Kundin Masoya GUDUN TSIRA Littafi na daya(1) Part A AYARI NE NA WATA KABILA wacce ake kira da BANU HANZAR.Shugaban wannan kabilar ya kasance Gwarzon Jarumi kuma sadauki na gaske wanda ake kira da SHARWAN IBN KILYIN.Itadai wannan kabilar asalinsu sun fito ne daga yammacin birnin Kisra ya zamana cewa rayuwarsu taci gaba a cikin zagaya duniya saboda neman inda tsuro da ruwa yake,domin kiwon dabbobinsu da kuma farauta.Masu bincike da hasashe na wannan zamani sun tabbatar da cewa a duniya kaf babu wadansu mutane wadanda suka lakanci iya kiwo da farauta sama da mutanen kabilar Banu Hanzar kuma su dama can tun farkon rayuwarsu a jeji suke rayuwarsu tun kafin ma birnin Kisra ta kafu don haka kabilar Banu Hanzar suna habaka a yawa kuma gashi suna da zaratan jarumai gwanayen yaki don haka yan fashi ko yan hari suna matukar shayinsu.Lokacin da kasar Kisra ta kafu kuma ta gawurta a zamanin wani azzalumin sarki wanda ake kira da suna RUGUZAN IBN MAULAS sai ya fara matsawa kabilar banu hanzar da biyan haraji mai yawa akan zaman da sukeyi a cikin yankin kasarsa.Ba komai ne yasa Sarki Ruguzan yayi haka ba saboda ganin kabilar ta banu hanzar take da yawa da kuma zaratan jarumai,yana tsoron kada wata rana suyi tunanin yi masa juyin mulki su karbe masa KARAGAR MULKINsa.A wannan lokaci Shugaba Sharwan ya fara manyanta shekarunsa sun haura sittin kuma Allah ya albarkaceshi da 'ya guda daya wata kyakkywar budurwa ta gaba kwatance mai suna SIYAMA.Siyama batafi shekara goma sha takwas ba a duniya kuma Allah ya hore mata tsananin jarumtaka da rashin tsoro fiye da mahaifinta sannan tana da matukar tausayi gami da jin kan makaskanci.A rayuwar Siyama babu abinda tafi tsana sama da zalunci da azzalumi.Tun da Siyama ta cika budurwa samarin kabilar sukayi caa?akan neman aurenta amma sai tayi watsi da kowa tace ita kam bataga gwani ba.Al'amarin daya dugunzuma hankalin mahaifinta shugaba Sharwan kenan ya kirata suka kadaita a cikin tantinsa da yake su basa gina gida saidai suka kafa tantuna a cikin daji saboda basa zama a waje daya.Idan sun gama cin gajiyar wannan dajin sai su matsa izuwa na gaba dashi.Lokacin da shugaba Sharwan ya kadaita da Siyama sai ya dubeta cikin tsananin damuwa kamar zai fashe da kuka sannan yace,yake 'yata inaso kiyi sani cewa ni dake ne kadai muka rage a cikin dangin zuri'armu kuma tunda aka kafa kabilarmu muke sarauta.Shin ba kya tunanin cewa idan kika mutu ba kiyi aure ba shike nan sarautar nan ta bar gidanmu?Koda jin wannan batu sai Siyama tayi murmushi sannan ta dubi Sharwan cikin nutsuwa tace,Ya kai Abbana inason ka fahimci dalilin da yasa bani da gwani a cikin dukkan samarin kabilar nan tamu.Su duka suna so nane saboda abu guda biyu,Abu na farko shine saboda kyawuna.Abu na biyu kuma shine saboda matsayina na 'yarka.Duk wanda ya aureno yana ganin cewa ya sami damar da zai sami mulkin kabilar Banu Hanzar a sama.Na daukarwa kaina alkawarin cewa ba zan taba aurar wani 'da namiji ba sai wanda na tabbatar da cewat zai so ni SO na gaskiya ba don kyawuna ba ko don matsayina ba.Abu na biyu shine bazan taba yarda nayi aure ba har saina tabbatar dacewar kabilarmu tana zaune a cikin kwanciyar hankali wanda bama tunanin fuskantar wata barazana daga sarkin Birnin nan.Sharwan ya dubi Siyama yace,abinda kika fada gaskiya ne,amma ai bamu isa muyi Yaki da sarki Ruguzan ba.Saboda yawan mayakansa kuma gashi ya kasance Azzamuli mara tausayi.Mu kuwa a matsayinmu na kabila kawai ba kasa guda ba,babu wanda zai bamu gudunmawar dakarun yaki saidai ma a kuramu da matsayin 'yan tawaye ayi mana taron dangi a shafemu gaba daya.Yanzu dai abinda ya kamata ayi shine,mu zauna tare da yan majalisata da kuma tsofaffun kabilartamu domin ayi shawara bisa abinda muke ganin zai fishshemu.Koda jin wannan batu sai Jikin Siyama yayi sanyi tayi shiru batace komai ba.Kamar yadda shugaba Sharwan ya fada hala al'amarin ya kasance,wato saida aka zauana taron yin shawara aka shafe sama da sa'a bakwai ana kace nace kowa na fadin albarkacin bakinsa,sai daga karshe wani tsoho wanda yafi kowa yawan shekaru a kabilar wanda yaga zamani da yawa ana kiransa da suna Wamhas ya daga hannu alamar yana son yace wani abu,dama shi kadaine baice komai ba tunda aka fara taron.Koda shugaba Sharwan ya hango tsoho Wamhas ya daga hannu sai yayi tsawa akayi tsit sannan ya baiwa Wamhas umarnin yayi magana.Wamhasa ya yunkura da kyar saboda tsufa yana mai dogara sandarsa ya mike tsaye sannan ya fuskanci shugaba sharwan yace ya shugabana ina son ka sani cewar Yaki ko Hijira duk bazasu kubutar damu ba saboda duk sarakuna na wannan zamani basu da wani adalci,azzalumai ne duk inda muka je zamu tarar da abinda muke gujewa.Bamu da wata mafita face mu nemi sulhu da sarki Ruguzan.Dole ne mu tashi wakilinmu guda daya wanda zaije har fadar Sarki Ruguzan ya kaskantar da kansa ya nemi alfarmar ya sassauta mana wannan haraji izuwa yadda ba zamu rinka takura ba,sannan kuma idan za'aje gareshi aje masa da kyautar shanu da tumaki kamar guda dari dari,manya manya kuma kosassu.Tabbas idan aka je masa ta wannan siga a gaban fadawansa zaiji nauyin yaki amincewa da bukatarmu musamman daya kasance mutum mai son abin duniya.Ya shugaba na kai da kanka ya kamata kaje ka gana da sarki Ruguzan amma tunda yanzu bakada cikakkiyar lafiya kamata yayi ka tura 'yarka Siyama ta wakilceka yin hakan zaisa Sarki Ruguzan ya dauki abin da muhimmanci.Koda jin wannan batu sai Majalisar ta rude da kace nace,wasu suna goyan bayan shawarar da tsoho Wamhas ya kawo wasu kuma basa goyon baya.Kawai sai Siyama ta mike tsaye ta tako kafafunta ta zo gaban Sharwan ta risina cikin girmamawa tace Ya shugabana,Wamhasa ya gama magana,shawarar sa itace kadai mafita a garemu tunda idan baka manta ba kasha gaya min cewa abinda na gaba ya hango na baya ko ya hau kan tsaunin dayafi kowanne girma da tsayi a duniya bazai hangoshi ba.Sannan kuma ance Durkusawa wadai ba gajiya bane.Sa'adda Shugaba Sharwan yaji bayanin Siyama sai hankalinsa ya dugunzuma har ya budi baki zaice wani abu sai gaba dayan 'yan majalisar suka rude da cewa sun amince da shawarar tsoho Wamhas.Don haka sai ya kasa cewa komai.Nan take aka yanke hukuncin kashe gari da safe Siyama tare da dakaru arba'in zasu tafi izuwa fadar saki Ruguzan dauke da shanu da tumaki dari dari.Kashe gari kuwa da sassafe Siyama da dakaru arba'in suka hau dawakai kuma suka tusa dabbobin a gaba suka nufi cikin birnin Kisra.Bayan tafiyar rabin sa'a kacal suka iso fada.A wannan lokaci Siyama da dakarunta duk sunyi shiga ne da fatun dabbobi.Siyama tana sanye da riga da wando na fatar damisa wadanda suka kasance matsattsu don haka duk suka fito da kyawun surar jikinta.Babu wani 'da namuji dazai ga Siyama a wannan yanayi bai kidime ba saboda tsananin kyawun kirar da Allah ya bata.Siyama ta kasance doguwar mace mai madaidaicin kaurin jiki,wato ita ba siririya bace kuma ba mai kauri bace.Tana dogon hanci da kuma dan karamin baki tamkar da wuka aka yanka mata shi.Kirjinta a cike yake kuma kugunta a bude yake,cikinta a shamule kamar bata ciin abinci.Gashin kanta dogo ne kuma baki sidik yana haske da walwali tamkar madubi.Siyama bata kasance Farar fatar jiki ba,kuma bata kasancewa baka ba,ita dai madaidaiciya ce a haske,.Wani irin launin fata gareta na musamman mai tsananin ban sha'awa wanda irinsu a duniya ma kaf basufi a kirga ba.A wannan lokaci Siyama na rike da wani dogon mashi a hannuta,a kuibin cinyarta ta hagu kuwa ta daure wata zabgegiyar takobi.Su kuwa gaba dayan Dakarun dake take mata baya su arba'in sunyi shigar yaki ne suna rataye da Takubba da Garkuwoyi.Da isowarsu Siyama kofar gidan sarautar birnin kisra tare da wadannan dabbobi sai dakaru suka taresu suka hanasu wucewa akaje aka gayawa sarki Ruguzan zuwansu.Jim kadan sai ka manzon ya dawo,da zuwansa sai ya dubi Siyama yace,Sarki yace na kaiku gareshi amma dole ne ku ajiye dukkan makaman dake jikinku anan sai kum fito da kayanku.Koda jin wannan batu sai jikin dakarun Siyama yayi sanyi kuma hankalinsu ya dugunzuma suka rasa abinda zasuyi.Ita kuwa Siyama sai ta dubesu tayi murmushi batace komai ba,kawai sai ta fara mika mashinta sannan ta cire takobinta ta bayar.Bisa dole suma dakarun suka bayar da dukkan makamanus sannan akayi musu jagora izuwa gidan sarautar har aka iso cikin fadar Sarki Ruguzan.Fadar ta cika makil da mutane duk inda mutum ya duba saidai yaga kawunan bil'adama fululu,babu masakar tsinke.Sarki Ruguzan na zaune akan Karagar Mulkinsa yana ta nishadi bisa kallon wadansu 'yan mata dake faman tika rawa,makidansu suna gefe daya suna ta buga ganguna.Sarki Ruguzan sai kyalkyala dariyar farin ciki yake domin shi a rayuwarsa babu abinda yake so sama da mata.Saboda tsananin son matansa nema ya kasa zama da matar aure daya,a shekara daya yakan auri mata kala ashirin.Da zarar mace tayi sati biyu ko uku sai yaji ta isheshi don haka sai ya saketa ya auro wata saboda da ruwan idonsa.Koda Siyama da dakarunta suka shigo cin wannan fadar kowa yayi arba da ita akaga tsananin kyawunta sai kowa ya kame.'Yan matan da suke rawa ma sai suka daina,masu kida suka kasa ci gaba da kidansu.Shi kuwa Sarki Ruguzan dimaucewa yayi bai san sa'adda ya mike tsauye ba ya kurawa Siyama idanu jikinsa na Tsuma ko kifta ido ba yayi sai kace Gunki. Hmm Nima danake typing ganinta yasa na kame kam na zuba mata ido,sannan na kasa ci gaba da rubutun danake. ★GUDUN TSIRA ★ Littafi Na Daya(1) Part B ★A-H Physicist★ Ko kifta ido bayayi sai kace gunki.har Siyama da dakarunta suka iso daf da karagar mulkin tasa suka zube kasa gabansa suka kwashi gaisuwa bai iya cewa komai ba.Siyama ta mike tsaye ta dago kanta sukayi arba ita da Sarki Ruguzan a lokacin da da fuskarta ya cika da annuri gami da murmushi mai taushi tace ya kai wannan sarki mai daraja gami da cikar mulki kayi sani cewa mu kabilar Banu Hanzar mun kasance talakawanka masu rauni da kaskanci don haka mun zone neman alfarama a wajenka bisa harajin da muke biya a duk wata guda. Muna son Sarki yayi mana adalci ya rage mana kaso biyu daga cikin kaso ukun abinda muke biya saboda tattalin arzikinmu ya fara lalacewa.Koda Siyama tazo nan a jawabinta sai Sarki Ruguzan ya bushe da dariyar farin ciki a lokacin da yaji wani irin girman kai ya shigeshi.Lokaci guda kuma ya hade fuskarsa ya dubi Siyama cikin nutsuwa yace,yake wannan budurwa ma'abociyar kyawu.Ke kuma wacece a cikin mutanen Banu Hanzar kuma me kuka zo mini dashi wanda zai sa na amince da bukatarku?Siyama ta dukar da kanta kasa tace Sunana SIYAMA BIN SHARWAN 'ya ga shugaban kabilar Banu Hanzar.Nazo ne bisa wakilcin mahaifina.Ya shugabana ba komai muka kawo maka ba face Shanu da Tumaki guda dari dari kacal don amfanin miyar gidanka. Bamu da wani abu wanda zamu iya baka amma muna neman aldalcinka da jin kanka.Koda Sarki Ruguzan yaji wannan batu sai ya bsue da dariya a karo na biyu sannan ya dubi wani babban hadiminsa yace dashi a kai Siyama da jama'arta izuwa masauki inda zasu huta kafin ya zauna da 'yan majalisarsa su tattauna dangane da bukatar datazo masa da ita.Koda jin wannan batu sai hankalin Siyama dana dakarunta ya tashi suka fara tunanin cewa lallai akwai wani abu wanda Sarki Ruguzan yake so yayi na yaudara a garesu. Nan take Siyama tayi dan guntun tunani sannan ta dubi dakarun nata tayi musu inkiya dasu kwantar da hankalinsu babu abinda zai faru.Nan take aka tafi dasu Siyama izuwa wani gida na musamman inda ba a saukar kowa sai manyan sarakuna da manyan attajirai.Shi dai wannan gida an kawata shi ainun ya cika aljannar duniya babu abinda babu a cikinsa na jin dadi.Da shigarsu suka iske an kawo masu abinci na alfarma irin wadanda ma basu taba ci ba sama da kala ashirin an shirya shi akan tebur sannan ga kayan shaye shaye ma iri iri cikin tambulan- tambulan wanda akayi shi daga 'ya'yan itatuwa nau'i nau'i.Koda ganin wanna daula sai dakarun Siyama suka dimauce basu san sa'adda suka hau kan teburin ba suka dasawa abincin wawa.Kawai sai sukaji Siyama ta daka mus tsawa. Cikin razana suka mike tsaitsaye suka sunkui da kawunansu kas.A sannan ne Siyama ta dubesu a fusace tace shin a tunaninku Sarki Ruguzan zai yi mana wannan kyau tane a banza?Ku tuna cewa iyayenmu da kakanninmu basu taba shigowa gidan sarautar nan ba fiye da shekaru dari da suka gabata.Basu taba dandanar abinci mai dadi ba irin wannan kuma sunyi zamaninsu tafiya sun tafi.Mu hakura da irin yanayin rayuwarmu da muka saba da ita kada a rudemu da dadin duniya a cutar damu.Na lura da wani irin kallo wanda Sarki Ruguzan ya dinga yi mini,kallo ne na sha'awa don haka idan harma zai biya mana bukatarmu bada zuciya daya zai taimakemu ba.Lokacin da Siyama tazo nan a zancenta sai dakarun nata suka shiga taitayinsu sosai.Babban cikinsu wanda ake kira da Ilmar ya dubeta yace,ya shugabata yanzu mene ne abinyi kenan?Siyama ta numfasa tace zamu jira daga nan zuwa yamma muji irin shawarar da sarki Ruguzan yayi da jama'arsa. Idan ban gamsu da ita ba nasan abinda zanyi.Amma abinda nake so daku shine dayanku ya zauna a cikin shirin komawa can daji sansaninmu nan da cikar dakiku kadan bayan na gama rubuta wasikar dazan bayar a kaiwa mahaifina.Koda jin wannan batu sai su Ilmar suka cika da tsananin mamaki kuma suka kasa gane abinda Siyama ke kokarin shiryawa.Har Ilmar ya budi baki zaiyi mata tambaya sai ta daka masa harara tace kada kuyi mini tambayar komai kawai ku zamo masu bin umarnina.Tana gama fadin hakan ta bude jakarta ta fata ta fiddo alkalami da tauwada gami da takarda ta koma nesa kadan dasu Ilmar ta zauna ta rubuta wasika. Bayan ta gama rubuta wasikar sai ta nannadeta ta mikawa daya daga cikin dakarun ya karba sannan ta dubeshi tace Ya kai Muzaru ka boye wannan wasikar a jikinka yadda duk duban da za ayi baza a ganta ba a lokacin da zaka fice daga cikin garin nan.Lallai ka ruga izuwa sansaninmu ka kaiwa mahaifina ita a cikin kankanin lokaci kuma ka bashi wannan wasikar a sirrance ba tare da kowa ya sani ba.Koda jin wannan batu sai Muzaru ya risina yace An gama.Nan take Muzaru ya shiga cikin bandaki ya kimtsa kansa sanna ya fito da sauri yana fitowa sai Siyama ta dubeshi tace duk wanda ya tuhumeka dalilin tafiyarka yanzu ka gaya masa cewar nice na aikeka wajen mahaifina domin ka gaya nasa halin da ake ciki don kar yaga mun dade bamu dawo ba ya zata ba lafiya. Muzaru ya sake risina yace An gama.Kawai sai ya juya ya fice daga gidan gaba daya da sauri.Kafin Muzaru ya fice daga cikin gidan sarautar saida ya ratsa ta cikin kofofi tara,kuma duk inda ya iso sai an caje ko ina a jikinsa ba aga wannan wasika ba da Siyama ta bashi,kuma sai an tuhumeshi dalilin dayasa ya fito shi kadai ba tare da sauran abokan tafiyarsa ba,daya basu amsar kamar yadda Siyama ta umarceshi sai a bude masa kofar ya wuce.Yana fita daga cikin gidan sarautar ya zaburi dokinsa da gudun tsiya ya nausa izuwa cikin daji,bai tsaye a ko ina ba saida ya iso sansaninsu inda suka kafa tantuna.Tun daga nesa aka hango Muzaru shi kadai ya dawo daga cikin Birnin Kisra,sai hankalin kowa ya dugunzuma aka fara tunanin ko wani abu ya sami siyama da sauran mukarrabanta.Koda isowar Muzaru sai ya tsaida dokinsa a daidai kofar tantin shugaba Sharwan ya sauka,wani badakare ya kama dokin nasa yaje ya daureshi. Nan take akayi masa iso ya shiga cikin tantin.Da shigarsa sai ya iske Sharwan tare da mahaifiyar Siyama a zaune sunyi jugum fuskokinsu a cike da alamomin matukar damuwa da tashin hankali.Koda ganin Muzaru sai mahaifiyar Siyama ta mike zumbur ta tareshi tana mai rike kafadunsa a lokacin da idanuta suka ciko da kwalla kamar zatayi kuka tace,ya kai Muzaru ka gaya mini iyakar gaskiya,menene ya faru ga 'yata?Muzaru yayi dan guntun murmushi yace,Siyama tana nan lafiya kalau kamar yadda kuka ganni,yanzu haka itace ma ta bani sako na kawowa shugaba,amma tace sai na kadaita dashi.Koda jin wannan batu sai shugaba