[02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: 💞💞💞💞💞💞💞 💞💞💞💞 💞💞💞 💞💞 💞 *YESMEEN* 💞💞💞💞💞💞💞 *WRITEN BY:* *UMMYN YSRH* *®PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S* *(P.M.L)* _MASOYA NA KWARAI HAR ILAYAU BAKI BAZAI IYA FURTA KALAMAN GODIYA DA ADDU'A AGAREKUBA DA BAZARKU NAKE RAWA💃🏻_ *MERMUE* *(MRS JABO)* *YESMEEN TAFEESU* *QUEEN MIEEMIE* *RASH KARDAM* _Fatan alkhairi agareku_ _Allah k'ara d'aukaka_ _Allah k'ara nisan kwana da tsawon rai mai amfani_ _Ina godiya Allah yabar zumunci_ _DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN K'AI TSIRA DA AMINCI SU TABBATA GA FIYAYYEN HALITTA ANNABI MUHAMMADU (S.A.W)_ *1~5* Babbar motoce d'auke da d'alibai,kowacce kaganta cikin farin ciki take na murnar kammala makarantarsu ta secondary,motar d'auke da tambarin Gov't Girls College Bauchi (G.G.C.B). D'alibaine da yawa wanda suka fito daga garuruwa da yawa ko wacce za'a kaita har garinsu. Garin Jos suka dosa,duk d'aliban garin basu wuce mutum bakwai ba,kowa murnar komawa gida yake,daga gefe na wango wata y'ar budurwa zaune duk wake_waken da d'aliban suke bata sauraransu tunda suka d'auko hanyar garin nasu taji duk jikinta yayi sanyi ga kuma fad'uwar gaba da takeji,sun kuyarda kanta tayi jikin seat d'in moton. Tunda suka shigo garin ba wani hayaniyar mutane wasu guraren ga k'onannun motoci,kwata_kwata ba wani alamar mutane sosai agarin sai d'aid'aikun mutane dakuma jami'an tsaro,tasha aka sauk'esu motar ta k'ara lulawa gaba don kai sauran d'aliban garu_ruwansu. Sunfi awa guda suna zaman jiran abun hawa don kaisu gidajensu amma ba kowa duk shagunan kasuwar arufe suke ba mutane masu d'oki da wak'ok'i duk jiki yayi sanyi. Gajiya sukayi da jira kowacce ta d'aura d'amarar da'bawa ak'ar don tafiya gida. Haka suka rabu daga wajen *Yesmeen* datun amoto batada wani kuzari haka ta kwashi kayanta tayi gaba itama,ahanya tahad'u da wani take tambayarshi meke faruwa agarin nan yake shaida mata fad'ane ya kaure kwana uku dasukawuce,cikin dare aka rink'a bankama gidajen musulmai wuta musamman unguwar rogo anyi ta'adi sosai,jin an ambaci unguwarsu yasa tad'au hanya bataredata tsayajin k'arshen zancenba. Sauri take batamasan inda take jefa k'afartaba, burinta kawai Allah kaita gida lafiya. Abunda tagani ya mugun firgitata,gaba d'aya gidansu ya k'one ba alamar wani abun amfani ko rai mai motsi awaje duk da gidan nasu tamkar unguwace guda don duk danginsu na cikin gidan sai k'alilan da suke wani garin,don mafi yawansu auren dangi suke kuma duk wanda zaiyi aure cikin gidan yake zama. Salallami kawai takena _INNALILLAHIWA'INNA'ILAIHIRRAJU'UN_ nima dake gefe tayata nake had'e da kwalla😥 ~UMMYN YSRH~ [02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: 💞💞💞💞💞💞💞 💞💞💞💞💞 💞💞💞 💞💞 💞 *YESMEEN* 💞💞💞💞💞💞💞 *WRITEN BY:* *UMMYN YSRH* *®PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S* *(P.M.L)* *6~10* Salati kawai take tare da tafiya da baya da baya,ji tayi tayi karo da wani abu juyawar da zatayi taga k'onannen motar mahaifinta,ga mashind'in yayan babanta shima yasha wuta duk ya k'one,wani sabon hawaye takumaji ya kuma gangaromata,kamar wacce aka tsikara ta zura aguje tayi cikin gidan ba komai ciki sai gayyar toka da k'onannun k'asusuwar mutane da kuma gawayi. Sassa kusan gomane cikin gidan amma duk angama dasu,wasu sassanda wuta bai kamasuba jinine kwance awajen tamkar kwata mayankar dabbobi,da gudu tajuya tabar wajen gefensu tashiga ba wani abu cukinshi komai ya k'one wajen ajiye Qur'anansu ta nufa mamakune ya kamata ganin duk wani abu dake cikin lokar ya k'one amma wuta bai tab'a Qur'ananba sai d'an gefe_gefe wajen daba rubutu tace "ALLAHU AKBAR." saikuma tasake rushewa da kuka,wajen ta d'urk'ushe rungumeda Qur'anan. Jitake kawai inama azo asake cinnama gidan wuta ko itama suyi gunduwa_gunduwa da ita kozata huta,don ayanzu bataga amfanin cigaba da rayuwartaba. "Wai yaushe garinsu zai sami zaman lafiya?" "yaushe za'a daina irin wannan kashe_kashen?" "yaushe za'adaina maida mata zaurawa?" "yaushe za'a daina maida yara marayu?" "marasa yanci,galihu,bamai kuladasu,saidai ad'ebesu akaisu gidan marayu a jibgesu bamai kuma waiwayensu,bamai basu wadataccen ci,sha,sutura,uwa uba Ilmi." "Wai ina masu kud'inmu shuwagabanninmu?" "Yaushe garinmu zata sami tsaro adainawannan tashin hakula?" Maganganu kawai take ita kad'anta tare da tambayoyon dabasuda wani amfani balle amsa. Lokaci maitsawo ta d'auka durk'ushe awajen,tana tunanin wani irin rayuwa zatayi ayanzun idan tace Bauchi zata koma wajen k'anwar babanta wazai bata kud'in moto?,ina zata sami moton ta shiga? don daga dukkan alamu garin bashiga ba fitane,yanzu ya zatayi?kodai tazaunanan ko cikin dare itama zatasami masu k'arasata. Zamatayi tareda dura kanta cikin cinyoyinta,tacigabada kukanta,chan nesa takejin maganganun mutane,ji take kamar cikin gidan suke shigowa yadda takejin tafiyar manyan takalma tasan masu k'arasatane duk jikinta ya k'ara d'aukar sanyi,ko yatsar hannunta bata fatan ya motsa balle har tajega d'aga kanta taga yanayin halittar makasanta, chan taji wani daga cikinsu yana "gatacen" cikin wani irin gurb'atacciyar turanci. K'ara tura kanta tayi cikin cinyoyinta tareda k'ara rungume Qur'anan dake hannunta bisa k'irjinta mai barazanar rusowa. Jitayi andafata tareda rungumata lokaci guda kuma sai kuka,ahankali take d'ago kanta saidai har yanzu idonta rufe yake,harta gama d'agokan bata bud'e idonba illa hawaye dake gangarowa bisa k'uncinta,wacce ta rungumata tace " *YESMEEN*bud'e idonki nice." Ahankali take bud'e idon har tawaresu kan fuskan k'anwar mahaifinta da sauri itama ta rungumeta tana kuka tana fad'in " *UMMAH HABIBAH* sun kashesu,sunkashemana kowa,sunmaidamu marayu." "kishiru akwai Allah,kitamusu addu'a" "Taya zan daina kuka?" "yaushe ruwan idona zaidana zuba bisa zaluncin da cin zalin da akamana?" "har abada bazan dainaba,zan rayuwa inama duk wanda akama danginshi irin wannan cin zalin addu'ar Allah mana sakayya Allah yasa suyi k'ask'antacciyar rayuwa,sannan suyi mutuwar wulak'anci." "naji kima me kitashi mutafi don yanzu unguwar ba kowa don ko jiya saida akasake kahomusu wani harin." "kije kawai nizan zauna gara nima suzo su kasheni don ayanzu rayuwata batadawani amfani." "bazan iya barinki ananba,yanzu duk danginmu mu uku kawai muka rage,kitashi muje yanzuma da taimakon sojojinnan nasamu nashigo garinnan." Batakuma cewa komaiba tamik'e suka yi waje,wani harara take zubama sojojin don aganinta basuda wani amfani tunda har za'ayi wannan ta'asar basuyi yunk'urin hanawaba. Fita sukayi daga konannen gidan suka nufi wajen motocinsu,kayanta data dawo dasu tahau d'iba suka sa cikin moton,kallon gidan kawai take tana k'ara rushewada kuka shikenan tagama rayuwarta agida? Shikenan yanzu rayuwarta ya koma wani garin? Meyasa basuyi jinkiri harsai ta dawo suhad'a da ita sukasheba? Meyasa sukabarta araye? Runtse idonta tayi yayindataji direban *UMMAH HABIBAH* Ya tada motor, har sukabar garin jos bata bud'e idontaba,saida sojojin suka fiddasu garin kafin suka juya. ✍🏻 ~UMMYN YSRH~ [02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: 💞💞💞💞💞💞💞 💞💞💞💞💞 💞💞💞💞 💞💞💞 💞💞 💞 *YESMEEN* 💞💞💞💞💞💞💞 *WRITEN BY:* *UMMYN YSRH* *®PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S* *21~25* Yau satinsu d'aya da dawowa,saidai sam batajin dad'in abin da ake ma Umman nata,yadda dangin mijinta da Uwargidan ta ke mata na gorin rashin haihuwa. Shekarar ta goma da aure Allah bai bata haihuwa ba kullum cikin gori da bak'ak'en maganganu take sha,wajen mijinta kawai take samun sauk'i. Wai da wanne za taji ne? yanzun da rashin dangin ta ko da matsalar kishiya da dangin miji na rashin haihuwa?. Me yasa mutane suke manta cewar Allah shi ke bada haihuwa ba wayon ka ko dabarar ka ba?. Wa za ta kai ma kukan ta a yanzu don ya sharemata hawayenta? Y'ar uwarta da ta ke gadara da ita ko kad'an basu gaban ta a yanzu giyar kud'i na d'ibanta ta manta da su tayi watsi dasu ta samu sabin dangi, su d'in ba kowa bane a gare ta. Zata ci gaba da kaima Allah kukan ta,shi zai mata maganin matsalolinta. Haka rayuwars u ta kasance cikin gidan,duk da ba wani shahararren arziki ga mijin Ummah ba,yana da rufin asirin shi daidai gwargwado, yana kuma iya bakin k'ok'arin shi kan iyalan shi. *YESMEEN* ta ware sosai sai dai ko da yaushe tunanin ta yana wajen y'an'uwan ta marayu,ko suna cikin wani hali?duk sanda zata wurga loman abinci bakin ta sai ta tuno dasu ko sun samu sunci?,idan sabon sutura zata sa sai tayi tunanin ko suma sun samu sun sa? Da sauri ta shiga gida kamar zata tashi sama, ko sallama babu ta nufi falon gidan daidai zata wucesu taji ance. "Toh jikan marasa kunya iyalan kalan dangi da chusa kai,kin shigomana gida ba sallama balle gaisuwa." Juyowa tayi tana kallon mai maganar ji take duk sanda taga matar kamar ta dab'a mata wuk'a don tsanar DA ta ke mata. Amsa tayi niyyar bata sai kuma ta fasa tace "Sannun ku masu gida." Wata daga gefe tace "fad'i ki k'ara fad'i yarinya,gida namu ne sai dai mutum yazo yaci arzik'i ya k'ara gaba." dariya tayi sannan tace "Ruky kike kowa? Kalleni tsaf kin san nafi k'arfin shigowa gidan nan inci arzik'i,ke kanki kinsani." Umma Habiba ce ta fito daga kitchen tace "ke Hanifa sa'i'on ki ne su da zaki rink'a musu magana haka?kul ko da wasa bana son hakan,wuce ciki k'awarki na d'aki." Wucewa tayi tana watsa musu harara Kishiyar Umma Hajiya Talatu tace "ai dole ki korata tunda kin sa ta gama yi mana rashin kunya,haka dai zaki k'are akwashe_kwashen y'ay'an mutane da cika mana gida da manyan kashi." Juyawa tayi ba tare da ta kuma tanka su ba. Zuciyarta sai k'una yake kamar ta Ciro shi waje ta huta don azabar zafin da ke mata. Ihu yaran suka sa lokacin da ta juya suna ma Uwar tasu kirari da Sai Mama uwar masu gida. D'aki Hanifa ta shiga tana kwalama Yesmeen Kira. "Ke wallahi kin fiya Kira kamar makauniya,ki k'araso gani ciki guga nakeyi." "Dallah ki tashi ki shirya anjima zamu unguwa." "Unguwa kuma? Wacce iri,kuma ina?" "Ohho! nidai ki tashi ki shirya zuwa k'arfe biyu zamu tafi." "Idan nayi niyar zuwa ko ban yiba zaki sani dole kenan?" "Malaman su aima dole kije Wallahi,bari ma ki gani b'ata lokacina nake gurin ki idan na had'aki da Ummah dole kije Baby." Fita tayi tana mitar mutum kullum sunk'ume a gida kamar wani mummunan amarya. "Me kikecewa?" "Nace Allah barmu da wannan k'awa tawa y'ar ra'ayi da jan aji." "zaki sani idan na rik'eki zaki gayan wace mummunar amaryar". "Au! ashe kin jinine." "A'ah kinsan na zama kurma." K'arasa ficewa tayi tana dariya. Kitchen ta nufa gunda Ummah keta k'okarin had'a abincin rana tace "Ummah dama nazo tambayar ki ne don Allah Yesmeen ta shirya muje wajen hidimar bikin d'iyar k'awar Hajiyata." "shine sai kin tambayeni? ai an zama d'aya." "ai nace ta shirya muje wai ba za ta ba." Tak'arasa maganar tamkar