M] +234 702 541 3080: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *ZINARE* NAFISA ALIYU SASAAL Arewabooks@sasaal *BISMILLAH* ✍️ 7:30pm 5-7-2025 *Labarin ZINARE ƙirƙirarren labari ne, gagaruwan ciki da wasu ƙasashen ciki duk ƙirƙirane, idan wani sashe na labarin ya yi kamaceceniya da rayuwar wata/ni to akasine* *CHAPTER 1* *"BA A RANAR DA MUKA SHUKA IRI ZA MU GIRBI AMFANINSA BA, DOLE SAI MUN JIRA, MUN YI HAƘURI, TARE DA YIN AIKI TUƘURU."* 01 Yankin Tudu, Daular Sarki Hammam, sassanin wasannin ƙarshen mako. Yara Matasa Maza da Mata ma su shekaru 15 zuwa ƙasa ne suka cika filin wasan. Ɓangaren Maza daban na Mata ma daban. A ɓangaren Maza, a tsakanin ƙungiyoyin biyu da suke gwabza wasan ƙwallon ƙafa kowa na ƙoƙarin nuna ƙwarewarsa, da zafin namansa. Wannan yasa ihu da tafi yake ta tashi daga kowani ɓangare, bakunan wasun su kamar zai yage saboda dariya da ihu. Kujerarsa ba ta kusa da ta kowa, fuskarsa daban take data kowa, ba bu murmushi balle dariya. Ba ya tafawa kamar ragowar kamar ma dai bai san me ake yi a wajen ba, ko wanda aka tilastawa zuwa sansanin wasannin dole. Tsayayyen dogon hancinsa ya shafo ya na lumshe fararen idanuwansa, Kamar ance ya waiyawaya bangaren da Matan suke wasannin su. A daidai lokacin wata matashiya mai irin Shekarunsa ta kwaso ƙafar ƙaramar yarinyar da bata wuci shekaru 6 ba, mugun dariya ya kwashe da shi yana ƙara waiwayowa kansu dakyau, zaman ƴan borin da yarinya tayi ne yasa ya ƙara kwashewa da dariya. Ya na son mugunta a rayuwarsa sai dai baya iya yiwa wani amma yana so yaga anyi a gabanshi, saboda daɗin da yake ji, musamman idan wanda aka kai ƙasan ba shi da gaskiya. A hankali yarinyar ta miƙe fuskarta duk hawaye da majina, nan ma dariya ya ƙara kwashewa da shi, ya na jin daɗi a ranshi. Mai ya kaita cikin manyan da ba sa'anninta ba yin wasa, banda ga ƙananu Yara Ƴan uwanta suna na su wasannin? Miƙewarta tana karkaɗe ƙasar jikinta haɗe da zare idanuwanta da hawaye ya ɓata ne ya ƙara sashi sakin dariya kafin ya ɗauke kanshi yana sauke ajiyar zuciya nishaɗin da ya samu. A take asalin fuskarsa da ba fara'a sam ta dawo yadda ta ke. A can nesa da shi Sufyan yaron da bai wuce shekaru 11 ba ne ya zubamai ido, ya daɗe ya na kallon duk wa su motsinsa har hankalinsa ya bar wajen wasannin da ake yi gaba ɗaya. Maiyasa ba ya dariya sai ya ga mugunta? Maiyasa ba ya magana sai da ƙwaƙwarar dalili? Ya na son ya matsa kusa da shi ya yi masa magana kamar yadda Mahaifinsa yake umartarsa duk ranar da zai fito ire-iren waɗannan guraren da shi kaɗai yake iya sumun damar ganinsa kai tsaye, amma tsoro ya ke ji duk da ratar shekaru hudu ne kacal a tsakaninsu. NAILA da aka kwashewa ƙafafu jikinta ta ƙarasa karkaɗewa har cikin ranta takejin takaicin abinda akayi mata, banda zafin da take ji a bayanta. Kalle-kallen wanda zata kaiwa ƙara ta fara yi har idanuwanta suka faɗa gurin dayake zaune shi kaɗai. Da gudunta na yaranta ta nufesa rabin fuskarta duk ƙasar da hannunta ya kwasa. Gabansa ta zagayo ta tsaya batare jin tsoro ko shakka ba. Da ƙaramin muryarta na yara ta fara koromasa bayani ta na sauke ajiyar zuciya. Ba ya wasa da yara, balle ya ce ya taɓa wasa da ita a wani wajen ne yasa ta zo har gabansa ta tsaya. Tsaf yake sauraronta, a bayanin na ta da yanda take kame-kamen dole sai ya bi mata haƙƙinta yasan itace bata da gaskiya amma take so a rama mata, rabin fuskarta ya kalla tare da tuno yadda aka kwashe mata ƙafafuwa tayi zaman ƴan bori, sai ya kwashe da dariyar mugunta Ya kai wasu daƙiƙu ya na yi kafin ya gimtse fuskarsa yana ɗauke kallonsa daga kan fuskarta. Tsayawa Naila tayi ko zai ce mata ta zo su je ya rama mata amma sai taji shiru. Ƙasar fuskarta ta ƙarasa karkaɗewa da kyau. Sai a lokacin ta gane wajen wanda ta zo. SULAIM ne ɗan gidan ABDUH DHAHAB ɗin daya zama ƙashin bayan Yankin su kuma Abokin Mahaifinta. Indai shine Dama bazai kulata ba, dan da tasan ma shine da bazata zo ba. Barin wajen ta yi tana tunano abinda zatayimai tunda yaƙi kulata dama kuma tasan kurma ne baya magana. A haka wasannin ya ƙare kowa ya fara haɗa kayan wasanninsa don tafiya Gida. NAILA; Sanyin iskar da yake busa ta ne yake ƙaramata ƙaimin tunanin abinda zata haɗamai lokacin da take kallon takun sawayensa shi kaɗai, saɓanin ragowar da suka jero da Abokannan su. ★washe gari ƙarfe bakwai na safiya a harabar gidan Abduh Dhahab ya yi mata, sanye cikin Uniform ma su tsafta, kafaɗarta rataye da jakar buhu shima a wanke ƙal. Baki Malik Mai share harabar gidan ya saki, lokacin da ya yi ido biyu da Naila, tambayarta dalilin zuwanta ya yi yana ajjiye tsintsiyar hannunsa. Dariya ta fara ƙyalkyalewa da shi sannan ta ce; "ina kwana Malik, dama Sulaim ne yace na biyo ya kaini Makaranta a kekensa" kai ya girgiza mamaki da wayon ƙaramar yarinyar na kamasa uwa uba ƙarfin halinta. Kafin yayi magana Sulaim ya fito da Kekensa shirye cikin Uniform ɗin daya bambanta da nata color. Sulaim kallo ɗaya ya yi wa Naila ya ganeta, duk ɓacin ran daya fito da shi sai ya nemi gushewa; "Anata tunanin zata iya ƙuntatamasa kenan?" Ya tambayi kansa. Kai kawai ya jinjina ya na karkata Kekensa mai kyau da tsada ta gefen da take tsaye. Dasauri ta ɗane tana sakin dariyar nishaɗi haɗe da ɗagawa Malik da ya saki baki hannu. Gudun dayasa Naila sakin kuka da majina Sulaim ya ke yi da ita a kan keken. Duk inda suka gifta sai an kalleta ma su dariya na yi. Kafin su isa Makaranta mazaunanta har ƙaiƙayi su ke mata. Bai ce mata komai ba bayan ta sauka ya bar wajen. Naila takai minti goma a tsaye tana kuka kafin ta shiga aji. Bayan kwana biyu Sulaim ya ɗauka Naila zata gajiya amma sai ya ga kullum sai tazo. Tun hankalin mutanen Yankin ba ya kansu har kowa ya fara Ankara haka ma Mahaifinsa sai dai bai ce komai ba. Tun ƙarfin halin Naila baya birge Sulaim har ya fara birgesa, ya dawo kullum da kansa yake tsayawa a ƙofar Gidansu ya ɗauketa. A ɗan kwanakin da suke zuwa Makaranta tare Naila ta fahimci Sulaim ba kurma ba ne Selective mutism ne. Tun yana yaro har ya kai shekaru huɗu bai iya maganar arziƙi ba, kuma a haka sai ya wuni baiyi magana ba musanman a cikin mutane. Ya na jin nauyin yin magana a wasu lokutan da ma wasu guraren. Da farko yawon kaishi Asibitocin wa su Yankunan Matar da Mahaifinsa ya aura bayan tafiyar Mahaifiyarsa ta yi-ta yi saboda son da takemai. amma duk inda taje amsa ɗaya ne ba sauyi. SULAIM; Rayuwar neman kuɗi da kafawa zuciya ra'ayin riƙau na tsayuwa kan matsaya ɗaya tare da aikin ƙarfi tuƙurun Mahaifinsa ya horar da shi a kai, wannan dalilin ne ya yaƙara duƙufar da maganarsa, saboda shima Abduh mahaifinsa ba gwanin surutu ba ne kuma tare suke wuni su na aiki, idan ya dawo daga Makaranta. Sannan Abduh Dhahab ya keɓancesa daga Abota da kowa musamman da ya ga sunfara tsokanarsa da kurma. Tun Sulaim yana jin ƙiwiya da nauyin yin aikin ƙarfin ƙera Tukwanen da sukeyi har ya haƙura ya saba. Sulaim ya fi jin daɗin saurarar maganganun mutane a kan ya yi. Daga Makaranta ba ya zuwa ko ina sai wajen sana'ar Mahaifinsa, sai kuma filin wasannin ƙarshen Mako. Sauraran hirarrakin mutane ba tare da ya tofa ba, ya taimaka ƙwarai wajen mayar da shi Yaro na daban a cikin dubban Yara ƴan uwansa saboda basirarsa. Matsowar ƙarshen watan cin Kasuwar babban Yankin ne yasa ko ina ya ɗauki harama don kusan dukka mutanen Yankin kowa da abinda yake siyarwa don samun kuɗin shiga daga baƙin da suke shigowa. Haka yake a Gidan su Sulaim da suke ginshiƙin Kasuwar gaba ɗayanta. Ba ji ba gani suke ƙera Tukwanen dake ɗaukar idon duk wanda ya kallesu tare da kwaɗaituwar son mallakar su. A gidan su Naila ma haka zancen yake. Mahaifiyarta kayan wasan Yara take ƙerawa na laka, irin su kwano, murhu, cokali, da randar ruwa ƙananu gwanin ban sha'awa, dukka na wasan Yara. Kuma da yawan gaske takeyinsu amma baya kwantai duk sai an siyeshi. Zuwan Naila Makaranta tare da Sulaim ya ƙara farfaɗo da zumunci a tsakanin Mahaifiyarta da Matar Mahaifinsa, tun da dama can akwai alaƙar jini amma Abduh Dhahab ya datsesa saboda hana Iyalinsa shiga wajen kowa da ya yi. A tsakanin kwana huɗun da ya rage aci Kasuwar Zinare, Ɓakin fuska a manya motocin da ya zama abin kallo ga Mutanen Yankin su ka bayyana a Daular Sarki Hammam. A fadar Sarki Hammam baƙin fararen fatar su ka shaida abinda ya kawosu, wato siyan Tukwanen Abduh. Har gidan Abduh Sarki Hammam ya sa akayi musu rakiya. Bayan sun kai, ƙememe Abduh yaƙi fitowa balle su gana, haka suka haƙura suka ƙara dawowa Fadar Sarki Hammam ya taimaka ya yiwa Abduh magana, ya siyar mu su da Tukwane. Sarki Hammam da kansa ya tura a kirawo masa Abduh. A ɓangaren Ɗayyib Ɗan uwa ga Abduh Dhahab kuma Aboki, Mahaifi ga Sufyan. Bai samu nutsuwa ba, har sai da aka bincikamasa dalilin zuwan Baƙin da kuma wajen wanda su ka zo, ta hanyar Aminansa da baƙin suka shigo Fada akan idanunsu. A ranar bayan Sallar Magriba labarin Faɗuwar Ɗayyib ya riski Abduh Dhahab. A dai-dai lokacin da kiran Sarki Hammam ya riskesa. Ɗan jim Abduh ya yi, yana sauraran ɗaya daga cikin Aminan Ɗayyib da yasa su ka bincikamai zuwan ɓaki da kuma dalilin zuwansu da wajen wanda suka zo, bayannan kuma ya yanke jiki ya faɗi. Wanda ko shakka ba ya yi akwai abinda Ɗayyib ɗin ya shirya. A tsarin Abduh baiyi niyyar Aminta da ɓakin da suka zo ba, don ko ganinsa bai bari sunyi ba ne saboda ba zai siyar musu ba. Tayaya zai kwashe dukka Tukwanen ZINAREN da mutane suke baro Yankunan su da jahohinsu don siya, ya siyarwa da mutane ƙalilan bayan yasan bazai iya ƙera wa su Tukwanen ba kafin zuwan ranar? Bayason Darajar Yankinsa da Kasuwar da ya sha gwagwarmaya kafin kafuwarsa ya yi faɗuwar Tasa, amma yana ganin lokaci ya yi, da ya kamata ya sallama komai. Godiya ya yiwa wanda ya kawo masa labari, sannan ya ɗauki hanyar zuwa ganin Sarki Hammam. "Mai zai sa Ɗayyib ya yanki jiki ya faɗi mai hakan yake nufi" Abduh ya tambayi kansa, lokacin da ya kutsa Fadar Sarki Hammam. Bayan Sarki Hammam ya gama koro masa jawabi bai ja da nisa ba ya ce ya amince, don haka Sarki Hammam ya ce yaje Sashen Baƙi suka ƙara tattaunawa da su. Kafin Abduh ya shiga wajensu sai da ya fara shiga Sashen Ɗayyib, yanayin yadda ya gano makirci ƙarara a ciwon nasa ne yasa kai tsaye bayan ya shiga wajen baƙin Fararen Fatar ya ce mu su;"Gobe su kawo kuɗi ku kwashi Tukwane" Jikinsa a sanyaye, ya yi musu sallama ya nufo gida. Bayan ya dawo gida, pillow da abin lulluɓarsa ya ɗauko ya dawo ɗakin Sulaim, rauni da tsoro na shigarsa akaron farko tun fara gwagwarmayasa...🏻 09132403788 [7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: 🔥ZINARE🔥 SASAAL Arewabooks@sasaal 02 SULAIM; ★washe gari da Safe. A shirye yake tsaf cikin Uniform fuskarsa a turɓune, da zafin nama ya ke yunƙurin fito da kekensa, kalaman Mahaifinsa na ƙara sukar zuciyarsa, kullum ya tambayesa kuɗin kashewa sai ya ce masa; "Ba a ranar da mu ka shuka iri, za mu girbi amfaninsa ba, dole sai mun jira kuma mu yi haƙuri, tare da yin aiki tuƙuru. Ka je Makaranta yau ma ba ni da kuɗin da baka" Waɗannan kalamai su Mahaifinsa yake yawan nanata mai, duk lokacin daya miƙamasa hannu da sunan ya ba shi kuɗin da zai siyi abu a Makaranta ko yin wa su uzururrukan da ba su zama tilas ba. Duk da ga kuɗin ya na ganin su muraran amma sisi ba zai ba shi ba. Kamar kullum da haushin hanasa kuɗin da ya yi ya yaƙarasa fito da kekensa ya bar Gidan, ƙofar gidansu Naila da ke kusa da na su gidan ya ja ya tsaya. Yana kaɗa kararrawar, ta fito a guje, Ta na hawa ya fige keken ko gaisuwar da take masa bai amsa ba. Yanayin yadda ya ke tsala gudu a kan keken kwatankwacin ranar da ya fara ɗaukarta ne ya sa ta ƙanƙamesa da siraran hanayenta da ko kusa ba su ratsa rabin cikinsa ba. A haka suka isa dogon ginin da ke kewaye da ajujuwan karatu. A hankali ya kwanto da keken duk da ba wani ƙato ba ne ta sauko. Idanuwanta ma su kalar tausayi ta ɗago ta kallesa, sannan ta ɗagamai ɗan ƙaramin hannunta. Kamar yanda ya saba bai ɗaga mata na sa hannun ba kuma bai ce mata komai ba, sai kanshi daya ɗan karkata gefe yana lumshe fararen idanuwansa haɗe da jinjina mata kai. Murmushi da ya bayyana ƙananun haƙoranta ta saki, kafin ta nufi ajinsu da ɗan gudu tana ƙara waiwayarsa. Shima murmushin da shi kaɗai yasan yadda ya ke yin kayansa da salo mai birgewa ya saki ya na juya kan kekensa ya bar wajen. GIDAN ABDUH DHAHAB Tarin Tukwane sababbun ƙerawa ma su kala mai kyan gani a ido da ƙwari a hannu ne jere a ƙaton filin da yake ƙerasu, Lokaci ɗaya ido bazai iya ƙirga su ba saboda yawansu, Ƙira mabanbanta akayiwa tukwanen. Gefe guda Abduh Dhahab da siffarsa ta fi kama da na tsoho, ko mai rangwamen hankali, a tsaye, duk da fuskarsa ta ɗan ƙuruciya kan gani kasan ba wai tsufar shekaru ba ne, tsufar bautar da ya ke yi ne, da kuma rashin tsaftace jiki. Fararen Fatar da suka zo Daular Sarki Hammam ne a gefensa, su na cinikin Tukwanen da ya jera da harshen nasararsa da ke fita fes kamar ba shi ba. A haka Sulaim ya dawo da kekensa ya same su. Hannu ya ɗaga musu haɗe rusunar da kansa alamar gaisuwa kafin ya wuce aihinin cikin gidan su. Yana ƙoƙarin sa ke fitowa cinikin su ya faɗa a kan idanuwansa su ka ajjiyewa Mahaifinsa kuɗi ma su yawan gaske a cikin jaka. Mamakine ya kama Sulaim, maiyasa Mahaifinshi zai siyar da Tukwanen da saura kwana uku a ci kasuwar su? mai zai cewa mutanen da za su taso da ga maƙotan Yankunan su da mutanen Birni ma su zuwa sara? Dole yasan wata sabuwar wahalar zai ɗora mu su, su sake ƙera wa su Tukwanen, amma ta yaya hakan zai yiwu? Ranshi a ɓace ya ƙara komawa cikin Gidan. Matar Mahaifinsa ya samu a ɗaki. Da hannu ya tambayeta ta san dalilin da ya sa Babansa ya siyar da Tukwanen da za su fita kasuwa da shi jibi ba? Alamar ba ta sani ba ta yi masa. Agogon ɗakinta ya kalla ya na fita da sauri ya bar Gidan gaba ɗaya. ABDUH Dhahab Bayan Fararen Fatar sun sa an ɗebe musu Tukwane, Ƙwalla ne ya tararwa idanunsa da su ka zama jajayen ƙarfi da yaji, saboda bauta da neman kuɗi da ya ke yi tsayin shekaru ba tare ya mora ko ya bari Iyalansa sun mora ba, shi dai kawai burinsa cigaban Yankinsa. Ɗakinsa ya wuce da tarin kuɗin. Yanayin yadda ya samu fuskar Ɗayyib jiya da ya shiga dubasa na ƙara dawomasa. A baya Zuciyarsa babu ɗigon rauni ko tsoro sai burin kafuwar Yankinsa, amma a wannan karon zuciyarsa tsoro ne fal a cikinta, a ransa ya yanke ya zama dole ya bar Yankin a wannan karon ya haƙura saboda ba shi da zaɓi ko don ginuwar rayuwar Sulaim da shi kaɗai Allah Ya mallakamai, bayan ya adana kuɗin ficewa ya yi ba tare da ya sanar da Iyalinsa inda zai je ba. SULAIM; Bayan ya baro gida Makarantarsu Naila ya wuce, kasancewar su sun rigasu tashi saboda jarabawar da suka fara. A bakin makaranta ya sa mu Naila da jakarta na buhu saƙale a kafaɗarta. Bai ce mata komai ba ya kwanto da keken ta hau. Har suka ƙaraso ƙofar Gidansu da ya ke maƙota da na su Gidan bai ce mata komai ba. Ya na sauketa dasauri ta sa ɗan ƙaramin hannunta tana lalubar jakarta, kwandala biyu ta fito da shi ta na miƙamai. "ga shi ka siya wani abun" Ta faɗa da ƙaramin muryarta na Yara, ta na jiran amsarsa. Saboda sarai tasan ya na magana. Ɗan mitsitsin hannunta ya kalla da kuɗin sannan ya girgiza kai alamar a'a ya na karkata kan kekenshi alamar tafiya zai yi. Ƙin matsawa ta yi daga gurin ta na kallonshi. Har ya fara tafiya ya kasa jurewa ya juyo. Hannunshi ya miƙa mata alamar ta kawo kuɗin. Da sauri ta miƙamai ta na dariyar da ya bayyana jerarrun ƙananun haƙoranta. Shima murmushin bazata ne ya tahowa laɓɓanshi wannan dalilin ya sa yabar wajen da zafin namansa. Har ya rage saura kwana biyu aci kasuwa, Sulaim bai ji mahaifinsa ya yi misa zancen ƙara ƙera wa su tukwane ba, kuma bai ga alamun ya na da niyyar yin wasu ba, wannan dalilin yasa yafara zargin abubuwa dayawa har ya kasa runtsawa, musamman daya ga Mahaifinsa ya tattara duk uban dukiyar da ya ɗauki shekaru yana tarawa a cikin ƙaton buhu ɗaya. ★Washe gari jikinsa sam ba bu ƙwari ya yi shirin Makaranta ya hau kekensa ya nufi ƙofar Gidan su Naila. Tana tsaye ta shirya tsaf cikin wankakkun uniform ɗinta, karkata keken ya yi ta hau. Bayan sun isa Makaranta ya na sauketa ya juya batare da ya kalleta ba. Sai taji sam ba daɗi a ranta, kafin ta haɗu da ƙawayenta ta manta da komai. NAILA; A na tashinsu ta taho da gudu, nan ma Sulaim bai amsa mata gaisuwar da ya saba amsawa da gyaɗa kai ba, duk sai ta ƙarajin ba daɗi, jikinta ya yi sanyi. Ya na sauketa ta fara lalubar jakarta, soyayyiyar Aya ta fito dashi mai yawa da ta siya kwandala biyu ta miƙamai. Bai karɓaba sai kallonta da ya tsaya yi. "ga shi Yaya" ta faɗa da tsoron yanayin fuskarsa. Murmushin yaƙe ya yi ya ce; "Naila" da muryarsa mai tsada a wajen mutane da daɗin sauraro ga wanda ya samu ji. kanta da ɗago dasauri ta na washe ƙananun haƙoranta kafin ta ce "na'am" "Idan kina so na karɓa to ki faɗi sunana na ji" ya faɗa yana kallon fuskarta. dariyar yaranta ta ƙyalkyale da shi, daɗi kamar ya sumar da ita, sai da ta tsagaita sannan ta ce. "Sulaim" ta ƙasara faɗa tana murmushi haɗe da rufe fuskarta. Shima murmushin fuskarsa ce ta faɗaɗa ya na kallon yadda take dariya kamar an bata aljanna. Hannunsa ya miƙamata, da sauri ta miƙamai Ayar ta na shigewa cikin Gidansu ranta fari fes saboda ya yi mata magana baki da baki, ba da kai ko hannu ba. Sannan ta matsu ta shiga gida ta basu labari. Bayan ya zura Ayar da ta bashi a aljihun gaban rigarsa kasa tafiya ya yi sai da ya ɗan jima a zaune a kan kekensa kafin ya bar ƙofar Gidan... ABDUH DHAHAB; bai dawo gida ba, sai dare, Iyalin Mairam ba ta tambayarsa inda ya je, saboda tunda da ya daina kwana a ɗakinta take fushi. SULAIM; A daren ranar ma kasa runtsawa ya yi, saboda tunani da hasashen da bai san dalilin su ba. Ya na jin ƙewar Naila ba tare da yasan dalili ba ga fargaban dalilin da ya sa Mahaifinsa ya sayar da Tukwanen da zai fitar da su kasuwa washe gari ba tare da ya ƙera wa su ba. Ƙarfe 2:00am ya ji alamar motsi, gefen Mahaifinsa da ya dawo kwana a ɗakinsa ya kalla ya ga alamar barcinsa ya yi nisa, miƙewa ya yi tsaye. Wani ƙaramin ƙarfe mai tsini da kaifi ya ɗauka ya soke a gefen ƙugunsa, kafin ya fara takowa tsakar gidan a hankali. Ya na ƙarasa fitowa tsakar gidan akayi masa yankar da ya sa shi buɗe dukka girman muryarsa a gefen kafaɗarsa na dama. Dole ya zube ƙasa zuciyarsa da gangar jikinsa na karɓar raɗaɗin azaba lokaci ɗaya. "Au ashe iskanci ne dama ka iya magana?" Wanda ya yankesan ya faɗa ya na sakin dariyar mugunta. Tsaf Sulaim ya ɗauki muryarsa duk da ba ya cikin nutsuwarsa. "Zan Barka a raye matsawar ka faɗamin ina Mahaukacin Ubanka ya ke" wanda ya yankesan ya faɗa yana ɗagoshi. Shiru Sulaim ya yi ya na kallon fuskarsa dake sakeye cikin baƙin ƙyalle. Ƙaramar wukar hannunsa yasa ya ƙara yankar gefen kunci Sulaim da ƙarfi haɗe da ƙara maimaita: " ina Mahaukacin Ubanka Abduh Dhahab ya ke, a ina ya zuba tarin dukiyar Tukwanen Zinaren da ya siyarwa Turawan da su ka zo kwana uku da suka wuce? Su na ina!" A wannan karon Sulaim bai saki ƙara ba, sai zaburar dayayi ya soke shi da ƙarfen da ya soke a gefen ƙugunsa a dai-dai saman kafaɗarsa tunda ya na da tsahon ƙafa. "yaushe Mahaifina ya gama girbar amfanin Irin da ya sha wahala da azabar shekarun shukawa, da har zakazo karɓan na ka kason!?" Sulaim ya tambayesa da sansanyar muryarsa da azaba ta sa ya ƙara yaushi. Sulaim Bai gama sauke hannunsa da haɗiye yawun kalamansa ba ya ƙara yankarmai gefen kafaɗarsa na hagu haɗe da fesar da hucin haushin kalaman da Sulaim ɗin ya jefesa da shi. Shima Sulaim bai zube ƙasa gaba ɗaya ba sai ya da ya zaro ƙarfen da ya sokamai a kafaɗa ya ƙara kafamai a tsakiyar cinyarsa da dukka ƙarfin daya rage mai. Kusan lokaci ɗaya su ka zube ƙasa. Kowannen su ya na sauke numfarfashin azaba ga jinin da ya ke bin jikin kowanne su. Kasa jurewa Matar Mahaifin Sulaim da ke laɓe ta yi ta fito ɗaga ɗakinta don tsaf ta haddace muryar wanda ya shigo musu gida. Da kuka ta fito ta na ba shi haƙuri. Wanda ya yanki ya na ganin fitowarta ya miƙe da sauri kamar ba shi ba, saboda hasashen mallakar dukiyar Tukwanen Zinaren da Abduh Dhahab ya ɗauki tsahon shekaru ya na bautar tarawa ba tare da ya bari ko shi kansa ya mora ba. Itama tambaya ya titsiyeta da shi ya na rintse idon azabar da ya ke ji, "a ina Abduh Dhahab ya ajjiye kuɗin Tukwanen Zinaren da ya siyarwa Turawan da suka zo? kuma a ina ya ke ɓoye dukka dukiyarsa ki faɗamin na ƙyaleki a raye?" Shiru ta yi ba ta ce masa komai ba, sai kallon bayansa da ya ga ta na yi. Bai kawo komai ba a ransa ya ɗauka halin da Sulaim yake ciki ta ke kallo. Ganin bazata faɗa ba yasa ya kai mata hauri ta bugi bango da ɗaya ƙafarsa mai lafiya. Ya na juyowa inda ya bar Sulaim yaga ba bu shi a wajen. Kenan Abduh Dhahab yana gidan? maiyasa bai fara bincika ɗakunan Gidan ba tukunna? "Abduh!!!!" ya faɗa da ɗan ƙarfi yana zare dukka girman idanuwansa da su ka yi jajir Pito ya yi, abokannan rakiyarsa da suka maƙale suna jiran umarninsa suka shigo Gidan. Biyu zama su ka yi ɗauremasa ciwukan da Sulaim ya ji mai, bayan sun zare ƙarfen cinyarsa, ragowar kuma suka hau bincika gidan. Sun samu Ɗakin Abduh Dhahab da duk amintakarsa da Mutum ba ya bari ya shiga, sun bincika amma babu ko sisi a ciki. Hanyar da jinin Sulaim ya ɗiɗisa su ka dinga bi su na haskawa, har suka samu ta inda Abduh Dhahab da Sulaim suka bi suka bar gidan, ta ƙofar da ba su san da shi ba. Zabura ya yi ya na haska ƙofar bayan da Abduh Dhahab ya bi har zuwa inda jinin ya tsaya. Dariya yaƙen azabar da ke nuƙurƙusarsa ya saki ya na kutsa kai cikin gidan bayan sun ɓalla ƙofar Moƙocinsa kuma Amininsa da suke kyautata zaton nan Abduh ya shiga. Da matar gidan su ka ci karo tana salla a tsakar gida. Bai amsa tambayoyin da ta ke jero mu su na dalilin shigo mata gida kai tsaye ba ya ce: "Sarah! Ina Mijinki ya ɓoye Abduh Dhahab da Ɗan shi? Asibiti ya kai shi, ko su na cikin Gidannan? kifaɗamin gaskiya ko na wulaƙantaki" ya ƙarasa faɗa ya na ƙare mata kallo ta hasken farin watan daya haske gidan. Da sunan Ubangijin da take ambata ta yi jarumtar furta "Mallam ba ya gari, ya tafi Fansar Litattafai, Asibitin kuma sati ɗaya kenan ba a yi aiki a cikinsa ba" dariya su ka bushe da shi don ko a ranar sun ga mijinta. Ƙasan Gidan ya haska ya na kai dubansa dai-dai wajen da Jinin da ya ɗiɗisa har zuwa inda ya tsaya. Dai-dai inda Mallam ya ke ajjiye kekunan hawarsa har guda biyu jinin ya tsaya. Dariyar ƙeta ya sa kafin ya ce. "ashe Mallam mai Asibiti da zai fita da dukka kekunansa ya fita Fansar Litattafai kenan? Ki faɗa min wanene ya tuƙa ɗaya keken?" Kai ta girgiza haɗe da yin duk addu'ar dayazo bakinta. "Wallahi kinji na rantse idan baki faɗamin gaskiya ba zan ƙona gidanan da ke da ƴaƴanki gaba ɗaya." kuka tasa ta na roƙonsa da magiya kala-kala. Ganin ta na ɓata mu su lokaci ya sa ya ce a ƙona Gidan tunda taurin kai ne da ita. Ta na jin haka ta ce Abduh Dhahab ya zo da Ɗan shi amma sun tafi Asibiti. Dasauri ya ce: "ya zo da kuɗi?" "Bansaniba amma dai yazo da buhu mai girma da abu a cik.." bai bari taƙarasa ba, su ka bar Gidan. Ko da sukaje Asibitin Mallam, ba bu Abduh Dhahab da Sulaim kuma ba bu ko sisi sai Mallam da su ka samu yana ƙoƙarin dawowa Gida. "A wani ɗakin ya ɓoye Abduh Dhahab da Ɗanshi da kuma dukiyar da ya ƙullo a buhu?" Suka tambayi Mallam. Shiru Mallam ya yi kamar kurma. Sunfi minti 15 su na ta tambayarsa kafin ya basu amsar Abduh Dhahab yana cikin Asibitin da dukiyarshi. "A wani sashe na Asibitin? kuma a wani ɗaki?" Su ka ƙara tambayarsa Tunda Asibitin ba laifi ya na da girma. Shiru ya yi yaƙi ba su amsa kuma ba bu inda ba su duba ba babu Abduh Dhahab kuma sun kasa gano shaidar ɗakin da zasu sameshi ga dai keken Mallam daya tuƙo a gefe jini duk ya ɓatashi. Kuma Mallam ya kafe Abduh Dhahab na cikin Asibitin da ɗanshi da dukiyarshi. Ganin kamar raina mu su hankali haɗe da son tona mu su asiri ya ke yi. Sai suka turashi cikin Asibitin su ka kulle. A can gidan Mallam Suna fita Matarsa ta tattara ƴaƴanta su ka nausa hanyar Yankinsu a cikin daren kamar yanda Mallam ya umarceta kafin ya zo ya samesu. Bayan sun tura Mallam cikin Asibitin sun kulle, wuta suka saka, sannan suka ƙara dawowa gidan Abduh Dhahab suka yiwa Matarsa kashedi mai zafin da ya kai ga guntule mata ƴan yatsu biyu, tare da yashe duk wasu dukiya da suka samu a ɗakinta na tarin kuɗin la'adar da Abduh yake biyanta idan ta tayasu aiki. ★washe gari labarin gobarar Asibitin Mallam ya karaɗe Yankin, Da farko ba'a fahimci gawar su waye a ciki ba, sai da Surikin Mallam ya biyo jin ba'asi bayan isar Matar Mallam Yankinsu anan ya tarar da mummunar labari, ya kuma tabbatarwa da Mutanen Yankin su Mallam ne suka ƙone, da iyakacin hujjar da ƴarsa ta bashi. Duk da a kwai waɗanda suka ɗan ji abinda ya faru a cikin daren, amma sukayi shiru su ka ƙi magana, kowa ya ja bakinsa ya tsuke, tunda matar Abduh Dhahab bata farfaɗo ba, tun cikin daren zuwa wayewar gari balle ta faɗi sunan waɗanna su ka aikata a ɗauki mataki a kansu, kamar yanda Sarki Hammam ya bayar da shela. Gawar Mutum huɗun da aka zaro sun ƙone ƙurumus bakyan gani don babu fuskar wanda aka gane balle a banbance. Ɗayyib ya na kwance lulluɓe cikin abin rufa sai kuka da ihu ya ke yi jikinsa ya na rawa, haɗe da sabbatun su fito masa da Abokinsa Abduh Dhahab, wallahi bai yarda Abduh Dhahab ya mutu ba, wanene ya kashemasa Abduh Dhahab Aminin ƙwarai? 0 09132403788 [7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: 🔥ZINARE🔥 SASAAL 03 A fadar Sarkin Hammam aka sallaci gawarwakin da Sarki Hammam da kansa ya jagoranta. Kafatanin Mazan Yankin ne sukayiwa gawarwakin rakiya izuwa makwancin su. Kafin dawowar su Dangin Mahaifin Mairam (matar Abduh Dhahab) sun zo sun ɗauketa saboda gudun abinda zai biyo baya, haka Malik maiyiwa Abduh Dhahab hidimar shara duk safiya shima ana dawowa da ga kai su Abduh makwanci aka nemesu aka rasa shi da Iyayensa. A wannan ranar kasuwar da Abduh Dhahab ya sha gwagwarmaya shekaru kafin kafuwarsa na siyar da Tukwane ma su Taken Tukwanen ZINARE don cigaban Yankinsa ya yi faɗuwar tasa da ba'a taɓa tunani ba. Domin duk wanda ya zo ya ji mutuwar Abduh Dhahab ba ya iya tsayawa ya ke juyawa inda ya fito. Dubban mutanen Yankin sun tafka asarar abincin siyarwa da su ka dafa da sauraran kayan amfanin da suka sarrafa don siyarwa baƙin da suke shigowa. Anya mutuwar Abduh Dhahab bazai kawowa yankin su Talauci mai ƙarfi da koma baya ba kuwa? tunda ta nan suke samun kuɗin shiga ta hanyar abubuwan da suke sarrafawa su siyarwa Baƙin da su ke shigowa, ga kuɗin hayar masauƙin da suke samu da ga wajen baƙin da suke zuwa daga nesa. Dukka wannan ya rushe kenan? Tambayar da Mutanen Yankin suke ta yiwa kansu kenan.. NAILA Ta fi minti Talatin a tsaye a harabar Gidan su Sulaim ta na jiran fitowarsa, bayan tasha kukan daya ɓata Kyakkyawar Fuskarta da hawaye da majina. Don ita bata yarda Sulaim ya mutu ba. Daƙyar Babanta ya janyeta shima na shi ran na suya. Da Surukin Mallam zai koma Yankinsu Sarki Hammam ya umarcesa ida anyi Ukun su Mallam ya kawo masa Sarah ya na son yi mata tambayoyi, tunda Matar Abduh bata hayyacinta. Da "to" Surukin Mallam ya amsa amma har cikin zuciyarsa bayajin Sarah ɗiyarsa zata ƙara taka Yankin.. Da yammacin ranar aka binne su Abduh Dhahab, sai gaba ɗaya mutanen Yankin suka koma zancen asarar da suka tafka, ba tare da sun ƙarabi takan abinda ya yi makasudin ajalin Abduh Dhahab da Ɗansa har ma da Mallam ba. Wannan lamari ya yi matuƙar sosa ran Dajjito Junaid. Junaid ɗaya daga cikin Dattawan Yankin ne, kuma na hannun daman Sarki Hammam, ba shi alaƙar Jini ko na dangantaka da su Abduh Dhahab. ★washe gari Dattijo Junaid tattaki ya yi har Yankin su Sarah Matar Mallam. Ya sameta a mawuyacin hali mai ban tausayi, iyayenta sun karramashi tare da bashi abin sha don jiƙa maƙoshi. Tambayar duniya Sarah taƙi faɗar waɗanda suka zo gidanta neman Mallam, ƙarshe da Dajjito Junaid ya matsa mata kuka ta fashe da shi raɗaɗin kisan gillar da akayiwa Mijinta na cigaba da sukarta. Ta yaya zata faɗa bayan tasan za su bibiyeta. Har Rana ta yi Dattijo Junaid bai bar Gidan su Sarah ba. A kan idonshi Iyayen Sarah da ita kanta da ƴaƴanta suka fito da kayayyakin su don yi balaguro tunda sun san dole a bibiyi ƴarsu gudun kar ta faɗi gaskiyar abinda ta sani. Hawaye Dajjito Junaid ya share ya na bin bayan su. Cikin taushin harshe da amon dake bayyana irin raɗaɗin dayake ji a ƙasar zuciyarsa ya ce; "Sarah tunda bazaki bani ƙarin haske akan abinda ya faru ba, ki taimaka ki faɗamin inda Mallam yake samun taimakon inganta babban Asibitin mu, da kuma Makarantun ƴaƴamu na roƙeƙi" ya ƙarasa faɗa yana haɗa fararen hannayensa waje ɗaya alamar roƙo. Tsayawa Sarah ta yi zuciyarta na karyewa tsananin tausayin Abduh Dhahab da Sulaim na bijiromata. Sai da ta tattaro dukka jarumtar daya bata damar shanye kukan dake neman cin ƙarfin maganganun da takeson faɗa sannan ta ce; "Abduh Dhahab shi ne wanda ya gina makarantu da Asibitin daya bawa Mallam amana bayan ya roƙi Mallam ya yi mishi alfarmar kar ya bari kowa ya sani har sai idan shi ya buƙaci hakan da kanshi. Ya ƙare rayuwarsa da Ɗansa wajen bauta muku da son ganin cigaban Yankinku, amma duk da haka sai da kukayi sanadiyar ajalinshi. Tir! da wannan Yanki na ku" ta ƙarasa faɗa tana fashewa da kuka haɗe da barin Dajjito Junaid tsaye da sakekken baki. Dattijo Junaid Tafiya yakeyi da iya ƙarfinsa amma sai yake ganin kamar baya sauri, burinsa ya isa Yankinsa ya ba su labarin da zai dawo da su hayyacinsu su binkico shaiɗanin dayayi sanadiyar rushewar Yankin su. Da Yammaci Dattijo Junaid ya iso Yankinsu da labarin alkhairin Abduh Dhahab, Ba bu wanda ya yarda da shi, sai ma cewa da suke yi; "Abduh Dhahab ɗin da yake mayen kuɗi ne, zai yarda ya bautawa Yankinsu da dukiya mai yawa irin wannan? Kawai ƙage da rashin son zaman lafiya Dajjito Junaid yake son kawowa Yankin su" ire-iren maganganun da sukai tayi kenan har da masu kwashewa Dattijo Junaid albarka. ★Duk da haka Dajjito Junaid bai gajiya ba washe gari ya ƙara ɗaukar harama ya na shela layi-layi. "Ya ku mutanen Yankin Tudu! Ina jiyemuku ranar nadamar da zakuyi nan gaba da kuma talauci mai raɗaɗi da azabar da zai iya riskarku matsawar kukayi butulci baku tsaya tsayin daka wajen ganin an binciko waɗanda suka kashe Abduh Dhahab da Iyalinsa ba, lallai sakayya mai raɗaɗi yana nan zuwa garemu, matsawar kuka yofintar da zance na. Haƙiƙa nan gaba kowa a cikinmu zai ɗanɗana kuɗarsa, Wannan wahalar nake jiyemana mutanen Yankina" Leƙosa sukeyi wa sun su na dariya tare da yin Allah wadai da kalamansa, su na cewa; "ai mu Abduh Dhahab ya cuta, tunda dama sihiri ya yi wa Kasuwar Zinaren da idan ya mutu Kasuwar da ya gina shima zai mutu baza mu moraba, tsabar mugunta da ya shiryamana har Tukwanensa ya kwashe kaf ya siyarwa da Turawa mu kuma ya barmu da tafka asara" har ya gama Shelarsa ya wuce Fadar Sarki Hammam babu wanda ya ƙullasa. Da Dajjito Junaid ya yi magana a fada Sarki Hammam, ansamu waɗanda hankalin su ya karkata kan anya labarin da Dattijo Junaid ya zo dashi ba gaskiya ba ne ba kuwa? Haka a ɓangaren Sarki Hammam ɗari bisa ɗari ya yarda da zancen Dajjito Junaid har ya bada tabbacin ƙara zurfafa binciken waɗanda suka aikata wannan mummunan aikin. Dama ya daɗe yana kokwanton waɗanda Mallam ya ce suke ɗaukar nauyin dukka ayyukan tun farkon buɗe Makarantun da Asibiti, da yanda ake biyan ma'aikatan jinya da malaman Makaranta albashi akan lokaci, da yanayin kulawar da ma'aikatan suke samu duk ba iri ɗaya bane da wanda suka samu gwamnati take ɗaukar nauyi. Ragamar binciken komai Sarki Hammam ya miƙa a hannun Dattijo Junaid. A wannan ranar da tsananin farin ciki Dajjito Junaid ya nufi Gida. bai runtsa ba har sai da ya fara kamo bakin zaren abinda yake zargi. A Yammacin wata Laraba ya shirya kaiwa Sarkin Hammam ziyara, don gabatar da shaidun da zai ƙara buɗe idon mutanen Yankin har su bashi goyon baya wanda ya yi dai-dai da cikar su Abduh Dhahab sati biyu a kaburburan su. Kafin ya buɗe gidanshi anrigasa buɗewa. ★washe gari, har rana ta fito Ba bu wanda yaji ɗuriyar Dajjito Junaid da Matarsa dama kuma Allah bai ba su haihuwa. Wannan dalilin ya sa aka ɓalla Gidan tunda ana da tabbacin su na ciki. Cikin jinin daya bushe aka samu Dattijo Junaid da wuƙa soke a gefen cikinsa, bakinsa ma jini duk a bushe ko da suka duba bakin anyanke mai harshe. Tsohuwar Matarshi kuwa tana Ɗaki a kulle tsoro da tashin hankali ya daɗe da sumar da ita. Mamaki da tsoron ne ya dirarwa mutanen Yankin Tudu, amma dayake yawancin su ma su ƙaranci tunani da kuma hangen nesa ne, sai suka fara surutun; "ai shi ya jawowa kanshi, tunda ya ce shi bazai kama bakinsa ba" Ba bu wani cikakken damuwa ko alhinin abinda ya faru da Dattijo Junaid a zuƙatan mafi akasarin mutanen Yankin, wannan ya sa suka cigaba da harkokin gabansu, tare da alƙawartawa kansu jan bakunansu su yi shiru tunda ba su shiryawa mutuwa ba, don babu wanda yaji ko da ihun naiman taimakon su Dattijo Junaid da Matarsa balle su sa ran idan sunyi ihu za su iya samun taimako. Cikin hikimar Ubangiji numfashin Dattijo Junaid ya dawo cikin tsananin azabar rayuwa ko mutuwa tunda Allah bai ƙaddara ajalinsa a hannun waɗanda suka zo kashesa ba, Itama iyalinshi ta farfaɗo banda kuka babu abinda take yi. Keɓantaccen wajen da babu mai shiga sai Sarki Hammam da mai Maganin da zai dinga duba lafiyarsa Sarki Hamman ya tanada a cikin Marasautar tare da kashe maganar bincike akan kisan su Abduh Dhahab. Ba bu wanda ya gamsu da maganar Sarki Hammam saboda sun san dole yayi bincike ta ƙarƙashin ƙasa. Don haka waɗanda suke da alhakin kisan suka shiga tararrabi tare da fara tunanin ƙirƙiro abinda zai kawar da hankalin mutanen Yankin da shi kanshi Sarki Hammam. NAILA; tun tana sa ran wata rana Sulaim zai dawo har ta gaji da cire rai, sai dai Gidan su ya koma dandali taruwa Yara abokannan wasanta tana ba su tahirin rayuwarta da Sulaim, har da tatsuniyoyi ta ƙirƙira na labarinta da Sulaim. Ba ta fita wasa kullum tana Gida kamar ba Naila mai son wasa da neman tsokana ba. A cikin watanni biyu da mutuwarsu Abduh Dhahab wani gagarumin Talauci yafara kunnowa Yankin kai. Rana ɗaya suka wayi gari babu Malaman Makaruntun su, Asibitin Mallam da Sarki Hammam yasa aka gyara dukka ma'aikatan jinyar sun gudu. A cikin yini biyu Mutane biyar suka rasa ransu saboda rashin ma'aikatan jinya. Ba bu wani Ɗan Yankin Tudu da hankalinsa bai tashi ba, ciki har da Ɗayyib da bai jima da samun sauƙi ba. A rana ta uku Mahaifin Naila da ya tashi da tsananin ciwon ciki shima ya rasa ransa zuwa yammaci duk da maganin gargajiyan da akayita ɗirkamai don sun je Asibitin Gwamnati ba ma'aikata. Asibitin Mallam dama tuni aka rufeshi tunda dukka ma'aikatan sun gudu. Rasuwar Mahmoud Maihaifin Naila wani babban gibi ne mai girman gasken da su Naila ba su da abin maye gurbinsa har abada. A cikin watannin da suka biyo baya wani irin Talauci ya yi wa Yankin mamaya mai ƙarfin gaske, ga shi babu wadataccen ilimi ba bu Ma'aikatan lafiya masu sanin makamar aiki. Zuwa Lokacin Dattijo Junaid ya samu lafiya amma babu damar yin magana. Suna cikin wannan yanayin Abdullah ya bayyana a matsayin ƙwararren Likitan da Gmannati ta turo. Sarki Hammam ya yi Farin cikin bayyanar Abdallah a matsayin Likitan da gwamnati na musamman, Saboda sabon abune a garesu, domin shi da al'ummar Yankinsa rayuwa suke yi tamkar ba ƴan ƙasa ba, babu gwamnati da hukuma sam a lamuransu, sai ɗan abinda ba'a rasa ba, shiyasa kowa yake yin abinda ya ga dama Bayan kwana biyu Cikin iko Allah marasa lafiya suka fara samun kulawa ta musamman. Mutanen Yankin sun saki jiki da Abdullah tare da wani irin so da sukeyimai saboda sauƙin kansa da iya mu'amalarsa. Wannan dalilin yasa ya buɗe aji koyawa Matasan da suka kai shekaru 18 mata da Maza dabarun kula da mara lafiya da karɓar haihuwa cikin Hikima. Da kayan aikin dayazo yake koyawa mu su. Kafin rufuwar wata biyu wasun su har sun ƙware. A hankali labarin alkhairin Abdullah ya fita ko ina na Yankin sai ya zamana har a maƙotan Yankin su ana zuwa ɗaukar Matasa wala Namiji ko Mace don duba majinyaci ko karɓar haihuwa. Cikin lokaci ƙanƙani talauci Yankin ya fara raguwa walwalarsu ta fara dawowa. A cikin watanni shida Abdullah ya yaye Ɗalibansa haɗe da ƙara ɗiban wa su. Sarki Hammam da Dattijo Junaid baƙaramin alfahari sukeyi da Abdullah ba, girmamashin da suke yi ma na daban ne. A na cikin haka aka tsinci ƙaramar Yarinya anyi mata fyaɗe mara kyan gani a bayan Ofishin Abdullah. Duka na rashin imani da manta halacci Mutanen Yankin sukayiwa Abdullah. kafin sanarwar ya isa ga fadar Sarki Hamman har sun sumar da shi. "Wani irin ƙwaƙwalwa ne a cikin kan Mutanen Yankin Tudu, kuma wacce irin zuciya gare su mai tsanin butulci da manta alkhairi? Ta ya ya Abdullah zai iya yiwa Yarinya ƙarama fyaɗe na rashin imani irin wannan? shin ina hankalin su yake? Maiyasa ake amfani da toshewar basirar su wajen sa su su dakushe cigaban Yankin su da kansu batare da sun sani ba?" Dattajo Junaid ya tambayi kanshi zuciyarsa na Suya. Daƙyar Fadawan Sarki Hammam suka fatattaki Mutanen Yankin da bulalai. Babu wani ƙwararren Likita a ƙasa da zai iya kula da Abdullah, sai masu maganin gargajiya aka nemo. ★washe gari duk da haka Mutanen Yankin basu haƙura ba gangami sukayi har Asibitin suna faɗin abi mu su haƙƙinsu, a cikin su har da waɗanda Abdullah ya koyar kuma suke samun alheri. A cewar su "dama sun san dole akwai wanda ya turoshi don cin mutuncin Yankin su" Daƙyar fadawan Sarki Hammam suka ƙara fatattakarsu da bulalai. ★washe gari da sassafe aka tashi da labarin guduwar Abdullah daga Asibiti bayan ya farfaɗo, fadawan Sarki Hammam ne suka bada labarin wani ne yazo da sunan dubanshi shikuma Abdullah ya yi mishi rakiya a daddafe zuwa motar daya zo dashi gabannin Asubahi daganan kuma basu ƙarajin ɗuriyarsa ba. Labarin sam bai yiwa Wa su marasa goyon bayan lamarin daɗi ba musamman Sarki Hammam da mutanensa. Dattijo Junaid kuwa har da kukansa. Labarin abinda mutanen Yankin sukayiwa Abdullah da labarin guduwarsa har wajen Yankin wannan sai ya sa musu baƙin jini tare da kafa tsoron su da ƙyaƙyamin kulla alaƙa da su a zuƙantan maƙotan Yankunan su. A wannan yanayin Mahaifan Maman Naila suka zo ɗaukarta tunda ta gama Takaba tuntuni. ko da aka buƙaci su tafi da Naila tunda Yarinyarce, ƙin amincewa sukayi bayan baƙaƙen maganganun da suka gasawa Mahaifiyar Mahmud kakar Naila tare da yin Allah wadai su tafi Yankinsu da jinin mutanen Yankin Tudu. Dole Naila ta koma wajen Kakarta ta wajen Uba da zama bayan kukan da ta sha har da zazzaɓi. Cikin watannin da suka biyo baya, Mutanen Yankin suka ƙara komawa Talaucin da yafi na baya muni da raɗaɗi. Ga ƙyama da suke fuskanta daga dukka ƙabilun dake kewaye da su, ko Aure ɗan Yankin Tudu yaje nema ba'a ba shi. Rana ɗaya dukka matasan Yankin suka yi zuciya suka koma Gona har da Ƴaƴa mata saboda raɗaɗin Talauci da rashin abin yi. Don ko aure Mazan Yankin suka fita nema a mokatan Yankin su ba'a ba su, balle su yarda Ɗan su ya auro mu su Ƴar Yankin Tudu. Wannan dalilin yasa suka fara auren Junansu cikin tsananin Taulauci. Bayan amfanin Gona ya yi, suka fara fita dashi kasuwanni Yanki-Yanki. Abin mamaki duk Yankin da suka kai ba'a siya sai su ce "Allah Ya raba su da cin kayan amfanin gonar mutanen Yankin Tudu" kamar waɗanda sukayi bar ruwa da guba haka Kayansu ya koma a idon Mutane. Ko wani bare daga wani ɓangaren da bai sansu ba ya yi niyyar siya sai aja kunnensa da kar ya kuskura idan ba haka ba kuwa, tamkar ya kirawa kansa mutuwa ne. Mutanen Yankin Tudu suna ji suna gani suka ƙara komawa Talaucin dayafi na da raɗaɗi da azaba Suna cikin wannan yanayin Salman ya shigo Yankin a matsayin mai koyar da sana'o'in da gwamnati ta turo...✍🏻 09132403788 [7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: 🔥ZINARE🔥 SASAAL 04 Bayyanar Salman a Fadar Sarki Hammam a matsayin mai koyar da Sana'o'i ya yi matuƙar faranta ran Mutanen Yankin kamar dai lokacin Abdallah, saboda ya zo akan gaɓar da suke tsananin buƙatar ire-irensa. Ɗayyib ne ya kawo shawarar mai zai hana a kai Salman Gidan marigayi Abduh Dhahab da tun bayan Mutuwarsa yake a garƙame a matsayin Masauki?. Ba bu jaa kowa ya yi na'am da shawarar Ɗayyib tunda Salman ya ce shi ma Maƙeri ne. Bayi Sarki Hammam ya bawa mukulli suka gyara gidan. Ɗayyib da kansa yayiwa Salman rakiya har gidan Abduh. Bayan sati ɗaya. Da tsananin Farin ciki da wani ƙauna mara iyaka Ɗayyib ya nufi Salman bayan ya gama kallon irin Tukwanen da Salman ƙera. Rungumesa ya yi ya sumbaci gefe da gefen kunchinsa, sannan ya ce; "A ina ka koyi ƙera irin Tukwanen da Aminina Abduh Dhahab yake ƙerawa? Tun bayan mutuwar Abduh muka shiga wani yanayin na ƙangin rayuwa, saboda mutuwar Kasuwar Tukwanen Zinaren da yasha wahala kafin kafuwarsa, ba bu wanda ya yi hikimar koya a cikin mu lokacin da ya ke raye, daga shi sai Ɗansa Sulaim ne kawai suka iya ƙerawa. Sai ga shi bayan munfidda rai da ƙarasamun rayuwa mai daɗi Allah Ya Kawo mana kai. Alhamdulillah!" Ɗayyib yaƙara faɗa ƙwalla kwance a ƙasan fararen manyan Idanuwansa. Salman bai ce masa komai ba sai murmushinsa daya faɗaɗa yana komawa wajen Tukwanen daya ƙera. Har Ɗayyib ya gama santin Tukwanen ya bar gidan Salman bai ce komai Da Ɗayyib ya kaiwa Sarki Hammam labarin Tukwanen da Salman ya ƙera, Umarni Sarki Hammam ya bawa Fadawansa su bi layi-layi suyi shelar Bayyanar Salman a matsayin mai koyar da Tukwanen Zinare sak irinna Marigayi Abduh Dhahab. A yammacin ranar suka cika umarninsa, Nan da nan farin ciki ya mamaye zuƙatan Mutanen Yankin, maimakon su godewa Allah su ƙara sanin amfanin Marigayi Abduh Dhahab a Yankinsu sai suka hau Sukarsa da ce wa; "Allah Ya sa shima wannan ba irin Abduh Dhahab ba ne mai mugun zuciyar da zai yi sihirin da Kasuwar Tukwanen Zinaren zai ƙara rushewa idan bayanan" da ire-iren kalaman sukai ta sukar Marigayi Abduh Dhahab kenan. Ba su tsagaitaba har sai da labari ya jewa Sarki Hammam. Da kakkausar Murya ya yi gargaɗin duk wanda yaƙara sukar Abduh Dhahab abisa son zuciyarsa to zai fuskanci hukunci mai tsanani. Ba bu kunya mutanen Yankin suka cika gidan Abduh Dhahab, Yara da Manya, Maza da Mata Don koyan ƙera Tukwane. ƊAYYIB Da wani irin takaici yake kallon ɗansa Sufyan, ba don kalamansa suna yimasa daɗi ba ya cigaba da saurararsa. "Baaba tayaya zan koyi ƙera Tukwane da wannan kyan nawa? Baabah ba ƙera Tukwane ne ya dace da Matashi kyakkyawa irina ba. Ni burina shine naje Babban Birni nayi Karatu mai zurfin da zan kawowa Yankina cigaba, amma ba koyan ƙera Tukwane ba gaskiya" Yaƙarasa faɗa yana yin ƙasa da kansa da suma baƙi mai laushi ke kwance luf a kai. Tabbas! Ɗanshi Sufyan kyakkyawane amma idan aka haɗa kyansa da na Sulaim daya ƙare rayuwarsa wajen bautar ƙera Tukwane to tabbas Sufyan ɗin ba komai bane. Da taushin Muryar da yake burin Sufyan ɗin ya fuskancesa har yagane abinda yake yimasa kwaɗayi ya ce; "Sufyan Idan har Sulaim da Allah Ya yiwa baiwar kyau ninkin baninkin naka zai ƙare rayuwarsa wajen ƙera Tukwane bisa umarnin Mahaifinsa, to banga dalilin da zai hanaka bin nawa umarnin ba. Sana'a baya hana karatu sai dai ma ya taimaka wajen ragewa Iyayenka ɗawainiya kuma kai kanka sai ka fi jindaɗin kayiwa kanka abu batare da ka jira an ɓata maka lokaci ba. Kaje kayi shawara da Mahaifiyarka amma kasani idan har ka saɓawa umarnina to babu ko sisina a harkar neman Iliminka." Ɗayyib ya na gama faɗa ya miƙe ya bar wajen. Sufyan ba a iya Cikin zuciyarsa yake jin raɗaɗi kalaman Mahaifinsa ba har a kan fuskarsa. Yaushe labarin kyan Sulaim zai gushe a zuƙantan mutanen Yankin. Ya na son ace yana da kyau duk da yayi imanin shi ɗin kyakkyawane, don matan Yankinsu da na maƙotan Yankinsu har so suke yi yayi musu magana. Amma duk wannan yabon kyan nasa da sukeyi da zarar hirar Sulaim ya ratso sai su hau ƙodashi da faɗin da Sulaim ya girma a raye to da babu wani Matashin da zai kamosa a kyau kaf faɗin Yanki, a wasu lokutan ma sai su ce har da maƙotan Yankunansu, duk ranar da irin haka ta ratso a gabansa ko labari yazo kunnensa yini yakeyi yana kallon ƙaton madubin Gidansu. Hindu Mahaifiyarsa mai taya ɓera ɓari kullum ƙara zugasa take yi da cewa; "ba wai su na zuzuta kyan Sulaim ba ne don dagaske ya na kyan ba, sai don Tukwanen Zinaren da Mahaifinsa ya ƙirƙirowa Yankin, idan shima yaje Babban Birni Ya yi karatu mai zurfin da kaf faɗin Yankin ba bu mai kwatankwacinsa to ba shakka shima zai zama abin kambabawa, kar ya kuskura ya yarda da batun Sana'ar da Mahaifinsa ya jima yana burin ya yi, idan ba haka ba Sulaim shi zai cigaba da zama Saurayi mafi kyau a Yankin duk da baya raye, idan ma ya lura sun mayar da labarin kyan Sulaim kamar wani Tarihin da suke kambawawa. musamman ga waɗanda ba su sanshi ba" har alƙawarin auren gata tayimai da wacce zata bauta mai kamar Sarki idan har ya cikamata burinta na zuwa Babban Birni karatu. Waɗanan huɗubobin da su Sufyan yake kwana kuma yake tashi. A ɓangaren Mutanen Yankin ma su koyan ƙera Tukwane a wajen Salman sosai suka nuna jajircewarsu da farko, amma da tafiya tai tafiya sai suka fara nuna gajiyawarsu har sai da Salman ya zaburar da su da kalaman asalin wanda ya ƙirƙiri Tukwanen; "Ba a lokacin da muka shuka iri, zamu girbi amfaninsa ba dole sai munjira kuma munyi haƙuri tare da yin aiki tuƙuru" waɗannan kalamai na Salman baƙaramin tsoratar da Mutanen Yankin ya yi ba, musamman ga waɗanda sukayiwa Abduh Dhahab farin sani. Tsoron kar su wayi gari wata rana su ga babu Salman don sun fi alaƙanta shi da aljali saboda kalamansa masu kamaceceniya da Abduh Dhahab, sai suka ƙara zage damtse. Labarin kamaceceniyar kalaman Salman da Abduh Dhahab dayake yawo a gari har kunnen Naila da Kakarta. Naila data kasa samun sukuni a sace ta tafi Gidan ba tare da sanin Kakarta ba. Sai da ta yi zuwa har biyu amma ta kasa shiga sai dai ta laɓe tana Kallonsa. A ranar zuwanta na uku Salman ya kamata. Har cikin gidan ya riƙo hannunta ya shigo da ita. "Maiyasa kullum kike zuwa ki maƙale kina kallona, mai kike nema?" Salman ya tambayeta yana kallon cikin idonta. Murya na rawa Naila ta ce "inaso nasan labarinka, inaji a jikina kamar Kanada alaƙa da su Sulaim, shin dagaske Sulaim yaƙone bazai ƙara dawowa ba?" Kamar wanda ya ke son haddace halittun fuskarta haka Salman yake kallonta kafin ya ce; " Ki je nan da Sati biyu ki dawo zan baki labari" ya ƙarasa faɗa ya na turata waje haɗe da kullo ƙofar Gidan. Daga wannan rana Naila ta fara lissafin kwanakin da Salman ya ɗebarmata ba tare da sanin Kakarta ba. A ɓangaren Mahaifiyar Naila tun bayan komawarta Yankinsu, zumuncin da dama can akwai shi tsakaninta da Mairam Matar Abduh Dhahab ya ƙara ƙarfi kullum ita take kula da Mairam a gidan take wuni sai dare take dawowa gida. Mairam tana samun sauƙi amma kullum a cikin kuka take ba magana. Ranar da ta buɗi baki ta tambayi Ruwa, gidan ruɗewa sukayi da farin ciki ba iya su kaɗai ba har mutanen Yankin da labari ya je wa. Murnar fara maganar Mairam kaɗan-kaɗan yasa Mahaifiyar Naila yanke shawarar kwana a gidan, acewarta " yau kwana zamu yi muna hira" ta ƙarasa faɗa tana dariya. Babu zato babu tsammani A daren ranar aka kawo mummunar harin da ya faɗa kan Mahaifiyar Naila. ★washe gari da Sassafe Jama'ar Yankin suka kewaye gidan. kuka mai raɗaɗi da ciwon gaske Kakannin Naila suka ƙanƙanme juna su na yi, lokacin da sukayi ido biyu da gawar ƴarsu. Ga shi Mairam da Mahaifanta sun gudu, tun Asuba.. Bayan an kimtsa gawar Mahaifiyar Naila kafin a kaita, Mahaifinta shi da Mutanen Yankinsa sukai gangami har Fadar Sarki Hammam, don suna kyautata zaton fara maganar Mairam ne yasa suka zo kasheta don karta faɗi abinda ta sani tsautsayi ya faɗa kan ta su ƴar. Bayan sun samu shiga Daular Sarki Hammam maganganun ma su nauyi a harshe da raɗaɗi a zuciya Kakan Naila da mutanen Yankinsa suka fara zazzagewa Sarki Hammam da Muƙarrabansa. Zafin kalamansu dayake nuna cin fuska ƙarara ga Sarki Hammam yasa Fadawansa nufarsu da manyan bulalai. Sarki Hammam dakatar da su ya yi, sannan ya yi wa Kakan Naila alƙawarin yin adalci matsawar ya bincika ya gano dagaske da hannun Mutanen Yankinsa akan kisan gillar da akayiwa Ƴarsu to zai hukuntasu dai-dai da abinda suka aikata. Da wannan yarjejeniyar Kakan Naila da mutanensa suka bar Yankin, ko kallon Naila dake kuka kamar ranta zai fita basu yi ba. Su na tafiya Naila da Kakarta suka shirya suka nufi Yankin. Abun takaici bayan isarsu ko wajen zama ba'a basu ba, a cikin bainar jama'a, Kakanninta suka ce sun yafe ta, babu su babu ita, kuma karsu ƙara ganin ƙafarta a Yankinsu. Naila tana kuka suka dawo Yankin Tudu. A yammacin ranar sai da Sarkin Yankinsu Kakannin Naila na wajen Uwa, yaje har Yankin Tudu duk dai akan kisan gillar Mahaifiyar Naila, alƙawarin da Sarki Hammam ya yiwa Kakan Naila shi yaƙara yiwa Sarkin su. Bayan Sarkin su ya dawo ya tattauna da Kakan Naila. A take Kakan Naila ya yafewa Iyayen Mairam tunda tafiyar tasu shine nutsuwar su da na Mutanen Yankin gaba ɗaya. Naila bayan sun koma Gida kafin dare ya yi zazzaɓi mai zafin gaske ya rufe ta har bata gani da kyau. A haka tasha jinyar da tayi sati Uku a kwance. Bayan ta wartsake ta tuna alƙawarinta da Salman sai dai babu damar zuwa saboda shirye-shirye bikin sake buɗe Kasuwar Tukwanen ZINARE, da za'ayi washe gari. A ɓangaren Salman tuni ya manta da batunsa da Naila ya cigaba da abinda ya kawosa. A daren washe garin da za'a buɗe Kasuwar Tukwanen Zinare, Sarki Hammam ya gayyacesa cin abinci.. Salman ya samu Tarba mai kyau daga Sarki Hammam, bayan sun kammala cin abinci, Sarki Hammam ya buƙaci tattaunawar sirri da shi game da shugabancin kasuwar Tukwanen Zinare. Sarki Hammam da kansa ya faɗi sunan wanda yakeso ya zama Shugaban Kasuwar da kuma Mataimakinsa. Salman bai musa ba, shi dama aikinsa koyar da Tukwane kuma ya yi ya gama. Sai dare sosai ya dawo Gida. ★washe gari kowa na Yankin bakinsa a washe, saboda dawowar Kasuwar Tukwanen Zinare babban nasara ne gare su baki ɗaya. Bayan anci ansha Salman ya fara jawabi; Bayan ya yi godiya ga Allah ya ɗora da jawabin godiya da kuma muhimmancin sana'ar da suka koya. Can murnar kowa ya tsaya lokacin da Salman yake ƙoƙarin sanar da Shugaban Kasuwar Tukwanen ZINARE. Kowa burinsa ace shine ko wani nasa ne. A bisa tattaunawar da Salman ya yi da Sarki Hammam bayan sun gama cin liyafar daya gayyacesa a daren jiya, ya sanar da ƊAYYIB a matsayin shugaba DATTIJO JUNAID kuma mataimakinsa. Hayaniya ne ya ɓarke wasu suna ganin Dittijo Junaid da baya iya magana bai cancanci ya zama Mataimakin Ɗayyib ba, wa su kuma daga Ɗayyib har Dattijo Junaid ɗin duk basa so. A haka taro ya watse wasun su rai a ƙuntace da alwashi kala-kala. Salman tare da Dattijo Junaid da Ɗayyib, gidan Abduh Dhahab dayake a matsayin Masauƙin suka wuce don yin bankwana saboda washe gari zai koma ƙasar su. Sun shafe awanni suna tattaunawa kafin dukkan su su miƙe suna ƙarayin musabaha. Dai-dai lokacin da suke yunƙurin fitowa sukaji ana kwaɗa sallama haɗe da ɗan bubbuga Gidan. Tare suka fito Salman ya buɗe ƙofa, kafin ya ankara aka fara sararsa ta ko ina... Kamar dai Shekarun baya lokacin su Abduh babu wanda ya leƙo, duk da anajin kururuwarsu✍🏻 09132403788 [7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: 🔥 ZINARE 🔥 SASAAL 05 ★washe gari da dukuku Maƙotan da suka ji kururuwarsu suka kai koken sun ji ihu a gidan Marigayi Abduh Dhahab jiya da daddare. Sarki Hammam a kiɗime ya miƙe shi da Muƙarrabansa suka nufi gidan Abduh. Kafin gari ya ƙarasa haske labari ya karaɗe ko ina. Kafatanin Mutanen Yankin Tudu ne suka yiwa Gidan Marigayi Abduh Dhahab zobe, kowannen su zuciyarsa cike da tsoro da wani fargaba mai girma gaske. Yunƙurin faɗar gaskiya a Yankinsu ko kawo wani cigaba ya zama babban musibar da Mutum zai iya rasa ransa a kai. A cikin Gidan Marigayi Abduh Dhahab Gawar Salman ne a yashe, ya yi kacha-kacha cikin jini, sai Dattijo Junaid da shima idonsa ɗaya yake a tsiyaye bayan raunuka marasa kyan ganin dayake jikinsa. Haka Ɗayyib shima wuƙa ne soke a gefen cikinsa sai raunukan da ba'a rasa ba. Sarki Hammam kansa ya ɗaga sama, sai da ya tabbatar ya shanye ƙwallar da ya yiwa ganinsa yana sannan ya ɗurkusa a gaban Gawar Salman. Baƙin cikin da yake ji bai tsaya a iya cikin zuciyarsa ba har saman fuskarsa, yana son Salman sama da son da ya yi wa Abduh, saboda ya taimaki Mutanensa a lokacin da suke da tsananin bukata, amma wannan baisa sun rangwantamai ba har sai da suka kaishi ƙasa kamar yanda su ka kai Abduh. Fari ƙal ɗin hannunsa da ya ɗan fara yamushewar tsufa yasa ya shafi fuskar Salman, kafin ya miƙe don a samu damar fitar da su daga Gidan. Fito da Salman a luluɓe har kaa, saɓanin ragowar yasa zuciyar kowa ƙara karyewa. Banda koke-koken muryoyi daban-daban ba bu abin yake tashi a ƙofar Gidan. To ko dai Tukwanen Zinaren ne ba'a so a Yankinsu tunda shine sana'ar da yafi kowawa Yankinsu kuɗin shiga? Wanene yake musu wannan Ta'addacin a Yanki? Daga Abduh Dhahab har Salman dukkan su maƙera ne, ma su kamaceceniya a ɗabi'u har ma da wasu maganganunsu. kenan anfiso su cigaba da rayuwa cikin azaba da ƙangin Talauci? Tambayar da Mutanen Yankin Tudu suke ta yiwa junansu kenan. Kamar shekarun baya da suka shuɗe, Daular Sarki Hammam aka wuce da Gawar Salman anan aka Sallacesa, bayan an miƙa su Dattijo Junaid da Ɗayyib Asibitin da babu likitocin azo a gani. Fargaba mai gusar da nutsuwa ne ya dabaibaye zuciya Sarki Hammam, dalilin haka yasa Jininsa ya hau dole aka buƙaci Likita daga Babbar Birnin Abyad don kula da shi da su Ɗayyib. Kafatanin Mazan Yankin Yaransu da Manyansu ne suka tafi kai Salman makwancinsa cikin su har da Manya masu faɗa aji a fadar Sarki Hammam. Daf da zasu shiga Maƙabarta aka sani harbin bindigar da yasa mutane dayawa darewa . Ma su ɗauke da Gawar Salman ma ajjiyesa su ka yi sai dai su ba su gudu ba, su na dai tsaitsaye. Ƙarar Harbin da'asaki sau biyu a jere ne yasa suma suka tarwatse aka bar Iya Gawar Salman. Mota mai tudu baƙi mai tsananin sheƙin dake bayyana girman dukiyar da'a zuba kafin mallakarsane ya yi parking a gefen Gawar Salman. Maza majiya ƙarfine suka fara fitowa ɗaya bayan ɗaya har su uku a jere kafin fitowar na huɗunsu. Fitowar na huɗunsu ne yasa Bashar kawun Ɗayyib kuma mai faɗa aji a Masauratar Yankin Tudu da ke laɓe a ɓoyarsa shi kaɗai kuma ya sawa zuciyarsa dole sai ya ga duk abinda zai faru zare dukka girman fararen manyan idanuwansa na Usul ɗin Mutanen Yankin Tudu. Fitsari mai ɗumin gaske na biyo jikinsa, a take ya ji idanunsa na ƙyaƙyayin azaba. Amma duk da haka taurin zuciya, da kafawa duk abinda yasa a gaba ƙahon zuƙa sai yaga bayansa yasa ya ƙi kulle idanuwansa kamar yadda ragowar su ka yi a maɓoyarsu. Ba bu rahama a fuskar na huɗunsu da yafi su girma da tsaho, hannu ya sa ya ɗauke Salman a makara, yanayin yanda ya ɗagashi na bayyana rauninsa. dasauri ragowar ukun suka buɗemasa bayan mota ya shimfiɗesa. Harbi suka ƙara saki amma duk da haka fararen idanuwan Bashar da suka koma jajaye na tsaye ƙyam a kansu. Yunƙurin shigar su Mota yasa ya ɗan lumshe idanuwansa na seconni ko zai samu sassaucin zugin azabar da idon yake mai. Ɓude idanuwan da Bashar zai yi ya tsinci Mutum biyu a gabansa, dama ba bu wani tazara a tsakaninsu. Ya kasa ihu saboda duniyar fargabar daya tsinci kansa a ciki. Kamar Kayan wanki haka suka ɗebesa har Gaban mutumin da Kallonsa daga nesa kaɗai ya sa shi sakin fitsari. Ƙasa Bashar ya yi da kanshi jikin da dama can lallaɓawa yake yi saboda yawan shekaru ya fara karkarwa. Ɗago shi ya yi suna kallon tsakiyar idanuwan juna, idon Bashar kamar an tsiyaya jini tsabar jan da sukayi. Ƙasa Bashar yaƙarayi da kanshi saboda gudawan daya tahowa mai, ba ya kuma burin ya ƙara kallon ko da fuskarshi ne balle cikin idanuwansa saboda tsoro. Bashar bai gama saƙe-saƙen da yake yi ba yaji ya ƙara ɗago Kanshi. Da ƙarfi ragowar suka buɗemai baki. Gurnanin azabar gaske Bashar ya saki lokacin da na huɗunsu ya ciremai harshe kwatankwacin yadda aka yanke na Dattijo Junaid. Watsar da shi su kayi suka faɗa Mota kamar iska haka suka bar wajen da Yankin Tudu gaba ɗaya. Gurnanin azabar da Bashar yake yi babu wanda bai jiyosa ba a maɓoyarsa ba, amma tsoro ya hana kowa fitowa duk da Matsayin da Bashar ya ke da shi a Daular Masarautarsu. A ɓangaren Sarki Hammam duk bai san wainar da'ake toyawa ba saboda barcin daya ɗaukeshi, suma waɗanda suka rage a Masarautar laƙwas su kayi kamar basusan abinda yake faruwa ba, tunda wanda zai tilasta mu su fita kai agajin bai san ma anayi ba. Sai da kowa ya yi hour biyu da ɗoriya a maɓoyarsa sannan duk su ka firfito, zuwa lokacin tuni Bashar ya yi suman azaba. Ko takan inda harshen da suka yanke yake basu bi ba suka saɓashi a guje sai Asibiti. Daga Asibiti kowa ya silale ya yi Gida haɗe da kulle ko ina. Har aka kwana aka wuni Yankin Tudu tsit kamar babu kowa. A ɓangaren Naila tayi kukan mutuwar Salman, har sai da ya saukar mata da ciwon kai mai nauyin gaske, gashi babu damar fita kaita Asibiti saboda tsoro. Haka Kakarta tayi ta yimata jiƙe-jiƙe har zuwa washe garin da ta ji ɗan dama-dama. Da wani kallo ta kalli Kakarta murya na rawa ta ce; "Maiyasa ake kashe kowa haka, shin su Abduh da aka kashe basu da dangine? su waye danginsa maiyasa ba su ɗauki mataki ba? da sun ɗauki mataki da yanzu ba akashe Salman ba, Kaka su waye dangin Abduh Dhahab? maiyasa suka wofintar da al'amuransa a haka?" Kaka murmushi ta yi tana shafa kan Naila ta ce; "Ki bari ki ƙarasa warwarewa In Sha Allahu zan baki labari" SARKI HAMMAM ★washe gari da Sarki Hammam ya farfaɗo ya samu labarin abin ya faru. A gaggauce ya yace a shirya mishi zuwa ganin Bashar. Lokacin da ya isa Asibiti da ake yiwa su Ɗayyib, Dattijo Junaid da Bashar maganin gargajiya kafin ya shiga Ɗakin da Bashar yake saƙon Dattijo Junaid ya riskeshi na; " idan ya shigo yane raye, a faɗamasa yazo gareshi yana da saƙo." Sarki Hammam ya na jin saƙon Dattijo Junaid ya fasa shiga Ɗakin Bashar ya wuce na Dattijo Junaid bayan ya dakatar da kowa daga bin bayansa. Kallon yadda Dattijo Junaid ya koma kaɗai wani abin fargaba ne. Bayan ya yi mai ya ya jiki ya naimi waje ya zauna. Alama da salon maganar kuramen da Dattijo Junaid ya saba yakeyiwa Sarki Hammam bayani, cikin ikon Allah, Ubangiji ya bawa Dattijo Junaid ikon yin bayani kamar da bakinsa yake magana tsabar yanda Sarki Hammam ya ke fahimtarsa. Bayan ya gama bayani Hannunsa Sarki Hammam ya kamo. Junaid Amininsa ne tun suna Yara amma banbancin Gidan da suka fito ne ya nisanta Amintakarsu dole, Bayan ya zama Sarki Junaid ya dawo ƙarƙashinshi Bashar ya maye gurbinsa na Amini. Sarki Hammam Ya na cikin wannan tunanin Allah Ya amshi ran Dattijo Junaid. Kuka ya zauna yi kamar ƙaramin Yaro. Ya yarda Bawa baya mutuwa har sai idan lokacin da Ubangiji ya ɗebarmasa sun cika, banda haka tayaya Dattijo Junaid zai yi ƙarfin zuciyar rayuwa bayan yana kallon ajalinsa a kusa dashi ko da yaushe kuma ya ja bakinsa ya yi shiru?. Mutuwar Dattijo Junaid da hasken da Sarki Hammam ya samu dangane da badaƙalar dake addabar Yankinsa a ɓoye bai tsaya a iya hawan jininsa ba har jinya ya kwanta, don dole aka fitar dashi Babban Birni Abyad. Mutuwar Dattijo Junaid da abinda ya samu Bashar ya kasa hankalin mutanen Yankin kashi-kashi. Wa su sun yarda waɗanda suka zo a Baƙin Mota sune suke yiwa Yankinsu aika-aika, wa su kuma suna ganin sam ba haka bane idan hakane aiba Bashar zasuyiwa haka ba kawai dai Ƴan uwan Salman ne suka zo ɗaukar fansa, to amma ta ya ya akayi suka san mutuwarsa? tunda babu komai na Salman da ba'a bincika ba amma an kasa gano daga inda yake. Daga wannan lokacin baƙin jininsu sai ya ragu a zuƙatan Maƙotan Yankinsu saboda da yawa sunfi yarda masu Baƙin Mota ne suke yiwa Yankin ta'asa tuntuni, ba wai Mutanen cikin Yankinba Bayan wani lokaci, Sarki Hammam ya dawo daga Babban Birni Abyad, Bashar shima ya samu sauƙi. A Fadar Sarki Hammam aka gayyato ƙwararrun ma su zane don su zana wanda Bashar ya haukace yana ta kwatance har da kaisu gidan Abduh Dhahab, duk wannan kwatancen na shi ba bu wanda ya ɗauki hasken komai Sai Sarki Hammam dashi ƙadai yasan wanda Bashar yake nufi daga bayanin da Marigayi Dattijo Junaid ya yi masa. Shara da tsaho yake ta kwatantawa, banda wannan ya kasa siffanta komai. Sai da ƙyar ya fara zayyano siffar wanda sam babu ko mai kamanninsa a Yankin. Dole yana ji yana gani masu zane sukayi tafiyarsu. Kwanaki bayannan Sarki Hammam yasa atara mishi mutanen Yankin don zaɓar sabon Shugaban Kasuwar Tukwanen ZINARE da Mataimakinsa tun da har lokacin Ɗayyib bai samu sauƙi ba.. 41 3080: 🔥ZINARE🔥 SASAAL Arewabooks@sasaal 06 Kamar ko da yaushe Layi-layi aka bi ana shelar Sarki Hammam ya na buƙatar ganin Mazan Yankin a Masarautarsa.. Kafin ka ce me, kafatanin Magidanta Yankin sun cika harabar Masarautar. Bayan an ansanar da su saƙon Sarki Hammam, na shin akwai Mai son zama Shugaban Kasuwar Tukwanen Zinare a cikinsu? Ba bu wanda ya ɗaga hannu, ɗaya bayan ɗaya suka dinga sulalewa kafin Minti Talatin filin ya dawo fayau babu kowa, dalili; kowa tsoro yake ji, kar ya karɓi Shugabancin shima a biyosa har gida akashe shi. SARKI HAMMAM; Da labarin guduwar Mutanen Yankin ya riskesa ajiyar zuciya ya sauke. Shikenan! Maƙiya Yankin sunyi nasara akan Mutanensa, dama tsoro da gudun mutuwa akeson dasa musu, su dawwama yin rayuwa cikin Talauci, da ƙin faɗar gaskiya ko da za'a kashe na su a gabansu saboda su tsira da rayukansu, duk da mutuwar dai da aka dasa musu tsoronta suke gudunta