Sharwan ya dubi Matarsa Ilela cikin murmushi yace barkanmu.Yanzu hankalinmu ya kwanta.Yake matata bamu wuri na gana da babban hadimi Muzaru.Ba tare da gardamar komai ba kuwa Ilela ta mike tsaye ta fice daga cikin tantin.Fitarta ke da wuya sai Muzaru ya kwance kitson kansa guda ya fiddo wata takarda wadda take a kanannade ya warwareta sannan ya mikawa Sharwan cikin sauri kuma hannunsa na karkarwa.Shugaba Sharwan ya warware takardar ya karantata.Yana gama karanta wasikar sai ya kurma uban ihu ya durkushe kasa bisa guiwoyinsa.Koda jin ihunsa sai Mahaifiyar Siyama ta shigo cikin tantin a firgice,ta rungumeshi sannan ta fashe da kuka tanace yakai mijina mene ya faru?Shugaba Sharwan ya dubeta fuskarsa cike da damuwa yace,yake matata kisani cewa damu da dukkan 'yan kabilarmu muna cikin babban tashin hakali. A wasikar ta Siyama ta rubuto tace dukkanmu mu hada inamu inamu mu bar wannan daji mu kara gaba,sannan tace mu hadu a wajen wannan katon dutsen,so take mu bar wannan nahiyar gaba daya.Bansan abinda take shirin shiryawa ba,amma naji a jikina abin ba dadi,in bamuy da gaske ba 'yan kabilarmu guda daya bazata tsira da ranta ba.Don haka yanzu mu fara shirye shiryen barin wannan waje.Koda jin wannan batu sai Ilela ta sake kankame Sharwan tana mai fashewa da matsanancin kuka. WANE ABU SIYAMA TAKE SHIRIN AIKATA WA? ME ZAI FARU A ZAMAN DA SARKI RUGUZAN ZAIYI DA 'YAN MAJALISARSA AKAN YANKE WANNAN HUKUNCI? KABILAR SU SIYAMA ZASUYI HIJIRA KO ZASU ZAUNA,IDAN SUNYI HIJIRAR MAI ZAI FARU DASU A GABA. Muhadu a GUDUN TSIRA kashi na biyu don jin ci gaban wannan kasaitaccen labari ★GUDUN TSIRA★ Littafi Na Biyu (2) Part A ★A-H Physicist★ A CAN gidan sarautar sarki Ruguzan kuwa bayan tafiyar Muzaru sai Siyama ta umarci sauran dakarunta su talatin da tara dasu dauko abincin guzurinsu dake cikin jakunkunansu su ci.Ba tare da gardamar komai ba kuwa suka cika umarnin suna ji suna gani suka hakura da wannan abinci mai dadin gaske na alfarma wanda aka shirya musu.Itama Siyama nata abincin guzurin taci bayan sun gama cin abincin kowa ya kimtsa sai Siyama ta dubesu cikin nutsuwa tace,abinda nake so daku shine lokacin da sarki ya turo a kirawoni ku biyoni a baya amma kafin mu iso inda zan gana da shi,ku sulale ku fice daga cikin gidan sarautar nan gaba daya ku nausa daji,zan hadu daku a can Dajin Zamhar inda kabilarmu gaba daya zasu yi zaman jiranmu na tsawon rabin sa'a kacal.Idan har muka wuce sa'a daya bamu riskesu ba a can to abu ne mayuwaci ni daku ya kasance mun tsira da rayuwarmu.Koda Siyama tazo nan a zancenta sai hankalin gaba dayan dakarun nata ya tashi ainun domin a sannan ne suka gane abinda take shirin yi.Cikin alamun firgici daya daga cikinsu ya dubeta yace haba ya shugabata saboda me zaki durfafi wuta alhalin kinsan cewa baki sha maganin konewa ba? Siyama tayi ajiyar numfashi sannan tace,ai abinda ya koro bera ya fada cikin wuta yafi wutar zafi.Sau tari sai mutum yayi kundumbala ya tari fadan da yafi karfinsa sannnan yake fita daga wata masifar.Nasan irin jarumtakarku kuma nasan iyakar irin abinda zaku iyayi.Ku jajurce duk wuya duk rintsi ku fice daga cikin garin nan a raye,kada ku damu dani don nasan duk yanda zanyi na kare kaina.Ku sani cewa daga yanzu mun daura damarar yakin ceto rayuwarmu data jama'armu gaba daya da kuma gyara rayuwar 'yan bayan mu don haka ranmu da lafiyarmu ba a bakin komai suke ba.Siyama ba gama fadin haka sai suka an kwankwasa musu kofa.Take Siyama ta dubi daya daga cikin dakarun nata tayi masa inkiya yaje ya bude kofar saiga hadimin Sarki Ruguzan wanda ya kawosu masaukin ya shigo da sauri fuskarsa cike da annuri.Koda yaga alamar su Siyama basu ci abincin da aka kawo musu ba sai nan take fuskarsa ta sauya yanayi ya dubi Siyama cikin alamun tsananin damuwa yace yake wannan ma'abociyar kyawu da kwarjini mene ne dalilin da yasa bakuci wannan abincin da aka kawo muku ba alhalin sarki ya karbeku hannu biyu a matsayin manyan bakinsa ya karramaku kuma ya baku masaukin da yake baiwa sauran abokansa sarakai.Koda Siyama taji wannan batu sai tayi murmushi mai taushi ga hadimin wanda ya kidimashi ya sukurkuce bisa ganin yadda kyawunta ya karu ainun tace,yakai wannan babban hadimi na sarki ka sani cewa mu mutanen daji ne wadanda suka saba da abincin 'ya'yan itatuwa da naman tsuntsaye da dabbobi,bamu saba da irin wannan abincin naku ba don haka idan muka cishi da yawa zai iya lalata mana cikinmu.Yanzu menene ya kawoka garemu?Hadimin ya maidawa Siyama martanin murmushin yace,Sarki ne yace nazo na tafi dake izuwa inda zaku gana dashi,domin ya gama zantawa da 'yan majalisarsa.Koda jin haka sai Siyama da dakarunta suka mike tsaye suka fito daga cikin dakin,amma sai wannan hadimi ya yasha gabansu ya dubi Siyama yace,ai ke kadai sarki yake son gani don haka dole ne masu tsaron lafiyarki su jiraki a anan.Koda jin haka sai Siyama ta sake murmushi tace,ai bazasu shiga cikin dakin da zan gana da Sarki ba saidai su tsaye a waje.Koda jin haka sai Hadimin ya juya ya wuce gaba yana mai yiwa su Siyama jagora suka nausa izuwa wani bangaren dabam na gidan sarautar,suka rinka shiga loko loko,sako sako masu kwanoni da lunguna masu zurfi wanda komai kular mutum bazai iya dawowa baya yabi ainihin hanyar da aka biyi dashi ba,amma Siyama tana haddace hanyoyin a cikin kanta tamkar akan takarda ake rubutasu da alkalami.Saida sukayi tafiya mai tsawo sannan suka iso kofar wani katon gida mai tsananin fadi da tsawo wanda indai mutum ya shiga cikinsa zaiji kamar an jefashi a RIJIYA GABA DUBU ne.Siyama na ganin wannan gida ta sake aiyana zargin abinda ta ayyana a ranta.Sarki Ruguzan ke shiryawa akanta taji ta sami tabbacin hakan babu wani kokwanto.Da isowarsu sai Hadimin ya waigo domin ya gayawa Siyama cewar dakarunta su tsaya anan yayi mata jagora izuwa cikin gidan,kawai sai yaga babu mutum ko daya daga cikin dakarun nata guda talatin da tara sai ita kadai.Abinda yai matukar bashi mamaki kenan ya dubeta yace,ina masu tsaron lafiyar taki?Siyama tayi dan guntun murmushi tace,Ai tun a can baya kafin mu fara shiga cikin sakon nan masu zurfi suka tsaya don kada su bace.Koda gama fadin hakan sai ya murda kofar gidan wacce ta kasance ta bakin karfe zalla mai nauyi da kaurin gaske.Take kofar ta bude suka kunna kai ciki.Cikin gidan iya hangen idanun mutum babu komai a cikinsa face ciyawa mai taushi wacce aka shukata a kasa ta zama kamar kilishi.A can nesa suka hango Sarki Ruguzan zaune akan wani gadon Sarauta ya dora kafarsa daya akan daya kuma yayi shigar yaki fuskarsa cike da murmushin farinciki.Koda Siyama ta hango Sarki Ruguzan a cikin wannan hali taga irin kirar da Allah yayi masa ta katon sadauki mai murdadden jiki gami da tarin kwarjini sai zuciyarta ta da karfi tsoro ya shigeta,amma data tuno da irin hadarin da take ciki ita da kabilarya sai taji zuciyarta ya kekashe ga barin tsoron kuma koda Girman Sarki Ruguzan yakai na tsauni bazata kasa tunkarasa ba.Lokacin da wannan hadimi ya hango Sarki daga inda yake zaune sai ya tsaya cak ya juyo ya dubi Siyama yace to nifa nazo iyakata zan juya na fita na barku keda sarki.Siyama na jin haka sai ta dubi Hadimin tayi murmushi tace,idan ka fita ka rufe kofar da kyau yadda ko ni ko Sarkinka babu wanda zai iya budeta ya gudu har sai dayanmu ya kar daya.Koda jin wannan batu sai hadimin ya firgita kuma ya kamu da tsananin mamaki bisa yadda akayi Siyama ta gane cewa akwai wani tuggu wanda sarki ya shirya mata.Cikin rawar jikin hadimin ya ruga da baya ya kulle kofar gidan ta waje yasa kuba ya dada rufeta sosai.Ita kanta kubar da aka kulle kofar ta isa abar kallo domin katuwa ce sosai don yaro dan shekara tara zuwa goma bazai iya rabata da kasa ba saboda girmanta.Sarki Ruguzan na zaune bisa wannan gado ya kurawa Siyama idanu yana mata murmushin mugunta kawai sai yaga ta tunkaro inda yake kai tsaye itama tana yi masa murmushin mugunta ba tare da shakkar komai ba har saida ya zamana cewa tazarar dake tsakaninsu bata wuce goma ba sannan Siyama ta tsaya cak ta rike kugunta da hannayenta biyu kuma ta murtuke fuskarta.Koda ganin haka sai Sarki Ruguzan ya takarkare ya bushe da mahaukaciyar dariya kamar bazai daina ba.Daga can sai ya turbune fuskarsa ya mike tsaye yana mai dakawa Siyama tsawa yace,ke yarinya kiyi sani cewar duk wanda ya rigaka kwana dole ne ya rigaka tashi.Na dade da samun labarinki kuma na dade ina jiran zuwan wannan rana wacce zamuyi GABA DA GABA domin na gama dake yadda ko a tarihi ba za a sake tunowa dake ba kuma baza a tuna da kabilarku ba tamkar ma baku taba wanzuwa ba.Yanzu kin kawo kanki cikin RIJIYA GABA DUBU inda IHUNKI BANZANE,banga wanda zai iya kubutar dake ba daga sharrina yanzu zan sumar dake sannan na kawar da kimarki ta 'ya mace alhalin babu wani 'da namiji daya taba samun wannan dama a gareki sai ni.Bayan nan sai nayi miki KISAN GILLA na cire kanki na aikawa da mahaifinki domin yasan cewaduk beran dana danawa tarkona bai isa ya iya tsallakewa ba.Lokacin da Sarki Ruguzan yazo nan a zancensa sai Siyama ta tari numfashinsa tana mai kyalkyalewa da dariya tace,yakai wannan tsohon azzalumin sarki kayi sani cewa kamar yadda ka dade da sanina gami da yin bincike akan komai nawa nima na dade da sanin komai akanka,kuma na dade ina tanadin hanyoyin dazan bi na kawo karshen zaluncinka a kasar nan.Ina mai tabbatar maka da cewar koda zaka sami nasarar tarawa dani to saidai ka tara da gawata.Yau kuma yanzu ko ni ko kai saidai a dauki gawar daya a cikin wannan gida.Na fito da nufin RAI KO MUTUWA.sai kayi shirin kare kanka.Siyama na gama fadin hakan sai ta zare takobinta ta ruga izuwa kan Sarki Ruguzan,shi kuwa saibua sake kishingida yana murmushi kamar ba hari za akawo masa ba.Koda ya rage saura baifi taku uku ba su hadu sai Siyama ta tako tsalle a sama ta kawo masa mugun sara da nufin ta cire masa kai.Cikin tsananin zafin nama sarki Ruguzan ya mirgina can gefe daya.Koda takobin Siyama ta dira akan gadon saita tsargeshi gida biyu tamkar ansa zabira an yanka kabewa an rabata gida biyu.Cikin ZAFIN NAMA sarki Ruguzan ya zare tasa takobin ya afka mata suka ruguntsume da azababben yaki ya zamana cewa sina kaiwa junansu SARA DA SUKA cikin tsananin zafin nama,juriya da bajinta ta ban al'ajabi. Nima ganin wannan Yaki nasu yasa na dakata anan domin nayi Kallo. UDUN TSIRA Littafi na biyu (2) Part B Cikin tsananin zafin nama,juriya da bajinta ta ban al'ajabi.Koda Sarki Ruguzan yaga cewa Siyama tana da horon yaki matuka gashi har sun shafe 'yan dakiku suna gumurzu amma bai sami nasarar koda lakutar jikinta ba sai ransa ya baci nan take ya shammaceta yasa kafarsa ya doki kirjinta.Saboda karfin dukan saida tayi can gefe daya tamkar an janyeta da majaujawa ta kife kasa da rub da ciki tana aman jini.Koda ganin haka sai Sarki Ruguzan ya bushe da dariyar mugunta.Kawai sai yayi jifa da takobin hannunsa ya tofawa Siyama yawu akan fuskarta yace zan more wannan jiki naki mai kyau sannan na muje kyakkyawar fukskar taki..Kafin ya gama rufe bakinsa sai yaji Siyama ta bushe da dariya kuma ta mike tsaye zumbur kamar sifirin tana mai goge jinin jikinta.Itama sai tayi jifa da takobin hannunta ta nunashi da dan yatsa tace,yakai wannan tsohon azzalumin Sarki,kayi sani cewa ina tabbatar maka da cewa karfin bashine komai ba a fada,naci,sa'a da juriya ma suna kaiga samun nasara.Tana gama fadin hakan sai ta afkawa Sarki Ruguzan suka sake kacamewa da sabon fada suka rinka naushi da bugun juna.Ai kuwa ana fara wannan gumurzun ne Siyama ta gane kurenta domin Sarki Ruguzan ya fita karfin damtse da zafin nama nesaba kusa ba kuma duk irin naushin datayi masa shanyeshi yakeyi,amma da zarar shi yayi mata naushi daya sai kaga har layi take yi tana neman faduwa,tsananin juriya ne gami da sabo da gumurzu yasa bata zuwa kasa.Koda Sarki Ruguzan yaga Siyama taki zuwa kasa kuma bata fasa gabza masa naushi ba a fuska harma ta fasa masa hanci da baki jini na yoyi sai ya fusata ainun ya daka tsalle sama ya gabza nata wawan naushi a fuska da dukkan karfinsa.Siyama ta kife kasa sumammiya ko kyakkyawan motsi batayi ba tamkar ta zama gawa.Cikin tsananin farinciki sarki Ruguzan ya cire rigarsa ya tsugunna akan Siyama ya juyo da ita yasa hannayensa biyu ya farke rigar jikinta.Koda ya yunkura zai afka mata sai kawai yaji ta soka masa wani abu a wuyansa,take jini ya kama kwararowa kasa.Sarki Ruguzan ya mike tsaye yana yin baya taga taga yana mai dafe abinda ta soka masa,kawai sai ya zare abin a lokacin daya kwarara uban ihu,sai yaga ashe kashin wata dabba ne ta soka masa.Nanfa jini yaci gaba da kwararowa daga jikin wuyan nasa amma yana tsaye bai fadi ba,sai ya rugo izuwa kan Siyama yana mai bude hannayensa da nufin ya damketa ya shaketa suyi MUTUWAR KASKO.Koda ya kawo mata sura sai ta sunkya ta shige ta karkashin kafafunsa ta dako gadon bayansa da kafafunta ta baya,kawai sai ya fadi kan katakon karyayyen wannan gado.Take wani icen gadon ya tsireshi a ciki ya hudo ta gadon bayansa.Sarki Ruguzan ya rinka kwarara uban ihu da kururuwa sannan idanunsa suka kafe,jikinsa gaba daya ya sandare ya zama gawa.A sannan ne Siyama ta mike tsaye tana layi sakamakon jinin dake zuba a gefen kanta saboda naushin da Sarki Ruguzan yayi mata dazu ya tsaga mata kanta kuma har sannan hancinta bai daina yoyon jini ba.Hakika ita kanta Siyama bata taba zaton cewar zata tsira ba daga sharrin Sarki Ruguzan ba,kawai ta saida ranta ne akan ko tayi nasara kota rasa rayuwarta.Lokacin da Sarki Ruguzan yayi mata wannan naushi a fuskar ta ta kife kasa ba suma tayi ba,amma ta fita daga cikin haiyacinta saita dauke numfashinta tayi kamar suman tayi.Damar datayi amfani da ita kenan ta shammaceshi ta zaro wannan kashi daga cikin aljihun wandonta cikin bakin zafin nama ta soka masa a makoshinsa.Lokacin da Siyama ta dubi gawar Sarki Ruguzan ta tabbatar cewar ta mutu sai tayi murmushin farin ciki amma data juyo ta dubi kofar gidan ta tabbatar da cewar bazata iya budeta ta fita ba sai hankalinta ya dugunzuma ainun sannan ta dubi ko ina a cikin gidan taga babu ta inda zata iya fita sannan ta tuno cewar idan fa aka sake jimawa akaji shiru za a bude kofar dakaru su shigo,in kuwa aka shigo aka ga ta kashe Sarki itama rubdugu za a yi mata a kasheta kuma tabbasa sarkin yawa yafi sarkin karfi.Kuma bayan an kasheta za a bi sawun dukkanin jama'arsu a hallakasu.Koda tazo nan a tunaninta sai hankalin ya kara dugunzuma fiye da ko yaushe ta rasa abinda ke mata dadi a duniya,nanfa ta kama kai kawo a cikin gidan tana mai ci gaba da kalle kalle da tunani.Tana cikin hakane ta daga kanta ta kallo rufin saman gidan saita ga ashe na katako ne.Nan take farin ciki ya lullubeta kawai saita daka tsalle sama ta kama rufin tayi ta tafiya a kansa da hannayenta da kafafunta tamkar kadangaruwa har saida ta iso wani wuri inda ta dan hango hasken wata yar karamar huda sannan tasa hannunta ta doki wajen take katakon daya rufe wajen ya burme.Tana zura kanta ciki ta shigo sai gashi ta fito a saman gidan.Cikin sauri tayi ruf da ciki akan rufin saman domin dakaru ta hango suna takai kawo a ko ina cikin gidan sarautar don tabbatar da tsaro.Saida ta shafe yan dakiku a kwance a saman ginin sannan taga dakaru sun rarrabu saura mutum daya jak a wani sako.Cikin hanzari ta daka tsalle ta duro a bayan wannan badakare ta murde wuyansa ya sulale kasa matacce,kawai sai ta jashi izuwa cikin wani sako mai duhu ta cire kayan jikinsa tayi canji da nata,kawai sai ta bude wani kwandon shara na karfe ta jefa gawar badakaren a ciki ta rufe kawai sai ta fito daga cikin sakon ta kunna kai izuwa hanyar fita daga gidan sarautar gaba daya kai tsaye ba tare da shakkar komai ba ta saje a cikin dakarun gidan sarautar masu fita.Duk da cewar ta saje da dakarun zuciyarta sai bugawa takeyi da karfi domin gani take yi kamar a koda yaushe asirinta zai iya tonuwa a gane ko wacece ita.Wani iko na Allah