mai shirin kuka. "tsokanarki take,jeki shirin ki zan mata magana." ✍🏻 *~UMMYN YSRH~* [02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: 💞💞💞💞💞💞💞 💞💞💞💞💞 💞💞💞 💞💞 💞 *YESMEEN* 💞💞💞💞💞💞💞 *WRITEN BY:* *UMMYN YSRH* *®PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S* *(P.M.L)* _THIS PAGE IS 4 U MY CHUCHU😍_ _ALLAH YABAR ZUMUMCI SO DA K'AUNAR JUNA_ *11~20* Saida sukayi nisa da tafiya kafin ta bud'e idon da taji *Ummah Habibah* nacewa "ohh! wato nan akazo aka zubara mutanenmu?" Kallon wajen nayi asannan na gane wani gari muke, *TILDEN FULANI* mutanene birjik awajen mafiya yawansu matane da k'ananan yara sai maza y'an tsiraru,kowanne ka kalleshi kasan fitowan rashin shiri yayi. Tsayawa moton tayi muka fita don duba y'an gudun hijiran ko Allah zaisa muga wasu daga cikin y'an'uwanmu. Makarantar bokoce aka ba y'an'gudun hiriran da suka haura sama da mutane dubu uku,ajujuwa shine wajen kwanansu,rijiya guda d'aya tak shine wajen d'iban ruwa domin yin ibadansu da kuma girki ahakan wasu daga cikin y'an garin suna d'iban ruwan cikin gara kuna suna kaiwa gari domin samun taro sisi. Kan sumintin da duk ya farfashe yayi rami shine makwansu, Babu tabarma balle kuma katifa, ga buhun shinkafa uku da garin masara biyu da gwamnati ta aiko musu dashi don girkawa. Jefe chan ga yara birjik sai kuka suke ba iyaye ba y'an'uwa,ankashe kowa nasu. Shin wazai tallafi rayuwar wad'annan yaran? Suwa zasu mayemusu gurbin iyayensu? Wani irin rayuwa zasu fuskanta? Wazai tallafi rayuwarsu ya basu ingantattaciyar kulawa? Ahaka rayuwarsu zata k'are ko kuma zasu sami masu tallafamusu domin zama manyan gobene da ake ikirari? Daga jefe nace mata babu mai iya baki amsar tambayarki,ki musu addu'ah kawai,Allah shine gatansu shine kuma jagoransu. Allah ya rayasu bisa turba madaidaciya. Juyawa tayi ta kuma ganin yadda yaran ke kuka da kiran iyayensu,juyawa tayi da gudu tana wani irin kuka mai tsuma zuciya,jitake kamar zuciyarta zai fito ya tarwatse. Tunda ta shiga moton ta duk'ar da kanta k'asa ta runtse idanuwanta bata kuma bud'ewaba tanaji Umman nata suka shigo direba yaja ahankali tace "Allah kawo muku sauyi cikin gaggawa." "Allah kawo masu tallafawa rayuwarku" "Allah bi mana hakkinmu,ya mana sakayya." *AMEEEEEEN* Ba wanda ya kuma magana har suka iso cikin garin Bauchi,unguwar Fedral low_cots suka nufa gidan Umman. Suna isa ta wuce d'akin Ummah Habiba,ta ajiye kayanta bayan gida kawai ta wuce alokacin shida harda wani abu,gashi ko sallar azahar bataiba,tun d'azu neman gafarar ubangiji kawai takeyi na had'a sallolin da tayi,tana watsa ruwa ta d'auro alola ta sunkuya bada farali. ✍🏻 *~Ummeen yusrah~* [02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: 💞💞💞💞💞💞💞 💞💞💞💞💞 💞💞💞💞 💞💞💞 💞💞 💞 *YESMEEN* 💞💞💞💞💞💞💞 *BY:* *UMMYN YSRH* *®PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S* *26~30* Haniface ta shigo cikin shirin tafiya,sanye take da riga da wando duk sun d'ameta sai after dress data d'aura,gawani takalmi mai uban tsini kamar kifiya. Haka ta shige d'akin Umma ba tare datama kowa maganaba. Tana shiga tasamu Yesmeen tagama shiri itama,atamfa tasa da gyalanta mai d'an girma da d'an flat shoe nata ba laifi tayi kyau. Kallo Hanifa ta bita dashi tace "ke wallahi har yanzu baki wayeba,saikace ba girman Jos ba." "wacce irin wayewa kikeso inyi?" "chasufa za'ayi, amma kin wani d'au atamfa kin saka habba! aisaikiban kunya." "Tooow! Shigar tawace bataiba kome?" "Eh." "Don Allah muje gida inbaki wasu irin nawa kisa." "Allah sauwak'emin." "Waiku me kuka baku fito kuntafiba,idan kun had'u sai kuntab'a hali." "gamu fitowa." Fitowa sukayi suna hira suna dariya kamar ba yanzu suka gama rigimaba. Y'an gidan sai binsu suke da kallo ana maganganu k'asa_k'asa. Suna fitowa Hanifa tace "d'an jira inshiga gida in d'auko aika saimu wuce." "ki sauri karki dad'e." Fitowa tayi hannunta d'auke da wani d'an madaidaicin jaka. "mujeko baby." Adaidaita suka shiga Hanifa tace "Malam Fadamar mada zaka kaimu d'angaba da asibitin Alwadata." Ciniki sukai ya kwashesu,lokacin da sukazo wucewa wajen Makarantar kwana ta G.G.BAUCHI Yesmeen jitayi kamar ta shiga,amma haka aka wuce. Shiga sukayi da sallama wata y'ar matashiyar budurwata ta lek'o da fara'arta tace "sannunku da zuwa kushigo." Falo suka shiga suka zauna,wata budurwa tafito da gani tad'an girmesu "sannunku da zuwa manyan bak'i." "yawwa sannu. kina lafiya?" Gaisawa sukayi,akata shigo musu da abinci da abunsha,gawani girmamawa da ake musu, itadai Yesmeen tazama y'ar kallo su Hany kuwa an sake sai hira ake. Itadai Yesmeen abun ya d'aure mata kai tunda sukazo bataga matan gidanba sai gayyar yaran gida masu kama d'aya,takuma rasa ina tasan mai wannan kamannin. Wajen k'arfe uku da rabi budurwar maisuna Salma tace "nakai muku ruwan wanka, kushirya zuwa k'arfe hud'u za'a tafi." Yesmeen tace "wanka kuma? ai munriga munyi wanka tun kafin muzo." Hanifa tace "Mungode Aunty Salma." Mik'ewa tayi taje tai wankarta ta dawo d'akin su Salma,nidai shiga nayi na gyara kaina dayake lokacin period d'inane. Ina fitowa naga Hanifa ta d'au kwalliya sanye da wasu riga da wandon,kawai baki nasaki ina kallonta. "Gashi kisanya tunda kink'i ki wankan." Dubawar dazanyi naga wasu riga da wando da kad'an zai wuce gwiwata idan nasa,wurgamata nayi nace "Bana buk'ata kema kinsan ida nayi niyar sawa tun agida gaban iyayena zansa ba abayan idonsuba,abunda banyi agaban idonsubako bazanyi abayan idonsuba,idansu basa ganina ALLAH yana ganina." Kwashe kayan tayi batace komaiba,kiransu akayi su fito ana jiransu waje. Godiya sosai sukayi suka fice,motar da Yesmeen tagani shiyasata fad'uwar gaba,motar abokin saurayin Hanifane. Sai yanzu ta gane 'yan gidan da abokin saurayin suke kama. Tik'ashi! dama gidan saurayi ta kawosu? ranta inyayi dubu ya b'aci,motar kawai suka shiga ba tare datace komaiba. Basu zame ko inaba sai School of armour, tundaga k'ofar hall d'in kid'a ke tashi fita sukayi daga cikin motan suna fita Hafiz juya abunshi,Hanifa da saurayinta Adam rik'e da hannun juna biye nake dasu har cikin wajen. Lokacin da mukashiga wajen cike yake da mata da maza,musulmai da chirista saidai ko kad'an bazaka tab'a iya banbance wace Saratu wace Sarah ba,duk shigar d'ayane sai rungememeniya ake tareda taka rawa wasu agefe sai shaye_shayen kayan maye suke Subhanallah! Mezamucewa ubangijinmu kan kiwon daya bamu. Kana iya k'ok'arinka wajen ba y'ay'anka tarbiya wasu b'ata gari suna warwarema. Allah kar kabarmu da iyawarmu kamana jagora wajen ba y'ay'ayenmu tarbiya. Fitowa kawai nayi daga cikin hall d'in don idona bazai iya jurar kallon wannan iya shegenba. Nafi awa tsaye awaje ina tunani yadda zan koma gida ga wajen da d'an karan nisa. Jinayi an rik'emin k'ugu tare da fad'in "fine baby ke bazaki shiga ayi rawar dake bane?" Juyowa naye da sauri na tureshi tare da kwad'a mashi mari cikin b'acin rai. ✍🏻 *~UMMYN YSRH~* [02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: 💞💞💞💞💞💞💞 💞💞💞💞💞 💞💞💞💞 💞💞💞 💞💞 💞 *YESMEEN* 💞💞💞💞💞💞💞 *STORY & WRITEN BY:* *UMMYN YSRH* *®PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S* _KINCHANCHANCI YABO TA KO'INA DOLE IN YABA KUMA IN GODIYA DA FATAN ALKHAIRI AGAREKI_ *SIST HALIEYMERH AMEEN* _ALLAH JA KWANA DA LFY MAI AMFANI ALLAH K'ARA D'AUKAKA YABAR ZUMUNCI_😘😘 *inaba masoya wanna novel hak'uri na rashin jina da sukayi na kwana da yawa amin afwa kunsan jiki da jini😥* *35~40* Fitowa tayi da sauri da nufin shiga kitchen don taji kamar miyarta na kamawa,bata kulaba ji tayi ta buge mutum,juyowa tayi don bata hak'uri,saidai kafintayi magana Hajiya Talatu ta rigata, cikin masifa tace "Tooow! Muguwa,y'ar bak'in ciki.shine kika taho aguje don ki bangajeni? Kina bak'in cikin cikin jikina ko? Burinki ya zube muzama d'aya ,toh ta Allah ba takiba,keda haihuwa saidai kiga munayi,mun ajiye biyar gana shida yana hanya." Ummah Habiba tace "don Allah ki hak'uri bada niyya na buge kiba,miyace naji tana kamawa na shiga sallah shine na fito da sauri,amma ki hak'uri." Sallama sukaji daga k'ofar falon da sauri Hajiya Talatu ta durk'ushe gurin tana rik'e ciki,tare da bubbuga y'ar yatsarta kamar mai nak'uda,lokaci guda ta fita hayyacinta. Umma Habiba ta amsa sallamar tareda yima mai sallamar barka da zuwa saidai ko kad'an batabi ta kantaba, "Subhanallah! Talatu meke faruwane?" Cikin muryar wahala tace "ina d'aki naji miya na kamawa a kitchen shine na duba na fito zan koma d'aki, shine Habiba ta fito ta nufoni gadan _gadan ya gulleni a cikina." "ita Habiban!!?" "eh,wai don meyasa zan tab'amata girki alhalin nasan baran girkina bane." "toh!muguwa mai bak'in hali,y'ar bak'in ciki,duk tsiyarki sai jikana na fito duniya,idanma burinki cikin ya zube toh k'aryarki munafuka,duk abunda yasami cikinnan k'arshen zamanki kenan agidannan wallahi." "wallahi bada sani na bugetaba Haj......." "rufemun baki,tunda tasamu cikinnan kike bak'in ciki,zamuje asibiti yanzu adubata kuma Wallahi ina k'ara gaya miki akasami wani abu ya tab'ata abakin aurenki." Kama Talatun tayi ta zaunarta kan kujera taje ta d'auko mata hijabi a d'aki sukayi gaba,juyawar da Umma Habiba tayi zatayi kitchen wani jiri ya d'ebeta ta zube k'asa. Tana kaiwa k'asa YESMEEN na shigowa hannunta rik'e da ledar aikar aikan a k'asa da gudu ta k'arasa gareta tana fad'in "UMMAH lafiya? meke faruwa.? "bakomai jirine ya d'ebeni,taimakamin intashi." Kamata tayi don ta mik'e saidai ina ta mata nauyi bazata iyaba,gashi gidan ba kowa koda akwima ba kulasu zasuyiba. Dagudu ta fita tayi gidansu Hanifa,rabondasu had'u tunranda abunnan ya faru. Har k'asa ta d'urk'usa tagaida Mommy tace "Mommy Hany tanan kuwa?" "tana ciki,ya jikinnaki tace bakiji dad'iba,bansami zamaba shiyasa banshigo na dubakiba." "jiki yayi sauk'i sosai." "Toh Allah k'ara afwa." "Ameen." D'akin k'awar tata ta nufa Hanifa na ganinta taji wani dad'i da farin ciki. "Don Allah idan bakya komai zo ki tayani wani abu." "lahh! bana komai dama kwanciya zanyi muje." Gidan suka nufa da sauri,inda ta barta nan ta sameta,gasu RUKY da k'annenta biyu zaune a falon ba wanda ya kulata. Suna k'ok'arin d'agata saiga Zarah ta fito hannunta d'auke da ruwa ta nufo gurinsu YESMEEN tace "Aunty YESMEEN ga ruwan Auntyce tace in d'ebo mata zata sha,nace ta tashi wai bazata iyaba." "eh,ZAHRA jiri takeji." Ruwan ta bata tasha sannan suka kamata su ukun da kyar don UMMAH HABIBA akwai k'iba kamar k'awata (HAMEBRAH MAI BABBAN DUWAIS🙊) Gado suka kwantar da ita ko zuwa anjima zataji tare. Sai wajen biyar Y'an asibiti suka dawo,Hajiya Talatu ras da ita kamar ba ita ake rik'ewa d'azunba. Su RUKY suka tarar zauna ana kallo ba batun sallar azahar balle la'asar,sun tasa T.V agaba kamar ibada. Hajiyace tace "Ina Bibanne taji mundawo don bak'in hali bazata fito ta duba muba?" Zahra data fito daga d'aki tace "sannunku da dawowa.Aunty na d'aki kwance batajin