wallahi sai na maka rashin mutunci." Mamaki ne ya kama shi don haka ya mike tare da cewa. "Allah ya kyauta ." Tsuki Mansur ya ja tare da bin bayansa da harara. "Da ka san yadda na tsani yarinyar nan da ba ka zo Mani da wanann zancen ba. Mtsww." _Ammar_ Kasancewar yana son barin garin ya saka ya yanke shawarar zuwa part ɗin su Zahrah da kansa. Knocking ya yi a ƙofar falon, Sadik ne da ya shirya cikin kayansa na lauya yana sauri zai je kotu. Yana shirin shiga yin sallama da Ummi ne ya ji knocking ya nufi kofar ya buɗe. Ammar ya gani a bakin ƙofar duk da ya ɗan yi mamakin ganinsa kasancewar sa abokin Hilal. Kuma Hilal shi kansa ba gaida Abbi da Ummi yake yi ba ballantana wata alaƙa ta shiga tsakanin abokinsa da su. Murmushi Ammar ya sakar masa tare da mika masa hannu. Gaisawa suka yi sannan ya ce. "Suna ciki?" "Eh bisimillah." Shiga ya yi yayin da Sadik ya mayar da kofar ya rufe. Ammar ya zauna a kujerar yayin da Sadik ya shiga ɗakin Abbi tare da sallama. Ya same shi yana duba wasu file. Abbi ya masa masa sallamar tare da cewa. "Barrister ka fito kenan." "Eh Abbi zan tafi ne sai ga wannan abokin Yaa Hilal ya zo yana falo." "Wane abokinsa wanda ya zo daga Ingila ?" "Eh Abbi yana falo yanzu haka." Shiru Abbi ya yi kafin ya ajiye file ɗin hannunsa ya bi bayan Sadik zuwa falo. Abbi na fitowa Ammar ya sauka daga kan kujerar da yake zaune ya durƙusa har ƙasa ya gaida Abbi. Abbi ya amsa masa cikin sakin fuska da walwala tare da tambayarsa gajiyan hanya. Amsawa ya yi da Alhamdulillah yayin da yake komawa ya zauna. Ummi ce ta fito daga cikin ɗakinta ita ma kallon Ammar take yi tare da yi masa barka da shigowa. Ita ma sai da ya durƙusa ya gaida ita kamar yadda ya gaida Abbi. Ita ma Ummin amsa masa ta yi cikin sakin fuska da walwala kamar yadda Abbi ya masa. Ammar ya fahimci cewa iyayen Zahrah suna da mutunci da karamci. Kasancewar ya san ba zaman dad'i suke yi da iyayen abokin nasa ba, duk da sun san alakar dake tsakanin sa da Hilal sun tarbe shi da kyau . Shiru ne ya biyo baya in da Ummi ta shiga kitchen ta kawo masa cake da ta haɗa sai kuma lemun kwali ta ajiye masa, kasancewar yau girkin mai aiki suka ci su ma . Haka kwai Ammar ya tsinci kansa da jin kunya irin na surukai. Ya kasa ci ya kasa sha sai sunkuyar da kai ƙasa ya yi . Abbi ne ma ke ɗan jan sa da fira, wanda ganin haka ya saka shi ma ya fara yin fitar. Sadik ne ya masu sallama ya wuce . In da Ammar ke cewa. "Allah ya bada sa'a barrister." Da Amin ya amsa yana murmushi ya fice. Ɗan jimawa kaɗan Ammar ya yi masu sallama ya fice daga part ɗin. Duk da su ba su san me ya kawo shi ba amma ba su kawo komai a cikin ransu ba. _Jidderh_ Jin ta a ƙasa ya saka ta saki ƴar ƙara tare da cewa. "Wayyo Inna ta ." Kallon tuhuma Aunty ta yi mata tare da cewa. "Wace ce ke, kuma me ya shigo da ke cikin gidan nan?" Sai a lokacin ta ɗaga kai ta kalli Aunty tare da cewa. "Ni ba kowa ba ce face marainiya." "Me kike ƙullawa a cikin gidan nan?" "Wallahi ba a abinda nake ƙullawa sai alkhairi." Tsuke fuska Aunty ta yi tare da cewa. "Duk yanayin rashin gaskiya ya bayyana a jikinki, ɗazu na fito na hange ki kina saɗa kika ce Mani Mama kike nema bayan kin san ba ta wajen. Bayan na koma ɗakina na hange ki kina biyiwa ta nan kina juye-juye alamar ba ki son wani ya ganki. " Shiru ta yi don ba za ta iya fada mata abinda ya kawo ta wajan ba, musamman da Asadullah ya ce kar ta faɗa mata. Yanzu ya za ta fitar da kanta take tunani. Maganar Aunty ce ta katse mata tunini. "Ina saurarenki me kike yi a nan, wajen da ba kowa a wajen me kika je yi?" "Kawai dai na ce bari na zagaya ne na ga Asadullah mansion ɗin na da girma ban sani ba sai...." "Ke raina mani hankali za ki yi ne?" Jan hannun Jidderh ta yi suka koma in da ta ga Jidderh ta fito, ta ce sai ta nuna mata abinda ta zo yi nan. Jidderh kuka ta saka mata tana cewa ba komai zagayawa kawai take yi. Ganin wurin ba wani abu na daban ya saka ta kalli Jidderh ta tare da sakin hannunta tana mata gargadi akan ta tsaya iya abinda ya kawo ta gidan. Jidderh ta wuce ciki tare da shiga ɗakin masu aikin gidan. Kallonta Mama ta yi tare da cewa. "Jidderh Lafiya kuwa?" Murmushi ta ƙakalo ta ce. "Lafiya lau Mama." Wayarta ta ciro daga cikin aljihun dogon rigarta ta nemi wani lamba ta tura sakon text message. Ba jimawa kira ya shigo wayar. Ganin mutanen dake cikin ɗakin suna kallonta ya sa ba ta ɗaya ba. Har Larai ta ce. "Ba kiranki ake yi ba?" "Uhm" Katse kiran wayar ta yi sannan ta tura text message. Kusan sau uku ana turo mata da messages tana mai da reply kafin ta tashi da sauri kamar wacce aka tsikara ta shiga ɗakin Mom." Sanin Mom ba ta gidan ya saka ta hau bincike a cikin ɗakin na ta. Ganin ba ta samu abun da take nema ba ya saka ta saki tsuki cikin takaici. Har ta nufi kofar sai ta juya ta kalli wani dorowa wanda sam hankalinta bai kai gare shi ba. Buɗewa ta yi sai ta saki murmushi lokacin da ta yi tozali da keys ɗin da ke cikin dorowar. Da sauri ta kai hannu ta ɗauki ɗaya daga cikin makullan dake cikin drawar ɗin. Saka shi ta yi cikin aljihunta sannan ta nufi ƙofar fita. Daidai lokacin da Mom take dawowa daga unguwa. Tana sanye da mayafin take sai handbag ɗin ta daje riƙe a hannunta. Gaban Zahrah ne ya fadi sakamakon ganin irin kallon da Mom ke yi mata. "Me kike yi a ciki?" "Mom na je na gyara maki ɗakin ne?" "Ina tun safe kika gyara Mani ɗakin ko?" "Eh na duba ko akwai abinda zan kara yi ne?" Wani kallo Mom ta yi mata na rashin yarda kafin ta ce "Shi kenan je ki." Ajiyar zuciya ta sauke ta fice da sauri daga ɗakin. Da kallo Mom ta bita zuviyarta cike da tarin tambayoyi. Sai da ta ga ta ɓacewa wa ganinta ne ta shige cikin ɗakin tare da tura ƙofarta ta rufe. Sulaiman take ta raba idanun nemansa amma ba ya nan. Sai dai sauran guard ɗin da wasu security. Komawa ta yi ta nufi wata hanya. Can sai ta fito dauke da wani galam na fetur da ashana a hannunta. Wannan karon ba ta bi hanayar da Aunty ta gan ta ba sai ta bi wata hanyar daban ta zagaya. Sai da ta ɓulle in da take son zuwa sannan ta buɗe galan ɗin fetur ɗin ta watsa a plate ɗin da ke wajen, sannan ta watsawa a na kusa da shi. Duk ta watsa bayan ta zuge glass din window har ciki ta watsa . Ja baya ta yi daga wajen sannan ta ƙyasta ashana ta jefa ciki. Take wuta ya tashi bal bal a wajen. A guje ta zagaya in da ba wanda zai hange ta a guje. _Hilal_ Motocinsa ne suka cinno kai cikin gidan. Bayan direban motar da Hilal ke ciki ya yi parking ne wani soja ya fito da sauri ta bude masa murfin motar. Ƙafarsa ɗaya ya ziro waje kafin ya fito da ɗayan kafar gabaɗaya. Ƙamewa sojojin suka yi ba ogan na su. Da sallama iya fatar bakinsa ya shiga babban falon gidan. Sautin dariyar da ya ji ne ya saka ya juya ya kalle su. Ammar ne da Zahrah yana ba ta labari ita kan sai dariya take yi masa. Kallo ɗaya yi masu ya ɗauke kai tare da nufar upstairs. Ba su san da shigowarsa ba sai yakin takalimnsa da suka ji yana hawa upstair. Ammar ne ya ce. "Man ka dawo?" "Eh Ammar ya faɗa ba tare da ya juyo ba." "Nabeela da Kusar ne suka fito daga part ɗin su. Ganin Zahrah da Ammar ya saka Kausar ɗura wata uwar ashar Da sauri ta koma tare da ƙwalawa Aunty Laila kira tana cewa. "Mum! Mum!!!" Da sauri Aunty Laila ta fito tana cewa. "Lafiya wannan kiran kamar na mafarauta?" "Mum zo ki ga wannan mayyar yarinyar yadda ta liƙewa Yaa Ammar ?" Ita dai Mum ba ga gane abinda take nufi ba ta sai biyu bayanta ne. Tana zuwa ta ga Ammar wanda ke zaune tare da Zahrah. Kallon sa Aunty Laila ta yi mata ya sa ta sunkuyar da kai ƙasa. "Ai dole ki sunkuyar da kai mana munafuka, tun da kin saba da bin maza kamar karya, shi ma wannan ɗin da yake kamilalle ne za ki saka shi cikin jerin ƴan iskan mazan da suke bin ki.?" Ammar kallon Aunty Laila ya yi da mamaki , don ya san ita ɗin Gwaggo ce a wajen Zahrah saboda don sanin kowa bayan an yaye Salis Muhammad Tafarki ne aka samu ciki aka haifi Laila Muhammad Tafarki. Mahaifin Zahra take bi. Tana matsayin uwa a gare ta take faɗin haka. Maganar Aunty Laila ya ke nazari can ya ji ta ce. "Kai ko Ammar me ya haɗa ka da wannan yarinyar?" "Son ta nake kuma aurenta zan yi." Ba iya Nabeela da Kusar ba hatta Aunty Laila ta tsorata gabanta ya fadi . Don ta ƙudira niyyar idan har Allah ya cikaata burinta Hilal ya auri ɗaya daga cikin yaranta sai Ammar ya auri ɗaya. Amma wannan Zharah ta zame mata ƙadagaren bakin tulu. "Haba Hilal yanzu duk matan da suke gidan nan ka rasa wacce za ka ce kana so sai wannan yarinyar? Wannan yarinyar fa angulu ne da kan zabo, kana ganinta kamar na Allah amma ba haka ba, kana ganinta nan har ciki ta zubar a cikin gidan nan, idan kana ganin ƙarya ne ka tambaye abokinka Hilal ka san dai idan ni ba ka yarda da maganata ba shi za ka yarda da ta sa. Duk da ya shiga cikin firgici amma sai ya daure ya ce. "Aunty wannan ba damuwa ba ce, zan iya aurenta kuwa a duka yadda take?" Nabeela da ta ƙulu da maganarsa ta ce. "Haba Yaa Ammar ai..." Kallon da ya jefa mata ne ya saka ta fasa ƙarasa maganar ta. Zahrah kuka take yi mai cike da ƙunar zuci, wace irin rayuwa ne a ce wai dangainta su ne suke mata irin wannan ƙazafi haka ne ta tare masu ne tashi ta yi zata bar wajen ya rike mata hijabi ya ce. "Daina kuka ki share hawayenki duk yadda kike duk yadda kike ina son ki a haka. Ko da a gidan ƙaruwai kike zaune wannan ba damuwa ba ne wallahi ina ƙaunarki fisabilillah." Yana sakin hijabinta ta ruga part ɗin Umminta tana kuka. Bai sake kallon in da Aunty Laila take ba ya juya ya nufi upstairs cikin wani irin yanayi. Jinjina kai Sunyi Laila ta yi tare da cewa. "Wallahi ba za ta saɓuba bindiga a ruwa, Zahra ba za ta auru ba ina cikin gidan nan. Ga sauran yayunta nan sai ita ce ƙaramar su. Ga farin jinin tsiya anya kuwa uwarta zaune take a kanta?" Kwafa ta yi ta koma part ɗin ta ƴaƴanta suka mara mata baya. _Jidderh_ Numfashi take maida wa bayan ta koma nesa da in da ta cinna wuta. Hankalin security ne ya fara zuwa ga wutan dake ci a wuri. Da mamaki kowa ke kallon wajen da aka ce gobara ya tashi don a iya saninsu ba kowa a ciki me ya kai wuta wajen. Uncle Adam ne tare da Mami suka fito daga part ɗin su, sakamakon hayaniyar ma'aikatan gidan da suke yi. Naseer, Maryam, Abida suka mara masu baya. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page4️⃣1️⃣ Uncle Adam ne tare da Mami suka fito daga part ɗin su, sakamakon hayaniyar ma'aikatan gidan da suke yi. Naseer, Maryam da Abida suka mara masu baya. Mamaki da al'ajabi haɗi da tashin hankalin ne ya bayyana a tare da su. Can sai ga Aunty da ƴarta Suhailat sun fito Mom da Fauziyya ne a bayan su. Gabaɗaya kowa ya shiga tashin hankali da ganin wutar yayin da security da ma'aikatan gidan ke ta ƙoƙarin kashe wutar. Amma kamar ana ƙara ilangiza masa fetur. Gabaɗaya hankalin kowa a tashe gidan duk ya hargitse kowa sai ƙoƙarin bada gudummawar sa yake yi. Hatta security dake bakin gate sun bar wajen kowa hankalimsa na kan wutar. _Jidderh_ A daidai wannan lokaci ne Jidderh ta nufi ɓangaren da Asadullahi yake. Hannunta rike da wani baƙin riga, Key ɗin sa ta ɗauko ɗakin Mom wanda take da tabbacin zai iya buɗe kowane ƙofa na gidan. Ajiyar zuciya ta sauke tare da sakin murmushi lokacin da ta ga ƙofar a buɗe. Daidai lokacin da motar kashe gobara ta shigo gidan. Jin ƙarar sautin motar ta ce. "Yallaɓai ka hanzarta mu bar gidan nan ba lokaci." Rigar sanyin ta ɗaura masa a saman kayan dake jikinsa, rigar kai hula ce sai ta janyo hular ya rufe kusan rabin fuskarsa, facemask ta saka masa don ta lura kamar jikinsa ba ƙarfi ko kaɗan. Ga ƙafarsa ma kamar ba za su iya ɗaukar sa ba. "Yallaɓai mu tafi ka sunkuyar da kai yanzu ba wanda hankalin sa zai zo gare mu, mu yi saurin fita akawai motar dake jiranmu a waje, idan wutar nan ya mutu hankalin wasu zai iya dawo wa ga jama'a har a gane mu. Jin haka ya tattara dukkan ƴar karfin dake jikinsa, sakamakon jikinsa ba ƙarfi don alluran da suke masa yana kashe masa jiki da kuzari dake jikinsa. Ta yadda ba zai iya yunƙurin cewa zai ƙwaci kansa ko ya gudu ba. Daƙyar take ɗaya ƙafarsa tana gaba yana bin bayanta. Hankali kowa na wajen wutar, hatta wadanda gidansu ke kusa da mansion ɗin sun shigo. Bai ɗaga kai ya kalli kowa ba amma daƙyar yake tafiya. Jikinsa sam ba ƙarfi kamar ba nasa ba. Kasancewar mansion ɗin akwai girma sun yi doguwar tafiya kafin suka iso gate ba kowa a wajen. Sai wani security dake waya hankalinsa ma baya jikinsa yana magana ne akan wutar. Ajiyar zuciya ta sauke daidai lokacin da suka fita daga gidan. Sai sai kuma wata mummunar faduwar gaba da ya ziyarce ta. Wanda har sai da ta dafe ƙirjinta. Suna ƙarasawa wajen motar da ta saka ya zo ta bude bayan motar ta ce. "Yallaɓai shiga." Yana shiga ita ma ta zauna gefensa sai kanta da ta ji yana ɗan juya mata. Direban ya ja motar suka bar wajen. Suna fita daga cikin unguwar suka kama hanyar in da Jidderh ta ce ya bi da su. Wato unguwarsu gidan iyayenta kenan take so ya kai su. Daidai kan wata kwana wata babbar mota ta zo ta daki motarsu wanda hakan ya saka motar ta gangara ƙasan titi ta daki wani bishiya. Gaban motar ta ragargaje sai sai cikin ikon Allah ba wanda ya fito daga cikin motar . Jama'a aka taru aka buɗe masu suka fito. Tabbas da Asadullah bai saka wannan hular da facemask ba da jama'a sun gane shi . Direban ya shiga tashin hankali sosai ba kaɗan ba. Sai kuka yake yi yana wayyo Allah ya zai yi da mutumin da ya bashi bayan motar ga shi bai da mutunci akan kuɗi ba zai dauki asara ba. Jidderh dai gata nan ne sai kallonsu take ta kasa magana. Sai dai ta dafe kanta tana yamutse fuska. Kowa na ta masu Allah kiyaye gaba, ganin kowa ya tsira da ransa. Ganin yadda direban ke sambatu ne ya saka wasu ba tausaya masa akan rashin mutunci na mai motar da zai masa. Dafa kafadarsa ya yi tare da cewa. "Zan biya ka kudin motar." Wani kallo ya masa tare da cewa "Kasan nawa kudin motar, kana da kuɗin siyen motar ne ka saka aka nemi ni? Ga direban da ya buge mu ya gudu." "Wallahi zan biya ka na ce ka kwantar da hankalinka." "Waye kai?" "Sanin waye ba shi ne ya fi mahimmanci a gare ka ba, yanzu ka bani takarda da biro zan aike ka wata kotu ne , idan ka je ka kai masa sakon zai zo tare da kai." Kwatancen ya yi masa sannan ya nemi ya bashi takarda da biro, ya nemo ya bashi ya yi wani rubutu ya ninke ya mika masa. "Idan ka je ba za'a bari ka shiga ciki ba, ka ba wa security wannan takardar ka ce a kawo Barrister Haris Umar wannan takarda. Sai ka jira ya fito. Karba ya yi da sauri ya nemi abun hawa ya hau suka bar wajen. Asadullah ya kalli Jidderh ya ce . " ki zauna a inuwa." Daƙyar yake magana saboda ba kwari ƙafarsa ma sun gaza ɗaukarsa jingina ya yi da motar. Ba ta ce komai ba sai kallonsa. Sau uku yana mata magana ita dai sai ido ba baki. Mamaki ne ya kama shi ganin yadda ta koma don haka. _Zahrah_ Da kuka ta nufi part ɗin su Ummi da fitowarta kenan daga kitchen ta bi ta tana kiran sunanta. "Zahrah me ya same ki?" Zubewa a gadon ta yi tana kuka mau cin rai, take Kuma sai numfashinta ya fara fita daƙyar. Hankalin Ummi ya tashi sosai da sosai don da alama ciwonta ne ya tashi. Cikin tashin hankali ta fara laluben in da za ta ɗauko mata Inhelar ɗin ta. Sai ta neme shi ta rasa handbag da ta fita last das shi ta nema ta rasa. Ga shi a cikin wannan yanayin da take ciki ba za ta iya shan magani ba, ɓangaren Dada Ummi ta shiga tare da sallama. Papa da Dada ne a falon ganin yanayin Ummin ya saka suka mike suna tambayarta meke faruwa. Da "Dada ko handbag ɗin Zahrah na nan ne?" "Eh to bari na duba ɗakinta ko yana nan?" Shiga Dada ta yi wanda Ummi ke ganin tafiyar Dadar ya mata nawa, sakamakon ciwon ƙafarta ba ta iya tafiya da sauri. Papa ne ya kalli Ummi ya ce. "Ba dai ciwon nata ne ya tashi ba ko?" "Eh Papa shi ne ya tashi." Tare suka hada baki da Dada wajen cewa. "Subhanallah" Ummi na karbar jakkar ta buɗe ta cire Inhelar daga cikin kakar ta ajiye harkar a kan kujera mai zaman mutum uku. Gabaɗaya suka fito Ummi na gaba Papa da Dada suna baya. Suna kawowa tsakiyar babban falon gidan suka ga Hilal da Ammar suna saukowa daga downstairs. Ganin halin da suke ciki ne ya saka cikin tashin Ammar ke tambayar su abinda ke faruwa. Hilal kam tun da ya gan su ya san kwanan zancen, don ba shakka ya san ciwonta ne ya tashi. Papa ne ya ce . "Zahrah ce ba lafiya." "Subhanallah" Ya bi bayansu yayin da Hilal ya taɓe baki ya nufi part ɗin su Dada, dama can za su je shi da Ammar ɗin. Suna shiga suka same ta cikin wannan halin, hankalin Ammar ya yi mugun tashi musamman da bai san Zahra na da ciwon athma ba. Inhelar Ummi ta rike bayan ta zauna bakin gadon ta janyo kan Zahra ta ɗaura a saman cinyarta ta kafa nata shi. Ba jimawa ta ja numfashi, sai a lokacin Ammar ya gane cewa tana da larurar asma. Sai dai duk da haka numfashin nata baya fita daidai yadda ya kamata. Kuma sai hawaye take yi daga ganinta kasan akwai bakin ciki a tattare da da ita. Da Hilal kuwa yana shiga part ɗin Dada ya zauna a kujera mai zaman mutum uku. Ganin Handbag ɗin ne ya san dai ba na Dada ba ne don wannan na ƴan mata ne. Miƙa hannu ya yi ya janyo jakkar don zuciyarsa ta bashi na wace ce. Wayoyinta ya fara cin karo da su, ɗaukar wayar ya yi cikin sa'a kuwa ba password a jiki. Tarin missed call ya gani dubawa ya yi ya ga mutane da yawa amma akasari kiran mutane uku ne ya fi yawa Amininta da Aminiyarta sai kuma Mustapha wanda yake Mustapha Umar da ya nace mata a school. Sai ya shiga wajen messages nan ya ga tarin sakonnin da ake tura mata masoyanta, sai dai ba ta masu reply. Har mamakin yawan masoyanta yake yi. Don kowa da ƙokon baransa yake akan ta masa soyayyarsa. Social media ya shiga nan ma ya ga bata cika ta'ammali da social media ba. Gallery din ta ya shiga, in da duk photo na school ko wanda ta ɗauka a waje to tana sanye da facemask da glass ne, idan kuma ta sanya Hijabi to za ka ganta da niƙab. Amma photon da a gidan aka dauke shi to shi ne za'a ga fuskarta. Sai kuma idan sun yi selfie 🤳 ita da Amininta da Aminiyarta ne takan sauke miƙa facemask ko ta ɗaga ñikab. A can bangaren Zahrah kuwa sai da numfashinta ya daidaita ne sannan Dada ta fito ita da Papa. Ammar ma ya mara masu baya bayan ya gama jera wa Zahrah sannu. Ummi ta yi masa godiya tana yaba kirkin yaron a zuciyarta. Ko da suka koma Part ɗin Dada Ammar ya zauna gefen Hilal ganin ya shiga what'sup ɗin ta ne ya saka Ammar cewa. "Me kake dabawa a wayar Zahrah?" Tsuki ya ja sannan ya ce. "Ƴa mace sai da saka idanu ana binciken wayarsu don sanin abinda suke aikatawa da waya." Jinjina kai Ammar ya yi tare da cewa. ",Haka ne, domin waya da kake illarta ta fi amfaninta yawa. Ya lalata tarbiyyar yara da yawa duk da dai ko da wasa ba zan kawo Zahrah za ta iya aikata wani abu na rashin daidai ba. Don na san na zaɓawa ƴaƴana uwa ta gari wacce zan yi alfahari da ita duniya da lahira." Taɓe baki Hilal ya yi don tare da ajiye wayar. Kallon Dada ya yi tare da cewa. "Yunwa nake ji." "Sai ka je ai na san ba'a rasa abinci a gidan nan ba." "Bana son cin abincin masu aiki kin sani." "Uhm to sai ka je ka saka Maryam ko Nadiya su dafa maka." Tsuke fuska ya yi tare da cewa. "Ba abinda yaran nan suka iya, ranar da na saka su dafa mani indomie kasa ci na yi." "To ka sanya Kausar ko Nabeela wata ta dafa maka." "Wallahi gara kowa da waɗan nan yaran ba abinda suka iya." "Hmmm Laila dai tana cutar yaranta ne, idan na yi magana ta ce wai na tsani yaranta kamar yadda na tsane ta ba na son su." Ammar ya ji dariya ya ce . "Ina fatan dai Zahra ta iya ko?" "Sosai kuwa ai Zahrah ƙarshe ce, idan tana girki sai kamshi ya cika ka ga dad'i a baki hannun uwarta ta ɗauka akwai dadin girki. Ya ka ji wannan sinasir da ka ci?" "Ita ce ta girka, ma sha Allah gaskiya ta iya girki ban taɓa cin abinci mai daɗin wannan ba." Kasancewar Papa ya juya ya fita Hilal ko ganin Dada ta biye wa Ammar ta share shi ya saka ya nufi kitchen. Dube-dube yake yi sai dai kamar Dada ma ba ta yi girkin ba, sai dai ya ɗebi meet pie da Cake ya ɗauko fresh milk ya jero da faranti ya fito. Tare da Ammar suka ci ya yi dadi sosai. Nan Dada ke fadin ai Zahra ta haɗa su. Cak Hilal ya tsaya ya dakatar da cake da yake kokarin ɗauka. Yamutse fuska ya yi tare da tashi ya bar part ɗin gabaɗaya. _Barrister Haris Umar_ Zaune yake a office ɗin sa ya na nazarin wani case da zai da zai zauna a kotu. Knocking aka yi baya bada izinin shigowa aka shigo, kallon matashin saurayin da ya shigo ya yi tare cewa. "Khalid ya aka yi.?" "Wani mutum ne ya zo yana son ganinka, na ce ya jira na sanar da kai sai ka bada izinin shigowarsa." "Ka san waye shi?" "Ban sani ba amma da dukkan alama aiko shi aka yi." Shiru ta yi kafin ya ce. Da "Okay ka shigo da shi." Fitarsa da kamar mintuna uku sai ga su tare, Khalid da ya fita ya bar su. Bayan sun yi musabaha Barrister Haris ya kalle shi ya ce. "Bisimillah zauna mana." Barrister Haris ya yi maganar yana nuna masa wajen zama. Zama ya yi sannan ya mika masa takardar dake hannnsa. Karbar takardar ya yi ya warware ta. Take ya zabura ya mike tsaye yana zare idanu, cikin tashin hankali yake kallon Direban da Asad ya aiko wajensa. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page4️⃣2️⃣ Take ya zabura ya mike tsaye yana zare idanu, cikin tashin hankali yake kallon Direban da Asad ya aiko wajensa. "Ina yake?" Ya tamabaya cikin tashin hankali. Na direban ya kwatanta masa in da abun ya faru. "Muje." Ya tamabaya yana ɗaukar wayarsa da makullin motarsa. Fita suka yi Barrister Haris na gaba Direban na binsa a baya. Suka karasa wajen motarsa. Suka shiga ya tada motar suka bar wajen. _Asadullah_ Duk yadda ya yi da Jidderh akan ta zauna sai kallonsa kawai take yi kamar ta sami hoto. Ba uhm ba uhm uhm. Mamaki yake yi yadda bakinta ya mutu lokcin guda. Motar Barrister Haris ne ya karaso wajen. Suka fito a tare suka karasa wajen. Kallonsa kawai Barrister Haris ke yi. Don tabbatar wa sai ya kai hannu da niyyar cire facemask dake fuskar Asadullah sai ya rike masa hannu tare da cewa. "Me kake son ka san?" Zaro idanu ya yi mamaki fal a kan fuskarsa zai yi magana Asad ya ɗaga masa hannu tare da cewa. "Mu bar wajen nan." Daga jin yadda ya yi maganar zai tabbatar maka da cewa a gajiye yake. "Okay sir Amma wannan fa?" Ya yi maganar yana nuna Direban. "Tare za mu tafi." "Okay mu je ko?" Asadullah ya kalli Jidderh ya ce . "Zo mu je." Bin bayansu take yi har wajen motar, sai kallonta Asad yake yi kamar ba ita ba. Asad ya bude mata bayan motar ta zauna ya zauna gefenta yayin da direban ya shiga wajan me zaman banza. "Ina za mu je mansion ko?" Kai ya girgiza sannan ya ce. "Sabbon gidan da na siya ana gobe zan ɓata." Kai kawai ya jinjina sannan ya yi wa motar key suka bar wajen. Doguwar tafiya suka yi sannan suka isa wani gida. Horn suka yi a ƙofar tangamemen gate ɗin gadin ne ya leƙo yana duban motar. Sai da Asadullah ya ja facemask din dake fuskarsa ƙasa ya Gandhi sannan ya nufi gate ɗin a guje ya wangale masu shi. Shiga suka yi cikin gidan in da Barrister Haris ya nufi parking space ya yi parking suka fito. Motoci guda biyu ne a parking lot ɗin. Maigadi ya zo ya zube yana gaida Asadullah. Shi dai har lokacin bai yi magana ba hannu kawai ya ɗaga masa. Zuwa lokacin Barrister Haris ya fahimci Asad baya son wannan direban da suke tare da shi ya san waye Asad. Don bai yarda ya bude fuskarsa ba da alama baya son Direban nan ya gan shi ne . Fitwawa suka yi gabaɗaya suka nufi ƙofar da za ta sada su da main falon gidan. Password ya danna a jikin ƙofar Sannan ƙofar ta bude, juyowa ya yi ya kalle su sannan ya masu alamar su shigo. Bayan sun shigo ne suka tsaya a babban falon gidan. Nan direba ya baki baki tana kallon Aljannat duniya. Jidderh dai kamar mutum mutumi haka take. Ciki Asad ya shiga yayin da Barrister Haris ya zauna akan ɗaya daga cikin kujerun dake falon. Kallon Direban da Jidderh ya yi tare da cewa. "Ku zauna mana." "Direban ya kalli Barrister Haris ya zauna a ƙasa saman Centre Carpet dake tsakiyar falon." Jidderh dai kallon ƙasa kawai take yi. Kallon Direban ya yi daidai lokacin da Asad ya dawo. "Tare da yarinyar nan kake ne?" "A'a Yallaɓai ta dai je tashar mu ta ce tana son na zo na dauke ta ita da wani mutum, ta fada Mani unguwar da lokacin da zanzo. Ya biya ni shi ne na je na dauke su amma ban san ta ba " Asad bai ce komai ba, ya zauna kan kujerar ya rubuta check cek ɗin kudi ya mikawa Direban. "Karbi wannan Naira miliyan goma ne, na san za su ishe ka ka gyara motar nan ka mayar wa mai ita , sannan kai ma ka ajiye ta ka ta motar ka cigaba da sana'a." Zubawa Direban ya yi yana godiya tare da kallon cek ɗin kudin yana kukan farin ciki yana jerowa Asad albarka. Da hannu ya masa alamar ya tafi don ya kosa ya bude fuskarsa kada wannan mutum ya gane shi kasancewar sa sanannen mutum a garin. Bayan fitarsa ya zubawa Jidderh idanu na wasu seconds sannan ya cire p cap dake kansa. Ya zare facemask kyakkyawar fuskarsa ta bayyana. Har lokacin idanunsa na kan Jidderh "Zauna mana har yanzu kima tsaye, ki zauna kafin mu yi magana na kai ki har gida." Ya uku maganar a gajiye don har yanzu jikinsa ba ƙarfi. Ganin duk maganar da yake yi ba ta iya cewa komai ba, kuma har lokacin Idanunta na ƙasa abun ya bashi mamaki matuka. "Meye ma sunanki?" Nan ma shiru kuma bata kalle shi ba. Zuwa can ya tuno da sunar ya ce. "Jidderh ko?" Nan ma shiru. Kallonta yake yi da alama ba ta jin me yake cewa. Kiran sunanta yake yi ta yi shiru ba ta ɗaga kai ta kalle shi ba ballantana ya saka ran tana jin sa. Cikin mamaki ya karasa yana kallonta . Ita ma shi take kallo a lokacin da ya tsaya gabanta. Alamar ta zauna ya yi mata akan kujera. Kallonsa ta yi ta gane yana nufin ta zauna ne sannan ta zauna. "Innalillahi wa'inna'ilahi raji'un. Lafiya fa muka fito daga mansion tana magana tana komai amma yanzu kamar an canza ta." "Wai me ke faruwa ne kuma wace ce ita ?" "Barrister na gaji yanzu ina bukatar hutawa. Ka kira Mani Doctor Isma'il ya zo ya duba ni, kuma bai san gidan ba, ko za ka iya sauko mani shi daga nan ka yi muna order na abici." "Ina Doctor ɗin ka yake ?" "Ba na son kowa ya san ina nan, ga gane ko?' Jinjina kai Barrister Haris ya yi sannan ya ce ,"Ba ka da matsala bari na je na dawo." Yana fadar haka ya fice. Asad ya tsaya tana ƙare wa Jidderh kallo sannan ya ce. "Bari na shiga na yi wanka kin ji.,?' Nan ma ba alamar ta ji shi, sama ya nufa ta bishi da kallo. Bayan kamar awa ɗaya da fitar Barrister Haris ya dawo bayansa tare da wani mutum na sanye cikin Suit. Mamaki ta kama Doctor yana kallon Asad dake saukowa ƙasa. Da alama ya yi wanka ne don ya sanye yake da riga JC Red colour sai wando three-quarter black colour sai ƙamshi yake yi . "Sir dama kana nan?" Murmushi Asad ya sake sannan ya ce. "Ina nan amma ba na din kowa ya sani sirri ne." Jinjina kai Dr Isma'il ya yi tare da y. "Sirrinka ba wanda zai ji dai dai idan kai ne k fitar da kayanka." Barrister Haris ya ajewa Jidderh leda ɗaya na takeaway da ya yo masu . Asad ya bude mata fry rice ne da siyayarn naman kaza, sai Lemu mai sanyi da ruwa. Alama ya mata da ta ci, sai ta fara ci shi kuma ya ajiye ɗyar ledar a Centre table dake gabansa. "Barrister za ka iya komawa wajen aikinka amma ina bukatar ganinka zuwa dare karfe takwas. Yanzu zan shiga Dr ya duba ni don har ruwa sai ya ƙara Mani." "Ina nan tare da kai Asad ba in da zan je." Tare suka shiga su uku wani ɗaki sai Jidderh dake zaune tana tsakuran abinci tana ci. Gwaje-gwaje Doctor Isma'il ya yi masa sannan ya bashi magunguna ya masa ƙarin ruwa a jikinsa. Take barci ya ɗauke shi don ya masa allurar. Ganin ya yi barci ne ya saka Dr Isma'il cewa. "Barrister kana tare da shi ko?" Jinjina kai ya yi tare da cewa. "Ina sha Allah." "Idan ruwan ya kare ka cire masa, in sha Allah idan ya tashi zai ji karfin jikinsa. Na ga jininsa ma ya hau sai dai abinda ke bani mamaki yaushe ya fara amfani da abubuwan da suke gusar masa da hankali ya shiga cikin wani hali kamar wanda baya cikin hayyacinsa?" Shiru Barrister Haris ya yi kafin ya ce. "Kana nufin Asad yana shaye-shaye ne?" "Ba zan ce ba gaskiya, amma yanayin halin da yake ciki tabbas wani lokacin hankalinsa na gushewa ya zama kamar yana cikin maye." Shiru Barrister ya yi kafin ya saki wata ajiyar zuciya ya ce. "Aikinka ne kuma ba zan ƙaryata ka akan abokinka ba, sai dai ina da yaƙinin cewa Asad ba zai taɓa ta'ammali da kayan maye ba, sai sai akwai wani ɓoyayyayen al'amarin da ya faru da shi wanda mu ba mu sani ba " "Allah ya kyauta, ni zan tafi." Sallama suka yi ya fice ya ja masa kofar. A can *Asadullah mansion* kuwa sai da aka samu nasar kashe gobarar sannan hankalin kowa ya kwanta. Sai sai abun da ya ke ba kowa mamaki shi ne yadda wutar ya tashi a part ɗin da ba kowa a ciki. Ta ya ya hakan za ta faru?" Tamabayar da Uncle Adam ke ta yi kenan. Nasir ya kalli mahaifin nasa cikin damuwa ya ce "Dad wallahi ni ma abun ya ɗaure mani kai matuka, da akwai mutane sai a ce ko ko sun kunna electronic ne ko makamancin haka." Mom cikin damuwa take cewa. "Allah ya san ko mene ne, kuka a godewa Allah tun da ba'ayi asarar rai ba." Nan kowa ya dinga jinjina lamarin, Sulaiman da dawowarsa kenan ya tarar da wannan tashin hankali. Don dama shi tunda aka nemi ubangidansa aka rasa bai cika zama mansion ɗin ba. Da ka ganshi ka san yana cikin damuwa. Kallon abinda ke faruwa ya yi sannan ya nemi karin bayani daga wajan ɗaya daga cikin abokan aikinsa. Nan aka sanar da shi komai. Jinjina kai ya yi tare da cewa. "Wannan ba gobara ba ne na haka kawai ba, shirya shi aka yi da wata manufa." Jinjina kai ya yi alamar tabbatar wa, sannan ya cire bakin glass dake fuskarsa. "Ko shakka babu ba yadda za'ayi wurin nan ya kama da wuta sai dai idan saka wutar aka yi. " "Meye hujjar ka na cewa haka kuma Meye amfanin saka wutar?" Naseer ya tambaya yana kallon Sulaiman da ya ji tambayar "Kada ka damu zan samo hujja akan haka matukar an bar wata wata hujjar, sai sai idan mai aikin yana da matukar wayau bai saki layi ba." Yana fadar haka ya zagaya in da wutar ya kama don neman hujjar da zai gani. *Washegari* Ammar ya shirya don komawa UK, ya so a ce ya saka Zahrah a idanunsa amma hakan bai samu ba, ga shi kiran gaggawa ne aka yi masa. Don lokacin ko da ya shiga part ɗin Ummi wanda Dada ta tabbatar masa da cewa can ta kwana. Ko da ya gaida Ummi yake tambayarsa jikin Zahrah ta sanar da shi da sauƙi tana barci. Sallama ya mata ya tafi, sai da ya shiga kowane part ɗin gidan ya masu sallama sannan ya ya tafi in da Hilal ya yi masa rakiya har airport. Sai da jirginsu ya tashi sannan ya dawo. _Sulaiman_ Yana zagaye a wajen da abun ya faru sai ya hago wata jarka da aka jefar. Ƙarasawa ya yi wajen tare da sunkuyawa ya ɗauki galan ɗin fetur da Jidderh ta jefar. Shinshina wa ya yi ya tabbatar da fetur ne ya juyo kenan sai ya ji ya taka abu. Ɗaga ƙafarsa ya yi ya duba , ashana ce da ta ƙyasta bar shi a wajen. Ɗauka ya yi ya dawo in da sauran mutanen suke, ɗaga galan ɗin fetur ya yi tare da ashana ya ce "Ga hujjar da za ku yarda cewa wannan shiryayyen al"amai ne." Gabaɗaya kowa ya zuba masa idanu ana kallon galan da fetur. "Waye ya kawo wannan a nan?" Kowa ya yi shiru zuciyoyinsu cike da mamaki ne hakan ya ke nufi. Ɗaya daga cikin security dake gate ɗin ne ya ce. "Tabbas akwai wacce ta shigo da da wannan cikin masu aikin gidan nan." Kowa ya juya yana kallonsa, Uncle Adam ya ce "Duk wanda aka kama da aikata wannan al'amarin sai ya yi nadama. Don sai na tabbatar ya tafi gidan yari." Sulaiman ya ce "To yanzu ta hanya daya za'a ga wanda ya shigo da shi tabbas za'a iya gane ko waye ta hanyar CCTV Camera." *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page4️⃣3️⃣ "To yanzu ta hanya daya za'a ga wanda ya shigo da shi, tabbas za'a iya gano wa ta hanyar CCTV Camera." Gabaɗaya sun ji dadin jin hakan sosai, musamman Mom ta ce . "Ko ma waye sai na tabbatar ya tafi gidan yari , wani irin ta'addaci kenan?" Mami ce ta taɓe baki tana cewa. "Ai wannan ma ya zama dole a gano don ku waye shirin yin kisan kai ya yi, don idan ba don Allah ya tsare ba ai sai sai dai aji labarin mutuwar mu. Don me ne ke kusa da part ɗin da abun ya faru. Aunty ce ta ce. Sai dai wani hanzarin ba gudu ba, Alhaji fa ɗan lelensa ne ai za su iya wannan aiki, don na ga su ne suke binciko duk abinda ya faru daga cikin ɗakinsu.," Idan suka ji an ce ɗan lelensa sun ɗan Asad take nufi, kai Sulaiman ya jinjina alamar haka ne. In da Aunty ta cigaba da cewa . "Sai dai a jira Alhaji daga tafiyar da ya yi, don ba zai yiwu a shiga ɗakinsa kai tsaye ba." Ta yi maganar tana jan hannun ƴarta Suhailat suka koma ciki. Kowa ya bita da kalli. Wayar Sulaiman ne ya yi ruri, yana dubawa ya ga lauyan uban gidansa ke kira. Ya ɗaga tare da yin sallama. Barrister Haris ya amsa tare da cewa. "Idan kana cikin mutane ne ka koma gefe." Jin haka ya saka shi komawa gefe. Bayan sun gaisa ne Barrister ya sanar da shi in da zai zo ya same shi. Jin wajen ya saka Sulaiman tambayarsa lafiya don ya san su biyu ne kawai suka san Asad na da gidan. Don haka ya ce. "Ko dai an samu cigaba ne ta hanyar ka?" Ka dai zo kawai ka same ni yanzu ba tare da ɓata lokaci ba Yana jin haka ya faki idanun mutanen gidan ya fice bai tsaya ɗaukar mota ba, don ya san yanzu Uncle Adam zai fara tambayarsa. _Zahrah_ Ko da ta tashi daga barci Ummi ke sanar da ita cewa Ammar ya zo sallamarta ya koma. Sai ta ji ba dad'i don ta so su yi sallama da shi ta gan shi ya gan ta. Ko don kulawar da ya nuna mata. Kasancewar rana cin abinci Ummin ke sanar mata, don haka sai ta faɗa duniyar tunani ta cigaba da juya cikali a cikin ruwan tea. Ganin daga fada mata ta faɗa duniyar tunani ne ya sa Ummi kiran sunanta. "Zahrah" Ɗaga kai ta yi tana kallon Ummi sannan ta ce. "Na'am Ummina." "Meye tsakaninki da shi ne?" "Ba komai Ummi?" "Ban gane ba komai ba bayan na san haka nan kawai ba zai dinga shigowa nan ba, kasancewar abokinsa da yake zuwa gidan don shi bai taɓa shigowa nan da sunan gaishe su ba ballantana abokinsa. Sau ɗaya Ummi ta ga Hilal ya shigo part ɗin ta, lokcin da ya saka Zahrah punishment tsabar wahala sai da ciwonta ya tashi ta ga cikin dare ya shigo part ɗin. Duk da ba ta ga shigowar sa a lokacin ba amma ta ga fitarsa bayan ya ɗauki alluran ciwon Zahrah, kuma har yau bai sake zuwa ko bakin part ɗin na su ba. "Meye sunansa?" Ummi ta tamabaya yayin da ta kafe Zahrah da idanu. "Ummi wai so na yake yi?" "Hmm na san za'a rina, gaskiya ba na son matsala ina zaman zamana. Yaron nan abokin Hilal ne kuma sanin kanki ne cewa Hilal da iyayensa ba za su goyi bayan ya aure ki ba. Musamman Gwaggon ku Laila da sai ta san yadda ta yi ta wargaza komai, kuma na san za ta samu goyon bayan Mahaifiyar Hilal da ta kasance kamar ƙawa ce a wajen mahaifiyar Ammar sakamakon abotarsu. Don haka kin fi kowa sanin ƙiyayyar da suke maki ba za su taba bari iyayen Ammar su yarda ɗan su ya aure ki ba, baki da mugun tabo amma sai sun yaɓa maki. Don haka lna mai shawartarki kada ki saka soyayyarsa a zuciyarki ballantana ya zame maki ƙalubale a gaba." Shiru ta yi Allah ya sani tana son Ammar, sai dai Ummi ta yi gaskiya da ta tunatar da ita haka, ga shi dama akan Idanunta Aunty Laila ta fara ɓata da mugayan kalamai amma ya ce ya ji ya gani." Ƙwalla ne suka cika mata idanu ta kauda kai tana gogewa. Ummi dai ta tashi ta bar ta a dinning area. _Asadullah_ Tare da Barrister Haris suka sauko Downstairs. Har lokacin Jidderh na zaune, abincin da aka ajiye mata tsakura kawai ta yi. Idanunsu a kanta. Da sauri Asad ya karaso wajen da take ya sunkuya a gabanta. "Me ya saka baki ci abinci ba?" Kallonsa kawai take ko motsawa ba ta yi ba. "Me kike so ki ci?" Nan ma shiru, sai da ya yi magana sau uku ba ta tanka ba kuma ba alamar tana jin me yake cewa. Cikin damuwa ya kalli Barrister Haris tare da cewa "Akwai matsala fa?" "Na me?" Ya tambaya idanunsa akansa yana neman ƙarin bayani. "Tana magana fa lokacin da muka taho tare, amma yanzu ba ta magana da alama ma ba ta ji?" Shiru Barrister ya yi tare da cewa. "Wai daga ina kuke?" "Daga mansion mana?" Da mamaki yake kallonsa tare da cewa. "Duk wannan abun dake faruwa kana cikin ƙasar nan kuma a garin nan a cikin Asadullah mansion?" "Yanzu ba ta wanan nake ba, zan sanar da kai komai, yanzu ƴar mutane da ta yi kasada saboda ni nake so na ga ta dawo daidai." Har Barrister Haris zai tambaye shi wace kasadar sai ya fasa, don ya ce zai sanar da shi, duk da abun ya ɗaure masa kai. "Ina tunanin ko accident da muka samu ya sa yarinyar nan ta shiga cikin wani hali. Da na ga da waya a hannunta muka bar can amma yanzu ba waya a tare da ita ko ta yar da wayar a mota ne?" Jinjina kai Barrister ya yi sannan ya ce. "Amma ai accident ɗin da sauki na ga dukanku uku ba wanda ya ji ko ƙwarzane Allah ya kare ku, ba na tunanin accident da kuka yi zai iya saka ta cikin condition ɗin." "Ta ya zaka ce haka bayan lafiya lau take." Sulaiman ne ya danna ƙararrswa, ta cikin glass suka hango shi. Don na ciki yana ganin na waje, amma na waje baya ganin wanda ke ciki. Wani remote ne Asad ya ɗauka akan Centre table ya danna. Take ƙofar ta buɗe Sulaiman ya shigo. Baki sake da mamaki Sulaiman ke kallon Asadullah. "Sir kai ne?" Jinina masa kai ya yi tare da cewa. "Ni ne?" "Sir saukan yaushe a ƙasar tafiya ba sanarwa, har ina ƙaryata masu cewa ka bar ƙasar na ce ban ga fitanka ba." "Daga kai sai Barrister Haris wato lauyana ku biyu ne kuka san ina da wannan gidan, wanda na mallake shi ko mahaifina bai san da shi ba, ba wai ba boye masa ba ne sai dai na so na kawo shi ne bayan komai ya kammala Allah bai yi ba aka neme ni aka rasa. Don haka ba na son kowa ya san da ma dawo sai lokacin da na bukata." Da mamaki Sulaiman yake kallon uban gidan nasa, a hankali ya ce. "Sir ba za ka koma can mansion ɗin ba ne, kuma na ga Dad da Mom sun nuna damuwa na rashin ka har da su kar a sanar da su?" "Eh." Ya faɗa a takaice. Sai a lokacin Sulaiman ya lura da Jidderh, cikin mamaki ya ce. "Wanna ba ƴar aikin nan ba ne, me ya kawo ta nan." Bai bashi amsa ba sai cewa ya yi ya kara masa Doctor Isma'il. Ba musu ya ciro wayarsa ya sanar da Doctor Isma'il saƙon uban gidansa. Cikin damuwa yake tamabayarsa ya bar shi kwance ko jikin ne, ya ce masa a'a sai ya zo dai. Asadullah ya saka Sulaiman ya je ya siyowa Jidderh kaya da Hijab, don yadda take ba zai yiwa ma ta iya sanar da su gidansu ba. Bayan tafiyar Sulaiman ne Barrister ya masa sallama kan cewa sai ya sake shigowa. Godiya Asad ya masa sannan ya kalli Jidderh ya yi mata alamar ta tashi tsaye. A hankali ta mike kamar yadda ya bukata. Ya mata alamar da ta bishi . Tana biye da shi a baya suka nufi wani bedroom dake nan downstairs." Babban ɗaki ne mai ɗauke da saitin furnitures komai na more rayuwa akwai. Kai tsaye ya nufi bathroom tana biye da shi a baya. Sai da ya haɗa mata ruwa mai ɗumi, ya yi mata alama da ta yi wanka. Ya nuna mata towel sabo a cikin ledarsa sabulu komai har ma man goge baki sannan ya fita. Bayan Sulaiman ya dawo da kayan ne ya karba ya nufi ɗakinta. Ya ajiye kayan saman gado ya duba dogayen riguna ne kala uku da takami da Hijab. Ƙwanƙwasa ƙofar ya yi ya ji shiru sai ya tuna da yanayinta. Don haka sai ya bude ƙofar a hankali. Hango ta ya yi tsaye kamar yadda ya bar ta . Da alama ba ta san yadda za ta yi ba. "Innalillahi wa'inna'ilahi raji'un, me yake faruwa da ƴar mutane?" Shigowa ya yi yana yi mata body language yadda za ta gane abinda za ta yi . Bayan ya ƙara ruwan zafi ne sai ya cire rigarsa ya rage daga shi sai singileti. Wandon ma ya cire ya saura daga shi sai gajeren wando. Karasawa ya yi ya goge baki sannan ya yi wanka yana nuna mata yadda za ta yi wanka yana nuna mata tana kallonsa. Sai da ya gana ya yi tsamo-tsamo sannan ya haɗa mata wani ruwan ya ciro sabon brush ya mika mata yana mamakin yadda cikin ƙanƙanin lokaci komai ya shafe a cikin kanta. Yana miƙa mata brush ɗin ya ɗauki kayansa da ya cire, sai ta ɗaga rigarta za ta tuɓe a gabansa. Ba shiri ya yi hanyar fita da sauri har yana cin karo da ƙofa. _Zahrah_ Sanye take cikin doguwar rigar abaya shuɗi. Ta yi rolling da mayafin abayar. Ta yi matukar kyau sosai ba kaɗan ba, duk da ita ba ma'abociyar kwalliya ba ce powder kawai ta shafa sai lips glow wanda ya saka pink lips ɗin ta ke shinning Sanyayyaen ƙamshin turerenta ke tashi daga jikinta. Ta fito daga part ɗin Umminta A babban falon gidan ta hadu da ƴan matan gidan. Nabeela da Kusar sau harararta suke yi, kausar na cewa "sai neman mazan tsiya kullun cikin kwalliya da ƙamshi." Nabeela ta ce. "Wallahi Ammar ya fi karfinki ba za ki taɓa samun namiji wanda ya kai Yaa Ammar ba, sai dai ku ji labarinsa yana can da amaryarsa a UK wata kila ma idan a gidan nan ne ki ga ana taro." "Sai dai ayi da ke dan ni kin san na mutu a son Yaa Hilal." Kausar ta faɗa tana zubawa ƴar uwar ta ta idanu. Harara ta watsa mata tana cewa "Idan za ki cire idanunku akan my Hilal ki cire, don na wa ne shi. Ai Yaa Ammar ɗin ma fa ya haɗu duk da bai kai Yasa Hilal ba amma shi ma mijin nunawa sa'a ne." Nan suka fara sa'insa Maryam dai kallinsu take tana murmushi yayin da Nadeeya ta ce "Iska na wahalar da mai kayan kara, ku dinga faɗa akan Yaa Hilal wanda ko kallon banza ba ku ishe shi ba. Da ni ma na ɗaurawa kaina son sa amma tun da na ga alamar ba zan samu soyayyarsa ba na cirewa kaina dakon wahala." Maryam suka kalla kasancewar ita ce suka fito ciki ɗaya da Hilal ya sa Nabeela cewa "Maryam ba ki taba jin ya ce ga wacce yake so ba?" Taɓe baki Maryam ta yi tare da cewa. "Wake sanin halin da yake ciki, ko Mummy jiya da ya shigo na ji tana masa fadar cewa yana nuna halin ko in kula da kowa har da ita ba ta sanin halin da yake ciki ta ce dole ya fitar mata a cikin ƴan matan da suke sonsa har da ku ta ambata amma budar bakinsa ya ce shi bai ga maccen da ta masa ba da zai sure ta ba." Nadeeya ta kece da dariya tana cewa " ku na jin..." Ƙasa karasawa ta yi sakamakon ƙamshin turarensa da suka ji, alamar yana kusa da su kenan. Nan kowacce ta yi shiru suka dakar da firan ballantana dariya, kamar ruwa ya ci su haka suka yi tsit. Jin takunsa kamar yana nufo un da suke ne ya saka kowacd ta juyo ta kalle shi. Ƙananan kaya ne a jikina ya zuba hannayensa a cikin aljihun wandonsa. Fuskar nan tamau ba fara'a kamar kullun. Kowacce ta kasa ƙwaƙƙwaran motsi. Don sun san halinsa idan ya samu suna hayaniya ba karamin aikinsa ba ne ya zare belt ɗin wandonsa sai kowacce ta ji jiki. "Kausar ce ya sake kallonsa hararar da ya wurga mata ne ya saka ta sunkuyar da kai da sauri. "Gyara mun ɗaki." Abinda ya ce kenan ya nufi ƙofar fita cikin takunsa na mazantaka. Gabaɗaya suka amsa da to tare da masa a dawo laflya. Bai tanka masu ba ya fice . Sai da suka tabbatar ya yi nisa sannan Maryam da Nadeeya suka ƙyalkyace da dariya. Maryam ta ce. "Yanzu kuka gama ciki baki akan son da kuke masa, amma yana fitowa kuka yi kamar ruwa ya ci ku a haka za'ayi soyayyar?" Nadeeya ta amshime da cewa. Ni ma haka na gani da sai wata ta tashi ta karasa wajensa tana tamabayarsa fita za ka yi ko na zo na raka ka ne?" Kausar ta dafe ƙarji tana cewa "Wace ni, ai sai ya ci ubana la'ada waje." Nabeela ta ce. "Na taɓa gwada wa sau ɗaya na tare shi da niyyar ya rage mani hanya zai fita, ai kafin na yi magana kallon da na ga ya mani sai na daburce na rasa ta cewa." Dariya suka yi Maryan ta ce. "Ya Hilal kenan shi ake kira kamar maza tana ga mazuru ko ba faɗa akwai mugun kallo." Dariya suka yi kafin suka su huɗun suka nufi ɗakinsa don gyara masa. Zahrah da ta shiga Part ɗin Kakanninta ta tarar da Papa yana tsaye a falo yana cewa Dada ta fito su tafi. Da sallama a bakinta ta shiga Papa ya amsa yana kiran sunanta tare da tambayarta ya karfin jiki. Ta amsa a Alhamdulillah. Tana shiga ɗakin Dada ta same ta tana yafa mayafinta. "Dada fita za ku yi ba ki ce na shirya mu tafi tare ba?" "To tun da kin zo ai sai ki juya mu tafi ." Ɗakinta ta shiga ta ɗauko facemask ɗin ta ta saka, a tare suka bar part ɗin. Papa na gaba Dada da Zahrah na baya. Wata mota ta ga sun nufa wacce ba ta san motar a gidan ba, ba ta yi magana ba tana jiran su ƙarasa. Papa ne ya buɗe gidan gaba ya zauna gefen mai zaman banza. Dada ta bude bayan motar ta shiga, Zahrah ma ta shiga ciki. Ƙamshin da ta ji ne ya haifar mata da faɗuwar gaba, da sauri ta ɗaga kai ta kalle shi, suka hada idanu ta cikin madubin dake cikin motar. Gabanta ya tsananta faduwa don ba ta san shi da motar ba, kuma Allah bai bata ikon tambaya ba. "Ita kuma wannan fa ina za ta je ko akwai sa'anta anan ne da za ta bi mu?" Papa ya ce. "Ba ta san in da za mu je ba ka san ta saba fita da kakar ta ku shi ne ta biyo ta." Harara ya watsa mata tare de cewa. "Get out!" Ya faɗa a tsawace. Yunƙurawa ta yi za ta fita Dada ta rike ta tana cewa. "Wallahi ba za ta fita ba akan me ba na son takura ehe." Zai yi magana Papa ya ce . "Ka ja mota mu tafi ka san gaba za mu je daga nan." Kasancewar baya yi wa Papa musu akan komai ya saka ya yi shiru . Zahra kam shirin fita take yi Dada ta ce ki zauna ba inda za ki je." Ita kanta ba ta so ba don da ta san ba direba zai kai su ba ko da wasa ba za ta biyu Papa ba Kunkuni take yi kuma ya ganta ganin facemask din da ta sa yana motsawa. Kwafa kawai ya yi tare da yiwa motar key yana cewa. "Idan kika shiga hannuna sai kin faɗa mani abin da kike cewa." Ba abinda ta ce ba na son sharri." Dada ta faɗa cikin fada. Tafiyar mintuna talatin suka yi kasancewar a a hankali yake tuki. Wani tangamemen gate ya tsaya remote ya danna dai gate ɗin ya wangale kansa, ya danna hancin motar a ciki. "Ma sha Allah." Shi ne abinda Dada da Papa suke faɗa, Zahra ma haka ta ce a zuciysryarta. Don babban gida ne mai girma wanda ya ƙawatu da abubuwan more rayuwa. Dada ta ce "Gida ya kammala saura a ajiye iyali, ba a abinda ya rage maka yanzu tun da ka kammala burina na ga auren wannan tuzurun." "Haba Dada ni ne tuzuru?" Kafin su shiga zagayawa suka fara yi har suka iso wani garden, wajen gwanin sha'awa ha waken hutawa nan ga kayan marmari nan daga gefe can kuma ga swimming pool, gafe ga wani gado na kwanciya yana ɗan kaɗawa. Ciki da suka shiga a babban falon wanda ya gaji da haɗuwa. Cikin tsautsayi Rigar abayar Zahra ya ɗan harɗe mata ƙafa lokacin da za ta bi su upstair, kifawa ta kusa yi wanda cikin ikon Allah ba ta faɗi ba sai dai ta ture wani glass da fulawa masu kyau ne ciki, wanda hakan ya saka suka tarwatse, ƙarar ya janyo hankalin su suka kalli abinda ya fashe wanda aka ajiye shi a gefen benen. Kallon Hilal ta yi ta ga ya zuba mata rikitattun idanunsa masu firgita ta , yana aika mata da wani kallo. Gabanta ne ya fadi ta fara ja baya za ta shiga cikin fasassun glass ɗin *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ ❤️YAR GIDAN TAFEEDAH Beauty world ❤️ Kayan Matta Pure and Natural with Zero Side Effect *YAR GIDAN TAFIDA KAYAN MATA PURE AND NATURAL WITH ZERO SIDE EFFECT* *Matan gidan nan mace seda gyara , Ina masu fama da rashin sha'awa to matsalar ku ta kau in sha Allah,muna da abinda za ki sha ya canza miki yanayin jikinki ki fara jin kema macece.* Kina fama da matsalar rashin gamsuwa ko gamsar da me gida ? To ga solution🥰🥰. Ina macen da takeson ko yaushe ta jita ajiqe muna da abinda zamu ba ki ,kisha ya saukar miki da ni'ima💃💃💃. Mata masu son su gyara fatar su ,su dinga sheki da ƙyalli da haske me kyau bana bleaching ba ki zama kalar hutu🧖 Kuma akwai naku .