kuma ta gaban wannan hadimi daya kaita inda Sarki yake ta wuce harma suka hada idanu amma bai shaidata ba.A Wannan lokaci hadimin ya kagu yaga Sarki ya bude kofar wannan gida ya fito amma sai yaji shiru.A wannan lokacin ji yake kamar ya bugawa sarki kofa amma saboda tsoron kada yayi laifi shi yasa bai buga kofar ba kuma yayi tunaniin ko har a sannan sarko bai gama more rayuwarsa ba da Siyama.Har Siyama ta iso bakin kofar karshe ta gidan Sarautar babu wanda ya tareta,amma tun kafin ta iso bakin kofar taga masu gadin su hudu sun kura mata idanu suna yi mata kallon rashin sani da rashin yadda.Nan take Siyama ta gane cewa lallai idan ta karaso bakin wannan kofa baza'a barta ta fita ba sai an binciketa,in kuwa aka binciketa sai an gano wacece ita.Koda ya rage baifi taku uku bata riski masu gadin sai ta daka tsalle sama ta makesu da kafafunta su duka hudun a fuskokinsu a lokaci guda suka zube kasa sumammu.Ai kuwa dakarun dake bayanta suka hango abinda ya faru suka falfalo da gudu,itama Siyama tana durowa kasa bisa kafafunta sai ta falfala da azababben gudu na ban al'ajabi ta fice gaba daya daga cikin gidan sarautar.A sannan ne fa dakaru suka bita duu!suna ihu suna harba mata kibiyoyi.Idan mutum yaga yawan dakarun da suka bi bayan Siyama suna son su kure mata gudu,kuma mutum yaga irin ruwan kibiyoyin da ake yi mata dole ne yayi rantsuwa cewa babu yadda za'ayi ta tsira da rayuwarta.A can kofar wannan gida na cikin gidan sarautar wanda Siyama ta kashe Sarki Ruguzan a cikinsa.Koda wannan hadimi yaga dakarun gidan sarautar gaba daya sun rude suna ihu kuma sun ruga izuwa can kofar fita daga gidan sai shima ya dimauce yayi zargin ko Siyama ce yabi ta wata hanyar daban ta gudu,don haka hannunsa na karkarwa yasa kuba ya bude kofar yaja wadansu dakaru masu yawa suka ruga izuwa cikin gidan.Suna isa inda gadon nan na sarki yake sai suka iske gawar Sarki Ruguzan soke a jikin katakon gadon.Koda sukayi arba da gawar sai kowa ya firgita ainun kuma suka cika da tsananin mamaki.Nan take wannan hadimi ya kurma uban ihu mai tsananin firgitarwa ya dakawa dakarun dake bayansa tsawa yace maza kuje ku gayawa sarki yaki cewar 'yar shugaba Sharwan ta kashe sarki kuma ta gudu.Nan take wadannan dakaru suka juya da baya da gudu shi kuma sai ya fara kokarin cire gawar daga jikin katakon da take tsire.Saida aka shafe sa'a uku da rabi ana tseren gudu tsakanin Siyama da wadannan dakaru su basu cimmata ba ita kuma ba ta bace musu ba,tun ana cikin birnin kisra har aka shiga cikin daji.Babu abinda ya daurewa dakarun kai yayi matukar basu mamaki face ganin yadda Siyama ta tsallake harin ruwan kibiyoyin da ake yi mata ta sama da kasa kai kace aikin sihiri ne.Koda aka shiga cikin wani daji wanda Siyama ta saba yin farauta a cikinsa tun tana yarinya karama ta lakanceshi ainun sai ta fada cikin wani surkuki mai yawan duhuwoyi,hanyoyi barkatai gami da koramai da kwazazzabai da kuma manyan ramuka da ciyoyin fadamomi da koramu.Tana shiga cikin wannan surkuki sai dakarun suka nemeta sama da kasa suka rasata tamkar anyi ruwa an dauke.Amma saboda naci har gari yayi duhu Dakarun basu bar dajin ba suna ta neman Siyama a cikin kowanne sako da lungu har cikin kogon duwatsu shiga suke suna haska ko ina da fitilun itatuwa.A karshe dai ba basu ganya ba sai sukayi hakurin dole suka koma izuwa can gidan sarautar.Suna zuwa ne suka iske gidan sarautar a cike da mutane ana gabatar da jana'izar sarki Ruguzan.Da yawa daga cikin mutanen garin murna sukeyi bisa mutuwar sarki Ruguzan saboda tsananin mulkin zaluncin da yake yi musu,to amma saboda tsoron dan'uwansa Yarima Darwaz wanda shine zai gaji karagar mulkin babu wanda ya nuna farincikinsa a fili. ★GUDUN TSIRA★ Littafi Na Biyu (2) Part C ★A-H Physicist ★ Babu wanda ya nuna farincikinsa a fili.A wannan lokaci tuni an binne Sarki Ruguzan a cikin kabarinsa,yarima Darwaz ya kwanta akan kabarin yana ta faman rusa kuka da ihu.Da kyar da sidin goshi fadawa suka bashi baki suka lallabeshi ya tashi daga kan kabarin.Yarima Darwaz da Sarki Ruguzan sun kasance uwa daya uba daya,kuma yarima Darwaz ya girmi sarki Ruguzan,asali ma shine ya kamata ya hau kan karagar mulki amma saboda tsananin son da yake yiwa dan uwan nasa Ruguzan ya hakura ya bar masa sarautar.A takaice dai a duniya babu abinda Yarima Darwaz yakeso a duniya sama da Sarki Ruguzan,don haka a wannan rana yana cikin tsananin bakin ciki wanda ba zai iya misaltuwa ba kuma gashi ya kasance mutum mai bakar zuciya gami da rashin imani fiye da Sarki Ruguzan,don haka a wannan rana hatta fadawan kasar ma a tsorace suke dashi suna baya baya don gudun kada ya huce haushinsa a kansu.Lokacin da wadannan dakaru masu wadanda suka tafi neman Siyama suka dawo sai suka zube kasa agaban Yarima Darwaz suka sunkui da kawunansu kas aka rasa wanda zaiyi bayanin cewar ba aga Siyama ba wacce ta kashe Sarki Ruguzan.Koda Darwaz yaga haka sai ya kara fusata ainun ya yunkura da sauri ya zare takobinsa da nufin ya hau Dakarun da sara,kawai sai yaji an daka masa tsawa.A fusace ya waiga,koda yaga wanda yayi masa tsawar sai jikinsa yayi sanyi ya sauke takobin tasa kasa cikin sanyin jiki.Ba wani bane yayi masa tsawar ba face matarsa ZUMAIRA.Zumaira ya karaso gaban Darwaz ta karbe takobin dake hannunsa ta dubeshi tace,idan ka kashe wadannan dakaru bazaka sami sakamakon komai ba face na dadin bacin rai da bakin ciki tunda asarace ga masarautarmu.Tunda dai Sarkin yaki da manyan zakwakuran dakarunsa sun bi bayan wannan Yarinya na tabbatar da cewar sai ka yanke mata hukuncin daya dace da laifin data tafka.Koda Zumaira tazo nan a zancenta sai Yarima Darwaz ya zubar da hawaye sannan ya matsa gaban kabarin dan uwan nasa ya dafashi yace,Na rantse da kaunar da nake yiwa Sarki Ruguzan sai nayiwa Siyama mugun kisan gilla irin wanda ba a taba yiwa wani mahaluki ba a doron kasa,kuma sai na shafe gaba dayan kabilarsu daga kan doron kasa yadda har abada ba za a sake tunowa dasu ba.Koda fadin hakan sai Darwaz ya sake kwantawa akan kabarin Sarki Ruguzan ya fashe da sabon matsanancin kuka har saida Zumaira tazo ta tasheshi tsaye ta shiga rarrashinsa ta jashi izuwa cikin gidan Sarautar sannan kowa ya kama gabansa. ¤¤¤¤¤¤¤ SARKIN YAKIn birnin kisra basu dawo daga bin sawun Siyama da jama'ar kabilarta ba sai bayan kwana uku.A wannan lokaci ma tuni anyi bikin nadin sarautar Sarki Darwaz ya hau karagar mulki amma a tsawon kwanaki ukun Sarki Darwaz bashi da wani sukuni da kwanciyar hankali,burinsa kawai yaga sarkin yaki ya dawo tare da Siyama.Da rana tsaka su Sarkin yaki suka shigo fadar birnin kisra suna shigowa fadar suka iske Sarki Darwaz zaune bisa karagar ya sunkui da kansa kas,gashi ana ta tafiyar da harkokin mulki amma shi Sarki Darwaz yayi shiru kamar bashi ne sarkin ba domin fadawa ne suke zartar da komai.Koda Sarki Darwaz yaji sawun dakaru da yawa sun shigo cikin fadar saiya dago da kansa da sauri amma dayaga sarki yaki akan gaba babu Siyama a tare dashi sai jikinsa ya kama tsuma,zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda tsananin fushi.Sarkin yaki ya zube kasa gaban sarki Darwaz bisa guiwoyinsa yana mai sunkui da kansa kas yace,ya shugabana munbi sawun Siyama har izuwa sansaninsu a daji inda muka isle babu ko kaza a wajen sun kwashe komai nasu sunyi hijira.Mun sake bin sawunsu izuwa cikin dajin har tsawon kwanaki biyu amma ko duriyarsa bamujiba domin sawunsu dana dabbobinsu ma ya dauke.Al'amarin dayayi matukar bamu mamaki kenan tamkar aikin sihiri.Koda sarkin yaki yazo na a zancensa sai sarki Darwaz ya mike tsaye a fusace ya kwarara uban ihi wanda ya firgita kowa a cikin fadar.Faruwar hakan ke da wuya sai ga Bokan Garin wanda ake kira HURGAS IBINI SALBARU ya bayyana tsulum a tsakiyar fadar.Hurgas ya karasa gaban Sarki Darwaz suka kurawa juna idanu sannan Boka Hurgas ya risina yace Ya shugabana,Siyama da sauran jama'arsu suna nan a cikin yankin kasarka sun saje da mutane a cikin daya daga cikin biranenka,bisa wannan dalili ne yasa ba a gano inda suka ba.Idan har ka bari suka fice daga cikin wannan nahiya tofa har abada baza a dauki fansa akansu ba kuma komai daren dadewa sai Siyama ta dawo kasar na ita da jama'arta ta rushe mulkinmu sun karbi karagar kasar bisa taimakon wata hatsabibiyar jaruma wacce zata addabi gaba dayan sarakuna da attajiran duniya.Koda Boka Hurgas yazo nan a zancensa sai hankalin Sarki Darwaz ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe ya dubi Hurgas cikin alamun tsananin damuwa yace,yakai abin dogarona iyaye da kakanni maza ka sanar dani birnin da su Siyama suke domin nayi shiri da kaina na jagoranci dakarun yaki masu yawa muke mu shafesu daga doron kasa.Koda jin wannan batu sai Boka Hargus yayi ajiyar zuciya cikin alamun karayar zuciya yace,ai nayi iya kokarina domin na gano inda suke amma na kasa saidai kawai na sami nasarar ganowa cewa suna bangaren gabashin kasar nan.Don haka ku hanzarta tunkarar dukkanin manyan birane da suke gabas har izuwa karshen iyakarmu.Koda jin wannan batu sai Fuskar Sarki Darwaz ta fadada da murmushi na farinciki nan take ya dubi Sarkin Yaki Amzad yace maza kaje ka shirya mana sabuwar runduna ta mayaka dubu dari uku,ni da kai zamu jagorancesu izuwa gabashin kasar nan kuma tun kafin mu tafi inason a tashi manzanni su tafi izuwa biranen dake karshen iyakokinmu a gayawa shugabanninsu cewar su rufe kofofin garuruwansu yadda ba shiga ba fita har sai na aiko da umarni.A sannan ne fada ta watse kowa ya kama gabansa.Har Sarki Darwaz ya jiya zai shiga cikin gidan sarautar saiya juyo da sauri ya dubi Boka Hurgas a cikin alamun damuwa a karo na biyu yace,yakai abin alfaharin birnin kisra waishin wace shu'umar budurwar jarumar da idan ta hadu da Siyama zata taimaketa har ta rushe mulkinmu?Koda jin wannan tambaya sai boka Hurgas yaja dogon numfashi gami da ajiyar zuciya sannan yace hakika kayi tambaya mai kyau kuma mai muhimmanci saidai a yanzu babu isasshen lokaci wanda zai isa na baka labarin wannan shu'umar jaruma wacce daidai take da GUGUWAR ZAZZAGAR BALA'I ga dukkan sarakunan duniya.Shawarar da zan baka kawai itace kayi hakuri zan baka labarin wannan jaruma ko da akan hanyarmu ne ta dawowa bayan mun sami nasarar gano inda su Siyama suke mun shafesu daga doron kasa. A WANE HALI 'YAN KABILAR SU SIYAMA SUKE CIKI? SHIN SARKI DARWAZ ZAI CIKA BURINSA? INA LABARIN SIYAMA DA TAKE GUDUN TSIRA? SHIN ZATA KOMA CIKIN KABILARTA? A WANE HALI MAHAIFINTA DA MAHAIFIYARTA SUKE CIKI? INA LABARIN ABOKAN TAFIYARTA DATA UMARCESU SUYI GABA,A WANE HALI SUKE CIKI? Mu hadu a GUDUN TSIRA kashi na uku don jin cigaban wannan kasaitaccen labari. Da alamu littafin bai karbu ba ko Dan ba samun comments. Barkan ku da Sallah.Allah GUDUN TSIRA★ Littafi Na Uku(3) Part A ★A-H Physicist★ KODA JIN WANNAN BATU NA BOKA hurgas sai Sarki Darwaz ya dubi hurgas cikin matukar mamaki yace,au dama tare da kai zamu tafi neman Siyama da jama'arta?Boka Hurgas yace kwarai kuwa ai na fika tashin hankalin idan har ban tabbatar da mutuwar Siyama ba da jama'arta saboda in dai wannan lokaci yazo to duk wani Boka dayake wannan nahiyar ma sai sun kashe shi sun shafe harkar tsafi gaba daya tamkar ba a taba yinta ba a wannan nahiyar,duk cikin bincikena na ga wannan al'amari.Sa'adda sarki Darwaz yaji wanann batu sai ya gyada kai yace ai kuwa indai muka hada karfi da karfe mu ta kai dole ne muga bayan wadannan makiyan namu.Yanzu zan shiga cikin gida nayi shiri in yaso ka samemu a can kofar fada inda zamuyi zuga mu tafi gaba daya.Lokacin da boka Hurgas yaji wannan batu saiya bushe da dariya sannan yace aini bana bin zugar mutane saidai ku riskeni a can gaba ko hanya ina jiranku.Nine zan zamo mai yi muku jagora har mu riski abokan gaba tunda nine zanfi kowa saurin gano inda abokan gabar suke.Koda gama fadin sai boka Hurgas ya bace bat daga cikin fadar tamkar bai taba wanzuwa ba a wajen.Koda ganin hakan sai sarki Darwaz ya ruga izuwa cikin gidan sarautar ya iso cikin ainihin turakarsa ya shiga kimtsa kansa yana sanya kayan yaki.Yana cikin wannan haline matarsa Larisa tare da 'yarsa gimbiya Husaira suka shigo cikin turakar da sauri cikin tsananin tashin hankali.Husaira ta kasance kyakkyawar budurwa abar kwatance domin da kadan Siyama zata fita kyau.Ga wanda ma bai iya tantance kyawu ba cewa zaiyi sunyi kunnen doki.Lasira da Husaira suka sha gaban Sarki Darwaz idanunua cike da kwalla suna shirin fashewa da kuka.Kawai sai Lasira ta kama kafadun Darwaz ta rike a lokacin da hawaye ya zubo mata ta dubeshi tace,haba yakai mijina saboda me zaka bar karagar mulkinka ka tafi farautar kabilar Banu Hanzar alhalin baka da tabbacin ganinsu tunda sunyi hijira sun gudu.Kayi sani cewa zata iya yiyuwar cewa tuni ma sun fice daga cikin nahiyar nan gaba daya.Ka tuna cewa fa kwananka uku kacal akan karagar mulkin nan,Idan har wani tsautsayi ya sameka a cikin wannan tafiya shike nan fa ka rasa karagarka nida 'yarka kuma rayuwarmu ta shiga cikin hadari kenan tunda ka san cewa kana da makiya da yawa a cikin majalisar garin nan da cikin jama'ar gari.Lokacin da Lasira tazo nan a zancenta sai Sarki Darwaz ya bushe da dariya,al'amarin dayai matukar baiwa Larisa mamaki da haushi kenan,ta kura masa idanu,ita kuwa Husaira sai ta sunkui da kanta kas tana zubar da hawaye kawai.Daga can sai Darwaz ya tsuke bakinsa kuma ya hade fuska ya dubi Lasira yace,yake matata yanzu ke ashe har kina tunanin cewa wani abu zai iya taba lafiyata a wannan fita da zanyi?Ashe kin manta da cewa ni mutum ne mai tsananin sa'a da rabo bisa dukkan abinda na sa agabana?A iya saninki dani tun muna matasa wane abune kika taba ganin ya gagareni?Larisa ta girgiza kai tace duk abinda kasa agabanka sai kaga bayansa amma wannan karon naji a jikina cewa lallai zaka riski matsala kasancewar mai Laya ya kiyayi zamani.Darwaz ya gyada kai cikin murmushi yace,ai ko Giwa ta fadi tafi karfin karnuka su dasa mata wawa sai a sannu.Kada ki manta cewar 'yarki Husaira ta gadoni a jarumtaka gani da taurin zuciya,don haka ko babu ni dole ne ayi shakkarki saboda ita kuma itace zata gaji karagata.Ke Husaira mene dalilin da yasa kike zubar da wannan hawaye daga idanunki?Shin kina tsoron kada na fita ne wani tsautsayi ya sameni?Koda jin wannan tambaya sai Husaira ta dago kai ta dubi sarki Darwaz cikin murmushi tana mai share hawayenta tace,ko kadan ni bana tunanin akwai wani mahaluki ko wani tsautsayi da zai sameka.Ina zubar da wannan hawaye ne saboda kawai takaicin kace bazaka tafi tare dani ba.Ka sani cewa a rayuwata ban taba fita yaki ba na daukar rayukan bil'adama da yawa.Wannan ce kadai damar da nake da ita wacce zan gwada tsantsar iyakar jarumtakata kuma a yanzu ne takobina za ta sami damar shan jini mai yawa ta more,amma gashi ka hana.Ina mai rokonka don darajar iyayenka da kakanninka wadanda suka shude kayi mini izini yanzun nan naje na kimtsa cikin gaggawa ayi wannan tafiya dani.Ka tuna cewa ni kaina jarumtakata ta ninka ta marigayi sarki Ruguzan sau uku,bare kai kanka.Ai abin kunya ne ma ace kaine da kanka zaka tari Siyama ka yaketa,ni ya kamata ka barni da ita a matsayina na 'ya mace kamarta nayi mata kisan gilla na ciro kanta nazo maka dashi.Lokacin da Husaira tazo nan a zancenta sai mahaifiyarta ta shara mata mari ta dubeta a fusace tace,yanzu ke dama manufarki kenan,ashe ban sani ba?Wato zuciyarki ta kekashe ta zama irin ta ubanki kin gadoshi da rashin imani da tausayi alhalin kina matsayin 'ya mace wacce nake son tayi aure ta bar mini zuri'ar dazanyi alfahari da ita mai farin jini a cikin al'umma?Koda Larisa tazo nan a zancenta sai Husaira da Sarki Darwaz suka duni junansu suka bushe da dariya.Husaira ta hade rai ta dubi Larisa tace yake ummina ki sani cewa kyan 'da ya gaji ubansa,idan mai mulki yana son ya sami karfi da biyayyar talakawansa dole ne ya kasance mara tausayinsu.Ni SARAUNIYAR GOBE ce wadda take da burin dama yafi na mahaifinta don ni so nake na mallaki duk kasashen dake nahiyar nan gaba daya su zamo a karkashin mulkina.Koda jin wannan batu sai Sarki Darwaz da Larisa suka kurawa Husaira idanun cikin tsananin kaduwa da mamaki,daga can sai Sarki Darwaz ya bushe da dariyar farinciki yace,tabbas yaune na san cewa banyi haihuwar banza ba tabbas na sami irin 'yar dana dade ina mafarkin samu.Koda gama fadin hakan sai Sarki Darwaz ya rungume Husaira cikin murna yana A*H PHYSICIST maicewa,jeki ki shirya yake 'yata lallai tare dake zamu tafu wannan gagarumin yaki.Kafin Sarki Darwaz ya gama rufe bakinsa tuni gimbiya Husaira ta ruga izuwa cikin turarkata.Ita kuwa Larisa saita durkushe a kasa ta fashe da kukan bakinciki.Ko kallonta Sarki Darwaz baiyi ba ya gama shirinsa ya zuba dukkanin makamansa na yaki a jikinsa sannan ya fice daga cikin turakar ya bar Larisa a zaune a kasa dirshen tana rusa kuka.Wannan shine abinda ya faru a cikin birnin Kisra bayan Siyama ta sami nasarar kashe Sarki Ruguzan da kyar da sidin goshi domin ta kawo karshen mulkin zaluncin da yakeyi a nahiyar harma jama'arsu su sami damar gudanar da rayuwarsu a cikin daji a kwanciyar hankali.Abinda bata sani bashine ALLURA TA TONO GARMA,domin babu wani sauki talakawa zasu samu face karin matsawa,talauci da fatara wacce sai sun gwammace mutuwarsu akan rayuwars a doron kasa.Kuma ta tsokano tsuliyar dodon daya shafe shekara da shekaru a kwance yana faman shara barci kuma ta kulla gabar da ba a san ranar karshenta ba. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤ AL'AMARIN JARUMA SIYAMA KUWA,lokacin da ta samu ta fice daga cikin gidan sarautar sarki Ruguzan tayi ta gudu a cikin daji har ta isa inda ta bacewa dakarun birnin Kisra,ashe cikin wata korama ta shige tayi nutso izuwa karshenta ashe akwai wata barauniyar hanya a kasan koramar nan wacce ta bulle har izuwa cikin wani kogon dutse wanda yake a cikin wani daji daban dake nesa sosai.Koda tayi doguwar ninkaya a kasan koramar ta tabbatar da cewar ta iso cikin wannan kogo sai ta taso izuwa saman ruwan ta shaki numfashi kuma ta tsaya ta dan huta sannan ta cigaba da tafiya a cikin ruwan har saida ta iso karshen katon kogon dutsen ta cikin wani dan karamin rami wanda mutum bazai taba tsammanin cewar za'a iya ficewa ta cikinsa ba. Tana fita daga cikin kogon ta tsinci kanta a cikin wannan katon daji wanda tace jama'arta su jirata.Nan take ta kama waige waige da kalle kalle cikin tashin hankali tana zargin ko wani abu ya sami jama'arta ne?Nan take tayi wani irin fito na inkiyar da sukeyi a daji a duk sa'adda suka shiga daji farauta a yayin da suka hango dabbar da suke son kamawa.Bisa mamaki sai taji an amsa mata da irin fion nata sai ga wani babban hadimi na mahaifinta ya fito daga cikin wanu surkuki daya buya ya dubeta cikin murna ya yafito ta da hannu.Cikin farin ciki ta ruga izuwa wannan hadimi shima ya juya ya ruga izuwa wani bangare dabam na dajin.Saida sukayi tafiya mai tsawo tana biye dashi taga an shiga wani sakon daban wanda ma bata taba shigarsa ba sai taga dajin ya zamo sabo a wajenta.Kwatsam sai ta an shigo da ita wani sabon tafkeken kogon dutse wanda ya akai girman gari guda wanda bata taba sanin wanzuwarsa ba a cikin dajin.Shidai wannan kogon dutse a karkashin wadansu dogayen bishiyoyi yake masu manya manyan ganyaye wadanda suka lillubeshi babu yadda za ayi mutum yaga wannan kogon dutse face ya ture ganyayyaki da bishiyoyi.Suna shiga cikin kogon sai Siyama tayi arba da gaba dayan mutanen kabilarsu mazansu da matansu,yaransu da manyansu.Shugaba Sharwan ne kadai a tsaye,amma kowa a zaune yake a kas sun jeru sahu sahu kuma duk sunyi shiru tsit tamkar babu mai rai a cikinsu.Koda aka ga shigowar Siyama cikin kogon dutsen sai kowa ya kamu da tsananin farinciki.Nan take Sharwan ya ruga gareta suka rungume juna yana mai cewa ni san cewar sai kin dawo a raye gareni.Jikina ya bani cewar bazaki mutu ba yake 'yata abar alfaharina.Cikin tsananin farin ciki Siyama ta janye jikinta daga cikin na Sharwan ta dubeshi cikin mamaki tace,yakai Abba yaya akayi ka amince da duk abinda na umarceka da ayi a cikin wasikata.Kuma yaya akayi kuka gano wannan boyayyan kogo inda Dakarun Kisra bazasu taba ganowa ba?.Koda jin wadannan tambayoyi sai Shugaba Sharwan ya bushe da dariya sannan yace yake 'yata kiyi sani cewa ba wani abu bane yasa na bi duk umarnin da kika bani ba acikin wasikar taki ba face na yarda da kwakwalwarki gami da tunaninki da hankalinki baki taba shirya wani abu ba wanda aka kasa samun nasara ba.Dalilina na biyu wanda shine ne mafi muhimmanci shine bamu da wani zabi na samu tsira daga sharrin Sarki Ruguzan face mu yanke hukuncin kashe shi kuma muyi hijira ta zuwa wani dan lokaci kafin a sami sauyin Sarki mai adalci...Saidai Kash!Mun saki reshe mun kama ganye domin sarkin daya hau karagar mulkin Birnin Kisra a yanzu masifarsa da bala'insa sun ninka na Sarki Ruguzan sau goma.Samun azzalumin sarki kamarsa a duniya sai an tona.Nidai a sanina Sarki.Darwaz wanda ya kasance yaya ga Sarki Ruguzan ya tafi wata nahiya dabam ya tare a cikin daji yana farauta kuma yace bazai dawo gida ba sai bayan shekara ashirin,ashe ya dawo birnin Kisra babu shiri sakamakon wata rashin lafiya da dan'uwan sa Sarki Ruguzan yayi bara.Ina mai tabbatar miki da cewar a duniya babu abinda Sarki Darwaz yakeso sama da dan'uwansa Sarki Ruguzan don haka duk yadda zai yi yaga ya dauki fansar ran Ruguzan a kanmu sai yayi don haka nasan cewa da kansa zai jagoranci dakaru ya fito farautarmu.Dole ne yanzu muci gaba da tafiya dare da rana babu sassauci,kuma dole ne mu kiyaye shiga cikin biranen kasar nan face mun tura 'yan leken asirinmu sun gano halin da birnin yake ciki ta hanyar batar da kamanninsu izuwa matsayin 'yan gari.Ba zamu taba samun kwanciyar hankali ba face mun ga mun fita daga cikin wannan nahiya gaba daya.Yake 'yata inason ki sani cewar muna cikin tsananin TSAKA MAI WUYA dole ne muyi niyar yaki da dukkanin karfinmu da ranmu kodai mu tsira ko kuma a shafemu daga doron kasa gaba daya.Lokacin da shugaba Sharwan yazo daidai nan a jawabinsa sai hankalin Siyama ya dugunzuma ainun fite da ko yaushe.Nan take idanunta suka ciko da kwalla tace,yakai Abbana ka yafeni kai da dukkan sauran jama'armu hakika na jefamu a cikin masifa.Koda jin wannan batu sai Shugaba Sharwan yayi murmushi yace yake 'yata kiyi sani cewa baki da wani laifi a wajenmu domin kokin yi abinda kikayi ko bakiyi ba sai mun shiga cikin wannan tashin hankali da masifa tunda tuni Sarki Ruguzan ya jefamu a cikin wannan tafarki.Inason ki kwantar da hankalinki kuma ki tattauna da dukkan dakarunmu domin mu san hanyar da zamubi mu kare kanmu harmu sami nasarar fita daga cikin wannan nahiyar gaba daya.Yanzu ba baku rabin sa'a kacal ku gama dukkanin shirinku domin mu cigaba da tafiya.Koda jin wannan batu sai Siyama ta kirawo gaba dayan dakarun nasu suka taru a gabanta,a sannan ne taga su Muzaru ashe tuni sunzo sun riski su Shugaba Sharwan.Saida Siyama da dukkanin Dakarunta suka shafe rabin sa'a cif sannan suka kammala dukkanin shirye shiryensu,nan take akayi wata dabara aka lullube jikin kowa da koren ganya,hatta dawakai da dabbobi saida aka lullubesu da ganyaye yanda ko kada ba a ganin jikinsu sannan aka fito daga cikin kogon dutsen aka ci gaba da tafiya,mata suka goya yara kanan,su kuma tsofaffi da miskinai matasa suka goyasu a bayansu akayi ta tafiya cikin sauri sauri gudu gudu.A ko yauhse dakarun da suka kware a iya leken asiri suna kan gaba sai sunyi tafiya mai nisa sun tabbatar da cewar babu wani mugun abu a gabansu sannan suke dawowa su bayar da umarnin a cigaba da tafiya.A bayan tawagar kuma a ko yaushe wadansu dakarun leken asiri ne suna bazuwa gaba da yamma,kudu da arewa don tabbatar da cewar ba wanda ya biyo sawunsu.Haka dai aka ci gaba da wannan tafiya ba dare ba rana har tsawon kwana uku ba tare da an gamu da wani mugun Abu bà. ★GUDÛN TSIRA★ Littafi Na uku (3) Part B ★A-H Physicist★ Ba tare da an gamu da mugun abu ba kuma duk sa'adda aka gaji ko lokacin barci yayi sai a nemi wuri mai huduwar gaske mai hadarin gaske inda baza a taba zaton cewa wani abu mai rai ba zai iya shiga wajen ba,sai a shiga a kwakkwanta.A safiyar kwana na ukun ne suka hangi wani babban Birni wanda ake kira MADINATUL SULTAN a can gaban dajin da suke,tazarar dabata wuce ziri'a dari da sittin ba.Koda hango wannan birni na Madinatul Sultan sai kowa ya cika da farin ciki musamman Shugaba Sharwan.Nan take Sharwan ya dubi Siyama cikin murmushi yace,yake 'yata ki sani cewa mun iso birnin Madinatul Sultan inda zamu iya hutawa har tsawon kwana uku a cikin kwanciyar hankali kuma mu kara hada guzuri mai kyau mu ci gaba da tafiyarmu.Koda jin haka sai Siyama tayi ajiyar zuciya sannan tace,yakai Abbana kayi sani cewa nikam bani da kwanciyar hankali a duk inda zamu shiga,ina mai shawartarmu damu hakura da shiga cikin birnin Madinatul Sultan kawai mu kewaye ta bayan birnin mubi ta cikin daji mu ci gaba da tafiyarmu.Yayin da Sharwan yaji wannan batu sai ya girgiza kai yayi murmushi sannan yace,shin kin manta ne cewar shugaban da yake mulkin birnin madinatul Sultan abokina ne kuma aminina?Tun muna yara kanana muka saba a daji wajen farauta saboda shakuwar da mukayi dashi ne ma na bashi 'yar kabilarmu guda daya ya aura a sirrance ba tare da Sarkin Kisra ya sani ba.Akwai amana da alkawari mai girma a tsakaninmu dashi,ai na tabbatar da cewa baza a hada baki dashi ba a cutar damu ba,kuma ko me ake ciki ma ai yanzu mun baro dakarun kisra a can bayanmu,koda an aiko manzon sai mun rigashi isa birnin Madinatul Sultan bare batun dakaru masu yawa wadanda zasu dana tarkon cutar damu.Siyama ta numfasa tace na yarda da duk abinda ka fada ya Abbana.Bazan hanamu shiga cikin wannan birni ba,amma kafin mu shiga din inason ka fara aikawa da manzo a sirrance yaje ya gana da Sultan ya sanar dashi duk halin da muke ciki,idan har yace mu shigo cikin birnin nasa sai mu shiga tunda dai mun bashi amanar kanmu.Koda jin wannan batu sai Shugaba Sharwan yayi murmushi yace,tabbas nima na gamsu da wannan shawara.Nan take aka tashi wani kwararran dan leken asiri wanda ake kira da Jamar yayi shiga irin ta fataken birnin Kisra aka bashi dukiya da dakaru kimanin mutum arba'in bisa keken doki suka durfafi birnin Madinatul Sultan.Suma dakarun nasa gaba daya shigar irin dakarun Birnin Kisra sukayi.Lokacin dasu Jamar suka iso kofar birnin Madinatul Sultan basu fuskanci matsalar komai ba don ana ganinsu aka bude musu kofa ko cajesu ba ayi ba suka kunna kai cikin birnin,sukayi ta tafiya basu tsaya a ko ina ba har saida suka iso kofar fadar birnin.Suna zuwa aka yi musu iso suka shiga cikin fadar suke zube a gaban Sultan suka kwashi gaisuwa.Sultan ya dubesu cikin alamun mamaki yace yaku wadannan bakin fatake ku gabatar da kanku domin ban sanku ba daga cikin fataken dana saba yin mu'amala dasu ba daga Birnin Kisra ba.Koda jin wannan batu sai Jamar ya zura hannunsa a cikin aljihu ya dauko wata wasika ya bayar a mikawa Sarki Sultan.Koda Sarki Sultan ya warware wasikar ya karantata a gaban fadawansa sai ya kamu da tsananin farinciki ya mike tsaye da sauri ya rungume Jamar yana mai yi musu lale marhaban tamkar yaga 'yan uwansa na jini.Al'amarin daya daurewa 'yan majalisarsa kai kenan.Nan take Sarki Sultan yasa aka kai su Jamar masauki mai kyau aka kawo msu abinci da abin sha mai rai da lafiya.Kafin ma su fara cin abincin sai ga Sarki Sultan da kansa yazo har cikin turakar da suke,dakarunsa na take masa baya.Nan take ya sallami dakarun nasa yace duk su kama gabansu su bashi wuri yana son ya gana da bakinsa.Nan take kuwa dakarun suka fice daga cikin gidan suka barshi tare dasu Jamar.Suna gama fita Sultan yasa aka rufe kofar turakar da tagoginta don kada ma iska ta dauki sautin zancen da zasuyi takai izuwa kunnen dakarun nasa.A sannan ne Sarki Sultan ya dubi Jamar yace,Ya kai wakilin babban aminina,kayi sani cewa lallai rayuwar kabilar Banu Hanzar tana cikin tsananin hadarin gaske domin tuni wani aljani yazo da sako daga sabon sarki na Kisra cewar da zarar kun iso Birnina na sa a kamaku gaba dayanku a tsare a kurkuku har Sarkin yazo ya riskeku.Tuni na karbi wannan sako kuma na tabbatar da cewar zanbi umarni a zahiri,amma a badini nayi watsi da umarnin Sarki Darwaz domin irin amanar dake tsananina da Shugaba Sharwan bazata barni na bari a cutar daku ba.Tuni wannan aljani ya juya da nufin ya koma wajen Sarki Darwaz ya sanar dashi cewa ya isar da sakonsa a gareni,amma sai na tura wani babban hadimina wanda yafi aljanin karfin damtse dana sihiri ya bishi a baya ya tsafanceshi ya kulleshi a cikin wata kwalbar sihiri domin kada ya ganku akan hanya yaje ya tona muku asiri a riskeku a kawar daku.Yanzi ina son ku bari sai dare ya raba sannan kuje ku shigo da mutanenku izuwa cikin garin nan.Hatta masu gadin kofar birnin nan zansa a sauyasu a cikin daren nan na yau na zuba yardaddu a kan aikinsu.Idan ku ka shigo zan rana muku dukkan kayayyakin daya kamata domin ku saje da jama'ata domin ku sami damar tanadar da guzurin da kuke bukata ku kammala dukkan shirinku sannan ki ci gaba da tafiyarku harku cimma burinku na fita daga wannan nahiyar gaba daya. Ina mai tabbatar muku da cewar sai kun bar birnina da kamar kwana bakwai sannan su Sarki Darwaz zasu iso kuma duk irin binciken dasuyi bazasu taba gano cewar na baku mafaka a birnina.Lokacin da Sultan yazo nan a zancensa Sai farinciki ya lullube su Jamar suka zube kasa suna yi masa godiya.Kamar yadda Sarki Sultan ya shirya kuwa haka al'amarin suka kasance wato saida dare ya raba san nan aka sauya nasu gadin birnin na Madinatul Sultan sannan akaje aka shigo da kabilar Banu Hanzar gaba dayansu izuwa cikin birnin a sirrance ba tare da kowa ya sani ba bayan an yi musu shiga irinta mutanen birnin.Siyama da mahaifiyarta da shugaba Sharwan kuwa har cikin ainihin turakar Sultan aka kaisu suna yin arba da juna sai Sultan ya ruga ga Sharwan suka rungume juna suna masu fashewa da kukan farin cikin sake saduwa domin rabonsu da ganin juna a kalla yakai shekara goma sha biyar.Sultan ya janye jikinsa daga cikin na Sharwan a lokacin daya Hango Siyama da mahaifarta ya dubi Siyama cikin tsananin mamaki sannan ya dubi Sharwan yace,yanzu wannan Siyama ce ta girma haka?Sharwan ya gyada kai cikin murmushi yace,kwarai kuwa wanna Siyama ce rabonka da ita tun tana da shekara uku kacal a duniya,wata rana sa'adda ka kawo mana ziyara a lokacin da ka fito farautarka ta karshe harka daura mata wata laya a wuyanta kace mu adanata a jikinta har abada.Yanzu haka layar na jikinta tun wancan lokacin tana bata tsananin kulawa yadda ya kamata.Koda gama fadin hakan sai Sharwan ya taka yaje inda Siyama take ya zura hannunsa cikin wuyan Rigarta ya janyo wata siririyar laya dake zagaye a wuyanta wacce akayita da hakorin zaki guda daya.koda Sultan yayi arba da wannan laya sai ya kamu da tsananin farinciki sannan ya dubi Siyama yace yake 'yata kiyi sani cewa asalin wannan laya ta kakana ce wanda ya haifi ubana nima gadonta nayi kuma ubana ya tabbatar mini da cewar duk wanda ya girma tare da layar a jikinsa babu makiyinsa dazai taba samun nasara akansa.Kuma duk irin tsananin rintsin da mutum zai shiga sai dai kawai yasha wuya.Har yau har gobe ban haihu ba kuma bisa binciken danayi a tsafi da wanda matsafa sukayi mini bazan taba haihuwa ba a takaice dai har na mutu bazan sami magaji ba.Mahaifinki yayimini abinda har na mutu bazan iya saka masa da komai koda kuwa zan bada raina a matsayin fansa ga nasa,bisa wannan dalili ne na sallama wannan laya tawa a gareki tunda kina yarinya karama,tunda shima bashi da wani 'da a duniya saike kadai.Rayuwarki taci gabanki har izuwa lokacin da zaki gajeshi shine kadai babban burinsa a doron kasa.Ina son mahaifinki yaga wannan rana da idanunsa kafin ajali ya riskeshi.Koda