dad'ine." "k'arya take ba wani rashin lafiya muna furcine kawai,don nace idan wani abu yasami surukata da jikana abakin aurenta shine bari ta kwanta ciwon k'arya." "Hajiya rabu da ita wani salon muna furcinne." "koma me ita ta sani Allah ya taimaketa ba abunda ya sameku ai." ✍🏻 *~UMMYN YSRH~* [02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: 💞💞💞💞💞💞💞 💞💞💞💞💞 💞💞💞 💞💞 💞 *~YESMEEN~* 💞💞💞💞💞💞💞 *STORY & WRITEN BY:* *~UMMYN YSRH~* *®PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S* *Dis page is 4 u my sist Luv* *YESMEEN TAFEESU* *Allah yabar zumunci yy rabaki da iyaye lfy ya miki zabi da miji na gari da zuri'a masu albarka* 👏🏻 *41~45* Har wajen magrib Ummah na kwance gawani matsanancin ciwon kai dake addabarta,gashi tak'i yarda inma Alhaji waya in sanarmai kasancewar baya gari. Har wajen k'arfe takwas na dare ba wanda ya lek'o duba Ummah y'an cikin gida,sai Zahra itama saita faki idonsun take shigowa gudu_gudu ta dubata ta fice,Mommyn Hanifa ma tazo ta duba Umman,Hanifa kuwa tunda suka shigo d'aga Umma bata komaba,jitake kamar tacire ciwon tamaida jikinta don harda kukanta. Yesmeen ce ta d'au wayar Ummah ta danna wayar k'awarta kuma kwararriyar likitanta, Hajiya Amira tana d'agawa Yesmeen cikin ladabi ta gaisheta sannan tamata bayanin abundake damun Umman nata,tace "Gatanan zuwa yanzu ta fito daga asibiti zata gida kenan." Sallama sukayi ta katse wayar. Ba'ad'au wani lokaciba ta iso gidan,Sallama tayi k'ofar falon ba wanda ya amsa mata sai Zahra,shigowa tayi tama Hajiya Talatu barka da dare,dak'ar ta amsa mata tayi wucewarta. Da sallama tashiga d'akin su Hanifa suka gaisheta,kan k'awar tata ta nufa tana fad'a "Habba! Hajiya nace kidaina yawansa damuwa ma ranki,komaifa d'an hak'urine da juriya,lafiyarki ayanzu ya fiyemiki komai,kinsani sarai Zuciyarki daf take da tab'uwa amma kinasa damuwa ma ranki,barin gwada B.P naki meyuwa yasake hawane?" "Subhanallahi! Jininki ya hau sosai,garin yaya? Wani irin damuwane haka ya sa jininki ya hau har haka? Ummah dake kwance hawaye kawai ke gangarowa daga idonta. YESMEEN dake gefe tambayar kanta take "dama Ummah nada hawan jinine? Koshiyasa take yawan zuwa asibiti? Allah sarki Ummahna." "Allah ka azurtata itama da sanyin idaniyarta,Allah ka bata lafiya." Da sauri ta shige bayan gida ta rufe kanta,tanaji Dr.Ameerah tagama yimata y'an nasihohi tare da bata magunguna da allurai,wasu Umman nadasu,wasu kuma sai zuwa gobe za'a siyo tunda dare yayi yanzun ba halin Yesmeen ta fita. Sallama sukayi da likitan,da k'ar Ummah ta rarrashi Hanifa taje gida zuwa gobe saita dawo,badon ranta yasoba haka ta fito Yesmeen ta biyota domin rakiya,bayan ta rakata ta juyo zata tafi idonta ya mata mummunan gamo, Ruky ta hango chan gefe jikin wani lunge rungume da saurayinta,gaba d'ayan hannayenshi na cikin rigarta. Wa'iyazu billahi hirar wasu samari da y'anmatan zamaninmu nayau kenana,Allah ka shiryamana zuri'a. Da sauri tashige gidan tambayar kanta take ko lafiya harabar gidan ba wuta d'azu dazata wuce taga wuta, ko kwan ya mutune ohho. Hannu takai jikin k'ofar da zai sadata da cikin gidan sai dai maimakon taji k'ofa sai taji kamar jikin mutum ta kama,da sauri taja baya cikin tsoro tana, Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un Ta juya zata sa gudu tayi waje taji charaf an chafketa,runtse ido kawai tayi tana jero addu'o'in dayazo bakinta don tasan yaukam tata ta k'are yaukam tayi gamo,don dagajin irin wannan damk'ar da akai mata bana bil'adama bane. Cikin sanyin murya kamar mai rad'a taji yace "Yesmeen! Don Allah ki taimakeni ko leb'en bakinki in tsotsa ko zan samu sukuni,kullum da sha'awarki nake kwana nake tashi." Dummmmmmm!!!!!! taji k'irjinta yabada sauti, ba kowa ya mata wannan aika aikanba face babban d'an Hajiya Talatu Sani. Kokawar yadda zata kwaci kanta take shikuma k'ok'arin cika burinshi yake,cikin ikon Allah sukaji bud'e k'ofar Gate d'in alamun shigowa,da sauri ya saketa yana ciza yatsa yace "Next time." K'ofar falon ya bud'e tayi saurin shigewa,shikuma ya wayance kamar wanda ya fito daga ciki Ruky na ganinshi tace "Ah! Yaya bakai baccibane?. cikin k'uluwa dajin haushi yace "banyiba y'ar iska jiranki nake,don kinga Alhaji baya gari shine bari kikai dare haka awajeko?" harararshi take cikin duhu tace "kaima yaud'in ai sa'a akaci kadawo gida da wuri." "naji wuce ni kuban waje,wutannan nazo dubawa naga ya d'auke." Wucewa tayi hannuta d'auke da ledodi guda biyu,tana wucewa yaje ya kunna wutan daya kashe dama yana ganin fitar Yesmeen ya fito daga d'akinshi da sauri ya kashe wutan domin cikar burinshi,saidai Allah bai bashi sa'a ba. Ahankali ta shiga d'akin gabanta sai fad'i yake tana tunanin k'aryar dazatama Ummah idan ta tambayeta musabbabin dad'ewarta. Hamdala tayi dataga tayi bacci,waje tasamu itama ta kwanta tare da addu'ar neman tsari dakuma fatan kar Allah yaba Yaya Sani galaba akanta. ✍🏻 *~UMMYN YSRH~* [02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: 💞💞💞💞💞💞💞 💞💞💞💞💞 💞💞💞💞 💞💞💞 💞💞 💞 *YESMEEN* 💞💞💞💞💞💞💞 *BY* *UMMYN YSRH* *®PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S* *31~35* Mutanen dake wajen duk suka juya don jin k'aran marin. Wata daga gefe tace "kai! yau JENTLE aka ma wanna marin? tashin hankali." Da gudu ta garzaya cikin hall d'in don isarda abunda ya faru. Cikin b'acin rai YESMEEN ta kalleshi rai b'ace take zazzagamai "Don tsabar iskanci uban wa yabaka izinin tab'ani? Kai waye cikin muharramaina da har zaka kai hannunka jikina? "ka dubeka,ka dubi shiganka ahakan idan an tambayeka zaka iya cewa kai musulmine." "kun maida tab'a jikin junanaku tamkar wani sabon salon wayewa" "ayau wai idan saurayi baitab'a jikinki ba sam baki wayeba." "meye wayewar awanna d'abi'ar da rayuwar." Waje yagama cikewa da mutane, "Kudubeku amatsayinku na y'ay'a mata kuduba irin shigar dake jikinku na tabbata mafi yawanku bada wannan shigar kuka baro gidajen iyayenkuba." "kunzo sai tabka zunubi da sab'ama ubangiji kuke." "su mazan da kuka bari suke rungumeku suke shafe ko ina na jikinku kunada tabbacin aurenku zasuyine?" "idan kunkai ga aure wani k'ima da daraja zakuyi a idonsu?" "ko kuna tunanin zasu gama daku wani ya kwasane?" "ko kad'an ba wanda zaiso zab'ama y'ay'a yenshi uwa ko ubanda bama gariba." "wasu daga cikinmu bada sanin iyayenmu mukazonan ba idan Allah ya d'au rayuwarmu ahakan mezamucema Ubangijinmu." "ga sab'ama ubangiji ga ha'intar iyayenmu dasuka d'au tsawon lokaci suna bamu tarbiya maikyau,mukuma muna ha'intasu." "babu uwa ko uban da zaiso ganin y'ay'anshi cikin wannan shiga da mummunan yanayi da wasu daga cikinku suke." "ayanzu mund'au rayuwar shaye_shaye wayewa da burgewa baga mazanba baga matanba." "munsai cuta da hannunmu mun banka ma cikinmu,akwan kad'an kaga mutum nabun hanya yariga yamai illah,kekuma kinriga kin b'ata mahaifarki da kanki." "wani riba akaci arayuwar shaye_shaye?" "karfa kumanta duk abunda d'a namiji yayi adone,keko yananan yana bibiyarki har k'arashen rayuwarki." "amatsayinmu na iyayen gobe idan mukaga iyayenmu cikin irin wannan yanayin ya zamuji azuciyarmu?" "ku kwatanta hakan don suma iyayenmu haka zasuji idan sungamu ayanzu." "muji tsoron Allah, muji tsoron randa zamu tsaya gaban ubangijinmu." Tana kaiwanan tajuya tabar waje Y'an isgili jikake "Allahu akbar malama." Suka juya sukayi ciki akacigaba da holewa Way'anda abun ya shigesu suka shiga domin tattara kayansu suyi gaba. Su malam JENTLE tunda yasha mari akabarshi tsaye sake da baki ranshi inyayi dubu ya b'aci yana tuna irin hukuncin dazai mata,kawai ganin bayanta yayi tayi gaba. Adam ya kalli Hanifa yace "Wai ina kika kwaso mana wannan y'ar k'auyen?" "Y'ar k'auyefa kace?" "YESMEEN d'ince baka saniba kome?" "idan nasanta seme? Baki gayamata inda zakizo bane duk ta b'atamana show yadda mukaci burin chashewa da kwasar garar y'an mata." "owwwohhhh! Nufinku kenan akanmu? Toh Allah bai baku nasaraba." "kuma kasani zan iya jure cin mutuncinda za'amin, amma kar mutum yasake ya tab'a YESMEEN don akanta sai inda k'arfina ya k'are." "kuma kasani duk bibiyar club danakeyi bantab'a saida mutuncina ga wani d'a namiji ba balle har kaci galaba akaina." Ahaka suka rabu baram_baram,ta kwashi kayanta tayi gaba. Lokacin data fito chan nesa ta hango YESMEEN tanata tafiya lokacin gari ya fara duhu,sauri sauri gudu gudu ta iskota tace "Don Allah ki yi hak'uri y'ar'uwa danasan hakan zai faru kodawasa bazan fara gayyatokiba,Don Allah kimin afwa na tuba." Juyowa tayi tamata wani irin kallo ta juya batace komaiba, adaidaita suka shiga, har suka iso gida ba wanda yakema kowa magana, suna sauka tashige gida,kafin Hanifa tasallami mai adaidaita harta shige. Jitayi kamarta bita saikuma ta fasa zata bata lokaci harta huce. Lokacin data dawo Umma Habiba taga duk yanayinta ya canza,tambayarta tayi " meke faruwa?" Taso ta b'oye mata tamata k'arya saikuma ta tuna idan tayi k'aryar ribarme zata samu, Kaf ta kwashe abundaya faru ta fad'a mata har rabuwarsu. Umma Habiba tace "amma bai kamata kurabu da Hanifa hakaba,idan kinga mutum ya kauce hanya k'ok'ari kiga ya dawo kan hanya baki barshi yacigaba da gurb'atacciyar rayuwaba." "hakane rainane kawai ya b'aci." "karki manta Hanifa mai son muce batada wani mummunan hali,duk abunda take cikin gidannan tanayine don jin haushin abunda ake mana badon rashin tarbiyaba." "yanayin shigarta kuma ahankali zata daina tunda cikin barikin sojoji ta taso cikin garin Lagos,dole yanayinta zai banbanta damu." "karki manta da taimakon babanta nasami shiga Jos na d'aukoki tunda shid'in babban sojane." "kiyi k'ok'arin daidaitawa da ita domin sata hanyardata dace." "Insha Allah Ummanah." *✍🏻 ~UMMYN YSRH~* [02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: 💞💞💞💞💞💞💞 💞💞💞💞💞 💞💞💞💞 💞💞💞 💞💞 💞 *YESMEEN* 💞💞💞💞💞💞💞 *STORY & WRITEN BY:* *UMMYN YSRH* *®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *(P.M.L)* *51~55* Wani sabon unguwa suka dosa,unguwar bai fiya yawan mutaneba,kowa damuwarshi yake bamai shiga sabgar wani,k'ofar wani d'an madaidaicin gida suka dosa,kafin YESMEEN su iso har sun shiga gidan. Mai napep d'in ta sallama sannan ta nemi waje ta zauna,takai wajen awa d'aya da rabi tana zaman jiran fitowansu. Fitowa sukaye,yanzu duk sun sauya shiga,budurwar sanye take da doguwar riga ta yane kanta da d'an k'aramin d'an kwalin,su Alhaji ansha jamfa da babbar riga. K'ok'arin bud'e k'ofar moton suke zasu shiga,da sauri Yesmeen ta taso ta iso gabar budurwar,ganin Yesmeen datayi ba k'aramin razana tayiba. Ahankali Yesmeen tace "IHSAN kece kodai idonakemin gizo,meya kawoki nan? Yaushe kikayi aure?" Kasa magana tayi,gyad'a kai kawai take. Alhaji dake cikin moto yace "shigomana kinsanfa Abuja zan wuce,waye wannan d'in." Wani kallo Yesmeen ta watsamai,na takaici da bak'in ciki. "kaje kawai Alhaji zamuyi waya, 'yar'uwatace." kallon Yesmeen yake