zai riskesu idan kwanansu ya ƙare. Kansa ya dafe, ya na jin raɗaɗi a cikin zuciyarsa kenan Mutanen Yankinsa sun gwammace ko shekara nawa Ɗayyib zai yi a kwance zasu jirashi ya jagorance su, idan ya ga zai iya idan kuma ba zai iya ba su haƙura da kasuwar gaba ɗaya. "Kaico" Sarki Hammam ya faɗa a sarari. ★Kasa jurewa ya yi, washe gari ya ƙarasawa ayi shelan; "shin da wanda ya ke so ya zama Mataimakin Ɗayyib idan ya warke?" Nan ma babu wanda ya amsa tsit sukayi a cikin Gidajensu kamar ruwa ya cinyesu. Da aka ƙara sanar masa babu wanda ya daki ƙirji ya fito, Gaba ɗaya sai ya rasa abinda yakemasa daɗi, ba shi da wanda ya yarda da shi a kusa da shi balle ya tattauna damuwarsa da shi, saboda masu aikata ɓarnar a kusa da shi suke ta yanda ba shi da yadda zaiyi ya yakicesu, kuma ko da ya faɗi ma su aikata ɓarnar kai tsaye babu wanda zai yarda da shi. Ya zama dole ya canza salon dabarar mulkinsa shima, don tsirar da Mutanen Yankinsa. Bayan wani lokaci... A ɓangaren Ɗayyib ba laifi yanata samun sauƙi saboda ƙwararrun likitocin da suke shigowa dubashi akai-akai, don da farko a Yankin Tudu ya yi ta jinya, sai dai rashin likitoci ya sa aka fitar da shi wani gari da yake kusa da Babban Birnin Abyad. A cikin watanni ya warke tsaf kamar bai taɓa jinyaba. Da tsananin farin ciki shi da Iyalinsa suka ɗauki hanyar Yankin Tudu. A ranar da ya dawo Gida bayan ya huta Sashen Bashar da yake a matsayin ƙanin Mahaifinsa Jalal uwa ɗaya uba ɗaya ya nufa. BASHAR Lokacin ya yi ido biyu da Ɗayyib da sauri ya rungumesa ya na yi mai kwataccen ya ya jiki? Amsawa Ɗayyib ya yi haɗe da jajantamai abinda ya sameshi. Bayan sun ƙara gaisawa, Ɗayyib ya tambayi Bashar garin ya ya haka tafaru? Da kwatancen Gidan Abduh Dhahab ya fara. Ɗayyib mutum ne mai kaifin Basira da saurin Fahimta, wannan dalilin ya sa kai tsaye ya fahimci dole wanda ya gutsewar Bashar harshe yana da alaƙa da Gidan Abduh Dhahab. "Sulaim ka gani, ko Abduh ko Mairam?" Ɗayyib ya tambayeshi a nutse. Shiru Bashar ya yi takaicin Ɗayyib na kamasa tayaya zai iya faɗamai bayan ya ambaci sunayen su dukka a lokaci ɗaya? Ganin ya yi shiru kamar mai tunanin yasa Ɗayyib umartar a nemo mai zane.... Bayan mai Zane ya iso.. Fuskar Abduh ya fara zanawa da kwatancen da Ɗayyib ya ke yi mai, Bashar ya ce ba shi bane an zana Sulaim da Mairam suma ya ce dukka ba su bane. Bashar miƙewa ya yi yana kwatanta tsaho da shara, har ya gama kwatanta iyakacin abinda zai kwatanta babu wanda ya fahimcesa. Dole Ɗayyib ba shi da zaɓi tunda sam yakasa fahimtar wanda Bashar yake nufi don haka ya sallami mai zane. Mai zane yana tafiya shima ya bar Sashen zuwa na Jalal Mahaifinsa ransa babu daɗi. Da Daddare Bayan Ɗayyib ya koma Gida, har dare ya nutsa, ya kasa runtsawa har wajen ƙarfe ukun dare. Babu irin tunanin da baiyi ba game da wanda Bashar yake nufi amma yakasa gano wanene wannan. Ba don yana jin barci ba ya kwanta haɗe da rintse idanuwansa. ★washe gari da Asuba da tsananin ciwon kan rashin samun isasshen barci ya ɗora alolar Sallar Asubahi, har lokacin da tunanin wanda Bashar yake nufi maƙale a cikin zuciyarsa. Dama baya zuwa Masallaci, a tsakiyar ɗakinsa ya shimfaɗa abun Sallah ya tayar. Ɗayyib yana cikin sallah raka'ar ƙarshe ƙwaƙwalwarsa ta harba. Shaidan ya samu damar wasa da hankalinsa haɗe da tuna masa abinda ya kasa tunawa "shara? tsaho? Anya ba MALIK Bashar yake nufi ba? WANENE MALIK; MALIK hadimin Gidan Abduh Dhahab ne, kullum shi yake sharar harabar Gidan duk Safiya kuma Ɗa ne ga Amininsu Ɗayyib da Abduh Dhahab. Tun yana Yaro Mahaifinsa ya bawa Abduh Dhahab shi yake masa Hidimar share-share. Bayan kai gawar su Abduh Dhahab makwanci aka naimi Malik da Iyayensa aka rasa sun gudu, babu wanda yakawo tunanin komai a ransa, sai tunanin sun gudune don tsiratar da rayuwarsu, tun da Malik yasan wasu sirrikan na Abduh Dhahab sama da su Ɗayyib da suke Abokanansa. Malik ya na da tsaho na gaban kwatacce don dalilin tsahonsa yasa Abduh Dhahab yake tsananin sonsa saboda irin siffar Sulaim Ɗansa dana Mahaifiyarsa Nanaah yake da shi, ba irin Siffar Mutanen Yankin Tudu ba, Taƙaitaccen labarin Malik kenan... Ɗayyib cikin rashin nutsuwar zuci da na gangar jiki ya sallame. Daƙyar ya taushi kansa har ya bari gari ya yi haske. Wani ƙulli ya ɗauka ya zura a aljihunsa, sannan ya bar gidan. Wajen masu zane ya fara biyawa ya taho da har mutum uku, suka nufi Gidan Bashar.. Bayan sun haɗu a Sashen Bashar da kansa ya kwatanta mu su Malik suka zanashi kamar zai yi magana. Bashar yana ganinsa ya miƙe jikinsa yana rawa haɗe da gyaɗa kai alamar shine. Ɗayyib bai ce komai ba har sai da ya tabbatar ya sallami ma su Zane sun tafi, saura isu-isu ƴan Gida sannan ya matso kusa da Bashar yana kallon tsakiyar idanuwansa ya ce; " Idan Malik da kowa yasan matsayinsa a Gidan Abduh Dhahab zai kamaka kai kaɗai akaf faɗin Yankinan ya yankemaka harshe to ba shakka kanada masaniya akan Kisan Abduh. Menene gaskiya?" Ɗayyib ya tambayi Bashar idanuwansu sarƙafe a cikin na juna. Wani irin yaushi idanuwan Bashar sukayi haka tattaurar zuciyarsa. Bai ce komai ba sai ƙasa da ya yi da kansa domin tambayar Ɗayyib alamu ne na shima ƙarshensa yazo. Jin shiru bai ɗago ba har na tsahon daƙiƙu yasa Ɗayyib dafashi, sharaf ya zube ƙasa daga zaunen dayake kamar Gini. Ɗayyib ne ya kinkimesa da sauri ya yi gaba, Kafin su je wajen mai magani rai ya yi halinsa. Da labarin mutuwar Bashar da abinda ake zargi, ya riski Sarki Hammam bai ce komai ba banda hutun da yake ɓukata don haka ya Yanke shawarar da zarar anyi bakwai zai bar Yankin na wasu watanni kafin nashi shima lokacin ya yi. Mutuwar Bashar ya sanya nutsuwa a zuƙatan mutanen Yankin don gani suke yi dama Bashar da Allah Ya tonawa Asirine kaɗai matsalar Yankinsu kuma gashi ya mutu, ba su yi tunanin ina magoya bayan Bashar ɗin suke ba, domin bai isa ya yi wannan ɓarnar shi kaɗai ba. Tuni kowa ya saki jiki suka fara ƙera Tukwane ba ji ba gani don tunkarar Kasuwar Tukwanen Zinare da ƙafar dama, har lokacin Ɗayyib ba shi da Mataimaki, shi kaɗaine Shugaba. NAILA; Tun tana tambayar Kakarta game da su wanene ahalin su Abduh Dhahab har ta gaji ta haƙura. Da kowa ya fara haɗa kayan sana'ar da zai shiga Kasuwar Tukwanen Zinare da shi, kayan wasan Yaran da mahaifiyarta take yi itama dama can ta iya, tafara ƙerawa Kakarta tana tayata. Gwanin sha'awa ta ƙera su Tukwane, randar ruwa, murhu harda talabijin duk na lakar ƙasa. Mutanen Yankin da ƙafar Dama suka shiga kasuwar Tukwanen Zinare, domin babu wanda bai siyar da kayan sana'arsa ba. ********************************************* Kwanaki sun miƙa, Shekaru sun shuɗe abubuwa sun sauya, yawanci daga sauƙi zuwa tsanani. SUFYAN ƊA A WAJEN ƊAYYIB; ya zama ƙosasshen Saurayi, kyakkyawan da yake taƙama da kyansa da kuma zamowar Mahaifinsa Shugaban Kasuwar Tukwanen ZINARE. ya yi niyyar ajiye burinsa na zuwa Babban Birni ya yi ilimi mai zurfi amma ranar da faɗa ya haɗasu da Kabeer Abokinsa ɗan Gidan ƙanin marigayi Dattijo Junaid ya ce masa; "Taƙamar mai kakeyi? Babanka Shugaban Kasuwar Tukwanen Zinare ne? Hmm! Kasuwar Zinaren da Abduh Dhahab ne yasha wahalar kafasa, bayan ransa kuke cin arziƙi shi kakeyiwa taƙama? idan ban da ajali waye ma yasan Babanka balle kai? Ko lokacin da Sulaim yake raye, shi da ma Mahaifinsa ne ya ƙirƙiri Kasuwar Tukwanen Zinaren daga filin da ya gada a wajen Mahaifansa, kuma fika kyau da nasaba bai yi mana abinda kake yimana. Kabari duk ranar da ku ka ƙirƙiri wani cigaba na ƙashin kanku a wannan Yanki ba na cin arziƙin wa su ba sai kazo ka ɗaga mana kai. Banza mai macacciyar zuciyar da bai san komai ba sai son ace masa ya na da kyau ɗan daudu kawai!" waɗannan kalamai na Kabeer sun sosa ranshi tare da sashi kukan da zuciyarsa ce kawai bai haɗiya ba. tsanar Kabeer kuwa babu inda bai ratsaba a jikinsa. A ranar ya fuskanci zamowar Mahaifinsa Shugaban Kasuwar Tukwanen Zinare kaɗai bai wadatar ba bai kuma zama wani abin kambabawa ko abin ayaba a wajen Mutanen Yankin ba, sai ma ƙara dawo musu da soyayyar Abduh Dhahab da Iyalinsa da ya yi a cikin zuƙatansu, shi kuma ba wannan ne burinsa ba. Burinsa kowa ya manta da Abduh Dhahab ne ya ƙirƙiri Kasuwar Tukwanen Zinare, su riƙi Mahaifinsa tamkar shi ya ƙirƙiri Kasuwar tun usul, su kuma girmamashi a matsayinsa na Ɗa Namiji ɗaya tilo a wajen Shugaban Kasuwarsu. Ko da ya bawa Mahaifiyarsa labari, maimakon ta tausheshi sai ta ƙara zugeshi tare da ƙara tadamai tsimin burinta na tafiya Babban Birnin ya yi ilimi boko mai zurfi. HINDU MAHAIFIYAR SUFYAN Tabbacin amincewar Sufyan da ta samu ne, ya sa ta shiryawa tafiya Yankinsu wajen Malaman dubanta, don su duba mata Matar data dace Sufyan aura don tafiya da ita Babban Birni ta dinga yi masa Bauta kamar yadda ta tsara a baya. NAILA Itama ta zama kyakkyawar Budurwa kuma makitsiyar da mutanen Yankinta suke alfahari da ita. Ba ta daina sana'ar ƙera kayan wasannin Yara na laka ba, sai dai ta daina fita da su Kasuwar Tukwanen Zinare saboda harajin da ake tsawwalawa ma su ƙananun sana'o'i irinta. A ɓangaren kitso tana samun ciniki don ba Makitsiyar da ta iya kowani kalar kitso kamarta. Har Daular Sarki Hammam take zuwa yiwa Iyalinsa kitso su biyata da kuɗi mai tsoka. Duk tsayin wannan shekarun fuskar Sulaim na manne a cikin zuciyarta don har kuɗi ta biya ƙwararren mai zanen Yankin ya zanata ita da Sulaim a waje ɗaya, ta kai Gidan hoto aka wanke mata ƙaraminshi, da shi take yawo duk inda zata je. ********************************************** Tsawwalawar Haraji ya kawo koma baya ga masu ƙananun Sana'o'i a Yankin Tudu harma da ma su manyan jari. Ga ɓullowar Gidan rawar daya zamewa Yankin musiba, a cikin Kasuwar. Gidan rawa an ƙirƙirar shine ne a cikin Kasuwar Tukwanen Zinare, har da Masauƙin da aka kewaya da katakwaye da langa-langa kamar Ɗaki ga waɗanda dare ya yiwa, kuma kowa ya kasa tunkarar Ɗayyib da yake shugaban kasuwar su ji wanene ya kawo gidan rawa, su kuma shaida ba sa so, saboda dalilin haka Matasan Yankin sai su sha wahala su ƙera Tukwane da zarar sun siyar sai su wuce Gidan rawa da Kuɗin, haka ɓaki ma su shigowa, wa su ma suna shigowa ne kawai don suyi sharholiyarsu su koma ba don su sayi komai ba. Wannan lamari yana ciwa Mutanen Yankin tuwo a ƙwarya amma tsoron rashin sanin wanda ya kafa Gidan rawan, tunda ga shi Shugaban Kasuwar Ɗayyib bai hana ba kuma bai kai ƙara wajen Sarki Hammam ba, wannan yasa suke Kwana da ɓakin ciki suna tashi da shi. Ƙewar Marigayi Abduh Dhahab da suka mayar abin zagi a baya na damun zuƙatansu, da maganganun Marigayi Dattijo Junaid. Ƙara ta'azzarar komai ga shi kowa yakasa magana yasa Kabeer Abokin faɗan Sufyan yanƙurawa, don bazaiyiwu saboda tsoron mutuwa su kashe kan su da Kansu ba. Faɗan da ya tada hazo ne ya ɓarke a tsakanin Kabeer da mai gadin gidan rawar. Dayake Kabeer matashine mai garin jiki da zafin nama sak Siffar mutanen Yankin Tudu kuma baya shaye-shaye ya sa yasamu damar yiwa Matashin da ba su ma san asalin ɗan ina bane saboda duhun fatarsa dukkan tsiya. Ba bu wanda baiji daɗin abinda Kabeer ya aikata ba, don wasun su sun cire tsoro sun fito sunata maganganun sam bai dace ace an gurɓata Kasuwar Tukwane da Gidan rawa ba... Kabeer ko a jikinsa zuciyarsa sakayau ko ba komai, yasamu ya amayar da abinda yake sukar zuciyarsa da na Mutanen Yankinsa. saɓanin Mahaifinsa da zuciyar ke cike da tsoron abinda zai biyo baya. Tun Mahaifin Kabeer yana jin tsoron martanin da zai biyo bayan abinda ɗansa ya aikata har ya saki ransa ya cigaba da harkokinsa.. Bayan wata ɗaya, watan cin Kasuwar Tukwanen Zinare yaƙara zagayowa. A gaggauce Kabeer da Mahaifinsa suke kimtsa Tukwanen su don fita Kasuwa. Su na zuwa suka tarar da Rumfar su.....✍🏻 09132403788 [7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: 🔥ZINARE🔥 SASAAL Arewabooks@sasaal 07 Su na zuwa su ka tarar da rumfarsu a rushe, yanayin shafewar wajen ma kamar ba'ataɓa kafa Rumfa ba. Kafin Mahaifin Kabeer ya dawo daga ɗimuwar da ya shiga, tuni Kabeer ya nufi kewayayyen rumfar da ke matsayin ofishin Ɗayyib. Abin mamaki kamar wanda ake jira tun kafin ya kaiga inda ya nufa, matasa masu irin Shekarunsa suka rufe shi da duka ta ko ina. Ihun naiman taimakon Kabeer ne ya fito da Ɗayyib haka Mahaifinsa daya ƙaraso a guje ya na haki. Dakatawa su kayi da dukansa saboda ihun da Mahaifinsa ya kurma, kowannensu na numfarfashi saɓanin Kabeer daya goge jinin bakinsa ya yinƙura ya miƙe yana kallon inda Ɗayyib yake tsaye. Da zafin da yake ji a cikin zuciyarsa da gangar jikinsa ya fara magana; " da a haka Abduh Dhahab da muka mayar abin aibatawa ya gina Kasuwar Tukwanen Zinare da bai kai ko ina ba zai mutu, ban nufo ofishinka don naci zarafinka a matsayinka na Shugaba garemu ba, sai don na kawo maka ƙorafin rushewa Mahaifina Rumfa da akayi. Menene laifina? Idan faɗan da nayi waccen watan ne, ina neman yafiyarka ka dawowa da Mahaifina Rumfarsa. Ni na haƙura da zuwa Kasuwar gaba ɗaya, don matsawar ina zuwa dole wata rana zan kasa jurewa nayi yunƙurin dakushe duk wani abinda zai kawowa Yankina koma baya ko akan waye kuw.." bai ƙarasa ba saukar naushin da yasa shi zubewa ƙasa warwas ya dakatar da shi daga Matasan da suka yi masa duka. Da gudu Mahaifinss ya nufoshi yana kuka haɗe da kiran sunansa. Ɗayyib ma tsawa ya dakawa Matasan da su ka bar wajen. Rige-rigen ɗaukar Kabeer kowa yake yi don kaishi Asibitin Mahaifinsa ya hana yace a barshi ya kaishi Gida yana da maganin da zai bashi. Bayan su Kabeer sun je Gida, aka Turo kiran Mahaifinsa daga Fadar Sarki Hammam, bai wani jima ba ya dawo.. Mutanen Yankin; Abinda ya faru da Kabeer yaƙara zama zanannen layin da kowa zai ji tsoron ƙetarawa, har ya yi azarɓaɓin faɗar gaskiyar a kan duk wani abu ba dai-dai ba da ake aikatawa. Jiki a sanyaye kowa yaci Kasuwarsa ta wannan rana. KABEER; Cikin tsananin Azaba Kabeer ya farka gabannin sallar magriba bayan ɗure-ɗuren maganin gargajiyan da suka yini suna yimai. Daga Mahaifinsa har Mahaifiyarsa hannunshi suka kamo suna rige-rigen yimai sannu da jiki. Cikin taushin harshe Mahaifinsa ya fara magana; " Kabeer lamarin Yankin nan sai addu'a faɗar gaskiya duk ƙanƙatarsa ya zama abin tsoro, amma naje Fadar Sarki Hammam na samesa da Shugaba Ɗayyib ya yi alƙawarin kawo ƙarshen gidan rawar da abokin kasuwancinsa ya ƙirƙiro kuma ya bani haƙuri, Kabeer ko da wata ɓaraka za ta kuma kunno kai, ba na so na ƙara jin bakinka idan ba so kakeyi su kashemin kai a banza ba na roƙeka!." ya ƙarasa faɗa da kuka mai sosa zuciya. Kai Kabeer ya ɗagamai alamar ya ji. Fara kiraye-kirayen Sallar Magriba ne yasa Mahaifinsa yin alola ya bar Gidan. Itama Mahaifiyarsa miƙewa tayi don yin alola kafin ta taimakamai shima ya yi. Ta na yunƙurin zuba ruwa a buta taji ana bubbuga Gidan a hankali. Fasa zuban ruwan tayi ta ɗauki mayafi ta lulluɓe jikinta. Ta buɗe ƙofar, wanda ya ke bugawa bai jira izininta ba ya yi gaba ya barta da buɗaɗɗen baki, zuciyarta na bugawa da ƙarfi ta nufo cikin Gidan ƙafarta na harɗewa. Mayafin fuskarsa ya yaye. A take fuskarshi da yake abin tsoro a wajen duk wani Mutumin Yankin Tudu a tun shekarun baya da'a yankewa Bashar harshe ya bayyana. Da sauri ta dafe bakinta hawaye na ɓulɓulowa wani kan wani. Kai MALIK ya girgiza mata sannan ya ce; " mai kike yiwa kuka?" Bata kaiga ba shi amsa ba Mahaifin Kabeer ya shigo don yakasa zaman Masallacin daya saba bayan sun idar saboda fargaba. Shima ruɗu da tashin hankali ya shiga sai dai shi ya yi ƙarfin halin zube gwiwoyinsa dukka biyu a gaban Malik ya na roƙonshi; " ka tausayamin, haƙiƙa ni bani da wata masaniya a kan yanke harshen ɗan uwana Junaid, haka Iyalina. Ka yi haƙuri ka barmin ɗana ya rayu da mu saboda shi ya rage a kusa da mu, na roƙeƙa" Kai Malik ya ɗaga sama yana kallon ƙofar Ɗakin da Kabeer yake tsaye yana Kallonsa ya ce; " na zo ku bani Kabeer na tafi dashi, wata rana nayi alƙawarin dawo muku da shi a yanayin da zakuyi alfahari da shi, ba lallai naushin Sihirin da su ka yimai ya barshi ya rayu ba, kuma ko da ya rayu wata rana dole zasu rabaku da shi" yana ƙarasa faɗa ya matsa inda Kabeer yake a tsaye. A kafaɗa ya saɓashi duk girmanshi, batare jiran amincewar su ba. fuskarshi ya ƙara lullɓewa ya nufi hanyar barin Gidan. Da ya juya baya, Kabeer hannayenshi duka biyu ya ɗaga a hankali ya na yiwa Iyayenshi sallama, tausayinsu na mamaye ilahirin zuciyarshi. Suma kuka suka saki bayan fitarsu suna ƙanƙame juna. Ba su yi tunanin zasu iya runtsawa ba bayan Malik ya tafi da Kabeer. Domin Malik tamkar mala'ikan ɗaukar rai haka yake a wajen Mutanen Yankin Tudu. Haka kawai suke jin nutsuwa a ransu tare da gasgata alƙawarin da Malik ya yi musu na zai dawo mu su da Kabeer wata rana a yanayin da zasuyi alfahari da shi. ★washe gari Mahaifin Kabeer ya fitar da labarin ɓacewar Ɗanshi, don ko mai zai faru bai isa ya ce Malik ne ya zo ya tafi da Kabeer ba, indai ba so yakeyi shima yabi Ɗan uwanshi Junaid ba. Babu wanda bai ƙara shiga taitayinsa ba. Ta ɓangaren Mutanen Yankin da basu da masaniya a kan komai, tsoron faɗar gaskiya da alwashin ɗauke ido akan komai suka ƙara sawa ransu. Ta ɓangaren waɗanda suke da hannu tsumu-tsumu da waɗanda suka san abinda yake faruwa amma basu da damar faɗa suma sun shiga ruɗun wanene ya ɗauke Kabeer?.... Bayan kwanaki.. Kamar komai bai faru ba haka kowa ya cije ya cigaba da harkokin gabanshi, saboda ma su ƙarfin haline ma suke iya shiga yiwa Mahaifan Kabeer jaje, ragowar kuwa tsoron shiga Gidan ma sukeyi saboda gani sukeyi da zarar sun shiga jaje za'a biyo su Gida suma a sace su, ko a yanke musu harshe. ***************************** A ɓangaren Hindu Mahaifiyar Sufyan taje Yankinsu, ta gana da Malaman tsibbunta har mutum Uku kuma amsar duk ɗaya ne; "Naila Makitsiya a Yankin Tudu itace tsanin hawar matakin nasarar Sufyan. Duk tsananin duk abinda zai faru karta kuskura ta bari Aurenta ya suɓucewa Sufyan, saboda sana'ar kitsonta shine mafarin nasararsa, daganan kuma zai haifar da gagarumin abinda zai sa Sunanta da na Mijinta Ɗayyib har da na shi kanshi Sufyan ɗin ya zama abin faɗe ga kowa ba a iya Yankin Tudu kaɗai ba har ma da duniya baki ɗaya. Canji mai girma gaske zai zowa Yankinku a wannan lokacin, amma fa dukka hakan bazai tabbata ba har sai Sufyan ya auri Naila ya samu matsuguni Babban Birnin Abyad." Kamar haɗin baki dukka amsa ɗaya ta samu daga bakin kowannen su sai dai sigar maganar da ya ke bambanta amma dukka ma'ana ɗaya yake bayarwa. Mallakar matsuguni a Babban Birnin Abyad ko da na haya ne abune mai matuƙar tsadar da duk kuɗin da Ɗayyib yake taƙamar yana samu a Kasuwar Tukwanen Zinare bazai wadatar ba balle ta lallaɓashi ya amince. Da farko bata taɓa kawowa Sufyan yin Karatu a Babban Birnin Abyad ba, sai hasashen garuruwan da suke kusa da shi, don ko a Yankinsu Sarki Hammam ne kawai yake iya zuwa can ya yi kwanaki amma ba ire-iren su masu iya arziƙin Yankin Tudu ba. Ta ina zata samu kuɗi masu yawan da zasu isa Sufyan ya tafi Makaranta har ya kama mu su matsuguni a Babban Birnin Abyad?... Mahaifiyarta da kusan dukka ɗabi'unta ta gada ta tunkara da batun. Cikin ƙwarin gwiwa ta bata shawarar mai zai hana su tara dukka kadarorinsu waje ɗaya su kasa shi kashi uku su siyar da kashi biyu.... Da farko Hindu ƙin amincewa tayi da shawarar Mahaifiyarta ta har na tsahon Kwana uku. Tuno da Sufyan zai samu gagarumin ɗaukakar da sunansu zai zama abin faɗe ba a iya Yankin Tudu kaɗai ba har da duniya baki ɗaya ya sa ta amince. Hindu bata dawo Yankin Tudu ba sai da kuɗi masu yawan gasken da ta zubo a Akwatin ƙarfe garƙame da mukulli. A daren ranar ta tari Sufyan da zancen. Manyan idanuwansa farare ƙal ya zaro, tsabar ruɗewa hannuwansa har rawa sukeyi wajen kamo nata hannun. "Ummi ki ka ce me? rayuwa a Babban Birnin Abyad? Kina nufin na kai matsayin da zan tafi can nayi Karatu Ummi ki ƙara faɗa dan Allah ko nine banji da kyau ba" Sufyan ya faɗa a ruɗe. Dariya ruɗewarsa ya bata, don haka da ta ɗan dara, kafin ta zayyanomishi duk abinda ya faru da shawarar da Kakarshi ta bata har ta samu ta dawo da kuɗi ma su yawan gasken da zasu isheshi ya naimi Makaranta, su kama Gida har na tsahon shekaru biyu. Lokacin da ta sa ɗan mukulli ta buɗe Akwatin kuɗin zabura Sufyan ya yi har sai da ya miƙe tsaye yana nuna kuɗin, duk girman kanshi da jinkanshi kasa jurewa ya yi yasa kuka yana ƙanƙameta, haɗe da faɗin; "Ummi ba Naila ba kowa kike so na aura na amince, na gode Ummi Allah Ya sa na cikamiki burinki kamar yanda kika cikamin Burina" Bayanshi take shafawa ranta fari ƙal. Bayan Ɗayyib ya dawo ya huta ta sanar dashi duk abinda ya faru bata ɓoyemai ba. Da farko ya ɗanyi jim da bata laifin da ba taje wajen Malaman tsibbu ba, da bata tono abinda yafi ƙarfinsu da zai kaita ga siyar da kadarorinsu na manyan kuɗaɗe irin wannan ba. Ƙara marairaice murya tayi har sai da tasan yanda tayi ta yaudareshi ya yi alƙawarin nemo kuɗi ma su yawan gaske domin Sufyan ya ƙara a kai, su biya kuɗin hayar shekaru uku maimakon biyu, kafinnan sun san komai zai bayyana kanshi. Hindu zata iya cewa bata taɓa kwanan farin ciki irin na wannan ranar ba. Shima Sufyan a ɓangarenshi yakice batun Naila ta taɓa abota da Sulaim ya yi ya amincewa rungumar Aurenta hannu bibbiyu kafin ɗaukakarshi ta bayyana. Kwana biyu bayannan Hindu ta bayyana a Gidansu Naila da sunan ta zo kitso. Ba iya Naila da Kakartane kaɗai ne sukayi mamaki ba, har da maƙotansu da waɗanda suka ga gilmawarta. A iya sanin da sukayiwa Iyalan Gidan MUSAA DHAHAB Magadan Sarautar Yankin Tudu kuma masu faɗa aji a Yankin Mutanene ma su girman kai, da kai Kansu inda Allah Bai kai su ba, kama daga kan asalin ƴan Gidan har zuwa kan baren da'aka auro, idan ka cire Marigayi Abduh Dhahab da ɗansa su kaɗai ne suka banbanta. Zuwan Hindu Iyali ga Ɗayyib Uwa ga Sufyan da yake ƙafafa da jin yafi kowa, saboda Shugabancin Kasuwar Tukwanen Zinaren dayake hannun Mahaifinsa waɗanda ganta ta shiga gidansu Naila suka san dole da manufa ba wai don zuwa wajen Naila kitso kaɗai ba. CIKIN GIDANSU NAILA; Rasa wajen da zata bata ta zauna Kakar Naila ta yi, duk da akwai ƴar tsama a tsakaninsu tun shekarun baya, amma saboda Sashensu na Masarautar Yankin Tudu ya fi nasu gidan kyau nesa ba kusa ba da ababen more rayuwa, duk da suma nasu Gidan ba laifi da kyansa dan yafi na dubban mutane a Yankin, yasa ta ke ƙoƙarin yi mata ƙara tunda batasan abinda ya kawota ba. Cikin sanyi hali da na murya da kuma sanin girman na gaba Naila ta buɗe matsakaicinta bakinta mai ɗauke da siraran laɓɓa ta ce; "Barka da Rana Ranki ya dade, da kin turo har gida zanzo nayi miki ba sai kinzo ba" murmushi mai kyau Hindu tayi tana dafa kafaɗarta saboda sanyi da daɗin muryarta da ya yi matuƙar birgeta ta ce; " Karki damu ɗiyata gaba idan zan ƙarayi sai kizo Gida kiyimin" Kai Naila da gyaɗa itama da kyakkyawar murmushi a saman fuskarta. Hindu da dabara take kallon duk wa su motsin Naila har aka fara yimata kitson da tace guda goma take so. Kuɗi mai yawa kwatankwacin wanda Iyalan Sarki Hammam suke bawa Naila idan taje Gidan yi musu ƙananan kitso ta bata. Daƙyar ta karɓi kuɗin don sai da Kakarta ta saka baki. Yanayin Naila da dabi'unta sun matuƙar burge Hindu, don da ba dan burin auren Mace ƴar Babban Birnin da takeyiwa Sufyan kwaɗayi ba, da ta amince Naila ta zama Surukarta ta din-din. 09132403788 [7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: 🔥ZINARE🔥 SASAAL https://www.arewabooks.com/dashboard/info 08 ƊAYYIB. Da ranar cin Kasuwa ya ƙara zagayowa, Harajin da zai kai iya adadin kuɗin gidan hayar da ya yi alƙawarin biyawa Sufyan na Shekara ɗaya a Babban Birnin Abyad ya tsawwalawa Ƴan Kasuwar Tukwanen Zinare. Wasun su har da kuka su na magiya amma ba bu wanda aka saurarawa. Sai bayan an tattara kuɗin ya zo yake basu haƙurin In sha Allahu Kasuwa mai zuwa hakan bazai faru ba. Dubban mutane ne suka koma Gida ransu a ƙuntace. Ko da Ɗayyib ya tattara kuɗaɗen basu kai adadin abinda yake nema ba har sai da ya haɗa da wanda ya jima ya na tarawa. Tun kafin zancen neman Auren Naila yaje ga kunnen Danginta da ita kanta da Mutanen gari Dangin Ɗayyib suka nuna sam basu amince ba. Ta ya ya Naila ƴar Gidan Mahmoud da yake Madinki talakan fitik zata shigo zuri'arsu? Hakan zubar da ƙima da mutuncin Masarautarsu ne don haka sam su basu yarda ba. Da labari yajewa Jalal murmushi ya yi a zuciyarsa tare da bada Umarnin a nemawa Sufyan Auren Naila ba tare da jinkirtawa ba. A ɓangaren Mutanen gari, ba su yi mamaki ba saboda sunyi zargin haka tun zuwan Hindu Gidan. A ɓangaren ƴan uwan Mahmoud da suke Uba ɗaya jiki na rawa suka amince ba tare da sanin Kakar Naila ko amincewar ita kanta Nailan ba. KAKAR NAILA; Da labari ya riske Kakar Naila tsabar zabura sai da miƙe bakinta yana rawa take ambaton Sunan Allah don tasan ruwa baya tsami banza kuma tun a zamanin Budurcin Babbar Ƴarta Yayar Mahaifin Naila tasan wacece Hindu da makircinta. Itace silar rushewar auren Ɗan uwanta da Yayar Mahaifin Naila saboda kawai ba su da kuɗi. Baƙin cikin rushewar auren ne ya yi sanadiyyar mutuwar Ƴarta. To idan zata hana Yayanta auren Yayar Mahaifin Naila saboda talaucisu tun a waccen zamanin wani dalili ne zai sa yanzu ta amince Ɗanta ya auri Naila tunda su dai sunanan a Talakawansu ba bu abinda ya sauya? Naila da take gyara dogon gashin kanta mai cika da tsaho a gefe ba tace komai ba, sai ƙwallar da yayiwa ganinta yana. Ba ta da abin cewa, tunda burinta macaccen burine a zahiri, amma a baɗini rayayye ne a cikin zuciyarta tunda da shi zata mutu. Tasan ko da Sulaim ya na raye ba lallai ya so Mace irinta ba. Sai dai Mutuwarsa ya sa tanajin ƙwarin gwiwar da wataƙila ya na raye da zai iya auranta suyi rayuwar farin cikin da take hasashe. Tasan dole wata rana, irin wannan ranar zata zo domin bazata dawwama a haka ba tayi aure ba, shiyasa tayi alƙawarin sawa kanta jarumtar amsar duk Namijin daya zo mata a matsayin Mijin aure, tunda son Sulaim a cikin zuciyarta ba Ɗan adam ba ne irinta balle ta yaƙeshi. Kusa da ita Kakarta ta zo ta zauna tana kamo dukka hannayenta daga tazar gashin da takeyi. Cikin tausayin jarabawar da yake samun Nailan akai-akai ta ce; " karki kiyi kukan zuci ke kaɗai Naila ki fito da shi sarari muyi tare" Naila tanajin haka ta saki Kukan daya maƙalemata tuntuni. Sun kai minti Talatin a haka kafin Kakarta ta jata Ɗaki. Manne da juna suka zauna kan Naila kwance a samar Kafaɗarta. A hankali Kaka ta ce; "Ba na jin tsanar Sufyan a raina duk da labarin ɗabi'unsa marasa kyau da nake ji a bakin mabanbanta Mutune, sai dai ina tsoron wani irin ƙulli Hindu ta ƙulla da har zaisa ta amince ki auri Ɗanta. Hindu Ƴar masu rufin asirce a Yankinsu, dalilin haka ta ƙulla makircin da ya haramtawa Habeebah yayar Mahaifinki auren Yayaanta saboda talaucinmu, domin sana'ar Ɗinki muka gada daga Iyaye da kakanni, dalilin wannan baƙin cikin Habeebah ta rasa ranta. Babban burin Hindu a waccen lokacin shine ta auri Ɗan babban Gida, Allah Kuma ya cika mata burinta. Babban Ɗa ga Ƙanin Sarki Yankin Tudu na wacce lokacin Ɗayyib ya nuna yana sonta, har sukayi aure. Abinda yake bani mamaki da tsoro shine idan har Hindu zata guji Ɗan uwanta ya auri Habeebah saboda Talaucin mu tun a waccen zamanin, wani dalili ne zaisa yanzu ta bari Ɗan da ta haifa a cikinta jinin Sarautar Yankin Tudu a wannan zamanin da burika suka yi yawa ya aure ki duk da ƙin amincewar da mutanen Masarautar suka nu na kamar yadda na samu labari?" Naila ba tace komai ba sai ƙara ƙanƙameta da tayi da dukka hannayenta, a haka barci ya fara ɗaukarta. Sai da aka kira Sallar la'asar sannan suka miƙe, kowannen su zuciyarsa ba daɗi. Har dare ya raba Kakar Naila ta kasa runtsawa, sai kai da take girgizawa lokaci zuwa lokaci saboda zuciyarta dake hasaso mata ai gara Halayyar Hindu da Halayyar mutanen cikin Masarautar Yankin Tudu. Hannuwanta ta sarƙe waje ɗaya, Allah Ya ɗauki ran Mahmoud da Mahaifiyar Naila a tsakankanin Shekaru kaɗan kuma Allah ya jarabceta da mugayen Ƴan uwan uwa da na Uba gaba ɗaya idan aka cireta ita kaɗai ba bu wanda ya ke son Naila ko ya raɓeta sai domin buƙatar kanshi. Idan har ta zuba Ido Naila ta auri Sufyan to tabbas taci amanar Naila ba kuma zata yafewa Kanta ba, dole ta samo mafita ko da kuwa zai kaita ga gaban Sarki Hammam ne, don Masarautar Yankin Tudu tamkar Masarautar Uƙubane ga baren cikinta har ma da Ƴaƴan cikinta. Naila shafa gefenta ta yi taji ba bu Kaka. A hankali ta miƙe, a tsakar gidansu ta hangota ta na zarya. Da sanyin tafiyarta ta ƙarasa bayanta. Cikin taushin harshe ta fara magana; "Lokacin da na wayi gari ba bu Sulaim ya ƙone, na ji raɗaɗi a raina, da na zo na rasa Mahaifi sai na ƙarajin raɗaɗi amma ba irin wanda naji lokacin da na rasa Sulaim ba. Da rasa Mahaifiya sai na ƙarajin raɗaɗin da sam ba shi da haɗi da irin waɗanda na ji a baya. Abin nufi zafin rasa abu a zuƙatan mu na da alaƙa ne da yanda matsayin abun yake a wajen mu, saboda haka nasan abinda kike ji Kaaka, amma karki bari hukuncin Ubangiji ya hanaki barci wajen tunani har ki kasa neman mafita a wajen Shi. Zuciyata mai kaushi ce akan abinda ba na so Kaaka. Auren Sufyan ba ya nufin komai gareni balle har ya hanani barci, abu ɗaya na sani, idan abu mara daɗi ya sameni kuma na jure na yi haƙuri to tabbas Ubangiji Zai musanyamini da mafi alkhairinsa." Naila ta ƙarasa faɗa da siririn kuka tana ƙanƙame Kakarta. Itama Kakaa da rawar murya ta ce; "Hakane Naila, amma ki sani zanyi iya yina don samar miki mafita domin nasan Hindu dole ta na da wata manufa, Naila ba na son rasaki, ke kaɗai nake gani na ji daɗi" dukkansu kuka suka sa, su na ƙara ƙanƙame juna a haka Naila ta jata suka koma ɗaki. Sun ɗauki tsahon mintina a haka kafin Naila ta ce; " Maiyasa ki ke tsoron Masarautar Yankin Tudu, ko saboda kashe-kashen da akayi shekarun baya ne?" Kai Kaaka ta girgiza tana lumshe idanuwanta labarin asalin Masarautar kamar yadda Marigayi Mijinta babansu Mahmoud ya bata labari na dawo mata, fuskantar Naila ta yi ta ce, "kinsha tambayata wanene Abduh Dhahab su wanene ƴan uwansa ban taɓa baki labari ba, amma yau zan baki ko don ki fuskanci gaba" ```MASARAUTAR YANKIN TUDU``` Sarki Musa shine Sarki na farko da ya kawo sauyi mai girma a Yankin Tudu lokacin Mulkinsa. Daga wannan lokacin mutanen Yankin suka samu ƴanci da sauƙin abubuwa da dama, da shigowar gwamnatin sama-sama cikin lamuransu. Sarki Musaa yana da ƴaƴa da yawa Maza da Mata daga Uwaye daban-daban amma wanda ya yi zarra a cikin su kuma ya fi ƙarfin arziƙi shine ABDULYASAR MUSA DHAHAB, Abdulyasar su biyu Mahaifiyarsu ta haifa, kafin Allah Ya ɗauki ranta. Matsi daga Kishiyoyi da asirce-asirce kala-kala da har ya yi sanadiyar mutuwar ƴar uwarsa, shi kuma yake fuskanta azaba daga ɓangaren kishiyoyin Mahaifiyar su bayan ranta ya sa Mahaifinsa Musaa ɗaukeshi daga cikin Ƴan uwansa zuwa Babban Birnin Abyad wajen Abokanan Kasuwancinsa don yin ilimin zamani dana Addini. Anan Babban Birnin Abyad Abdulyasar Dhahab ya yazama Babban Ɗan kasuwa. Kasuwanci Zinare yakeyi da taimakon Bature Francis Ɗan Aminin Mahaifinsa da ya ɗorasa a hanya har yazama hamshaƙin mai Arziƙi. Dalilin wannan Kasuwanci na Zinare da ya ɗauka da matuƙar muhimmanci sama da Abokanan Kasuwancinsa ya sa suka sauya mai Suna daga Abdulyasar Musaa zuwa Abdulyasar Dhahab. Bayyanar Abdulyasar Dhahab a Yankin Tudu a matsayin hamshaƙin ɗan Kasuwa babban abin alfahari ne a wajen Mahaifinsa Sarki Musa. Bayan dawowar Abdulyasar, babu wanda yasan dalili Gaba mai ƙarfi ya sarƙe a Masarautar tsakanin ƴan uwa biyun da suke aminai wato Sarki Musa Jamil Kakan-Kakan Ɗayyib Mahaifin Sufyan. Abdulyasar bai jima da dawowa ba Allah Ya amshi ran Mahaifinsa Sarki Musa. A waccen lokacin anso naɗa Abdulyasar a matsayin magajin Mahaifinsa ko dan ƙarfin arziƙinsa amma ya nuna bayaso da suka takura ya tattara ya gudu na ɗan lokaci. Dole aka naɗa Yaya ga Sarki Musaa Mahaifin Sarki Hammam. Ƙarfin arziƙin Abdulyasar Dhahab da taimakon shi ga Talakawa Yankin sai ya shafe sunan kowa a Masarautar su kamar shine Sarkin Yankin. Lamarin ya na sosa ransu matuƙa, wannan dalilin yasa suka fara kaiwa dukiyarsa hari ta kowacce siga tare da alƙawarin kaishi ƙasa ko ta halin ƙaƙa. Su na cikin wannan yanayin matar Abdulyasar Dhahab ya aura bayan dawowarsa ta haifa ɗa Namiji Ubaidullah. Da taimakon Iyalinshi bayan ta haihu saboda kwaɗayin abin duniyar da sukayi alƙawarin za su ba ta na kaso maiyawa, ta taimaka musu suka kai Abdulyasar ƙasa, duk da haka Abdulyasar Dhahab bai bar rayuwar Ɗanshi Ubaidu ya lalace kamar yanda suka so ba, ya miƙa amanarshi hannunshi abokannan kasuwancinshi suka tafi da shi can wata nahiyar, shi kuma ya cigaba da gwagwarmaya da azzaluman Masarautar su. Ubaidu bai tashi dawowa Yankin Tudu ba sai da kowa ya fara mantawa da shi, da kyakkyawar Matarsa da Ɗansa mai kama da shi Abdullah(Abduh Dhahab) ya dawo, lokacin Abduh har zama ƙaton saurayi, har da ƴar Yayar Matarshi Aysha da Mahaifiyarta ta mutu suka dawo Yankin Tudu. Ga dukiya mai tarin yawa da Ubaidu Dhahab ya dawo da shi. Dawowar Ubaidu Dhahab da dukiya da kuma zankaɗeɗiyar Matar da babu ma su irin siffarta a Yankin Tudu ya yi matuƙar sosa ran maƙiya Masarautar. Maimakon su yaba sai suka hau kushewa da aibata Ubaidu Dhahab ya auro bare mai kyan da zata kashe shi ta kwashe dukiyar da ya tara. Duk Abdulyasar na sane da su sai dai bai ce komai ba, sai jikansa Abdullah da yaja a jiki. Sanin matsawar Abdulyasar ya na raye ba zai barsu su kai Ubaidu ƙasa kamar yadda su ka kaishi ba, ya sa suka fara shayar da shi guba a sirrince ta hanyar amintacciyar hadimarshi. Cikin ruwan sanyi suka kashe Abdulyasar ba tare da kowa ya ankara ba, sai daga baya Mutanen gari suka ji ƙishin-ƙishin. Mutuwar Abdulyasar ba iya Ubaidu da Iyalansa kawai ya taɓa ba har da mutanen gari, saboda alkhairinsa. Bayan wani lokaci suka dawo kan Ubaidu. Duk da sun kashe Abdulyasar sun kasa kai Ubaidu ƙasa ta cikin ruwan sanyi kamar Mahaifinsa, sun tusawa ɗanshi Abdullah ƴaƴansu ya aura yaƙi yarda, saboda alƙawarin auren da ke tsakanin Abdullah da ƴar Yayar Mahaifiyarsa Aysha da suka taho tare da ita. Babu yadda su ka iya, haka suka haƙura Abdullah ya auri Aysha. Daga wannan lokacin ne suka ƙara duƙufa wajen ganin bayan Ubaidu ko ta halin ƙaƙa, da suka ga sun kasa, sai suka bishi har Gida suka yi mai kisan gillar da ya tashi hankalin mutanen Yankin. A lokacin Iyalinshi Mahaifiyar Abduh Dhahab Nanaah tayi ƙururuwar abi mata haƙƙinta amma babu wanda ya saurareta sai ɗanta Abduh Dhahab da ya tayata fafutuka, sai dai shima a lokacin ba shi ƙarfin yin komai. Baƙin cikin hakan yasa ta tattara kayanta ta bar Yankin Tudu aka nemeta aka rasa. Shima Abduh tattara komai nashi ya yi ya bar masaurata zuwa Gidan ɗaya daga cikin gidan da Mahaifinsa ya gada a wajen Abdulyasar Dhahab tsakiyar Talakawa. Daga wannan lokaci Abduh Dhahab ya barrata kansa da masaraurar Yankin Tudu, ya dawo kamar kowanni ɗan gari. Ba bu tsinke daga dukiyar Ubaidu da ba su ga bayanshi ba. Duk da wannan abubuwan da suka faru Ɗayyib da yake nunamai tsananin ƙauna ya na tare da shi. A sabuwar Unguwar da Abduh ya dawo ya yi sababbun Amanai, Mallam, Mahaifin Malik da kuma Mahaifinki Mahmoud, duk da sun girmewa juna a shekaru hakan bai hana amintarsu saboda hali da ya zo ɗaya. Abduh ya na da buri mai zurfi, da kuma kishin Yankinsa, ya na son ya kawowa Yankinsa cigaba, kamar yadda Kakanshi da Mahaifinshi sukayi yunƙuri Allah bai ƙaddara ba. Wannan dalilin yasa ya fara tunanin mai zai ƙirƙiro sabo da zai kawowa Yankinsa cigaban da kowa zai amfana??? Abduh ya share sama da wata ya na tunanin abinda zai ƙirƙiro amma ya kasa samun mafita. A wani dare Ubangiji ya sanya masa tunanin ƙirƙirar Tukwane. To amma ai akwai mutane ma su ƙera Tukwane da yawa, ƙirƙirarsu kaɗai ba zai zama wani sabon abu da zai ja hankalin mutane ba, dole sai ya haɗa da wani sabon abinda mutane ba su san da shi ba. Har ya gama saƙe-saƙensa a wannan rana bai samu mafita ba. ★washe gari har Iyalinsa Aysha da ke ɗauke da tsohon ciki ya tuntuɓa itama ba bu wani basirar da ya zo mata. A haka Abduh ya ƙara shafe wata ya na tunanin abinda zai sa Tukwanensa su zama ma su jan ra'ayi da kwaɗayin mallakar su a wajen Mutane. Ya na cikin wannan tunanin sana'ar Kakanninsa na Zinare ya faɗo mai. Mai zai hana ya yi wa nashi Tukwanen laƙabi da Tukwanen Zinare, ya tambayi kansa, hakan zai zama sabon abu a wajen mutane, kuma abin rububi domin ko da mutum ba shi da niyyar siya zai so ya ga yaya Tukwanen Zinaren su ke, daganan wataƙila yaji sun yi mai ya siya. Da ya yi shawara da iyalinsa ɗari bisa ɗari ta amince, amma daga baya da ta fuskanci ɗan abinda ya rage mu su suke samu su ci, su sha Abduh yakeson kwashewa ya kafa sana'ar Tukwane sai ta nuna sam bata yarda ba, dama can lallaɓawa takeyi ta gaji da talaucin da suke ciki shine yanzu zai ƙara kwashe abinda ya rage ya yi jarin Tukwane da shi. Da lallaɓawa da kuma nuna mata gagarumin nasarar da zasu samu, cike da yaƙini Aysha ta amincewa Abduh. Da zallar basirar ƙere-ƙeren da ya koya a wajen a Abokansa na bakin Kasuwar Iyakar Yankin Tudu, Abduh ya ƙera Tukwanen da ya yiwa laƙabi da Tukwanen ZINARE zuciyarsa cike da ƙwarin gwiwa da kuma yaƙinin ko bai siyar ba a take wata rana zai siyar. Lokacin da mutanen Yankin suka ga Tukwanen da Abduh ya ƙera dariya suka bushe da shi haɗe da faɗin " Abduh ya zo da abinda ba shi da wani amfani zai zallar yaudara, shikenan dan Kakansa da mahaifinsa sunyi kasuwancin ZINARE sunyi arziƙi, sai ya ce shima sai ya yi, to ai zasu ga waɗanda za su siyi waɗannan ruɓaɓɓun Tukwanen na sa, wai Tukwanen ZINARE tunda ya ɗauka kowa Mahaukaci ne irinsa." Tsaf surutansu yake dawowa kunnen Abduh, ya na kuma sukarsa, sai dai ba shi zaisa ya ja da baya ba, sana'ar Tukwanen Zinare ba gudu ba ja da baya. A ranar ta farko da Abduh Dhahab ya fita da Tukwanen Zinare Kasuwar maƙotan Yankinsu ba bu wanda ya siya, da ya tarkatosu ya dawo Gida sai mutanen Yankin suka dinga yi masa dariya. Matarshi Aysha da baƙin ciki ta kwana, dalilin haka ta tashi da naƙuda washe gari. A hannun mai maganin gargajiya Aysha ta haifi Sulaim. Kallon fuskar jaririn kaɗai ƙarfin gwiwa yake ƙarawa Abduh Dhahab haka Aysha domin bai bar komai na Kakarshi Mahaifiyar Abduh Nanaah da basusan inda take ba, kamar ita ta haifeshi. Da yawa idan suka shigo Barka da hassadar kyan jaririn suke barin Gidan. Tsahon lokaci Abduh Dhahab ya cigaba da gwagwarmayar fita da Tukwanensa Kasuwanni ba tare da gajiyawa ko ƙosawaba. A haka ya shafe shekaru biyu ya na wannan bautar babu wani cinikin arziƙi. Matarshi Aysha ta sha yunƙurin guduwa saboda talauci ya na lallaɓata ta haƙura. A cikon shekaru na biyar ɗin da ya yi yana bautar bin Kasuwanni Allah Ya amshi roƙonsa aka siye Tukwanensa tsaf, har da neman ƙari. Addireshin Yankin Tudu yake ta basu tare da yi musu alƙawarin ƙera wasu Tukwanen ma su yawa ga waɗanda suka nuna su na son sari domin siyarwa. Lokaci da rana Abduh Dhahab ya tsayar mu su, tare da alƙawarin ba za su bar Yankin Tudu ba tare da iya adadin Tukwanen Zinaren da suke buƙata ba. Da tsananin farin ciki ya nufo Gida, sai dai ya na zuwa ya tarar Aysha ta gudu, sai Sulaim da ya tarar da takarda a hannu. Abduh ya yi kuka shi da Ɗanshi kafin su haƙura su fuskanci rayuwarsu da sam babu walwala a ciki. Ba ji ba gani Abduh ya ke ƙera Tukwane. Ranar da ya rage saura kwana biyu ranar da ya yi alƙawarin kafa Kasuwar Tukwanen Zinare ya cika bai runtsa ba kwana ya yi kaiwa Allah kukansa.... Wane fata kuke yiwa Abduh Dhahab da masu irin zuciyarsa??? SASAAL 09 ★Washe gari Abduh ya tuntuɓi Abokanansa su Ɗayyib, Mahmoud( Mahaifin Naila), Mallam da Mahaifin Malik su fito da Kayan sana'ar su idan da rabo sai su sayar batare da sunyi wahalar bin Kasuwanni da suka saba ba. Ga mamakin Abduh babu wanda ya yi yunƙurin tankamai, kamar ma ba su san abinda ya ke faɗa ba. Kunya suke ji su fitar da Kayansu azo ba'a siya ba ayi mu su dariya. Mahmoud Madinki ne, kayan yara da na manya dinkakku yake bi Kasuwanni yana siyarwa, Mallam kuma Qur'ani da littafan addinin musulunci yake fansarwa, Mahaifin Malik kuma maganin gargajiya yake siyarwa. Ɗayyib ne kawai baya sana'ar hannu taƙamaimai sai abinda ba'a rasa ba. Da Abduh ya fuskanci inda suka dosa sai ya nuna kamar bai damu ba, amma har cikin zuciyarsa baiji daɗi ba. Da yaƙini Abduh ya share ƙaton filin Ubaidu Mahaifinsa da kaɗai ya rage filinsa basu wawashe ba, ya jere Tukwanen da ya ƙera. A gefe ya shimfiɗa buhu shi da Sulaim suka zauna bakinshi bai gajiya ba da ambaton Sunan Allah. Har lokaci ya fara tafiya babu wanda ya zo daga waɗanda sukayi alƙawarin zuwa. Mutanen Yankin sai suka fara leƙoshi su na dariya, bai nuna ya gansu ba, balle su gane abinda suke yi mai yana sukar zuciyarsa. Yunwa da ƙishi ne yasa Abduh Dhahab yunƙurin miƙewa tunda yasan ko yunwa zai kashe Sulaim ba zai yi magana ba. Har ya miƙe hayaniyar mutane daga nesa ya dakatar da shi. Fuskokin mutane ƙalilan ya gane a cikinsu amma ragowar duk yawon kasuwannin da ya gamayi bai taɓa ganin su ba. Waɗanda sukayi alƙawarin zuwa siyan Tukwanensa ne, bakin Abduh kamar zai yage wajen tarbar su, kafin shuɗewar hour ɗaya sun yi ciniki sun siye Tukwanensa gaba ɗaya. Mutum ɗaya a cikin su ne ya tambayi ina zai samu fansar Qur'anin akan sari?. Abduh Dhahab manta abinda su Mallam suka yimasa ya yi, ya nufi hanyar Gidajensu da sauri kamar zai tashi sama, batare da tunanin za'a iya sace masa Ɗansa ko dukka kuɗin cinikin da ya yi ya zuba a ƙarƙashin buhu ba, shi dai burinsa ya kira Abokansa ayi musu ciniki. Jiki na rawa, Mahmoud da Mallam da Mahaifin Malik suka nufo Kasuwar Tukwanen Zinare da Kayansu. Da rububi akan siye kayan har sai da suka ƙara komawa Gida suka ɗebo wasu. Mahaifin Malik ne kawai maganin gargajiyarsa ta ɗan yi ragowa. Bayan Kasuwa ta tashi kowa ya adana kuɗinsa bakin kowannen su a washe, sai suka ɗaga Abduh Dhahab sama suna dariya jindaɗi da waƙeshi da waƙe kala-kalan da ke nuna jarumtarsa da dagiyarsa. Daga wannan rana Abduh Dhahab ya kafa Kasuwar Tukwanen ZINAREN da kafatanin mutanen Yankin su ke amfana da shi. Bayan komai ya dai-daita Abduh Dhahab ya fita wani Yankin ya auro Mairam. A dalilin Mairam Mahmoud ya ga Mahaifiyar Naila ya aura saboda yawan zuwa Gidan da takeyi, kafin daga baya Abduh Dhahab ya haramtawa Mairam shiga ko ina, don dalilin shigarta Gidan Mahmoud ne aka fara samun masu zugata, ta dinga yi masa Satar kuɗi tun da baya bata sai tayasa aiki.. Halaccin Abduh Dhahab yasa Mahaifin Malik ba shi Malik ya dinga yi masa hidima, tunda lokacin Sulaim ba shi da ƙarfin da zai taimakawa Abduh da wasu hidindimun. A sirrince ba tare da sanin kowa ba Abduh Dhahab ya ƙirƙiri Makarantun boko da na Islama da Asibitoci a Yankin da taimakon abokanan kasuwancinsa na Babban Birnin Abyad, amma babu wanda ya sani nima Mahmoud ne ya sanar da ni ko Ɗayyib bai sani ba. Ya damƙa amanar komai a hannun Mallam ne saboda shi kaɗai ne mai ƴan uwa masu ƙarfin arziƙi a Babban Birnin Abyad da Sarki Hammam da mutanen gari zasu gamsu taimakon daga garesu yake, amma a baɗini Mallam ko ƙofar Gidajen Ƴan uwan nasa bashi da matsayin zuwa. Abduh Dhahab ya yi hakane don kawar da idon mutanen Masarautarsu akan lamuransa duk da sun san yana samun kuɗi amma ba su isa su ƙiyasta iya adadin abinda yake samu ba. Abin mamakin duk da wannan girman halaccin na Abduh Dhahab ga mutanen Yankinsa bai sa sun ɗagamai ƙafa ba, a wasu lokutan sai su ce "ai Mahaukaci ne, banda Mahaukaci wanene zai zaɓi sadaukar da iya Gadon da Mahaifinsa ya barmai domin ya yi suna ya burge mutanen gari?" Babu wasu kalmomin su na ɓatanci da baya dawomai amma bai taɓa damuwa ba domin yasan a sannu zasu gane ranarsa. Mutanen Yankin Tudu a ɓangaren halayya mutane ne ma su son kansu, butulci da rashin damuwa da damuwar Ɗan uwansu. A ɓangaren siffa kuma Usul ɗinsu suna da kyan fuska da haske fata, manyan idanuwa buɗaɗɗu, yalwataccen kashin kaa da kaurin jiki, mafi akasarinsu ba su da tsaho daga gajeru masu faɗi da jiki sai masu matsakaicin tsaho da kaurin jiki, idan kaga mutum da siffa saɓanin wannan to Mahaifiyarsa ko Mahaifinsa ba asalin ɗan Yankin Tudu bane. Kamar dai ke Naila baki da irin siffarsu sai irin gashin kansu haka Sufyan ɗan wajen Ɗayyib shima ba laifin yana da tsaho da ginannan jiki amma duk da haka ya sirko da irin ƙibarsu da idanuwansu, dukka saɓanin Sulaim ku ke domin Sulaim ba shi da siffa ɗaya na mutane Yankin tudu kalar fatarsa idanuwansa, tsayuwar ginannen jikinsa tun yana yaro dukka ba irin nasu bane, shi yasa suke ganin a kaf faɗin Yankin babu Matashin da daya girma a raye zai shafe Tarihin duk wani Matashi ɗan ƙwalisa a Yankin Tudu. Sai shima Malik irin hasken fatarsu da idanuwansu ya ɗauko amma sam siffarsa tsayuwarsa kamar sun aroshi daga Mahaifiyar Abduh Nanaah da Sulaim yake kama da ita. Wannan dalilin yasa Abduh ya ke son Malik har ranar da waɗanda ba'asan su waye ba, sukayi nasarar kaishi ƙasa. Wannan shine asalin labarin Abduh Dhahab da Masarautar Yankin Tudu, sai kuma abubuwan da suke waɗanda ba ni da sani akai ```DOWAWAR LABARI``` Idanuwan Naila da suka ɗanyi jaa ta lumshe tana ƙara ƙanƙame hannun Kaka, itama Kaka ƙara ƙanƙame hannun Naila tayi cikin kuka ta cigaba da magana; "Su na kashe junansu abisa son zuciyarsu, ba tare da wani haƙƙi ba. Ba su taɓa nuna ƙin bare ya shigo cikinsu kai tsaye ba sai a kanki Naila, saboda talaucinmu. Shiyasa nakejin tsoro da fargabar kar kema su kashemin ke a banza, domin bani da ƙarfin gwiwa da dukiyar da zan jaa da su." Da ƙarfin gwiwa Naila ta girgiza mata kai tana rungumeta cikin taushin lafazi ta ce; "bazan mutu ba har sai lokacina ya yi, idan kuma lokacina ya yi ko ba na cikin Masarautar Yankin Tudu Allah zai ɗauki raina Kaka, batun cewa a'a ko ki kai kanki gaban Sarki Hammam abisa ƙin amincewarki duk mu haƙura mu gayawa Allah, In Sha Allahu zai sauƙaƙa mana." Da haka sukayi barci hannunsu ƙanƙame da na juna. ★washe gari Kakar Naila ta tattauna da Ƴan uwan Mahaifin Naila kan su bawa Iyayen Sufyan haƙuri Naila ta kammala Makarantar sakandare tunda saura wata bakwai. Da yake babu Allah a lamuransu sai suka taso mata bakinsu a haɗe, acewarsu su kansu basu da tacewa duk abinda Shugaba Ɗayyib ya yanke dole shi zasu haƙura su bi. Zuciyar Kakar Naila na tafasa ta nufi Gidan su Sufyan kai tsaye. Bayan sun gaisa Kaka ta koro bayanin abinda ke tafe da ita.. Wani irin kallo Hindu take yimata da soyayyun idanuwanta da suke ƙananu a tsaitsaye farare ƙal. Murmushi ta yi kafin ta ce; "Haba Ummu Habeebah(Kaka) ai da baki zo da kanki ba, Ni dai ina neman afuwarki akan abinda ya faru shekarun baya, sannan na fuskanceki amma bazan iya yanke hukunciba tunda Maigida Jalal( Mahaifin Ɗayyib) shi ya tura mutane da kanshi nemarwa Sufyan auren Naila. Ki bari Mahaifin Sufyan ya dawo In Shaa Allahu zan isar da saƙonki" godiya Kaka tayi mata tana yunƙurin miƙewa. Da sauri Hindu ta dakatar da ita ta hanyar faɗin; "Bari na kawo miki abun motsa baki mana" kai Kaka ta girgiza haɗe da cewa; "bakomai Hindu, fuskantata da kikayi yafi komai yimin daɗi, Allah Ya ƙara arziƙi" duk da haka Hindu bata bar Kaka tabar Gidan batare da abinda tayi niyyar bata ba. Dama kuma tuntuni ta tanadeshi ne domin tasan har gaban abadan Mahaifiyar Habeebah bazata taɓa ƙaunarta ba. Bayan Ɗayyib ya dawo Ko zancen Hindu bata yi masa ba, sai shirye-shiryen tafiya Babban Birnin Abyad da suke yi domin duba Gidan da Sufyan zai zauna da Naila saboda a gaggauce takeson ayi komai duniya tasan tasan da zaman ɗanta. A ɓangaren Kakar Naila bayan ta koma Gida ajjiye Tufar da Hindu ta bata tayi a gefe, ta na bawa Naila labarin abinda ya faru. Murmushi mai tsayawa a iya saman laɓɓa Naila ta saki zuciyarta a raunane. Da nishaɗi Kaka ta ce "kinji daɗi ko ba ki ji ba Naila?" Naila sai da haɗiye abinda take ji sannan ta ce "na ji daɗi Kaka Allah Ya biyaki da Alkhairin Sa" Kaka ɗauke kanta tayi tana amsawa da "Amin". Da yammaci aka turo ana sallama da Naila, ba ta tsaya ɓatawa kanta lokaci ta zura doguwar rigar da aka yiwa ado da saki baƙi da malulluɓinsa. A tsaye ta hango Sufyan, ya yi ado cikin ƙananun kayan da suka dace da siffarsa, fuskarsa ta maza masu raina mutane na tsaye ƙyam akan ƙofar Gidan su. Mutanen Yankin kowa ya wuce sai ya waiwayo ya ƙara kallonsa shi kuma yana ƙara hura siririn hancinsa. Tsaf yake ƙarewa Naila kallo haɗe da wassafa yadda zamansu zai kasance, tana da komai da yakeso dangane da Ƴa mace abu ɗayane kawai ya yi mata cikas a wajenshi shine rashin zamantowarta ƴar hamshaƙai ko wayayyiyar Babban Birni. Ya na son ƴar masu kuɗin ba irin Naila ƴar Madinka jikar Madinka ba. Ƙarasowarta ne ya dawo dashi hayyacinsa, da girmamawa ta gaishe shi, ya amsa yana tattare girarsa, har ya fara hura hanci sai ya tuna da hudubar Mahaifiyarsa; na ya sakarwa Naila fuska har ya samu ayi auren. A take ya saki ranshi yana janta da hira cikin aji da kamewa. Daga "eh, a'a, uhm" sune amsoshin Naila. Sufyan kamar ya shaƙeta yana ji a ransa maiyasa bazata ɗago ta kalleshi ba kamar zata lashe shi, ko dai itama har yanzu fuskar Matacce Sulaim bai bar zuciyarta ba? Tuna wannan kaɗai sai da zuciyarsa tayi bugawar daya ɗan dafe ƙirjinsa, jin kansa da ƙarin tsanar Sulaim na dirarmasa lokaci ɗaya. Tarin sumar kanshi ya shafo cikin isa da ɗacin dayake ji a cikin zuciyarsa ya ce " ki shiga Gida, ba ni da wani shagali da zanyi kamar yadda bani da lokacin ƙara dawowa gareki, ina fatan zakiyimin kyakkyawar fahimta" ya yi tunanin zata ji babu daɗi tayi magiya da nuna zumuɗin son dawowar kyakkyawan Matashi irinsa wajenta amma sai ya ga ta ɗaga kai alamar da gamsu. Kafin ta kai ga barin wajen tuni ya tashi lafiyayyen mashin ɗinsa ya baɗeta da ƙura. Kai Naila ta girgiza mamakin abinda ya tunzurashi na kama zuciyarta. Kaka bayan fitar Naila ta janyo Tufar da Hindu ta bata kamar ana fizgarta ta ɗauko ta wanke ta soma ci, har Naila ta shigo tana gutsirar Tufar suna hira a hankali. Tana gama ci barci ya ɗauketa. Da mamaki Naila take kallon yadda ta kwanta a jirkice kafin ta gyara mata kwanciya ranta cike da mamaki. ★washe gari Ɗayyib da Hindu suka ɗauki hanyar Babban Birnin Abyad, sai da sukayi kwanaki a hanya. Maimakon Babban Birnin Abyad ɗin su yi niyyar kama gida sai a Birnin Abyad suka kama, saboda zaman Babban Birnin Abyad da kuɗin Makarantarsu yafi ƙarfinsu amma sun yanke shawarar ba zasu gayawa Sufyan ba idan ya zo ga ne wa idanunsa. Su da suka tafi da sunan kama hayar shekaru uku daƙyar suka samu mai sauƙi shima ba da asalin tsakiyar Birnin Abyad yake ba suka kama na shekara biyu. Sai guntun kuɗin da suka adana don biyan kuɗin Makaranta Sufyan idan sun samu sun haɗa da wani. Saboda Hindu shawarar siyar da ragowar kadararsu ta yanke idan ta koma. Har suka iso Gida labarin kyan ƙasar Abyad bai bar bakinsu ba, shima Sufyan tuni ya fara tada kafaɗa zuciyarsa da kanshi tsabar yanda yakejin girmansu gani yakeyi kamar gangar jikinsa ba zai iya ɗaukar su ba. Domin shi a yanzu yafi ƙarfin duk wani Matashi a Masarsutar su bama Yankinsu kaɗai ba tunda ko Ƴaƴan Sarki Hammam mace ɗayace ta taɓa Aure a can shima bawai cikin Babban Birnin Abyad ɗin ba ne daf da shine. A ƁANGARENSU NAILA; Har gari ya yi haske Kaka bata motsa ba wannan dalilin yasa Naila ta birkitota da ƙarfi, idanuwanta ta gani a kakkafe. Cikin yanayinta na nutsuwa ta fara ambaton Allah kafin ta nufi Gidan Yayyan Mahaifinta. Kwanan su biyu ana yiwa Kaka maganin gargajiya taji sauƙi amma magana kam sai a hankali, sai ta wuni batace komai ba ko baifi tayi sau ɗaya ba, tanason bawa Naila labari da yunƙurin daƙile Hindu. Saboda kai tsaye ta fuskanci Hindu ce ta bata Tufa mai ɗauke da sirihin da zai duƙufar da ita ayi komai batare da ta iya yin yunƙurin komai ba, amma ba bu hali. Sai dai tayi ta hira da zuciyarta. Naila tayi kuka musamman da zancen zaman Aurenta a Babban Birnin Abyad ya cika lungu da saƙon Yankin. Har shishigi Ƴammatan Yankin suka fara yimata da fadanci kullum suna Gidan. Daga wannan lokacin Naila ta fuskanci dole ta auri Sufyan, musamman idan tanaso ta tsira da lafiyar Kakarta domin itama ta gane Tufar da Hindu Mahaifiyar Sufyan ta bawa Kaka ya mayar da ita haka. Kakarta tana cikin wannan yanayin Masarautar Yankin Tudu suka fara gudanar da shagalin gagarumin bikin da ya tashi kan mutanen Yankin, har ma da maƙotan Yankunansu. Da ido da hannu Naila take magana da Kaka kuma ta fahimceta, duk shagulgulan da suka yi, ɗaya aka gayyaci Naila da ƙawayenta ƴan shishigi sai ƴar Yayan Mahaifinta Laila. Sufyan ya yi kyau kamar ka sace ce shi ka gudu murnar tafiya Babban Birnin Abyad na ƙara haukata kanshi yanajin inama da Kabeer yana nan ya nuna masa shi ba'asan yinsa bane, kuma ba da iyakacin Shugabancin Kasuwar Tukwanen Zinare suka dogara ba. Wani irin kyau Babban Birni Abyad yake da shi har Sufyan da bai taɓa zuwa ba yakewa zumuɗi???...✍🏻 [7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: 🔥ZINARE🔥 NAFISA ALIYU SASAAL *CHAPTER 2* *TAFIYAR NAILA DA SUFYAN BABBAN BIRNIN ABYAD* Pg 10 NAILA; A dai-dai lokacin da mutanen Yankin su ke ji inama da su ne zasu tafi Babban Birnin Abyad Naila na maƙale da Kakarta ranta ba daɗi. Gabannin sallar magrib Malamin da ya ke yiwa Kaka rubutu ya aiko da shi. Kaka da ke cikin matsanancin damuwa saboda abubuwa ma su muhimmancin da takeson sanarwa Naila amma babu hali laƙwas tayi idonta ƙyam a kan dogayen yatsun Naila da ke juyemata rubutu a kofi. Kanta Naila ta kamo bata saketa ba har sai da ta gama sha. Yunƙurawa tayi ta miƙe, sai dai ko taku ɗaya ba ta yi ba ta ji Muryar Kaka na ambaton sunanta "Naila" Da sauri ta juyo cikin mamaki kafin ta rungumeta da ƙarfi haɗe da kai mata sumba a gefe da gefe ƙuncinta. Da tsananin farin ciki ta ce; " na ji daɗi sosai Kaka fargaba da komai ya gushe da ga gareni tunda ga shi kin faɗi sunana sosai Allah Ya cigaba da karemin ke Kaka" Kaka da tsananin farin ciki ta amsa da "Amin" sai dai bayan amsawarta ƙwallane ya cika idanuwanta da su ƙyam a kan Naila. Ta yunƙura zatayi magana Naila ta dakatar da ita, ta hanyar girgiza mata kai. Amma duk da haka bayan wasu daƙiƙu sai da ta numfasa cikin karyewar zuciya ta fara magana; "Kafiyata da nuna ikona ba za su yi tasiri a garemu ba, tunda tun kafin muje ko ina Hindu ta fito mana da manufarta ƙarara. Amma Allah Ba ya barci Naila, da ƙarfin mulkinSa zuwanki ƙasar Abyad babban nasara ne a gareki, makircinsu shine matakin nasararki In Shaa Allahu." maganganun Kaka sun ƙarawa Naila ƙwarin gwiwa a kan wanda take da shi, har tanajin zata jurewa duk wasu ƙalubale da zasu biyo bayan zaman auren su da Sufyan. A haka suka raba wannan dare su na hira saboda washe gari Naila za ta bar Gidan, mafi rinjayen hirar ta su a kan Tufar da Hindu ta ciyar da Kaka ne da kuma shawarwari da dabarun zaman Gidan Miji. ★washe gari da sassafe Dangin Mahaifin Naila su ka zo ɗaukarta, saboda sunfi son a zo ɗaukarta a inda su ka tsara. Kaka bata tanka ba sai rungume Naila da ta yi bayan ta sumbaci goshinta. Cikin ƙarfin halin danne kukan da ta ke yi ta ce; "Ki kula Naila, inanan ina jiran dawowarki wata rana da dumbin nasarar da zaki zamemin abin alfahari da Mutanen Yankinki gaba ɗaya, ki mayar da hankali kan sana'arki saboda sana'ar kitso baiwane mai girma a ƙasar Abyad. Daga ƙarshe ki tuna da shawarwarina, haƙuri, juriya da biyayya sune matakan nasararki" daga haka Kaka ta saki hannun Naila da ke kuka kamar zata shiɗe. Barin Gidan Kaka zuwa Gidan ƙannen Mahaifinta ya tabbatarmata da ta bar Gidan Kaka kenan sai kuma wata rana idan da rai da lafiya. Bayan sun kai can zagaye ta su ka yi kowannen su na faɗar albarkacin bakinsa da sunan nasiha. Ba bu nisihar Kawunnanta ɗaya da ya shigeta saboda kallon maƙiya ta ke yi mu su, kamar yadda su ka nunamata ƙiyayya a zahiri. Ba ya tabbatar da ita cikakkiyar Marainiya ba ce, sai da dangin Mahaifinta su ka miƙata Masarautar Yankin Tudu. Sufyan ya na zaune a tsakankanin Iyayensa, wannan ya tunamata da nata Iyayen dalilin haka sai kukanta ya ƙaru, takaicin yadda ƴan uwan Mahaifinta su ka dinga ƙasƙantar da kansu duk don samun wajen zama a wajen Ɗayyib kamar ya kasheta. A ranar ta zagaya Masarautar Yankin Tudu ta kuma tabbatar da kyansa da mutane su ke zuzutawa, har gaban Sarki Hammam sai da ta kai gaisuwa. Bayannan aka miƙata ɓangaren da zata kwana. Bata shafe hour biyu da kwanciya ba Matasan mata ma su kusan shekaruna su ka shigo, da alama turosu akayi don tayata kwana. Ba su san ba barci ta ke yi ba su ka fara hira. Cikin jimami ɗaya ta ce; "Ai ni na jiyo abinda yafi ƙarfina, ni dama na yi zargin Uwar gida Hindu bazata taɓa yarda wannan makirin ɗan nata ya auri ƴar ƙaramin Gidan da su ke talakawan fitik ba sai da wata manufa" Cikin rashin yarda ɗayar ta ce "Ni kam sam na kasa yarda da zancenki Ƙawata, ta ya ya zata sadaukar da dukiyarsu da ake zuzutawa a kan abinda ba ta da tabbaci a kai, anya kuwa kin jiyota da dakyau?" "Wallahi tsaf na jiyota, ke harda sharaɗi ta ce ta kafamai, karya kuskura ya kusanci Matar kar a haifo mu su ƙasƙantaccen jika, ya bari su ga kalar ɗaukakar da zai samu." Naila tana jin su suka kwashe da dariya haɗe da tafawa, kafin ɗayar ta ƙara cewa; "To wallahi ki adana wannan dogon bakin naki idan ba haka ba shi zai kai ki ya baro kin ji na gayamiki." Da sauri ta damƙi bakin na ta kafin ta saki su ƙara kwashewa da dariya. Daga kwancen da Naila take jikinta ya fara rawa, gumi da zazzaɓi su ka lulluɓeta lokaci ɗaya. Kuka mara sauti mai fitowa tun daga ƙasar zuciya na zuwar mata, ƙwarin gwiwarta na bin iska. Ta ɗauki lokaci tana kuka mara sauti kafin wahalallen barci ya fara ɗaukarta, har barci ya ƙarasa ɗauketa ba su daina tattaunawa ɓoyayyun sirrinkan da su ka shafi Masarautar ba. ★washe gari da ta farka da su tayi tozali su na barcinsu hankali kwance, daga yanayin suturun jikinsu ta gane ba Bayi bane Ƴaƴan Gida ne. Shagali na musamman aka ƙara shiryawa kafin tafiyarsu Ƙasat Abyad. Faɗa sosai Jalal kakan Sufyan da Mahaifinsa Ɗayyib su ka yimata. A ɓangaren Mahaifiyar Sufyan Hindu faɗar hannunka mai sanda tayimata mai surke da baƙaƙen maganganun da ke nuna ba Mata ta aurawa Sufyan ba Baiwa ta auramai. A gabanta ta ƙara jaddadawa Sufyan Umarninta, wanda bata raba ɗayan biyu akan hirar da taji ƴammatan jiya su na yi ne. Ba bu wani mai faɗa aji a Masarautar Yankin Tudu da baiyimata nasiha ba, wa su na su nasihar ta lallami suka yi mata wa su kuma gori da nuna iyaka ne kai tsaye. Daga haka Drivern da zai kaisu iyakar Yankin Tudun da zasu hau Motar ƙasar Abyad ya ƙaraso. Sufyan da ke sanye cikin tsadadden farin yadi mai taushi, malalacin murmushin da ke nuna jin kanshi ya saki haɗe da ɗagawa Mutanen Yankin da su ka yi kirco-kirco su na washe baki hannu. Idanuwansa a kan Mahaifiyarsa suka tsaya daga ƙarshe, alamar jinjina ya yi mata kafin ya shigo Mota ya na gyara zamansa a gefen da Naila ta ke. Da sannu da sannu motarsu ta fara motsawa har lokacin mutanen Yankin na ɗaga musu hannu, kukan da Naila take ɓoyewa ya bayyana saboda tuna Mahaifana da Kakata da na san tana can tana kuka. Naila ta bar Yankin Tudu da tarin rauni da tabo a cikin zuciyarta, ko yaya zamanta a ƙasar Abyad zai kasance?? Kuyi manage [7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: .