Sultan yazo nan a zancensa sai na take Siyama taji ta kamu da tsananin kaunarsa don haka bata san sa'adda ta ruga gareshi ba ta runguemshi tana mai fashewa da kukan farin ciki domin ta tabbatar da cewa basu da wani masoyi a doron kasa wanda yafi Sultan.Bayan hake ne Sultan ya kirawo Matarsa wacce ta kasance 'yar uwar Ilela mahaifiyar Siyama uwa daya uba daya wacce ake kira da suna SHAMIRAT.Koda Shamira ta shiga cikin turakar tayi arba da yar uwarta Ilela sai ta cika da tsananin mamaki gami da farinciki.Lokaci guda suka ruga suka rungume juna suna masu fashewa da kukan murna suna kankame jikinsu tamkar kara aka tsaga,kuma a danginsu su kadai ne suka rage.Bisa dole aure ya rabasu suna kuka kuma tin daga ranar da Sultan ya auri Shamirat ya dawo da ita birnin Madinatul Sultan ita da Ilela basu sake ganin juna ba,kuma basu taba zaton zasu sake saduwa ba,domin a ka'idar dokar Birnin Kisra duk mutumin da aka bashi mukamin shugabanci na wani Birni to shida Iyalansa shiga cikin Birnin Kisra da dukkan dazuzzukan da suke kewayenta sun haramta gareshi.Saida Ilela da Shamirat suka dade a kankame da juna suna kukan murna sannan Shamirat ta farga da Siyama ta hangota a tsaye a can gabansu.Da yake Siyama tana kama da mahaifiyarta,Shamirat na ganinta ta gane cewa 'yar suce,don haka sai ta cire jikinta daga cikin na Ilela ta bude hannayenta a lokacin da hawaye ya zubo mata tana kallon Siyama tace,taho gareni yake 'yata naji dumin jikinki kafin mu sake rabuwar karshe.Nice kadai 'yar iwar mahaifiyarki wacce tayi saura a doron kasa.Koda jin wannan batu sai Zuciyar Siyama ta karaya,nan take itama idanunta suka ciko da kwalla ta fara zubar da hawaye bata san sa'adda ta ruga izuwa ga Shamirat ba suka rungume juna suka suna kuka.A'amarin daya baiwa su Sharwan matukar tausayi kenan suma suka ci gaba da kukan.Kamar yadda Sultan ya tsara haka duk al'amarin ya kasance wato saida Kabilar su Siyama suka kwana biyu a cikin Birnin Madinatul Sultan ba tare da wani dan garin ya fahimci hakan ba,sannan Sultan yasa aka shirya musu guzuri mai yawan gaske,kuma aka nuna musu hanya mafi sirri wacce zasu fice daga cikin nahiyar gaba daya.Lokacin da Sharwan yazo suyi bankwana da Sarki Sultan sai duk su biyun suka kasa cewa komai suka fashe da kuka suka rungume juna.Tsawon 'yan dakiku suna kankame sannan Sultan ya janye jikinsa daga cikin na Sharwan ya dubeshi a lokacin da hawaye ya zubo masa yace,yakai abokina kayi sani cewa wannan rabuwa da zamuyi yanzu ina ganin cewa itace rabuwarmu ta karshe wadda har abada baza mu sake saduwa ba tunda zaku bar wannan nahiyar tamu ne gaba daya,bansan ranar da zaku sake dawowa ba.Wata kila kafin ku sake dawowa bana raye,wannan hawaye nawa da kaga ya zubo bisa dalili biyu ne.Dalili na farko shine na SO da KAUNAr dake tsakanina dakai.Dalili na biyu kuma hawaye ne na takaici bisa zamu rabu alhalin har yanzu ban sami damar dazan iya saka maka bisa abinda kayi mini a baya ba.Koda Sharwan yaji wannan batu sai nan take shima hawaye ya zubo masa yace,yakai Abokina kayi sani cewa bana fatan naga ranar dazaka saka mini bisa abinda nayi maka a baya.Kuma ko a yanzu ka gama saka mini tunda harka bamu mafaka a cikin birninka a irin wannan lokaci wanda babu wani shugaban birnin dake karkashin masarautar Kisra yayi kundunbalar dakayi domin ka siyar da rayuwarka ne Domin tamu. ★GÛDÛÑ TSÎRA★ Littafi Nà uku ( 3 ) Part C ★A-Haleefah Physicist★ Domin ka siyar rayuwar ka ne domin tamu.Koda jin wannan batu sai Sultan yayi murmushi yace ai taku rayuwar itace mafi amfani akan tawa domin kune kadai zaku iya kawo sauyin rayuwa a wannan Nahiya gaba daya,ku kawar da zalunci ku shimfida adalci.Abokina idan har hakan zata tabbata raina fansa ne akan naku.Inason ka saurara da kyau kaji shawarar dazan baku yanzu wacce idan karkuyi amfani da ita sai mafarkinku ya tabbata gaskiya a wannan Nahiya.Abinda nake nufi shine sai sauyi yazi mana an kawar sa zalunci irin nasu Sarki Darwaz.A duk sa'adda kuka hadu da wadansu mutane wadanda suka zo muku da wani sabon addini to ku yarda dasu kuma ku karbi addinin nasu.Sa'adda Sharwan yaji wannan batu shida Siyama da Ilela sai suka cika da tsananin mamaki.Sharwan ya dubi Sarki Sultan yace,yakai abokina yanzu kana nufin kenan akwai wani addini wanda shine na gaskiya wanda yafi duk Allolin da ake bautawa a wannan Nahiya,kuma yafi tsafi da dukkan Aljanun da akayi imani dasu?Sarki Sultan ya gyada kai yace kwarai kuwa kuma saduwa da ma'abota wannan addini shine burina na karshe.Tuni na dade da samun labarin wannan addini a wajen iyayena kuma suma tun suna yara suka sami labarinsa a wajen nasu iyayen.Da zarar na sadu da wadannan mutane zan ajiye tsafi na rungumesu.Lokacin da Sultan yazo nan a zancensa sai Sharwan ya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan ya dubi Sultan yace,yakai abokina yanzu yaza ayi na shaida wadannan mutane a duk sa'adda na sadu dasu?Sultan yayi gyaran murya sannan yace zaka iya shaida wadanan mutane ta hanyoyi guda biyu,hanya ta farko itace yanayin shigarsu.Ko yaushe zaka gansu a cikin sutura ta kamala mazansu da matansu,basu barin tsiraicinsu ya bayyana ba.Abu na biyu kuma shine sun kasance mutane masu gaskiya,amana gami da rikon alkawari.Basu dauki duniya a bakin komai ba.Babu abinda suke gudu sama da dukiya da mulki.Koda jin wannan batu Sai Sharwan ya girgiza kai yace,ni kuwa zan sa ido sosai duk ranar dana sadu da wadannan mutane zan karbi addininsu hanni bibbiyu domin kana fadin halayensu yanzu naji na kamu da tsananin kaunarsu bisa kyakkyawar mu'amalarsu,wanda duk wani mahaluki daya dauki irinta zai gudanar da rayuwarsa cikin kwanciyar hankali dajin dadi na har abada.Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube Sultan ya rungume Sharwan yana mai masa godiya sannan ya sake janye jikinsa daga cikin nasa suka fuskanci juna ya ce,yakai abokina kayi sani cewa tafiyar dake gabanku da kuma hadarin dake cikinta ba kadan bane domin kafin ku sami damar fita daga cikin Nahiyar nan sai kunyi tafiya ta a kalla wata bakwai da rabi,kuma akwai manyan kasashe guda uku a gabanku.Wannan birni nawa na Madinatul Sultan yayi iyaka da wata babbar lasa da ake kira DARUL HUNAN.Kafin ku isa iyakar sai kunyi tafiya ta kwana arba'in da daya.Indai kuka ketare wannan iyaka lafiya ba tare dasu Sarki Darwaz sun riskeku ba kun tsallake dukkan hadari.Ina ji a jikina cewa abune mayuwaci ku isa har can su Sarki Darwaz basu cimmuku ba domin nasan cewa sai sunyi amfani da kowacce hanya don ganin sun riskeku saboda da zaarar sun iso nan Birnina sunga bakwa nan zasu tabbatar da cewa kun wuce gaba.Tunda bani da tabbacin zan tsira da rayuwata,ina son ku tafi da matata Shamirat tunda kune kadai kuka rage mata a doron Kasa.Idan kuka barta anan tare dani Sarki Darwaz zai iya kashemu tare.Koda jin wannan batu sai Shamirat dasu Ilela suka fashe da kuka,shi kansa Sharwan bai san sa'adda ya kama kukan ba.Sultan ya dubi Siyama yace,yake 'yata kiyi sani cewa sai kin gaji da wannnan GUDUN TSIRA da kukeyi kinji kamar ki tsaya a kasheki ki huta,amma inason ki kasance mai juriya bisa duk irin tsananin da zaki fuskanta,kisa a ranki cewar dukkan tsanani yana tare da sauki.Idan gaba dayan Kabilar Banu Hanzar zasu kare ya zamana cewa ke kadai kada ki sare kuma kada ki cire babban burin dake ranki nason dawowa wanna kasa tamu domin kawar da zalunci.Koda gama fadin hakan sai Sultan yayiwa Sharwan bankwana na karshe inda matarsa Shamirat ta rungumeshi suka fashe da matsanancin kuka na bakin cikin rabuwa.Da kyar yar uwarta Ilela ta janyeta daga cikinsa,ai kuwa sai Sharwan ma ya sake rungumeshi ya fashe da kuka yana mai cewa Abokina bazan yarda na tafi na barka basaidai na zauna azo a kashemu gaba daya tare ko kuma mu tafi tare mu mutu a cikin wannan GUDUN TSIRA da mukeyi.Sa'adda Sultan yaji wannan batu na abokinsa Sharwan sai yakamu da tsananin tausayinsa ya dubeshi yace,na sani cewa babu ranar bakin ciki sama da ranar rabuwa da masoyi,to amma babu yadda zamuyi da kaddara,haka tamu kaddarar tazo,babu abinda zamuyi face mu kasance masu tunawa da junanmu tare da yiwa junanmu fatan alkhairi har sa'adda mutuwarmu zata riske mu,zanji dadi mutukar ka rike wannan a ranka.Haka dai Su Sharwan suka yiwa Sultan Sallama suka tafi matarsa Shamirat tana waigensa tana faman rusa kuma ana janye da ita.A lokacin Sharwan da Siyama ma suka yi ta waigen Sultan Suna zubar da hawaye zuciyarsu na kuna kamar zasu fasa yin tafiyar.A cikin daren ne su Sharwan suka sake sulalewa daga cikin Birnin Madinatul Sultan suka fice suka sake nausa cikin daji suna tafiya cikin sauri sauri gudu gudu kamar yadda suka saba ba dare ba rana har tsawon kwana bakwai.Duk sa'adda suka hadu da gungun yanfashi ko wadansu mugayen dabbobin daji sai kaga sun tarwatsasu farat daya sunci gaba da tafiyarsu. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤ A DAREN KWANA NA BAKWANI NE DA tafiyarsu Sharwan,Sarki Darwaz ya iso cikin Birnin Madinatul Sultan tare da rundunarsa ta yaki,'yarsa Husaira na daf dashi bisa kan doki sun jera.Suna isowa kofar Birnin saiga Boka Hurgas ya baiyana tsulum a gaban Sarki Darwaz yana mai kyakyacewa da dariya.Cikin fishi Sarki Darwaz ya dubeshi yace da kana ina muka shafe wannan doguwar tafiyar baka bayyana ba sai yanzu alhalin kace kaine zaka yi mana jagora a cikin tafiyar?Yayin da Boka Hurgas yaji wannan tambaya sai yayi murmushi yace ya shugabana ai tunda aka fara wannan tafiya ina biye daku kuma ina muku jagora saidai na baku tazara mai yawa,domin na iso nan Birnin tun a kwanaki shida da suka wuce.Tabbas zuwana da wuri yayi amfani domin na samo mana wani labari mai muhimmanci dangane da abinda muke zargi.Ko shakka babu shugaba Sultan yayi wadansu baki daga birnin Kisra a matsayin yan kasuwa,wato fatake,amma a cikin kwanaki biyu aka nemesu aka rasa acikin birnin nan.Bisa bincikena danayi na tura wadansu zakwakuran hadimaina na aljanu sun bi bayan wadannan fatake basu gansu ba kuma basu ji duriyarsu ba.Ya shugaba kasani cewa Sultan gawurtaccen matsafi ne don sihirin tsafinsa yafi nawa karfi,Ni abinda nake zargi shine wadannan fatake da akace sunzo fatauci kabilar banu Hanzar ne,kuma Sultan ne ya basu mafaka suka sauka har tsawon kwana biyu sannna suka sulale suka bar birnin nasa.Idan har Sultan yana son ya kubuta daga wannan laifi toya gaggauta fada mana inda wadannan fatake suke ko kuma ya gaya mana garin da suka nufa tafi muje mu gansu da idanunmu.Abu na biyu shine a bisa binciken danayi kafin mu baro Birnin Kisra na gano cewa akwai wata tsohuwar alaka ta zumunci mai karfi tsakanin Sultan da shugaban Kabilar banu Hanzar tun suna yara kanana,sa'adda suke haduwa a daji wajen farauta Kaga kenan akwai yiyuwar shugaba Sultan zai iya taimakon Kabilar Banu Hanzar ta kowacce Siga.Koda Boka Hurgas yazo nan a zancensa Sai Sarki Darwaz ya fusata ainun har jikinsa ya kama tsuma,zuciyarsa kuma ta kama tafarfasa,kawai sai ya yunkura zai sakarwa dokinsa limzani ya zabureshi da gudu izuwa Birnin Madinatul Sultan,amma sai Boka Hurgas ya daga masa hannu yana mai tsayar dashi.Kawai sai Boka Hurgas ya tsugunna ya debo kasar kofar Birnin ya shinshinata kawai yayi murmushi ya dubi Sarki Darwaz yace,ba shakka babu mutanen kabilar Banu Hanzar sun shiga cikin wannan birnin gaba dayansu don haka duk inda ma suke shugaba Sultan ya sani domin naji kamshin sawayensu a kan wannan kasa.Kafin Hurgas ya gama rufe bakinsa tuni Husaira ta zare takobinta ta sakarwa dokinta limzami ta banke masu gadin kofar birnin da karfin tsiya ta kunna kao cikin birnin a fusace.Ai kuwa sai Sarki Darwaz da sauran Dakaru suka rufa mata baya suka bar Boka Hurgas a tsaye anan yana ta kyalkyala dariyar mugunta da farinciki.Kai tsaye Gimbiya Husaira suka durfafi gidan sarautar Sarki Sultan.Bisa mamaki suna isa gidan sarautar sai suka iskeshi a bude wanwar ko masu gadi babu.A cikin gidan sarautar kuwa gaba dayan dakarun suna zazzaune sun ajiye makamansu a kas,kuma basa shirin tararsu.Koda suka iso tsakiyar gidan sarautar inda wani badakare yake sai suka iske wani mutum guda daya jal a cikin gagarumar shigar yaki.Koda suka matso daf dashi sai sukaga ashe ba wani bane face Shugaba SultanKoda suka zo dab dashi sai suka ja Linzamin dawakansu suka yi tirjiya kuma suka yi masa KAWANYA.Cikin tsananin fushi Sarki Darwaz ya dakawa Sultan tsawa yace,yakai Sultan kayi sani cewa kaci amanarmu ka hada kai da makiyanmu da basu mafaka,idan kana son ka tsira da rayuwarka data iyalanka to ka hanzarta sanar damu inda kabilar Banu Hanzar Suke.Koda jin wannan tambaya sai Sultan ya bushe da dariya,Al'amarin dayayi mutukar baiwa su Sarki Darwaz mamaki kenan.Daga can sai Sultan yayi shiru ga barin dariyar ya murtuke fuskarsa ya dubi Sarki Darwaz yace,ko me zai faru bazan sanar daku inda Kabilar Banu Hanzar suke ba kuma matata tana tare dasu.Yakai wannan azzalumin shugaba nawa kayi sani cewa ni bani da sauran buri a rayuwata face guda daya jal,wanda ko ban cika shi ba wadda ta kashe Dan'uwanka Sarki Ruguzan sai ta cika mini shi,wato Siyama 'yar aminina shugaba Sharwan.Na sani cewa zan mutu a hannunku amma ku sani kafin a kashe Gwaggon Biri sai yayi muguwar barna.Sultan na gama fadin hakan sai ya zare takobinsa ya daka tsalle sama kamar tsuntsu ya hau dakarun Birnin Kisra da SARA DA SUKA a saman yana fille musu kawuna tamkar ya kasance mai fuka fukai,yana shawagi a kansu saboda karfin sihirinsa.Koda Sarki Darwaz da Husaira suka ga irin mummunar barnar da Sultan yake yi musu sai suma suka zare takubbansu suka daka tsalle sama suka tare shi aka ruguntsume da sabon azababben yaki mai tsananin ban tsoro da ban al'ajabi. WAYE ZAI SAMU NASARA A WANNNAN GAGARUMIN GUMURZU TSAKANIN SU SARKI DARWAZ DA SARKI SULTAN? SHIN SARKI SULTAN YANA FADUWA KASA KUWA? A WANE HALI KABILAR BANU HANZAR SUKE CIKI? SHIN ZASU SAMI NASARAR FITA DAGA NAHIYAR NAN HAR SU HADU DA MA'ABOTA ADDININ MUSULUNCI SU MUSULUNTA? SIYAMA NA CIKA BURINTA NA DAWOWA NAHIYAR TA KAWAR DA MULKIN ZALUNCI? YAUSHE ZA'A YI GABA DA GABA TSAKANIN SIYAMA DA GIMBIYA HUSAIRA 'YAR SARKI DARWAZ,INDAN SUN HADU ME ZAI AFKU A HADUWAR TASU? WANE IRIN BURI BOKA HUGAS YAKE DASHI A RAYUWARSA? Mu hadu a GUDUN TSIRA kashi na hudu don jin ci gaban wannan kasaitaccen labari Amsa: Su Sarki Darwaz ne suke samun Nasara. Eh Sarki Sultan yana faduwa kasa. kwarai kuwa suna samun damar fita bayan sun sha wahala har su hadu da ma'abota addinin musulunci. Eh Siyama tana cika burinta,amma ba'azo gunba. Idan Siyama da Husaira sun hadu ana tafka azababben yaki mai tsoratarwa. Burin Boka Hurgas ya mallaki Birnin Kisra da Nahiyar tasu. Sorry fah na barku kuna ta jira,ba nan ne shi yasa. Daga: GUDUN TSIRA Littafi na Hudu(4) Part A Lokacin da aka rungumtsume da masiffafen yaki tsakanin shugaba Sultan dasu Sarki Darwas sai ragowar dakarun nasu sarki Darwaz suka zama yan kallo,suka koma kwashe gawarwakin yan'uwansu suna koma gefe daya.Dama wadannan dakaru sun firgita ainun da al'amarin shugaba Sultan saboda a cikin abinda bai wuce dakika dari biyu ba ya kashe sama da dakaru dari takwas da karfin sihirin tsafi gami da karfin damtse da kwarewa a iya yaki.Koda aka fara wannan baki artabu sai Gimbiya Husaira da sarki Darwaz suka gane cewa lallai Sultan ba karamin jan gwarzo bane,tunda gashi sunyi masa rubdugu su biyun,amma tsawon dakika dari dayansu ya kasa koda lakutar jikinsa.Babban abinda ya bata musu rai mashi ne a hakan ma dada zullewa yake yana ci gaba da saran dakarunsu yana mai ci gaba da yin mummunar barna.Koda ganin haka sai Sarki Darwaz da Huraisa suka kara fusata ainun suka kara kuntata shi.Lokaci guda sai Sarki Darwaz da Huraisa suka dubi junansu a sannan suka yi wata alama,kawai sai suka doki kirjin Sultan da kafafunsu lokaci guda.Saboda karfin dukan sai da Sultan ya fado kasa tim yana aman jini,amma saboda tsananin naci da tsananin