zuciyarshi na ayyanamai irin dad'in dazai kwasa wajenta inda zai sameta dun wasu tarkacen 'yan mata zai watsar dasu. "Gawannan kuyi kud'in napep." Karb'a Ihsan tayi ta duba dubu biyune,sallama sukayi ya k'ara gaba. Tafiya sosai sukayi kafin su fito bakin hanya dak'ar suka sami abun hawa,ba wacce tama wani magana har suka isa wajen saida maganin,ta saya ta dawo suka d'au hanyar gida. Ummah sai zurga_zurga take duk hankalinta atashe yake,tun k'arfe tara da rabi Yesmeen ta fita har yanzu sha biyu da wasu mintoci ba labarinta,Hanifa ta fita dubata har chemist d'in ba ita ba labarinta. Sallamar Yesmeen taji daga falo wani dad'i taji,tare taga sun shigo da wata,sai kallonta take tarasa inda tasanta,tambayar Yesmeen tayi "lafiya taje ta zauna haka?" Kaf takwashe abunda yafaru ta sanar mata Ummah ajiyar zuciya tayi don ta fuskanci irin rayuwar da yarinyar take ciki,kowa hidimar gabansa yake basu buk'aci jin komai daga garetaba saida dare yayi kowa y rufe k'afa Ummah ta tarasu ta fara tambayarta "Amatsayina na mahaifiya agareki koda banji labarinkiba tabbas na fuskanci irin rayuwar da kike ciki ayanzu,naji zafi da ciwon abun,garin yaya kika jefa rayuwarki haka? Meyasa kika zab'i kisaida mutuncinki ga mazanda mijin Aurenkiba?" Kuka kawai take takasa furta komai "ba kuka nakeso kiyiba tambayarki nayi idan baki buk'atar sanar dani shikenan kiyi hak'urin kukan dana saki,Yesmeen tashi kuje ku kwanta. "kuyi hak'uri ba k'in sanar daku nayiba,tabbas Abunda kika fad'i hakane, A dalilin maraici yasa namaida mutuncina tamkar haja, A dalilin rashin mafad'i yasa nake komai ba tare da kwab'aba." _Toh fah🤔_ _kumin afwa zuwa gobe zanci gaba insha Allah_ ✍🏻 *~UMMYN YSRH~* [02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: 💞💞💞💞💞💞💞 💞💞💞💞💞 💞💞💞💞 💞💞💞 💞💞 💞 *YESMEEN* 💞💞💞💞💞💞💞 *STORY & WRITEN BY:* *UMMYN YSRH* *®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *(P.M.L)* *56~60* Labari taci gaba da basu. "Kamar yadda kuka sani gidaje hud'une kawai tsakanin mu daku agarin Jos,kwatsam wata rana cikin dare aka rink'a cinnama gidajenmu wuta,wuta da yayi sanadiyar salwantarda rayukan al'umma da dukiya mai d'umbin yawa,duk 'yan gidanmu sun k'one nida mahaifiyata kawai muka samu fitowa daga gidan ta k'ofar baya sana diyar wutan bai sami ta wajenba". "Wani rami mukasamu muka b'uya nida Mamina,kwananmu biyu b'oye cikin ramin duk mungama galabaita,da mukaji fad'an yad'an lafa ansa jami'an tsaro shine muka fito da sand'a muke tafiya kamar wa'yanda za'a kamamu,bamuyi nisa da tafiyarba naji Mamina tace". "Wash!" cikin wani azababben murya ,zama tayi arud'e nace "Mamina lafiya? Meya faru?" "k'afata Ihsan." "Dubawa nayi naga wani k'aton kwalbane ya shige ciki ashe tun randa abun ya faru taji ta taka abu tsabar tsoro bata tsaya dubawaba,sai yau data taka k'afar taji. "Mami ki k'ok'arta mubarnan karsuzo su kamamu." "Ihsan ki gudu kawai,bazan iya tafiyaba." "nima bazan iya tafiya ba tare dakeba,gara kawai muzaunanan suzo su k'arasamu." "A'ah kije kawai." "Cikin kuka tace" "me amfanin tafiyar tawa bake,wani jin dad'in rayuwa zanyi? Gara mu mutu tare Maminah." "Toh muje" "zaki iya tafiyarne?" "Murmushin k'arfin hali ta sakarmata tace" "Eh". " _Allah sarki mahaifiya mai hak'uri juriya,sadaukarda rayuwarta domin farin cikin 'ya'yanta😰_ ". " _Allah kayiwa iyayenmu kyakkyawar sakamako,kabamu ikon yimusu biyayya har k'arshen rayuwarmu wanda suka rigamu gidan gaskiya ka gafartamusu,kasa aljannah tazam makimarsu._ ". "Haka ta tashi da k'yar take taka k'afar,muna tafiya tana hutawa,bamukaiga k'arasa fita daga Unguwarba wata moto ta tsaya gabanmu,cikinta da mutane da yawa,sukace mushiga kamar bazamu shigaba amma ganin bamuda mafita yasa muka shiga,ashe masaukin 'yan gudun hijira za'a kaimu,ansaukemu a garin TILDEN FULANI saurankuma aka wuce dasu wasu garuruwan har zuwa garin BAUCHI." "Kwananmu biyu awajen ba wani kyakkyawar kulawa sai d'ankaran wahala daga cikin garin mutane suke kawomana tallafin abinci da kayayyakin sawa". "Ganin K'afar Mamina sai hawa yake yasa naje na rok'i wani mai chemist yazo yaga k'afar,sanda yazo masifa sosai yamin ganin yadda k'afar yake,yace maza in d'auketa inkaita asibiti cikin Jos tunda yanzu fad'ar ya lafa,kud'in moto yabamu nayita mai godiya ina kuka haka da rarrafe Mamina ta iso bakin hanya da k'ar muka sami moto don har yanzu ba'ashiga garin sosai". "Lokacin da muka iso abun hawa muka sake hawa wani k'aramin asibitin kud'i mukaje don duk asibitin gwamnati ma'aikatansu sun gudu sai d'ai_d'aiku,suma sunk'i karb'armu,sanda muka iso wani Likita muka samu,namai bayanin komai da kuma rashin kud'in da bamu dashi yace ba komai wanda ya taimaki wani Allah zai taimakeshi. Yace ya d'au nauyin komai,aka bamu d'akin ba kowa saimu kad'ai". "Da dare yazo yaba Mamina magunguna ya mata allura,yace insameshi a office". "Bayan fitarshi bada jimawaba bacci ya d'auki Mamina,kayan abincin da mukaci na tattara na maidasu gefe na jamata k'ofar na fita ba tare da fargabar komaiba". "Da sallamata na tura k'ofar,ya amsa waje yanunamin inzauna,zama nayi yafara magana kamar haka". "a gaskiya k'afar mahaifiyarki na buk'atar aiki sosai,da nayi tunanin k'aramin abune saidana duba naga aikin sosaine." "yanzu doctor ya za'ayi?" "Abunyi kawai shine nanda kwana biyu kije kinemo wasu kud'i idan ya haura hakan dole saida ayanke k'afan don kwalbar ya riga ya rub'ar mata da k'afa." "Wallahi ayanzu bamuda komai don Allah ka taimaka." "taimako zan iyayi miki ammafa inhar kema zaki taimakamin." "Banda abunda zan taimakama dashi." "keko kikeda abun taimakamin idan kin yarda ..........................agobema za'aiwa mahaifiyarki aiki." "Agigice tamik'e donjin kalmardata fito daga bakin likita". "bafa abundamuwa bace,zab'i nabaki ko kud'i ko kanki daga gobe zuwa jibi kije ki tunani." Fitowa tayi gaba d'aya bata cikin hayyacinta maganar kawai ke mata yawo a kwakwalwarta. _ko kisamo kud'i ko ki fanshi lafiyar mahaifiyarki da ni'imar da Allah ya miki_ _Tirk'ashi_ ✍🏻 *~UMMYN YSRH~*. [02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: 💞💞💞💞💞💞💞 💞💞💞💞💞 💞💞💞 💞💞 💞 *YESMEEN* 💞💞💞💞💞💞💞 *STORY & WRITEN BY:* *UMMYN YSRH* *®PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S* *(P.M.L)* *Tako ina kunchanchanci godiya da jinjina agareku* *hazik'ai,jarumai,jajirtattu,masana sanin darajar d'an adam* *Kunyine ta ko'ina😍* *Allah k'aramana had'inkai,zaman lfy da hak'urin zama da juna* *Allah karemu daga sharrin masu sharri, da hassada* *PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*☺☺ *UP* *UP* *UP* *KUNA ZUBA K'AMSHI INA BINKU DA HUMRAH☺☺* *ALLAH K'ARA D'AUKAKA* *46~50* Juyi kawai take sam bacci yak'i d'aukarta,mik'ewa tayi taje tayo Alwala ta fara sallah don kai damuwarta ga Mahaliccinta. Saidatayi sallar asuba ta kwanta. K'arfe bakwai daidai Ummah ta tashi,tana mamakin irin nisan baccin da tayi,taji dad'in jikinta kam,yanzu ba jirin sai rashin k'arfin jiki da d'an ciwon kai. Motsin da YESMEEN tajine yasata bud'e ido,Ummanta tagani tana k'ok'arin tashi tace "Lahh Ummah kin tashine." "Eh bayan kinki tashina inyi sallah akan lokaci." "A'ah bak'in tashinki nayiba,gani nayi kinsha magani nasan kuma shiyasaki bacci,kar in tasheki in k'ara miki ciwon kai." "Aikam naji sad'in baccin don yanzu jikin da sauk'i." "Allah k'ara sauk'i Ummahnah." "Ameen." "barin in samiki ruwan wanka idan kinyi zaki d'anji k'arfin jikin." "aiko dakin kyauta. Allah miki albarka." "ameen Ummah nah." Kafin ta fito wanka ta gyara d'akin tsaf,ta ciromata doguwar riga mara nauyi ta shimfid'a mata Sallayah sannan ta fita,gabanta sai bugawa yake tana Addu'ar kar Allah ya had'ata da YAYA SANI. Duk wayewar gari saitaje ta gaida HaJIYA TALATU kodako bazata amsaba da harsu RUKY take gaidawa dataga iskanci suke mata idan tazo gaishesu ta sauwak'e ma kanta. Kitchen ta nufa d'auko musu abun karyawarsu,ZAHRA ce kawai a kitchen d'in tanata aiki,ganin YESMEEN ta shigo tace "Aunty Yesmeen ya jikin Aunty?" dariya Yesmeen tayi tace "ZAHRA bako gaisuwa sai tambayar jikin Aunty." "Allah na damune jiya ban iya bacciba,gashi tun d'azu Hajiya na falo tak'i shiga ciki balle inshaga indubata." Tana maganar tana kwalla. "Karki damu Zahrah Aunty taji sauk'i,yanzuma wanka ta shiga." "Allah k'ara mata lfy,ga abun karyawarku tun d'azu na had'a muku." "Toh,mungode." D'auka tayi ta nufi d'aki,tasamu Har Ummah tayi Sallah,tana zaune. Bayan sun gama karyawa ta shiga wanka,lokacin daya fito ta tadda HANIFA da MOMMYNTA sunzo gaida UMMAH. Bayan ta gaishesu ta shirya Kud'in magani ta karb'a da takardan maganin. Ummah tace "kije shakatafi can k'ofar Central market nan zaki samu duka,Allah kiyaye hanya akula kuma." "Ameen. Saina dawo" Tafiya take amma jikinta ya bata tabbas yana waje,tambayar kanta take "Meyasa duk inda yake indai ta doshi wajen sai jikinta yabata?" "meyasa batajin hakan ga sauran mutane saishi kad'ai?" "Wai meke faruwa da itane?" Wata zuciyar tace "Kinfad'a soyayyah Baby,meyuwa shid'in wani sashene na jikinki." "Soyayyah kuma?yaushe? Mutumin dako magana bai tab'a had'amuba." Bata kaiga k'arshen tunanintaba taji magana daga bayanta "Amincin Allah ya tabbata agareki." Cak ta tsaya ta juyo dan ganin mamallakin wanan muryar, ido biyu sukayi dashi yanata zubamata murmushi, kasa amsamai tayi. Yace "ba magana? Dama jinayi zuciyarki nata kirana shiyasa nazo gareki,ashe k'arya tamin." Juyawa yayi yace "Nabarki lafiya tunda bakya buk'atata,duk sanda kike buk'atar ganina zuciyarki zaya kirani." D'agowa tayi taga tafiyar yake azuciyarta tace "tafiyar kayi kuma?" Juyowa yayi da murmushi yace "eh,tunda bakya bukatata kink'i kimin magana" Rufe bakinta tayi da hannuwanta tace "Ashe yajini." "ban jikiba zuciyar da kike magana da ita ita gayamin." Juyawa tayi tana addu'a yau ta gamu da aljani,harta fita titi bata k'ara juyawaba. Tad'au lokaci mai tsawo tana jiran abun hawa amma shuru. Dak'yar tasamu mai keke napep,sunyi gaba kad'an suka sami wata suka d'auketa zata sauk'a wajen CITY STORE tunkafinsu k'arasa tsayawa wani shirgegen Alhaji ya fito daga cikin waje wata 'yar matashiyar budurwa biye dashi,hannunta rik'e da manyan ledodi guda biyu wani banzar shiga da tayi ko kad'an baza'a tab'a zaton d'iyar musulma bace. Tundaga nesa YESMEEN ke mamakin yadda taga yarinyar da suka fito cikin wajen da wannan mutumin,tana tunanin anya itace kuwa? tsayawarsu yayi daidai da shigarsu moto su tayar matar na sallamar mai napep d'in YESMEEN tace "Malam don Allah mubi bayan wannan moton." "kinsansune?" "Eh kawai tace." "Toh kud'inafah?" "muje zanbaka karka damu." Nidai dake gefe nace Kunga d'an'uwan kawata MSB masoyan kud'i😂😂😛 ✍🏻 *~UMMYN LABEEB~* [02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: 💞💞💞💞💞💞💞 💞💞💞💞💞 💞💞💞💞 💞💞💞 💞💞 💞 *YESMEEN* 💞💞💞💞💞💞💞 *STORY & WRITEN BY:* *UMMYN