🤩🤩 1. Gumban kwakwa da madara 2. Original tsumin Tabani ka ji ruwa 3. Original tabaje 4. Sweetener powder 5. Sweetener milk 6. Dilka soap 7. Snow whitening soap 8. Morroccan whitening soap 9. Pure sha butter 10. Special yaji and more Ina matan da suke son su zama na musamman agun oga,in nace ta musamman ina nufin karshen_ karshen ta musamman ajin farko ..... To ku matso nan kuji Yar gidan Tafida ta kawo muku ingantattun kayan mata 100% pure ba side effects in nace muku pure to pure Wanda akayi su da itatuwa masu kara lafiyar dan Adam 💃💃💃💯💯. *YAR GIDAN TAFIDA* Tana da alaidi Akwai pure man kadai Akwai gumba ta madara da kwakwa Akwai kuma hakki,akwai tsumi da original tabaje, sai kin gwada za ki gane sirrin 😜😍. *Duk products dinmu are 100% natural baby chemical,with zero side effects. Zaku iya tuntubata ta wannan layin 09032036606 Yar gidan Tafida 💯💯 Page4️⃣4️⃣ Kallon Hilal ta yi ta ga zuba mata rikitattun idanunsa masu firgita ta, yana aika mata wani kallo. Gabanta ya faɗi ta fara ja baya za ta shiga cikin fasassun glass glass ɗin. Ba abinda take tunawa sai ranar da ta shiga ɗakinsa Dada ta aike ta sai ta ga wani frame an zana butterfly cikin tsautsayi ta taɓa wanda hakan ya saka frame ɗin ya faɗo. Da ya ga ɓarnar da ta yi har ya saka ta punishment wanda tsabar azaba dai da ciwon athma ɗin ta ya tashi ta sume don wahala. Ga shi yanzu ta sake masa wata ɓarnar wacce tafi waccen ta san halinsa dole sai ta yabawa a aya zaƙinta. Hawaye ke bin fuskarta tana sake ja da baya. Dada da Papa na cewa ta dakata kada ta ji wa kanta ciwo za ta taka kwalba. Amma ina ba ta ma san me suke cewa ba tsoron Hilal ne fal a zuciyarta wanda ta san ba raga mata zai yi ba. Ta masa ɓarnar da ba ta kai wannan ba ya sumar da ita wanda har ta kasa tafiyar da ƙafarta ballantana wannan . Zame facemask dake fuskarta ta yi za ta bashi hakuri ganin yana matsowa in da take Ɗaga ƙafar da zata wanda idan ta aje ƙafar za ta ɗora shi ne akan wani tsinin kwalba da ke tsaye a sama, cikin zafin nama ya janyo ta da ƙarfi ta faɗo jikinsa. Bakinta ya mannu da ƙirjinsa. Tsabar firgita ba ta san ta ƙanƙame shi da hannayenta duka biyu ba. Idanunta a rintse suke gabanta na faɗuwa jiran hukuncin da zai ɗauka akanta kawai take jira. Kalaman da ta ji a ƙunnenta ne suka firgita ta ta zare idanu tare da sakinsa ba shiri . "Ban yi mamaki ba tunda kin saba bin maza kina haɗa jiki da su, to ni ba ƴan iskan samarinki ba ne da kika saba haɗa jiki da su kuna iskanci, kuma sai kin faɗa mani uban da ya maki ciki kika zubar a kwanakin baya." Ca baya kawai take yi tana kallonsa hawaye na wanke mata fuska tana girgiza masa kai. Kasancewa tana jikinsa ya yi maganar kuma a hankali ya yi hakan ya saka Dada da Papa ba su ji mugayen kalaman Hilal ɗin ba . "Zaharah lafiya kuma?" Dada ta tamabya ganin yadda take girgiza kai tana kuka. A tunanin su Papa sun ɗauka rumgumar Hilal da ta yi ya saka take ja baya tana tsoronsa kamar yadda yaran gidan sun tabbatar kowa na tsoronsa. "Ki kwantar da hankali Fatima Zahrah ai tsorata kika yi ba komai ba ne." Cewar Papa lokacin da ya karasa ya riko hannunta. Cikin kuka ta ce. "Papa wallahi ni ba ƴar iska ba ce ban taɓa aikata fasiƙanci ba." "Kada ku damu mun sani ku kwantar da hankalinki." "Zo mu shiga ciki mu ga ni ko?" Girgiza kai ta yi alamar ba za ta shiga ciki ba, rarrashinta suke yi ta yi shiru ta ce. "Zan jira ku a nan." Ganin ta kafe Papa ya ce . "Ba za ki shiga ki ga gidan Yayanki ba?" Murmushin ƙarfin hali ta ƙaƙalo ganin yadda Kakannin na su suka damu don haka ta ce . "Zan biyo ku yanzu bari na kwashe fasassun glass ɗin nan." Tana dube dube-dube idanunta suka sauka akan abun shafa har da kwandon zubawa ta hanga a wani corridor da za ta sada ta da wata hanya wanda ba ta san hanyar ina ba ne. "Papa mu je?" Ya faɗa yana masu jagora zuwa sama yayin da Dada ke ta mitar cewa ƙafarta na mata ciwo ya kawo ta in da za zata wahala. Zara kuka take yi tana share wajen zuciyarta na mata zafin Kalaman da Hilal ya faɗa mata. Tambyar kanta take yi shin me ta yi wa Ahalinta ne da zafi haka, gabaɗaya kowa na mata kallon ƴar iska watsatstsiya Kakanninta ne kawai ta san cewa ba sa mata wannan kallon sai iyayenta da yayunta. Da farko Aunty Laila wacce ta kasance ƙanwar Mahaifinta uwa ɗaya uba ɗaya ce ta fara jifarta da kalmar ƴar iska. Sai Mummy mahaifiyar Hilal da ita ma ta bi bayan Aunty Laila suke kiranta da karuwa. Haka ma Umma , Hawaye Masu zafi suka zubo mata. Sai da ta share wajen tass ta kwashe fasassun glass ɗin da kwalaben ta samu wuri ta rakuɓe ta kasa haurawa saman. Takunsa ta ji yana saukowa kafin ta ankare har ta gan shi a gabanta. "Ba ke kin iya barna kamar ɓera ba, to wannan karon ba ƙyale ki zan yi ba, albarkacin idanun du Papa kika ci ya saka ban maki komai ba, amma ina mai tabbatar maki sai kin biya ɓarnar da kika yi." Murya na rawa ta ce. "Nawa ne zan biya?" "Au har kina da kudin biya ne? Oh na manta ko wace ce ke kin sani kuɗaɗe wajen gasar karatun Alkur'ani ko? Sannan ga na samari da ake baki. To sai dai wannan ba da kudi za ki biya ba." Da sauri ta kalle shi ta ce. "Da me zan biya?". Shiru ya yi kamar ba zai ce komai ba kafin ya ce. "Ba kuma da jikinki za ki biya ba, domin kamar yadda kika..." Kuka me sauti ta sake wanda ya saka ya dakata da zancen da yake yi "Kukan uban me kike yi ƙarya aka yi maki ne, ina a gabana Aunty Laila ta ce ciki kaka zubar na dauke ki na kai ki asibiti Doctor ya sake tabbatarwa ƙwayoyin zubar da ciki kika sha ciki ya zube. Dan an yi magana ki dinga yi wa mutane kuka ƴar iska mai fuska biyu ana ana maki kallon nitsatstsiya mai kamun kai saboda ilimin addini da kike da shi alhakin bakya aiki fa duk Musa a baki ne Fir'auna a zuci." Sautin kukan ta ne ya ƙaru wanda ya saka har ta ji numfashinta baya fita daidai. "Uban me na maki kike kuka? Na dake ki ne, yanzu zan maki dukan tsiya a wajen nan kiyi kuka mai dalili." Ya yi maganar yana ɗora hannunsa akan belt ɗin wandonsa. Ganin haka ya saka ta kalli fuskarsa da sauri. Fuskarsa ɗaure tamau Babu sassauci ko kaɗan. Hannunsa ya dora a saman lips ɗin sa alamar ta yi shiru. Haɗiye kukan ta yi sai ajiyar zuciya take saukewa, ga numfashinta ya fara fita sama-sama alamar ciwonta zai iya tashi. Suna cikin wannan halin ne sai su Papa suka fito suna ta yaba kyawun gidan tare da masa fatan alkahiri da samun mace tagari. _Jidderh_ Ko da ta fito daga bathroom ɗaure da towel kamar yadda ya nuna mata. Ya shigo ya ajiye mata wasu kayan. Ya ganta tsaye . "Akwai matsala." Ya faɗa yana ƙarasowa wajen. "To idan mutum ma ya yi ya rasa tunaninsa sai ya rasa komai a ƙwaƙwalwa? Har wanka da shirya kanta ma ba za ta san yadda za ta yi ba.?" Ya ƙarasa maganar tamkar wanda zai yi kuka.ledar ya duba ya ga har da pant. Ɗaukar daya ya yi ya nuna mata yadda za ta yi sannan ya ɗauki doguwar rigar ya karasa in da take ɗure da towel, sai da Allah ya sa towel ɗin mai girma ne ya sauka mata. Bayan ya zira mata rigar ne ya nuna mata yadda za ta sake pant ya fice yana jinjina lamarin a zuciyarsa cikin damuwa. Yana fita ya tarar da Dr Isma'il ya karaso. Nan suka gaida ya tamabaye shi jiki ya amsa da Alhamdulillah. Bayanin lamarin Jidderh ya bashi da yadda take . Shiru Dr Isma'il ya yi kafin ya ce. "Maganar gaskiya dole sai an kai ta asibiti." Jinjina kai Asad ya yi tare da cewa. "Sulaiman sai dai ku tafi tare da ita." "Okay Sir " Sulaiman ya faɗa yana miƙewa. Asad ya koma dakin ta bar su nan tsaye.ba jimawa suka fito tana sanye da Hijabi ya masu jagora suka fita. Sai da ya ga wucewarsu sannan ya dawo ciki zuciyarsa fal tausayin yarinyar. _Maryam_ Suna shiga dakin Hilal kamar yadda ya basu umarnin su je su gyara masa part ɗin sa. Suna shiga falon nasa wani daddaɗen ƙamshi ya ziyarci hancin na su. Nabeela ta ce. "Yanzu wata rana fa nan ne falona ni da Yaa Hilal har na hango ni ina zuba masa shagwaɓa yana ta lallaɓani muna zaune s wancan kujerar." Ta yi maganar tana nuna kujerar mai zaman mutum uku dake falon. Gabadaya suka saka mata dariya wanda hakan ya saka Nabeela ƙuluwa da haushi. "Kin san Allah idan ma kina mafarkin cewa ko kin auri Yaya Hilal za ki masa shagwaɓa ta ɗauka kin yi kuskure. Domin shi bai san rarrashi ba ballantana lallaɓa mutum Abu guda ya sani shi ne hukunci a duk lokacin da kika masa ba daidai ba." Maryam ta yi maganar tana dariya. Kausar ta taɓe baki tana cewa. "Ni zan yi daidai da shi don na iya zama da shi kuma zan koya na jure." Nadeeya dai zama ta yi tana cewa "Kanku ake ji ƴan wahala kawai." Hotonsa dake manne a bango ne Kausar ta kalla. Sanye take da kakinsa ya yi kyau sosai. Shafa hoton ta yi tana murmushi. Madadin su yi aikin da ya saka su sai suka zauna suka ɓige da yin fira. Kusan mintuna talatin suna a haka suna fira kafin Maryam ta ce. "Mu tashi fa kada ya zo ya same mu ba mu yi masa aikin da ya saka mu ba." Nan suka tashi in da suka yanke shawarar mutane biyu su shiga su gyara bedroom su wanke toilet, sai mutane biyu su zauna su gyara falo. Da wannan shawarar suka yi amfani. Nabeela da Nadiya suka shiga don gyara masa bedroom. Maryam da Kausar suka tsaya gyara masa Falo. Nan ma suna shiga bedroom ɗin Nabeela ta zube a gadon tana shaƙar daddaɗen ƙamshisa. Nadiya ta ta shiga don wanke toilet. Tana shiga ta ga toilet ɗin tsaf . "Ni ban ga abinda za'a wanke a anan ba komai tas yake." Nabeela ta taso ta gani ta ji kamshi ne ma a ciki. Don haka ta ce. "Watsa ruwa kawai ki fito." Haka kuwa aka yi tana watsa ruwa ta fito. Suka dawo suna dube-dube a wajen madubi. "Kalli duk waɗan nan maiyuka da turaruka duk na mutum ɗaya ne, sai ka ce mace, duk nan fa mayukan jiki ne da ba gashi, sai turaren jiki da na jiki. Komai na sa disigner ne. Nadiya ta faɗa tana dudduba su yayin da Nabeela ma ke dubawa tana cewa. "Bari na fesa turaren masoyi." "Kada ki fesa kin san dai tutarensa ba gamagarin turere yake amfani da shi ba, sai an gane ki idan kika fita ko shi idan ya shigo zai gane ne kin san halinsa ." Jin haka ya saka ta ajiye tana cewa su gyara gadon. Duk da ba yamutsewa ya yi ba zanin gadon ma a gyare yake. Sai suka yaye bargon da zanin gadon suka hau kici-kicin gyarawa. Amma sai suka kasa shimfida zanin gadon da kyau, sun yi iya iyawarsu don ganin sun gyara gadon sun kasa. Sai haki suke yi duk sun gaji amma sun kasa shimfida zanin gado. Cikin ƙosawa Nabeela ta ce. "Wallahi Nadiya na gaji, ke ma kin san ba iya gyara ɗaki muka yi ba saboda masu aiki ke gyara muna ɗaki ta ya ya za mu iya wannan aikin tun da ba mu taba yi ba." "Gaskiya ne to yanzu ya za mu yi yanzu?" "Mu kira su Kasar ko za su iya gyaran." Fita suka yi nan suka same su a falo suna kuciniya su su ma ba iya aikin suka iya yi ba. Maryam ta jika towel da ruwa ta zuba omo sai kuma yake yi haka take ta laptawa Tv da duk wani abu dake wajen. Da suka abinda ya shafi glass dake wajen. Kausar kuwa ita ma ta sai mofin take tana goge tiles ɗin sai kumfa yake yi sosai ta zuba detergent. Suna cikin wannan halin suka zo suka same su, nan suka ce sun gama na su suka ɗunguma bedroom ɗin . Nan ma suka hadu su hudu suna kokarin gyara wajen amma sun kasa. Haka suka lulluɓa zanin gadon suka ɗora bargo akai. Irin mopping stick 🏒 suka ɗauko nan ma suka jiƙa masa ɗakin suka fice. Maryam ce ta ce "Kun san ba iya aiki muka yi ba tunda masu aiki ke gyara mana ɗaki ba za mu kira su nan su shigo su gyara masa ba?" "Ke ma kin san baya yarda mai aiki ta shigo masa part ɗin sa. Ko girkinsu kina ganin bai cika ci ba sai dai ya sha tea. Ko kuma ya tafi part ɗin Dada saboda ba ƴar aiki ke mata girki ba." "Wai ba Yaa Faisal ke gyara masa ɗaki ba, me ya saka yau bai yi masa ba?" "Yau da wuri ya fita kasuwa ." Maryam ta faɗa suka janyo masa kofar suka sauko Downstairs. Ba kowa don haka Kausar da Maryam suka nufi part ɗin su. Yayin da kuma Maryam da Nadiya kowace ta nufi part ɗin mahaifiyarta. _Sulaiman_ Yana nan zaune a asibitin yayin da Likitoci ke kan Jidderh don gano matsalar dake damunta. Yana nan zaune sai ga wayar Mom ya shigo cikin wayarsa. Ɗauka ya yi bayan sun gaisa daga can ɓangaren Mom ta ce. "Sulaiman ina ka shiga ne daga maganar CCTV Camera aka neme ka aka rasa?" "Mom na ɗan fit ne yanzu zan dawo." Kashe wayar ya yi yana fita da sauri don sanar da uban gidansa. Motarsa ya shiga ya yi mata key ya bar wajen . A falo ya samu Asad wanda ganin shigowarsa ya ce. "Ya aka yi ne ina take?" "Ban sanar da kai ba ne wallahi Mom ta kira ni akan bincike da za mu yi na gobarar da ya tashi to zan bincik..." "Kada ka yi wannan bincike ka ɓatar da komai da y faru." Kallonsa Sulaiman yake cikin mamakinsa. Jinjina masa kai Asad ya yi alamar tabbatar wa. Jinjina kai ya yi cikin girmamawa ya fice daha gidan. _Zahrah_ Tana nan tsaye a wajen da take sai haɗiyar kuka take yi , yayin da Hilal ke aika mata wani kallo. Har lokacin numfashinta baya fita daidai. Fita suka yi gabaɗaya don Zahra ta ce ba za ta shiga ba. A motar ne Dada ke cewa Zahrah za su biya gidan abokin Papa ɗansu ya rasu. Ko za ki je mu mu tafi tare?" Girgiza kai ta yi alamar a'a don tana don tana ji. Yadda numfashinta ke fita ba ta don Dada ta sani. Sai da Hilal ya fara ajiye Papa da Dada gidan rasuwa Sannan suka fita. Zabarah na bayan motar y dskata bai tayar da motar ba ya yi shiru. "Waye Direban ki da za ki zauna Mani a bayan mota?" Fitowa ta yi ta zo ta shiga gaban motar wajen me zaman banza. Gajeren tsuki ya ja sannan ya ja motar suka bar wajen. Har suka isa gidan ba wanda ya yi magana sai sanyin AC da ƙamshin dake tashi a motar. Bayan sun isa gidan ne ta fito da sauri don neman magani. Tana zauna kofar falo ta tura kofar tare da sallama. Mummy ce da Umma sai Aunty Laila. Ba su amsa ba kuma ba ta saka ran za su amsa ba . Sai da ta zo daidai in da suke har ta gifta Aunty Laila ta daka mata tsawa. "Ke!" Tsayawa ta yi ta juyo tafe da zuwa in da suke. Wani kallo Ne Mummy ta yi mata tana cewa. "Ya na ji ƙamshin turaren Hilal a jikinki?" Gabanta ya fadi tuna lokacin da ta tuna tsorata da ta yi ta rungume shi . "Ba komai." Ta fada da daƙyar. "Iskancin da kike yi da maza a waje yau ya zo kan Ɗana?" Umma ce ta ce. "Wannan mkirar yarinyar ba za ta fada ba, ya aka yi turaren rigarsa ya shafi rigarki?" Daidai lokacin ya shigo fuksar nan kamar kullun a murtuƙe. Kallonsa suka yi Aunty Laila ta taso da sauri tana duba gabar rigarsa in da shape ɗin laɓɓan Zahrah ya fito a rigarsa sakamakon fadawa jikinsa da ta yi da karfi lokacin da ya janyo ta . Maiƙon ne ya fito a a rigarsa kamar an zana. Zahrah tuni ta nufi part ɗin Umminta. Wani kallo Mummy ke yi masa. Aunty Laila ta ce "Son daga ina kake yanzu ?" "Sabon gidana da na kammala." Wani kallo suka masa kafin ta ce . "Waccen yarinyar Zaharah fa ina ka haɗu da ita?" "Tare muke tafi " Cikin yanayin rashin damuwa da yanayin da suke kallonsa ya nufi upstairs Yana cewa . "Bari na yi wanka." Daskarewa suka yi suna kallonsa.Yana shiga falonsa ya ɗauke idanunsa akan TV Wanda ya yi jirwayen fari-fari saboda kumafa. Haka duk abinda suka goge suka yi Centre table ma haka duk jirwayen. Ga tiles ma dake me duhu ne duk ya yi ya jirwayen wani wajen kuma ga ruwa nan kwance. Ransa ne ya yi mugun ɓaci ya taka zuwa bedroom. Ya ga sanin gadon an ɗan yafa ne har da bargon ga pillow duk a karkace. Toilet ya shiga nan ma ya sake ganin wani ɓacin ran.Turarrukansa ma da alama sun yi masa wasa da su Zuciyarsa har tafarfasa take yi ya nufi downstairs. Daidai lokacin da Faisal ke dawowa kallo ɗaya ya yi wa Yayan nasa a zuciyarsa ya ce . 'Tau fa waye ya taɓo wannan birkitaccen?' "Ka kira mani yaran nan dukkansu!." Ya faɗa yana zuba idanunsa da suka canza launi zuwa ja. "Yaa Hilal wasu yaran?" Hararar da ya jefa masa ne ya saka ya nufi part ɗin ƴan matan gidan don kiransu, a zuciyarsa kuma yana tausaya masu. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ ❤️YAR GIDAN TAFEEDAH Beauty world ❤️ Kayan Matta Pure and Natural with Zero Side Effect *YAR GIDAN TAFIDA KAYAN MATA PURE AND NATURAL WITH ZERO SIDE EFFECT* *Matan gidan nan mace seda gyara , Ina masu fama da rashin sha'awa to matsalar ku ta kau in sha Allah,muna da abinda za ki sha ya canza miki yanayin jikinki ki fara jin kema macece.* Kina fama da matsalar rashin gamsuwa ko gamsar da me gida ? To ga solution🥰🥰. Ina macen da takeson ko yaushe ta jita ajiqe muna da abinda zamu ba ki ,kisha ya saukar miki da ni'ima💃💃💃. Mata masu son su gyara fatar su ,su dinga sheki da ƙyalli da haske me kyau bana bleaching ba ki zama kalar hutu🧖 Kuma akwai naku .🤩🤩 1. Gumban kwakwa da madara 2. Original tsumin Tabani ka ji ruwa 3. Original tabaje 4. Sweetener powder 5. Sweetener milk 6. Dilka soap 7. Snow whitening soap 8. Morroccan whitening soap 9. Pure sha butter 10. Special yaji and more Ina matan da suke son su zama na musamman agun oga,in nace ta musamman ina nufin karshen_ karshen ta musamman ajin farko ..... To ku matso nan kuji Yar gidan Tafida ta kawo muku ingantattun kayan mata 100% pure ba side effects in nace muku pure to pure Wanda akayi su da itatuwa masu kara lafiyar dan Adam 💃💃💃💯💯. *YAR GIDAN TAFIDA* Tana da alaidi Akwai pure man kadai Akwai gumba ta madara da kwakwa Akwai kuma hakki,akwai tsumi da original tabaje, sai kin gwada za ki gane sirrin 😜😍. *Duk products dinmu are 100% natural baby chemical,with zero side effects. Zaku iya tuntubata ta wannan layin 09032036606 Yar gidan Tafida 💯💯 Page4️⃣5️⃣ Hararar da ya jefa masa ne ya nufi part ɗin ƴan matan gidan don kiransu, a zuciyarsa kuma ya tausaya masu. _Sulaiman_ Ko da ya koma Asadullah mansion ba kowa a wajen da abun ya faru, da alama kowa ya koma ɓangarensa. Kai tsaye ɓangaren su Mom ya nufa. Tana zaune a falo ita da Fauziyya. Wacce ke kallon Mom cikin damuwa take cewa. "Yanzu Mom waye zai aikata irin wannan aika-aikar?" "Sulaiman nake jira ya zo mu tabbatar da ko waye." Knocking aka yi suka bayar da izinin shigowa, Sulaiman ne ya gaida Mom. Ta amsa tana bashi izinin shiga part ɗin Asadullah ya bincika. Kasancewar Sulaiman amintaccen bodyguard ɗin Asadullah ne, ko lokacin da Asadullah kenan yana shiga part ɗin kai tsaye har cikin bedroom ɗinsa. Bayan ya shiga don tabbatar da wanda ya haddasa wannan gobarar ne ya janyo computer a gabansa bayan ya zauna kan kujerar dake gaban computer ɗin. Binciken abinda ya faru juya ya soma yi har zuwa yau . Ya girgiza matuƙa lokacin da ya ga Jidder ta nufi wata hanyar da abu a cikin hijabinta sai waige-waige take yi alamar ba ta da gaskiya. Sai dai bayan ta nufi bayan part ɗin ba ya iya hango ta, Don ba'a dasa cctv Camera ta bayan ba Sai dai ɓacewarta ba jimawa ya ga ta bar wajen a guje yayin da wuta da hayaƙi ke tashi daga can baya. Bayan Jama'a sun taru ga motar kashe gobara ta ƙaraso ne ta koma wancan hanyar a guje. Sai ta dawo tare da wani ya rufe rabin fuskarsa da hula sannan ga Facemask. Yana biye da ita. Duk da ba ganin fuskarsa ya yi ba amma ya tafiyarsa ya kalla da kyau ya gane cewa ubangidansa ne. Abin da ya girgiza shi kenan yana mamakin abun da idanunsa suka gani. Danne-danne yake yi yana sarrafa computer cikin ƙwarewa. Sallamar Mom ce ya ji ta shigo bayan ya amsa. "Sulaiman akwai abinda ka gani ka ga ko waye ya haddasa mana wannan ta'asar ko? Don a gakskiya ba za mu taɓa barin ko waye ba, duk da ba wani daga waje ba ne don akwai matakan tsaro a nan ba wanda zai shigo daga waje dole na ciki ne." "Mom a gaskiya tsawon kwanaki bakwai kenan da CCTV Camera ɗin nan ta daina aiki. "Abinda ya faru daga kwanaki bakwai zuwa yau duk ba sa cikin nan." Ya faɗa yana zuba mata idanu. "To ta ya hakan za ta faru?" Nan ya yi mata danne-danne yana nuna mata yana tabbatar mata da ba komai. Shiru ta yi kafin ta ce. "To ba hanyar da za'a gane ko waye?" "Gakskiya yanzu babu komai a nan, amma ina da hanyoyi da yawa da zan iya gane abinda ta faru ki bani kwana biyu." Jinjina masa kai ta yi cikin sanyin jiki tana cewa. "Allah ya ya sa." Da amin ya amsa sannan ya mata sallama ya fice. Zuciyarsa cike da tarin tambayoyi, me hakan ke nufi, dama kenan ta tabbata Asad na cikin gidan nan kamar yadda ya dage bai ga fitarsa daga cikin gidan ba a gidan ba har Uncle Adam na ganin laifinsa. Tsawon wannan lokaci ne hakan ke nufi kuma ya aka yi Jidderh ta san da zaman Asadullah a wajen. Sannan me ya sa Asad ya hana a sanar wa da Mom da Dad? Wadannan tarin tambayoyi sune fal a zuciyarsa ba shi da mai amsa masa waɗan nan tambayoyi dole sai shi uban gidansa. _Zahrah_ Tana shiga part ɗin Umminsu ta tarar ba kowa a falon, bedroom ɗin ta ta nufa cikin matsanancin sauri don ta ga numfashinta ya fara fita sama-sama. Side drawer ta buɗe. Inhelar ta ɗauko ta yi saurin kai shi bakinta har hannunta na rawa. Bayan ta shaƙa ne ta fara jin numfashinta ya na daidaita a hankali. Kwanciya ta yi tare da lumshe. Daidai lokacin Ummi ta shigo tare da Sallama. Ganin yamma ce kuma Zahrah in dai lafiya take ba ta kwanciya ta yi barci da yamma. Sanin haka ya saka ta ƙarasa gaban gadon da sauri. "Auta me ya same ki ne, ko ciwon ki ne ya tashi?" Gyaɗa mata kai kawai ta yi alamar eh, kafin ta sake lumshe Idanunta. Mayafin abayar dake kanta ya zame Ummi ta shafa gashin kanta tana mata sannu. Ya kamata a ce duk in da za ki je kuna tare da Inhelar kullum sai na fada maki." Ganin kamar Ummin ta shiga damuwa ya saka ta yi kokarin kawar da yanayin da take ciki, mumrmushi ta sakarwa Ummin sannan ta tashi tana cewa. "Bari na tashi Annabi ya hane mu da barcin yamma." Ta fada tana murmushi yayin da Ummin ma murmushin take sakar mata cikin so da ƙauna hadi da tausayin ƴarta. _Faisal_ Ko da ya shiga part ɗin ƴan matan gidan a nan ya same su a falonsu. Duk da kasancewar ba su cika kwana a part ɗin ba sun fi kwana part ɗin iyayensu. Amma idan ba dare ba ne nan suka zauna su yi fira. Sallama ya masu suka amsa suna masa sannu da dawowa har da tambayarsa tsarabar me ya kawo masu yau. Mumrmushi ya yi sannan ya ce "Tsarabarku na wajen Yaa Hilal." Gabansu ne ya faɗi suka kalli juna. A tare suka hada baki wajen cewa. "Ya dawo ne?" Kai ya jinjina masu sannan ya ce "Hope dai ba wata matsala." "To ai kiransa wallahi ba alkhairi ba ne." Maryam ta faɗa kamar za ta yi kuka. "Ba ku sani ba sai kun ke kun tambaye shi za ku san dalili." "Yaa Faisal me ya saka yau ba ka tsaya ka gyara masa part ɗin sa ba ne?" Nadiya ta yi maganar kamar za ta yi kuka ita ma. "Yau da wuri na wuce kasuwa customers na jira na, shi kuma bay tashi barci da wuri da na ga bai tashi ba na tafi bayan na tura masa text message a waya ." Kausar ta ce. "Allah ya sa mun masa daidai tsoro nake ji ya ce mu gyara masa part ɗin sa. Mu kuma ba iyawa muka yi ba tun da ba mu ke yi ba masu aiki ke mana, haka nan muka ƙoƙarta muka yi masa." Sai a lokacin Faisal ya gane dalilin ɓacin rai da ya gani akan fuskarsa. Dariya ce ta taso masa amma sai ya shanye ya ce su je yana jiransu kada su ƙara wa kansu laifi. Nabeela ce ta fara tashi ta ce su tashi su je su gani. Suna zuwa babban falon gidan suka ga Mummy da Umma sai Aunty Laila. Ganin yanayinsu Umma ta ce. "Lafiya kuwa kuke?" "Wai Yaa Hilal ne yake kiran mu." "Okay to ku je ku same shi ku ji." "Wallahi tsoro nake ji" Nabeela ta yi maganar tana kallon mahaifiyarta Aunty Laila. Ganin haka ya saka Sunyi Laila ta ce. "Ke ba na son rashin hankali daga kira sai ku fata tsoro wata kila akwai abinda za ku yi masa ne?" "Mu tafi don Allah kada mu yi laifi." Cewar Maryam ta na yin gaba zuwa hanyar matattakalar stage ɗin. Mara mata baya suka yi har zuwa falonsa layi suka jera kamar an ce su jeru. Sallama suka yi suka shiga ƙofar falon ya amsa can ƙasan maƙoshinsa. Kansa a ƙasa yana kallon ƙasan tile ɗin kamar me karantar wani abu a ƙasan Ɗago kai ya yi ya kalle su, yatsarsa manuniya ya saka ya shafi dogon karan hancinsa wanda ya dace da kyakkyawar fuskarsa. Ganin yanayin da suka same shi sun tabbatar ransa ya yi ƙololuwar tashi. Zuba masu rikitattun idanunsa ya yi ɗaya bayan ɗaya yake kare masu kallo kafin ya ce. "Me na saka ku kafin na bar gidan nan?" "Gyaran part ɗin ka?" "Me kuka yi yanzu?" Nan suka hau bashi hakuri suna cewa wallahi ba su iya ba ne. Cikin mamaki da takaici ya kalle su ya ce "Shut up!" Ya daka masu tsawa wanda ya saka suka zube a gabansa saman guiwoyinsu. "Ko kunya ba ku ji ba, kuna ƴaƴa mata ace ba ku san yadda za ku kula da muhalli ba? Tur da wanan rayuwar ta ku." Ji ya yi kansa ba masa ciwo ba zai iya dogon magana ba. "Na baku mintinan ashirin na ga komai yadda ya dace. Idan ba haka ba." Ya faɗa yana cije laɓɓansa na ƙasa. Ficewa ya yi ta ƙofar baya da ke cikin part ɗin na su. Cikin tsoro kowaccensu ta kasa magana sai aiki suke yi ta ko ina. *Washegari* _Asadullah_ Yana zaune kan sofa ya jingina bayansa idanusa alumshe kamar mai barci. Sallamar Dr Isma'il ne ya dawo da shi cikin duniyar da ya lula. A hankali ya bude idanunsa ƙawayan idanunsa da suka kasance blue ya sake su a kan Jidderh. Jallabiya ce a jikinsa fara duk wanda ya san shi kallo ɗaya za ka masa ka san ya rame. "Dr ya jikin na ta ina fatan dai ba wata matsala ko?" Asadullah ya tambaya cikin tausaya wa Zama Doctor Isma'il ya yi ba tare da ya ce komai ba. "Ka yi magana mana akwai matsala ne?" Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya kalli Jidderh sannan ya mai da dubansa ga Asad. "Yallaɓai a gaskiya duk binciken da aka yi ba wata matsala a tattare da ita. Ƙwaƙwalwarta lafiya lau take ba wata matsala. "Ban gane ba wata matsala ba yarinyar nan ba haka take ba accident muka samu " "Ban yi maka musun cewa ba accident kuka samu ba, ina mai tabbatar maka da cewa ƙwaƙwalwa yarinyar nan lafiya lau take babu wata damuwa s tattare da ƙwaƙwalwarta. Ko bugawa ba mu gani ba ƙalau take." "Ba ƙalau take ba!" Ya faɗa rai a ɓace. Duk yadda Doctor Isma'il ya so fahimtar da shi ƙi ya yi daga karshe dai hakura ya yi ya masa sallama akan gobe zai dawo. Kallonta ya yi ta zauna kan kujera ta dubawa TV. Sulaiman ne ya yi sallama ya shigo. Bayan ya gaida uban gidansa cikin girmamawa ne ya mika masa ledar hannunsa. Wata kwali ne y ciro daga cikin ledar, waya ce ya fito da ita daga cikin kwalinta. Har da sim card an yi register an yi komai. Saka sim card a cikin wayar ya yi ya saita komai. Har lokacin fuskarsa ba walwala. Sulaiman ne ya ce. "Sir zancen CCTV Camera na yi yadda ka ce yanzu ba wata matsala in sha Allah." Ya yi maganar yana kallon Jidderh wacce ba ta san me ke faruwa ba. "Gud job." Ya faɗa idanunsa akan wayar dake hannunsa. "Za'a kai yarinyar nan wani asibiti a ninki matsalar ta." "Sir me Doctor Isma'il ya faɗa?" "Wai laflya lau ƙwaƙwalwarta take." Da mamaki Sulaiman ke kallonta don tabbas ba haka ya san yarinyar. "To yallaɓai ya kake so ayi yanzu?" Shiru Asad ya yi kamar ba zai yi magana ba kafin ya ce. "A canza mata wani asibitin don gano matsalar amma ban gamsu da zancen cewa ƙalau take ban yarda ba." Jinjina kai Sulaiman ya yi kafin ya ce. "Ba damuwa zan kai ta asibiti maikyau ƙwararrun likitoci za su duba ta." Jinjina kai ya yi kafin ya tashi ya haura upstairs. Kai tsaye bedroom ɗin sa ja shiga. Ya wani na'ura ya danna dake manne jikin bango, take dai ga wata dorowa ta bayyana wanda ba za ka taɓa cewa akwai ta wajen ba. Kuɗaɗe ne a ciki jere daga kan Dollar har zuwa Naira. Ɗiba ya yi ya zuba a wata ƙaramar jaka kafin ya fita zuwa falo in da ya samu Sulaiman. Zama ya yi a in da ya tashi kafin ya ce. "Ya kamata ka nemo mata abun da za ta ci kafin ku tafi zuwa wani asibitn." Jinjina kai Sulaiman ya yi sannan ya mike tsaye ya nufi ƙofar fita ya fice. _Hilal_ Tsawon mintuna talatin ya ɗauka a wajen garden ɗin kafin ya bi ƙofar baya ya koma part ɗin sa. Ko da ya shiga tsaye ya same su dukkansu kowacce a tsorace take . Falon ya fara dubawa ya ga ba abinda suka gyara da alama iya iyawarsu kenan ba su iya komai ba. Idanunsa ne suka sauka akan home theater da ruwa ke ɗiga daga sama na shi zuwa ƙasa. T.V ma haka, Centre table ma haka. Bedroom ya koma ya ga sun gyara shimfidar zanin gadon amma lillubashi suka yi filon ma a karkace. Cikin ɓacin rai ya karasa in da suke yana zuwa kan Maryam dake ita ce farko ya ɗauke mata wani lafiyayen marin da sai da ta ji ji da ganinta ya ɗauke. Kafin ta ankare ya saka ƙafa ya harɗe mata ƙafa tare da zubar da ita ta fadi ƙasa wanwar. Haka ya yi masu dukkansu sai da suka zube suna ihu. Daga nan ya saka su tsallen kwaɗo suna yi suna kuka. Har sun gaji amma sun kasa tsayawa wa, sai da ta tabbatar sun gaji kafin ya dakatar da su. Kuka da majina suke yi iya jigatuwa sun yi. Kafin ya ce. "Kodayake ba laifin ku ba ne, saboda an sabgarta ku ba'a koya maku ba kasancewar ku mata waɗanda za su je gidan wani. Ko wane namiji ne zai yarda a ce yar aiki ke masa aikin gida?" Shiru ya yi kafin ya ce. "Ku tashi ku fice mani daga nan." Sun kasa tashi da rarrafe suka fice. Sai dai zuwa wajen matattakalar ya saka kuka don ba za su iya taka ƙafar ba. A zaune suna jan mazaunai suka sauko har lokacin kuka suke. Mummy, Umma, Aunty Laila da suke falon suka taso cikin tashin hankali jin kukan yaran na su. Cikin tashin hankali suka taso suke tambayar abinda ke faruwa. Ba su iya amsa masu ba, shi kuma Hilal ya hangi ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan ta fito bangaren Aunty Laila. Kiranta ya yi ya sanar da ita cewa ta kira masa duk ma'ikatan gidan, ta wuce jikinta na rawa . Cikin ƙufula Mummy ke kallon su Kausar kafin ta ce. "Me suka yi maka ne haka kana neman illata su?" Kafin ya yi magana masu aikin gidan suka karaso wajen . Kallonsu ya yi kafin ya ce . "Su waye ke gyara masu part ɗin su?" Ya yi maganar yana nuna su Nabeela dake jigace. Wasu ƴan mata masu suna Saude da Lami suka ce su ne. Jinjina kai ya yi kafin ya ce "Daga yau ba ƴanta ku daga yi masu aiki, kuma idan na ji labarin cewa kun gyara masu part kai ko tsinke idan kuka kawar sai kun bar gidan nan." Da sauri suka bashi hakuri suna cewa za su kiyaye. Mai da dubansa ga wata dattijuwar mata ya yi wacce suke kira da Baaba ya ce. "Mama duk sanda za ki yi girki a cikin gidan nan ki tabbatar yaran nan suna cikin kitchen kina koyar da su girki. Idan gari ya waye za ki shiga kitchen ki aika a kira su haka da rana ko yamma sai dai idan sun je school wannan ba matsala. A cikin sati biyu da koyon nake son su fara gwada wa. Idan wata ta yi maki rashin kunya ko cin mutunci ki sanar da ni." Jinjina kai Baaba ta yi sannan ta ce . "In sha Allah za'ayi yadda ka ce." Sallamar su ya yi suka fice, har lokacin su Maryam na kuka . A ƙufule Mummy ta sake magana . "Akan me za ka yanke irin wannan hukuncin sai ka ce ba na gaba da kai. Akan me za ka ce su za su dinga aiki sai kace Kai?" "Sunyi Laila ta ce. "Hilal me kake yi haka ne?" Daidai lokacin da Papa da Dada suka shigo bayan direba ya dauko su. Cikin damuwa suka karasa wajen in da Dada ke cewa "Meke faruwa haka me ya same su?" "Dada ki bar su tarbiyyar da aka kasa ba su ne nake ƙoƙarin ba su shi a matsayin wa tun da iyaye sun gaza ba su gatar da ake bawa kowace ƴa mace." Jin haka ya saka suka fahimci komai Papa ya ce wa Hilal ya rabu da shi haka, kafin ya nufi part ɗin su Dada na biye da shi a baya. Mummy ta sake ɓata rai ganin tana mahaifiyarsa bai saurare ta ba. "Ba da kai nake magana ba Hilal mu kake cewa ba mu ba wa yaran nan tarbiyyar ba sai kai ne za ka basu? To ka fita daga idanunna ba wanda ya isa ya saka yaran nan aikin da ka ce su yi tun da ba jakai ba ne, akan me me za ka wahalar da shi Allah ya hutar da su to wannan karon dole na taka maka birki." Mumrmushin takaici ya yi, Aunty Laila ta ce "Akan me za ka mayar da yara kamar marasa gata har da aikace-aikace ba za su yi ba." "Shikenan ku kuma mu zuba ni da ku wanda ya fasa." Cikin rawar murya suka hada baki wajen cewa za mu yi aiki. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ ❤️YAR GIDAN TAFEEDAH Beauty world ❤️ Kayan Matta Pure and Natural with Zero Side Effect *YAR GIDAN TAFIDA KAYAN MATA PURE AND NATURAL WITH ZERO SIDE EFFECT* *Matan gidan nan mace seda gyara , Ina masu fama da rashin sha'awa to matsalar ku ta kau in sha Allah,muna da abinda za ki sha ya canza miki yanayin jikinki ki fara jin kema macece.* Kina fama da matsalar rashin gamsuwa ko gamsar da me gida ? To ga solution🥰🥰. Ina macen da takeson ko yaushe ta jita ajiqe muna da abinda zamu ba ki ,kisha ya saukar miki da ni'ima💃💃💃. Mata masu son su gyara fatar su ,su dinga sheki da ƙyalli da haske me kyau bana bleaching ba ki zama kalar hutu🧖 Kuma akwai naku .🤩🤩 1. Gumban kwakwa da madara 2. Original tsumin Tabani ka ji ruwa 3. Original tabaje 4. Sweetener powder 5. Sweetener milk 6. Dilka soap 7. Snow whitening soap 8. Morroccan whitening soap 9. Pure sha butter 10. Special yaji and more Ina matan da suke son su zama na musamman agun oga,in nace ta musamman ina nufin karshen_ karshen ta musamman ajin farko ..... To ku matso nan kuji Yar gidan Tafida ta kawo muku ingantattun kayan mata 100% pure ba side effects in nace muku pure to pure Wanda akayi su da itatuwa masu kara lafiyar dan Adam 💃💃💃💯💯. *YAR GIDAN TAFIDA* Tana da alaidi Akwai pure man kadai Akwai gumba ta madara da kwakwa Akwai kuma hakki,akwai tsumi da original tabaje, sai kin gwada za ki gane sirrin 😜😍. *Duk products dinmu are 100% natural baby chemical,with zero side effects. Zaku iya tuntubata ta wannan layin 09032036606 Yar gidan Tafida 💯💯 Page4️⃣6️⃣ Cikin rawar murya suka haɗa baki wajen cewa za mu yi aiki. "Gud" Ya faɗa yana amsa kiran wayar da ake masa ya fice daga falon. Nan suka saka masu aikin suka taiamaka wa su Kausar zuwa part ɗin su. Zahrah bayan ta samu yi nutsuwa ne ta na zaune tana karatun Alkur'ani da kanta kasancewar ta haddace ta . Suratul Maryan take ƙarantawa cikin muryarta mai zaƙin sauraro. Kitchen ta nufa da niyyar taya Umminta aiki, sai Ummin ta fito take sanar da ita yau abincin gidan za su ci su ma, ta je ta yaya Dada girkin. Fita ta yi ta nufi part Dadar da sallama a bakinta. Suka amsa kafin Dada ta cigaba da cewa. "Ban ga laifin Hilal ba daidai kenan, iyayensu ba son gaskiya suke yi ba." Sannu da dawowa Zahrah ta yi masu kafin ta ce. "Dada me za ki girka ne, ko na gidan gabaɗaya za ki ci?" "Eh saboda yau na gaji ba zan iya girki nan ba, amma tun da kin zo shiga ki sama mana abu mai sauƙi." Kitchen ɗin ta nufa Daidai lokacin da Sunyi Laila ta shigo da sallama. Amsa mata suka yi ta shigo ta zauna tana cewa . "Barka da warhaka Papa. Dada ina wuni?" Ba wanda ya amsa mata, ita ma sai ta tsuke fuska. Tabbas ba sa jin daɗin abinda Aunty Laila da su Mom suke yi. Sai dai Aunty Laila ce suka haifa ita ce ƴarsu. Su Mummy da Umma surukai ne hakan ya saka ba su cika matsa masu ba sai Aunty Laila. Papa ne ya yi gyara murya ya ce. "Laila." "Na'am." Ta amsa bayan ta daga kai ta kalle shi. "Ba na sanar da ke cewa ki kwashi su Nabeela da Kausar ki mayar da su gidan ubansu ba?" Kara ɓata rai ta yi tana cewa. "Mutumin nan fa ya sake ni ya dauki matarsa sun bar ƙasar nan. Zan taho gidan ubana ne bar su wajen waye tun da bai damu da yaran ba. Kuma nan gidan Kakansu ne ai gidan Mahaifina ne. Ba na da inda zan kai su bayan nan Papa ka duba lamarin nan." Shiru ya yi kafin ya ce "Duk in da za ki kai su bai fi a ce suna gidan mahaifinsu ba ai da uba ake ado ba uwa ba." "Amma a baya lokcin da mahaifiyar Zahrah ta ce za ta tafi gida ta gaji ai cewa kuka yi ba za ta tafi da Zahrah ba don ba ta da in da ya fi nan. To ita kun yarda za ku rike ta ballantana yara na Kausar da Nabeela a ce su bar gidan nan." "Zahrah nan ne gidan mahaifinta ba ta da in da ya fi nan don nan ne adonta ba dangin uwarta ba." Nan ta basu haƙuri tare da cewa za ta mayar da su, amma a. Zuciyarta ta ayyana ba abunda zai raba ta da yaranta. Zabarah na kitchen tana jin duk tattaunawar da suke yi ta cigaba da aikinta. Shinkafa dafa duka na gargajiya ta yi, na manja ne ta zuba Daddawa da da busashshen kifi ya ji kayan miya amma ban da tumatir. Sai da ta kammala ta fito Daidai lokacin da ake kiran sallar magrib. _Isah_ Cikin damuwa ya yi sallama ya shigo cikin gidan, Inna da Aunty Sa'adatu ne ke zaune a tabarma tsakar gidan. Kallo ɗaya za ka yi masa ka san cewa suna cikin damuwa. Amsa sallar suka yi Inna ta mike tsaye da sauri tana cewa. "Isah ya ake ciki sun sun bar ka kuwa ka shiga cikin gidan?" Girgiza kansa ya yi cikin damuwa. Kuka Inna ta fashe da shi tana zubewa bisa gwuiwarta. "Innalillahi wa'inna'ilahi raji'un, ina yarinyar nan ta shiga ne, na yarda da ƴata na san ba za ta gudu zuwa wani wajen ba. Sai dai ban san hannun da ya faɗa ba bisa la'akari da zamanin da muke ciki." Sa'adatu ce ta kalli Mijinta wanda shi ma dauriya kawai yake yi, idanunta cike da ƙwalla ta ce . "To yanzu ina ya kamata a ke neman ta kuma?" "Duk in da nake tunanin ta je na je ban gan ta ba, hatta ƙawayenta ba su san in da take ba." "Gidan da take aiki fa ka sake zuwa ne?" "Ban sake zuwa ba Inna, waɗan nan security da nake daga masu ina neman ƙanawata dake aiki a gidan na masu kwatancen ta sun ce ba ta kai wa yamma take tafiya. Na nemi su bari na shiga ciki na gana da masu gudun ba su bari ba. Sai wata buduwarwa mai suna Suhailat it ce ta tabbatar mani da cewa Jidderh ba ta gidan su yake wa aiki." Ba karamin tashin hankali suka shiga ciki ba. Inna ta saka wa ranta za ta koma mansion ɗin ta nemi jin ta baki iyayen gidan Jidderh. _Hilal_ Ba shi ya dawo gidan ba Sa ƙarfe goma na dare . Har lokacin ransa a jagule yake. Bai nufi part ɗin sa ba ya nufi part ɗin Dada, kasancewar yunwa yake ji kuma har ga Allah ba ya son abincin masu aikin gidan. Kuma Mummynsa ba girki take yi ba sai dai Dada ba kullum take cin abincin masu aikin ba ita da Papa sai part ɗin su Abbi kuma. Da sallama ya shiga part ɗin wanda b wanda ya ji sallamar shi kaɗai ya ji kayansa. Zama ya yi a kan kujera mai zaman mutum ɗaya. Ganin yanayin fuskarsa ya sa sun fahimci har a lokacin ransa a ɓace yake. Dada ce ta ce "Abgona waye ya ɓata maka rai ne yanzu ya ga ɓacin raina?" Murmushi kawai irin ta su ta manya Papa ya yi kafin ya ce. "A bashi abu mai sanyi da abinci ya sha tukunna dai." "Ni fa ina fama da ƙafa ya je kitchen da kansa." "Angon ne kuwa?" Murmushi Dada ta yi ta nufi kitchen, abincin da Zahrah ta dafa ta zuba masa, sannan ta ɗauko jug wanda Zahrah ta haɗa masu zobo wanda da dafa shi da kayan ƙamshi. Ga cucumber 🥒 da ta yayyanka a ciki ana shan soɓon ana tauna cucumber. Sugar bai yi yawa ba daidai wa daida. Gefe kuma sai ga farfesun kazar da Zahra ta yi shi tun jiya suka saka shi a fridge, nan da nan Dada ta ɗumama ta kawo masa. Kasancewar a yunwace yake ya fara cin abincin, ya ji dadin shinkafar da ta ji Daddawa da kifi. Yana ji yana shan zobon wanda ya ji daɗinsa sosai da sosai. Sai da ya ci ya ƙoshi sannan ya ci farfesun. Kallonsa suke yi cike da so da ƙaunar jikan na su, wanda daga Zahrah sai shi ne suka fi soyuwa a cikin zuƙatansu. Yana tunanin yadda zai yi ya koma part ɗin sa. Ga shi kuma yadda aka ɓata part ɗin Faisal ba zai iya gyara masa shi yadda zai so ba. Gajeren tsuki ya ja wanda bai san ya fito ba. Papa ya ce. "Lafiya kuwa?" "Papa wallahi ɗakina ba gyara yadda ya lalace ma Faisal ba zai iya gyara Mani shi ba." Shiru suka yi kafin Dada ta ce. "Ina zuwa." Tashi ta yi daidai lokacin da ya koma kan kujera mai zaman mutum uku ya kwanta. Idanunsa a lumshe Dada na shiga ɗakin ta samu Zahrah ta shirya cikin riga da wando ba barci farare. Ta tufke kanta da ribbon ta sanya farin hula wanda ya kama kanta. Sanyayyaen ƙamshin turarenta ke tashi daga jikinta. Kallon Dada ta yi tana cewa. "Dada yau da wuri zan kwanta shi ya sa ban fito ba." Mumrmushin ta mayar mata da mrtani ta ce. "Don Allah ki Mani wata alfarma mana." "Dada kin fi ƙarfin kowace alfarma a wuri na, ki fadi ko me zan yi in sha Allah." "Ƴaƴanku ne ya nake so ki je ku gyara masa part ɗin sa saboda ba zai iya kwanciya a yadda yake ba." Da sauri ta sake kallon ta cike da mamaki take cewa. "Yaa Mahmud ko Yaa Sadik?" "Ai ba su kadai ne yayyunki ne yayyunki kadai ba, kada ki banbanta su da sauran duk da kasancewar ciki ɗaya kika fito da su na sani." Shiru ta yi cikin sanyin jiki ta ce. "Me zan yi Dada?" "Ki je part ɗin Babban yayanku ki gyara masa yanzu don Allah?" Sai da gabanta ya fadi sakamakon jin maganar Dada. "Yaa Hilal kuma?" "Eh don Allah ki je yanzu na san ba za ki jima ba, ya sa ƴan uwanki sun bata madadin gyara, kuma baya son masu aiki su shiga masa. Kuma Faisal ba zai iya yadda ya dace ba." Ba ta ce komai ba don ba t son ta tsaya jayayya da Dada don haka ta saka Hijabi ta fito. Papa ne a falon dai Hial wanda ya kwanta ya lumshe Idanu. Ƙamshin turaren ta da ya ji ya saka bude idanu sai zai bai ganta ba har ta fice. Kai tsaye ta nufi part ɗin nasa. Toilet ta fara shiga ta wanke shi tas sai kamshi yake yi. Kafin ta dawo bedroom, in da take tuninin za ta samu zanin gado nan ta duba, wani zanin gadon ta ciri ta zo ta shimfida ta gyara, rigunan pillows ta saka ta jera su yadda ya dace. Ta fesa turaren zanin gado a gadon. Ta ɗauko blanket ta shinfiɗa yadda ya dace. Mopping stick ta dauko ta yi mopping ko ina tas. Falo ta koma nan ma ta fara aikin goge kayan kallon. Sai da ta goge ko ina sannan ta yi mopping nan ma tas. Ta goge Centre table Centre Carpet dake jiƙe da ruwa ta cire ta fita da shi ta baya. A corridor ta hangi wani ta dauko ta shinfiɗa Sai da ta tabbatar ta gyara komai ta goge ta fesa room freshener spray ta maida hijabinta da ta ajiye . Fita ta yi bayan ta ja masa ƙofar. Komawa ta yi part ɗin Dada da sallama suna zaune su uku. Amsawa suka yi Dada ta kalle ta tare da Murmushi ta ce "Sannu ƴar albarka har kin gama." Eh kawai ta ce ta shige bedroom ɗin ta. "Ka tashi ga Zahrah can ta gyara maka part ɗin." "Zahrah kuma?" Ya faɗa fuksa a tsuke. "To idan ba ita ba ni ce zan gyara maka?" Bai ce komai ba ya mike ya nufi kofar fita, Papa na masa sai da safe bai amsa ba ya fita . "Wallahi wannan yaron lamarinsa sai shi." Yana zuwa part ɗin na sa ya tura ƙofar falon. Kamshin da ya ziyarce shi ne ya saka ya saki ajiyar zuciya. . A hankali ya furta. "Ma sha Allah." Ganin komai yadda ya dace har ɗaukar Idanu ya ga falon na masa. Komai sai sanbarka. Badroom ya nufa nan ma ya gan shi tass, ga shimfidar zanin gado an canza ya yi yi kyau. Toilet ya shiga ya ga ya fita tass. Kayan jikinsa ya rage ya shiga bathroom don yin wanka. Bayan ya fito ya shirye cikin kayan barci ya kwanta bayan ya yi addu'ar kwanciya barci. Ƙamshin da gadon ke yi ya saka ya tsinci kansa cikin nishaɗi. _Asadullah_ Sai Safa da marwa yake lokaci zuwa lokaci yake sauke idanunsa akan Jidderh. Kallon Sulaiman ya yi kafin ya fitar da huci mai zafi ya fara magana. "Abun mamaki ta ya ya za'a ce asibitoci uku kowanne suke cewa wai ƙwaƙwalwarta lafiya lau?" "Sir gaskiya sakamakon iri daya ne ba wani banbanci." "Idan nan sun kasa gano abinda ke damunta zan saka a fitar da iya waje." "Waje kuma yallaɓai?" "Eh ko kana da wani zaɓin ne?" Girgiza kai ya yi sannan ya ce. "Babu Yallaɓai " "Okay hakan za'syi ka san sun fi mu ƙwararrun kayan aiki in sha Allah za'a dace." "To Allah ya sa a dace." "Amin ya Allah, wace ƙasar za'a kai ta?" "India." Ya faɗa a takaice har lokacin idanunsa na ga Jidderh. _Innar Jidderh_ Tsaye take a tsakar gidan sanye da hijabi tana jiran fitowar su Isah da matarsa don zuwa Asadullah mansion. Tare suka fito daga cikin ɗakin Sa'adatu na gaba isah na biye da ita a baya. Ta goya yaronta a baya. A tare suka fita duk wanda ya kalli fuskarsu ya san cewa suna cikin damuwa. Mai keke napep suka samu a bakin titin layin na su . Sanar da su unguwar da zai kai su Isah ya yi kafin suka shiga ciki. Hanyar da za ta sada su da hanyar unguwar suka ɗauka. _Asadullah_ Yana zaune a falonsa shi da Barrister Haris. Cikin damuwa ya kalli Barrister Haris ya ce. "Kafin s tafi da yarinyar nan kasar India dole ina bukatar mace da za ta kasance tare da ita. Sai dai a yanayin da nake ciki yanzu ina bukatar sirri, akwai abubuwa da yawa a gabana wanda ya kamata a ce na aiwatar da su, amma halin da yarinyar nan ke ciki ya dankwafar da duk wani motsi nawa, ba na da burin da ya wuce a ce na samawa yarinyar nan mafita kafin na yi aiwatar da abubuwa dake gaba na. A yanzu ba na da wani burin da ya wuce na ga ta dawo daidai kamar yadda take a baya. Yanzu Ina son ka samo mani wata mace wacce za ta rike mani sirri. Ta zo ta kula da yarinyar nan su tafi tare zan biya ta ko nawa yake so in dai za ta yi Mani Mani abun da nake buƙata." " Shiru Barrister Haris ya yi kafin ya ce. "Akwai wata ƙanwar Matata mijinta ya rasu tana nan zaune tare da mu a gidana wajen matata. Na san za ta amince sai ta zo ta kula da aikin da kake bukatar na san ba za ta ba mu matsala ba zan mata gargadi sosai akan haka." "Okay ba damuwa za ka iya kawo ta." Sallama suka yi ya tashi ya mika masa hannu suka yi musabaha, kafin Asad ya ce . "Idan ka dawo za mu yi wata magana in sha Allah akwai binciken da nake so ayi Mani." "Okay in sha Allah." Daga haka suka yi sallama ya fice. _Inna_ Suna fitowa daga cikin keke napep ɗin Isah ya sallame shi. Da ƙafa suka ƙarasa har bakin gate ɗin Asadullah mansion. Nan security suka kore su ba su ma tsaya sauraren me ke tafe da su ba. Kuka Inna ta saka tana rokonsu su bari su shiga za ta yi magana da masu gidan ne. Daidai lokacin wata motar ta ƙara so wajen. Gainsu ya saka motar ta tsaya a hankali Glass ɗin motar ya zuge. A tare suka mike tsaye suka karasa jikin motar da hanzari jikin Inna har rawa yake yi. *Naman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ ❤️YAR GIDAN TAFEEDAH Beauty world ❤️ Kayan Matta Pure and Natural with Zero Side Effect *YAR GIDAN TAFIDA KAYAN MATA PURE AND NATURAL WITH ZERO SIDE EFFECT* *Matan gidan nan mace seda gyara , Ina masu fama da rashin sha'awa to matsalar ku ta kau in sha Allah,muna da abinda za ki sha ya canza miki yanayin jikinki ki fara jin kema macece.* Kina fama da matsalar rashin gamsuwa ko gamsar da me gida ? To ga solution🥰🥰. Ina macen da takeson ko yaushe ta jita ajiqe muna da abinda zamu ba ki ,kisha ya saukar miki da ni'ima💃💃💃. Mata masu son su gyara fatar su ,su dinga sheki da ƙyalli da haske me kyau bana bleaching ba ki zama kalar hutu🧖 Kuma akwai naku .