juriya bai yarda takubban hannunsa ba.Cikin zafin nama ya mike tsaye zumbur a daidai lokacin da Sarki Darwaz da Huraisa suka duro kasa gabansa aka ci gaba da gumurzu.Wohoho,wanda ya iya ya huta.Hakika su Sarki Darwaz sun sha matukar mamaki,domin basu taba zaton cewa Sultan yana da jarumtaka da karfin sihiri a haka ba.Ba wai tsagwaron karfin damtse ne da Sultan ba,amma ya sami tsananin horo na iya yaki gami da tsananin zafin nama,tabbas ya cika tshoho mai dakawa yara gumba.Saida aka shafe sa'a guda da rabi cif ana fafata kazamin yaki tsakanin Sultan dasu Sarki Darwaz amma ya zame musu alakakai,kuma saida ya samin nasarar fitar da jini a jikin kowannansu,duk da cewar suma sun yanke shi,domin a kalla sunyi masa manyan raunika guda tara.Sakamakon jinin dake zuba a jikinsa ne jiri ya fara dibarsa ya fara gigta.Damar dasu Sarki Darwaz suka samu kenan suka ci gaba da kai masa sara da suka gami da naushi da bugu da dukkan karfinsu.Nan da nan suka sami lagonsa ya zamana cewa tun yana tsaye saida ya durkushe kasa bisa gwiwoyinsa.Babban abinda ya fusata Sarki Darwaz shine Sultan yayi masa wani siririn yanka a kumatu,yayi masa billen dole,wanda har abada tabonsa bazai bata ba.Ita kuwa Huraisa a kan cinyarta ta hagu ya yanketa kuma wurin yayi dan zurfi dole ne tayi jinya ta kamar tsawon kwana uku,tsananin juriya ne da jarumtaka tasa taki sarewa.Sultan na tsugune a kasa sai Sarki Darwaz da Huraisa suka ci gaba da saran jikinsa suna sukar cikinsa da takobi yana ihu,jini na tsartuwa da fallatsi a jikinsa har saida sukayi fata- fata da sassan jikinsa.komai rashin imanin mutum idan yaga yadda aka daddatsa sultan sai tausayi ya kamashi,amma duk wannan abu da akayi masa bai mutu ba saboda taurin rai.Ana cikin haka ne Kan Sultan ya lankwabe kasa ya daina motsi,Sarki Darwaz da Gimbiya Huraisa suka dubi Junansu sukayi murmushin murna bisa ganin sun sami nasarar kashe shi.Kwatsam ba zato ba tsammani sai suka ga Sarki Sultan ya dago kansa sama ya dubi Sarki Darwaz yayi masa murmushin mugunta sannan yace,ko ba komai harka mutu billen danayi maka bazai face ba daga kan fuskarka dashi a za'a binne ka a cikin kabarin ka.Kafin Sultan ya gama rufe bakinsa tuni Sarki Darwaz yasa takobinsa ya fille masa kai.Take Kan yayi tsalle can gefe daya ya rinka mirginawa da gudu har saida bango ya tokare shi,sannan gangar jikin nasa ma ta bingire kasa.Cikin tsananin fushi Sarki Darwaz yaje inda kan Sultan yake ya sunkuya ya dauka sannan ya mikawa wani hadimi nasa yace,inason a tsire wannan kai a daidai kofar shiga fadata ya zamana cewa,kullum sai nayi arba dashi idan zan shiga,kuma ya zamo abu na farko wanda baki zasu fara tozali dashi a duk sa'adda suka zo.Hadimin ya risina yace an gama ya shugabana.Kawai sai hadimin ya jefa kan Sultan a cikin wata jakar fata ya kunshe.Adaidai wanann lokaci ne Gimbiya Huraisa ta fara dingisa kafarta ta hagu wacce ke zubar da jini,kawai kuma sai ta kasa daukar nauyin jikinta ta fadi kasa,cikin dimauta Sarki Darwaz ya ruga izuwa kanta ya dauke ta ya ruga izuwa cikin gidan Sarautar Sultan yana mai bada umarnin a je a nemo babban likitan shugaba Sultan.Bayan likitan ya gama sawa Gimbiya Huraisa magani kuma an dinke raunin saboda yayi zurfi;sa'a mata yi kaifin takobin Sultan bai taba kashin cinyarta ba.Nan take Huraisa ta kama barci akan gadon shugaba Sultan dake tsakiyar turakarsa,sakam akon maganin barcin da likitan ya bata ta sha.A wannan lokaci ne likitan ya mike tsaye daga kan gefen gadon ya dubi sarki Darwaz cikin alamun damuwa yace,Akwai bukatar gimbiya tayi kwana biyu a kwance tana jinyar wannan rauni nata kafin ta fara takawa saboda kyakkyawan motsi ma zai iya sawa dinkin ya farke.Koda jin wannan batu sai ran sarki Darwaz ya baci ainun,zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda kin haushin cewar babu dama a cigaba da wannnan tafiya a yau bare a hanzarta cimma su Shugaba Sharwan.A daidai wannan lokaci ne billen Sarki Darwaz ya dameshi da zogi har ma yana digar da jini.Koda likta ya lura da hakan sai ya shiga tsaida jinin sannan ya dubi Sarki Darwaz a tsorace yace ya shugabana akwai bukatar ayi masa dinki a kan wannan rauni naka.Cikin matukar takaici Sarki Darwaz ya ce idan ka dinke raunin zai fatar da tabonsa har abada?Jikin likitan na rawa yace,ai har abada tabon wannan yanka bazai taba bacewa ba daga kan fuskarka.Kafin likitan ya gama rufe bakinsa tuni sarki Darwaz ya 11 hours ago Abubakar Haleefah Physicist zaro wata sharbebiyar wuka a kugunsa ya kirbawa likitan a cikinsa,kuma ya damki makoshinsa ya daga sama da hannu daya a lokacin da yake kakarin mutuwa yace,kai ne mutum na karshe wanda zai sake ganin wannan bille.Yana gama fadin hakan yayi wurgi da gawar likitan sannan ya bude kofar dakin ya kirawo dakaru suka dauke gawar likitan suka fice da ita kuma aka goge jinin daya fara zuba a kasa.Tun a wannan Sarki ya ruge fuskarsa da rawani,idanunsa kadai ake gani.Nan take yasa aka kawo kuyangi guda hudu wadanda zasu lura da Gimbiya Huraisa,sannan ya fice daga cikin daki.Yana fita ya jagoranci wadansu dakarun nasa sukayi ta yawo a cikin gidan suna bincika cikin dakuna,lunguna da sako-sako ko zasu ga matar Sultan,amma shiru ko alamarta babu.Saida suka bincike ko'ina sannan sarki Darwaz ya hakura ya koma can falon Sultan ya zauna don hutawa.Bayan an kawo masa abinci da abin sha yaci yayi hani'an sai ya kori kowa daga cikin falon hatta kuyangin dake cikin dakin suna jinyar gimbiya Huraisa kuwa saida suka fice,sannan ya kullo kofa da kansa yaje gaban wani katon madubi ya tsaya.A sannan ne ya kwaye rawanin dake fuskarsa yaga billen da Sultan yayi masa.Bille ne mai tsawo da fadi,wanda yasa masa muni,nan take zuciyar Sarki Darwaz ta kama tafarfasa kamar zata kone a karo na biyu har saida kwallar takaici ta cika amsa idanu.Ba komai ne yasa shi zubar da wannan kwalla ba face sani cewa shugaba Sultan ya karya masa tarihin jarumtakarsa,domin tunda yake yaki da gumurzu a rayuwarsa ba'a taba fitar da digin jini ba a jikinsa,amma yau gashi ma anyi masa raunin da indai zai bar fuskarsa a bude kowa sai ya gani.Sarki Darwaz ya tuna cewa duk wannan abu daya faru Siyama ce silarsa tunda inda bata kashe dan'uwansa ba da ba zai fito farautarta ba har yayi yaki da Sultan yayi masa wannan bille.Nan take Sarki Darwaz yaji ya kara tsanar Siyama fiye da koyaushe kuma ya tabbatar da cewar ransa bazai taba yin fari ba face a ranar dayaga ya sare kan Siyama kamar yadda ya sare na abokin mahaifinta wato Sulta.Nan take Sarki Darwaz ya kudurce a ransa cewar bazai sawa wannan rauni masa magani ba,kum bazai yarda a dinke shi ba saidai yayi ta ciwon da zaiyi har ya daina son kansa yayi warkewar dole,sannan kuma ya kudirci niyar cewa babu wanda zai sake ganin fuskarsa saidai idan ya zama gawa hatta matarsa da 'yarsa kuwa.Koda ya gama aiyana hakan,sai Sarki Darwaz ya sake rufe fuskar tasa da rawani sannan yaje kan wata doguwar kujera ya kishingida yana kwanciya barci ya saceshi saboda tsananin gajiya gami da tsamin jiki bisa gumurzun da yayi da shugaba Sultan. ¤¤¤ ¤¤¤ ¤¤¤ Al'amarin su shugaba Sharwan kuwa suna cikin tafiya a daji a cikin ayarin nasu gaba daya sai kawai suka ga Shamirat matar Shugaba Sultan taja linzamin dokinta ta tsaya cak a lokacin da jikinta gaba daya ya kama tsuma kuma kirjinta ya kama daka kamar zuciyarta zata faso kirjin ta fado.Koda ganin haka Sai hankalin Shugaba Sharwan,Ilela dana Siyama ya dugunzuma suka rugo gareta aka sauko da ita daga kan dokinta akayi mata shimfida a kasa saboda tsammanin ko kamuwa tayi da wata rashin lafiya.Nan fa suka shiga tambayarta inda uakeyi mata ciwo a jikinta.Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa Shamirat ta dubi Sharwan tace,sun kashe mijina,naji a jikina baya numfashi a doron kasa.Koda jin wannan batu sai Sharwan ya takarkare ya kurma uban ihu wanda ya tsorata kowa a wajen sannan ya fashe da matsanancin kuka kamar bazai daina ba.Al'amarin daya karya zuciyar Ilele da Siyama Kenan suma suka rungume Shamirat suka taya ta kukan.Saida shugaba Sharwan ya jima a tsugunne bisa gwiwoyinsa yana kuka sannan ya dago kai ya dubi Shamirat,bisa mamaki sai taga yayi mata murmushi yace,mijinki bai mutu rago ba.Na tabbatar da cewar kafin su Sarki Darwaz su kashe shi saida yayi musu mummanar barna saboda nasan irin jarumtakar abokina gami da taurin ransa.Bana raba daya biyu,sai ya bar shaida a jikin Sarki Darwaz.Ina son ku sani cewa zamanmu a waje daya yana da matukar hadari,don haka zaifi kyau mu tashi muci gaba da tafiya.Ba tare da gardamar komai ba kuwa aka kimtsa aka cigaba da tafiya ana keta dazuzzuka masu sarkakiya,kwazazzabai,koramai da fadamomi iri iri suna masu tunkarar hanyar da zata kaisu Birinin Darul Hunam.Saida suka shafe kwanaki arba'in suna tafiya sannan suka iso wani daji mai tsananin fadi mai cike da sahara.Iya hangen mutum a cikin dajin babu bishiyu ko daya,babu duwatsu ko alamar wani danshi na ruwa sai rairayi tsabarsa tsubi-tsubi,wani rairayin ma tudunsa yakai na tsauni.Da isowars wannan wuri sai Shugaba Sharwan ya bada umarni aka tsaya aka yada zango.Bayan an kafa tantuna anci abinci kuma an huta,sai Siyama ta dubi Sharwan tace,yakai Abbana menene dalilin da yasa ka bada izinin mu yada zango a nan wajen?Lokacin da Sharwan yaji wannan tambaya sai yayi ajiyar zuciya sannan ya dubeta cikin alamun takaici yace,yake 'yata idan baki manta ba abokina Sultan ya gaya mama cewa tsakanin birninsa da birnin na gaba wanda ake kira Darul Hunam tafiya ce ta kwana arba'in da daya,yau kuma kwananmu arba'in cif muna tafiya.Kinga kenan saura tafiyar kwana daya jal mu riski birnin Darul Hunam.Dole ne mu tsaya daga nan mu tura dakarun leken asiri domin su gano mana halin da garin ke ciki.Idan an dana mana wani tako ne mu san yadda zamu tsallakeshi.Idan kuma garin bazai shigu ba mu nemi hanyar dazamu kewaye shi.Sa'adda shugaba Sharwan yazo nan a zancensa sai gaba dayan jama'ar banu Hanzar suka aminta da shawarar tasa.Nan yake aka tashi wadansu kwararrun dakarun sumame guda uku wadanda akeji dasu aka turasu izuwa cikin birnin Darul Hunam. Dafatan zakuy commenting da liking sosai dan karin karfin gwiwa Daga: GUDUN TSIRA Littafi na hudu(4) Part B Nan take aka tashi wadansu kwararrun dakarun sumame wanda ake ji dasu aka tura su izuwa cikin birnin Darul Hunam. ¤¤¤ ¤¤¤ ¤¤¤ A can birnin marigayi Shugaba Sultan kuwa tunda Sarki Darwaz da gimbiya Huraisa suka kama barci basu farka ba har saida gari ya waye rana ta take.Huraisa ce ta fara farkawa tana bude idanunta sai ta yunkura da nufin ta mike tsaye,amma sai wata kuyangarta mai suna Badura tayi sauri ta dannan kafadunta kasa ta dubeta tace,yi hakuri ya shugabata,kiyi sani cewa likita yace kada mu bari kiyi kyakkyawan motsi,domin yin hakan zai iya janyi farkewar dinkin da aka yiwa rauninki.Koda jin wannan batu sai bakin ciki ya turnuke Gimbiya Huraisa ta koma ta kwanta,sannan ta dubi Badura cikin tsananin takaici tace yanzu ina mahaifina yake? Badura tace yana falo yana ta fama shara bacci tun jiya bai farka ba.Huraisa tace maza ki koma wajensa yanzku ki gani,idan har ya tashi daga wannan barcin kice dashi inason na gana dashi yanzu yanzu cikin gaggawa.Badura ta risina tace an gama ya shugabata.Nan take Badura ta mike tsaye ta fice daga cikin dakin ta nufi babban falon na marigayi Sultan.Fitarta ke da wuya sai idanun Huraisa suka kai kan wata babbar akwatin karfe dake jikin bangon arewa na dakin,wacce aka kulleta da wani katon kwadon madubi.Huraisa ta dubi wata kuyanga dabam tace,maza kije ki nemo mini makeri ina son na cire wannan makulli domin naga abinda ke cikin wannan akwati,domin koma meye a ciki yana da matukar muhimmanci ga shugaba Sultan,amma kuma menene dalilin da yasa ya barshi anan bai kaiwa matarsa Shamirat ta tafi dashi ba? Kuyanga ta risina tace an gama ya shugabata.Itama sai ta mike tsaye ta fice daga cikin dakin.Jim kadan da fitar wannan kuyanga saiga Sarki Darwaz yashigo cikin dakin kuyanga Badura na biye dashi kuma fuskarsa na rufe cikin rawani idanunsa kadai ake gani.Koda Huraisa taga Sarki Darwaz a cikin wannan yanayi sai ta yunkura ta mike zaune,sannan ta dubi gaba dayan kuyangin dake dakin tace,ku bamu wuri.Take kuwa kuyangin suka fice suka janyo kofa suka rufe.Sarki Darwaz ya zauna a kan gefen gadon data ke kwance,ya dubeta yace,ki gafarceni yake 'yata,daya yau kema bazaki saki ganin fuskata ba,domin bana son kowa yaga wannan shaida da Sultan yayi min.Koda jin wannan batu sai Hankalin Gimbiya Huraisa ya dugunzuma ainun ta dubeshi cikin alamun tsananin damuwa da takaici a lokacin da idanunta suka ciko da kwalla,tace haba yakai Abbana ai idan har zaka boyewa kowa fuskarka bai kamata ace ni da mahaifiyata ka biye mana ba,saboda zamu iya zama da kai a cikin kowacce siffa ko da kuwa fuskarka tafi komai muni a cikin wannan duniya,tunda ba fuskar taka muke so ba,ruhinka muke bukata ya kasance tare damu dimun da'iman.Lokacin da Gimbiya Huraisa tazo nan a zancenta sai Sarki Darwaz yayi murmushin farin ciki,yace,yake 'yata na sani cewa kuna kaunata kamar yadda kuke son kanku.Ina so ki sani cewa abin kunya ne kuma abin kaskanci a cikin tarihin jarumtakata duniya ta san cewa gwamnan da yake karkashina shine yayi mini rauni a fuskata.Idan kika ga wannan fuskatawa a fili to gawata ce a kwance.Mene ne dalilin da yasa kika aika kina son yin magana da ni yanzu?Koda jin wannan tambaya sai Huraisa tayi ajiyar numfashi sannan tace, ba wani abu bane yasa na aika kazo ba,sai domin na nemi gafararka bisa sakacin danayi har Sultan ya sami nasarar yi min rauni a kafata gashi hakan ya haddasa matsala a cikin tafiyarmu.Kamata yayi ace munci gaba da tafiya yanzu don karfa abokan gaba su kara bamu tazara sosai.Na kirawo kane yanzu domin na baka shawara,shawarar kuwa itace ku kara gaba kada ku tsaya jirana har izuwa gobe don ci gaba da wannan tafiya.Ka tuna cewa idan har wadannan abokan gaba namu suka sami nasarar fita daga cikin nahiyarmu shikkenan sun tsira.Lallai ya kamata mu kure musu wannan GUDUN TSIRA da sukeyi mu kawo karshensu.Yayin da Gimbiya Huraisa tazo nan a zancenta sai hankalin Sarki Darwaz ya rabu gida biyu,ya rasa hukuncin daya kamata ya yanke..Kwatsam sai suka ji ana kwankwasa kofar dakin.Cikin fushi sarki Darwaz ya daka tsawa yace wane ne nan yake kwankwasa mini kofa?Kawai sai sukaji muryar Boka Hurgas yana mai cewa nine ya shugabana.Cikin hanzari Sarki Darwaz ya mike yaje ya bude masa kofar ya shigo.Hurgas ya risuna sannan ya dubi sarki cikin biyayya yace ya shugabana zamanmu a wannan gari har izuwa gobe zai iya janyo mana dalilin dazamu kasa cimma abokan gaba da tazarar kwana daya rak.Abinda za'ayi shine,a dauki Gimbiya a sanyata cikin keken doki a cigaba a tafiyar a haka.Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube gimbiya Huraisa,ba tare da sarki Darwaz yayi wata gardama ba sai ya bada umarni nan take aka fara shirye shiryen tafiya.Kafin abar garin saida Sarki Darwaz ya dora wani babban hadiminsa mai suna Zukairu akan kujerar marigayi Sultan,sannan akayi hawa aka fice daga cikin birnin gaba daya aka durfafi hanyar da zata kaisu birnin darul Hunam. ¤¤¤ ¤¤¤ ¤¤¤ Lokacin da dakarun leken asiri na kabilar Banu Hanzar suka tafi izuwa cikin birnin Darul Hunam domin su gano halib da birnin ke ciki da kuma sirrin komai na birnin,Saida suka kwana suka yini basu dawo ba.Al'amarin daya dugunzuma hankalin su shugaba Sharwan kenan suka fara tunanin ko an kama sune,don haka suma a koyaushe za'a iya kawo musu harin sumame.Nan da nan shugaba Sharwan ya hada taron gaggawa domin suyi shawara bisa abinda ya kamata ayi.Nan fa shawara ta yawaita wasu suce kawai ayi shirin yaki a bi sawun dakarun da aka aika guda uku.Wasu kuma suce a sami wuri a buya a dan kara saurarawa a gani.Saida kowa ya fadi albarkacin bakinsa san nan Siyama ta daga hannu akayi tsit.Siyama ta dubi shugaba Sharwan tace,yakai Abbana inason ka tuna cewa dakarun sumamen da muka tura suyi mana leken asiri a cikin wannan birni na darul Hunam sune suka fi kowa kwarewa a aikin leken asiri a can birnin Kisra gaba daya,kuma sama da shekaru goma suke rike da wannan kambu ba'a taba turasu aikin dasu ka kasa ba.Haka kuma sun kasance dakaru masu tsananin karfin damtse da tsananin karfin gudu da iya jure wahala ta tsawon kwana uku.Bisa wannan dalili nake ganin cewa duk rintsi ko da mutum daya ne daga cikinsu sai ya sami nasarar dawowa nan garemu a raye ya bamu labarin abinda ke faruwa,saboda haka zaifi kyau mu dan kara musu lokaci daga nan zuwa tsakar date ko zuwa gobe da safe,saboda babu mamaki ma yanzu haka suna kan hanyarsu ta dawowa.Lokacin da Siyama tazo nan a zancenta sai jikin kowa yayi sanyi,aka sake yin shiru tsit aka rasa wanda zai soko shawarar data kawo.Kawai Sai shugaba Sharwan yayi murmushi ya dubi Siyama yace,yake 'yata hakika kina da kaifin tunani gami da hangen nesa,don haka na amince da wannan shawara taki.Lallai zamu ci gaba da sauraron dawowar dakarunmu na leken asiri,daga na har zuwa wayewar gari.Amma duk da haka yanzu zamu tura dakarun tsaro mutum bibbiyu izuwa kowane bangare na wannan daji.Wato gabas da yamma,kudu da arewam,nisan tafiyar zngo guda domin su labe su zuba ido.Da zarar sunji wani motsi wanda basu aminta dashi ba,ko sunga wata zuga ta dakaru su rugo su sanar damu.Koda jin wannan batu sai gaba dayan yan majalisar suka mince.Ai kuwa saida dare ya raba sannan akaji dawowar dakarun sumamen da aka aika birnin Darul Hunam,sun taho a guje suna yin alamarsu ta kukan wani tsuntsu.Dama babu wanda yayi bari a cikin ayarin,sai kuwa kowa ya mimmike aka tarye su.Dakarun sumamen suka iso su uku suna ta faman haki kamar ransu zai fita.Suka zube kasa wanwar suna numfashi da karfi kamar ransu zai fita.Saida suka bari suka huce sosai,suka dawo cikin hayyacinsu sannan aka basu ruwa suka sha.Bayan sun nutsu ne Siyama ta dubi babbansu mai suna Hatmara tace ba mu labari yakai tauraruwa mai wutsiya,mu kuka gano a cikin birnin Darul Human? Sa'adda Hatmara yaji wannan tambaya sai yayi ajiyar zuciya sannan yace ya shugabata kiyi sani cewa an sanya tsattsauran tsaro a cikin birnin darul Hunam da kewayensa.Babu ta inda mutum zai ratsa ba tare da ya fada hannun dakaru ba walau ta gabas,yamma,kudu da arewa,amma duk da haka saida mukayi amfani da kwarewarmu muka shiga har cikin tsakiyar birnin ta cikin bututun ruwan kwata dake karkashin kasa,amma da zamu dawo sai wannan hanya ta gagare mubi dole saida muka rafke dakarunsu guda uku a cikin daren yau mukayi shigarsu mukayi kasadar biyo hanyar cikin gari,a kyar da sidin goshi muka iso bakin kofar birnin.Anan ne fa muka gane kuskurenmu saboda saida asirinmu ya tonu aka kama mu aka kai mu wajen shugaban masu gadin kofar.A nan ne akayi kuskure aka shigar da mu cikin wani daki domin gana mana azabar da zatasa mu fadi ko mu su waye.Cikin sa'a muka bubbuge dakarun da suka kamamu a cikin dakin,muka sumar dasu suma mukayi shigarsu muka dawo baki kofa.Inda anan ma mukayi wani yakin na sumame muka bazar da gaba dayan masu gadin kofar kimanin mutum saba'in sannan muka bude kofar garin muka fito muna masu falfala azababben gudu,har sai da muka iso nan yanzu.Ya shugabata a cikin binciken da mukayi a cikin birnin darul Hunam mun gano cewa aljanu sun kai labarin guduwar jama'armu daga can birnin kisra,kuma gwamnan garin ya kafa doka cewa duk dan garin daya boye irin jama'armu a cikin gidansa hukucin kisa ne a kansa.Yanzu shawara ta rage garemu mu san matakin dazamu dauka amma komai zai iya faruwa domin gwamnan birnin darul Hunam zai iya turo dakarunsa su biyo sawunmu su iso har nan su riske mu gaba daya,kuma zau iya tsayawa a bakin birninsa yayi mana mugun tanadi na yakarmu.Babban abinda ya tayar mana da hankali shin yawan dakarun birnin sun ninka namu sau uku,inda mukace zamuyi fito na fito dasu zasu iya karar damu gaba dayanmu.Lokacin da badakare Hatmara yazo nan a jawabinsa sai hankalin kowa ua dugunzuma ainun har da shugaba Sharwan aka rasa wanda zaice kala har izuwa tsawon yan dakiku masu yawa.Kwatsama sai Siyama ta dubi Sharwan tace,zama bai kama mu ba yanzu,dole ne mu tashi yanzu muyi shirin yaki muje mu tari dakarun birnin darul Hunam a kan hanya tun kafin su iso nan.Amma yakin sunkuru zamuyi musu,kuma dole ne mu gaggauta gamawa dasu,sannan muyi shigar su su shiga izuwa cikin birnin muyiwa gwaman garin juyin mulki,domin mu sami damar shiga garin har mu kwana,inyaso da safe mu kara guzuri mu ci gaba da tafiyarmu tunda bamu da wata hanya dazamu bi face ta cikin birnin.Lallai bamu da wani zabi wanda yai muyi kamar yadda na shirya yanzu ni ba haka ba kuwa karshen mu ya yazo.Sa'adda Siyama tazo nan a jawabinta sai wani babban dan majalisa mai suna Dairuf ya dubeta yace,ai juyin mulkin da zamuyi bashi da wani amfani tunda dai bazamu iya sani daga cikin jama'armu ya hau karaga ba,kuma babu wani dan gari dazai yarda ya karbi karagar saboda tsoron Sarki Darwaz.Siyama tace ai bukatarmu bata son karaga bane sai dan kawai mu sami damar kwana a garin da samun garin guzuri da ikon wuce gaba.Shugaba Sharwan yayi ajiyar numfashi sannan ya dubi Siyama yace na yarda dake a kan cewa bamu da wani zabi wanda yafi muje mu yaki wadannan mutane,amma fa hadarin dake cikin yin hakan yana da yawan gaske,kuma ban ga hanyoyin daza'abi a sami nasara.Siyama tace nayi nazarin duk irin hadarin da kake tunani,kuma nayi tunani akan irin dabarun da ya kamata muyi don ganin mun sami nasara.Abinda nake bukata kawai shine ka bani dakaru guda dari biyi kacal daga cikin dakarunka na musamamn masu tsaron lafiyarka,zan jagorance sumu kai ga nasara.Sa'adda Siyama tazo nan a zancenta sai Shugaba Sharwan Sharwan yayi shiru yana mai sunkui da kansa kasa ya fada cikin kogon tunani ba tare daya nemi shawarar yan majalisarsa ba.Daga can sai ya dago kai ya dubeta yace,yake 'yata kiyi sani cewa dalili daya ne zaisa na yarda dake na baki dakaruna na musamman don zuwa aiwatar da wannan aiki mai mugun hadari.Dalili kuwa shine tun kuruciyarki kawo iyanzu ban taba ganin wani abu ya gagareki ba muddin kinyi niyyar aiwatar dashi,haka kuma ban taba ganin kin shiga hadarin da kika kasa fita ba.Zanyi kundubala a yanzu na baki dama,amma ina gargadinki daki sani cewa idan har kika kasa samun nasara kika janyo dalilin da kabilarmu ta tarwatse ko kuma mukayi asarar dumbin rayuka da dukiya mai yawa bazan taba yafe miki ba.Idan kin yarda da wannan sharadi na baki izini ki debi dakarun anwa yanzu ki tafi.Koda jin wannan batu na shugaba Sharwan Sai hankalin Siyama ya dugunzuma ainun saboda tasan abinda yake nufi bazai taba yafe mata ba,yana nufin cewa zai datse duk wata alaka dake tsakaninsa da ita tamkar ma bai taba sanin taba,amma saboda ki fadi da tashin karayar zuci irin ta Siyama sai taki nuna tashin hankalinta a fili kawai ta dubi shugaba Sharwan cikin murmushi tace na yarda da wannan sharadi naka ya shugabana.Tana gama fadin hakan sai ta waro wadannan dakaru na musamman guda dari biyu tayi musu umarnin suje su shirya cikin gaggawa.Nan take kuwa suka sanya bakaken tufafi suka rufe ko'ina na jikinsu idanunsu,bakinsu da hancinsu kadai ake gani.Wani irin talakarma suka sa a kafafunsu masu taushin gaske,gami da duhu yadda komai suka daka baza aji sautin sahunsu ba sannan a jikin kowanne daya daga cikinsu akwai wadansu kananan wukake masu azabar kaifi da tsini sirara guda dari.Haka kuma suna dauke da kwari boye a bayansu mai cin kibiya dubu da kuma karamar baka rataye a bayansu da kuma sharbebiyar takobi.Sudai wadannan dakaru an basu horo na musamman wanda yasa suka kware ainin a wajen iya kisan mummuke.Bayan wadannan dakaru sun gama shirinsu sun jera akan layi sahu biyu,sai ga Siyama ta fito daga cikin tantinta itama tayi shiga iri daya da tasu.Al'amarin daya baiwa kowa mamaki kenan a sansanin domin ba a taba ganinta ba a cikin irin wannan shiga,kuma babu wanda ya san cewa ita ma tana da horo irin na wadannan dakaru.Nan take Siyama ta karaso gaban Shugaba Sharwan ta bukaci yasa nata albarka,kuma ya nema mata sa'a a wajen iyaye da kakanni saboda su dai wannan kabila ta Sharwan basu da wani addini guda da sukyi imani dashi face iyayensu da kakaninsu amma dai suna aiki da tsafi ko sihiri.Nan take Shugaba Sharwan ya dafa bayan Siyama kuma ya sumbaci goshinta yasa mata albarka,kuma yayi mata addua.Nan take Siyama taji wani irin gagarumin karfin gwiwa ya shige ta.Kuma taji dukkan tsoro ya kau daga cikin zuciyarta.Ba tare da bata wani lokaci ba sai Siyama taja wadannan dakaru suka falfalwa da gudu izuwa cikin daji suna yin wani irin gudu na ban al'ajbi tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya,kafin kace wani abu tuni sun kule uma sun bace a cikin duhun daren.Saida su Siyama sukayi 'yar doguwar tafiya ta yan dakiku masu yawa tana kan gaba sannan ta tsaya cak suma dakarun guda dari biyu sai sukayi cirko cirko a bayanta.Siyama ta tsuguna kasa ta kara kunnenta a kasa tayi sauraro dan kadan sannan ta mike tsaye zumbur ta yafito dakarun su duka sukayi mata kawanya,tayi musu radar wata magana.Nan take dakarun sukayi wani sihiri su duka a lokaci guda.Kawai sai kasa ta tsage suka shige cikinta kuma kasar wajen ta koma ta hade kamar wani abu bai taba faruwa ba a wajen.Itama Siyama ta shige cikin kasar ta kule.Faruwar hakan keda wuya da kimanin tsawon rabin sa'a saiga dakarun birnin Darul Hunam su da yawa bisa dawakai dauke da muggan makamai sun iso daidai wannan wuri.Da isowarsu sai shugaban nasu ya daga hannu ya tsaya.Take sauran yaran nasa ma suka ja linzamin dawakansu,dawakan sukayi turjiya da haniniya.Shugaban dakarun ya shaki kamshi har sau uku yace,tabbas zuga ta bil'adama ta tsaya a nan.Kafin ya gama rufe bakinsa sai sukaji kasar wajen ta kama tsagewa,dawakansu na ruftawa ciki.Kafin dayansu yayi wani yunkuri duk an wurgo musu wukake masu tsani sun caccake su a wuya da makogwaro.Nan fa suka rinka sulalewa kasa daga kan dawakansu suna bajewa kasa matattu,kafin kiftawar ido su duka sun zama gawa,sauran shugabansu shi kadai a tsaye jikinsa na karkarwa yana waige waige da dube dube,amma baiga wanda yayi musu wannan barna ba.Bazato ba tsammani kuma sai yaga kasar ta kara tsagewa,sai ga dakaru na fitowa sama daga cikin karkashin kasa su dari biyu suna yi masa kawanya.Saida suka gama fitowa gaba dayansu sannan na cikon dari biyu da daya ya fito,kuma ba wani bane face Siyama.Kafafunta na dira kan kasa saita durfafi shugaban wadannan dakaru kai tsaye tana rike da sharbebiyar takobi,a lokacin dashi kuma ya nutsu ya daina tsoron komai ya kura mata idanu kawai yana mai sadudar jin kaifi ya ratsa shi.Bisa mamaki sai yaji Siyama ta dora fadin takobin akan kafadarsa sannan ta dubeshi cikin murmushin mugunta tace shin kana da iyali? Mutumin yace kwarai kuwa inda da mace daya da 'ya daya.Siyama tayi murmushin murna tace nasan zaka so ka koma garesu a raye,don bazasu so su rasaka ba,kaima bazaka so ka rasa su ba.Idan kabi umarnina da dokokina zaka koma garesu a raye kuma cikin koshin lafiya,amma fa idan ka sabawa umarnina da dokokina ko gawarka ma iyalin naka bazasu shaidata ba.A yanzu inason ka yi mama jagowa mu koma har izuwa cikin birninku kuma har cikin gidan sarautarku gaban sarkinku a matsayin mune jama'arka ba a kashe maka ko yaro daya ba,ka bar sauran yaranka ne a baya.Kada ka kuskura kayi rawar baki ko ka munafuncemu yadda asirinmu zai tonu.Idan kayi haka tabbas a bakacin ranka.Koda gama fadin hakan sai Siyama ta dubi dakarun nata tayi musu alama,nan take suka tube kayan matattun dakarun suka sanya,kuma suka dau makamansu suke haye kan dawakansu.Ita kuma Siyama sai tayi irin shiga irin wannan,sannan tasa wannan shugaban dakarun ya hau nasa dokin itama ta hau dokin suka jera da ita dashi.Sauran dakarun nata na biye dasu a baya.Babu abinda zai baka mamaki a cikin wannan hikima da Siyama tayi face yadda ta shirya dakarun nata girman jikinsu yazo iri daya dana dakarun da suka kashe masu bin wannan shugaba a baya.Ita kanta sai gashi jikinta yazo iri daya dana mataimakinsa kai kace wancan din ne wanda aka kashe.Karkakara Kaka.Laifin dadi karewa.Muje ga littafi na biyar don jin ci gaban wannan kasaitaccen labari.In kuna so to ku karamin karfin gwiwa. Daga: GUDUN TSIRA Littafi na Biyar (5) Part A HAKA DAI SU SIYAMA suka ci gaba da tafiya a cikin shigar dakarun birnin darul Hunam,har suka iso birnin.Da isowarsu bakin kofa sai daya daga cikin masu gadin kofar ya dauki fitila ya bude wata yar karamar taga a jikin kofar wacce ta kasance ta karfe ya haska.Koda yayi arba da fuskar sadauki Samhur wanda shine ya jagoran dakarun da suka fita dazu sai yayi murmushi ya bude kofar.Nan take su Siyama suka kunna kai izuwa cikin birnin.Kwatsam sai sukaga wasu dakaru masu yawa sun taso musu sunyi musu kawanya suna masu ritsa su da makami.Daya daga cikin dakarun ya dubi sadauki Samhur yace,yaya dazu ka fita tare da dakaru kimanin dubu uku,amma yanzu ka dawo da yan tsiraru,kayi bayani mu ji idan bamu gamsu ba yanzun nan zamu kaddamar daku.Koda jin wannan batu sai sadauki Samhur ya dakawa mai maganar tsawa yace kai Zambaru shin ka sami tabin kwakwalwa ne?Ya za ayi na dawo tare da dakaruna gaba daya alhakin harin sumame muka kai don gamawa da yan kabilar Banu Hanzar?Ai mun isa har can sansaninsu mun tarwatsa su sun gudu,kuma sun bazama izuwa cikin daji.A dalilin hakane na bar dakaruna a can suka lallabe domin idan suka dawo su gama dasu.Yanzu na dawo ne da tsirarun yarana domin na sanar da gwamna halin da ake ciki,saboda asan matakin da ya kamata a dauka a gaba.Lokacin da Zambaru yaji wannan batu sai jikinsa yayi sanyi bisa dole ya gusa daga kan hanya,suma yaran nasa suka kauce suka baiwa su Siyama hanya suka wuce gaba.Har su Siyama suka bace musu da gani suna nan a tsaitsaye suna wasuwasin bayanin da Samhur yayi musu.Haka dai suka ci gaba da tafiya a cikin birnin na Darul Hunam suna wuce unguwoyi da gidaje har suka iso gidan gwamna.A bakin kofar shiga gidan gwamnan ne aka sami matsala aka ki bude musu kofa.Aka ce sai an tantance su daya bayan daya.Koda Siyama taga cewa lallai asirinsu zai tonu sai tayiwa yaranta alama aka ruguntsume da yaki cikin kankanin lokaci suka kashe gaba dayan dakarun dake bakin kofar suka falfala cikin gidan da gudu.Siyama na tusa keyar Samhur yana nuna mata hanya har saida da yakaita har cikin turakar gwamna.Duk inda suka iske dakarun tsaro saidai kaga yaran Siyama sunyi musu kisan sunkuru sub zubar dasu kasa.Lokacin da suka iso bakin kofar falon gwamna sai Siyama tasa kafarta ta dama ta doki kofar.Saboda karfin dukan nata sai da kofar ta jijjigo daga cikin gini ta fadi kasa rikica Kawai sai Siyama ta hango gwamna zaune a kasa dirshen ya harde kafafu yana jan dogowar casbaha kuma yana fuskantar bakin kofar,sannan kuma yayi shiga gagaruma shigar yaki.Al'amarin dayai mutukar razana Siyama kenan,kuma yai matukar bata mamaki,kawai sai ta saki Sadauki Samhur ta dubeshi tace,maza ka fice daga cikin gidan nan ka tafi wurin iyalanka idan baka son su rasa ka.Batare da gardamar komai ba kuwa Samhur ya juya da baya da gudu ya bace daga wajenTun daga nesa Siyama ta karewa gwamna kallo tayi nazarinsa sosai sai taga ashe basamuden kato ne mai kira irin ta sarkinsu na kisra wanda ta kashe,amma shi nasa jikin ma har yafi na sarkin kauri,murdewa gami da tarin jijiyoyi.Nan take Siyama taji zuciyarta ya buga da karfi ta ayyana a ranta cewa lallai yau fa ta gamu da gamonta.Kuma ta taro fadan da bata da tabbacin samun nasararsa.Amma data tuno da kalamin mahaifinta Shugaba Sharwan cewar idan bata sami nasara ba a wannan yaki data kirkiro har abada bazai taba yafe mata ba,sai taji dukkan tsoro ya gushe daga zuciyarya,kawai sai ta zura hannu cikin wuyan rigarta ta tabo wannan sarka wacce