YSRH* *®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *(P.M.L)* *61~65* Yadda naga rana haka naga dare,bacci ya d'auke a idona,duk tunanina ya tsaya, ina zanje in samo kud'i,anya zan iya saida mutunciga ga wani k'ato kuwa,haka na k'areshi atunani,gari na wayewa bayan nayi sallah nayi wanka,Mamina zaune tayi sallar nasa mata ruwa tayi wanka,Doctor ya kawo mana abun karyawa nikam kasacin komai nayi,nama Mamina sallama zani cikin gari gun 'yan'uwa kozamu sami wani abun,likita yace akwai magungunan daza'a saya kafin afara aikin,Addu'an samun nasara tamin na fice. Wuni nayi ranan ina zaga gidajen 'yan'uwa wanda rikicin ya shafa da wanda bai shafaba duk cemin suke basudashi inyi hak'uri,rikicinnan yasa duk 'yan kud'ad'ensu sun tafi,daga mai ban naira d'ari,d'ari biyu hamsin,harkan hanya natsaya neman taimako amma ba wanda ya kulani. Gidanmu na nufa ta gefen da wuta bai ciba kozan samu abun sayarwa saidai ba komai cikin wajen,dama sabon ginine Yaya Kamal yayi inda zai zauna da matarshi,ba'akai ga bikinba ta rutsa dashi. Fitowa nayi na nufi hanyar asibitin duka duka kud'in dana samu d'ari tara da ishirin,mu masu neman dubu ishirin,sanda na dawo Mami na zaune rik'e da k'afar sai azabar zafi,da zugi yake mata,ga yunwa gashi yau likitan bai lek'oba tun safe dayazo bai kuma zuwaba,na tambayeta ko 'yan'uwanmu sunzo tace ba wanda yazo,fita nayi naje na samomata abinci taci mukayi sallar magriba,office d'in likitan na nufa don ganin ko lafiya ba ba Mami maganindake hana k'afar zugiba,kafin in k'arasa naga sun fito da wata kodaga yanayin shigarta kasan ba d'iyar kirkiceba,wucewa sukayi ko kallon inda nake baiyiba haka na koma jiki ba kwari,haka Mamina ta kwana ranan cikin rad'ad'i da zafin ciwo ga k'afar har ruwa yake,nayi kukan zuci nayi na fili narasa yadda zanyi intaimakama Mamina yanzu rayuwa kowa kanshi ya sani bamai taimakon wani koda ciki d'aya kuka fitoda mutum burinshi yaganka cikin k'askanci, zanbada Mutuncina domin ceton ran mahaifiyata. Ganin irin wahalar da Mamina keshe yasa na yanke hukuncin bama likita abundaya buk'ata gareni,washe gari na je na sanarmai na amince da fara'arshi baki har kunne yace gobe za'a mata aiki,wunin wunin ranan kula na musamman muka samu,nidai duk jikina ba kwari idan nai runanin fasawa inna tuna yadda Mamina ke wahala sai inhak'ura da dare yazo yaba Mamina magani ya mata wani allura,tambayata yayi yaga jikina ba k'arfi nace kaina ke ciwo yace inje inkarb'i magani a office d'inshi. Saida Mamina tai bacci sannan na nufi gun likita,wani kwayar magani yabani da ruwa nasha band'au lokaciba naji gaba d'aya nakasa gane wani yanayi nake raye nake ko amace,bacci nake ko ido biyu nida kamar gunki haka nake jina,haka yafi sama da awa hud'u yana abu guda,sai kusan asuba nafara dawowa hayyacina,yadda naganni nasan mai afkuwa ya afku,tashi nayi nasa kayana da k'ar nakejan kafata don azabar ciwo,d'akinmu na nufa har yanzu Mami na bacci,bayan gida na nufa na zauna naci kuka iya kuna nayi tsarki na yi wanka na fito,nayi sallah ina zaune Mami ta farka mik'ewa nayi da nufin kawo mata d'auki zuwa bayan gida saida ina taka kafata naji wani azabar zafi har kwakwalwar kaina,da kyar nake tafiya Mami ke tambayana lfy nace sulewa nayi a bayan gida,tamin sannu. Ranan wuni likita yayi yana mana sintiri yanason mukeb'e sam nak'i yarda,danamai maganar Aikin yace sai gobe yanzu basuda wasu kayan aikin sai ansayo. Muna hira da Mamina tanatamun nasiha kan rike mutuncina da hakuri da rayuwa aduk yadda yazomin likita ya shigo albarka Mami tayi tasamai bisa taimakon da yake mana,yace ba komai yiwa kaine. Kamar kullum allura yamata ya bata magunguna,ya zauna sunata d'an hira da Mami,can dayaga bacci ya d'auketa ya mik'e yace yama jirana,zuwana shine kwarin gwiwar yin aikin rashin zuwana shine koma baya ga aikin. Ba yadda na iya haka nabishi yau baiban komaiba saidai naci bak'ar azaba,yana gamawa ya juya yacigaba da bacci nima nayi gaba,nayi sallah ina jiran farkawar Mami shuru,har wajen tara bata tashiba zuwa nayi na tab'ata gaba d'aya jikinta ya saki ba alamar numfashi,jijjigata nashigayi shuru da gudu nanufi office d'in likita bako sallama na bud'e k'ofar na shiga abundana gani yasani fitowa ba shiri,likita nagani da wata ma'aikaciyarsu sunata zabga masha'arsu. D'akunan asibitin nayita dubawa amma duk ba mutane,d'akin k'arshe naga wani namiji kwance damai jinyarshi nace don Allah su taimaka sudubamin Mamina bata motsi ko dogon suma tayi na duba likita bayanan. Tare da d'ayan mukazo yadubata Yace "Saidai kiyi hak'uri wanda yafimu sonta ya karb'i abunshi." Kawai jinayi nazube wajen asume Nima sumewar zaune nayi sanadiyar gajiya danayi da typing😛 ✍🏻 *UMMYN YSRH* [02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: 💞💞💞💞💞💞💞 💞💞💞💞💞 💞💞💞 💞💞 💞 *YESMEEN* 💞💞💞💞💞💞💞 *WRITEN BY:* *UMMYN YSRH* *®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *(P.M.L)* _THIS PAGE IS 4 U BIEEBEE YAREEMA_ _ALLAH BAR ZUMUMCI SO DA K'AUNAR JUNA_ _ALLAH K'ARA BASEERAH,HAZAK'A 'DAUKAKA,KWARIN IDO DA ZAK'IN HANNU👏🏻_ *71~78* Gaba d'aya mutanen falon sun rud'e kad'an daga cikinsu masu k'arfin imanine suka iyayima Alhaji fatan Allah maida Alkha'iri,yasa da abunda ya tsare,sauran kuwa daga mai tsinewa sai masu koke_koke,ahaka taron ya watse. Bayan y'an kwanaki al'amura sun fara canzawa,sun fara fuskantar yanayin rayuwa,ga Hajiya Talatu tsurfar yau daban ta gobe daban,haka suka tasa Alhaji gaba ita da Hajiya Mama akan sai Ummah ta rage yaran d'akinta tunda suma yanzu basu wadataba. Hak'uri kawai yake basu na indai abun da zasucine da yardar Allah bazai gagaraba. Itama Ummah dataga abun yak'i sauk'i ta tattara Ihsan ta kaita ga y'an uwanta tare da yimusu y'ar nasiha ta dawo gida. Ummah Habiba cikin shirin bacci ta nufi d'akin Alhaji hannunta d'auke da wani bak'in leda,waje ta samu ta zauna kasancewar Alhaji na wanka,saida ya yafito ya gama shiryawa tsaf sannan Ummah ta mik'omai ledar data shigo dashi. Dubawa yayi yace "Wannanfa na meye?" "Nakane Alhaji." Cikin mamaki yace "nawa!!" "Eh. Naka." "Ai yanzu banda kud'i mai yawan wannan." "Tunda ina dashikam ai tamkar nakane." "ke ina kika samo kud'i har dubu d'ari biyar haka?" "Filayena guda biyunnane nasaida d'aya dama na bari sai Auren Yesmeen ya tashi sai insaida ayi hidima tunda wani matsalar ta fad'o kaga gashi yayi amfani." "Toh amma shine zakiban wannan kud'i haka? Kemafa kud'inki na sarin kaya ya salwanta atafiyannan,ni ya kamata in k'ara miki jari idanna samu bake ya kamata ki bannakiba." "Habba Alhaji don k'addara ta gifta sai ince ka biyani kud'ina? Kaifa ka bamu jarinnan har na juyashi ya zama kadarori,don yau baka dashi sai in kasa tallafama,idan nayi haka nayi butulci." Godiya ya shiga jero mata ta dakar dashi "Habba ba godiya tsakaninmu,kaina gatanmu arayuwa,ka cancanci fiye da haka arayuwarmu,kacirema masu binka dubu d'ari biyunnan sauran sai a lallab'a Allah k'ara rufa asiri." "Ameen nagode." "kinga na manta d'azu da magriba nayi suruki,yazo neman izinin zuwa neman Auren 'yata Yesmeen,bisa ga yanayinshi naga yarone mai nutsuwa da kamun kai,ban amince mishiba nadaice sainayi shawara da mahaifiyarta idan yaso sai ya nemeni yaji amsarshi." "Habba Yesmeen ai d'iyace agareka,duk hukuncin da zaka yanke kansu Zahra itama haka zaka yanke kanta,indai ka yaba dashi,ba matsala." "Gaskiya ne nagode ka karramawarki gareni,yaron da gani baida matsala,sab'anin matasan yanzu zaiyi wuya kiga anzo tambaya kafin fara hira da budurwa,saidaimai idan ya iso ya danna horn na moto ko mashin ko k'iran waya,ita kuma jiki na rawa zata fita." "Ummah na dariya tace "Ashe Alhaji kasan komai." "Nasani mana bagani da 'yaranba duk cikinsu wa yatab'a zuwa neman izini,saidai kiga yarinya na rab'e_rab'e zata fita,da kayi magana ace kafiya tak'urama yara kabarsu lokacinsune,yanzu taurarinsu ke haskawa,duk Hajiya ke d'aure ma Talatu ta ke yadda taso baka da ikon yimusu magana amatsayinka na Uba,son jikoki ya rufe mata ido." "Hummm! Sai hak'uri Alhaji Hajiya Uwace fah haka zamuyi mata biyayya domin aljannarka na gareta,Addu'a zakayi tamusu,da fatan Allah shiryasu ya karesu da fad'awa mummunan rayuwar wannan zamanin." Lokaci mai tsawo suka d'uka suna tattaunawa kan matsalolinsu daga baya suka kwanta. Cikin sand'uwa yake tafiya kaman tsohon b'arawo har ya isaga k'ofar d'akin ya murd'a saidai yauma arufe kamar kullum,ciza leb'enshi yayi cikin ta kaici ya juya yace *YESMEEN duk randa kika shiga hannuna kun kad'e,sau uku ina kawomiki hari bana samun nasara,muje zuwa idan kere na yawo zabo na yawo za'a had'une saikin raina kanki." _nidai nace in Allah ya yarda Allah bazai baka nasara kan marainiyar Allah ba akan mugun nufinka SANI_ ✍🏻 *~UMMYN LABEEB~* [02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: 💞💞💞💞💞💞💞 💞💞💞💞💞 💞💞💞 💞💞 💞 *YESMEEN* 💞💞💞💞💞💞💞 *WRITEN BY:* *UMMYN YSRH* *®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *(P.M.L)* *Du'a hai ki kamyabi ke har sikhar pe aap ka naam hoga,* *aapke har kadam par duniya ka salam hoga,* *Himat se mushkilon ka samana karna hamari du'a hai ki waqt bhi ek din aapka gulam hoga.* *HAPPY BIRTDAY MY MERMUE* *Allah karo shakaru masu albarka tsawon rai,da lafiya mai amfani,Allah cika miki burinki na rayuwa yasa jin kirin yazama alkhairi*👏🏻 *76~80* _Washe gari_ Alhaji ya had'a kan iyalanshi ya sanarmusu alherin da Hajiya Habiba ta mishi,nan Hajiya Talatu tace "Habba dagaji wannan zance shiryayyiyane,ta ina ita Habiban ta sami wannan mak'udan kud'ad'en da har zata baka, saidai idan wani shirin kukayi." "Haba Talatu cikin filayenta biyu ta saida d'aya,jarin dana baku shi taketa juyawa har yanzu kuma Allah yasa mata albarka ciki." "wannan zancen k'aryane, jarin kusan shekara uku kenanfa daka bamu,tun yaushe nawa ya karye na bika kaban wani har yau shuru." "Nasan koda na baki ba juyawa zakiba." "kasanfa inada yara wasu hidima dole inyi musu,itafa wata ajiye?" "ya isa haka Talatu!!" "Aidole kace inyi shuru tunda ba ka adalci adaiji tsoron Allah." Bud'e baki yayi zaiyi magana sai kuma ya fasa Hajiya Mama dake gefe tace "komadai menene ai dole ta maka tunda dama ta dalilinka ta sami dukiyar." "Yauwa Alhaji batun dubu hamsin da kace inkasami kud'i zakaban na sayan kayan baby da zannuwana,tunda kud'i ya samu sai a ciremin." "Gaskiya Talatu bazaki sami dubu hamsin ba zandai baki ishirin." "Habba ishirin mezai min ai gara in hak'ura wallahi." "Waikai bakasan ciki da goyo yana kashe kaya bane,ai dole zata nemi k'arin tufafi don haka ka k'ara mata." "Toh Hajiya zan bata talatin." "Yaushe? Aigara ka mik'omin yanzu don kana fita dashi nasan bazai dawoba." Talatin cif ya lale ya bata yaba mahaifiyarshi dubu biyar,taro ya watse,Ummah Habiba dake gefe dama kallonsu kawai take k'ala bata tankaba,taro na watsewa itama ta k'ara wuta. _Bayan kwana biyu_ ANWAR ya dawo gun Alhaji