🔥ZINARE🔥 SASAAL 11 Duk kukan da Naila ta ke yi, Sufyan ya na jinta amma bai ce kanzil ba. Sai da ya fuskanci ba kukan ganin ido ba ne na gaske ne, sannan cikin isa da izzar fitarshi zakka a kaf faɗin ahalinsa saboda samun nasarar tafiya ƙasar Abyad yin karatu ya ce; "Kukan na menene? Kinsan ina zakije kuwa? Dan Allah karki ɓatamin farin cikina, ke da ma baki da Iyaye, ko ni da na ke da Iyaye a raye bandamu sai ke. Kar ki bari tun kafin tafiyarmu ta yi nisa ki fara saɓawa umarni na kinji na gayamiki" da ga haka ya ɗora farin yatsun hannunsa da bai san wahalar komai ba a saman dogayen yatsun Naila. Maganganunq sun soketa irin sukar da Marainiya ƴar uwa ta ce kawai za ta san zafin su, saboda ƙara jaddada matan da ya yi da gaske bata da Iyaye don haka bata da abin yiwa kuka. Bata ƙara ko da tari ba sai idanuwanta da ta lumshe tana jin yadda Drivern Motar su ya ke kwarara gudu. A tashar da zasu hau Motar da zai yi tafiyar kwanaki kafin isarsu ƙasar Abyad Drivern da ya ɗaukosu ya sauke su. Hannun Sufyan maƙale da nata, ya je ya siyamusu tikiti, suka shiga ƙaton Mota mai ɗaukar fasinja da yawa zuwa ƙasar Abyad. Ba su jima a ciki ba bayan sunci abinci, aka fara sanarwa tashin motar da komai na cikinsa ya ke kamar na jirgin Sama. A gefen Sufyan ta ke zauna, kamar zai sumbaceta haka ya sunkuyo da sunan ɗauramata belt. Bayan ya ɗauramata ya ƙara kamo hannunta ya sarƙewa da na shi. Murmushi mai ciwo ta saki a cikin zuciyarta, tana ganin ba lallai Sufyan ya cika alƙawarin da ya ɗaukarwa Mahaifiyarsa ba. Tafiyar su bana yini da kwana ba ne tafiyar kwanaki ne, saboda da su Sufyan hamshaƙan ma su arziƙine da jirgin sama za su biya masu ba mota ba. Duk inda zasu tsaya ba bu magana a tsakaninta da Sufyan sai kayan guzurin da Mahaifiyarsa ta zubamai a ƙaramin Akwati mu ke ci akai-akai. ```BIRNIN ABYAD``` Lokacin da Motarsu ta iso Birnin Abyad, yanayin sanyin ƙasar, hasken Mutanen ciki, gina-ginensu, da wasu irin motoci ma su kyan gani a ido da kwaɗayin son shigarsu ne su ka haske mudu idanuwa. Idanuwan Naila da ta ke jinsu kamar madara saboda haske a Yankinsu sai ta ke jin su a Birnin Abyad kamar sun koma jajaye saboda kyawun mutanen Birnin da take gani da gine-ginen su. Sai ta ke hasaso Yankinsu kamar wani kusurgumin daji mai duhu da ya ke da ƙaracin kayan more rayuwa. Fatarsu da na ke ganinsa mai haske da kyau a Yankinsu a take ya dusashe a idanuwanta ya koma sak na ƴan karkara, ƴan karkarar ma su ƙarancin komai na cigaban rayuwa. A maganganunsu ta fuskanci ba sa kai ƙarshen zance sai sun haɗa da harshen nasarar da Malaminsu yake ta kwaɗaitar da su, su koya. Wa sun su kuma nasarar kawai su ke yi babu sirki. Tunano yadda Mutanen Yankin Tudu su ka dinga ɗago musi hannu lokacin tahowarsu sai tausayin su ya ƙara tsargamata musamman Kakarta da Mahaifanta. Mahaifinta ya ƙare rayuwarsa a dinki ƙarshe rashin gatan Asibiti ya yi sanadiyar ajalinsa, haka Mahaifiyarta. Kakarta ce dai ba ta cire rai tare da Yaƙini haɗe da fatan wata rana ta zo taga duniyar Birnin Abyad ba. A ɓangaren Sufyan shima ji ya yi duk ya muzanta, wannan jiji da kan da sumarsa da ya tara duk domin ya zo ya Yaƙi Ƴammatan Birnin Abyad sai ya bi ruwa, ya na jin inama da yana da hula a kusa ya lulluɓe gashin saboda Kunya. Farin fatar da ya ke yiwa Mutanen Yankin Tudu yanga da shi sai ya ga ashe da sauransa, Kananun kayan da idan ya sa a Yankinsu maza da mata su ke bi su na kallo har da tuntuɓe sai ya tashi kamar na ƴan Karkara. Lambar wayar wanda zai kai su gidan da Iyayen Sufyan su ka kama musu ya zaro a ƴar ƙaramar jakar da ya ɗauko ya na yanga da shi a Yankin Tudu saɓanin isowar su Birnin Abyad da ya ɓoyeshi a hammata. Cikin ƙarfin hali ya tambaya aka nunamai wajen kira. Shi kanshi sakayayyen wajen kiran da aka sakaye da gilashi abin a yaba ne. Naila Nutsuwar ya ne ya ta taimaka wajen sakaya gidadancinta, saɓanin Sufyan da dama can ba wani cikakken nutsuwa ce da shi ba, dan dole ya ƙaƙabawa kanshi nutsuwar dole kamar ba Sufyan Ɗan gidan Ɗayyib shugaban kasuwar Tukwanen Zinare ba😂. Ba su wani jima ba, Uban gidan Ɗayyib mazaunin Birnin Abyad ya zo ɗaukarsu. Sai da suka tashi hawa Motar inda zamu je Makka ta fahimci ABYAD sunan ƙasar ne Birnin Abyad kuma shine inda aka sauke su kuma anan Mahaifan Sufyan su ka kama Gida, BABBAN BIRNIN ABYAD kuma shine asalin Babban Birnin da kaf faɗin ƙasar ba bu kamar shi. To idan har Babban Birnin Abyad da take ji a bakin Mutanen Yankin Tudu ya fi inda suke ciki kyau da tsari to ya ya kyansa da mutanen cikina za su kasance??? Naila ta tamabayi kanta, lokacin da suka isa inda zasu shiga Mota. Bayan sun shiga motar da za ta kai su Gidan da aka kama musu, idanuwanta su ka faɗa kan Motocin da akace su ne masu shiga Babban Birnin Abyad, ko da batayi karatu mai zurfi ba, bata kuma saba riƙe kuɗi ma su nauyi ba tasan ba motocin shigar mutane ne irinsu ba. Tafiyar Motocin take kallo tana jin kamar ta fito ta bi su. Sai ta ke jin kamar tana ƙewar abinda ita kanta batasan menene a inda za su je ba, tana kallon tafiyar motocin wani yanayi na tsarga zuciyarta, haka ta yi taji har Motocin suka ɓacewa ganinta. Kasa jurewa ta yi ta tambayi wanda ya zo ɗaukarsu; " hour nawa ne tsakanin Birnin Abyad da Babban Birnin Abyad" Amsar "hour biyar" ya ba ta tare da shaidamata mutum zai iya zuwa a ranar ya dawo a ranar. Sufyan da ya ke tunanin ta yi tambayar ne domin ta nuna Iyayensa ƙarya suke yi, da su ka ce sun kama mai Gida a Babban Birnin Abyad harara ya watsomata ya na cije baki. Unguwar su da Gidan da aka kama musu abun a yaba ne, duk da ba ta jin komai akan Sufyan na soyayya ko makamancin haka sai da ta ji ya ɗan birgeta, saboda gida ne da bata taɓa mafarkin zata kwana a cikin irinsa ba har ƙarshen rayuwata. SUFYAN; Da Sufyan ya yi tozali da living room da two Bedrooms ɗin da su ka sha kayan ado dai-dai misali a matsayin hidimar da Mahaifansa su ka yi mai sai ya ji kwaɗayin son karya alƙawarin Mahaifiyarsa akan Naila na bin iska daga gangar jikinsa. Da farko kafin tahowar su ya yi zargin ashe dukiyar da ake zuzutawa Kakansa na wajen Uwa ya mutu ya bari duk ƙaryane, banda ƙarya ne tayaya za'ace da dukka wannan dukiyar da wanda Mahaifinsa ya samo akayi hidimar kamamai Gida ba ma Siyamai ba da biya masa Makaranta a Birnin Abyad? Sai da ya gani da idonsa sannan ya tabbatar da dagaske ba ƙananun dukiya ba ne za su zaunar da mutum a unguwar da aka kama mu su Gida ba.( a nasa ganin kenan, domin a wajen masu zuzurutun dukiya, gadon da ake taƙamar Hindu tana da shi, bai wuce kuɗin kashewar mai arziƙi a yini biyu ba). Idan har Mahaifiyarsa za ta yi irin wannan sadaukarwa saboda ɗaukakarsa ba tare da damuwar komai ba, to ba bu abinda zai hana shima ya sadaukar mata da na sa farin cikin. Amma duk da haka dole ya rage zafi, domin ba zai iya kwana ɗaki ɗaya da Naila ya tashi da ita ba tare da ya rage zafi ba. Gidan ba su su ƙadai ba ne, mutum huɗu ne a Gidan amma kowa rayuwarsa yake yi, ba tare da damuwa da rayuwar Ɗan uwansa ba. NAILA; wanka ta yi ta ƙimtsa jikina. Sai a lokacin taga kamar ta ɗanyi kyan gani, saboda dattin Motar da ta wanke daga jikina. Ɗakin da Sufyan ya bata a matsayin nata take ƙarewa kallo, nutsuwa na saukarmata. Cikin baƙaƙen Abayoyin da ta taho da su masu adon saƙi ta shirya ta tayar da Sallah ta inda ta ga an shimfiɗa abun Sallah alamun nan ne gabas. Bayan awannin; Uban gidan Ɗayyib ya hidimta musi ƙwarai da jikinsa da lokacinsa har ma da kuɗin aljihunsa. Abinci mai daɗin da basu taɓa ci ba ya siyomusu Da Suturar sawa kala biyu da ya siyo Sufyan don fara zuwa Makaranta sai wayar hannu da layi a ciki shima mai kyau dai-dai misali. A kunyace Sufyan ya sa hannu ya karɓa ya na ƙara tabbatar da ashe ba shi kaɗai bane ya raina kayan jikinsa ba dagaske kyan ne ba su da shi. Da yake saukar Safiya suka yi bayan sunci abinci, Uban gidan Ɗayyib ya yi mu su Sallama da sunan washe gari zai dawo. Barci ya kwashe kowannensu a ɗakin da ya ke. Ba su farka ba sai azahar shima babu wanda ya fito a cikin su tunda kowanne da abinci da zai ci a na dakin. Sai wajen ƙarfe 9 da ƴan mintina na dare Sufyan ya shigo ɗakin Nsila. Gaisheshi ta yi ta ƙara gyara lulluɓin kanta. Wayo da kuma shekarun da Sufyan ya fita yasa ya fara goge maganganun ƴan matan da ta ji a Masarsutar Yankin Tudu. Da farko kusa da ta ya matso ya zauna saboda ya lura kamar ta na da sani ko hasashe a kan abinda ya ke ranshi. Cikin taushin lafazin da lumshe idanuwansa da su ke tsaye ƙyam a kan fuskarta ya ce; "Na san surutai da yawa za su yi ta zuwa kunnenki Naila, amma iyakacin wannan Gidan da kuɗin motar da Iyayena suka kashe mana ya kamata ace kin watsar da surutun auren manufa akayimana da ke, Mahaifiyata Mace ce mafaɗaciya kuma tana tsananin so na wannan dalilin yasa ta kuɗiri niyyar auramin matar da zata bauta min kamar Sarki da Baiwarsa, amma kisani Naila har cikin raina ban zaɓe ki domin kisha wahala a Gidana ba, sai domin muyi zaman aure ki bani goyon baya ɗari bisa ɗari akan karatu na. Mun zo nan ga shi kuma kuɗin Mahaifana ya ƙare a wannan hidimar da suka yimana, kuma a halin yanzu ina buƙatar suturun sawa kuɗin hidindimun makaranta da kuma abinda zamu ci Naila." Naila da batasan sanda ta ɗago kanta ba, idanu ta zubamai domin sam bata fahimci ina ya dosa ba. Fahimtar hakan ya sa ya cigaba da magana cikin ƙaramin sauti. "Naila da Baiwarki zaki taimakamin Ni kuma na yi alƙawarin mayar da ke mace ƴar gata a cikin ƴan uwanki Mata." Still Naila bata fahimci ina ya dosa ba don haka ta ƙara gyara zama. Da kame-kame ya ce "ina so ki bi dukka Gidajen Unguwarnan ki sanar da su kina kitso, a kwai ma su ra'ayin kitso a cikin su, da wannan kaɗai zaki taimakamin Naila na roƙeki" Dan jim Naila ta yi maganganun Kaka na dawo mata "ki mayar da hankali kan sana'arki saboda sana'ar kitso baiwane mai girma a ƙasar Abyad." Cikin yarda da rauni irina ƴa mace Naila ta ɗaga kai alamar ta gamsu ko dan Kaka tayi alfahari da ita. Da sauri Sufyan ya rungumeta kafin ya yi dabarar ragewa kanshi zafi, Bayan wani ɗan lokaci ya tattara ya bar ɗakin. NAILA; Da murmushin raɗaɗin da marata yakemin na mirgina na kwanta, abinda Sufyan bai sani ba zuciyata Macacciyace ba bu rai balle a yaudareta, da sha'awa yana da yare da ko ya taɓani baza ta ji komai ba sai dai bani da ikon hakan. "Idan ƙarya yakemin domin ya zalunci ne Allah Shi ne gatana," daga wannan hirar zucin Barci mai nauyi ya ɗauketa...✍🏻 [7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I1wZrvGJP2s3QIyUuJ4ig7?mode=r_c 🔥ZINARE🔥 SASAAL 12 ★washe gari bayan nta yi sallar Asubahi bata koma barci ba, har sai da gari ya yi haske. Barcinta bai yi nisa ba, Sufyan ya tasheta. Da kayan da aka siyomai jiya ya yi ado, ya yi kyau dai-dai misali domin baza ta ce sosai ba, a matsayinsa na Mazaunin Birnin Abyad. Bayan ta gaishesa ya ji bataƙara da komai ba sai ya haɗe rai ya na ƙara shafa wuyar Rigarshi. Sam bata fahimci ina ya dosa ba, sai da ya yi tsaki haɗe da faɗin; " Anya kuwa Naila ki na da lafiyar ido, na san babu Macen da za ta ce banyimata ba, amma ke kullum sai ki dinga nuna kamar Ni ɗin ba wani mai kyau ba ne, ko Hassada ki ke yimin?" ya tambaya da iya gaskiyarsa haɗe da murza zoben silver da ya ke matuƙar ji da shi. Dariya ƙeta musamman a kan mugunta ba halinta ba ne, amma da ta ƙaremai kallo na tuna irin siffar Mutanen da suka gani a lokacin da suka iso Birnin Abyad sai da ta dara har jerarrun haƙwarana su ka bayyana. Tunda ta ke bata taɓa ganin Namiji mai son ace mai ya na da kyau ba irin Sufyan domin ko Mace albarka, "shi kuma kalar jarabawarsa kenan." Ta faɗa a cikin ranta amma a zahiri miƙewa ta yi kafaɗunsu na gogar na juna ta ce; "Kai kyakkyawane ko ba ka yi kwalliya ba, balle yanzu da kayi ado da kayan da aka siya a Birnin Abyad, Godiya ta tabbata ga Ubangijin halittun da ya halicci Namiji kyakkyawa irinka Mijina." Dariya da bata taɓa gani ya yi irinsa ba ya saki, ya na kamo fuskarta, sumba ya saukemata a goshi tsabar daɗin da yake ji har wani lumshe ido yake yi yana binata da kallo kamar zai lasheta. Sallama ya yi mata, Har ya fita ya ƙara dawowa ya na jaddadamata alƙawarin da ta yi mai. Bayanshi ta bi da kallo maganar Kaka na faɗomata; " ko wani Namiji da kalar halinsa, halin Mijin wata ba zai taɓa zama irin naki halin Mijin ba, dole a samu banbanci duk ƙanƙantarsa, don haka ki karanci halayyar Mijinki saboda samun sauƙin zama da shi." Ta gazgata zancen Kaka a kan Sufyan saboda duk daɗin soyayya ko kwalliyar da Mace za tayi domin ta ja ra'ayinsa ba ya ɗaɗashi da ƙasa a kan ta zauna ta na zuzuta kyansa da yaba kwalliyarsa sama da kyan da ya yi. Kamar yadda nta alƙawartawa Sufyan da maƙotansu da su ke cikin gida ɗaya ta fara, ba ta jin turancin arziƙi amma kuma hakan bazai daƙusar da ƙudirinta ba. Ko da kwatacce ne da haɗe-haɗen iya wanda ta iya zata yi mu su bayani har su fahimta. Biyun dukka Mata ne kuma tayi sa'a dukkansu gashinsu na kitsawa ne amma ɗaya kai tsaye ta shaidamata bata da ra'ayin yin kitso saboda zafi ya ke mata. Cikin ƙanƙan da kai kamar ta saba da ita ta kwantantamata ta zo ta gwada yimata hannuna ba shi da zafi. Ga mamakinta cikin raha ta ce to ta je around 2:00pm na dawo. Abinda Ruwaida Maƙociyarta ta ce mata na ta je ta dawo ya ƙaramata ƙarfin gwiwar tunkarar ko ina domin tallata sana'arta. Mutum na ƙarshe a gidansu Namijine ɗan asalin ƙasar Abyad fatarsa fara fat. Ta na shiga Sashensa Da sauri ta fito duk kiran da ya ke ƙwalamata bata juyo ba, tama jiyoshi ya na dariya da alamun mamakin Gidadancita ya ke yi. Duk Gidan da zata shiga Daƙyar ake barinta, wasu su yimata tarba mai kyau wasu kuma su wulaƙantata. Gida na ƙarshe kuma mafi kyau a layin shi ta tunkara sai dai kai tsaye dakarun da su ke gadin Gidan su ka hanata Shiga. A gajiye na dawo Gida, saboda ba laifi ta yawatu, ba kuma komai yasa ta dage ba, sai don sauya tunanin Sufyan daga wanda Mahaifiyarsa ta ɗorashi a kai. Kamar yadda Ruwaida ta ce ta dawo ƙarfe biyu haka ta koma akan lokaci. Yanayin ɗiban kitson da yadda ya kwanta a saman farin tafin kan Ruwaida ya yi matuƙar ƙayatar da ita ga shi sam ba zafi, godiya tayimata da tsananin farin ciki a saman fuskarta. Da Ruwaida ta tashi sallamarta, da iya adadin kuɗin a ke biyan makitsa a Birnin Abyad ta biyata, nutsuwarta ce kawai ta riƙe Naila. A lissafin kuɗin da tayi zuwa na ƙasarsu, ko Iyalan Sarki Hammam da ake matuƙar ji da su, suke biyanta da kuɗi ma su ƙauri ba su taɓa bata kwatankwacinsa ba. Ƙwalla ƙwance a ƙasan idanuwanta ta ke yiwa Ruwaida godiya. Dariya Ruwaida ta saki cikin mamakin yadda Naila ta damu ta tambayeta daga ina take? Saboda ta ƙara tausayamata ta naimomata customers, Naila ta fara ba ta labarin ita da Mijin tane su ka zo, ya zo Karatu ne kuma kuɗin iyayensu sun ƙare shine suke neman kuɗin cin abinci da sauran buƙatun rayuwa. Dafata Ruwaida tayi cikin tausayawa ta yimata alƙawarin zata naimo mata mutanen da zata dinga yi musu kitso ta na samun kuɗi amma na tambayi Mijina shin zai barta zuwa Gida-gida yin kitso? Naila ba ta zaɓi yanke hukunci ba tare da ta tambayi Sufyan ba, don haka ta ce ta bari na yi shawara da shi idan ya dawo. Daga haka dukayi sallama kuɗinta ma ƙanƙame a hannunta. SUFYAN; Lokacin da su ka isa Jami'ar Birnin Abyad da Ubangidan Ɗayyib ya yi cuku-cukun samo masa ya yi mamaki tare da ƙaƙabawa zuciyarsa cika alƙawarin Mahaifiyarsa babu gudu babu ja da baya. Bayan sun gama yin komai. A ranar ƙarfe 12:00pm Sufyan ya fara ɗaukar lectures saboda tuni su ka fara ba bu shi. Bayan sun gama lecture Harabar Makarantar ya fito ya naimi wajen zama, tunanin kuɗi da yadda zai yi kalar rayuwar da zai samu Mace wayayyiya ƴar Birnin Abyad ɗin da zai yaƙi mutanen Yankin Tudu da ita na ya zauna yi. Ya na cikin wannan yanayin wata matashiya mai kyan gaske ta raɓa gefenshi ta zauna. Sanye take cikin ƙaƙanun kayan Saint Laurent riga da wandon da suka amshi farin fatarta sai lulluɓin da ya lulluɓe iyakacin wuyarta bai sauko kafaɗunta ba. "Barka dai kyakkyawan Matashi, sunana Sumaya, kai fa?" Ta faɗa da harshen nasara mai ɗauke da cikin wani irin sanyi murya tana miƙamai hannu. "Kyakkyawan Matashin" da ta faɗa ya fi bugar da kan Sufyan a kan kyan fuskarta. A ƙiyastin da ya yi a cikin daƙiƙu zata yi sa'ar shekaru da shi, babu wani abu mai kyau a saman fuskarta da gangar jikinta da Naila da take cikin talauci bata da shi currently. sai wayewar da ta fi Naila da kuma hasken fatarta mai tsananin haske sosai. Cikin salo da yadda ta birgesa har cikin ransa da jin nan take ya samu Abokiyar rayuwa ta zahiri matsawar ba ta fi ƙarfinsa ba ya ce; " Barka dai ya ke kyakkyawa Sunana Sufyan na ji daɗin haɗuwa da ke" ya ƙarasa faɗa yana damƙar hannunta. Daga haka kamar wasa hira mai cike da aji da zuzutawa kyansa irin yadda ya ke buri da ga Naila batayi ya ɓarke a tsakaninsu, har da musayar lambar waya. Kan Sufyan bai ƙara ɗaukar zafi da kwaɗayin mallakar dukiya ba sai da yaga Sumaya har ɗan ƙaramin mashin mai kyau take da shi, ba irin na shi na Yankin Tudu ba. Da aka tashesu Da sakin fuska ta yi masa tayin hawa, ba tare da ɓata lokaci ba ya ɗane. A hirarrakin su kafin su isa Gida Sufyan ya fuskanci Sumaya ba wata ƴar ma su kuɗi ba ce a Birnin Abyad, naiman kuɗi ne ya kawo Mahaifanta har su ka haifeta a nan ta kuma yi dacen samun scholarship a Makarantarsu. Ran Sufyan fari fes Sumaya ta saukeshi a layin Gidan su, kamar kar su rabu haka su ka yi sallama, Sufyan ya nufi hanyar Gate ɗinsu da ƙayataccen murmushi a saman fuskarsa. NAILA; Wanka ta yi taƙara shirya kanta cikin abayar ta dai mai adon saƙi, sai dai ba baƙi ba ne kamar ragowar. Ta na ƙoƙarin shiga kitchen don duba abinda zata iya dafawa daga Abinci da Ubangidan Ɗayyib ya kawo mu su, ta ji ana knocking. ƙofar ta nufa da saurinta, tana buɗewa taga ashe Ruwaida ce, kanta ba bu kallabi da alama bata da mu dashi ba duk da kasantuwarta cikakkiyar Musulma. Mazubin abinci mai kyau ta gani a hannunta. Cikin gwari-gwarin Turanci da zata fahimta Ruwaida ta shaidamata Abinci ta kawomata sannan gobe idan Mijinta ya amince ta shirya zata kaita wani Gida a ƙarshen layinsu da zan ta yi kitso. Godiya mai tarin yawa Naila ta yi mata sannan su ka yi sallama. Bayan Naila ta koma ciki Kasa taɓa abincin ta yi, ta zauna zamam jiran dawowar Sufyan su ci tare. Sufyan; Da murmushi a saman fuskarsa ya ƙwankwasa Naila ta buɗe mai ya shigo, yana ganinta ya kalli Abayar jikinta sai ya sauya fuska. Har cikin ranta bata kawo komai ba, sai ɗaukar da ta yi masa a matsayin bauɗaɗɗen mutum mai saurin fushi. Fuska ba walwala ya amsa gaisuwata haɗe da sumbatar ƙuncinta kamar yadda al'adar Yankinsu ya ke. Ruwan wanka ta nufi hanyar ɗakinsa domin haɗa mai ya dakatar da ita, ya miƙe ya shige har da mirzo mukulli, ita dai Na'ilah ba ta damu, ta dawo ta zauna Bayan ya fito ta gabatar masa da Abincin da Ruwaida ta kawo musu, ba bu tambayar ina ta samo? Ta ci ko ba ta ci ba? Ya zauna ya take cikinsa sai kaɗan da ya ragemata. Jiki a sanyaye ta ɗauka ta ci ranta babu daɗi. Sufyan fahimtar sauyi a fuskar Naila yasa ya fara ƙorafin ai bai san bata ci ba, kuma maiyasa ma ba tasa hannu sunci tare ba? Batace mai komai ba, amma na ɗan ji sanyi a raina yadda ya nuna kulawarsa. Bayan ta gama ci ta kai kwanukan madafi, ta fito da kuɗin da Ruwaida ta bata, da kuma naiman izininsa akan Gidan da ta ce zata kaita, ga mamakinta Sufyan ƙanƙameta ya yi yana dariyar nishaɗi, ba tare da wani jinkiri ba ya fara kasafta kuɗin. "Naila kuɗinnan kawai abinda ya kamata shine na ƙara riga ko kala ɗayane ragowar kuma na samu na cin abinci a Makaranta Kinga yau ma da yunwa na wuni. Allah Ya yi miki albarka Naila" ya ƙarasa faɗa yana shafa duk inda hannunsa ya kai. Tambayar izinin fitarta gobe da ta tambayesa murya na rawa ya ce ya amince ya na ƙara samata albarka. Cikin dabara da girman zaluncin rashin tunanin halin da zan faɗa idan tasa buƙatar ta biya ya fara ragewa kanshi zafi, har sai da yaji ya gamsu dai-dai misali sannan ya tattara ya yi daƙinsa ya bar Naila a wajen. SUFYAN; Bayan ya shiga ɗakinsa wanka ya ƙarayi fuskar Sumaya da ya ke maƙalemai a cikin zuciyarsa na wasa da nutsuwarsa, sai ya ke ganin anya batafi Naila kyau ba? Dariya ya saki ya na lalubo wayarsa. Ba shi da kati kamar yadda ya sanar da Sumaya don haka ya zauna zaman jiran kiranta. Kiranta ya na shigowa ya yi maza ya ɗaga. Sun jima su na hira kafin su yi sallama ran kowannen su fari fes. Sumaya da Sufyan soyayyar da zai kai su ga aure sukewa junansu, duk da yinin su ɗaya da haɗuwa. Sumaya tana ganin ta samu Talaka irinta tunda Sufyan ya gayamata Karatu ya zo yi da Yarinyar da Mahaifansa su ka dage sai sun aura mai kar ya zo Birnin Abyad ya na neman Mata, idan ya so duk ranar da ya gama Karatu ya saketa idan kuma ya ji yana sonta to su cigaba da zamansu, shi kuma baya sonta ba kuma zai iya rayuwa da ita bayan ya gama Karatu ba. Ɗari bisa Ɗari Sumaya ta yarda da zancen Sufyan. Shima Sufyan gani ya ke yi Sumaya itace Macen nunawa. Mace ƴar Birnin Abyad mai kyan sifa da tarin ilimi kuma ba ƴar talakawar fitik irin Naila ba. Tabbas! Mahaifinsa Ɗayyib zai yi alfahari da shi Kuma Tarihi zai maimaita kansa domin kamar yadda Marigayi Ubaidullahi Dhahab ya dawo Yankin Tudu da tarin dukiya da kuma zankaɗeɗiyar Matar Aure haka shima zai koma Yankin Tudu da tarin Dukiya da kuma Sumaya a matsayin Matarsa..✍🏻 [7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I1wZrvGJP2s3QIyUuJ4ig7?mode=r_c 🔥ZINARE🔥 SASAAL 13 Har Dare ya yi Sufyan bai ƙara fitowa ba, dama ba wani damuwa ya yi da nemi Masallaci ba, kuma ya riga ya cika cikinsa.. NAILA; Ba ta damu da rashin fitowar Sufyan ba tayi kwanciyarta bayan ta shiga Madafi da samawa cikinta wani abun.. ★washe gari bayan Sallar Asubahi ba ta koma barci ba kamar jiya. Bayan ta gama azkar ta tashi na ƙimtsa ko ina. Abinci mara nauyi ta dafa musu, ta jere a kan teburin cin abinci. Da ta tabbatar komai ya kammala sai ta koma ɗakinta domin yin wanka. Sufyan ranshi fari fes ya tashi, saboda mafarkin ya zama hamshaƙin mai Dukiya sanadiyyar Sumaya. Bai koma barci ba, sai dai ba zama Karatun Alkur'ani ko azkar ya yi ba, wanka ya shiga. Har Naila ta kammala girki gaban madubin washroom ya na kallon kansa, fatarsa kuwa tsabar dirza da soso a tunaninsa hakan zai sa ya ƙara haske, har zafi ya ke mai. Duk motsin Naila ya na jinta har ta kammala ta wuce daƙi. Da sauri ya fito ya cinye kusan dukka abincin, yanajin alamun fitowarta ya tattara ya fita da sauri. NAILA; Lokacin da ta fito ta ga son zuciyar da Sufyan ya aikata bata yi mamaki ba, saboda tana san ran zai iyayin sama da haka matsawar hudubar Mahaifiyarsa bai bar zuciyarsa ba. Ragowar ta ƙarasa cinyewa, bayan abincin ya ɗan sauka ta nemi waje ta kwanta tana jiran zuwan Ruwaida. Misalin ƙarfe ɗaya da rabi na rana Ruwaida ta ƙwanƙwasa ƙofar sashensu. Da hanzari Naila ta lulluɓe sumar kanta har zuwa ƙasan kafaɗuna da yalwataccen malulluɓi. Da fara'a sosai na tarbe Ruwaida. Kamar dai jiya ba bu lulluɓi a ƙanta sai ƙaramin scarf ɗin data nannaɗe gashinta da shi. Ba ta karɓi tayin shigowarta Sashen su ba ta ce ta taho su tafi. Su na tafe su ɗan hira har su ka kusa kai wa ƙofar Gidan da ya yi matuƙar birge Naila, amma jiya da ta je zata shiga tallata kitsonta aka hanata shiga. Nunawa Ruwaida gidan tayi haɗe da yimata bayanin abinda ya faru. Da farko dariyar da ya sa ta ɗan ranƙwafawa Ruwaida ta yi kafin ta ƙara kallon Naila ta kuma sakin murmushi, da sauƙin turancin da ta san zan fahimta ta ce "Karki ƙara zuwa saboda ba wajen zuwanki ba ne" "Saboda me?" Naila ta tambaye Ruwaida da mamaki kwance a saman fuskarta. Babu wasa a saman fuskar Ruwaida ta ce; "Gidan Simbi ne, Matar Uzair. Ahalin Shahararren ɗan kasuwa a Babban Birnin Abyad, ta zo gudanar da wani bincike ne a Asibitin jami'ar mu. Rayuwata ba bu sakewa sam, yawan zuwanki da sunan makitsiya zai iya janyomiki matsala don haka ki kula." Naila jigum ta yi mutum ɗaya ta taɓa ji da irin sunan a Yankinsu, kuma itace ƴar autarsu Malik uwa ɗaya uba ɗaya. Don haka faɗar sunanta sai ya dawomata da tunanin abinda su ka faru shekarun baya. Simbi sun bar Yankin Tudu ta na yarinya ƙarama ta girmemata da Shekara ɗaya. Naila a ranta ta ce; "Nasan ma ba ita ba ce domin babu yadda za'ayi ko Malik da ya ke Babban yayansu ya mallaki irin wannan Gidan a Birnin Abyad balle ita." Bata ƙara cewa Ruwaida komai ba har suka zo giftawa ta dai-dai saitin Gidan. Naila ba ta da ciwon ido balle ta ce shi ya haddasamata ƙarancin gani, fitowar Mota mai ɓakin gilashin da akayi ƙasa da shi kaɗan saboda ɗagawa dakarun da su ke gadin gidan hannu ne yasa Naila tayi baya kafin ta saki ƙarar da ya ja hankalin har na cikin motar ya ɗago kai saitin da suke kafin ya zuge gilashinsa gaba ɗaya ya fice daga layin. "SALMAN!" Naila ta faɗa a sarari, sai kuma ta tuna Salman to ai ya mutu, tun shekarun baya, to idan ba Salman ba ne wanda ta gani yanzu a Mota to wanene wannan? ko ƙaninshi ne? Ta tamabayi kanta. Da hanzari Ruwaida ta tarota ta na faɗin "Naila! Menene ya sameki, kinsan shi ne? Ko bakyajin daɗi ne mu koma gida?" Razanarta Naila ta shanye ta miƙe tsaye ba tare da bin bayan Motar da kallo ba ta ce; "Na shiga razani ne sai na ke ganin kamar na sanshi" Ajiyar zuciya Ruwaida ta sauke kafin ta ce "ohh Allah! Naila kin bani tsoro to ai mutane ma su kamaceceniya su na da yawa a duniyar nan ki kwantar da hankalinki kinji?" Kaina Naila ya ɗaga mata alamun na gamsu. Gidan da suka je dukka su ƴammatane su biyar kuma abokanan karatun Ruwaida. da alama Makarantarsu a kusa da nan yake. Jarumtar Naila da son ta tara kuɗi domin cikawa Kaka burinta yasa ta yi juriya kitsa mu su gashin kansu dukka irin na Ruwaida ta yi mu su. Waje ɗaya suka haɗamata kuɗin da ya sanyaya rainta ta ji zazzaɓin da ya ke shirin rufeta ya sauka. Ba su wani jimaba bayan ta gama yi mu su suka bar Gidan. Yanayin shiru-shirun da ta koma lokaci ɗaya ya sanya Ruwaida itama cikin damuwa. Dalilin haka ya sa bayan sun kai ta ja Naila ɓangaren kafin Sufyan ya dawo. A kan kurajerun living room ɗinta ma su taushi Naila ta lafe tana kallon shige da ficen Ruwaida daga parlo zuwa Madafi. Cikin yanayinta na barkwanci Ruwaida ta ce Naila ta taso taa tayata girki. Naila ta na shiga idanuwanta suka sauka a kan Tukunyar girkin Ruwaida, sunan jiki ne yasa ta ƙarasa kusa da Tukunyar da sauri, "DHAHAB" ne rubuce a jikin Tukunyar kuma tare da sunan a ka ƙera Tukunyar ba sticker aka manna ba. A take zuciyarta ta yi bugawar da ya sa na jingina da bango ƙwaƙwalwarta na tariyo mata shekarun baya. Ruwaida da raha ta ce " kema Tukunyar ya birgeki ko?, ai Kamfanin ahalin su Simbi ne, Yayana a can ya ke aiki shi ya yi min kyautarsa ranar murnar zagayowar haihuwa ta, kinsan kuwa nawa ake siyar da Tukunyar nan, Tukunya ne mai matuƙar tsada, Ni kaɗai ce mai shi a cikin ƙawaye na, Tukunya ne da Sarakuna da ma su dukiya su ke girki da shi, shi kanshi Yayana da yake aiki a can da albashi shi muke rayuwa da ahalina a wadace, kinga kuwa ai ba ƙananun kuɗi ba n.." zubewar Naila ƙasa kamar gini ne ya dawo da hankalin Ruwaida da ke surutun Tukunyar Dhahab kanta. Hankali a tashe ta ja Naila da ƙyar zuwa living room. Sashen Dr. Yasar moƙocinsu da Naila ta gudarwa Ruwaida ta nufa. Da taimakon Yasar Naila ta dawo hayyacinta ko da su ka tambayeta abinda ya sameta ta faɗi bata ɓoye mu su abinda ya rikita ta ba. Bayan ta gama ba su taƙaitaccen labarin Yakinsu Ajiyar zuciya dukkan su, su ka sauke. Har cikin ranta Ruwaida ta yarda da gaske kamanceceniyar Mutumin da Naila ta gani sak Salman da Tukunya mai irin sunan Abduh Dhahab ne kawai su ka rikitata a matsayinsu na mutanen Yankinta ba tare da wani alaƙa ba a tsakaninsu ba, saɓanin Yasar da ya kasa yarda Naila ba ta da haɗin komai da abinda ya rikitarta sai alaƙar Yanki kawai. Sai gabannin la'asar Ruwaida ta taimakamin na koma sashena. SUFYAN; Bayan sun fito daga lecture, Sumaya ya sa rakasa ya zaɓo kalar rigar da take so. Sauƙin kayan sawar Ƙasar Abyad da abincin cin su ne yasa itama ya siya mata irin rigarsa su ka yi anko, ragowar kuɗin kuma abinci ya siya mu su mai lafiya suka ci suka ƙoshi, ɗan canjin da ya rage ya loda kati saboda kiran Mahaifinsa Ɗayyib. A ɓangaren su Ɗayyib da Hindu lokacin da Sufyan ya kirasu ya basu labari sun sa masa albarka tare da nu na tsananin jin daɗin yadda Naila ta fara samun kuɗin da zai yi karatunsa hankali kwance, saboda Ɗayyib ya shaidamai bayan tafiyarsu da kwana ɗaya akaci Kasuwa bai san dalili ba sam babu cikini. Bayanin Mahaifinsa sam bai ɗaga mai hankalin ba, tunda ya samu Naila ta fara sana'ar da su ke samun kuɗin shiga. Bai ba su labarin haɗuwar sa da Sumaya ba saboda ya san bazasu ba shi goyan baya ba, za su ce yayi wuri ya ɗakata shi kuma abinda ba ya son ji kenan. A wannan yini da Sufyan da Sumaya su ka ƙarayi a Makaranta, shaƙuwa mai ƙarfin gaske ya ƙara shiga tsakaninsu. Kowannen su ya na jin ya yi dace da Abokin rayuwa dai-dai burinsa. Kamar jiya ita ta koshi har bakin Layi. NAILA; Bayan ta dawo kasa aikata komai ta yi, barcin ma da ya ɗauketa a zabure na miƙe saboda mummunar mafarkin da ta yi, wai ga Salman ya biyota zai ciremata harshe. A take wani irin tsoro da kaɗaici ya soma tsargata. A haka Sufyan ya shigo ya same ta. Bai tantace muryata da kuka ya dusasar ba, balle kayan jikinta da batayi wanka balle ta sauya su, kuɗin da'aka biyata a wajen kitso ya tambaya bayan ya zauna. Dama su na gefeta, don haka ta ɗauko ta miƙamai. Da ƙarfi ya ce "Allah! Naila sannu da aiki, Naila idan na gama Karatu na samu aiki sai kinfi kowa jindaɗi, kuɗin da kika ba ni yau ma riga ɗaya kawai na siya da shi, haka na wuni da yunwa. Yanzu kinsan mai za'ayi zan ɗauki kuɗinnan na ƙarasa siyan kayan sawa kinga mun gama da wannan, ɗan abin ya rage kuma na riƙe kuɗin makaranta ko ya ya kika gani, ko da yake bari na tashi na je yanzu saboda gobe lecture 7:00am zan shiga." Ya ƙarasa faɗa ya na miƙewa. Kafin Naila ta ahaɗiye hawayenta tuni Sufyan ya fice, ko tambayar dalilin da ya sa ban tayi girki ba baiyi ba. Sufyan ya zaɓi zuwa ya siyo ba tare da jiran gari ya waye ba ne saboda Sumaya karta sa ran zai kuma siyamata wa su kayan. Ko tsinke baiyi hikimar siyawa Naila ba tunda itama kayanta duk Abaya ne ma su arahar gaske ga adon da aka yi mai na saƙi sak na ƴan karkara. Chocolate kawai ya iya siya da Naila shima kuma sai da ya haɗa da na Sumaya. Daɗin samun komai da sauƙi yasa yake ta murmushi shi kaɗai har ya dawo Gida. Lokacin da Sufyan ya dawo Naila ta ga bai siyomata ko tsinke ba kasa shiru ta yi ta ce; "Ba ka kyauta ba, tayaya zaka siyo kaya iya kai kaɗai bandani? " Da farko da zafinsa ya ɗago amma kome ya tuna sai ya fasa ya fara lallashita haɗe da tambayar abinda ya ke damunta. Da salon dabaru Sufyan ya kalamacata har ya yi nasarar tserewa daƙinsa bayan ya bata abinda ya siyomata. Naila ta so ta ba shi labarin abinda ta gani amma gudun kar ya kira ya fesawa Mahaifiyarshi ya sa taja bakinta ta yi shiru. Daga wannan ranar Sufyan ya ƙara zage damtse wajen yin ado da kaya kala-kala, da zarar ta samu kuɗi zai siyeta da daɗin baki ya karɓe, har Mahaifinsa ya sa ya tura Yaro a kaiwa Kaka waya suka gaisa Naila. Ranar da Naila ta gaisa da Kaka bata runtsaba, saboda tanaso ta bata labarin abinda ta gani da wanda Sufyan yakemata amma babu hali domin zama Sufyan ya yi gadinta da sunan kallon talabijin. A haka rayuwar ta miƙawa Naila da Sufyan, da kuɗin sana'ar kitsonta ya ke komai na Makaranta har ya yi wa Budurwarsa Sumaya hidima, duk Naila bata sani ba, da kuɗinta dai ya ƙara ƙawata living room ɗin su har da ɗakin kwanansa. A ɓangarena Suturar sawa kuwa Naila bata da na arziƙi, idan tayi ƙorafi sai ya ce mezatayi da sutura ita da ba fita na ke yi ba, kitso kawai yake zuwa, shi dama kuma ba ya son idan zataje yiwa Mutane kitso ta yi kwalliya kar wani ya ƙwacemasa ita, shi ya fi son ya ganta ta yi ado da kayan da ta taho da shi saboda hakan na tunamai da Yankinsu. A kwana a tashi Ruwaida ta fuskanci Sufyan cutar Naila yake yi domin kuwa duk ta rame tayi duhu saboda ƙewa da damuwa. Shawarar Naila ta fara ɓoye kuɗinta Ruwaida taba ta, idan sun taru za ta rakata ta siyi suturun sawa, idan Sufyan ya tambayeta ina ta samo ta ce ita ta siyamata da kuɗinta. Bayan kwana biyu Sufyan ya jera kwanaki uku ya na tambayar Naila kuɗi sai ta ce babu, da ya ga dai dagaske ta ke babu kuma aljihunsa ya yi ƙasa sai titsiyeta da tambayoyi, ƙarshe tana Madafi tana girki ya shiga ɗakinta ya bincike har sai da ya samu kuɗin da take ɓoyewa. Ta na tsaye ya shigo Madafi da kuɗin a hannunshi kafin ta yi magana ya kwasheta da mari cikin zafin rai yake masifar yasan Ruwaida ce take zugata, wallahi ta ci darajar itace take naimomata customers da sai ya ci mutuncinta ya wulaƙantata. Sufyan ya yi tunanin ganin sauyi ko wani gagarumin ɓaci rai a saman fuskar Naila, amma sai ya ga akasin haka kamar baiyimata komai ba, cikin neman magana ya ce "gaba zakiyi da ni saboda nayi miki faɗa ko,? to wai Naila saboda wa nakeyin wannan karatunnan? Saboda ke nake da ƴaƴan da zamu haifa, Naila saboda tsoron kar mu zo mu tara ƴaƴa babu kuɗin kula da su yasa kikaga na daure har yau ban kusanceki ba, duk wannan bai sa ki tausayamin ba haba Naila sai a fara zugaki ki na ɓoyemin samunki." Murmushin mai ciwo Naila ta yi ta kalli fuskarshi ta ce; "matacce ai ba shi da ran yin rigima da rayayye, idan kuma kasan yau ai ba kasan gobe ba, dalilin baiwar kitson da Allah Ya bani yasa ku ka kawoni Birnin Abyad, ga shi kana mora har ka na da ƙarfin halin yin iko da shi. Ba ni da ƙarfin yi ma iyaka amma lokaci zai yi maka a yanayin da baka taɓa tsammani ba"....✍🏻 [7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: https://chat.whatsapp.com/I1wZrvGJP2s3QIyUuJ4ig7?mode=r_c 🔥ZINARE🔥 ( ```The Gripping family saga with high Caliber) ``` SASAAL 14 Sufyan sak ya yi a tsaye har Naila ta gama magana ya kasa ce mata komai, har na ɓacewa ganinsa. Bayan tafiyarta kafaɗarsa ya ɗaga A ganinsa mai zai jiyewa takaici? kuɗi ne dai dole ya karɓesu saboda da su ya dogara. NAILA ★washe gari kamar ko yaushe bata koma barci ba, sai da ta gama Breakfast. Ko da koma barci ta farka misalin tara na safe, ta fito Parlo a yadda ta jera abincin haka na samesa Sufyan bai ci ba. Tasan ya yi hakane saboda kuɗaɗents da ya karɓe, a karon farko hawayen takaicinsa su ka zubomata, bata tsawaita zubda hawayenta ba, bata kuma hana cikina abinci ba. Bayan ta ci na ƙoshi na fito harabar Gidan shan iska. Yasar ta hango ya na yunƙurin fitowa, da farko ta yi niyyar guduwa saboda ba ta son haɗuwarsu, amma da na tuna taimakon da ya yi msta ranar da accident ɗin sashen Ruwaida ya faru sai ta jirkirta. Yasar manazarcin halayyar Ɗan adam ne, kuma likita a babban Asibitin Birnin Abyad. Gaishesa kawai ta yi ta matsar da kanta gefe. Matsowarsa kusa da ita ya sa ta juyo tana zare ido. Yadda ta zare ido na ne ya sa shu saki dariya ya na shafa tarin sumar kanshi da ya tattara wajen ɗaya ya ɗaure kamar Mace. Ba bu zato ta ji ya ce; "Maimakon zama haka mai zai hana Mijinki ya naima miki gurbin karatu a jami'ar su, idan ma ba shi da hali ki naimi izininsa ni zan biya miki Fisabilillah." kalamansa sun wanke dattin da ya jima danƙare a cikin ƙwaƙwalwar Naila na tsahon lokaci, maganarsa abun dubawa ne a gareta, kuma shawara ne mai kyau amma tuna Sufyan ya sa ta ce; "mijina ba zai yarjemin ba" ta faɗa da murya da ya bayyana rauninta. Yasar ya kai wa su daƙiƙu ya na kallonta kafin ya murmusa da cewa; "idan Mijinki ya na da sauƙin kishin da zai barki zuwa Gidajen da maza da mata su ke rayuwa, kamar Campus ɗin su Ruwaida kiyiwa Ɗalibai kitso, to babu dalilin da zai sa ya hanaki naiman ilimi. Menene amfanin neman da ba zamu gina gobenmu da shi ba?" Kamar talabijin haka Naila ta zubawa fuskar Yasar mai tsananin haske da kyau ido, ba haskensa da kyansa ta ke kallo ba, gaskiyar da ya faɗa take gani a saman fuskarsa. YASAR Duk da ya san Naila ta gamsu ɗari bisa ɗari kuma ta yarda da maganarsa amma tana kwakwanton naiman mafita sai ya ƙara ce mata; "ga hanya mafi sauƙin warwarewa kanki komai, ki fara naiman izininsa a kan na ce zan biyaki kuɗi mai yawa ki kitsamin kaina, ki ji mai zai ce, idan ya ce a'a sai ki san dabarabar da za kiyi ki tambayesa izinin naimar miki jami'a, idan kuma ya ce eh, kin samu hanyar da zaki tafi Jami'a cikin sauƙi, ki nutsu ki warware komai dalla-dalla za ki fahimce ni da kyau". Cikin nauyin baki Naila ta yi mai godia. Har ya ɓacewa ganinta bata daina kallon hanyar da yabi ba. Yinin ranar a tunani ta ƙaresa domin ta kasa yarda Sufyan ba ya kishinta, shi da ya ce kishin ta ne ya ke hanashi siyamata kaya kar wa su, su ga kyanta, duk da tasan ba ya sonta sosai kamar kuɗin da na ke samu, amma ta yarda da zancensa. Kusantowar lokacin dawowar Sufyan ya sa ta miƙe ta ƙarayin wanka, kayan dai da ta taho da su daga Yankinmu ta saka, duk sun ƙode sun jeme. SUFYAN; Sufyan kayan ciye-ciye da ice cream kala-kala ya siya mu su shi da Sumaya, har sun dawo sunyi lecture ya tuna rashin siyawa Naila kaya zai ƙara tunzura ta, har ta ɓullo da wata dabarar tara kuɗin a inda ba zai gani ba balle ya ƙwata, musamman wajen Ruwaida, kuma siya mata kayan zai kawar da tunanin ba ya sonta ba ya son farin cikinta a ranta. Bai naimi rakiyar Sumaya ba ya tafi, kusan rabin kuɗin da ya ɗaukemata ya siyamata kaya da su ba dan ransa ya so ba. Da ya dawo Makaranta da Kayan Ƙiri-ƙiri Sumaya ta nuna ƙishinta, ranar ko ƴar hirar da su ke yi a kan hanya ba su yi ba, bakinta a gaba take tuƙi, takaici da kishi na nuƙurƙusarta. Ko da ta sauke Sufyan kafin ya yi mata sallama ta figi mashin ɗin ta. Jiki a sanyaye Sufyan ya shigo gida. Da Sufyan ya shigo bai bawa Naila kayan da ya siyo ba, ɗakinsa ya wuce da kayan ransa fal kokwanton ko dai gobe ya kaiwa Sumaya, saboda bai ji daɗin yadda su ka rabu ba. Jikinsa ba kuzari ya tsakuri abincin da ta girka, itama Naila tata fuskar sam ba fara'a. Bayan ta tabbatar ya huta ta sako masa hirar neman izininsa zata yiwa Yasar moƙocinsu kitso tare da bayyana masa irin kuɗin da ya ce zai ba ta. Ga mamakinta Sufyan ko alamar banbanci tsakanin jinsi Namiji da na Mace bai nuna ba yace ai neman kuɗi ne babu Matsala. Zuciyarta da jinina na gudana da sauri-da sauri ta tambayesa izinin komawa Makaranta, kai tsaye ya ce mata; "ba ni da kuɗi, ko kuɗin da kike ba ni kike yiwa baƙin ciki Naila?" Muryarta ta na rawar kukan da ya tahomata tana ƙoƙarin dannewa ta ce; "ance ba sai ka biya ba za'a samomin Scholarship" kamar an tsikaresa haka ya miƙe ya na masifa kamar zai taune harshensa. Sai da ta bari ya gama kumfar bakinsa, sannan ta miƙe haɗe da cewa; "zuwa Makaranta da sunan naiman ilimi sai zama aji ɗaya da Maza, amma kowa da Mazauninsa, ba bu kuma tilas ɗin mu'amalantar juna, iskanci ne. Amma zuwa Gidan da Maza su ke rayuwa da sunan sana'a haɗe da kama kansu na kitsa saboda za su bani kuɗi mai yawa shi ba Iskanci ba ne Sana'a ce ko? Idan ka rayu a matsayin miji a gareni sannan ka zaɓi zaluntata da duƙushemin rayuwa wacce riba za ka samu Sufyan?" Ƙasa ya yi da kansa, ganin ba shi da mafita sai ya fara lallashinta haɗe da garzayawa ɗakinsa a hanzarce ya kwaso kayan da ya siyo mata yake kokwanton ba ta. Kamar zai yi kuka haka yake magiyar gwadata ya ke yi kamar yadda akasarin Maza suke yaudarar Mata da sunan gwaji. A cewarsa idan banda gwadata ya ke yi ta ya ya zai yarda ta yiwa Yasar kitso sai ka ce ba Musulmi ba, shi kansa Yasar ɗin ai ba mutumin ƙwarai ba ne, idan ban da haka ta yaya zai ce Matar aure ta yi mai kitso. Da ire-iren waɗannan kalaman ya so yaudarata. Ba bu daɗin bakinsa ɗaya da ya samu gurbi a cikin zuciyar Naila, amma ta ji daɗin kayan da ya siyomata. Kamar komai ya wuce haka ta nunamai, domin ya ƙara shashantar da ita sai ya fara ragewa kanshi zafi kamar yadda ya saba. Bayan ta koma daƙina kuka da ya sanyamsta ciwon kai ta yi, ba ta da wanda zats buɗewa zuciyarta ta zazzage masa dukka damuwarta sai dai tasha kukanta ita ɗaya a ɗaki. ★washe gari da Sufyan zai fita Makaranta Cikin dabara ya ke ja mata kunnen rage mu'amalantar Ruwaida idan ba haka ba zata kaita ta baro. Abinda bai sani ba Kalaman Ruwaida ga Naila ma su taushi ne haka zuciyarta da niyyarta dukkan ma su kyau ne a kan Naila, idan ma cuta ce Ruwaida ta rasa wacce zata cuta sai irin Naila. Naila Ba ta ce mai kanzil ba har ya bar Gidan. Da ga ranar ta ƙauracewa zaman harabar Gidan saboda Yasar, idan ka ganta a waje to Ruwaida ce ta haɗata da customer, ko kitso idan aka biyota Gida a living room ta ke zama su yi. A hankali a hankali Naila ta fara rama mai busar da Mutum tambayar duniya idan Ruwaida ta yi mata sai na ce mata"ba komai". Sufyan ya haramtamata gaisawa da Kaka kullum sai ya ce ya kira Ɗayyib Mahaifinsa ba ya samu. A kwana a tashi cikin hikimar Ubangiji suka shekara ɗaya da rabi a Birnin Abyad. A ɓangaren Sufyan ya canza ya ƙara haske ya yi kyau sak mazaunin Birnin Abyad, saɓanin Naila ta da ta bushe ta rame idan ta yi dariya sai haƙora su cikamata fuska. Ta ƙara samun customers wa su ta je Gida tayi musu wa su kuma su biyota Gida, duk tarin kuɗin da take samu Sufyan ne yake kwashewa domin akwai ranar da ta ɓoye kuɗi a wajen Ruwaida, har ya titsiyeta da tambaya. Bata ɓoye masa su na wajen Ruwaida ba, a ranar sai da ya yi mata dukkan da ya hanata motsi. Bayan ya fita Makaranta ya kira Mahaifinsa ya yi mai bayani. A take shima ya sanar da Uban Gidansa, washe gari jami'an tsaro mata suka zo har Gidan su ka jawa Ruwaida kunne haɗe da karɓe kuɗin da na ke tarawa, bayannan su ka yi mata tsakani da ni. Ruwaida ta na tsoron abinda zai taɓa karatunta. Ba tare da ta nemi ƙara ganin Naila ko tambaya ta sane abinda aka yi mata ko ba na sane ba, ta tattara Kayanta ta tashi bar Gidan, sai ma su kwashe kayanta kawai Naila ta gani. Tun da ga lokacin sai Naila ta ƙara zama kamar sha-sha-sha. Ga shi Yasar tun da ya ya bata shawara na yi watsi da shi har take gudun haɗuwa da shi ya tattara lamarinta ya watsar ko haɗuwa sukayi ta gaishesa daƙyar ya ke amsawa. Yasar bai ƙara tsanar Naila ba sai da ya ji labarin abin da ya faru tsakanin Sufyan da Ruwaida. Daga wannan ranar ko gaishesa Naila ta yi baya amsawa. Abubuwan da su ka faru da Naila sun sa ta yi losing hope, sai ta ke ganin sakarwa Sufyan komai ya yi iyakacin zaluncin da Allah Ya ƙaddara a cikin rayuwata shi kawai ya fiyemata sauƙi. Da ga wannan dukan farkon da Sufyan ya yimata ya mayar da ita kamar jaka, akan abu ƙalilan sai ya zaneta, ɗai-ɗaikun ranaku ne baya kai hannunsa jikinta, ga dabaru da ya ɓullo da shi, haka zai sakamata videon tsaraicin wa su ya ce ta nutsu na kalla irinsa zata yimai. Da farko gardamar bazan yi ba ta yi mai, ai kuwa ya kamata ya yi mata dukan tsiya, abisa tilas ɗin rashin zaɓi ta fara bin umarnin Sufyan. A haka su ka ƙara shafe shekara ɗaya cikin uƙuba da tsanani, ba ta gaisawa da Kaka, ba ta da abokin hira, domin wacce ta tare a ɓangaren Ruwaida sai da Yasar ya ja mata kunnen kar ta kuskura ta kula Naila idan ba haka ba zan ƙulla mata sharrin da Allah ne Kaɗai zai wanke ta. Da kuɗin guminta Sufyan ya ke rayuwa, da kuɗin guminta ya ke tari a Bankin da Ubangidan mahaifinsa ya yi mai jagora ya buɗe, da kuma kuɗin guminta ya ke yiwa budurwasa Sumaya siyayya. Ita kuma ko cikakken Suturar sawa ba ta da shi, idan ta yi dariya tsananin munin ta sai ya bayyana saboda rashin namar fuska har wani yamushewa fatatar ta yi. Sufyan ma ya kance ba ta da abinda zai mora a jikinta duk ta rame sai ƙasusuwan da zasu jimai ciwo, da wannan yake fakewa sai dai ya tuɓe ya yi ta umartata tana yimai abinda zai gamsar da shi. A ɓangaren Sumaya da Sufyan soyayyar su kullum ƙara armashi ya ke yi saboda basa ɓoyewa junansu komai sai na ɓangaren da ya shafi sirrin su, Sumaya ko sunan Naila bata son ji a bakin Sufyan wannan dalilin ya sa baya yi mata hirar ta. A yammacin wata asabar Naila ta shirya zuwa Gidan ƙawayen Ruwaida da ta taɓa kaita, domin ba ta muzantata a wajen kowa ba, dukka ƙawayenta waɗanda su ke kiranta ta yi musu kitso ba su daina ba, Ruwaida ce dai kawai ta ƙauracewa haɗuwa da ita. Ta na fitowa na haɗu da Yasar, da ta gaishesa daƙyar ya amsa yana gyara zamansa a han ɗan tudun da ya ke zaune. Naila bata yi nisa da Gidan su ba, ta hango lafiyayyen mota mai farin gilashin da mutum zai iya ganin na ciki, fuskar Salman ta gani kamar dai yadda ta gani a farkon zuwanta Birnin Abyad. Da gudu ta tunkari mota da ya ke tafiya a hankali ta na kuka haɗe da magana da iyakacin ƙarfin muryarta; "Salman na san kai ne ka tsaya ka cikamin alƙawarina na roƙeka, ina shan wahala ka taimakeni ba ni da kowa a Birnin Abyad ka ji ƙaina ka faɗamin ina SULAIM yake? da gaske ya ƙone ya mutu?" kamar yadda Naila ta yi tsammani bai tsaya ba tana ji tana gani su ka haɗa ido cikin ido da mutumin da ta ke ganin sak Salman sannan yaƙarawa Motarsa gudu ya barta a wajen. Ƙasa ta zube ina kuka. Yasar da ya ga komai kuma ya kasa jurewa nufo inda Naila ta ke ya yi, ya kamo hannunta ya kawota har harabar gidansu. Cikin taushin murya ya ce; "Naila menene ya ke damunki, ka faɗamin gaskiya daga ina ki ke(ma'ana Yankinta) " kasa magana ta yi saboda shesheƙa. Naila ta ɗauki mintina a haka, kafin ta daki ƙirjinta saitin zuciyarta inda ke ji kamar zai fashe, sannan na fara magana sheshekar kuka na tare ta; " ina shan wahala🥹, ina so na koma Yankina, ina ji kamar zan mutu..."✍🏻 [7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: https://chat.whatsapp.com/I1wZrvGJP2s3QIyUuJ4ig7?mode=r_c 🔥ZINARE🔥 SASAAL 15 Tana na gama furta ciwo da raɗaɗin da ta ke ji a cikin zuciyata, sai ta ƙasa magana saboda kukan da ya ci ƙarfina. Kamar talabijin haka Yasar ya zubamata fararen idanuwansa. Ta kai wa su daƙiƙu tana kuka, kafin ta cigaba da magana; "Sufyan ya na ganamin azaba, ya na dukana, ba ya barina na mori kuɗin da na ke samu. Ruwaida ita ce take taimakamin kuma ya yi mata sharri saboda ina tara kuɗi a wajenta ta bar gidan nan. Ni marainiya ce, ba ni gata kuma ba ni da ƙarfin yin komai ka taimakamin na koma Yankina" Kai ya sunkuyar ƙasa saboda tausayi ya jima a haka kafin ya ɗago ya ce; "Ina ne Yankin ku Naila? Kuma maiyasa ƴan uwanki tunda sun san ba su da halin da za su iya taimaka miki a ko wani lokaci su ka ba wa Sufyan ya taho da ke har Birnin Abyad? Wannan gangancine mai girman gaske" Ba bu ƙarya a maganarsa amma ƙaddara ta riga fata. Cikin sanyin yanayin da ya ɗan fara shigar Naila ta ba shi labarin Yankin da ta fito. Amma ba ta ba shi labarin dalilin da yasa ta ke bibiyar mutumin da ta ke zargin Salman ba ne. Yasar ya gamsu da bayaninta, amma sai ya ƙara jefomata tambayar "maiyasa ki ke kiran Mutumin da ya wuce ɗazun har ki ke cewa ya taimaka miki? Wanene kuma Sulaim ɗin da kike tambayarsa ɗan uwanki ne? Ki faɗamin gaskiya idan da hali zan iya taimakawa." Ƙur Naila ta yiwa Yasar da ido, tarihin abinda ya faru na kusantowa ganina kamar a lokacin su ke faruwa. Waje ta samu ta zauna Yasar ya biyo bayanta. A baya labarin Yankinta da mahaifanta sun mutu kawai ta faɗamai da rashin adalcin danginta na ɓangaren Uwa da na ɓangaren Uba, amma tunda ya nuna zai taimaketa ta koma Yankinta to dole ya san asalin inane Yankin Tudu da kuma surƙullen da ya ke cikinsa. Kamar Yasar ya na ganin komai haka ta ke ba shi labari tun da ga lokacin da ta yi wayo har zuwa mutuwar Salman da abubuwan da suka faru bayan nan har aurenta da Sufyan da kuma manufar Mahaifansa a kanta. Mamaki ne zalla a saman fuskar Yasar, banda yana da ilimin nazatar Ɗan adam da kai tsaye zai ƙaryata Naila, wani irin Yanki ne wannan? Wa su irin mutanene ma su ƙaracin basira ne a Yankin? Kusantowar lokacin dawowar Sufyan ya sa Yasar gajarta tunaninsa. Cikin alhini ya ce; "Tabbas! Naila akwai DHAHAB CITY a Babban Birnin Abyad, Unguwar da wani mashahurin mai arziƙi ya gina, Shekaru goma sha biyar baya. Ahalina ne ma su tsauri da tsantseni domin dai-dai ma su gadin alƙaryar Dhahab ababen tsoro ne, sai dai shi ba sunanshi Abduh ba sunansa Muhammad Dhahab kuma a zahirin da mu mutanen gari mu ka sani Ɗan asalin ƙasar Abyad ne, amma wa su na cewa ba shi da asali babu wanda yasan gaskiya. Duk wani mai hidima da ma'aikatan Company's ɗin su, su na da record ɗin komai na sa, rayuwar su ba bu sakewa sam duniyar su tamkar daban ya ke da namu, ba bu wanda yasan sirrinsu sai makusantan su, Tun shekarun baya na naimi aikin tsaron sashen Mahaifiyar Muhammad Dhahab a yanar Gizo kamar yadda na ga an wallafa saboda ma su irin ilimina ake nema, amma saboda sun kasa samun cikakken bayani asalin ni ɗan inane da kuma inda Mahaifana su ke zaune, sai su ka fasa ɗaukata duk da cancanta ta, na yi kuka a waccen lokacin saboda albashin aikin ninkin wanda na ke samu a yanzu ne sau huɗu. Gane rashin samun cikakken asalina ya sa suka hanani aikin sai na tattaro Mahaifana na tara kuɗi na siya mu su Gida a Birnin Abyad, saɓanin daa da su ke zaune a bayan gari. Sai dai duk da na yi haka samun aikin sai ya gagareni haka na gaji na haƙura. Bayyanar Simbi ahalin Gidan Muhammad Dhahab a Asibitin mu sai ya dawomin da burina na baya, wannan dalilin yasa na fara bibiyarta ta taimakamin saboda zan ƙara samun sakewa wajen taimakawa mahaifana har na samu na yi aure, amma sai Simbi ta wulaƙantani dalilin da ya sa nayi zuciya kenan na haƙura da aikin. Amma Naila dole yanzu zan ƙara zage damtse har Simbi ta saurareni, saboda shigata Dhahab zai bayyanarmin alaƙar tarihin Yankin Tudu da rayuwar su, fatana ki tayani da addu'a." Baki, hanci, da ido dukka Naila ta saki tana kallon Yasar, cikin kokwanto ta ce "menene sunan wanda aka ce shine Mijin Simbi mutumin da ya ke yimin kama da Salman?" Ɗan dariya Yasar ya yi kafin ya ce; "A binciken da na yi Simbi sam ba ta da Miji, kuma wanda ki ke gani sunansa Uzair, ba shi cikakken lafiya sosai saboda ya taɓa ciwon da ya yi shekara shida a kwance kafin ya warke, bansan wani ciwo ba ne, amma na samu bayanin ne da ga Yayan Ruwaida amintaccen ma'aikaci a kamfanin su, shima a sirrince ya faɗamin don haka ki kiyaye" kafin ya ƙarasa tuni Naila ta ɗora hannuwanta dukka biyu a kan bakinta alamun ba bu wanda zai ji. Dariya Yasar ya yi kafin ya ɗora da nasihar ta kwantar da hankalinta da ƙarfin mulkin Allah sai sunyi nasarar shiga Dhahab ko a masu goge-goge ne. Naila sai ta ji dukka ƙuncinta ya yaye sai ta ke ganin kamar komai ya zo ƙarshe, da wannan farin cikin sukayi sallama ta koma ciki ta yi wanka ta ci abinci. Gidan kitson da bata je ba kenan ta kwanta barci. Daga wannan ranar Naila bata ƙara ji daga Yasar ba gaba ɗaya ma sai ta daina ganinsa. Da farko ta ɗan damu sai da ya ba da gajeran saƙonsa na suturar sawa ma su kyau da kayan ciye-ciye ya risketa ta kwantar da hankalinta. Babban akwatinta ta sauko da shi, na ɗura kayan a cikin gudun kar Sufyan ya gani saboda ya kusa dawowa. Ta na kici-kicin mayar da akwatin hotonta da na Sulaim da ta sa aka wanke mata ƙaraminsa ya faɗo, da sauri ta ɗauke saboda har ga Allah batasan ya na cikin aljihun bayan Akwatinta da ta taho da shi ba, kuma tasha zuba kuɗi a ciki na kwashe amma hoton bai taɓa bayyana kansa ba. Da wani irin farin ciki ta ke kallon hoton. Batasan ta ɗauki lokaci a haka ba sai da taji Muryar Sufyan a bayanta, dama kuma da ɗayan key ɗin Parlon ya dawo tafiya Makaranta. Firgitarwar da bayyanar Sufyan a lokacin da bata yi tsammani ba ne, yasa ta saki ƙara haɗe sakin ƙaramin hoton ƙasa, kallon hoton Sufyan ya fara yi sannan ya yunƙuro dasauri zai ɗauka ransa na suya, kafin ya cimma hoton tuni ta yi hanzarin ɗaukewa tana zare ido. Fes Sufyan ya ga waɗanda suke jikin hoton, ciwon da ya jima da shafesa a tarihin rayuwarsa ya yunƙuromai. Cikin ɗacin zuciya ya fara dukanta ya na ƙwallo da ita, ya na cewa; "ba ni hoton nan wato amanata ki ke ci ko? Shi yasa kullum bakya ganin kyawuna, kina maƙale da wannan hoton shaiɗanin da ya addabi mutane duk da ba ya raye, wallahi idan baki bani ba sai na kusa kashe ki" maganganun sa ba su ƙarawa Naila komai ba sai ƙaimin ƙara dunƙulewa da ta yi da hoton waje ɗaya, idan ya kasheta ma ai ta huta da uƙubarsa. Har ya gama dukanta bata warware daga ɗunƙulewar da ta yi ba, cikin azabar kishi ya sa mukulli ya kullota yana huci... Kuma ya yi rantsuwar ba zai buɗeta ba har sai ta bubbuga da kanta ta yarda bashi hoton ya ƙona sannan ta ba shi haƙuri. Haka Naila ta kwana ta wuni kulle, inda Allah Ya taimaketa akwai kayan ciye-ciyen da Yasar ya aikomata da su, idan ta ɗanci sai ta kora da ruwan banɗaki ta ɗoro alwala ta kaiwa Ubangiji kukanta. A haka ta shafe kwana uku tana manejin abinda Yasar ya bata tana korawa da ruwa kuma cikin hukuncin Ubangiji sai ta ji na ƙoshi. A ranta take faɗin; Banda shirmen Sufyan idan har shi da ya ke a iya haka yana ganin yafi ƙarfina to ina ga SULAIM da ya fishi komai ace ya na raye mai zai yi da ita? Sulaim tamkar Aboki ya ke a gareta har ya bar duniya, ba bu soyayya balle alƙawarin aure a tsakaninsu. Dalilin da yasa soyayyarsa ta samun matsuguni a cikin zuciyarta shine barinsa duniya, ta hanyar da dole a tausayamai, a kuma kasa mantawa da shi. Amma ko a raye ko a Mace bazata taɓa sawa ranta lallai Sulaim sai ya so ta ko ya aureta ba, matsawar ba ƙasƙancin da Sufyan yake nunamata dama take so ta fuskanta ba. SUFYAN; A kwana na biyu da kulle Naila a ɗaki kafatanin kuɗin da ya ɗan rage a Bankinsa saboda ya turawa Gida kuɗi a rabawa Danginsa har da Dangin Naila da Kakarta da sukai ta samai albarka tare da farin cikin Naila tana cikin daula, su ka ƙare, ga shi ya saba siyawa Sumaya kaza, da su ice cream da sauransu har Gida ya ke siyamata ta kaiwa Iyayenta. Tun washe garin da ya kulle Naila yake sa ran yunwa zai ci ƙaniyarta ta buga ƙofar ta ba shi haƙuri haɗe da ba shi hoton, amma ya ji shiru. Kwana uku da kulleta daƙyar ya kalato canjin aljihunsa ya tafi Makaranta. Ranar ba su ci abincin arziƙi ba don haka ya keɓe ya kira wayar da ya tura kuɗi aka siyawa Mahaifiyarsa . Hindu masifa takeyi bayan gama saurarar Sufyan kamar zata cijeshi ta waya.. "yanzu kai saboda ba ka san ciwon kanka ba shine zaka kulleta ka janyowa kanka asarar kuɗi ma su yawa, a kwana ukun nan banda kulletan da kayi da nawa zata samo maka? Amma wallahi Sufyan sam ba bu basira a cikin ƙwaƙwalwarka, har yanzu ba zaka daina kishi da Sulaim da yake matacce ka gina rayuwarka ba, Yankin Tudu kowa ya na samaka albarka, kai kana can kana shirme? To idan bata so Sulaim ba a matsayinsa na mutumin da su ke tafiya Makaranta tare su dawo tare su yi raha tare kuma ya ƙone lokaci ɗaya ba wa kake so ta so eh? dabba mara tunani!" Saukar kalamanta sai da ya sauya kalar fararen idanuwansa, ya na jin kamar ana barbaɗa masa yaji, zagin da Ɗayyib Mahaifinsa ya ɗoramai da shi bayan ya karɓi watan ne yaƙarasa birkitasa, cikin rawar murya ya ke ba su haƙuri amma still Ɗayyib faɗi ya ke " to yanzu haka Kasuwar Tukwanen Zinare ya mutu miɗis, sabuwar yunwa ta kunnowa Yankin mu kai, saboda an samu hamshaƙin mai arziƙin da ya saci fasaharmu ya mayar da su Tukwane na alfarma a kaf faɗin duniya ba bu inda ba'a siya, mu kuma an watsar da namu saboda ya zama tsohon yayi. Shine kai mun samu ka tsira zaka dawo damu baya, Allah Ya wadaran wannan son kyau na ka Sufyan! kai kullum ba ka da zance sai zancen Mutumin da tuni ya ruɓe a ƙarƙashin ƙasa, idan ka dama ka gyara to, idan kuma baka dama ba kai sani. Kasan da abinda zaka biya kuɗin hayar ku idan ya ƙare" Sufyan kanshi ne ya ɗauki zafi a take ya fasa kuka yana ba su haƙuri. Shi gaba ɗaya ya manta da kusantowar biyan kuɗin hayar su. Tahowar Sumaya inda ya ke ne yasa ya yi mu su sallama haɗe da yi mu su alƙawarin komai ya wuce, In Shaa Allahu zai gyara. NAILA Kayan ciye-ciyen da Yasar ya aikomata da shi ba laifin ya na da yawa, amma ba irin sosai ɗinnan ba, rashin sanin ranar da Sufyan zai buɗeta yasa take cancanensa kar ya ƙare ta rasa abin ci, saboda ko zai mutu bazata ba shi Hotonta da Sulaim ya ƙona ba. Da yammaci ta na zaune a inda ta yi sallar la'asar ta ji ya buɗe kofar, fuskarsa ba yabo ba fallasa. Bai ce mata komai ba, ya bar ƙofar a buɗe ya juya ya fice. ★washe gari saboda rashin kuɗi ko Makaranta bai je ba. Ya na ɗaki ma su zuwa tambayar kitso su ka zo har mutum uku, ɗam jim Naila ta yi kamar ta ce mu su ba ta da lafiya, amma yadda su ka nuna su na son kitson ya sa ta amince. Sufyan dake laɓe yana kallonsu ajiyar zuciya ya sauke bayan ta amince ya koma ya kwanta yana murmushi. Bayan ta gama su na fita ya yi zumbur ya fito ya ƙwace kuɗin fuskarsa ƙunshe da dariya. YASAR; duk wata hanya da zai bi ya samu ganin Simbi abin ya ci tura, abinda ma ya lura da shi kamar ba iya son haɗuwa da shi ne ba ta yi ba, gaba ɗaya gudun mutane ta ke yi. Ranar da ya ji labarin saura kwana ɗaya ta gama abinda ya kawota ta koma Dhahab a bakin ofishinta ya wuni. Ta na fitowa ma su gadin lafiyarta su ka rufa mata baya, kai tsaye tasa a hana Yasar bin bayanta. Sai dai kafin su kaiga riƙeshi ya taka da gudu zuwa inda motarta ya ke dai-dai inda ta ke tsaye yadda za ta jiyosa cikin yanayin maganar da matsawar tasan Naila zata fahimcesa a hankali da kuma sauri ya ce; "Yankin Tudu, Daular Sarki Hammam Naila ƴar Gidan Mahmoud madinki, Aminin Abduh Dhahab....✍🏻 [7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: https://chat.whatsapp.com/I1wZrvGJP2s3QIyUuJ4ig7?mode=r_c 🔥ZINARE🔥 SASAAL 16 "Yankin Tudu Daular Sarki Hammam, Naila ƴar gidan Mahmoud madinki, Aminin Abduh Dhahab." Yasar ya ƙarasa faɗa zuciyarsa na bugawa da sauri. Dukan mai laifi kai tsaye ba tare da gudanar da ƙwaƙwaran bincike ba laifi ne mai girman gaske a ƙasar Abyad. Wannan dalilin yasa ko da jami'ai masu tsaron lafiyar Simbi suka cimma Yasar ba su taɓasa ba sun dai yi mai katanga tsakaninsa da ita. SIMBI; Designer jakar hannunta mai tsananin nauyin kuɗin da ya dace da arziƙinsu ta ƙanƙame da fararen hannunta ma su sanyi kyau ga mai Kallonsu, kafin ta juyo da kyakkyawar fuskarta. Idanuwanta da suke farare ƙal ta zubawa fuskar Yasar, batason dogon magana da shi, saboda doguwar magana a tsakanin su tamkar karya alƙwarin Alhalinta ne, don haka ta ce; "A ina kasan dukka wannan?." Jira take yi ya saki layi ta sa akamashi saboda gudun shigarta matsala amma da yake Yasar wayayyene akan aikinsa da kuma fahimtar inda ta dosa kai tsaye ya ce; "Layinmu gidan na uku hannun hangu makitsiya mai ƙaracin shekaru." Jami'an tsaronta shirme suka ɗauki kalaman Yasar saboda ba su fuskanci ina kalamansa su ka dosa ba tunda ba su ji abinda ya faɗa lokacin da ya risketa ba. Umarnin barin wajen suka ba shi, bayan Simba ta shiga Mota. Yasar bai musa ba ya juya ya bar wajen, maimakon ya koma Gidansa sai ya wuce na Iyayensa saboda yasan dole abi bayansa, domin ko shakka ba ya yi labarin tare Simbi da ya yi da tsayawarta ya isa Babban Birnin Abyad. SIMBI; bata manta fuskar Yasar ba, saboda tun ranar da ta gansa ta ji ya birgeta a ƙofar Gidan da ya faɗa, kuma a wannan ƙofar Gidan ya naimi taimakon aiki da gareta gaba da gaba na ƙarshe lokacin ta fito workout, gudun matsala da sanin abun da take saƙawa zuciyarta akansa ba zai taɓa tabbataba yasa tasa a wulaƙantashi saboda ya yi zuciya kar ya ƙara bibiyarta. Bata manta Naila ba, ba kuma zata mantata ba har abada, saboda ƙawarta ce kuma maƙiyiyar Ƴar uwarta Barirah. WAIWAYEN SHEKARUN BAYA Lokacin wasannin ƙarshe mako a Daular Sarki Hammam akwai wata matashiya mai kusan Shekarun Sulaim da ta kwashewa Naila ƙafafu saboda ta matso kusa da inda su ke wasa, har Naila ta kawo ƙararta wajen Sulaim. Ƙanwar Malik ce Uba ɗaya Sunanta Barirah. Mahaifinsu Malik, ya auri Mata biyu matarsa ta farko ita ce Mahaifiyarsu Malik, tun da suka haifi Malik ba su ƙara samun wani ba har Malik ya kai shekaru biyar, son ƴaƴa ya sa shi ƙara aure, ya auri Mahaifiyar Barirah. Bayan wani lokaci ta haifin Barirah sa'ar Sulaim daganan itama ba ta ƙara ba, sai Mahifiyar Malik da ta ƙara haihuwar Simbi, baƙin kishi da rashin son zaman lafiyar Mahaifiyar Barirah ya sa Mahaifin Malik sauwwaƙemata ya kuma karɓi ƴarsa Barirah. Barirah muguwar gaske ce musamman idan taga ta fika ƙarfi, ba ta baro komai na halin Mahaifiyarta ba. Da farko bata tsani Naila ba tana dai cin zalinta matsawar suka haɗu, amma daga lokacin da Sulaim da take son ya kulata ya riƙe Naila a matsayin ƙawa ta tsaneta ko aikota akayi Gidansu sai ta ranƙwasheta. Wannan tsanar bai sauya zani ba duk tsayin shekarun da su Barirah suka kwashe a cikin daula. DAWOWAR LABARI A cikin Mota Simbi take hira da zuciyarta Tabbas! bata manta fuskar Naila ba, amma mai ya kawo Naila Birnin Abyad? Allah Ya sa ba wani Yaƙinne yake shirin tunkaro su ba. Bayan kwana ɗaya kafin Komawar Simbi Babban Birnin Abyad, ta yi yunƙurin bincike don tabbatar da ainihin abinda yasa Yasar ya iya yin kasadar tararta kai tsaye saboda matsalar Naila kawai da kuma abinda ya kawo Nailan Birnin Abyad, kafin komai ya lalace. Ta hanyar kiran Bushra da take sa'arta, wacce suka zama tamkar zuri'a ɗaya a Dhahab, kuma take kyautata zaton zata iya yimata bincike akan Naila, saboda ba ta so take wajen Naila da kanta ta ganeta. babu ja Bushra ta amince dama kuma tana Birnin Abyad itama bata koma ba. NAILA ; kamar kullum da sassafe ta yi ayyukanta bata wahalar da kanta wajen girkawa Sufyan Breakfast ba saboda ba ci zaiyi ba, idan ta yi a wajen yake barmata kayanta. Wanka ta yi ta ɗauko Abayar da ta zamemata tamkar ta gado ta saka, saboda tana jin tsoron saka wanda Yasar ya aikomata da su gudun duka da ga Sufyan, domin wanda Sufyan ɗin ya siyomata masu sauƙin kuɗine marasa quality duk sun zaizaye wa su guraren ma duk sun yage. Bayan ta gama saka kaya turare ta fesa saboda customers kamar yadda Rufaida ta ɗorata a kai tuntuni saboda a wasu lokutan jikin mutum ya kan ɗanyi tsami wanda hakan ya ke takurawa ma su zuwa kitso musamman idan suka ɗora kansu a tsakanin ciyoyi. Sana'ar da ya zamemata jiki ko da yaushe ta zauna yi( tunani) wa ni lokacin ta saki kuka wa ni lokacin kuma ta yi dariya. Ta na cikin tunani ta ji ana ƙwanƙwasa ƙofa. Da hanzari ta miƙe ta nufi ƙofar, ta buɗe. Bata taɓa ganin fuskarta ba, don haka tayi mata tarba na musamman tana washe haƙoran da suke ƙara bayyana ramata. Ƴar gayu ce kuma da alama daga Gidan arziƙi ta fito. A lokutan baya Naila ba ta da yawan surutu ba ta da yawan dariya irinna rashin kamun kai, amma tunani da ƙunci rayuwa suka sa ta zama mai tsananin surutun da ita kanta batasan tanayi ba, ga dariya da take yawan yi na rashin dalili wanda ya zarta a kirashi fara'a. Ba mai yawa wacce yazo kitson ta ce ta na so ba, don haka ta yi mata irin yadda take buƙata. Da ta tashi tafiya kuɗi mai yawan da daa abayane ta bawa Naila su ihun murna zatasa saboda tana da yaƙinin zata tara ta gina Gobena da su, amma yanzu Sufyan ya na dawowa zai ƙwace. Rashin fara'ar Naila da yadda ta yi ƙasa da kaine yasa wacce ta zo kitson ta magantu; "Baiwar Allah ko kuɗin ne ba su yi miki ba, na ga kamar ranki a ɓace" ta ƙasara faɗa tana karantar yanayin Naila. A hankali Naila ta ɗago idanuwanta da ƙwalla yasa ta ke ganinta dishi-dishi ta ce; "Na gode! na gode!! Allah Ya biyaki, amma dan Allah daga ina kike na baki kuɗin ki taramin?" Naila ta ƙarasa faɗa kamar wacce batasan me take yi ba. Idanu ta zaro ta ce; "ta yaya ba ki Sanni ba zaki bani ijjiyar kuɗi bakya tsoron na gudu da su? saboda me ke bazaki ɓoye a ɗakinki ba ko ɓarayi su na damunku na sanar da jami'ai?" Kai Naila ta girgiza hawayen da bata iya yiwa idanuwanta shamaki da su ya tahomata. Idanuwa wacce ta zo kitso ta ƙara zarowa wannan karan da mamakin bayyane a saman fuskarta, cikin tashin hankali ta ce; "Menene matsalar Baiwar Allah?" Cikin kuka Naila ta ce; "Inaso na koma Yankina amma bana iya tara kuɗi Mijina kwashewa ya ke yi domin gina gobensa, ya na dukana kullum, ki taimakamin kinji Don Allah nasan kinfi ƙarfin su bazaki Gudu da shi ba" kamo Naila ta yi zuwa jikinta tana shafa bayana ta ce; " Ya ya sunanki kuma ina ne Yankin ku? Ko zan iya taimakawa" Da sauri Naila ta ce ; " sunana Naila, yankin mu shine Yankin Tudu" Naila tana jin lokacin da zuciyar wacce ta zo kitso wajenta ya ya buga da sauri, saboda kanta dake jingine har lokacin a saman Kafaɗarta. Da sanyi murya wacce ta zo kitso wajenta ta ce; " Maiyasa ba zaki bawa Mijinki kuɗinki ya gina gobensa ba, gina gobensa ai tamkar gina na ki ne" Kuka Naila tasa tana roƙonta ganin kamar ba ta fuskanceta ba. Gwauron numfashi ta sauke, tana kallon Naila ta ce; "Zan karɓa amma sai kin sanar da ni dalilin dayasa baƙyason mijinki ya mori kuɗinki alhali kuna tare bai sake ki ba" Kamar wacce take jira haka Naila ta soma sako mata zance da wanda ta tambaya da wanda bata tambaya ba. Da Naila ta gama labari Ba ta ce mata komai sai bayanta da ta ɗan bubbuga tayi mata sallama ba tare da karɓi kuɗinba. Ba kowa Ba ce tazo wajen Naila kitso ba fa ce Bushra wacce Simbi ta Turo, kuma ta naɗi dukka hirarsu da Naila. SIMBI; Recording ɗin da Bushra tasa mata, da yake Bushra gwanar tausayi ce ta kuma sauraro tana kuka. Daga wannan ranar kullum sai Simbi ta tura Bushra Gidan Naila da sunan tayata hira a haka suka samu dukka bayanan da suke so, amma har lokacin Simbi ba ta tuna fuskar Sufyan ba tunda sun bar Yankin Tudu ya na yaro. Har lokacin komawar Simbi Dhahab ya yi, ba su samu damar bincikar Sufyan ba, don haka ta bar ragowar aikin a hannun Bushra ta tattauna da Yasar a sirrince domin ya taimaka musu wajen bibiyar Sufyan. NAILA Dalili yawan tambayoyin Bushra da yadda ta saki jiki da ita duk da kasancewarta ƴar masu hali yasa Naila ta fara zargin ko Sufyan ne ya turota, da ta fara zargin haka sai ta daina bata kuɗinta ya ɓoyemata ta nuna mata ta sauko ta fison Mijinta ya gina gobensa domin su tashi tare su tsira tare. Babu kalar tambayar da Bushra batayiwa Naila ba akan wasu sirrika na Sufyan da ta gano amma Naila taƙi faɗa saboda tsoro. YASAR; kamar yadda ya yi zargi bayan barin wajen Simbi za'a bibiyi bayansa haka kuwa a kayi, A sirrince ɗaya daga cikin masu tsaron tafiyar Simbi ya bi bayansa ya bincika babu makitsiya a gidan, daga haka ya ɗora mizanin maganganunsa akan shirme kamar yadda sukayi zargi tun farko. Da sunan Ganin likita Bushra ta samu keɓewa da Yasar daya koma gaban Mahaifansa da zama saboda tsaro. Alƙawarin naimarmasa aiki ta yi matsawar ya gayamata Ɗan gidan wanene Sufyan a Yankin Tudu. Ko batayi alƙawarin cikamai burinsa na samun aiki a Dhahab ba ya yi alƙawarin taimakon Naila ta koma Yankin su ta kowacce fuska. Bai ɓoyewa Bushra komai ba, ya kuma roƙeta ta riƙe amana, kuma a shirye yake domin ba da gudunmawa idan hakan ta taso. BUSHRA A wannan rana kwanan tunani Bushra ta yi. Matsawar Simbi tasan Sufyan jinin masarautar Yankin Tudu ne, to ba shakka ba za ta taimaki Naila ba, dama kuma can ba wai tana son taimakon Naila ta wata fuskar bane daban sai na mayar da ita Yankinsu. Amma ga Bushra ba irin wannan taimakon takeson yi wa Naila ba, wanda zatayi farin ciki na har abada takeson yi mata. Ko da sukayi waya da Simbi kai tsaye ta sanar mata bata gama bincike ba. A cikin kwana biyu Bushra ta binciko Sufyan ciki da wajensa har da soyayyarsa da Sumaya da abinda yakeyi da kuɗin Naila saboda ta samu tabbacin baya sana'ar komai. Ta na son Naila taje Dhahab amma ta yaya? Ta na kuma son Sufyan ya ɗanɗani azaba ƙiri-ƙiri irin ɗanɗanar da zai gusar da nutsuwar zuciyarsa yana ji yana gani, amma dole sai ya riski Dhahab to amma ta yaya riskarsa Dhahab zai yiwu? Tsakiyar Dare ta naimi layin Mahaifanta, sunyi magana ya fi na hour huɗu, kafin ta suyi sallama, ba tare da jinkiri ba, ta dannawa Yasar kira. Suka tattauna yadda zasu ɓullowa Sufyan. ★washe gari Bushra da ke lulluɓe cikin shigar larabawa ita da Yasar suka kaiwa Sufyan ziyara Makaranta. Sufyan tsaf ya gane Yasar, wannan dalilin yasa ya tsamke fuskarsa ya na bawa Sumaya umarnin ta jirasa yana zuwa. Da suka keɓe bayan sun Gaisa sama-sama Suka ce masa takardunsa daga kan na primary har na secondary suke so da kuma shaidar takardun jami'ar da ya ke zuwa zasu samar masa aiki a Dhabah amma sai takardun Makarantarsa sun kasance na Birnin Abyad, za kuma a samar mishi sabon jami'a a can idan ya kama aiki. Kwaɗayin da burin duniya su suka taru suka lulluɓewa Sufyan ido ya kasa tantace cuta da so da kuma tantance ina ne Dhabah maiyasa suka zaɓi naima mai aiki. Jikinsa na rawa ya tashi gefe ya kira Mahaifinsa. Ɗayyib ihun murna yasa ba tare da tsayawa saurarar sunan Ma'aikatarba ya kira amininsa. Ɗayyib ya na kiran Amininsa ya sanar da shi buƙatarsu Kai tsaye amininsa ya sanar da shi bashi da hanyar da zai samarwa Sufyan takardun bogin primary da sakandaren ƙasar Abyad. Ko da Ɗayyib ya kira ya sanar da Sufyan a take jikinsa da ke rawar murna ya yi sanyi laƙwas. Jiki a sanyaye ya dawo wajensu Yasar ya yi musu bayani. Bushra da ke tantance son banza irin na Sufyan kai tsaye ta ce zata samar mai amma sai ya yi mata alƙawarin barin matarsa ta naimi jami'a ya kuma daina karɓe mata kuɗin sana'arta. Son banza bai sa Sufyan ya tambayar kanshi ina Bushra ta samu labari ba, ya ce ya amince amma a iya bakinsa ya tsaya, domin har cikin ransa ya yi alƙawarin jami'a sai dai Naila ta ga anayi.... A cikin kwana biyu Bushra da ƙarfin ikon Mahaifinta a ƙasar Abyad suka samarwa Sufyan takardun bogi. Tare da Takardun Yasar Bushra ta shigar ta hanyar yanar Gizo tare da addu'ar dacewa,.domin batason Malik yasan aikinta kai tsaye duk da akwai kyakkyawar fahimta a tsakaninsu. Duk wannan wainar da ake toyawa Naila batasan ana yiba, sai shige da ficen Sufyan da take gani a ruɗe. BUSHRA ★washe gari abinda ya shigar da Bushara Toilet ya fi sau uku shine Ɗaukar Sufyan aiki tare da wani irin albashin da ya tsoratata. Ba ita kaɗaiba dai-dai da Mahaifinta ya shiga zullumi da ta sanar mai, ya kuma gano akwai babban Yaƙi domin ko rantsuwa ya yi bazai yi kaffara Malik da ya ɗaukesa aiki ya gano wanene SUFYAN.....