🤩🤩 1. Gumban kwakwa da madara 2. Original tsumin Tabani ka ji ruwa 3. Original tabaje 4. Sweetener powder 5. Sweetener milk 6. Dilka soap 7. Snow whitening soap 8. Morroccan whitening soap 9. Pure sha butter 10. Special yaji and more Ina matan da suke son su zama na musamman agun oga,in nace ta musamman ina nufin karshen_ karshen ta musamman ajin farko ..... To ku matso nan kuji Yar gidan Tafida ta kawo muku ingantattun kayan mata 100% pure ba side effects in nace muku pure to pure Wanda akayi su da itatuwa masu kara lafiyar dan Adam 💃💃💃💯💯. *YAR GIDAN TAFIDA* Tana da alaidi Akwai pure man kadai Akwai gumba ta madara da kwakwa Akwai kuma hakki,akwai tsumi da original tabaje, sai kin gwada za ki gane sirrin 😜😍. *Duk products dinmu are 100% natural baby chemical,with zero side effects. Zaku iya tuntubata ta wannan layin 09032036606 Yar gidan Tafida 💯💯 Page4️⃣7️⃣ A tare suka mike tsaye suka ƙarasa wajen jikin motar da hanzari jikin Inna har rawa yake yi. Don sun tabbatar da cewa masu gidan ne suka zo, Kuma ganinsu da jin ta bakinsu zai iya tabbatar masu gaskiyar abun da suke son sani. Dad ne a bayan motar sai Mom wacce take zaune a gefensa yayin da direbansa ke gaban motar sun je ɗauko shi daga airport. "Bayin Allah lafiya?" Inna ce ta ke ƙoƙarin durƙusawa Mom ta yi saurin dakatar da ita da cewa. "Haba Mama don Allah ki tashi ba sai kin durƙusa ba, tashi mana." Ta faɗa fudkarta ɗauke da Murmushi. Kuɗi take ƙoƙarin ciro wa daga cikin jakarta, Inna ta yi saurin cewa. "A'a Hajiya ba abun da ya kawo mu kenan ba." "To me ya kawo ki?" "Zancen ƴata dake aiki da ku ne." "Okay ku shiga ciki sai mu yi magana ko?" Security ɗin ta sanar da su cewa a bari su shiga ciki. Nan suka bi bayan motar su zuwa cikin mansion ɗin. _Maryam_ Tun daga ranar da Hilal ya saka masu dokar yin aiki da kansu ya kafu. Domin ba ƴar aikin da ta shiga ɓangaren su da sunan yi masu aiki. Haka zalika duk sanda za'ayi girki a gidan suna nan su za su yi amma da taimakon masu aiki. Dan Maryam da Nabeela ke zuwa school su ma suna shekarar su ƙarshe ne, Nadeeya da Kausar kam sun gama. Zaharah dake ita ce ƙaramar gidan yanzu tana level 2. _Hilal_ Fitowa ya yi daga part ɗin sa shi da ɗaya daga cikin sojojinsa. Wanda ake kira da James. Yana gaba James na binsa a baya. James ya nufi ƙofar fita hannunsa rike da wata ƴar jakka. Hilal kai tsaye part ɗin mahaifiyarsa ya nufa. Daddy da Faisal ne a falon. Gaida Daddy ya yi sannan Faisal ya gaishe shi. Ya amsa sannan ya sanar wa Daddy zai koma America yanzu in sha Allah. Kallonsa Daddy ya yi sannan ya ce. "Dama yau za ka tafi sau da ka shirya muke sani?" "Kiran gaggawa na samu shi ya sa zan koma yau, da na so sai next week zan koma sai na sanar da ku yau." Jinjina kai Daddy ya yi cike da gamsuwa sannan ya masa fatan alkahiri. Faisal ma ya masa fatan alkahiri, kallonsa ya yi ya ce. "Ina Maryam?" Ya yanzu ta tafi school." Jinjina kai ya yi tare da cewa. "Okay" Bedroom ɗin Mummy ya nufa, knocking ya yi sai da ta bayar da izinin shiga sannan ya shiga. "Assalamu alaikum" "Ba ta amsa masa ba don a ƙule take da shi dama. Bai damu da rashin amsawar ba sai ya shiga ɗakin tana zaune a bakin gado fuskarta ba walwala. "Barka da safiya Mummy." Ba ta amsa masa ba sai ya yi shiru na sakanni kafin ya ce "Dama tafiyar gaggawa ce ga taso mani, zan koma US yau in sha Allah." Sai da ta yi kamar ba za ta yi magana ba sanan ta ce. "Hilal wai me ka ɗauke ni ne?" Ina matsayin mahaifiyarka amma idan ka shigo ka gaishe ni shikenan, ba za ka bani lokaci mu yi magana ko wata fira tsakanin uwa da ɗa ba sai dai waɗan can tsofaffin Kakanninka su ka mayar uwa da uba ko? Ka fifita matsayinsu da kowa a wajenka. Ba ka da wajen cin abinci sai wajensu. Ba ka da wajen fira sai ɓangarensu. Hatta gidanka da ka kammala kafin ka kai ni ko Daddynka sai da ka kai su abin takaici har da wannan yarinyar mai ƙirar aljanun har da ita ka kai. Wai ma Meye hadinka da ita dama jira nake ka amsa mani ya aka yi turaren rigarka ya shafi rigarka, sanan ga shatin laɓɓanta a gaban rigarka alamar ka rungume ta kenan. To ka sani matukar kana son zamanka lafiya cikin salama ko magana ba na ƙaunar ta sake shiga tsakaninka da Zaharah ba da iyayenta kamar yadda kowa gidan nan ya killace kansa daga gare su amma kai na lura kai kaɗai ne a cikin yaran gidan nan ke da ra'ayin riƙau wanda sai abinda ka ga dama kake yi. To ka sani kan wannan yarinyar zan iya aikata maka komai akanta." Ta karasa maganar tana huci. A ciyar zuciya ya yi yana duba agogo dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa. "Mommy na ga don na yi kusanci da Dada da Papa ba wani abu ba ne, su suka haifi Mahaifina da sune sanadin zuwansu duniya . Kuma gaskiya na fi jin dadi da samun nutsuwa a tare da su in dai ina kasar nan. Zancen Zahrah ko kusa ba na da wata ɓoyayyen alaƙa da ita ko iyayenta da yayunta." "Na dai faɗa maka ko Gaisuwa ban yarda ta haɗa ka da su ba don wallahi idan ka ce za ka bijire wa magana ta akan waɗan nan mutanen zan iya yafe masu kai ko ma na cire ka daga cikin ƴaƴana. Duk yadda ya kasance ƙanin mahaifinka kuwa." Bai ce komai ba don dai in da sabo ya saba jin tana masa fadar ya rage shigewa Kakannin na sa wai ba sa ƙaunarsu kowa sai Abbi da iyalansa. Sallama ya yi mata ya fice tana sake jaddada masa abun da take faɗa. Ɓangaren Abba ya nufa in da ya sake su gabadaya a falo. Gaishe da Abba da Umma ya yi sai Mansur da Nadiya suka gaishe shi. Sallama ya yi wa masu suka masa fatan sauka lafiya ya fice daga part ɗin . Daga nan ya nufi part ɗin Aunty Laila. Sallama ya yi Aunty Laila dake zaune a falo taasa masa. Bayan ta gaishe ta ne ya sanar da ita tafiyar da zai yi . Murmushi ta sakar masa tana cewa. "Yanzu da ka aminci an yi aurenka da Kausar ko Nabeela ai da ka ga sai ka tafi da matarka can American." Gajeren murmushi kawai ya yi wanda ya laɓɓansa kawai ya tsaya. Da "Na san a cikin su biyu ba za ka rasa wacce ta kwanta maka a rai ba. Mun yi magana da Mummyn ta ka ta ce za ta maka magana akai." "Aunty bari na wuce zan iya rasa jirgi." Ba haka ta so ba sai dai ta yi masa fatan sauka lafiya . Don ta tsara cewar idan Hilal ya auri ɗaya daga cikin yaran na ta sai ta san yadda ta yi Ammar ya auri ɗaya daga cikinsu. Daga nan ne ya nufi part ɗin Kakannin na su. Da sallama ya shiga ciki falon, Zaharah dake fitowa daga kitchen hannunta dauke da food flask da alama girki ta gama. Amsa masa sallamar ta yi daidai lokacin da suka haɗa Idanu. Harara ya galla mata fuska a murtuƙe. Ɗauke Idanunta ta yi daga kallonsa cikin sanyin muryarta ta ce. "Yaa Hilal da safiya." Bai tanka mata ba dama ta sani kuma hakan bai dame ta ba in da sabo ta saba. Wucewa ya yi ɗakin Papa duk da ya san cewa wanna lokacin yana barci. Kwance ya same shi yana barci kamar yadda ya yi tunani, 'Tsoho ni zan tafi sai mun yi waya in sha Allah.' Maganar da ya yi a zuciyarsa kenan sannan ya fice bayan ya shafi kan Papa wanda ke cike da furfura. Fita ya yi in da ya tarar da Dada a falo tana yi wa Zahrah sannu da aiki. Ganinsa ya sa ta saki fara'a tana cewa "Yaushe ka shigo?" "Yanzu, kuma zan koma U.S ne? "To kafin ka tafi ka zauna ka ci abinci ko?" "Ina sauri ne kin san jirgi baya jiran mutum." Addu'ar sauka lafiya ta yi masa ya amsa ya fice cikin zafin nama yake tafiya. Zaharah ta cigaba da jera abincinta sannan ta kalli Dada dake daman kwararo masa addu'o'i. _Mom_ Bayan direba ya yi parking motar ne ya yi saurin fitowa ya buɗe wa Daddy da Mom bayan motar suka fito. Sannan ya dauko kakar kayan Dad ya bi bayansu da shi. Bayan ya ajiye jakar a falo ne Mom ke sanar da shi idan wadan nan baƙin sun iso ya yi masu jagora zuwa ciki. Wato su Innar Jidderh kenan. Yana fita ya hange su suna t waige-waige suna kallon Mansion ɗin mai girma wanda suka kasa gane ko wanne ne za su nufa don su Mom sun ɓscewa ganinsu. Alama ya masu da hannu daga in da yake hangen su. Don haka suka nufo ɓangaren da suka gan shi. Jagora ya yi masu har zuwa bakin ƙofar falon. Bayan ya ce su shiga ne shi kuma ya fice. Shiga suka yi yayin da wani ƙamshi da sanyi ya ziyarci hancinansu. Ba kowa a falon don su Mom da Dad sun wuce falon ciki. Zama suka yi a saman tattausan Carpet ɗin da ke tsakiyar falon. Kasancewar Mom ce da girki ba Aunty ba. Don haka ta aiki ɗaya daga cikin masu aikin gidan akan ya je ta kai wa bakin dake wancan falon ruwa da lemu har da abinci. Fitowar Aunty daga part ɗin ta kenan don yi wa Dad Barka da zuwa. Fauziyya ma ta fito bayan Mom ta kira ta. Rungume Dad ɗin na ta ta yi cike da farin ciki tana ta dariya. "I miss you so much Dad." "Miss you more my Daughter." Kallon Aunty ya yi ganin bai gan ta tare da ƴart ba." "Ina Suhailat?" "Tana ciki." Ba ki fada mata zan dawo ba ne ko kuma dawowa ta?" "Ban fada mata ba Abban Asad." "Saboda ba ni ne mahaifinta ba ko?" "Ba haka ba ne..." Ba wani abun da za ki fada na dade da sanin turbar da kika ɗora ƴarki a kai, ki yi yadda kike so na ɗauke ta tamkar sauran yaran da na haifa amma dake ba ni ne ubanta ba ya saka kike mata shamaki da ni, da ma kowa na gidan nan bakya bari ta yi mu'amala da su musamman Asadullah nan san manufarki ba, Alhamdulillah ni ma na haifa." Kallon Mom ya yi yana cewa. "Zan shiga na yi wanka." "To Alhaji a fito lafiya. Bari na taiamaka maka da kayan da idan ka fito za ka saka." Ta yi maganar tana bin bayansa. Taɓe baki Aunyi ta yi tana bin bayanta da kallo. Fauziyya kam idanunta na kan wayarta da alama chatting take yi. Suna nan zaune Mom ta fito tana duba abincin da masu aikinta duka jera. Ba jimawa shi ma ya fito daidai lokacin da Mom ta fara ƙoƙarin yin savin ɗin sa. Kai tsaye ya nufi dinning area ɗin. Bayan ta zuba masa ne dai ga Aunty ta karaso wajen kasancewarsu tare suke cikin abinci in dai yana gari. Gudun ka da ya sake nuna ɓacin rai akan rashin zuwa. Suhailat ya saka Aunty ta kira wayar ƴar ta ta, shaida mata ta fito ta yi kafin ta katse kiran wayar. Mom ta zuba wa Aunty sannan ta zuba na ta abincin. Kusan a tare Suhaila dake part ɗin Aunyi da kuma Fauziyar dake chatting tare suka ƙarasa wajen dinning table. Mom ta kalli Dad da ya kasa cin abinci ta ce. "Dad ɗin yara na san meke damunka, ka yi hakuri ka ragewa kanka damuwa, muna muna ta addu'a kuma na saka malamai su yi masa addu'a in sha Allahu Allah zai bayyanar mana da shi ." Murmushi ya yi cikin jin dadin kalamanta. Sai dai ba damuwar Asadullah kawai ba ne a zuciyarsa yanzu har da damuwar Kamal dake prison akan mugayen halayyarsa. "Ba damuwoyi sun yi Mani yawa, ga ya rashin san in da Asadullah yake ga kuma matsalar Kamal dake gidan yari." Mom ta kalle shi ta ce. "Damuwar rashin Asadullah ce kawai a wajena, amma Kamal ba abun da ya dame ni da shi duk da ni na haife shi amma a yanzu na fi kowa tsanarsa ko sunansa ba na so na ji ana ambatar mani, mutumin da ya yi yunkurin kisan kai, kisan ma dai ɗan uwansa da ya zame masa gata a rayuwa? Me ya yi masa? Akan abun duniya wanda duniya za mu barshi gidan aro? Da ya yi kashe Asad da tabbas ya dade da mutuwa. Ko yanzu kamar matacce yake a wajena domin na riga da na rufe shafinsa dag cikin rayuwata." Taɓe baki Aunty ta yi tare da cewa. "Uhmm in ji mai ciwon hakori." Kallonta Mom ta yi tana girgiza kai kawai ba tare da ta ce komai ba. Dad ne ya kalli Aunty ya ce. "Zulaihat wai ke ba za ki taba sauyawa ba, har a wannan halin da muke ciki?" "To me na ce maku ne?" Tashi ta yi ta bar wajen abincin ma ba ta ci ba, ta koma main falon gidan. A can ne ta tarar da su Inna, kallon su ta yi sannan ta zauna kan ɗaya daga cikin kujerar dake falon. Inna da Isah da Sa'adatu suka gaishe ta. Ta amsa masu ba yabo ba fallasa. Ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ta jijjiga ƙafa. Bayan kamar mintuna goma sai ga Mom ta shigo tana kallonsu Inna da Murmushi a fudkarta . "Don Allah ku yi hakuri bayin Allah, na ɗan sha'afa ne kasancewar dawowar mai gidan kenan daga ƙasar." Murmushi Inna ta yi tana cewa. "Ba komai Hajiya." Zama ta yi sannan ta kira mai aikin gidan ta ce ta kawo masu abinci. Nan suka ce sun ƙoshi ba za su ci ba. Dole ta bar su don sun dage. "Me kuka ce yana tafe da ku ne ma?" Cikin rawar murya irin ta mai shirin kuka Inna ta ce. "Ƴata Jidderh dake maku aiki muka nema muka rasa tun shekaranjiya" Da mamaki Mom take kallo Inna, sai ta ce. "Haba Baiwar Allah tun shekaranjiya shi ne sai yau kike zuwa nemant" Isah ne ya ce. "Hajiya kwana biyu ina zuwa ba na samun shihowa saboda masu tsaron kofar ba su bari ba." Kallon Aunty Mom ta yi kafin ta ce. "Zulaihat kin ji wai yarinyar nan aka nema aka rasa." "Allah ya bayyanar da ta." Ta fada tana tuna turin kai irin na yarinyar. Mom ta ce. "Tun ranar da muka yi gobarar nan ta tafi gida ai ba ta dawo ba. Amma. Bari na kira abokan aikinta na ji ta bakinsu." Nan ta kira masu aikin gidan mata ta tambaye su kowa ya ce tun shekaranjiya na su sake ganinta ba. Kula Inna ta saka suka tashi suka mike don tafiya. Mom ta basu kudi masu yawa tare da masu addu'a Allah ya bayyana ta. Sa'adatu ce ga karbi kudin wanda za su iya kai dubi dari ta ciri a cikin jakkarta. Fita suka yi isah na rike da Inna suka fice daga mansion ɗin. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ ❤️YAR GIDAN TAFEEDAH Beauty world ❤️ Kayan Matta Pure and Natural with Zero Side Effect *YAR GIDAN TAFIDA KAYAN MATA PURE AND NATURAL WITH ZERO SIDE EFFECT* *Matan gidan nan mace seda gyara , Ina masu fama da rashin sha'awa to matsalar ku ta kau in sha Allah,muna da abinda za ki sha ya canza miki yanayin jikinki ki fara jin kema macece.* Kina fama da matsalar rashin gamsuwa ko gamsar da me gida ? To ga solution🥰🥰. Ina macen da takeson ko yaushe ta jita ajiqe muna da abinda zamu ba ki ,kisha ya saukar miki da ni'ima💃💃💃. Mata masu son su gyara fatar su ,su dinga sheki da ƙyalli da haske me kyau bana bleaching ba ki zama kalar hutu🧖 Kuma akwai naku .🤩🤩 1. Gumban kwakwa da madara 2. Original tsumin Tabani ka ji ruwa 3. Original tabaje 4. Sweetener powder 5. Sweetener milk 6. Dilka soap 7. Snow whitening soap 8. Morroccan whitening soap 9. Pure sha butter 10. Special yaji and more Ina matan da suke son su zama na musamman agun oga,in nace ta musamman ina nufin karshen_ karshen ta musamman ajin farko ..... To ku matso nan kuji Yar gidan Tafida ta kawo muku ingantattun kayan mata 100% pure ba side effects in nace muku pure to pure Wanda akayi su da itatuwa masu kara lafiyar dan Adam 💃💃💃💯💯. *YAR GIDAN TAFIDA* Tana da alaidi Akwai pure man kadai Akwai gumba ta madara da kwakwa Akwai kuma hakki,akwai tsumi da original tabaje, sai kin gwada za ki gane sirrin 😜😍. *Duk products dinmu are 100% natural baby chemical,with zero side effects. Zaku iya tuntubata ta wannan layin 09032036606 Yar gidan Tafida 💯💯 Page4️⃣8️⃣ Fita suka yi Isah na rike da Inna suka fice daga mansion ɗin. _Asadullah_ Fitowa ya yi daga bedroom ɗin ya sauko downstairs. Sanye yake da wando three quarter baƙi da jan shirt. Ya ɗan canza a cikin kwanaki biyu da barinsa wajen da aka ɓoye shi. Kyawunsa da cikar haibarsa sun kara bayyana. Zama ya yi a saman sofa ya kai hannu ya shafa tattausan gashin kansa wanda ya kwanta ya kwanta luf irin na fulanin usuli ya shafa tare da yin gajeren tsaki. Daidai lokacin ya ji ƙarar ƙararrawar ƙofa. Ta jikin gilashin ƙofar ne ya ya hango Barrister Haris tare da wata mace a tare da shi, wacce ba za ta wuce shekaru ashirin da biyar ba Remote ya danna ƙofar ta buɗe kanta suka shigo. Da sallama a bakinsu suka shigo falon, ya amsa ba tare da ya sake Kallansu ba. Barrister Haris ya karaso gabansa ya mika masa hannu suka yi musabaha sannan suka gaisa. "Ga ta nan ita ce ƙanwar Matata mijinta ya rasu ne kamar yadda na faɗa maka. "Ina wuni ranka ya daɗe?" Kallonta ya yi ya amsa ba yabo ba fallasa. Murmushi Anisa ta sake ' Barrister Haris ya ce. "An gama yi mata komai na shirin tafiya." Jinjina kai ya yi tare da cewa. "Ina fatan kin gane dalilin da ya sa na ɗauko ki, ina bukatar ki kula da iya fiye da yadda za ki kula da kanki." Kallonsa ta yi sakamakon jin kalaman Asad ɗin, wato ma fiye da yadda za ta kula da kanta. 'So so ne, amma son kai ya fi, kafin na hango abun da zai faranta ran wani dole sai na hango wanda zai faranta mani rai.' A fili kuwa sai cewa ta yi. "In sha Allah zan yi fiye da yadda kake bukatar." "Na wa ne farashin da zan biya ki? Sannan kuma ina bukatar sirri ba ma son kowa ya san wani abu game da ni ko wajen da nake ina fatan kin gane?" Jingina kai kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba. "Ba kya ji na ne?" "Kada ka damu yallaɓai na san kai sanannen mutum ne so ba zan taba fadar komai game da kai ba. Sannan farashi kuma ba sai ka biya ba don ni ka taimake ni ma a haka?" "Ki faɗa dole ne sai na biya ki kamar yadda na faɗa. "To ko nawa ne Allah ya sa albarka." "Account details." Ya faɗa yana sarrafa wayarsa. Karanto masa account number ta yi bayan ta gama faɗa take sai ga shigowar saƙo. Tana budewa ta ga 2 million ne ya tura mata Zare Idanu ta yi tare da cewa. "Miliyan biyu yau na Mallaka ta wa ta kaina?" Ta fada har da ihu tana kallon Barrister Haris. Murmushi ya yi tare da cewa. "Allah ya saka da alkhairi sir." Nuna mata ɗakin da Jidderh take ya yi sannan ya ce . "Ga ɗakinta nan, gobe in sha Allah za ku tafi. Tare da wani Doctor ku uku za ku yi tafiyar." Ba ta amsa ba sai zuba masa Idanu da ta yi kamar za ta cinye shi. Jin yanda Idanu ke yawo a jikinsa ya saka ɗaga kai ya kalle ta, da sauri ta ɗauke idanunta tana cewa. "Bari na shiga na same ta ." Bai sake magana ba ita ma ba ta jira cewar ta ba don ta ji kunyar kallon da ya mata. Tana tura ƙofar ɗakin da sallama ta shiga. Jidderh na kwance kan gado na barci take yi ba. Amma jin ƙarar ƙofar ya saka ta tashi zunne. Yanayin Anisa ne ya canza sakamakon ganin Jidderh cikakkiyar budurwa, kyakkyawar gaske. Ita a zatonta yarjnya ce ƙarama za ta kula da ita. Kuma ta shigo da niyyar yadda za ta samu kusanci da Asadullah ne. Sakamakon son da take masa. Duk da ba ta ji dadin da Barrister Haris ya sanar da shi cewa ta taɓa yin aure ba, ta so ya dauka budurwa ce ita . Sai dai abin tambaya Meye alaƙarasa da wannan yarinyar? A hankali ta tako zuwa in da take kwance kan gadon, har lokacin ba ta daina kallon Jidderh ba. Ita ma a ɓangaren ta ta zuba mata dara-daran Idanunta ne tana kallon bakuwar fuskar. Zama ta yi a gefen gadon, tana kallon Jidderh tare da sakar mata mumrmushi, don dole sai yarinyar ta saki jiki da ita. Doguwar rigar Material ce a jikin Jidderh, kanta ba ɗankwali. Kitson dake kanta ya fara tsufa. Rike hannunta ta yi tana murmushi sannan ta ce. "Sannu ƙanwata." Ba ta magana illa iya ka ta yi mata murmushin da ita ma shi ta yi mata. Tashi ta yi ta nufi gaban dreessin mirror ta duba kayan da aka jera a wajen. Komai sabo ne, don haka sai ta ga abun kwance kitso ta ciro. Zama ta yi bakin gadon sannan ta janyo Jidderh ta kwantar a saman ƙafarta. Ta fara tsefe mata kitson. Asadullah ne ya shigo tare da sallama. Anisa ta amsa masa ta daga kai ta kalle shi. Shi ko Jidderh yake kallo wacce ke yamutse fuska alamar tana jin tsifar. Ƙarasa wa ya yi gabansu har lokacin idanunsa na kan Jidderh. Har lokacin tana ɓata fuska kuma da alama ita ma irin masu jin zafin kai ne da ba sa son ana yi masu kitso ko tsifa. Alama ya nuna hakan bisa la'akari da yadda kitson ya tsufa alamar ya daɗe ba'a kwance shi ba. Sai dai ba datti alamar tana wankewa kitson ne dai ba ta so. "Ki yi mata a hankali akwai zafi." Ɗan karawa ta yi kafin ta ce. "Yallaɓai a hankali nake mata ba zafi." "Ya za ki ce ba za fi ga shi yanzu tana yi kamar za ta yi kuka." Ya karasa maganar cikin rashin jin dad'i. Daga nan ya fita ta bi bayansa da kallo. Har yanzu tana son jin alkarsa da yarinyar amma ba wanda za ta tambaya. Shi dai ba ta ga fuska ba. Yana komawa falon sai ga Sulaiman ya iso. Bayan sun gaisa ya kalli Asadullah ya ce. "In sha Allah nan da kwanaki biyu za'a kammala binciken, na jima a can don ban sake shi ba, ko da ya karaso yana da baƙi sai da na jira." Jinjina kai Asadullah ya yi tare da cewa. "Okay." "Sir ya kamata na rage yawan fita da nake yi, wannan zirga-zirga da nake ba na wajenka ba na gida zai iya janyo hankula jama'a ya dawo kaina. "Haka ne ya kamata ka koma idan da bukatar wani abu zan kira ka a waya." Sallama suka yi sannan Sulaiman ya bar gidan. Ko da ya koma Asadullah mansion ya samu security suka gaisa, ciki ya shiga ya fara gaisawa da abokan aikins. Wani mai suna Auwal ne ya ce. "Ina kake zuwa ne kwana biyu kuma sai ka fita, wani lokacin ma sau daya ko biyu ba. Alhaji ya dawo har ya tambaye ina ka je." Da sauri ya kalle shi jin Dad ya dawo. "Yanzu ya dawo?" "No ba yanzu ba ya jima da dawowa." "Okay." Ya nufi part ɗin Dad don yi masa sannu da zuwa, sannan yana addu'a Allah ya ba ba zai dame shi da tambayar kwakkwafi ba. Dad, Mom Aunty. Duka suna zaune a falon Sulaiman ya ya shigo bayan ya masu sallama sun amsa. Cikin girmamawa ya gaida Dad Ya amsa masa cikin sakin fuska da walwala. Sannan ya dora da tambayar sa. "Wai ya ake ciki ne zancen uban gidanka har yanzu ba wanda ya ji labarin ko an gan sa a wani wajen?" Girgiza kai ya yi kafin ya ce. "Har yanzu muna ta kokari kuma muna addu'a in sha Allah Zai bayyana mana da izinin Allah. Kallonsa Aunty ta yi kafin ta ce. "Na lura kwana biyu ba ka zama kamar yadda ka saba, ina kake zuwa " "Ba in da nake zuwa sai dai idan wani uzurin ne ya fitar da ni." "Wani uzuri ne zai fitar da kai wanda a baya ba ka fita?" Kafin ya bada amsa Dad ya ce. "Haba Zulaihata tun da ya ce uzuri ne dole sai ya faɗa maki?" "Hmm amma ai ɗaukarasa aiki aka yi kuma biyansa ake yi, duk da uban gidan na sa baya nan, ai an biya su ko last month duk da uban gidansu baya nan. Ni da kuɗin da ake kashewa na ciyar da waɗan nan ƙartin da salary na su ban ga amfanin su ba dan..." Dad ne ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu. "Ya Isa haka." Kallon Sulaiman ya yi sannan ya bashi izinin tafiya. Ya fita jiki ba ƙari don kalaman Aunty sun masa zafi." Bayan ta fita ne Dad ya ce. "Hajiya Zulaihat bakya kyutawa abun da kike yi." "Dama ai ba abinda za ka goyi bayana saboda ba matarso ta faɗa ba ." "Allah ya kyauta." Mom ta faɗa tana mikewa don komawa part ɗin ta. Aunty ta bi bayanta da harara. *Prison/ Gidan yari* Kasancewar yau ranar ziyara ce ga duk ilahirin ƴan gidan yarin. Wasu an kawo masu ziyara suna cikin nishaɗi. Wasu iyayen su ne suka zo masu wasu kuma abokansu ne suka zo masu, wasu kuma wasu daga cikin danginsu . Ɓangaren Kamal ma haka ne, an zo masa sai dai ba danginsa ba ne Family Doctor ɗin su ne ya zo masa. Suna tsaye a ƙafar da z ta sada su da in da Kamal yake. Kallo ɗaya za ka masu ka fahimci ran kowa a ɓace yake a cikinsu. Wani banzan kallo Kamal ya yi wa Doctor kafin ya ce. "Idan ma kana mafarkin cewa zan kara ba ka wasu kudi ne to ka farka. Me ka tsinana mani da zan ɗauki wasu kudade na baka?" Cikin ɓacin rai Doctor ya ce "Au haka ma za ka ce butulu, ko da yake ban yi mamaki ba, tun da har ka iya yunƙurin kashe Ɗan uwanka da kuka fito tsatso ɗaya Asadullah, mutumin da ya dauki so da yarda ya baka ka ci amnarsa ai ba abinda ba za ka iya aikatawa ba, aiki ka saka ni kuma na yi maka dole ka biya ni hakkina." "Wani hakkin zan ba ka Doctor? Ina ce ba ni na sace Asadullah ba, ban san su waye ba kuma ban san shirin su ba, abu ɗaya na saka ka shi ne ka kashe mani Asadullah shi sai na biya ka, burina na ji labarin mutuwarsa. Ka kasa yin komai lokacin da kake da damar yin komai dai da aka neme shi aka rasa ne za ka zo Mani da zancen banza wai na baka kuɗi akan me? Wallahi ƙwandala ba zan ba ka ba." Kallonsa Doctor ya yi kafin ya ce "Zan tona naka asiri idna har ba ka cika Mani alkawarin da ka yi Mani na cewa za ka bani miliyan goma." Dariya Kamal ya yi kafin ya ce "Don Allah ka yi sauri ka tona Mani asiri, a ranar da ka tona mani asiri a ranar ina mau tabbatar maka da cewa sai ka tsinci kanka a cikin gidan yarin nan. Kuma tsab zan fitar da kaina na bar ka a ciki. Domin ba ni na kama shi ba n na rufe shi ba ban san inda aka ajiye shi ba. Kuma ba ka da wata hujjar da za ka ce ni na saka ka. Tun wuri ka je nemi mafita ba zai ka nemo duk in da Asad ya shiga a faɗin garin nan.' Murmushi Doctor ya yi a kafin ya ce "Me kake ci na baki na zuba wandada suka kama shi har ya samu guduwa suna nan ana neman ruwa a jallo. Hankalinsu ya yi masifar tashi sosai don gudun tonuwar asirinsu." *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. ❤️YAR GIDAN TAFEEDAH Beauty world ❤️ Kayan Matta Pure and Natural with Zero Side Effect *YAR GIDAN TAFIDA KAYAN MATA PURE AND NATURAL WITH ZERO SIDE EFFECT* *Matan gidan nan mace seda gyara , Ina masu fama da rashin sha'awa to matsalar ku ta kau in sha Allah,muna da abinda za ki sha ya canza miki yanayin jikinki ki fara jin kema macece.* Kina fama da matsalar rashin gamsuwa ko gamsar da me gida ? To ga solution🥰🥰. Ina macen da takeson ko yaushe ta jita ajiqe muna da abinda zamu ba ki ,kisha ya saukar miki da ni'ima💃💃💃. Mata masu son su gyara fatar su ,su dinga sheki da ƙyalli da haske me kyau bana bleaching ba ki zama kalar hutu🧖 Kuma akwai naku .🤩🤩 1. Gumban kwakwa da madara 2. Original tsumin Tabani ka ji ruwa 3. Original tabaje 4. Sweetener powder 5. Sweetener milk 6. Dilka soap 7. Snow whitening soap 8. Morroccan whitening soap 9. Pure sha butter 10. Special yaji and more Ina matan da suke son su zama na musamman agun oga,in nace ta musamman ina nufin karshen_ karshen ta musamman ajin farko ..... To ku matso nan kuji Yar gidan Tafida ta kawo muku ingantattun kayan mata 100% pure ba side effects in nace muku pure to pure Wanda akayi su da itatuwa masu kara lafiyar dan Adam 💃💃💃💯💯. *YAR GIDAN TAFIDA* Tana da alaidi Akwai pure man kadai Akwai gumba ta madara da kwakwa Akwai kuma hakki,akwai tsumi da original tabaje, sai kin gwada za ki gane sirrin 😜😍. *Duk products dinmu are 100% natural baby chemical,with zero side effects. Zaku iya tuntubata ta wannan layin 09032036606 Yar gidan Tafida 💯💯 Page4️⃣9️⃣ "Me kake ci na baka na zuba? Waɗan da suka kama shi har ya samu guduwa suna nan suna nemansa ruwa a jallo. Hankalinsu ya yi masifar tashi sosai don gudun tonuwar asirinsu." Tsuki Kamal ya ja tare da cewa. " Wannan kuma matsalar su ce, ko na ce matsalarku ce, don idan asiri ya tono dole kai ma sai an kama ka. Don kai ma maci amana ne, kana matsayin likitansa amma suka siye ka don ka dinga yi masa alluran da da zai illata rayuwarsa ko? Ba su ne suke cikin tashin hankali ba kai ma kanka kana cikin tashin hankali don na tabbatar ba zai rasa sanin ko kai waye ba." Cikin Doctor ne ya ɗori ruwa domin ya san tabbas asirinsa zai tonu, dan wasu lokutan ma idan ya je don yi masa alluran yana cikin hayyacinsa, bisa la'akari da kallon da yake jifansa da shi wasu lokutan, sai dai bakinsa da hannunsa suna ɗaure ba halin ya ɗauki wani matakin akansa. Ya ɗauka a hankali alluran za su yi tasiri a jikinsa ne har ya kai ga rasa rayuwarsa, amma abun mamaki sai ga Asadullah garau sai abun da ba'a rasa ba. A zuciyarsa ya ce. 'Wane irin mutum ne shi?' Sai ji ya yi Kamal ya ce. "Ni ma tambayar da na sha yi wa kai na kenan, irin sukar da muka yi masa da wuƙa amma bai mutu ba." Sai a lokcin Doctor ya san cewa maganar zuci ce ta fito fili. "Ba na da lokacin ɓata wa alƙawari ka yi mani akan cewa za ka biya ni kuɗin..." Tsawar da Kamal ya daka masa ne ya saka shi dakawa da maganar da yake yi. "Idan ma ka na mafarki kan cewa zan. Aka kudi ka farka. Domin kuwa na saka ka kashe shi ka saka ba amfanin da ka yi mani, sannan idan har kana son na cika maka alkawarin da na maka to ya zama dole ka nemo in da yake ka kashe shi, idan ba haka ba kada na sake ganinka a in da nake." Ya ƙarasa maganar cike da gargaɗi. Wace wa ya yi ya bar Doctor yana bin sa da kallo. Karshe shi ma ya wuce don barin gidan yarin. _Zahrah_ Sanye take cikin riga da siket na atamfar, ta yafa mayafi da zai sauka ya rufe jikinta kasancewar rigar ta kama ta, kuma ta san akwai maza a gidan ba muharramanta ba ne. Wayarta ce ta soma ringing ganin Ammar ne ya saki mumrmushi ta zauna bakin gadon tana amsa wayarsa. kasancewar yau Juma'a kuma dama duk ranar jama'a wajibi ne ilahirin jama'ar gidan su ci abinci a tare. Kamar kowane juma'a yau ma wasu na zaune a dinning wasu na shirin fitowa. Dad, Abba, Mummy, Umma ne a dinning table ɗin. Abbi ya karaso wajen bakinsa ɗauke da sallama. Ba wanda ya amsa masa cikinsu kamar kullum. Ba sa amsa wa kuma baya fasa yi masu, sai dai idan suna ganin Papa da Dada ne suke masa masa sallama har da gaiswa na ganin Idanu. Zama ya yi bayan ya ja kujera ya zauna. Zamansa kenan sai ga Ummi ta karaso wajen sanye take da doguwar rigar Abaya. Sallama ta yi ita ma haka ba wanda ya amsa sai mijinta Abbi yana sakar mata mumrmushi. Kafin ya zauna ne sai ga Yaa Mansur da Faisal sun fito daga part ɗin su. Fira suke yi suna dariya. Suka karaso wajen suka gaida Dad da Abba, sai Mom da Umma. Ba su gaida Abbi da Ummi ba kamar yadda iyayensu suka ɗora su a tafarkin gaba da ƙanin na su da iyalansu. Sunyi Laila ma ta yafi daga part ɗin ta tana waya da wata ƙa ƙawarta. Bayan ta zauna ne ta yi wa kawarta sallamarsa ajiye wayar. Kallon Dad, ta yi ta ce. "Yaya ina kwana?" Ya amsa mata cikin walwala kamar kullum. Sannan ta kalli Abba ta ce. "Yaya Ina kwana." "Lafiya lau Autar Dada ya kike?" "Alhamdulillah" Suka gaisa da su Mummy da su Mummy da Umma. Mansur da Faisal suka gaishe ta, ta amsa tana saka masu albarka. Abbi duk da kasancewar sa Yaya ne ne ga Sunyi Laila amma hakan bai hana shi ce mata. "Ina kwana Laila?" "Auhm mutum dai ba Zuciya kamar ya yar kare ya ɗauka. Ko dole ne sai na yi maka magana. "Wai Abbi ka dole ne sai ka shiga sabgar su ne, ko a wajen Allah ba ka da laifi ka fita hakkinsu . Ka yi masu magana sau daya biyu uku ba sa amsa maka to meye amfanin ci gaba da gaishe su. Ka yi rayuwrka da Ummi da Yaa Mahmud ga Auta Zahrah mun ishe ku don Allah ku fita daga harkar mutanen nan. Wanda ya ce baya yi da kai ka manta da shi ka ɗauka cewa sun mutu." "To fitsararre mara kunya, dama na san sai kai da ka fita Zakka." Ta karasa maganar tana yi wa Sadik wani banzan kallo. Taɓe baki ya yi da niyyar zai sake mayar mata da martani Ummi ta daka masa tsawa. Dole ta saka ya yi shiru. "Ƙanwar mahaifinka ce ita ce abikinyar sa'insa a gare ka?" "Ummi don ki bar ni na fada masu gaskiya. Ita da take masa rashin kunya ai Yaya ne a wajen ta. Me kuka yi masu a ce kuma jini ɗaya uwa ɗaya uba ɗaya amma ku ware mutum ɗaya ku ɗora masa karan tsana bisa wani banzan dalilin ku da bai da tushe." Abba ya tashi a fusace ya ce. "Za ka rufe wa mutane ba ki ko sai na saka yanzu an koya maka tarbiyyar da iyayeka suka ba ka?" "Ai a gidan nan ban ga mai tarbiyyar da zai koya mani tarbiyyar da aka kasa ba ni ba." "Ka iya bakinka Sadik wallahi yanzu zan kwaɓe riga mu daku a nan a banbance tsakanin aya da tsakuwa." Mansur ne ya yi maganar yana tashi tsaye yana huci. Dariya Sadik ya yi tare da cewa. "Oh ashe ba dad'i ka ga ana cin mutumcin iyayenka ka ƙyale, da ake yi wa Mahaifina ina kallo har da murnushi kake, yanzu da na mayarwa mahaifinka da martani ka ji zafi ko?" Yaa Mahmud ne ya rike hannun ƙanin na sa Sadik yana cewa "Ya isa haka Sadik." Zai yi magana amma ganin kallon da Abbi da Ummi ke masa ya saka ya yi shiru. Don da ido sukan tsawatar da yaransu kuma su hanu. Daidai lokacin Maryam, Nadiya, Kausar, Nabeela suka fito daga kitchen hannunsu rike da food flask. Kasancewar Hilal ya saka su yin girkin dole tun daga ranar tare da su ake girki kuma suke service ɗin mutanen gidan dokar da Hilal ya saka masu kenan. Papa da Dada ne suka fito tun daga nesa suka hango Mansur da Sadik suna yi wa junansu kallo mai cike da gargaɗin juna. Gyaran murya Papa ya yi wanda ya saka kowa shiga taitayinsa. Don ba wanda baya baya shakkar Papa a familynsu gabaɗaya. Kowa ya nemi wurin zama. Sai dai masu zuba abinci ne kawai a tsaye suna serving ɗin su. Kowa ya gaida Papa da Dada cikin girmamawa. Ganin ba Zahrah ne ya sa Papa cewa. "Ina Zahrah?" Ummi ta ce. "Na barta ta fito wanka ta ce tana zuwa ga ta shiru har yanzu." "Idan ta ji yunwa ai za ta fito da kanta, yunwa ba ƙanwar uwa ba ce uwa ce da kanta." Aunty Laila ta yi maganar tana tura soyayyen ƙwai a baki. Kafin kowa ya yi magana sai ga Zaharah ta ƙaraso da sallama. Kasancewar ta gaida iayakinta da yayunta shi ya sa da ta yi sallama ta suka amsa gabaɗaya, don su Papa na wajen ne kowa ya amsa mata. Cikin girmamawa ta durkusa ta gaida Papa da Dada. Suka amsa mata cikin sakin fuska da walwala cike da so da ƙaunar da suke mata. Kuma ba komai ya saka suke son ta ba sai don halayyar ta da ɗabi'unta wanda ya sha banbanci da sauran yaran gidan. Daddy ta fara gaisar wa, ya amsa mata kamar an yi masa dole. Daga nan ta gaida Abba shi ma haka ya amsa mata. Daga nan ta gaida su Mom suka yi kamar ba su ji ba, sai da Papa ya yi fada suka ba shi haƙuri wai ba su ji ba ne. Kallon su Mansur ta yi da niyyar gaishe su duk da ta san ba amsawa za su ba Sadik ya dakatar da ita ta hanyar watsa mata harara, tura baki ta yi ta zauna. Zaman ta ke da wuya sai ga kiran Ammar ya shigo wayarta. Ɗauka ta yi tare da yin Salma ta ce. "Assalamu alaikum, Yaa Ammar zan kira ka anijma." Gabaɗaya kowa ya kalle ta, Nabeela da Kausar na sakin tsuki a tare. Ruwan shayi kawai ta ɗiba sai bread. Don ba z ta iya cin girkin su ba, don ba dad'i yake yi mata ba. Dada da aka zuba mata farfesu kasa ci ta yi, Papa ne ya ɗan ci dankalin turawa ya ɗan ci, nan ma ya ji bai soyu ba. Haka ya ajiye . Yaa Mahmud da Yaa Sadik da suka saba da daddaɗan girkin Ummi da na Zahrah. Ba za su iya cin wannan ba. A baya suna cin na masu aikin, amma tun da yanzu ƴan matan ba sa yarda masu aikin su nuna masu yadda za su yi komai, take za su fara masu masifa. Abincin dai ga shi nan haka dai kowa ya ɗan tsakura ba su iya cin na kirki ba. Haka dai a hankali kowa ya watse da wajen masu zuwa office suka tafi. _Asadullah_ Fitowa ta yi daga bedroom ɗin sa zuwa falon. Daidai lokacin da kukunsa ya ke jera abinci a dinning table. Kasancewar yau Barrister Haris ya nemo masa kuku da zai dinga dafa masu abinci a gidan. Sualaiman ne ya shigo kasancewar sun yi magana ya ce masa ya ƙaraso. Hakan ya saka ya fito. Bayan kukun ya gama jera abincin ne ya karaso wajen su yana cewa "Barka da dare Yallaɓai." Kai ya jinjina masa ba tare da ya ce komai ba. "An kammala jera komai a dinning table." "Okay sannu da aiki." Ya amsa yana barin wajen. Asadullah ya kalli Sulaiman ya ce. "Idan Allah ya kai mu da safe za su tafi tare da Doctor Isma'il. Sai dai mu yi mata addu'ar Allah ya bata lafiya. Na san duk in da iyayenta suke hankalinsu ya tashi sakamakon rashin sanin halin da take ciki ba." Jinjina kai Sulaiman ya yi sannan ya ce. "Gaskiya ne, da irin wannan gara ko gawar ɗanka ne ka gani ka san cewa ka rasa shi da rashin sanin halin da yake ciki." "Ka gwada yin bincike ko Allah zai sa a samu bayanin in da iyayenta suke." "Okay sir." Sannan abu na biyu, ina son duk in da family Doctor na mu yake, ka tabbatar ka kawo Mani shi a cikin gidan nan, saboda duk da wani lokacin ba na sanin abin da ke faruwa amma tabbas ba zan mance fuskarsa ba, kamar yadda na baka labarin komai." "Bayan shi ba za ka iya tuna komai ba?" "Ba abin da zan iya tunawa, sai dai yakan yi waya a gabana, da alama umarni yake karba, bayan ya yi Mani allura ba na sake sanin komai." "Kar ka damu zan kamo shi zai yi bayanin wadanda suka saka shi wannan aiki." "Ka tashi ka je ka ci abinci." Tashi ya yi ya nufi dinning area. Asadullah kuwa ya nufi ɗakin da su Jidderh suke. Sai da ya yi knocking Aninsa ta amsa sannan ya shiga . Jidderh na zaune tana kallon TV kamar Idanunta za su fito, Anisa na zaune a gefenta tana danne-danne a waya. "Barka da dare." Anisa ta faɗa tana ajiye wayarta. Zama ya yi gefen Jidderh yana sakin murmushi. "Kallo ne haka kamar za ki fitar da Idanun waje?" Kallonsa ta yi ganin yana mumrmushi ita ma ta masa tana kallonsa. "Gobe da safe za ku tafi Allah ya baki lafiya." "Amin." Cewar Anisa tana murmushi, kallonta ya yi ya ga shi take kallo fuskarta dauke da murmushi. "Ku fito ku ci abinci." "To za mu fito." Ya fita ya bar su. Yana fita Anisa ta dauki waya ta kira Barrister Haris. Yana ɗagawa suka gaisa . "Wai Yaya Haris Meye tsakanin Asad da yarinyar nan, ina nufi alƙarsu da ita?" ",Aiki ya kai ki ko binciken dangantakar su da yarinyar?" "Aiki mana." "To ki tsaya iya abinda ke gabanki." Tura baki ta yi kafin ta kashe wayarta. Tashi ta yi tana sake zaman riga da siket dake jinkinta, wanda kamar za ta yi nishi su yage. Don sun bayyanar da surar jikinta sosai. Ba tare da mayafi ko hijabi ba ta tashi tana jan hannun Jidderh wacce ke zaune sanye da doguwar riga kanta ba ɗankwali. Gashinta da Anisa ta gyara mata ya sauka a kafaɗarta da ta tufke mata shi. Jin kishin yarinyar ta yi don haka ta dauki hula bayan ta nannaɗe mata gashin ta saka mata hula don kar ma ya birge Asadullah idan suka je. Tare suka fita tana rike da hannunta suka fito daidai lokacin da Sualaiman zai tafi, Asadullah na sake tabbatar masa gobe ya tabbatar ta zo da Family Doctor na su ko ta halin yaya. "Okay sir, good night." Ya faɗa ya fice. Asadullah na zaune a dinning chair yana shan shayi, Anisa ta zaunar da Jidderh kan kujera sannan ta zauna ka. Kujerar dake fuskantar Asad. Zuba wa Jidderh jollop ɗin cuscus ta yi sannan ta zuba na ta, sai farfesun kazar da ta zuba masu. Nan suka hau ci bayan ta zuba masu ruwa da lemo. "Yallaɓai na zuba maka ne?" "No need." Ya faɗa. Yana kallon Jidderh dake cin abinci. "Amma na ga ruwan shayi ba abinda zai maka." "Haka nake buƙata." Ganin yadda hankalinsa ke kan Jidderh ya saka Anisa ba wa Jidderh kulawa na musamman har tana ba ta abinci a baki. Hakan ba karamin daɗi ya masa ba. Har ya saki jiki suka fara fira da Anisa kuma duk akan Jidderh. Tana ƙoƙarin bugun cikinsa don gane dangantar dake tsakanin su. Amma bai ba ta damar jin abinda take son ji ba. Sai dai ta gane cewa ta hanyar Jidderh ne kawai haƙanta za ta cin ma ruwa. Don haka sai nata saki murmushi da ita kadai ta san ma'anarsa. Kati ya mika mata mai ɗauke da lambar wayarsa. "Idan kun je can sai ki nemi ni bayan an saka maki kayi na can ƙasar." Tashi ya yi yana yi masu sai da safe ya haura upstairs. Anisa na masa murmushi har ya ɓacewa ganinta. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: https://chat.whatsapp.com/DK3nAxNaxVV6U3giyRUZQO?mode=r_c Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/DK3nAxNaxVV6U3giyRUZQO?mode=r_c *Albishir! Albishir!! Albishir!!!* Jama'a na ina maku albishir da cewa na kawo maku kayan kitchen masu kyau da inganci. Za ku darje ku zaɓi kayayyaki masu dangareren kyau. Duk a cikin farashi mai sauƙi da rahusa daidai da aljihunku. Ƴar uwata idan kina son ki damu kayayyakin da babu kamarsu masu bigewa da inganci to Hajiya ga dama ta samu .muna siyar da kaya kamar haka.👇 Flasks Cups Dinnerset Kitchenware Pot Jugs Food processor bedsheet lamps Second hand gas Duk wani kitchens items na kayan kitchen muna saidawa. Zu ku iya tuntubar mu ta wannan lambar waya 07018401887 *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page5️⃣0️⃣ Tashi ya yi yana yi masu sai da safe ya haura upstairs. Anisa na masa mumrmushi har ya ɓacewa ganinta. Yana shiga bedroom ɗin sa ya zube kan gadon. Abubuwa sun yi masa yawa a cikin kansa. Kullum da tunani yake kwana. Ba abinda ya fi tsaya masa a zuciya kamar idan ya tuna zancen da ya ji Doctor na yi a waya lokacin da suke masa allurai. "Ka ga ka kwantar da hankalinka ba kai kaɗai ke son ganin bayan Asadullah ba. A cikin gidan nan ma maƙiyansa ne zagaye da shi. Kuma sun yi mani tayin makudan kudade idan na kashe shi. So ka bi komai a hankali , yanzu haka allura da magungunan da nake bashi a hankali suke raunana jinsa da ganinsa, za su yi masa illar da zai rayuwar da gwamma mutuwarsa ma akan rayuwarsa, domin rayuwa ce mara amfani ka jira lokaci." Hawaye ne ya ci ya ciko Idanunsa, domin ya san alluran da magungunar da ake masa amfani da su ba don ƙarfin iko na Ubangiji ba da yanzu ba wannan zanen ake yi ba. "Su waye suka saka ka, lallai ina bukatar waɗan nan amsoshin daga bakinka Doctor." *America/New York City* Motoci guda uku ne suka shigo harabar gidan, kai tsaye wajen da aka tanada don parking motoci suka nufa. Mitacin na tsaya wa suka fara fitowa daga cikin motar yayin da James ya fito ya buɗe wa Hilal ɓangaren da yake. Fitowa ya yi tare da zubawa motar wata motar da suka ganin Idanu. Bayan ya ɗauke idanunsa daga kallon motar ya sauke su akan sojan da ya bari yana gadin gidan. Tsoro ne y bayyana a Idanunsa ganin irin kallon da Hilal ke jifansa da shi. Cikin rawar murya ya fara magana. "Sorry sir wallahi ba laifina ba ne, sai da na ce kar ta shiga oga ya hana amma ta wuce ba ta saurare ni ba." Shi kaɗai ya nufi ƙofar da zai shiga yayin da James ya bishi da jakarsa. Yana tura ƙofar ya sauke Idanunsa akan wayarta dake ajiye a saman ɗaya daga cikin kujerun falon. Alama ya yi wa James da ya ajiye ta fita. Take kuwa ya ajiye ya fice bayan ya ka masa kofar ya rufe. Bedroom ɗin sa ya nufa ya fara cire hularas. Riga kakinsa yake ƙoƙarin cire wa ta turo ƙofar ta shigo. Dakata wa ya yi daga cire rigar ya juya ya kalle ta da rikitattun idanunsa fuska ba fara'a. Yayin da ita kuma sai murmushi take sakar masa. "Barka da dawowa soja na." Cewarta cikin harshen Hausa. Daga jin Maganar ta za ka fahimci cewa cikakkiyar bahaushiya ce, sai sai dai zama a cikin turawa ya saka yanayinta da shigarta ba za ka taɓa cewa bahaushiya ba ce. Suraiya kenan ƴa ga ga wani minister Abdulƙadir Muhammad kenan. Ita kadai ce ƴa ɗaya da Allah ya bashi, ya ɗauki son duniya ya ɗaura mata. Mahaifiyarta ta rasu kuka ba ta jituwa da matar mahaifinta saboda gafara da take nuna wa matar uban. Akan dukiyar da mahaifinta ya tara mata. Tun da ta gama karatu ta komawa gida Nigeria ta tare a nan ƙasar Amurika. Tana sheƙe ayarta da turawa. Sai lokaci zuwa lokaci yake zuwa ta ga mahaifinta da kakanninta su ma sai ta gaji da mita kafin ta je. Sai dai mahaifinta na yawan kawo mata ziyara ƙasar. Fuska ba annuri Hial ya cire hannun Sumayya wacce suke kira da Sury. "Me ya kawo ki gidsn nan, sau na wa nake fadar cewa idan ban bukaci mace ba kada ta zo mani a nan." Madadin ta damu sai ma murmushi ta yi masa. "Ai ni ta daban ce shi ya sa." Ta bayansa ta rungume shi tana dariya ta yi maganar." "Sury don Allah ki barni abubuwa sun yi Mani yawa a kaina, ina bukatar hutu." "Why not ka huta a jikina na san za ka samu mutawa ka yi duk abinda kake so cikin kwanciyar hankali." Ta sani sarai baya taɓa yin sex da mace, amma lokuta da dama yakan rage zafi da ita. Ko shi din ma sai idan shi ya nemi hakan. Har ta fara tunanin cewa ko baya da lafiyar mazantaka ne, ganin zai yi wasa da mace har ya kai ƙololuwa amma da zaran ya yi kamar zai yi sex da mace sai ya fasa. Kasancewar magrib ta gabato ne ya saka ya yi saurin cire ta daga jikinsa. Tana shirin sake shige masa sai ta ja baya, sakamakon kallon da ta ga ya jefa mata. Cire kayansa ya yi ya saura daga shi sai boxer ya nufi bathroom. Ta bi shi da kallo tana tura baki. "Na rasa wani irin mutum ne wannan, sai ya yi ta ji da kansa don ya ga ana binsa." Ficewa ta yi daga cikin ɗakin ta koma ɗaya daga cikin bedroom dake falon. Nan ta ajiye jakar Kayanta. Sai mita yake take yi. Akan halin Hilal ɗin. Shi ba ma harka da shi ba, sai kun fara more juna ya kai ka ƙololuwa madadin ya biya maki bukata sai ya bar ki cikin halin matsuwa. Amma ina mai tabbatar maka in dai Ni ce sai ka yi abinda kake gudu. To wai ma Meye a ciki, wanda har ua iya wasa da mace ya sunmbace ta son ransa ya luguiguita ta son ransa amma ya ce yana gudun sex to me ya rage, ai idan za ka sha giya ka sha ta dubu." Ita ma wanka ta shiga yi don tana son wannan daren ya kasace na musamman ne a wajenta. Ko da ya fito daga wanka man shafawansa ya shafa, da turare. Sannan ya saka gajeren wando ya saka jallabiya. Sallar magrib ya yi sannan ya zauna akan sallaya yana lazimi. Sai da ya ga lokacin sallar Isha'i ya yi sannan sai gabatar. Falo ya nufa don ya samu shayi ya sha. Kitchen ya shiga, ba jimawa ya fito da mug ɗin shayi a hannunsa. Kasancewar ya san ba shi kadai ne a cikin gidan ba. Hakan ya saka ya koma bedroom ɗin sa don baya son damuwa. Zama ya yi kan sofa akwai Centre table dake gabansa system a gabansa yana bincike. A hankali yake shan shayin. Har ya shanye. _Asadullah_ Tare suka fito zuwa harabar gidan. Shi da Barrister Haris sai Doctor Isma'il da zai jagoranci tafiyar su Jidderh. A baya kuma Anisa ce tare da Jidderh. Har parking lot Asad y raka su. Barrister Haris ke driving gefen sa mun Doctor Isma'il. Sai Anisa da Jidderh dake bayan motar. Addu'a ya yi masu da fatan alkhairi kafin suka bar gidan yana ɗaga masu hannu. Suna barin gidan Asad y kira Sulaiman a waya bayan sun gaisa ne ya ce. "Ya ake ciki ne?" "Na bari ne sai na fara kawo maka maci amanar likitan nan kafin na bincike in da iyayen yarinyar suke." "Okay." "Yanzu haka na fito zan je gidan Doctor ɗin ne, idan ban same shi ba zan je asibitinsa ne." "Ina jira." Daga nan ya katse wayar ya shiga cikin gidan. _Doctor_ Fitowa ya yi daga cikin gidansa ya shiga motarsa zai tafi asibitinsa. Yana tsaka da tafiya akan tati sai wayarsa ta yi ruri, ganin mai kiran wayar ya sa ya samu gefen hanya ya tsaya. Shiru ya yi kafin ya ce. "Okay." Fitowa ya yi daga cikin motar ta sa ya tsaya gaban motar har lokacin waya na kunnensa. Ba zato ba tsammani wata babbar mota ta yo kansa gadan-gadan, kafin ya aknkare ta bi ta kansa. Daidai lokacin da motar Sulaiman ke ƙarasowa wajen. Babban motar kuwa barin wajen ta yi jama'a aka yo kan Doctor ana salati. Duk wanda ya kalle shi ya san cewa rai ya yi halinsa. Cikin sanyin jiki Sulaiman ya shiga motarsa ya bar Wajen. Wasu kuwa duk da sun san baya da dai bai hana su ɗaukarsa zuwa asibiti ba. Tuki Sulaiman yake yi amma gabadaya ba ya hankalinsa na ga abun da ya faru. "Marasa mutunci kawai." Har ya karasa gidan Asad yana cikin damuwa. Kallon fuskarsa kawai Asad ya yi ya gane cewa akwai matsala. "Laflya meke faruwa?" "Sun kashe shi." Ya faɗa yayin da yake kokarin zama a daya daga cikin kujerun falon, yayin da kuma Asad ya mike zumbur kamar wanda aka tsikara. "Innalillahi wa'inna'ilahi raji'un. Su waye suka kashe shi.?" Shiru ya yi masa ya rasa wace amsar zai ba shi. "Ina tambayarka ka yi Mani Shiru." "Ban san su waye ba, amma na san hakan za ta iya faruwa. Saboda sun san cewa ka kuɓuta kuma tun da su ba ka san su ba sun san dole za ka nemi sanin su waye, ta hanyar Doctor kawai za ka iya gane ko su waye. Saboda shi ne tsanin dai zai kai ka zuwa gare su. Shi ya saka suka sa mota ta taka shi yadda ba ka da wata hanyar da za ka iya gane su." Dafe kai Asad ya yi cikin damuwa ya ma rasa abun da zai ce. "Waye zai yi mani wannan aikin Sulaiman?" "Yallaɓai Allah shi ne masani. Amma gaskiya duk ma waye ya shirya wannan munaƙisar na cikin gida ne." "To na rasa akan wane dalili ne na kusa da ni zai yi mani haka, Meye ban masu ba. Na dauke masu nauyin komai cin su shan su suturarsu da laflyarsu duk a wuyana yake. Motoci kudade Ga gabadaya mansion ɗin nan ba abinda da ban ɗauke masu ba. Amma suke ƙoƙarin ganin bayana why?" Ya karasa maganar yana hawaye. Tausayinsa ne ya cika Sulaiman. "Ba abinda ka yi masu, jarabawa ne Allah ya baka ikon cinyawa." "Amin ya Allah." Ya furta cikin sanyin murya. _Zahrah_ Tana zaune babban falon gidan tana karatu saboda za su fara text. Kasancewar tana da son karatu ya sa ba ta wasa da ta samu zama za ta fara karatu. Kausar ita da Nabeela ce suka zo suka same ta. Harara suka watsa mata sannan Nabeela ta ce. "Ke lambar Yaa Ammar za ki ba mu." Karatun ta take yi ta cigaba da yi ba tare da ta ɗaga kai ta kalle su ba. Musamman da ta san cewa ko magana ba ya haɗa ta da su. Don haka ba ta kai hankali wajensu ba ballantana ta san cewa da ita suke yi." " Ke!, magana fa muke yi da ke amma kin mana banza waye sa'anki a nan?" Sai a lokacin da ɗaga kai ta kalle su, jin yadda suka daga mata tsawa wai kuma suna kiranta da ke, su sun fi karfin su kira sunanta. Ci gaba da karatu ta yi ba tare da ta bi ta kansu ba. Kausar ce ta ƙwace takardar a hannun Zahrah. Zahara ta mike tsaye tana cewa. "Wai me ya saka kuke neman tashin hankali ne a tare da ni?" "Dan wulakanci kuna jin ina maki magana kuka share ni?" "Na ji kuna cewa ke, ni kuma ba suna na ke ba." "Lallai yarinyar nan ba ta da mutunci." Cewar Nabeela tana kallon Kausar. Ita ma Kausar ɗin kallonta ta yi kafin ta sake magana cikin isa da gadara." "Lambar wayar Yaa Ammar za ki bani." "Ba na da shi ." Ta fada tana ci gaba da karatun da take yi. Da mamaki suke kallonta jin kalamanta. "Za ki bayar ko sai kin sh wahala kafin ki bayar?" Ba ta ce masu komai ba ta cigaba da karatun ta. Barin wajen suka yi, karatun da take yi ta cigaba da yi. "Ba jinawa sai ga su sun fi dawo kowacce ta kaskon turaren wuta an zuba gawayin kanti suna zuwa suka buɗe wata kwalba suka zuba turaren a cikin garwashin da yawa su duka biyu suna kora hayaƙin da hannu daidai saitin fuskarta. Jin haka ya saka ta ɗago da sauri zata mike ta bar wajen. Ganin haka Kausar mayar da ita ta karfi ta zauna. Kafin ka ce me har numfashinta ya fara barazanar ɗauke wa. Hakan bai saka sun dau7kata ba sai ma ƙara turaren wutan suke a cikin wuta. Wanda ƙamshin sa ma ba dad'i sai uban hayaƙi Take ta fita daga hayyacinta tana ko omarkn barin wajen ta kasa take da ke ta sume a wajen. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) https://chat.whatsapp.com/DK3nAxNaxVV6U3giyRUZQO?mode=r_c Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/DK3nAxNaxVV6U3giyRUZQO?mode=r_c *Albishir! Albishir!! Albishir!!!* Jama'a na ina maku albishir da cewa na kawo maku kayan kitchen masu kyau da inganci. Za ku darje ku zaɓi kayayyaki masu dangareren kyau. Duk a cikin farashi mai sauƙi da rahusa daidai da aljihunku. Ƴar uwata idan kina son ki damu kayayyakin da babu kamarsu masu bigewa da inganci to Hajiya ga dama ta samu .muna siyar da kaya kamar haka.👇 Flasks Cups Dinnerset Kitchenware Pot Jugs Food processor bedsheet lamps Second hand gas Duk wani kitchens items na kayan kitchen muna saidawa. Zu ku iya tuntubar mu ta wannan lambar waya 07018401887 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page5️⃣1️⃣ Take ta fita daga hayyacinta tana kokarin barin wajen ta kasa, take ta sume. Barin wajen suka yi ba tare da tausaya wa ba suka bar ta a wajen. *America/New York City* Har dare ya fara tsalawa bai kwanta ba, yana nan yana wani binciken a cikin computer. Sury ce ta shigo ɗakin sanye da rigar barci wanda babu maraba da tana tsirara. Yana jin ta bai tanka mata ba ya cigaba da aikinsa. Har mamakin karfin halin yarinyar yake yi. Ta zo ta tare masa gida ba tare da izinisa ba, sannan tana ƙoƙarin ta saka shi abun da bai yi niyya ba, kuma bai bukata ba. Ya ƙudura a zuciyarsa yau zai nuna mata iyakarta. Shi ba'a masa haka, idan bai bakaci mace ba ba ta zuwa in da yake. Tana rangad'a da yanga ta karaso wajen da yake zaune. Zama ta yi a gefensa tana manna jikinta da na shi. "Har yanzu ba ka yi barci?" Bai tanka mata ba daidai lokacin da ya kammala abun da yake yi ya rufe computer. "Jarumina, na yi kewarka wallahi ina son ka don Allah ka yarda mu yi aure mana." "Ni kuka ba na son ki ko kaɗan." Rintse Idanunta ta yi cike da jin ba dadin jin kalamansa masu tarwatsa zuciya ta ce. "Me ya saka?" Ta yi maganar tana shafa gefen fuskarsa tare da matso da fudkarta dab da ta shi za ta sumbace shi ya daka mata tsawa. Wan da sai da ta firgita da jin tsawar sannan ya nuna mata hanyar fita. Da mamaki take jallonsa me yake nufi da ita ne yau. Ko dai ta fara gundurarsa ne. Tana tsaka da tunani sai ta ji ya finciki hannunta. "Meke faruwa ina za ka kai ni?" Bai saurare ta ba ya cilla ta zuwa falo, sannan ya ɗaga mata hannu yana nuna ta da yatsa alamar gargaɗi ya ce. "Kar na sake ganinki a inda nake sai dai idan ni ne na neme ki, kuma ki tabbatar kafin karfe takwas na safiya kin bar gidan nan." Daga nan ya tura kofarsa ya shiga ya bar ta nan durƙushe tana kuka. Sai da ta yi kuka mai isar ta sannan ta tashi ta shiga bedroom ɗin da kayanta suke. Tana shiga ta fada a kan gadon ta kufa ciki tana hawaye. Sai dai duk wulakancin da ya mata ba ta jin za ta fita daga harkarsa. A haka barci ya ɗauke ta ba tare da ta sani ba. Ba ita ta farka ba, sai karfe bakwai na safiya, tunawa da gargaɗin da ya yi mata ya sa ba ta tsaya wani ɓata lokaci ba ya tattara na ta ya nata ta bar gidan, don yadda ta ga fuskar nan ta sa ba sassauci a tattare da shi. Shi kam dama tun asuba ya tashi ya yi wanka ya gabatar da sallar asuba. Sannan ya zauna yana azkar ɗin safiya. Sai ƙarfe goma ya shirya suka bar gidan in da ya tarar da sojojin na jiransa a wajen motocinsu. _Uncle Adam_ Zaune yake cikin iyalansa suna fira duk da cewar rabin hankalinsa na wajen fitar ne rabi kuma na wajen tunanin Asadullah. Mami ce ya kalle shi ta ce. "Alhaji lafiya kuwa?" Murmushin ƙarfin hali ya ƙaƙalo, sannan ya ce. "Lafiya lau Mamin yara" "A'a ba lafiya ba kullum na zuba maka idsnu sai na ga kana ta aikin tunani idan na tambaye ka sai ka ce ba komai." Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kalli yaransa Nasir, Maryam da Abida ganin shi suke kallo. Ya da ya sake wani murmushi don ganin ya kawar da damuwarsa. "Ba wani abu illa tunanin rayuwar nan kawai nake yi." "Bs tun yau ba kake yawan wannan tunanin idan ban manta ba tun bayan da aka nemi Asadullah aka rasa ne." "Haka ne. Dole na shiga damuwa sosai ba kaɗan ba, domin Asadullah Ɗa ne a wajena, tun da Ɗan wa na ne, yadda ya dauki mahaifinsa haka ni ma ya ɗauke ni a matsayina na ƙanin mahaifinsa. Ba abun da bai ɗauke Mani na ci da sha da sutura da karatun ƙannensa tun da ya kammala karatunsa ya dawo ƙasar nan aka mallaka masa dukiyarsa nake cin arzikinsa uwa uba kuma fawowar mu cikin mansion ɗin nan, ga karatun yaran nan duk a wuyansa ne. Ko ina ya shiga oho." Abida ce ta saka kuka tana cewa. "Wallahi ina nan ina jiransa har sai ya dawo ban ga namijin da zan iya rayuwa da shi bayan Yaa Asad ba " Harara Maryam ta watsa mata tare da da cewa. "To shikenan ba sai ki tsaya jiransa ba. In Allah ya yarda ba zai..." Nasir ne ya saka masu tsawa wanda ya saka su yin shiru. Shiru falon ya yi ba wanda ya sake magana. Kafin Nasir ya kalli Uncle Adam ya ce. "Dady yanzu ya za'ayi ne rabin sanin halin da yake ciki ya dame ni. Kullum idan na ke kamfanin nan ba na jin dad'i sakamakon rashin sanin halin da yake ciki. Ga ma'aikatansa ma sun damu sosai na rashin sanin halin da yake ciki, kasancewar ni ne kaɗai Ɗan uwansa a kamfanin da suka sani ya sa kullum sai wasu sun shigo office ɗin na don jin halin da yake ciki" "Kada ka damu komai da yardar Allah." Cewar uncle Adam yana mikewa tsaye, kafin ya cigaba da cewa. "Bari na je ɓangaren Yaya na same shi ko an ji wani bayani daga in da yake ." Jinjina kai Naseer ya yi kafin ya ce. "Shikenan Dad Allah ya taimaka ya mana jagora." Da Amin suka amsa kafin ya fice ya bar su. Nasir ya mike don shirin zuwa kamfanin ASADULLAH GLOBAL RESOURCES. Nasir shi ne Head of marketing department, na kamfanin Asadullah global resources. _Zahrah_ Tana kwance sume bayan su Nabeela sun tafi sun bar ta da kimanin mintuna goma sai ga Yaa Mahmud ya dawo gidan. Ganin halin da ƙanwarsa take ciki ne ya saka ya karasa wajen da take kwance da hanzari. Ganin ta suma ne ya saka ba tare da ɓata lokaci ba ya ɗauke ta ya nufi part ɗin su da sauri tana kiran sunan Umminsu. "Ummi! Ummu!! A tare Ummi da Abbi suka fito daga cikin ɗakin, ganin halin da Zaharah ke ciki ne ya saka hankulansu ya tashi sosai da sosai. "Me ya same ta?" Abbi da Ummi suka tambaya a tare cike da tashin hankali. Cikin tsantsan damuwa Mahmud ya ce. "Wallahi ban sani ba, na dawo kenan na ganta a sume, sai dai da dukkan alamu karatu take yi ciwon na ta ya tashi. Don na ga takardu a gabanta. Inhelar Ummi ta dauko daga ɗakinta aka shaƙa mata, amma bai yi mata amfani ba don ko motsi ta kasa. Sai Abbi ya umarci Mahmud da ya kwantar da ita a kan doguwar kujerar haka kuwa aka yi sai ya kwantar da ita yayin da Abbi ya yayyafa mata ruwan don ba ta farfaɗo daga sumar da ta yi ba. Ga shi ba ta cikin hayyacinta ballantana a ba ta magani ta sha. "Mu tafi asibiti kawai." Yayin da Mahmud ya yi maganar yana nufar kofar fita. Kasancewar dama Hijabi ne a jikin Ummi ya saka ta bi bayansu da sauri. Abbi ma ya fito su uku ne Yaa Mahmud na ɗauke da Zahrah. Ba kowa a babban falon gidan. Sai dab da za su fita suka ji dariya, a tare suka juyo suka ga Nabeela ce da Kausar. Ba su bi ta kansu ba suka fice har zuwa parking space. Direba ya nufo su da sauri yana cewa. "Alhaji asibiti za mu tafi." "Bar shi kawai Sa'idu zan kai ta da kaina." Ya faɗa yayin da ya nufi motarsa, cikin sauri Sa'idu ya bude masa bayan motar. Ya saka ta. Ummi ce ta shiga baya gefen Zahrah ta zauna tare da ɗora kan Zahrah akan cinyarta. Yayin da Mahmud ya zauna mazaunin direba Abbi na gefensa suka fice daga gidan bayan ya figi motar da ƙarfi. Ma'ikatan da suka ga lokacin da aka shigar da ita motar ko motsin kirki ba ta yi. Lokacin da aka kai ta asibitin emergency room aka kai ta saboda ganin halin da take ciki. _Asadullah_ Wayarsa ce ke ruri ya duba ya ga Doctor Isma'il ne ke kiransa daga India. Cikin rawar jiki ya ɗaya kiran wayar ya yana addu'a Allah ya sa Jidderh ta samu lafiya. "Doctor ina fatan wannan karon an samu nasara." Ajiyar zuciya Doctor Isma'il ya sauke sannan ya kasa magana. Cikin kaguwa da son jin halin da Jidderh ke ciki ya ce. "Ina fatan an samu nasara a wannan karon." Ta cikin wayar ya ji Muryar Dr Isma'il ya na cewa. "Duka sakamakon ɗaya ne, ina nufin ba wani abu da ake gani. Bincike da gwaje-gwaje da aka yi an tabbatar ƙwaƙwalwarta lafiya lau take kamar yadda sauran asibitoci suka tabbatar." "Innalillahi wa'inna'ilahi raji'un." Shi ne kalmar da ya fito daga bakin Asadullah. Cikin sanyin jiki ya zauna akan kujera yana dafe kansa. *Ku yi hakuri ba na jin daɗin jikina ba zan iya dogon typing ba* *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) https://chat.whatsapp.com/DK3nAxNaxVV6U3giyRUZQO?mode=r_c Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/DK3nAxNaxVV6U3giyRUZQO?mode=r_c *Albishir! Albishir!! Albishir!!!* Jama'a na ina maku albishir da cewa na kawo maku kayan kitchen masu kyau da inganci. Za ku darje ku zaɓi kayayyaki masu dangareren kyau. Duk a cikin farashi mai sauƙi da rahusa daidai da aljihunku. Ƴar uwata idan kina son ki damu kayayyakin da babu kamarsu masu bigewa da inganci to Hajiya ga dama ta samu .muna siyar da kaya kamar haka.👇 Flasks Cups Dinnerset Kitchenware Pot Jugs Food processor bedsheet lamps Second hand gas Duk wani kitchens items na kayan kitchen muna saidawa. Zu ku iya tuntubar mu ta wannan lambar waya 07018401887 Page5️⃣2️⃣ Shi ne kalmar da ya fito daga bakin Asadullah, cikin sanyi jiki ya zauna akan kujera yana dafe kansa. "Ya Salam." Ya faɗa a zuciyarsa. Yana tausaya wa yarinyar nan da kuma halin da iyayenta za su shiga. Jin shiru ne ya saka Doctor Isma'il sake magana. "Yallaɓai kana tare da ni kuwa?" "Ina tare da kai Isma'il hakika hankalina ya tashi sosai ba kaɗan ba." "Ka da ka damu in sha Allah za ta samu lafiya a ci gaba da yi mata addu'a." Jinjina kai ya yi tare da cewa. "Yanzu ba wata ƙasar da kake ganin za su iya wannan aiki?" A gaskiya tun a ƙasar mu Nigeria ya kamata ka amince da aka ce maka ba wata matsala a tare da ita, ƙwaƙwalwar yarinyar nan lafiya lau take ." "Ba lafiya take ba!" Ya faɗa a tsawace. Jin furucin Asad ya sa Doctor Isma'il ya san cewa ransa a ɓace yake. "Calm down yallaɓai. Yanzu ya kake so ayi?" " Gwada kai ta wat ƙasar , ina ganin a kai ta ƙasar larabawa. Su na su gwada yin na su kokarin ko kuma a kai ta Germany." Shiru Dr Isma'il ya yi don yana da yakinin duk in da za su ce ƙashe kudi kawai za'ayi, amma duk sakamakon iri daya zai kasance. "Ya na ji ka yi shiru?" "Ba shiru na yi ba, ina tunanin in da ya dace a kai ta." "To ina kake ganin ya dace a kai ta?" Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Akwai abokina mai suna Kamal Jamil Balaraben kasar Egypt ne, tare da shi muka yi karatu a ƙasar Madina. Mahaifinsa cikakken likitan ƙwaƙwalwa ne, yanzu haka yana da Asibiti a Abu Dhabi Ina ha a kai ta can ƙasar ko Allah zai sa a dace." Har cikin zuciyarsa ya ji daɗin shawarar da Doctor Isma'il ya bayar, godiya ya yi masa sannan ya ce anijma zai kira shi sai su tsara yadda tafiyar zai kasance." Sallama suka yi sannan ya kashe kiran wayar. _Zahrah_ Kwance take a gadon asibiti an saka mata ruwa. Barci take yi yayin da Umminta ke zaune saman gadon wajen saitin ƙafarta. Abbi na zaune a kan kujerar yayin da Yaa Mahmud ke tsaye ya jingina da bangon ɗakin. Dukkansu zuba mata idanu suka yi suna kallonta. Dada da Papa ne suka fito ƙofar dakin suka shigo da sallama a bakinsu. Sai direban da ya kawo su wanda shi ne yake sanar wa Papa halin da suka ga Zahrah a ciki an kai ta asibiti. Babu ɓata lokaci kuwa sai suka ce ya kawo su tun da sun san asibitin da suke zuwa dole nan za su kai ta. Bayan sun amsa sallamar su Papa ne suka shigo . "Abbi ya ba Papa kujerar da yake zaune ya zauna, yayin da Dada ta zuba saman wani kujerar dake kusa da na Papa. "Ya aka yi ciwon na ta ya tashi na ga yanzu ba lokacin yawan tashinsa ba ne?" Mahmud ne ya ce. "Wallahi Papa ban san dalilin rashin ciwon na ta ba, sai dai kawai na dawo na ganta kwance a ba ya motsi, kuma da dukkan alamu karatu take yi, don na ga takardar da take karantawa a gefenta." Shiru Ummi ta yi kafin ta ce. "Na yi mamakin halin da ka ce ma Ni ka same ta, saboda yanzu ba lokacin sanyi ba ne, ciwon na ta ya fi tashi a lokacin sanyi. Kuma yanzu ciwon na ta bai cika tsananta haka idan tana gida, don idan tana gida ta zaran ta ji alamar ciwonta zai tashi take take neman magani, shi ya sa kwanan nan baya mata tsanani, saboda tana kiyaye wa sosai." Shiru suka suka yi kowa da tunanin da yake yi a ransa. Yaa Sadik ne ya shigo kamar an jefo shi daga sama. Ƙarasawa ya yi wajan gadon yana kallonta. "Ammi harin ya hakan ta faru?" "Wallahi ban Sani ba Sadik, Yayanka ne y kawo ta rungume a hannunsa wai ya ganta a gidan ta sunfi." "Anya ba wani abu aka yi mata kuwa? Ta yaya har za ta kai ga suma bayan..." Abbi ne ya ya dakatar da shi ta hanyar cewa "Ya isa haka Sadik, ba na son jin wata magana kuma. Na san halinka kada ka janyo mani wani tashin hankali ka bar mu mu ji da halin da take ciki." Shiru kawai ya yi ba don ransa ya so ba, sai dai zancen sa ya sanya Mahmud cikin tunani, saboda lokacin da Mahmud ya ɗauki zabarah zai kai ta asibiti ya ji sautin dariya kafin ya fita daga falon gidan, bayan ya juya dai ya ga Kausar da Nabeela suna dariya. Da a lokacin Sadik na wajen ko kuma shi ya dauko Zaharah to ba makawa sai ya ajiye Zaharah ya ci ubansu ko sama da ƙasa za ta haɗe, don shi ba tsoron tashin hankali yake yi ba. Shiru Mahmud ya yi don idan ya faɗa Sadik ya ji ya san zai iya komawa gidan kuma ya tuhume su don ko shi bai da tabbas Kuma Abbi ba zai ji dadin hakan ba ko kusa. Don haka ya yi shiru don samun zaman lafiya a cikin wannan zuri'ar. Wayar Papa ce ya yi ruri ya fita waje ɗin dubawa. Har zuwa lokacin Sa'idu direba na jiran su Papa da ya kawo. Bawan ya matsa ya ba Papa hanya ya fita ne shi ma ya samu wata kujera ya zauna. Daga cikin ɗakin kuwa wayar Zaharah ke ruri, don kuwa lokacin da Mahmud ya ɗauko ta ya ga wayarta a wajen ya ɗauka. Har sau uku ana kira kafin Sadik ya ce . "Wai waye ke samun mutane ne yanzu haka, ga mai wayar na kwance a karfe wayar gabaɗaya mana." "Ammar ne ke kiranta." Daga Dada har Ummi suka kalli wayar. Kafin Sadik ya ce . "A fada masa halin da take ciki ba ta laflya mana." Dada ta mika masa hannu alamar ya bata wayar. Mika mata wayar ya yi bayan ya yi picking zalla ɗin. Cikin wayar ta ji ya ce. "Masoyiya ta laflya kuwa ina ta kira shiru?" "Ba ita ba ce Ammar, tana kwance a gadon asibiti ne yanzu haka tun a gida aka ɗauki ta a sumammiya.' Cikin tashin hankali Ammar ya ce. "Subhanallah Dada me ya same ta ne?" "Ciwonta ne ya tashi." "Subhanallah lallai zan zo Nigeria gobe in sha Allah." Cikin mamaki Dada ta ce. "Wani irin za ka zo gobe kuma, ka kwantar da hankalinka Ammar, ciwonta ne ya tashi ba wani bakon al'amari ba ne ya same ta, in sha Allah za'a sallame ta yau ko gobe." "Allah ya sa haka Dada, kuma Allah ya bata lafiya, amma hankali na ya dawo Nigeria ba zan iya haƙura ban zo na hanta ba." Duk yadda Dada ta so ta hana Ammar zuwa ki ya yi , don haka ma ta bar shi dole ganin ya kafe akan abu guda. Addu'ar Allah ya kawo shi lafiya ta yi masa. Kafin suka yi sallama ta ajiye wayar daman Drawar na yi gadon mara lafiya. Kallon Abb da Ummi ta yi kafin ta ce. "Ammar ne wai zai zo gobe ya sun jikin Zajrah." " Ummi ta ce "Da dai ya yi zamansa Dada mutum ya taso tun daga London ya zo duba ta akan Meye, mun yafe ya yi zamansa kawai." "Ni ma haka na ce masa amma ya daga kan cewa sai ya zo duba ta, wai masoyiyarsa ba lafiya." Da mamaki Abbi ke kallon Dada yana cewa. "Soyayya suke yi ne?" Murmushi Dada ta yi irin ta su ta manya, kafin ta ce. "Idan Allah ya ba ta lafiya sai ku ji daga bakinta." Don shi Abbi bai san da zancen ba, ya dai san Ammar ya taba zuwa gaishe su kar part ɗin su, wanda hakan ya ba su mamaki ganin abokin Hilal ne kuma shi Hilal bai taba zuwa gaishe su ba ballantana abokinsa ya zo, ashe soyayya suke da Zahrah. Cikin sanyin murya Ummi ta ce. "Ba na son alakar soyayyar Zajrah da yaron nan, saboda kun san irin zaman da muke yi da su a cikin gidan nan, tsabar aminta dake tsakanin Hilal da Ammar har ya sa iyayensu mata suka zama ƙawaye suna zumunci da juna. Wanda har ya kai ko ƙasar suka je a gidan su Ammar suke sauka. Ko kun mance rashin lafiya da Papa ya yi a ƙasar yana jinya. Lokacin da muka shirya gabaɗaya zuwa gidan su Ammar suka sauka a ƙasar London ɗin, amma ni da Abbi ya samar Mana hotel a ƙasar. Na tabbatar ba za su bari ɗan su ya auri Zahrah ba saboda sai mahaifiyar Hilal da Laila sun ɓata lamarin. Hakan ya saka na ba wa Zahrah shawara akan cewa ta fita harkar yaron kada sai ta yi zuri a cikin son sa sannan su yi mata yankan ƙauna ta zo ta shiga cikin wani hali." "Kar ki damu in dai suna son juna zan yi wa Papa magana akan lamarin bayan mun ji ta bakin Zahrah, na san zai saka hukunci mai tsanani akan lamarin akan ita Laila da Maimuna, wato Mummy. Shiru ta yi amna dai hankalin ta bai kwanta da al'amarin ba. Daidai lokacin aka shigo ɗakin da sallama. Papa ne tare da abokinsa Alhaji Modibbo, mahaifin UmmI. (Idan masu karatu ba ku manta ba dama na fada maku a baya cewa da Mahaifin Abbi da mahaifin Ummi abokan juna ne, lokacin da Abbi ya gana karatunsa ya dawo Nigeria Papa ya tura shi ya je ya ga Ummi idan ta yi masa su daidaita. Daga nan suka daidaita aka masu aure) Alhaji Modibbo ya kalli gadon da jikar ta sa take kwance idanu a lumshe. Sai yake kallonta kamar Ummi lokacin da take da shekarunta. "Barka da zuwa." Kamilalliyar fuskarsa ya ɗauke daga kallon jikar ta sa ya maida ita zuwa ga kallon ƴar ta sa wacce kullum yake jin tausayinta a zuciyarsa fiye da sauran ƴaƴansa, saboda yanayin zaman da take yi da sauran jama'ar gidan. "Lafiya lau ya jikin Amaryar ta wa." Murmushi ta saki tana cewa " jiki da sauki." Daga nan su Sadik da Mahmud ma suka gaishe da kakan na su. Sadik ya ce . "Modibbo ina tsohuwar matar taka ce ka zo kai kaɗai" "Ina hanya ne kakanku ke sanar da ni, abin da ke faruwa sai na zo nan kawai." Amma ina hanya na sanar da su na san suna nan zuwa ita da ƙanwar mahaifiyar ku Bilkisu sai ƴar da ƴarta Amal. Nan suka gaisa da kowa ya zauna akan kujerar da aka ba shi ya zauna. Bayan mintuna goma sai ga Didi mahaifiyar Ummin Zajrah tare de ƙanwar Ummin sai ƴar ƙanwar Ummin buduwarwa wacce ba za ta wuce sa'ar Zahrah ba. Kuma suna ɗiban kamanni da Zahrah sai dai ba ta kai kyawun Zahrah ba. Su biyu ne Allah ya mallaka wa Modibbo Daga A'isha wato Ummin Zahrah sai Bilkisu mahaifiyar Amal. Akwai kuma Yayan Amal mai suna Doctor Khalil, wanda yake shi likita ne bai daɗe da dawowa ƙasar ba. Suna nan zaune Zahrah ta fara motsawa tana a hankali. Numfashi da ƙarfi ta bude idanunta wanda ta ji sun mata nauyi. Amal da mahaifiyarta Amal ɗin Hajiya Bilkisu suka karasa wajen gadon yayin da Hajiya Bilkisu ta ke cewa. "Daughter sannu ko." Gyaɗa mata kai kawai ta yi yayin da Amal ta rike hannayenta tana sakar mata murmushi, ita ma murmushin ƙarfin hali ta sakar mata. Kowa a dakin hamdala ga Allah suka yi, ganin ta dawo normal cikin farin ciki suka karasa wajan ta suna tambayar ta jikinta . Doctor ne ya shigo duka bashi wuri ya duba ta, tambayoyi ya yi mata ta ba shi amsa. Magani ya bata tare de bata shawarin yadda za ta kiyaye tashin ciwon ta. Sallama aka rubuta masu, don ba ta jin komai numfashinta ma t daidaita. Kiran wayar Dr Khalil ne ya shigo cikin wayar mahaifiyarsu wato Hajiya Bilkisu. Wayar na ajiye a saman gadon yayin da Hajiya Bilkisu da ke sa wa Zahrah hijabinta. Zahrah ta kalli wayar ta ga sunan da ya bayyana LOVELY SON. Zahrah ta ce " Aunty wayarki." "Okay yayanki ne maybe ya karaso asibitin." Ɗaukar wayar ta yi bayan ta yi sallama. "Eh nan ne ka shigo." Ba jimawa ya turo ƙodar ya shigo, sanye yake da Suit black sai farin glass dake Idanunsa. Ƙamshin turaren da Zahrah ta ji ne ya saka ta kalli kofar ita shi ma Idanunsa akan ta suna kallon juna. "Innalillahi wa'inna'ilahi raji'un" Kalmar da ya firgita su kenan ya saka suka juya suna kallonsa. *Maman Ihsan ce*✍️ [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ https://chat.whatsapp.com/DK3nAxNaxVV6U3giyRUZQO?mode=r_c Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/DK3nAxNaxVV6U3giyRUZQO?mode=r_c *Albishir! Albishir!! Albishir!!!* Jama'a na ina maku albishir da cewa na kawo maku kayan kitchen masu kyau da inganci. Za ku darje ku zaɓi kayayyaki masu dangareren kyau. Duk a cikin farashi mai sauƙi da rahusa daidai da aljihunku. Ƴar uwata idan kina son ki damu kayayyakin da babu kamarsu masu bigewa da inganci to Hajiya ga dama ta samu .muna siyar da kaya kamar haka.👇 Flasks Cups Dinnerset Kitchenware Pot Jugs Food processor bedsheet lamps Second hand gas Duk wani kitchens items na kayan kitchen muna saidawa. Zu ku iya tuntubar mu ta wannan lambar waya 07018401887 Page5️⃣3️⃣ Kalmar da ya firgita su kenan ya saka suka juya suna kallonsa. "Haka yarinyar nan ta girma ban sani ba, ina wace ƙasar ne hakan ta faru?" Modibbo ya zo kawo masa duka da sanda ya kauce yana cewa "Subhanallah za'ayi kisan kai." Kowa dake dakin sai da ya yi dariya. "Yanzu dama saboda girma da ka ga Zahrah ta yi maka ne ya saka ka tayar mana da hankali kamar wanda ya ga wani abu mara kyau ko aka fadawa sakon mutuwa?" Murmushi ya yi tare da ya. "Kawai n ji ne don hankalin kowa ya dawo kaina ku ga abun da nake kallo." Gaida su Papa da Dada ya har da ƴar tsokanarsu ko da bai saba da su ba yana jin labarinsu wajen kakanninsu su Modibbo da suka kasance abokan juna. Daga nan y gaida Abbi da Ummi, sannan ya gaisa da Yaa Mahmud da Yaa Sadik bayan sun yi musabaha. Yaa Mahmud ne ya girme Dr Khalil amma Dr Khalil ya girmi Sadik da shekara ɗaya. Zahrah ta gaishe shi cikin sanyin muryarta ta ce. "Ya Khalil ina wuni?" Don ta gane shi a hoto saboda Amal na yawan posting ɗin photonsa duk da baya ƙasar. Madadin ya amsa sai ya fara tsokanarta. "Wai mara lafiyar ce anan, ai ba wanda zai kalli wannan ya ce ba ta da lafiya ai ma ta fi ku lafiyar gaskiya." Dariya suka yi suka fito daga cikin ɗakin, kai tsaye suka nufi wajen ajiye motoci. dama Modibbo shi kaɗai ya zo da direbansa. Didi suka zo da motar Hajiya Bilkisu, yanzu sai Didi ta bi mijinta don Hajiya Bilkisu ta ce za ta bi su Zahrah gida. Don haka ita da Amala ne suka shiga motar sai Zahrah da Ummi suka shigo motar Hajiya Bilkisu. Ummi na gefen ƴar uwarta yayin da Amal da Zahra ke bayan motar. Dada da Papa ma tuni sun shiga Direbansu ya ja su Mahmud, Sadik, Khalil kowa ya shiga motarsa shi kadai suka bar Wajen. Khalil ma bin bayansu ya yi don zuwa gidan yar mahaifiyarsa. Motocin guda biyar suka jeru a bakin gate suna danna horn, security ya leƙo jin horn daban-daban. Ganin su jere ya saka ya wangale masu gate ɗin suka shiga. A parking space suka yi parking dukkansu. Aunty Laila da sauran mutanen gidan da suke falo ne suka tashi kowa ta nufi part ɗin ta. Don sun san idan suka zauna wajen Papa ya zo ya dame su sai ya wanke su tas. Bayan kowa ya fito daga cikin motar ne Dada da Papa suka yi gaba daga nan sauran suka take masu baya. Part ɗin su suka nufa su dukansu yayin da su na su Hajiya Bilkisu suka bi bayan su. A falon Ummin suka zauna su duka, dai dai Abbi da ya nufi bedroom ɗin sa. Ummi ta shiga kitchen ta jido masu meet pie cake pizza duk ta jido a manyan farantai. Sai lemuka da ruwa mai sanyi. Nan suka hau ci suna fira, sai dai duk ɗaya idanun da za ta daga kai sai ta kama Kamal yana kallonta . Kuma sai ya sakar mata sanyayyar murmushinsa wanda ta zame masa ɗabi'a. Hakan ya saka ta kasa sakin jiki ta nufi bedroom ɗin ta, Amal ma ta bi bayanta bayan ta dauki meet pie da lemu a hannu ta bi bayanta. *AMERICA/ NEW YORK CITY* Motocin sojojin ne suka dumfaro gidan na Hilal. Motarsa ce a tsakiyarsu. Can ya hango Sury na zaune ta haɗa tagaumi da alama tana jin tsoron ta shiga irin n ranar ya sake wulakanta ya kote t kamar yadda ya mata last time. Murmushn gefen baki ya sake daidai lokacin da suka hada idanu. Alama ya mata da ta shigo. Bayan motocin sun taya ne aka bude mata shi ma ya fito. Daidai lokacin da ita ma take shigowa . Da hannu ya mata alamar da ta zo gare shi . Da sauri take tafiya don shi din digo ne kuma komai cikin zafin Nana yake yinsa. James na ajiye masa wasu file a falo ya fito yayin da Hilal ke jiran ƙarasowarta. Tana ƙarasowa ta fada jikinsa tana kuka.jan ta ya yi zuwa falon. Yana zaune a kujera da dukkan alamu a gajiye yake sosai, yayin da Sury ke sake shige masa jin take yi. "Ina wuni?'" Ta fada tana kallon zara-zaran yatsun hannunsa ya take masa wasa da su. "Kina lafiya ?" Ya faɗa idanunsa a lumshe, don kwana biyun nan a gajiye yake dawowa sakama aiki da ya masu yawa. Yanzu haka daga wani daji suke. "Na hada maka ruwan wanka ne?" Kai kawai gyafa mata alamar eh Da rawar jiki ta tashi ta je ta haɗa masa ruwan wanka nai dan ɗumi. Tashi ya yi ya nufi bathroom ɗin sa. Zama ya yi a bakin gado tana tsaye ta ce. "Ko na taya ka rage kayan jininka ne?' "Ki bar shi na gode.' Ba haka ta so ba sai dai ba yadda za ta yi." "Ki koma falo idan na fito zan zo na same ki ." Tura baki ta yi don ita ba ya ga ranar da burin ta zai cika akan Hilal ba, amma da sannu akuya take shiga gidan kura har ta ci ta da yaƙi. Fita ta yi daga cikin ɗakin ta bashi wuri kamar yadda ya ce. Kayan jikinta ya rage sannan ya shiga wanka. Ya kwashe kusan mintuna talatin yana yin wanka kafin ya fito sanye da bathrobe a jikinsa. Sury kam tana falo tana jiran fitowarsa. Loka-lokaci take sakin murmushi ita kaɗai. Har ya fito sanye da ƙananan kaya a jikinsa. Ƙaramar riga da kuma wando Three quarter. Kitchen ya shiga ya fito dauke da wani biscuit da lemu. Zama ya yi kusa da ita ya fara ci. Ita ma ta saka hannu kasancewar biscuit ɗin babba ne a cikin gwangwani a tare suka ci biscuit ɗin suka sha lemun. Da misalin karfe goma na dare ya goma na dare ya gama shirin kwanciya don yau baya jin zai iya wani aiki kafin ya kwanta . Sury ce ta shigo ɗakin da sallama ya amsa mata, wani irin turare t shafa a jikinta wanda tun ya ji kamshin sa dai da ta haifar masa da kasala. Lumshe udanu ya yi tare da sakin ajiyar zuciya sakamakon kamshin ya masa daɗi, dama shi mutum ne mai son jin ƙamshi shi ya sa kullum yana cikin ƙamshi. Zama ta yi bakin gadon tana sakar masa murmushi, yana kishingide yana kallonta . Da hannu ya mata alama, gane me yake nufi ya saka ta haurawa saman gadon ta faɗa jikinsa. Wani remote ya danna hasken ɗalin ya ɗauke, cikin farin ciki ta ƙanƙame Hilal tana addu'a Allah ya sa kada ya yi mata abun da ya saba yi wa sauran mata da ta ji suna faɗa. Sai ya kai su ƙololuwar bukatar kasancewa da shi sai ya tashi ya bar su ba tare da ya biya masu bukata ba. Hakan ya saka ta sa aka kawo mata wannan turaren akan cewa ina dai har ya shaki kamshin turaren dole sai ya yi sex da ita duk taurin kansa kuwa. Sai ta tsinci kanta cikin farin ciki don ta ji yadda turaren ya ji rasiri akan sa har yana sakin ajiyar zuciya. Dama babu riga a jikinsa wando ne Three quarter ya sake sa wani. Janyo ta ya yi cikin bargon Yamutse fuska ya tare da yi mata alama da ta cire rigar jikinta. Cikin azama ta cire rigar dama ba ta saka bra ba, pant ɗin ma ta cire shi. Bakinsu ya haɗe waje guda suna sumbatar juna. Kamar dai kullum yau ma haka ne, sai da ya gama sarrafa ta son ransa ya taba duk in da yake so ya shafa duk in da yake so amma bai yi gigin yin sex da ita ba kuma bai da niyya. Ganin take-takensa kuma an fada mata in dai ya shaƙi kamshin turaren nan duk abinda take so shi zai mata ne ya saka ta kai hannu zuwa wandonsa da niyyar cire wa. Tsawar da ya daka mata ne ya saka ta firgita tare da ƙanƙame shi. Kamar za ta yi kuka ta fara magana. Babu wani wajen da ba ka sani a jikina ko ka taɓa ba, to akan me kai ba za'a ga jikinka ko a taba kamar yadda kake yi wa matayen da kake mu'amala da su?" Haka tsarina yake kuma kowace macen da ta sanni a haka ta san ɗabi'ata, babu macen da zan iya sex da ita sai dai idan na tabbatar da cewa akwai igiyar aurenta a kaina, lalacewar ta wa bai kai da zan iya shiga gonar da ba ta wa ba na yi ban ruwa, amma matukar gona ta ce zan shiga na yi ban ruwa har na samar da yabanya mai kyau. Ba ke kaɗai ba ce kuna da yawa kuma kin san wasu da nake harka da su za ki iya tambaya ko akwai wacce na taɓa yin amfani da ita. " "To ai idan za ka sha giya ka sha ta dubu, tun fa ka iya romancing ɗin mace ka iya kissing Higgins da mace shi halal ka aikata da kake tsoron zina su Meye kake yi?" "Ke tashi ki fita kafin na sauya maki kamanni!" Ya faɗa a zafafe ba shiri ta mayar da kayan jikinta ta fice daga ɗakin. Sai ƙarfe tara na dare sannan Hajiya Bilkisu da yaranta suka shirya don komawa gida. Don tare suka yi girki da Ummi Khalil kuwa tare da Sadik da Mahmud suka tafi masallaci. Da za su tafi Khalil ya so keɓewa da Zahrah bai samu damar hakan ba, don haka ya ɗauki wayar da ya gani akan kujerar wanda ya ke da tabbacin na Zahrah ne, dubawa ya yi ba password take ya saka lambar wayarsa ya kira. Sai da ya ji kiran ya shigo wayarsa ya ajiye. Ganin kowa ya zuba masa idanu ne ya faske tare da cewa. "Akwai maganin da zan kawo mata ne shi ya sa na ɗauki lambar idan zan kawo sai na sanar da ita" "Yes Doctor." Amal ta yi maganar tana sara masa. Dariya Sadik da Mahmud suka yi don su kadai ne a wajen Ummi da ƙanwarta suna cikin ɗaki suna magana. A tare suka fito daga cikin ɗakin tana sauri ganin kiran mijinta na shigowa wayar. Har parking space suka taka su sai da suka ga wucewarsu suka koma ciki. _Sulaiman_ Yana magana da Dad wayarsa ta yi ruri. Ganin Asadullah ne ya saka bai ɗaga a gaban Dad ba. Magana suke yi akan Asad don Dad ya damu da rashin sanin halin da yake ciki, ga ramar da ya ys yi . Dad yana cikin damuwa sosai sai dai yanayin da ya ga Sulaiman a ciki ya saka shi cikin wani tunanin. A baya idan ya ga Sulaiman yana hango tsantsan damuwa da tashin hankali, sabanin yanzu da yake ganin kamar bai damu da rashin uban gidan na sa ba. Dole akwai wani abu a ƙasa. Bayan ya sallama Sulaiman ne ya koma ciki yayin da Sulaiman ɗin ya fito daga falon Dad ɗin. A can bakin gate kuwa hayaniya ce ta kaure a tsakanin Isah Yayan Jidderh da security. Ya zo ne saboda ya sake jin ko an samu labarin ta, security suka hana shi shigowa shi kuma ya dage sai ya shigo. Sulaiman na sauri don zuwa gidan Asadullah kenan ya ji hayaniya. A can bakin gate kuwa Isah ne yake yi wa security magiya akan su bar shi ya shiga ciki karo na karshe kenan. "Don Allah daga yau ba zan sake dawowa ban nan ba, zan so na yi magana da..." "Kai wallahi ba zan bari ka shiga ba, wani irin bakin naci ne da kai, idan mutum ya ɓata ai police station za ka je ko gidan rediyo ba nan ba." Dole isah ya hakura ya goge ƙwallar da ta cika masa idanu ya juya zuwa wajen babur ɗin da ya kawo shi. Wato abokinsa tun safe suna ta yawon nemanta. Yana hawa babur ɗin daidai lokacin Sulaiman ya fito hannunsa rike da waya ya kara a kunnensa, suka haɗa idanu da Isah daidai lokacin da babur ɗin ke shirin barin wajen. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page5️⃣4️⃣ Yana hawa babur daidai lokacin Sulaiman ya fito hannunsa rike da waya ya kara a kunnensa, suka haɗa idanu da Isah daidai lokacin da babur ɗin ke shirin barin wajen. Kallon ɗaya daga cikin security ɗin ya yi sannan ya ce. "Hayaniyar ne nake ji?" "Wasu mahaukata ne suke neman kawo mana shirme a nan, idan mutum ya fadi a police station amma sun damu mutane da hayaniya anan." "Wani ne ya ɓata?" Cewar Sulaiman yana tsare securityn da idanu. "Wai wata ce da take aiki a gidan nan suka nema suka rasa?" A kiɗime Sulaiman ya tambaya security ɗin. "Wai tun ranar da aka yi gobarar nan aka..." Kafin security ya karasa fada masa tuni Sulaiman ya bi hanyar da ya ga sun bi da babur ɗin a guje. Security da suke waje suka saki baki suna kallonsa cike da mamaki. Ganin ba alamar su ya saka ya dawo da sauri yana cewa security su bude masa kofar gate ɗin da sauri. Da gudu ya nufi parking space ya shiga daya daga cikin motocin da ke wajan ya saka makullin ya yi mata key ya fige ta. Zuwa lokacin har an wangale masu gate a guje ya bar wajen suka mamakin rikicewar da ya yi lokaci ɗaya . _Washegari_ Jirginsu na sauka a filin jirgin sama, tun daga nesa suka hango kakan na su da direban na sa, fuskarsa dauke da murmushi yayin da shi ma murmushin take sakar masa. Ita ma murmushin take yi. Kowa na rike da madaidaicin jakarsu. Direban Kakan na su ne ya karbi jakarsu ya saka a bayan motar . Rungume tattijon Ammar ta yi ita ma Humaira ta rungume shi ta baya. Farin ciki ne ya daka idanun Dattijon ciki da ƙealla, cike da son jikokin na sa ya ke saka masu albarka. Don Allah ya sani yana son kusanci da iyalinsa, sai dai ɗan na sa wato mahaifin su Ammar ya nisanta kansa da gida. Sai shekara yake zuwa da iyalansa. Sai dai wani lokaci ya kan ga Ammar ya zo shi ma dalilin abotarsu da Hilal ne idan ya kawo masa ziyara. Saboda Hilal yakan shigo ko na lokacin ziyara da suka saba zuwa . ba. Yanzu kuma dalilin zuwan na su saboda Zahrah ce, tun da aka fada masa ba ta da lafiya ta kwanta asibiti shi kenan hanakilinsa ya tashi ya ce dai ya zo ya ga halin da take ciki. Lokacin da ya kira wayar da niyyar ya haɗa Zahrah da ƙanwarsa Humaira don su gaisa ne dai Dada ta ɗauka take sanar da shi rashin da Zahrah ke fama da shi . "Ba shi kaɗai ya shiga tashin hankalin ba Humaira da yake tare da ita a lokacin ta shiga damuwa sosai ba kaɗan ba. Don haka da ya ce zai zo da ta ce za ta biyo shi, iyayen sun ɗauka cewa za su zo saboda kakanninsu ne amma su kam sun san dalilin zuwansu ba don ziyara ga kakanninsu suka zo ba. Shi ma Baba Alhaji wato Kakansu ya ɗauka sun zo don su sada zumunta ne, shi ya sa har ƙwallar farin ciki ya yi . Mota suka shiga Direban ya ja don kai su gida. Ko da suka isa gidan Kakansu mace wato Hajiya Mama ta yi farin cikin ganin jikokin na ta. Farin ciki sosai ya cika gidan. Sail da suka yi wanka suka ci abinci ne sai suka ce za su fita Mutanen gidan sun yi mamakin jin cewa za su fita, sai ya sanar da su gidan Aninin na sa zai je. Ba su da wani zaɓi suka bar su. Ɗaya daga cikin motocin ya ɗauki key ɗin, sannan ya basu tsarabar su bayan ya ce wa Humaira ta kai na Zahrah mota. Bayan ya ji wa motar key ne ya danna horn maigadi ya wangale masu gate ɗin suka bar gidan. Suna ta fira duk yana bata labari akan Zaheah har suka karasa gidan. A parking space ya yi parking ba tare da ya fito ba. Kallonsa Humaira ta yi tare da cewa. "Lafiya kuwa Yaya?" "Ina tunanin yadda zan shiga gidan ne da sunan wajen Zahrah na zo, ai ba baki labarin irin zaman da suke yi a cikin gidan nan. Ta ya ya xan kalli iyayen abokina bayan na san ba jituwa a tsakanin su da su Zahrah. Wancan zuwan na ga kallon da suke yi wa Zahrah." Taɓe baki ta yi sannan ta ce. "Kada ka damu Yaya ka share su ka yi abinda da ya kawo ka." Wayarsa ya ɗauka sannan ta lalubo lambar Zahrah, tana ganin kiransa da ɗauka da sauri ganin lambarsa ta Nigeria ce "Assalamu alaikum Ya Ammar ka zo ne?" Mumrmushi ya yi sannan ya ce. "Ina mota har da ƙanwata ki fito ki same mu a parking space." "Okay" Ta fada ta kashe wayar sannan ta kalli Dada dake kallonta. Don su biyu ne a falon Dada . "Wai Yaa Ammar ne ya zo da ƙanwarsa suna parking space wai na je." "To jeki amma ki tabbatar iyakar ki wajen kada ki fita daga cikin gidan nan." "In sha Allahu." Ta saka hijabinta har ƙasa sannan ta saka flat shoe ɗinta ta fita . Mutanen gidan kuwa suna fakon gidan suna fira, don gabaɗaya sun hallara idan aka cire ƴan part ɗin su Zahrah. Maza da mata iyaye da yara, har da iyayen maza suna cikinsu sau fira suke yi cike da nishaɗi. Zahrah ta zo ta wuce su ta nufi hanyar fita. Tun daga nesa suke hango ta tana karasawa in da suke cikin takunta na nutsuwa. "Wow" Humaira ta furta tana murmushi. "Gaskiya Yaya Zahrah hadaddiya ce, wannan tsantsar kyau haka?" Mumrmushi kawai yake yi idanunsa na ga Zahrah. "Ba iya kyau kawai take da shi ba, tana da kyawun zuciya da halayya masu kyau, Zahrah nagartacciyar mace ce wacce ko wane namijin da ya san kansa zai yi kokari mallakar ta a matsayin mahadin rayuwarsa uwar ƴaƴansa." Gakskiya ka yi sauri ka aure ta kada ka tsaya kallon ruwa kwaɗo ya yi maka kafa. Ba namijin da zai ganta ya kaida kai." Haka ne, shi ya sa kullum take sanya niƙab ko Facemask idan za ta fita waje." Daidai lokacin ta karaso bakinta ɗauke da sallama cikin zazzaƙar muryarta. Amsa mata suka yi s tare suka fito daga motar. "Yaa Ammar sannu da zuwa ." "Yauwa Sanni sarauniyar mata, kin warke ma ko?" Ya faɗa yana mata murmushi. "Tare da ita kuka zo tun daga London ne?" "Eh wai za ta zo ta duba jininki." "Sannu da zuwa ƴar uwa, ya hanya?" Ta faɗa tana murmushi, rike hannun juna suka yi suka shiga daga cikin gidan. A falon gidan suka yi sallama dukkansu, gabaɗaya suka juyo suna kallonsu. Humaira ta sunkuya cikin girmamawa ta gaida mutanen gidan. Ganin ta da Zahrah ya saka ba wanda ya amsa, sai dai Mommy da Aunty Laila suna mata kallon sani, sai dai sun rasa ina suka san ta. Jan hannunta Zahrah ta yi suka nufi part ɗin Dada, da sallama Dada ta amsa masu cike da fara'a. Nan Humaira ta gaishe ta ta amsa mata cikin sakin fuska da walwala. Sallamarsa ne ya saka suka amsa suna kallonsa. "Yaa Ammar." Da mamaki kowa ke kallonsa, ganin cewa bai taba zuwa idan Hilal baya nan ba, duk zuwansa sai Hilal na ƙasar yake zuwa. "Ammar saukar yaushe a ƙasar?" "Yau na zo." Da fara'a kowa ya tarbe shi ya zauna suka gaisa da kowa. "Ga shi abokin na ka baya ƙasar." Cewar Mummy. "Eh wajen Zahrah na zo." "Wajen Zahrah?" Suka haɗa baki kusan dukkansu wajen furta kalmar." "Eh na ji labarin ba ta da lafiya shi ne muka zo ni da ƙanwata don duba lafiyarta." "Wai wannan yarinyar da suka shigo da Zahrah ita ce Humaira ?" Cewar Mummy cike da takaici. ",Eh ita ce dama ba ki gane ta ba ne?" Tsabar takaici kasa magana ta yi, kowa dake wajen ba wanda ya yi farin ciki da jin jin zancen Ammar. Tashi ya yi yana cewa . "Bari na gaida Dada " Bayan tafiyarsa Aunty Laila ta ce "Sai na bi duk hanyar da zan bai don ganin na hana Ammar auren wannan yarinyar, matukar ina numfashi a duniyar nan ba zan taba bari na wani ya zo neman aurenta ban lalata maganar ba." Jinjina kai Mummy ta yi tare da cewa "Ina bayanki ɗari bisa ɗari. Ba za ta taɓa yin rayuwar farin ciki ba daga ita har Iyayenta mu zuba mu gani." Jinjina kai Umma ta yi tana murmushi tare da masu alamar Jinjina. A ɓangaren Dada suke a falonta, Dada, Ammar, Zahrah, da Humaira. Fira suke yi cikin annashuwa da farin ciki,, duk da cewar Zahrah ba ta saki jiki ba saboda Ammar na wajen kunyarsa take ji An cika masu gaba da kayan ciye-ciye da na sha. Bayan sun kammala ne Suka tashi suka nufi part ɗin Abbi. Su uku ne Zahrah da Humaira na rike da hannun juna sai Ammar dake bayansu. Har lokacin jama'ar gidan na falo.suna ganinsu bakin cikinsu ya kafa ninkuwa. Don sun san in dai Ammar ya auri Zahrah ta huta. Za ta samu duk wani abun da take buƙata na more rayuwa. Su kuma ba haka suke so ba, so suke yi su ga rayuwarta ta tagayyara. Da sallama suka shiga part ɗin Ummi tana zaune da alƙur'arni mai girma tana karantawa . Tana kai aya ta ajiye ta tarbe su da fara'a duk da ba ta yi mamakin ganin Ammar ɗin ba. "Bisimillah." Suka zauna bayan sun gaishe ta, ta amsa cikin farin ciki da walwala. Abbi ya fito daga ɗakinsa ya ya karaso falon. Suka gaishe shi kasancewar weekend ne kowa na gida, Yaa Mahmud da Yaa Sadik ma duk sun fito an gaisa. Nan ma Ummi ta kawo masu abun sha duk da sun ce sun cika ciki a bangaren Dada. _Asadullah_ Wayar Sulaiman yake kira baya daga wa. Jikinsa ne ya bashi akwai wata matsala dake faruwa . Sake kira ya sake yi a daidai lokacin da yake driving yana ƙoƙarin barin layin Asadullah mansion, ɗagawa ya yi tare da kara wayar a kunnensa. "Yallaɓai zan kira ka ina ƙoƙarin bin bayan wadanda suka zo neman Jidderh ne, da alama Yayanta. Yana faɗin haka ya katse kiran wayar da alama sauri yake yi sosai. Asadullah bai san sanda ya saki murmushi ba, saboda ya ji dadin wannan labarin da ba ya ji. Ya kuma yi addu'ar Allah ya bayyana ta. Kiran waya ne ya shigo wayarsa dubawa ya yi ya ga sunan da ya bayyana akan fuskar wayar. Inspector Bashir. Shi ne sunan da ya bayyana akan fuskar wayarsa. Ɗaga wa ya yi tare da yin sallama.bayan ya amsa sallamar daga can ɓangaren ne Asadullah ya ce. "Ya aiki?" "Alhamdulillah." Inspector ya amsa sannan ya ce. "Shi wannan sagir ɗin da ya yi ƙoƙarin kashe ka a baya tare da ɗan uwanka mun gano in da yake." Da sauri Asadullah ya mike tsaye yana cewa. "A ina yake yanzu?" "Bayan mun yi bincike mun gano cewa yau satin sa ɗaya kenan da ya dawo ƙasar, kuma yana garin Lagos ne a yanzu haka." "Da kyau." "Mun gano cewa akwai yarinyar da yake nema a garin ne, ta hanyar ta za mu fara bi, ita ce tsanin da za mu bi ta kai mu zuwa gare shi. Don yanzu yana taka tsan-tsan da mutane ba zai saki jiki yadda zai kamu cikin sauki ba." "Okay" "Yanzu ka jira za ka ji daga gare ni, don akwai abubuwan da nake bukatar ji daga gare ka." "In sha Allah." "Kada ka damu zai shiga hannu kamar yadda Kamal ya shiga hannu yana prison, wata kila ma yana da saka hannu a abinda aka yi maka na rufe ka tsawon lokaci. Bisa la'akari da ya zauna a cikin mansion ɗin tsawon lokaci ya san komai na ciki." *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page5️⃣5️⃣ Kada ka damu zai shiga hannu kamar yadda Kamal ya shiga hannu yana prison,watakila ma yana da saka hannu kan abin da aka maka na rufe ka tsawon lokaci. Bisa la'akari da ya zauna a cikin mansion ɗin tsawon lokaci ya san komai na ciki." Ɗan jim Asad ya yi kafin ya ce. "Ta iya kasance wa haka ne, amma abun da hankalina ya fi karkata wani ne daban ba Sagir ba." Ta iya yiwuwa haka ne, ta iya yiwuwa ba haka ba ne, amma bincike zai tabbatar mana da ko waye ya aikata wannan laifin. Ku shi ne ko kuma wani ne daban daga gefe". "To shi kenan inspector Bashir Na gode sosai." Daga haka suka yi sallama ya kashe kiran wayarsa. _Zahrah_ Wunin ranar yin shi ta yi tare da Ammar da kuma ƙanwarsa. Ta yi shi ne cikin farin ciki da jin dad'i. Don Ammar ya shiga ranta duk da idan ta tuna da zantukan mahifiyarta jininta yana sanyi sosai. Don ta ga alamar cewa su Mummy ba za su bari Ammar ya aure ta ba. Ko da ba su san waye iyayen Ammar ba za su yi iyakar kokarinta ganin sun ɓata komai. Ballantana akwai mutunci da zumunci a tsakanin Mahaifiyar Ammar da mahaifiyar Hilal ɗin Sai kusan magrib Ammar ya ce wa Humaira ta tashi su koma gida. Don lokacin sun bar part ɗin Ummi sun koma na Dada. Wata shaƙuwa ce ta shiga tsakanin Humaira da Zaharah a cikin yini guda . Tamkar Wadanda suka shekara da sanin juna Dama sun yi wa su Ummi sallama don haka suka yi wa Dada sallama a lokacin da za su tafi. Ko da suka karaso main falon gidan ba kowa. Da alama kowa ya koma part ɗin sa kenan. Kallon Humaira Ammar ya yi kafin ya ce. "Ya kamata na shiga na gaida Mummyn Hilal, idan na tafi ban shiga ban kyauta ba." "To ka shiga ka dawo mana." "A'a tare da ke za mu je." Da mamaki take kallonsa. "Ni kuma wallahi Yaya bana son zuwa na ga take-taken mutanen gidan nan ba su da mutumci. " "Eh ba da da shi amma dole sai mun je mun gaida mahaifiyar Hilal." Tura baki ta yi kafin ta kalli Zahrah ta ce. ", Sister mu je ki raka ni." Da sauri ta girgiza kai, don ta san matuƙa ta ke part ɗin Mummy sai ta gwammace dama ba ta shiga ba. Don haka ta ƙaƙalo murmushi ta ta ce. "Ku dai je ku dawo." Zata sake wata magana dai Ammar ya ja hannunta suka nufi part ɗin Mummy, ba tare da ya ba ta damar sake magana ba . Da idanu Zahra ta taka su tana murmushi. Da sallama suka shiga kofar part ɗin. Daddy, Mummy, Faisal, Maryam duk suna falon, amsa masu sallamar suka yi yayin da suka karaso ciki. Cikin girmamawa suka gaida Dad da Mom. Suka amsa masu ba yabo ba fallasa. Faisal da Maryam ma suka gaishe su "Dama har yanzu kuna gidan nan ne?" "Eh Mummy wannan karon kun ga ban zo lokacin da Hilal kenan ba ko, wannan karon zuwan na Zahrah ne." Amma tun wancan zuwa Laila ta baka shawarar cewa ka fita harkar Zahrah domin ƴar iska ce bin maza take yi ko?" Shiru ya yi kafin ta cigaba da cewa. "An fada maka bar cikin shege ta yi ta zubar shi ne ba za ka nemi yar mutunci ka aura ba sai ita ko? Idan ma ya zama dole a cikin wannan family na Tafarki kake neman aure ga ƴan mata nan muna da su da yawa sai wacce ka zaɓa, why not ka zaɓi ɗaya ka mance da Zahrah." Ɗago idanu ya yi ya kalle ta kokarin ita ma shi take kallo ya ce. "Mummy wallahi zuciyata Zahrah take so, bayan ita ban ga wata ƴa mace da ta kwanta Mani a rai ba, Mummy ana zuwa gidan ƙaruwai a auri mace jihadi ne domin an tairatar da ita daga halaka. Wallahi duk yadda Zahrah ta kai ga lalacewa ina son ta a haka , kuma in sha Allah kafin na bar garin nan zan tura a nema mani aurenta." Sakin baki suka yi suna kallonsa, yayin da ya ce wa Humaira. "Tashi mu tafi." A tare da ita suka mike suna masu sallama ba wanda ya amsa sai Maryam. Mamaki da al'ajabi ya hana Humaira da Ammar magana har suka karaso in da Zahrah take. Ƙoƙarin daidaita kansu suka yi don kafa ta fahimci komai. Sai ma murmushi da suka yi mata lokaci guda. "Kun fito?" Ammar ya ce "Eh mun fito, jibi xan dawo ni kadai don yau wannan yarinyar ta takura Mani, ba ta bari mun samu isasshen lokacin da za mu yi zance ba, ta cika ku da surutu." Humaira ta yi saurin cewa "Ai ko za ka dawo ba biyo ka zan yi ba, na zo na ga Zahrah, dama ai ni ka kawo na ganta . Idan ka sake dawowa Sai ku ci soyayyarku." Umarnin ɗauko sakon da suka zo da ji ya ba Humaira. Ta karbi key ɗin motar ta fita don dauko sakon. Manyan kedoji ne guda biyu shaƙe da kaya, ta ajiye tare da cewa "Ga su." Kallon Zahrah ya yi tare da cewa "Ga tsarabar ki nan gimbiyata." Kallon kayan ta yi tare da cewa. "Yaa Ammar don Allah ka bari na dauki ɗaya sun yi yawa, dayan ma na don Ummi ma sai ta yi faɗa. " Duk yadda ta yi akan su rage kayan ba su saurare ta ba suka fice suna mata sallama. Ba ta da wani zaɓi ta ɗauki kayan niƙi-niƙi ta nufi part ɗin Dada, don tana tsoron Ummi, saboda Ummi ta hana ta karbar komai daga hannun wani ɗa namiji. Da sallama ta shiga wajen Dada, tana kokarin shiga bedroom ta ga Zaheah da kaya niƙi-niƙi a hannunta. "Wadan nan kayan daga ina haka?" Kamar za ta yi kuka ta fara magana. "Yaa Ammar ne ya bani, kuma Ummi za ta yi Mani faɗa ya sa na kawo nan, na ce ya rage kayan amma ya ƙi." Shiru Dada ta yi kafin ta ce. "Umminki ba ta yi laifi ba gaskiya, domin babu amfanin ki yi ta karɓar abun samari bayan ba aurensa za ki yi ba." Da sauri ta kalli Dada jin zancen ta, Allah ya sani tana don Ammar har cikin zuciyarta. "Kada ki damu ki yi addu'ar Allah ya zaba maki mafi alkhairi a gare ki, idan Allah ya sa Ammar mijinki ne sai kin aure shi." Jinjina kai ta yi tare da cewa. Ki kai kayan ɗakinki daga wannan ɓangaren ba ɓangaren Umminki ba, zan yi magana da ita in sha Allah." Daga haka ta kai kayan bedroom ɗin ta dake kusa da bedroom ɗin Dada, sannan ta yi mata Sallamar za ta koma part ɗin Ummi." "Ba nan za ki kwana ba ne?" "A'a wajen Ummina zan kwana sai da safe." Daga nan ta fice Dada na cewa. "Yarinyar nan ƴar ganin dama ce, sai in da kika dama za ki kwana ko? To Allah ya tashe mu lafiya." Daga haka ta koma part ɗin Umminta. *Washegari* Kamar yadda Ammar ya ce zai zo bayan kwana biyu kasawa ya yi, sai ga shi ya zo a ranar. Ko da ya kira ta a waya lokacin tana part ɗin Dada. Don cewa ya yi ta fito ba zai shiga ciki ba, don baya son Mummy ko Aunty Laila su sake ɓata masa rai ko su ɓatawa Zahrah rai. Sanye take da hijabi har ƙasa onion colour ya mata kyau. A hankali take tafiya wanda tun da ya hango ta ya fito daga cikin motar.sanye yake cikin ɗanyar shadda fara, ɗinkin daidai jikinsa na zamani wanda ya dace da shi. Sai baƙar hula da bakin takalmin dake ƙafarsa, ƙamshin turarensa ke tashi a jikinsa ya rungume hannayensa a ƙirjinsa yana sakar mata sanyayyar murmushinsa. "Assalamu alaikum" Zazzaƙar muryarta ta daki don kunnensa. Sai da ya lumshe Idanu ya bude a kanta kafin ya amsa mata. "Ina wuni Yaa Ammar." "Lafiya lau. Ya ƙarfin jikin?" "Alhamdulillah na warware." "Yau ba zan shiga ciki ba" Hakan ya saka ta nufi wajen kujerun da aka tanada dan zaman shan iska daga can gefe. Bin bayanta ya yi suka zauna suna fuskantar juna. Sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da yatsun hannunta da suka sha jan lalle. *America/New York City* Dawowarsa kenan gidan ya ɗauko ruwa a fridge, tsiyaya wa ya yi a kofin glass zai sha. Wayarsa ce ta soma ringing, ya duba ya ga Mummy ce. Ɗaukar wayar ya yi ya kara a kunnensa, ya dauki kofin ruwa ya riƙe. "Hello Mummy dawowa na kenan, ina son idan n huta na kira ki." "To ya kake ya aiki?" "Alhamdulillah Mummy." "To ma sha Allah." Ta fada kafin ta ce. "Wai abokinka nake son ka ba shawara." "Wane abokin kike nufi Mummy." "Ammar mana." Ruwan da ya zuba a kofi ya sha kafin ya ce. "Okay." Ya ce yana jiran jin abun da za ta ce "Wai shegiyar yarinyar Zahrah zai aura, kuma ya samu goyon bayan Kakarku." "To ni me zan yi akai?" Ka bashi shawara yarinyar nan fa Yar iska ce bin maza take yi, ta sha zubar da ciki, ja bashi shawara ya rabu da ita ya nemi wata ya aura." "Mummy saboda wannan dalili ya saka kika kira ni?" "Eh mana, Hilal na san Ammar ba ka da wani abokin sama da shi zai ji maganarka." "Mummy ki mai da wajen abun da yake gabanki. Na gaji yanzu zan huta sai mun sake magana." Bai jira cewarta ba ya katse kiran wayar. Daga can ɓangaren kuwa Mummy kallon wayar take yi tana mamaki. Kallon wayar kawa ta yi tare da ajiye wa. "Dama na sani yaron nan ba zai taba saurara ta ba, duk maganar da zan masa, ya fifita waɗan can tsofaffin akan kowa, su kadai za su yi masa magana ba zai tsallake ba, ba zai yiwu ba dole na yi wa tufkar hanci. Idan ba haka ba ina ji ina gani zai fi karfina." "Fin ƙarfinki na nawa kuma ?" Da sauri ya juya ta kalli Aunty Laila dake tsaye a bakin ƙofa. "Ai Hilal dama tun can baya jin maganarki ko na Mahaifinsa, mutum daya ke masa magana ya ji shi ne Papa sai kuma Dada, su yi iko da ɗa sannan su yi da jika." Jikin Mummy ne ya yi sanyi, sai jin muryar Aunty Laila ta yi ta sake cewa. "Na tabbatar da Papa ne ko Dada suka ce ya dakatar da Ammar wallahi da ya dakatar da su. Don su ya dauka uwa da uba, shakuwar dake tsakaninsa da su baya tasaninki da shi ko wani shawara da su yaje yi me kika dauki hakan?" Shiru Mummy ta yi kafin ta ce. "Na ɗauka shakuwa ce saboda kin san shi ne jika na farko a gidan nan, kuka tun da aka yaye shi ya fi zama da su Papa ya kan fita da shi ko Dada ma na fita da shi ko abinci ya fi cin na su na ɗauka shakuwa ce. Sai bayan ma da aka haifi shegiyar yarinyar can Zahrah na ga sun raba kaunar da suke masa gida biyu sun ba ta gida ɗaya shi na gida ɗaya. Tun lokacin da na ga Zahrah ta shaƙu da kakanni suna sonta hankali na ya tashi amma da na tuna yadda suka nunawa mahaifin ta kauna da fifiko ya sa na gane hakan ya saka ita ma soyayyar mahaifinta ya shafe ta. Na so janye Hilal daga wajan su don kada shakuwa ta shiga tsakaninsu da yarinyar amma bai saurare ni ba. Sai sai na yi nasarar cusa masa tsanar yarinyar a cikin zuciyarsa. Kuma Alhamdulillah ya tsane ta wanda na lura ba sa zama inuwa ɗaya." Mumrmushi Aunty Laila ta yi kafin ta ce. "Da sauran rina a kaba." Daga nan ta juya ta bar Mummy tana aikin fashin baki akan kalmar Sunyi Laila. Duk yadda Sulaiman ya yi kokarin ganin ya samu yayan Jidderh ya kasa. Don da ya hau titin ma bai ga mai kama da mashin ɗin da ya gan su da shi ba Wunin ranar haka ya dinga yawo amma bai gan su ba, cikin takaici ya koma mansion ɗin. Wanka ya yi ya canza kaya ya ɗan yana son komawa wajen uban gidansa ya sanar da shi halin da ake ciki. Yana fitowa Falo wayarsa dake cikin aljihu ya fara ringing ɗauka ya yi tare da cewa. "Hello Yallaɓai ban same su ba, amma gani nan zan sanar da kai komai, ka gafarce ni mai gidana na kasa cika maka burinka. Amma in sha Allah sai na samo maka su a duk in da suke, gani nan zuwa . Yana ajiye wayar suka yi Idanu biyu da Dady da alama tun kafin ya fito yake nan, kuma alamu sun nuna ya ji duk maganar da ya yi a wayar. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ https://chat.whatsapp.com/DK3nAxNaxVV6U3giyRUZQO?mode=r_c Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/DK3nAxNaxVV6U3giyRUZQO?mode=r_c *Albishir! Albishir!! Albishir!!!