don jin yadda zancensu ya kwana,ya amince mishi ya bashi daman ya fara zuwa sannan bai buk'atar dogon lokaci da sun fahimci juna sun gama bincikensu za'ai maganar Aure,tafiya yayi don fara shirin zuwa zance yau,ji yake tamkar sallah. Ummah ke sanarda Yesmeen yau zatayi bak'o don haka tashirya ta kuma zama mai kamunka,nutsuwa da tsare mutuncinta a duk inda take. _7:30pm_ Bayan sallar isha Malam Anwar tsaye k'ofar gida yana jiran d'an aika ya fito daga k'iran Yesmeen,yasha shaddar sai walwali yake kamar wani sabon ango kamar kullum fuskarshi sake yake d'auke da murmushi. Yaron ya fito ya sanar mai tana zuwa ya shigo daga ciki,harabar gidan ya shigo ya zauna kan wasu kujerun roba daya gani awajen. Zaune take amma jikinta na gaya mata tabbas makusancin zuciyarta na kusa da ita,rabon data ganshi tun ranan da suka had'u da Ihsan,Ummah ta lek'o tace tanada bak'o awaje. Jiki ba kwari haka ta mik'e kamar kullum babbar hijabinta tasa ta nufi hanyar waje gabanta sai fad'uwa yake,gashi ba wuta balle taga fuskar mai k'iranta. Tana fitowa harabar gida ana kawo wuta daidai fuskarshi wutan ya hasko mata ba k'aramin razana tayiba data ganshi wato har yafara mata gizo kenan har ta juya zata tafi taji yace "K'araso mana nine." Cak tayi mutuwar tsaye ta kasa motsi. _nima cak na tsaya sanadiyar gajiya danayi da typing😛_ ✍🏻 *~UMMYN YSRH~* [02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: 💞💞💞💞💞💞💞 💞💞💞💞💞 💞💞💞💞 💞💞💞 💞💞 💞 *YESMEEN* 💞💞💞💞💞💞💞 *WRITEN BY:* *UMMYN YSRH* *®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *(P.M.L)* *66~70* A storace mutumin yayi kaina ya duba yaga da numfashi,da gudu ya fita duba likita saidai ba likita ba alamarshi,gaba d'aya asibitinma ba kowa. D'akinsu ya koma ya d'auko ruwa ya sake dawowa d'akin da muke ya yayyafamun,wani dogon numfashi naja zuciyata na rayamin mafarki nake,ahankali na bud'e idona saidai ina gaskene Mamina ta rasu ba mafarki nakeba,wani irin kuka kawai na sake,ga rashin Mamina gakuma kimata dana badashi ga wani k'ato,bakina kawai ba abunda yake furtawa sai kiyafeni Mamina na salwantar da darajata,kimata,y'ancina. Da taimakon wannan mutumin naje na sanar da 'yan'uwanmu rasuwar,sanda naje kame_kame suka hauyi akan yau zasuje dubata.k'annenta biyu muka taho dasu aka d'au Mamina mukayi gaba,akamata wanka aka kaita makwancinta,tundaga nan nafara fuskantar k'ask'antacciyar rayuwa,gidan k'anin Ma mina,ba wadataccen abinci,sutura,kulawa,bawai don babuba. Da nagaji nace ya nemamin 'yan haya asa ad'aya gefen dabai k'oneba kud'in sai in rink'ayin wasu uzurina,masifa sosai sukamin na wai na raina abunda sukemin indai hakane in tattara in koma gun dangin mahaifina,haka koma wajensu nanma zaman gashinanne. Ahaka na had'u da wata k'awa maibin maza tun tana jan ra'ayina inak'i har na yarda. Da aka fahimci rayuwar da nake ciki shine aka korani wai bazasu iya zama da karuwaba kar in lalata musu tarbiyar yaraba,haka na tattara na koma gidanmu nida k'awata,nan muke fita musaida mutuncinmu abiyamu mu biyama kanmu buk'ata don itama batada kowa yak'i ya cinyesu. Har gari_gari ake tafiya damu,idan mun gama mu dawo gida,ahaka rayuwata takasance. Dogon numfashi Ummah taje tace "ikon Allah." Yesmeen tace "ya labarin likita kuma?" Bayan na dawo hayyacina na koma don ganin likitan sai cemin akayi ai dama an rufe asibitin ba'a aiki cikinta sabida lalata mata da likitan yakeyi,yanzunma ganin fad'an da akayine hankali baya kanshi yasa ya nud'e a boye. Nayi kuka iya kuka na yadda na salwantarda rayuwata,saidai idan banyi hakanba banda ma fita. Ummah Ta mata fad'a sosai da nasiha mai shiga jiki,takuma ce idan ta kwana biyu zata maidata gun danginta ta basu hak'uri. Ahaka muka d'au lokaci mai tsawo kafin muka kwanta. Ummah ta ware sosai don ta karb'i girki,gashi yau Alhaji zai dawo,kowa murna yake don wannan karon ya jima a Lagos,gashi mafi yawan lokaci ba'a cika samun wayarshiba. Hajiya Talatu tunda ta kyalla ido taga Ihsan hankalinta ya tashi kullum cikin gori da habaici,yauma tana kan abunda tasaban "Mutum saidai ya k'are' a kalen dangi azo anacin arzik'i amma badai ya haifaba." "Hajiya kenan Allahn daya baki ba wayo ko dabararki yasa ya bakiba,nida ya hana ba k'ina yayiba,haihuwa nufin Allah ne,idan yaso ya baka inyaso ya hanaka,da kike batun gado duk cikinmufa ba wanda yasan gawan fari." "Lah ha'ila ha'illallahu!!! Kice so kike kawai Alhaji ya mutu,tunda bakida d'a dashi bakida asarah,tah Wallahi ta Allah ba takiba,saidai ke ki mutu kibar Alhaji muguwa kawai,inda kinada yara bazakiso ya mutu yabarsu da maraiciba." Ta bud'e baki zatayi magana kenan saiga Hajiya surukarsu wani matashi ya shigomata da akwatin kayanta. "Lafiya kuke tsaye cirko_cirko kaman zakaru?" "Hummm!!! Inafa lafiya. Wannan muguwar kema Alhaji fatan mutuwa." "Mutuwa? Auko saidai ki mutu kibarshi muna fuka,ai duk bak'in cikinki nakan wannan cikin ta saiya fito duniya saida ki mutu,shiyasa na tattaro kayana na dawo gidan gabad'aya,don kar kije kima Talatu wani mugun abun." "kiyi hak'uri Hajiya Wallahi ba..........." "Dallah rufemin baki,da anfara magana ki su kuy da kai kina bada hak'uri kamar mutumiyar kirki,ni b'acen da gani." Jiki ba kwari Ummah ta wuce,haka ta gama girkinta ita dasu Ihsan,duk wucewa sai an watsomusu bak'ar magana bamai tankasu. Sai wajen takwas Alhaji ya iso gida,da kaganshi kasan baya cikin hayyacinshi,gaba d'aya ya fad'a yayi bak'i,ba wani walwala sosai a fuskarshi,haka suka mai sannu da zuwa ruwa ya watsa yayi sallar isha sannan yazo yad'an raba abinci kad'an,babban falon gidan ya had'a iyalanshi harda mahaifiyar tashi,nan yake sanar musu tafiyar da yayi ya had'u da 'yan danfara kaf sun yasheshi gashi kusan duk dukiyarshi ya kwashe ya tafi sarin kaya ciki harda na mutane,sunyi binceke amma sam ankasa gane mutanen don gari irin Lagos ganesu ba abune mai sauk'iba. Gaba d'aya d'akin yad'au salati wasu ihu,wasu ashar suke antayowa. Hajiya Talatu kam mutuwar zaune tayi,saida d'an cikinta ya motsa tsabar tsoro. _nima gefe na koma ina tayasu jimami yanzu shikenan ba wani gado dazamuci😭_ *UMMEEN YUSRAH* [02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: 💞💞💞💞💞💞💞 💞💞💞💞💞 💞💞💞 💞💞 💞 *YESMEEN* 💞💞💞💞💞💞💞 *WRITEN BY:* *UMMYN YSRH* *®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *(P.M.L)* *86~90* *Jinjina gareku 'yan JUST NOVEL GROUP BY ABBA BESST Allah bar zumunci* Gidane na sama da k'asa amarya da ango suna sama sai mahaifiyar ANWAR ak'asa,su biyu mahaifiyarsu ta haifa shine babba sai k'aninshi MUNEEB. MUNEEB d'angatane na k'arshe gun mahaifiyarshi sab'anin ANWAR ko kara ta ajiye baida ikon giftawa ba tare da izinintaba,mahaifinsu ya rasu tun MUNEEB nada shekaru biyar aduniya duk waniso da k'auna ta iza kan Autannata duk hukuncin daya yanke a abu ta zauna. Yanzu haka yana makaranta a kano. ANWAR ma'aikacine a maikatar Ilmi dake cikin garin Bauchi,duk da ba wani Babban ma'aikaci bane akwai rufin asiri. Duk wani aiki na gidan Tasakarma YESMEEN Masu aikinta ta sallamesu,hakan sam bai damun YESMEEN tunda tasan Uwa take gareta,ga tsana datake nuna mata bata tab'a gayama kowa ba,tana rok'on Allah ya sassauto da k'iyayyar da Hajiyar ke mata. *BAYAN WATA BIYU* Yau gidan UMMAH HABIBA d'auke yake da manyan bak'i HAJIYA ASMA'U ne yau Allah yayi zuwanta duk da Umman na fushi da ita amma tayi farin cikin zuwanta,sunyi hirar yaushe gamo sannan suka rank'aya gidan Amarya YESMEEN. Tayi murna da farin cikin ganinsu,sun tami tarba wajen HAJIYA LAMEE mahaifiyar ANWAR ba yabo ba fallasa,Ummah Habiba ke tambayarta lafiya taga ta fad'a,tace tayi rashin lfy amma da sauki,basu d'au wani lokaciba suka tafi,YESMEEN hadda kuka. Kwana biyu HAJIYA ASMA'U tayi ta koma ta tausaya masu Ummah halin da suke ciki yanzu don abun ya k'ara ja baya,saidai muce Allah k'ara rufa asiri. Aikin kawai take amma sam batajin dad'in jikinta ga jirin da takeji sama_sama ga tashin zuciya, saidai bata isa race batada lafiyaba Yanzu HAJIYAR ta farmata,adaddafe ta gama abincin ranan ta gyara wajen tayi sallah ta kwanta. Tunda ANWAR ya dawo yaganta kwance yasan ba lafiyaba sanda ya tambayeta tamai bayanin yadda takeji,shiryawa yace tayi suje asibiti. Gwajin farko ya gwada tana d'auke da ciki na wata uku,duk kunya ya rufeta ANWAR kuwa yarasa inda zaisa ranshi don Murna,haka suka koma gidan cike da farin ciki. Sanda ya sanarwa mahaifiyarshi ba laifi tayi murna,dalilin cikin harta d'an sami sauk'in wasu aiyukan,tana samun kulawa ba laifi. Ummah Habiba tayi murna sosai sanda labarin cikin ya isketa,har gida tazo taga d'iyar tata. *BAYAN WATA HUDU* cikin YESMEEN yana wata shida yanzu,yau sun tashi da shirye_shirye,d'an lelen Hajiya zai dawo,anmai girke_girke iri iri an k'ara gyara gidan kaman wani shugabane zaizo,shima ANWAR baki har kunne yana murnar dawowar k'anin nashi,YESMEEN kuwa sam ta kasa gane wani yanayi take tana murna amma hakanan zuciyarta takejin wani iri. K'arfe Uku daidai MUNEEB ya iso gidan bako sallama sai Ihun k'irar mahaifiyarshi da yayanshi da kuma AUNTY YESMEEN da sauri Mahaifiyar tashi ta fito suka rungume juna cikin murna,ANWARMA ya sauka daga samansu suka rungume juna cikin d'oki tace "Wai ina My Aunty ne? Inga ko yayan nawa ya iya zab'e,idan bataiminba acanzota." Dariya dukansu sukayi daidai lokacin YESMEEN na sauk'owa daga sama sanye da Hijabi,juyowa sukayi duka lokaci guda, wani kallon tsana MUNEEB ya mata lokaci guda,har abada bazai tab'a mantawa da wannan fuskarba,yau wai itace cikin gidansu kuma matar YAYANSHI ina sam bazai yuwuba,saidai tabar musu gida,itama wani mummunan fad'uwar gaba taji sanda taga MUNEEB TOH FAH🤔 WAYE WANNAN MUNEEB DIN? MUJE ZUWA TAKU HAR KULLUM *UMMYN YUSRAH* [02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: 💞💞💞💞💞💞💞 💞💞💞💞💞 💞💞💞 💞💞 💞 *YESMEEN* 💞💞💞💞💞💞💞 *WRITEN BY:* *UMMYN YSRH* *®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *(P.M.L)* _Dole in jinjina muku👍🏻_ _Hameebrah mai babban Duwais🙊_ _Aunty Ruma_ _Mom Sultan_ _Bahijjah_ _Xinniey Smart_ _Hajiya Ameerah_ _Iya mai taushe_ _Ameshty_ _kai kunada yawa🤔_ _dukanku fatan Alkhairi_ *81~85* "Ki k'araso mana,ko baki farin cikin zuwata bane in koma?" Juyowa tayi ahan kali ta nemi waje ta zauna,kanta sunkuye,Sallama ya mata ta amsa ahankali zuciyarta tas ji take kamar anbata kyautar kujerar saudiya. Bayan gaisuwa tareda d'an tak'aitaccen bayaninshi,da kuma musabbabin zuwanshi gareta. Lokaci k'ank'ani soyayya mai k'arfi ya k'ullu tsakaninsu,soyayya mai tsafta,basu yini guda batare da sunga junaba. Lokacinda yaji labarin Yesmeen ya tausaya mata matuk'a yamata Alk'awarin duk rintsi duk wuya yana tare da ita. Yau anwayi gari Hajiya Talatu ta tashida nak'uda,banda ihu da surutai ba abunda take,ahaka aka kaita asibiti,bayan dogon nak'uda da tayi dak'ar aka samu yaron ya fito,baidai wani lokaciba Rabbi ya karb'i abunshi tayi