✍🏻 [7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: 🔥ZINARE🔥 SASAAL 17 Har yamma ta yi liƙis nutsuwar Bushra bai dawo jikinta gaba ɗaya ba. Idan wayarta ta yi vibrating har firgita takeyi. Dole zancen Mahaifinta ya zama gaskiya banda haka Sufyan bai cancanci ya samu aiki lokaci ɗaya haka ba, dama dai Yasar ne da takaddunsa suke nunawa gogewarsa. Har dare Mahaifinta bai kirata ya samu kira daga saman Dhahab ba wanna dalilin yasa ta ɗan samu nutsuwa a ranta, amma duk da haka sai da ta kira Simbi. Yanayin muryar Simbi da shawarar da take bata na ta dawo ta ƙyale Naila domin ita ta fasa taimakonta ne yasa Bushra ta ɗan jo sanyi a ranta, saboda da an samu matsala zata ji a bakin Simbi, sai a lokacin ta samu sukunin kiran Yasar tayimai bayani. Shawarar su haɗu washe gari a Gidansu Naila suka yanke. NAILA; tunda ta ɗauke yardata a kan Bushra ta miƙawa Allah komai tare da alƙawarin ba zata ƙara naiman taimako a wajen kowa ba. A tsakanin kwana da wuni Sufyan sam bai tambayeta kuɗi ba, kuma a kan idonsa ta kitsa kan mutum biyu. Bata yi mamaki ba, domin ga dukkan alamu akwai gagarumin al'amarin da ya tisosa a gaba. A daren cikon kwana na huɗun da ya yi da daina tambayarta kuɗi, kuma itama bata ba shi ba, ya kirata ɗakinsa. Cikin muzurai yake sanar da ita samun aikinsa dalilin tonon Asirin da ta yi masa a wajen Bushra ɗaya gano daga baya, to ga kuɗinta ya barmata amma ta jira hukuncin da zai biyo baya. Har ya gama kumfar bakinsa da maganganun izgilancinsa Naila batace masa komai ba. Daga ƙarshe ya jamata kunnen karta kuskura Bushra da Yasar su naima mata jami'a ta yarda ta je. Idan kuma ta saɓawa umarninsa wallahi sai ya hukuntata da hukuncin da har ta mutu bazan manta da shi ba. Babu abinda ya motsa daga jikinta balle ya gane na fahimcesa ko bata fahimcesa ba, takaicin hakan yasa ya haureta da ƙafa ya na faɗin; "Fice min daga ɗaki, sha-sha-sha kawai ai gashi garin ki tonamin asiri kin janyomin daukaka, kuma wallah na rantse bazaki ci ko sisi daga arziƙina ba" Sam surutansa ba su dameta ba, tunda zai barta ta dinga tara kuɗinta. Kuma ko su Bushra sun tambayeta tanason zuwa jami'a da babban murya zata amsa "eh". Kanzil ba tace ba har ya gama masifarsa ta bar Ɗakin. SUFYAN; ranshi fari fes yake ji, sunan ma'aikatar da za'a samarmai aiki na kai kawo a cikin zuciyarsa, anya babu wani sirri a cikin wanda ya kara DHAHAB(ZINARE) a cikin sunansa, Abdulyasar Dhahab Ubaidullahi Dhahab, Abduh Dhahab, duk ba su bar duniya ba sai da suka zama ababen koyi, ga shi ya kuma samun wani mai arziƙin a Babban Birnin Abyad shima Dhahab. Tabbas! A kwai wani ɓoyayyen abu a cikin wannan sunan tunda shi kanshi asalin DHAHAB(zinare) ba abun yadawa bane abune da ake kokawa a kansa. Kakanninsa da suka ƙi kwantar da kai subi Abdulyasar Dhahab tun farko ai gashi za su mutu babu wanda ya sansu sai ƙananun muƙamin Sarautar da suke taƙama da ita. Anya bazai koma Sufyan Dhahab ba kuwa? Dariya ya bawa kanshi yana shafa sumar kanshi, tare da ayyanawa ransa irin girman kuɗin da zai dinga kashewa sumarsa, duk da dai bai san iyakacin albashin da za'a biyasa ba. Yanzu matsalarsa ita ce Naila, hanyar da zai rabu da ita ya korata Yankin Tudu kawai yake nema ba tare da su Bushra da Yasar sun ga baƙinsa ko butulcewarsa ba, tunda ko yana so ko baya so Naila ce sanadi. Da Sumaya yake son su tare a Babban Birnin Abyad idan komai ya yi masa yadda yake so. Tuna irin abubuwan da zai yi idan ya fara aiki yasa ya tashi yana taka rawa. NAILA; bayan ta koma ɗaki kuɗinta ta ƙara adanawa tana lissafa irin kayan da zata siyawa Kaaka duk ranar da Allah ya ƙaddara tafiyarta, godiya tayiwa Allah sannan na godewa Bushra tare da alƙawarin naiman yafiyarta duk ranar da Allah Ya haɗata da ita abisa munana mata zato da tayi. Ranta babu damuwar komai sai godiyar sauyin da ta fara samu nayi alwalar kwanciya barci, cikin abinda bai gaza minti biyu ba, bayan tayi addu'o'i barci mai nauyi ya ɗauketa. ★washe gari iyakacin abincin cikinta ta girka. Sufyan fita ya yi ya jubgowa kanshi siyayyar lafiyayyen Breakfast daga kuɗinta da yake tarawa a Banki. Daga dawo Ko kallonsa batayi ba ta tattara na bar living room ɗin. Hakan da tayi ba ƙaramin haushi ya bashi ba, don haka ya hau zage-zage da gorin ai ta kusa daina ganinsa sai ta dafa gidan ta cinye ni kaɗai idan ta samu kuɗin biyan haya, domin wallahi shi bazai biya ko sisi ba, ko ta tattara ta koma Yankin Tudu tunda bata da kunya ta fara rainashi bazatw roƙeshi ya sammata abinda ya siyoba ta sawa kanta girman kai alhali ita ba ƴar kowa ba ce face ƴar Madinkin da ya ke talakan fitik ta sanadiyyar rashin kuɗin zuwa Babban Asibiti ciwon ciki ya kasheshi. Kamar babu mutum a gidan haka Naila tayimai shiru, amma a ɗaki kuka takeyi zuciyarta na suya. Bai daɗe da gama Breakfast ba su Yasar suka iso Gidan. Jiki na rawa ya shigo da su Living room yana baza kunnuwar jin dalilin zuwansu har Gida. Ba su fara bayani ba sai dai suka bashi umarnin kiran Naila. Da ya shigo kiran Na'ilah sai da ya Na mata kunnen karta kuskura ta saɓawa abinda zai ce ya yi mata, sannan ya kamo hannunta muka fito tare. Naila tana hangosu ta ƙwace hannunta ta nufi Bushra. ƙam ta rungume Bushra tana nanata kalmar ta yafemata ta zargeta da cin amanarta ashe tanadin da ban taɓa tunani ba tayimata. Sufyan harara yake watsowa Naila ta ƙasan ido saboda ya matsu ya ji dalilin da ya kawo su. Sai da Naila ta nutsu tukunna sannan Bushra ta fara yi mai bayanin samun aikinsa da kuma irin albashin da za'a dinga biyansa duk wata. Duk yadda Sufyan ya so yaja aji ko ya kame kansa kasawa ya yi ya miƙe zurbur yana zaro idanunsa, kafin ya fashe da kuka yana yi musu godiya. Kai suka girgiza a tare suna haɗa bakin faɗin; "Naila zaka yiwa godiya dalilin gwagwarmayarta kakai matsayin da kake kai a yau, don haka karka manta alkhairinta domin shine tsanin nasararka" da gigin farin ciki ya fara nanata "Naila na gode! na gode!! na gode!!!" A tunanin Naila Sufyan ya sauya kenan don haka ta taso ta ƙanƙamesa tana yiwa su Bushra godiya, suma murmushine kwance a saman fuskokinsu. Bushra bata nanata naimarwa Naila jami'a ba tunda sun riga sun yi maganar da Sufyan tun farko kuma ya nuna ya amincewarsa. Bayan wani lokaci Yasar yayimusu sallama Bushra kuma ta zauna Naila ta kitsa mata kanta. Shima Sufyan barin Gidan ya yi da sunan zuwa Makaranta, zuciyar Bushra na suya tabi bayansa da kallo saboda ko shakka batayi wajen Sumaya zaije. Kenan Sufyan ba zai taɓa sauyawa ba. Naila da bata fahimci komai ba bakinta a washe take yiwa Bushra kitso tana janta da hira. A hankali a hankali hirarsuu ta faɗo kan Sulaim da yadda suka haɗu da sanadiyyar mutuwar Mahaifiyarta da ko Yasar Naila ba ta faɗawa ba, ta dai ce masa Mahaifiyarta ta mutu. Bushra tari ne ya sarƙeta ta hau yi babu kakkautawa, sannu Naila ta fara yimata kafin ta wuce kitchen ta ɗauko mata ruwa. Bayan tarin ya tsagaita sai ta yiwa Naila murmushi ta ce; "idan har kin aminta dani inaso ki ɗaukomin hoton Sulaim na gani." Da hanzari Naila ta miƙe tana dariya na nufi Ɗakina. Bayan ta ɗauko ta miƙawa Bushra, Bushra ta ɗebi mintina tana kallon hoton, sannan ta miƙamin tana janyo gilashinta mai ɗan duhun da Naila take iya ganin idanuwanta amma ba sosai ba ta manna. Naila ba ta kawo komai ba a ranta ta hau yaba gilashin da ƙoda irin kyan da ya yi mata. Bushra ba ta ta cewa Naila komai ba sai ɗan danne-dannen da ta yi a waya. kamar daga sama Naila ta ji Bushra ta ce; "Idan yau ace Mairam Matar Mahaifin Sulaim kuma ƴar Uwar mahaifiyarki da Mahaifiyarki ta rasa ranta wajen hidimtamata amma tabi umarnin iyayenta ta gudu ta barki duk da tasan zakisha wahala, kika ganta cikin daular da take da damar nemanki ta taimaka miki amma batayi ba yaya zaki ji?" Kanta Naila ta ɗago dakyau hawayen tuna irin mutuwar azabar da Mahaifiyarta tayi na zubowa ƙuncinta, cikin dakiya da kyakkyawar fata ga kowa ta ce; "wataƙila tana da dalili, ina kyautatamata zato a duk inda take, idan da rai da rabo wata rana Allah zai ƙaddara saduwarmu, amma gareni na yafe mata duniya da Lahira." Ta ƙarasa faɗa tana fashewa da kuka. Rungumeta Bushra ta yi cikin ƙosawa ta ce; "Yaushe zaki daina barin hawayenki suna zuba Naila? dole duk wani matakin nasara na tare da ƙalubale, Karki bari yawan kukanki yazama lagonki a wajen maƙiyanki" Kai Naila take girgizawa. A haka Bushra tayi ta lallashinta har ta yi shiru. Kafin ta bar Gidan sai da ta bata kuɗi masu yawa tace ta ɓoye zata ƙara dawowa kafin ta wuce Babban Birnin Abyad. SUFYAN; Kuɗin Naima da yake tarawa kaf ya kwashe sukayi ƙwarya-ƙwaryar walima shida iyayen Sumaya da ƙawayenta, tare da alƙawarin da zarar yaje Babban Birnin Abyad ya samu yadda yake so shirye-shiryen auren su da Sumaya zai kankama. Sai dare sosai ya dawo Gida. ★washe gari ma da sassafe ya bar gida. Duk Naila ba ta damu ba, ta bar shige da ficen nasa a matsayin shirye-shiryen tafiya Babban Birnin Abyad. Ranar da jirginsu zai tashi a bakin Bushra da zo gidan Naila ta ji labari, sai dai bata nunamata batasaniba. Bushra ta yiwa Naila kyautar kuɗi masu yawan gaske ta kuma yimata alƙawarin zata zana jarabawar share fagen shiga jami'a da taimakon Yasar. Da ta tashi tafiya waya mai kyau da tsada ta bata ta ce ta ɓoye kar ta bari Sufyan ya gani. Naila bata fahimci tsanarta ya yi nisa a zuciyar Sufyan kuma har abadan bazai taɓa ƙaunarta ba, sai da taga dare ya yi babu Sufyan ko da ta kira Yasar da wayar da Bushra ta bata da lambobin su a ciki, a nan takejin labarin ashe Sufyan tun da yamma jirginsu ya tashi. Ta yi kuka mai raɗaɗi da ciwon da bansan iyakarsa ba bayan sunyi sallama da Yasar, kafin ta haƙura ta kulle kanta a ɗaki. Tafiyar Bushra da Sufyan ne yasa Yasar dawowa ɓangarensa tare da ƙaramar ƙanwarsu da zamu zasu jarabawa tare sai dai Naila ta girmeta amma ta fi Naila girman jiki. Naila ta ji daɗin dawowar Yasar da ƙanwarsa, da kai tsaye ɓangarenta ya turota don tayata kwana. A take Naila ta saki ranta domin fuskantar sabuwar rayuwata. SUFYAN; kafin tafiyar Babban Birnin Abyad tunda sassafe Naila tana barci ya ɗauki iya ƴan kayan da zai ɗauka ya bar gidan, a Makarantar suka wuni da Sumaya tana kukan zatayi ƙewarsa. Gudun lalacewar komai yasa bai barta ta rakasa airport ba kamar yadda ta buƙata. Tare da Bushra suka hau jirgi.. Bayan sun isa filin jirgin Babban Birnin Abyad mota daban-daban suka hau da Bushra baima ƙara ganinta ba, kamar ba tare suka taho ba. Ma'aikacin Company ya kira kamar yadda Yasar da ya kira ya yi mai bayani haɗe da turomai Number. Kamfanin Dhahab bai ƙarasa c Tsakiyar Babban Birnin Abyad ba kuma anan inda Company ya ke anan staff quarters ɗinsu yake. Apartment ɗin da yasa Sufyan zubewa ƙasa yana yiwa Allah godiya aka kaishi. Ranar kwana ya yi bawa Sumaya labari haka su Ɗayyib da ya kira. Sam ya manta da Naila. Kan Sufyan bai ƙara kwancewa ba sai da aka kaishi Office ɗin da ake ce nashi ne. Duk da Sufyan yana da son banza da kwaɗayin son tara abin duniya sai da ya tsorata ba kaɗan ba. Tayaya ya samu matsayin da ko da dukka karatunsa ya kammala ba zai samu ba? anya Bushra da Yasar da Naila ba haɗa baki sukayi domin a siyar dashi ba tunda yana cinyemata kuɗin kitso? Hannunsa na karkarwa ya lalubo wayarsa😂. 🔥 SASAAL 18 Duk number wanda ya kira ba ya samu hatta number Bushra da bai ƙara gani ba a kashe yake. A take nadamar rashin siyawa Naila waya ya lulluɓesa, da yanzu ita zai kira yayiwa barazana tunda yasan matsoraciyace. Fatar hannunsa, takalmin ƙafarsa da kayan jikinsa ya kalla, ya ƙara kallon ofishin bai san sanda ya fashe da kuka ba. Sam Chemistry bai haɗu ba dole akwai manufa. Cikin kuka yake ƙara zagaye ofishin har da Bedroom da washroom. Lokacin da ya gama ƙarewa komai na ofishin kallo sai ya ƙara sakin kuka, hannunsa na tsuma ya ƙara lalubo wayarsa a karo na biyu ya dannawa mahaifinsa kira, saboda daa baiyi niyyar kiransu ba kar ya ɗaga musu hankali. Duk son duniyar Sufyan a bayan Hindu Mahaifiyarsa yake haka itama duk son duniyarta a bayan Ɗayyib suke, domin shi bashi da tsoro akan duk wani abu daya kafawa ƙahon zuƙa. Sufyan cikin kuka yake bawa Ɗayyib labari. Maimakon ya ji tashin hankali a muryarsa sai ya ji ya saki ƙaramin dariya. Da ƙwarin gwiwa ya ce; "Naila bata da muguwar zuciyar sayar da kurwarka Sufyan" Kai Sufyan ya girgiza idanuwansa ƙyam akan kujerar alfarmar da yake a matsayin mazauninsa. "Baaba bazaka fahimta ba, ba su kirani interview ba balle na tantance ƙwarewa ta ce yasa suka bani wannan ofishin, babu wani abu daga neman aiki sai shiga ofishi, tun daga ranar da na sauka ko Bushra banƙara gani ba, Baaba ni dai kawai haƙura zanyi da aikin nan" Da zafin muryar da zai nutsar da Sufyan kar yaja musu asara Ɗayyib ya ce; "Ka kwantar da hankali ka, duk na sa Ubangidana ya bincikamin komai, kana tunanin rayuwar kara zube kakeyi a Birnin Abyad? Har soyayyarku da Sumaya na sani, da bushashar da kakeyi da Kuɗin sana'ar Naila, dama abinda muka turaka kayi kenan? To ka buɗe kunnuwanka dakyau ka saurareni. Ka mayar da hankali kan aikinka domin fansar dukiyar da Mahaifiyarka da ni kaina muka sadaukar akanka ba ka zauna yin shirme ba. Inaso ka tara kuɗi Ubangidana yaƙara bincikamin komai a kan ma'aikatarku domin sanin muhimman abubuwa akan mai kuɗi sai da kuɗi. Yaya ma sunan ma'aikatar taku ka ce?" Kafin Sufyan ya ɓude bakinsa da ya yimai nauyi saboda kalaman Mahaifinsa da suka sanyaya mai jiki, an buɗe ƙofar ba tare da naiman izini ba. A gigice ya katse kiran. Rashin nutsuwar da yake ciki da kuma rashin sanin matsayin da aka bashi yasa bai tuhumi wanda ya shigo maiyasa bai naimi izini ba. Ɗayyib bai haƙura ba ya cigaba da kira Sufyan a ɗan gajarce ya ɗaga ya ce ya bari idan yaje Gida zasuyi waya. Cikin ƙwarewa bayan sun Gaisa da wanda ya shigo yake koyawa Sufyan yadda zai gudanar da aikinsa. Fara'ar fuskar Baturen da yadda yake nunamai yadda zai gudanar da aikinsa ne yasa Sufyan ya ɗan saki jiki. Ko da Baturen ya fita sai da ya ƙara ƙarewa komai kallo yanajin alfahari da girman kansa na ƙaruwa a hankali. Murmushi ne ya kufcemai bayan ya sauke ajiyar zuciya wawtar dayaso tafkawa na dawomai. Bayan Sufyan ya isa Gida ko cikakken hutun minti biyu bai yi ba, aka aiko mai da lafiyayyun kayan fita Office. Cikin isa yake gwada kowanne kanshi na ƙara girma. Da yake Sufyan sha-sha-sha ne ko da ya nutsu maimakon ya kira Mahaifinsa sai ya kira Sumayya suka yi ta waya har barci ya ɗaukesa. ★sai washe gari da safe ya tuna da kiran Mahaifinsa, a gurguje ya kirasa suka gaisa sama-sama. Irin motar da aka zo ɗaukarsa zuwa office ne yasa ya ji daɗi kamar ya kashe shi, cikin isa ya gyara kwalar rigarsa haɗe da motsa kafaɗunsa kafin ya shige. Daga wannan rana aikin Sufyan da ya mayar da kai ya miƙa, cikin kwanaki ya ƙara gogewa ya fara ɗaukar hanyar zama Sufyan Dhahab ɗin da yake fata. A computer yake ganin irin Tukwanen da Company Dhahab suke ƙerawa amma bai taɓa ganinsu ido da ido ba, domin ma'aikar da ake ƙera Tukwanen daban yake da na sarrafa shinkafa da yake aiki. Sai dai labarin Tukunyar da ya ke datsa jefi-jefi a wajen Abokanan aikinsa. Hankalin Sufyan ya ƙara tsayuwa waje ɗaya bayan samun tabbacin Turawane manyan Company, ƴan asalin ƙasar Abyad tsirrai ne a ciki. Cikin ɗumbin narasa, kwanciyar hankali, ƙaruwar soyayyarsa da Sumaya, manta Naila gaba ɗayanta, rayuwar Sufyan ya miƙa. BUSHRA; tun ranar da ta sauka a Babban Birnin Abyad bata samu nutsuwa ba sai da ta tattara ta bar ƙasar gaba ɗaya. Saboda har lokacin bata cire ran samun kira daga Malik ba. Lokacin da taje Dhahab ma a tsaitsaye suka gaisa da Simbi Uzair ya dawo da ita Gida. Daga wannan rana ta ƙauracewa ƙasar Abyad gaba ɗaya, sai saƙon kuɗi da take aikawa Yasar ya bawa Naila. NAILA; Duk da ta saki jikinta a wasu lokutan tanajin ranta babu daɗi, tanaason magana da Kaaka amma bata da hanyar samunta. Tana cikin wannan yanayin ta zana jarabawar share fagen shiga jami'a ita da ƙanwar Yasar. Har lokacin babu kira daga Sufyan, kuma bai zoba, ko Yasar ya daina kira a waya. Kwanaki biyu da gama zana jarabawar su aka kira Yasar Interview a Dhahab Babban Birnin Abyad. Rai babu daɗi Yasar ya fara shirin tafiya Babban Birnin Abyad. Bazata taɓa manta alkhairin da ya yimata ba, da abubuwa dayawa da bazan taɓa iya mantawa da su ba, ya yi mata alƙawarin zaman ƙanwarsa a tare da ita. Sai dai da yaje yiwa Iyayensa sallama ƙememe suka nuna ba su amince ƴar su ta zauna a inda babu mafaɗi ba, da yake Naila ta rakasa domin dawowa tare da ƙanwarsa a gabanta suka dinga sakin maganganu marasa daɗi da nuna ita ɗin ba wata abar aji tausayi ba ce. Bata yi kuka ba, ba kuma taga laifinsu ba amma ta ɗan ji haushinsu tunda ko ba komai ai sai su yi tunanin suma tasu ɗiyar zata iya tsintar rayuwarta a cikin kwatankwacin irin wanda ta riski na ta a ciki. Har suka dawo Gida haƙuri Yasar yake bata, ta na ta nunamai babu komai. A washe garin ranar da ya rage saura kwana ɗaya Yasar ya tafi Babban Birnin Abyad ya kai Naila ya buɗemata asusun ajiyar kuɗi a Babban bankin Birnin Abyad, tare da siyayyan kayan abinci da kayan maƙulashe kala-kala. ★washe gari da sassafe Yasar ya fito zai tafi. Ta yi kuka irin kukan da ban san iyakarsa ba, sai take ji kamar ita kaɗaice a duniyarta, sai ta ke jin kamar ta bishi taga inane wannan Dhabah ɗin, su waye a ciki, tanaji a jikinta kamar ta san su, kamar tana da alaƙa da su. Cikin kuka ta ce idan ya je ya gaishemata da mutanen cikin Dhahab. Duk yadda Yasar yaso ya jure kasawa ya yi yasa kuka da haka suka rabu da Naila ba tare da sanin ranar da zasu ƙara ganin juna ba. Naila bata taɓajin kaɗaicin da ta ji ba a kaf rayuwata irin ranar da Yasar ya bar Birnin Abyad. Ko ina yayimata shiru wa su lokutan sai ta ji kamar motsi a bayanta wa su lokutan kuma sai ta ji kamar ana kiran sunana. A wannan dare ta gane girman rahamar zama da mutum a waje ɗaya. A haka wahalallen barci ya ɗauketa cike da mafarkai ma su ban tsoro. A haka ta shafe kwana uku cikin kaɗaici duk da tana waya da Yasar jefi-jefi a rana. Tun tana jin tsoro har ta haƙura ta sanyawa zuciyata dakiya. Da sannu zuciyarta ta ƙeƙashe ta daina jin tsoron komai. Zata tashi da safe ta yi Breakfast ta ci na ƙoshi idan rana tayi ta tafi Gidan Customers ɗinta wa su kuma su biyota Gida. Idan Dare ya yi ta ɗauki kuɗi a cikin kuɗin sana'arta ta je nasha Ice cream a wajen da Yasar ya nunamata. A haka rayuwata ta miƙa, jarabawarau ta fito tayi kyau. Da taimakon Abokin Yasar ta samu gurbi a jami'a mai zaman kanta na Birnin Abyad duk Bushra ce ta biya ta hanyar Yasar, shi kuma ya turawa amininsa. Kuɗin siyayyar kayan abinci da abubuwan amfani Yasar ya turomata. Da ta rasa kalar godiyar da zanyi musu shi da Bushra kuka na sanya. Duk da Bushra ta ƙauracewa waya da ita, ta ƙauracewa zuwa inda take domin ta jima da dawowa Babban Birnin Abyad amma saboda tana tsoron kar ta cigaba da zuwa wajen Naila asamu matsala, sai ta daina kiranta, ta daina zuwa wajenta ko ta shigo Birnin Abyad gudun kar ta ƙara saka Naila a cikin matsala. Da taimakon Abokin Yasar Naila ta kammala komai na fara attending lectures A ranar da ta fara zuwa Makaranta da yamma bayan sallar la'asar ta fita siyayyar abinda zatayi amfani dashi tunda a Hostel zata zauna saboda tazarar Makarantar da Gidansu. Doguwar Riga mai taushi da faɗi taa sa ta naɗa mayafin da ya yiwa fuskarta da ya rage rama kyan gaske. Waya da card ɗin da zatayi siyayya dashi kawai ta ɗauka. Wajen siyayya mafi girma a Birnin Abyad ta nufa saboda a can zata samu duk abinda take so. Tun shigowarta ta hango Sufyan hannunsa sarƙafe da na Macen da bata sani ba (Sumaya). Ya yi kyau irin kyan da yake buri, ya ƙara haske da ƙiba kamar ba Sufyan ba. Macen ce ta fara hangota kamar ta Santa, sai ta ƙara ƙanƙame hannun Sufyan cikin kishin da ya bayyana a saman fuskarta. Naila ba ta nuna ta gansu ba, ta fara ɗaukar abinda ya kawota. Duk yadda Matashiyar da ke tare da Sufyan ta so janye hankalin daga ɓangaren da Naila take sai da ya waiwayo. Da farko bai gane Naila ba sai daga baya. Hannun Sumaya ya saki da sauri ransa na suya, hassadar yadda ta canza har ta samun ƴanci da kuɗin yin siyayya a wajen da ya kawo Budurwarsa na cin zuciyarsa. Naila tana sane da tahowarsa kafin ya ƙaraso ta yi wuf ta nufi wajen biya. A kwai mutane a wajen don haka ya juya ya na ɗaukar komai a hanzarce don suyi su gama, bai damu da yadda Budurwartasa take ƙunci ba. Lokacin da ya iso da jibgin kayan siyayyarsu lokacin Naila ta nufi ƙofar fita. Yaso jirkintawa su gama biya amma ganin kamar hakan zai ɗauki lokaci har Naila ta ɓacemasa kawai sai ya miƙawa Sumaya card ya bi bayanta da sauri ba tare da tsayawa kallon ƙuntatacciyar fuskar Sumaya ba. Ya na fitowa Naila tana shiga Taxi kafin ya shiga Mota tuni mai Taxi ya bar wajen. Lafiyayyen motar da Company Dhahab suka siyamasa ya shige a hanzarce. Da speed ya bi bayansu kar su tsere mai, ganin sun ɗauki wani hanyar daban ba na gidan daya sani ba sai ya ji hassada na naiman kassarashi zuciyarsa na tiriri. Naila suna isa gare ɗin Makarantarsu da ɗan hanzari ta sauko daga Taxi dama tun a ciki taa sallamesa. Gate ɗin Makarantar nufa hankalinta a kwance duk da ta hango motar da na ke kyautata zaton na Sufyan ne. ID ta nuna ta Securities su ka barta ta wuce. Tana shiga ta ƙara shiga Motar da zai kai ta har bakin Hostel ɗinsu. Sai a lokacin ta saki ɗan dariyar da ya ƙaramata kyau tana hasaso irin ƙuncin da Sufyan zaiji domin tasan ko shi yafi kowa kuɗi baza'a barshi ya shigo ba, tunda bashi da Numbern wayar kowa kuma bai san kowa ba a Makarantar. Sufyan sai ta nutsuwarsa ya yi bayan ya yi parking domin kai tsaye suka hanashi shiga kamar yadda ya so. Ba irin bayanin da bai yi ba, babu kuma irin rantsuwar da baiyi ba shi Mijin Naila ne amma suka nuna su sam basu santa ba duk kwatancen da ya yi musu. "shin yamasan a gaban wani University yake tsaye kuwa? Securities suka tambayeshi. Sai a lokacin ya ɗaga kai yana kallon sunan da yake jiki saman Dogon Ginin ɓaro-ɓaro a take ya ji hassada na naiman kasheshi jirin baƙin ciki na naiman kai shi ƙasa. Sum-sum ya dawo wajen Motarsa yana jin muzanta a karon farko tun bayan tafiyarsa Babban Birnin Abyad. Da ya shiga Mota kasa jurewa ya yi, ya fara dukan kujerun motar ya na surutai "Ni Naila zata yiwa taurin kai, har ta yarda su kawota jami'a irin wannan, wallahi! Wallahi!!! Wallahi!!! Sai nayi sanadiyyar barinta Birnin Abyad wayyo zuciyata zata fashe" ya ƙasara faɗa ya na dukan saitin zuciyarsa....✍🏻 [7/24, 9:20 PM] nafisaaliyusasaal: 🔥ZINARE🔥 SASAAL 19 Sufyan ba wannan ne zuwansa Birnin Abyad na farko ba. Tun lokacin da aikinsa ya miƙa komai ya yi mai yadda yake so ya fara kawowa Sumaya ziyara. Sumaya macece tasan kuma abinda Sufyan yake yiwa Iyalinsa ba daidai ba ne, a addini har ma da al'ada amma son kai da tsanin son zuciyar kutsa kai cikin abinda batasan mafarinsa ba yasa take ganin kamar Sufyan ma son Iyalinsa ya ke yi banda haka ya saketa mana kawai ita ya gabatar da ita a wajen Iyayensa suyi aurensu. Har layin tasha zuwa taga yaya Naila take.. Son zuciyar Sumaya kaɗan ne akan na Mahaifanta, domin su cewa su kayi bazasu ba shi Sumaya ba har sai ya saki Naila. SUMAYA Da Sufyan ya dammaƙa mata Card zuciyarta ce kawai bata haɗiya ba, kishi ya toshe komai nata gani take yi duk kuɗin da Sufyan yake ikirarin ba shi da shi Naila yake kashewa ba Iyayensa yake turawa ba kamar yadda ya faɗa. Saboda tun fara aikin Sufyan ranar ne kawai tasan ya yi mata siyayya ma su nauyin kuɗi, duk zuwa idan ya yi ƴan kuɗine yake rabawa Mahaifanta. Amma ga Matarsa nan tayi kyau tasa sutura na alfarma, saboda kishin ma kar wani ya ganta har rufa mata baya ya yi yana muzurai sai ka ce wani sakarai. To kenan yaudararta ya ke yi da ya ce ba ya zuwa wajen Naila? Da kuka shaɓe-shaɓe ta tari Taxi ta nufi Gida. SUFYAN; bayan ya gama bige-bige da ayyana irin ramuwar gayyar da zai yi akan abinda Naila ta yi mai sai ya ɗauki hanyar Gidan su Sumaya. Kukan da take yi da irin maganganun da take saki Iyayenta na ƙara tunzura ta ne su ka ƙara harzuƙa Sufyan, cikin tsananin fushi ya buge kofin tangaran ɗin da su ka zuba masa lemo a ciki, a take ya fashe. Sumaya tana yunƙurin zaginsa ya zuba mata marin da ya taɓa zuciyar Iyayenta, Babanta ma na yunƙurin kwasamai mari ya riƙemai hannu, kafin ya jefar da hannun da iya ƙarfinsa. Cikin isa da takaici ya ce; "ki je mun rabu! kuma karki ƙara nemana tunda har yau baki fuskanci Naila itace mukullin ƙofar nasarata ba" yana gama faɗa ya bar madaidacin living room ɗin da aka ƙawata da kuɗin Naila kafin ya samu aiki. Da sakakken baki ya bar su, saukar kalmarsa na "sun rabu" na cakar zuƙatansu sama da raɗaɗi marin da ya saukewa Sumaya da hannun Mahaifinta da ya jefar, saboda Sufyan da shi suke taƙama domin sanadiyyar haɗuwarsa da Sumaya rayuwarsu ta sauya ba kaɗan ba. Sumaya kuka take yi har da birgima, danasanin abinda ta aikata na mamaye zuciyarta. Sufyan baya ɓoyemata tasan da kuɗin kitson Naila suke ci suke sha a makarantar kuma sanadiyyar Naila ya samu aikin da ya ke yi, amma ita ta rasa dalilin da ya sa ta tsani Naila. Daga wannan rana Sufyan ya ƙauracewa kiran Sumaya. Ga hotuna da ya ke saki masu kyan gaske a shafukansa, duk domin Sumaya tasan ko a jikinsa. Ya yi narasa kuwa domin Sumaya ƙara gigicewa tayi. Ba dare ba rana kullum sai ta turamai saƙo. Rasa yadda zata shawo kanshi yasa ta turamai saƙon tayasa fakon Naila, har ya samu damar mayar da ita Yankin Tudu kamar yadda yake yawan faɗe tun kafin ya tafi Babban Birnin Abyad. cikin jimami ta zauna zaman jiran amsar da zai bata. NAILA; cikin nasara da wadatacciyar nutsuwa ta fara gudanar da karatunta. A ɓangaren sana'arta kuɗi ta ke samu ba kaɗan ba, saboda ƴaƴan manyan mutane da suke Campus ɗin su waɗanda kansu ya ke kitsuwa a wajenta suke yin kitso. Cikin watanni ta ƙara zama wayayyiyar mace sai sanyin kyau da ɗabi'a. Ba ta shiga sabgar da bai shafeta ba tana kuma tsayawa a iya matsayina. Tana zuwa Gida jefi-jefi musamman ranar sati. Batun Sufyan kuwa tuni ta share shi a ranta, ta mayar da hankali kan abinda ya kaita Makaranta. Yasar kullum shi yake ba ta ƙarfin gwiwar yin karatu idan sunyi waya, domin shine matakin zamanta a Birnin Abyad na din-din har ta kawo Kaaka su ƙarasa rayuwarsu. Wannan ƙwarin gwiwar da Yasar yake bata ba ƙaramin dadinsa ta ke ji ba. A hankali komai ya yi ta sauyawa watanni na shuɗewa, shauƙin son zuwa Yankin Tudu domin ganin Kaaka na ƙara mamaye ran Naila, a haka suka fara shirye-shiryen zana jarabawar da zamu yi hutu mai ɗan tsahon da zata iya zuwa Yankin Tudu ta taho da Kaaka. Kamar yadda Yasar ya shawarceta tunda tana samun kuɗi. SUFYAN; bai daina son Sumaya ba amma yanason ta gane shi ɗin Namijin da za'a lallaɓa ba wanda za'ayiwa hargagi ko rashin kunya ba. Ko da yaga saƙonta fuska ya yi, domin yasan ba ta da wani abun tsinanawa, kawai don ya kulata ne. Magiya da nacinta ba dare ba rana ne ya dawo da soyayyarsu har ya fara yunƙurin tarar Mahaifansa da batun ta, tare da shawarar da ya yanke na sawwaƙewa Naila kafin ya aiwatar da ƙudirinsa a kanta. Cikar Sufyan shekara ɗaya a ma'aikatar Dhahab yasa sukayi mai kyautar da ya hanasa runtsawa. Waya kuwa kwana sukayi suna yi da Ɗayyib, cikin isa Sufyan yake bada umarnin abinda za'ayi da kuɗin. Ba bu lissafin yinƙurin yin wani abu na cigaban Yankinsu a kason kuɗin da duk wani kuɗi da yake turawa sai Gidan Sarautar su da aka ƙara ƙawatawa, musamman ɓangaren Mahaifansa Ɗayyib da ɓangaren Kakansa Jalal. Ba bu wani tsarin tallafi da suka tsiro da shi a matsayinsa na Ɗan Yankin da ya samu cigaba a Babban Birnin Abyad sai dai mutanen gari su gani a jikin Iyayensa, ƴan Masarautar su da Gidajensu, duk da mummunar talaucin da suke fama da shi. Har lafiyayyen titi aka shimfiɗa daga farkon shigowa Yankin Tudu har ƙofar Masarautar su. A ɓangaren Ɗayyib da Sufyan ya fara samun kuɗi Gidan Game ya buɗe ƙato matasa su samu kuɗi suyi ta bugawa Yara kuma su sato kuɗin Mahaifansu. Abun takaicin sai Matasa da Iyayensu sun sha wahala sun ƙera Tukwane sun samu an siya daƙyar sai Ƴaƴan su kwashe kuɗin su gudu gidan Game ɗin Ɗayyib. Cikin ƙanƙani lokaci shima ya fara zama hamshaƙi. Dukka wannan facakar sai dai ƴan uwan Naila da Kaakarta su ji labari, kamar dai gama garin mutane ba surukan Sufyan ba. Ɓullowar batun auren Sumaya da Sufyan, ya tayar da ƙura a tsakanin Hindu da Ɗayyib don sai da sukayi faɗan da ya kaita ga tafiya Gidansu. Ta kafe bata yarda da auren ba matsawar ita ta haifi Sufyan domin malaman tsibbunta sun sanar da ita sakin Naila zai rusa komai, haƙurin mutanen da suka zubawa Sufyan ɗin ido ya na zaluntarta har suka ɗaukesa aiki zai ƙare daganan suyi masa ɗaurin talalar da zai mutu a ɗaure. Sam Ɗayyib bai yarda da batun Hindu ba, acewarsa ɗaukakar Sufyan daga Allah ne, babu wata Naila don haka dole su bar Sufyan ya rayu da abinda yake so. Ankai ruwa a tsakanin su har sai da Jalal Mahaifin Ɗayyib ya shiga faɗan da suke yi a sirrince don bakowa ba ne yasan Hindu bata gidan ba. Sai da Mahaifiyar Hindu ta saka baki, sannan ta yarda da auren amma da sharaɗin ko zai saki Naila sai lokacin da ta yarjemai. A kan haka suka bar zancen. Da tsananin rawar kai Sufyan yake rabon katin aurensa ga Manyan ma'aikatarsu. A cewarsa ma bai taɓa Aure ba. Labarin auren Sumaya da Sufyan sai da yaje har kunnen Bushra, ba tare da ɓata lokacin ba ta naimi Yasar ya toshe duk wata hanya da Naila za ta iya jin labari, saboda kar hakan ya kawomata tsaiko a jarabawar da take zanawa. Kuma da zarar ta gama ya shirya mata tafiya Yankin Tudu. A rabon Invitation card da Sufyan yake yi ne, Baturen da yake sama da shi ya bashi shawarar ya shirya katin gayyata na musamman ga GM wataƙila ya samu alheri mai yawan gaske. Da yake Sufyan ɗan son banza ne a daren ya biya kuɗi mai yawa aka shiryamai katin gayyata na musamman. Washe gari kafin ya shiga office ya miƙawa ogansa ya bawa GM ba tare da nutsuwa ya yi tunanin maiyasa tunda ya ke aiki a Dhahab bai taɓa ganin GM ba, ko da gilmawarsa ne. Gaba ɗaya sai Sufyan ya matsu ranar Aurensa ya zo, irin shagalin da ya tanadi maƙudan kuɗi za'ayi a Yankin Tudu na sanyashi jin alfaharin da bai taɓa jiba. Ɗayyib da su Sarki Hammam da ya yi kwantan ɓauna kamar yana tare su ne su suka zo Birnin Abyad Gidansu Sumaya naimawa Sufyan aure. A take Iyayen Sumaya da suka matsu da komai suka ce sun bashi sati mai zuwa a ɗaura aure su tafi da Ita Yankin Tudu su je can suyi Biki, a maimakon wata ɗaya da suka tsara da Sufyan tun kafin zuwan Iyayensa ya yi rawar kan buga katin gayyata. Iyayen Sumaya sun ce su basu da wani shagali da zasu yi bayan ɗaurin Aure. Abin takaici daga Ɗayyib har da muƙarabansa da suka zo Birnin Abyad tare ba bu wanda ya tambayi ina ƴarsu Naila Ƴar Yankin su take? a wani yanayi take ciki?. Kowannen su fuska ya yi yana dirzar duniyar da ya samu. Da rawar jiki Sufyan yake ƙara bawa manyansa haƙurin matso da lokaci kusa an samu akasi. Wa su sun nuna zasu je wasu kuma tambayarsa suka yi babu wani shagali da za'ayi ranakun da zasu biyo bayan ɗaurin auren da zasu iya zuwa? Da sanyin jiki ya sanar da su na Yankin Tudu tunda yasan ba lallai su je ba. Ga ɗumbin mamakinsa washe gari ya samu saƙo GM ya ce ya amsa gayyata amma ba zai samu zuwa ɗaurin aure ba, sai dai na Yankin Tudu da za'ayi In Shaa Allahu. Sufyan ihu yasa ya na tsalle, har ya fara hango irin ƙafafa da zafin kan da zai yi, inama da Naila tana wajen ya nunamata ko babu ita shi ya zama kafin Allah a Dhahab sai dai ta mutu da baƙin ciki. Cikin walwala da son Daular da ya ke iya canza tunanin ɗan Adam lokaci ƙanƙani su Ɗayyin suka cika sati guda a Birnin Abyad. Ranar Ɗaurin aure Irin fareren Turawan da suka zo ɗaurin auren Sufyan da Sumaya a Birnin Abyad ne yasa bakin Ɗayyib yaƙi rufuwa. Bayan komai ya lafa sun keɓe Ɗayyib ya murmusa cikin alfahari ya ce; "Sufyan ina alfahari da kai akanka na fara samun cikar burina na tsayin shekaru, kaga Ubangidana ko, sam bai halarci ɗaurin aure nan ba kuma nasan yana gari, dama ina sane da shi, tun daga kan takardun da na ce ya samar maka ya ƙauracewa waya dani, to dama haka rayuwa take, yau ina jina na daban ya ya ma kace sunan wannan Ma'aikata taku mai albarka." Ya ƙarasa faɗa yana kafa lemo mai tsada a baki. Sufyan da ke murmushin isa ɗan dariya ya yi kafin ya ce "DHAHAB" Azababben tari ne ya sarƙe Ɗayyib lemon da ya kurɓa ya soma biyomai ta hanci da baki... NAILA; A dai-dai lokacin da Tari ya sarƙe Ɗayyib Naila ta kammala haɗa kayan tafiya Yankin Tudu....✍🏻 Wanene General manager company sarrafa shinkafar Dhahab da Sufyan yake aiki a ƙarƙashin shi?😄 Maiyasa ya zaɓi zuwa wata ƙasar shagalin ta ya murnar ma'aikacin da ya ke ƙasan-ƙasansa duk da girman matsayinsa. Yaya zaman Naila a Yankin Tudu zai kasance shin zata dawo ko bazata dawo ba? Kaaka tana raye ko bata raye? Wani 🔥🔥 ne zai kama a Yankin Tudu? Next page In Shaa Allah [7/25, 8:47 PM] nafisaaliyusasaal: 🔥ZINARE🔥 NAFISA ALIYU SASAAL *CHAPTER 3* *YANKIN TUDU🔥* Page 20 NAILA; da ƙananun kayan Calvin Klein ta yi sauƙaƙaƙiyar adon da ya dace da siffarta ya kuma haska kyanta. Fuskata ƙunshe da murmushi take kallon mutanen Birnin Abyad, farkon zuwansu Birnin ita da Sufyan na dawomata. Rashin banbancin da ke tsakanin fatarsu ta ɓangaren murjewa a yanzu yasa ta ɗan faɗaɗa murmushinta. Ashe komai zai sauya, ashe itama zata zama ƴar gayu kyakkyawar Macen da zatayi alfahari da kanta wata rana. Dogon mota mai kyau ta hau, idonta tsaye ƙyam a kan hanyar Babban Birnin Abyad. A wannan karon tana alaƙanta kallon hanyar da Yasar da Bushra da suke can tare da Sufyan, murmushi ta yi data tuna abinda su Bushra suka ɓoyemata, duk da Bushra tasa Yasar ya ɓoyemata koma sai da taga komai a shafin Sufyan kamar yadda take bibiya lokaci zuwa lokaci. Babban sauyin da ta samu a komawarta Yankin Tudu shine jirgin da ta bi a maimakon Mota da taimakon mutumin Bushra bayan isarta Airport. Cikin ɗan tsoron da ya mamaye ranta saboda hawarta jirgi a karon farkon kenan jirgin su ya ɗaga zuwa Iyakar Yankin Tudu da Babbar tashar da filin saukarsa ya ke. SUFYAN; Da hanzari ya nemo ruwa ya miƙawa Ɗayyib, haɗe da nanata kalmar "sannu" da yake tayi ba ƙaƙƙautawa. Ɗayyib ya ɗauki tsahon mintuna ya na tari, fararen idanuwansa da suka ƙara haske saboda daular da ya samu na kwana biyu ya juyewa zuwa jajaye marasa kyan gani. Da salon murya da Sufyan bai san Mahaifin nasa da shi ba ya ce; "Kasan menene DHAHAB" cikin rashin fahimtar ina ya dosa Sufyan ya ce; "Zinare mana Baaba" "Sufyan ina nufin kasan mafarin ƙirƙirar Dhahab, tunda kake a duniyarka ka taɓajin mai inkiyar banda Ahalin Marigayi Sarki Musa" cikin rashin fahimtar abu da wuri Sufyan ya ce; "Waccen Dhabah ɗin ai zuri'arsu ta mutu Baaba, waɗannan turawa ne ba ma ƴan asalin ƙasar Abyad ba ne, kusan dukka manyan da suke samana Turawa ne." Ɗayyib cikin rashin gamsuwa ya ce; " Wanene mamallakin ma'aikatar ba ina nufin GM ɗin da zai zo shagalin bikinka ba, tunda ance suna da reshe da yawa, asalin mamallakin Dhahab ɗin nake nufi gaba ɗayanta, kasan sunansa da inda yake da zaune" Sufyan ido ya zaro cikin mamaki ya ce; " Babaa ba ni da issue da duka waɗannan abubuwan da ka lissafo burina kawai na samu kuɗi, Ni ma na zama Dhahab ɗin kaina, tunda na lura sunan ya na da wani ɓoyayyen sirri, shine kawai." Kamar talabijin haka Ɗayyib ya zubawa bakin Sufyan ido, zuciyarsa kuwa Allah Ne kaɗai yasan faɗinta da sirrikan data ƙunsa. Da kaushin murya ya ce; "Daga ranar irin ta yau kafara saka lissafin abinda na tambayeka a cikin ƙwanyarka, domin ba ra'ayi ba ne ko ganin dama ba, tilas ne musan su wanene masu Dhahab, aikinka zai fara daga yau Sufyan!" Ɗayyib yana gama faɗa ya miƙe jiri na ɗibansa sama-sama. Kafaɗa Sufyan ya ɗaga alamun ko a jikinsa, shi ba shi da wannan ra'ayin da dai maganar kuɗi ne da kyau to da sai iya inda ƙarfinsa ya ƙare, amma ace duk Kuɗin da ya tara sai ya je yana binciken abubuwan da basu shafesa ba, why not ya ba shi shawarar ƙirƙirar wani hanyar da zai ƙara tara dukiya shima ya zama Dhahab ɗin da'akewa kokawa shekara da shekaru har ake salwantar da rayuka duk domin a kawar da su. SUMAYA Tasha gyara kyanta da farin fatarta sun ƙara fasowa. Sufyan daya ganta kamar ya siɗeta bini-bini ya kirata a waya su share mintina suna hira. Kayan alfarmar da zai fitar da Sumaya ta zama ta musamman sama da yadda Ubaidullah ya kawo Kakar Sulaim Nanaah Yankin Tudu aka tanadarwa Sumaya da taimakon Ɗayyib da kansa aka fitar da adon kayan da ya dace da Masarautarsu. Bayan komai ya kammala tsirran ƴan uwan Sumaya da kansu yake rawar Ƴar uwarsu tayi dacen gidan kuɗi da Sarauta suka fara shirye-shiryen tafiya Yankin Tudu. Ranar Alhamis da ya rage saura kwana biyu shagin Yankin Tudu suka ɗugunzuma dukkansu, abin birgiyar daga Company su Sufyan aka turo da motoci na alfarmar da zai kaisu Airport. Sarki Hammam da ya jima da yin kwantan ɓauna domin tsiratar da rayuwarsa da samun bayanai murmushi yake saki cikin ransa ya na mamakin ɗabi'unsu. WAIWAYE Shekarun baya... Labarin da Dattijo Junaid ya bawa Sarki Hammam, labari ne akan ɓarnar da su Ɗayyib suka kwashe shekaru su na yi a ɓoye. Bayan rasuwar Dattijo Junaid Sarki Hammam ya shiga ɗimuwa da zullumi. Saboda yasan shi ma wata rana matsawar zai yi tsayuwar tsayin daka akan gaskiya to tabbas zai bi sawun su Dattijo Junaid ba da jimawa ba.. Rasuwar Bashar ya ƙara jefa zuciyarsa cikin ɗimuwa, musamman da ya ji ƙishin-ƙishin ɗin ba fa mutuwar Allah da Annabi Bashar ya yi ba, ana zargin Ɗayyib ne ya shaƙamai guba. A hutun da Sarki Hammam ya tafi Babban Birnin Abyad bayan rasuwar Bashar ya haɗu da Malik, ya kuma gano Dhahab ɗin da su Ɗayyib suke kokawar sai sun ɓaddashi ya na nan daram a Babban Birnin Abyad, amma kamar yadda Malik bai sanar masa wanene yaƙara kafa Dhahab daga cikin zuri'ar Marigayi Sarki Musa ba, shima bai zurfafa dole sai ya sani ba. Sun yi taƙaitacciyar tattaunawa da Malik. A cikin tattaunawarsu Malik ya bashi shawarar ya shiga jikinsu Ɗayyib domin sanin motsinsu, ya zubawa zaluncinsu ido har zuwa lokacin da Ubangiji zai ƙaddara ƙarshensu. Idan kuma suka yi zaluncin da ya ratso da haƙƙin wani to ya sanar masa, shi kuma zai yiwa kowaye a cikinsu hukunci dai-dai da abinda ya aikata.. Bayan dawowar Sarki Hammam daga Babban Birnin Abyad sai ya zama ɗaya daga cikin Informer Malik a cikin Masarautar Yankin Tudu, da ma Yankin baki ɗaya ba tare da kowa ya ankara ba... *YANKIN TUDU* NAILA; lokacin da jirgin su ya sauka a iyakar mafarin shiga Yankunan su, murmushi ta saki, zuciyarta na azalzalata tanajin ƙarfin gwiwar da bata taɓa jiba. Cikin kasuwar chanjin wajen da yake kusa da Airport ta shiga aka canza mata kuɗin ƙasar Abyad zuwa na ƙasarsu, bat rage ko sisi ba. Kuɗine masu yawan gaske don haka ta zuba su a cikin jakar da ta tanada domin su. Masauƙin baƙi ta nufa na canza Suturar jikint zuwa Abayar da suka fi amfani da shi a Yankin Tudu duk da wanda bata da ɗan bambanci. Drivern da ya ɗaukosu ita da Sufyan shekarun baya shi ya ƙara ɗaukarta. Da shi da Motar tasa duk sun tsufa sun jeme. Gudu yake yi amma sai take ganin kamar baya sauri saboda yadda ta matsu ta riski Kaka ta ga ko ita yaya ta koma? Hirar yadda Yankinsu ya koma Driver yake yimata muryarsa a raunane da yadda Sufyan ya ke kashe Kuɗi a iya Masarautarsu da mutanen cikinta. Naila bata tsawaita magana da shi ba, saboda yadda zuciyarta take suya. Lokacin da suka shigo Yankin Tudu batasan sanda dariyar da ya bayyana jerarrun haƙwaranta ya kufcemata ba. Suna isa ƙofar gidan Kaka da zumuɗi ta buɗe murfin motar, kuma tayi sa'ar babu mutane. Duk suna cikin Gidajen su sai tsirran da ba'a rasa ba. Da taimakon shi ta sauko da kayan tsarabar da ta jibgo. Kuɗi ma su nauyi ta ɗauko ta bashi da sunan kuɗin da ya ɗaukota. Ƙasa ya zube yana kuka cikin shesheƙa ya ce; "Allah Ya aramin ranar da zan saka miki da abinda kikayimin Allah Ya haska gabanki Ya haska bayanki, Na gode! Na gode!!!" Kai ta girgiza mai haɗe da kutsawa Gidan Kaaka. Murnarta ce ta koma ciki sanda tayi ido biyu da yadda Kaaka ta rame ta lalace fatarta ta yamushe kamar babu ruwa a jikinta. Da farko Kaka bata gane Naila ba, sai daga baya, da gudu ta taso garin ta iso inda Naila ta ƙame a tsaye ta zube ƙasa saboda tuntuɓen da ta yi. Da sauri Naila ta ƙarasa suka ƙanƙame juna, tana kuka itama Kaka tana kuka. A haka Drivern ya gama shigo mata da kayanta. Kaka kallon Naila tayi ta shafa fatarta sai ta fashe da kuka, ta yi haka ya kai sau uku, kafin ta miƙe tayi hanyar waje. Naila bayanta tabi da kallo tana share hawayebta. Jakar kuɗin da ta zo da shi ta adana tana sakin murmushi. Layi-layi Kaaka ta bi tana kuka tana cewa; "Ya ku ƴan uwana mutanen Yankin Tudu ku fito ga jikata Naila ta dawo daga Ƙasar Abyad, ku fito ku ganta Mutanen Yankin Tudu" Kafin ka ce me, dangin Mahaifin Naila, da mutanen gari daga kowani ɓangare sun cika Gidan. Kowannensu idan ya yi dariya sai dai kaga haƙoransa ya cika masa fuska saboda rama. Maza da mata haka suka cika Gidan Kaka. Da Naila ya kalli fuskokinsu da yadda suke dariyar da yake nuna irin farin cikin da suke ji sai ta fashe da Kuka. Suma da yawansu sai suka saka kuka suna zayyanomata labarin irin talaucin da suke ciki. Tsabar da ta taho da shi a take ya ƙare wa su ma basu samu ba. Bayan kowa ya watse Mahaifiyar Kabeer da ta kasa tafiya ta matso kusa da Kaka, da ƙaramin murya take roƙon ita bata samu ba su taimaka mata, da Naila ta kalleta ta tuna da ɗanta Kabeer ɗaya fita Zakka a ƴaƴansu saboda zafin naima sai ta fashe da kuka, da sauri ta miƙe shiga Ɗakin Kaaka na ɗauko kuɗi ta bata. A wannan dare kwanan labari Naila sukayi da Kaka cikin kuka mai taɓa zuciya. Da ƙarfin gwiwar Kaaka dana Yasar Naila ta yanke shawarar ƙin zuwa Gidan su Sufyan idan ya ji haushi ya bata takardarta ta. ★washe gari labarin dawowar Naila da shirye-shiryen shagalin bikin Sufyan da ƙin zuwan Naila gaishe da Mutanen Masarautar Yankin Tudu ya bazu ko ina, har kunnen Hindu mahaifiyar Sufyan da Kakansa Jalal. Ƙura ba taƙara tashi ba, sai da Naila ta ɗebi dubban mutane Yankin suka shiga Kasuwar Maƙotan Yankinsu abisa shawarar Kaaka suka siyo ɗayyan abinci a farashi mai rahusa. Aka fara rabawa Talakawan Yankin. A wannan rana sai da hankalin duk wani mai faɗa aji a Masarautar Yankin Tudu ya tashi, domin ɗabi'ar da Naila ta tsiro da shi ɗabi'un Zuri'ar Marigayi Sarki Musa ne. Labari bai tsaya a iya Yakin Tudu ba har kunnen Sarki Hammam, Sufyan da Ɗayyib da suke can Birnin Abyad suna shirye-shiryen tahowa. Sufyan kishine ya kamashi, shi kuma Ɗayyib da yake komai nasa a lissafe yake tafiya, a take ya alaƙanta kalan taimakon da Naila ta da mamallakin Companyn Dhahab da ɗansa yake aiki, kenan dole akwai ɓoyayyen dalilin da yasa aka ɗauki Sufyan aiki kai tsaye, saboda ko maƙaho a Yankin Tudu yasan irin taimakon da akace Naila ta yi yasan irin na jinin Marigayi Sarki Musa ne. Domin su ne suke taimako da gumin su, su kuma kawowa mutanen Yankin su cigaba da ƙwaƙwalwar su. Lokacin da labari ya riskesu su na Airport, don haka suka matsu su iso ayi shagalin biki agama su kawo ƙarshen komai. A can Yankin Tudu wajensu Naila Ba bu tsangwama babu nuna waccen nawa ne, wannan ba nawa bane, Naila ta bada umarnin su kasafta abincin a tsakaninsu. kuka da addu'o'in Tsofaffi, Maza da mata, Matasa, da Yara ne yake ta tashi tare da kabbarorin su ta ko ina. Maimakon sanya idon da bindiddigin auren Sufyan sai Mutanen Yankin suka mayar da hankali wajen yiwa Naila addu'o'i da fatan nasara mai ɗorewa. A wannan rana Naila ta wuni cikin jindaɗi da soyayya daga ɓangaren Mahaifi harma da ɓangaren Mahaifiyarta da suka samu labari. Kaf kuɗin da Naila ta ɗauki shekaru tana bautar yin kitso da wanda Bushra da Yasar suke bata ta tattara ta bayar aka siyi kayan Abinci, sai abinda ba'a rasa ba daya ragemata ta bari a jikinta, tana addu'ar Allah Ya kawo ninkinsu. Barci mai cike da nutsuwa suka yi ita da Kakaa. Ranar da su Ɗayyib suka sauka wanda ya yi dai-dai da ranar cin kasuwar Zinare Naila da Mutanen Yankin sukayi shawara sukayi shawarar rushe Gidan Game ɗin Ɗayyib, da suma ƙiris suke jira har da matasan da suka ƙara ganin mutuncinta saboda abincin da rabawa Iyayensu, tsanar Ɗayyib ya yi kane kane a zuciyarsu. Bayan gama cin Kasuwa kowa ya addana abinda ya samu suka taru suka rushe ƙaton wajen da Ɗayyib ya kewaye da langlanga. Sannan Mazansu da Matansu sukayi tattaki har ƙofar Gidan Sarki Hammam da saukarsu kenan sukayi ƙorafin basason Gidan Game da Gidan Rawa lalata masu Yanki yake yi!. Kayan Game ɗin cikin wajen da suka rusa babu wanda ya taɓa ko ɗaya, Matasa majiya ƙarfi ne suka Tattaro suka zuɓe a ƙofar Masarautar Sarki Hammam. Da yake bikin Sufyan suke burin suyi hankali kwance sai Sarki Hammam ya fito ya basu haƙuri. Ɗayyib mutuwa ne kawai baiyi ba. Jalal Mahaifinsa da muƙarabansa a ranar suka shirya taro a kan Naila saboda sun samu labarin ita ta kitsa komai, tare da bawa Sufyan umarnin sakinta da gaggawa, da shawarar kama Naila da Kakarta suka fara yankewa sai dai hakan zai tunzura mutanen Yankin da dama can a gajiye suke ayi tashin hankalin da ba sa so, shine suka yanke shawarar Sufyan ya saki Naila. Hukuncin su Jalal gagarumin rigima ya tayar domin Hindu a take ta nuna Sumaya ba ta yimata ba idan kuma Sufyan ya sakeni sai ta tsinemai. Sumaya dake lulluɓe cikin mayafi bata fuskanci duk abinda yake faruwa ba, ita da ƴan uwanta sai zare ido sukeyi. Jalal ne ya daki ƙasa kai tsaye ya ce ƙaryar Hindu ya na so kafin rufuwar mintuna Talatin takarkar Sakin Naila ya isa ga ahalinta. GIDAN KAKA Sarki Tsafin Yankin Tudu da su Jalal suka butulcewa saboda ɗaukakar da Sufyan ya samu ne yasa Maza majiya ƙarfi masu ƙarfin tsafi a Jikinsu su yi gadin kaf faɗin kewayen Gidan Kaka saboda Naila. A ɓangaren Matasan Yankin suma ƙofar Gidan Kaka suka mayar majalisar su har da abin shiffiɗar kwanciyar su saboda tsaron kar a biyoni cikin dare, Ni ma kuma ban gajiyaba wajen ambaton Ubangijin halittu. NAILA; bayan ta huta suka ƙarayin waya da Yasar ya kuma ƙaramata ƙarfin gwiwar kar ta gajiya nasara na nan tafe In sha Allahu kafin dawowarta. Da bayin Gidan Sarki Hammam Mata ta ɓangaren Jalal suka isar da saƙon Jalal na sakin Naila a gidan Kaka da rufa ido ɗaya a cikinsu da dama don abinda aka turota da ragowar kenan ta ɗauke wayar Naila. Su Naila ba su ankara ba sai bayan tafiyarsu. A daren Ɗayyib ya yi duk wani bincike shida Sufyan da ƙwararren masanin na'ura mai ƙwaƙwalwa a Masarautar amma basu ga alama ɗaya daya haɗa Naila da Ma'aikatar su Sufyan ba. Cikin ɗacin hali Sufyan ya farfasa wayar ya cire layin ya karya. ★washe gari layi-layi fadawan Sarki Hammam suka bi suna gayyatar mutanen Yankin filin wasannin ƙarshen mako don gudanar da shagalin bikin Sufyan. ★ Ranar da ya kama shagalin bikin Sufyan da Sumaya. Sufyan ya yi ado na kece raini duk da ba haka yaso ba Naila ta ɓatamai komai. Sarakuna daga Yanki-Yanki ƴan kasuwa da ƴan siyasa, su aka warewa waje na alfarma har da wajen da GM ɗin Sufyan da sukayi waya suna kan hanya zai zauna. A cikin Dattawan da suka je gudun abinda zai biyo baya har da Mahaifin Kabeer da ya tsufa ya yanƙwane saboda wahala. Lokacin da taro ya yi taro motocin Ɗayyin da Sufyan ya sabunta suka tafi taro GM ɗin Companyn sarrafa shinkafa ta Dhabah. Isowarsa Motar da Gm yake ciki da saukarsa daga Mota duk akan idanuwan Mahaifin Kabeer. Dark blue suit mai nauyin kuɗin gasken daya kwantawa farin fatarsa da kakkaurar jikinsa ya sanya. Gashin kansa dake amsar gyara na kwance luf. Lokacin da ya fara takawa, Mahaifin Kabeer da yunwa tasa ya ranƙwafa ya yanko wajen da aka hanasu ƙetarawa saboda su talakawa ne da gudu. Cikin ihun da ya haɗe da kuka ya ke faɗin; "Ashe Malik zai cikamin alƙawarin da ya ɗaukarmin! sai dai ya shammceni, da na san irin wannan alfaharin yake nufi da na tattara masa dukka Ƴayana ya tafi da su. kabeer Ɗana ashe da gaske zaka dawo garemu bayan mun cire rai, lallai Allah Abun godiya ne." Cak Kabeer ya tsaya haɗe da buɗe dukka hannayensa da ke fitar da wani irin ƙamshi. Cikin soyayyar Uba da Ɗa kabeer ya rungume Mahaifinsa. Babu wanda bai miƙe ba, babu kuma wanda bai razana ba daga waɗanda suka san Kabeer har waɗan da basu sanshi ba. Da wani irin fushi Ɗayyib yake taka ƙasa kamar zai hudasa, gaban Sufyan da shi ma yake tsaye kamar mutum mutumi ya tsaya ya na kai hannunsa saitin ƙugun wandonsa. Da zafin zuciyar azabar dake neman halakasa tashi ɗaya ya ce; " Lallai ban haifo ɗa ba sai soko kaicona! Nasan Malik ya ɗauke Kabeer ya inganta masa rayuwarsa da turomana shi a irin wannan lokacin domin ya nuna mana iyakar mu, kuma ya yi nasara. Amma idan har Malik zai mallaki dukiyar da zai sauya rayuwar Kabeer, Kabeer kuma ya sauya taka kai kuma ka sauya namu to tabbas su na da Ubangida, Uban gidan da ya kamata ace kasani tuntuni, amma sai gashi ko Kabeer ɗin ma baka sani ba Balle kuma Ubangidan su, daga yanzu har zuwa ajalinka ba zan taɓa yafe maka ba Sufyan har sai ka gano min wanene DHAHAB 🔥????? Ɗayyib ya ƙarasa faɗa yana yankar ƙuncin Sufyan da wuƙar da ya zaro a ƙugunsa, a take jinin kumatun Sufyan ya yi tsartuwar da ya fallatsa har saman fuskar Ɗayyib....✍🏻 Barka da Jumu'a. [7/27, 9:52 PM] nafisaaliyusasaal: 🔥ZINARE🔥 NAFISA ALIYU SASAAL Page 21 Sufyan kansa ya sunkuyar ƙasa, raɗaɗin yankar da Mahaifinsa ya yi mai a kunci da yankar da Kabeer ya yi masa a zuci na naiman zautar da shi. Shi da kansa kunyar kansa yake ji, baƙin ciki mai girma na da ɗa mamaye zuciyarsa. Ɗayyib da ya juya ya kalli irin gyaran da Masautar Yankin ya samu da dukiyar da kai tsaye za'a kirasa da na Malik da irin manyan mutanen da ya ɓata dukiya ya gayyata saboda Kabeer kawai, sai ya ƙara juyowa. Da wani irin fushin mai girma yake yankar Sufyan ta ko ina yana maimaita "Ko Marigayi Sarki Musa zai dawo duniya a raye ba zan yimasa irin wannan hidimar ba na rantse da Sarki Allah! Sufyan ka cuceni! Ka cuceni!!" Daƙyar aka ƙwace Sufyan da ya yi kacha-kacha da jini a hannun Ɗayyib da ya zama kamar Mahaukaci. Mutanen Jalal ne suka ja Ɗayyib cikin Gida, shi kuma Sufyan aka wuce da shi Asibiti yana ihun azaba kafin ya sume. Sarki Hammam a take ya bayarda umarnin a rufe iyakar Yankin Tudu, kuma a turo masa Kabeer cikin Iyayensa da gaggawa. Da ƙananun gulmammaki taron shagalin bikin Sufyan ya watse maimakon yabo da ya ci burin yasamu a wajen Mutane. Kamar yadda Sarki Hammam ya bada umarni haka akayi sai dai babu Kabeer babu Iyayensa. Da gaggawa Sarki Hammam ya ƙara bayarda umarnin abi duk Yankin da yayyen Kabeer mata suke aure a kamo su. Sai dai suma duk basanan acewar Surukansu sun bar Gida da sunan zuwa shagalin bikin Ɗan shugaban kasuwar zinaren Yankinsu tare da rakiyar Mazajen su da Ƴaƴan su. Babu inda ba su bincika ba amma babu Kabeer babu ahalinsa. Dagaske dai Kabeer ya gudu da dukka ahalinsa. Ɗayyib da labarin ɓacewar Kabeer da ahalinsa ya riskesa Ihu ya kurma haɗe da ɗaura ɗamarar binciko Kabeer da ahalinsa a duk inda suke. Fadawan Sarki Hammam majiya ƙarfi Jalal ya bawa umarnin tare Ɗayyib daga barin Masarautar, ya na fizgewa suna tarosa, daƙyar suka danneshi aka nemo likita ya yi mai allurar barci. WAIWAYE Da Malik ya ɗauko Kabeer daga gidansu a sirrince ya fitar da shi iyakar Yankin Tudu sukabi Jirgin samansu zuwa ƙasar Abyad. Daga wannan rana Malik baiyi ƙasa a gwiwa ba sai da Kabeer ya zama abinda zai sosai zuciyar Ɗayyib da shi. Ya na shirin ɗauko Iyayen Kabeer, bikin Sufyan ya Kunno Kai, don haka suka turasa bayan sun shirya yadda zai taho da Iyayensa da zarar taro ya hargitse. A zahirin gaskiya Kabeer shugaban Sufyan ne a wajen aiki amma ba shi ne GM ba, Uzair da Naila ta taɓa ganin mai tsananin kama da Salman ne GM. DAWOWAR LABARI Lokacin da Ɗayyib ya fara yiwa Sufyan magana, Kabeer ya sulale da Mahaifansa har da ƴan uwansa suka bar Yankin, dama kuma tuni motocin ɗaukar su Kabeer yana Yankin amma saboda taron mutane yasa babu wanda ya ankara. NAILA; ɗaukemata waya da Bayin Gidan Sarki Hammam sukayi ya zama iyaka tsakaninta da Yasar, saboda tanan kawai yake iya sanin halin da take ciki. Lamarin ya sosa zuciyarta tare da ɗaga mata hankali sama da Sakin da Sufyan ya yi mata, domin ko bai saketa ba, dama tayi alƙawarin bazata ƙara iya rayuwar auren rashin ƴanci da shi ba. Damuwar da ta shiga akan hanyar da zan ƙara samun Yasar ba ƙaramin tashin hankalin Kaka ya yi ba, cikin ƙarfin halin ɓoye ta ta damuwar take jaddamata ko da karo-karon ne zasu haɗamata kuɗin Mota ta koma Makaranta ita da ƴan uwan Mahaifinta dana Mahaifiyarta har ma da mutanen Yankin. Wannan ƙarfin gwiwa da Kaka ta bawa Naila sai ya gusar da duk wani damuwa da fargaba da ke danƙare a cikin zuciyarta na fara walwala kamar kowa. A haka suka kwashe kwanaki uku cikin gidajensu, ba tare da dogon zirga-zirga ba, abisa umarnin Sarki Hammam. SUFYAN; yasha azaba irin azabar da bai san akwai irinsa ba, kullum cikin kuka yake tunda ya farfaɗo daga duniyar azabar da Mahaifinsa ya kaisa. Sumaya ta na gefe itama tasha kuka idanuwanta duk sun koɗe, wahalar da bata taɓa tunanin zatasha ba har su gama rayuwar Aurensu da Sufyan shi take sha, idan zai yi fitsari da Toilet duk ita take taimaka mai gashi da raki kuma ita dama can ba saba aikin wahala ta yi ba. Ga shi Bayin ma da aka bari Maza ne masu gadinsu balle su taimaka mata. Ƴan uwanta suma gaba ɗaya sun matsu su koma Birnin Abyad, danasanin rako Sumaya Yankin Tudu na damun zuciyarsu. A ɓangaren Hindu bayan barinta Yankin Tudu zuwa Yankinsu, kai tsaye wajen Malaman dubanta ta wuce. Tabbacin suka bata na; nasarar Sufyan da isarsa tsakiyar Babban Birnin Abyad da kuma samun ɗaukakarsa mai girman gaske ya na tare da Naila, babu abinda ya sauya. Amma ita da Sufyan sun karya dokar da aka shimfiɗa musu tun farko. Na farko zaman Sufyan a Birnin Abyad saɓanin Babban Birnin Abyad da aka sharɗan ta musu, na biyu gaggawar Sufyan na yin Soyayya da Sumaya har da aurenta. Na uku sakin Naila da ya yi, shi ya ƙara wargaza komai. Da rawar murya kuka Hindu take roƙon asama mata wata mafitar tun da wannan ya lalace. Sihirin da za'a shayar da Naila ya bata na tsahon kwanaki uku ba tare da rarrabewar kwanaki ba. Zata dawwama a ciwon da babu magani, bayan tasha wahala Sufyan zai je da sunan taimakonta. Idan har Iyayenta sun amincewa Sufyan ya samu damar ɗaukarta zuwa Masarautar su to ta dawo za'a bata maganin da zai karyar sihirin da sukayimata ta samu sauƙi, daga nan sabon shirin tunkurarsu Babban Birnin Abyad zai kankama da zafin da dole nasara ta tabbata. (Anya wannan nasarar zata tabbata🤔) Da wannan ƙwarin gwiwar Hindu ta fara shirye-shiryen dawowa Yankin Tudu, bayan tayi kwanakin da ta ɗibarwa kanta. ƊAYYIB Har sati ɗaya ya shuɗe idanuwan Ɗayyib ba su washe ba, baya iya magana saboda baƙin cikin da suka yi mai karo. Ko Asibiti yakasa zuwa duba Sufyan, itama Hindu tattare lamarinta ya yi ya watsar, burinsa ya samo ina Kabeer da Malik su ke, su bashi labarin wanene Uban gidansu. Babban Malamin duba da suka musanya bayan faɗarsu da Sarkin Tsafin Yankin Tudu Jalal ya gayyato tun daga wata ƙasar domin fayyace musu abinda Ubangiji ne Masani akai. "Ina su Malik da Kabeer suke? A wacce duniya suke rayuwa? Shin dagaske Kabeer shine Uban gidan Sufyan. Wanene ko wacece asalin Uban gidansu? Waɗannan tambayoyin shi su Ɗayyib suke neman haske a kansu ido rufe. Bayan sun gama korowa Malamin duba bayani. A duban da ya yi Abu ukun da suka tambaya bayyanannu ne amma na ukun saninsa sai Allah. Na farko inda Malik da Kabeer suke da duniyar da suke rayuwa, na biyu kuma shin dagaske Kabeer shine Uban gidan Sufyan, Na ukun da ya kasa gonowa shine sanin asalin Uban gidan su. Amma ya kuɗurce a ransa bazai gayamusu ba sai abinda zai faranta ransu su biyasa kuɗi mai tsoka, don haka ya gyara zama ya yace; "Kabeer da Malik suna wani gari ne Daf da shiga Babban Birnin Abyad, kuma suna rayuwa ne kusa da Company da Sufyan yake aiki ba a cikin asalin ƙwaryar Babban Birnin Abyad ba. Kabeer kuma ba shine Uban gidan Sufyan ba, a yadda dubana ya nunamin Kabeer ba shi baya aiki ma da Ma'akatar su Sufyan kawai rufa ido ya yi muku. Asalin Ubangidan Malik kuma Macece wacce ta taɓa zama a nan Yankin Tudu amma nakasa gano asalin wacece" Da sauri Ɗayyib ya miƙe yana dariya, cikin yaƙini ya ce idan ba Nanaah Faɗima ba ( kakar Sulaim matar Ubaidu) to Aysha ce( matar Abduh Dhahab Mahaifiyar Sulaim). Da sauri malamin duba ya gyaɗa kai alamar gaskiya ne. Kuɗi masu nauyin dake bayyana jindaɗinsu suka sauke mai. Da murmushin samun nasarar duƙunƙune sun da ya yi, ya saɓa jakarsa ta zallar fata ya yi musu sallama. A zahirin gaskiya Kabeer da Malik tabbas a kusa da Company Dhahab suke rayuwa, amma da gaske Kabeer shine Uban gidan Sufyan yasan idan ya faɗi gaskiya a matsayinsa na babban malamin duban da suka ɗauko tun daga wata nahiyar ba zai samu kuɗi mai tsoka ba, batun Macece ko Namiji ne asalin Uban gidan su Malik ba shi da sanin komai akai, shima ya faɗa ne don ya faranta musu shima su faranta mai. Da mugun murmushi malamin duba ya hau motar da zai sadashi da iyakar Yankin Tudu da tumulin kuɗinsa a jaka. Da gaggawa Ɗayyib da bai taɓa zuwa duba Sufyan ba ya ɗauki hanyar Asibiti, ɗauke da wayar Sufyan da ya jima a kashe. Bai damu da halin da Sufyan yake ciki ba, ko yaya yanayin jikinsa yake ya naimi waje ya zauna. Cikin sanyi murya Sufyan ya gaisheshi. Da sakin fuska ya amsa yana yi mai yaya jiki, ko kallon inda Sumaya take baiyi ba, balle ya yi mata godiyar hidimar da takeyi da ɗansu, sai ta basu guri zasuyi magana da ya faɗa a kausashe. Jiki a sanyaye Sumaya ta bar Ɗakin nadamar auren Sufyan na mamaye ruhinta, tausayin Naila da ta fita shaƙar takaici da rashin samun rayuwar Ƴanci na tsarga mata, "ashe haka Naila take ji? Wallah na cuci kaina kaicona!" Ta faɗa ƙasa-ƙasa cikin kuka. Bayan fitar Sumaya Ɗayyib ya mayar da kansa kan Sufyan. Wayar Sufyan ɗin ya miƙamai. Babu wasa a fuskar Ɗayyib kamar ba Mahaifinsa daya sani a baya ba. Jiki a sanyaye Sufyan ya kunna ya ajjiye yana jiran umarnin da zai biyo baya. "A baya ina lallashinka domin ka yi min biyayya akan abinda kai ne zaka samu cigaba ba ni ba, amma ka bijiremin, to a wannan karon ba cigabanka bane kai kaɗai cigabanmu baki ɗaya, mun gayyato malami daga wani Birni, ya kuma shaida mana Kabeer ba shine Uban gidan ka ba, rufa ido ya yi mana, ba wai don ban yarda da shi ba, sai don na ƙara tabbatarwa nakeson ka kira wanda ya miƙa katin gayyatar bikinka wajen GM ɗinku ka ji dagaske ne ko a'a" Sufyan yaso ya musa, amma tuna irin yankar da ya sha yasa ya fara lalubo number jikinsa yana rawa. Bugun farko aka ɗaga da Muryar jimamin da ya nuna andaɗe ana naiman mutum ba'a samesa ba. Bayan sun gaisa da hanzari Baturen yake tambayar lafiya, bai dawo aiki ba ko fushi yake yi GM bai samu halartar taron shagalin bikinsa ba, ya yi haƙuri uzuri ne ya tareshi, ga ayyuka ta ko ina a office amma ba bu shi, don Allah ya dawo. Daga Sufyan har Ɗayyib ajiyar zuciya suka sauke mai ƙarfi kafin Ɗayyib ya tashi ya rungume Sufyan cikin kukan farin ciki ya ce; "ɗana Sufyan ina mai neman afuwarka, sai dai banason wannan damar ya zama abin sakankacewa garemu, inaso ya zama fitilar haska mana asalin wacece ta ƙara dawo da Dhahab a tsakanin Nanaah Faɗima da Aysha" Sufyan da yake son tambayar su wanene Faɗima da Aysha shiru ya yi tuna Mahaifinsa zai iya tuhumar mai yasa bai sansu ba. A haka Ɗayyib ya share hours ya bar Sumaya zaune a waje ba tare da damuwar komai ba. A wannan yanayin Hindu ta iso Asibitin kallon inda Sumaya take batayi ba balle ta amsa gaisuwarta. A wannan karon ma ɗari bisa ɗari Ɗayyib ya amince da batun da Hindu ta zo dashi, tare da bawa Sufyan umarnin sakin Sumaya da zarar sun koma Birnin Abyad ya ajjiye maganar Soyayya ya fuskanci gobensa. Sai dai dole sai sunyi taro na musamman a kan yadda za'a shayar da Naila sihirin da Hindu ta zo da shi. Shi dai Sufyan kai kawai yake ɗaga musu saboda tsoron yin magana ma yake yi. Tun a baya kowa yasan mutanen Yankin Tudu da son kansu da tsananin butulci, sai dai talauci da tsananin rayuwa ya sa suka sauya zuwa mutanen ƙwarai, amma duk da haka ba'a rasa nono a ruga kuma baza'a taɓa taruwa a zama ɗaya. NAILA Sartaj ya na ɗaya daga cikin matasan da suke yawan shigowa Gidan Kaka, kuma yana daga cikin waɗanda suka dinga bata kariya, yawan shigowarsa ya haifar da shaƙuwa a tsakaninsu har yakan ci abinci Gidansu. Da ƙwaɗayin asalin jinin Yankin Tudu da butulcinsu da bai gama barin jinin Sartaj ba su Ɗayyib su ka samu dama sukayi amfani da shi. Sai dai shure-shure baya hana mutuwa....