* Jama'a na ina maku albishir da cewa na kawo maku kayan kitchen masu kyau da inganci. Za ku darje ku zaɓi kayayyaki masu dangareren kyau. Duk a cikin farashi mai sauƙi da rahusa daidai da aljihunku. Ƴar uwata idan kina son ki damu kayayyakin da babu kamarsu masu bigewa da inganci to Hajiya ga dama ta samu .muna siyar da kaya kamar haka.👇 Flasks Cups Dinnerset Kitchenware Pot Jugs Food processor bedsheet lamps Second hand gas Duk wani kitchens items na kayan kitchen muna saidawa. Zu ku iya tuntubar mu ta wannan lambar waya 07018401887 Page5️⃣6️⃣ Yana ajiye wayar suka yi Idanu biyu da Dad da alama tun kafin ya fito yake nan, kuma alamu sun nuna ya ji duk maganar da ya yi a wayar. Murmushi Sulaiman ya yi kafin ya ce. "Dad yau..." Dakatar da shi ya yi ta hanayar daga masa hannu. "Rainin hankalin ya ishe ni haka Sulaiman, tun yaushe kake ɓoye Mani gaskiyar abun da ke faruwa?" Shiru Sulaiman ya yi ya kasa cewa komai, in da Dad ya cigaba da cewa. "Dama na yi tunanin abin da kake boye mani, domin na ga canji a tattatre da kai. A lokacin da Asad ya ɓata ko kuma na ce ya gudu tun da nemansa muka yi muka rasa, a lokacin ka shiga damuwa sosai ba kaɗan ba, kai ka la shiga wannan damuwar wanda duk wanda ya kalle ka ka ya san cewa kana cikin damuwa. Amma dawowar nan da na yi ban ga alamar damuwa a tattare da kai ba. Kuma na san a baya akwai damuwar saboda kana da kusanci da Asad ko zai boye wa wani kai ba zai boye maka ba." Numfasawa ya yi sannan ya cigaba da magana cikin rauni. "Ban san me ya ɗauke ni ba, ko kuma ya mayar da ni matsayina na mahaifinsa dole ba shiga cikin damuwa sosai ba kaɗan ba. Shi me na yi masa da ya guje Ni?" Ya yi maganar kamar zai yi kuka. Sulaiman ya yi saurin cewa . "Dad bai guje ka ba, yana da dalilinsa na aikata hakan, yanzu ka shirya mu tafi wajensa. Amma da sharadi." Da mamaki Dad ke kallonsa wai shi za'a gindaya wa sharadi akan zai je ya ga ɗansa. "Dad ba wani sharadi ba ne, ina son kada ka faɗa wa kowa in da za mu, kafin nan wannan maganar ta zama sirri a tsakanin mu, akwai dalilin hakan ne, idan muka je za ka k ji komai daga bakinsa. Kai ya jinjina sannan ya ce . "Muje ko?" ' "Dad je ka shirya na ga jallabiya ce a jikinka?" "Muje haka nan n shirin da zan yi." Ya yi maganar cikin ɗokin zai ke ya ga gidan jininsa. A tare suka fito har parking space suka nufa. Kallonsa Sulaiman ya yi kafin ya ce "Dad ba Direban ka zai kai ka ba fa, ni zan kai ka da kaina kuma na dawo da kai ." Kafin Dad ya yi maganar har Direban ya karaso Wajen, don ya ga Dad a parking space ya san fita zai yi . "Barka da warhaka Dad." "Yauwa Barka, ka yi zamanka a yanzu zan dawo in sha Allah, a motar Sulaiman za mu tafi." Jinjina kai ya yi sannan ya bar wajen yana masu Allah tsare hanya. Su kuma suka shiga motar suka bar mansion ɗin. _Zahrah_ Suna zaune wajen shan iskar nan ita da Ammar. Fira suke yi mai cike da so da kaunar juna. Kuma da zaran ka kalli fuskokin su ka san ba karamin so suke yi wa juna ba. Don suna cikin nishaɗi sosai b kadan ba. Mummy bayan ta gama waya da Hilal cikin takaicin yadda bai nuna damuwa akan abinda ta fada masa ba ta miƙe, jikin window ta karasa ta yaye labulen window ɗin, dama ta gansu ne shi ya sa ta kira Hilal ta sanar da shi komai. Sake hango su ta yi har lokacin fuskokinsu cike da farin ciki. Komawa ta yi ta zauna bakin gadon cike ta takaici. Sallama Ammar ya yi mata don gobe yake son komawa London. Sai ya yi shiga ya yi wa Dada da Ummi sallama sannan ta raka shi parking space ya tafi. Duk da ya so shiga gaida Mummy sai dai ya san muddin ya shiga sai ya tarar da ɓacin rsi don sai ta yi masa abun da zai bata masa rai kamar yadda ya yi masa a a daren jiya. Bayan ta ga tashin motarsa ne ya bar gidan gidan sannan ta koma ciki. Magana ɗaya da ya yi mata ya tsaya mata a rai ta kasa yadda za ta iya sanar wa Ummi ko Abbi zancen. Wato cewa da ya yi ta sanar da Abbi zancen zai turo magabatansa s nema masa auren ta. Ta nuna masa cewar sai ta kammal karatunta. Ya nuna mata cewar bai yarda ba kuma ba zai iya jira yana can wani ya yi masa sakiyar da ba ruwa ba, sai dai a yi auren ta cigaba da karatunta a can ƙasar London ɗin. Da wannan tunanin ta koma ciki, sai dai ta saka wa ranta ba za ta sanar da iyayen ta komai ba, don tana son sai ta kammala karatunta na digiri kafin ta yi aure. *America/New York City* Sai Safa da marwa yake yi a ɗaukinsa,, gabaɗaya ya kasa gane abun da ke damunsa. Amma haka kawai yake jin zuciyarsa babu nutsuwa a cikinta . Kalaman Mummynsa ke yawo a cikin kansa. Da maganganunta da ta yi masa da yadda ta nuna ɓacin rai da damuwa kan lamarin. Yana tsaka da yin tunani sai ga kiran Ammar ya shigo wayarsa. Ƙarasowa ya yi ta kalli fuskar wayar sai ya ga Ammar ne ke kira. Haka kawai sai ya ji ya tsinci kansa da jin haushin kiran da ya yi masa da kuma jin haushin Ammar ɗin shi kansa. Sau biyu yana kira bai ɗaga ba, sai a na uku ya ɗaga cikin takaici. Bai yi magana ba har tsawon sakanni goma, sanin ba zai yi magana ba ne ya saka Ammar yin murnushi ya ce. "Hello." "Ina jin ka." Shi ne abin da Hilal ya ce masa. Murmushi ya sake yi duk da ya san mishkilanci irin na Hilal amma yau sai ya ji yanayin da ya yi magana kamar akwai damuwa . Don haka ya ce "Abokina kana lafiya kuwa? Oh sorry yanzu kai Yayana ne tun da ina shirin yin auren ƙanwarka nan da watanni kaɗan." "Abinda ka kira ni ka faɗa Mani kenan?" "Eh. Ina neman..." Kafin ya karasa abin da zai fada sai ya ji Hilal ya katse kiran wayar. Gabaɗayasu ya kashe wayar don ya san in dai Ammar ne sai ya sake kiransa. Takaicinsa ne ya karu a cikin zuciyarsa . "Dole na tafi Nigeria a cikin satin nan," Ɗayar wayarsa ya ɗauka ya kunna Data. What'sup ya shiga in da ya ci karo da sakonnin mutane da yawa, kusan duka yan gidansu Tafarki Family ya ga sakonni su idan aka cire Abbi da iyalansa. Har da sakon Ammar ya ga ya shigo a lokacin, bai bude ba ya cigaban da duba wasu sakonnin. Na Mummy ya shiga ya duba. Voice message ne ta yi masa, budewa ya yi yana sauraro. "Wato ni yanzu ban da mahimmancn da zan saka ka yin abu ka yi idan dai ba waɗan can tsofaffin ba ne ko? Na kira ka akan ka bawa Abokinka shawara ya janye kudirin sa na auren yarinyar nan ka yi biris da ni ko? Ai za ka iya juya masa tunani musamman da ka san yarinyar nan yar iska ce ita, ta gana yawon banza da iskancin ta ga gama zazzage 'ya'yanta a kwararo za ka bari ya aura, ina amintar ta ku yake ai ba amana. Ka dakatar da shi idan bai dakatu ba zan sanar da mahaifiyarsa ne." Shiru ta yi kafin ta yi mata reply ta hanyar typing. "Zan zo a cikin satin nan in sha Allah." Daga nan ya ajiye wayar, system ɗin sa ya janyo ya cigaba da wani binciken da yake yi. _Asadullah_ "Bude kofar falon ya yi ya sauke idanunsa akan Dad ɗin sa, sannan ya kalli Sulaiman. "Dad dama..." Dakatar da shi ya yi ta hanyar cewa "Ba abun da za ka faɗa Mani, dama burina na san halin da kake ciki, kuma na sani yanzu tun da na ganka, Alhamdulillah." Yana gama fadar haka ya juya ya kalli Sulaiman ya ce. "Za ka iya maryar da ni gida yau ko na kira direba na ya zo ya ɗauke ni?" Kafin Sulaiman Ya yi magana Asadullah ya ce "Dad don Allah ka tsaya ka saurare ni, ba yadda kake tuninin na guje ka ba ne.". "Ba abinda zan saurara daga gare ka, Asadullah ka bani mamakin ina matsayin mahaifi a gare amma wasu ne su san halin da kake ciki da ni?" Cikin takaici ya nufi gate ɗin zai fice. Asadullah ya bi bayansa a buɗe ya durkusa a gabansa ya rike ƙafarsa. "Don Allah Dad ka saurare ni, wallahi ba yadda kake tunani ba ne." Ganin Idanun Asadullah ya cika da ƙwalla ya saka Dad ya saurare shi "Ina jin ka " "Mu shiga ciki Dad." Tare suka shiga ciki Sulaiman dai bai bi su ba, mai yiwuwa za su yi wani sirri tsakanin uba da ɗa. Bayan sun zauna suna fuskantar juna ne Dad ya kalli Asadullah ya ce "Ina jin ka." Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce. "Dad na san kana zaton cewa ni na bar gida da ƙafuduna ko? To ba haka abin yake ba, a zahirin gaskiya ma sace ni aka yi bayan an gusar Mani da hankali. Dad a cikin ɗakin barcina aka shigo, kafin na juya na ga waye hakan bai samu ba, sai farkawa na yi na ganin a wani ɗaki an daure Mani hannu da baki. Da idan ba wanda yake na gida makusanci na ba wanda yake da zarra da zai iya shigo Mani har cikin ɗakin barcina . Hakan ya saka na kasa yarda da kowa. Wallahi na kwashe tsawon lokaci a cikin wannan halin. Ba wanda zan iya cewa shi ne ya yi Mani wannan aikin. Family Doctor ɗin mu shi ne yake zuwa ya yi mani allurai wandanda sauke gusar Mani da hankali Ba na iya gane komai sai dai a duk lokacin da nake cikin wannan halin sai na ji wasu muryoyi bayan na Doctor suna bani wani takarda akan na saka masu hannu. Ta yadda kamfanin zai zama mallakinsu. Sai sai dai duk da ba na cikin hayyacina Allah bai bani ikon cika masu burinsu ba. Tsawon watanni na ɗauka a haka kafin wata rana Allah ya kawo Jidderh. Ban san ya aka yi ta san ina wajen ba, sai dai kullum sai ta kawo Mani abinci a ɓoye." Nan ya cigaba da ba wa Dad labarin komai har zuwa ranar da ta kuɓutar da shi da da accident da suka samu har zuwa yau. Kuka Dad ke yi kuma ya tabbatar da Ɗan sa yana cikin makiya ne sai dai ba wanda ya san ko su waye. "Amma ya jikin ita Jidderh?" "Dad abun ya na bani tsoro an yi yawon asibitoci da ita nan da ƙasashen waje amma duk sakamakon ɗaya ne, wai ba wata matsala a cikin kanta." "Innalillahi wa'inna'ilahi raji'un." Dad ya ambata cike da damuwa, bayan ya numfasa ya ce. "Lokacin da take cikin hayyacinta ba ta taɓa sanar da kai unguwar su ko wani na ta ba.?" "A'a Dad tun bayan da ta je office kamfani na taimaka mata da kuɗaɗe kan matar yayanta ba ta da lafiya. Daga baya ta zo neman aiki na dauke ta. Bayan haka idan ba mun hadu a mansion ta zo aiki sai mu gaisa. Sai daga baya da ta fahimci halin da nake ciki ta taimaka ta fitar da ni." Ya karasa magana hawaye na bin fuskarsa. Dukkansu sun yi shiru ba wanda ya sake yin magana. "Yanzu ya ake ciki?" Dad ya katse shirun da suka yi ta hanyar yin maganar. "Yanzu mun yi magana da inspector Bashir Ibrahim akan an gano in da Sagir yake , kuma za su yi iyakar kokarin su wajen kama shi, wai yana garin Lagos ne, an gano cewar wata yarinyar yake son ya aura a can." "Okay yanzu yaushe za'a dawo da Jidderh?" .ina tunanin za su dawo zuwa wani satin." Shiru ya yi kafin ya ce. "Dad ina neman alfarma a wajenka?" "Wace irin alfarma kake nema?" "Ba na son kowa ya san cewa na bayyana ko an gano in da nake, har sai bayan an gano waɗanda suka aikata Mani wannan aiki." "In sha Allah ba wanda zai ji har da Mom ɗin ka kuwa." Daga nan ya yi masa sallama don yana da meeting da zai je. *Bayan sati ɗaya.* *America/New York City* Kayansa ya gama jerawa a cikin trolley bag ɗinsa ƙarama kasancewar ba kaya da yawa ya ɗiba ba, kayansa na can ma sun ishe shi. Fitowa ya yi. Don ba zai je tare da kowa ba ko James ba zai je da shi ba. Sallama ya masu tare da ihisani, inda Wasu daga ciki suka raka shi zuwa airport. A can ya hadu da Sury a airport ita ma za ta tafi Nigeria. A tare suka hau jirgi, ta ji daɗin hakan har cikin ranta, Kuma ta kudirri niyyar sai ta bi Hilal har Gidansu . Haka kuwa aka yi, sai da ya kira Faisal a waya akan cewa ya zo ya dauke shi. Faisal ya yi mamaki don bai sanar da kowa yau zai dawo ba, har da Papa kuwa . Yaga Sury tsaye a gefensa tana kallonsa, bai kula ta ba, sai da Fisal ya zo ta ga ya nufi motar ta bi bayansa. Faisal ya rungume shi cike da farin ciki yana masa Barka da zuwa. Bai yabo ba fallasa ya amsa masa. Yana shiga motar ya ga Sury ta shiga baya, su suna gaba, da mamaki suke kallonta. "Yaya wace ce ita? Bai bashi amsa ba ya kalli Sury ya ce "Nan ba US ba ne, kada ki yi kokarin kawo Mani shashanci a nan, ki fita kafin ranki ya ɓaci." Sanin idan ba ta kwantar da kai ba ne za ta samu matsala da Hilal ya saka ta kwantar da murya. "Don Allah ka taiamaka mani ba na da kowa a anan, kuma Dad ɗina ya ce sai gobe Direba zai zo ya ɗauke ni, ban sanar da zan dawo ba kuma ka san akwai nisa." "Za ki samu Fly ai." "Na fi son na tafi da motar ga yamma na yi." Zai yi magana Faisal ya ce . "Ka bar ta don Allah Yaya Gobe da safe sai ta tafi duk da ban san wani gari take ba." Godiya ta masa ya ja motar suka bar airport. "Ba na son kowa ya san ta zo har zuwa gobe da za ta tafi." Ba ta so hakan ba ta so kowa na gidan ya ganta saboda wani dalilin na ta. "Gakskiya ba zai yiwa ba ko da ka ce ta kofar baya na part ɗin ka za ka bi da ita ka san dai Mommy ta shigo dole za ta ganta. "Eh na sani, ka bi ta baya mu sauke ta a garden ta jira sai na fito zan shiga da ita a part ɗi na, bayan Mummy ta fita, na san tai dole ta zo part ɗina." "Amma Yaya me ya saka za ka sauke ta a part ɗin ka bayan ga..." Kallon da ya masa ne ya saka ya yi shiru suka cigaba da tafi har suka karasa. Kamar yadda ya bukata haka Faisal ya yi, ta baya ya ajiye motar, sannan Sury ta shiga garden ta zauna zaman jiran Hilal ba don ranta ya so ba. Daga haka suka shiga cikin gidan. Faisal na ihun kiran mutanen gidan daya bayan ɗaya. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA* Page5️⃣7️⃣ Daga haka suka shiga cikni gidan Faisal na ihun kiran mutanen gidan ɗaya bayan ɗaya. Sai da Hilal ya dakatar da shi ne sannan ya yi shiru, don ya san Faisal zai iya tara masa mutanen gidan. Ga ji kuwa baya son hayaniya. Ba wanda ya ji dawowarsa kasancewa kowa na part ɗin sa. Kuma Hilal ya hana Faisal ya masa gayyatar da ta yi niyya, shi ya sa bai sanar da kowa zuwansa ba ballantana su dame shi da hayaniya . Part ɗin sa ya nufa, sai ya tuna Faisal zai iya faɗa sanar wa Mummy zuwansa. Don haka ya dawo ya nufi part ɗin Mummy gudun kada ta zo da tarar da Sury a part ɗin sa anjima. "Assalamu alaikum warahmatullah" Ya yi sallamar ciki-ciki kamar yadda ya saba. Bakinsa kawai idan ka kalla ne za ka san ya yi sallama amma ba wai don ka ji sautin sallamar Sa ba shi kaɗai ya ji kayansa. Haɗa idanu suka yi da mahaifiyarsa, wacce kallo ɗaya ya yi mata ya gane har yanzu ba ta sauko ba akan zancen Ammar da Zahrah da ta yi masa a waya. Kuma dama wannan ne ƙarfin zuwa nasa. Ba ta san ya karaso gabanta ba sai da ta ji sautin muryarsa yana gaishe ta. Dubansa ta yana durkushe a gabanta. "Ina wuni Mummy." Bata amsa ba sai cewa ta yi . "Yanzu yau za ka dawo shi ne ko ka faɗa Mani a shirya maka tatrbo ba musamman ko? Ko don kasancewar ba ka cin girkin masu aiki ai sai ka kira." "Mummy kar ki damu kanki na san a part ɗin Dada na san za ta yi girki." Tsuke fuska ta yi kafin ya ce "Wato ni mahaifiyarka ban san za ka dawo ba amma ka iya kiran waɗan nan tsofaffin ka sanar da su ko ? Saboda matsayin su ya zarce nawa a wajenka ko?" "Mummy don Allah ki yi hakuri ki daina wannan zancen, su fa kakanni na ne su suka haifi Mahaifina ke kuma kika haife ni, matsayin kowa daban ne, a duniyar nan ba na da kamarki, ki daina hada kanki da kowa, fushimki masifa ne a gare ni, ki yi hakuri komai zai koma daidai." Ji ya yi kansa ya fara yi masa ciwo, don haka ya ce mata zai je ya yi wanka ya huta. Cikin sakin fuska da jin dadin kalamansa ta yi masa Allah huta gajiya. Part ɗin Umma ya je ya gaishe ta, daga nan ya je part ɗin Sunyi Laila ita ma ya gaishe ta. Part ɗin Dada ya nufa sai dai ya yi sallama a falon ya ji ba kowa. Sai ya juya ya haura stairs kafin ya dawo wajen Dada ya ci abinci. Yana shiga falon sai ƙamshi yake yi da alama yanzu aka gyara masa, ɗakin, ya san aikin Faisal ne. Yana gama wanke masa toilet ya shigo. Godiya ya yi masa sannan Faisal ya ce. "Yaya kar ka manta da ƴar mutane da ka ajiye a lambu." Yana gama fadar haka ya nufi kofar fita ya fice daga ɗakin. Yana fita Hilal ya dafe goshi, duk da a gajiye yake sai ya bi ta kofar baya dake part ɗin nasa. _Zahrah_ Tana cikin lambu tana ɗaukar tsuntsaye hoto, tana yi tana murmushi. Tana yi tana cin kayan marmari dake cikin lambu. Ta jima ta ja ɗaukar su a wajen har sai da ta gaji sannan ta yi tunanin fitowa daga lambun. Daga farkon shigowa lambun kuwa Sury ce zaune ta cika ta yi fam. Sai ga Hilal ya ƙaraso. Kamshin tutarensa ya sanar da ita karasowarsa. Zama ya yi a gefenta tana cewa "Ba na son kowa ya san da zuwanki, nan ba US ba ne family house din mu ne, ku nutsu a ɗaki zan je na kawo maki abinci. Ki tabbatar gobe da safe kin bar gidan nan." "To na ji ni dai ka kaini na huta na gaji." "Ta yi magana tana mikewa tsaye, sai kuma ta yi saurin dawowa ta zauna a saman cinyarsa. Ta kwantar da kai a ƙirjinsa. "Ke Meye haka kuma?" Na gaji ba na jin daɗi ga jikina ya yi zafi sosai. Da mamaki ya kai hannu wuyanta ya taɓa don tabbatar da abinda take faɗa. Zahrah da ta hangi tsutsuwar da take so ta hanyar fita garden ɗin sai ta saita Camera lokacin da take fitowa dan ta dauki tsuntsuwar, sai dai kash tsuntsuwar ta tashi ko da ta ɗauka ba tsunsuwar daidai za ta dauka ta tashi sama , a rashin sani sai ta dauki hoton Hilal wanda Sury ke zaune a saman cinyarsa, shi kuma yana taba wuyanta don tabbatar da zafin jikin da ta ce masa, wanda ɗora hannun sai ya yi kamar ya rungume ta ne, Daidai lokacin Zahrah ta ɗauke su hoto ba ta ma lura da suna wajen ba, Idanunta na kan tsuntsuwar da ta tashi sama da ba ta samu damar ɗaukar ta photon ba. Da sauri ta fita don ko za ta hango ta sam ba ta lura da su Hilal ba, amma shi ya ganta lokacin da take fita hannunta rike da wata ƙaramar Camera wacce Abbi ya siyo mata a Saudiyya. Ko da ta fita ba tsutsuwar Don haka ta koma don ta nuna wa su Dada . Jin jikin Sury ba zafi ya sa hila cewa "Ke tashi mun ko ranki ya ɓaci yanzu , Ni za ki rena wa hankali?" Ganin ba wasa a fuskarsa ya saka ta mike tsaye. Yana gaba tana binsa baya har suka shiga kofar part ɗin sa. Zabarah na shiga part ɗin Dada ba kowa. Sai ta nufi bedroom ɗin ta shiga da sallama. Dada da ta gama saka kaya kenan ta kalli Zahrah ta ce. "Ina kika shiga ne tun ɗazu ina nemanki." "Na je garden wajen abokaina ne." Dada ta zauna bakin gadon ta ce. "Fatan suna lafiya ko?" "Eh bari ki gan su." Ta mikawa Dada Camerar yayin da Dada ta shiga rana kallon hotunan da Zahrah ta ɗauka ɗaya bayan ɗaya . Zuciyarta ce ta tsaya cak dadai lokacin da ta ga photon Hilal ɗauke da wata mace a saman cinyarsa ya sakala hannu a wuyanta, duk wanda ya ga photon zai yi tuninin cewa rungeme ta ya yi . Kallon Zaharah ta yi kafin ta ce. "Yayanku Hilal ya dawo ne?" Shiru Zaheah ta yi kafin ta ce . ",Ban sani ba Dada, to ni Meye hadina da shi ne wai, wallahi gara ya yi zamansa a can US ɗin baƙin mugu idan ya dawo ta cigaba da zalintar mutane, ya zauna can har Mahadi ya bayyana." Dada hankalin ta baya kan Zahrah mikewa ta yi ta nufi hanyar fita, ganin haka ya saka Zahrah ta ce. "Ina za ki kai mani camera ne?" "Zan nuna wa Kakanku abokanku ne." Jin haka ya saka Zahrah ta yi shiru ta koma falon ta zauna. _Hilal_ Yana na komawa part ɗin sa tare da Sury ta dame shi yunwa take ji. Dan haka ya sauko daga stairs ɗin ya nufu kitchen ɗin don ya san ba za'a rasa ma'iakata a ciki ba, sai kuma ya fasa ya nufi part ɗin Dada don shi ma yunwa yake ji kuma baya cin abincin masu aiki. Don haka ya nufi part ɗin Dada. Zahrah na zaune a falo ta tura kofar ya yi sallama can ƙasan maƙoshinsa. Ba ta ji shi ba sai dai ƙamshin turarensa da ta ji ne ta haddasa mata faduwar gaba wanda ba ta san dalili ba. Juyawa ta yi suka yi ido biyu ya watsa mata harara, da sauri ta ɗauke idanunta daga kallonsa. Duk da ta san ba amsa mata Gaisuwa yake yi ba amma sau ta bude baki ta ce. "Yaa Hilal Barka da dawowa." Kamar bai ji ta ba dama ta san hakan za ta faru don haka ba ta damuwa da rashin amsa gausuwarta da bai taba yi ba. Ɗakin Dada ta shiga ya ga bata ciki a tunaninsa unguwa ta tafi, sam bai yi tunanin Papa na gidan ba, don baya zama gidan haka kawai. Kitchen ya shiga don neman abinci, ya san cewa da ace ya sanar wa Dada daowarsa da ta aika masa da abinci har part ɗin sa. Dada na shiga ɗakin Papa ta same shi yana shirin fita. Ganin yanayin da take ciki ne ya saka shi cewa "Lafiya kuwa?" "Ka zauna ka gani." Ba musu tsohon ya zauna yana kallon matar ta sa. Camerar ta mika masa ya karɓa yana duba wa. Wani abu ya ji ya tsaya masa a ƙahon zuciya, "Innalillahi wa'inna'ilahi raji'un." Shine kalmar da ya maimaita har sau uku a zuciyarsa. "Yaushe aka ɗauki wannan hoton, kuma wannan kamar Camerar Zaharah ko?" "Yau ne ta dauke su ba tare da ta sani ba ita ma." "Yaushe ya dawo daga US ɗin ?" "Ina wanka na ji shigowarsa amma sai na ɗauka kunnena ne ya jiyo mani ba daidai ba. ashe shi ɗin ne." Jikin Papa ne ya yi sanyi yanzu har an kai matakin da daya daga cikin jikokinsa zai kawo masa mace har cikin gidan nan, kuma duk wanda ya kalli hoton nan zai tabbatar da cewar sun saba mu'amalar banza ba wannan ne na farko ba, daga ganin yarinyar ƴar duniya ce . Ransa ya kai ƙololuwar ɓaci ya ce "Zan yi abinda nake ganin ya dace." Ya mika mata Camerar ya ce . Ya taso suka nufi falon a tare, Daidai lokacin da Hilal ya fito kitchen ɗin dauke da ture da food flask a kai sai plate 🍽️ spoon. Mamaki ne ya kama Zahrah ganin yadda ya dauko flask ɗin gabadaya. Ita da ta girka abincin ko ci ba ta yi ba ga shi yunwa take ji. Ga shi lokacin zuwa haddarta da take koyar wa ya yi ba lokacin da za ta sake wani grikb, dama Papa da Dada suka sun ci na su . "Yaa Hilal abincin duka zai maka yawa, kuma Ni ban ci ba don Allah bari na ɗebi kadan zan tafi islamiya yau Alhamis muna zuwa hadda." "Ke! Har kin yi tasirin idon da za ki tari gabana ki fada mani magana haka don rashin kunya, ba na ɗaukar iskanci." "Har yanzu ban ga iskancin da ake kira wa yarinyar nan ba, hasalima ana zaton wuta a makera ne abun mamaki sai aka same ta a masaƙa." Da mamaki ya juya yana kallon Dada dake maganar.Papa ne a bayanta fuskarsa a murtuƙe, kallo ɗaya za ka masa ka fahimci zallar ɓacin ran dake fuskarsa. Mamaki ne ya kama Hilal jin kalaman Dada don tun da yake yi wa yaran gidan nan magana ba ta taɓa cewa komai ba, amma yau ita ce da masa magana mai harshen damo. Tambyar zuciyarsa ya yi 'Ko dai yarinyar nan ta fada masu ta ganshi garden tare da Sury ne? Kai ba za ta fada ba ai da za ta fada da ta sanar da su lokacin da suka je Kaduna ta kama shi a ɗaki shi da Alexandra babu kaya a jikin Alexandra yana romancing ɗin ta da sauri Zahrah ta fito ta bar masu ɗakin. Kuma ta kama shi a nan gidan shi da Alexandra lokacin da Dada ta aike ta wajensa ta kai masa kwaɗon zogale, duk ba ta faɗa ba ta yi shiru ta tabbata ganinsa a garden da Sury ma ba za ta fada ba sai sai ta yi shiru. Don haka ya juya ransa a ɓace da kalaman Dada. Papa ya zauna yana kallon Zahrah ya ce. "Ki yi hakuri ki nemi wani abun da za ki ci, kafin ki makara. Ko Amminki yau girkin gidan suka ci." "Eh Papa dama idan Abbi na gida ne take shiga ta girka masa ba tare da ta bari ya ci abincin masu aiki ba." "To ga lokacin tafiyarki islamiyya ya yi." "Ba damuwa akwai sauran cake da na yi juya bari na ci kawai na tafi." Murmushi Papa ya yi ya ce. "Amminki da Dada sun koya maki rashin cin abincin gidan ko? Ai yanzu ƴan uwanki suke yi kuka na tabbatar za ki samu abinci sama da kala uku ." "A'a Papa ba zan ci ba." Ta yi maganar tana nufar kitchen. Hilal na komawa ya kai wa Sury abinci, ya ce ta dauki abun sha a fridge. Ta buɗe ta ga tuwon shinkafa ne leda uku da miyar egusi da ganyen Ogun ya ji naman rago. Sai kuma farfesun ɗanyen kifi. Tura baki ta yi tana cewa . "Sojana ba na son tuwo." "Sai ki ci farfesun kifin." "Ba na cin kifi, ko za mu fita zuwa restaurant." Wani kallo ya mata, wanda ya sa ba ta sake masa magana ba. Bedroom ya shiga ya rage kayan jikinsa, ya shiga bathroom don yin wanka. Papa kuwa sai safa da marwa yake yi a Falo, abinda ya ga Hilal na aikatawa ya tsaya masa a rai. Kallon Dada ya yi tare da cewa. "Ki kira mani Laila a waya." Ba musu ta kira ta bayan ta daga ta sanar da ita kiran da mahaifinta ke mata. Dadai lokacin da Aunty Laila ke shigowa Zahrah ta shirya za ta je islamiyya. "Aunty Laila ina wuni?" Sai da ta watsa mata harara a fakaice kafin ta amsa da "Lafiya ." Zahrah ta yi wa su Dada sallama ta fita sanye da dogon hijabi da niƙab. Aunty Laila kanta ta tsorata da ganin yanayin fuskar mahainta. Ki kira Mani mutanen gidan nan manya amma ban da yaran. Iyayen nake buƙata maza da mata. Wadanda ba sa gidan ma a kira su a waya su dawo gidan." Ya yi magana cikin bayar da umarni ba wasa. A fuskarsa ballantana ta yi masa wata tambayar. Jiki ba ƙwari ya ta bar part ɗin ta tafi don aiwatar da umarnin Papa. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA NE* Page5️⃣8️⃣ Ya yi maganar cikin bayar da umarni ba wasa a fuskarsa ballantana ta yi masa wata tambayar. Jiki ba ƙari ta bar part ɗin ta tafi dan aiwatar umarnin Papa . _Dad_ Ko da ya koma gida a daren kasa rintsawa ya yi, saboda halin da ɗansa Asadullah ya tsinci kansa a ciki, shin a cikin mansion ɗin nan waye zai iya farmakan Asadullah? Da ba don Allah ya yi yana sa sauran kwana a duniya ba da ta wannan hanyar ma kaɗai zai iya rasa rayuwarsa. Waye ko suke ƙoƙarin ganin bayan sa, ta wace hanya zai iya taimaka masa don ganin ya tseratar da rayuwarsa. Ga shi ba wata hanyar da za su gane su waye su a cikin sauki. Shi family Doctor na su da ya za su iya gane ko su waye an kashe shi don ɓatar da hujja. Nan ya dinga tufka da warwara amma ba wata hanya da ya hango wanda zai kai su magance matsalolin da suke ciki . Kasancewar ranar Aunty ce da girki ya saka ita ce tare da shi a ɗakinsa. Dare ya tsaka sosai gari ya yi tsit. Tsawon kokaci Dad ya ɗauka yan ta aikin tunini har Aunty ta ta juya akan gado cikin barci ta ji alamar Dad baya nan, sake lalubawa ta yi na.n ma ba ta ji alamar sa ba. Sai ta bude idanunta tana kallonsa a tsaye ya Lula can wata duniyar na tunini "Alhaji lafiya kuwa?" "Lafiya lau." Ya bata amsa a takaice. "To me zai saka ka kasa barci kana tunini a cikin wannan tsohon dare?" "Ba komai." Ƙarshe ya yanke shawar yin sallar dare ya kai kukansa ga Allah. Don haka ya nufi bathroom ya ɗauro alwala, sallaya ya shimfida ya tayar da sallar nafilfili . Ganin haka ya sa Aunty ta koma barci tun da ba fada mata zai yi ba _Asadullah,_ Shi ma ɓangarensa haka abun yake, tun da ya dawo gidan nan bai yi barci mai tsawo ba, taɓa dare yake yi yana kai kukansa ga Allah. Musamman yanzu da nakiya suka taso shi a gaba. Tsaye yake akan sallaya, farar jallabiya ce a jikinsa yana tsayuwar dare. Tun karfe biyun dare da ya farka sai karfe huɗun asuba ya idar da sallar . Addu'o'i ya yi sosai akan makiyansa da addu'a Allah ya ba da Jidderh lafiya. Don Doctor Isma'il ya sanar da shi dawawarsu nan da kwanaki biyu, zuwa jibi kenan in sha Allah. _Aunty Laila_ Part ɗin Daddy ta fara nufa, ta tarar da Mummy a falo ita kaɗai, ganin Aunty Laila ya saka ta ce . "Kin shigo?" "Eh.' "Yanzu nake shirin zuwa na ga ɗan na ki da ya dawo." Aunty Laila ta ce "Duk ba wannan ba, da alama gidan ba lafiya . Don Papa ya ce na tara masa kowa na gidan nan. Ban da yara amma yana son ganin iyaye maza da mata." Gaban Mummy haka kawai ta ji yana faduwa . "Daddyn yara da baya nan fa?" "Ya ce wadanda ba sa nan a kira su a waya Cikin sanyin jiki ta dauki wayart ta lalubo lambar Daddy, bayan ya daga ta sanar da shi sakon mahaifinsa. Hankalinsa ba ya tashi don ya san ba dai laflya Papa zai kira su dawo gida b. Cewa ya yi ga shi nan dawowa. Daga nan Sunyi Laila ta nufi ɓangaren Umma nan ma ta sanar da ita yadda ta sanarwar Mummy. Ita ma waya x ɗauka t kira Abba ta sanar shi kiran da Mahaifinsa ke masu. Sunyi Laila ta fito kamar za ta nufi part ɗin Abbi sau ta yi tsuki ta koma part ɗin Papa ta sanar da shi yadda suka yi . "Yayanki Salis da?" "Ban ke part ɗin ba.' Cikin bayar da umarni ya ce. "Ki je ku sanar da su kafin na hucr haushi na akanki." Ba ta da wani zaɓi dole ta wuce Part ɗin Abbi. Tura kofar ta yi rai a ɓaci babu ko sallama ta shiga falon. Ƙamshi ne ya ziyarce ta mai daɗi, tabe baki ta yi tana karawa Falon kallo. Wanda ko ba'a fada ba an san yana shan gyara, don alma ya nuna mamallakin falon akwai tsananin tsafta da son ƙamshi. Nan Zahara ta yi gado. Ƙarar buga kofar ne ya saka Ummi fitowa ta ga Aunty Laila. Mamaki ya kama ta don ganin Aunt Laila a part ɗin. Shanye ta ce "Barka da shigowa bisimillah ki zauna." Tsuki ta yi kafin ta ce "Ki kira mijinki duk abinda yake yi ya ajiye ku zo tare a bangaren Papa." Tana gama fadar haka ta juya su ta ta fice Cikin sanyi. jiki Ummi ta dauka oh wayarta ta kira Abbi ta sanar da ji komai . Shi ma ɓangarensa jikinsa ya bashi ba lafiya ba, tattara takardun da zai dawo gidan da su. _Hilal_ Yana zaune a dinning table Yana cin abinci tuwon shinkafar ne, Sury da ta ga alamar ba zai kia ta restaurant ba sai ta dole ta zauna suna cin tuwon a tare. Sai dai shi baya cikin walwala musamman idan ya tuna kallon da Papa ke maza wanda bai taba yi masa irin sa ba . Falon ya yi shiru kamar ba mutane a ciki, Papa, Dada, suna zaune a ka kujerar yayin Mummy, Daddy, Abba, Umma Abbi, Ummi suke zaune kasa kowa yana jiran jin dalilin kiran. Camera da Zahrah ta ɗauke Hilal da Sury ba tare da ta san ta yi ba ya mikawa Daddy da Mummy da suke zaune a tare. Karba Daddy ya yi ya duba Mummy ta matso dab da shi tana dubawa. Gabansu ne ya fadi a tare lokacin da suka ga babban ɗan su dauke da wata mace a cinyarsa ya rungume ta. Salati suka hau ya yayin da Abba ya karba suka duba a tare da Umma, nan su ka suka yi mugun gani tare da yin salati. "Salis karba ka gani." Papa ya yi maganar yana kallon Abbi. Cikin sanyi. Jiki Abbi ya karba ya matsa kusa da Ummi inda suka yi karo da photon,. "Innalillahi wa'inna'ilahi raji'un." Shi ne kalmar da Abbi da Ummi suka furta a tatet. Hannun Sunyi Laila na rawa ta amsa tana dubawa. "Na shiga uku na lalace, yaushe Hial ya fara mu'amala da matan banza?" "Ba wanda zai baki amsar wannan tambyar sai shi. Wannan daowar da ya yi tare da mace ya dawo wato ita wannan yarinyar." Mummy ce ta yi saurin cewa. "A'a Papa wannan ba halinsa ba ne, ba zai kawo mace har cikin gidan nan ba ." Murmushin takiaci Papa ya yi kafin ya ce. "Wannan hoton yau Zahrah ta ɗauke shi a garden, ita kanta ba ta san cewa ta ɗauke su ba, ta je tana ɗaukar hoto a can kamar yadda take yi shi ne bayan ta gama Allah ya yi asirinsa zai tonu yau din nan. Idan kun fahimta a hoton a karkace ta ɗauke shi ba tare da ta sani ba ne . Amma tun x kin ce ɗanki ba zai kawo mace ba zan tabbatar." Kallon Aunty Laila ya yi kafin ya ce. "Laila tashi ki je ki duba Mani ɓangaren sa idan shi da mace ce ki tabbatar ta bar gidan nan, sannan shi kuma ina bukatar ganinsa yanzu ." Sunyi Laila ta mike da sauri tana cewa. "Lallai za ta ci ubanta yau kuwa yar iska karuwa." "Kada ki sake ki taba lafiyar jikinta, ki kore ta na ce ta bar gidan ban da duka na san halin ki." "To Papa" Ta fada tana ficewa da sauri . Haka ta haura stairs ɗin da sauri -sauri, knocking ta yi jin kofar a rufe. Daidai lokacin da suka gama cin abincin. "Tashi ki shiga bedroom." Da sauri Suryta mike ta shiga ɗakunan yayin da ya bude ƙofar. Don ya san ko waye ba zai shiga masa bedroom shi yana fakon ba Ganin Aunty Laila ya ce. "Aunty lafiya ko?" Bata saurare shi ba ta kutsa kai ciki tana huci, kafin ya yi wani yunkurin har ta shiga bedroom. Nan ta yi ido biyu da Sury dake kwance kan gadon. Afusace ta nufe ta wanda tuni Sury ta tsorata ta yi toilet za ta rufe. Zo ki tattara kayanki ki bar gidan nan, idan kika shiga kika rufe sai na saka an yi maki dukan mutuwa. Jiki na rawa ta zo ta dauki trolling bag ɗin ta da handbag har tana hada hanya ta fice. Ita a tununta mahaifiyar Hilal ce. Ta kofar baya ta fice kafin Aunti Laila ta juya tana kallon Hilal da ya haɗe fuksa. "Ka je yanzu bangaren Papa yana son ganinka." Sai da gabansa ya fadi amma ya dake ya riga ta fita yana gaba tana baya. Da sallama ya shiga falon, amma ganin dukkan iyayensu a falon ba da yaran gidan ba sai shi kuma ga abinda Sunyi Laila ta aikata ya saka shi shiga tashin hankali, sai dai kasancewarsa yana da jarumta ya saka ba wanda zai kalle shi ya gane tashin hankali ga yake ciki. A hankali ta taku ya zauna bayan su Abbi kasancewar sune karshe. "Hilal" Papa ya kira sunansa, ɗago kai ya yi ya kalli Papa wanda idanunsa suka canza launi zuwa ja, kafin ya ɗauke kai ya ce. "Na'am." "Ashe kai mutumin banza ne ban sani ba, Haba Hilal ka yi aure mana idan kana bukatar mace Meye amfanin aikata fasikanci ." "Ban taɓa aikata fasiƙanci ba, kuma ba zan aikata ba in sha Allah." Kowa dake falon sai da ya kalle shi jin abinda ya ce. Papa ya kalli Abbi ya ce. "Salis ka bashi Camerar nan ya gani." Abbi ya mika masa ya karɓa yana dubawa . Ganinsa ya yi dauke da Sury akan cinyarsa.wanda idan ba shi ba ba Wada zai ce ba rumgumar ta ya yi ba. 'Lallai sai na illata yarinyar nan,, wato da na ganta a garden wato hoton mu ta ɗauka, lallai ta tafka babban kuskure don sai na illata ta.' "Za ka iya rantse Mani cewa wannan ne karo na farko da ka kawo mace a gidan nan?" Shiru ya yi yana tuna Zahrah ta san cewa ya kawo Alexandra tabbas ita ta fada masa ga kuma hoto ta ɗauka. Bai gama tunanin ba ya ji Papa na cewa. "Yau Alhamis gobe juma'a zan zartar da hukuncin da na ga ya dace kuka zai kawo daidaito a cikin zuri'a" Yana gama fadar haka ya mike ya nufi part ɗin sa kafin ya shiga ya ce. "Gobe kowa ya shirya karbar hukuncin da zan yanke ko ya yi maku dadi ko kada ya yi maku biyayya dole ne ga umarnina. Kowa ya tashi ya tafi na sallame ku." A fusace Hilal ya bar part ɗin, burinsa ya yi ido biyu da Zahrah, yadda ta saka ya shiga cikin wannan takaicin kowa ya shiga damuwa musamman kakanninsu suka ji haushinsa sai ya tabbatar ta ji a jikinta. Cikin sanyin jiki Daddy da Mummy suka mike Mummy na cewa. "Allah ya wadaranki ki Zahrah." Dada ta yi saurin cewa . "Akan me za ki za ki yi kokarin aibata ta, ai godiya ya kamata ki yi mata a dalilin ta aka gano banzar halin da yaron nan yake yi a ɓoye yanzu za'ayi wa tufkar hanci." Rai s ɓace Mummy ke shirin sake yin magana Daddy ta daga mata hannu ta yi shiru ta fice rai a ɓace, nan kowa ya watse aka bar Dada ita kaɗai a falon. Ammin Zahrah ta shiga damuwa sosai ba kaɗan ba, da suka shiga cikin falonsu Ammi ta kalli Abbi ta ce. "Zahrah ta ɓallo mana ruwa." Ta yi maganar cike da jimami.' "Ki kwantar da hankalinki ba wani ruwa da ta ɓallo mana, a dalilin haka kowa zai san abun da yake aikatawa a dauki mataki akansa." "To yanzu wane irin mataki Papa zai ɗauka?" "Allah masani, sai dai goben mu ji hukuncin da zai ɗauka. Tabbas ban taɓa ganin Papa cikin irin wannan ɓacin rai haka ba, kuma fa alama hukuncin na san ba zai yi wa kowa dad'i ba." *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA* Page5️⃣9️⃣ Allah masani sai dai goben mu ji hukuncin da zai ɗauka. Tabbas ban taɓa ganin Papa cikin irin wannan ɓacin rai haka ba, kuna da alama hukuncin na san ba zai yi wa kowa dad'i ba." Jingina lamarin Ummi ta yi kafin ta ce. "Tabbas da alamar haka." _Zahrah_ Horn ta yi a bakin gate yayin da security ya bude mata ƙofar ta shigo da motarta ciki . Hilal dake tsaye a harabar gidan ya hangi shigowarra. Dama ita yake jira ya hadu da ita. Kai tsaye ya nufi parking space ɗin, tana gama parking ta turo murfin motar za ta fito. Tana saka ƙafa ɗaya a waje ta ganshi tsaye rike da murfin motar fuskarsa a murtuƙe. Ɗaga niƙab dake fuskarta ta yi don ya samu damar ganinta yadda ya dace, ita a tunaninta bai gane ta ba ne tun da ko magana ba ta haɗa su, Gaisuwa ma idan ta masa baya amsawa. Hakan ya saka ta yi tunanin bai gane ta ba ne tun da ya zo wajen motarta ya tsaya. Sai dai tana cire niƙab ɗin fuskarta ta bayyana ya shaƙo wuyan hijabinta ya murɗe. Nan take hijabinta ya shake mata wuya ta fara fafutuka da rayuwarta, Idanunta sun firfito waje, sai da ya ga kamar za ta dauke numfashi sannan ya sake ta ta fadi ƙasa yaraf. Kin yi kuskure na shiga gonata, har kin yi tasirin idanun da za ki ɗauki photo na ki kai wa Papa?" Ɗago ta ya yi ta mike tsaye tagwayen maruka biyu ya sauke mata a fuska, kafin ya yi jira da ita ta fadi a wajen ta ƙoje sai ga jini ya fara zuba daga hannunta. Zare belt ya yi daga jikin wandonsa yana cewa . "Ke ga munafuka ko? Mai kai rahoto wallahi wata rana ko an ce ki shiga harkata ba za ki shiga ciki ba." Belt ɗin ya rike ya dinga dukanta da shi, ihun azaba da take yi ne ya saka ma'aikatan gidan ƙsrasowa wajen don ganin meke faruwa. Carko-carko suka yi suna kallon yadda yake dukan Zahrah kamar Allah ne ya aiko shi. Tausayin ta cika su, don sun san cewa Zahrah ba ta da hatsaniya ko wani abu da zai saka ya dake ta, hasalima tafi sauran yaran gidan nutsuwa, hankali, da sanin ya kamata. Take jini duk ya ɓata farin hijabin dake jikinta. Ganin da suka yi ba su da zarrar da za su tari gabanshi ne ya saka ɗaya daga cikin direban gidan ya ruga don kiran wani daga cikin gidan. Zuwa lokacin Zahrah ko motsi ba ta yi jikinta duk ya farfashe da duka ta daina motsi kamar matacciya, sai da ya ga ta daina motsi sannan ya bar ta nan kwance, motarsa ya shiga ya fige ta, da sauri maigadi ya wangale masa gate saboda tsorata da yanayinsa. Ya bar gidan a guje. A babban falon gidan ya yi sallama sai dai ba kowa a falon, don haka ya karasa part ɗin Dada ya ya yi sallama . Dada ta amsa tare da bashi izinin shigowa. "Dada ku kawo ɗauki soja zai kashe Zahrah." Salati Dada ta saka tana ƙwalawa Papa kira, ba shiri ya fito yana tambayar me ya faru. "Wai Hilal ne zai lashe Zahrah." "Suna ina?" Papa ya tambaye direban. "Suna parking space don daowarta kenan." Da sauri suka fita don zuwa parking space, duk da kasancewar su tsofaffi ne amma suna da ƙwarin jiki. Suna ƙarasowa parking space daidai lokacin motar Mahmud ta karaso. Ganin suna cikin tashin hankali ya saka ya fito daga cikin motar da sauri, ya bude baki da niyyar ya tamabaye su abun da ya faru sai ya yi tozali da Zahrah dake kwance ba ta motsi. "Innalillahi wa'inna'ilahi raji'un." Shi ne kalmar da ya furta ya karasa wajen da take kwance yana cewa. "Accident ta yi ne?" Ba wanda ya iya magana don Dada da Papa ma sun kiɗime da ganin halin da suka gan ta a ciki. Mahmud ya durkusa ya ɗauke ta yana cewa. "A kai ta asibiti mana." "A'a ka kai ta ɗakinta dake ɓangarena zan kira Doctor ya zo da kayan aiki, zai yi mata duk abinda ya dace." Daga haka ya yi gaba Mahmud ya bi bayansa suka koma cikin gida. Ɗakinta dake bangaren Dada ya Mahmud ya kai ta. Akan gadonta ya shimfidar da ita. Har lokacin ba ta motsi. Daidai nan Papa ya kira Doctor a waya, bayani ya yi masa ya ce ya zo da kayan aiki gida. Nan Doctor ya ce masa ga shi nan zuwa. Mahmud ya kalli Papa cikin damuwa ya ce. "Me ya same ta haka ne?" "Wai Hilal ne ya yi mata duka ." Zaro idanu Mahmud ya yi yana cewa "Wane irin duka ne haka kashe ta ya yi niyyar yi ko me?" Fita daga dakin ya yi da sauri zuciyarsa na masa zafi, ganin ƙanwar ta sa a cikin wannan halin ba karamin tashin hankali ya saka shi ba, duk da cewar ba ƙaramin abu ba ne idan aka ce Hilal ya yi wa mutum irin dukan nan, saboda yana da zafi, amma ya tabbata Zahrah ba za ta aikata masa laifin da zai yi mata irin wannan dukar ba, Gara kowa a gidan nan idan ya dake su amma ban da Zahrah. Ba za ta yi masa laifin da zai mata haka ba. Yana shiga part ɗin ya dinga ƙwalawa Abbi Kalifa, da kuma Ammi. "Abbi Ammi." Ya fada cikin daga murya. Ba shiri Abbi da Ammi suka fito daga cikin falon, don su san wannan kiran ba na laflya ba ne, musamman jin Muryar da sun san ba komai yake magana a kai ba saɓanin Sadik. "Lafiya Mahmud.?" "Zahrah ce Hilal ya yi wa mugun duka ko motsi ta kasa yi." "Innalillahi wa'inna'ilahi raji'un." Ummi ta fada cikin tashin hankali. Gabaɗaya suka fita zuwa part ɗin Dada har dakin Zahrah suka shiga . In da suka tarar da Papa da Dada akanta. Shigowarsu ba jimawa sai ga ga Daddy da Mummy sakamakon kiran da Papa ya yi masu. Suna shigowa suka zuba idanu akan Zahrah, sai Ga Umma da Abba sai Aunty Laila a ƙarshe. Kowa ya kasa yin magana suna ta tambayar kansu abinda ya dame ta. Gyaran murya Papa ya yi tare da kallon Daddy ya ce . "Kun ga abinda yaron nan Hilal ya aikata wa yarinyar nan ko? Akan abu da ba t d masaniya akai, lallai sai ya biya bashin abinda ya aikata, sai ya gyara abinda ya ɓata." Kowa ya kasa magana Ummin Zahrah sai zubar da ƙwallar tausayin ƴarta take yi. Doctor ne ya shigo cikin ɗakin bakinsa ɗauke da sallama. Gabadaya suka amsa masa ya shigo hannunsa dauke da kakar kayan aikinsa. Gaisawa ya yi tare da suka gaisa sannan Papa ta ce sun fita su ba Doctor wuri ya yi aikinsa." Gabaɗaya suka yi daga dakin Ummi ta nufi part ɗin su da sassarfa ƙwalla na ciko mata idanu. Ganin haka Abbi da Mahmud suka bi bayanta. Tana shiga ciki ta tarar da Sadik wanda dawowarsa kenan ya ga ba kowa a part ɗin. Cikin tashin hankali ya nufi mahaifiyarsa yana rike hannunta ya ce "Subhanallah! Ummina ya aka yi ko mutuwa ce ka yi ban sani ba." Kasa magana ta yi sai kuka , Mahmud ya rike hannunta yana cewa "Dan Allah ku yi hakuri Ummi ba cewa aka yi ba za ta tashi ba, in sha Allah yanzu za ta farfaɗo tun da Doctor ya zo ," Sai a lokacin hankalin Sadik y je ga Zahrah yana cewa. "Ina Zahrah ne ya same ta, ba dai ciwonta ne ya tashi ba ko?". Haka y jera masu tambayoyi, yana kallonsu cikin tashin hankali. Mahmud ne y yi karfin halin cewa. "Yaa Hilal ne ya yi wa Zahrah dukan mutuwa ga ta can ɓangaren Dada ko motsi ta kasa yi." "What's!" Kai Mahmud ya jinjina masa alamar tabbatar da cewa maganarsa haka take . Ciki. Fusata Sadik ya fara magana. "Wannan wani irin cin zali ne, na tabbatar da cewa Zahrah ba za ta shiga sabgarsa ba, na ji shaidar cewa Zahrah ko mu fa muke uwa ɗaya uba ɗaya ba za ta aikata mana abun da za mu dake ta ba, ballantana shi da yaran gidan ne tsoronsa." Nisawa ya yi kafin ya ce . "Yanzu wane mataki akan ɗauka akan abinda ya yi wa Zahra.?" "Kai ma ka san ba wani matakin da za'a dauka akansa tun da ya zaba hukunta yaran gidan sai dai a ce wannan karon ya uku tsauri da yawa." Da mamaki Sadik ke cewa . "Ai ko wannan bai dace a yake shi ba, don na ga alamar gabadaya gidan nan shakkar sa ake yi, ba mai iya dakatar da shi . Zan same shi na fada masa gaskiya duk abinda zai faru ya faru." Yana gama fadar haka ya ce. "Ina za ka je?" "Zan je na samu Hilal ne sai na fada masa duk maganar ta zo bakina, tunda anan gidan ba mai iya magana , ka duba yadda ya saka Mahaifiyar mu kuka ba zan ƙyale ahi ba. Sai dai ya kashe ni." 'idan ka fita a nan sai ranka ya ɓaci " Cewar Ummi tana goge hawayen fuskarta, kafin ta cigaba da cewa "Na tabbatar da cewa Papa da Dada ba za su bar shi ba har shi ba." Nan da daina kuka sabida sanin zuciyar zuciyar Sadik , kuma ba su fada masu komai abinda ya saka ya dake Zahrah. Sai da Ummi ta saka wa ta ya Zahrah na warkerwa zata kwshe yaranta su bar gidan ne ta gaji. _Hilal_ Bayan ya bar gidan kai tsaye sabon gidansa ya nufa, zuciyarsa a cunkushe yake, abinda Zahrah ta yi masa ya kunyata yau, tun da yake a rayuwarsa bai taɓa jin kunya irin na yau ba, sannan Papa yana cewa zai yanke hukunci akan wannan al'amari to wane irin hukunci yake shirin yanke wa akan sa oho. Ummi duk juriya da kawaici yau sai ta kasa hakura, don haka ta koma part ɗin Dada dan ta dubo halin da Autarta take ciki. Kamar wacce aka tsikara ta nufi kofar fita, Abbi dake cikin damuwa shi ma ya kalle ta ya ce. "Ina zuwa kuma yanzu?" "Am zan je na duba ko ta farka ne." Jinjina mata kai kawai ya yi, ta nufi hanyar fitowa, a babban falon ta ji muryar su Umma da Aunty Laila sai Mummy suna tattaunawa. Aunty Laila na cewa. "Duk da ban ji dadin abinda Hilal yake aikata wa ba, amma na ji dadin dukan mutuwar da ya yi wa shegiyar yarinyar nan." Umma ta daura da cewa "Dama ai sakamakon abinda ya kamata ayi mata kenan." "Ba ku kai ni tsanar yarinyar nan ba wallahi." Ran Ummi ya ɓaci da jin yadda suke aibata mata yarinya suna zaginta akan abun da ba laifinta ko da sanin ta ne ta aikata ba. Cikin ɓaci rai ta ce. "Don Allah me yarinyar nan ta tsare maku a duniyar nan ne, Meye laifinta akan abinda ya faru? Ita kanta ba da saniya ne ta aikata wannan abun na daukar photo ba. Ga ɗanku nan da ya kamata ku mayar da hankali wajen bincikar lamuransa da mu'amalarsa da mutane don ku gane me yake aikata wa ba, shi ne Idanun ku ya rufe ba ku ga laifinsa ba sai na Zahrah ko?" Murmushin takiaci ta yi tare da cewa. "Ba yadda za ku yi da mu sai dai cikin..." Abbi ya kira sunanta da ƙarfi wanda hakan ya saka ta kasa karasa maganar da take da niyyar yi. Duk abinda suke yi ko suke cewa akan ta da yaranta ba ta taɓa cewa komai ba sai yau , yau din ma don ranta a nace yake ne, tana ƙoƙarin ganin ta bi ra'ayin Abbi da ya hana ta tanka masu a kan duka abinda za su ce akan ta da yaranta . Don haka ta yi shiru ta nufi part ɗin Dada yayin da shi kuma ya bi bayanta. Ko da suka shiga ɗakin Zahrah sun tarar tana barci, an yi mata ƙarin ruwa, Dada na zaune a gefenta cikin damuwa . Kallonsu ta yi ba tare da ta iya cewa komai ba, ta san suna hakuri da zaman gidan nan, da ba don Papa ba da tuni sun bar gidan nan, don sau tari Abbi na yunkurin tashi daga gidan Papa na hana shi. "Kada ku damu ta farfaɗo za ta samu lafiya in sha Allah." *Washegari* Yau ne ta kama ranar juma'a, kuma rana irin ta yau jama'ar gidan Alhaji Muhammad Tafarki wajibi ne su ci a abinci a tare, ko Dada da Papa da sukan yi na su a part to ranar juma'a gabadaya suke cin abincin a tare. Kamar kullum yau ma sun hadu a babban teburin cin abincin dake dinning area. Papa, Dada, Daddy, Mummy, Abba, Umma, Abbi Ummi, da kuma Aunty Laila duk sun haɗu. Haka jikokin gidan ma duk sun haɗu sai sai ban da mutane biyu. Wato Hilal da Zahrah wacce ke kwance taba barci sakamakon rashin lafiyar dukan da Hilal ya yi mata. Faisal, Mansur, Mahmud, Sadik sun hallara. Nabeela, Kausar, Nadiya, Maryam duk suna nan. Masu aikin na tsaye in da suke zubawa kowa abinda ransa ke so. Papa ya kalli Faisal ya ce. "Je ka kira mani Babban Yayanku." Faisal ya tashi ya nufi stairs ɗin, ɗakin Hilal ya shiga, kasancewar kofar ɗakin a buɗe yake . Ganin baya falo ya saka ya nufi bedroom ɗin sa. Lokacin ya fito daga wanka yana sanye da bathrobe a jikinsa. "Assalamu alaikum warahmatullah" Muryar Faisal ya ji tana sallama. Ciki-ciki ya amsa masa sallamar iya ƙasan maƙoshinsa wanda shi wanda ya yi Sallamar bai ji ba. ' "Barka da safiya Babban Yaya." Bai amsa masa ba ta fara ƙoƙarin shafa man shafawarsa a jikinsa bayan ta tsane ruwan dake jikinsa da kansa. Har lokacin fuskarsa a murtuƙe take tamau, don ko barcin kirki bai yi ba, karfe dayan dare ya dawo gidan. Faisal ya ga ko gaisuwarsa bai amsa ba ya share shi fuska a murtuƙe ya ce. "Allah ya huci ran maza gu..." Ɗaga masa hannu ya yi alamar dakatarwa, sannan ya nuna masa kofar fita. Murmushi Faisal ya yi kafin ya ce "Zan fita, dama Papa ne ya ce na kira ka." Yana fada masa haka ya fice. Shi kuma ya cigaba da ƙoƙarin shafa man shafawarsa da yake yi. Ko da Faisal ya koma a dinning area ya sanar da Papa cewar yana zuwa . Jingina kai kawai Papa ya yi yana shan ruwan shayin dake gabansa. Bayan kamar mintuna goma sannan Hilal ya sauko zuwa downstairs Ƙamshin turarensa na Armani Georgia hade da Valentino ke tashi a jikinsa, ƙamshi ne ya fara yi masu sallama, wanda ko bai fesa turaren ba ƙamshin na nan a jikinsa. Ciki-ciki y yi sallama wanda ba wanda ya ji shi, ƙarasowa ya yi kan kujerar dake gabansa ya ja ya zauna suna fuskantar juna da Papa. Sai dai bai kalle Papa ba duk wajen ba wanda ya kalla, bude baki ya yi ya ce "Morning." Daga nan bai sake magana ba ya dauki wayarsa ta hau danne-danne. Ƙannensa suka hau gaishe shi da ina kwana ba wanda ya kalla a cikinsu ballantana a saka ran zai amsa wa ko mutum guda ne. Wato saboda yana fushi ne ba zai yi wa kowa magana ba, ya masu gaisawar jam'i wai Morning. Kwafa Papa ya yi don har yanzu shi ma ransa a ɓaci yake da abinda ya faru. Don haka dama ya gama shan shayi kawai ya iya sha Har Papa zai bar dinning area ɗin ya juyo ya kalle su ya ce. "Wannan sallar juma'a da za'ayi yau ɗin nan ba na bukatar a ce kowa ya tafi da motarsa yadda kuke yi ku shirya akan lokaci kuma ba wai daga wajan aiki ko kasuwa za ku tafi ba, ku tabbatar kafin lokacin sallar ta yi kun dawo gidan an tafi tare, ba na bukatar wani ya kawo Mani wani uzuri." Yana gama fadar haka ya juya ya cigaba da tafiya zuwa part ɗin sa. *Maman Ihsan ce* 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page6️⃣0️⃣ Yana gama fadar haka ya cigaba da tafiya zuwa part ɗin sa. *LAGOS* Wata bakar mota ce ta yi bakin daidai ƙofar wani madaidaicin gida. Fitowa mamallakin motar ya yi sanye da rigar mai hula sai bakin Glass da ya sanya wa fuskarsa hular ta rufe kusan rabin fuskarsa. Kasancewar safiya ne ba yawan jama'a dake kai kawo a unguwar. Wayarsa ƙarama ya fito da shi daga aljihun wandonsa. Wata lamba ya dannawa kira, bayan an daga kiran wayar ne ya ce. "Ki fito da sauri ina son zan bar garin nan yau ne?" Yana fadar haka ya katse kiran wayar. Bayan kamar mintuna uku sai ga wata budurwa ta fiti daga cikin gidan. Sanye da riga da siket na atamfa, sai mayafin da ta yafa a kanta madadin Ɗankwali. Yamutse fuska take yi Aalamar daga barci ta tashi . "Assalamu alaikum." Ta yi masa sallama ya amsa da. "Wa'alaiki Salam " "Sagir wai wannan sammakon na tafiyar ne?" "Eh ina sauri ne." "Wai me ya saka kullum cikin sauri kake ne, sai ka dinga yin abu. Kamar mara gaskiya wani lokacin." Kallonta ya yi kafin ya ce. "Sadiya na yi maki kama da mai laifi ne?" "A'a ba haka nake nufi ba, na ga dai kullum idan ka zo ƙasar nan sai ka yi ta ɗari-dari, ba ka sakin jiki sosai, da zaran ka zo ba ka dadewa kake barin Wajen nan, sai ka yi ta kalle-kalle kamar bai neman wani abu, gabaɗaya ba ka da sukuni ne. Ko ja zo ba ka dadewa." "Eh saboda yanayin aiki na ne ba na da lokutan kaina, amma fa zaran mun yi aure na dauke ki mun bar ƙasar nan, za ki samu isasshen lokacina yadda kike so." Kuɗaɗe masu yawa ya miƙa mata sannan ya yi mata sallama ya shiga motarsa ya bar unguwar. Jinjina kai Safiya ta yi ta dubu yawan kuɗin da ya bata sannan ta ce. "Sagir kenan." Komawa ta yi cikin madaidaicin gidan na su, gidan ne mai ɗauke da ɗakuna guda uku. Ɗaya na Mamanta sai ɗaya na mahaifinta sai ɗayan kuma na ta. Watanni biyar kenan da rasuwarsa. Ɗakin mamanta ta shiga da sallama a bakinta, Mama na barci ta ci Sallamar Sadiya. Ta amsa tana tashi zaune, ganin ta ajiye kudi a gefen filon ne ya saka Maman tashi zaune ta ce. "Ke Sadiya wai Sagir ne ya baki kudi masu yawa haka ?" "Eh Mama." "Wai yaron nan ɗan albarka ne akwai son kyauta." "Uhm." Sadiya ta ce tare da tashi ta barwa Mamanta kuɗaɗen. _Hilal_ Saukowa yake yi daga upstairs ɗin sakamakon kiran wayar da Papa ya dame shi da ita. Sanye yake cikin ɗanyar shadda fara, ya sanya bakin hula da bakin takalmi. Sai kamshi ke tashi daga jikinsa. Ya rasa dalilin da ya saka Papa cewa yau sai dai gabaɗaya familyn Tafarki su haɗu zuwa babban Masallacin juma'a na garin. Bayan ba tare suke zuwa ba, wasu ba nan masallacin sune sallah ba. Dan Yaa Mahmud masallacin da ke kusa da bakinsu su yaje zuwa. Haka Faisal Masallacin juma'a dake kusa da kasuwa yake zuwa kasancewar sa dan kasuwa. Amma yai Papa ya tsiro cewa yau da ƴaƴansa da jikokin sa tare za su tafi sallar juma'a. Ko da ya sauko Downstairs ɗin nan ya tarar da kowa da kowa. Sun hallara da alama saukowarsa ake jira. Yana saukowa Papa ya yi gaba kowa ya bi bayansa suka nufi parking space. Papa ya kalli Sadik wanda shi ne karami a cikin jikokin ya ce. "Ku tafi a motarka dukakkan ku." Mansur ya bude baki zai yi magana sai ya faɗa sakamakon kallon da ya ga Papa ya jefa masa. Ba wanda ya iya magana don fuskar kakan na su kamar zai yi aman wuta haka yake. Sadik ya shiga mazaunin direba yayin da Mahmud ya zauna gefensa. Hilal dake jin kansa wani iri ya bude bayan motar ya shiga don baya da wani zaɓi. Ganin ya shiga ya saka Faisal ya shiga Mansur ma ya shiga. Papa ya zauna gefen direbasa wato wajen me zaman banza, ya ce wa su Daddy duk su shiga baya. Daddy ya shiga sai Abba sannan Abbi ya shiga bayan suka zama su uku a baya. Daga haka motocin suka bar gidan. _Zahrah_ Koda ta fara da safe jikinta duk ya yi mata tsami sosai.don ko ina ciwo yake yi mata a jikin na ta, ga wani zazzaɓi da take jin ya rufe ta. Daƙyar ta iya buɗe idanunta da suka yi mata nauyi sosai. Da taimakon Dada ta tashi zaune, har bathroom ta raka ta,sannan ta tabbatar ta haɗa masa ruwan zafi ta yi wanka da shi ta gasa jikinta da ya yi mata tsami sosai. Tana wanka tana kuka tana tuna irin dukan da Hilal ya yi mata wanda ita har yanzu ba ta san laifin da ta yi masa ba da ya yi mata irin wannan dukar har ta fita hayyacinta. Bayan ta gana wanka ta ɗauro alwala, haka ta tako a hankali tana jin ƙirjinta na bugawa da karfi. Fargaba ne ya shige ta wanda ba ta san dalilin da ya saka take jin faɗuwar gaba ba. Doguwar riga ta janyo daga cikin Kayanta ta zira a jikinta bayan ta fesa turaren jiki a sassan jikinta, duk da ba ta da lafiya amma ba ta iya zama ba ƙamshi a jikinta. Hijabi ta saka sannan ta shimfida sallaya, salloli da ake binta ta rama. Sannan ta yi sallar asuba. Tana kishingide taba azkar Dada ta shigo da kofin shayi da soyayyen ƙwai dai bread ta jera su a faranti. Duk yadda ta so Zahrah ta ci ƙwai da bread ƙi ta yi sai dai ta ɗan sha ruwan tea shi ma kadan ta sha. Sai magungunan da Doctor ya bayar Dada ta ba ta , bayan t karba ta sha ne ta sake kwanciya. Yayin da gabanta ta tsananta faduwa, sai ta dinga karanta innalillahi wa'inna'ilahi raji'un a zuciyarta. Ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita . Bayan sun yi parking a in da aka tanada don ajiye motoci dukkansu suka fito daga cikin motocin. Sai dai abu ɗaya da ya ɗaure wa su Daddy kai su ne. Ganin surukansu sun ƙaraso wajen wanda ba su taba ganin su a wannan masallacin ba. Wato kakan Hilal mahaifin Mummy kenan, da kuma Kakan su Mansura mahaifin Umma da kuma Modibbo mahaifin Ummi da kuma wasu daga cikin dangin mahaifiyarsu. Sai kuma mahaifin su Kausar da Nabeela. Bayan an gaggaisa suka shiga cikin masallaci don ba damar su yi wata tamabya, suka bar Papa yana gaisawa da su Modibbo suka shiga cikin masallaci. Bayan an idar da sallar juma'a an yi addu'a aka sanar da ɗaurin aure da za'ayi a masallacin. Daga bayan motar ɗin motar Papa aka dinga fito wa da goro dabino da ai drinks da ruwa daga motar Sadik wanda ba wanda ya san da su . Kamar daga sama aka ji sanar da ɗaurin auren. *Hilal Abubakar Tafarki tare da Fatima Zahrah Salis Tafarki.* Hilal ya ɗago kai a firgice yana kallon wajen da su Papa suke, suna farin ciki har da kakansa mahaifin Mummy da wasu dangin mahaifiyarsa. Wani abu ya ji ya tokare masa ƙirji mai nauyi ya sunkuyar da kai yana kallon darduman dake shimfide a masallacin. Sai kuma aka ji sanarwar ɗaurin auren *Mahmud Adam Tafarki tare da Nabeela Nasir Isah* daga nan kuma *Mansur Adam Tafarki tare da Maryam Abubakar Tafarki* sai kuka *Sadik Salis Tafarki tare da Nadeeya Adam Tafarki* *Sai kuma Faisal Abubakar Tafarki tare da Kausar Nasir Isah* dukkansu akan sadaki Naira dubi ɗari biyu. Gabaɗaya angwayen da suka ji wannan sanarwar ɗaurin auren na su tashin hankali ya bayyana ƙarara akan fuskarsu. Duk wanda ya kalle su zai shaida hakan, ya san hankulansu a tashe yake . Hilal ne kawai idan ka kalla ba za ka iya gano rashin hankali a tattare da shi ba, domin yana da wuya ka gane halin da yake ciki ko ka iya karantar abun da ke ransa, da yake yana da jarumtar da zai iya shanye ko wane irin tashin hankali ba tare da kowa ya san halin da yake ciki ba, don haka, ko da Papa ya kallo in da jikokin na sa suke duk suna cikin tashin hankali sosai mai da dubansa ya yi ga Hilal wanda bai hango tashin hankali a tattare da shi ba, sai sai ya san cewa dole zai ji shi kasancewar ba sa jituwa da Zahrah hasalima ya tsane ta, amma da yake namijin duniya ne shi ba wanda ya iya hango hakan a fuskarsa ko a yanayinsa . Goro da dabino aka dinga rabawa dai drinks da ruwan roba. Ana ta Allah ya sanya alkhairi da fatan zaman lafiya a tsakanin ma'uratan. *Ku yi hakuri da wannan* *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LrTZNGwF35IKXX4sLRvFug?mode=ac_t *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA NE* Page6️⃣1️⃣ Goro da dabino aka dinga rabawa da drinks da robar ruwar roba. Ana ta Allah ya sanya alkhairi da fatan zaman lafiya tsakanin ma'uratan. _Mom_ Zaune suke a dinning table sana cin abinci, Dad ne a gefenta sai Aunty Zulaihat dake fuskantar su. Gefe kuma Fauziyya ce da Suhailat suna yin breakfast. Mom sai juya cikali take yi a cikin ruwan shayi. Ta yi tagaumi tana tunani. Dad ya kalle ta ya ce. "Hajiya lafiya na ga ba ki wani ci abincin kirki ba ga kowa na cin abinci." Ajiyar zuciya ta sauke cikin damuwa kafin ta ce "Ba komai Dad ɗin Asad ." "A'a akwai komai." "Alhaji damuwa ta ɗaya ce rashin sanin halin da Asadullah yake da kuma rashin sanin in da yake." Ta yi maganar tana goge ƙwallar dake cikin idanunta, zuba mata idanu Dad ya yi cike da tausayinta, ya san tabbas akwai Shakuwa tsakanin ta da Asadullah, kusan a hannunsa ta ya tashi, ɗan ɗakinta ne shi. "Hake ne, amma in sha Allah yana cikin ƙoshin lafiya, ki rage damuwa don Allah, fatana ki yi ta yi masa addu'a Allah ya kare shi ya toni asirin waɗan da suka yi masa wannan aiki." Da sauri ta kalle shi taɓa mamakin jin kalaman sa kafin ta ce. "Ban gane Allah ya bayyanar da shi ya toni asirin wadanda suka yi masa haka na, don Allah ka faɗa Mani me aka yi masa kuma su waye suka yi masa, kada ka ce an cutar mana da Asadullah don Allah." Ta karasa maganar tana hawaye. Cikin kokarin boye mata gaskiyar abinda ya sani ya ce. "Kin ga ki kwantar hankalin ki ba haka nake nufi ba ina nufin Allah ya bayyanar mana da shi a duk in da yake ba tare da wasu sun cutar da shi ba." "Dad ɗin Asad ni fa ba yarinya karama ba ce, kada ka ce za ka boye mani komai, ka faɗa Mani wani hali ɗan mu yake ciki walalhi ina cikin damuwa na rashin sanin halin da yake ciki . Nan Dad ya dinga ba ta baki da kwantar mata da hankali, kafin ta saki ranta amma duk da haka ta kasa cin abincin kirki a cikin ta. Tausayi ta ba Dad don ba don ya yi wa Asadullah alkawarin cewa ba zai fada wa kowa ba da ya sanar da ita halin da Asadullah ke ciki. Don baya zargin za ta iya cutar da shi, bisa la'akari da a hannunta ya tashi akwai kauna a tsakaninsu tun mahaifiyar Asadullah na raye. Tashi ta yi ta koma bedroom ɗin ta cikin damuwa. Fauziyya ta tashi ta bi bayan mahaifiyarta ranta a ɓace. Tana shiga ta samu Mom ta haɗa tagumi ta kalle ta cikin ɓacin ran da mahaifiyar ta su ke nuna halin ko in kula akan Yayanta ta ce. "Mom yanzu ɗan kishiya ya fi ɗan da kika haifa a wajen ki?" Kallonta Mom ta yi ba ta yi magana ba ta share ta kamar ba ta ji komai ba ta ce. "Mom Asadullah ba ke kika haife shi ba ɗan kishiyarki ce shi, duk kin bi kin daga hankalinki akan sa kin damu kin saka rashin wakawlaa tun lokacin da aka rasa ina yake. Amma ke ce kika haifi Kamal ɗanki ne ga shi can yana rayuwa a gidan yari rayuwar rashin ƴanci da ƙasƙanci ba ki damu da hakan ba , ko sau daya ban ji kina magana akan sa ba shi ki da yake prison, amma kin damu da wanda ba ka ke kika haife shi ba wa ya sani ko ya guje mu ne yana..." Tsawar da Mom ta daka mata ne ya saka ta yin shiru ta fice rai a ɓace, don Allah ya sani tana tsananin ƙaunar ɗan uwanta Kamal. Duk da cewar Asadullah ma tana son sa, saboda yana kyautata mata sosai, amma Kamal da suka fito ciki ɗaya ta fi jin sa a ranta fiye da Asadullah. _Papa_ Gaisawa yake yi da jama'a dake taya shi murnar aurar da jikokinsa,bakinsa ya ki rufuwa fatan shi Allah ya sa wannan auren ya zama sanadiyar haduwar kan Family ɗin sa. Suka kebe shi da surukan na sa wato iyayen matan ƴaƴansa, da kuma mijin Aunty Laila suka dan yi magana kafin ya masu sallama. Ƙarasowa ya yi wajen motocinsu in da ya tarar shi suke jira, don hatta ƴaƴan na sa bai yi shawara da su ba wajen aurar da jikokinsa, don ya san ba za su taba amincewa da wannan hadin ba, don haka sai dai suka ji ɗaurin auren daga sama. Daddy, Abba, Abbi, ba karamin tashin hankali suka shiga ciki ba saboda ba su taba tunani ba. Babban tashin hankalin su yadda dukkansu uku aka haɗa aure a tsakanin ƴaƴan Abbi da na su. Sam ba sa da hadin kai da Abbi cikin yaran Papa huɗu shi kadai suka ware a cikinsu . Amma yau Papa ya kulla igiya mai daraja sun hadu a matsayin surukan juna. Girgiza kai Dad ya yi a zuciyarsa yake magana . 'Wato dukkan mu da muka ware Salis a cikin mu sai da Papa ya haɗa yaran dukkanin mu da yaran Salis, a tunanin Papa wannan zai kawo masalaha kenan, to ai yaran ba sa son junansu na tabbatar Papa ya ƙara ruguza a halinsa wajen kokarin ya kawo sauyi. Musamman Hilal na san da wahala ya yarda da wannan auren.' Papa ya karaso wajen fuska cike da farin ciki, ya kalli angwayen yana cewa. "Angwaye kun sha ƙamshi." Ko wa ya sake tsuke fuska ba wanda ya kula shi sautin murmushin sa ta suka ji ne ya saka suka kalle shi amma ban da Hilal ' Papa da ya karaso wajen kallonsu ya yi ɗaya bayan ɗaya duk sun yi cirko-cirko kamar wadanda aka aiko wa sakon mutuwa suka yi. Ku shiga mota mu tafi, kuma idan mun koma gida ina son ganin kowa a part ɗin na." Ya yi maganar yana shiga gefen direba, cikin sanyi jiki su Daddy da Abba suka shiga bayan motar yayin da Abbi ya shiga daga karshe. A can kuwa wajen angwaye kasancewar motar Sadik suka shiga wajan zuwa kamar yadda suka zo, sai dai kowa a cikinsu kamar baya da laka a jikinsa. Sadik kasa driving motarsa ya yi, ganin haka Hilal ya fito daga bayan motar ya bude gefen Direba tare da yi wa Sadik alamar ya fito ba tare da ya yi magana ba, ganin haka ya saka Sadik fitowa daga cikin motar ya koma baya. Hilal ya yi wa motar key tare da fisgarta da ƙarfi ya bar wajen. Har ya wuce su Papa da suka riga su tashi, gudu yake yi kamar zai tashi sama, su kansu sun lura da irin Yulin da yake yi. Amma ba wanda ya iya yin magana har suka ka ce karasa. Danna horn yake yi ba kakkautawa. Mai gadin ya leƙo ya bude da sauri. Ko parking din kirki bai yi ba ya fito ya shiga cikin gidan. Kamar wakjiya su da suke falo ba su ga shigowarsa ba, sai dai suka jin takun hawa steps da ƙamshinsa da ya bar masu. Har tsallaken stage ɗin yake yi ya haura zuwa ɗakinsa. Su kuwa cikin sanyin jiki suka shigo, sai dai tunawa da maganar Papa da ya ce su wuce Part ɗin sa su same shi shi ya saka shi ya sa ba su wuce Part ɗin su ba, kowa kowa ya nufi part ɗin Papa kamar yadda ya sanar da su. Mutanen dake falon suka ga yanayinsu take jikinsu ya yi sanyi, don haka suka bi bayansu ba da kallo. Kafin su yi wani yunƙuri suka ga Papa ya ba shigo su Daddy na biye da shi a baya. Kallonsu Papa ya yi tare da cewa. "Ina son ganin kowa a part ɗi na." Ya kalli Abbi tare da cewa. "Salis ka kira matarka don na ga ita kadai ce ba ta nan." Da to Abbi ya amsa sannan ya nufi part ɗin sa don kiran Ammi. Haka suka bi shi daga su har yaransu su matan da ba su san meke faruwa ba kansu a daure yake . Bayan kowa ya hallara gabadaya, ganin ba Hilal ya saka Papa kiransa a waya ya bashi izinin zuwa. Ba jimawa ya shigo da sallama. Wuri y samu ya zauna a ƙasa saman Centre Carpet. Zahrah dake kwance ba lafiya ne kawai ba ta wajen. Ita ma sai da Papa ya ce wa Dada ta taimaka mata ta fito. Dada ta tashi ta nufi ɗakin Zahrah don taimaka mata ta fito. Suna zaune ba wanda ya iya cewa komai. Dada ce ta fito rike da hannun Zahrah wacce kallo ɗaya za ka mata ka san ba ta da lafiya, don tafiya ita kadai ma ta kasa da taimakon Dada suka karaso ta zaunar da ita a ƙasa ita kuma ya zauna kan kujerar dake bayan Zahrah. Sallama Papa ya yi masu sannan ya kalli kowa dake wajen ɗaya bayan ɗaya. Kafin ya kalli Daddy ya ce. "Abubakar." Daddy ya amsa da "Na'am Papa." "Akan idanunka na zartar da hukuci akan ƴaƴanka, saboda na san cewa na isa da kai, ba za ka taɓa bijerawa umarnin da na aka ba." Sannan ya dubi Abba ya ce. "Adam." Shi ma Abba ya amsa da "Na'am Papa." Kai ma na yanke shawarar da na yanke akan yaran Abubakar wanda na san kai ma ba za ka bani goyon baya akan abinda na saka a gaba." Duban Abbi ya yi tare da cewa. "Kai ma haka Salis, na san dama duk hukuncin da na yanke akan ƴaƴanka kai mai biyayya ne." Duban Aunty Laila ya yi tare da cewa. "Laila." "Na'am Papa." "Ina da iko dake amma ba na da iko akan ƴaƴanki, saboda ubansu ya fi ki iko da su, hakan ya saka na nemi amincewar sa akan shawarar da na yanke akan ƴaƴansa Nabeela da Kusar. Kuma sai ya yi Mani biyayya akan duk abinda na zartar akan ƴaƴan sa shi mai biyayya ne. Don haka na yanke shawarar da nake ganin zai kawo karshen duk wata matsaloli dake cikin wannan zuri'ar." Ajiyar zuciya ya sauke yana kallonsu daya bayan daya, yayin da matan kirjinsu ke bugawa don suna fargaban jin abinda Papa zai fada. "Na ɗaura auren Hilal da Zahrah, Mahmud tare da Nabeela, Mansur tare da Maryam, Sadik tare da Nadiya. Faisal tare da Kausar. Tashin hankali ne ƙarara ya bayyana akan fuskokinsu, Zahrah kam gaba ɗaya ji ta yi numfashinta ya ɗauke. Duhu kawai take gani sai maganar Papa dake mata amsa kuwa a cikin kunnuwanta. Na ɗauka auren Hilal da Zahrah, take ta ji numfashinta ya ɗauke Amminta kuwa mutuwar zaune ta yi. Ga wani abu da ta ji ya tokare mata ƙirji ya mata nauyi, ji ta yi yawan jinta na neman tashi. Sauran jama'ar dake falon matan su Mummy da Umma kuwa ji suka yi kamar an soka masu mashi a zuciyarsu, Aunty Laila kasa haɗiye bacin ranta ta yi ta ɗora hannu akai tana kuka da fadin ta shiga Uku. Tsawar da Papa ya daka mata ne ya saka ta yi shiru . "Na gama yanke hukunci ba na son jin komai. *Na kusan kammala book 1 kamar yadda tsarin yake book 2 na kudi ne. Za ku same shi akan Naira ɗari biyar ne kacal 500* *Da zaran ya zama complete document kuwa kudinsa Naira ɗari bakwai ne* Za ku tura kudin ku ta wannan account ɗin 2242538358 Zainab Abdullahi U.BA bank Sai a tura shaidar biya ta wannan lambar 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA NE* Page6️⃣2️⃣ "Na gama yanke hukunci ba na son jin komai." Gabaɗaya suka yi shiru Mummy kam tana cikin mawuyacin hali a wannan yanayin, kamar za ta haɗiye zuciya ta mutu. "Na san dukkan ku ba ku kammala gidan da kuke gina wa ba, saboda ba ku shirya aure ba ko? Alhamdulillah zan ba kowanne gidan da zai zauna da matarsa ." Kallon Hilal ya yi wanda tsabar ɓacin rai kamar ya yi Amon wuta ya ce. "Kai na san ja kammala komai na gidanka, kuma duka gidajen da zan rabar ba su kai na ka gidan ba, amma duk da haka kau ma zan baka kamar yadda ba ba kowa ." "Ba na bukata." Ya fada a takaice ba tare de ya kalli Papa ba. Murmushi Papa ya yi dama ya san ba zai taba karba ba, don ya san Hilal ɗin ma ya tara dukiya sosai . Dada ce ta kalli Hilal ta ce. "To maganar lefe fa kai da ƴan uwanka, kowa dole ya yi wa matarsa kayan lefe don ba Sadaka aka ba ku ba, ku bar ganin kun same su daga sama. Kakanku ya biya sadaki ya ba ku gida, lefe dole ne ku siyawa matanku da kanku, wannan karon aljihunku ne zai yi bayani, don haka kowanne ya bayar da kuɗin da za'a haɗa lefe, ko kuma na kira Hajiya Amina ƴar Aminin Papa ta zo mu tafi da ku ko ta sanar da ku yawan kufun da za'a kashe sau mu je da ita a hada kayan." Kallon Hilal ta yi ta ce "Ya ka ce?" Ba tare da ya kalle ta b ya ce "Akwai matar abokina tana kasuwanci zuwa Dubai, za ta hado komai." "Ma sha Allah, na ka za ta hado daga can kenan." "Ba nawa kadai ba, ba dukkansu za'a a hado wa na ɗauke masu nauyin." Ya yi maganar yana kallon ƙannen na sa wanda kalli ɗaya za ka gane suna cikin tashin hankali, idanunsu duk ya ya yi ja. Dada da Papa ba karamin farin ciki suka yi ba. Tashi Hilal ya yi ba tare da ya kalli kowa ba, ya fice ransa na masa suya, da kallo suka bi shi kamar baya cikin wata damuwa idan ka kalle shi a zahiri, saboda jarumta da juriya da wuya ka ga rauninsa. Amma a baɗini ba ƙaramin zafi da zugi zuciyarsa ke yi ba. Papa ne ya lura da Zahrah da ta sandare tana jijjiga. Cikin tashin hankali ya ce. "Subhanallah Zahrah." Umminta da Abbi suka karasa kanta. Ummin tana cikin wani hali, don zama ta yi tana dafe kanta dake sara mata kamar zai fashe. Mummy ta mike tana hada hanya tana ganin duhu ta fita, tana fita zuwa falon gidan ta saki jiki za ta zube a wajen, Hilal dake tsaye ya kasa motsawa ya hango ta, cikin zafin nama ya tare ta hakan ya saka ta faɗa a jikinsa. Da sauri ya nufi bangarenta da ita cikin tashin hankali. "Kowa ya tafi kafin anijma zan neme ku." Papa ya yi magana ganin kowa na cikin tashin hankali. Tashi suka yi kowa ya bar fakon cikin mawuyacin hali. Aka bar Abbi dake fama da Ummi, don Dada da Papa suna kan Zahra, ga Ummi na yi kamar za ta shiɗe ita ma. Abbi ya kira Doctor domin ya zo ya duba su. Aunty Laila da Umms ikon Allah ne masu ya kai su part ɗin su. Angwaye tashi da suka yi cikin sanyin Jiki suka bar part ɗin bisa umarnin Papa, duk da Sadik da Mahmud sun so tsayawa saboda halin da Ummi da Zahrah ke ciki, Papa ya ce su tafi. Nan da nan Doctor ya zo saboda kiran gaggawar da Papa ya yi masa, Abbi ya ɗauki Zahrah ya nufi ɗakinta da ita, ya kwantar akan gado. Taimakon gaggawa Doctor ya shiga ba wa Zahrah, ga zazzabi mai zafi da ya rufe ta lokaci guda. Dai kuka take tana suratai bayan ta farfaɗo, sai dai dole ta saka Doctor ya yi mata alluran barci, wanda hakan ya saka barci ya yi awon gaba da ita nan take. Mummy dai shock da ta shiga lokaci guda ne, Hilal ya ajiye ta akan gadonta ya kwantar, ganin halin da take ciki ne ya saka ya ɗauko mata magungunan hawan jininta ya ba ta. Bayan ya dauko mata robar ruwa daga cikin fridge ya tsiyaya mata ruwan a kofi ta gama shan maganin ta koma ta kwanta. Hawaye ne kawai ke zuba daga cikin Idanunta, kawai ta juya masa baya wanda hakan ya saka ya bar ta ya fice, don ya ga ta ɗan samu Sa'ida. Shi kansa karfin hali ne kawai yake yi, don zuciyar sa sam ba dad'i, jarumta ce kawai yake da ita wanda ba za ka kalle shi ka gane yana cikin damuwa ba. Bedroom ɗin sa ya nufa, ba tare da ya cire kayan jikinsa ba ya sakarwa kansa shower 🚿 tsawon mintuna talatin ruwa na zuba a kansa kafin ya cire kayan jikinsa ya yi wanka. Ya fito ɗaure da farin towel a ƙugunsa. Wayarsa dake saman bedside Drawar ce ta soma ruri. Bai kalli wayar ba ya tsaya gaban mirror yana kallon fuskarsa dake ɗaure tamau, ga idanunsa har yanzu sun yi jajir da su. Wayar ce sake turi ya karasa yana kallon wayar. KB shi ne sunan da ya bayyana akan fuskar wayar. Ɗaga wayar ya yi tare da karawa a kunnensa ba tare da ya yi magana ba. "Ango! Ango!! Ango!" Muryar KB ce ta karade kunnensa yana masa kirari. "Waye angon?" "Kai Mallam na san komai fa, Granny ɗi na yake sanar da ni akan idonsa aka daura maku aure, wato ko gayyata babu ko? Haba ai sai ka sanar da ni, ko auren sirri ne ai bai kamata ka boye Mani ba." "Kai ban san komai ba, ni ma ɗaurin auren kawai na ji tsoron nan ya yi ba tare da izininmu ko amincermu ba." Dariya KB ya yi tare da cewa. "Gaskiya wannan tsohon ya kyauta sosai ba kaɗan ba, ya taimaka wa wannan Gwauron Allah ya kara masa lafiya da nisan Kwana." Hilal dai bai ce komai ba, yana shirin Sallamar sa ya ji Kb yana cewa "Na ji an ce dukkan ku aka aurar maza da mata, wato ba zai bari bare ya zo ya aure masa zuri'a ba ko, a cikin ku waye mai sa'ar da aka aurawa Fatima Zahrah?" "Mai sa'a ko kuma mara Sa'a ba, to ni ne wannan mara sa'ar nan da aka aurawa ita. " "Haba Man me kake cewa haka ne, ai ka godewa Allah da ya saka ba daya daga cikn yaran gidan nan aka aura maka ba, don kaf ba mai tarbiyya da hankali irin na Zahrah. Duk da cewar ba wai wani saninta na yi ba, amma na ji labarin ta a wajen Granny da kuma lokacin da hotunan ta suka dinga yawo a social media da gidajen Tv da..." "Dalla kar ka dame ni da yawan magana, ka bar ni na ji da halin da nake ciki." Yana fadar haka zai katse kiran wayar ya ji Kb ya ce. "Please minti ɗaya." Hilal cije leɓensa na ƙasa ya yi yana cewa . "Meye?" "Tambayar ka zan yi don Allah ka bani amsa ta gaskiya." "Waye kai da zan yi maka ƙarya, kai ma ka san ba na faɗin karya ko na taba yi maka ne?" "A'a, dan Allah ya ake ciki ne, ka san mune abokan na ka ya kamata mu san halin da ake ciki, akwai wani shirye-shirye da za'ayi ne?" "Babu." "Ba wani reception ko dinner da za'ayi ne?" "KB ka bar ni ko za'ayi ni ba abinda zan yi, sannan kuma kar ka sake..." Dakatar da shi KB ya yi ta hanyar cewa. "Wait tunda ba na shiri ba ne amma na san lefe dole za ku yi masu ai." Cikin ƙosawa Hilal ya ce. "Ka fadawa matarka ta haɗa masu kayan lefe kowacce ta miliyan biyar." "Dukakkan su matan biyar za'a haɗawa lefen, kowanne ango ka ɗauke masa kenan?" "Eh ita abinda zan iya yi masu kenan, idan an gama wanda ya ga zU karawa matarsa sai ya kara mata." "Ka kyauta babban Yaya, amma gaskiya Zahrah kam ta fi ƙarfin ka haɗa mata lefen miliyan biyar, su sauran dai za'a haɗa masu na miliyan biyar din da ka ce su hudu amma Zahrah sai dai na miliyan goma za'a haɗa mata." KB ya faɗa masa cin n tabbatar wa. "Saboda ita ƴar Gold ce ko, ai ba ta fi su ba, don haka zan ba ka 25 million kowace 5 million." Yana fadar haka ya katse kiran wayarsa tare da ajiye wayar. _Sadik_ Ko da ya karasa zuwa part ɗin sa shi da Yaa Mahmud ba wanda ya iya yin magana, don sun bar Abbi da Ummi a part ɗin Dada. Sadik ya kalli Yaa Mahmud ya ce. "Ya wallahi a cikin wannan al'amari ba wanda nake tausaya wa sai Zahrah." Mahmud ya kalle shi tare da cewa. "Kai ma kanka abin tausayi ne, don na tabbata da sai mun ji jiki a wajen yaran nan, don tarbiyya ba ta ishe su ba." Dariya Sadik ya yi tare da cewa. "Wallahi a duniyar nan ba macen da zan ji jiki a hannun ta, sai dai ta ji jiki a hannuna, don wallahi ita ce abin tausayi ba ni ba ." Mahmud kallon Sadik ya yi don ya san waye Sadik, karye ne wani ya taka sa ballantana macen da aka aura masa, sai dai dukkannin su za su ji jiki idan ba ta kwantar da kai ba. Bedroom ɗin sa ya nufa ba tare da ya sake yin magana ba. _Mansur_ Ko da ya shiga part ɗin su ya tarar da Abba da Umma suna a falo kowa ya yi jigum cikin damuwa . A fusace Sadik ya ce. "Wallahi ban yarda da wanan auren ba ta ya ya za'a aura mani wata da ban ce ina son ta ba, sanann wani karin abun takaicin ma wai Nadiya ƙanwata ce za'a aurawa Sadik , yaron da sam baya da mutunci. Na tsane shi daga shi har ƙanwar ta sa Zabarah na tsane su, don da a ce ni aka bawa auren Zahrah sai dai wata rana aji labarin mutuwarta. Sai sai ko Yaa Hilal ɗin ma ba baya ba, na san sai ta ɗanɗani kuɗarta kafin mutuwarta. Ita kuma Nadiya na san haryar da zan ɗora ta, ina take ne?" "Da kyau." Cewar Umma cikin damuwa. _Faisal_ Bayan fitar Hilal daga wajan mahaifiyarsu shi ne ya shiga ɗakin na ta bakinsa da sallama. "Ni wallahi duk cikin dalilin nan ba wanda aka cuta sama da ni, a rasa wanda za'a aura Mani sai Kausar ɗin Aunty Laila, yarinyar da ta fi kowace yarinya rashin tarbiyya, Aunty Laila fa aka ce ƙarshen masifa da bala'i wallahi Papa ka cuce ni." Dad da shigowar sa kenan ya ce. "Faisal dama ba ka da kunya kai ma, ƙanwar ta wa ce masifa da bala'i?" Faisal bai sake magana ba ya fice, yayin da Daddy ya nufi Mummy dake kwance tana jin su ta kasa magana. _Hilal_ Hilal bayan ta kammala saka kaya ya shirya cikin ƙananan kaya sai ya ji knocking. Bai bada izinin shigowa ba ya fa KB ya shigo yana murmushi. "Dama ina kusa da ku shi ne na karaso don gobe matata za ta je Dubai na ji ka yi maganar lefen shi ne na tuna na zo ka bayar da kuɗin." Ya yi maganar yana zama kan sofa. Sanin halinsa na tsokana ya sa Hilal ba i ɓata lokaci ba ya shiga cikin bedroom ɗin sa, don ya sallame shi Bayan mintuna sai ga shi ya fito rike da wayarsa. "Nawa account ɗin ka ke ɗauka?" "Mallam idan za ka tura Mani kudi ka tura Mani, ka ɗauka karamin account ne da ni?" Danne-danne ya yi a wayarsa ya sannan ya ajiye, take alert ya shigo account ɗin KB. Kallonsa ya yi tare da cewa. "Na ga ka tura Mani miliyan asirin da biyar, talatin za ka tura, don na Zahrah kayan miliyan goma za'a haɗa mata, sauran miliyan biyar-biyar." "Mallam abinda zan iya kenan, ko ƙwandala ba zan kara ba, ai ba fin su ta yi ba." "Wallahi tafi su, ko a ilimi da tarbiyya ga kyawun..." Kallon da Hilal ya masa ya saka ya kasa karasa wa, amma ya share tare da cewa. "Mallam dole sai ka cika 5 million ɗin nan." Bai ce masa komai ba, ya nufi kofar da za ta sada shi da garden ɗin gidan. KB na masa magana ya share shi. _Asadullah_ Fitowa ya yi daga cikin gidan, sanye da riga mai hula, ya janyo hular ta rufe masa rabin fuskarsa. Ya sanya bakin glass a idanunsa. yya nufi parking space, ɗaya daga cikin motocin dake wajen ya bude wata bakar motar ya buɗe ya shiga, wanda ba wanda zai iya ganinsa sai dai shi ya kalli mutum. Horn ya yi maigadi ya bude masa gate ya fice da motar. Kai tsaye shopping mail ya nufa. Abakin wajen ya yi parking motarsa ba tare da ya fito ba, wayarsa ya ɗauka yana danne-danne, da wayarsa ya yi siyayyan da zai yi ya tura masu kudin ta wayarsa, sai ga ma'ikatan wajen sun fito rike da ledoji suka saka masa a bayan motar. Bayan sun gama saka wa ya ja motarsa ya bar wajen. Ja tsaye airport ya nufa da kansa. Daga nesa ya hango su suna fitowa daga airport ɗin. Kallonta yake yi ta cikin bakin glass dake kan fuskarsa. Sanye take cikin jallabiya baƙa ta yi kyau kuma ta kara haske. Har wajen motar suka karaso kasancewar Doctor Isma'il ya sanar wa Anisa da Asad yana jiran su. Anisa da Doctor Isma'il na rike da kaya yayin da Jidderh kuma tana rike da hannun Anisa ɗaya Doctor Isma'il ya saka kayan a bayan motar, sannan ya zagaya zai shiga gefen mai zaman banza, Asadullah ya masa nuni da Jidderh, don Doctor Isma'il murmushi ya yi tare da cewa Jidderh ta shiga. Ba musu ta shiga ta zauna, shi da Anisa suka shiga baya. Kallon Jidderh ya yi tare da janye hularas baya, ya cire bakin glass ɗin ya saka . Kamilalliyar fuskarsa kai cike da haiba ta bayyana. Sanyayyar murmushinsa ya sakar mata. *Masu sha'awar karanta book 2 za su tura kuɗinsu Naira ɗari biyar ₦500 ta wannan account ɗin. 2242538358 Zainab Abdullahi UBA bank sai a tura shaidar biya ta wannan lambar waya 09065327995* [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA NE* Page6️⃣3️⃣ Kallon Jidderh ya yi tare da janye hularas ya ya cire bakin glass ɗin da ya saka. Kamilalliyar fuskarsa mai cike da haiba ta bayyana. Sanyayyar murmushinsa ya sakar mata. Tayar da motar ya yi suka bar wajen. Suna cikin tafiya ya ji muryar Anisa tana gaishe shi. "Ina wuni Yallaɓai?" "Lafiya lau fatan kun iso lafiya?" "Lafiya lau, na ga ba ka lura da kowa ba Jidderh kawai ka sani da ita ka damu." Ta yi magana cike da takaicin share ta da ya yi. "Afuwa Anisa na bari ne mu je gidan sai mu gaisa da kyau ko?" Murmushi ta yi tare da cewa. "Ya kake ya lokaci, sau tari ina tura maka message ba reply, kuma na ga kana amfani da social media." Bai ce komai ba illa iyaka ya mayar da hankalinsa ga tuƙi, ya kalli Jidderh yana cewa . "Kina lafiya?" Ta jikin madubi ya kalli Dr Isma'il ya ce. "Ya jikin na ta?" "Da sauƙi." "Alhamdulillah." Ya faɗa yana kallon titin yayin da yake driving, abubuwa da yawa ne suke yawo a cikin ransa. A bakin gate ɗin gidan ya yi horn maigadi ya leƙo, ganin uban gidansa ya saka ya wangale masa gate ɗin gidan ya shiga cikin gidan. A parking space ya yi parking ɗin motar, fitowa suka yi yayin da shi da kansa ya bude wa Jidderh murfin motar ta fito cikin sanyin jikinta. Maigadi ne ya taya su ɗaukar trolley bag ɗin da suka dawo da su. Ciki suka shiga dukkansu suka zube a Falo, Jidderh ta zauna kusa da Anisa. Kuku ne ya kawo masu abun sha, bisa umarnin uban gidansa. Dr Isma'il ya mike yana cewa. "Zan je gida na ga iyalina zan dawo mu yi magana, daga baya." "Yanzu Doctor har yanzu tunanin na ta bai dawo daidai ba, gaskiya da sauki kam." Cikin damuwa Asadullah ya ce. "Innalillahi wa'inna'ilahi raji'un, ta ina zan fara neman iyayen yarinyar nan ballantana har na damƙa ta a hannunsu." "Kada ka damu in sha Allah za'a gane in da suke, bari na dawo mu yi magana." Ya karasa maganar yana ficewa don zuwa gidansa ga iyalansa. Jinjina kai Anisa ta yi jin ta samu amsar da take nema, wato sanin shin Asad na da alaƙa ta jini da Jidderh ne ko a'a. Hakan ya saka ta gane wato bai ma san su waye iyayenta ba." Murmushi ta saki tare da ayyana abubuwa da yawa a zuciyarta. "Za ku ci abinci ne ko sai kun yi wanka kun fito?" "Sai mum yi wanka mun fito." Cewar Anisa tana nufar ɗakin da aka sauke su ita da Jidderh. Kallonta da mamaki ya yi kafin ya ce. "Ita kuma fa me ya saka kika tafi kika bar ta a tsaye." A fakaice ta harara Jidderh sannan ta ƙaƙalo murmushi wanda iya fatar bakinta ya tsaya ta ce. "Oh sorry ƙanwata ba ki biyo ni ba." Ta fada tana jan hannunta suka bar wajen zuwa cikin bedroom ɗin su. Da ido ya bi su kafin ya haura upstairs zuwa ɗakinsa. Suna shiga Jidderh ta kalli Anisa da ta murɗe mata hannu da karfi wanda sai da ta ji zafi ta kalle ta. "A gidan uban wa ba ya samo ki da kika zo kika tare masa a gida, ga shi ya bi ya damu dake, duk in da kike idanunsa na kanki sai dai idan baya wajen, ta zan yi da ke ne, duk yadda zan yi sai na yi na fitar dake daga cikin gidan nan, idan ya tambaye ni zan ce ban san in da kike ba ina barci, sai na tabbatar na nisanta ki da gidan nan yadda ba za ki iya dawo wa ba kafin na dawo. Don na ga alamar kece katangar da za ki yi Mani shamaki da abun so na." Jan hannunta ta yi da karfi suka shiga bedroom ɗin dake cikin ɗakin. _Dada_ Shirya amaren gidan take yi babu kama hannun yaro, kasancewar sati ɗaya za su yi a gidan kafin su tare, wato bayan daura auren da sati ɗaya kenan za su tare. Dada ka cewa ta yi duk da ba lokaci za ta ɗan yi masu gyaran da ba zai cutar da su ba, wanda ko ba mu'almar aure suka yi a farkon auren ba to amaren ba za su shiga wani hali ba. Don gyaran amarya take yi masu Sai dai ba wanda zai basu matsala ba, bisa la'akari da yanayin yadda auren na su ya zo, ba na soyayya ba ne. Duk da ba su don gyaran da take yi masu amma ba yadda suka iya, dole kowane safiya dai sun zo da yamma ma sai sun zo. Don idan ba su zo ba Dada da kanta take zuwa part ɗin kowa ta yi wa uwar yarinyar tas, dole yarjnya ta biyo ta. Zahrah dai dama tana na nan part ɗin, kuma har yanzu jikin na ta bai warware ba, amma duk da haka Dada ba ta ƙyale ta ba cewa ta yi rashin son auren ta saka ki sakin jiki ballantana ta warware. Kasancewar sun yi hutun school daman Islamiya kawai take zuwa. Papa ya kira Daddy da Abba, da Abbi ya sanar da su ranar juma'a kowace ƴa za ta tare a gidan mijinta, don haka kowane uba ya yi wa ƴarsa kayan ɗaki a kai a jera mata a gidanta kafin ranar juma'a. Ya sanar da su cewa ya riga ya siye wa kowane yaro gida Hilal ne bai karba ba, don haka su je su siye kayan daki a kai a jera. Kafin ranar juma'a. Ba yadda suka iya da to suka amsa masa kafin suka yi masa sallama. Sannan ya nemi ganin angwaye don so yake ya mallaka wa kowa takardun gidan da ya bashi da makullin gidan. Zahrah dai tana ɗan shan wahala wajen gyaran da Dada ke masu, sakamakon dukan da Hilal ya yi mata jikin na ta akwai raunin ciwon saboda belt ɗin ya ɗan fasa mata jiki, ga shi da ruwan lalle da wasu hadin take masu wanka, hakan ke saka tana jin zafi a wajen ciwon. Kamar yadda Papa ya ce haka kuwa ya damƙa masu makullayen gidajen da takardun. Dukkansu huɗu, Mahmud, Mansur, Sadik da Faisal. Godiya suka yi masa, duk da cewar dukkanin su suna da gini da suka fara ba su mayar da hankali ne ba kawai ba su yi ba ganin ba saka auren nan kusa suka yi ba. Haka suka je kowa ya nufi gidan da ka bashi bisa umarnin Papa, kowane gidansa Madaidaici ne, mai ɗauke da babban falo, da ɗakunan barci uku, kowane da toilet a cikin ɗakin, sai kitchen da dinning area. Kasancewar sabbin gidaje me dukkansu ba wanda aka shiga, fenti ne kawai za su yi. Duk da cewar ransu s jagule yake sakamakon auren dolen da Papa ya yi masa, amma ganin kyautar da ya yi masu sai suka ji kaso ashirin na haushin sa da suke ji ya ragu. Zahrah da wayarta kwana biyu kenan tana kashe sai yau ta kunna ta, messages ta gani da yawa musamman na Ammar. Duk ya damu akan rashin jin daga gare ta, kamar za ta kira shi sai ta fasa, ajiye wayar ta yi tana kuka. Kamar yana jira sai ga kiransa ya shigo cikin wayarta. Ba suna da emoji ta yi served ɗin sunansa. Har ya katse ba ta ɗaga ba, yayin da kuka sosai da tausayin rayuwar da za ta yi a gidan Hilal take yi. Kasancewar yau sauran kwana huɗu tarewarsu, kuma ranar da za'a tare za su yi taron biki, hakan ya saka Papa ya ce ma kowace ta je ta samu mijinta a ɗakinsa su yi shawarar yadda za su tsara bikinsu ko akwai wani dinner da za su yi ko wani shagali dai. Dan haka da kansa ya saka Dada ta tabbatar kowacce cikinsu ta tafi ta samu mijinta sun yi magana. Hakan kuwa aka yi kowacce Dada ta tura ta ta je su yi shawara da mijinta. _Mansur_ Yana zaune a falonsa yana kallon wani program da gidan TV da yake aiki suka saka. Maryam ce ta shigo bakinta ɗauke da sallama. Ɗagowa ya yi ya kalle ta ba tare da ya amsa mata ba. Kallon banza ya yi mata kafin ya ce. "Lafiya?" Ganin kallon da yake yi mata da yanayin yadda ya yi magana ya ɓata mata rai, duk da cewar ita ba ta da masifa amma ba ta daukar raini da wulaƙanci, kuma ta san Mansur ɗan wulakanci ne da rainin hankali. Shi ya sa baya jituwa da mutane da yawa. Ganin ta masa shiru ya ce. "Kin matsu ki tare ne shi ya saka kika kawo Mani kanki da kanki ko ya aka yi, idan ma kina tunanin zan kalle ki a matsayin macen aurena kin yi kuskure. Don wallahi sai kin yi nadamar wannan ..." "Ya ishe ni haka nan Yaa Mansur, ka ɗauka sonka nake yi ne ko kuma da son raina na zo ɗakinka, yadda kake gani an yi maka dole ni ma haka aka yi mani, ba sonka nake yi ba ballantana ka wulakanta ni." "Ku je ku fadawa Papa bakya so na." "Kai da kake namiji ka je ka same shi mana." Tsawa ya daka mata tare da cewa "Fita a ɗakin nan kafin na yi maki shegen duka." Da gudu ta fita tana gunguni. _Mahmud_ Dawowarsa kenan daga aiki a gajiye yake, yana shirin rage kayan jikinsa kenan sai aka turo ƙofar aka shigo cikin ɗakin . Juyawa ya yi yana kallon ƙofar sai ya ga Nabeela ce ta shigo cikin ɗakin. Harararsa take yi a wulakanci, shi ko kallonta kawai yake yi cikin da mamakin abun da ya kawo ta. "Ba alkhairi ne ya kawo ni ɗakinka ba, Hakazalika babu abin alkhairi da zan yi tarayya da kai akansa. Ina mai maka albishir da cewa daga ranar da aka kai ni gidanka daga ranar ka yi bankwana da farin ciki. Sai ka ɗanɗani kuncin rayuwa wallahi sai ka yi nadamar kasance wa ta a matsayin matarka." Tana gama fadar haka ta fice daga ɗakin, karo ta yi da Ummi a falo, ɗauke kai ta yi tare da sakin tsuki ta fice daga ɗakin, don dama Aunty Laila ta zugo ta akan ta yi masu rashin mutunci daga shi har uwarsa. Cikin sanyin jiki Ummi ta zauna kan kujera tana tausaya wa ɗanta Mahmud. Domin ta san shi da sanyin hali da wuya ya yi magana akan abu. Ballantana wannan auren ta san sai Mahmud ya ji jiki a wajen Nabeela. Da a ce ƙaninsa Sadik ne to da za su yi daidai da juna. Don shi m kansa ba kanwar lasa ba ne, don ma Ummi da Abbi na taka masa burki, amma karya ne a taka shi ko a taka iyauensa ya ƙyale mutum ko waye kuwa. _Faisal_ Yana zaune a falonsa yana lissafin kuɗi, kasancewar sa ɗan kasuwa. Kausar ta shigo ɗakin ba sallama. Kallonta ya yi sannan ya ɗauke kansa lissafi da ya cigaba da yi. Harararsa take yi ta ƙasan idanu, shi ko kallon banza ma ba ta ishe shi ba. Tsawon mintinan ashirin ta gaji ta yi ficewarta, don ita dama Aunty Laila ba ta yi mata hudubar ta yi wa Faisal rashin kunya ba, saboda shi ɗan Mummy ne, kuma akwai mutunci tsakaninsu. Amma Mahmud kasancewar ɗan Ummj ne ya saka Aunty Laila ta zuga Nabeela ta yi masu rashin mutunci. _Sadik_ Yana zaune saman kujerar yana nazarin wani Shari'a da za su yi a kotu. Wasu takardu yaje dubawa wanda yake karanta muhimman abinda wanda ke kara ya sanar masa . Da sallama Nadeeya ta shigo ɗakin. Amsa mata Sallamar ya yi sannan ya ɗago suka hada Idanu. Kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kai ya cigaba da abinda yake yi. Ƙarasowa ta yi idanunta akansa ta ce. "Ina wuni Yaa Sadik." Ba tare da ya kalle ta b y ce. "Lafiya lau ya kike?" Ba ta san lokacin da Murmushi ya suɓuce mata ba , don ba ta yi tunanin zai kula ta ba, musamman da iyayen su ba jituwa suke yi ba. Duk da ta san shi iyayensa ba sa da matsala kowa ta sani ba ruwan Abbi haka Ummi ma, haka Mahmud da Zahrah. Dama shi Sadik ɗin ne ya fita daban kamar ba su suka haife shi ba. 'Gaskiya ba zan yi wa kaina sagegeduwa ba, tabbas Yaa Sadik haɗaɗɗen namiji ne, duk da cewar na san zan fuskanci ƙalubale daga wajen Abba da Umma da kuma Yaa Mansur. Amma ba zan yi sake na rasa wannan kyakkyawan saurayin a matsayin mijina. Walau dole na rungumi mijina in dai har zai so ni.' Haka ta dinga magana a zuciyarta. Shagala ta yi da kallonsa, ba ta san yana da kyau ba sai yau, ga shi yana matukar Kama da Zahra. Ji ya yi a jikinsa ana kallonsa don haka ya ɗago manyan idanunsa ya kalle ta, da sauri ta kau da kai cikin jin kunya. Shi kansa bai yi zaton za ta kalle shi da idanun rahama ba, sanida a gaban idanunta kwanakin baya ya yi wa Abba mahaifinta rashin kunya har don ya nemi zargin Abinsa, kuma sun sha dambe da Yayanta Mansura ba sa jituwa gara kowa da shi a wajen Mansur. "Lafiya dai ko?" Sunkuyar da kai ta yi tana addu'a Allah ya sa kada ya kore ta. Ga mamakin ta sau ta ga ya nuna mata gefensa kusa da shi ya ce. "Ki zauna." Kamar jira take ta zauna. "Make ke tafe da ke?." "Am fama Papa da Dada ne suka ce ki za mu shirya dinner party." "Ba na bukata." "Am to ko wani reception ba za mu yi ba?" "To ba auren soyayya ba ne to me za mu je yi wa wani reception ba shiri ba komai." Da sauri ta kalle shi tare da cewa. "Kenan kai ba ka so na?" "Ke kina so na ne?" Murmushi ta yi tare da cewa. Rufe fuskarta da tarin hannunta. Murmushi shi ma ya yi tare da cewa. "Yanzu ina tsaka da aiki gobe za mu yi magana kin ji?" Tashi ta yi tare da cewa. "Sai da safe." "Okay Allah ya bamu alkhairi." Har ta bude kofar za ta fita ta juyo ta kalle shi, ta ga ita yake kallo, da sauri ta fice, murmushi ya yi ya cigaba da abin da yake yi. _Zahrah_ Tana kwance kan gado sanye da wandon Pallazo purple colour top fara, gashin kanta tufke da ribbon ya ɗauka har gadon bayanta. Dada ke ta fama da ita akan ta tashi ta je part ɗin Hilal su yi magana, ƙi ta yi sai da Papa ya shigo sannan ta saka dogon Hijabinta fari ta nufi part ɗin sa. A hankali take tafiya tana taka step ɗin saboda ƙafarsa na yi mata ciwo bai gama warke wa ba don ba karamin duka ta sha ba Ta jima a kofar kafin ta sami ƙarin guiwar yin knocking. Jin shiru ya saka ta shiga falon, ba kowa dai sanyin A.C ke tashi da ƙamshin air freshener. Kamar za ta koma dai ta tuna dole sai Papa ya tambaye ta ya suka yi, don haka ba ta da wani zaɓin da ya wuce ta shiga bedroom ɗin sa. Knocking ta yi daidai lokacin da ya fito daga wanka ɗaure da towel a ƙugunsa, izinin shigowa ya bayar a tunaninsa Faisal ne . Tura ƙofar ta yi ta shiga bakinta ɗauke da sallama, ƙaramin towel ne a hannunsa yana tsane ruwan kansa towel ɗin fari kamar yadda na ƙugunsa ma fari . Gabanta ya faɗi ganinsa da ta yi ba riga sai towel dake ɗauke a ƙugunsa. Ya zuba mata rikitattun idanunsa masu firgitata. Da sauri ta juya za ta fice ta ji muryarsa ya ce . "Wait." *Ga mai bukatar karanta complete book 2 zai tura kudinsa Naira ɗari biyar ₦500. Za ku tura kudin ku ta wannan account number 2242538358 Zainab Abdullahi UBA bank. Sai a tura shaidar ta wannan lambar 09065327995* [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA NE* Page6️⃣4️⃣ Gabanta ne ya faɗi ganinsa da ta yi ba riga sai towel dake ɗaure a ƙugunsa. Ya zuba mata rikitattun idanunsa masu firgita ta. Da sauri ta juya za ta fice ta ji muryarsa ya ce. "Wait." Tsayawa ta yi ba tare da ta juyo ba, bayanta ya zuba wa idanu kafin ya ɗauke kansa daga kallonta. A hankali ya tako zuwa gabanta fuskarsa a murtuƙe, gabanta ya tsaya yana kallon ta kanta a ƙasa, dama ta rintse Idanunta jin ya kira ta. Ƙamshin da ta ji ne ya saka ta bude idanunta. Ta sauke shi akan faffaɗan ƙirjinsa da gashi suka kwanta luf a ƙirjin na sa. Da sauri ta rufe idanunta da rafin hannunta. Mamaki ne ya kama shi sau biyu kenan tana ganinsa ba kaya sai ta firgita, sai dai abun da ke ɗore masa kai shi ne. Yadda su Aunty Laila da Mummy da Umma suke cewa ƴar iska ce bin maza take yi, babban dalilinsa na yarda da cewa tana bin maza shi ne ranar da ya ganta kwance a falon tana murƙususu kayanta ya ɓaci da jini, Aunty Laila ta ce ciki ne ta zubar. Ga shi da ya ɗauke ta ya kai ta asibitin kuma Doctor ya tabbatar masa da cewa ciki ta zubar. A lokacin hankalinsa ya tashi sosai wanda har ya ba yi mata duka don ta fada masa wanda ya mata cikin ta ƙi faɗa. To macen da ta san maza me zai saka idan ta kalle shi haka take firgita, ko dai wani sabon munafurci ne. Ji ya yi ransa ya ƙara ɓaci kamar yanzu ne lokacin da abun ya faru. '"Open your eyes." A hankali ta buɗe idanunsa kanta a ƙasa. Haka kawai ransa yake sosuwa idan ya tuna da abinda ake cewa tana aikatawa, ko da ya ƙaryata ba zai ƙaryata Doctor ɗin ba, tunda aikinsa ne, ya kasa magana zafi kawai yake ji zuciyarsa na masa tare da jin haushin ta. Gajeren tsuki ya saki kafin ya ce. "Me kika zo yi a ɗakin nan?" Shiru ta yi masa kuma ba ta bude idanunta ta ba. "Okay na gane, wato kin kasa haƙura zuwa ranar da za'a kai ki ga mijinki shi ne kika ɗebo ƙafa kika kawo Mani kanki da kanki ko, saboda tsabar jaraba ko, to ba na buƙatar jikin na ki sai ki juya ki koma in da kika fito. Tsabar ɓacin rai da kalaman sa durkushe wa ta yi a wajen tana kuka, zuciyata na mata suya, wai me ya saka mutanen gidan nan suke yi mata kallon ƴar iska mai bin maza ne, yanzu har ta kai wanda aka aura mata yana yi mata wannan zargin. Maganarsa sun soke ta amma dai ta dake ta miƙe ta kalle shi ta kau da kai. "Zato zunubi ne ko da ya kasance gaskiya. Ba zan ce ku daina zargina ba, ku cigaba da zargina Allah ne shaida ta ban taɓa aikata fasikanci ba, babu wani ɗa namiji da ya taba rike ko da hannuna ne wanda ba muharramina ba." Tsawar da ya daka mata ne ya firgita ta sosai. "Kar ki sake fada mani wannan banzar maganar uban waye yake zargin ki, ki ba kin manta me Doctor ya faɗa ne da na kai ki asibiti.?" Kuka ne ya ci ƙarfinta wanda yake fitowa daga kasan zuciyarta, take numfashinta ya fara barazanar ɗauke wa. Dama ga ciwon ba wai ya sake ta ba ne, ga zazzabin dake jikinta suka taru mata. Zubewa ta yi a wajen numfashinta ya ɗauke, kallo ɗaya ya yi mata ya dafe goshi yana cewa. "Oh Allah Papa ka haɗa ni da aiki ka hada ni da wahala, dama na faɗa a baya duk wanda ys auri yarinyar nan na tausaya masa, ashe ni ne abun tausayi ba kowa ba, gaskiya ba zan iya ba." Ya fada yana nufar closet ɗin sa ya shiga. Bayan mintuna kadan ya fito sanye da riga da wando farare na barci. Sai ƙamshi tutarensa ke tashi a jikinsa. Kallon agogo ya yi ya ga karfe goma sha ɗaya na dare ne. Ƙarasawa ya yi wajen da take kwance, ganin ta suma ne ya saka ta ɗauko robar ruwa a fridge ya ɓalle murfin ya watsa mata. Ta ke ta ja wani ajiyar zuciya ta sakin numfashi da ƙarfi. Sai dai rawar sanyi take ta yi sakamakon sanyin dake ɗakin ya kure gudun A.C ita kuma ciwonta baya son sanyi, ga sanyin tiles da take kwance ga ruwan sanyin da ya zuba mata hakan ya saka jikinta ke kakkarwa har haƙoranta suna karo da juna saboda rawar sanyin da take yi. Ganin yadda ta jiƙe ne ya saka ya zare mata hijabin na ta da ya jike da ruwa . Nan ma ya ga kayan jikin na ta ya jiƙe, don haka ya fara ƙoƙarin zare mata rigar jikinta ta ta jiƙe, girgiza masa kai take yi alamar a'a amma bai kalli fudkarta ba, ga zazzaɓin jikinta ya dawo sabo. Don ba ta da karfin hana shi. Tana ji ya cire mata rigar jikinta sai bra fari da ta saka. wandon Pallazo da ta saka ma ya cire mata shi. Hawayen baƙin ciki ne ya ke gangaro mata a fuska. Shi ko tsaya wa ya yi yana kallon surar kikinta mai matukar ɗaukar hankali, ga fatarta dake santsi da ƙyalli har ɗaukar idanu take yi. Duk yawace-yawacen da ya yi a ƙasashen duniya, da jikin matan da ya gani bai ga surar da ta ɗauki hankalinsa kamar na ta ba. Gabadaya ya rasa meke damunsa. Ita kam kikinta kara zafi ya yi wanda cikin sauri ya ɗauke ta ya ɗora kam gadonsa. Gabanta ya fadi ta yinkura da niyyar tashi sai ta kasa. Barinta ya yi ya nufi wani corridor sai ga shi ya dawo da bowl da ruwa a ciki sai ƙaramin towel a hannunsa. Ɗago ta ya yi bayan ya haura saman gadon, bra ɗin ya ɓalle yayin da ta fashe da kukan takaici da bakin ciki. Daga ita sai pant ɗin jikinta kawai ya rage mata. Ƙirjinta ya zubawa idanu yana kallon su yadda suke tsaye ƙyam kamar za su tsokane masa idanu. Wani abu ya ji ya tsarga masa tun daga tafin ƙafarsa har ƙwaƙwalwarsa, abu ne da bai taɓa jin irinsa ba a rayuwarsa. Shagala ya yi da kallon ƙirjinta da suka saka shi wani yanayi, don duk ƴan matan da suke kawo masa kansu ba wacce ya ga surarta ya ɗimauta shi lokaci guda kamar na Zahrah. Sautin kukan ta ya ƙaru ganin yadda ya cire mata kaya yana kallonta. Sai a lokacin ya dawo cikin tunanin da ya shiga. Towel ɗin yake jiƙawa da ruwa idan ya ɗan matse yana shafa mata a jiki, saboda zafin jikin ya ragu. Babban abinda ya bashi mamaki da ɗore kai yadda jikinta suke a kame, saɓanin macen da ta san namiji. Don idan har mace ana taɓa jikinta dole zai fara sakewa amma ita ga jikinta a kame ƙirjinta ƙyam nipple ɗin ta ma kamar sun ɗan shige babu wata alama da ya nuna cewa namiji ya taba jikinta, da ace ta san namiji ba haka jikinta zai kasance ba ballantana ita da aka ce ta saba zubar da ciki. Tsayayyun ƙirjinta da ya gangaro wajen da towel daidai kan na shanunta ta tsayar da hannunsa yana gogawa cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara. Kan nonon na ta da ya ga kamar ya shige ne ya sa yatsunsa biyu ya ɗan janyo su, ƙara ta saki sakamakon zafin da ta ji. "Me nake gani ne, kuma me ke faruwa ne?" Ya faɗa a fili cike da mamaki a ƙirjin na ta ya kai kai hannu ya taɓa, nan ma ya sake tabbatar wa kansa sabo ne fil ba alamar an taɓa wasa da su ba su saki ba. Gabaɗaya kansa ya ɗaure, saboda ya san komai ba sai an faɗa masa ba, sai da ya gama shafa mata ruwan a jiki ya tabbatar zafin jikin ya ragu kafin ya tashi ya bar ta. Ba jimawa ya dawo da farar jallabiyarsa ya zira mata, sai dai har lokacin bai cire mata pant ɗin jikinta ba. Magani da bottle watar ya ɗauko ya bata. Kallonsa kawai take yi tana hawaye, ganin haka ya saka shi ya ce. "Za ki sha ko sai na ɗura maki." Jin haka ta sha maganin sai dai kanta kamar zai fashe a hankali take magana. "Wayyo Ammina kaina zai fashe." Ciwon kai mai tsanani take ji kallon pink lips ɗin ta yake yi da take motsawa tana kiran sunan Ammi da Dada tana cewa kanta. Kallonta yake yi yana mamakin yadda ya ga jikinta, wanda duk macen da take harka da maza harka da maza karya ne a ga jikinta haka, gefe ɗaya yana tuna raunin da ya yi mata na tabon da ya gani da bai gama warkewa ba, ya san dukan da ya yi mata ne. 