bak'in ciki sosai don taci buri sosai kan wannan haihuwar. Bayan gama bincike da manya sukayi akasa ranar biki lokaci k'alilan,saida ansha Artabu da mahaifiyar Anwar kafin ta yadda da auren acewarta sunfison 'yar dangi dak'ar ta yadda da auren. Shirye_shirye aka sadidan,Ummah duk wani abu da akema d'iya tayima d'iyar tata,lokacin da aka aikama K'anwar Maman Yesmeen Hajiya Asma'u zancen Auren cewa tayi bazata sami halartan bikinba don Alokacin zasu tafi Ummura da Alhajinta,ta Turo musu da gudumawar Dubu ishirin,Ummah Habiba taji ciwon abun sosai wato ta gwada kud'i yafi d'an'uwa,batada lokacinsu tunda ta maidasu mabuk'ata barita turomusu kud'i. Biki yataso k'awayen Ummah daga kano,Kaduna,sokota,maiduguri,da wasu jahohin duk sun sami Hallartan biki Hajiya Mermue (Mrs Jabo) ita tad'au d'awainiyar gyaran amarya,tayi kyau tayi shar da ita. Angaida mutan Sokoto,Su Hajiya fatima (Mom sultan) suma sun samu isowa,ga iyalan Ummyn Ysrah novel grp duk sun sami hallarowa tsabar yawan jama'a gidan saida ya kasa musu,wasu gidan su Hanifah aka sauk'esu,Ummah da Yesmeen sunyi kukan farin cikin ganin irin cikowar da akayi dukda basu da dangi yau Allah ya basu wasu dangin masoyansu. Cikin Kwanciyar hankali akayi biki lfy aka kai amarya d'akinta sai fatan Allah basu zaman lfy da hak'urin zama da juna,Allah kad'e fitina. ✍🏻 *UMMYN YSRH* [02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: 💞💞💞💞💞💞💞 💞💞💞💞💞 💞💞💞 💞💞 💞 *YESMEEN* 💞💞💞💞💞💞💞 *WRITEN BY:* *UMMYN YSRH* *®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *(P.M.L)* _K'aunarku gareni ta musammane😍_ _har kullum kuna raina_ *FATY AXLAN* *Maryam s bello* *(M.S.B)* *MY YESMEEN TAFEESU* *MY SISTO FHARIEEDART* *SUHANA* *JANNART* *DELU CHOGAL* *MR FAWWAZ* *AUNTY KHADY* *SADNAF (LALATA😂)* *ZAHRAH SURBAJO* *AYSHA ALI GARKUWA (NAMIJI BAYA KA'DAN)* *UMMU YAHYA SISIN MAMA (GOYON KAKA)* *UMMI HAMBALI* *UMMI GARKUWA* *DIJA WAZIRI* *HUSNAH BAUCHI* *WALIDA WAZIRI* *RUFAIDA* *HAFSAT MUSA* *RAFEE'AT* *SAMRAH* *BIEBIE DEE* *BIBA WADATA* *SEEMALUV* *MMN KHADIJA* *MMN SULTAN* *UMMU HANEEFAH* *NANA FA'AD* *XARAH* *FATY KHALID NA SHUKA* *SHAFA ABDULKADIR* *MARYAM ABDOOL* *SUMY BASH* *SALMA* *ROOKY KAZ** *NEERATLUVE* *AYSHA HANWA* *AYSHA GANA* *ZEE YABOUR* *UMMU SAFWAN* _ALKHAIRIN ALLAH YA TABBA GAREKU 'YAN P.M.L DA WANDA TAGA SUNANTA DA WACCE BATA GANIBA AYI HAKURI IDAN DAMBU YAYI YAWA......_ _INASONKU KAWAYEN KWARAI😘_ _INA ALFAHARI DAKU AKODA YAUSHE_😍 _ALLAH K'ARA DAUKAKA P.M.L YA RABAMU DA SHARRI MAKIYA MAHASSADA_ _ALLAH KARA DAUKAKA P.M.L YASA MUFI HAKAN👏🏻_ *91~95* Nunata yake da yatsa yace "Kece matar yayan nawa,keda kika gama yawon barikinki,kika gama saida mutuncinki a titi,shine aka lallab'i yayana aka mak'ala mishi ke,Wallahi ba agidannanba, Hajiyata 'yar iskacefah." "Kai auta kasantane?" "Nasanta Hajiya,Ranar da muke party jarabawar jam d'inmu harda ita,aranar muna cikin murnar ta sha wasu kwayoyin zubarda ciki,mu muka kaita asibita akace ciki ta zubar,kinga ai wannan ba matar aure bace." "zubar da ciki!! Kasan abunda kake cewa kuwa? A cikin hayyacinka kake kuwa? Kalleta da kyaufa matatace,ban tab'a ganin alamar bin maza atare da itaba,karka kuskura ka kuma gayawa matata irin wannan kalama,na yarda da ita nasan irin tarbiyarta." "Dakyau kasan irin tarbiyartako tunda tare kukazo duniya har kake k'aryata d'an'uwanka ko?" "Hajiya wannan ai dagaji k'aryane,kema kodaga yanayinta ai kinsan ba yadda yake fad'a bane,Habba Hajiya karki yarda da wanna zance wallahi karyane saidai ko da wani abunda ya had'asu." "yarda kam na yarda dama can banta kwantaminba,don haka amatsayina na mahaifiyarka ayau basai gobe ba atanzu basai anjimaba inason ka damk'a mata takardar sakinta." "Innnalillahiwa'inna'ilaihirraji'un!!! Saki Hajiya don Allah ki hakuri muntuba." Har k'asa ya durk'usa yana bata hak'uri amma inna ko ajikinta,MUNEEB ranshi tas,YESMEEN d'urk'ushewa tayi wajen banda kuka ba abunda takeyi,tarasa bakin magana. "ko ka saketa ko in tsinema kuma wallahi idan ka saketa kaje gareta ban yafemaba duk randa akace ka je wajenta." "HAJIYA don Allah kibari ayi bincike,kiyi hakuri." "bincike ai anyishi tunda gaban k'aninka akayi komai,mik'omin takarda kai da biro." Saki d'aya ya rubuta mata yanayi yana hawaye,kan table d'in ya ajiye ko kallon YESMEEN ya kasayi kawai ya fice waje,haka Hajiya da MUNEEB suka kad'ata ko tsinke bata d'aukaba. Banda chaji😬 *UMMYN YSRH* [02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: 💞💞💞💞💞💞💞 💞💞💞💞💞 💞💞💞💞 💞💞💞 💞💞 💞 *YESMEEN* 💞💞💞💞💞💞💞 *WRITEN BY:* *UMMYN YSRH* *®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *(P.M.L)* *96~100* Gaba d'aya hankalinta a jagule yake,haka tad'au hanyar gida taimakonta d'aya ba mutane sosai duk sun shiga sallar la'asar,ko sallama bataiba kawai d'akin Ummanta ta wuce,Ummah na sallah taji shigowarta,takardan sakin ta ajiye kan gado ta nufi bayan gida. Har Ummah ta iddar da Sallah ta ninke mayafi da sallayar YESMEEN bata fitoba,har ta fice daga d'akin ta sake dawowa,shuru ba motsin Yesmeen. Tambayar kanta take ko lafiya ta shigo ba sallama ta nufi bayi kusan awa guda ba labarinta. Hanyar bayin ta nufa don ganinko lafiya,saidai takardan datagani kan gadon yasata tsayawa,d'auka tayi da niyar dubawa abunda ta gani cikin takardan ya mugun kad'a mata hankali a tsorace race "Saki!!! Garin yaya? Meta mishi zai cuci marainiyar Allah,Innalillahiwa'inna ilaihirraju'un." Shi kawai taketa maimaitawa har ta isa k'ofar bayin murd'awa tayi tajishi rufe bugun duniya tak'i bud'ewa. "Habba Yesmeen ki bud'e zaman baida wani amfani,karkiyi k'ok'arin cutarda kanki da abundake cikinki." "Kin rasa danginki kinyi hak'uri kin yarda da hakan k'addarace ta Ubangiji,wannanma ki yarda dacewa muk'addarine tun ran gini ran........" Kasa k'arasa maganar tayi tanadiyar tarindaya rik'eta ga numfashinta ya fara sama2. Yesmeen dake zaune cikin bayan gida taketa rabka kukan jin Umman nata tafara shiga cikin wani yanayi yasa ta fito da sauri ba shiri. Zaune ta taddata rik'e da k'irjinta sai zufa take had'awa ga tari harda jini gaba d'aya Yesmeen tagama rikicewa da gudu ta fito falon gidan don neman mai taimako duk suna zaune gaban Hajiya Talatu ta k'arasa tana nuna mata d'akin Umman "Hajiya don Allah ki taimaken Ummah zata mutu gatacan sai aman jini take,don Allah ki taimaketa." Alhaji dake fitowa daga cikin d'akinshi jin abunda Yesmeen ke fad'a da gudu ya rufta d'akin,Yesmeen na ganinshi itama ta rufamai baya Sam ta manta da wani ciki ajikinta ta shafe babin damuwarta kawai damuwarta Kar Ummanta ta mutu. Duk tsiyar Hajiya Talatu itama saida taji tausayin kishiyar tata,d'akin ta nufa sauran yaran suka rufa mata baya. Asume Alhaji ya taddata,cikin kid'ima haka ya sunkuceta ko nauyinta baijiba ya nufin hanyar waje yana sanarda Zahra ta d'aukomai keyn motor,baya ya kwantar da ita Yesmeen ta zauna ta d'aura kanta bisa cinyarta Hajiya Talatu ta shiga gaba. Basu zame ko inaba sai Asibitin AL_AMEEN dake titin Nassarawa,suna zuwa aka karb'esu sunyi iya bakin k'ok'arinsu don ta farfad'o amma shuru dole sukasa mata abun numfashi. Yesmeen kuka kawai take Hajiya Talatuma ba k'aramin tsorata tayiba d'azu lafiyanta laufa amma dubeta lokaci guda yadda ta fita hayyacinta,lallai rai ba bakin komai yakeba. *UMMYN YSRH* [02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: 💞💞💞💞💞💞💞 💞💞💞💞💞 💞💞💞💞 💞💞💞 💞💞 💞 *YESMEEN* 💞💞💞💞💞💞💞 *WRITEN BY:* *UMMYN YSRH* *®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *(P.M.L)* *101~105* Anhana kowa shiga wajenta,doctor ya k'ira Alhaji yake Sanar dashi zuciyarta na gabda bugawa dole aguji duk wani abunda zai rink'a tab'a matashi yanzu,rayuwarta na cikin had'ari aduk lokacnda hakan ya kuma faruwa yanzunma Allah ne ya tak'aita. Har Doctor ya gama bayaninshi Alhaji jinshi kawai yake,yana tunanin yaushe Habiba ta kamu da ciwon zuciya baisaniba shidai yasan tanada hawan jini toh zuciyarfa yaushe ta sameshi? Meyasa ta b'oyemai?. Har Doctor ya sallameshi zuciyarshi na mai tambayoyi gakuma maganar Doctor namai yawo a kunne "A yanzu matarka rayuwarta na cikin hatsari,ko ta rayu kota mace." Yana fitowa sukayi kicib'us da Yesmeen durk'ushe bakin k'ofar tana zabga kuka da alama taji komai Alhaji yace "Tashi Yesmeen,kibar kuka zonan." da k'ar ta iya tashi k'afafunta duk sun kumbura. Kan wani dogon benci suka zauna sannan ya fara magana "Kuka ba abune mai amfani agaremuba,addu'a da fatan Allah tashi kafad'unta shiyafi cancanta muyi mata ayanzun,ki duba yanayin da kike ciki kema zaki iya jama kanki wani cutan,zafin ciwo baya kawo mutuwa don Allah kisama zuciyarki hak'uri,kamar yadda nasanki da hak'uri da juriya inason yanzunma kizama kamar yadda nasanki." Hawaye kawai ke gangara kan k'uncinta bata iyace komaiba Cigaba yayi da magana "Bayan na koma gida d'azu d'ebo wasu kaya naci karo da wani takardan da nima yayi mugun d'agamin hankali,Wanda nasa shiyayi sanadiyar fad'awar Ummanki cikin wannan hali,yanzu ba lokacin bin ba'asin meya faru bane duk mujin gine gefe mubari har Ummannaki ta sami lafiya da kaina zannemi waliyanshi mijin naki. Yanzu don Allah kisa hak'uri da juriya yin hakan shizaisa ta sami kwarin gwuiwa,nuna damuwarki shizaisa ta kasance cikin irin wannan yanayin." "Insha Allahu Abbah zanzama mai boye dukkan damuwa don samun farin cikin Ummahna,muna kuma godiya da yadda kake kulawa damu,Allah biyaka da gidan Aljannah." "Bakomai yiwa Kaine. Allah miki albarka ya sauk'eki lafiya." Kunya taji ta rufe fuskarta da tafukan hannunta tana murmushi lokaci guda kuma sai hawaye data tuna basu tare da mahaifin abundake cikinnata. Yesmeen na barin gidan MUNEEB GENTLE yaji kamar ya sauk'e wani nauyi akanshi itama taje ta d'and'ana irin bak'in cikin da yad'au tsawon lokaci yana k'unsa,sanadiyar Marin data mai cikin jama'a yasa suka rabu da masoyiyarshi don baid'au matakiba,dalilin hakan yad'au alwashin rama abun datamai,sai gashi cikin sauk'i sun had'u kuma yasami nasarar cimma burinshi,yau zuciyarshi fes. Wajen k'arfe biyu na dare Ummah ta farfad'o da sauri ma'aikatan suka cire mata abun k'arin numfashin,sukai duk wani aiki nasu na ma'aikatan jinya. Yesmeen tana zaune kan abun sallah tun tana sallah a tsaye har ta dawoyi azaune. Ganin ta dawo daidai yasa aka canza mata d'aki saidai ba'a buk'atar hayaniyar jama'a. Satinta biyu a asibiti ta ware sosai kamar ba itaba,itakam har mamakin yadda taga 'yar tata take ta ware kamar batada wani damuwa hakan yasa itama ta ware. Ansallameta ta dawo gida sunci gaba da al'amuransu,saidai yanzu Hajiya Talatu anfara rusuna. Alhaji yaje ya sami Manyan ANWAR don jin musabbabin yin sakin sukace basuma da labari amma zasu sami mahaifiyar yaron don jin yadda ya kasance,zasu nemeshi idan sunje. Lokacin da sukaje Hajiya Lamee ta bad'ama idonta toka tace bazata dawo mata gidaba yarinyar data gama barbad'a