✍🏻 Na gode da Addu'o'inku Allah Ya bar mu tare Ya kuma bar zumunci. [7/28, 9:46 PM] nafisaaliyusasaal: 🔥ZINARE🔥 NAFISA ALIYU SASAAL Page 22 Kuɗi masu nauyi a hannu da rashin albarka wajen sauke buƙatu Jalal da kansa ya biya Sartaj, bayan ya siyar da yardar da amince dake tsakaninsa da su Naila. Da tattacen kayan marmari Sartaj ya fara amfani. Ya na zaune suna hira da Naila har ta shanye. A kwana na biyu da yankakkun kayan marmari ma su kyan gani a ido ya yi amfani. A kwana na ukun da ya kasance na ƙarshe da abincin Gidan Kaka ya yi amfani. SUFYAN; Sufyan bai ƙarasa warkewa ba suka tattara suka koma Birnin Abyad da sunan idan sun isa ya miƙawa Sumaya takardar ta kafin ya wuce Babban Birnin Abyad bakin aikinsa. NAILA; Labarin tafiyar Sufyan bai zama abin damuwa a gareta ba, domin abinda kake so shi kakeyiwa kishi. A hankali ta fara ramewa ƙasusuwan jikinta suka fara bayyana kansu kamar ba ta cin abinci, kasalar rashin son yin Sallah a kan lokaci da ƙinyi azkhar na neman zamemata jiki. A cikin kwana biyar tayi wani irin ramar da ya tsoratar da kowa. Kaka bata wahalar da kanta wajen kai Nsila Asibiti ba, tunda tasan su wanene Iyayen Sufyan. Malamin da ya taimaka mata a waccen lokacin da Hindu ta ciyar da ita Tufa mai ɗauke da sihiri ta nufa. Bai buƙaci a kawo Naila ba da kansa ya zo. Ya na ganinta ya tabbatarwa da Kaka abinda take zargi, sai dai sihirin da aka yiwa Naila ba irin nata bane, samun maganinsa abune mai matuƙar wahala domin a wajen wani Malami da ke gabashin Yankin Tudu za'a iya samu maganin karya Sihirin. Cikin kuka Kaka take faɗin; "wanene ya zaɓi Duniya akan lahira?, wanene ya zaɓi shayar da marainiyar Allah sihiri irin wannan, Allah bamu da kowa sai Kai!" Babu wanda bai tausayawa su Naila ba. Cikin fusata matasan Yankin suka nufi da suka samu labari suka nufi Gidan Sarkin tsafin Yankin Tudu ya duba musu wanene ya shayar da Naila Sihiri?.. A take kuwa yana dubawa ya gano Sartaj ne. Gangamin Matasan Yankin Tudu ne sukayiwa Gidansu Sartaj zobe, Sartaj ba shi da Uba sai Uwa itama ta fara tsufa. Cikin alhini da fargaba take sanar da su yanzunan Sartaj ya ce mata zaije Fadar Sarki Hammam gurin Mai girma Jalal wai yana naimansa. Bayaninta ya ƙara fusatar da Matasan tare da ƙara tabbatar da maganar Sarkin Tsafi, don haka suka koma Gidajensu kowa ya ɗebo makamai sai fadar Sarki Hammam. A fito musu da Sartaj su yankemai hukunci dai-dai da abinda da ya aikata. Suke ta nanatawa bayan isarsu Harabar gidan Sarki Hammam. Ihun su da maganganunsu ma su khaushi ne yasa Sarki Hammam umartar fadawansa su lallashesu su kuma sanar da su Sarkin Tsafin Yankin Tudu ba gaskiya ya faɗa ba, so yakeyi ya hanasu zaman lafiya tunda ya ci amanar Masarautarsu ta koresa shiyasa su ma yake so ya tunzura su. Kuma lallai ya na bada umarnin kar wanda ya taɓa lafiyar Sartaj idan ba haka ba zai fuskanci hukunci mai tsanani. Duk da an sanar da Matasan Yankin Tudu wannan jawabi na Sarki Hammam basu motsa ba, har sai da Sarki Hammam ya fito da kanshi ya taushesu da kalamai ma su taushi tare da tabbatar musu da ƙarya Sarkin Tsafin Yankin Tudu yake yi, Sartaj da ya ke na hannun damar Naila tayaya zai ciyar da ita sihiri? Ba don sun gamsu ba sai don bin umarnin Sarki Hammam wajibi ne a garesu suka tattara suka dawo Gida. Da labarin abinda ya faru ya isa wajen Kaka ba tace komai ba sai kuka da takeyi tsoron mutane da rashin yarda da su na ƙara kamata. Bayan zuwa Matasa wajen Sarki Tsafi, da kansa yazo duba Naila har ya faɗi wasu maganganun da Kaka tayi watsi da su nan take. ★washe gari Matasan Yankin suka yanke shawarar fita naimo Malamin da zai yiwa Naila magani a Yankin gabashin da ake ce yake ko kuma ya basu maganin su kawomata. Kaka da tana dama da ta hanasu domin ko sun karɓo bazata iya yiwa Naila amfani da shi ba, saboda bata yarda da kowa ba. Matasan Yankin mu su Goma sha uku, sun kwashe kwanaki huɗu a gabashin Yankin Tudu amma ba su samu Malamin ba, sai maganin da suka ƙarbo daga takwarorinsa. Da hannu bibbiyu Kaka ta karɓi maganin su, tare da tarin godiya mai yawa. Sai dai tana karɓa ta zubashi a shara. Sartaj ya fito yana rayuwarsa kamar kowa amma bayayin nisa da Gida a wayonsa kar wani ya yi mai wani mugun abu. Hanyar Gidan Kaka tuni ya zama haramiya a garesa. Cikin watanni biyu Naila ta ƙanƙance ta tsotse ta dawo kamar ba ita ba idan Kaka ta kalleta sai ta fashe da Kuka tana cewa; "Ba sai mun nemo mai warware mana sihiri ba, mai warware mana yana tare da mu, kuma In Shaa Allahu da ƙarfin mulkinsa sai kinga har jikokinki Naila" idan Kaka ta faɗi haka Naila fuskarta da ta dawo ƴar ƙarama ta yamushe take kawarwa gefe tayi kukan da batasam iyakarsa ba. Kaka bata gajiyawa wajen kaiwa Allah kukansu, dare da rana, Safiya da yammaci. Jinkirin samun sauƙin Naila bai sa Kaka ta karaya ba. Taimako da ake basu ne ya farayin ƙasa, abincin ci ya fara gagararsu, yunwar da ya yi sauƙi a Yankin Tudu ya dawo sabo fil, amma duk da haka da zarar sun ci kasuwar Tukwanen Zinare Matasan Yankin zasu haɗowa Kaka kuɗi, haka ƴan uwan Mahaifin Naila, a wasu lokutan har da Kakanninta na wajen uwa. Shawarar dawo da sana'ar Mahaifiyar Naila na ƙera kayan wasan Yara na lakar ƙasa Kaka ta yanke. Drivern da yake fita iyakar Yankin Tudu ta roƙi alfarma ya dinga kaita bakin tasha tana siyarwa idan tayi ciniki ta biyashi, tunda kullum sai yaje. Kai tsaye ya nuna mata kyauta zai dinga kaita ya dawo da ita amma tana ganin barin Naila a gida ba zai zama matsala ba, mai zai hana ta dinga lulluɓeta suna tafiya tare? Da sauri Kaka ta amince domin itama fargabarta kenan yadda zata bar Naila ita kaɗai a Gida. Ba ta naimi shawarar kowa ba, kwana biyu bayannan suka fara bin Driver zuwa Iyakar Yankin Tudu. A gefe Naila take rakuɓewa, Kaka kuma matafiya take bi tana tallata musu su zo su siya kayan lakar da ta ƙera Fisabilillah. Cikin hukuncin Ubangiji, sai tausayin Kaka da tausayin yadda Naila ta koma ya sa mutane suka yi ta siya har da masu ba su kyautar kuɗi. kullum ba sa dawowa Gida da rogawa sai ya ƙare. kuma Driver bai taɓa karɓar ko sisinsu ba. Duk wannan wahalar da Kaka take sha haka take ƙara raba dare a zaune tana kaiwa Allah kuka, domin bata iya tsayuwa saboda shekaru da wahalar da take sha. Ƴan uwan Mahaifin Naila sun kawo ƙorafin ta dinga barin Naila a Gida, amma ta nuna sam bata yarda ba, tunda suma ba zama sukeyi ba kowa nema yake fita, matansu kuma ba lallai su kula da ita ba. A lokacin da suka cika sati shida da fara fita Iyakar Yankin Tudu, jirginsu Sufyan ya sauka. Ya dawo Yankin Tudu, Motocin Mahaifinsa ne suka je tarbarsa amma da yake gulmar halin da su Naila suke ciki ya je mai tun kafin ya iso, sai ya gwada zuwa inda suke zama, don kawai yayimusu izgilanci kafin ya wuce. Lokacin da ya iso ɗan rumfar da suke zama Kaka tana can tallatawa matafiya kayansu Naila kuma tana rakuɓe da ruwan shan da Kaka ta bata a gefenta. Dariyarsa kawai Naila ta ji a kanta. Kafin ya fara magana Cikin izgilanci; "Naila korarriyar Ɗalibar da talauci ya hana iyayenta naima mata magani ta warke ta koma Makaranta, ba kina ganin zaluntarki mukayi ba, lokacin da muka yi miki gata muka kaiki Birnin Abyad muka baki makwanci. Amma saboda butulci don kawai ina karɓar kuɗin kitson da kike yi kika zaɓi tozartani, yanzu gashi Ni da ke waye yake ji a jikinsa, kalleki dan Allah." Naila bata ɗago ba sai yawun da take ta tofawa ruwan hannuna kamar zautacciya. Farar fuskarsa da ya ke matuƙar ji dashi ya shafa dai-dai satin Yankar da Ɗayyib ya yi masa da bai gama bajewa ba ya ƙara ce wa; "Banso haukarki tasa bakya gane maganganuna ba, amma wannan yawun da kike tofarwa da adanawa kikayi wataƙila kya rage wannan yamutsewar da kikay..." Saukar ruwan har cikin bakinsa yasa ya kurma ihu haɗe da tsalle kamar ƙaramin Yaro kafin ka ce kwabo tuni Matafiya sun cika wajen, suna kallon Sufyan da yake ihun "Saliva! Saliva!!" Haɗe da waftar ruwan hannun mutane yana wanke fuskarsa da bakinsa. Gudun abun kunya ba tare da bin ba'asi ba Fadawan Sarki Hammam suka jashi Mota. Abinda Sufyan bai sani ba maganar Naila ta koma kamar ta ƴan yara ba kowane yake Fuskantar ta ba, ko azabar ciwon ya tashi sai dai ta yi ta kuka bata iya bayani yadda za'a fuskanceta. Shiyasa Kaka bata wahalar da kanta wajen tambayar abinda ya faru ba ta koma wajen tallata kayanta, suma mutanen da suka taru kowa ya kama gabansa. A hanyar su ta dawowa Naila tke yiwa Kaka kwatancen abinda ya faru. Dariyar da rabonta da yin irinsa har ta manta Kaka ta ƙyalƙyale da shi, har suka isa gida lokaci zuwa lokaci sai ta saki dariya. A wannan dare Naila tasha azaba irin azabar da batasan yadda zata misaltashi ba, da taimakon addu'o'in da Kaka take tofamata barcin ya ɗauketa. Kafin wayewar gari ta ƙara fita hayyacinta, babu wanda hankalinsa bai tashi ba. SUFYAN; har ya suka isa gida bai sanar da Fadawa abinda ya faru ba suma kuma ba su tambayesa ba sai sannu da suke ta jeromai. Ya yi wanka ya fi sau biyar haka bakinsa ya wanke yafi a ƙirga. Da daddare bayan Sallar isha suka ɗauki hanyar Yankinsu Hindu Mahaifiyarsa shi da da ita. A daren Malaman Hindu Suka turo jinnun da zasu matsawa Naila da zarar Sufyan ya zo da buƙatar komawarta tare da albishir ɗin samo Malamin gabashin da suke nema Su Kaka za su amince a mayar da aurensu. Sufyan aka bawa maganin da Naila zata sha sihirin ya karye ya zura a aljihun bayan wandonsa. Gaba ɗaya sai ya matsu gari ya yi haske domin a daren suka ƙara dawowa Yankin Tudu. Da Safe ko wanka bai yi ba balle ya karyawa ya nufo Gidan Kaka da sunan duba jikin Naila kamar yadda suka tsara a daren bayan dawowarsu kafin zuwan su Ɗayyib. Babu wanda ya rakosa, fuskarsa a tsamke alamun dai ba'a son ransa zai zo ba. Sallama ya yi Kaka da batasan shi ba ne ta basa izinin shigowa. A tsakar gida ya samu Kaka ƙannen Mahaifin Naila su na ɗaki tare da ita kowa ya na tofamata duk addu'ar da ta zo bakinsa. Kaka tana ganinsa ta dakata daga hura wutar da takeyi. Cikin ladabi kamar gaske ya tsugunna yana gaisheta. Kafin ya ɗago Kaka ta rarumo ƙaton iccen da ya ke ci da wuta ta nufesa. Sufyan ya na hangota ya yunƙura ya miƙe a guje, garin wannan yunƙurawa Maganin bayan aljihunsa da aka basa tun daren jiya baiyi wanka ba kuma bai cire kayan ba, dama kuma aljihun bawani zurfi ne da shi ba ya faɗo ƙasa ba tare da ya ankara ba. Ƙur Kaka take kallon magananin, kafin ta yi Bismillah ta na yunƙurin kai hannunta. Muryar mutum taji a bayanta.....✍🏻 [7/29, 10:01 PM] nafisaaliyusasaal: 🔥ZINARE🔥 NAFISA ALIYU SASAAL Page 23 Da hanzari Kaka ta ɗauke ƙullin maganin ta wurgashi kwanon gefenta. Yayyan Mahaifin Naila ne suke yunƙurin fitowa. Sallama su kayi mata, tare da alƙawarin kawo wani malamin ya ƙara duba jikin Naila. Su na fita Kaka ta sauke ajiyar zuciya, ba ta koma ɗakin ba tasa mayafi ta lalluɓe jikinta sai gidan Mallam. Mallam Juya maganin yake yi a hannunsa fuskarsa da yalwataccen murmushi ya ce "Tabbas! Allah ba Ya barci, sun biyota har gida sun shayar da ita sihiri, Allah kuma Ya ƙaddara su zasu ƙara biyota gida da makarin sihirin." Kaka da ke ta zare ido alamun bata fahimta ba domin ta ɗauka wani bala'in Sufyan ya ƙara kawo musu. Dalla-dalla Mallam ya yi mata bayani. Ko Cikin kuka Kaka takai goshinta ƙasa tana yiwa Allah godiya. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, shayar da Naila maganin a Yankin Tudu zai dawo da hannun agogo baya, domin da zarar sun ga ta warke zasu ɓullo ta wata hanyar, mai zai hana tunda Naila tana da matsugunin haya a Birnin Abyad da kuɗinsa bai ƙareba tunda Bushra kuɗin shekaru uku ta biya kamar yadda Naila ta faɗa, Kaka ta bi can suyi jinyar tare. Kaka wani irin kallo take yiwa Mallam fuskarta ɗauke da murmushi, kafin ta fashe da kuka domin ta rasa abun faɗa, bata taɓa kawo irin wannan shawarar a cikin zuciyarta ba balle ta samu mafitarsa a zahiri sai gashi Mallam ya haska mata hanya. Ta na godiya tana kuka. Bayan tasha kuka sai ta ƙara naiman shawararsa akan yadda zasu tara kuɗin motar zuwa Birnin Abyad. Kaka da murnar da ta danne a cikin zuciyarta ta dawo Gida, cikin jakar da take adana muhimman abubuwa ta anada maganin makarin sihirin jikin Naila. Kaka har Yankinsu Mahaifiyar Naila ta yi tattaki ta kai mu su koken ance akwai malami a Birnin Abyad da zaiyiwa Naila magani ta warke kuma ita bata da halin da zasu iya tafiya tare, su taimaka mata da abinda suke da shi. Kakan Naila mutum ne mai jama'a, don haka kafin tafiyar Kaka ya shiga layi-layi yana roƙon a taimaka mai za'a kai jikarsa ƴar gidan marigayiya Birnin Abyad neman magani kuma basu da hali a taimaka. Kafin rufuwar hour uku sai ga kuɗi masu yawa sun taru. Kakannin Naila ba su cire ko sisi ba suka bawa Kaka kuɗin tare da alƙawarin kowawa Naila ziyara kafin su wuce. Kaka ɓoye kuɗin ta yi ta tunkarin yayyan Mahaifin Naila bayan ta dawo, suma ɗari bisa ɗari suka bayarda da goyon bayansu, saboda samun lafiyar Naila ta koma bakin karatunta shine burinsu domin daga gareta suke sa ran samun canji. Suma layi-layi suka bi suna shela. A ranar dai ba'a samu waɗanda suka bayar da kuɗi ba, amma washe gari bayan sun ci Kasuwar Tukwanen Zinare suka dinga kawo kuɗi, kafin kace me kuɗin zuwa Birnin Abyad har da na cin abinci da extra sun haɗu. Su ma Yayyen Mahaifin Naila tasu gudummawar suka kawo, tare da tattaunawa sirri da Kaka, akan idan Naila ta warke kar su dawo, su yi zamansu a can ta dinga kula da Naila, tunda ta iya riƙe Sufyan har da taimakon Mahaifansa da sana'ar kitsonta to suma zasu samu ingantacciyar rayuwa a chan, za su ƙara taro wasu kuɗin da zasu dinga cin abinci kafin jikin Naila ya ƙarasa warwarewa. Kaka tana kuka tana godiya suma kukan suke yi suna nuna mata cigaban Naila shine burinsu. Bayan komai ya lafa Kaka ta koma gidan Mallam domin yimasa godiya akan shawarar da ya ba ta. Wa su addu'o'in yaƙara bata, domin yasan duk daran daɗewa su Jalal za su samu labari warkewar Naila, duk da ba lallai Sufyan ya ba su labarin yardar da maganin da ya yi ba. SUFYAN; bayan ya fito daga gidan Kaka daidaita tafiyarsa ya yi kamar komai bai faru ba. Bayan ya kai gida ɓangarensa ya wuce ya yi wanka ya yi Breakfast dukka ransa ba daɗi da abinda Kaka tayi mai lokaci zuwa lokaci sai ya saki tsaki, a haka ya koma barci Bayan ya yi wayar sirri da Sumaya. WAIWAYE Sufyan lokacin da ya bar Yankin Tudu da Sumaya abisa umarnin Mahaifansa na idan sunje Birnin Abyad ya saketa, su na isa Birnin Abyad maimakon ya cika umarninu kai tsaye masauki ya wuce da Sumaya ƴan uwanta kuma suka wuce Gida. Bayan sun nutsu sunci abinci sunyi wanka da Maganganu ma su daɗi yake ta lallashinta tare da nunamata duk wasu abubuwa da suke faruwa akwai dalili ba wai laifin Mahaifansa ba ne har da ce mata; "Mahaifina mutumin ƙwarai ne mai sauƙin kai, amma rashin fahimta da butulcin mutanen Yankina yasa suke ganinsa kamar azzalumin da ya hana Yankinsu cigaba. Mahaifiyata Macece mafaɗaciya amma da zarar kun saba ta sauko daga fushin sakin Naila da na yi zata fara sonki, fushinta na wani lokaci ne, kuma Ni bazan taɓa son Naila ba, saboda mutumin da na fi tsana a rayuwarta take so har yanzu, da hotonsa take yawo, kuma akansa ta zaɓi bijiremin. Saboda haka nake roƙonki Sumaya ki kwantar da hankalinki ki bani haɗin kai" A kaf maganganunsa ba bu wanda Sumaya ta fahimta tunda ya ambaci ba ya son Naila ne saboda tana yawo da hoton maƙiyinsa. Cikin kasa danne kishin Naila da ya yunƙuromata ta ce; "Kenan da ba don tanason wanda ka tsana ba, ka na sonta kenan? Dama can itace bata sonka kakeyimin ƙarya? Sufyan banajin aurenmu zai kai labari saboda kowa naka ba ya sona, hatta Mahaifinka ƙiri-ƙiri na hango tsanata a cikin idanunsa. Tun kafin komai na mu yayi nisa kawai ka sauwaƙemin." Sufyan murmushi ya saki yana kallonta, tayaya zai sha dukka wannan Yankar daga mahaifinsa kuma ya ɓata shekaru yana kashe mata kuɗinsa da na Naila ta ce haka kawai zata suɓucemai shi ba zai moreta ba? Su kansu Mahaifansa da zai bayyana musu bautar da ya yi mata da basu ba shi umarnin sakinta ba. Sai da ya numfasa sannan ya fara yaudararta da yaudararrun kalamansa da rabi da kwantansa duk ƙaryane, saboda yasan har abada Iyayensa ba za su taɓa sonta ba, amma shi kam bazai yi gangancin sakinta da wuri ba, sai ya samu wacce ta kwanmai ko Naila ta dawo hannunsa kamar yadda suka tsara. Da dare ya yi, Sumaya da yake gwanace wajen son duniya tana ganin Sufyan ya fita ya dawo da lodin Siyayya ta fara sakin ranta, sannan ya kuma cewa ta biyosa Babban Birnin Abyad idan taji batason zama da shi yayimata alƙawarin sakinta, babu ja ta amince. ★washe gari suka je har Gidan Iyayenta ta yi musu bankwana. Muguntar Sufyan yasa ya biya tsohon Gidan su ko zai samu mukullin sashen Naila kafin su tafi, ga mamakinsa hanasa shiga Gidan akayi gaba ɗaya, haka ya dawo suka ɗauki hanyar Babban Birnin Abyad ransa a ƙuntace. Kyan matsugunin Sufyan na Babban Birnin Abyad ba ƙaramin tafiya da imanin Sumaya ya yi ba, a take ta manta irin ƙiyayya da wahalar da ta sha a Yankin Tudu. Tana jin ko Iyayen Sufyan ba su isa su rabasu ba. Bayan kwana biyu da zuwansu Babban Birnin Abyad. A zahirin gaskiya yanayin yadda yake yiwa Naila gadara da abinda yaga dama wajen sauke buƙatarsa sam ba iri ɗaya bane da na Sumaya, ƙiri-ƙiri take nuna ita batason wannan ita bazata iya wannan ba. Wannan dalilin yasa ya ƙara karɓar shawarar Iyayensa hannu bibbiyu, Naila tamkar baiwa take sai yadda ya ga dama zai yi da ita, ta ƙiyi kuma jikinta ya gayamata tunda bata da gatan kowa dalilin dawowarsa Yankin Tudu kenan. DAWOWAR LABARI ★washe gari Ɗayyib ya tura wakilansa kan komen Naila ta hanyar Yayyan Mahaifinta da suka yaudara da kuɗi a baya. Da ƙarfin gwiwarsu dukkansu suka haɗa bakin ba su yarda Naila ta komawa auren Sufyan ba har sai ta samu sauƙi, kuma ko ta samu sauƙi sai sun ji ta bakinta idan ta amince. Idan kuma har da gaske Sufyan magani zai nema mata kamar yadda suka faɗa to yafara naima mata kafin ta koma Gidansa. Martanin Yayyan Mahaifin Naila akan komenta gidan Sufyan mummunar labari ne a wajen Ɗayyib, Jalal, Hindu da Sufyan kanshi. A wannan dare dukkasu sukayi tafiyar Sirri zuwa Yankinsu Hindu, suka bawa Malamin duban Hindu kuɗi maiyawa ya ƙara tura mugayen aljanun da zasu addabi Naila ta ji kamar zata mutu har sai ahalinta sun sallama sun amince da komenta. SARTAJ WANDA YA CIYAR DA NAILA GUBA Fitar su Ɗayyib da rashin dawowarsu da wuri ne, yasa Sartaj gajiya da zaman jiransu kan gulmar da ya kawo musu; na ga Naila can an shirya kaita Birnin Abyad gobe da sassafe neman magani. Da ya ga dai bazai samu ganin su ba, haƙura ya yi ya nufo gida.. Ya na ɗanyi nesa da Masarautar Sarki Hammam, MALIK da ya sauko daga mota ya bayyana a gabansa gaba ɗayansa.... Bayyanar fuskar Malik ga duk wani ɗan Yankin Tudu, babban abun fargaba ne. Saboda ba ya zuwa ya tafi bai bar shaida ba. Sartaj mummunar gani ya yiwa Malik saboda bai sakaya fuskarsa da hutu ya yi kamu mai kyau ba, a zallarsa ya fitomai. Fararen idanuwansa masu tsananin haske da girma Malik ya zubawa ƙafafuwan Sartaj da suketa rawa kamar an jona mu su shocking. Da zafin takunsa ya ke tunkaro Sartaj da gumi ke tsiyayowa tun daga cikin gashin kaa, har cikin suɗaɗɗen takalminsa. Da sauri Sartaj ya yunƙura zai gudu, fitsari da bayan gida na zuwarmai lokaci ɗaya. Munfashi Malik ya sauke kafin ya taka sawun da ya basa damar cafkar Sartaj. Guri ɗaya ya tsayar da fuskar Sartaj yana kallonsa shima ya na kallonsa. A hankali Malik ya ɗage girarsa ɗaya ya ce; "kasanni?" "Ni dai ina neman afuwa, wallahi na daina" Sartaj ya faɗa daƙyar muryarsa na karkarwa. "Na ce kasanni?" Malik ya ƙara tambayarsa kamar bai ji abinda ya ce ba. "Na sanka! Au wallahi bansan ka ba" Sartaj ya faɗa a ruɗe. "Tabbas ba ka sanni ba, domin da ka sanni da bakayi abinda ka yi ba" Malik yaƙarasa faɗa yana kai hannunsa bayan wandonsa. "Au na tuna, na sanka wallahi! kuskure ne daga yau na daina, na daina kai gulmar kowa kuma ba zan ƙara cutar da kowa ba, Dan Allah ka yafemin wallahi sharrin shaiɗan ne." Yana ƙoƙarin ƙarayin magana Malik ya kwantar da shi ƙasa ya na cewa; "Bayyanata a Yankin Tudu na mutane ne ma su kafiya irinka, ba na zuwarwa laifi ɗaya sai sun taru. Idan na barka gobe sharrin shaiɗan zai sa ka ƙara kai musu wani rahoton, ba tare ka tuna da kashedina ba amma idan na bar maka shaida Fa??" Azabar ficewar ƙafar Sartaj ɗaya ne yasa ya shi sakin ihun da ya karaɗe Yankin. Kafin fitowar Fadawan Sarki Hammam babu Malik ya shige Mota ya bar wajen, sai Sartaj da ke kwance cikin jini da ƙafarsa ɗaya da aka yanke rungume a hannunsa, kamar yadda Malik ya maƙalamai a tsakanin Hannuwansa. Ihu su ma suka kurma. Tuni mutane suka fara firfito daga Gidajensu. Duk da Sartaj ya ba wa Mutanen Yankin Tudu tausayi hakan bai hanasu murmusa a ɓoye ba, acewar su sakayyar abinda ya yiwa Naila ne. NAILA; A wannan dare tasha azaba irin wanda bantaɓa ji ba, Kaka tana kanta, da ƙarfin gwiwa tare yaƙinin samun sauƙi daga wajen Ubangiji take tofamata addu'o'i wasu ta tofa a ruwa ta shafa mata. Bayan wani lokaci barci ya ɗauke Naila. Hannunta Kaka ta ɗaga sama tana ce wa; "Ya Ubangiji! da wanda ya ke zuwa ya biya kuɗi a sanyawa Naila ciwo, da wanda yake turo ciwon, da shi kanshi jinnun da yake assasa ciwon duk Kaine Ubangijinsu Ya Allah! Ya Allah kayimin maganinsu da gaggawa Don ƙarfin Mulkinka, Ka sauƙaƙamin tafiya da ita Ya Allah." Itama Kaka a kusa da Naila barci ya ɗauketa ★ washe gari da asuba Driver ya iso ƙofar Gidansu Naila, kafatanin mutanen Yankin da suka san da tafiyar duk sun hallara a ƙofar Gidansu, duk suna kuka da addu'o'i kala-kala ɗauke a bakunansu. Ɗaya bayan ɗaya suka dinga rungume Naila, suna sumbatar ƙuncinta, Naila ta zaune a Mota tayi laƙwas Hannuna a cikin na Kaka, Yayyan Mahaifin Naila suna kuka suma suka rungumeta, Naila dai bata iya kuka sai kai da take ɗaga musu. Suna yunƙurin tafiya Kakannin Naila na wajen uwa suka iso da mutanensu, kalaman su ga Naila na ƙarfin gwiwa ne, tare da tarin yaƙini a kanta. Da haka Motar Naila ta fara tafiya kaka tana kuka Naila itama sai a lokacin hawaye ya zubomata tana ɗagamusu kai, Mutanen Yankin Tudu suna kuka su na kuka suka rabu. Misalin ƙarfe Takwas na safiya suka isa Iyakar Yankin Tudu da wajen hawa motar Ƙasar Abyad. Driver shi ya taimaka musu har motar su ta tashi, shima da yaga Motarsu ta fara tafiya hawayensa ya sharce yana ɗago mu su hannu...🥹[7/30, 8:44 PM] nafisaaliyusasaal: 🔥ZINARE🔥 N. A. S Page 24 SARTAJ ★washe gari yana farfaɗowa daga dogon sumar azabar da ya yi da ihun kiran Malik yafara yana roƙo da magiya. A surutan Sartaj da aka sanarwa su Ɗayyib da su kayi dawowar cikin dare suka fuskanci Malik yana bibiyarsu, irin bibiyar da basu san ta hanyar da zasu toshesa ba. Kuma sun kasa gano wane yake kai masa rahoto. Mutanen Yankin da suka ji ai aikin Malik ne ya yankewa Sartaj ƙafa, tsoron gulmar kowa da cin amanar junansu ne ya ƙara shigarsu. Tunda ga shi an yankewa Sartaj ƙafar da yake zaryar kaiwa su Ɗayyib gulma dashi. "Amma mai yasa Malik bai taimaki Naila ba, ko bai san halin da take ciki ba ne??????" Tambayoyin da suke ta yiwa junansu kenan. Duk nacin da akayi Sartaj ya buɗe baki ya faɗi ina yaga Malik har ya yanke mai ƙafa, ƙin yin magana ya yi. Washe gari da su Ɗayyib suka zo dubasa ihu ya kurma yana rufe fuskarsa, alamun bayason ganinsu. Har suka bar ɗakin bai buɗe fuskarsa ba. Har Sartaj ya warke ba ya iya yin gulmar kowa, balle ya ambaci sunan Malik, gani yake yi kamar idan ya ambaci sunansa zai bayyana a gabansa. Ranar da su Ɗayyib suka yanke shawarar neman mafita akan Sartaj a Fadar Sarki Hammam gudun tonuwar asirinsu washe gari aka nemesa aka rasa shi da tsohuwar Mahaifiyarsa. Ɓatan Sartaj da mahaifiyarsa ya yi matuƙar tayar da hankali Mutanen Daular Sarki Hammam, sama da yadda labarin tafiyar Naila da Kakarta Birnin Abyad ya tashi hankalin su, domin sun san ko su Naila sunje dole su dawo, saboda maganin matsalarta ya na wajensu. Saɓanin talakawan Yankin da suke ganin Sartaj ya gudune saboda abun kunyar da ya aikata. A karon farko aka fara saka jami'ai a duk wani hanyar da zai kai mutum cikin Yankin Tudu domin kawo ƙarshen Malik, shima Sufyan cikin gaggawa ya shirya komawa, saboda ɓacewar maganin da yasan dole idan ya cigaba da zama za'a tambayesa ya na ina? da kuma gudun kar ɓarna Malik ta ratsa da shi, domin zuwa lokacin ya fuskanci a kwai wasu manyan sirrikan da bai san da su ba... NAILA Allah Ya amshi addu'ar Kaka. A tafiyar kwanakin da suka yi, ciwon Naila ya na yawan tashi, amma da zarar ya tashi Kaka za ta rungumeta ta yi ta tofamata addu'o'i har sai jikinta ya yi yaushi barci mai nauyi ya ɗauketa BIRNIN ABYAD Da taimakon Allah suka isa Birnin Abyad. Kaka ta zuba ƙauyanci wasu lokutan garin Kallon Mutane har tuntuɓe takeyi. Da ɗan ƙarfin da Naila take ji, take yi mata raɗar motar da zasu hau a kunne. Da hannu kaka take kwatanta mu su komai tunda batajin turanci, kuma batajin asalin yaren ƙasar. Kamar ko da yaushe idanun Naila maƙale a hanyar Babban Birnin Abyad, ƙewar Bushra da Yasar na bijiromin, suka wuce hanyar. Gidansu Naila ba ƙaramin burge Kaka ya yi ba. Ba ta hutu ba bayan sunyi salla ta fara gyara ko ina na sashen. Da taimakon Kaka bayan ta gama gyare-gyarenta Naila tayi wanka. A ranar Kaka ta farayimata amfani da maganin su Sufyan kamar yadda Mallam ya koya mata. Bayan wannan ta haɗa har addu'o'in da ya bata. Da guzurin kayan abincin da suka taho da shi daga Yankin Tudu suka fara amfani, kafin Naila ji sauƙi su canza ƙudi su siyo wasu. A cikin kwana uku sauƙi ya fara samuwa, Naila tana iyayin komai da kanta, har tayi Sallah a tsaye a kan ƙafafuwanta. Kwana biyu bayan nan Naila ta shirya ita da Kaka suka tafi Gidan Iyayen Yasar domin jin halin da yake ciki. Yasar ya na kwance babu lafiya tsohon watanni biyar kamar yadda Mahaifiyarsa ta faɗa musu bayan sun gama gaisawa, ta ce Accident ya yi a kan hanyarsa ta dawowa daga Babban Birnin Abyad. Ya na barci lokacin da su Naila suka isa, bai farka ba har sai da suka fara haramar tafiya. Da mamaki yake kallonsu kamar bai ganesu ba, har sai da Naila ta gaisheshi ta faɗamai sunana sannan ya fahimci ita ce. Da zafin naman ɗan ƙarfin da yake ji ya gyara zamansa ya na faɗin "Naila! Maiyasameki kika koma haka? Ciwo kakayi? Maiyasa baki dawo Makaranta ba? Na so zuwa har Yankin Tudu cigiyarki Saboda na kira wayarki bana samu wannan tsautayin ya afkamin ki gafarceni." Kai Naila ta sunkuyar ƙasa tana Kuka. Kaka ce ta basu labarin jinyar da Naila ta yi. Dukkansu sun tausayawa Naila har Iyayen Yasar da a baya suke gudunta. Sun ɗan jima a Gidan kafin su dawo Gida. ★washe gari sai ga siyayyar kayan abinci da kayan motsa baki kala-kala har da kayan sawar Kaka, da wayar amsa kira duk daga Gidansu Yasar. Su Naila sunyi farin ciki matuƙa tare da godiya mai tarin yawa. A hankali a hankali jikin Naila ya fara murjewa saboda canjin cima, muhallahi da kuma lafiyar da take ƙara samu. Itama Kaka tsaf ta yi kyau, su na waya da mutanen Yankin Tudu lokaci zuwa lokaci da number da suka rubuto mata a jikin takarda. Bayan Naila ta samu sauƙi, Yasar da kansa ya jagoranceta har Makarantasu duk da baya iya tafiya sosai saboda karayar ƙafarsa da bai gama warkewa ba. Naila bata samu matsalaba albarcin Yasar da kuma shaidun da suka gani da ido, saboda har lokacin akwai banbanci da yadda nake a baya kafin ta bar Birnin Abyad. Da farin ciki Naila ta dawo Gida, itama Kaka daɗi ne ya kamata, tayi ta yiwa Yasar godiya tana samai albarka. A cikin watanni biyun da Makarantarsu Naila suka ƙaramata a matsayin hutu, jikinta ya yi kyau kamar bata taɓa jinya ba. Da kanta ta kai Kaka sukayi siyayya kafin su wuce Gidansu Yasar. Irin motocin da muka gani a harabar gidanne yasa Naila ta cewa Kaka su juya, domin jikinta ya na bata wakilai ne daga wajen aikinsa na Babban Birnin Abyad. Sam Kaka ta nuna bata san zanceba ba, a cewar ta; "mu ina ruwanmu da su? mu da ba wajensu muka zo ba." A living room ɗin farko idanuwan Naila suka sauka a kan mutumin da ta ke gani tamkar Malik, duk da ya sanya tabaran rage hasken ranar da ya sakaye idanuwansa, ga kuma tarin ƙasumbar da ya bari a fuskarsa. Sai mace ɗaya da take zaune a kujera daban itama Naila ta kasa gane ina ta santa ina ta taɓa ganinta kuma da wa take yi mata kama. Kamar yadda Naila take Kallonsu bayan ta gaishesu haka Macen da ba wani shekaru bane da ita ta ƙuramata ido. Kaka tunda ta gaishesu ta nufi cikin Gidan wajen ƙannen Yasar da suke wasa da dariya. Namijin ne ya fara miƙewa gaba ɗayansa yana miƙawa Yasar hannu. Miƙewarsa ya sa ya fito sak a Malik ɗin da Naila take zargi, kallon da ta yi masa shekarun baya a gidan Abduh Dhahab yana shara da safiya ya ƙara dawowa idanunta. Zumbur ta miƙe tana kallonsa kamar zata cinyesa, kafin ta ambaci sunansa mahaifiyar Yasar da take ganin girmansu a matsayin su na Manyan Iyayen Gidan ɗanta ta ja hannun Naila ta zaunar da ni a gefenta, a tunaninta ciwon jinnun da Kaka tace ta yi ne ya ƙara dawowa. Da harshen ƙasar Abyad take ba su haƙurin Naila ba ta da lafiya ne. Macen ce ta amsa mata amma Namijin fita ya yi. Itama Macen miƙewa tayi Zinaren da ta yi ado da shi na walwali a kunnenta da wuyarta. Har mota Mahaifiyar Yasar da Yasar suka yi musu rakiya, har lokacin Naila tama zaune kamar an dasata. Bayan sun dawo Yasar yake tambayar Naila n Ta san su ne? Naila yasan ko tayi masa bayani ba lallai ya yarda da ita ba don haka ta ce mai "a'a." Har suka bar gidan bata saki jikinta ba, duk Yasar yana ankare da ni. Rashin walwala da yadda Makka take haɗe rai bayan sun koma Gida yasa Kaka ta ce ta zo ta rakata su siyo abu, Yasar ya bata kuɗi. Waccen wajen Siyayyar da ta taɓa haɗuwa da Sufyan ta ce suje. Ƙananun kayan CK da Yasar yake yawan siyomata ta sanya sai malulluɓi mai girman da ta nannaɗe har rabin fuskata da shi gudun haɗuwa da Sufyan, ko Sumaya. Bayan isarsu Su na cikin siyayya idanuwanta suka faɗa kansa da jami'ai biyu a bayansa, wannan dai mutumin da na gani a Gidan su Yasar da rana ne. Ya na fita ta rufamai baya da hanzari ba tare da ta saurari Kaka da ke tambayar "Naila ina zaki je?" Yana ƙoƙarin zura gangar jikinsa a Mota Naila ta ƙaraso ɗan nesa da Motar da Gudu, cikin ɗan ɗaga murya ta ce "Malik, dan Allah idan kaine ka tsaya na roƙeƙa"...✍🏻 Duk mai son Ɗaukar Malik haya a Yankinsu tayimin DM saboda irin su Sartaj😂😂 I came in peace ☹️ [7/31, 10:04 PM] nafisaaliyusasaal: 🔥ZINARE🔥 NAFISA ALIYU SASAAL Page 25 A kaikace yake kallonta, irin kallon da batasan yadda zata fassarashi ba. A kan idanunta Driver ya tashi mota, duk da haka Mutumin yana kallonta kamar wanda bai Santa ba amma yake tunanin a ina ya taɓa ganinta Tana ji tana gani mutumin da take kyautata zaton Malik ne ya yi tafiyarsa. Tafiyarsa ba tare da ya buɗe baki ya cemata komai ba ya yi matuƙar sosa zuciyarta, har ya sata ta fara tunanin to maiyasa take bibiyar duk wani wanda abu ya taɓa haɗasa da Sulaim? mai take so su sanar da ita? Kenan batsyi imani da ƙaddara ba. Ko so take yi su cemata Sulaim yana raye? To idan ma Sulaim ɗin ma ya na raye cewa ya yi damacan ya na sonta ko zai iya aurenta? Maiyasa bazata rungumi maraicinta ta rufawa kanta asiri ba kamar yadda Allah Ya rufamata. Abinda da ya yi Sufyan shi ya yi Sulaim saboda daga tsatso ɗaya suka fito sai dai banbancin ra'ayi da ɗabi'a. Jikina a sanyaya ta koma wajen Kaka, har suka dawo Gida bata saki ranta ba. Tun Kaka tana lallashinta da tambayar abinda ya ke damunta har ta gaji ta shareta. Naila Sanyawa zuciyarta lallai sai ta manta Sulaim da duk wani abu daya dangacesa ne, ta fuskanci abinda zai kawowa Yankinta cigaba ne ya sanyamin zazzaɓi mai zafin gaske. ★Da Asubahi ta yi ko miƙewa da kyau bata iya yi saboda ciwon kai. Kaka hankalinta ne ya tashi, cikin kuka takeyimata faɗar idan zaman Birnin Abyad ɗin ne banaso to na tattara su koma Yankin Tudu, su ƙarasa kasheta tunda ba zan kwantar da hankalina ba. Da sassafe ta kira Yasar tana mitar ƙuncin da da Naila ta kwana da shi, yanzu gashi ta tashi da zazzaɓi. Naila tana jin Yasar ya na tausarta Kaka tana ƙara haƙiƙancewa ya zo ya tambayeta idan zaman Birnin Abyad ɗin ne bataso sai su tattara su koma Yankin Tudu. Ba su yi hour biyu da yin waya da Yasar ba, sabon Drivern da'aka Ma'aikatarsa ta ajjiye masa ya kawo shi gidansu. Kaka ta na ganinsa ta miƙe zubur tana cewa; "Ni bani da zaɓi, tunda bata tausayin kanta, tafison na mutu ina ƙunsar baƙin ciki, kuma daga yau Ni dai ba bu ruwana da ita" murmushi Yasar ya yi yana gaisheta, daƙyar ta haƙura da mitarta ta amsa gaisuwarsa kafin ta bar ɗakin. Kafin Naila ta gaishe da Yasar ya katseta da ambaton sunanta "Naila" A hankali na ce "na'am" "Menene alaƙarki da su Malik Dhahab? domin tun jiya ina sane da sauyin yanayinki, baki taɓa ɓoyemin komai ba amma jiya kin ɓoyemin Naila, menene gaskiya? " Yasar ya ƙarasa faɗa yana kallonta. Haɗin sunan Malik da Dhahab shine abinda ya ƙara tsananta ciwon kan Naila lokaci ɗaya, kenan dai da gaske Malik ɗin Yankin Tudu mai gutsirewa mutane harshe ta gani, to ko dai da harshen mutanen dayake gutsirewa ya yi kuɗi har ya koma Malik Dhahab? Tunda a sanin da ra yi musu a shekarun baya talakawa ne fitik. "Naila kinyi shiru, ko dai da gaske Yankin Tudu kikeson ku koma kamar yadda Kaka ta faɗa?" Yasar da ya gaji da dakon jiran amsarta ya tambaya. Kanta ta girgiza sannan ta fara magana muryata a sanyaye; "Nasan Malik a Yankinmu shekarun masu yawa baya, ina bibiyarsa ne domin na tambayesa ina Sulaim da gaske wuta ta ƙoneshi ya mutu, sai dai ƙiri-ƙiri Malik ya nuna bai Sanni ba bai ma taɓa gani na ba, wannan ne ya yi min ciwo har ma tashi da zazzaɓi." Da mamaki Yasar ya ce; "Anya kuwa Naila kinsan wanene Malik? Su Malik fa asalin ƴan ƙasar Abyad ne, domin da harshen da mafi rinjaye kuma mafi wahala na ƙasar Abyad dukka ahalin Gidan su ke amfani, yare ne mai wuyar koya a wajen bare, ko dai kama yake yi miki da waccen Malik ɗin?" Tasan dama ba lallai ya yarda da ita ba, don haka kai tsaye ta karɓi yardar Malik kama yake yimata da waccen Malik ɗin. Nasiha Yasar ya yimata tare da tunamata yaƙinin da mutanen Yankinta suke da shi a kanta, don haka na mayar da kai tayi karatu bakin iyawarta. Kamar zata iya cire komai a ranta ta amsawa Yasar da "to" haɗe da yimasa godiya. Ya na ɗan jima a Gidan kafin a mayar da shi gida. Bayan tafiyarsa dalla-dalla Naila ta zauna ta warwarewa Kaka komai. Kaka tsohuwace mai saurin fahimta da sauƙin hali bata da birkicewar wa su tsofaffin. Cikin hikima ta nusantar da Naila, ko da ace Sulaim yana raye ba Mijin aurenta ba ne, ta tsaya a iya matsayinta ta kuma tsaya tsayin daka wajen manta baya ta fuskanci gaba, kar ta manta haɗakar kuɗin Mutanen Yankin Kakanta, da na Mutanen Yankin Tudu ne ya kawosu Birnin Abyad ba domin komai ba sai don ta yi karatu, saboda daga gareta suke sakaran samun canji, kar ta bari tunanin wanda da zai samu damar ƙara dawowa duniya bata kai matsayin da zai sota ba ya lalatamata tunaninsa har ta kasa zama abinda mutanen Yankinta suke yi min fata. Sufyan da bai gaji arziƙiba, bai kuma gaji sarauta ba ya gujeta balle Sulaim da ya gaji Sarauta gaba da baya tare da tarin arziƙine zai so ta, Karta kuma wahalar da kanta wajen tunanin Sulaim yana raye ko baya raye, ta ƙaddarawa ranta ya mutu, ba kuma zai ƙara dawowa ba har abada! Maganganun Kaka gaskiya ne, amma ɗaukarsu ga Naila a lokaci ɗaya abune mai kamar wuya, amma tasawa ranta zatayi iyakar iyawata don ganin ta fidda mutanen Yankinta kunya. Kwanaki bayannan, ta fara bin gidajen Customominta, ta kuwa yi sa'a hannu bibbiyu suka karɓeta har ta samu kitsa kan wasu, A ranar da kuɗi masu nauyi ta dawo gida. Daga wannan rana Naila ta ƙara himma akan sana'arta, har zuwa lokacin da ranar komawarta Makaranta ya yi. Yasar ne yayimata siyayyar komai. Shi da Kaka da ƙannensa ne sukayi mata rakiya har Makaranta. Kasantuwar Naila a Jami'ar ƴaƴan masu wadatar Birnin Abyad bai sa ta kai kanta matsayi da su ba, kitsonta takeyi ido rufe, kuɗi kuwa kamar anayimata yayyafin su, domin wasunsu biyan fariya da isa sukeyimata ita kuma na karɓa hannu bibbiyu tana godiya. Watanta ɗaya a Makaranta ta dawo tayi weekend tare da Kaka, sannan da bata ajjiyar kuɗin kitson da ta samu ta dinga tara musu. SUFYAN. Babu abinda ya sauya tsakaninsa da Sumaya, yawan ƙorafi, batason wannan, ita wannan take so da dai sauransu. Rashin mafita yasa Sufyan yake lallaɓawa, kuɗi kuma idan ya samu na su Ɗayyib ne. Sumaya sai dai ta samu ɗan abinda ba'a rasa ba. Wata rana taro ya kai Sufyan Companyn Dhahab da suke ƙera Tukwane. Lafiya qalau suka gama taro ya fito, a hanyarsa ta fitowa ya ga mutumin da ya zo Yankinsu a matsayin Kabeer saboda shi dai ya kasa yarda da gaske Kabeer ne. Basarwa ya yi, ya nufi Motarsa. Har ya shiga Mota ya tuna ya manta tabaransa a teburin da ya zauna. Da ɗan zafin nama ya juya saboda aikin dayake jiransa a office. Baya ya dawo yana matse idanuwansa da suka farayimai yaji. Masu tsananin kamanceceniya da Malik, Salman, Kabeer ya gani a waje ɗaya. Ƙara buɗe idanuwansa ya yi gaba ɗaya yana zaresu. Babu wanda ya kallesa a cikinsu har su ka gama gaisawa suka tafi sai wanda yake tsananin kama da Malik ne ya rage a tsaye yana duba wayarsa. Sufyan bai motsa ba sai gumin dayake tsiyayomai, yana cikin wannan halin Maigidanshi Baturen da suka zo tare ya fito daga ɗakin taron, da sauri ya ƙaraso kusa da shi yaja hannunsa har gaban wanda yake kallo. A gabatarwa da Baturen yake yi Sufyan ya ji ya ambaci Malik Dhahab shugaban Companyn Tukunyar Dhahab na ƙasar Abyad. Malik baya kallon fuskar mutum sai cikin idanuwansa, kamar yadda ya koya daga iyayen Gidansa, don haka kai tsaye cikin idanun Sufyan da suka fara canza kala yake kallo Tafin hannun Malik mai girma da faɗi ya miƙawa Sufyan, shima Sufyan ƙasa ya yi da kansa kafin ya ɗago hannunsa da ya jiƙe da gumi tare da yimai nauyi ya miƙawa Malik bayan ya laso laɓbansa don ya tabbatar da harshesa ya na bakinsa bai fita ba. Haɗuwar tafukan hannuwansu waje ɗaya yasa Sufyan ya ɗan ɗago kansa a hankali don satar kallon fuskar Malik, charaf idanuwansa suka faɗa cikin nashi, kafin ya sunkuyar da kansa ƙasa Malik ya ce; "Sufyan Ɗayyib Jalal right?" Ambaton sunansa da salon da yasan dole sai wanda ya sanshi a Yankin Tudu ne zai iya faɗa da kuma Muryar da ya tabbatar masa da dagaske Malik ne a gabansa yasa idanuwansa juyewa numfashinshi ya ɗauke nan take ya zube ƙasa. NAILA. A makaranta ta haɗu da ƙawa ƴar masu arziƙin da take biyanta kuɗin kitso mai nauyi, da style kala-kala take zuwa a wayarta ta yi mata sak irin wanda ta kawo. wannan dalilin yasa suke ɗasawa da ita har sukan yi hirar da ya shafi Kaka da Yankinsu da ita. Amira mai zuwa kitso wajen Naila da suka fi ɗasawa sun riga su Naila gama Exams. Ana saura kwana ɗaya zata tafi Gida ta zo da wani style ta ce Naila mata. Bayan mun gama take shaidawa Naila Babban Birnin Abyad zataje tsare-tsaren Bikin ƴar uwarta, wataƙila idan kitson ya yiwa ƙawayenta su zaɓeta ta zo tayi mu su, domin dalilin da yasa tace tayi mata irinsa kenan. Ko Kakarta ba zata amince ba? Naila Tuna muradinta na son zuwa Babban Birnin Abyad yasa ta ji kamar ta amsata mata kai tsaye sai dai da ta tuna faɗan da Kaka tayimata akan Sulaim, sai tace bata ba, amma ta bari idan taje gida zata tambayeta idan ta amince zata sanar mata.... A akan haka suka rabu. Shin Kaka zata amince kuwa??😄 🔥ZINARE🔥 SASAAL Page 26 Har su Naila gama Exams bata daina tunanin tattaunawarsu na zuwa Babban Birnin Abyad da Amirka ba. Amma ta sawa ranta amincewar Kaka shi ne nata. Ranar da ta koma gida Da murna Kaka ta tarbeta bayan girki-girke ma su daɗi da ta shiryamata, sai da ta huta ta ci abinci, takasa sakowa Kaka zancen zuwanta Babban Birnin Abyad yin kitso saboda tsoron yadda Kaka zata fassara zancen take yi. ★har washe gari ta kasa yi mata zancen tafiyar, Sai Kaka da kanta ce ta kalleta cikin dariyar da ya haɗe da mamaki ta ce; "Me kikeson faɗa kika kasa Naila? Tun jiya ina ankare da ke, karki ji nauyi ki faɗamin zan fahimceki kinji" Murmushi ta yi tana murza goshinta, cikin kame-kame ta ke bata labari yadda sukayi da Smira. Kaka kallon Naila takeyi maganganu Sarki tsafin Yankin Tudu lokacin da ya zo duba Naila na amsa kuwa a cikin kunnenta "Naila zata warke amma akwai jarabawar da ya fi wannan raɗaɗi a gaba, domin zata isa Babban Birnin Abyad, da ƙarfin ikon Allah! Amma daga lokacin ƙullin shekarun da aka kasa warwaresa zai fara warwarewa da kansa, arziƙin da Sufyan ya yi gajen haƙurin ya riskesa zai bayyana, wannan yana ɗaya daga cikin abinda Mahaifiyarsa take kwaɗaitar masa ya gaza fahimtarta, da ya yi haƙuri da zai zama wankakke abisa laifin da Kakannin-kakanninsa suka jima su na aikatawa aban ƙasa, ko da Naila ta warke ta koma Birnin Abyad, Birnin Abyad ba mazaunin Naila ba ne. Ba lallai ki yarda da maganganuna ba, amma daga ranar da sanadi ya kai Naila Babban Birnin Abyad, zaki gasgata batuna" furucin Sarkin Tsafin Yankin Tudu kenan lokacin da ya zo duba Naila, amma Kaka tayi watsi da zancensa acewarta; Boka Ɗan uwan shaɗai ne, don haka babu gaskiya a maganarsa.. Tuna wannan yasa Kaka a zafafe ta ce; "Wallahi ban amince ba Naila, kinsan abinda kike faɗa kuwa? Babban Birnin Abyad har abada ba wajen zuwanki ba ne, karma ki ƙara tambayata don bazan lamince ba na gayamiki" Kaka taƙarasa faɗa cikin masifa! Tsabar masifa har rufe idanuwanta take yi kafin ta fashe da kuka. Birkicewar Kaka lokaci ɗaya da yadda take magana har da su fashewa da kuka ba ƙaramin tsoro abin ya bawa Naila ba, cikin haushin yadda ta hantare ta har da su kuka ta ce; "Kaka kukan me kike yi, ni fa kawai shawararki na nema, bance dole sai na je ba, sannan ke kika ce na gayamiki kar na ji nauyin komai zaki fahimce ni, amma gashi akan kawai na faɗa miki gaskiya shine kike masifa har da su kuka, dama can dai haushina kike ji, daga dawowata zaki sanyani cikin damuwa, na fara ciwo kuma kiyimin sharrin Yankin Tudu nake son komawa, gaba ɗaya kin canza Kaka." Tsit ta yi tana kamo hannun Naila. Ɗan fizgewa Naila ta yi tana cewa; " ki ƙyale ni Kaka, tunda kin fara jin haushina a ɓoye bansani ba, ni ma daga yau babu ruwana da ke" Hawayenta ta share still ba ta saki hannun Naila ba, da sanyi jiki ta ce; " to zauna na faɗa miki gaskiya ina fatan kema za ki fahimceni, ki janye batun zuwanki Babban Birnin Abyad" Son labari irin Naila yasa ta zauna da sauri jikin su na gogar na juna. Abinda Sarkin tsafin Yankin Tudu ya faɗa ta maimatamata sannan ta ɗora da; " Naila bawai na gazgata maganganun sa bane ɗari bisa ɗari, amma a yanzu a jikina nake jin ko dukka maganganunsa ba su zama Gaskiya ba, to baza'a rasa gaskiya ko da yaya bane ciki, duba da yadda su Hindu suke fafutukar dole sai kin koma cikin rayuwar ɗansu, Naila inajin tsoron matsalar da zai ƙara kunnowa rayuwarmu kai a yanzu, ki gafarceni" Da mamaki Naila ta kalli Kaka tana tattare girarta waje ɗaya ta ce; "Saboda iya wannan dalilin zaki haramtamin samun kuɗin da zai sauya rayuwar Yankina? Kinsan nawa za'a biyani Kaka?. Rayuwarmu bazai taɓa cigaba da tafiya a haka ba, dole sai da gwagwarmaya tare da ƙalubale Kaka, baƙin ciki da farin ciki basa dawwama a rayuwar Bawa, idan warware ƙullin ne zai zama cigaban Yankinmu mai zai hana mu tunkari warwaresa ko da hakan zaisa mu rasa rayukanmu, tun da dai dole zamu mutu wata rana. Kaka kiyi tunani tunda na ki tunanin yafi nawa zurfi, ba kuma zanyi yin kaina ba dole zan jira umarnin ki, amma Kaka ki tuna gina kanmu da Yankinmu wajibunne, saboda Yasar shine ƙarfin gwiwar zamanmu a Birnin Abyad, to idan ya mutu fa? ko ya gaji damu fa? Jira zamu yi tayi sai dai wani yayimana gwagwarmaya mu muji daɗi mu ba za muyi da Kanmu ba? Saboda muna tsoron mutuwa? Kaka kiyi tunani a nutse, kuma karki ji shakkar sanar da ni duk abinda kika yanke, In Shaa Allah zan yi miki biyayya kin ji." ta ƙarasa faɗa tana rungume kaka bayan na sumbaci goshinta. Tun a lokacin bugun zuciyoyinsu ya sauya daga tsoro zuwa ƙarfin gwiwa. SUFYAN Da ya farka ya ganshi a gadon Asibiti baiyi mamaki ba. Sumaya tana ganin ya farka ta ajjiye wayar hannunta tana matsowa kusa da shi, sannu take ta nanatamai tana kamo hannunsa. Laƙwas Sufyan ya yi. A hankali ya buɗe bakinsa ya zaro harshensa. "Sumaya kina ganin harshena, yana cikin bakina?" Ya yi tambayar yana karkaɗa harshensa. Da mamaki Sumaya ta ce; "gashinan kana karkaɗawa, maiyasa zaka yimin irin wannan tambayar Baby, relax har yanzu zafin ciwon bai gama sakinka ba, bari na kira Likita" ta ƙarasa faɗa tana sakin hannunsa haɗe miƙewa ta bar ɗakin. Ajiyar zuciya Sufyan ya sauke, sai dai kafin ya yi relax ɗin da Sumaya ta ce, asalin fuskar Malik da babu Tabarau babu komai sai ƙasumbar da shima an ragesa sosai saɓanin jiya da ya cikemai rabin fuska ya bayyana a ɗakin, mai kamannin Salman sak na biye da shi a baya. Jikin Sufyan ne ya saki, tabon tsoron Malik da ya kwana da shi washe gari ya ɓace na dawowa sabo fil, idanuwansa ya kulle gam kamar mai barci. Ido Malik ya lumshe kafin ya saki murmushin da sam bai masa kyau ba saboda bai saba ba, da iya ganin fuskarsa kaɗai zai iya kawar da Sufyan a doron ƙasa ta hanyar bugawar zuciyarsa. Amma Yaron tausayi yake bashi bai san komai ba sai abinda suka ɗorasa akai, ya jima da karantar Sufyan shi ba faɗan kawar da wani ne a gabansa ba, shi dai burinsa ya zama kyakkyawa ya tara kuɗi shima ya zama Dhahab ɗin kansa kamar yadda suke sauraran duk wa su hirarrakinsa ta offishinsa har ma da Gidan da yake kwana. Da buɗaɗɗen muryarsa mai nauyin dake amsa amo da ya dace da kalar siffarsa Malik ya ce "sannu da Jiki Sufyan Ɗayyib Jalal, Allah Ya ƙara afuwa, ga colleague ɗina Uzair ku gaisa" ya ƙarasa faɗa yana nuna Uzair. Sufyan daya kasa gaishesu da sunan ya na barci, kuka ya fasa idanuwansa a kulle, kansa a can gefe. Hannuwansa biyu ya haɗa waje ɗaya ya ɗagashi can sama dai-dai saitin su alamar roƙo. Tsabar kukan da yakeyi kafaɗunsa da ko ina nasa rawa yakeyi. Malik miƙewa yayi zai fita saɓanin Uzair da ya tsaya kallon Sufyan da mamaki. Da taushin Muryar da sam baya kama da na Salman yake tambayarsa da yaren ƙasar Abyad "maiyasa kake kuka?" Damacan Sufyan ba wani sanin Murya Salman ya yi ba balle ya tantance. Sufyan bai amsa ba still yaƙi kallon gefen da Malik ya bar Uzair a tsaye. Sufyan na jin Muryar likita ya ɗan saki ajjiyar zuciya sai dai ƙara jin Muryar Malik a bayansa ya sa ya sume kansa ya karyo kamar zai faɗo daga kan gadon. Hannun Malik Uzair ya ja suka fito waje. Da fuskar tausayi Uzair yake tambayar Malik wanene Sufyan? Maiyasa yake jin tsoron da ya ke sashi sumewa idan ya gansu? "Yankin Tudu, Babban Ɗa namijin Ɗayyib Jalal" Malik ya faɗa yana kallon Diamond Bracelet ɗin hannunsa. Wayar Uzair ne ya faɗi kasa a take gilashin baya da na gaba yayi kwatsa-kwatsa. Dariyar muguntar da ba kasafai Malik ya fiye yi ba yasa ya na kama hannun Uzair da ya sanƙame a tsaye. Wayarsa ya sunkuya ya ɗaukarmai suka bar wajen. Sufyan sai da ya yi kwana biyu yana fama da zazzafan zazzaɓi jininsa har hawa ya yi, baya iya ɗaga kiran kowa, da zarar ya ji motsin ƙofa gabansa yake faɗuwa, hankalinsa baya dawowa jikinsa har sai yaga wanda zai shigo. Likita ne ya zaunar da shi yayi mai faɗan yana so ne ya kashe kanshi? Ko wani abun ake yi mai a Asibitin da yake sashi yawan fargaba? Hannu likita Sufyan ya kamo yana kuka yana bashi labarin su Malik ne suke basa tsoro. A wannan ranar daƙyar Sufyan ya nutsu ya kwantar da hankalinsa tunda likita ya yi masa alƙawarin su Malik ba zasu ƙara dawowa ba. Da yammaci ya dannawa Mahaifiyarsa kira, bayan Sumaya ta tafi Gida ta ɗan huta. Kamar tayi shekaru tana jinya haka Sufyan ya tsinkayi Muryar Mahaifiyarsa. Saitin zuciyarsa da bugunsa yake fita da ƙarfi ya dafe ya ce; "Menene yake damunki Ummeena? Kwanana biyar bani da lafiya babu wanda ya nemeni a cikinku, ashe idan ba buƙatar kuɗi ba, ba ni da wani amfani a gareku" Murmushi tayi kafin ta ce; "Sufyan ɗana na fika shiga halin jinya, domin ciwona ba irin naka bane" gyara zama Sufyan ya yi yana yi mata sannu cikin tausayawa. Kamar daga sama ya ji tace; "Ina ka jefar da makarin sirihin jikin Naila Sufyan?" Kame-kame ya farayi, sauƙin dole na zuwarmasa lokaci ɗaya. Murmushi taƙarayi ta ce; "Sufyan! Malik zai iya riskarka a koda yaushe, amma kafin na baka labari, inaso duk halin da kake ciki karka ɗara kwana biyu baka isa Birnin Abyad wajen Naila ba, duk iya yadda za kayi karka bar Naila ta isa Babban Birnin Abyad ba tare da ta amincewa komen aurenku ba, ko kwanciya ne kayi a ƙasa ka roƙi yafiyarsu, domin Naila itace Makamin tsirarka daga su Malik albarkacin matsayin da take da shi a Dhabah. Karkayi watsi da umarnina kamar yadda kayi watsi da shi ka cigaba da zama da Sumaya, idan ka isa Birnin Abyad duk abinda ka riska ka yi gaggawar kirana domin na baka wasiyyata ta ƙarshe." Tana gama faɗa ta datse kiranta. Shi dai Sufyan bai san abinda ya samesa bayan katse wayar Mahaifiyarsa ba, sai da ya wayi gari yaga Sumaya tsaye a kansa tana kuka.. Daƙyar Sufyan ya daure ya ƙara kwana ɗaya a Asibiti. A gaggauce ya sanar da Sumaya ta shirya kayanta, a kwai aikin da zaiyi a Birnin Abyad. NAILA Suna zaune da Kaka kiran Amira Customarta ya shigo wayarta. Domin Kaka taji komai a sarari ta saka Muryar Amira bayan ta ɗaga. Bayan sun Gaisa cikin zumuɗi take sanar da Naila kitsonta ya yi matuƙar jan ra'ayinsu kuma sunyi alƙawarin biyanta kuɗi masu nauyin gaske. Amma zatayi kwana biyu acan tana yi musu, sannan tayi mata bayanin tace musu tana da Kaka, sun ce zasu turo tikiti da komai mu taho tare. Kallon Kaka Naila tayi tana jiran umarninta. A hankali ta ɗaga kai alamar ta amince!!!!.....😄 Shin Sufyan zai riski Naila.??? 🔥ZINARE🔥 NAFISA ALIYU SASAAL Page 27 Bayan sun yi sallama Naila ta katse wayar, rungume kaka ta yi, ta sumbaci ƙuncinta tana dariya. Kai Kaka ta girgiza jikinta a sanyaye. Kamar Naila bata lura da sanyi da jikin Kaka ya yi ba ta ɗauko waya ina kiran layin Yasar. Da tsananin farin ciki Naila ta basa labari. "Alhamdulillah!" ya furta da daukakkiyar sauti kafin yafara tsokanarta da "Finally yokel sister ta zata leƙa Babban Birnin Abyad, har na hango idanuwanki wallahi" Kaka da ke sauraronsu dariya tasa haɗe da sakin ajjiyar zuciya. Da tsokana Naila suka ƙare waya da Yasar. Da yammaci Kaka Mallam ta kira, ta yi tsammanin zai soki zuwansu Babban Birnin Abyad amma sai taji ya furta "Alhamdulillah" ƙwarin gwiwa da addu'o'in tsari kala-kala ya ƙara bata domin acewarsa; abinda zaiyi sanadin zuwan Naila Babban Birnin Abyad ya daɗe ya na jira kuma gashi Allah ya kawo. Kafatanin kuɗin da Naila take tarawa A banki ta turawa account ɗin mutanen Yankin Tudu. Kafin dare ya yi kiraye-kirayen su sai shigowa yake yi, abun dariyar duk da wayan mutum biyu ake wayan, talauci ya hana da yawansu mallakar wayoyin hannu. Kaka bakinta kamar zai yage, banda "Ameen Ya Allah! Ameen thumma Ameen!" Babu abinda take maimatawa. Ba su daina kira suna Godiya da addu'o'i ba har sai da chajin wayar ya ƙare. A jiyar zuciya Kaka ta sauke, lokaci zuwa lokaci sai ta saki murmushin farin ciki. Kusa da ita Naila ta matso taa zauna ta ce ; "ya ya zakiji idan akace mutanen Yankin mu, sun samu farin cikin da ya fi wannan?" "Zan ji daɗi Naila sama da wanda na ji a yanzu" Kaka ta faɗa da murmushi kwance a saman fuskarta. "To ki saki ranki mu shiga Babban Birnin Abyad, In Shaa Allah ba zamu dawo ba sai da nasarar da zai kawowa Yankinmu gagarumin sauyi." Murmushi suka sakarwa juna. Da yake Yasar ya zo hutun ƙarshen Mako Gida, ziyarar bazata shi da ƴan gidansu suka kai Gidansu Naila don tayata murna. Kaka baki ta saki da ta ji abinda ya kawosu kafin da kwashe da dariya ta na cewa "wai ni kuyimin bayani wani irin arziƙi Naila zata samo a wannan Babban Birnin Abyad ɗin da kowa yake farin ciki, kar fa muje a siyar da mu" Dariya Yasar da Iyayensa suka kwashe da shi, ƙannensa da suka saba wasa da dariya su na tsokanarta. Cikin raha Yasar yake bawa Kaka labarin da zarar ta shiga Babban Birnin Abyad zatasan ko wanda ya yi wanke-wanken rana ɗaya dole ya fito da kuɗi mai tsoka. Ana raha da wasa mukayi Dinner da su Yasar. Sai dare sosai suka tafi Gida. ★washe gari su Naila suka fara kimtsa kayan da zasuyi tafiya da shi, amma har lokacin abinda yake bawa Naila mamaki shine tayaya za'ace zuwansu na kwana biyu ne zai warware ƙullin shekaru aru-arun da ko Kakanta ba haifa ba lokacin, ko dai ta Kaka kashesu za'ayi. ★washe gari daya kamar ranar tafiyarsu, tsaf Naila ta shirya cikin baƙin Abaya haka Kaka irin Abaya ɗaya suka sanya na Company ɗaya. Har Gida ƙanin Yasar ya zo ya ɗaukesu saboda tare zasu wuce da Yasar don haka sai sun fara biyawa Gidansu tukunna A dai-dai lokacin da Motarsu Naila ta gifta ta hangi Sufyan A cikin Motar da take kyautata zaton Taxi ne. Mamakin abinda ya kawoshi ta yi cikin daƙiƙu kafin na tattara lamarinsa na watsar tana danna wayarta. SUFYAN. Ƙwallane ya tararwa manyan idanuwansa da suka ƙara zama farare ƙal lokacin da mai gadi ya tabbatar masa da su Naila sun fita yanzunan ita da Kakarta. Yasan kuma ba Makaranta ta je ba, domin can ya fara biyawa akace sunyi hutu, a hankali ya nemi waje ya zauna ya zaro wayarsa. Bugu ɗaya Hindu ta ɗauka. Ko sallamarsa Hindu bata amsa ba ta ce; "Ka riski Naila?" Jiki a sanyaye ya ce; " a'a" Kuka ta saki na tsayin mintuna shida kafin ta ɗora da; "Son zuciya shine mafarin halakata, bayan tafiyarka muka gano ka yardar da maganin makarin asirin jikin Naila a gidansu kamar yadda Malamin Yankinmu ya sanar mana, maimakon Jalal da Mahaifinka su ga laifinka, sai suka juye laifin akaina, acewarsu duk nina tsiro musu da wannan musibar, sun tisani a gaba da asiri kala-kala kullum cikin ciwo nake, na je wajen Mahaifiyata Ɗayyib ya zugeta ta koroni. Sufyan mafita ɗaya ya ragemaka, ka koma bakin aikinta ka riƙi aikinka da gaskiya da amana, amma a kowani yanayi ka ji tsoron Allah kuma kaji tsoron Malik, domin baya ganinka ba kuma ya tare dakai amma ka sani yana saurararka a duk inda kake a Babban Birnin Abyad kamar yadda malamin duba ya sanarmin, a yanzu amfaninka a wajen Ɗayyib shine ka bincikomai su wanene DHAHAB? banda wannan baka da wani amfani a gareshi, su kuma su Malik suna tare da kai ne domin ganin iya gudun ruwan Jalal, kamar taku ɗaya haka kake da mutuwarka Sufyan a tsakanin Ɗayyib da su Malik, amma abinda na faɗawa Ɗayyib ya hukuntani shine wanɗanda suka ƙirƙiri sabon Dhahab ba abokanan yaƙar su ba ne, saboda suna da damar shafe Yankin Tudu da mutanen cikinta, domin ko kai kanka da kake cikin Daularsu har yanzu mai asalin Dhahab ɗin bai san dakai ba, wataƙila da ya sani da tuni ka jima da ruɓe a cikin ƙarƙashin ƙasa. Ina gayamaka dukka wannan ne domin kayi takatsantsan kamar yadda malamin duba ya sanar da ni, ina nadama Sufyan, ka yafemin. Ba lallai mu sake magana makamanciyar wannan da kai ba, ba kuma lallai ka dawo ka riskeni a raye ba, amma Allah Ne shaida bani da masaniyar komai a kan kisan su Abduh da ahalinsa." Ɗif wayar Hindu ya katse kamar dai waccen ranar. Wayar Sufyan ya bi da kallo yana zare idanuwansa da suka koma jajaye cikin ƙarajin da ya tashi dukka jijiyoyin wuyarsa da goshinsa ya na furta "Ummee! Ummee!! Ummee!!!" A lokaci ɗaya yana ƙara kiran layinta da baya shiga kwata-kwata. Hankali a tashe Mai gadin gidansu Naila ya kiran layin agajin ƙasar. Kafin su iso Sufyan ya zube ƙasa idanuwansa a juye. NAILA. Wannan hanyar da take bi da kallo tsayin shekaru yau gashi zata tunkareshi da ƙarfin ikon Allah. In Shaa Allah anan Free pages ɗin ZINARE ya tsaya. Ga waɗanda suka bibiya ba su da halin biya na gode da comments da addu'o'in ku, ga waɗanda suke da wadatar biya suma ina godiya mai tarin yawa Allah Ya bar zumunci. Kuɗin motar zuwa Babban Birnin Abyad Naira 500 ne kacal, ta wannan account ɗin Nafisat Aliyu Muhammad First Bank 3207955182 tare da tura shaidar biya ta 09132403788,08138665117. Ga masu bibiya kuma ta Arewabooks sai su ɗora. In Shaa Allah zamu cigaba da Posting ranar Monday, 4, August, 2025 da misalin ƙarfe 8:00pm Na gode🙏🏻 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 ZINARE. 