'To ko dai haka yanayin jikinta yake ne?' Take sai barci ya ɗauke ta yana kiran sunan Yaa Sadik yana cewa ya zo ya ɗauke ta. _Dada_ Ganin har awa biyu Zahrah ba ta dawo ba ne ya saka ta kalli Papa ta ce. "Yarinyar nan fa ba ta dawo ba." "Wace yarinyar?" "Zahrah mana, daga ta je ta samu Hilal ko za su yi wani abu kafin tare wa fa shiru." Ganin bai ce komai ba ya saka ta maimaita maganar na ta. "Ka yi shiru a kira ta sai ta dawo." "Ki bar ta mana, ai tana tare da mijinta ne, ko kwana ta yi a wajensa ba laifi ba ne." "To ai ba ta tare ba." "Kada ki damu mijinta ne ko kwana ta yi kada ki ce komai." Ka san fa ba jituwa suke yi ba, ya tsane ta kada ya yi mata wani abun, ni wannan hadin auren da ka yi ina tausayin Zahrah ne yaron nan fa wallahi ni kaina tsoronsa nake yi akan lamarin sa baya son ta fa. Murmushi Papa ya yi tare da cewa. "Wannan hadin shi ne daidai za ki gane abinda ya sa na ce haka zuwa gaba, amma na tabbatar daga ranar da aka aura masa ita ba zai iya yi mata abubuwan da yake yi a a baya ba." "Allah ya sa haka." Da Amin Papa ya amsa yana murmushi. Zahrah kuwa barci ne mai mai nauyin ta ɗauke ta ba tare de ta shirya yin barcin ba. Shi kam kallonta kawai yake yi abubuwa da yawa ne sake a cikin ransa. Ga shi gabaɗaya surar jikinta ne ke masa yawo a cikin idanunsa da ƙwaƙwalwarsa ya kasa sukuni gabaɗaya, wani yanayi ne yake ji a jikinsa wa da bai taɓa jin irinsa ba a rayuwarsa. Kayanta ya tattare ya kai toilet ya zuba cikin washing machine. Kayan jikinsa ya cire ya yi wanka sannan ya fito sanye da bathrobe. Wasu kayan barcin ya saka sannan ya koma can ƙarshen gadon nesa da ita ya kwanta kasancewar tana farkon gadon ne. Bargo ya ja masu sannan ya rage hasken ɗakin. Madadin ya yi barci sai ya saka rintsawa, ba abinda yake masa yawo a idanunsa da ƙwaƙwalwarsa sai kyakkyawar surar jikinta. Awa ɗaya biyu shiru ba barci sai juyi yake yi a cikin bargo. Yanayin da yake ciki ba zai iya barinsa barci ba. A zuciyarsa yake cewa. 'Wai keke damuna haka ne, yarinya kamar mayya gabadaya tunda na kalle ta ta sukurkuta ni ta hana ni nutsuwa.' Tsuki yake ja lokaci zuwa lokaci zuwa lokaci har karshe biyun dare bai runtsa ba, daga karshe ya tashi ya sakarwa kansa ruwa sannan ya doro alwala ya zo ya gabatar da sallah. Sai ƙarfe huɗun asuba sannan barci ya yi nasarar ɗaukarsa. Haka ya saka bai farka da ba har ya makara sallar asuba. Ita dama tun da take rashin lafiya magunguna da take sha yake saka ta barci. Don kullum sai Dada ta tayar da ita sallar asuba, amma kafin nan da lokacin sallar ya yi take farkawa. Amma yau ita ma ta makara. Sai ƙarfe bakwai na safiya suka tashi. Don ita ta farka a hankali ta buɗe idanunta. Ganin ɗakin da take kwance ya saka komai ya dawo mata sabo. Kuka ne sosai ta dake da takaicin abinda ya yi mata, tana ji tana gani ya raba ta da kayan jikinta ya dinga wasa da jikinta da sunan wai yana taimaka wa zafin jikinta. In da Allah ya taimake ta bai cire mata pant ba da ya gama da ita. Kukan da take yi na ya saka shi ya farka, tashi zaune ya yi yana addu'a. "What's happen?" Banza ta yi masa ta mike tana harararsa, abinda ba ta taɓa yi masa ba kenan a rayuwarta. Kallon ta ya sake yi ya tabbatar harararsa take yi, ya cije lips ɗin sa na ƙasa ya yi tare da tashi ya shiga bathroom ganin lokacin sallah ya tafi . Sauri-sauri ya yi wanka ya fito, closed ɗin sa ya shiga ya shirya cikin ƙanana kaya dai ƙamshin tutarensa yake yi. Sallah ya tayar yayin da ita kuma ta yinƙura da ƙyar ta tashi, sai a lokacin ta lura da kayan jikinta. Sanin ba za ta iya fita haka ba ne ya saka ta tsaya tana jirsnsa sai cika take tana batsewa. Bayan ya isar ta kalle shi ta ce. "Kayana fa?" Kau da kansa ya yi kafin ya ce. "Ki ɗauro alwala ki zo ki yi sallah." Banza ta yi masa, ya ɗauka ba ta ji ba ne, sai ya daga kai ya kalle ta, ga mamakinsa ya ga tana tura baki. Tsuke fuska ya yi tare da cewa. "Ba magana nake maki ba ne, kika ce za ki yi mani taurin kai za ki sha wahala ne." Bathroom ta nufa ta ɗauro alwala ta fito, sai dai ba hijabin da za ta saka. Tsaya wa ta yi tana kallonsa, gane me take nufi ya saka shi cewa. "Kayan ki sun jiƙe har da hijabin ba na da hijabi anan." Ciki-ciki ta yi magana tana cewa. "Dama ai ba za'a samu hijabi ba, tun da karuwanka da kake kawo su ba sa sallah suke yi ba sai iskanci, ni dai wallahi Allah ya isa na abinda ka yi Mani a daren jiya." Mikewa ya yi tsaye yana mata wani kallo, sai a lokacin ta san cewa ashe Maganar ta ya fito ya ji ta. "Wa kike yi wa Allah ya isa?" Shiru ta yi gabanta na tsananta faduwa, don ta san tabbas idan ya rike ta ko bai sumar da ita ba sai ya bar ta kwance. "Daga na taimaka maki, kin warke har kina da bakin rashin kunya ko, wai ma uban me ya shigo dake ɗakina? Allah ya isa na banza da kofi, ai duk abinda na yi dake daidai ne, domin akwai igiyoyin aurena uku a kanki. Na auren ƙaddarar da aka ɗaura mani, da ba don haka ba kin isa na kalle ki a mace?" Cikin takaici ta ce mata suna suka tara, ban kai ka kalle ni mace ba, saboda ni ba ballagaza ba ce dake barin kowane jaki da doki su kalli jikina . Ba zan taɓa hada jiki ba, duk da kana mani kallon ƴar iska mai bin maza amma Alhamdulillah sai dai zargi ba wanda ya taɓa ganina tare de wani namiji ya rike ko da ƙumbata ballantana jikina, amma kai na ganka tare da mace a Kaduna kuna romancing ɗin juna babu kaya a jikinta kuna kissing lips ɗin juna, sannan na ganka da wata mace a garden tana zaune a saman cinyarka ban kira ka ɗan iska ba, to kai wata hujjar kake da shi a kaina? Ba zan taɓa hada jiki da kai ba, don ƙyamar hakan nake ji daga gare ka, kuma taba ni da janyo jiya ba zan yafe ba na ji na tsane ka." Idanunsa ya zuba mata cike da mamakin yarinyar. "Wato ni kike faɗa wa haka ba, to zan yi maki abinda ya fi na daren jiya mai kankat zan yi maki sai ki yi Allah ya isa da tushe, zan yi maki abinda ban taɓa yi wa wata mace ba, amma ke ina da lasisin hakan daga gare ki, dama abinda ya kawo ki kenan daren jiya saboda ba bakon abu ba ne a wajenki." Nufo ta yi gadan-gadan wanda hakan ya saka ta nufi kofar fita za ta fice, sai dai ta ga kofar a rufe da key. Jikinta ya soma rawa tana ja da baya ganin ya nufo ta, tana jikin bango Ya rankwafo saitin fuskarta ta rintse Idanunta. Abubuwa ne ke daure masa kai da lamarinta, yadda ya ake faɗa da yadda ya ga jikinta daren jiya, tabbas yana cikin duhun kai sai dai baya ƙaunar bin hanyar da zai gano gaskikiyar yadda take 😳 Zaharah Allah ya fitar da ke, idan ya gane cewa ke cikakkiyar buduwarwa ya samu budurcin ki da wane ido zai kalle ki. *Book 2 na Gabar cikin gida na kudi ne, za ki same shi akan Naira ɗari biyar kacal. Za ku tura kudin ku ta wannan account number 2242538358 Zainab Abdullahi UBA bank, sai a tura shaidar biya ta wannan lambar 09065327995* [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page6️⃣5️⃣ Abubuwa ne ke ɗaure masa mai da lamarinta. Yadda ake faɗa da yadda ya ga jikinta a daren jiya, tabbas yana cikin duhun kai sai dai baya ƙaunar bin hanyar da zai gano gaskiyar yadda take . Ƙamshin turarensa ya cika mata hanci, saboda rigarsa da ya saka yanzu ya fesa tutarensa. Ba ta aknkare ba ta ji ya gada jikinsa da na ta ya ce . "Maimaita abin da kika faɗa." Tsabar tsoro fitsari ne kawai ba ta yi ba. Wayarsa ce ta soma ruri wanda jin hakan ya saka ya nufa wajen wayoyinsa, sanin wayar kiran gaggawa ne ya saka ya duba tsadadden agogon hannunsa ya saka. A hankali ta buɗe idanunta ta ga yana saka takalmi, ajiyar zuciya ta sauke da karfi ganin yana sauri zai fita . "Don Allah kayana." "Suna cikin washing machine." Da sauri ta nufi bathroom ɗin, na ta duba ta ga kayanta da kayan da ya cire ya zuba don dama kowane safe mai mashi wanki yake zuwa yi. Ciro riga da wandonta ta yi sai hijabi da bra. Duk sun jike, haka ta ɗauko su ta fito. Idanunta suka sauka akan bindigar da ya soke a ƙugunsa. Ɗauke kai t yi da sauri ta nufi ƙofa, jin ta a rufe ta tuna ta juyo za ga yi magana kenan sai suka kusan cin karo da shi har sai dai gabanta ya fadi ganin yanayin fuskarsa a sauye daga gani bai ras nasaba da kiran waya da aka yi masa. Buɗe ƙofar ya yi ta fice da sauri tana rungume da kayan da ta cire sannan tana sanye da jallabiyarsa a jikinta. Addu'a ɗaya ta yi Allah ya sa kada ta hadu da kowa a babban falon gidan. Takun tafiya da suka ji ne ya saka suka juya suna kallon hanyar matattakalar. Mummy, Daddy, Abba, Umma, Aunty Laila, Mansur, Faisal, Nadiya, Maryam, Kausar, Nabeela. Duk suna falon suna yin breakfast. Sai dai ba Abbi da iyalansa, don dama ba su cika zuwa ba saboda matsalar da ke faruwa, sai an yi masu ba daidai ba, ga Sadik baya iya hakuri duk wanda ya yi wa iyayensa maganar banza sai ya mayar maka da martani duk girmanka kuwa. Gabaɗaya suka sake baki suna kallon Zahrah dake saukowa daga part ɗin Hilal, ga jallabiyarsa a jinkinta, ga Kayanta a hannu, kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci daga can ta kwana. Wani malolon bakin ciki ne ya tokare zuciyar Mummy. Aunty Laila ma mamaki ta takiaci ya lulluɓe ta, wanda har ta kasa yin shiru ta saka salatai tana kallon Zahrah. Hakan ya saka hankalin kowa dake wajen ya koma kanta suna kallonta. Ita kuma sai ta tsargu da kallon da suke mata, don duk wanda ya ganta da Kayanta a hannu ga rigarsa a jikinta zai yi tuninin wani abu. Wani kallon tsana Aunty Laila da Mummy suke yi mata, yayin da Aunty Laila ta ce. "Tsabar jaraba da sabawa da maza ya saka daga jin an ɗaura maki aure da mutum kin kwashi jiki kina binsa ɗakinsa don ya yi maki abinda kika saba ko? To burinki ba zai taba cika ba duk harkar kasuwanci kin iya su." Umma ce ta ce. "Burinta ba zai taɓa cika ba na nawa kuma? Ai daga ganin ta da kayanta a hannu ga ta sanye da rigarsa ai mai afkuwa ta afku." Kallon Mummy ta yi kafin kafin ta cigaba da cewa. "Ke da kike cewa za ki hana shi ya kasance ta kin makara domin mai afkuwa ta afku." Zahrah da sauri ta nufi part ɗin ta, gaisuwar da ta yi niyyar karasawa ta yi masu ji ta yi ba za ta iya jure jin mugayen kalaman su akanta ba. "Ai ba laifin kowa b ne laifin Hilal ne, tun da shi ma bai san ciwon kansa ba." Cewar Mummy cike da takaici. Aunty Laila ta ce. "Ai kar ki yi mamakin ba banza ya kula ta ba, uwarta ta koya mata kisisina, idan kika yi wasa sai yadda ta yi da Hilal kina ji kina gani, ko kin manta yadda uwarta ke iko da ubanta. Baya. Don baya son ɓacin ranta sai abinda ta ce yake yi. Ƙiri-ƙiri ta hana shi cin abinci a cikin mu sai dai na ta ita yaranta su ci, ranar Friday kawai take barinsa ya ci abinci a cikin mu shi ma don dokar Papa ne. Kika yi wasa sai sun raba ki da Hilal." Daidai lokacin yake saukowa daga downstairs, har yana tsalleke step, cikin sauri yake tafiya. Karasawa ya yi cikinsu ya gaishe su cikin girmamawa. Kowa ya amsa ban da Mummy. Ganin yanayin ta kuma ya san dama tun bayan da aka ɗaura auren nan take fushi, sanin idan ya tsaya zai ɓata lokaci ya saka bai yi mata wata magana ba ya fice yana sanar da su sauri yake. Da kallo suka bi shi ya tafi ya bar su da ƙamshin turarensa. Ƙwalla ne ya cika idanun Mummy, don tabbas tana son Hilal sosai fiye da sauran yaranta, don haka ba ta ji za ta yi saken da zai suɓuce mata. Abincin da ba ta iya ci ba kenan duk da lallaɓa ta da suka dinga yi. Ƙarshe tashj ta yi ta bar dinning area ɗin ta koma part ɗin ta. _Dada_ Tana zaune a falonta tana shan kunun gyada da ƙosai, Zahrah ta shigo da sallama. Sakin baki Dada ta yi tana kallonta. Direct ɗakinta ta nufa ta cire jallabiyar ta yi cilli da ita. Wanka ta shiga yi a bathroom ɗin ta dake cikin ɗakin. Ko da Dada ta shigo sai ta ga ba ta cikisai dai ta ji ƙarar ruwa a bathroom ɗin. Zama ta yi bakin gadon tana jiran fitowarta. Wanka take amma kuka ne kawai mara sauti take yi, tana tuna abinda ya faru a tsakanin su a daren juyae, yadda ya kalle mata jiki cikin sauki, tana ji tana gani ta kasa hana shi. Tuan yadda ya zubawa ƙirjinta ido kamar ya ga sabon halitta ta yi. Da yadda yau ya ce sai ya yi mata mai gabaɗaya akan ta yi masa rashin kunya. Jin haushin kanta kawai take yi kenan da ba don kiran wayar da ake yi masa ba da ya yi abinda ya faɗa da ita kenan. "Ba za ka taba samun jikina ba, ko da wasa ma ba zan yarda mu kasance mu biyu ba a waje daya ballantana ka samu galaba a kaina, na tsane ka mugu azzalumi." Alwala ta ɗora ta fito daure da babban towel. Doguwar riga ta saka bayan ta saka underwear. Hijabi ta saka sannan ta shimfida sallaya. Har lokacin Dada na ɗakin ba ta ce mata komai ba, sai dai ta fahimci ta sha kuka, sai dai ta karkata ga cewa ko Hilal ɗin ne ya kusanci Zahrah ganin yadda ta yi kuka ga kayan hukunta ta Kudundune ta taho da su. Maganar zuci take yi tana cewa. "Ikon Allah wanna yaron da nake yi wa kallon mishkilanci ba zai bari ya kalle ta ba shi ne har ya yi mata wani bun da ko kusa ba wanda ya yi tunanin. Ga uwa uba ba ta taɓa ganin Zahrah ta yi makarar sallah ba amma ita ce yau har gari ya waye. Duk da ta yi mamaki ganin yanayin tafiyar Zahrah bai sauya ba, sai sai ta tabbata ko bai shige ta ba ya kama hanya. Dole ta fara ba ta abubuwan da take tsoron ba ta su. _Asadullah_ Zaune suke a falonsa shi da Dr Isma'il, yana yi masa godiya sakamakon kudade masu yawa ya bashi kyauta, sakamakon ƙoƙarin da ya yi na tafiye-tafiye da aka yi na neman mata lafiya . "Na gode Yallaɓai Allah ya saka da alkhairi, ya tsare gabanka da bayanka, ya kare ka daga sharrin maƙiya." "Amin ya rabbil izzati." "Yallaɓai dama akwai shawara da nake son na baka." "Go ahead." "Dama akan Jidderh ce, tun da an yi bincike ƙasashen duniya ankai ta har yau ba'a gano matsalar ta ba mai zai hana a gwada na gargajiya ko na iskancin ko za'a dace." Shiru Asadullah ya yi na lokaci kafin ya ce. "To an yi bincike a asibitoci ba'a gane ba sai na gargajiya ne za'a gane?" "Ai Yallaɓai idan lalura ya kasance na jinnu ne ko sihiri ko maita asibiti ba sa sanin ko Meye, sai dai su ce ba komai ko da mutum na jin jiki ba za su taba ganowa ba, don haka na kawo shawara a gwada na Islamic." "To yanzu ya kake gani ina za'a kai ta." "Ba sai an kai ta ba, domin akwai wani Mallam Mamman aikinsa ne, in sha Allah na sanar da shi har gida zai zo ya same ta, ko ma mene ne zai sanar kuma zai yi mata magunguna da ayoyin Ubangijin talikai, in sha Allah za ta koma cikin hayyacinta." Cike da gamsuwa Asadullah ya ce. "Ba damuwa, yanzu ina son zuwa Katsina wajen kakannina da suka haifi Mahaifiyata, Dad ya sanar da Ni suna cikin damuwa, kwana biyu zan yi a can in sha Allah idan na dawo nan da kwana uku kenan sai ka kawo shi ya ganta ." "Allah ya dawo da kai lafiya ." "Amin ya Allah." Bari na tashi ina da marasa lafiya suna jira na a asibiti." Sallama ya yi masa ya tafi . Jidderh dake labe tana jin su ta sake ajiyar zuciya ta koma ciki. Tana tunanin yadda za ta aiwatar da shirinta bayan tafiyarsa. Tashi tsaye ya yi yana zaga falon, na tsawon lokaci . Kafin ya kalli ɗakin da su Jidderh suke, a hankali ya karasa yana knocking, kafin ya shiga tare da sallama, Jidderh na kwance kan sofa tana barci, gashin kanta sun zubo sun rufe gefen fuskarta. Anisa dake waya ta ga shigowarsa cikin rashin gaskiya ta yi saurin katse kiran wayar tana kame-kame, rashin gaskiya ƙarara ya bayyana a tare de ita. Kallon tuhuma ya yi mata na sakanni kafin ya ce. "Lafiya ?" Sosa kai ta yi tare da cewa. "Amm uhm la lafiya lau." Bai bi ta kanta ba ya nufi kujerar da ya ga Jidderh kwance ya ce. "Ta ci abinci kuwa?" Sunkuyawa ya yi tare da janye gashin da ya zubo ya rufe rabin fuskarta. Zama ya yi kan kujerar ya tattara gashin ya tufke da ribbon da ya zame daga kanta. Murmushi ya sake yana kallon fuskarta. Fita ya yi Anisa ta bishi da kallo tana takaicin fashin kulata da baya yi, idan ya yi mata magana to na Jidderh ne, ko yana zaune ta zo don su yi fira ba ta samun kansa. Wayarta ta duba ta kira lambar da suke magana, ta cigaba da magana abun ta. Yana fita ya kira Sulaiman a waya ya sanar da shi ya zo ya same shi. _Zahrah_ Zaune take a falon Dada inda Dada take ta fama da ita akan magungunan mata da take ta ɗinkira mata, ita kuma har da kuka ba ta so. Ba ta saurare ta ba ta miƙo mata robar wata zumar mata da wata roba dake da tsumin rake. "Za ki karba ki shanye ko sai na ɗura maki da kaina?" Tura baki ta yi tare da cewa. "Dada ni fa ba na son waɗan nan abubuwan in dai akan wannan mugun ne." "Waye mugun?" Ba ta ce komai ba ta kau da kai tana ayyana cewa ba abinda zai shiga tsakaninta da shi ballantana har ta yi abinda zai ji dad'i da ita." "Dalla shanye ki ajiye robar, da na san mijin na ki ba ƙyale ki zai yi ba ai da tuni na fara tsuma ki, amma yadda jiya ya rike ki kika kwana na tabbatar idan na kai ki ba ƙyale ki zai yi ba." Hajiya Bilkisu ƙanwar Ummin Zahrah ta yi sallama ta shigo, daga wajan Ummi take ta sanar da ita Zahrah na wajen Dada shi ne ta biyo nan. Cikin jin dadi Zahrah ta tashi ta rungume ta tana tambayar ina Amal, ta sanar da ita tana school zuwa anijma ko gobe Khalili zai kawo ta. Nan Dada ta kalle ta tare da cewa. "Yauwa tun da ke uwa ce za ta ji tsoron ki." Mika mata magungunan Dada ta yi tare da cewa. "Ga su ki tabbatar ta sunaye su duka." Tashi ta yi ta basu waje ta koma bedroom ɗin ta. Fuska babu wasa Hajiya Bilkisu ta tsuke fuska ta mikawa Zahrah robar, tana hawaye ta karba ta sanye tas, sannan ta mika mata ɗayar, shi ma ta shanye sannan ta mika mata wani cup da aka yi wani hadin nan ma ta bata, ta shanye tana kuka. Janyo ta ya yi ta rungume tana bubbuga bayanta alamar rarrashi, har sai da ta ji ta sassauta kukan da take yi sannan ta ɗago ta tana cewa. "Daughter ki yi hakuri kin ji, Yaya ta fada Mani komai na halin da kike ciki, da yadda auren ya kasance, da abubuwan da suka faru tsakanin Hilal ɗin da ke a baya duk na san komai." Nisawa ta yi tare da cewa. "Ki yi hakuri kin ji, ki rungumi ƙaddararki a duk yadda ya zo maki, kada ki watsawa tsofaffin nan ƙasa a ido, na san irin kaunar da suke yi maki ba za su yi abun da zai cutar da ke ba. "Aunty wallahi ba so na yake yi ba, wahala kawai zan sha a hannunsa, ina nan gidan ya azabtar da ni ina ga na tare a gidansa?" Rarrashinta Hajiya Bilkisu ta dinga yi tare da ba ta shawarwari. Ita dai ba abinda ta tsana ji take jin tsanarsa kamar idan ta tuna yanayin da da gan shi da wasu matan, duk da ba ta gan shi yana yin sex da su ba amma ba ta yi tuninin iya abinda da yake yi kenan ba. "Me ya saka bakya son sa, na ga duk in da ɗa namiji ya kai ya kai. Ba wai ina fada maki haka ba ne saboda na kwantar maki da hankali ba. Hilal namiji ne da kowace mace mai hangen nesa za ta yi fatan mallakarsa a matsayin mijin aure, yana da kyau da kwarjini sannan da kin ga idanunsa kin ga zarra, ga shi da ƙirar jaruman maza kuma zarata, kin yi mijin wimuce sa'a fa Daughter." Ta karasa maganar tana shafar gefen fuskarta. Ita kam ba ta ga nagartarsa da ƙanwar mahaifiyarta ke faɗa ba, sai dai ba ta taɓa fada wa kowa ta gan shi da wata a cikin wani yanayi ba, ta bar abun a zuciyarta. "Na san kina fargaba na cewa baya son ki ko? To ina mai tabbatar maki da cewa matukar za ku rike sirrinkan da zan baki duk taurin kai na ɗa namiji ko ƙaho ne a saman kansa sai ya dawo kasa yana bin ki." Daidai lokacin Dada ta dawo Hajiya Bilkisu ta kalli Dada tana cewa. "Na ga lokaci ya kure ba'a fara yi mata gyara da wuri ba, idan ba damuwa ko za ku iya bani ita mu tafi gidana nan da kwanaki uku sai na dawo da ita ta tare a gidan mijinta. Akwai wata maƙociyata kuma ƙawata tana gyaran amare sosai, za ta taimaka Mani wajen cigaba da gyaran a cikin kwanaki ukun ko hudu da suka rage mana." Shiru Dada ta yi kafin ta ce. "Ba matsala, idan Papa ya dawo zan sanar da shi, zuwa yamma sai ki aiko a dauke ta." Murmushi ta yi kafin ta ce. "Zan aiko Khalili ya ɗauke ta in sha Allah." Godiya ta yi mata sannan ta ɗauki handbag ɗin ta ta fice tana masu sallama Zanrah dai kuka kawai take yi, har ga Allah ba ta kaunar abubuwan da suke mata. Bayan fitar Hajiya Bilkisu da kamar mintuna talatin ta ji kamshin turaren sa, wanda ya haddasa mata faduwar gaba, ta juya ta kalli ƙofar, tsaye yake bakin ƙofar suka hada Idanu, fuskarsa kamar kullum a murtuƙe. Kallon daya ta yi masa ta ɗauke kai. Ƙsrasowa ya yi dadai lokacin da Dada ta fito tana kallonsa. "Ka ci abinci kuwa ban ga ka shigo yau ba." Yamutse fuska ya yi sannan ya ce. "An kira ni abokina matarsa ta haɗo kayan da akwatuna nan za'a kawo maki ne ko ya ya?" "Ma sha Allah, a kawo nan ɗin ai." Wayar Zanrah ce ta yi ruri dukkansu uku suka kalli wayar, ba suna da emoji aka yi seved sun lambar wayar. Ɗaga wa ta yi tare da karawa a ƙunnenta, Ammar ne don dama da emoji ta yi seved number sa. Magana take yi da shi a hankali, ko Dada da Hilal da suke falon ba mai jin abinda take faɗa. Da Ƙamshinsa ne ta ji ya ƙaru sosai don haka ta daga kai ba tare da ta cire wayar a kunnenta ba, ganinsa ta yi gabanta dab da ita fuskar nan a murtuƙe fiye da kullum. Idanun nan kamar wuta za su fito. *Book 1 ya kawo gangara book 2 na kudi ne za ku same shi akan Naira ɗari biyar #500. Ta wannan account ɗin 2242538358 Zainab Abdullahi UBA bank sai a tura shaidar biya ta wanan lambar 09065327995* [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page6️⃣6️⃣ Ƙamshinsa ne ta ji ya ya karu sosai, don haka ta ɗaga kai ba tare da ta cire wayar a kunnenta ba. Ganinsa ta yi gabanta dab da ita fuskar nan a murtuƙe fiye da kullum, idanun nan kamar wuta za su fito. Hannu ya mika mata alamar ta bashi wayar, ganin yanyainsa ya tsorata ta sai ta mika masa wayar, yana karɓa ya ji muryar Ammar na cewa. "Na ga kin canza mani masoyiya kwanan nan ba ki ɗaga wayata idan na messages ba reply, any problem?" "Ammar daga yau kada ka sake kiran wayar nan." Ya fada a kausashe, jin Muryar Hilal ya saka Ammar cewa. "Man wai barazana kake yi mani ne?" "Ba barazana ba ne gargaɗi ne." "Wai kai Meye matsalarka da yarinyar nan ne, akan idanuna na fa ranar da ba ce ta raka ni na gaida Ummi ka harɗe mata ƙafa, bayan haka ka daki bakinta, tun ranar na rike wanan abun da ka yi mata akan ido na ..." Katse shi Hilal ya yi da cewa "Ai da ka ɗauki mataki da ka san hakan ya zafe ka. Wallahi Ammar ka sake kiran wayar nan zan shayar da kai madarar mamaki." A fusace Ammar ya ce . "Wai me kake taƙama da shi ne, ba ka da iko da Zahrah ballantana ka yi Mani shamaki da ita , kuma aurenta zan yi ko da hakan zai kawo karshen abotarmu ne." "Okay don't be a loser." Daga nan ya karfe kiran wayar, ya duba in da take zaune rai a ɓace, sai dai bai ganta ba. Tana can bayan Dada ta tsaya don ta san halinsa idan ransa ya ɓaci komai na iya faruwa. Don haka ta tsaya kusa da Dada. Kallonta ya yi da idanunsa da suka rikide zuwa ja ya ce. "Zo nan." Ba ta motsa daga in da take ba, ta san dai dole sai ya wuce Dada zai isa gare ta, kuma Dada ba za ta bari ya taba ta ba. "Za ki zo ne ko ni na zo na same ki nan?" "Me ta yi maka, kake zare mata idanu haka, yanzu fa ba kamar baya ba ne , matsayin mata take a wajen ka, ya kamata ku zama masu fahimtar juna. " Cikin ɓaci rai har yana huci ya ce. "Dada wani fahimta kuma, ki duba da waya take yi da wani namiji a matsayin wai macen aure da?" "A'uzubillahi minash shaiɗani rajim, Zahrah ta yanzu ba ki san hakkin aure ba duk ilimin ki?" "Dada wallahi ba yadda kika dauka ba ne, tun ranar da aka ɗaura Mani aure, ko wayarsa ba na ɗagawa ko text message ba na masa reply. Yau ma na ɗauki kiran na sa me da niyyar na sanar da shi auren dake kaina ne." "To ka yi hakuri na san Zahrah ba za ta taɓa aikata abinda ba daidai ba." Bai tsaya sauraren wani zancen ba ya fice rai a ɓace. A Aljihun wandonsa ya saka wayar ya nufi parking space. Motarsa ya shiga ya fice daga cikin gidan. Kai tsaye gidan KB ya nufa kamar yadda ya sanar da shi matarsa ta haɗo kayan lefen. Gidan ya tsaya ya yi horn, maigadi ya bude masa gate ya shiga da motarsa , parking ya yi sannan ya kira KB a waya, ba bata lokaci ya fito ya shiga da shi cikin gidan. Nan ya ga babban falon ya cika da akwatuna, zama ya yi ɗaya daga cikin kujerun dake falon. "Na ga wat saura Zahrah." Bai tanka masa ba ya yi kamar bai ji shi ba. "Angon Zanrah ka sha ƙamshi, ya Amaryar ta mu ce.?" Nan ma shiru y yi masa kafin ya ce. "Mallam ba na da lokacin ɓata wa Meye dalilin kiran da ka yi Mani na zo." Daidai wannan lokacin Hafsat matar Kb ta fito zuwa falo. Ganin Hilal ta saki fara'a tana cewa. "Barka da zuwa ango." Ba yabo ba fallasa ya amsa mata. Ruwa da lemu ta kawo masa sannan ta gabatar masa da kayan da hado. Ta ware masa na sa akwatuna goma sha biyu, sannan ta ware masa na sauran yan uwan na sa kowace akwatuna guda takwas za ta samu , sarauniyar ka kuma akwatuna goma sha biyu ne na ta, kuma komai na ta ya fi na su tsada, don abokin ka ya ce su miliyan biyar ne za'a kashe wa kowacce, amma gimbiyarka miliyan goma ya ce idan na dawo za ka bani miliyan biyar, don 25 million ka bayar saura 5 million za ka bayar cikon na gimbiyarka " Kallon KB ya yi wato da ya ce kowace miliyan biyar shi ne ya ya sa aka kashe wa Zahrah miliyan goma. "Bani account number da zan saka maki, don bai isa ya ce ba zai bayar ba " Take ya tura mata miliyan biyar. Sai dai kasancewar motaras ba za su kwashi kayan duka ba, don haka sai KB ya fito da motarsa da taiamakon masu aikin gidan aka jera kayan a motocin. A yammacin ranar ne kuka Dr Khalil dan Hajiya Bilkisu ya zo ya dauki Zahrah, bisa umarnin Mahaifiyarsa. Dama Papa bai hana ba Abbi ma ya amince. A ranar da aka kai ta gidan Hajiya Bilkisu aka fara yi mata gyara ciki da waje ba ƙarya. Kuma Zahrah ta saki jiki sosai saboda ta hadu da yar Hajiya Bilkisu mai suna Amal, Kuma jininsu ya hadu dama. Ita ma ta ji dadin ganin Zahrah. A part ɗin Dada aka ajiye komai in da Hilal ya nunawa Dada na shi sannan ya nuna mata na sauran Nan fa Dada ta kira sauran matan gidan don su gani, sai sai ganin kayan ya saka jininsu ya kusan hawa. Sakamakon yadda Hilal ya hada kayan har da yaran Ummi wato Mahmud da Sadik. Babban ta tashin hankalin na su shi ne yadda suka ga kayan Zahrah da akwatunan da ya yi mata ga kaya masu tsada da aka zuba ciki, koma mai tsada ne aka zuba ga sarƙar gold da zobe da warwaro na zinari duk ya zuba. Mummy cikin bacin rai take cewa. Akan me kayan Zahrah za su fi na sauran yawa , da me ta fi su da aka kasa sakawa ya ko Yar Gold ce ita? Nan Dada ta fara faɗa dole suka watse, Mummy tsabar bakin ciki kasa magana ta bar wajen kamar za ta yi kuka, ganin yadda ya kashe wa Zharah kudi leshi masu tsada ya zuba Kowace daga cikin amaren dangin mahaifiyarta sun zo an kai kayan ɗaki da na kitchen don yin jere. Haka aka yi don ko Papa ne ya bayar da makullan gidan Hilal, su Hajiya Bilkisu da wasu ƙawayen Ummi zuwa jerin. Don Abbi ya yi kokari saitin kayan ɗaki biyu ya siya wa Zanrah. Tun daga kan kujera har gado da da sauran kayan ɗaki. Ɗakuna biyu aka yi mata jeren kayan ɗaki Kowa sai yaba kyau da tsaruwan gidan yake yi sosai, don gida ne kamar wata fada. Kitchen ma ta ji kayan kitchen na zamani masu kyau da tsada, don kudi Ummi ta bayar Hajiya Bilkisu suka je suka hado komai . Da kuɗin suka kare ta sake tura masu. Duk da cewar ita da Abbi ba sa farin ciki da auren amma ba yadda suka iya, haka suka hakura suka yi wa yaran na su addu'o'i ba dare ba rana , har sallar dare sukan yi suna kai kukansu ga Allah. Maryam ma an je gidan Mansur an yi mata jeran kayan daki da na kitchen. Nadiya ma an jera mata kayan ta a gidan Sadik in da Umma take ta masifa tana zage-zae. Gidan Mahmud Duk da kasancewar mahaifin Nabeela ne ya yi komai . Aunty Laila ba ta fasa fada ba, wai an kashe kudi akan auren da ba zai je ko ina ba. _Asadullah_ Fitowa ya yi daga part ɗin sa dake upstairs, Sulaiman na rike da trolley bag ɗin da zai yi tafiyar . Dakin su Jidderh ya tura ya ji a datse, kasancewar safiya ce y saka ba su tashi b. Ya ji ba dad'i sosai don so yake ya ga Jidderh kafin ya tafi zuwa tafiyar da zai yi hadin Katsina. Kamar zai yi kuka ya cewa Sulaiman. "Ba su tashi ba, ba na so na katse masu barci sai dai hakan bai samu ba. " Nisawa ya yi kafin ya ce "Doctor Isma'il ya ce zai kawo wani malami da zai dinga yi mata mata addu'a da sunayen Allah, ki za ta dawo hayyacinta." Jinjina kI Sulaiman ya yi ya kalli Asadullah ya ce. "Shawara mai kyau Allah ya dawo da kai lafiya ya ba ta lafiya ." Da Amin ya amsa yana yin gaba Sulaiman a binsa a baya. Wata bakar mota tinted glass ya nufa, shiga Sulaiman ya shiga mazaunin direba, don da shi kadai zai ke Dad ya ce dole su je da Sulaiman, bai yarda a Asadullah ya je shi kadai ba, hakan ya saka za su je su biyu da Sulaiman. *Bayan kwana uku* Rana ba ta ƙarya sai dai uwar ƴa ta ji kunyar, yau ne ya kama ranar da amare za su tare gidan mazajen su. A cikin kwanaki ukun nan Zahra ta canza ta yi kyau da sheƙi , fatarta ta yi kaishi kamar na auduha ga wani ƙamshi na musamman dake tashi daga jikinta, ko fisari ta yi wani ƙamshi ke fitowa. Idan ta shiga ɗaki sai ya kwana bai daina ƙamshi ba. Ko kusa da ita ka tsaya sai ƙamshin jikinta ya rabe ka. Hajiya Bilkisu ta bada umarnin a shirya ta a kai ta gidan tafarki, don zuwa daren nan kowacce za ta kasance a gidan mijinta . *Book 2 na kudi ne ki tura kudin ku ta wannan account number 2242538358 Zainab Abdullahi UBA bank, sai a tura shsidar biya ta wannan lambar 09065327995* [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA NE* Page6️⃣7️⃣ Hajiya Bilkisu ta bada umarnin a shirya ta a kai ta gidan tafarki, don zuwa daren nan kowacce za ta kasance a gidan mijinta. Ko da aka shiga ɗakin aka tarar da ita Kudundune cikin bargo zazzaɓi mai zafi ya rufe ta. Kuka da take yi har idanunta sun kumbura. Amal da ƙawayenta sai A'isha ƙawar Zanrah ce a tare da ita. Don ta ce ba wanda za ta gayyato, Amal ɗin ma da ta gayyato ƙawayen ta ba da izinin Zahrah ba. Ƙawar Zanrah daya ce A'isha sai kuma amininsu wanda Zanrah ke kira da amini, shi ma niya ya zo ta fita zuwa falo suka gaisa ya yi mata Allah sanya alkhairi. Duk yadda Amal da A'isha suka yi da ita akan ta ci abinci duk wunin ranar ƙi ta yi, ba abunda ta ci a cikinta. Wanka ma ta shirya ta gagara tashi. Hakan ya saka Amal ta je ta sanar wa mahaifiyar ta abinda ke faruwa. Jin jikinta da zafi ya saka Hajiya Bilkisu ta damu, ta san ba komai ya kawo mata wannan zazzaɓi ba sai yawan kuka da damuwa da ta saka wa ranta. Taimaka mata ta yi ta tashi suka shiga bathroom dake cikin ɗakin Amal ɗin. Ruwa mai ɗumi ta haɗa mata ta je ta daure ta yi wanka za ta iya, kuka kawai take yi. Kafin ta fito Hajiya Bilkisu ta fito mata da wani hadaddiyar leshi fari an yi masa ado da kalar golding da pink colour, sai gyale pink colour, doguwar riga ɗinkin bubu, sai sarka da ɗan kunne na gold ta aiye mata a saman kayan, da underwear farare sannan ta fita ta nufi kitchen don kawo mata tea, don an ce mata duk yau ba ta saka komai a ciki ba, ga shi yamma ta yi. Don ita ba ta sani ba ta fita zuwa kasuwa da kuma can gidan Hilal don kai wasu kayan kitchen ɗin ita da ƙawar Ummin Zahrah. Daƙyar take wanka don jikinta ba ƙarfi ko kaɗan, ba abinda yake saka ta bakin ciki da kuka kamar idan ta tuna cewa daga yau da shi kanan za'a kai ta gidan wannan mugun, da ya tsane ta. Sai da ta yi brush sannan ta sake wanke jikinta ta ɗauki towel ta ɗaura. Dakyar take tafiya ga yunwa ya ci ƙarfinta. Daidai lokacin Hajiya Bilkisu ta shigo rike da kofin tea. Man shafawa ta ɗan shafa sama-sama sannan ta saka underwear, Hajiya Bilkisu ta taiamaka mara ta saka rigar. Nan su Amal da A'isha suka shigo. Suka taya ta shirya wa dama an kira mai makeup don ta tsantsar mata makeup, sai zai fir ta ƙi yarda ta ce b ta so har tana kara sakin kuka. Hakan ya saka Hajiya Bilkisu ta sallame mai makeup ɗin ta tafi. Shayi ma ƙin sha ta yi dole Hajiya Bilkisu ta matsa mata sakiyar ta sha kadan . Amal ce ta yi mata simple makeup shi ma sai da ta ga ɓacin ran Hajiya Bilkisu sannan ta amince. Bayan ta gama mata sai ta yi kyau kuwa ƙaramin bakinta da ya kasance pink sai shinning yake yi. Takalmi da jaka golding ta saka. "Mu ke sai kiran waya ake yi wai ni ake jira na kawo ki." Wayarta ta ɗauka ta kira Dr Khalil akan ya zo ya kai su tun da yana gidan. Hannunta na rike cikin na Hajiya Bilkisu suka fita zuwa harabar gidan. Wajen motar Dr Khalil suka nufa, ita da Hajiya Bilkisu suka zauna baya, yayin da Amal ta zauna gefen Yayanta. Suna isa gidan kukanta ya ƙaru.daƙyar ta iya takawa Hajiya Bilkisu na rike da hannunta. Gabadaya ilahirin jama'ar gidan suna babban falon gidan. Nan ta samu waje ta rakuɓe kusa da Yaa Mahmud. Papa, Dada, Daddy, Mummy, Abba, Umma, Abbi, Ummi da Aunty Laila, kowa na falon. Sai sai kallo ɗaya za ka yi masu ka gane ɓaci rai da suke ciki idan aka cire Papa da Dada. Gefe suma ga Mahaifin Mummy da mahaifinta, sai mahaifin Umma da Mahaifiyarta, sai kuma Modibbo mahaifin Ummi da matarsa da mahaifiyarta. Sai tsohon mijin Aunty Laila wato mahaifin Nabeela da Kausar. Sai su amaren da angwayen kowa na nan an hadu. Papa ne ya fara buɗe taro da addu'a sannan ya yi masu nasiha daga amaren har an angwayen. Sannan ya mahaifin Mummy, Kakansu Hilal kenan ya yi masu masu nasiha sosai akan zaman aure da haƙuri. Sannan ya gargadi Mummy akan tayar da fitina ko saka idanu a cikin lamarin yaran matukar ba gyara ne za ta yi ba, ya kuma sanar da ita matukar ya ji wani matsala ya fito daga gare ta ranta ne zai ɓaci. Shiru ta yi tana sauraren sa tana kuma ayyana ba abinda zai sa ta bar Hilal ya zauna da Zahrah matukar tana raye. Sai mahaifin Umma ma ya yi masu na su nasihar ya kuma gargadi iyayen akan su cire idanunsu akan lamuran yaran. Don dama Papa ya sanar da su abinda ke faruwa a gidan da kuma dalilin hada auren, yana ganin ta haka ne zai gyara kuskuren da ya yi a baya, don fifiko da banbanci da ya nuna wa Sauran ƴaƴansa sune umul'aba'isin faruwar komai. Da ya nuna adalci a tsakanin yaransa da ba su tsinci kansu cikin kaso saba'in na wannan matsalar da suke fuskanta ba. Modibbo mahaifin Ummi ya yi nasa nasihar sannan aka ba wa iyayen damar fadar abinda suke da shi da za su faɗa. Kasancewar dukkansu ba wanda ke farin ciki da auren ya saka suka yi shiru. Ummi dai sai hawaye take yi. Abbi ne ya yi karfin halin cewa. "Hilal." Ɗago kai ya yi ya kalli Abbi ba tare da ya ce komai ba. Abbi ya cigaba da cewa. "Zahrah ba isashshiyar lafiya ce da ita ba, kusan kowa a nan ya san tana dauke da ciwon athma mai tsanani, wanda yakan uwan tashi mata lokuta da dama. Musamman lokutan sanyi don ciwon baya son sanyi. Ko hayaƙi ko kura na san dai ka sani kai ma ba sai na yi ta lissafa maka ba, wani lokacin ko kula take yi ko ranta ya ɓaci ba wuya ciwon ya tashi. Hakan ya saka na sa a raina ba zan aurar da ita ga kowane irin mutum ba, har sai wanda na ga ya cancanci zama da ita, kuma na sanar da shi yanayin ta idan zai iya ɗaukar ɗawainiyar ta kuma ya yarda zai kiyaye lafiyar ta sannan zan bashi aurenta. Sai ga hukuncin da Papa ya ɗauka na aurar da ita ba tare da sanin ya shirya hakan ba, kuma ba na bakin ciki da hakan, don na tabbatar akwai babban dalilin da ya saka ya aikata hakan. Kuma ba zai yi abu don cutar da daya daga cikin ahalin gidan ba." Nisawa ya yi kafin ya cigaba da cewa. "Na san ba ka son Zahrah kuma ba lallai k jure ɗawainiyar ta ba, sai dai ina rokon ka da ka rike ta amana fisabilillah ba tare da cuta ko cutarwa ba ko da ba za ka so ta ba, ko ba za ka yi mata kallon macen da kake so ba, ka bata kulawa a matsayin ta na ƙanwa a gare ka, na sani jini ba ƙarya ba ta samu wannan kulawar daga gare ka a gidan nan ba, to a yanzu ina son ka zame mata uwa uba Yaya jigo kuka Garkuwa a gare ta. Zahrah tana da rauni, ka yi hakuri da ita, idan ta saɓa maka ko bijire maka ka sanar da ni zan ɗauki mataki akan ta Allah ya yi maku albarka." Ya karasa maganar ƙwalla na cika Idanunsa. Jikin Hilal ya yi sanyi da kalaman Abbi sunkuyar da kai kawai ya yi ba tare de ya yi wata magana ba. Zahrah kukan ta ne ya ƙaru har ta ji numfashinta na neman ɗauke wa tashi ta yi ta nufi part ɗin Umminta, ganin haka ya saka suka ga alamar ba ta jin dadi za ta dauki maganin ta ne. Tana shiga madadin ta samu Maganin ta ko Inhelar ta shaƙa sai ta kwanta kawai ba ta nemi komai ba. A can kuwa ganin dare na yi ya saka aka ce kowane daga cikin angwayen ya ɗauki Amaryarsa su tafi Allah sanya alkhairi. Mansur ya mike tsaye Papa ya kalli Maryam ya ce . "Maryam tashi ki bi Mansur, ku yi hakuri da juna Allah ya maku albarka." Tana kuka ta tashi tsaye, Papa ya kalle shi ya ce. "Rike hannunta." Ba musu ya rike hannunta. "Kada ka taɓa sake hannunta ka rike ta duk rintsi da wuya kada ku rabu ka rike ta kenan har ƙarshen rayuwarku." Fita suka yi tana kuka suka fice daga falon. "Sadik ka kama hannun Nadeeya ku tafi, Ku yi hakuri da juna ku zauna lafiya, kowace mace ta yi hakuri da mijinta, idan da wata matsala za ku iya sanar da iyayen ku ko kuma ni da Dada, kada wacce ta yi yaji ta zo nan gidan." Kallon Nadiya ya yi tare da cewa. "Tashi ki bi mijinki Allah ya yi maki albarka." Tashi ta yi tana hawaye ta bi bayan Sadik, ya masu sallama, shi ma hannunta Papa ya ce ya rike tare da bashi amanarta kamar yadda ya yi wa Mansur. Yana rike hannunta sai ita ma ta ƙanƙame hannunsa da ƙarfi wanda sai da ya kalle ta, sai dai ba shi yake kallo ba kanta na ƙasa. Kallon Umminsa ya yi ya tana kuka, girgiza mata kai ya yi Alamar ta kwantar da hankali, gyada masa kai ta yi ya nufi hanyar fita suka fice, jama'a dake falon suna masu fatan alkhairi. A parking space Mansur dauke shirin ya wa motarsa key ya hango Sadik da ƙanwarsa suna nufo wajan motar Sadik ɗin, da alama su ma tafiya za su yi . Wani baƙin ciki ya cika masa zuciya cike da tsanar Sadik ya fito daga cikin motar ya nufi in da suke, har Nadeeya ta shiga gaban motar ta ji Muryar Yayan na ta na cewa. "Ke Nadeeya fito zan yi magana da ke?" Kallon Sadik ta yi sanin ba sa jituwa da Mansur, ba ta mance dambe da shi yi a parking space dun ba kwanakin baya. Ta ga Sadik ko kallonta bai yi ba. Ta buɗe murfin motar ta fito. "Yaya ga ni." Ba yadda na iya ne zan bar ki ki tafi da wannan, amma idan har ya yi maki wani abun da ba daidai ba ki kira ni, sai na koya masa hankali. Kada ki yi shiru ya zalunce ki, kuma kada ki sa a ranki zaman aure za ki yi da shi, ki ɗauka zaman wucin gadi ne, don ba zan taba bari ki zauna da shi ba ." Sadik yana jin sa bai tanka ba, sai ya ji Muryar Mansur na cewa. "Kai kuma idan ka sake wani abu ya samu ƙanwata sai na koya maka tarbiyya, kada ka ce za ka yi zaman aure da ƙanwata domin ba ka kai ba, kuma ba za ka kai ba." Sadik ya bude murfin motarsa y fito ya kalli Mansur cikin ido ya ce "Idan ban kai ba ga ƙanwarka nan sai ka je ka ɗauke ta ka ba wanda ya kai, ko an fada maka son ta nake yi ne da z ka ka cika ni da suratai na banza da wofi, ba don biyayya ga na gaba da ni ba har ka isa ka faɗa mani zancen banza ne?" "Nadeeya kina jin me yake fadawa yayanki ko? Kar ki manta har mahaifinki ya yi rashin kunya, idan ke ƴar halak ce ki nuna masa mahimmanci mahaifinki." Kuka kawia take yi ta tuna ranar da Sadik ya yi Abbi rashin kunya, amma ai Abbin ne bai kama girman sa ba, kuma ba dan da zai ga ana cin mutumcin iyayensa ya yi shiru. Nan suka cigaba da sa'insa har Mansur ya ɗaga hannu ya mari Sadik, shi ma kafin ya sauke hannu ya sauke masa marin dambe ne ya kaure, ga Kukan Nadeeya. Ma'ikatan gidan suka shiga tsakani. Jin an ce za'a sanar da Papa ya saka Sadik da Mansur kowa ya shiga motar sa Nadeeya m ta shiga ya yi wa motar key suka bar wajen. Maryam dai tana zaune har Mansur ya shigo yana huci. Papa ma ya sallami Mahmud Mahmud da Nabeela kamar yadda ya yi wa Sadik shi ma fatan alkhairi ya yi masu da sauran kakannin da suke gidan. Sai kuma aka zo kan Faisal shi ma aka bashi Kausar suka fita ana sanya masu albarka bayan mahaifinsu Alh. Nasir ya masu nasiha. Duk an sallame su ba kowa a wajen, Ummi ta mike ta nufi part ɗin ta. Papa ya kalli Hilal ya ce . "Me kake jira ka dauki matarka ku tafi mana ." Kallon Abbi ya yi tare da cewa. "Salis ka bashi matarsa su tafi ." Da to ya amsa ya mike ya fice, yayin da Papa ya ce ya bishi can su tafi Allah sanya alkhairi ya rike amanar da mahaifinta ya bash. Abbi na gaba cikin sanyin jiki yake tafiya, Hilal na biye da shi a baya. A falo ya yi sallama in da Abbi ya amsa, ya shiga in da ya tarar da Ummi na kuka sosai kamar an yi mata mutuwa. Ƙasa ɗayaejafa ya yi sai ya tsaya kallon Abbi. Ganin Hilal ya saka Ummi ta shiga dakin Zahrah, nan ta tarar da Zahrah kwance tana rawar sanyi Aunty Sai Amal da ta shigo ta sane t tana jera mata sannu. Don Sunyi Bilkisu na can. Zafi jikinta ya yi sida zazzaɓi mai zafi ya rufe ta. Ga numshinta sama-sama. Papa ne u shigo yana fadar dare na yi su tashi ku su tafi. Ganin ba ta ba iya tashi Papa ya kalli Hilal dake tsaye ya ce. "Ka ɗauke ta ku tafi, ba za ta iya tafiya ba. Amal ki bishi mota ki kai masa magungunan ta ." Ummi danne kukan da yazo mata take yi, don Allah ya sani tana tsoron zaman Hilal da Zahrah. Saboda wahalhalun da ta sha a hannunsa ballantana yanzu da aka aura masa ita bay son ta. Ga shi ba ta da isasshen lafiya. Kuka me tsanani Zahrah ta saka tana basu hakura tana rokon Papa akan ya raba auren mutuwa za ta yi . Hajiya Bilkisu ce ta ɗaura mata ɗankwali a kanta , sannan ta yafa mata gyale ta zira mata takalmi. Kallon Papa ta yi tare da cewa . "Ko za mu iya raka ta?" "A'a tabi mijinta kamar sauran ƴan uwanta." Tashi ta zo yi sai ta kasa tsayawa ta fada jikin Umminta tana sakin kuka mai tsuma zuciyar mai saurare. "Hilal ɗauke ta ku tafi ba ƙarfi a jikinta." Papa ya ce. "Eh haka ne dauke ta ku tafi ka bata kulawa don Allah." A hankali ya tako zuwa in da take tsaye jikin Umminta ta rike rigarta sai kuka take yi sosai. Ya kai hannu zai ɗauke ta sai ta ƙanƙame Ummi ita kuka Ummi kuka, wanda duk wanda ya gan su a wannan yanayi sai ya tausaya masu. "Ummina don Allah kada ki bari ya tafi da ni." Daƙyar Abbi ya cire hannunta daga jikin Ummi Hilal ya ɗauke ta kamar yadda Papa ya faɗa. Kai tsaye motaras ya nufa, in da Amal dake binsu da magungunan Zahrah ta bude masa murfin motar ya shigar d Zahrah, maganin ta bashi ya shiga ya yi wa motar key suka bar gidan. A hanya sai kuka take yi sosai, ba shiri ya ci burku tare da daka mata tsawa a hassle. "Ki rufe Mani baki tun ba sato ki na yi ba, wallahi kika fusata ni sai na baki mamaki a daren nan. Ki yi Mani shiru ba na son jin ko tari ne a cikin motar nan." Ajiyar zuciya ta sauke wanda ya yi daidai da sauyawar numfashinta. Gudu kawai yake yi a titin har ya karaso katafaren gidansa. Parking ya yi a bakin gate ɗin gidan wanda bayan na'urar dake jikin gate ta yi snapping lambar motar sai ga gate ɗin ya zuge da kansa, ya cinna hancin motar cikin gidan. Yana parking ya kashe Mota yana cewa. "Idan kin ga dama ki fito idan ba ki ga dama ba ki kwana a wajen sangartacciya kawai ." Ficewa ya yi ba tare da ya kalli inda yake ba ya shiga cikin gidan *Saura 3 page na kammala book 1, ga mai sha'awar cigaba da karanta wannan labarin zai biyu kudin book 2 Naira ɗari biyar #500 na saka shi a paid group, idan na kammala book 2 ya zama complete document kudinsa Naira ɗari bakwai ne #700 za ku tura #500 ta wanan account number 2242538358 Zainab Abdullahi UBA bank sai a tura shaidar biya ta wannan lambar waya 09065327995* [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *SANARWA* *Na samu tambayar cewa shin labarin Gabar cikin gida ƙirƙira na yi ko labarin wata ce da ya faru da ita, saboda labarin Zahrah ya yi kama da labarin rayuwar wata baiwar Allah dake Zamfara. To hasalima ba na da kowa a Zamfara ko ƙawa ba na da ita ba wanda ya bani labarin. Ƙirlireren labari ne ban rubuta shi dan wata ko wani ba, idan hali ya zo ɗaya to ba da niyyar hakan na yi ba. Arashi ne mai kashe auren wawa* Page6️⃣8️⃣ "Idan kin ga dama ki fito idan ba ki ga dama ba ki kwana a wajen sangartacciya kawai." Ficewa ya yi ba tare da ya kalli in da take ba ya shiga cikin gidan. Falon ya tsaya yana kallo ganin yadda aka tsara mata shi. Don kallo ɗaya za ka yi wa falon ka san cewa iyayen Zahrah sun narka dukiya wajen aiye mata kayan ɗakin. Don tsaya wa fadar haduwar falon ɓata lokaci ne. Upstairs ya wuce ya zauna a falon na sa, jingina bayansa ya yi da jikin kujera yana tuna abubuwa da suka faru yau. Ransa a jagule yake tura hannu yana yamutsa gashin kansa. Maganar Abbin Zahrah ke masa yawo a cikin kansa in da yake cewa. 