da bin maza ace d'anta ya zauna da'ita Sam bata yadda ba. Hakadai suka rabu baram bara. Hak'uri sukaba Alhaji kan ya bari zuwa wani lokaci kannan tad'an huce. Sanda Ya sanar ma Ummah cewa yayi arabu dasu indai bata da hak'k'insu da Kansu zasu nemeta. _BAYAN WATA BIYU_ Su Ummah ba zama anata hidimar bikin d'iyar k'anwar Alhaji. Ummah ta gama yima Yesmeen shirin tafiya Kano wajen aminiyarta don cigaba da karatunta idan ta haihu tunda takusa shiga watanta,kuma gidansu ANWAR ba wani labari,gara ta koma makaranta. Yau suna yinin biki bakowa gidan sai YESMEEN itama yau batajin dad'i shiyasa bata sami zuwaba. Yamma lis taji wani bacci mai dad'i na d'ibanta gashi la'asar ya wuce batason bacci amma dake bacci b'arawone haka ya kwasheta. Shigowa yayi gidan da 'yar fitonshi shiru yaji gidan da alama ba kowa,kitchen ya nufa don d'aukar Kofi,k'ofar Ummah ya gani bud'e yasan kuma suna wajen bikin,zuwa yayi da nufin lek'awa falon shuru ya wuce har uwar d'aki kwance ya hangota tana baccinta cikin kwanciyar hankali, Wani farin cikine ya rufeshi don yau zai cire maitarshi, jiki na rawa ya hau cire kaya,bekaiga gama cirewaba yaji salati daga bayanshi "La'ilaha'illallah......" Batagaiga k'arasawaba ta zube k'asa shirim. Nima tsabar tsoro juyawa nayi na ficeda gudu. ✍🏻 *~UMMYN YSRH~* [02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: 💞💞💞💞💞💞💞 💞💞💞💞💞 💞💞💞 💞💞 💞 *YESMEEN* 💞💞💞💞💞💞💞 *Written by:* *UMMYN YSRH* *®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *(P.M.L)* _Ina muku barka da zuwan Ramadan Iyalan gidan_ *ALHAJI ISAH MUDA LAWAL* *Accountant general of Bauchi state Audit* _Allah karb'i ibada ya gafarta zunubai_ _inayima dukkan d'aukacin 'yan'uwa musulmai maraba da zuwan Ramadan Allah karb'i ibadunmu yasa muna daga cikin 'yantattun bayi_👏🏻 *116~120* 🔚 Ta isa gida daidai ruwan ya d'an ya anata k'iraye2 sallar magrib,d'aki ta wuce ta rufo k'ofar sannan ta wuce bayi ta watsa ruwa ta d'auro alwala. *BAYAN WATA 'DAYA* Yesmeen tun safe takejin wani iri daurewa kawai take,ahaka ta wuni har zuwa dare,saida tazo kwanciya ciwo yace salamu alaikum,duk dauriyarta saidata gaza. Asibiti aka garzaya da ita ba ita ta haihuba sai wajen k'arfe hud'u da wani abu na asuba,ta sami santaleliyar d'iyarta,amma ta galabaita sosai,saida aka gyarasu ita da Babyn kowa kagani murna yake da fatan Allah raya. Wayar Ummanta ta d'auka tama babyn hotuna ta turama Anwar,tare da guntuwar magana. "Nasauka lafiya 'Diya mace,ga hoton babyn." Sanda ta tura yana Masallaci yabar wayar a gida. Saida sukai awa shida ta huta aka tabbatar ba wani matsala gareta aka sallamesu. Lokacinda Anwar ya bud'e wayarshi yaga sak'on Yesmeen da gudu ya sauk'a k'asa wajen Hajiya cikin d'oki da murna ya mik'a mata wayar yana cewa "Hajiya kinyi jika Yesmeen ta haihu." Gaba d'aya yama manta da abundaya faru karb'a tayi itama cikin murna tana kallon jikar tata,lokaci guda taji son 'yar yarinyar [02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: 💞💞💞💞💞💞💞 💞💞💞💞💞 💞💞💞💞 💞💞💞 💞💞 💞 *YESMEEN* 💞💞💞💞💞💞💞 *WRITTEN BY:* *UMMYN YSRH* *®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *(P.M.L)* _Inamai Baku hak'urin rashin jina da kukayi na kwana biyu masoya wannan Novel hakan ya farune bisa wani uzurin amin afwa👏🏻 *106~110* K'arar fad'uwarta da salatin datayi shiyayi sanadiyar farkawar Yesmeen cikin fad'uwar gaba hakan kuma yayi silar dawowar Sani cikin hayyacinshi,suna had'a ido da Yesmeen ya sunkuya tattara kayanshi ya ari na kare. K'ok'arin mik'ewa tayi cikin zafin nama sada tana mik'ewar taji wani k'uttt a kwankwasonta sanadiya tashin sauri datayi,taka k'afar tayi don k'arasawa wajen Umman nata tana taka k'afarta taji wani zafi tundaga k'ugunta har k'afarta rik'e wajen tayi,sannan tayita maza ta k'arasa ga Umman. Kafinta iso bakinta da hancinta jini kawai yake fitarwa sai motsi take da bakinta,baka Iyajin me take fad'a,cikin razana da fad'uwar gaba Yesmeen ta zauna ta d'ago kan Umman tana sambatu. "Wayyo Ummahna don Allah ki tashi karki mutu ki barni kece gatana,wallahi bemin komaiba." "Kitashi Banda kowa ayanzu saike,ki bari in rigaki tafiya." "Kimin magana don Allah Ummahnah." Maganganu kawai take wani kalmarma batasan metake fad'iba,tanayi tana jijjigata tana goge jinin take gangaro mata,can taji wayar Ummah na k'ara cikin jaka,jawoshi tayi taga Alhaji ke k'ira ai da sauri ta d'aga waya cikin rud'ewa tace "Alhaji kana inane? Gamu agida kazo Umma ba lafiya." Ai baigama jin mezataceba ya fita daga cikin moton ya turo get ya fad'a cikin gidan aguje,dama ya k'irata ya sanarmata ya dawo gidane. Yana shiga yaganta kwance,ba magana ba motsi gaba d'aya jikinta ya saki,da sauri ya sunkuceta sukayo waje sauri2 gudu2 haka suka isa bakin get ta bud'emusu suka fita da ita,sannan taje ta bud'emai motar suka shiga sai asibiti. Suna isa aka karb'eta sai emergency,suna k'ofa suna tsaye likitan ya fito jiki sanyaye,gawani zufa dake tsatstsafomar,suna ganinshi suka taso da saurinsu,tare suke tambayar likitan labarin mai jikin. Saida yayi ta maza sannan ya fara magaka kamar haka "Alhaji saidai muyi hak'uri domin Wanda yafimu sonta ya karb'i abunshi,gunda kowa ko jiran k'ira yau ta amsa k'iran ubangiji,don Allah kuyi hak'uri karku d'aga hankalinku,addu'a zaku mata shine k'arshen gata da soyayar da zaku nuna mata bayan ranta." Duk bayanin da likita yake gaba d'aya ba Wanda ya fahimta cikinsu don kamar an toshe musu jinsu,Abu guda kawai suka iyaji da yace bayan ranta. Yesmeen cikin kid'ima race "Kamar ya bayan ranta? Mutum da ranshi kace bayan ranshi, kai ka kasheta kenan? Alhaji kaji me wannan mutumin yake fad'a." "Ki kwantarda hankalinki baiwar Allah cikine dake karki jefa kanki cikin wani yanani. Tun kafin Ku iso da ita ta riga ta cika." Alhaji kam zubewa yayi kan kujerar dake bayanshi,Yesmeen gadan2 ta nufo likita tana sambatu "K'arya kake bata rasuba,kasake dubata,ba yanzu zata mutuba,zamu cigaba da rayuwarmu da Ummana kawai tayi suma irin na rananne." Kanta k'araso ga likitan said luuuuuuuuu ta zube k'asa da gudu likitan ya rik'eta,ya kwalama wash ma'aikatan wajen k'ira sukazo sukayi gaba da ita. _Nina zubewa nayi awajen tsabar firgicin rasuwar Ummah_ ✍🏻 *~UMMYN YUSRAH~* [02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: 💞💞💞💞💞💞💞 💞💞💞💞💞 💞💞💞 💞💞 💞 *YESMEEN* 💞💞💞💞💞💞💞 *Written by:* *UMMYN YSRH* *®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *(P.M.L)* *Ahar kullum baki bai tab'a Gajiyawa da addu'a da fatan Alkhairi garekuba iyalan gidan* *ALHAJI ISAH MUDA LAWAL* _ACCOUNT GENERAL BAUCHI STATE_ *INA MUKU FATAN ALKHAIRI GABAKI 'DAYAN AHALINKU* *RABBI YA MUKU SAKAYYA DA GIDAN ALJANNAH*👏🏻 *111 ~115* Afirgice ta farka daga mummunan mafarkin da take bakinta d'auke da salati,da sauri ta kai dubanta inda taga Umman tata ta zube saidai wayam ba komai,ta sake kai dubanta ga inda taga Sani yana d'ebe kayanshi wani mummunan fad'uwar gaba taji,ganin data mishi dagashi sai gajeren wandonshi,wato shi wannan gaskene ba mafarkiba. K'ok'arin mik'ewa take amma Sam ta kasa don gaba d'aya jikinta ba kwari sanadiyar mafarkin mutuwar Ummah datayi,ganin ta farka har tana k'ok'arin tashi yasa ya haye gadon yana k'ok'arin kamota ja da baya take daga zaunen,k'afarta ya cafko tayi wutsil2 ta fizge k'afar ta k'ara ja da baya,tanason mik'ewa amma Sam ta kasa magana ya farayi "Gara ki tsaya in miki ahankali,don yadda kika shiga hannuna bamai rabani dake." Addu'a kawai take jerowa cikin zuciyarta na Allah ya kawomata d'auki gaba d'aya fuskarta ya wanke da hawaye sake yunk'urin mik'ewa tayi cikin sauri saidai wani irin azababben ciwo taji mararta da k'ugunta,sake komawa tayi ta zauna. Sake mik'o hannunshi yayi karo na biyu don jawota saidai ji yayi kamar Wanda ya d'aura hannun kan igiyar wutan nefa don shokin,gaba d'aya ji yayi hannun tamai sanyi,Yesmeen da idonta ke rufe ta fara magana "Inamai tunatar dakai cewa zina daud'ace,zina ba abune mai kauba,tana d'aya daga cikin many an laifuka da aka yima dukkanin musulmai hani da ita,kada mu kusanci zina,idan kayi da y'ar wani,za'ayi da taka,idan kayi da k'anwar wani za'ayi da taka k'anwar,idan kayi da matar wani ko mahaifiyar wani kaima za'ayi da naka,nasa Ubangiji bazai tab'a baka nasara akainaba,kasani idan har kaci galaba akaina ba Wanda ya ganka akwai na ukunmu ALLAH." Daga haka bata kuma cewa komaiba tana jiran mai afkuwa ya afku idonta rufe har yanzu. Karo na biyu daya sake kai hannunshi gareta saidai azabar yanzu tafi ta d'azu wani k'ara ya saki tare da Komawa da baya ya sauk'a daga kan gadon yahau kwashe kayanshi ya fice daga d'akin. K'arar daya sake yasata bud'e idon tana gani ya sauk'a bar yabar d'akin,wani hamdala da ajiyar zuciya tayi tana godiya ga Allah daya kareta. Takai kusan minti talatin zaune kafin yayi yunk'urin tashi,aiko sai taji ta mik'e tace wato harda tsoro yasa d'azun ta kasa mik'ewa. Ji tayi bazata iya zama cikin gidanba tasa hijabinta tayo wake,ba gurin zuwa Hanifa ma run bayan bikinta da wata biyu akama mahaifinta chanjin wajen aiki suka koma Kaduna gidan ba kowa yanzu. Tafiya ta farayi don motsa jikinta ga hadari ya had'u ruwa zai iya saukowa ko wani lokaci hakan bai dametaba don tanason ruwan sama idan ya sauk'o bata shigaba batajin dad'i. Yayyafine ya fara sauk'a hakan baisa ta komaba saima k'ara tafiyarta datayi cikin nutsuwa,ta d'anyi nisa kad'an da gida ruwa ya k'ara yawa tsayawa tayi cak ta d'aga kanta sama idonta rufe kamar mai k'irga zuban ruwan. Yadda ruwan ke sauk'a kan fuskarta jin wani nishad'i take saidai kuma lokaci guda hawaye ya gauraya da ruwa fuskarta ya sauwa daga annuri zuwa akasinshi. Tunowa tayi da Anwar d'inta adaidai irin wannan lokacin suna manne da juna,yana bayanta ya sak'alo hannayenshi kan k'ugu ko cikinta ahaka zasu tsaya har ruwan ya d'auke suna cikin nishad'i. Allah sarki ko yana wani hali yanzu ohho? Wani fad'uwar gaba taji da yadda jikinta ya sauya tabbas duk yadda akayi Anwar na kusa da inda take,da sauri ta bud'e idonta,tsaye taganshi gabanta ya k'ura mata ido,gaba d'aya ya canza,ya rame yayi bak'i ga wani gashi daya sami muhalli a fuskarshi. Tausayi ya bata ta bud'e baki zatai magana ta fasa ta juya ahankali da nufin komawa gida k'iranta ya shigayi amma Sam tak'i juyowa "Habba Yesmeen bai kamata ki gujeniba rayuwata tana cikin garari ki taimaka ki tsaya ko lafiyarki inji,zuciyata,ruhina kullum tana tare dake." Yadda yake maganar duk yabata tausayi juyowa tayi race "Kabi Umurnin mahaifiyarka,karka manta tace duk randa ka taka kazo gareni zata tsinema,ko mak'iyina bana fatan tsinuwar iyaye ta tabbata akansh,kabi umurnin mahaifiyarka karka manta ana sake mata amma ba'a sake uwa da 'yan'uwa." Tana kaiwa nan tajuya,shikam yama rasa tacewa harta k'ule yana tsaye,jiki ba kwari shima ya juya. _Nima juyawar nayi tare da tausayawa masoyan_ ✍🏻 *~UMMYN SADEEQ~*