2 BY NAFISAT ALIYU SASAAL CHAPTER 1; *DOGON TARIHIN AHALI MAI ƊAUKAR HANKALI DA ƘARFIN ARZIƘI TARE DA DARAJA TA MUSAMMAN A BABBAN BIRNIN ABYAD*🔥🔥🔥 Page 1 SUFYAN Hour biyu ya yi a kan Gadon Asibiti kafin ya farka. Gefensa Iyayen Sumaya ne da ƴan uwanta . A can gefe kuma Sumaya ce a zaune itama idanuwanta sun kaɗa sunyi jajir alamun tasha kuka. Guri ɗaya ya ƙurawa ido farkon zuwan Bushra da Yasar makarantarsu na dawomai; "Bushra tayimin alƙawarin komawa Makaranta bayan na fara aiki a Babban Birnin Abyad, maiyasa ban ƙara ganinta ba?" Wani sashe na zuciyarsa ya tambayi wani sashe. Ƙasa-ƙasa Sufyan ya ce; "Ni na wargatsa komai da kaina, ni na cuci kaina da kaina, son zuciyata ya sa na zaɓi Sumaya na wulaƙanta Naila. Kwaɗayin duniya da shagala yasa na manta batun komawata Makaranta na baje a Gida mai na'urar sanyaya ɗaki da Ofishi, yanzu gashi duk komai ya hargitse a cikin kwanaki ƙalilan, tayaya Malik yake iya saurarata bayan baya ganina, sannan kuma bai kasheni ba mai yake nufi da ni? Maiyasa ya yankewa Baffan Mahaifina Bashar harshe? Mai Mahaifina Ɗayyib yake nema da zuri'ar amininsa Abduh Dhahab dayake kukan rashinsa kullum? Menene suka jima suna ƙullawa tun zamanin kakannin-kakanni na? A kwai abubuwa dayawa da ya kamata ace na sani, amma son kyau irin nawa ya jagoranci mayar dani mai ƙaramin ƙwaƙwalwa da ƙaranci tunani. Kurakuraina a bayyane suke, amma ta yaya zan gyara su? Na ɗauki darasi mai girma, domin duk Namijin da yaba kyawunsa zai zama lagonsa to tabbas wata rana zai faɗa a komar danasani, saboda da shi Sumaya ta rijayeni har muka fara soyayya ba don tafi Naila kyan siffa ko na haliba sai don zuzuta kyawuna da take yawan yi. Gane lagona na son a cemin ina da kyau yasa bamayin hirar minti goma bata nanata baiwar kyan da Allah yayimin ba, tare da zuzutani, irin zuzutawar da tasan zai ɗimautarni, Ni kuma gareni hakan shine so, domin ni bandamu da na yabeta ba amma ita bata gajiyawa kamar karatun bita. Har a wasu lokutan ta kan cemin babu Namijin daya kaini kyau, maimakon na fahimci kalamanta a matsayin yabo, a matsayina na masoyinta sai na ɗauka dagaske Ni ɗin Namijine dana fi duk Mazan Abyad kyau, samun irina sai an tona" babu wanda ya ji abinda Sufyan yake faɗa sai bakinsa da suka ga yanata motsi. Sumaya da ta kasa jurewa ƙananun maganganun da yake yi da iya motsa laɓɓansa ta ce; "Sufyan ka nutsu ka sawa zuciyarka salama, In Shaa Allah komai zai yi sauƙi banason wannan ƙananun surutan da kakeyi Kaji" Kamar an mintsinesa ya miƙe. "lafiya Sufyan?" Ta tambaya itama tana miƙewa "Zan wuce bakin aikina, kwana ɗaya na tambaya" ya faɗa yana ƙoƙarin tattara Rigarsa. Baijira ƙorafin da sukeyi ba, ya ɗora rigar saman shirt ɗinshi da aka ciremai ya kwashi wayoyinsa da Card ɗinsa ya bar ɗakin. Da sauri Sumaya ta rufamai baya tana kiran sunansa. NAILA; A zahirin gaskiya ta so ace tafiyar Mota zasuyi domin ta kalli gagaruwan da suka fi kusa da Babban Birnin Abyad, amma haka ma bata ɓaci idan suna dawowa sai su biyo Mota. Kamar ta yi tsuntsuwa ta ganta a Babban Birnin Abyad haka take jinta, Yasar sai dariya yakemata yana tsokanata da "ƴar ƙauye zata je Birni" Ita da Kaka duk sai da sukaji tsoron hawa jirgi duk da ita Naima wannan ne karonta na biyu. Da sannu jirginsu ya ɗaga daga Birnin Abyad zuwa Babban Birnin Abyad. Bayan sun sauka A kwai banbanci mai girma tsakanin airport ɗin Birnin Abyad da na Babban Birnin Abyad. Ɗan waiwayowa Yasar ya yi ya ce; "ki kirata idan babu nisa, sai nasa Drivern da zai zo ɗaukata ya fara saukeku kafin mu wuce" "Okay Sir!" Naila ta ce tana saramai, dariya suka saki dukkansu har da Kaka. Bugu ɗaya Amira ta ɗaga, jindaɗin Naila ta ce mata gata ta iso bayyana a cikin muryarta suka gaisa. Cikin zumuɗi Amira ta ce, zasu turo Driver idan kuma zata yya tarar Taxi to ta ce masa ya kawota DHAHAB. Cire komai da Naila ta yi a ranta tun kafin tahowarsu dangane da Sulaim ne yasa batdamu da sunan da Amira ta ambata ba amma duk da haka sai da zuciyarta tayi bugun ɗakiƙu. Bayanin Yasar zaisa Drivern da zai zo ɗaukarsa zai sa ya ɗaukesu tayiwa Amira basai sun turo Driver ko sun hau Taxi ba. Godiya Amira tayi tare da cewa ta kirata idan dun iso. "ta ce Dhahab za'a kai mu" Naila ta faɗa bayan ta sauke wayar daga kunnenta tana kallon Yasar Murmushin fuskar Yasar ne ya ɗauke lokaci ɗaya. "Dhahab? Dhahab fa kikace Naila? Ki ƙara kiranta ki ji ko jine bakiyi da kyau ba, domin bare baya shiga Dhahab kai tsaye" Musu da haƙiƙancewa ba halinta bane don haka ba tare da tace komai ba ta ƙara dannawa Amira kira, a sarari ta saka wayar saboda Yasar yaji da kunnen sa. Tabbacin can za'a kaisu da Amira ta bayar yasa Yasar shafa gefe da gefen fuskarsa haɗe da furzar da huci ya ce; "Kin ce biki zasu yi ko?" Da sauri Naila ta ce "eh" Wayar Abokin aikinsa ya kira ya tambaya. Ya shadamai bai san da wani biki ba, amma bari ya bincika sashen hadimai yaji. Domin yaji kamar ƙiƙishin-ƙishin ɗin amincewar Sir Malik akan wani biki da za'ayi a Ɓangaren. Naila da Kaka dukkamsu shiru sukayi kowa da abinda yake saƙawa a ransa. Burina ta isa Dhahab ta ga menene a ciki. Kaka kuma mamaki takeyi saboda sunan da yayi mata kamanceceniya da na ahalin su Marigayi Abduh da kuma yadda Yasar sam bai nuna farin cikin inda zasu je ba kamar yadda ya nuna kafin tasowarsu. Ko minti biyar ba'a rufaba aka ƙara kiran Yasar. Tabbacin shagalin Bikin ƴar ɗaya daga cikin masu dafa abincin ɓangaren Hadiman Dhahab aka bawa Yasar, kuma da izinin Sir Malik akeyin komai. Tsaki Yasar ya saki, bawai baya son Naila taje bane tsoro yake ji kar wani abun ya samesu. Bayani ya yi musu a can yake aiki shima, amma bai san da biki ba Gidan, ashe ɓangaren masu dafa abincin Hadiman Gidanne suke aurar da Ƴa. Jakar daya so faɗuwa ta ƙanƙame. Irin kuɗin da Amira ta ke kashewa a Makaranta da irin motocin da take hawa na faɗomata. Bayan gama wannan tunanin a zuciyarta Naila ta ce; "Hadimai kuma? Yanzu saboda kitson ƴaƴan Hadimai masu girki, girkin ma bana mutan Gidan ba a'a na Hadimai ƴan uwansu shine zasu gayyotoni tun daga Birnin Abyad har su biyamin kuɗin jirgi ni da Kakata? to ko dai suna nufin da kuɗin da zasu bayani muka hau jirgi? Wallahi bazai saɓu ba" maganar Yasar ne ya katsemata zancen zucin da take yi. "Da nasan Dhahab zakije da ban amincewa zuwanki Babban Birnin Abyad ba, wallahi tsoro nake ji, amma Allah Ya sa ku shiga lafiya ku fito lafiya" Da sauri Naila ta amshe da; "Ameen, Nima da sani banzo ba, tayaya zanzo yiwa ƴaƴan Hadimai masu yin girki Hadimai kitso tun daga Birnin Abyad, nawa suka ci nawa suka bayani, ni dai kam sun cuceni wallahi" "In dai Hadiman Dhahab ne zasu iya biyanki kuɗi sama da hasashenki Naila" Yasar ya faɗa ya na shigewa lafiyayyen Motar da ya zo ɗaukarsu. Lokaci zuwa lokaci sai ya ja tsaki har muka fita daga Airport gaba ɗaya. TSAKIYAR BABBAN BIRNIN ABYAD Naila ba ta yadda zata fasalta kyan Babban Birnin a zahiri ba, amma yana da kyau irin kyan da bata taɓa gani ba ko a talabijin, Gine-ginensu da komai nasu na alfarma ne. Mutanensu masu kyan gani ne sama da na Birnin Abyad, babu hayaniya da karamniyar abubuwan hawa duk masu tsada ne da kyan gani a ido, dai-dai da Motocin sufurinsu abin kallone. Baki, hanci da ido Naila ta saki ta kallon komai tare da haddacewa don ta bayar da labari wata rana. DHAHAB A zuciyar Naila ta ce; "Zan iya kiran Dhahab haɗaɗɗiyar Daula ko na ce wata duniya da wani Attajiri ya ƙirƙira a Babban Birnin Abyad" A Gajaren Gate ɗin dayake bawa na wajen damar ganin rukunin Gidajen da aka yiwa gini na alfarma Motarsu ta dakata. Jami'ai masu murɗaɗɗen fuska da jiki ne suke gaɗin ɗan gate ɗin da mutum zai iya haurawa a guje. Wayarta Naila ta zaro ta kira Amira domin ta sanar da ita isowarsu. Kafin Yasar ya sauka daga motar kanshi ya juyo bayan Naila ta gama waya, daga kujerar gaban da yake zaune zuwa saitin inda take. A hankali yadda Kaka bazata ji sa da kyau ba ya ce; "Abune da bai taɓa faruwa ba barin Hadimai suyi shagalin bikinsu a Dhahab, don haka ku kula da kanku Naila, ba lallai na ƙara kiranki a waya ba domin ga dukka alamu Sir Malik yasan da zuwanki, idan har ya san da zuwan naki kamar yadda na faɗa to dukka maganganunmu da zarar mun shiga Dhahab tamkar a kunnensa mu keyi, haka tsarinsu yake kuma ina kyautata zaton shine Malik ɗin da kike nema. Ko da wani zai tamabayeki game da Yankin Tudu, karki nuna kinsani ko kin taɓa rayuwa a ciki. Karki sanar da Kaka abinda na faɗa domin zata iya sakin layi har Sir Malik ya gane mun tattauna dake, duk da zuwa yanzu nasan labarin muna tare ya je mai. Ki barta tayi maganganunta domin nasan bamu da wani mugun abu da zata faɗa wanda zai iya kawomana matsala. Ki kula Naila domin daga yanzu zakiyita ganin abubuwan da zasu baki mamaki da tsoro matsawar dagaske shi ne Malik ɗin da kike nema." Yasar yana gama faɗa ya gyara zaman rigarsa yana barin Motar. Zuciyarta tsabar bugu kamar zai fasa ƙirjinta ya fito. Yasar ya na fita suma Naila suka fito ƙafafuwan Naila da take ƙoƙarin saitawa suna rawa. Kaka kuwa har ƙanƙance idanuwanta takeyi wajen kallon rukunin Gidajen haɗe da yiwa Ubangijin da ya halicci talaka da mai arziƙi tasbihi. Naila itama ƙarewa gine-ginen kallo takeyi tana ganinsu kamar furen da aka shuka. A kan idanuwansu Yasar da Driver su ka nuna shaidar shigarsu Dhahab suka bar su Naila a tsaye. Suma ba su fi minti uku ba mota mai kyan gasken dayasa kaka ƙara ƙanƙame luggage ɗinta ya fito ɗaukarsu. Kafin su shiga motar sai da aka caje kayansu da su kansu, Naila da Kaka sai zare idanuwa sukeyi, ƙarfin gwiwar da sukejin suna da shi na kawowa Yankinsu cigaba ko ta halin ƙaƙa nayin sanyi. Naila da Kaka kallon duniya daban sukeyiwa inda zasu shiga Musamman da zancen Sarkin tsafin Yankin Tudu yake yawan faɗomusu, ashe shiyasa Allah Ya haramta duba, da yanzu bazasu wani damuba hankalinsu kwance. Da Bismillah suka shiga motar da ƙamshinta ya sa Naila lumshe idanuwanta, yanayin fargabar da take ciki na barin zuciyarta. Mota ce da bata taɓa hasasowa kanta shiga irinta ba, ko ba komai suma zasu bayar da labari idan Allah Ya ƙaddara komawarsu Birnin Abyad. Duk da Kasantuwarsu a cikin mota hakan bai hanasu yin Bismillah da addu'a yayin shiga gate ɗin Dhahab ba. MALIK A ɓangaren da idanuwansa suke Lumshe yana sauraran maganganun da Yasar ya gama faɗawa Naila ta na'urar dake maƙale a kusa da Yasar ɗin bai sani ba, miƙewa ya yi yana yana gyara zaman earpod ɗin kunnensa. Yaƙi taimakon Naila ne saboda bayason dawo da hannun agogo baya, shiyasa lokacin daya gane Bushra ta shigar da takardun bogin Sufyan na naiman aiki kai tsaye ya ɗaukesa don gina rayuwar Naila, sai dai daga baya ya fahimci Sufyan fa ba Naila yakeso ba, kuma ba zai taɓa sonta tsakani da Allah ba.. lamarin Naila lamarine da bai isa yayimasa kutse kamar na ragowar Mutanen Yankin Tudu ba, saboda wasu dalilai, shiyasa ya haƙura ya zubawa komai ido, ko ranar da ya ganta a gidansu Yasar tsaf ya ganeta har a wajen Siyayya duk ya gane, amma bashi da zaɓi akan lamarinta banda ya zuba ido. kwatsam satin da ya wuce Sashen Hidaman Gidan suka naimi alfarmar mai kitso zata zo tayimusu kafin su fara shagalin Biki acan gidansu, da ya bincika ya gano Naila ce zata yi musi, sai ya basu dama su yi bikin ma a Dhahab gaba ɗaya ko Allah zai sa a wannan karon ya samu damar takarar lamarin Naila.. Barkanmu da zuwa DHAHAB BABBAN BIRNIN ABYAD🤗 [8/8, 8:33 AM] nafisaaliyusasaal: SASAAL 2 A ɓangaren Sufyan Duk kiran da Sumaya take ƙwalawa masa bai saurareta ba har ta cimmai. "Menene dukka wannan Sufyan? I'm tired of all this, har sai tsahon wani lokaci zamuyi zaman farin ciki a tsakaninmu? kai ne kullum Baabanka da Ummeenka su kiraka tambayar kuɗi, yaya kake rayuwa? mai kakeyi yanzu? su yi ta tambayarka kamar baka da Iyali, it seems kamar ma ɓoyemusu kakeyi muna tare. Yau ka firgita gobe ka zabura duk sai wahalar da ni kakeyi, yanzu gashi ka fito kanaji ina kiranka amma kayimin banza, gaskiya na gaji" Sumaya ta faɗa cikin fushi. "Ina ruwanki da kuɗin da suke tambaya, kuɗin ki ne? Okay so kikeyi kar su kira su tambayi lafiyata saboda ke ko? Kinsan ya ya akayi ma na zo nan eh!? Kin gaji da zama da ni kika ce ko? To kije na sakeki mun rabu nima na gaji" Sufyan ya ƙarasa faɗa ko a jikinsa, yana ƙoƙarin tarar Taxi . Cikin masifa da hargagi Sumaya ta zagayo saitin fuskarsa ta ce; "Daga ganin wannan Yankin naku dole ka zama Violet person! tunda na lura kamar da rashin zaman lafiya da wulaƙanta Ɗan adam aka gina Yanki..." Marin da zai sauƙaƙawa Sumaya gane da gaske Sufyan Violet person ne ya sauke mata a dama da hagun fuskarta yana tura ta gefe, har sai da ta faɗi ƙasa dafe da ƙuncinta. Kafin ta yunƙura ya tari Taxi ya shige. Ƙurawa Taxin idanuwa tayi kamar zasu iya dawo da Taxin baya. Ganin dai da gaske Sufyan ya tsere mata bayan furta kalmar sun rabun da ta tsana, sai ta durƙushe a ƙasa tana kuka. A haka ƴan uwanta da suka ji shiru suka sameta. Tana kuka ta na fizgewar su ƙyaleta ta bi Sufyan suka turata cikin Mota. A ɓangaren Naila Daa can yawan surutu da rawar kai ba halinta ba ne, amma maganganun da Yasar ya faɗamata kafin shigowarsu Dhahab yasa ta ƙara nutsuwa tare da gumtse bakinta. Basu yi wata tafiya mai nisa ba, suka sha kwana, anan rukunin Gidaje masu kyau suka bayyana, ba irin waɗanda suka wuto ba. A hankali Driver ya dai-daita parking duka sauko. Cikin rashin riƙe zance duk ƙanƙantarsa Kaka ta ce; "Yanzu Bawan Allah menene abun hawowa Mota a nan? ji fa ga baki ga hanci, ku dai kam masu arziƙi akwai ku da son jiki wallahi" ta ƙarasa faɗa tana kallon hanyar da suka biyo. Hannunta Naila ta kama haɗe da ɗan matsawa. Maimakon tayi shiru tunda ta fahimci abinda Nailar take nufi sai ta ƙaracewa; "au to nayi shiru." Kamar kurma haka Drivern daya ɗaukosu yake babu magana babu murmushi balle dariya. Da farin cikin Amira ta tarbi su Naila zuwa ainihin cikin gine-ginen. Kai Naila a ƙasa su ka shiga saɓanin Kaka da take kallon komai dalla-dalla domin idan ta koma Birnin Abyad ta samu abun bayarda da Labari. Tarba na ban girma aka yimusu a living room ɗin daya amsa sunansa. Kowa ya shigo sai ace wannan itace mai kitson da Sir Malik ya amincewa shigowarta Dhahab daga Birnin Abyad. Ko sun juya da sunan tafiya sai sun ƙara waiwayo sun kalleta, ga shi babu damar yin magana kar su je ana jinsu. A wannan rana hutawa kawai su Naila su kayi sai ɗan hira sama-sama da Kaka take yi da yayar Mahaifin Ameera da take aurar da Ƴa. Duk Hadiman da suke shigowa Masha Allah masu kyau da su, ga kyan fatar dake nuna kwanciyar hankali da wadataccen cima mai kyan da suke samu, uwa uba albashin mai tsokar da zai sauya rayuwar mutum da ahalinsa, amma fa banda munafiki da maci amana. Masauƙin Ɗaki daban-daban aka yiwa Naila ita da Kaka amma suka nuna ɗaya ya ishesu. Daga Naila har Kaka kallon ko ina na ɗakin da aka kaisu sukeyi kamar ba mazauna Birnin Abyad, to idan Hadiman Gidan suna da irin wannan gatan to ina ga mutan Gidan? Kaka ta tambayi kanta tana dariya. Duk yadda Kaka take jan Naila da hira Naila ba tacemata komai ba, cikin takaici ta ce; "Wai ni Naila wanene wannan Sir Malik ɗin da idan aka ambaceshi sai na ga sun ƙara waiwayo sun kallemu anya babu wata a ƙasa kuwa?" Shiru Naila tayi kamar bata jita ba, wannan dalilin yasa ta fusata tana cewa; "Wai ni Naila mai ya canzakine kin zama kamar wata kurma, sai surutu nakeyi kin ƙi kulani, ko don kinga zaki samu kuɗi shine zaki fara wulaƙantani tun yanzu?" Kaka ta ƙarasa tambayar tana kallon Naila. Naila batasan sanda ta saki dariya ba har da kwanciya. "Kaka har wani irin kuɗi zan samu da zan kasa yi miki magana, ko na wulaƙanta ki? Kaka idan aka je baƙonta kame kai akeyi, kuma na ga kamar kin manta da abinda ya kawo mu" Naila ta faɗa bayan ta tsagaita da dariyar da take yi. Ɗan jim Kaka ta yi kamar mai tunani sai kuma ta zaro wayarta batare da ta ƙaracewa komai ba. Har barci ya ɗauke Naila Kaka suna waya da Mallam yana yi mata bayani tare da ƙaramata wasu addu'o'in. ★Barcin mai daɗin da sukayi a lallausar katifar audigar dake Ɗakin da aka basu yasa suka makara sallar Asuba Kaka har da ɗan yawun barcinta a gefen kumatu. Da sauri Naila ta watsa ruwa ta ɗoro alolar sallar Asubahi saboda Masallin da ta ke kyautata zaton a gidan yake har sun tayar da Sallah. Da gari ya yi haske bayan an kawo musu lafiyayyen Abincin kari, sun karya, Ameera ta zo tafiya da Naila. Yini sukayi tana kitsa musu gashin kansu mai tsaho da shaiƙi, duk hirarrakin da sukeyi Naila batasa musu baki ba, na dariya dai takan ɗan murmusawa lokaci zuwa lokaci. Basu gama ba sai wajen ƙarfe taran dare. A wannan dare cikin fargabar da ya ragewa su Naila saura kwana ɗaya su koma Birnin Abyad ba tare da sunga wani canji daga abinda suke zargi ba Barci ya ɗaukesu. A rana ɗaya Ubangiji yake ƙaddara ɗaukaka ko kawo ƙarshen zaluncin da al-umma suka jima a ciki, duk da za'ayi shafe shekaru ana gwagwarmaya ba tare da anci nasara ba. ★Washe gari da Safe kamar jiya Ameera ta shigo kiran zamu gaisa da BARIRAH tace kitson da ta gani a kawunansu ya birgeta a kira Naila ta ganta ko zan yimata irinsa. BARIRAH itace wacce aka wakilta daga cikin Dhahab ɓangarensu Malik domin ta isar da kyautar da Mahaifiyar Malik tayiwa Amarya saboda ita bazata samu damar fitowa ba. Ta canza irin canjin da zaiyi wahala idan mutanen Yankin Tudu suka ganta su ganeta, ta ƙara fari da kyan jiki kamar ka saceta ka gudu, taƙama da izzarta da talauci ya danne a shekarun baya ya bayyana daga yanayin zamanta. Kamar bata taɓaganin mai irin halittarta ba haka Naila ta nuna tare da gaisheta tanayin ƙasa da kanta alamar girmawawa. A ɗan firgice Barirah ta amsa tare da furta tambayar da ta kasa dannewa; "Ya ya sunanki? " A taƙaice ta ce "Naila" Sai da ta ƙara gyara zamanta tana matse yatsun hannunta da zobunan zinare ke jere waje ɗaya ta ce; "Daga wani Yanki kike bayan Birnin Abyad, ina nufin asalin ƴar ina ce ke?" Cikin ladabin da ya ɓoye rawar da jikin Naila yake yi ta ce; "Birnin Abyad shine asalin Yankin da na fito" Ba ta gamsu ba tace akira mata Kakar Naila. WAIWAYE; Shekarun baya rashin jituwar Mahaifin Naila da ƴan uwansa yasa Mahaifinsa bayason Mahaifiyar Naila, wannan dalilin yasa ya hana Kaka zuwa Gidansu Naila, a waccen lokacin sai ya ce ita take zuga Mahaifiyarta basa jituwa da Matan Yayyan Mijinta tunda ba ita ta haifesu ba. Wannan dalilin yasa su SIMBI da BARIRAH ba su wani san Kaka ba, sannan kuma daga Shekarun da suka bar Yankin Tudu zuwa yanzu Kaka ta ƙara tsufa, irin tsufan da shekarunta ba su kai ba, saboda jarabawar da yayita samun mu. DAWOWAR LABARI Wannan dalilin yasa ko da Kaka ta fito Barirah bata ganeta ba, itama Kaka da bawani saninta tayi ba sam bata ganeta ba. Ko da ta tambayi Kaka, bayan Kaka ta gaisheta kai tsaye Kaka tace mata su asalin ƴan Birnin Abyad ne. Cikin rashin gamsuwa da kuma son ƴar uwarta Simbi ta bambance mata da gaske Naila ce ko ba ni bace ta ce; "Salon kitson ki ya birgeni matuƙa, kuma an sanar dani lokacin tafiyarku ya yi, inason ku ƙara kwana biyu gobe sai kiyimin jibi ku wuce. Hadimai zasu rako ki." Bata jira amsar Naila ba ta miƙe tana sharce gumin daya tsatsafomata a goshi duk da na'urar sanyaya wajen da yake aiki 24/7. Bayan ta kai ƙofa sai da ta ƙara waiwayo ta kalli Naila sannan ta bar living room ɗin. Su na shiga ɗaki Naila ta zube akan katifa tana dafe saitin zuciyarta. Tambaya Kaka ta titsiyeta da shi; "Naila wacece wannan? sam banyarda da ita ba, ki yimin bayani menene ya haɗaku? kinsan ta ne a wani wajen? maiyasa take son sanin ko daga wani Yanki muke?" Rasa tambayar da zata fara amsawa a Kaka tayi. Don haka ta fara bata labarin wacece Barirah ba tare da tsoron Malik yana jin su ko baya jin su ba kamar yadda Yasar ya faɗamata, tunda Ubangijin da zai karesu Yana tare da su. Manyan idanuwanta Kaka ta zaro kamar zasu zubo ƙasa "Barirah ƙanwar Malik?? tayaya Naila????" MALIK! Duk maganganunsu Naila da abubuwan da Barirah ta aikata duk bai samu damar saurara ba saboda uzurin da ya taso mai. Kafin ya tafi uzurin da ya taso masa sai da ya kira Bushra ya kwantar mata da hankali ta juyemasa labarin rayuwar da Naila tayi da Sufyan da kuma wanda take kanyi da Kakarta. Kamar yadda yafi tafiya a lokutan Asubahi kafin ketowar alfijir ko Cikin dare, a yau ma haka ya yi. Baƙaƙen kayan da ya fi amfani da su ya sanya hatta gilashinsa da ya sakaya idanuwansa dashi baƙine. Da ƙaramin Luggage ya bar Dhahab zuwa nahiyar Turai. YANKIN KAHALA BIRNIN HONOLULU JAHAR HAWAII Lemon da aka ajjiyemai Malik ya taɓa haɗe da ɗanyi balance yana danna wayarsa. Ƙarfin ƙamshi da takun dake ƙara kusantosa ne yasa ya ɗan zabura yana gyara zamansa haɗe da zame baƙin tabaran fuskarsa. Balmin Shirt dark blue, da Black three quarter trousers Matashin da ya bayyana a gaban Malik yake sanye da su. Zama ya yi a Couch ɗin da ke kallon na Malik suna fuskantar juna. Malik zamansa ya gyara tare da haɗe yatun hannusa waje ɗaya bayan ya tattaro nutsuwarsa sannan ya ce; "Barka da yamma" Maimakon amsa fararen idanuwansa dake kan fuskar Malik ya lumshe, wanda a wajensa shine a madadin amsar gaisuwa. A hankali Malik ya ɗago fuskarsa bayan ya ƙara saita nutsuwarsa, cikin daƙiƙa biyu ya ƙarewa Matashin da ƙirar jikinsu yake kusan iri ɗaya kallo, sai ɗan tsaho da Matashin yafishi, kansa ya mayar ƙasa a hankali ya motsa laɓɓansa da tambayar "ya ya mai jiki?" Tambayar ya ya mai jikin da Malik ya yi masa ne yasashi ƙara ɗago idanuwansa yana kallon cikin idanuwan Malik. Da ɗaurarrariyar fuskarsa mai tsananin kyan gasken dake ɗauke da idanuwa masu haske ya cigaba da kallon Malik ba tare da ya ce komai ba. Kasa jurewa kallon fuskarsa yasa Malik yin ƙasa da nasa kan yana murza Diamond Bracelet ɗin hannunsa. ya ɗauki daƙiƙu yana karantar Malik kafin ya furta; "Alhamdulillah" da muryasa mai tsada a wajen mutane da daɗin sauraro ga wanda ya samu ji😄 KAFIN MU SAN WANENE WANNAN MATASHIN BARI MU SAN AINIHIN DALILIN DAYA JANYO KASHE-KASHE A MARAUTAR YANKIN TUDU DA KUMA SU WANENE SUKE AIKATA SHI, SANNAN MUSAN SHIN DAGASKE SU ABDUH DHAHAB SUN MUTU, KO KUWA SUNA RAYE KU BIYO NI; [8/8, 8:34 AM] nafisaaliyusasaal: SASAAL 3 Kamar yadda Kaka ta taɓa bawa Naila labari a baya a zamanin mulkin Sarki Musa ya yi sauƙin kai ga mutanen Masarautarsa da na Yankinsa wannan yasa kowa yake sonsa. Jamil Kakan Jalal shine Aminin Musa tare suke komai, sai dai daga lokacin da Sarki Musa ya tura Abdulyasar Babban Birnin Abyad wajen abokanan hulɗarsa da sunan naiman ilimi ya dawo da dukiya har ya samu laƙabin Dhahab, komai ya canza a ɓoye a ɓangaren Jamil acewarsa; "mai zaisa Sarki Musa ya munafurceni ya kai ɗansa inda zai zama Attajiri amma bai haɗa da nawa ƴaƴan ba?" Wannan arziƙi da Abdulyasar ya dawo da shi, shi yazama tsatsa a zuciyar Jamil da zuri'arsa ba tare da kowa ya sani ba. Jamil mutum ne mugun gaske kuma mai riƙo da kafiya. A kwai fahimta sosai tsakaninsa da Sarki Musa, amma wannan dawowar ta Abdulyasar Dhahab da arziƙi mai tarin yawa daga Babban Birnin Abyad sai ya gurɓata son dayakewa Sarki Musa, a take ya fara shirya kaishi ƙasa duk da bayanin da Sarki Musa ya yi mai dayaga alamar kamar baiji daɗi ba; " Ni ban tura Abdulyasar domin ya naimi kuɗi ba balle ya tara arziƙi. Na turashi ne domin ya naimi ilimi ya kuma samu kariya daga ragowar Iyalina" maganganun Sarki Musa tamkar rainin hankali suke a wajen Jamil da kuma ƙara tunzura zuciyarsa, amma bai nuna ba ya barwa zuciyarsa. A hankali shida ragowar Iyalin Sarki Musa da suke ganin ya fifita Abdulyasar akansu suka yi masa sihirin da ya sashi kwanciya dogon jinya har Ubangiji Ya ƙaddarar ajalinsa. Cikin ikon Allah, Allah Ya bawa Jamil tsahon rai har Ubaidullahi Dhahab Ɗan Abdulyasar ya ƙara zama mai arziƙi akan idanunsa. Wannan yasa ya yi alƙawari tare da alwashin yaƙi da wannan Laƙabi da suke amfani dashi, har ƴaƴansa ya cewa; "laƙabin Dhahab(Zinaren) da suke yiwa kansu sai ya zama Tarihi a Yankin Tudu nayi alƙawari! Kuma ko bayan raina ku sanar da jikokina su shirya Yaƙar Dhahab har sai sun ɓatar da fuskokinsu a Yankin Tudu da duniya gabaki ɗaya. Tunda Musa ya ci amanata to nima zanyi ramuwa gayya gareshi, ramuwa mafi ciwon da babu kamarsa!" Jamil bai ɗora zuri'arsa akan komai ba sai hassada ƙyashi da tsananin mugunta tare ramuwar gayya ga duk wanda ya cucesu. Da haka ya raini Mahaifin Jalal, shima Maihaifin Jalal da haka ya raineshi, shima Jalal ya raini Ɗayyib a haka Ɗayyib kuma ya kasa rainon Sufyan daya fita Zakka. Kamar yadda Jamil ya yi alƙawari kuma Allah Ya cikamasa Kafin ya koma gareSa ya girbi abinda ya shuka, Jamil bai bar duniya ba sai da yaga gawar Ubaidullah, kuma ya mallaki filin mafi girma a kaf faɗin Yankin Tudu ya haɗa har da na Al'umma a ciki... Tun suna yara aka shirya Abotar Ɗayyib da Abduh Dhahab saboda da Ɗayyib zasu yaƙi Abduh. Ɗayyib tun yana yaro akwai basira da nuna kamar bai san komai ba kuma shi babu ruwansa a kan duk wata badaƙala dake faruwa a Masarautarsu wannan dalilin yasa Abduh ya yarda dashi irin yarda dake tsakanin Aminai. Irin wannan Abotar Ɗayyin yaso ƙullawa tsakanin Sufyan da Sulaim sai dai Zaren ba kalar yadin ba ne! *Menene ya faru da Abduh da Sulaim? Da gaske sun mutu? Wanene ya kashe su? Wanene ya yankewa Dattijo Junaid harshe? Wanene Abdallah kuma wanene ya ƙullamai sharrin fyaɗe? Da gaske Salman ya mutu, wanene ya kashe shi? Idan da gaske ya mutu to wanene Uzair? Ya ya akayi Malik ya yi kuɗi? ABDUH DHAHAB; tun da ya kalli fuskar Ɗayyib lokacin da ya je dubashi a Gidan Jalal, maganganun da Abokin Ɗayyib ya faɗamai a sirrince ya faɗomai na Ɗayyib yana son ganin bayansa ya shirya sayar da komai ya bar garin ya hana shi sukuni. A take Abduh ya yankewa kansa shawarar tafiya amma ya yi alƙawarin ko ya tafi zai turo wakilin da zai kawowa Yankinsa cigaba, domin da wannan kuɗirin Iyaye da Kakanninsa suka rasa Ransu. Tun bayan sayar da Tukwanensa ga Baƙin Turawa, ya je Iyakar Yankin Tudu ba tare da sanin kowa ba, ya kira Abokanan Kasuwancinsa da suke mutunci su Naima mai Matsuguni a ƙasar Abyad. Tunda ya dawo a ranar yake tsammanin zuwan wani daga Masarautar amma ya ji shiru. Bayan kwana biyu da wannan Mutanen Masarautar Yankin Tudu suka cimmai. Baisan san da Sulaim ya tashi ba, amma ihun Sulaim na farko ne ya tashesa. Tsaf ya ke kallon yadda Ɗayyib yake yankarmai jikin Ɗa mafi soyuwa a garesa domin ta muryarsa ya gane Ɗayyib ne. Bai motsaba domin bashi da ƙarfin yaƙar su saboda yasan bashi kaɗai bane dole akwai wasu. Sai dai cikin ikon Allah, hankali Ɗayyib ya kai kan Iyalinsa Mairam. Ɗayyib yana tafiya wajen Mairam Abduh ya sanɗa ya fara jan Sulaim a hankali dai-dai lokacin da Mairam take kallonsa, saɓa Sulaim ya yi a kafaɗa yana jan buhun kuɗin da yake rinjayarsa a hankali. A hankali ya bi ta ƙofar baya ya isa gidan Mallam. Mallam da ya riga yasan da batun shirin Masarautar Yankin akan Abduh kamar yadda Abduh ya sanar mai a tsakar gidan yake sallar dare ba ya komawa cikin ɗaki har sai yayi sallar Asubahi ko Allah zaisa Abduh ya ƙwanƙwasa. Don haka Mallam yana ji an ƙwanƙwasa ƙofa ya buɗe da sauri kafin ya nufi kekenunsa, da ƙarfin hali Abduh ya iso wajen Mallam da sauri. Mallam shi ya ɗauki kuɗin Abduh ya goya a baya kekensa, shi kuma Abduh tuni ya nufi Asibiti da Sulaim da ɗaya keken. Mallam saƙon Iyalinsa ta tafi Yankinsu ya bata idan Asubahi tayi, zai biyo bayansu idan ya dawo. Bayan sun isa Mallam a gaggauce ya ɗaurewa Sulaim ciwo ya ce; "Abduh ku tafi wataƙila su iso garemu, bana so su cimmana, In Shaa Allahu wata rana zamu sake haɗuwa ka ji" ya ƙarasa faɗa da rauni a muryarsa. Kuka Abduh ya fashe dashi yana ƙara saɓa Sulaim a kafaɗarsa. Suna tafiya suna kuka, sai da suka ɗanyi nisa kaɗan sannan Mallam ya ajjiye buhun kuɗin yana kallon Abduh kafin ya fashe da kuka, Abduh yana kiransa da magiyar ya dawo ya bashi kuɗi amma Mallam bai juyo ba sai hannu daya ɗagamai. Da gudu Mallam ya ƙaraso Asibitin sai dai yana buɗe ofishin likita ya samu ƴan shaye-shayen wasu Yankin su uku maza a zaune wai suna neman likita, yana zuwa Mallam ya ce musu ya nufi hanyar fita domin zuwa Gida. yana fitowa yayi cikiɓus da su Ɗayyib. Zage-zage da neman da suke yiwa su Abduh yasa ƴan shaye-shaye neman maɓoya gudun karsu kashe su, sai dai tura Mallam ciki tare da sanyawa Asibitin wuta ne yayi ajalinsu dukka. Wannan dalilin yasa aka samu gawar mutum huɗu. Nannaɗewar Ɗayyib cikin abun rufa na da alaƙa ne da ƙarfen da Sulaim ya cakamai gudun Iyalinsa da mutanen gari su sani, dama kuma ya ƙirƙirarwa kansa ciwo ne, don kawar da hankalin Mutanen Yankin daga kansa, Surutai da Kukan da yake yi duk don ya kawar da zargin mutanene a kansa tunda kowa yasan shi ɗin Aminin Abduh ne. Tun lokacin da Dattijo Junaid ya ɓullo da zance bincike aka waɗanda suka sakawa Asibitin Mallam wuta, Bashar ƙani ga Jalal uwa ɗaya uba ɗaya ya fara shirin kawo ƙarshen Dattijo Junaid. Sai dai sun tsayar da shawarar kashesa ba mafita bane, Bashar da kansa ya kawo shawarar a cirewa Dattijo Junaid harshe, kuma ya jagoranci Ƙattin matasan da suke yi musu aiki har gidan Dattijo Junaid. Bayan matasan sun banƙare Dattijo Junaid, Bashar da hannunsa ya yankemai harshe. Tare da gagargaɗin idan ya bari kowa ya sani ko ya ƙara tsoma baki akan mutuwar su Abduh kansa zasu cire. Abduh ya ci baƙar Azaba shi da Sulaim. A jeji suka kwana, sai da gari yayi haske suka samu amalanken daya fitarsu da su Iyakar Yankin tudu. Ba su yi minti biyu da zuwa ba Abduh ya naimi mai maganin gargajiya domin duba ciwukan Sulaim, saboda duk azabar dayake ji baya magana sai rawa da jikinsa yake yi. Duk irin jan da Abduh yake yiwa ƙaton buhun hannusa babu wanda ya kawo zunzurutun kuɗi ne a ciki. A lokacin babu masu musayar kuɗi a Iyakar Yankunan balle ya canza su zuwa na Ƙasar Abyad, kuma tsoron kai kuɗin Ɗan ƙaramin Bankin da ke gurin yake yi kar wani ya cucesa. Cikin ƙasa da hour biyu Sulaim ya samu Barci a rumfar mai maganin da suka raɓe. Shima mai magani bai san kuɗi bane a ƙaton ɓakin buhun wajen Abduh har yamma tayi suka samu Motar Kayan da zai tafi Birnin Abyad. A bayan mota Abduh da Sulaim sukayi tafiyar kwanaki. Ko da suka isa, a bayan garin Abyad suka naimi matsuguni. Washe gari da tambaya Abduh ya samu addireshin Abokin kasuwancinsa daya kira a waya. Harun ɗan asalin Abyad ne da ƴaƴansa biyu Abdallah da Bushra. Bayan sun haɗu da taimakon Harun suka kai Sulaim asibiti. Har suka gama hidimar Asibiti Abduh bai nunawa Harun tarin kuɗin da ya zo da su ba saboda tsoron kowa yake ji. A lokacin Abdallah babban ɗan Harun saurayine daya yi karatun likitanci yake kan naiman aiki Bushra kuma tana ƴar mitsisiya. Bayan kwana biyu Abduh ya kasa daina tunanin mutanen Yankinsa da su yake kwana yake tashi. Cikin girmamawa Abduh ya roƙi alfarmar Abdallah yaje Yankin Tudu ya koyamusu aikin likitanci da zasu dogara da kansu, ya yi alƙawarin biyansa duk wata. Da farko Harun bai amince ba amma dayaga Abduh ya lissafo kuɗin wata biyar ya bawa Harun ya canza zuwa na ƙasar Abyad, a take suka shirya tafiyar Abdallah. A wannan lokacin ne Abdallah ya bayyana a Yankin Tudu a matsayin jami'in jinyar da Gwamnati ta turo. Ɗayyib da kansa yayiwa Yarinya fyaɗe ya ajjiyeta a bayan ofishin Abdullah. A wacce lokacin Harun Abokanan hulɗarsa na bakin Iyakar Yankin ya tura suka ɗauko Abdullah a Yankin Tudu, domin tun a daren da abun ya faru bayan Abdallah ya dawo hayyacinsa ya kira waya ya sanar. Bayan Abdullah ya tsira daga Mutanen Yankin Tudu Daga lokacin Harun Mahaifin Abdallah ya tattara komai nasa ya bar su Abduh batare da ƙara waiwayarsu ba. Jin mutuwar Mallam a bakin Abdallah yasa jikin Abduh ƙara rikicewa kullum ba shi da aiki sai kuka.. Sulaim baya magana, komai Mahaifinsa ya yanke dai-dai ne, sai dai a gaɓar da mutanen Yankin Tudu suka ƙullawa Abdallah sharri suka kashe Mallam Sulaim ya cewa Mahaifinsa ya kamata ya manta da al'amarin mutanen Yankinsu su fuskanci rayuwar da take gabansu, domin komai yawan kuɗin da yake tunanin ya tara wata rana zai ƙare. Tunanin halin da mutanen Yankin Tudu suke ciki da wanda Mallam yake cikine ya kwantar da Abduh ciwo duk da nasihar da Sulaim ya yi masa, sannan Bautar da ya kwashi shekaru ya na yi ba tare da hutawa ba ya taka rawar ganin kwantar da shi jinya mai tsaho. A lokacin Sulaim ya fara fuskantar rayuwa, ya kuma tsaya tsayin daka domin gina Dhahab ɗin da Jamil yayi alƙawarin rusawa. Da farko buhun kuɗin Mahaifinsa ya ɗauka zuwa kasuwar canjin da suke yawan zuwa da Harun, saboda kaɗan-kaɗan Abduh yake canza kuɗin har Harun ya gujesu bai taɓa sanin akwai dukiya mai yawa a tare da Abduh ba. Wuƙa Sulaim ya soke a ƙugunsa. Su kansu masu canjin sai da suka tsorata da irin kuɗin da Sulaim ya kawo a buhu, bayan sun canza masa ya ƙara ɗuresu ya taho gida. Ashe wasu sun biyosa sun ga Gidan. A wannan dare ƴan daban da aka turo daga kasuwar canji suka farmaki Sulaim ya kawo kuɗin da ya canzo. Sulaim ya yi yanke-yanken daya ƙara gusar da imaninsa a wannan dare domin bai barsu sun tsira da ko sisi ba. Duk Abduh yana kwance jikinsa babu ƙarfi sai kuka da yake yi. Sulaim sai da ya share sama da sati baya barcin dare na ranar ma na lokaci ƙalilan yakeyi, suma ɓarayin haka suka share kwana uku suna zuwa su yayyaki juna da Sulaim, ƙarshe su gudu babu ko sisi. A fuska Sulaim sai ya koma kamar Ɗan daba saboda ƙaton Yankar da ke tsakanin kuncinshi da idonsa. Mai mota ya nemo suka tattara kayansu zuwa cikin Birnin Abyad, a ranar Sulaim ya binciki ofishin dillacin gidaje suka kama gida mai sashe-shashe. Washe gari da tambaya Sulaim ya samu Banki bayansa ɗauke da Abduh a goye. Bayan ya buɗe komai ya wuce da Babansa Asibiti. A Asibiti Sulaim yake kwana, har Abduh ya yi sati biyu suka tattaro suka dawo gida ba don ƙarfin jikin Abduh ya dawo gaba ɗaya ba, sai lallaɓawa da yake yi. A ranar da Sulaim ya ƙarasa kai dukka kuɗaɗensu Banki tunda kaɗan-kaɗan yake kaiwa, a ranar ya yi fafutar neman maƙera a Birnin Abyad. Ƙaramin ma'aikatar ƙera Tukwane na Salman Ɗan asalin ƙasar Abyad mai ƴaƴa ƴan biyu Maza Zubair da Uzair Sulaim ya samu. Sai dai bai ɗaukesa aiki ba ya ce yaje ya dawo. ★washe gari da Sulaim ya koma, Salman ƙin kulasa ya yi acewarsa Sulaim kama yake yi mai da Ɗan daba kar ya zo ya kasheshi ya kashe mai ƴaƴan da yake ji dasu....✍🏻 [8/8, 8:36 AM] nafisaaliyusasaal: SASAAL 4 Haka Sulaim ya haƙura ya dawo Gida. Bai haƙura ba, kullum ya na gama hidimar Mahaifinsa sai yaje gaban ma'aikar maƙeri Salman ya zauna. Tun maƙeri Salman bai amince da Sulaim ba har ya haƙura ya bashi dama. A ranar da Sulaim ya fara yi musu Tukwane Salman ruɗe ya yi yana tambayarsa daga ina yake, Sulaim bai iya surutu ba don haka amsoshinsa sam basu gamsar da Salman ba, wannan dalilin yasa yace yana son ganin Mahaifinsa da ya ce suna tare. Sulaim bai musa ba, ya kaishi har Gidansu. Cikin bayanin da Salman zai gamsu Abduh da damuwa da ciwo suka ramar da shi yake bashi labari. Sosai Salman ya tausayamusu ya kuma ɗauki nauyin abincin cin su kullum, domin Abduh bai sanar da shi akwai tarin dukiya a tare da su ba. A zaman wata ukun da Sulaim ya yi da Salman da ƴaƴansa Zubair da Uzair ya gane mutane ne masu amana da dattako, don haka Sulaim ya samu lokaci ya tattauna da Mahaifinsa Abduh kan jan Salman a jiki su ƙirƙiri Ma'aikata mai girma da dukiyarsu da ke ajjiye. Kai kawai Abduh ya ɗagawa Sulaim alamun ya amince, Sulaim yakai minti biyar yana kallon Mahaifinsa shima yana kallonshi, kowannen su yana kallon iri lalacewar da Ɗan uwansa ya yi, ba su da kowa ba su da kwanciyar hankali, Harun da suka sani ya gujesu. Kukan da ba kasafai Sulaim ya cika yi ba, ya saki yana rungume Mahaifinsa. Shima Abduh kuka yake yi yana cewa ; "Allah Ya zama gatanka Sulaim yasa maka albarka a duk abinda ka sawa hannu, duk tsananin karka manta da mutanen Yankina idan ka samu sukunin rayuwa ka naimi Kakarka da Mahaifiyarka ka faɗa musu irin ƙewarsun da na yi, idan Allah Ya ƙaddara haɗuwarku da Mairam ka roƙamin yafiyarta. Iyalan Mallam suma ka nemesu ka ji halin da suke ci. Gwargwadon samunka gwargwadon kyautarka Sulaim karka gajiya, Allah yana tare da Kai, ko bayan raina inaso ka kafa Dhahab ka raya mutanen Yankina a cikinta, kayi aure ka hayayyafa, sannan ka faɗa musu har bayan barowata Yankinmu ban daina son su da begen su ba, na roƙeƙa Sulaim, idan da hali ka tura Yankin Tudu wani ya koyamusu ƙera Tukwanen da zasu dogara da kansu kayimin alƙawari!" Sulaim wani irin juyi yayi da Kansa yana zaro Mahaifinsa daga jikinsa, laƙwas Abduh ya yi yana kallonsa da fararen idanuwansa da suka ƙara haske alamun alƙawarinsa ya ke jira. Cikin kuka Sulaim ya ce; "na yi alƙawari amma dan Allah karka tafi ka barni Baaba ba Ni da kowa" "Ka na da Allah Sulaim! Sannan ka tuna Naila? ƴar gidan Abokin Mahmoud?" gane wayo yake son yimai yasa ya girgiza kansa yana kamo hannunsa. A wannan rana daƙyar Sulaim ya fita aiki. Ko da ya je wajen aiki yakasa yin komai balle su tattauna da Salman kan zuba jarin da sukayi magana da Mahaifinsa. Yamma na yi ya taho gida bayan ya biya ya siyowa Babansa kayan marmari. A kwance ya samesa kamar kullum, sai dai daya mirginasa ya gane dagaske wannan Baaban daya rainesa da izinin Allah ya wahala kan bauta da ƙera Tukwane don cigaban mutanen Yankinsa ya yi barcin da ba zai ƙara farkawa ba anan gidan duniya ba. Hannunsa dayake wani irin rawa yasa ya kamo farar Fuskarsa Mahaifinsa daya koma ɗan siriri ya bushe. Rayuwarsu na Yankin Tudu ne yake dawomai da yadda Mahaifinsa yake bugun ƙarfe dare da rana, yau gashi ya mutu bai mori ko sisinsa ba, Sulaim hawayensa basu gusheba har sai suka jiƙa gaban rigarsa. Bayan mintuna Sulaim ya saɓa Abduh da jikinsa ya saki gaba ɗaya, zuwa Asibiti ko zasu ce mai dogon suma ya yi. Da gaske Abduh ya mutu ya bar Sulaim cikin maraici! Sulaim ya yi kuka irin kuka da har duniya ta tashi bayajin zai ƙarayin irinshi. Da taimakon Salman da mutanen Ma'aikatarsa aka binne Abduh. A tsakanin kwanakin da Sulaim ya rayu shi ɗaya ya fuskanci kuɗi suna gaba da komai a rayuwar wasu Mutanen, na wasu Mutanenma muninsa ya yi yawa. Kamar Salman tunda ya turo su Zubair sau ɗaya bai ƙara turosu ba balle ya zo da kansa acewarsa aiki ya yi musu yawa a Ma'aikata. Idan har kuɗine sune gishinƙin da zai cika masa burikansa mai zai hana ya neme su? Cikin tsanani da wahala Sulaim ya fara gwagwarmayar kafa kansa da zuciya da ƙwanjinsa bai bi takan komawa Makaranta ba tukunna har sai komai ya dai-daita. Garin shiga can faɗa nan Sulaim ya samu mutumin da zai taimakamai ba tare da yaƙarabin takan Salman ba. Cikin ƙanƙani lokaci tunda da kuɗi masu yawa a ƙasa Sulaim ya fara kafa Ma'aikatar Sarrafa shinkafa. A kwai mabaratan da suke yawan zuwa bakin ma'aikatar tun kafin gininsa ya yi nisa, wata rana Sulaim ya taho da Baturen da aka haɗashi da shi zai taimakamai, ya gane ashe su Malik ne. A yadda ya tsani duk wani jinin Yankin Tudu baiyi niyyar kulasu ba, sai dai tuna wasiyyar Mahaifinsa yasa ya isa garesu. Da farko sun tsorota tare mamakin dama basu mutu ba suna raye? Mahaifin Malik da suke Bara tare yayi kuka da yaji labarin mutuwar Abduh, shima Sulaim ya tausayamusu jin tsahon lokacin da suka ɗauka a Birnin Abyad suna Bara tare da kwana dukkansu a ɗaki ɗaya. Daga wannan rana su Malik suka samu muhalli mai kyau. Malik da Iyayensa sun san halin Sulaim tuntuni balle yanzu da yake jinsa shi kaɗai a duniyarsa, dalilin wannan yasa suka zaunar da jununsu suka yiwa kansu nasihar riƙon amana da riƙo da gaskiya komai ɗacinta. Labarin kafuwar Ma'aikatar Sulaim ne yasa Salman naimansa da kansa, ya kuma baiwa Sulaim haƙuri. Sulaim bai manta halaccin Salman ba kuma ya yi masa uzuri tunda da ma'aikatar suke ci suke sha, sakaci dashi kan damuwarsa shi kaɗai zai iya rusa masu kasuwancinsu. A cikin wannan tsukin Harun ya ƙara dawowa, daƙyar Sulaim ya sauraresa suka dai-daita shima da yaji mutuwar Abduh har da kwanciya a gadon Asibiti. Har Yankin Tudu Sulaim ya tura Malik ya sirrince, ya kwaso rahoton halin da Yankin yake ciki. Malik ya dawowa da Sulaim mummunar labarin irin talaucin da mutanen Yankin suke ciki. Kamar yadda Mahaifinsa ya roƙesa kafin ya bar duniya Sulaim ya samu Salman da batun tura wani Yankin Tudu ya koyawa Mutanen Yankin ƙera Tukwanen da zasu dogara da kansu. Cikin kasada Salman ya amince Ɗansa Zubair ya je ya koyamusu ƙera Tukwanen da Abduh yake yi kamar yadda Sulaim ya koya musu tuntuni. Sai dai Uzair ne zai fara zuwa tunda yafi Zubair iya tsara kalami, idan yaso idan suka bashi masauƙi sai ya dawo Zubair ya zauna. Zubair shine ya rayu a Yankin Tudu da sunan Mahaifinsa Salman, yawancin maganganun Abduh da yake yi Malik ne yake faɗamai ta ɓoyayyiyar wayar da ya tafi da ita. Bashar da muƙarabansa har da Jalal su sukayi ta'asar kashe Zubair da Dattijo Junaid, wuƙa suka ɗan sokawa Ɗayyib gudun tonuwar asirinsu. A daren da abun ya faru labari yajewa Malik ta hanyar waɗanda ya saka gadin lafiyar Zubair. Dama kuma a daren suka iso iyakar Yankin domin tafiya da Zubair, kafin labari ya isa kunnen Sulaim da baya ƙasar Abyad Malik ya yanke nasa hukuncin akan Bashar . Lokacin da gawar Zubair ya isa ga ɗan uwansa Uzair da mahaifinsu Salman sunyi kuka, tare da tsanar Yankin Tudu da mutanen cikinta. ƊAYYIB Baƙin cikin bayyanar hannun Bashar a cikin kisansu Abduh maimakon ya nuna bai san wanda ya yanke masa harshe ba ne ya tunzura zuciyar Ɗayyib, har ya shaƙawa Bashar gubar daya tanada tuntuni a aljihunsa lokacin da suke yunƙurin kaishi Asibiti. Dama ya tana de shi ne idan har ya tabbata da gaske bayanin ɗaya daga cikin iyalin Abduh Bashar yake kwatantawa, Gara ya mutu daya tona musu asiri. Mairam Matar Abduh Dhahab a ranar data fara magana ɗan leƙen asirinsu ya kai musu labari, a daren ranar ya tura ƴan daba su kashe Mariam, fitowar Mahaifiyar Naila kama ruwa ne yasa suka ɗauka Mairam ce, don haka suka farar sararta ta ko ina har sai da ya daina numfashi, Iyayen Mairam da sukayi laƙwas a ɗakunansu, ƴan daban suna tafiya suka fito suka tattara kayansu suka bar Yankin. Ɗayyib Babu irin bincike da naiman da baiyiwa Sarah Matar Mallam ba, amma babu wanda yasan duniyar da suke. Menene burinsu Ɗayyib? Su kashe sunan Dhahab su kuma samu ɗaukaka da dukiya ko da jinin dukka mutanen Yankin zai salwanta, su dasa tsoro a ran Mutane yanda zasuci karansa babu babbaka ba tare da wani ya tanka musu ba. SULAIM Kisan Zubair yasa ya dakatar da Malik daga sanar da shi duk wani abu daya shafi Yankin Tudu da kowa na cikinta, duk wanda yaga ya cancanta ya taimakamai albarkacin Mahaifinsa ba sai ya sanar da shi. Wannan dalilin yasa Malik kasa taimakon Naila saboda yasan ita ba taimako take buƙata ba, burinta tasan Sulaim ya mutu ko yana raye. Sulaim ya zama hamshaƙin Attajirin gaske a ƙasar Abyad da ya sakaye Sunansa da Muhammad Dhahab kowa da haka ya sansa, ya kafa Unguwa guda da Rukunin Gidaje masu yawa mai suna Dhahab a Babban Birnin Abyad da kuɗi masu nauyi. Malik da ahalinsa, Salman da Iyalinsa, sai su Kabeer, har da Mariam da Iyayenta da Malik ya binciko su ma suna aikatau a Birnin Abyad, sai wasu mutanen Yankin Tudu da cirani ya kawo kusa da Birnin Abyad sukayi katari da Malik. Su suka taru suka raya Dhahab suke rayuwa a ciki. Matar Mallam babu inda Malik bai bincikaba amma ya kasa samunta. Malik bai gajiya ba sai da ya binciko Mahaifiyar Sulaim da Kakarsa bayan ya kashe dukiya masu nauyi. Wannan ya ƙarawa Malik daraja a idon Sulaim. Ranar da Malik ya kawo Aysha mahaifiyar Sulaim da Kakarsa Nanaah da kuma Farheen ƴar ƙanwar Aysha Dhahab Sulaim ya zo daga inda yake rayuwa domin ganinsu, wannan zuwa nasa sai yasa kishi ya lulluɓe zuciyar Mairam duk da Abduh baya raye, a ganinta kamata ya yi Sulaim yafi ƙaunarta akan Mahaifiyar data haifesa, tunda ta gudu ta barshi. Da Sulaim ya tashi tafiya ƙasar da yake rayuwa da Kakarsa Naanah da yaji ya fi so a ransa ya tafi, saboda ciwon zuciya da take fama da shi, Mahaifiyarsa kuma aka ware mata Sashe na alfarma tayi rayuwa ita da ƴar ƙanwarta Farheen A ina Sulaim yake rayuwa?? Kahala Birni mai daraja a Honolulun Hawaii, banbancin daɗin rayuwarsa da Babban Birnin Abyad, kamar babbancin Babban Birnin Abyad ne da Yankin Tudu. Rashin son ya raɓi kowa yasa yaje can ya kafa Kasuwanci siyar da zinare da kayan sawa da kayan ƙyala-ƙyalai, cikin ikon Allah ya samu karɓuwar da ya ƙara mayar da shi Attajiri a can. Duk wani hukunci da Malik ya yake yakewa, akanki kansa yake yi kamar yadda Sulaim ya sakarmai ragamar komai. Amma duk da haka rashin yarda da baiyi da kowa ba, yasa ya ajjiye Ma'aikata na musamman masu lura da motsin Malik a sirrince a harkokin da suka shafi Dhahab ba tare da shi kansa Malik ɗin ya sani ba. SULAIM Ya manta da Naila da dukka wani abu daya shafeta a zahirinsa ya kuma toshe duk wata hanya da wani zai sakomai zancen aure. Batun wanzuwar Sufyan a ɗaya daga cikin ma'aikatansa da Kabeer, bai sani ba, shi ko Kabeer ɗin da ya fi Sufyan matsayi bai san dashi ba, Uzair da Malik kawai ya sani. A can Dhahab Mutanen da suke rayuwa a cikinsa suna rayuwa a matsayin sun san Sulaim yana raye bawai don suna ganinsa da idanunsu ba ko mu'amalantarsa. Tsantsenin Cikin Dhahab da kula da motsin komai duk Sulaim ne ya tsarashi Malik yake kula da komai da taimakon ragowar Ma'aikata, domin da mutum ya yi cin amana a Dhahab gara ya barta gaba ɗaya. Maiyasa Mairam bata taimaki Naila da kakarta ba duk da tasan inda samesu? Kishi da burin son Sulaim ya dawo gareta yasa take ƙoƙarin duk ranar da Allah ya ƙaddara dawowar Dhahab tun bayan tafiyar da Kakarsa ta gabatar mishi da Barirah domin har biyayyar dole takeyiwa Aysha Mahaifiyar Sulaim, duk don su yi masa taron dangi ya auri Barirah. A ganinta idan Sulaim ya auri wata mantawa zaiyi da ita gaba ɗaya ƙarshe ta koma Yankinnsu da suka gudo, jawo Naila a jikinta gani takeyi shima matsalane kar Sulaim ya ganta ya tuna da shaƙuwa daya wanzu a tsakaninsu shekarun baya har ya nuna yana sonta, daganan ya aureta itama tasa ya koreta saboda kashe Mahaifiyarta da akayi ta dalilinta, gara Barirah da bawani sonta tasan zaiyi ba. Wannan dalilin yasa Barirah take yiwa Ummi Mairam kamar yadda suke kiranta biyayya sama da Mahaifiyar Malik da yake ruƙonta. Malik yasha jawa Baririh kunnen karta ɓata shekarunta wajen jira Mutumin da bai san da ita ba. Amma kallon mahassadi takemai. ..✍🏻 SASAAL 5 *Wani irin rayuwa Sulaim yake yi Kahala?* Rayuwa sakewa da morewa arziƙinsa, kyansa da Mutanen Yankin Tudu suka kasa mantawa dashi yaƙara fitowa, ginannan jikinsa dake samun hutu, cima mai kyau, da motsa jikin da ya dace, yaƙara zama abin so ga duk wata Ƴa Mace musamman Mace mai son Naira da Namijin liƙawa a goshi. Rashin yawan son maganarsa bata sauya ba sai abinda ya yi gaba. A cikin zuciyarsa kuwa babu ƙiyayya, babu ramuwa, sai dai ya goge kafanin Mutanen Yankin Tudu daga cikin rayuwarsa. Babu yadda rayuwa Namiji kamar Sulaim zai gudana ace babu Mace a ciki, wannan daliline ya shigo da Noorhan ƴar asalin ƙasar Lebanon cikin rayuwarsa. Noorhan; Kyakkyawar gaske, ƴar Attajirai gaba da baya kuma ƴar gatar da ta yiwa addininta na Musulunci riƙon ganin dama, su ma Mazauna Kahala ne da Mahaifanta. Bata da burin lallai SM Dhahab ya aureta kamar yadda take kiransa da wasu Abokanan Kasuwancinsa. Burinta soyayyarsu ta faɗaɗa ya wuce sumbata da sauransu, ya mayar da ita kamar Iyalinsa idan da hali harta haifa mai ƴaƴan da zai ƙulla alaƙa mai ƙarfin tsakaninsu har ya kaiga Aurenta ko baya so. Kallonsa, salon tafiyarsa, iya riƙe matsayinsa da izzarsa, da rashin son hayaniyarsa wani irin birgeta suke yi, uwa uba Nairan daya tara babu magaji. Wasu lokutan tana kuka da magiyan ita ta sallama masa kanta amma sai ya yi biris da ita, idan ta matsa sai ya tuna mata abinda take so ya wuce ƙa'idarsa da ita. Tasha sanya masa abu a lemo ya zubar, abinda bata sani ba, yarda da Mutum wani tsohon abune da Sulaim ya jima da daina yayinsa, idan har kaga ka cucesa akan kuɗi ko wani abun kasha to tabbas Allah ne ya ƙaddara hakan amma ba dai dabarar mutum ba. Da ya ga taƙi dainawa fuska da fuska ya gargaɗeta idan ta ƙara ba iya rabuwa da ita kaɗai zai yi ba har ƙararta zai kai. Babu wanda ya yiwa Sulaim cushen Noorhan da kanshi ya ganta ya tura aka haɗasu, domin ragewa kansa kaɗaici. Kakarsa Nanaah da ya ɗauko rayuwarta kusan rabi a Asibiti yake gudana domin bini-bini jikinta ya tashi. Malik ne kaɗai yake yawan kawo masa ziyara idan buƙatar aikinsa ya taso. Tsakaninsa da Malik akwai girmamawa mai faɗin gaske, kasantuwarsa Ubangidan Malik kuma mai ɗauke kai da bashi damar yin duk abinda ya ga dama da dukiyarsa. A ɓagaren hira, hirar aiki ne kawai yake haɗa su banda na mutanen Yankin Tudu, kuma shima sunfi yi a rubuce saboda rubutu yafi yiwa Sulaim sauƙi akan doguwar magana, yakan jima ya na yin hira da Malik a rubuce amma idan da baki ne hirarsu taƙaitaccen ne. Wannan shine Matashin da Malik ya je wajensa da abubuwan da suka faru tun shekaru baya a Yankin Tudu. *DAWOWAR LABARI* Murmushi Malik ya saki yana ƙara gyara zamansa don jiran abinda zai ƙara cewa. "Na turo maka saƙo, idan aikin komai ya kammala sai ka wuce" Sulaim ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa. Sai dai har ya miƙe ya fara yunƙurin tafiya Malik yana zaune bai motsa ba. A wajensu dukka sabon abune rashin miƙewar Malik ɗin, don haka Sulaim ya fahimci Malik yana da saƙon dayake buƙatar attention ɗinsa. Dawowa ya yi ya zauna idanunsa ƙyam a kan fuskar Malik dake sunkuye kafin ya ce "menene matsalan Malik?" Sai da Malik ya saita kansa sannan ya ce "ka gafarci furucina da kuma labarin da nake tafe da shi" kai Sulaim ya ɗaga alamun ya basa dama. A ɗan rarrabe Malik cikin kame-kame tsoron abinda zai biyo baya ya ce; "Nailar Yankin Tudu, ƴar Mahmoud maɗinki..." Ido Sulaim ya lumshe har baya ganin fuskarka Malik dakyau, a hankali yayi baya ya jingina da Couch ɗin dayake kai. Hakan da yayi ne ya bawa Malik damar cigaba da maganarsa Kamar mai karanta labarai a gidan radiyo ko talabijin haka Malik yake koromai labarin komai dalla-dalla tunda ya basa dama, har zaman Sufyan da abinda ya aikatawa Naila da cin zalin da yayi mata, da ciwon da tayi kamar yadda ya kwantarwa da Bushra hankali ta bashi labarin komai ta waya kafin zuwansa Kahala, da zuwansu Babban Birnin Abyad a yanzu a matsayin makitsiya, kuma Mahaifiyarsa ta hanasa taimakonta saboda abinda Mairam ta tsiro da shi. Malik bai rage komai ba, tunda ɗorewar zaman amanarsu shine rashin ɓoye-ɓoye. Domin ko Noorhan Malik ne kaɗai yasan da ita a matsayin Budurwar Sulaim shiyasa yake jawa Barirah kunne. Idanuwansa da ya zuƙe ya ɗan buɗe kaɗan yana gyara zamansa, kamar daga sama Malik yaji sassanyar muryarsa; "Inji Ni ka sanar da Naila da Kaka! A Sauya mata Jami'a a Babban Birnin Abyad,a basu mazauni na musamman a Dhahab ta kuma daina kitso har abada. shi kuma Sufyan ku barshi ya ci abinci shi da Iyayensa daga dukiyar da Allah Ya bamu." ya na gama faɗa ya ɗan sosa ƙarshen dogon hancinsa yana miƙewa. Har lokacin idanunsa da suke bayyana jin daɗinsa ga abu ko akasinsa a lumshe suke ba a ganinsu da kyau, balle Malik ya tantace yadda ya ɗauki zance. "Ka sauka lafiya Malik ina gaida kowa" ya ƙara faɗa yana barin living room ɗin daya lashe manyan kuɗaɗe. LV Maimi Mule ɗin daya haska kyakkyawar ƙafarsa Malik ya bi da kallo kafin shima ya miƙe a hanzarce yana ɓoye ainihin yanayin dayake ciki. Malik ya na fitowa harabar Gidan ya samu waje ya zauna yasha murmushin da ya kasayi a ciki, yana godewa Allah domin matsalar Naila ce Matsala ta Farko tun bayan barowarsa Yankin Tudu da ƙiri-ƙiri yasan arziƙine maganinsa amma ya kasa maganceshi, saboda wanzuwar Naila a Dhahab kamar dawo da Tarihin Yanki Tudu ne a rayuwar Sulaim, shiyasa bai isa ya yisa kai tsaye ba shi kaɗai. Yasan da wahala Namijin da ya taka Matsayin Sulaim ya so Mace irin Naila, da wannan saƙe-saƙen ya duba saƙon Sulaim kafin ya wuce addireshin wajen taron daya turamai. Sai yamma liƙis su Malik suka gama taro ya nufi masauƙi, ko Rigarsa bai gama cirewa ba saƙo ya shigo ta E-mail ɗinsa. Bai kawo saƙo mai muhimmanci ba ne, don haka ya shiga wanka ya gabatar da Sallah. Bayan ya ci abinci yakira Ummeensa yana bata labarin abinda ya faru, hamdala tayi kafin suyi sallama, Bushra ya yi niyyar kira amma yafasa ya janyo ɗaya wayarsa don turawa Sulaim saƙon yadda komai ya wakana ga mamakinsa ashe saƙon Sulaim ne ya shigomai tuntuni. Sunan Jami'a ya turomai da taswirar Dhahab sannan ya yi pointing ɗin wani guri, ko Malik bai tambaya ba yasan yana nufin anan yake so a ajiye su Naila, sai guntun rubutun nemarwa dukka ahalinta da suka nuna suna ra'ayin aiki a Dhahab, a bashi aiki da matsuguni na musamman a estate ɗin Companynsu( inda Sufyan yake). Sai da Malik ya gama ƙyaƙyata dariyar muguntarsa daya haɗe da zallar nishaɗi sannan ya binciko sunan jami'ar da Sulaim ya turomai. Iya adadin kuɗin Makarantarne yasa Malik ƙara sakin dariya, kafin ya ƙara zuƙo Taswirar Dhahab daya turamai dakyau, inda Sulaim ya yi pointing gine ne dake tsakanin inda Mahaifiyarsa da Danginta da suka ƙara biyota daga baya suke rayuwa, ginin babu kowa a ciki domin an tanadeshi da can saboda Sulaim ɗin kansa amma ya nuna baya so, kuma ɓangaren shine ɓangare mafi samun tsaro dakyau a Dhahab. "kenan anan Naila da Kakarta zasu zauna?" Malik ya tambayi kansa wani dariya ya ƙara kwashewa da shi har da kwanciya. Rasa wanda zai kira da yasan Naila suyi sharing ɗin daɗin dayake ji yasa ya kira Bushra. Bayan sun Gaisa ya gama bata labari ihun Bushra ihu murna tasa tana tsalle tare da alƙawarin baro ƙasar da take domin taya Naila murna. "amma kana ganin Mahaifiyarsa(Aysha) zata amince baza'a samu matsala da ita ba, tunda ba wai auren Nailan ya ce zai yi ba" Bushra ta faɗa murnarta na komawa ciki. Dariya da kai tsaye za'a kirasa na isa Malik ya saki ya ce "Bushra! baki ji na ce miki ya ce "Inji shi" ai ya gama magana kenan, Mahaifiyarsa Macece mai sanyi, kuma barinsa da tayi tsayin shekaru yasa take lallaɓashi babu shaƙuwa a tsakaninsu. Baya magana mutum ya sauyamai sai dai Allahn da Ya haliccesa! Don haka ina jiran zuwanki" Dariya Bushra ta saki tana jero Sulaim kiraraki, da shaƙiyancinsu suka ƙare wayar. Ajiyar zuciya Malik ya sauke Noorhan da yake ganinta a matsayin katanga mai tsaho a tsakanin Sulaim da Naila na faɗomai domin bayasa Barirah a lissafinsa.... Washe gari da Asuba ya ɗauko hanyar Ƙasar Abyad, bayan ya ajjiyewa Sulaim saƙo don bai koma gidan ba... [9/5, 8:36 PM] Maman Amatullahi: SASAAL 6 SUFYAN; Bai yi nadamar furucinsa ga Sumaya ba, saboda yana ganin abinda ya dace da ita kenan, burinsa kawai ya gansa a Babban Birnin Abyad a ofishin aikinsa ba su sallamesa ba. Masauƙin da suka sauka shida Sumaya ya je, ya kwashe kayan amfaninsa ya nufi Airport. Gabansa ya na faɗuwa ya nufi estate ɗin Companynsu. Ajiyar zuciya ya sauke lokacin daya da zura ɗan mukullin ɓangarensa yaji ya buɗu. A gaggawace ya shirya cikin baƙin kayan da suka yi mai kyau, sannan ya lalubo wayarsa hannunsa da zuciyarsa suna rawar amsar da Driver zai ba shi ya danna masa kira ya ce ya zo ya kaishi Office. Da girmamawa ba tare da ɓata lokaci ba Driver ya ce gashinan zuwa. Sufyan bai san sanda ya zamo ƙasa ya yiwa Allah sujjud ba, domin ya yi imanin a yanzu shine Kaɗai gatansa. Babu abinda ya sauya a ofishinsa sai ƙamshi ma da yake yi a gyare tsaf. Rintse ido Sufyan yayi yana yiwa kansa alƙawarin riƙo da gaskiya tare da aiki da amana. Bayan ya dawo gida Da dare ya raba kasa barci ya yi ƙewar Naila da yadda yake bautar da ita ya juyata yadda yaga dama na addabar zuciyarsa, babu ƙewar Sumaya ko wani abu daya dangaceta a cikin ransa, saboda don ita da Mahaifinsa ya kashe wayarsa Karma su kira su samesa. Sallar daren da Sufyan bai taɓayi ba a rayuwarsa ya ɗauko prayer mat bayan yayi alola ya tayar, zuciyarsa cike da yaƙinin samun mafita a wajen Ubangijinsa. ★washe gari da ya fita ofishi yaƙara ganin abubuwan da suka ƙara kwantar dashi, saboda zazzaɓi mai zafin da ya rufe sa. Ya ga Kabeer ido da ido a matsayin Uban gidansa, sannan ya ga Dr. Abdallah da ya taɓa zuwa Yankin Tudu shekarun baya. Menene yake faruwa? Daga ina suke ɓullowa, ko dai kasheshi suke son yi? Tambayoyin da yake ta yiwa kansa kenan Har gari yayi haske Sufyan bai runtsa ba. A daddafe ya nufi office kansa kamar zai faɗo, Misalin ƙarfe tara na safiya ya shiga ɗakin taron da zasuyi, fuskokin wasu daga cikin mutanen Yankin Tudu ya fara gani ciki har da Sartaj da'aka nema aka rasa. Bibbiyu ya fara gani kafin ya ƙwala ƙarar da ya janyo hankalin mutane kansa. Rai a hannun Allah aka wuce da shi Asibiti a karo na uku. NAILA; Ita da Kaka kwanan fargaba sukayi, har ɗaki Ameera ta biyo Naila tana bata haƙurin irin tambayoyin da Barirah ta titsiyemsu da shi. Ɓarawon barci ne yayi nasarar ɗaukesu bayan sallar Asubahi. Da gari ya yi haske bayan sun karya Ameera aka turo ta kirasu, wai Barirah tace su taho har da Kaka, ɗan yamutsa fuska Naila ta yi ta ce; "ba ta da hurumin da zata ce don zan yimata kitso sai na tafi da Kakata, idan bata son zuwana ni kaɗai ku biyani haƙƙina mu koma inda muka fito" Dan jim Ameera tayi kafin ta ce; "okay ba damuwa muje" Naila ta na kallon Kaka ta na yunƙurin kamo hannunta tayi kamar banganta ba, ta bi bayan Ameera. Da suka fito Parlon Mama Yayar Mahaifin Ameera da zata raka Naila da mamaki take tambayar ya ya basu fito tare da Kaka ba? Abinda Naila ta gayawa Ameera na maimaita mata. Itama ɗan jim tayi kafin tayi gaba Naila binta a baya. Ɓangaren Mahaifan Malik suka fara zuwa jami'an wajen suka sanar da su saƙon Barirah, wai ta ce su biyota ɓangaren Ummi Mairam. Cikin biyayya Maman da ta raka Naila ta sunkuyar da kanta haɗe da ƙarayin gaba. Zuciyar Naila kamar ana hura wuta saboda takaici. Babu hassada living room ɗin su Ummi Mairam abin a yabane ta kuma jinjinawa ƙwararren da ya tsarashi. Mairam Matar da Mahaifiyar Naila ta fuskanci mutuwar azaba ta sanadin kula da ita, idanuwan Naila suka ganemata, Tayi kyau irin kyan dake bayyana hutu da sukunin rayuwar da take ciki. Kamar bata taɓa ganin Naila ba haka ta ɗauke kai tana shan ruwan tataccen kayan marmarin da yake hannunta. Barirah tana zaune a gefenta tana latsa waya. Naila tsayawa a matsayinta abune da ta jima da sanyawa zuciyarta shi, don haka ta naimi ƙasa na zauna, kamar bata sansu ba dukkan su. "Ina Kakarki, maiyasa baku zo tare ba?" Barirah ta tambaya cikin isa. A take Naila ta bata amsa! "Banzo da ita ba, saboda ba ta iya tafiya mai nisa, kuma ai bata iya kitso ba, Ni kaɗaice na iya." wayar hannunta Barirah ta ajiye a gefe tana ƙanƙace idanunta, sannan ta ƙara cewa; "Ke har kina da Audacityn bani irin wannan amsar, lafiyar ƙwaƙwarki kuwa?" Cikin kameme Mama tace; "Ayi haƙuri kinsan halin Yara, Kakarta ta ce batajin daɗi" "Ko bata jin daɗi a ɗaukominta ita haka, tambaya nakeson zanyi musu tare" Barirah ta ƙara faɗa a gadarance tana juya wayar hannunta. Zuciyar kamar ana hura wuta a maƙera, baƙin ciki tuni ya lulluɓe ganinta, kamar zata amayar da wuta ta ce; "Ƙarya kike Barirah! Bakiyi wannan arziƙin ba, wacece ke? Ko da bansan ƙaddarar arziƙi ba babu yadda za'ayi mai sana'ar maganin gargajiya ya mallaki Dhahab, dole arziƙin wani kuke ci." Naila tƙarasa faɗa tana huci. Mari Barirah ta taso zata tsinkawa Naila. Naila ta kama hannunta na gantsara mata cizon da iya kaifin haƙwarana daya da Barirah kwarara ihu. Cikin zare ido Mairam ta saki kofin hannunta ta ce; "Ke fita ki kiramin Securities su fitarmin da wannan abun" Mairam ta ƙarasa faɗa tana pointing Naila. Ƙasa Mama ta durƙushe tana bata haƙuri Cikin zafin murya da zafafan kalaman da suke fitowa tun daga ƙasar zuciyar ta ce; "Ba iya kamani zakisa ayi ba kisa akasheni kamar yadda kikayi sanadiyar mutuwar Ummeena kika gudu kika samu daula kika manta dani, idan kuwa baki yi haka ba to tabbas! baki cika butulu ba Mairam dake da ahalinki! Wallahi da na cigaba da ganin fuskarki Gara kisa ayimin kisa mafi ƙanƙanci akan na Mahaifiyata," Naila ta ƙarasa faɗa kamar zata daketa. Mairam batayi gigin kawo farin sol ɗin hannunta ba gudun abinda Nailar tayiwa Barirah. Sak Mairam tayi tana kallon Naila, kafin rufuwar Seconni saiga Mahaifanta da kuɗi yaƙara gyarasu sun bayyana. Kamannin Mahaifiyar Naila a bayyane yake akan fuskarta da gangar jikinta don kallo ɗaya sukayimat suka shaida ta amma saboda su tabbatar sai Mahaifinta ya ce; "yarinya daga ina kike?" Babu shakka balle kwana-kwana Naila tace ; "Yankin Tudu Daular Sarki Hammam, Naila ƴar gidan Mahmoud Maɗinki wacce ta rasa Mahaifiyarta dalilin baiwa Mairam Matar Abduh Dhahab kariya." Ido Mahaifin Mairam ya rutse son zuciya na bijiromasa da kuma burin da suka san ya jima a zuciyar ƴarsu ya ce; "Yarinya bamu sanki ba, Barirah maza kira jami'ai" Kallon tsohon Naila takeyi bata ce komai ba. Mahaifiyar Mairam ba tayi magana ba, sai kuka da takeyi alamun lamarin baiyi mata daɗi ba. Za'a iya kiran musayar yawunsu da Naila na farko daya taɓa faruwa tsakaninsu da masu yi musu Hidima tun bayan kafuwar Dhahab. Don haka kafin kace kwabo ƙofar sashen su Ummi Mairam ya cika da asalin mutanen Dhahab. Ita dai Mama da ta rako Naila kuka takeyi tana magiyar suyi haƙuri. Mahaifiyar Sulaim ce ta fito cikin shigar dake nuna matsayinta, kafin a tafi Naila kamar yadda Barirah ta basu umarni ta buƙaci jin abinda ya faru ta bakin Mama dake kuka a durƙushe tana magiya. "Daga ina yarinyar take" Ummi Aysha ta tambayi Mama. Da rawar murya Mama ta ce; "Allah Ya taimake ki daga Birnin Abyad take ƴar ƙanina ce ta gayyatota kitso kuma da izinin