'Na san ba ka son Zahrah ba lallai ka jure ɗawainiyar ta ba, sai dai ina rokon ka da ka rike ta da amana fisabilillah ba tare da cuta ko cutarwa ba ko da ba za ka so ta ba, ko ba za ka yi mata kallon macen da kake so ba, ka ba ta kulawa a matsayin ta na ƙanwa a gare ka na sani jini ba ƙarya ba, ba ta samu wannan kulawar daga gare ka a cikin gidan nan ba. To yanzu ina so ka zame mata uwa uba Yaya, jigo kuma garkuwa a gare ta. Zahrah tana da rauni ka yi hakuri da ita, idan ta saɓa maka ko bijire maka ka sanar da ni zan ɗauki mataki akan ta Allah ya yi maku albarka ' Ya tuna yadda Abbi ya karasa maganar ƙwalla na cika masa idanu. Haka da Hilal ya tuna sai jikinsa ya yi sanyi, ya ji bai kyauta ba. A hakikali ya mike tsaye ya nufi downstairs, ƙofar falon ya bude ya fice ya nufi motar da ya shigo da ita. Buɗe murfin motar ya yi ya ganta a sume, hannu ya kai ya ɗauko ta kamar ƴar Baby cikin gidan ya koma da ita, har upstairs ya haura da ita. Bedroom ɗin ta ya shiga da ita, kwantar da ita ya yi kan gadonta. Kallonta ya yi na tsawon mintina biyu, kafin ya yi magana . "Oh Allah Papa ka haɗa ni da aiki, yanzu mata aka kawo mani ko majinyaciya ni ne mai jinyar.?" Fita ya yi ya nufi motaras ya ɗauko ledar magungunan ta da Amal ta kawo masa. Komawa ciki ya yi ya rufe kofar falon ta ciki. Upstairs ya koma zuwa bedroom ɗin ta. Sai sai lura da sumewa ta yi ba wai ciwon ne ya tashi ba ya saka ya ajiye Inhelar da ya ciro. Bottle watar ya ciro cikin fridge dake cikin ɗakin na ta. Zama ya yi bakin gadon tare da matsala kusa da ita, bai yi tuninin zazzaɓi ma akwai shi a jikinta ba, duk da jikin na ta ya gashe. Robar ruwa mai sanyi ya watsa mata a jiki, in da ta farfaɗo a firgice tana kuka mara sauti, wanda Muryar ta dakushe saboda kukan da ta sha, ga idanu ya kumbura ga yunwa ya ci ƙarfinta. Sanyin da ya ratsa ta ne ya saka ta ƙanƙame shi da ƙarfi ta shige jikinsa tana kuka tana magana da Muryar ta da ta dakushe. "Ummina ki taimake ni kada ki bari ya tafi da ni, Ummi don Allah, baya so na Ummina tsane ni don Allah ki yi wa Papa magana ya raba auren nan, ni ma ba na son shi na tsani ganinsa." Sai kuka take yi tana ƙara ƙanƙame shi da alama ba ta cikin hayyacinta. "Ummina sanyi nake ji, Ummina riga ta a jiƙe take ki cire mani ki lulluɓa Mani bargo." Ta yi maganar har haƙoranta na kakkarwa. Tana kiran a cire mata rigar. Idanunta har lokacin a rufe kuma a kumbura Cire mata rigar ya yi cikin hikima da dabara, sai dai ya rage daga shi farin bra da farin pant. Ga wani sihirtaccen ƙsmshi dake fitowa daga jikinta. Ga fatarta dyai glowing take yi. Kau da kansa ya yi da suri daga kallonta ganin ya shiga wani yanayi daban. Ƙoƙarin zare jikinsa daga nata yake yi, ita kuma sai ta kara shigewa jikinsa ta rungume shi tana cewa. "Ummina ba zan bishi ba ina tare da ke ba mai raba mu. Sanyi Ummi me ya jika mani jiki ne? Ummina ki cire Mani bra ki saka mani wani rigar sanyi." Gabadaya bata cikin hayyacinta ga zafin zazzaɓi dake saka ta sambatu. "Bra ɗin jikinta ya ɓalle mata, take na shanunta suka bayyana da suke tsaye ƙyam ba su rankwafo ba ballantana su zube, mantawa ya yi da halin da take ciki ya zubawa ƙirjin na ta idanu, duk yan matan da ya saba ganin kirjinsu bai wanda ya ɗauke masa hankali kamar na ta, wani abu ya ji yana fisgarsa game da ita, wanda ya ji shi tun daga ƙwaƙwalwa har tafin ƙafarsa. Pink lips ɗin ta dake rawa ya dubawa idanu, bai san lokacin da ya kai bakinsa saman lips ɗin ta ba. Kissinga na ta yake yi cikin ƙwarewa, tun daga lips ɗin ta har tongue ɗin ta yake tsotsa cikin wani irin salo da shauƙin da bai taɓa jin irinsa ba a rayuwarsa. Daɗin lips ɗin na ta na musamman ne wanda ya ji ya daga banban da na sauran matan da ya sani. Jin bakio al'amarin da ta ji ne wanda ba ta taɓa jinsa a rayuwarta ba ya saka ta buɗe kumburarrun idanunta da suka yi mata nauyi ta sauke akan rikitattun idanunsa da suka fara janza launi zuwa ja. Gabanta ne ya yi muguwar faɗuwa sakamakon tuna a in da take, dama ba tare da Umminta take ba. Ƙoƙarin ƙwatar kanta take yi ta kasa don jikinta ba ƙarfi ko na sisin kwabo. Ga yunwar da ya galabaitar da ita. Ganin tana kokarin zame jininka ya sa ya kare ƙanƙame ta yana yawo da harshensa a cikin bakinta. Hawaye ne ke gangarowa daga cikin Idanunta, ta fawwalawa Allah lamuranta. Ƙamshim dake jikinta yake shaka wanda ke ƙara masa kaimi wajen abinda yake yi mata. Hannunsa daya ya sa ya shafa lallusan gashin kanta wanda ta ƙi yarda ayi mata kitso. Har ya gangaro zuwa dogon wuyanta da ƙirƙirjinta. Har lokacin bai daina shan bakinta ba, jikinsa kara rawa ya yi daidai lokacin da ya sauke hannunsa akan lumtsatstsun na shanunta kamar an hura balloon. Jikinsa rawa ya fara yi sosai ya fara fita hayyacinsa. Ya shiga wasa da canser na shanunta yana murza su son ransa. Kuka sosai take yi ganin ba Hilal ɗin da ta sani ba ne yau a tare da ita. Ga jikinsa sai rawa yake yi kamar mazari. Nipple ɗin ta yake murzawa wanda ya sa ta kara sakin kuka zafi da takaici. Breast ɗin ne yake kara zautar da shi. Zare bakinsa ya yi daga cikin nata ya kai kan cikakkun Breast ɗin ta dake rikita shi ya fara tsotsa kamar jaririn da ya kwana biyu bai sha nono ba. Yana shan nononta ɗaya yana wasa da ɗaya, kuka take yi tana kokarin ture shi amma ta kasa, sai kuka take da Muryar da ya gama dakushe wa. Wasa yake yi da ita son ransa ya zauce akan ta abinda bai taba zaucewa akan wata mace ba, duk da cewar mata su suke kawo masa kansu da kansu za su yi cire kayan a gaban sa bai taba rikicewa haka ba, ko ya fita hayyacinsa don ya yi romancing ɗin mace, amma ita iya ganin jinkinta kawai ya rikita shi . Gabadaya ya gama zaucewa akan yarinyar ya fita hayyacinsa. Ƙoƙarin zare mata pant yake yi, tana girgiza masa kai alamar a'a amma ina bai ma san halin da take ciki ba, baya ji baya gani. Sai da ya raba ta da pant ɗin jikinta ne ya kai hannunsa ƙasanta dake wadace da ruwan ni'ima. Sake gigicewa ya yi ya saka yatsarsa ciki ya ji ta gam. Da mamaki ya ɗaga kai ya kalle ta da idanunsa ke rufe tana kuka tana girgiza masa kai. Sake tura yatsarsa ya yi ko za ta shige sai ya ji ta gam. Abin ya bashi mamaki ta ya hakan za ta faru, wacce har ta taɓa yin ciki ne zai ji ta haka. "'No ba yadda hakan za ta kasance." Ya fada yana. Sake gwadawa a karo na uku, sai dai wannan karo ya yi niyyar tabbatar wa daga waje ne take a haka ciki a buɗe yake ko kuwa gabaɗayannta haka take. Ƙarar azabtar da ta saki ne ya saka ya kalle ta da sauri don tabbas wannan abun da ya tabo ya tabbata budurcinta ne ya taba. Ba ta rasa shi ba ta kasance cikakkiyar budurwar da ta kare mutuncinta na ƴa mace ba ta yarda wani ya raba ta da shi ba ganin yadda take kuka ne alamar zafi take ji ya saka ya cire yatsarsa daga wajan. Cikin sanyi jiki ya mirgina gefenta ya kwanta, idanunsa na kanta ko ƙyafta idanu baya yi. Bargo ya lulluɓa mata ya rufe ta da shi bai ma tsaya neman kayan zai saka mata ba, ficewa ya yi daga ɗakin abubuwa da yawa na masa yawo a ƙwaƙwalwarsa. A sanyaye yake tafiya har ya shige ɗakinsa. _Asadullah_ Kwana biyu ya yi a wajen kakanninsa, sun yi matukar farin ciki da zuwansa. Sun nuna damuwa akan rashin jin sa da ba sa yi a waya. Kasancewar Dad ɗin sa ya ɓoye masu ya ce baya kasar aiki ne suka yi masa yawa. Don Haka shi ma ya amsa da aiki ne suka rike shi. Ranar da suka cika kwana uku suka shirya dawowa. Suna kan hanyar dawowarsa kudin su shigo cikin gari ne suka yi karo da wata mota, sai ga motar bayansu ma ta dake su ta baya. Wanda hakan ya saka motarsu ta kangara gefen titin, sai dai duka masu motocin ba wanda ya tsaya suka wuce suka bar su. In da Allah ya taimake su dukkansu sun ɗaura belt ba wanda ya fita daga cikin motar, duk da motar ta kwararraɓe. Cikin ikon Allah suka fito daga cikin motar, kasancewar ba su da nisa da gari ya saka Sualaiman kira wani a waya, ya sanar da shi in da zai zo ya same shi. Ashe ma yana kusa da su. Nan ya zo ya tarar da su ya ɗauke su, duk da bai gane Asadullah ba sabods har yau bai fita da yanayin da za'a gane ko shi waye. Har aka kai su unguwar suka shiga cikin gidan. Yana shiga gidan ko zama bai yi ba, ya kira Doctor Isma'il ya sanar da shi ya zo da Mallamin ko zuwa dare ne. Sulaiman jikinsa ya yi sanyi,sosai da hatsari da suka yi. Bayan sun ɗan huta ne ya shiga dakin da su Jidderh suke amma ba Anisa sai dai Jidderh kawai take zaune ta rakuɓe. Bayan ya duba Anisa ba ta gidan ransa ya ɓaci sosai da rashin samun ta. Abun takaicin ma tun ranar da ya wuce Jidderh ke sanye Da Kayan da ya same ta da shi yanzu. Da alama yau kwana uku kenan ba ta yi wanka ba, ransa ya ɓaci sosai da abun Gashin kan Jidderh na ga shi nan a hargitse ba'a gyara mata ba. Dafa kafaɗarta ya yi ta ɗago kai ta kalle shi, ransa ya ƙara ɓaci sakamakon ganin busashshen hawayen dake gefen fuskarta. Ganinsa ta yi ta mike tsaye tana kallonsa kamar kullum ba magana dai dai ido, murmushin karfin hali ya sakar mata. Sai ya ga har ta ɗan yi rama a kwanaki ukun da baya nan. Ganin yanayin da take ciki ya tabbatar masa da yunwa take ji. Kuma ba komai take yi ba ita Jidderh, wanka sai an taiamaka mata, saka kaya ma, abinci ne kawai ta kan iya ci da kanta. Fita waje ya yi rai a ɓace, ya samu kuku, tambayar sa ya yi akan ba abicin da za'a ci ne, nan Kulsum ke sanar da shi kwana biyu baya ganin Anisa ko ya yi knocking a dakin sai dsi Jidderh ke budewa amma ba za ta fito ba sai ta koma ciki. Wani lokaci idan ta fito sai dai ta sha ruwa da lemu. Ransa a ɓace ya dauki waya ya kira lambar Anisa. Sai da ta kusa katsewa ta ɗaga, gaishe shi ta yi bai amsa gaisuwar ba, ya ce. "Kina ina?" "Ina gida." "Wane gidan?" "Oh yallaɓai ka dawo ne, ga ni nan dawowa na dan fita dubiya ne." "Look Anisa kike ko wa, na dauke ki aiki ne saboda ki kula da yarinyar nan kafin ta samu lafiya, amma amma kika bar ta cikin datti?" "Ka yi hakuri Yallaɓai ga ni nan dawowa." "Idan har ba za ki iya ba ko kin gaji ne you can go, amma ba zan ɗauki wanna hanayar da kika dauko ba." Hakuri ta dinga bashi ya katse kiran wayar. Ba dadewa ta iso ta tarar da ya saka Jidderh a gaba da kansa yake bata abinci a baki tana ci. Sallamr ta kawai ya amsa daga nan bai ko kalle ta ba ballantana ya amsa Barka da dawowa da take yi masa. Tashi ya yi ganin Jidderh ta ƙoshi. Har ya kai bakin matattakalar ba tare de ya juyo ba ya ce. "Ki tabbatar ta yi wanka an gyara mata gashi ta fito yadda ya dace." "An gama yallaɓai." "Waye ba lafiya?" "Ƙanwar mahaifiyata ce, aiki za'ayi mata na je kai kuɗin." Account number ta ya lalubo ya tura mata miliyan daya wai ta tura masu a siye magani. Godiya ta yi masa ya nufi upstairs. Wani kallon tsana ta yi wa Jidderh kafin ta ja hannunta suka shiga cikin bedroom. Da misalin karfe takwas da rabi na dare Doctor Isma'il ya tare da Mallam Mamman. Nan ya kalli Jidderh ya tabbatar da sihiri ne a jikinta, bisa la'akari da labarin da Doctor Isma'il ya bashi ya fahimci cewar an juya mata ƙwaƙwalwa ne." Manyan gallam na ruwan zamzam da aka saka ganyen nagarya ya ce a bata ya zama ruwan shan ta. Da magunguna da za'a ba ta ta shi duka ya bayar da sannan ya bayar da man shafawar ta wanda ya yi mata addu'o'i a cikin man shafawa ya ba ta da sabulun wanka. Ya ce in sha Allah nan ba da dadewa ba za ta samu lafiya. Bayan tafiyarsa ne Sulaiman ya dawo gidan, bayan sun gaisa ya ba ga kamar akwai magana a tare da shi, don haka ya ce su tafi sama. Kasancewar Anisa d Jidderh na a wannan falon na ƙasa. A falonsa da ke upstairs suka zauna, Asad ya kalli Sulaiman ya ce. "Akwai wata matsala ne?" "Yallaɓai akwai babanbu Matsala." Tattara nutsuwarsa ya yi sanan ya kalli Sulaiman yana jiran jin me zai ce. "A wannan kebe kanka da ka yi saboda maƙiyanka ya zama kamar shukan gyaɗa ne s gaban kurege." "Me kake nufi?" "Wannan hatsarin da ya faru da mu a hanyar mu ta dawowa kamar hari ne aka kai maka." Da mamaki ya kalle shi kafin ya ce. "Me ya sa ka yi tunanin haka, na ga ba Wands ya san in da nake sai mutane huɗu, Dad, Barrister Haris, Doctor Isma'il sai Anisa." Jinjina kai ya yi tare da cewa. "Tabbas a cikin akwai wanda ya ke kokarin ganin bayanka. " "Ba na tunanin a cikin su ne domin Meye dalilin yin haka daga gare su ba. Dad mahaifina ne, ba zai cutar da ni ba, Barrister Haris kuma amintaccen lauya na ne, wanda ya ke kula da dukiyata. Doctor Isma'il kuma na aminta da shi ba zai cutar da ni ba. Anisa ba ta sanni ba labari na kawai take ji da dalilin Jidderh ta fada haduwa da ita " Kallonsa Sulaiman ya yi kafin ya fuzrzar da iska mai zafi kafin ya ce. "Ko ma waye a cikin wadanda ka Aminta da su ne, watakila yana cikin maƙiyanka da suka cutar da kai a baya, watakila yanzu aka siye su za'ayi amfani da su don a cutar da kai. Sualaiman na gama fadar haka ya yi masa sallama ya fice. *Saura page guda biyu na kammala book 1, book 2 na kudi ne za ki same shi akan Naira ɗari biyar ₦500 kacal. Idan na kammala ya zama complete document kudin sa zai kama Misra dari bakwai ₦700 ne, za ki tura kudin ki ta wannan account number 2242538358 Zainab Abdullahi UBA bank sai a tura shaidar biya ta wannan lambar 09065327995* [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA NE* Page6️⃣9️⃣ "Ko ma waye a cikin waɗanda ka Aminta da su ne,watakila yana cikin maƙiyanka da suka cutar da kai a baya, watakila yanzu aka siye su za'ayi amfani da su don a cutar kai. Sulaiman na gama fadar haka ya yi masa sallama ya fice. _Mansur_ Bayan sun gama rigima da Sadik gidansa ya nufa, shi kadai sai masifar yake yi akan ba zai taɓa barin Sadik ya zauna da Nadeeya ba dole sai ya sakar masa ƙanwa. Maryam ta kalle shi da damuwa ta ce. "Yaa Mansur don Allah ka yi hakuri, ka janye kudirin cewa sai ka raba auren Yaa Sadik da da Nadeeya. Ka bar su watakila sai..." Tsawar da ya daka mata ne ya saka ta yin shiru, tana tausaya wa kanta don Mansur masifaffen mutam ne." "Wace ce ke da har za ki yi kokarin dakatar da ni akan kudirin da na yi, ke kanki ba ki ishe ni kallo ba ballantana zantukan banzar ki su yi tasiri akai na, banza sakarya kawai." Ranta ne ya ɓaci, domin ba ta yi niyyar tayar da hanakilin Mansur ko bijire wa aurensa ba, za ta yi biyayya su zauna lafiya saboda ba wata rashin jituwa a tsakanin iyayen na su, kowa ya san akwai shakuwa tsakanin Daddy da Abba. Haka Mommy da Umma, ba su yi bakin cikin hadin su ba. Kuma kowa ya san ba rashin jituwa tsakanin Maryam da Mansur, girmamawa ce kawai har fira sukan yi. Amma daga ranar da aka aura masa ita yake jin haushin ta. Maryam ba ta da masifa ko mugun hali, amma idan aka tsokane ta ba ta barin mutum. "Iskancin banza kawia." "Ina fatan dai ba da ni kake yi ba ko?" "Idan dake aka yi sai me? Ke da ke nake yi." "Wallahi ni kam ba ƴar iska ba ce." Ta fada cike da ɓacin rai. Daidai lokacin da ya yi horn maigadi ya wangale masa gate ɗin gidan. Parking ya yi tare da cewa. "Na ce waye ɗan iskan." "Ko ma waye ya san kansa." Ta fada tana ficewa daga motar. Da mamaki ya saki baki yana kallonta." "Lallai zan ci uban yarinyar nan." Da sauri ta nufi kofar da take tunanin nan ne kofar shiga falon. Tana murda handle ɗin kofar ta ji ta bude. Shiga ta yi bakinta ɗauke da sallama. Fada ta yi tana cewa. "Wannan wace irin rayuwa ne, ba 'yan kawo amarya na kowa, sannan wanda aka ce ango ya rufe ni da masifa sai baƙin tai yake yi a daren farko?" Da Karfi ya banko ƙofar yana cewa. "Na ce waye ɗan iskan?" Ba tare da Fargaba ba ta ce. "Na ce ni ba yar iska ba ce wallahi, ɗan iska ai shi ya san kansa." Kafin ta rufe baki ya ɗauke ta da mari, wanda sai da ta faɗi, ganin ya yo kanta zai dake ta ta ja baya, don idan ba ta kare kanta ba ta san za ta sha wahal ya saka ta yi kokarin ɗaukar wata yar tukunyar fulawa da ta gani a gefenta. Jifansa ta yi a goshi wanda tukunyar ta fashe a goshinsa sai ga jini na zuba. Tsaro ya kama ta ta fara kuka tana cewa. "Don Allah ka yi hakuri ban san yadda aka yi har..." Ƙasa ƙara sawa ta yi sakamakon ƙwallo da ita da ya yi, daka nan ya far dukanta, ganin zai illata ta ya saka ta yi karfin halin sake fuskar wata tukunyar fulawa ta jefa masa, sai dai cikin zafin nama ya goje tukunyar ta daki bango ta tarwatse, cikin sauri kafin ta yi wani yunkurin ya damƙowuyarta da hannunsa ya shaƙe ta, jin shaka tun kafin ta galabiat ta gantsara masa cizo a hannunsa, da ƙarfi ta datse masa fatar wanda har sai da jini ya fito. Tsabar zafin da ya ratsa shi ne ya saka ya sake wuyanta, jini ya gani ya sake yo wa kanta gadan-gadan, tana ganin haka ta mike ta bi wani corridor wanda ba ta san ko ina ba ne ta dai nufa ne. Kitchen ne tana shiga ta tsaya cak tana masa kallon banza ta ce. "Zai fi kyau a ce ka rabu da ni, ka yi harkar gabanka, idan ba haka ba wallahi sai sai mu yi kare jini biri jini da kai a gidan nan, don ni ba sakarya ba ce da zan zauna ka mayar da ni tamkar tabarmar zamanka ba ne. Hannu ya daga da niyyar kai mata mari ta kauce da sauri, ya sake kai wa a karo na biyu ya ta tare da hannunta da ya sha zanen jan lalle. Cikin azaba ta saki ƙara tare da kai hannu ta ɗauki toaster oven dake kan kitchen cabinet ta buga masa, sai dai kafin ya kau ce ya sa same shi a hannu. Daga nan kowa ba ya fara ba kokarin ka wa ɗan uwansa hari tare da ƙoƙarin kare kansa. Duk abun da ta rarumo z ta jefa masa wani ya kauce wani kuma ya same shi. Kasancewar ita ma jajirtacciyar mace ce ya saka ba ta gaji ba, duk da dukan da yake kai mata, ko ya rike hannun ya kwace abun da ta ɗauka za ta buga masa. Tsawon mintuna suna cikin wannan halin, ga jikinta jini na zuba a goshinsa, har ya fara ganin kiri, ita kanta ta gaji sosai karfin hali kawai take yi. Sai da suka gaji kowa ya jigata daga shi har ita kafin suka zube a wajen suna mayar da numfashi. Kowa ya gaji a cikinsu, ji kam har jure ke ɗibarsa, yana tunanin Maryam aljanu ne da ita yadda ta dage duk abinda ya fltati gabanta sai ta jefa masa ko ta buga masa, wanda ganin haka ke saka yana ja da baya ɗin gudun kada ta illata shi. Tsawon mintina fmgoma suna zHnd ka mayar da numfashi ba wanda ya iya ko motsin karki. Cikin karfin halin da ya ta taso masa ya mike tsaye ya fice daga kitchen ɗin yana rike da kansa dake fitar da jini ta goshinsa. Ita ma daƙyar ta iya tafiya ta nufi wani bedroom da take tuninin nan ne na ta, cikin ikon Allah tana shiga ta ga nan ne. Murza key ta yi ya rufe ta ciki, bathroom ta nufa ta cire Kayanta , ruwa mai zafi ta fada jikinta da shi, sannan ta fito ta sanya kayan barci ta kwanta, tana tuninin irin rayuwar da za su yi da Yaa Mansur a cikin gidan, don tabbas da ta akama matukar ba ta tsaya ta ƙwatarwa kanta ƴanci ba to ba za su daidaita ba, amma idan ya ga ita ma fa janwuya ce zai shafa mata lafiya, daga ta yi masa magana kawai sai ya hau zaginta ba za ta dauki rayuwar ƙasƙanci a gidan aurenta ba, dole sai ta jajirce domin rumgumar ƴancin rayuwar gidan aurenta _Sadik_ Bayan sun gama rugimar su da Mansur ya nufi gidansa, yana direbin sai huci yake yi saboda shi ma zafin zauciyar ne da shi, kamar ba Abbi Ummi suka haife shi ba, sam bai ɗauki sanyin halinsa ba, gara Mahmud da Zahrah su suna da sanyin hali, duk da Zahrah idan aka kure ta tana da kafiya da taurin kai, amma Mahmud sanyin halinsa ya yi yawa. Driving kawai yake yi yana huci domin abun da Mansur ɗin ya yi masa ya masa zafi, kawai don an aura masa ƙanwarsa shi ne zai masa wannan rashin mutuncin, har yana zuga kanwar akan ta yi masa wulakanci a gabansa. To ai ba son ta yake yi ba, ballantana ayi masa haka, don da son ransa ne ai ba zai ce zai aure ta ba, tun da ya san ba zaman lafiya da jituwa ga iyayensu. Da ace kowa zai yi ƙanwarsa haka ashe shi ma da ya yi wa Zanrah muguwar huduba da ka aura mata Hilal. Kwafa kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba, Nadeeya ko duk ta damu , saboda Allah ya gani ko da aka ce an aura mata Sadik ta yi farin ciki a zuciyarta, ba ta nuna ba ne ganin iyayen na ta na bakun ciki da lamarin. Amma tabbas ita ya yi mata don tana son namiji kyakkyawa don dama yaran Ummi kaf kyawawan gaske ne su ita suka dauko kamanninta ne da su. Kyakkyawar bafulatana. Don Zahrah har ta so ta kere Ummi a kyawu, kuma dukkansu uku Mahmud, Sadik, Zahrah, duk wanda ya kalle su ya san jini ɗaya ne saboda suna kama da juna sosai har dai ita da Sadik ɗin. Horn Sadik ya yi a kofar gidansa, Maigadi ta leƙo ya ga shi ne ya bude masa gate. Yana gama parking kafin ya fito ya ji muryar Nadeeya na cewa. "Am sorry." Bai kalle ta ba ya ce. "Sorry for what?" "Wallahi ba za ka samu matsala da ni ba na yi maka alkawari." "Wannan kuma matsalar ki ce don idan ma zuga ki suka yi don ki yi Mani rashin mutunci, to daidai da zamaninki nake, don wallahi ba za ku ci riba da Ni ba sai dai ki sha bakar wahala, ko shi yayan na ki bai ci galaba a kaina ba, don haka duk wanda ya kwana lafiya shi ya so, ba ni na ce ina son ki ba ballantana a tsane ni don an aura mani ke." Dum gabanta ya faɗi, sau biyu kenan tana nuna baya son ta , ranar da ta je ɗakinsa bisa umarnin Papa akan ko zasu yi wani event ne, ya nuna ba auren soyayya suka yi ba me za su je yi wa event, ta ce baka so na ne, ya ce ke kina so na, tun da ya ce ta tafi za su yi magana yana aiki ta yi ta tsammanin jin sa amma shiru bai bi ta kanta ba. "Yaa Sadik." Shirin fita yake yi daga motar amma sau ya juyo ya lalle ta jin ta kira shi cikin sanyi. Bai amsa ba ta cigaba da cewa. "Ba ka yi hakurin ba ne?" "Ni ba ki yi Mani laifin komai ba Nadeeya." "Amma a dalilina aka yi maka haka." "Kada ki damu." Yana fadar haka ya fice daga cikin motar, ita ma fitowa ta yi ta bi bayansa. Bude kofar ya yi ya shiga da sallama, ita ma Sallamar ta yi, maida kofar ya yi ya rufe da key. "Ga ɗakinki can ki shiga ki kwanta." Ya yi maganar yana nuna mata ɗakin dake kusa da na shi, shiga ɗakinsa ya yi ba tare da ya kalli ko in da take ba ya yi shigewa ciki. Tsaye ya bar ta ta bi bayansa da kallo tana murmushi wanda har cikin zuciyarta take jin kaunarsa. Kuma ta yi alkawarin ba za ta nesanta kanta da shi ba. Bedroom da ya nuna mata ta shiga, nan ta ga komai na ta, kayan jinta ta cire ta shiga wanka, bayan ta fito ta shafa man shafawa da turare sai ta sanya riga da wando na barci. Tunanin Sadik ɗin ne a ranta, ta na murmushin ta ce. "Allah ya sa ya shigo kamar yadda kowane angon dake farin ciki zai kasance tare da matarsa a daren farko, ko da ba wani abu za su yi ba.' Ganin har karfe goma da rabi bai shigo ba ya saka ta tashi ta nufi kofar fita tana cewa. "Dole na sabar maka da kasancewa da ni domin kusanci da shakuwa ya shiga tsakanin mu, ko da ba ka so na, amma kuma ai kamar na zubar da ajina ne ko?" Komawa ta yi ta dauki wayarta ta kira wata ƙawarta mai suna Deejah, ita Deejah matar aure ce, Nadeeya ta yi mata bayanin komai , sannan ta dora da cewa. "Yana dakin sa ban ga alama zai shigo ba, ni kuma ba na son na nisanta kai na da shi. Idan na bi shi dakinsa ban zubar da ajina ba kuwa, shi ya kamata ya zo." Dariya Deejah ta yi kafin ta ce. "Ai ba zai taɓa zuwa ba, musamman da yadda komai ya kasance, ke za ki ha hankalinsa akan ki tun da kina son sa, kuma yana da saukin kai da alama tun da bai hantare ki ko ya yi maku wani abu ba, ko maganar banza, shawo kansa ba zai baki wahala ba turaren da na kawo maki ki shafa yanzu nan idan za ki je wajensa." Zaro idanu ta yi tana cewa. Turaren ba na komai ba ne ko, don wallahi tsoro nake ji . Kada ku damu ba na komai ba ne ki shafa Kadan. Nan ta ba ta shawarwari sannan suka yi sallama ta katse wayar. Turan ta duba a cikin handbag ɗin ta ta shafa. Fita ta yi bisa shawarwarin da Deejah ta bata, knocking ta yi a bakin kofar dakinsa. Har ya kwanta don karfe goma sha daya ne Yanzu. Kwanciyarsa kenan ya ji knocking, mamaki ya kama shi me kuma ya kawo ta. Hasken ɗakin ya kunna sannan ya mike, sanye yake da farar singileti da wando 3-quarter. Bude dakin ya yi ya zuba mata manyan idanunsa. Ba ta ce komai ba ta shigo kanta a ƙasa b ta yadda ta kalle shi ba. "Lafiya dai ko?" Ya tambaye ta yana kallonta. "Yunwa nake ji." "Ba ki ci abinda ba ne?" "Ban ci komai ba." "Yanzu dare ya yi ba in da zan samu abinci, za ki iya shan fresh milk?" "Eh zan iya." Okay ya faɗa ya nufi fridge dake bedroom nasa. Zama ta yi a bakin gadon ko da ya kawo mata shi cikin kofi karba ta yi tana masa godiya. Ga ƙamshin turaren dake jikinta ya fara kai masa ziyara, don yanayinsa ya fara sauyawa. Shanye wa ta yi tas sannan ya tamabaye ta ko ya karo mata ne, ta ce a'a. "Tashi kije ɗakinki ki kwanta." Don ya matsu ta tafi saboda kamshin tutaren ya fara tasiri a gare shi. "Ni ba zan iya kwana ni kadai ba tsoro nake ji." Tsoro kuma , a guda ke da wa kike kwana, muna haduwa dukkan mu ba tare da Maryam, wata ran har d su Kausar da Nabeela." Shiru ya yi kafin ya ce. "Yanzu ya za'ayi?" "Ni dai ba zan iya kwanciya ba tare da kowa a kusa da ni ba, ko za ka sami wacce zata taya ni kwana?" "A ina a wannan daren?" Shiru ya yi kafin ya yi magana a kasalance ya ce . "Za ki iya kwana a ɗakin nan?" "Eh zan iya." "Okay bisimillah zo ki kwanta." Ya yi maganar yana zuba mata lulun idanunsa. A hankali ta kwanta a saman gadon tana jan bargo ta rufe jikinta da shi. Shi ma kwanciya ya yi ya kashe hasken ɗakin. Kasancewar suna kwance a gado daya ne turaren ya kara tasiri akansa, wani feeling yaje taso masa, ita kam duk ba ta san meke faruwa ba, don ta ɗauka turaren gamagarin turere ne, ba ta san amfaninsa ba. "Nadeeya." Ya kira sunanta kamar mai yin raɗa. Amsawa ta yi cikin sanyin murya. "Za ki iya zaman aure da ni?" "Eh zan iya ai ina son ka kai ne baka so na." "Da gaske kike yi?" "Eh kai ma kana so na?" Bai bata amsa ba ya janyo ta jikinsa yana cewa. "Wannan turaren da?" Ya yi magana yana shinshinar wuyanta. Dakyar ta yi karfin halin cewa "Ƙawata ce ta bani." Matse ta ya yi a jikinsa tare da shaƙar kamshin turaren jikinta. Tsoro da fargaba suka cika mata zuciya musamman da an ta ji hannunsa na yawo a cikin rigar barcinta. Bata aknkare ba ta ji ya ba fara kissing dinta. Lokaci daya ya rikice mata kamar ba shi ba, komai zafi-xafi yake yinsa. Tana ji tana gani ya raba ta da kayan barcinta ya shiga sarrafa ta yadda yake so. Tsoro da fargaba duk sun cika ta ganin dai kissing lips ɗin ta yake yi ga hannayensa dake ta shafar jikinta ta ko ina , ya shafa nan ya tsotsa can. Gabansa jikinsa har rawa yake yi, tsoron yanyainsa ya saka ta yin kuka da farga. Duk da cewa bakinta na cikin nasa amma yana jin hawayenta ya zore bakinsa c in kin nata, ya yi magana murya kamar mai maye ya ce. "Ba kin ce ki a so na ba?" "Eh." "To daina kuka ki bar ni na samu nutsuwa da ke, idan ba haka ba akwai matsala." "To don Allah ka yi Mani a hankali tsoro nake ji." "Okay." Kayan jikinsa ya cire wanda hakan ya sake daga mata hankali dai dai ba ta jin za ta iya masa gardama "Thank you." Ya fada yana sake haɗa bakinsu waje daya hannayensa daya na kan krjinta yana wasa da dukiyar fulaninata, ɗayar hannunsa yana shafa gashin kanta. Tana ji tana gani ya buɗa kafarta, ya shiga tsakiya yana karanta addu'ar saduwa da iyali. Ƙara ta saki tare da fashewa da kuka, duk da a hankali yake bin ta, bai riga ya shige ta duka lokaci guda ba, wani kukan ta saki lokacin da ya shige ta duka. Kuka take yi tana kiran sunan Yaa Mansur ya zo ya taimake ta. Sai da ya dauka mintuna hamsin a kanta sannan y saurara mata, zuwa lokacin muryarta har ta dakushe saboda kuka. Daukarta ya yi ya kai ta bathroom ya haɗa zuwan zafi, zai taimaka mata ta ce zata iya ya fita kawai. Ba musu ya yi mata sannu ya fita. Shifdar gadon ya canza ya jira fitowarta, yadda take tafiya ya kalla yana yi mata sannu. Ba ta kalle shi ba, ta zauna bakin gadon tana daure da towel. Shiga ya yi shi ma don yin wanka, yana shiga ta shige bargon ta kwanta. Lumshe idanu ta yi kamar mai barci. Ko da ya fito ya saka kaya ya ɗauka barcin take yi. Don haka ya ja masu bargo ya rufe su. Sam bai taba tunanin wannan daren za ta zo ba tsakanin sa da Nadeeya, shi kansa ya rasa dalilin da ya saka ya kasa rike kansa a daren nan. Barci ya ɗauke su kusan a tare kowa da abinda ke zuciyarsa. _Faisal_ Tun da suka bar Tafarki Family bayan ya dauko matarsa Kausar, ba wanda ya yi wa wani magana tsakanin shi da ita. Har suka karasa gidan ba wanda ya yi wa wani magana, kowa ransa a ɓaci yake. Suna shiga ta nufi wani bedroom ta ga ba na ta bane, sai ta duba dayan ta ga nata ne sai ta shiga tare da banko kofar da karfi wanda sai da Faisal ya kalli kofar. "Mahaukaciya." Ya fada yana nufar bedroom ɗin sa ransa a ɓace, don ya san zamansa da kausar akwai matsala, ya san yaran Aunty Laila ba tarbiyya ne da su ba. A haka kowanne cikinsu ya kwanta dakinsa cike da bakin ciki. _Mahmud_ Bayan Papa ya bashi umarnin ya rike hannunsa Nabeela su tafi, suna fita ta fisge hannunta tare da cewa. "Wallahi ka sake taɓa Ni sai na yi maka rashin mutunci ." Bai ce mata komai ba, ya shiga mota yana zaman jiranta, tsabar wulakanci sai da ta shafe mintuna goma kafin ta shiga ya ja motar suka bar gidan. Suna hanya sai faman masifa take yi tana zage-zage, bai tanka mata ba, har suka isa gidan ya yi parking. Da Fitowa ya ya yi ita ma ta fito ta bi bayansa. Suka shiga tai masa wani banzan kallo sannan ta kalli ko ina ta ce. "Ina ɗakina?" Da hannu ya nuna mata yana cewa . "Ga shi can." "Yunwa nake ji kuma kaza zan ci, na ga a farkon layin nan ba nisa akwai mai gasashshen kaza ja je ka siyo Mani." Banza ya yi mata ya nufi kofar dakinsa. Da sauri ta tari gabansa tare da cewa. "Mahmud magana nake yi maka, don ba zan iya laƙaba maka kalmar Yaya ba. Wallahi wa billahillazi idan ba ka siyo Mani kaza ba ai ba za ka taba rintsawa a cikin gidan nan ba. Idan kuka kana ganin ƙarya ne bisimillah." Baya son tashin hankali ne ya saka ya fita ya siyo mata kazar, har ya dawo tana falon sai dai ta zauna . Yana miƙa mata ta fisga ta wuce dakinta rana murguda masa baki. Wanka ya yi ya yi alwala ya kwanta. Sai da ya raba dare yana Sallah kafin karfe uku ya yi shirin kwanciya barci. Da karfi aka buga kofar kamar za'a ɓalle ta. "Waye?" Ya fada yana nufar kofar?" "Uwar da ka ajiye ce." Tsaye ya ganta ta rike kugu tana jijjiga. Barcin da bai samu ya runtsa ba kenan, don yana idar da sallar daren kenan zai kwanta ta buga masa ƙofar. Masifa da bala'i ta fara yi masa idan ya shiga dakin ta dinga buga kofar yadda ba zai iya barci ba. Har kafe biyar ne asuba ba ta bar shi y runtsa ba, alwala ya yi ya nufi masallaci don yin sallar asuba. Sai karfe bakwai ya dawo gidan, yana dawowa ya ya shiga kitchen don zai tafi aiki. Ruwan tea ya dafa ya zuba a flak ƙwai ya soya ya ɗauko kayan ya ajiye a falo saman Centre Carpet. Ɗakinsa ya shiga ya yi wanka ya shirya cikin bakin Suit, ya sa Black cover shoe sai kamshi yake yi . Fitowa ya yi don yin breakfast. Nan ya tarar da Nabeela tana kallon kayan da ya jera na breakfast. _Mansur_ Ko da ya tashi da asuba ya tayar da ita suka yi sallah, ta koma barci akan gado , shi kuma bayan ya dawo masallaci ya shiga ya shirya mata breakfast, ya kai har bedroom ya ajiye mata a kan tebur. Baya son tashin ta daga barci don haka ya ajiye mata takarda da lambar wayarsa ya ce ta kira shi idan ta tashi. Barin gidan ya yi yana tunanin halin da ɗan uwansa yake ciki, don ya san Aunty Laila ba za ta bar Nabeela ta bari Mahmud ya kwana lafiya ba. So yayje yi ya je ya ga ya ɗan uwansa yake ciki. Mahmud na zaune a kan Centre Carpet dake tsakiyar falon, tea ya haɗa a cup yana sauraren zai je aiki, ga soyayyen ƙwai da ya zuba a plate sai ya debi yankakken bread biyu. "Au ni ma yunwar nake ji ki ka kawo Mani abinda zan ci ne?" Bai ce komai ba ya ɗauki wani cup ya haɗa mata shayi, ya zuba Milo ya tura mata plantain da ƙwai ɗin da ya soya. Ɗaukar kofin tea ɗin ta yi ta masa wani kallo sannan ta ɗauki kofin shatin ta wasa masa a jiki. Kallonta ya yi da idanunsa da suka rikeɗe zuwa ja ba. Daidai lokacin aka yi knocking, kafin su yi wata magana Sadik ya tura kofar ya shigo. Kallon Yayan nasa ya yi ya ga yadda ruwan shayin ke ɗiga tun daga fuskarsa har zuwa jikinsa. Ransa ya ɓaci zuciyarsa har tafarfasa take yi ya karaso wajen, Ganin yanayin Sadik ya firgita Nabeela, don ta san shi baya daukar raini. Cikin ɗakiya ta ce "Kai kuma uban wa ya ce ka shigo wa mutane ba izini da safiyar nan?" "Ubanki ne?" "Wallahi ba dai ni ba." Ganin yadda gefen fuskar Yayansa ya yi ja lokacin da ya goge fuskarsa alamar tea ɗin da zafi. Sadik ya ɗaga hannu a fusace zai kai wa Nabeela mari, Mahmud ya yi saurin mikewa tare da rike masa hannu. "Yaya kana kallo wannan yarinyar na yi maka wannan cin kashin za ka ƙyale ta?" "Ai da ka bar shi ya mare ni, wallahi sai ya yi nadama." "Haka aka koya maki rashin tarbiyya?" "Kana mamaki ne?" Murmushin takaici Sadik ya yi kafin ya ce "Ban yi mamaki ba, domin idan ba ki aikata haka ba, ai ba ki amsa sunan Laila ta haife ki ba?" "Sunan mahaifiyar tawa kake kira gatsai?" "Ko za ki ki rama ne?" Ya yi maganar yana ƙoƙarin kwace rikon da Yaa Mahmud ya yi masa. Wayarsa ce ta yi ruri, ya kalli Mahmud ya ce . "Sake ni na amsa waya." Jin haka ya saka Mahmud ya sake shi. Ciro wayar ya yi ya duba mai kira, True caller ta nuna masa sunan Nadeeya Adam Tafarki. Hakan ya sa ya gane ita ce don bai da number ta. Haka kawia sai ya tsinci kansa da jin farin ciki da nishaɗi. Yana daukan wayar ta saka masa kukan shagwaɓa. "Haba Baby kukan ya isa haka mana kada kanki ya yi ciwo, kuka tun jiya har yau, ki yi hakuri na tuba ba zab sake wahalar dake ba kin ji baby?" Nabeela ta kalle shi tana mamakin da wa yake magana, ta dai san tare aka yi masu huduba da Nadeeya to me ta aikata haka, ganin yadda Sadik ya koma wani iri ya tashi hankali jin kukanta ya sa ta gane mai afkuwa ta afku." "Kin ga ki kwantar hankalin ki daina kuka, yanzu ki daure ki sake shiga ruwan zafi, magani na nan na ajiye maki da tare da breakfast, ba zan dade ba zan dawo." Mumrmushi ya yi ya kashe kiran wayar. Nabeela mamaki da takaici ya cika ta. Muryar Mahmud ya ji yana cewa " Bari na sake shirya wa sai mu fita tare." Mahmud na nufar bedroom ɗin sa Sadik ya mike rai a ɓace ganin ya tunkaro Nabeela ya sa ta ruga a guje ta shiga bedroom ta rufo kofar. Don ta san yanzu ba Mahmud da zai dakatar da shi kuma ta lura da ɓacin ran dake fuskarsa. Fita ya yi harabar gidan ya shiga motarsa yana zaman jiran Yayan nasa ya fito. _Aunty Laila_ Cike da tashin hankali ta nufi ɓangaren Mummy, don tana da tabbacin Umma na can yanzu . Ganin yanda ta shigo ne ya saka Umma ta mike da sauri. Mummy dake kwance ba lafiya da ido ta bi ta. "Laila laflya me yake faruwa?" Umma ta yi tambayar cike da damuwa. "Komai ma ya faru, yanzu ƴarki Nabeela sai da ta bamu matsala ta wargaza mana shiri duk jan kunnen Da aka yi mata?" "Me ta yi?" "Ta bawa wannan mara mutunci kanta mana." "No hakan ba zai faru ba, yaushe suka samu fahimta da wani abu zai shiga tsakaninsu?" "Nabeela ta kira ni wai Sadik ya je wajen Mahmud ta kara shi a waya, sai lallaɓa ta yake yi yana ce mata ta shiga ruwan zafi ya ajiye mata magani." "Idan kuwa haka ne tabbas Nadeeya ta cuce mu ta wargaza komai, kai ba zai yiwa ba." "Tun da kina kokwanto zan je gidan yau ɗin nan, sai na saka ta ta kwanra na duba ta kafin mu yanke mata hukunci, duk da na ga baki yarda ba." Ƙarar mota suka ji ta shigo gidan, ta window Umma ta leka, ganin Mahmud da Sadik ta ce. "Ga su nan sun zo gaida uwarsu." Kallo ɗaya suka yi wa Mahmud suka gane yana cikin tashin hankali. Sunyi Laila ta saki uwar dariya tana sawa Nabeela albarka. Sadik ne ba za ka iya karantar yanayinsa ba tashin hankali ko akasin haka, don cikin farin ciki yake ganin halin da ɗan uwansa yake ciki ya gurguntar da farin cikin da ya tsinci kansa a ciki. "Zan je na duba Nadeeya don ga tashin hankali a tattare da wanna mai taurin kai da zuciyar ba." Part ɗin Dada suka je suka gaishe da Papa da Dada, in da suke kara masu nasiha da sanya albarka sannan suka nufi part ɗin Umminsu. Hankalin ta ya tashi ganin Mahmud a firgice, ya sa Ummi ƙwalla ya cika idanunta, sai ta dauke da sauri. Don ta san halin Mahmud da Sadik ne ba za ta damu ba. Albarka ta sanya masu suka shiga sauka gaida Abbi suka tafi. _Zahrah_ Tun bayan da Hilal ya ja mata bargo ya ya tafi yake kuka. Duk da ba ta san dalilin da ya saka ya bar ta yana mata kallon mamaki ba, ta lura jikinsa ya yi sanyi ya yi mata kallon da bai taɓa yi mata ba a rayuwarsa. Lallaɓawa ta yi tana bin bango ta rufe kofar ta da sakata. Tana kukan abubuwa da ya yi mata. Goge bakinta ta yi tuna yadda ya dinga tsotsan bakin ta kamar ya samu sweet. Bathroom ta shiga da jin bango ta dauki brush da toothpaste ta dinga wanke bakib tana tofar da miyau cike da ƙyankyami. *Saura page ɗaya na kammala book 1 wacce ta shirya siyen Book 2 zata tura kuɗinta ta wannan account number 2242538358 Zainab Abdullahi UBA bank sai a tura shaidar biya ta wannan lambar 09065327995* [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page7️⃣0️⃣ *LAST FREE PAGE* Bathroom ta shiga da bin bango, ta ɗauki ta ɗauki brush da toothpaste ta dinga wanke ta dinga wanke baki tana tofar da miyau cike da ƙyanƙyami. Sau uku tana saka toothpaste tana wanke baki kamar za ta canza haƙoranta da harshe take ji. Wanka ta yi da ruwa mai ɗumi sannan ta fito ɗaure da towel, wankan da ta yi sai ta ji jikinta ya ɗan yi mata ƙarfi. Sai dai har lokacin yunwa na ɗawainiya da ita jin ta take yi tamkar fanko. Riga da wando na barci ta saka farare, wandon da kadan ya wuce guiwarta, ji ta yi ba za ta iya yin barci ba yadda yake jin yunwa don duk yai sau daya ta ɗan sha ruwan tea kaɗan, ga yanzu dare ya yi bata san ya za ta yi ba. Hawaye ne ke bin fuskarta ta Kudundune ta cire wuri ɗaya hannayenta a cikinta wanda take ji har ciwo yake yi mata. _Hilal_ Sai faman Safa da marwa yake yi a cikin ɗakinsa. Ransa a ɓaci idanunsa sun sauya launi zuwa ja kamar zai su fitar wuta. Yana tuna yadda mahaifiyar sa da ƙanwar mahaifinsa ke ta aibata Zahrah da zancen lalata da cikin da aka ce tana zubarwa. Ƙarin abunda ya saka ya yarda da cewa maganarsu gaskiya ce ranar da ya ganta kwance cikin jini ya kai ta asibiti likita ya sanar masa da zubar da ciki ta yi. Ga shi kuma Family Doctor na su ne wanda suka yarda suka saba da shi tsawon lokaci. Sannan ga shi ya tabbatar da cewa yarinyar cikakkiyar budurwa ce. Shin me ya saka suka yi mata haka sun saka ya tuna Abba, Ummi, Mahmud, Sadik, Zahrah. Yadda ake nuna masu wariya a cikin gidan, kullum sai nufar su da sharri ake yi wanda su kuma har yau bai ga wani aibu ko mugun balin da aka ƙakaba masu ba. Cikin ƙaraji ya ce. "Meye dalilin da za ku yi wa ƴar mutane shaidar zina? Mummy, Aunty Laila da Doctor dole za ku amsa mani tambayoyin da zan yi maku, tabbas ba na jin zan iya saurara wa kowa. Musamman yadda na cutar da ƴar mutane ba tare da hakkinta ba." Ya tuna ranar da ya kai ta asibiti aka ce ciki ta zubar ya tuna maruka da dukan da ya yi mata akan laifin da ba ta aikata ba. Da sauran abubuwan da ya yi mata cikin takaicin halin ta yana mata kallon kura lulluɓe da fatar akuya." Ƙofar fita ya nufa don ya ga halin da take ciki Zuwan lokacin karfe biyun dare ya yi. Tana nan tana tausayin sabuwar rayuwar da ta tsinci kanta sai ta ji ƙamshin turarensa. Cikin faduwar gaba da firgici ta kalli ƙofar sakamakon jin ƙamshin turarensa. Tsaye yake jikin bango yana sanye da wando 3-quater da farin singileti ƙirarsa na ƙaƙƙarfan namiji ne bayyane a jikinsa saboda yawan motsa jikin da yake yi. Hannunsa ɗaya a cikin aljihunsa ɗayan kuma yana rike da handle ɗin kofar. Ya zuba mata rikitattun idanunsa. Gabanta ne ya faɗi ta kara matsawa can ƙarshen ta ƙara Kudundune jikinta, gani take yi kamar zai yi mata wani abun. A hankali ya ƙaraso bakin gadon, fuskarsa babu walwala. "Are you okay?" Banza ta yi masa kamar ba ta ji shi ba, kallo mata ya yi na mintuna biyu kafin ta ɗauke idanunsa ya ce. "Meke damunki." "Ni wajen Ummina za ka mayar da ni, ba na son auren." "Auren ne ba ki so ko kuma ni ne ba ki so?" Shiru ta yi ba ta ce komai ba. "Talk to me, ni ne ba ki so auren ne baki so?" "Ba na son ka." Shiru ya yi tare da cije lips ɗin sa na ƙasa. Kafin ya yi wata magana ne ya ji tana cewa. "Don Allah ka sake ni ba zan iya zama da kai ba." Bai yi mamaki don ta ce ba ta son sa ba, saboda shi ya gina mata tsanarsa a cikin zuciyarta, sai dai bai taba tunananin za ta bijire wa auren ba. "To yanzu wa kike so." Ba tare de jin shakkar sa ba ta ce "Yaa Ammar." Sai da rintse ido ya buɗe sannan ya ce. "Okay ki daina kuka." "Don Allah ka taimaka ka sake ni, wallahi yanzu ni kadai na san me nake ji a cikin zuciyata, matukar na ci gaba da zama da kai tabbas sai an ɗauki gawata a cikin gidan nan." "Me za ki ce wa su Papa dangane da mutuwar auren idan kika koma gidan.?" "Zan fada masu ni ce na nemi ka sauwake Mani." Yana tunani ta ina zai fara sai ya ji tana cewa. "Ka yi Mani alkawarin za ka sake ni." Kai kawai ya jinjina ya fita daga ɗakin. Ba jimawa sai ga shi ya dawo da cup ɗin tea da biscuit a hannunsa. Mika mata tea ɗin ya yi Wanda ya haɗa mata shi da kauri. Kauda kanta ta yi don ko kallonsa ba ta son yi, tsuke fuska ya yi cikin dakiya ya ce. "Za ki karba ko sai na baki da kaina?" Kallonsa ta yi ta ga ya koma mata asalin Hilal ɗin da ta sani. Kamar ba yanzu shi ne yake yi mata magana cikin taushi ba. Ganin kallon da ya yi mata ne ya saka ta ɗauke idanunta da sauri ta karɓa tana maganar zuci." 'Mai hali ba zai taɓa canzawa ba, duk macen da ta zauna da shi za ta sha wahala, a haka Aunty Bilkisu ke cewa sai yadda na yi da shi?' A hankali take tauna biscuit ɗin tana shan ruwan tea ɗin. Kallonta yake yi har lokacin fuskarsa a tsuke, ta ci rabin biscuit ɗin ta shanye ruwan shayin ta ce masa ta ƙoshi. Karba ya yi ya fita daga cikin ɗakin da cup ɗin a hannunsa. Sai a lokacin ta ji yunwar da take ji ta ragu da kashi hamsin ta fara jin daidai. Hamdala ta yi tana mamakin yadda ya hado mata tea ya kawo duk jin kai da isar sa. Dawowa ya yi ya kalle ta ya ce. "Akwai abinda kike bukata ne kuma yanzu?" "Takardar sakin da na roke ka nake so zuwa safiya sai na tafi." Shiru ya yi yana kallon ta kafin ya ce. "Zan baki tun da haka kike bukata ki bani nan fa zuwa jibi idan na kammala abinda na saka a gaba." "Ton na gode." Bai ce komai ba ya ja mata kofar bayan ya kashe switch ɗin ɗakin. _Asadullah_ Zaune yake a falo shi da Jidderh da Mallamin dake mata addu'o'i. Ruwan zamzam da ya tafa addu'a a ciki take sha . Tun da aka fara yi mata magani ba ta da abun yi sai barci. Kowane lokaci cikin barci take, da Asad ya yi wa Mallamin complain na yawan baecin ya ce ya ba damuwa alamar nasara ce. Anisa na zaune a gefen kallinsu kawai take yi, ganin yadda Asad ke bata magani da kansa tun da Mallamin ya zo shi je yi mata komai. Wankan ne kawai yake bari Anisa ke yi mata shi ma sai ya tabbatar an yi mata da sabulun da Mallam ya bayar. Mallam ya tashi tafiya Asad ya mike zai raka shi zuwa wajen mashin ɗin sa dake waje. Da Bayan ya raka shi ne Isa wajan mashin ɗin sa ya hau mashin ɗin ya tafi. Har lokacin Facemask ne a fuskar Asad wanda idan ba ka yi masa farin sani ba to ba za ka gane shi ne ba Tashin mashin ɗin kenan yana barin wajen Asad ya juya da niyyar komawa cikin gidan. Da sauri ya durƙusa don kare kansa. Ta jikin gate ɗin gidan ya kalli wanda ke bayan da rike da wani karfe zai buga masa a kai. Sake yunkurin buga masa ya yi a karo na biyu, nan ma ya kauce daga nan suka fara kokawa da shi, sosai suke kokawa da juna. Cikin ikon Allah Asad ya kayar da mutumin ƙasa yana ƙoƙarin cire cire masa abinda ya rufe fuska da shi indanusa kawai ake gani. Suna tsaka da kokowa sai motar Sulaiman ta karaso wajen, a lokacin mutumin ya samu wani karfi har ya iya ƙwayar kansa daga hannun Asad ya ruga a guje kafin Sulaiman ya karaso wajen. Bin bayansa ya yi suna gudu kafin ya cin masa ya ga ya hau bayan wani mai mashin da alama jirsnsa yake yi. A guje suka bar wajen Sulaiman ya dumƙule hannu ya naushi iska. Dawowa ya yi ya samu uban gidansa tsaye kamar wanda aka dasa a wajen. "Sir." Sai a lokacin ya ɗago ya kalli Sulaiman ba tare da ya ce komai ba. "Are you okay?" Kai kawai ya jinjina sannan ya yi magana cikin kamilalliyar muryarsa mai cike da nutsuwa ya ce. "Am okay" Cikin gidan suka shiga in da suka yada zango a falo. Jidderh ce kawai ke barci a falon kan kujerar mai zaman mutum uku. Asad ya zauna har lokacin ya sa magana a abubuwa sun yi masa. Indanusa sun yi ja ya dafe kansa da hannayensa biyu. "Me ya faru ne har hakan ta faru?" "Mallam dake wa Jidderh magani ne ya zo sai na raka shi iya ka ta bakin gate ɗin. Yana hawa mashin na juyo zan dawo sai na hangi mutum ta jikin glass ɗin, da ba don Allah ne ya kare ni ba dan Allah ya kare ni wannan karfe bai daki kai na ba da yanzu sai dai wani labarin ake yi." "Sir, shi ya na ce ka yi tunani cikin mutane ukun da suka san inda kake tabbas ko ma waye yana daya daga cikin masu son ganin bayanka. Amma kai ka yarda da kowa, kuka a wannan yanayin da ake ciki bai kamata a ce kana saurin yarda da kowa ba, domin wani lokacin wanda ka yarda shi ko ba ka yi zato ba sai a wayi gari ya cuce ka Tashi ya yi ya nufi upstairs Yana cewa. "Ka tafi ina son kadaici z ka iya dawowa gobe." Yana fadar haka ya haura sama. _Hilal_ Fitowar sa daga wanka kenan yana goge jikinsa wayarsa ta yi ruri, yana dubawa ya ga Jamilu ne mijin Sumayyaa da suka sauka a gidansa shi da Zahrah. Ɗagawa ya yi suka gaisa da shi. "Ina Amarya ne wallahi ga Sumayya sai farin ciki take yi tun da na sanar da ita aurenka da Zahrah." Bai ce komai ba in da Jamilu ya cigaba da cewa. "Gaskiya na taya ka murna ka yi sa'ar mace tagari, ai ina ga yadda ta dame ni zuwa next week za mu shigo mu ga Amarya. Kafin nan tana son ta yi magana da ita." "Ban sani ba ko ta tashi yanzu." "Kamar ya kai kana ina?" "Ina ɗakina." "Ita kuma tana ina?" "Tana ɗakinta." "Man idan za ka ajiye girman kai da izzar da kake da shi ka ajiye, mata duniya ne." "Ba sai kun yi wahalar zuwa ba." "Saboda me?" "Saboda ta ce na sake ta ba ta sona, idan ba haka ba za'a wayi gari a ga gawar ta." "Subhanallah, kai yanzu za ka iya sakinta?" "Why not?" "Kada ka biye mata na san idan ka cigaba da lallaɓa ta da kyautata mata za ta so ka, domin ita zuciya an halicce ta na bisa ga son wanda ya kyautata mata da kuma kin wanda ya munana mata." "Akwai wani abokina Ammar na san ka san shi, to ya fara nemanta suna soyayya ta ce Mani shi take so, ta nemi na sake ta." "To yanzu sakinta za ka yi?" Murmushin gefen baki ya saki kafin ya ce. "To ya zan yi?" Ganin ɗayar wayarsa na ruri ya saka ya yi wa Jamil Sallama ya katse kiran wayar. _Aunty Laila_ Bayan sun gama magana da Umma akan za ta je gidan Sadik ta binciko gaskiyar magana ko Sadik ya yi mu'amalar aure da ita kamar yadda Nabeela ta faɗa. Mummy da Ummar sun goyi bayanta idan har da gaske ne to Aunty Laila ta yi mata dukan tsiya, sannan ta tabbatar tare da ita ta bar gidan Sadik, ba za su kawo ta nan ba, sai dai za su kai ta gidan ƙanwar Umma." Direba ta saka ya kai ta gidan Sadik ɗin, kai tsaye ya dauki hanyar zuwa gidan, horn ya yi maigadi ya bude yana masu sannu da zuwa. Tambayar sa ta yi ko Sadik na gidan, ya ce mata baya nan ya fita. Ta ce wa Direban ya ajiye motar a waje yanzu za ta dawo. Tana shiga falon ko sallama babu. "Nadeeya dake waya da Sadik tana ta zuba masa shagwaɓa wai har yanzu ba ta warke bai tsaya jinyar ta ba ya wuce ya bar ta. Tana wayar cike da shagwaɓa, tana jin dadin yadda yake kula da ita yana biye wa shagwaɓa da take masa abun da ba ta yi tuninin samun kansa cikin sauki ba, amma saboda samunta ya dace ta kawo masa mutumcin ta gidan sa ya saka yake ganin wani ƙimarta a idanusa. Ba ƙaramin firgici Nadeeya ta yi ba na ganin Aunty Laila, ta san ba alkhairi ya kawo ta ba. "Aunty kece da safen nan?" Sadik da ya ji Muryar ta cikin firgici ya saka ya katse kiran wayar, ƙara taka motar ya yi sakamakon ya san Sunyi Laila ce ta je gidan. Kuma da gangan ya yi maganar a gaban Nabeela saboda ta isar da sakon ga iyayenta. Don ya san komai Hakuri yake bata akan cewa tana ransa ga shi nan dawowa. Don a lokacin Driving yake yi suke waya. Ganin Aunty Laila ta shigo cikin mamaki ta ce "Aunty kece?" "Wato ke dake yar banzar yarinya ce duk maganar da muka yi maki ya shiga ya fita daga kunnenki ne ko?" "Aunty me na yi?" "Ba komai je ki kawo Mani ruwa na sha." "Lah ga ruwa a nan ai yanzu na dauko ban sha ba." Ta yi maganar tana ɗaukar bottle watar mai sanyi za ta zuba wa Aunty Laila. "Ba lemu a gidan ne?" Sanin halin Sunyi Laila da bin ƙwakkwafi idan ta tashi zarta gane wani abunne ya faru tsakanin ta da Sadik, tunda yanayin tafiyarta ya canza. "Aunty ba lemu ruwa ne kawai a gidan, tun da jiya muka tare sai yau zai kawo." Jinjina kai Aunty Laila ta yi tare da cewa. "Okay wannan ruwan ya mani sanyi ina mura, je ki kawo mara sanyi." Jikinta ne ya yi sanyi, amma ba wata hanyar dole sai ta tashi. A hankali ta mike ta fara tafiya cikin kokarin daidaita tafiyar yadda Aunty Laila ba za ta fahimci komai ba. Shigar ta kitchen ba jimawa sai ga ta ɗauke da faranti da ruwa har da lemu. Tana zuwa ta zauna bayan ya ajiye mata a gaban ta saman Centre table. "Ina fatan dai kin dauki zantukan da muka yi maki, kina gasa masa aya a hannu." "Sosai kuwa." Finciko ta ta yi tare da cewa . "Munafuka zo na dubu ki ban yarda da ke ba sai ba duba ki, kwanta na gani Allah sai na dub ko na tabbatar bai taba ki ba." Ta yiagamar yana nuna wa Nadeeya doguwar kujerar wai ta kwanta. Kuka Nadeeya ta saka tana cewa ba abinda ya faru tsakanin ta da Sadik. "Za ki tsaya na duba ki ko sai na ci mutuncin ki a wajan nan?" A hankali ta durkusa tana kuka. "Kum yanzu za ki bar gidan nan, ba za ki kwanta na duba ki ba sai na Maki dukan tsiya. "Tana kuka za ta kwanta kenan sai ga Sadik ya turo kofar y shigo." "Akan me za ki duba ta saboda ta aikata zunubi?" "Kai mara kunya ka iya bakinka ko uwar ka A'isha ba ta isa..." Kafin ta yi wata magana sai ya finciki hannunta y yi waje da ita, a harabar gidan sannan ya sake hannunta. Alama ya yi wa Maigadi, wanda a guje ya tashi ya nufi ɗakin karnuka. A bude karnukan suka yi kan Aunty Laila, a guje suna haushi. Ihu ta ƙwala ta nufi hanyar gate ɗin. Takaliminta ma faduwa suka yi, sai da ta fadi ta fasa baki kafin ta tashi da ƙyar ta cigaba da gudun. Mayafinta ma faduwa ya yi, tana fita ta fada mota ba tare da ta jira direban ya bude ba. Sai haki take yi tana tsinewa Sadik albarka. "Hajiya lafiya ?" "Dalla mu je ina ruwanka." Bakinta da ya fashe jini ke fita ta goge tana cewa. "Allah ya tsinewa Sadik albarka A'isha ta haifo mana masifa da bala'i a cikin zuriya." Tsinewa Sadik take yi har suka isa gidan. _Hilal_ Fita y yi daga cikin gidan bayan ya yi order abinci ya ajiye wa Zahrah. Driving yake yi ransa a ɓace , sai magan yake yi shi kadai a cikin motar. "Mummi, Aunty Laila, Doctor why? MD ya saka kuka aikata haka? Tabbas zan aikata abinda ba yi maku dadi ba, Doctor yau zan hadu da ko kuma za ka girbi abunda ka shuka. Ba abinda zan wanke Zahrah da shi kamar na sex da ita a cikin gidan tafarki, na kira Sunyi Laila da Mummy zan ce su taimaka mata, a lokacin za ku amsa Mani tambayoyin da zan yi maku tambayoyi dole ku amsa Mani tambayoyin da zan yi maku." _Asadullah_ Yana zaune bakin swimming pool ya yi nisa cikin tunani, Wata mace sanye da bakin kaya har da niƙab a fuskarta. Hannunta rike da wauka, tana zuwa bayansa ta soka masa wuƙar ta bayansa . Daidai lokazin Jidderh ta farka ta daki wani ihu mai ƙarfi, tana cewa. "Yallaɓai.!?" Ihu ta yi fa kati sakamakon mafarkin an soka wa Asadullah wuka ta rikice. " Guje ta fito daga dakin ta hadu da kuku, kallonta yake yi yana mamakin jin tana magana. Son shi bai taɓa jin ta yi magana. "Ina yallaɓai yake yake?" Mamaki yake yana farin ciki da alama ta samu lafiya. Fita ta yi zuwa harabar gidanz, zare idanu ta yi tana kallon wajen, kafin ta ruga zuwa wajen guje. *Alhamdulillah na kammala book 1 ga mai son karanta book 2 sai tura ₦500 ta wannan account number. 2242538358 Zainab Abdullahi UBA bank sai a tura shaidar biya ta wannan lambar waya.09065327995*