marigayi Sultan ya bata tun tana yarinya Karama.Nan take sabon karfin gwiwa ya shigeta kawai sai ta bude hannunta mai rike da takobi ta durfafi inda gwamna yake zaune cikin sauri ba tare da shakkar komai ba.Yayi daya rage saura baifi taku biyar ba ta isa gareshi sai kawai taga ya daga hannunsa yana mai dakatar daita,kuma yayi shiru yana ci gaba da kan wannan casbaha ta tsafi dake hannunsa har saida yakai karshenta,sannan ya ajiye casbahar ya mike tsaue suka fuskanci juna,akayi kallon kallo na tsawon yan dakiku.Gwamna yayi wani irin murmushin mugunta sannan yace.Haba yarinya saurin ne kike haka na gaggawar karbar mutuwarki.Kiyi sani cewa Sunana Gumaizu Ibini Kamzaru,kuma ni jinin sarautar kisra ne,sarki da kika kashe 'da ne ga baffan mahaifina.Nasan duk abinda kika aikata a birnin kisra kawo izuwanki nan,don haka dama ina cikin shirin jiran isowarki domin na dauki fansar ran dan'uwana a kanki.Ina mai tabbatar miki da cewa wannan buri dake cikin ranku keda mahaifinki da kabilarku ta Banu Hanzar mafarki ne wanda ba zai taba tabbata gaskiya ba,domin har duniya ta nade zuri'armu ce zata ci gaba da mulkin birnin kisra badai wata zuria ba kuma har abada babu wani talaa dazai sami yancin kansa tunda babu mai iya hana mu yin mulkin zalunci,danniya da murdiya.Ina fatan dai kinyi bankwana da iyayenki kafin ki iso nan fadata don ki gutsuren sassan jikinki guda daya jal bazasu sake gani ba.Koda gwamna yazo daidai nan a jawabinsa sai jaruma Siyama ta tari numfashinsa tana mai daka masa tsawa tace,kai tsohon annamimi bakin azzalumi kayi sani cewa zuciyata ta kekashe ga barin tsoron duk wani azzalumi domin komai rintsi da tsanani sai na sami nasara a kanka.Koda jib haka sai gwamna ya fusata ainun ya zare wata sharbebiyar takobi daga kuibin cinyarsa ta hagu ya rugo da gudu izuwa kan Siyama yana mai kwarar uban ihu mai tsananin firgitarwa.Ai kuwa ita ma sai taruga izuwa kansa tana mai kurma ihu amma sai karfin ihun nasa ya danne nata,kamar yadda ruwan teku ke kwararowa cikin gari ya shafe komai.Suna haduwa suka ruguntsume da azababben yaki,ana fara yakin Siyama ta raina kanta domin kuwa karfin saransa ya ninka nata sau uku.Duk sa'adda ya kawo mata sara ta kare sai taji kamar katon dutse mai nauyin tsiya aka buga akan takobinta da kyar take iya tareshi,wani lokacin ma har durkushewa take kamar zata fadi kasa,amma saboda juriya da naci sai kaga ta mike cikin hanzari taci gaba da artabu.Lokacin da dakarun Siyama suka ga anayin wannan azababben yaki tsakanin Gwamna da Siyama sai suka firgita ainun bisa ganin irin jamrumtakar gwamna da tsagwaron karfin damtsemsa gami da kwarjininsa.Da farki sai suka fara wurga mugayen makamansu da nufin su hallakshi,amma duk makamin da aka jefa masa sai ya dawo da baya ya soke maishi ya fadi matacce.Kafin kace wani abu kimanin dakaru arba'in na Siyama sun zama gawa.Abinda yayi matukar razana dakarun kenan suka ja da baya.Suna buya suna kallon gumurzun a firgice.Lokacin da aka shafe kusan sa'a guda ana wannan artabu ya zamana cewa dayansu bai sami nasarar koda lakutar jikin daya ba.kuma karfin sihirinsu na tsafi yayi kunnen doki sai ran gwamna ya baci,zuciyarsa ta harzuko ya sauya salon fada ya hada da naushi gami da bugu da kafa da hannu.Naushin farko da yayiwa Siyama saida tayi katantanwa sau uki a tsaye,sannan ta sulale kasa magashiyan.Gwamna ya sunkuyo ya kamo gashin kanta a wulkance da nufin ya kara gabza mata naushi a fuska.Ba zato ba tsammani sai yaji tasa kafarta ta naushi tasa fuskar da dukkan katfinta.Saboda karfin dukan saida yayi tsalle sama da baya tamkar an janyeshi da majaujawa,bayan sa ya gwaru da bango ya fado kasa,jini na yoyo a hancinsa da bakinsa mma sai ya mike tsaye zumbur ya rugo da gudu izuwa kan Siyama ya sureta da hannayensa biyu yayi wurgi da ita sama,fuskarta da cikinta suka gwaru da rufin dakin taga wadansu irin taurarin wuya a idanunta kuma taji cikinta ya kulle kamar zata amayar da hanjin cikinta.Tana fadowa kasa sai Gwamna ya cafke ta ya juyata da nufin ya buga gadon bayanta akan gwiwar kafarsa don ya karairaya kasusuwan gadon bayan nata.Cikin wata irin gwaninta da tsananin zafin nama Siyama ta wulkila jikinta ta zulle daga cikin hannayensa kuma ta kamo kansa ka kafafunta biyu ta wurga shi sama.Ai kuwa sai gadon bayansa ya maku a jikin wani karge dake rataye a jikin bangin dakin.Take gwamna ya kurma uban ihu sakamakon tsananin zafi da zogin da yaji,a zatonsa ma daya daga cikin kasusuwan bayan nasa ya karye domin daya fado kasa tim kasa mikewa yayi ya rike kugunsa yana yoyon jini daga cikin hancinsa.Damar da Siyama ta samu kenan ta mike tsaye tana layi har a sannan itama bata daina zubar da jini ba daga cikin hancinta da bakinta.Kawai sai ta gyara tsayuwarta ta dunkule hannayenta biyu ta tsaya tana jiransa.Gwamna ya shafa gadon bayansa yaji babu inda ya karye,sai ya mike tsaye zumbur.Kawai sai ya kama rigar jikinsa wacce ta kasance mai kaurin gaske ce ta kirgi amma saiya tsargeta ta rabe gida biyu,yayi jifa da ita sannan ya ruga da gudu izuwa kan Siyama yana mai sake kwarara uban ihu a karo na biyu.Koda ganin haka sai ita ma ta rugo gareshi zuciyarta ta tasa cike da mugun nufi.Duk wanda yaga yadda wadannan jaruman suka rugo da gudu izuwa kan juna yasan cewa idan suka hadu dole ne abu daya ya faru cikin biyu,kodai suyi ragas ko kuma dayansu ua sami nasarar kashe daya.Ashe shi gwamna niyyarsa itace yakaiwa Siyama wawura ya matseta da hannauensa yadda zai karya kasusuwan bayanta.Ai kuwa cikin zafin nama ta shige ta karkashin kafafunsa bisa taimakon santsin dutsen Jauhar din da aka malale falon,kafin ya juyo ya fuskanceta sai ta kama kansa da hannayenta biyu ta murde masa wuya.Kawai sai gani akayi gwamna ya sulale kasa matacce,saboda tsananin mamaki da murna sauran dakarun Siyama basu san sa'adda suka kama tsalle da shewa ba,sunayi mata jinjina.Ita kanta Siyama tasan cewa tsananin sa'a ce tasa tayi nasara,duk da cewa kuwa tayi amfani da tsagwaron jarumtakarya da kwarewarta a horon iya fada.A daidai wannan lokaci ne dubunnan dakarun birnin suka shigo cikin gidan gwamna 'du...su da yawa rike da makaman yaki,amma duk wanda yazo yaga gawar gwamna sai jikinsa yayi sanyi ya yarda makaminsa.Dama gaba dayan mutanen birnin darul Hunam sun gaji da irin zaluncin shugaban nasu hatta kuwa dakarunsa ya matsa musu da zalunci don haka babu wanda yayi bakin ciki da mutuwarsa.Nan take jama'ar gari suka rude da shewar farinciki.Gaba daya dattawan garin da masu fada a ji kuwa sai suka taru a kofar gidan na gwamna.Siyama da dakarunta guda dari da sittin suka tsaya a gabansu.Nan take Siyama ta hau kan wani mumbari ta tsaya a tsakiyar miliyoyin jama'a tamkar an ajiye dan tsako a tsakiyar dubunnan kaji tace,yaku jama'ar birnin Darul Hunam kuyi sani cewa bamu shigo cikin birnin kuba da nufin mu cutar da dayanku ba sai domin mu sami damar da zamu ci gaba da yin GUDUN TSIRAn da mukayi saboda mu kubuta daga Sharrin sarkinku Darwaz bisa kasancewar bamu da wata hanya sai nan.Yanzu zan aika aje a taho da jama'armu su shigo cikin wannan gari domin mu kwana anan kuma mu sami karin guzuri inyaso gobe da safe mu ci gaba da tafiyar mu.Burinmu kawai shine mu fice daga cikin wannan nahiya gaba daya saboda ta haka ne kadai zamu iya tsira da rayuwar kabilarmu amma ina mai yi muku alkawarin cewar komai dadewa zamu dawo wannan kasa taku domin kwato muku yancinki a wajen azzaluman sarakunanku.Koda jin wannan batu sai gaba dayan jama'ar garin suka dada rudewa da shewa gami dayiwa Siyama tafi da jinjina.Nanfa aka shiga yiwa Siyama da jama'arta hidima ana basu masauki da abinci ana karramasu.Ba tare da bata wani lokaci ba Siyama ta aika da manzanninta mutum uku izuwa can daji inda suka baro Ayarin Kabilarsu.Koda suka isa suka sanar dasu Shugaba Sharwan cewar Siyama ta sami nasarar shiga har cikin birnin Darul Hunam harma ta kashe gwamnan su sai kowa ya kamu da tsananin farin ciki,saboda hakan ne ma shugaba Sharwan,Ilela da 'yar uwarta suka fashe da kukan murna.Kamar yadda Siyama ta shirya haka al'amarin ya kasance wato bayan jama'arsi sun iso cikin birnin darul Hunam sun kwana sai suka tashi da sassafe sukayi shiri aka basu guzuri mai yawan gaske,suka bar birnin jama'ar gari nata kukan rabuwa dasu domin sun san cewa da zarar sarki Darwaz da tawagarsa sun iso birnin mulkin zalunci ya dawo kenan.Haka dai mutanen birin darul Hunam suka yiwa su shugaba Sharwan rakiya har izuwa karshen gari sannan sukayi musu bankwana suka koma da baya izuwa cikin birnin darul Hunam suna kuka da bakin ciki.Bayan tafiyarsu Shugaba Sharwan da cikar kwanaki biyar daidai sai ga tawagar su Sarki Darwaz sun iso birnin darul Hunam.Boka Hurgas nayi musu jagora,koda suka iso birnin suka iske irin mummunar barnar dasu Siyama sukayi ta kashe gwamna tare da dakarunsa masu yawa,sai Sarki Darwaz ya dimauce ya zama kamar wani mahaukaci sabon kamuwa,domin zare takobi yayi yahau kowa yana maiyin kan uwa da wabi.Har saida 'yarsa Gimbiya Huraisa tasha gabansa ta rike hannunsa sannan ya dawo cikin hayyacinsa.Da yaje gaban kabarin gwamna kuwa saiya kwanta a gaban kabarin yana ta kuka da bakin ciki.Da kyar da sidin goshi Huraisa ta lallameshi ta janyeshi daga bakin kabarin takaishi gaban Boka Hurgas inda suka zauna suka shiga tattaunawa.A sannan ne sarki Darwaz ya dubi boka Hurgas yace,yakai abin dogaron birnin kisar yanzu yaza ayi mu riski wandannan abokan gaba namu kafin su sami damar fita daga cikin wannan nahiya tamu?Lokacin da Boka Hurgas yaji wannan tambaya sai yayi shiru yana mai sunkuo da kansa kas,kawai sai ya dauko wata farar sandar tsafi daga cikin aljihunsa ya saketa,maimakon sandar ta fadi kasa,sai ta kama yin zane a kasa da kanta,ta rubuta wadansu dalasiman kalmomi na tsafi wadanda babu mai iya karantasi face mashahurin boka kuma yaren da akayi amfani dashi aka rubuta kalmomin ya kasance bakon yare wanda babu wanda ya taba jinsa.Nan take Boka Hurgas ya karanta wadannan kalmomi a fili cikin wannan bakon yaren sannan yayi ajiyar zuciya ya dubi sarki Darwaz yace,ya shugabana bisa binciken da nayi yanzu idan muna son muke mu riski wadannan abokan gaba namu saidai mu dauko wadansu bakaken aljanu wadanda suka kasance hadiman sarkin aljanu na birnin HIMRAL.Idan kuwa kanason sarkin aljanun ya baka hayar wadannan aljanu nasa iya adadin yawan dakarunka da kuma mu uku don zuwa wannan gagarumin aiki,dole ne kayi masa alkawarin bashi jinin jama'arka mutum dubu uku bayan kowacce shekara uku har tsawon zamanka a kan karagar mulki.Idan ka saba wannan alkawari koda sau daya ne saika daura damarar yin yaki dashi Sarkin Aljanun.Lokacin da Sarki Darwaz da 'yarsa Gimbiya Huraisa sukaji wannan jawabi na boka Hurgas sai hankalonsu ya dugunzuma ainun suka rasa abinda ke musu dadi a duniya.Kawai Sai Gimbiya Huraisa ta kama hannun Sarki Darwaz tajashi izuwa can gaba nesa da inda Boka Hurgas ke zaune,domin suyi shawara ta dubeshi tace,yakai Abbana inaso kayi sani cewa da asara gwara gidadanci.Ni a ganina da dai mu rasa mulkinmu da rayuwarmu gwara mu rasa dubunnan rayukan talakawanmu,domin kuwa shi rai ba a bakin komai yake ba muddin akwai biyan bukata.Ya zama wajibi a garemu yanzu mu dauki wannan alkawari ga sarkin aljanu na birnin Hinral domin muga bayan makiyanmu,in yaso bayan mun cika burinmu sai mu nemi sihirin da zamu gama da sarkin aljanun,domin mu ci gaba da mulkinmu a cikin nustuwa da kwanciyar hankali.Ka sani cewa niyanzu bani da wani buri wanda yafi nayi gaba da gaba da jaruma Siyama domin na kasheta da hannuna saboda ni a ganina ma abin kunya ne a ce kai da kanka kayi yaki da ita,tunda duniya ma tasan cewa ruwa ba sa'an kwando ba ne,kuma ya ma za'a yi ace sarko mai babbar daraja kamarka ya yaki makaskanciya jaruma wacce ta fito daga cikin wulakantacciyar kabila ta talakwa.Lokacin da Gimbiya Huraisa yazo na a zancenta sai Sarki Darwaz ya bushe da dariyar farin ciki sannan ya rumgume ta a kirjinsa yace yake 'yata hakika ina alfahari dake,saboda kaifin hankalinki gami da basirarki da kuma hangen nesanki, lallai na karbi wannan shawara taki hannu biyiu.Koda gama fadin hakan sai Sarki Darwaz ya yafito Boka Hurgasa da hannu ya taho garesu,da isowarsa sai ya zube kasa a gaban sarki Darwaz cikin biyayya yace ya shugabana me kuka shawarta kai da Gimbiya bisa wannan al'amari?Sarki Darwaz ya numfasa yace,mun yanke hukuncin cewa zamu nemi taimakon sarkin aljanu na birnin Himral kuma na dauki wannan alkawari na bashi jinin jama'a ta mutum dubu uku a duk bayan shekara uku har izuwa karshen mulki na.Koda Boka Hurgas yaji wannan batu sai ya firgita ainun kuma ya kamu da tsananin mamaki bisa yadda sarki Darwaz ya aminta da daukar wannan alkawari mai tsananin wuya da hadarin gaske.Har Boka Hurgas ya bude baki zaice wani abu sai Sarki Darwaz ya daka masa tsawa yace,ka sani cewa bana magana biyu don haka na umarce ka daka hanzarta sanar da sarkin aljanu na birnin Himral amsar bukatarsa don cika tamu.Jikin boka Hurgas na karkarwa ya shafi kasa da hannunsa na hagu sannan ya ajiye wannan farar sandar tasa ta tsafi a kasa ya karanta wadansu dalasimai na tsafi ya tofa akan sandar.Faruwar hakan keda wuya saiga hoton fuskar sarki aljanu ta bayyana akan sandar tsafin.Saboda tsananin munin fuskar da kwarjininta saida Sarki Darwaz da Gimbiya Huraisa suka mike tsaye zumbur a firgice sukaji kamar su ruga da gudu amma saboda dakewar zuciya irin ta manyan sadaukai sai suka tsaya kyam suka kurawa fuskar sarkin aljanun idanu,amma duk da haka jikinsu na tsuma.Ba tare da bata wani lokaci ba Boka Hurgas ya zayyanewa sarki aljanu duk abinda sarki Darwaz ya shaida masa.Koda jin haka sai Sarki Aljanun ya bushe da wata mahaukaciyar dariya mai tsananin ban tsoro mai kama da saukar kwarankwatsa wacce ta kara firgita sarki darwaz da gimbiya huraisa sosai,shi kansa boka hurgas saida ya fadi kasa jikinsa na karkarwa bai ma san sa'adda ya saki fitsari ba a wando saboda tsananin firgita da razana.Lokacin guda sarkin aljanun ya tsuke bakinsa yayi shiru ga barin yin mahaukaciyar dariyar sannan ya dubi sarki Darwaz yace,shi kenan gobe iyanzu dakarunmu na aljanu wadanda zasu kaiku inda abokan gabarku suke zasu iso,amma ku sani cewa karya mana alkawari daidai yake da gayyato GUGUWAR ANNOBA wacce ba"a san farkonta ba da karshenta,kuma daidai yake da gayyato GOBARA DAGA KOGI wacce batada magani.Gama fadin hakan keda wuya sai fuskar sarki aljanu ta bace bat daga kan wannan sandar tsafi,kawai sai sarki Darwaz ya kama hannun 'yarsa gimbiya huraisa yajata suka tafi izuwa cikin gidan gwamna suka bar boka Hurgas a kasa dirshen yama mai binsu da kallo kawai cikin razani da tsananin mamaki. Al'amarin su Shugaba Sharwan kuwa lokacin dasuka bar birnin Darul Hunam suka nausa cikin daji sukaci gaba da tafiya don isa birni na biyu wanda daga shi saura birni daya kacal su fice daga cikin nahiyar gaba daya sai katsam sukayi gamo da wata runduna ta wadansu mayaka wadanda basu wuce su dari da arba'in ba.Wadannan mutane sunyi shiga ta kamala,suna sanye da fararen tufafi mazansu da matansu,ko wannensu ya boye tsiraicinsa.Har dakarun Su Siyama sun zare makamansu da nufin su yaki wadannan tsirarun mutane sai Siyama ta daka musu tsawa ya dubesu tace,ai babu yaki tsakaninmu a wadannan mutane,domin sune wadanda aka hana mu da yin yaki dasu,sune ma'abota addinin MUSULUNCI... ME ZAI FARU TSAKANIN KABILAR SU SIYAMA DA WANNAN RUNDUNA TA MUSULMAI? IDAN RUNDUNAR SU SARKI DARWAZ SUKA RISKI RUNDUNAR SU SIYAMA WANE IRIN AZABABBEN YAKI ZA'AYI? SHIN SARKI DARWAZ ZAI CIKA ALKAWARIN DAYA DAUKARWA SARKIN ALJANUN? Mu hadu a littafi na shida don jin yadda zata kasance. Saidai Littafi na shida (6) bai fito ba,sai mu tsaya sai ya fito.Dafatan za ai liking and commenting. Again ko akwai wanda zai iya mana providing din ALLON SIHIRI 3,4 and 5 if possible mu dora dashi next.Sai naji daga gareku.