Sir Malik, amma yanzu naji tana cewa daga Yankin Tudu take" Mama ta ƙarasa faɗa cikin kuka. Ummi Aysha idanuwata da suke iri ɗaya da na ɗanta Sulaim ta lumshe soyayyar Abduh Dhahab daya kasa barin ranta na bijiromata. Kai tsaye ta ce akiramata Malik kafin a tafi da Naila domin bata yarda da garaje ba a rayuwarta, domin garaje ne yasa ta tafi tabar Abduh a ranar da nasararsu ta tabbata. Kafin su samu layin Malik, Armored Toyota LC300 Baƙi mai shaiƙi ya karyo kwanar Ɓangaren. Basa dariya sai sunga mugunta wannan inkiyar Malik ne da Ubangidansa. Don haka fuskarsa da babu fara'a sam yake ɗaure tsam kamar ya ɗauresa da igiya. Baya yiwa kowa a cikin su aiki balle yayi musu biyayya don haka kowa ya kame kansa, Barirah kamar ta fashe don takaici. Mahaifin Mairam daya biyewa farin cikin ƴarsa, gumin daya tsatsafomasa ya sharce. Ita dama Mahaifiyarta tana ciki ko leƙowa batayi ba. Bayan ya zuro da gangar jikinsa waje, ɓakin tabaran fuskarsa ya zame. Malik yana da salon tsayuwar da yakeyi wanda dole kowa ya shiga taitayinsa. "Menene yake faruwa" Malik ya tambaya da nannauyar muryarsa. Da harshen nasara shugaban Securities daya zo wajen dai-dai zuwan Malik yake tambayar kowa na wajen da karfi. Dukkansu Barirah data kirasu suke kallo, domin babu bayanin komai tace su zo su tafi da Naila. Haɓarsa Malik ya ɗan shafa yana matsowa wajen da kyau, sai a lokacin yaga Naila dake tsugunne taci kuka jijiyoyin goshinta sun fito sunyi ruɗu-ruɗu. "Kowa ya koma bakin aikinsa" Malik ya faɗa idanuwansa akan Barirah data yi ƙasa da Kanta. A zafafe Ummi Mairam ta ce; "Babu inda zasu je, domin nice Uwar data raini wanda suke yiwa aiki don haka dole su tafi da ita, su hukuntata sannan su mayar da ita asalin Yankinta" Baki Malik ya taɓe yana yiwa Mairam kallon da bai taɓa yimata ba ya ce; "Ya ce in ji shi! ta rayu a Dhahab ita da ahalinta da duk wanda taga dama, bazaki sauyamin aiki ba, amma yanzu ki kirashi tunda ke Uwa ce idan ya canza magana sai muma canza" Hannu na rawa Mairam data kwashe imaninta ta siyarwa Shaiɗan ta dannawa layin Sulaim na musamman kira" Abune mai wahala ka kirasa ya ɗauka nan take amma tana kira ya ɗaga, cikin kukan take koramai jawabin ga wata tazo tanayimata rashin kunya ta ce akamata Malik ya ce bata isa ba. Mahaifiyar Sulaim Ummi Aysha ƙwallane ya cika idanuwanta saboda yadda Mairam take yaƙin lallai sai ta rabata da ɗan da batasha wahalar haifarsa ba, bata wankemai bayan gida ba, bata wankemai fitsari ba, kawai abincin da Mahaifinsa yake siyowa take dafawa su ci, amma dai-dai da tarbiyya Sulaim Abduh ne yayi masa da Kansa domin barcine kawai yake rabasu. Sulaim Cikin taushin murya dake bayyana izzarsa ya ce; "wacece ita? Maiyasa zatayi miki rashin ɗa'a? Kunsan juna ne?" Shiru Ummu Mairam tayi, ta kai daƙiƙu biyu kafin ta fara lalubo abin faɗa sai da ta gama kame-kamenta ta gane ya jima da katse wayar tun bayan tambayar da ya yi mata, tayi shiru. Saƙon Sulaim ne ya shigowa Chief securityn Dhahab. Umarnin kora ya rubuto ga Securities ɗin da suka amsa umarnin Barirah saboda bai san kallon wani iri matsayi sukeyi mata ba, da har zata bayarda umarni subi batare zurfafa bincike ba. Sannan kowa yabi umarnin Malik a cikin daƙiƙu, wanda yaƙi a gaggauta fitar dashi daga Dhahab gaba ɗaya kuma babu dawowa. Chief security na gama sanar da saƙon Sulaim a sarari, Malik ya goge gilashinsa da salo ya mannawa idanuwansa haɗe da bawa Securities mata Umarnin su taimakawa Naila ta miƙe. Har Malik ya juya Ummi Aysha da ta kasa jurewa tace; "Ka roƙamin alfarmarsa ya bar securityn da aikinsu" ta faɗa da tausayi a muryarta. Malik bai jirkintawa maganar Ummi Aysha ba ya turamai saƙo. Rashin bayar da amsarsa na nufin amincewarsa don haka Malik ya ce abar Securities da aikinsu, amma ayi suspending ɗinsu na watannin da suka dace domin kiyaye gaba. Babu halin musayar yawu da hukuncin Sulaim, don haka Ummi Mairam da Barirah harma da Mahaifin Mairam da kunyar Malik ya hanasa sukuni suka shige ɓangarensu. Itama Ummi Aysha ɓangarenta ta nufa fuskarta ɗauke da murmushin alfarmar da Sulaim yayimata a matsayin biyayya akaron farko. UMMI AYSHA tambayar da take yiwa kanta shine; "Wacece Naila, menene matsayinta a wajen Sulaim har da zai shiga lamarin Dhahab akanta" tattaunawar da suka wuni sunayi kenan ita da ƴan uwanta. A ɓangaren Barirah da dare ya yi tazo kwanciya maganganun Naila ta tuna; "Ƙarya kike Barirah! Bakiyi wannan arziƙin ba, wacece ke? Ko da bansan ƙaddarar arziƙi ba babu yadda za'ayi mai sana'ar maganin gargajiya ya mallaki Dhahab, dole arziƙin wani kuke ci" Waɗannan Kalamai su suka addabi zuciyar Barirah, a wannan dare bata runtsa kuka kuwa tayisa kamar zata makantar da idanuwanta. Wanda yaji daɗin cizon da aka yiwa Barirah ya dannamin like😂 In Shaa Allah gobe zai zama ranar hutu. Na gode [9/5, 8:36 PM] Maman Amatullahi: SASAAL 7 SULAIM Bayan ya gama waya da Ummi Mariam mamaki ne ya kamasa. A kaf zamansa da ita bai san wani hali taƙamaimai na ta da zai kwatanta ta da shi ba, domin rayuwarsa a gidansu na Yankin Tudu daban yake da na ta, a wasu lokutan ma sai dare suke haɗuwa ko Safiya idan zai je Makaranta, kawai dai abinda ya sani suna kwana a gida ɗaya. Abu ɗaya zai iya faɗa akanta shine tayi wahalar kai shi Asibitoci domin yayi walwala ya dawo kamar kowani Yaro, kenan banda wannan halin kirkin nata, tana da wani hali daban da bai sani ba? Kulle idanuwansa ya yi saboda jin alamun shigowar mutum, yasan ba zai wuce Noorhan ba, domin ita kaɗai ce take da wannan alfarmar. Babu alamar tana da haɗi da musulunci a yanayin shigarta, kyakkyawar fuskarta a ɗaure ta ƙaraso inda yake bakinta ɗauke da sallamar daya kafamata sharaɗinsa. Ɗan ɓata fuska taƙarayi tana gaishe shi, kafin ta ajjiye siririn dogon farin takardar dake ɗauke da sunayen abubuwan buƙatarta. Lumsassun idanuwansa da suka ɗan sauya kala ya ɓude akan takardar. Card ɗin daya tanada don zuba kuɗin buƙatar Noorhan ɗin ya miƙa dogon hannunsa ya ɗauko ya miƙa mata. Tuni fuskarta ya washe tunda dama ta ɗauresa ne saboda tasan tambayar kuɗinta ga Sulaim ya zarce ƙa'ida ko Iyayen da suka haifeta, bata isa su kashe mata kuɗin da take chajar Sulaim ba. Murmushi tayi tana juya idanuwanta ta ce; "Inajin daɗin yadda kake kashemin kuɗi Habibi, na gode" Kai Sulaim ya jinjina mata, tana yunƙurin sako hirar data saba yimai taga ya miƙe, kafin ta yi ƙorafi ya dakatar da ita ta hanyar sumbatar saman goshinta ya bar wajen. Baki ta saki tana bin bayansa da kallo. Card ɗin hannunta ta zauna jujuyawa, tunanin abin yake neman sauya mata shi lokaci ɗaya takeyi mata. Ta ɗan jima kafin ta miƙe tabar Gidan. ★washe gari da yammaci da sabon kwalliyarta Noorhan ta kawowa Sulaim ziyara. Maimakon samunsa a zaune a irin wannan lokacin yana aiki, sai ta samesa a kishingiɗe da System a gefensa idanuwansa a kulle kamar dai yadda ta samesa jiya. Cikin ɗan takaicin abin yake shirin taɓamata shi ta ce; "Tun zuwan Malik kwana biyu da suka wuce ka sauyamin why the Sudden change?" Idanuwansa da suka tara ruwa aƙasa ya buɗe amma ba dukka ba, yanayin lumshewarsu kamar wanda yake fama da zazzaɓi mai zafi, cikin taushin muryar dake ƙara matar da zuciyar Noorhan akansa ya ce; "Beg your pardon?" Gashin kanta ta ɗan hargitsa tana matsowa kusa da shi da kyau, sai dai takasa kallon cikin idanuwansa da har lokacin suke a kan fuskarta, domin wasu lokutan idanuwansa tsoro suke bata. Kuka ne ya fara zuwarmata kafin ta fara koro bayanin ya sauya tun zuwan Malik kuma shima yasan haka dan Allah karya bari a rabasu, ta roƙesa. Ita bazata takuramai ba duk lokacin daya shirya aurenta zata jirashi. Har ta gama magana Sulaim bai motsa ba bai kuma daina kallonta ba, wannan dalilin yasa takai hannunta gefen wuyarsa. Zafin jikinsa yasa tayi ƙasa da Kanta, sai a lokacin ta raina wayonta da kuma dasa Ayar tambaya wa soyayyar da take yi mai anya ba na kyansa da kuɗinsa ba ne? Idan da gaske tana sonsa yakamata ta fahimci bashi da lafiya tun daga sauyin idanuwansa da zaman da yayi yakasa aiki, domin Sulaim baya wasa da naiman kuɗi. Kanta ta juyar gefe kunyar kanta na mamayeta, cikin ƙarfin hali ta ce; "I'm sorry" Idanuwansa ya ɗan lumshe alamun ya karɓa kafin ya ɗauki wayarsa ya tura mata saƙo. Yana tura mata ya miƙe, kunyar bin bayansa yasa tabi shi da kallo. Tasani Allah ne yake sonta ya turomata Sulaim cikin rayuwarta amma ta lura ba lallai ya zama mallakinta ba saboda sam yanayin halayyarsu ba ɗaya bane, tsabar son da takeyimai gaba ɗaya sai ya zamana kamar tana shiga haƙƙinsa ta hanyar takuramai, gani take yi dole fa sai ta zaƙe kar a ƙwace mata shi. Sulaim bayan ya shiga ɗaki kwanciya ya yi. Ya kai wasu daƙiƙu a kwance kafin ya lalubo wayarsa ya danna Kiran layin Malik. Bayan Malik ya amsa sallamarsa, da muryasa da ta yi sanyi, irin sanyi da Malik bai taɓa ji ba ya ce; "Yaya Naila ta daina kuka? Kana ganin zamanta a Dhahab kaɗai zai sata farin ciki ko nazo ta ganni? ko kar nazo saboda kar ta ji tsoro?" A ɓangaren Malik katse kiran ya yi, domin bai yarda Sulaim bane, ko da ya duba ya tabbatar layin Sulaim ne, kai tsaye masu kula da lafiyarsa ya kira, su shiga Gidan su bincika wani ya shiga har ya samu nasarar ɗauke wayar Sulaim. Sulaim dake kwance da Noorhan dake zaune har lokacin a living room mamakin ƙarar da suka ji na alamun akwai matsala ne ya tashi kowannensu tsaye. A ɓangaren Sulaim kansa ya dafe yana jinjina Soyayyar Malik garesa don ko shakka bayayi aikin Malik ne. Tunanin zasu iya riƙe Noorhan da tuhumarta a matsayin mai laifi yasa ya fito daga ɗaki. Ya kuwa samu sun zagayeta wasu na ƙoƙarin bincika Bedrooms ɗin da suke cikin Sashen. Fitowarsa yasa sukayi ƙasa da Kansu tare da shaidamai Umarnin Sir Malik ne, bayan tabbatar da lafiyarsa suka bar Noorhan da sakakken baki. Suna fita kiran Malik ya shigomai bai ɗaga ba ya katse kiran nauyin kalaman da ya furta har yasa Malik yake tunanin ba shi bane ya sashi sakin ƙaramin murmushi. Malik Noorhan ya kira, jiki na rawa ta ɗaga, kai tsaye tun kafin Malik ya tambayeta ta fara zubomai labarin sauyin Sulaim da zazzaɓin da ta samesa da shi. Dan Allah ya sanar da ita menene matsalar? Kwantar mata da hankali Malik ya yi tare da bata shawarar ta koma Gida ciwone kawai ya sauyasa amma babu matsalar komai. MALIK; Ajiyar zuciya ya sauke bayan gama waya da Noorhan, ya ɗauka wanda ya san da zaman Naila ne ya tafi har can Kahala yake kiransa ta wayar Sulaim, "to amma ta yaya hakan zai faru?" Ya tambayi kansa. murmushi ya saki ya ɗan marin fuskarsa. Anya hasashensa bazai zama gaskiya ba kuwa? Na Sulaim zai dawo da soyayyarsu da Naila. Wajensu Naila da yayi niyyar zuwa ya nufa. NAILA; Har aka kaita bakin Sashen su Mama a motar Malik bata daina Kuka ba, fuskar Mariam da ta wulaƙantata na sukar zuciyarta. Ta yi tunanin da ta ganta zataci albarkacin Mahaifiyarta a wajenta ko da bazata nuna ta santa ba, ta hana Barirah wulaƙantata, ashe ita zata bawa Barirah lasisin mayar da ita abar kwatance. Kaka hankalinta a tashe ta tarbi Naila domin tun tafiyarta ta kasa zaune ta kasa tsaye, saboda tsoron tozarcin da Barirah za iya yimata. Ko ɗakin da suke daa ba'a barsu sun koma ba Malik ya cewa Mama ta canza masu ɗaki. Ɗakinta dayasha ƙawa ta kai su jikinta yana rawa. Tashin hankali bai sa Kaka ta gane Malik ba. Da Naila ta zo bawa Kaka labari kasawa ntayi saboda kukan dake sarƙemata murya. Rungumeta Kaka tayi tana bubbuga bayanta. Kafin Sallar magrib zazzaɓi mai zafi ya rufeta. Malik daya bada umarnin gyara sashen da zamu koma Mama ta kira. Gudun matsala Malik ya turawa Ubangidansa saƙo. Umarnin akaita tsadadden Asibiti Sulaim ya bayar. Sai bayan sun kai Asibiti anbawa Naila gado Kaka ta gane Malik. Ɗimuwarta da Kaka ta shiga ne yasa Malik kiranta guri na musamman a cikin Asibitin. Sai da Kaka ta tofe Naila dake barci da ƙarin ruwa a hannu da addu'o'i sannan tabi bayan Malik, zuciyarta cike taf da tsoro. Bayanin komai da wanzuwar Sulaim a doron ƙasa yayimata, tare da shaidamata mutuwar Abduh bayan barinsa Yankin Tudu. Kaka tayi sabon kukan mutuwar Abduh Dhahab, ta kuma yi farin cikin Sulaim dayake raye da zaman da zasuyi a Dhahab. Sai dai a take Shaiɗan ya fara bijiromata da maganar Sarkin Tsafin Yankin Tudu dayaƙi barin zuciyarta ta huta, nan take jikinta ya yi taji murnarta na komawa ciki. Duk da wannan Kaka bata musawa Malik zamansu a Dhahab ba, sai dai tace bazata iya shaidawa Naila Sulaim yana raye ba, duk ranar da Allah ya ƙaddara haɗuwarsu zata gani da idonta. A kan haka sukayi sallama da Malik ya wuce Gida. Sai tsakiyar dare Naila ta farka, itama Kaka da idarwarta daga Sallar nafila kenan miƙewa tayi ta zauna a gefenta. "Sannu" take ta maimaitawa Naila. Sai da Naila ta ɗan huta Kaka ta haɗa mata Shayi tasha sannan ta fara bata labari abinda ya faru, sai bayan ta gama Kaka ta sakomata hirar zamanmu a Dhahab. Ɗan jim Naila tayi itama maganganun Sarkin tsafin Yankin Tudu da Kaka ta sanar da ita na neman yiwa nutsuwata Illa, ambaton Allah tafarayi a cikin zuciyarta tana neman tsari daga sharrin shaiɗan. Haka suka ƙare wannan a kan tattaunawar zamansu a Dhahab. ★washe gari maimakon a sallami Naila sai akace saita ƙara hutawa. A yammacin rana Malik ya zo duba su, da zai tafi ya buƙaci mukullin sashensu na Birnin Abyad domin kwaso takardun Makarantar Naila da kuma bawa masu gida mukullinsu. Jakar da ke tare da Kaka ta duba ta ɗauko mukullin ta basa.. Bai jima ba ya bar Asibitin. Washe gari sai ga Bushra ta kawo musu ziyara. Naila tayi farin cikin ganin Bushra bayan tsahon lokacin da suka kwashe Basu ga juna ba. Ta wayarta suka gaisa da Yasar, ya tayamu murnar zaman da zasuyi a Dhahab da kuma nasihar Naila ta mayar da hankali kan karatuntaa daga haka suka yi sallama, duk da akwai abubuwan dayawa da Naila take so su tattauna. Da aka sallami su Naila washe gari Bushra da Driver ne suka zo ɗaukarsu, maimakon su nufi Gida wajen siyayyar kayan sawa suka wuce. Ba su yi mamakin irin siyayyar da Malik ya bawa kuɗi Bushra tayi mu su ba kamar yadda ta faɗa, sun jima Bushra tana kwasar suturar sawa da duk wani kayan buƙatarsu sannan su ka nufo gida. Kyan Muhallin da aka basu a Dhahab ba ƙaramin birgesu ya yi ba, saboda ba su san ma yadda zasu kwatanta kyan matsugunin na su ba, a taƙaice dai zasu iya kiransa da aljannar duniya. Kaka manta ƙalubalen dake gabansu ta fara takawa bayan tayi sujudar godiya ga Ubangiji. Bayan sun gama murna sun huta, Naila ta kalli kan Bushra dake tsafe tace ta taho tayi mata kitso. Kai Bushra ta girgiza ta ce; "mai Dhahab ya ce babu ke babu kitso har abada, ko kina so afara hukuncin ta kaina ne? ke da ma baki da lafiya" Ƙyam Naila tayi da idona akan fuska Bushra ta ce. "wanene mai Dhahab? Shin shi zai dinga biyana kuɗin da zan kai cigaba Yankina ne da har zai hanani yin sana'ar kitso?" Naila ta ƙarasa faɗa tana haɗe fuskarta Da mamaki Bushra ta amsamata daa; "Malik bai faɗamiki wanene shi ba, sannan ai yace ku faɗi duk wanda kuke so a ɗauka aiki a danginku" Naila ko a jikinta ta ce; "Ban san shi ba, kuma bashi da hurumin dakatar dani, idan ya ɗauki Matasa masu ƙarfin a jiki aiki, waɗanda suka tsufa fa kuma ba su da ƴaƴa ko Mijin da zasu turo ya ya zasuyi?" Dariya Bushra ta saki haɗe da kama bakinta mamakin irin son da Naila take yiwa Mutanen Yankinta na kamata. Bushra zata ƙara magana Kaka ta katseta da ce wa; "Bushra ɗan zo mana kinji" Ba musu Bushra ta miƙe tabi bayan Kaka. Jan kunnen Bushra Kaka tayi, kar ta sanar da Naila komai ta yi shiru har sai ranar da idonta ya gane mata. Duk nacin da Naila tayi Bushra bata bari n tayi mata kitso ba har ta bar Dhahab. Bayan tafiyar Bushra Da lallashi da ban baki Kaka ta taushi Naila ta haƙura da zancen kitso, amma duk da haka da Malik ya dawo sai da Naila ta ƙara tuntuɓarsa. Malik murmushi ya ɗanyi yana waskewa daga tambayar data yi mai na wanene Mai Dhahab, sai amsar biyanta albashi duk wata da ya yi. Tare da alƙawarin ɗaukar duk wani ɗan Yankin Tudu aiki matsawar zai dinga tura kuɗi gida. Babu wanda ya leƙo su Naila har suka yi kwana biyu. A kwana na ukun su a Dhahab Mota da Drivern daya sa Naima jinta wata ta musamman ya zo ɗaukarta wai Inji Sir domin kaita Makarantar da batasan yaya yake ba Malik dai ya turo mata Numbern wanda zata kira. Shigar Naila Jami'a mafi tsada a Babban Birnin Abyad kamar yadda ta duba sunan Makarantar a wayar hannunta yasa ta ƙara tambayar kanta. "Wanene mai Dhahab? Wani irin zuciyar taimako ne da shi?" UMMI AYSHA Da yammaci ta naimi Malik a waya saboda tambayoyin daya hanata ita da ƴan uwanta sukuni. Bayan Malik ya isa Sashenta sun gaisa, ya ɗan motsa bakinsa da kayan da suka jeramai Ummi Aysha ta kallase da kyau ta ce; "Wacece Yarinya da Sulaim ya zaɓi ajjiyewa a kusa dani? daga ina take? Menene alaƙarsu?....✍🏻 [9/5, 8:36 PM] Maman Amatullahi: SASAAL 8 SUFYAN; A wannan karon shi kaɗai ya yi jinyarsa da nurses da suke kula da motsinsa, sai kuma coworkers da suke shigowa dubasa. Ya yi zuru-zuru kamar ba Sufyan ba. Tun kafin a sallamesa ya yanke shawarar zuwa Yankin Tudu ya ga halin da Mahaifiyarsa take ciki, domin ya kira wayarta sau babu adadi baya samu. Jikinsa ba ƙarfi ya kunna wayarsa. Ko minti biyu baiyi da kunna wayar ba kiran Ɗayyib ya shigomai. Jiki a sanyaye ya ɗaga da Sallama. Cikin alhini kamar gaske Ɗayyib ya ce; "Ɗa na Sufyan mai kake gudu daga gareni ka ƙauracewa waya da ni?" Kai Sufyan ya ɗan girgiza kamar Ɗayyib yana ganinsa ya ce; "Baaba ba ni da lafiya, amma cikin satinnan ina nan zuwa duba lafiyar ku" Duk nacin da Ɗayyib yayi wajen sanin taƙamaimai abinda yake damunsa, Sufyan bai faɗa ba, daga ƙarshe haka sukayi sallama ran kowannen su cike da zullumi. Kwana biyu bayannan aka sallamo Sufyan ya naimi alfarmar zuwa dubo Mahaifiyarsa. A ranar ya kimtsa kayansa ya nufi Yankin Tudu. Lokacin da ya isa iyakar Yankin Tudu, wani Matashin da bai taɓa ganinsa ba, ya miƙomai farar Takarda a nannaɗe wai inji Sir Malik. Tuni gumi ya fara tsatsafowa sassan jikinsa, hannunsa yana rawa ya warware takardar don ganin maiya ƙunsa.... BARIRAH; A ɓangaren Barirah kullum fuskar a kumbure kamar an kwaɓa fanke ya tashi. Breakfast ma bata sonyi. Dama ba wani ɗasawa sukeyi da Simbi ba a wasu lokutan, don haka Simbi da take jin haushin abinda Barirah ta aikata duk da sunan son abinda yafi ƙarfinta tattarata tayi ta watsar kamar batasan abinda ya faru ba. Ummu Malik data kasa jurewa yanayin Barirah janyota a jiki tayi saboda Mahaifinsu bayanan. Da taushin murya ta fara yi mata nasiha; " Ba ina yimiki iyaka da Mairam ba ne, amma ina yi miki gargaɗi akan abinda take ƙoƙarin ɗoraki akai, daga mu har ita babu mai gadon Dhahab a cikinmu, domin tuni Sulaim ya fitar mata da haƙƙinta. Ba ita ba ko Aysha da ta haifesa rayuwa suke yi a mabanbanta duniya, sannan ke saboda sokuwa ce sai ta ƙara ɗoraki akan lallai sai kin auri mutumin da ya yiwa duniyar iyayenki da Iyayensa nisa. Kiyi tunani Barirah ko Sulaim bai taka wannan Matsayin ba, ba ajin aurenki ba ne, kuma itama Mairam tasan haka, Nailar da kike ƙoƙarin mayar da kanki sakarya akanta ki tuna ita ce ta samu damar raɓarsa bayan Mahaifinsa, kuma kinji labarin da Malik ya bayar da kunnenki, lokacin da Maihaifinsa zai taushesa da mutanen da zai iya riska bayan mutuwarsa har da Naila a cikinsu. Nasan baki ɗaukeni a matsayin Uwa ba tuntuni, amma ki sani Macen da tayi butulci wa irin halaccin da Mahaifiyar Naila tayi mata to tabbas kema wata rana zata yimiki wanda ya fisa Zafi" Ummu Malik ta ƙarasa faɗa muryarta cike da haushin abinda Mairam take ƙoƙarin ɗora Barirah akai. Barirah ba tace komai ba, sai kuka da takeyi kamar ranta zai fita. Da Ummu Malik ta faɗa mata sashen da aka kai su Naila su zauna a Dhahab da irin Makarantar da Naila fara zuwa birkicewa tayi, kuka harda bige-bige tana cewa; ita tafiya zatayi. Domin zuwan Naila Babban jami'a irin wannan a Babban Birnin Abyad na bata tabbacin labarin zuwan Naila Dhahab ya riski Sulaim. Tana cikin wannan rashin kirkin Malik ya shigo, bai yi wata-wata ba ya wanketa da marukan da sukayi connecting jijiyoyin ƙwaƙwalwarta ta dawo hayyacinta ta nutsu waje ɗaya tana sauke ajiyar zuciya. Da zafin muryar takaicinta ya ce; "Za ki tafi who cares? Za ki kashe kanki who cares? Kinsan wa ma kike so kuwa? Sau nawa nake ja miki kunne? Ohh wannan yawon Barar da mukayi a Birnin Abyad ne bai isheki ba ko so kikayi ki koma? Wallahi Daga yau idan na ƙarajin motsinki akan Naila sai na maimaita miki Tarihin shekarun baya da suka wuce, fool!" Babu wanda ya motsa a living room ɗin, saboda girman muryarsa da ya cika ko ina. Ya na fita Barirah ta bi bayansa da kallo kamar zata haɗiyi zuciyarta. A ɓangaren Ummi Aysha; Babu wani kwana-kwana Malik ya sanar da ita gaskiyar komai. Bayan tafiyarsa hirar su ce take ta kai kawo a cikin zuciyarta, ba ta ƙin Naila, amma tabbacin Sulaim yanayin dukka waɗannan abubuwan ne domin faranta ran Naila yasa ta buƙaci ganinta, ta ga menene take da shi wanda sauran mata basu da shi, ko kuma kawai sa'ace Allah Ya bata.... ROYAL UNIVERSITY ABYAD; har Naila ta bar Makaranta bayan ta haɗu da wanda Malik ya ce ta kira ya cikemata komai, bata daina sawa wanda ya biyamin kuɗin Makarantar albarka ba. Da Driver ya zo ɗaukarta a Mota mai taushin kujeru da sanyin raɓa sai ta lumshe ido daɗi kamar ya sumar da ita har wani matse hannu takeyi tana ɗan zaro harshe ko wa take yiwa gwalo oho? Ta faɗa a cikin zuciyata tana sakin dariya. Wajen cin abincin da ya dawo da ita asalin ƴar Yankin Tudun da bata taɓa zuwa ba Driver ya kai ta, wai ta huta ta ɗan ci abinci karta ƙarasa gida da yunwa inji Sir Malik. Driver yana fita kafin ya zagayo ya buɗemata ƙofa ta saki dariya tana jijjiga kaina tare da juya idanuwana kamar zata wurgosu ƙasa. Gaba ɗaya ɗan daɗin da ta ɗanɗana na wannan rana sai ya sata jin kanta da ganin kanta kamar wata ta musamman. Da ta kai Gida Kaka tasha labari har da ƙari da zuzutawa kamar a gabanta akayi komai. Bayan Magrib saƙon kiran Ummi Aysha ya riskesu ita da Kaka. Zuciyarsu fal tsoro suka nufi Sashen. Sautin Hermes flat shoe da ƙamshin turaren ta ne ya ankarar da su Naila fitowarta, Naila da Kaka nutsuwarsu suka tattaro waje ɗaya. Bayan mun gaisheta ta amsa sai da ta ɗan ƙarewa Naila kallo na ɗakiƙu sannan ta ce; "Naila" Da sauri Naila ta amsa tanayin ƙasa da kanta alamar ladabi. Da maganar mai cike da nutsuwa Ummi Aysha tace; "Sunana Aysha Matar Abduh Dhahab, Mahaifiyar Sulaim" ta ƙarasa faɗa tana kallo yanayin Naila A zabure Naila ta miƙe ta nufeta ta rungumeta da ƙarfi kamar zata ɓallata tana cewa; "Dama nasan dole jinin Sulaim ne ya kafa Dhahab, kema kin ji labarin ƙonewarsu ko?" Ido Ummi Aysha ta zaro tana kallon Kaka dake saitinta, kai Kaka ta girgiza mata. Jin tayi shiru yasa Naila ta dawo hayyacinta ta saketa da sauri tana zamewa ƙasa. Kafin Naila ta fara bata haƙuri Ummi Aysha ta ce; "Ban sani ba Naila! dama Sulaim ya ƙone har ya mutu shine Malik ya kasa sanar dani don yaga bazan iya zuwa Yankin Tudu ba, maiyafaru bayan tafiyata? wanene ya ƙona min Ɗana da Mijina Abduh" Ummi Aysha ta faɗa kamar gaske, dama kuma ta jima tana naiman wanda zai bata labarin bayan tafiyarta don ta kasa tambayar kowa saboda kunyar guduwar da ta yi. Ita dai Kaka kallonsu take yi musamman Ummi Aysha. Kamar an kunna gidan radiyo haka Naila ta zauna tana bawa Ummi Aysha labari, wasu labaran duk ba a haifeta ba aka yi su a bakin Kaka ta ji. Wasu Labaran Ummi Aysha ta murmusa wasu kuma ƙwalla ya tararmata a ido. Sai da ta gama taji maganar Ummi Aysha "Idan Sulaim zai dawo a raye zaki so shi kuyi Aure?" Ummi Aysha ta tambayetahar cikin zuciyarta domin a bayaninta ta fuskanci sam Nailan batasan Sulaim yana raye ba. NAILA; murmushi nayi kunyar maganarta ya sata ƙarayin ƙasa da kanta, sai lokacin kunyar zubar da ta dage tanaayi, ita a dole masaniyar tarihin rayuwar Sulaim ya kamata. Ummi Aysha bata ƙara ce mata komai ba, har masu hidimar shashenta suka gabatar mu su da Abincin dare. Bayan tafiyarsu Naila.. Ummi Aysha kasa runtsawa tayi har sai da ta shawarci ƴar ƙanwarta Farheen da Naila ta taɓa gani a Birnin Abyad a gidansu Yasar lokacin dayake jinya. Farheen Bata yanke hukunci ba ta ce ta bari gobe da safe taje har sashensu Naila ta ganta kafin su san abin yi. ★washe gari da yamma Farheen ta nufi Sashensu Naila. Tarbar dake nuna asalin tarbiyyar da su Naila suka samo tun daga tushe Farheen ta samu daga garesu ƙarin abinda ya birgeta shine wasa da dariyar su, tsayawa a matsayinsu duk da karramawar da Sulaim yayi musu na kawosu cikin su. Bayan ta koma Sashen Ummi Aysha suka haɗa Plan ɗin da dole zai dawo da Sulaim Naila ta gansa, "ko yaya zata ji?" Ummi Aysha ta tambayi Farheen. Dariya suka saki lokaci ɗaya. MALIK; Bayan ya gama abubuwan da zai yi ya shirya komawa Kahala don dubo lafiyar Sulaim kafin ya isa ya kira Managernsa ya haɗasa da likitan Sulaim da bai ma san ba shi da lafiya ba, tunda bai sanarwa kowa ba Malik sai da ya jira likita suka nufo Gidan... A living room suka samu Noorhan lulluɓe cikin Abaya fuskarta babu kwalliyar da Malik ya saba ganinta da shi. Yana ganin haka yasan ba lafiya ba. Itama tana ganinsu ta miƙe tana kukan su taimaka, Habibi baya ɗaga kira kuma tafi hour biyu a zaune bai fito ba, tayi knocking bai amsa ba. Malik ɗan harararta yayi ta ƙasan ido wai "Habibi mtsw" ya faɗa ƙasa-ƙasa yana nufa hanyar daƙin da Sulaim yafi zama a ciki. Shima ya buga bai buɗe ba, don haka ya fara bi ɗakunan yana dubawa. Malik yana cikin haka Sulaim ya shigo Gidan, Kyakkyawar fuskarsa ta faɗa sosai kamar ya yi shekara yana jinya. Da gudu Noorhan ta miƙe sai dai yanayin tsayuwarsa da yanda yake kallonta yasa ta dakata tana wasa da yatsun hannunta. Maimakon rungumarsa da ta yi niyyar yi sai ta kamo hannunsa. Da kai ya amsa gaisuwarsu yana zama a gefen Likitansa, hucin zafin zazzaɓinsa na busowa likitan. Shima Malik waje ya samu ya zauna, zuciyarsa cike da mamakin rayuwar Sulaim, to ko dai kashe kansa yake son yi, tunda yana ganin kamar bashi da kowa. Banda haka tayaya namijin daya mallaki hankalinsa kamar Sulaim zai zauna yana wasa da lafiyarsa?... Bayanin Sulaim ya haƙura su tafi Asibiti likita yake ta yi da sigar lallashi da tausasa harshe, har da ce mai Naanah Kakarsa kullum sai ta ce Sulaim ya rage zuwa. Kalllon Likita Sulaim ya yi a hankali ya ce; "Maiyasa zaka yi ƙarya daga wajen Naanah fa nake" Dariya likita da Malik suka gimtse ganin ya harbo Likita kai tsaye. Banda Noorhan da burinta kawai Sulaim ya miƙe su tafi Asibiti ya yi ya warke su komawa Soyayyar su. Malik yana shirin yin magana wayarsa ta fara vibrating. Bayan ya gama saurarar Farheen miƙewa yayi ya na furta "Innalillah! When accident ɗin ya faru?" A ɓangaren Farheen dasauri tace " a safiyar ranar". Kai Malik ya ɗan girgiza kafin ya naimi excuse ɗin zai ƙara kiranta. Suka yi sallama Idon da Sulaim ya zubawa Malik na nufin ƙarin bayani, don haka Malik ya ce; "Ummi Aysha ce ta yanke jiki ta faɗi jiya da daddare, garin zuwa dubata Naila ta zame I think kamar Farheen na bayanin ƙafar ya samu matsala, kuka ma takeyi." "Ka shirya komai zuwa safiya mu isa Abyad" Sulaim yana faɗa ya miƙewa. "Habibi ni fa" Noorhan ta tambaya kamar zata yi kuka...☹️ Ma su son a tafi ƙasar Abyad da Noorhan ya danna❤️ mara so kuma su danna👍🏻 Mu yi voting 😂 [9/5, 8:36 PM] Maman Amatullahi: SASAAL 9 A ɓangaren Sufyan; Yana buɗe takardar yaga an rubuta; "Barka da zuwa Iyakar Yankinka Sufyan! Rubutu na bazai tsawaita ba saboda wa su dalilai, amma duk tsananin da komai zaiyi babu zuwan Jalal da Ɗayyib Babban Birnin Abyad. Dawowarka zai tabbata ne idan ka ƙauracewa abincin cin su da shan su. Daga ƙarshe ina tayaka alhinin rashin da kayi. Ba lallai ka fahimceni ba amma ka haddace saƙona ka kuma sanya kunne da ido akan komai, ga na'urar naɗar komai ta sirrin da zaka saurara kai tsaye ta wayar hannunka. Zaka fahimci abinda na rubuta dalla-dalla." Sufyan gumin fuskarsa ya zarce hannunsa yana rawa ya yaga dakartar gudun kar wani ya gani sannan ya ciro ƙaramar na'urar dake ciki envelope. A karo farkon da ya fara wasa ƙwaƙwalwarsa ya nutsar da kansa kafin ya kutsa cikin Yankunansu. Maimakon ya wuce Yankin Tudu sai ya wuce Yankinsu Mahaifiyarsa Hindu. Ya samu Kakarsa cikin daular rayuwar da baiyi tsammani ba, tayi masa tarba ta musamman duk da bata san da zuwansa ba. Yana kallonta komai saƙon Malik ya na dawo masa, wannan dalilin yasa bai taɓa komai da Kakarsa ta gabatarmai ba, sai Mahaifiyarsa da ya tambaya tana ina? Murmushi tayi tare da shaidamai Hindu ta tafi Nahiyar Turai jinya, ai shi yasa ma baya samunta a waya. waje ta bashi wai huta ya ci abinci, Sufyan amfani ya yi da basirarsa wajen jagwalgwala abincin kamar ya ci, abinda bai sani ba Kakarsa tana laɓe tana kallonsa. Bayan yayi mata sallama kafin ya isa Yankin Tudu ta kira Ɗayyib ta sanar dashi isowar Sufyan amma fa baici komai ba tana zargin jimamin rashin samun Mahaifiyarsa ne ya hanasa ci. Lokacin da Sufyan ya isa Yankin Tudu abubuwa sun sauya, Talakawan Yankin sun samu cigaba ƙwarai kamar ba Yankin Tudu ba, ko da ya tambaya bayan ya huta sai ake sanar dashi ai Naila ce da Kakarta suke turo kuɗi, yanzu haka da safe kafin isowarsa dogon mota ta kwashi matasa sun samu aiki a ƙasar Abyad duk ta sanadin Naila, shiyasa jinin Jalal ya hau yanzu haka yana kwance babu lafiya. Sufyan yana jin haka ya nufi ɓangaren Sarki Hammam da sunan isar da gaisuwa, domin ko da suka haɗu da Mahaifinsa ya dai jashi a jiki da bashi umarnin ya kwanta ya huta amma bai sanar da shi Jalal bashi da lafiya ba. Sufyan yasan Ɗayyib da Jalal basa dogon hira gudun kar wani ya ji su don haka daya isa living room ɗin Sarki Hammam dayake zama wasu lokuta da Iyalansa ko baƙi masu muhimmanci sai ya ajjiye na'urar da Malik ya basa a gefen da bazasu ankara da wuri ba. Da ya je Sashen Jalal ba a barsa yaga Jalal ba don haka ya koma nasu sashen, a living room ɗin Mahaifiyar ya zauna yayi shiru. Har zuwa wasu ɗaƙiƙu yana zaune zaman jiran tsammani da abu maƙale a kunnensa, yana ƙoƙarin miƙewa sai ga Ɗayyib da sallamarsa. lallashinsa ya hau yi akan rashin Mahaifiyarsa da ta tafi nahiyar Turai jinya kafin ya sako masa zancen yana so ya bishi Babban Birnin Abyad idan zai koma domin ya ga yaya ma'aikatarsu take. Sufyan kai tsaye ya ce; "haba Baabah ba Lallai su amince ba kuma ai babu abinda zaka je yi, amma bari mu gani zuwa safe idan na tuntuɓesu" Shafa kanshi Ɗayyib ya yi da wani irin salo ya ce; "Babu Matsala Sufyan ka tuntuɓesu, yanzu bari a kawo maka abinci da abin sha ko?" Kai Sufyan ya ɗaga alamar ya ji. Ɗayyib yana fita ƙwaƙwalwar Sufyan ya harba maganganun Malik suka ƙara dawomai kenan cin abinci daga garesu na nufin dole ya kaisu Babban Birnin Abyad ko da a ɓoyene su rayu da shi domin kutsawa cikin Dhahab, shin maiyasa Mahaifansa basason kwanciyar hankalin Talakawansu wacce iriyar zuciya garesu da babu tausayi da imani? Yana cikin wannan tunanin Abinci ya iso, maimakon zama a inda yake, abincin ya ɗauka ya shiga chan ƙuryar ɗakin Mahaifiyarsa mai duhun da babu wanda zai iya ganinsa sai Mahalaccinsa. Yana shiga ya ajjiye abincin a gefe ya mayar da hankalin kan hirar da Sarki Hammam yake yi da iyalinsa. Minti uku bayannan Muryar Ɗayyib Mahaifinsa ya bayyana. ƊAYYIB Bayan sun gaisa da Sarki Hammam, Sarki Hammam yake tambayarsa "ya ya jikin Jalal?" Ɗayyib baiyi magana ba ya yi shiru har na wasu daƙiƙu sannan ya ce; "Abincin da Jalal ya tanada ya isa ga Sufyan, ranar tafiyarsa zamu tafi tare da shi, mu bincika ina mutanen Yankin Tudu suke zuwa a cikin ƙasar Abyad, sannan mu san wanene mamallakin ma'aikatar su Sufyan" Gwauron numfashi Sarki Hammam ya sauke ya ɗan kalli abinda Sufyan ya ajjiye danna ya ce "Amma kana ganin babu wanda zai faɗawa Sufyan azabtar da ka ganawa Hindu bayan yin wayarsu ta ƙarshe, har binnenta da kayi shekaran jiya da ranta" Sarki Hammam da zuciyarsa sam babu sukuni ya tambayi Ɗayyib yana fatan Sufyan ya jishi. A kasashe Ɗayyib ya ce; "Babu wannan Mutumin a duniya, domin babu wanda ya sani kuma duk wanda ya ci amana a tsakaninmu to zai bi Hindu inda taje, na binne Hindu da ranta a tsakiyar ɗakinta ne domin ta girbi abinda ta shuka, saboda itace ta ɓata komai ta zuga Sufyan ya tafi Birnin Abyad, har da Naila. Yanzu gashi Talakawa duk suna walwala a Yankin Tudu su na jinsu kamar kanmu ɗaya da su, ba ni da haufi akan hukuncin da na yankewa Hindu ko da Sufyan zai ji wata rana. Domin abinda ya shuka shi ta girba" A ɓangaren Sufyan kuka ya kece da shi jikinsa ya na rawa, katse komai ya yi, ya kuna fitilar wayarsa, cikin zafin nama ya ɗaga gadon Mahaifiyarsa, guri ya gani manne da tiles ɓaki sabo. Kuka ya saki yana kwanciya a wajen, saƙon Malik ya tuna "ina tayaka alhinin rashin da kayi" tayaya Malik ya sani, tabbas yana buƙatar ganin Malik ko ta halin ƙaƙa amma ta yaya zai tserewa su Ɗayyib???? SULAIM kallon mamaki ya yiwa Noorhan na daƙiƙu, amma ko don tasan matsayinta ya kamata taje ƙasar Abyad. Idanuwansa ya mayar kan Malik da yake jiran umarninsa ya rausayar da kansa alamar ya amince aje da ita. LV Jogger da free size shirt dukka baƙaƙe sai GG sneaker ya yi sassanyar adonsa mai birgewa, don tafiya Airport. Noorhan dake lulluɓe cikin Abaya kallon takunsa take yi zuciyarta na ƙara macewa Soyayyarsu. Idanuwanta ta lumshe a hankali tunanin na zurfafa a cikin daƙiƙu, wai gasu sunyi aure har sun haifi yara kyawawa irinsu.. A gurguje Noorhan taje gida ta kwaso Kayan buƙatarta da Passport. Sulaim bayason takura shiyasa shi da Noorhan kowa ya zauna a mabanbanta waje. Hakan ba ƙaramin daɗi yayiwa Malik ba, itama Noorhan bata wani damu ba tunda zata je Abyad ƴan uwansa su san da zamanta. Ummi Aysha; Ummu Malik da Simbi ne suka je dubata, laƙwas tayi kamar gaske, tana amsawa daƙyar don tasan Malik ne ya sanar da su. Daganan su Ummu Malik da Simbi ɓangarensu Naila suka wuce don duba nata jikin, sai dai a tsaye suka samu Naila tana ciye-ciye haɗe da bawa Kaka labari. Naila batayi rawar kan nuna murnarta ba kar su gwaleta, saboda wannan ne karonsu na farkon haɗuwa fuska da fuska tun bayan barin su Yankin Tudu. Sai dai yadda suka rungumen Naila da Kaka kuma suka saki jikinsu yasa itama Naila nuna farin cikinta. Bayan sun motsa baki da cookien da kaka ta gabatar musu Ummu Malik ta ce; "Ashe ƙafa ya yi sauƙi Naila, ai a bayanin Malik ya ce Farheen ta kira tana kuka, wallahi sai muka ɗauka ƙafar karyewa tayi, Allah Ya kiyaye gaba, itama Ummi Aysha Allah ya tashi kafaɗunta" Naila da Kaka wayancewa suka yi suka amsa da "Ameen" har da Simbi data ƙurawa Naila ido. Domin Ita bata yarda da jin ciwon ƙafar Naila ba wani abun take zargi daban. Gaba ɗaya sai hirar ta su ya koma kamar na yaƙe domin daga Naila har Kaka jira sukeyi su Ummu Malik su tafi Naila taje ta tambayo Farheen abinda ya faru. Fuskantar hakan yasa Ummu Malik yi musu sallama amma a nata ɓangaren gani takeyi baƙonta ce tasa suka kasa sakin jiki da su. NAILA; Suna fita kaka ta ce; "Maza tashi kije kiji menene ya sameta" Guntun light orange rigar da bai ƙarasa ƙasa bane sosai a jikin Naila Abaya mai maɓallai ta ɗauko ta ɗora akai ta ɓame maɓallan da sauri, bata damu da Ɗankwali ba tunda duk cikin gida ne, yasa ta yafa malulluɓin Abayar a kanta... Ummi Aysha; Bayan sun shirya faɗuwarta ita da Farheen da karyewar ƙafar Naila har sukayi nasarar Sulaim ya ce zai taho, sai ta rasa kuma ta hanyar zata nunawa Sulaim fuskar Naila ta hanyar bazatan da zai birgesa, don haka ta fara neman layin Malik, cikin sa'a tana kira ta samesa, ya shaida mata sun iso Airport ɗin Ƙasar Abyad. Tana yunƙuri kiran Farheen domin samun mafita amintacciyar Hadimarta ta naimi izinin shigowa. Tana jin ta ce Naila ce tazo gaisheta ta gyara zamanta tace ace ta shigo. A ɗan gefen Couch Naila ta zauna ta gaisheta har ya sanar da ita shigowarsu Ummu Malik Sashensu amma kuma takasa tambayarta maiyafaru su Ummu Malik suka ce ta karye a ƙafa. Ummi Aysha ta gane ina Nailan ta dosa tunda ta sanar da ita shigowarsu Ummu Malik wajen su. Cikin dabara da sanyi Ummi Aysha ta ce; "Naila ɗan taimaka ki dafamin Noodles mana ɗazun Farheen ta dafamin sam banji daɗinsa" Da sauri Naila ta ce "to" tana miƙewa. Dakatar da ita Ummi Aysha ta yi ta hanyar cewa; "rage wannan Abayar Naila karki samu matsala da wuta, ga scarf can ki ɗaure kanki" Babu damar musu, don haka Naila cikin kunya ta ɓalle maɓallan Abayar jikinta, ta cire ta ajjiye a gefe da mayafinsa, sannan ta ɗauki ɗan Scarf ɗin da Ummi Aysha ta nuna mata. Zata tafi Ummi Aysha ta ƙara dakatar da ita tana cewa; " ɗaura mana mu gani Naila" Cikin kunyar daya kasa sakin Naila ta ɗan ɗaurashi, kwantaccen sumar kanta ya bayyana agaban goshinta da bayan ƙeyarta. Murmushi Ummi Aysha ta yi kafin ta bata umarnin tafiya. Da taimakon masu Hidimar sashen Naila ta isa madafin Ummi Aysha. Bayan fitar Naila ajjiyar zuciya Ummi Aysha ta sauke tana gyara kwanciyarta. Sai dai kamar ana jiran fitar Naila, motsin Dhahab ya sauya saboda motsin motoci da ƙarin jami'an tsaron da suka fara mamaye kowani sashi na Dhahab. Ummi Aysha murmushi ta saki lokacin da ta ji alamun kusantowar motocin sashenta, dalilin jiniyar da ke bawa Securities alamar buɗe ƙaramin gate ɗin da yayiwa Sashenta iyaka da ragowar sashen dake cikin Dhahab, tun kafin isowarsu kar Sulaim ya ɓata lokacin zaman daƙiƙu a cikin mota. Farheen dake sama tanajin alamar chanjin da rabonta da jin irinsa tun shekarar da Sulaim ya ɗauke Naanah tayi wuf ta zura tsadadden abayarta, turare kuwa kamar zata juyeshi dukka ajikinta. Kamar zata faɗo haka take saukowa daga stairs da gudu kar ayi babu ita, domin tasan da zarar ya shiga to ma su tsaron lafiyarsa da zasu jirasa a living room bazasu barta ta shiga ba kuma ko sun kira Malik ba zai bari ba. A hankali ƙarfin ƙamshin Sulaim ya fara mamaye living room ɗin Ummi Aysha kafin ya fara gangarawa ɗakunanan sashen da madafin abincin da Naila take ciki. Ido Ummi Aysha ta lumshe ƙwalla na taruwa a cikinsu lokacin da tayi tozali da jarumin Ɗanta. Bai yiwa kansa mazauni a ko ina ba sai gefen lafiyayyen tattausar katifar dake saman gadon da take kwance a kai, kafin ya gaisheta sai da ya fara rungumarta ya sumbaci goshinta da hannunta, sannan ya gaisheta Cikin taushin murya da Yaren ƙasar Abyad da sukafi amfani da shi. Kuka ta fashe dashi tana ƙanƙame hannunsa ta kasa amsawa. Noorhan da Malik da suka zauna a Couch ɗaya Ummi Aysha ta kalla. Cikin girmamawa suka gaisheta, da kai ta amsa kafin ta yafito Malik da hannu, raɗa tayimasa a kunne, kan ya yiwa Securities magana su bar Naila ta shigo. Kafin Malik ya fita aiken Ummi Aysha suka gaisa da Farheen, Sannan Noorhan da take kallon komai dalla-dalla tana lissafa iya adadin dukiyar da aka kashe kafin mallakarsa ta gaishe da Farheen tana hura hanci. Da Sulaim Farheen tayi gaisawar ƙarshe tana murmushin jiran ta inda Naila zata ɓullo. Noorhan zamanta ta gyara tana jiran Sulaim ya gabatar da ita ko su Ummi Aysha su tambayesa wacece ita, amma sai taji shiru har Malik dayake gimtse dariyar gano Plan aka shiryawa Ubangidansa ya dawo daga aiken Ummi Aysha ya zauna. Naila ƙamshin turaren Sulaim har cikin siririn hancinta, jin alamun jiniya yasa ta matsu ta koma gurin Kaka taji menene yake faruwa. A plate mai kyau ta juyo Noodles ɗin dayake tiriri da ƙamshi mai daɗi, Securities ɗin data gani yasa ta ɗan ja da baya, amma suka bata umarnin ta shiga inji Ummi Aysha. Jiki a sanyaye Naila ta kutsa da Sallama. Malik, Noorhan, da Farheen, idanuwansu kamar zasu zazzago wajen kallonta, musamman Noorhan da Malik. Gaishesu Naila tayi Noorhan da Malik da kaa suka iya amsawa, saɓanin Farheen da ta amsa tana ɓoye dariyarta, da yaba basirar Ummi Aysha. Sulaim bai damu da shigo ba tunda bai san wacece ba, hannun Ummi Aysha ya ƙara kamowa zai sumbata, jajayen siraran laɓɓansa suka maƙale a kai dai-dai lokacin da Naila ta ƙaraso ta ajjiye abincin hannunta a table ɗin dake gefen bedside. Da tsoron ganin baƙin fuskar dayasa ta jin kunya tana ɗan zare ido ta kallesa da harshen ƙasar Abyad daya kama sassanyar muryarta ta ce; "Ina wuni Sir," Sulaim ya kasa amsawa ya kuma kasa cire laɓɓansa daga hannun Ummi Aysha balle ya ajjiye hannun, lumsassun idanuwansa da zazzaɓi ya kama ya ɗago ya zuba mata.... 😄 [9/5, 8:36 PM] Maman Amatullahi: SASAAL 10 SUFYAN; Zamewa yayi daga saman wajen yana kallon baƙin tiles ɗin da jajayen idanuwansa. dagaske Mahaifiyarsa Hindu ce a ciki. Kenan ba zai ƙara ganinta ba, ta yi wahala ta ɗorashi akan aƙidar gina kansa da kawowa Yankinsa cigaba ba zaman yin gasa ko kashe wasu ba. Ita ta fara tunamai, Sulaim da Abduh sun maƙale a zuciyar mutanen Yankin su ne saboda cigaban da suka kawo, don haka shima ya fita ya yi ilimin da babu mai irinsa ya kuma kawo cigaban da zai zama abun yabo wa mutanen Yankinsa, kuskurenta ɗaya don zuciyarta akan kowa matsawar zai zama abinda take buri, saɓanin Mahaifinsa da burinsa ya tusa masa aƙidar da suka taso akai na kashe-kashe da ramuwar gayya. Da ace idan ya fasa ramin domin bazai kirasa kabari ba, zai samu masu tsayamasa su karesa daga Ɗayyib ya ciro Mahaifiyarsa da ya cirota ya yi mata wanka ya kaita Maƙabarta ya binne kamar kowa, amma ba shi da wannan damar. Tuna irin azabar da ya san dole zatashashi a hannun Mahaifinsa, wanda kuma ita kaɗaice zata iya basa labari amma bata raye yasa ya fashe kuka. Tsanar Mahaifiyar da ta yi masa ƙarya saboda duniya na mamaye ko ina nashi. Ɗayyib har ya yunƙura zai miƙe idanuwansa suka sauka kan ɗan na'urar da Sufyan ya ajjiye, kallon Sarki Hammam ya yi yana nazartar yanayinsa kafin ya ce ; "Sufyan ya shigo nan ne?" Sarki Hammam cikin Basarwa,dakiya da shariyar da ya ɗauki tsayin shekaru yanayi ya ce; "Ya shigo ya gaisheni bai jima ba ya miƙe, da alama sauri yake yi." Kai Ɗayyib ya jinjina ya wayance ya durƙusa ya ɗauke na'urar. Da yake dare ya yi sosai Ɗayyib sashensa ya wuce da Na'urar bai nemi Sufyan ba. washe gari da sassafe yana fita kai tsaye wajen mutumin da ya taɓa bincikamai wayar Naila ya nufa da kansa. Tabbacin na'urar naɗar sautin da ake amfani da shi don naɗar sirri ya tabbatarmai, tare da shaidamai dole wani ne ya taho dashi daga wata nahiyar, Sarki Hammam ba shi da ikon mallakarsa ta daɗin rai. Kamar zai huda ƙasa haka Ɗayyib yake taka sawayensa, zuciyarsa kamar ana gobara saboda yadda ko ina nasa ya ɗauki zafi. Dakewa ya yi, ya cije bayan ya dawo Gida har sai da ya bari dare ya yi sannan ya nufi wajen Sufyan. Kaifaffen wuƙar ƙugunsa ya shafa yana lumshe fararen idanuwansa kafin ya buɗe su, sun koma jajaye. Babu sallama ya kutsa sashen Hindu.... UMMI MAIRAM; Tun ranar da hatsaniya ta haɗasu da Naila take kuka, Mahaifinta mai son zuciya da fifita farin cikin nasa akan na wani, sai mita yake yi yana kwashewa Naila albarka, acewarsa bai san uban daya kawosu Dhahab ba. Dama daga gani Malik baƙin ciki yake yi da zamansu. Ban da haka tayaya zai marawa Naila baya kai tsaye ba tare da bari a yankemata hukunci ba? Kukan da Mairam ta dage tanayi kamar ƙaramar yarinya da zugata da Mahaifinta yakeyi ne yasa Mahaifiyarta ta magantu; "Kina ba ni mamaki Mairam, mahaifiyar yarinyarnan tun kafin Mijinta Mahmoud ya mutu take hidima da ke, Mijinta ya mutu ta dawo kula dake gaba ɗaya, sanadiyyar haka ta rasa ranta, a tunanina duk ranar da kikaga Naila sai kin fi kowa farin ciki, amma son zuciya na neman makantar da ke, Yaron nan da kike kwaɗayin abinda ya tara yana da Uwa kuma ko ya mutu baki da gadonsa, yana kyautata miki dai-dai iyawarsa, amma ke burinki ya manta uwarsa ya nunawa duniya ke ce kika haifesa tun da shi mahaukaci ne ko? Ko Barirah kinsan ba halin ƙwarai gareta ba, amma duk kin toshe jinki da ganin ki burinki kawai ya aureta ki samu fada a wajensa, ai sai mu ga idan kina da ikon auramai son ranki, sha-sha-sha mara tsayawa iyakarka kawai" Kaf maganganun Mahaifiyarta Mairam bata ɗaukesu da muhimmanci ba, a ganinta ai Ummi Aysha guduwa tayi mai zai sa a yanzu ta dawo Sulaim yafi fifitata a kanta? Ummi Mairam bata ƙara birkicewa ba, sai da Barirah ta kirata a waya ta sanar da ita ai tuni ma Sulaim yasan da zaman Naila tunda har Malik ya naima mata tsadadden Makaranta da matsuguni na musamman ɗin da ko ita da ta zauna da shi bayan Mahaifiyarsa ta gudu ta barshi bata samu ba. Tana cikin jinyar zamansu Naila a waje na musamman a Dhahab, sauyin Dhahab alamar Sulaim ya dawo ya ƙara hargitsata. idanuwanta har zurma sukayi ciki kamar zasu faɗo saboda zarensun da takeyi tana jiran Sulaim ya fara shigowa Sashenta ya gaisheta kafin ya isa ga Mahaifiyarsa. SASHEN UMMI AYSHA; ido Naila ta ɗan zare tana kallon laɓɓansa da ya kasa ɗaukewa da ga kan hannun Ummi. Ƙara maimaita gaisuwarta ta yi da harshen nasara ko Yaren ƙasar Abyad ne baya ji. Still bai amsa ba sai kallon fuskarta da yake yi kafin ya gangaro da kallonsa kan kyawawa ƙafafuwanta da take tsaye a kai. Ido Naila ta ƙara zarowa, Ummi Aysha da daɗi yakama kamar ta tashi ta rungume Naila, a hankali ta ce; "Zaki iya tafiya Naila, ki ce ina gaishe da Kaka" Sulaim hannun Ummi Aysha ya zame a hankali daga kan laɓɓansa, sai dai bai ajjiye hannun ba mannawa ya yi a gefen fuskarsa yana lumshe idanuwansa. Kunya ce ta mamayesa son Mahaifiyarsa na ƙara kamashi. Don ya gane plan ta shiryamai tunda ga Naila tsaye akan ƙafafuwanta kuma saboda ta nunamai Naila a lokacin da zai fi birgesa sai tasa ta dama mata Noodles domin ya yi tozali da ita. Ƙara buɗe idanuwansa ya yi ƙaɗan yana kallon yadda Naila take yunƙurin ɗaukar Abayarta da sauri, ba tare da ta zura ba ta nufi hanyar fita. Kamar wanda ya ƙware haka ya ƙirƙiro tarin dole. Ummi Aysha da sauri matse dariyarta tana ce wa Naila; "Naila tsaya ki nutsu ki lulluɓe jikinki kinji" Malik da Farheen kamar jiran fitar Naila sukeyi. Tana fita suka saki dariyar da babu sauti haɗe da dafe bakunan su. Sulaim hannun Ummi Aysha dake gefen fuskarsa ne fara motsawa, alamun dariyarsa takeyi. Cikin taushin Muryar dake fita da sautin mai sanyi ya ce; "Ummiih, kinsa na ji kunya, wani iri nake ji, dama wayo kikayimin" Ummi Aysha miƙewa ta yi zaune tana dariya haɗe da rungumoshi, shima ƙaramin dariya ya saki yana ɓoye fuskarsa a bayanta. Noorhan hannunta da ƙafafuwanta ne suka fara rawa, wayarta da ta riƙe tana dannawa kamar batasan abinda suke yi ba, shima yafara rawa. "Wacece wannan yarinyar, Sulaim bai sanar da ni yana da ƙaramar ƙanwa ba, maiyasa yake kallonta irin haka?" Noorhan ta tambayi kanta tana satar kallonsu Malik da har lokacin suke ɓoye dariyarsu... NAILA; Tana isa Sashensu ta ƙwalawa Kaka kira "Kakaaa!!!" Kaka da sauri ta fito tana tambayar "menene ya faru Naila?". "Kaka wani mutum na gani tare da su Malik a sashen Ummi Aysha, Kaka kinganshi,?" "A'a Naila banganshi ba, maiyasa sameshi" Kaka ta tambaya da son jin zance. "Kaka yana da kyau, kinga yadda yake kallona, Ni kuma na ɗan zaro ido, kai Kaka ya ruɗarni wallahi" Kaka da labarin yake yiwa daɗi dariya tasa ta ajjiye cokalin hannunta haɗe da cewa; "sai ya ce miki me? Yana sonki?" Tsabar yadda zancenta yayiwa Naila daɗi sai da ta saki dariya tana juya idanuwa ta ce; "Kaka ko fa magana baiyi ba, kinga bakinsa hmmm😄!" "Bakinsa me?? Ke ki saki jiki ki bani labari mai ya samu bakin na sa?" Kaka ta faɗa tana dariya. "Kaka fa tsabar kyawuna da yake kallo kasa cire bakinsa ya yi daga hannun Ummi Aysha, ga idanuwansa masu kyau, shiyasa fa nima na ɗan zaro nawa idon, saboda ya ƙara ganin kyansu, yasan nima kyakkyawa ce. Ko da yake ni fa bai wani birgeni ba, kamar zai yi tsaho da yawa" A wannan karon Kaka garin dariya har cokalin gefenta ta wurga, da salon ƙara zurma Naila tunda tuni ta samu labarin zuwan Sulaim ta bakin Hadimansu ta ce; "Kuma baiyi miki kama da wani wanda kika sani ko kika taɓa gani ba?" Ɗan jim Naila tayi kafin ta ce; "Ai Sulaim ne kawai da ya girma a raye ya samu kuɗi zai yi irin wannan kyan, wai Kaka kinga idanuwansa kuwa? Sak irin na Sulaim idan yana kallona a Yankin Tudu, amma wannan sai wani iyayi ko gaisuwata fa bai amsa ba" Kaka da dariyarta yaki yankewa miƙewa tayi tana hasaso duk ranar da Naila ta gane Sulaim yana raye yaya zata ji??.. Kamar sakarya haka Naila ta koma lokaci zuwa lokaci sai ta zaro ido ta ƙyaƙyale da dariya. A living room ta zauna tana roƙon Allah Ya sa Ummi Aysha ta aiko kiranta, amma har wajen goman dare bata turo ba don haka ta haƙura ta kwanta barci. A SASHEN UMMI AYSHA Farheen ce ta fara miƙewa tana yiwa Noorhan maganar ta zo ta kaita masauƙi, kafin Malik ya bi bayansu, don duba gyaran da aka yiwa Masauƙin Sulaim. Bayan sun fita zame jikinsa Sulaim ya yi, ya zauna da kyau sannan a hankali ya furta; "Na gode" Kai Ummi ta janjinamai haɗe da cewa; "Nasan ba lallai ka ziyarceni ko da kaji ina halin jinya ba, saboda girman laifina daka kasa mantawa, amma idan na haɗa da ni da ita, nasan dole ka ziyarcemu, ba ni da abinci mai daɗin da zan gabatar maka ko wani abu da zan shiryamaka da zai birgeka sama da nuna maka fuskar masoyiyarka da ka manta tun zamanin ƙuciya. faɗamin ya ya kaji da ka ganta? Ka ganta kyakkyawa ko? Tun da gashi hannuna har maƙalewa ya yi" A karon farko Sulaim ya saki dariyar da ya bayyana jerarrun haƙoransa yana miƙewa saboda kunya. Itama Ummi Aysha haƙoranta ta ƙara washewa ranta fari fes, zata iya rantsewa tun bayan sanin Sulaim yana raye bata ƙarajin daɗin da ta ji irin na yau ba. Ta ji zafin jikinsa ba kamar na mai cikakken lafiya ba don haka bayan fitarsa ta lalubo wayarta ta kira Malik. Malik Bai ɓoyemata zazzaɓin da Sulaim ya kwana biyu yana yi ba. Likintanta tayiwa waya, bayan sun gama tattaunawa ta miƙe ta ɗauki Noodles ɗin da Naila ta ajjiyemata, ai ko babu daɗi dole ta ci, balle daɗinsa abin a yabawa Nailan ne da tukwaici mai tsoka. Ƙaramin Sashen dake jikin na Ummi Aysha aka gyarawa Sulaim, masu tsaron lafiyarsa zagaye da ko ina na sashen da Dhahab gaba ɗaya. Noorhan; tana wanka tana Kuka, kenan Sulaim ya kawota ƙasar Abyad ne domin ya nuna mata matsayinta, suma mugayen ƴan uwansa suna kallonta amma ko su tambayesa wacece ita? Wallahi dole Sulaim ya sanar da su matsayinta idan ba haka ba ita ta sanar da su da kanta... SULAIM; Yana wanka fuskar Naila da yadda ta zare ido tana gaishesa da muryarta da ya sauya daga na ƴan yara zuwa na ƴar budurwa na kai kawo a cikin idanuwansa, kunnen da zuciyarsa. Nailarsa da zama ƴan mata ta girma, to maiyasa bata gane shi ba? Ya tambayi kansa bayan ya fito daga wanka ya na zura Soft Pyjamas ɗin da Malik ya kawomasa, tunda baya tafiya da kaya sai dai idan yaje ƙasa ko gari ya siya idan zai tafi ya barsu a can. Yana shirin kwanciya bayan ya taɓa sassauƙar Abincin da Malik ya kawomai Ummi Aysha ta iso da Likita. Yana son taji daɗi ya nuna mata itama Uwa ce data isa ɗanta kamar ko wacce Uwa don haka ya amince Likita ya dubasa haɗe da samai ruwa. Noorhan; tayi tunanin za'a kirata Dinner amma sai ta ji shiru, sai ɗaki da'a biyota da shi. ★washe gari ma tana sa ran zasu kirata shima ta ji, shiru. Wanka tayi ta shirya cikin kalar Abayar daya haskata tana girgiza ƙafarta tana jiran Sulaim zai turo a kirata ko bazai turo ba, ta kirasa ta WhatsApp baya ɗauka kuma ita bazata kira Malik ya fahimci halin da suke ciki ba. Ummi Aysha da Farheen. Ummu Aysha bayan ta dawo daga wajen Sulaim sun sha hira Farheen cikin farin ciki, musamman Farheen da har kwaikwayar kallon Sulaim takeyi. ★washa gari Ummi Aysha da kanta ta shiryawa Sulaim Breakfast, kuma ta ɗauka ta nufi Sashen. A kwance ta samesa cikin Armani lounge wear jajayen da suka yi mai kyau, har lokacin ganinsa bai dawo dai-dai ba jikinsa a mace. Shi ya fara gaisheta ta amsa tana yimai ya ya jiki? Da kai ya amsa mata yana gyara zamansa. Ɗagowa ya yi a hankali ya kalleta kafin ya ce; "Tana zuwa Makaranta?" Ummi Aysha da daɗi yasata sakin murmushi saboda gane ina ya dosa amma sai tayi fuska kamar ba ta gane ba ta ce; "Wacece? Ai Farheen tuni ta gama Makaranta, ko su Simbi ƙanen Malik kake nufi?" "Ummiiih" ya faɗa yana ɗage cikakkiyar girarsa ɗaya da murmushi kwance a saman fuskarsa. Ummi Aysha wani irin daɗi takeji ɗanta ya saki jiki da ita a karon farko. Saboda taga yadda zai yi sai ta ƙara cewa; "To ai bangane ba, auuw! ohhh! Naila ka ke nufi😄?" Juya mata baya yayi yana dariyar da ke motsa kafadunsa. Itama Ummi Aysha dariya tasa kafin ta kira sashen Hadimai su sanar da Naila tana nemanta a sashen Sulaim idan bata gane ba su rakota. Bata ajjiye wayar ba sai da ta kira Malik ya sanar da Securities su bar Naila idan ta iso ta shigo. NAILA; lokacin da saƙon Ummi Aysha ya jewa Naila, daƙyar ita da Kaka suka daure Hadiman suka fita, suna fita Kaka tasa dariya tana dafa Naila dake juya idanuwa kamar zasu zazzago. Ta ɗauko dogayen Riguna sufi kala goma tana nunawa Kaka, Kaka tace basu yi kafin ta zaƙulo Royal blue mai kyau. Bata wani fesa turare sosai ba, kar ace sonshi takeyi da addu'ar sa'a Kaka ta rakata suna dariya...✍🏻 [9/5, 8:50 PM] Maman Amatullahi: SASAAL 11 SUFYAN; Tuna abinda ya ajiye a living room ɗin Sarki Hammam yasa ya ɗebi rabin abinci ya watsar a lungu, ya dai-daita zamansa amma har lokacin ya kasa tsaida hawayensa. Tun yana sa ran Ɗayyib har ya cire. ido buɗe ya kwana yana kallon inda Mahaifiyarsa take ciki. ★har gari ya waye dare ya kuma sallace kawai take tashinsa ya kasa saka komai a cikinsa.. Yana zaune ya jiyo zafin takun Ɗayyib, miƙewa ya yi kafin ya shigo ɗakin ya riskesa. Domin da ga yanayin takunsa da jiyo ya fuskanci yaga abin ya ajjiye, don haka maganar ɓoye-ɓoye ya kau tsakaninsu. Ɗayyib ya na shigowa Sufyan ya taresa da cewa; "Don me zaka binnemin Uwa da rai! Na ce don me zaka binne min Uwa da rai!! Ka zo ka sareni da wuƙa ne? ka sare ni nima ka binne Ni? To ka sareni mana!!!" Sufyan yaƙarasa faɗa yana kallon cikin jajayen idanuwan Ɗayyib haɗe dukan ƙirjinsa. Murmushi Ɗayyib ya yi yana cije haƙwaransa sai dai kafin ya zaro abinda ya yi niya Sufyan ya kai mai naushin daya sashi zubewa yana mayar da numfashi, kafin ya yunƙura ya miƙe, ihu ya karaɗe Daular gaba ɗayanta da kiran sunan Ɗayyib. "Menene ya ke faruwa?" WAIWAYE Ranar da saƙon Malik ya isa ga Sufyan kafin ya shiga Yankin Tudu, A ranar Su Malik sauka baro Kahala. Sanin hatsaniya zai iya biyo bayan zuwan Sufyan Yankin Tudu kamar yanda Sarki Hammam ya sanar mai yasa ya shirya tafiyarsa Iyakar Yankin Tudu bayan isarsa Kahala. Malik da suka dawo Dhahab da Sulaim Bayan ya duba, Masauƙin Sulaim komai ya yi dai-dai ya miƙa masa abinci yayi sallar magrib ya kimtsa zuwa Iyakar Yankin Tudu ta ɗaya daga cikin jiragen da suke amfani da shi, sai dai da dirarsa waya ya riskesa daga Sarki Hammam Ɗayyib ya gano abinda Sufyan ya ajjiye, a wannan dare Malik da masu yi masa Hidimar sirri a Iyakar Yankunan suka isa Yankin Tudu har ɓangaren Jalal. Da farko Jalal da ya ke kwance bai gane tsayuwar Malik ba saboda babu wadataccen haske, sai dai yankar da Malik yayiwa ƙwaurin ƙafarsa ne ya sashi miƙewa jikinsa yana rawa. Cikin tsoro da ganin mutuwa muraran Jalal ya ce; "wanene ya turoka? mai kake nema da n..." Wani irin Yanka mai shiga jiki Malik ya ƙara yiwa rabin fuskar Jalal dayake kallonsa da shi ya na tambayarsa. Ihun azabar da ya amsa Masarautar ya saki yana lalube domin ko baiyi magana ba, yasan Malik ne ya riskesa. Da ƙarfin Muryar da bai san yana da shi ba yake kiran Ɗayyib dake wajen Sufyan. DAWOWAR LABARI Da gudu Ɗayyib ya miƙe ya nufi Sashen Mahaifinsa Sufyan ma ya bi bayansa. Babu wanda ya leƙa wajen Jalal saboda tsoro kowa laƙwas ya yi saboda suna kyautata zaton Malik ne ya bayyana a wajensa. Wa su dai sunyi ƙarfin halin fara neman Ɗayyib ta hanyar kiran Sunansa. Malik tsayuwarsa ya gyara. Ɗayyib yana Kunno kai ya yaye mayafin fuskarsa suna kallon juna. Cikin kuka ga jinin da ke bin jikin Jalal da har lokacin yake yashe a ƙasa a gefen Malik yake cewa; "Ka ceceni Ɗana Ɗayyib haƙiƙa Malik ya bayyana gare ni.." Wani irin ɗauka Malik yayiwa Jalal kamar tsumma, ya ɗaga wuƙar hannunsa ya Chaka mai a saman kafaɗarsa yana kallon tsakiyar idon Ɗayyib ta ɗan hasken da Malik ɗin ya kunna da kansa.. Ihun azaba Jalal ya saki.. Cikin kaushin Muryar dake nuna zafin kan Malik da haushinsu daya rayu da shi ya ce; "Bayan tasha uƙubar watanni daga gareka yanzu awoyinka hamsin da huɗu da binneta, ka je ka cirota da hannunka Ɗayyib! a wanketa a kaita Maƙabarta idan ba haka ba, wallahi! Wallahi!! Sai na tafi Babban Birnin Abyad da kawunanku" Malik yaƙarasa faɗa yana murza wuƙar da bai cire ba a saman kafaɗar Jalal da azaba ya jima da sumarwa. Tsayawa Ɗayyib ya yi yana jin kamar ya taro ƙarfin duniya a jikinsa ya kashe Malik da Sufyan nan take, amma abin taƙaicin ko Bafade ɗaya babu, kowa yana gudun ransa. Ganin Ɗayyib ya ƙame a tsaye yasa Malik ya ce; "Iya adadin mintocin da ka ɓata iya adadin jinin Ubanka da zai salwanta har ya rasa ransa, kaga ka rasa Shaiɗanin Uban daya horar dakai yake kan tayaka ɓarna" Malik ya ƙarasa faɗa yana watsar da Jalal a gefe.. Gane gaskiya Malik ya faɗa kuma babu abinda ya isa yayi mai idan Jalal ya mutu, ya sa Ɗayyib fita da sauri, waɗanda suka tayasa binne Hindu ya nemo da Gatari da komai da sukayi amfani suka fasa da sauri, sai gashi sun cimma gawar Hindu da ya karaɗe ko ina da wani wari... Sufyan wajen Malik ya je ya ɗurkushe ƙasa yana kuka haɗe da haɗa hannayensa da suke rawa waje ɗaya alamar godiya domin tsoron Malik ba zai barsa ya yi magana ko ya iya kallonsa ba. Ɗayyib suna tono gawar Hindu ya komo wajen Mahaifinsa sai dai babu Malik babu Sufyan. Da sauri ya ɗaukesa zuwa cikin Mota da taimakon abokan ɓarnarsa suka nufi Asibiti da shi. A wannan dare Sufyan ya dinga bi gidajen Dattawan Yankin yana kukan su taimakamai, tunda Malik tuni ya bar Yankin. Jin abinda Ɗayyib ya aikatawa Hindu ya sa suka tausaya mai, duk suka ɗaure hancinansu suka dumfari gawar Hindu.. Da taimakon Matar Babban limamin Masarautar da ma'aikatan Jinya aka suturta gawar Hindu iyakar yadda zasu iya.. ★washe gari Dandazon Mutanen Yankin Tudu ne suka yiwa gawar Hindu rakiya zuwa makwancinta. Sufyan ya yi musu godiya yana kuka. Bayan ya tsaya a kabarin Mahaifiyarsa ya yi mata addu'a ko minti biyar bai ƙaraba ya koma gida ya ɗauki jakarsa da bai taɓa komai a ciki ba ya bar Yankin Tudu zuwa Babban Birnin Abyad. Tare da sawa zuciyarsa ya tafi kenan har abada. NAILA; Da taimakon Hadiman sashen Ummi Aysha Naila ta isa sashen Sulaim. Ƙofar Sashen a buɗe yake don haka tana zuwa Securities suka barta ta shige. Ƙamshin sashen da tsaftarsa yasa Naila ƙara nutsuwa. A zaune ta samesu shi yana Breakfast Ummi Aysha kuma tana danna waya. Gaisuwar Naila kawai Ummi Aysha ta amsa da fara'a a kan fuskarta ta miƙe tana kafa waya a kunnenta alamun amsa kira. Da harshen nasara Naila ta gaisheshi tana yin ƙasa da kanta. Da kaa Sulaim ya amsa mata yana nuna mata gefenshi, wajen da Ummi Aysha ta tashi. Ƙafafuwan Naila su na harɗewa ta taso ta zauna, gaba ɗaya sai take jin saman kanta kamar an ɗora mata duniya saboda girma. Kofin hannunsa ya ajiye yana gyara zaman da ya bashi damar fuskantarta da kyau. "Naila" ya faɗa yana kallonta. Still Naila da zuciyarta take bugawa da sauri-da sauri bata ɗago ba. "Ki ɗago ki kalleni ko zaki ganeni, tunda kin kasa tuna muryata" ya faɗa a hankali kamar mai tsoron magana. A hankali Naila ta ɗago, ƙwaƙwalwarta ya shiga lissafin kyansa amma har lokacin kai tsaye ta kasa gano wani abu ɗaya na shi. Domin fuskar waccen Sulaim ɗin da ban da wannan, shi waccen aikin wuta ne sana'arsa, ga rayuwar ƙunci da kaɗaici da yakeyi saɓanin na yanzu da yake rayuwarsa cikin raɓa dare da rana, iyayensa da danginsa duk su na kewaye da shi, kowa gudun ɓacin ransa yake yi, dai-dai da muryarsa ya canza yaƙara zama mai sanyi da daɗin sauraro, irin sanyin da kuɗi da nutsuwa ne kawai suke iya samar da shi. Ganin da gaske Nailan ta kasa tunashi sai ya ɗan motsa laɓɓansa tare da buɗe muryarsa kaɗan yadda zata ji shi da kyau.. "Yankin Tudu! Daular Sarki Hammam, sassanin wasannin ƙarshen mako, gidan Abduh Dhahab maƙerin Tukwanen ZINARE! Sulaim mai kaiki Makaranta a keke" Sulaim yaƙarasa faɗa yana ɗage dukka girarsa murmushin yadda Naila ta zaro dukka idanunta na ƙara faɗaɗa a saman fuskarsa. Da sauri, ƙwaƙwalwar Naila yake ƙara lissafa mata komai na fuskar Sulaim, kafin idanuwanta suyi juyewar da tayi baya zata kife ƙasa. Da sauri ya kamota ya gyara mata kwanciya. Bayan wani lokaci Lokacin da Naila ta farfaɗo babu mutumin da ya ce mata shi Sulaim ne, sai Ummi Aysha. Da taimakon Ummi Aysha ta koma sashensu. Tana kwance Kaka ta shigo da Dinner a hannunta, kafin ta karɓi abincin ta ce; "Kaka da gaske ne?" "Da gaske me? Tunda ke babu nutsuwa a lamarinki" Kaka ta faɗa kamar zata kai mata dukka. "Kaka to kiyimin bayani, ni fa gani nakeyi kamar na daina gane komai, Yasar ya taɓa faɗamin Muhammad Dhahab shine ya kafa Dhahab kuma babu wanda ya san Asalinsa amma wa su sunce ɗan asalin ƙasar Abyad ne, Ni fa kamar ma na ƙara manta fuskarsa" Naila ta faɗa da iyakar gaskiyarta. Abincin Kaka ta dangwarar mata tana jan ƙaramin tsaki, haɗe da cewa; "idan zaki nutsu ki nutsu domin da gaske Sulaim kika gani, idan ya shigo dubaki mutuwa zaki yi ba suma ba, tunda kuɗi da raɓa sun sa kin zama fara🦗, daga ganin mutum ya ce miki Yankin Tudu sai ki Sume, kuma a haka ki ishi mutane da daa Sulaim yana raye da shine kaza da shi zaima kaza, Ni ce ma shi ina zan kulaki na zama mai arziƙi" Kaka taƙarasa faɗa tana taɓe baki kafin ta bar daƙin Naila ta miƙe da sauri tana sha gabanta.. "Kaka dan Allah to kiyimin bayani, yanzu Ni ce fara🦗?" Naila ta tambaya tana marairaice fuskarta. Domin sauƙaƙawa Naila saboda an turo neman izinin Sulaim zai shigo dubata Kaka ta zaunar da ita. Bata rage mata komai ba a labarin da Malik ya bata, sannan ta ɗora da nasihar Nailan ta kula, saboda daga yanzu komai zai iya sauyawa. Naila bata motsa ba, a hankali komai yake warware mata, irin kuɗin da Malik yake kashewa da irin girman da yake ba su ashe da dalili, Dagaske kamar yadda take ji ajikinta ashe Sulaim bai mutu ba ya na raye. Naila bata kawo zuwansa kusa ba tunda ba'a daɗe da yin sallar magrib ba, living room ta fito ta zauna, Kaka da bata yarda da Mai hidimar dafa abinci ba tana madafi tana shirya kayan tarbar Sulaim duk da tasan ba lallai ya ci ba. Ana knocking Naila ta tashi da kanta ta tafi buɗewa. Tana buɗewa da fuskarsa tayi tozali babu kowa a bayansa, jikinsa sanye da kaya masu kauri baƙaƙe, sai hular sanyi mai taushin daya rufe rabin girarsa. Hannayensa zube cikin aljihun wadonsa, da alama sanyi yake ji. kallonta Sulaim ya tsaya yi yana karantar yanayinta, ganin zasu jima a haka ba tare da ta iya cewa komai ba sai ya kamo hannunta suka dawo living room ɗin tare, a gefen Couch ɗin da ya zauna, ya zaunar da ita. "Ina wuni" Naila ta faɗa a hankali tana kallon dogon hancinsa ta gefen fuskarsa. Hannunta dake cikin nasa ya matse alamun ya amsa. "Ka yi haƙuri" shima bai amsa ba still hannunta ya ƙara ɗan matsawa alamun ya ji. Waiwayowa ya yi yana kallon fuskarta da ta sunkuyar, cikin sanyin muryar daya haɗe da zazzaɓin dayaƙi barinsa ya ce; "Na dawo Abyad ina murnar zan ganki har ciwo nake yi amma kin ganni kin suma, kin daina son abotarmu ko?" Naila da daɗi ke neman gusarwa da nutsuwa dasauri ta ɗago kanta tana girgizashi. Daɗin muryarsa da yadda kai tsaye yake nuna kulawarsa akanta ya sata sakin murmushi kafin kuka mai sanyi ya biyo baya. Yau ga ta ga Sulaim sun girma sun zama manya kuma a raye ba a mace ba. "Na tafi bakyason ganina?" Ya tambaya kamar ba Sulaim ba. Kai Naila ta girgiza da sauri tana ƙanƙame hannunsa. Ƙarar faɗuwar cokalin hannun Kaka dake laɓe tana kwallon su ne, yasa Sulaim ɗan sakin murmushi, itama Naila murmushi ta saki tana dafe bakinta. Kaka akwai son bin diddigi. "Ki kirata mu gaisa zan tafi tunda kuka kikeyi bakyason gani na" Sulaim ya faɗa da wasa. Naila da take jin kamar su dawwama a haka kai ta ƙara girgizawa da sauri. " Kiyimin magana Naila, ki kalleni a waccen Sulaim ɗin, ba wannan ba, ( ya faɗa yana nuna ƙirjinsa) kiyimin hirar da kika saba, ki bani labari, Kinyi kuka da ake ce na Mutu?" Ya tambaya idanuwansa na kai kawo a saman fuskarta.. Naila da daɗi yayiwa yawa har ta rasa wajen zuba extra kuka ta fashe da dashi mai tafe da dariya lokaci ɗaya... Barkanmu da dare🍜 [9/5, 8:51 PM] Maman Amatullahi: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 ZINARE 2 BY NAFISA ALIYU SASAAL CHAPTER 2; *WASIƘAR ALƘAWARI* 12 NAILA; Bansan yadda zata misalta daɗin hirarsu a wannan dare ba, amma ya tunamata da abubuwa da dama, sai take jinta kamar lokacin da take yarinya ƙarama a Yankin Tudu. Sulaim bai bar Sashensu ba sai 11:00pm. Barcinta na wannan rana na musamman ne mai cike da mafarkan cikar muradi, domin Sulaim da ta rayu da soyayyarsa a cikin zuciyarta a matsayin matacce ya bayyana a zahiri gareta matsayin rayayye, sam bata hasosa dukiya ko girman Dhahab da ƙawarsa a matsayin abinda zai zama linzamin Soyayyarsu ba, kulawarsa da mutuntawarsa garesu ya fiyemata komai. Noorhan; tun tana sa ran Sulaim zai biyota masauƙinta ko ya turo aka kirata har ta cire rai. Tana kuka ta kira Mahaifinta ba tare da bin ba'asi ko sanin gaskiyar abinda ya haɗasu ba, Mahaifanta ya ce ta turamai number Malik don bazai iya kiran Sulaim kai tsaye ba. Ko da ya kira Malik kai tsaye Malik ya shaidamai wannan lokacin na Ahalin Sulaim ne kuma itama Noorhan tasan da haka shekararsu nawa suna tare bai ziyarci Gida ba? Idan zata jure to, idan kuma bazata jure ba zai sakota a jirgi ta dawo Gida. Bayanin Malik ya soki zuciyar Mahaifin Noorhan, a ganinsa ƴar sa abar da za'a tattalace duk uzurin da Sulaim zai gabatar ya zamana tana gefensa. Batare da Shawara da Noorhan ba, ya ce wa Malik su sako ɗiyarsa a jirgi ta dawo Gida. Gajeran Saƙo Malik ya turawa Sulaim, tabbacin ya gani kuma bai ce komai ba, yasa ya naimi tikitin tafiyar Noorhan nan take. ★washe gari Noorhan tana gama Breakfast Malik ya tura mata saƙon ta kimtsa Jirgin karfe biyun Rana zata bi, da mamaki take kallon saƙon kafin ta kira Mahaifinta. Da yake bawani tarbiyya aka horar da ita a kai ba, kai tsaye bayan ta ji shi ya yanke hukuncin tafiyartata ba tare da naiman shawararta ba ta fara yimai rashin kunya da faɗar maganganun masu kaushi. Tasan bata isa ta jawa dukiyar Sulaim asara ba tare da wani dalili ba don haka ta shirya kayanta tana kuka. Ummu Malik; duk da Sulaim bai shigo gaishesu ba tukunna taji daɗin aiken kuɗin da ya yi musu, hatta Barirah da ƙunci ya hana sukuni ta ji daɗin kyautar kuɗin. Bayan sunyi Dinner Ummu Malik take yiwa Simbi da Barirah faɗan su ja Naila a jiki, kishi tsakaninsu ya kau, su tuna Yankin ɗaya ne ya samar da su, kar su bari son duniya ya makantarsu, su yi biyu babu. Barirah kai tsaye ta nuna sam bazata iya mutunci da Naila ba, saɓanin Simbi da take ganin hakan kamar wani dama ne na sanin halin da Naila da Sulaim suke ciki, idan ta ja Naila a jiki dole duk zurfin cikin Naila tasan wani abu akan Soyayyarsu. Ummi Mairam; Duk kyautan kuɗin da Sulaim ya yi musu bai birgeta ba sam, burinta ya zo gareta ta gabatar masa da Barirah ko Allah zaisa ya amince mata. Gaba ɗaya bata sa abincin kirki a cikinta ba har zuwa washe garin da aka sanar da ita Sulaim zai shigo gaisheta zuwa yammaci. SULAIM Duk da, da zazzaɓi ya kwana hakan bai hanasa yin mafarkai masu daɗi riskar barcinsa ba, sai ya ke jinsa kamar lokacin da Mahaifinsa yake raye suke rayuwar ƙere-ƙerensu a Yankin Tudu. Ba iya son Abota yake yiwa Naila ba kamar na shekarun baya, son aure yake yi mata idan zata amince da alƙawarinsa.. Kafin gari ya yi haske zazzaɓin jikinsa ya sauka, Da abin karin Ummi Aysha ya karya. Ummi Aysha murmushin fuskarta ƙim ɗaukewa ya yi har ta bar sashen saboda daɗin yadda Ɗanta ya saki jiki da ita. Bayan fitarta Malik ya ziyarceshi... Da Muryar da zai fahimcesa dakyau Malik yake yimai bayani akan su Ɗayyib karon farko tun bayan haɗuwarsu, saboda Malik ya na ganin Yaƙine da bazai iyashi shi kaɗai ba. Bayan Sulaim ya gama saurarar Malik kansa ya ɗago yana dangana wayar hannunsa ga ƙaramin table ɗin dake gefensa.. ya ce; "Wa su burika ka taɓa sanar da ni Naila tana da su ma? sannan Menene hukuncin da kake ganin ya dace a yiwa Ɗayyib" Sulaim ya tambaya yana kallon tsakiyar idon Malik. Kai Malik ya ɗan sosa, a ganinsa bayaninsa ba shi da haɗi da burin Naila amma sai ya daure ya ce; "Burinkanta biyu ne, cigaban Yankinmu da kuma samun tabbacin kana raye ko Dagaske ka mutu, ina ganin kuma ai muradanta sun cika, Ɗayyib kuma kasheshi shine hukuncin da ya dace da shi" Kai Sulaim ya ɗan karkata gefe ya ce; "A mayar da Ma'aikatar Tukwanen ZINARE tushen da aka ƙirƙiresa, duk wanda zai siya ya je har Yankinmu ya siya, Sufyan nake so ya zama GM sauran naɗe-naɗen yana hannunka, daga yau nakeson komai ya fara aiki. A filin da aka fara cinikin Tukwanen a filin za'a kafa Ma'aikatar. Ɗayyib kuma abarsa tukunna" Sulaim ya ƙarasa faɗa yana miƙewa haɗe da ɗaukar wayarsa ya bar ƙwaƙwalwar Malik da lissafi. Mayar da Companyn Dhahab na ɓangaren Tukwane na nufin burin Naila ya kammalu domin Yankin Tudu zai zama babban Yanki kuma kowa zai samu aikin yi Matasa Maza da Mata. Bayyanar babban Maka'aitar Tukwanen Zinare da a yanzu a ƙasar Abyad ya fi rogowar shigowa da Sulaim kuɗi a Yankin Tudu da naɗa Sufyan a matsayin GM na nufin bugawar zuciyar Ɗayyib da Jalal... Idan ya fahimci Sulaim so yake yi su mutu da baƙin cikin abinda suka kasa kawo ƙarshensa.. Dariyar mugunta Malik ya saki har hawaye na tararwa gefen idonsa, Da zafin naman fara aiki nan take ya miƙe ya na zaro wayarsa .. Misalin biyar na Yammaci Sulaim ya shirya cikin guntayen ƙananun kayan da suka dace da siffarsa, ƙafafuwansa sanye da Miami mule ɗin daya ƙara musu kyau. Babu iso tsakaninsa da sashen Mahaifiyarsa, don haka ya fara shiga ya duba lafiyarta tare da shaida mata hukuncin da ya yanke a kan Ma'aikatarsa. Ummi Aysha jin abin tayi banbarakwai yau Sulaim ya shaida mata wani yunƙuri nasa akan dukiyarsa, dariya ta saki tana nuna jinɗaɗinta, kafin addu'o'in nasara su biyo baya. Domin ƙaramai ƙarfin gwiwa ta ce; "Da Abduh yana raye, wannan yunƙurin naka sai ya zama babban abin alfahari a gareshi, Allah Ya kai rahama kabarinsa" A hankali Sulaim ya ce; "Amin" Ƙwarin gwiwarta gareshi sun taɓasa don haka ya share sama da hour a sashenta, tana yi mai hira yana murmushi. Ya yi godiyan tare da nuna jindaɗin yabonta akansa. Ummi Aysha bata barshi ya tafi ba sai da ta shiryamai abu mai sauƙi ya sawa cikinsa. Ummi Mairam; leɓunanta har rawa suke yi saboda maganganun da suka cika bakinta da zuciyarta, bayan surutun da take yi lokaci zuwa lokaci ita ɗaya. Tana jin tsayuwar Motar da take kyautata zaton Sulaim ne ta miƙe da sauri. Saboda rawar jikin tarbarsa har tuntuɓe ta yi, bai lura ba balle ya tareta don haka ta kife ƙasa. Bata damu ba ta miƙe tana kama hannunsa zuwa ɗaya daga cikin Couch ɗin dayake parlon. Babu cikakken nutsuwa balle karantar yanayin mutum ta fara zazzago abubuwan da suka daɗe suna damunta. Bayan ta gama ta sako masa zancen Barirah kamar wacce ake kora.. Ɗan nisawa Sulaim ya yi sannan ya ce; "Bansan mai irin sunan da kike magana akai ba, amma maganar ya tsaya a iya na yau, ba ni da muradinsa" Da sakakken leɓunanta da yawu ke ƙoƙarin biyowa Ummi Mariam take bin Sulaim da kallo. Ɗan raɓo jikinsa mai ƙamshi yayi ya ɗan rungumeta sannan ya bar sashen. Mahaifinta da ke laɓe ya na jin komai da sauri ya fito, dalilin haka yasa tayi saurin shanyen yawun da yake ƙoƙarin zubowa gaban rigarta, kafin ta fashe da kuka.. SASHEN UMMU MALIK Bayyanar Sulaim a ɓangaren Ummu Malik ya ƙara tsuma soyayyarsa a zuciyar Barirah, tare da bawa Simbi ƙarfin gwiwar ƙulla Abota da Naila.. Kamar yadda bai naimi iso a sashen Mahaifiyarsa ba haka ya nufi sashen su Naila. Har bakin ƙofarsu Driver ya kaishi, kafin ya kaiga saukowa mai tsaron ƙofar har ya danna alamar zuwan baƙo... Kaka ce ta buɗe, ta na ganin Sulaim ta saki fuskarta, har tsakiyar living room ɗin tayi masa Rakiya, kunyar jin sautin faɗuwar cokalinta da suka ji jiya na kamata, Naila da batasan da zuwansa ba, daga madafi ta fito hannunta riƙe da kofi mai kyau, haɗin kayan marmari ne a ciki tana sha, tana bawa Kaka labari.. Sauyin ƙamshin living room ɗinsu yasa ta fara raba idanuwanta, tana ganinsa ta tafi da gudu ta zauna a gefensa tana dariya. Kaka dake kallon Talabijin da rabin ido ɗaya rabin a kansu dariya ta saki. "Ina wuni" Naila ta faɗa tana kallon fuskarshi, lumshe mata ido ya yi alamar ya amsa. Idon da ya amsa dashi ta kalla kafin ta saki dariya. Naila har cikin zuciyarta ta ce; "Idan ka tafi zan yi ƙewar idanuwanka" Sulaim ƙara zaresu ya yi yana juyasu. Dariya mai ban sha'awa Naila ta ƙyalƙyale da shi. Shima murmushin ganin farin cikinta ya saki yana karɓar kofin hannunta. "You prepared the fruits yourself?" Ya tambaya ya na jiran amsarta. Da sauri Naila ta amsa. Ba tare da naiman wani cokalin ba ya kai cokalin ciki bakinsa.. Ɓata fuska ya yi yana girgiza kai alamar babu daɗi, a haka ya shanye yana girgiza kai, Naila da ta gane wasa yake yi mata, madubi ta mayar da shi tana murmushi. Kaka tuni ta daina fahimtar abinda take kallo, gaba ɗaya hankalinta da rabin idonta yana kansu.. Naanah ya kira Video call, ya kamo hannun Naila ta dawo kusa da shi sosai. Naanah murmushi take yi tana kallonsu. A hankali ya ce tayi guessing wacece wannan ya faɗa yana nuna Naila. "Naila??" Ta ambata da sigar tambaya. Ɗaga mata kai ya yi yana dariya. Tsananin kamanceceniyar Sulaim da Naanah yasa Naila ƙura mata ido, cikin kokwanto Naila take tambayar wacece ta haifesa "Naanah ko Ummi Aysha?" Dariyar mara sautin da Naanah ta jima ba tayi ba tasa, son Naila da burin aurensu da Sulaim na ƙara samun matsuguni a ranta. Sun ɗan jima suna waya don har da Kaka suka gaisa kafin su yi sallama. Da ya tashi tafiya har ƙofa Naila ta rakoshi. Sallamarsu taƙaitacciya ce, don haka Naila ta dawo ciki ranta fari fes... ★washe gari saƙon sabon waya da saƙon farin Takarda ya riski Naila. Da mamaki take kallon wayar da farin envelope ɗin, a tunaninta zamani yasa an daina rubutu a takarda sai ta hanyar waya da sauransu. Daƙinta ta shige ta kullo kanta. Saboda Yadda ta matsu da sanin abinda takarda ya ƙunsa bata wayar da aka aiko tare da shi ba. Ga abinda wasiƙar ta ƙunsa "WASIƘAR ALƘAWARI Amintata ƙalilan ce, saboda da Aminta ake kai mutum ƙasa. Inajin nutsuwa a raina tun ranar da na ganki Naila! Amma nutsuwata ba zata tabbataba har sai kinyimin alƙawari! Ba na ci ko sha daga kowa sai Naanah da Mahaifiyata, sai kuma Malik, da ke dana yarjewa. Bazan rabaki da Kaka ba, amma kiyimin alƙawari bayan Kaka bazaki Aminta da kowa ba, har ƙarshen rayuwarmu. Rashin Aminta ba yana nufin yanke zumunci ko ƙin kyautatawa amma yana nufin tsantseni da kiyaye sirri. Na koma da ƙewarki da sonki mara iyaka a cikin zuciyata Naila! ba kuma zan dawo ba har sai kin ɗauki alƙawari, domin ki fahimci girman alƙawarin da zaki ɗauka yasa na rubatashi da alƙami, ki kiranta har iyakar yadda zaki fahimta.. Idan baki gamsu ba, ki sanar da ni, hakan ba zai dakatar da ni daga kula dake ba har bayan rayuwarki da Ahalinki. SULAIM ABDALLAH" Naila ta maimaita karanta saƙon Sulaim ya fi sau uku, da ta rasa yadda zata yi sai ta nufi wajen Kaka. Kamar Kaka zata ƙumeta haka take kallonta kafin ta ce " da wacce dama Sartaj ya samu hanyar ciyar dake sihiri?" "Da damar amintar da mukayi da shi" Naila ta bawa Kaka amsa muryarta a sanyaye. "To ba Sulaim ko ni saikin ɗaukarmin wannan alƙawarin Naila"...✍🏻 Gobe Asabar hutu In Shaa Allah 🤗 [9/5, 8:52 PM] Maman Amatullahi: SASAAL 13 ƊAYYIB; kwanan su biyu aka sallamo Jalal da ɗauraren ciwo, domin ya ce shi ba zai yi zaman jinya a Asibiti ba. Har Jalal da Ɗayyib suka iso Gida zuciyar kowannensu a ƙuntacce cike da ƙudirin ramuwar gayya ko ta halin ƙaƙa. Babu wani mutum ɗaya da Jalal ya lamuncewa zuwa dubashi ciki harda Sarki Hammam. A ganinsa Sarki Hammam ba shi da wani amfani shi da fadawansa da mutanen gari baki ɗaya, tunda suka kasa kawo masa ɗauki ko ɗaukar mataki cin zarafin da Malik ya yi masa har cikin Gidansa. Sufyan kuwa sunyi masa mummunan shirin da duk ranar da Allah Ya ƙaddara haɗuwarsu sai dai wani ba shi ba. Bayan kwanaki Harajin da ya tashi hankalin kowa Ɗayyib ya ƙaƙabawa Kasuwar Tukwanen Zinare. Mutanen gari har gaban Sarki Hammam suka kai kokensu. Sarki Hammam haƙuri yasa aka ba su tare da yi musu alƙawarin duba kokensu. Da dare yayi Sarki Hammam ya buƙaci ganin Ɗayyib a keɓantaccen wajen hutawarsa. Ba a matsayin Ɗan uwa ya bashi Umarni ba a matsayinshi na Sarkin Yankinsu ya bashi umarnin ya janye harajin da ya ƙara ƙaƙabawa Mutanen Yankin. Ɗayyib bai cewa Sarki Hammam komai ba, har ya tashi daga gurin, ɓakar zuciyarsa na suya. ★washe gari gaggamin ɓata garin wasu Yankunan Ɗayyib ya gayyato suka zo suka shafe duk wasu rumfuna na Kasuwar. A take suka kewayeshi da guntun langa-langa, aka fara fitar da ɗakuna a ciki. Dattijawan Yankin ne suka yi gangami har cikin filin, Ɗayyib yana zaune fuskarsa a ɗaure kamar an musanyoshi. Cikin Taushin harshe Dattijon da ya jagoranci gangamin ya ce; "Ka tuna wannan filin magajinsa Abduh Dhahab tuni ya sadaukar mana da shi a matsayin Kasuwar da zamu gina Yankinmu ta hanyar samun kuɗin shiga, nuna iko da kangeshi domin buƙatar kanka kai kaɗai rashin adalci ne Ɗayyib, kuma zaka tauyemana rayuwarmu har da na Ƴaƴanmu da jikokinmu da zasu so nan gaba." Ɗayyib gyara zamansa ya yi, yana jin kamar ya zaro wuƙar jikinsa yayi gutsi-gutsi da naman jikin su. Muryarsa babu alamar tausasawa, haka kalaman da yake shirin furtawa kalamai ne masu tsananin kaushi da ya tane da su ga duk wanda ya ƙalubalanci kuɗirinsa ya ce;. "Na yi muku uzuri, amma ku sani daga ranar irinta yau duk wanda ya ƙara yunƙuri dakatar da ƙudirina ko ƙalubalantar hukuncin da na yanke wallahi sai na yi ajalinsa na rantse bazanyi kaffara ba. Sannan ku sani wallahi ko da Abduh zai dawo a raye bai isa ya ƙwace wannan filinba" Ƙosassun Motocin Malik da aka yiwa ƙira mai ƙwarin hawa tsaunuka ne suka kunnawa Yankin kai. Ɗayyib na cikin surutansa na cin mutunci ga Dattijawan Yankin, Motocin suka biyo takan langa-langar da dama tsofaffi duk sun ji jiki. Da gudu Ɗayyib ya miƙe ganin Motocin sunyo kansa gadan-gadan. Dai-daita parking Drivern Malik ya yi, ragowar suma suka dai-daita nasu a gefen na Malik. Baƙin gilashin fuskarsa Malik ya ɗan zame. Yana tafiya ya na faɗin; Waɗanda yasaka aikin su rusheshi da kansu a cikin daƙiƙu, su kuma koma Yankunan su kafin na juyo kansu. Babu gardama tunda Ɗayyib ɗin da ya gayyatosu ya fisu tsaurin ido ya zabura balle su, dasauri suka fara kwashe komai. Malik da har tsakiyar kan Ɗayyib yake kallo lokacin da ya matsa kusa da shi, dariyar mugunta ya saki yana shafa kan haɗe da kamoshi. Wata mitsitsiyar wuƙa mai ƙaifin gaske Malik ya zaro daga aljihun gefen wandonsa. Kan Ɗayyib ya saki ya koma fuskarsa da hannunsa ɗaya ya matse, nan take farar fuskarsa Ɗayyib ta yi jajir. Karon farko kenan da Ɗayyib ya ji tsoron da fitsari ya zubomai nan take a tarihin rayuwarsa. Sai da Malik ya kuma sakin dariyar mugunta, sannan ya rubuta mai sunan Sulaim ɓaro-ɓaro a gefe da gefen kuncinsa a rarrabe. Jini ne ya fara tsatsafowa yana biyo har gaban rigar Ɗayyib, su dama Dattijawa da suka tsaya da farko tuni suka gudu tunda suka fahimci Malik ne. Murmushi Malik ya yi ya ce; "Nasan baka da ilimin nasara, amma kaje wajen shaiɗanin da yake duba maka wayoyi da na'urorin mutane ya sanar da kai abinda na rubuta maka, zaka tuna wanene yakeson yi maka iyaka da ƙudirinka" Malik ya ƙarasa faɗa yana sakinsa haɗe da kama gefen rigar jikinsa ya goge wuƙarsa. Ɗayyib kuka ya saki yana jin fuskarsa kamar an watsamai wuta, shi da kanshi yasan shi mungune amma sai yake ganin kamar Malik ya fishi iya mugunta. Maimakon ya yi gida Asibiti ya wuce don yasan idan Jalal ya gansa a haka zuciyarsa ce zata buga ya mutu. Duk da azabar da yake ji bayan ya isa Asibiti mudubi ya ce su bashi, sanin matsayin Ɗayyib ɗin yasa suka naimomai Mudubi a gaggauce. Fuskarsa ya kalla kafin ya cewa Nurse ɗin; " karantamin abinda aka rubuta a gefe da gefen kuncina". A rarrabe Nurse ɗin ya ce Sul-aim, dukka da Nurse ɗin bai faɗa dai-dai ba, sai da gilashin hannun Ɗayyib ya suɓucewar da yayi kwatsa-kwatsa a ƙasa.... SUFYAN; walwalarsa gaba ɗaya ta ɗauke wasu lokutan sai ya ji kamar wayarsa tana yimai gizon Hindu Mahaifiyarsa tana kiransa. A haukace zai fara neman inda ya ɗora wayar sai ya ɗauko sai ya ga babu wanda ya kira shi. Wasu lokutan kuma sai yayi ta mafarkin ga su Ɗayyib da Jalal nan sun zo zasu kasheshi. Baya samun hutu ko sukunin zuciya ta kowani ɓangare, ga Sumaya da ta nace da kiransa. Shi kuma ya riga yayiwa kansa alƙawarin babu zaman aure tsakaninsa da ita, saboda Hindu Mahaifiyarsa tasha faɗamai Sumaya morarshin da take yi ne yasa take son shi, ba zai yarda da maganarta ba sai ranar da Allah Ya jarabceshi da Talauci.. Shirmen da ya farayi a wajen aikin ne yasa ya yiwa Kansa faɗan ya nutsu ya kula da aikin saboda shi kaɗai ne abinda ya rage mai. Wata rana bayan ya dawo daga wajen aiki saƙon Malik na mayar da Companyn Tukwanen Zinare tushen da aka ƙirƙiresu ya riskesa. Sam bai fahimta ba sai da Malik ya turomai dogon saƙo mai ɗauke da bayani dalla-dalla da ƙarin matsayin da ya samu. Rabonsa da farin cikin da zai bayyana dariyar dake fita tun daga ƙasar zuciyarsa har ya manta sai da ya karanta saƙon Malik. Ya murmusa ya dara yayi surutai shi ɗaya tunda bashi da abokin gayawa. Ƙewar Mahaifiyarsa, da tuna burin kafuwarsa da yayi sanadiyyar ajalinta yasa shi fashewa da kuka. Ga shi zai zama mutumin da kowa zai so ya dama da shi, zai zama abin kambabawa a Yankin Tudu kamar yadda ya jima yana buri, amma mai tayashi kokawar cikar muradin nasa ƙasa ya lulluɓe idanuwanta, inama da tana raye.. ya faɗa yana tuno Fuskarta. NAILA; "Na yi alƙawai Kaka" Naila ta faɗa jikinta a sanyaye. Hannunta Kaka ta kamo, itama cikin sanyin da ya haɗe da tsoron rayuwar da za su iya fuskanta anan gaba tace; "Allah Ya baki ikon cikawa Naila, shima ki turamai saƙon kinyi alƙawari, ba iya na baki ba har cikin zuciyarki, Allah Ya na tare mu kinji" A hankali kamar mai raɗa Naila ta ce; "Kaka kina ganin alƙawarin bai yi tsauri da yawa ba, kar wata rana ya canzamin bayan na guji kowa" "Wa kike da shi bayan ni Naila? Wa zaki aminta da shi bayan ni? Ba fa zumunci ya ce karkayi ba, bai ce karki kyautatawa kowa ba, to me kike nema? mai kike yiwa fargaba?" Kaka ta faɗa tana kallon Naila da tayi ƙasa da kanta. A hankali Naila ta girgiza kanta alamar babu komai. A jiyar zuciya Kaka ta sauke ta ce; "maza tashi kije ki turamai saƙo". Ɗaukar alƙawarin Naila shi ne mafarin soyayyar mai ƙarfi tsakaninta da Sulaim. A hankali ta fahimci Sulaim wani irin so yake yiwa abu da iyaka yardarsa da dukiyarsa da kuma zuciyarsa. Wa su lukutan haka zai kirata ya yi ta kallonta ba tare da yacemin komai ba. Ciwonsa, damuwarsa farin cikinsa duk Naila ta karance su, maganganunsa ƙalilan ne, amma kulawarsa gareta ba shi da iyaka. Yana yawan tunamata har yanzu bai daina jinsa a matsayin Maraya ba, duk da Ummi Aysha tana raye amma rashin samun kulawarta tun farko da rayuwar gwagwarmayar da yayi bayan mutuwar Mahaifinsa, yasa yake jin kansa a wannan yanayin. Amma idan yana kallonta ko yana saurarar muryarta sai ya ji kamar Mahaifinsa ya na raye a kusa da shi bai mutu ba, dalilin raɓar rayuwarsu da tayi lokacin da babu wani abin nishaɗi a cikinsa sai kaɗaici. Bani da matsala da Ummi Aysha duk ƙarshen sati sai ta aikomin da kyaututuka na musamman. Motoci daban-daban da Driver Mace Sulaim yasa ake kai Makaranta a ciki masu kyau da tsada. Komai na daya dangi Naila ƙarara Sulaim yake nuna muhimmancinsa ga kowa. Cikin watanni su Naila suka yi wani irin kyau ita da Kaka. Tsakanin Naila da Yasar sai dai su gaisa da ƴan uwansa da Iyayensa domin duk yadda ta kaiga ƙoƙarin dawo da zumuncinsu na baya sam Gasar bai bata haɗin kai ba, acewarsa ta fi ƙarfinsa yana tsoron kar yin waya da ita ya kawowa aikinsa matsala. Ba don Naila t so ba haka zumuncinsu ya yanke da Yasar, kamar bamu taɓa sanin juna ba a baya. Wata ranar sati Simbi ta kawowa su Naila ziyara. Basu wani saki jiki da ita ba har ta tafi. ★washe gari ta ƙara dawowa, yadda ta saki jiki da fuskarta abin ya ƙayatar da su Naila, har hirar Yankin Tudu ya fara shiga tsakanin su. A cikin wannan satin kullum da daddare Simbi a sashensu takeyin dare, su na hira da Kaka wasu lokutan har da Naila. A cikin sati biyun da suka biyo baya shaƙuwa ya fara shiga tsakaninsu da ita, a kwai wani dare ma a sashensu ta ce zata kwana, Naila ta yi yunƙurin kaita wani ɗakin daban amma ta nuna bata da matsalar kwanansu ɗaki ɗaya. A tunanin Naila barci ya ɗauke Simbi don haka ta zubo abinci ta kira Sulaim video call. Babu jimawa fuskarsa ta bayyana yana sanye da Pyjamas alamun ya shirya kwanciya. Kamar kullum da ta gaisheshi bai amsa ba sai ido da ya Lumshe ya aikomata da sumbatar daya sata sakin dariya. Tashi ya yi ya zauna, yanayin fuskarsa na sauyawa haɗe da buɗe dukka girman idanuwansa da bai fiyayi ba. Dariyarta Naila ta gimtse tsoron sauyin da ban taɓa gani daga garesa ba na shiga zuciyarta. kamar daga sama ta ji saukar maganar da banyi tsammani ba daga bakinsa; "Ina jin idon mutum a kaina, wacece a ɗakinki Sa'aadati?" [9/5, 8:52 PM] Maman Amatullahi: SASAAL 14 Wani irin bugawa zuciyar Naila ya yi. Dariyar yaƙe ta ƙaƙalo kafin ta ce; "Ido kuma bayan nawa?" Bayason ya ƙarayin magana don haka yayimata sallama kamar komai bai faru ba. Yana katsewa Naila ta juya gefen da Simbi take kwance da sauri, amma sai taga Simbi ba ma gefenta take kallo ba, kuma ba taji alamun motsin juyawarta ba. Ajiyar zuciya ta sauke amma duk haka ta kasa cin abincin da ta zubo sai kitchen ta mayar da shi. Har tsakiyar dare Naila ta kasa runtsawa, living room ta fito ta haɗa kanta da gwiwarta ta fashe da kuka. Tsoron gayawa Sulaim gaskiya take yi kar ya ce yarda da Simbi ne yasa ta barta har ta kwana a ɗakinta. Kasa jurewa tayi ta koma ta kullo ɗakin ta waje sannan ta kira shi Video call ko Allah zaisa ya ɗaga. Bai ɗaga ba, kuma bata daina kira ba, har barci ya ɗauketa. Ba tafi hour uku ba ta farka, ƙara ɗorawa ta yi da kiransa, cikin sa'a ya ɗaga. Yana zaune idanuwansa da barci sosai a cikinsu don haka ya rage girmansu kamar baya kallonta.. "Kayi haƙuri" Naila ta faɗa tana fashewa da kuka haɗe da dafe bakinta. Bai ce mata komai ba sai wayan da ya kai saitin laɓɓansa ya sumbata sannan ya ɗan saki murmushi. Ta yi tunanin zai tambayeta dalilin da yasa take bashi haƙuri har da su kuka, sai ta faɗamai gaskiya, amma sai ta ji bai tambaya ba. Maimakon haka da muryarsa da ya ɗan yi nauyi ya ce; "Kalli yadda kike kuka Sa'aadati, matso daina kuka faɗamin menene?" Ido Naila ta rintse tana jin soyayyarsa kamar ya yi mata yawa. Kai ta girgiza saboda ta kasa cewa komai. Murmushi ya yi kaɗan yana shafa sumar kanshi kafin ya ƙara sumbatar wayar. Noƙe kafaɗa Naila tayi alamar ba wannan take so ba. Girarshi ya ɗage alamar tambayar "dagaske?" Ɓata fuska tayi tana sosa hancinta. "Babu laifin da zakiyimin, na kasa hukuntaki Sa'aadati, saboda ina sonki, son da babu rabuwa, amma karki bari ta ƙara kwana a Ɗakinki kinji" Naila da sauri ta ɗaga kai, tana share hawayenta. Mamakin yadda yasan Simbi tana ɗakinta na kamata amma babu damar tambaya. "Ki je wani ɗakin ki kwanta" ya faɗa yana jingine wayar a saitin fuskarsa Fara buɗe Simbi Naila tayi Sannan ta shiga wani ɗakin ta kulle har lokacin Sulaim yana kan layi. Kwanciya tayi ta duƙunƙune cikin abin rufa tana kallon yadda yake kallon wani waje daban da alama labarai ko wani abun yake kallo mai muhimmanci. Yanayin fuskarsa da babu wasa sam sai yana kallonta na matuƙar birgeta, takan ji a ranta kamar tafi kowacce ƴa mace Sa'a. "Na gama" Naila ta faɗa tana kallosa hankalinsa ya maido kanta. Maimakon ya yi magana, sai ya yi mata alamar da hannu ta matso. "Ta ina zan matso" Naila da faɗa tana dariya. Shima murmushi ya yi, kamar yadda ya saba ya kai wasu daƙiƙu yana kallonta, sannan yaƙara sumbatar saitin inda goshinta ya bayyana a tasa wayar. A kunnen Sulaim Naila tayi addu'a kafin ya mata alamar ta jingine wayar tayi barcinta. A kan Bedside lamp ta jingine wayar. Sanin waya ɗaya ne a tare da ita yasa ya kunna karatun Abdurrahman Bin mus'ad ta ɓangarenshi haɗe da rage sautin labaran da yake ji. A hankali sanyin sautin karatun Alqur'anin yake shiga kunnen Naila yana sanya mata nutsuwa a cikin zuciyarta, tun tana ɗan buɗe ido tana kallon gefen fuskarsa idan tayi sa'a ya juyo suka haɗa ido ya aiko mata da sumba har barci mai daɗi ya ɗauketa. Sai da ya tabbatar barcinta yayi nisa sannan ya katse kiran. SULAIM Tun bayan komawarsa Kahala Noorhan ta fara ziyartarsa babu dare babu rana. Bai ɓoyemata ya rabu da ita ba, amma sam ta nuna wallahi bai isa ba, ita zai rainawa hankali ko ya ɗauko ita irin Matannan ne da Namiji zai so a lokacin dayaga dama kuma ya rabu da su a lokacin dayaga dama?. Ko don yaga yana da kuɗi? Ita babu inda zata je idan zai dawo hankalinsa ma ya dawo. Duk mitar Noorhan da kalamanta masu kama da nuna iyaka ko gadara Sulaim bai taɓa kulata ba. Lamarin su yayi ƙaramari ne data fara binsa har office da duk wani wajen taro da zai je sai ya ganta a harabar wajen, hatta Asibiti wajen Naanah zuwa takeyi ta zauna a harabar wajen. Kuma duk haɗuwar da zasuyi sai ta biyosa har jikin mota tana mita. Bai taɓa sawa a wuƙantata ba. Noorhan anata ganin Sulaim ya ƙyaleta tana cimai zarafi ne don yasan ba shi da gaskiya kuma itama Mahaifinta ai mai kuɗine. Ranar da ta kaishi ƙarshe ta biyoshi har cikin office tana zage-zage, kai tsaye ƙararta ya shigar kan shiga haƙƙinsa, cin zarafi, takura da ɓatamai suna. Abu kamar wasa Sulaim ya nuna mata ikonsa da dukiyarsa da take ganin kamar zasu aunu a ma'auni ɗaya da na Mahaifinta. Da kuka da magiya tare da alƙawarin ɗauke Noorhan su mayar da ita Lebanon Iyayenta suka shawo kan Sulaim ya janye ƙarar da ya shigar.. Wannan ne sanadiyyar fitar Noorhan daga cikin rayuwarsa. Al'amarin Naila gareshi babba ne, domin ba iya kallon Matar da zai aura yake yi yiwa Naila ba, harda kallon aminiya ƙanwa kuma uwar ƴaƴansa yake mata. Babu rabuwa da ita a tsarinsa amma ya lura Naila sam bata da wayo, kuma ita mutum ce da zata iya sadaukar da farin cikinta don na kusa da ita yaji daɗi, da wannan damar Simbi take neman shiga jikinta. Tun zuwanta Simbi sashen a ranar farko labari ya riskesa, ba shi wani makusanci da ya yarda da shi ɗari bisa ɗari, domin ko Malik akwai wanda kawai aikinsa lura da motsin Malik ne , ba tare da shi kanshi Malik ɗin yasan da zamansa ba sai manyan Securities ɗin Dhahab, domin a matsayin mai bawa shukoki ruwa yake rayuwa a Gidan. Saukar numfashin Simbi da yasan tana fitarwa ne da gan-gan ya bashi tabbacin tana ɗakin kamar yadda aka bashi rahoton tunda ta shiga sashen bata fito ba. Idan ya yiwa Naila kashedi akanta har sau uku bata ji, to zai yimata hukuncin daya dace da ita... SIMBI. Tana sane ta dinga fitar da numfashinta da ƙarfi saboda tasan waye Sulaim, ba zai taɓa son kwanciyarta a ɗakin Naila ba, kuma gaskiya ya faɗa lokacin daya bayyana akan screen ɗin wayar Naila, idanuwanta ƙuri suke akansa sai dai dayake bata saitin Camera shiyasa bata fito ba, a hankali ta juya domin tasan dole Naila ta waiwayota bayan ya katse kiran. Da Naila ta kullota a ɗaki dasauri ta miƙe ta ɗauki ɗayan wayar Naila da ta bari. Babu password babu komai sai Apps ɗin karatun Alkur'ani kala-kala har ta gama bincikenta bata ga komai ba, asalima babu layi akan wayar. ★washe gari bata tsaya jiran tashinsu ba ta tattara ta bar sashen. Tsaf ta zauna ta karya da Iyayenta har tana tsokanar Barirah da take cika tana batsewa. Bayan ta shiga Ɗaki Taswirar Dhahab da aka yiwa ado da kaloli ta manna shi a bangon ɗakinta take kallo. Zama tayi tana tunano irin dukiyar da Sulaim ya mallaka a iya ƙasar Abyad, amma ace Naila ita kaɗaice ta samu zama a cikin zuciyarsa. Mai zai hana ya ɗauko bare haɗiɗɗiya ƴar manyan mutane mai kyau da aji daga wata nahiyar ya aura? Naila fa? Naila ƴar Mahmoud madinkin da bai taɓa ɗanɗanar arziƙi ba har ya bar duniya. Ina laifin ma ya zaɓi Barirah tunda tafi Naila ilimi da wayewa.. Banbancin kishin Barirah da Simbi. Barirah mace ce mai faɗa saurin fushi lokaci, ɗaya da son cin zalin yara ta hanyar Dukansu tun tana yarinya ƙarama, son girma da mulki tun bata san zasu riski kansu a Babban Birnin Abyad ba. Amma bata da baƙin ƙishin cutar da wani ta hanyar sharri ko asiri, barta da masifa da ƙunci. Saɓanin Simbi bata da hayaniya amma wani irin kishi ne da ita daya haɗe da hassada, kuma akan cikar muradinta bata ƙi tayiwa mutum sharri ba, a baya hassada yasa take ganin wawtar ƴar uwarta akan son Sulaim duk da itama dama ne bata samu ba, amma yanzu da yake son Naila sai take ganin gara kawai ya je ya ɗauko bare. Naila da Barirah ba su dace da shi ba, ko kuma dai ya ɗauki Barirah ya rabu da Naila. Simbi har ta gama Makaranta bata yarda kina ƙawance da ita kiyi da wata ba, da zarar ta ganki da wata musamman wacce ta fita sai ta fara kishi, waɗanda ba su fuskanceta ba sai suke yimata kallon wata manufa daban.. ƊAYYIB Ko ina na jikinsa rawa yakeyi, sai da ya share mintuna goma bai dawo nutsuwarsa ba. Gumi kuwa kamar an watsamai ruwa suna zubowa yana sharcewa. Da sauri Nurse ya fito don kiran babban Likita kar Ɗayyib ya mace ba tare da yayi yunƙurin komai ba Fargaba yasa jinin Ɗayyib ya yi mugun hawa bayan likita ya gwadashi dole suka bashi gado. Da dare yayi Ɗayyib fitik-fitik ya yi sai sun sallamesa ya koma Gida saboda bayaso Jalal yaji labari ko ya ga fuskarsa balle yasan gaskiyar abinda ya faru. Bai nufi sashen Jalal kai tsaye ba sai da ya fara tsayawa a nashi sashen yayi wanka tukunna. Jiki a sanyaye ya nufi Sashen Jalal fargabar sunan da Malik ya rubutamai a kuncinsa har lokacin bai gama sakinsa ba, duk da yasan ba'a mutuwa a dawo. Ko da ya isa wajen Jalal ya tambayeshi game da aikin filin daya fara shiru yayi kamar bai ji sa ba, har sai da ya ƙara maimaita tambayarsa. Sannan Ɗayyib da har lokacin jikinsa yake a sanyaye, ya sanar da Jalal abinda Malik ya ce akan filin ya kuma saka an rushe komai. Shiru Jalal ya yi, yana runtsewa idanunsa, irin azabar da Malik ya ganamai na dawomai. Hukuncin da yake ganin shine mafita Jal ya sanar da Ɗayyib, na zuwansa wajen Bokan Tsaunin da shi kaɗai ya rage musu. A wannan dare Ɗayyib ya yi sallama da Jalal, ya koma sashesa ya shirya kayansa. ★washe gari da Asubahi ya saɓa jakarsa domin tafiya ƙasar Abyad, wajen ƙasurgumin Bokan Tsaunin da Jalal ya kwatantamai, a wajen wasu tsaunuka bayan garin Birnin Abyad... NAILA; Bayan ta idar sallar Asubahi alfijir ya fara ketowa ta kira wayar Sulaim kamar yadda ta saba. Ya ɗaga amma bai buɗe idanuwansa ba, jingine wayar yayi ya barta tana kallon fuskarsa. Naila kallonshi take yi tana murmushi kamar wacce ta samu matsalar kai. Farin hannusa ya miƙo, Naila ta na dariya da tai kai bakinta kan wayar dai-dai saitin inda hannun yake ta sumbata, shima murmushi ya saki yana gyara kwanciyarsa. Naila tana kallon Sulaim da idanuwansa suke kulle har ta koma kan gado ta jingine wayar, a haka Barci itama ya ɗauketa, wayar da kanta ta mutu bayan chajinta ya ƙare. Wannan shine daily routine ɗin Sulaim da Naila.. Da gari yayi haske, Kaka ta umarci Naila ta taso Simbi suyi Breakfast. Wayam ta samu ɗakin. Daga ita har Kaka basu wani damu ba, saboda kai tsaye tunaninsu kan wataƙila dan Kar ta takura musu ne tayi tafiyarta. Da yammaci sai ga Simbi ta ƙara dawowa, hirar tana son yin wani cos a makarantarsu Naila take yi musu, dan haka ta roƙi dan Allah idan zata je tayimata waya su fita tare.. Naila bata kowa komai ba a ranta, washe gari bayan ta kimtsa ta kira Simbi ta layin wayar da ta bata. Da Simbi ta fito Kai tsaye Driver ta hana shiga, ran Naila babu daɗi takeyiwa Drivern ƙorafin ɗaukar Simbi ai ba wani matsala ba ne, tunda Makaranta ɗaya zasu je. Abinda Naila bata sani ba Simbi bata da mai biyamata irin jami'ar da take zuwa, kawai tayi hakane saboda tasan labari zaijewa Sulaim, kuma ƙorafin Nailan akan lallai sai an ɗauketa tamkar Sulaim tayiwa tunda da yawunsa Drivern take magana. Driver zuwa tayi ta dawo, ba tare da ta ƙaracewa komai ba tace Simbi ta shiga su tafi. Har sun yi nisa Simbi tafara lalubar jakarta, tsaki ta saki tana faɗin; "Subhanallahi wallahi na manta takarduna a gida Please Driver ajjiyeni anan" "A'a mai zai hana mu koma ki ɗauko" Naila ta faɗa da zuciya ɗaya "Karki damu zan fita da motata kawai" Simbi da fuskar alhinin manta takardun da tayi a gida, acewarta sukayi sallama da Naila. Murmushi Simbi ta saki bayan ta sauka, tana ƙoƙarin lalubo wayarta don kiran Drivern su, Mota mai kyau ya tsaya a saitinta. Kyakkyawan matashine, farinsa har kashe mata ido yakeyi, yana tsayawa ya sauko ba tare da ɓata lokaci ba yana yi mata sallama. Fuskarsa take kallo har zuwa takalmin ƙarfarsa baƙi wuluk, baƙin har wani irin gizo yake yimata. Amma da yake taga alamar tarin dukiya a tare da shi, sai ta amsa sallamarsa tana ɗauke kai, amma zuciyarta cike da farin cikin babban kamun da tayi, wayancewa tayi da kiran Driver kamar bata damu da Mutumin da ya tare ta ba [9/5, 8:59 PM] Maman Amatullahi: SASAAL 15 SIMBI Cikin salo da iyayi take sanar da Driver ya taho mata da Motarta, haɗe da kwatantamasa inda take. Cikin ɗan kame fuska ta dawo da hankalinta kan Matashin da ya tsaya jiran ta gama amsa waya. "Barka da safiya Hajiya Simbi, ina fatan ban dameki ba ko?" Matashin ya faɗa yana kallon fuskarta. Daɗin muryarsa da daɗin da take ji acikin zuciyarta yasa ba tayi tunanin ina Matashin yasan sunanta ba. "Sunana Ɗayyib amma zaki iya kirana da Dee, ni mazaunin Babban Birnin Abyad ne, mamallakin kamfanin sarrafa shinkafa na D&J a Birnin Abyad, na ji daɗin haɗuwa da ke, ina fatan kema haka?" Matashin ya yi bayanin kansa a taƙaice yana karantar yanayin Simbi. Wani irin fari tayi da ido tana ƙaremai kallo, kafin ta saki murmushi tana miƙamai hannu alamun ya kawo wayarsa. Wayar hannusa ya miƙa mata yana murmushi. Ƙirar wayarsa da kyanta sam ba irin manyan wayoyin ƙasar Abyad ko ta ce na duniya gabaki ɗaya data Sani bane, "kenan ƙera mishi tashi akayi daban? Gaskiya na yi babban kamu, yau na fito a sa'a yaushe rabon da wani ya tare ni da sunan yana so na, hmm! gaskiya Allah Ya na so na" Simbi ta faɗa a cikin zuciyarta lokacin da take jujjuya wayar Dee a hannunta kafin tasamai Number wayarta. Tana samai, ya karɓi wayar ya juya ya shiga Mota. Simbi tayi tunanin tafiya zai yi sai taga ya fito da abu a nannaɗe a cikin takarda mai tudu da kauri. Sai da ya miƙa mata yana murmushi sannan ya ce; "Ga wannan kisha Ice cream babu yawa, sai na kiraki ko?" Ya ƙarasa faɗa yana yimata alamar kira da hannunsa. Kuɗin Simbi ta shafa, wani irin kuɗi ne dashi haka, da zai yimata kyautar kuɗi irin wannan daga haɗuwa?, "gaskiya na yi babban kamu" ta faɗa ƙasa-ƙasa tana murmushi Bayanshi tabi da kallo tana shafa kuɗin hannunta har ya shige mota ya tasheta yabar wajen. Daa Simbi tasan Ɗayyib ɗin Yankin Tudu lokacin da yake Matashi kamar yadda su Malik suka sanshi, da ganin fuskar Matashin da ya tsayar da ita kaɗai sai ya sata yin gudun da bata taɓayi ba, ko zuciyarta ta buga nan take. Amma maimakon wannan tsoron tunda ba sanin Ɗayyib tayi yana Matashi ba, sai tayi ta sakin murmushi har Driver ya zo ɗaukarta.. MALIK A ɓangaren Malik tun safiya yayiwa Yankin Tudu tsinke, domin duba yadda aikin Ma'aikatarsu ya ke gudana. Bayan ya yi sallar Magriba yana ƙoƙarin kimtsawa domin tafiya Masauƙi, kwatsam ya ji Muryar mutum a gefensa. Malik bai zabura ba, saboda bashi da tsoro ko ƙanƙani sai tsayuwarsa da ya gyara yana waiwayo gefensa. Sarkin tsafin Yankin Tudu ne ya bayyana a idon Malik. Malik bai ce komai ba sai tsayuwarsa da ya ƙara gyarawa haɗe da ƙara matse fuskarsa, cikin ƙasa-ƙasa da murya ya ce; "Mai kake nema? Mai ke tafe da kai yi bayani a gaggauce" "Yau kwana biyu da tafiyar Ɗayyib wajen Bokan Tsauni, ɗaya daga cikin Bokaye mafiya hatsari a Ƙasar Abyad, zai iya bayyana ba iya wajenku ba har a cikin Dhahab, Zai shafe Tarihin Dhahab da wanda ya kafata idan har ya bayyana a cikinta ba tare da an dakatar da shi ba, lokaci ƙalilan ne ya rage, ƙarin haske na wajen Simbi ƴar uwarka" Sarkin Tsafin Yankin Tudu yana gama faɗa ya ɓace. Motsi biyu Malik yayi shine ɗauko wayarsa da turawa Sulaim bayanin komai nan take. Idan Malik ya ce bai ji tsoro ba ya yi ƙarya, amma babu wani Mahaluƙi daya isa ya rusa Dhahab matsawar su na raye.. Tsoron da ke neman mamaye zuciyarsa ya fatattaka ya dannawa Driver kira. Cikin mintuna ƙalilan Driver ya ƙaraso. Bayan Malik ya shiga Mota saƙon Sulaim ya shigo wayarsa, gumin da rabonsa da yin irinsa ne ya shiga tsatsafomai mai yana sharcewa, hannunsa yana rawa ya dannawa Sulaim kira... NAILA A ɓangaren Naila bayan sun tashi, bata tsaya wani ɓata lokacin biyawa wajen cin abinci ba Driver ta dawo da ita Gida.. Kamar yadda ta saba bayan ta iso gida ta huta, wayar Sulaim tafara kira, amma har sau uku bai ɗaga ba. Tasan bazai wuce fushin tafiya da sukayi da Simbi Makaranta tare ba, ita gaskiya ta gaji, to so yake yi ta dinga wulaƙanta su tana nuna musu ita tafisu, gaskiya bazata iya ba. Kasa riƙe zancen tayi, ta fara bawa Kaka labarin ko ƙarasawa Makarantar fa basu yi ba Simbi ta sauka amma shine zai yi fushi har ya ƙi ɗaga kiranta.. Kaka bata tofa ba, a ganinta faɗan masoya ne zasu shirya daga baya. Naila har ta gama cin abinci bata daina mitar "gaskiya ni bazan jurewa wannan ƙa'idojin nasa ba" SIMBI A ɓangaren Simbi har takai gida bata daina murmushin babban kamun da ita yi ba. Tana isa cikin sashensu kai tsaye ɗakinta ta wuce har da kullo ƙofar ɗakin da mukulli gudun kar wani ya shigo ya ga kuɗin data samu, Surprise take son yi musu. Kafin ta shiga wanka sai da ta ɗan yaga takardar da aka lulluɓe kuɗin da shi taga Dagaske dai kuɗaɗe ba ɗan kaɗan ba. Dariya ta saki har da tsalle tana juyi. A ɗan hanzarce ta wuce Washroom tana juyi har da juya idanuwanta. Bayan ta fito daga washroom, kimtsawa tayi cikin kayan shan iska, da murmushi ta juyo don ɗaukar kuɗin ta fita da su ta nunawa Ummee da Barirah su ga irin Babban kamun da tayi, tana waiwayo inda ta ajjiye kuɗin sai ta ga wayam babu kuɗin babu dalilin sa.. kuyimin afuwa da guntun paji uzurine ya riƙeni, Na gode🙏🏻 [9/5, 8:59 PM] Maman Amatullahi: SASAAL 16 SIMBI; Dukka idanuwanta ta zaro tana dafe saitin zuciyarta da yake tsananin bugu. "Wanene ya shigomin ɗaki?" Ta tamabayi kanta tana kallon inda ta ajjiye mukullin ɗakin. Yananan yadda ta ajjiyeshi. Cikin sanɗa ta nufi ƙofar, ta murɗa a hankali, tana murɗawa ta ji shi a kulle alamar ba'a buɗe ba. Da sanɗa taƙarasa kusa da mukullin ƙofar tayi wuf ta ɗauke, hannuwanta na rawa ta zura ɗan mukullin, tana buɗewa ta fito a guje ta nufi hanyar ɗakin Ummeensu tana ƙwala Ihu kiran sunanta. A ɓangaren Ummu Malik daƙyar ta iya samun waje ta zauna, tunda Sulaim ya kirata da kansa ya sanar da ita naɗar duk wani motsin Simbi ko kalamanta, yana zargin ansamu matsala, kuma karta kirata ta bari har sai ta dawo. Abunka da zuciyar Uwa sai ta kasa sukuni, tana tunanin mai Simbi ta aikata da har zaisa Sulaim ya kirata a karon farko a rayuwarsu, tasan koma menene baƙaramin abu bane. Da ta ga tunanin zai yi mata yawa sai ta ɗoro alola ta tayar da Sallar nafila tun da lokacin ƙarfe 9:40 ne na safiya. Ba ta jima da idarwa ta ji ihu, kamar na Simbi. "Yaushe Simbi ta dawo gidannan bansaniba?" Ta tambayi kanta asarari tana miƙewa, bayan ta saita wayarta ta ajjiye a gefe. A bakin ƙofa suka ci karo da Simbi tana zare idanuwa. "Simbi! Lafiyarki kuwa? Wannan ihun naki ai sai ya firgita mutum" Ummu Malik taƙarasa faɗa tana kamota zuwa jikinta. Da rawar murya Simbi ta ce; "Ummee kuɗi saurayina ya bani, daga ajjiyesa akan gado na shiga washroom, ina fitowa naga babu kuɗin kuma wallahi na kulle ɗakin da hannuna" Da alamar tambaya Ummu Malik ta ce; "Saurayi kuma? Yaushe kikayi Saurayin da yake baki kuɗi bansani ba Simbi? Kina son ki fusata Yayanku ko?" Kai Simbi ta girgiza. Babu wani nutsuwa a tattare da ita take bawa Ummeenta labarin yadda suka haɗu da Ɗayyib. Da mamaki da tsoro Ummu Malik ta ce; "Ai Companyn masarrafin Shinkafar D&J da ke Birnin Abyad na Mahaifin Bushra ne, anya ba Ɗan damfara ko Aljani kika haɗu da shi ba Simbi???? Sai a lokacin ta gano ina Sulaim ya dosa, ashe baƙaramin matsalane yake ƙoƙarin kunna musu kai ba. Hannunta da yake rawa tasa ta janyo wayarta, duk bayanin da Simbi take koromata sam ba ta fahimta har sai da tabbatar saƙon Muryar Simbi data naɗa ya isa ga Sulaim.... SUFYAN; A ɓangaren Sufyan tun bayan samun saƙon Malik ya ke cikin farin ciki, ƙuncin da yake fama da shi kwana da kwanaki sai ya kau, hankalinsa ya mayar kan kammala ayyukan da suka ragemai bai ƙarasa ba. Ba su taɓa haɗuwa da Kabeer sun yi gaisuwar dake nuna sanayya ko abota a tsakaninsu shekarun baya ba. A matsayin Ubangidansa kullum yake gaishe da Kabeer. Bayan sati ɗaya, yana zaune a office kiran Kabeer ya shigo ta wayan ofishinsa. Bayan ya ɗaga Kabeer ya shaidamai yana nemansa idan ya gama abinda yake yi. Sufyan ji yayi gabaki ɗaya aikin da yake yi a lokacin ya fitarmai daga rai, burinsa kawai ya ji, wani babban daliline zai sa Kabeer ya nemesa a irin wannan lokacin. Bayason Kabeer ya yi zargin wani abun ko nuna zumuɗinsa kan kiran da ya yi mai, wannan dalilin yasa ya danni zuciyarsa yaƙara Minti Talatin kafin ya miƙe. A gaggawace ya nufi ofishin Kabeer da ya jima da sani, amma bai taɓa samun damar shiga ba. A ɓangaren Kabeer Babu kowa a ofishinsa sai shi ɗaya yana danna wayarsa. Naiman izinin shigowar Sufyan ne yasa shi ajjiye wayar a gefe yana ba shi izinin shigowa. Kamar yadda suka saba gaisawa haka suka gaisa bayan Sufyan ya zauna a kujerar da ke fuskantar na Kabeer. Gyaran murya Kabeer ya yi sannan ya ce; "Jiya na haɗu da Mahaifinka Ɗayyib amma shi bai ganni ba, ina tunanin zai iya riskarka a kowani yanayi, kuma ina gudun abinda zai biyo baya, mai zai hana ka dawo wajenmu da zama, kafin saƙon ganinsa dana tura ya isa ga Sir Malik". Tun lokacin da Kabeer ya ce ya haɗu da Mahaifinsa, Sufyan ya sunkuyar da kansa ƙasa Cikin kuka Sufyan da yake ganin kamar gashi ga ajalinsa ya ce; "Idan har ya samu ƙwarin gwiwar isowa Babban Birnin Abyad menene ya ragemin Kabeer, Gara na tsaya ya kasheni duk guje-gujena wata rana zai riskeni ya kasheni, Kabeer tsoro nake ji" Tasowa Kabeer ya yi ya matso kusa da shi yana lallashinsa... NAILA; A ɓangaren Naila har ta gama mitarta ta shige Ɗakinta Kaka bata tanka mata ba. Kasa jurewa tayi bayan ta shiga ɗaki, ta ƙara neman layin Sulaim amma ba'a ɗaga ba. Jifa ta yi da wayar tana hura siririn hancinta. A ganinta zaƙewar Sulaim ya yi yawa, tayaya zaisata ta guji Simbi alhali shi yana tare da Yayanta dare da rana ta waya? So yake yi ita tayi baƙin jini kenan?.. ta tambayi kanta. Babu kalar tambayar da Naila bata yiwa kanta ba kafin ɓarawon barci ya sace ta. Ba ta farka ba, sai gab da Magriba shima Kaka ce ta tasheta. Bata jima da yin wanka ba aka kira Sallar magriba a masallacin Dhahab. Dama tayi alolarta bayan ta yi wanka. A ɗakinta tayi sallah saɓanin daa da takeyi a ɗakin Kaka. Bayan ta idar gajeran saƙo ta turawa Sulaim tana tsimayin kiransa. Tana zaune har aka kira Sallar ishsha'i amma Sulaim bai kira ba, zuciyarta babu daɗi ta miƙe ta tayar da Sallah. A ɓangaren Kaka. Ta yi mamakin rashin fitowar Naila , amma da ta tuna ƙorafin Sulaim da ta wuni tanayi tun bayan dawowarta daga Makaranta ta gane dalilin maƙalewarta ta a ɗaki. Dama sararin yin waya Kaka take nema, don haka ta kulle ɗakinta ta kira mutanen Yankin Tudu, don jin labarin abubuwan da suke wakana. SULAIM; A ɓangaren Sulaim tun lokacin da aka sanar da shi, Naila ta kafe dole sai sun tafi Makaranta tare da Simbi ya ce abi bayansu. Sulaim ya samu labarin Saukar Simbi daga Motarsu Naila da murmushi akan fuskarta, sannan bayan ɗan daƙiƙu wata Mota ta tsaya a gefenta. Amma har wanda ya bi bayansu ya share mintuna kusan goma daga inda yake zaune cikin mutanen da suke hada-hadarsu bai ga kowa ya fito daga cikin Motar ba, sai Simbi da ya hango tana magana ita kaɗai bayan tagama amsa waya. Bayan ɗan wani lokaci, ya ga motar ta bar wajen ba tare da kowa ya fito daga ciki ba, bayan tafiyar Motar, Motar gida ya iso ya ɗaukarta... Bayan Sulaim ya gama saurarar bayanin wanda ya tura, Bayanin Drivern da take kai Naila Makaranta ya shiga ya duba. "Simbi ta sauka ne dalilin manta takardun Makarantarta a gida kamar yadda ta ce" yana gama karantawa ya rintse idonunsa. Bai yi ƙasa a gwiwa ba a wannan tsakankanin ya kira Ummu Malik.. Duk kiran da Naila take yi bai san ma tanayi ba saboda kansa da ya ɗau zafi. Ba shi da niyyar ramuwar gayya a cikin zuciyarsa, amma yana ganin idan bai motsa ba, babu abinda zai hana burin Jamil na shekaru aru-aru cika akansa, tunda yanzu shi kaɗaine ya rage sunyi nasarar kashe ragowar. Abokanan Kasuwancinsa ya fara kira, su naimo mai Babban Islamic scholar kafin dare ya rufa. Sallah ce kawai take tashinsa daga inda yake, tsabar kallon System idanuwansa har jaa sukayi. Bayan Magriba da saƙon Malik ya riskesa na batun Sarkin Tsafin Yankin Tudu sai ya ƙara tabbatar da mai siffar Ɗayyib aka turo, domin yayi amfani da Simbi wajen rusa Dhahab tunda zuciyarta cike take da ƙyashi da hassada. A wannan dare Sulaim ya shirya tafiya ƙasar Abyad. Sai da ya yazo kwanciya sannan ya tuna kwata-kwata bai kira Naila ba tun wayar Asuba da sukayi. Yana ɗauko wayarsa da suke waya da shi ya samu miss calls ɗinta rututu. Ɗan murmushi ya yi, a zuciyarsa yana faɗin "Allah Ne kaɗai yasa kukan da zatayi da irin zagin da zansha a wajen Kaka" Bayan ya danna kiranta ya jingine wayar yana jiran ɗagawarta.. NAILA; A ɓangaren Naila kukan takaici tasaka, baa ta alaƙanta ƙin ɗaga kiranta da Sulaim ya yi da komai ba, sai don ya nuna mata ita ɗin ba komai ba ce, amma har wani irin laifi zatayi mai da zata kirasa kusan sau talatin yaƙi ɗagawa? Da lallashin Kaka ta ci abincin dare tana ci tana ƙorafin rashin ɗaga kiranta da Sulaim ya yi, har ta gama mitarta kamar kullum Kaka bata tofa mata ba. Naila ta yi tunanin lamarin zai zo mata da sauƙi bayan ta koma ɗaki ta manta komai ta kwanta tayi barcinta hankali kwance, amma sai ta ga lamarin ya gagareta. Tana cikin jan tsaki kiransa ya shigo mata... [9/5, 9:01 PM] Maman Amatullahi: Nafisat Aliyu Sasaal Page 17 NAILA; Hannunta yana rawa ta janyo wayarta, zaman hular kanta ta gyara saboda video call ne. Sai da ta ɓata fuska sannan ta ɗaga.. fuskar Sulaim ce ta bayyana yana kwance. Murya ciki-ciki Naila ta ce; "Barka da dare" Sulaim bai amsa mata ba ya ce; "Kin jini shiru ko, aiki ne ya riƙeni ina fatan kina lafiya" Sai da Naila ta marairaice fuskarta sannan ta ce; "Nasan babu wani aikin da ya yi maka yawa kawai kaƙi ɗaga kirana ne, saboda munje Makaranta tare Simbi, ban san maiyasa kake son shafamin baƙin jini ba, bayan kai kullum kana tare da Yayanta" A ɓangaren Sulaim lumshe idanuwansa ya yi yana saurararta Har ta ɗisa aya bai ce mata komai ba. Naila jin Sulaim ya yi shiru kamar ma baya kallonta sai ta fashe da kuka tana mitar ita fa ba wai aminta tayi da Simbi ba, kawai mutunci suke yi, a matsayinsu na ƴan Yanki ɗaya. Sulaim dai bai ce mata komai ba, har sai da ta haƙura tayi shiru dan kanta sannan ya ce; "Me kikeso Nailaa bayan alƙawarin da kika ɗaukarmin?" Da sauri Naila ta share hawayenta ta ce; "ka barni muyi zumunci Ni da Simbi" Sulaim idonsa da sukayi ɗanyi jaa ya buɗe saɓanin daa da suke lumshe ya na kallon fuskarta, sun kai wajen minti ɗaya haka yana kallonta tana kallonsa sannan a hankali ya furta; "Na barki Naila shikenan?" Kai Naila ta ɗaga, alamar eh tana murmushi, "kamar sunana na ji ya kira" ta tambayi kanta a cikin zuciyarta. Maganarsa ce ta cire mata kwakwanton da take yi a cikin zuciyarta; "Na gaji Naila da safe zan kira ki, anan Kahala yanzu dare ya raba" Da rawar murya Naila ta ce. "Maiyasa yau ka kiran sunana baka ce Sa'aadati ba, ko har yanzu fushi kake yi da ni" Sai da Sulaim ya ɗanyi murmushi sannan ya ce; "Na tambayeki me kike so bayan alƙawarin da kika ɗaukarmin, kika ce na barki da Simbi. kuma na ce na barki, karki ƙarawa kanki damuwa, Allah Ya tashemu lafiya" Da wani irin zare idanuwa kamar zasu faɗo ƙasa Naila take tambayarsa "ka barni? ka barni fa ka ce? to ai ban fahimci ka barni ba, kayimin bayani" Babu bayanin komai Sulaim ya datse kiransa. A ɗimauce Naila tafara kira layukan wayarsa amma yaƙi ɗagawa. Batasan sau adadi nawa ba ta kira layukan wayarsa a wannan dare ba amma sam bai ɗaga ba. Da dai ta fuskanci Dagaske bazai ɗaga kiranta ba Kuka ta rushe da shi tana dafe kanta. A ɓangaren Kaka ƙarfin kukan Naila ne ya tasheta daga barcin da bata jima da farasa ba. A ɗimauce ta nufo ɗakin, babu irin bugun da batayi ba amma Naila taƙi buɗewa. Kaka masifa da mitar maza ta kashe kanta ta fara yi tana cigaba da bugun ƙofar. Amma Naila tayi biris da ita. Har dare ya raba Kaka bata koma ɗakinta ba tana tsaye jikin ƙofar Naila tana lallashinta ta ɓude tunda tayi masifa da zage-zage bata buɗe mata ba. Gajiya Kaka tayi da tsayuwa da zama ta koma Ɗakinta, haushin kafiyar Naila na damun zuciyarta ★har washe gari da Safe Naila ƙin buɗe ƙofarta tayi, duk naci da magiyar da Kaka tayi mata bata buɗe ba, wannan dalilin yasa ta nufi Sashensu Simbi. SIMBI A ɓangaren Simbi daƙyar Umminsu ta kwantar mata da hankalin ta nutsu, amma gargaɗeta da ta kiyaye, kuma duk inda taga mutumin ta riƙe addu'a a bakinta karta ƙara kulashi ko da yayi mata magana. Har dare ya yi Simbi bata wani saki jikinta ba. Rashin sukuni da yadda ta dawo shiru-shiru ne yasa Barirah bayan ta dawo daga wajen aiki ta ce tazo ta rakata su je Siyayya. Ba don hankalin Ummu Malik ya kwantaba ta barsu suka fita. A motar Barirah suka bar Gidan. Wajan Siyayyar kayan shafe-shafe suka shiga, Barirah tana gaba Simbi tana binta a baya. Kamar ance Simbi ta waiwaya gefen hagunta ta hango Dee cikin shigar wasu kayan daban ba irin wanda ta gansa da shi da safe ba. Ya yi matuƙar yimata kyau a ido, tuni addu'ar da Mahaifiyarta ta ce tayi idan ta gansa ya bar kanta, burinta hankalinsa yayo kanta ta bashi labarin kuɗinfa da ya bata aljanun gidansu da batasan da su ba sun ɗauke. Tana so kuma ta tambayesa maiyasa bai kirataba, ta manta tsarin data saka wayarta na idan bata da lambar mutum ko ya kira ba zai zo ba. Maimakon Simbi tabi bayan Barirah sai tasha kwanar inda ta hango Dee. Tana kuwa matsawa tayi sa'a Dee ya hangota. A ɓangaren Dee da murmushi ya nufo Simbi da wani salon tafiya da zai ƙara siye zuciyarta. Da Muryarsa mai daɗin daya siye zuciyarta ya ce; "Barka da dare Gimbiyata Simbi" Ido Simbi ta lumshe, tana ƙanƙame wayar hannunta saboda daɗi. Murmushi Dee ya yi, kafin ya ƙara ce wa; "idan babu damuwa zamu iya tattaunawa daga waje" ya ƙarasa faɗa yana giftata ya nufi hanyar fita. Kafaɗunta Simbi ta ɗage dukka biyu tana juya idanuwanta kafin tabi bayansa. Tsayuwarsa Dee ya gyara lokacin da Simbi ta ƙaraso gefensa. Sai da yayi gyaran murya Sannan ya ce; "Wai wanene ya kafa Unguwarku, kyansa ya birgeni." Shiru Simbi tayi kamar bata wajen. Dee kansa ya ɗan dafe ya ce; " Ohh kiyi haƙuri naga kamar tamabayar bata yi miki daɗi ba, kyan Unguwar ne yasa na tambaya, amma kamar yanzu fuskarki tafi annuri Gimbiyata, da safe da muka haɗu kamar akwai abinda yake damunki ko kuma akwai wacce take son yi miki shishigi a cikin rayuwarki, kinsan ni ina da ƙwaƙwalwar saurin nazartar mutane, ko zan iya sanin wacece wannan, na taimakamiki da shawara ko wani abun?" Simbi, Dee ya sosa mata inda yake yimata ƙaiƙaiya, duk da tana ganin kamar bai dace su tattauna irin wannan matsalar daga haɗuwarsu ba, sai dai a cikin zuciyarta ji takeyi kamar ana ingizata. Zata yi magana kenan suka hango Barirah ta fito tana rarraba ido alamun ita take nema. Dasauri Dee ya kamo hannun Simbi ya dunƙulamata wani ɗan kulli, sannan a gurguje ya ce "Ko wacece ki sa mata a abinci zata koma inda ta fito ta bar muku Gidanku, amma baki faɗamin sunan wanda ya kafa Unguwarku ba" Da harshenta da ya yi mata nauyi ta buɗe baki zata bashi amsa Barirah data hangota ta ƙwala kiran Sunanta. Da saurin da ya bawa Simbi mamaki Dee ya shige tsakankanin Motocin dake wajen. Ƙullin da ya damƙa mata ta riƙe da kyau. Kafin Barirah ta ƙaraso tuni ta saita nutsuwar haɗe da zura ƙullin da Dee ya bata a ciki jaka. A ɓangaren Ummu Malik, bayan fitarsu Simbi, baifi da mintuna goma ba, Malik ya kirata kar a bari kowa ya fita, ya kira Securities su datse Dhahab ba shiga ba fita. Da fargaba take sanar da shi ai su Simbi da Barirah ba su jima da Fita ba, ihun salatin daya tashi hankalinta Malik ya saki, kafin ya ce takirasu kuma idan sun dawo babu shiga babu fita. Ko da su Simbi suka dawo Simbi bata gayawa Mahaifiyarta ta haɗu da Dee ba. Ummu Malik Kashedin da Malik ya ce ayi musu ta sanar musu jikinta a sanyaye. Bayan Barirah da shiga ɗakinta bakinta ta turo aganinta kawai izzar Malik ɗin ne ya motsa banda haka, maiyasa zai ce ba shiga ba fita Sai kace ana wani tashin hankali, ko don kawai an ɗaukewa Simbi kuɗi shine zasu takurawa Mutane. Ita ma Simbi ɗakinta shige ta kullo kanta ba tare da ta naimi jin ba'asin hukuncin Malik ba. Ƙullin da Dee ya bata ta fito da shi tana kallo, zuciyarta na kitsa mata kawai ta sawa Naila ta tattara ta koma Yankin Tudu, Sulaim ya auri Barirah ko ya samo wata can daban, sai dai tayaya zata sa bayan Mahaifiyarta ta sanar da su ba fita ba shiga? Ɗakyar ɓarawon barci ya saceta. ★washe gari suna cikin yin kari Kaka ta shigo, tunda batasan sharaɗin da Malik ya zana ba, kuma Securities basu hanata zuwa ba. Da magiya Kaka take yiwa Ummu Malik bayanin tanason Simbi ta biyota su lallaɓa Naila ta buɗe ƙofarta tun jiya ta kulle kanta taƙi fitowa. A zuciyar Simbi Allah-Allah takeyi Mahaifiyarta ta amince. Barirah kuwa tashi tayi tabar wajen tana taɓe baki. Sai da Ummu Malik ta ɗan nisa sannan tace Simbi ta ɗauko Mayafinta su je, amma karta daɗe ta dawo da wuri. Jikin Simbi har ɗan rawa yakeyi tabi bayan Kaka bayan ta soƙe ƙullin maganinta a ƙugu. NAILA; Kwana tayi kiran Sulaim, amma bai ɗaga ba, bayan Sallar Asubahi da ta ƙara kira sai ta ji wayar a kashe. Tabbacin Kaka bazata tankawa matsalarta ba ne yasa tayi biris da ita taƙi buɗe mata ƙofa. Bayan sallar Asuba da Kaka ta dawo tana ƙwanƙwasawa barci mai nauyi ya fara ɗaukarta . Ko da ta farka ta fito bata ji motsin Kaka ba, bata damu ba. Kitchen ta wuce ta haɗa ɗan shayin da zata iyasha. Tana cikin shan shayin Kaka da Simbi suka shigo. Sama-sama Naila ta amsa gaisuwarsu, tana cigaba da shan shayin dayake ƙona mata baki. Ƙin tashi Simbi tayi ta koma Sashensu. Guri ta naima kusa da Naila t ta zauna tana janta da hirar da ba wani amsar kirki take samu ba. Kaka dama Ɗakinta ta wuce, bata zauna ba. Naila surutun Simbi ne yake hawa kanta, sam bata son hayaniya tafison ta zauna shiru ko zata samo mafitar bawa Sulaim haƙuri. Naila tunanin tayiwa Ummi Aysha wani abu mai daɗi ta kai mata ne yazo zuciyarta, daganan sai ta sanar da ita abinda yake faruwa ko zata taimaka mata. Da ƙwarin gwiwarta ta miƙe ta nufi Kitchen, Simbi tayi wuf ta rufamata baya. Simbi tana maƙale a gefen Naila tana yimata hira, Nailan tana amsa mata sama-sama tare da cigaba da abinda take yi. Da salon dakar ciki Simbi ta ce; "Me kike haɗawa haka da safenan, ayi dani nima zanci" "To " kawai Naila ta ce ta cigaba da aikinta. Naila ji tayi kamar wayarta da ta bari a parlor yana ƙara, da sauri ta saki aikin tana addu'ar Allah Ya sa Sulaim ne. Bayan fitar Naila ta wannan damar Simbi tayi amfani, kafin ta biyo bayan Naila tana faɗin; "Yau na ga bakyason kulani, bari na koma Sashenmu sai anjima" Haushinta da Naila take ji yasa ko gefenta bata kalla ba ta cigaba da amsa kiran Abokiyar karatunta. Bayan Naila ta koma Madafi ta gama aikinta, wanka tayi ta shirya, har ɗaki tabi Kaka ta sanar da ita zata je ɓangaren Ummi Aysha ta dawo. Addu'ar a dawo lafiya Kaka tayimata. Yadda Naila ta samu sashen Ummi Aysha anata hidima ne ya sanyaya jikinta, bayan ta miƙa mata Snacks ɗin da ta nannaɗe da foil paper sai ta kasa faɗar abinda ya kawota. Ummi Aysha, da farin ciki ta karɓi kyautar Naila, tana ɗan janta da hira. Amma bata yimata hirar Sulaim ko abinda ya dangacesa ba har Naila ta bar Sashen. UMMI AYSHA Batasan akwai matsala a tsakanin Naila da Sulaim ba, don haka ta ajjiye abinda Naila ta kowamata domin nunawa Sulaim idan ya iso. SULAIM A ɓangaren Sulaim duk kiran da Naila takeyi baisan tana yi ba, saboda wayar a Silent take, batun barinta da ya ce yayi, ya faɗa ne, don ta dawo hankalinta saboda ya lura son dayake mata na naiman kawo rashin girmamawa a tsakaninsu. ★Da Asubahi aka sanar da shi ansamu Malamin daya ce a naimomai, kai tsaye ya haɗa Malamin da Malik. Bayan gama wayarsa da Malik ya ankara da tarin kiran da Naila tayi mai, maimakon ya amsa kiranta data cigaba da kira da Asubahi sai ya kashe wayar gaba ɗaya. Kamar yadda ya tsara bayan gari ya yi haske ya kira Mahaifiyarsa ya sanar da ita zuwansa. Ummi Aysha tayi mamakin zuwansa a irin wannan lokacin tun da bai jima da tafiya ba, sai da yayi mata bayanin uzurine zai kowasa. Da wasa da dariya take tsokanarsa ko dai Naila zai zo gani? Sulaim murmushi kawai ya yi bai ce komai ba har sukayi sallama. Shirye-shiryen tarbarsa Naila ta samu anayi a ɓangaren Ummi Aysha. Kafin Sulaim ya isa Dhahab, Malik da Mallamin da daya je ya ɗauko sun rigasa isowa. A ɓangaren Malik bayan sun iso Dhahab da Mallam, a sashensa yayiwa Mallam masauki. Mallamin ko hutawa baiyi ba ya ce akirawomasa Simbi. Ko da Malik ya je, Simbi ta kulle kanta a ɗaki da sunan tana barci, da Malik ya dawo ya gayawa Mallam Simbi tana barci cewa yayi su tasheta, idan taƙi tashi su kirasa.. Lokacin da Sulaim ya iso ƙasar Abyad a sirrince aka ɗaukosa zuwa Dhahab babu chunkoson jami'an tsaro da yawan Motoci. Ɓangaren Ummi Aysha ya sauka kamar waccen karon. Ummi Aysha bakinta ya kasa rufuwa sai fara'a takeyi, tana jansa a jiki. Abincin data shiryamai da kanta ta gabatarmai har da Snacks ɗin da Naila ta kowamata masu kyan gani a ido ta jera a gefe. Maimakon ya ɗaibi abinda yake gabansa, sai ya kai hannunsa kan Snacks ɗin da sukayi matuƙar burgesa. Ummi Aysha dariyarta ta ƙunshe tana jiran yakai bakinsa sannan tayimai tsiyar wato Naila ta gayamasa ta kawo mata Snacks shine zai ajjiye nata girkin ya fara dana Naila. Ya na kaiwa baki ya gutsira ya tauna ya haɗiye. Dariyar Ummi Aysha ta saki tana yi mai tsiya ba tare da ta lura da sauyinsa ba. A hankali ya jingine bayansa da kujerar dayake kai, Fuskarsa ya sunkuyar ƙasa, kafin wuyar ya karye kamar wanda barci ya kwashe a zaune. Dariyar Ummi Aysha ne ya ɗauke lokaci ɗaya, ta miƙe ta nufosa tana faɗin; "lafiyarka Sulaim menene haka ka karya wuya, kayimin magana mana!"