*DEEN* (The heartbreak💔) An amazing love story💘 Story written by Ashaanty love💖 Marubuciyar _AUREN KWANGILA_ _Am back again! Alhamdullilah!🧚🏻‍♀️_ *001* _"So let me know, if you no wan do again, I no go disturb you, I no go hold you!... Let me know uwo uwo if you no wan do again, I no go disturb you, I no go hold you... But no call me back oo, no call me backkk! When you see sey I dey with another person, baby no call me back oo, no call me baaaack when you see sey I dey with another gele..."_ Kpaaam! Kpaaam!! Kpaaam!!! Aka sake bubbuga kofar toilet din kamar za'a 6allata Inaa? Batama San anayi ba saima qara volume din muryarta datayi tana bin waqar dake tashi a earphones din kunnenta _"Even if you call e no go connect, cos I no go dey, I no go dey make you forget, come another day..."_ tafada tana lallauye jikinta kamar wata macijiya tana shashafa jikinta dake lullu6e da kumfa cikin wani irin salo Qara bubbugo kofar akayi da wani mahaukacin qarfi wanda saida taji qarar dukda earphones din kanta Saurin waigawa tayi ta kalli kofar tana zame earphones din kanta a lokaci daya "Wai don ubanki bazaki fitoba!!" Aka fada daga waje ana qara bubbugo qofar Wara manyan idanuwanta tayi kamar zasu fado daga raminsu sannan tashiga dauraye jikinta cikin rawar jiki *"ZAINAB!"* aka sake kwala kira daga waje, daga ji kasan mammalakin muryar amatuqar fusace yake "Na... Na'am mummy, wlh yanzu zan...fito" tafada cikin rawar murya tana jawo towel dake rataye a hanger ta daura ba don ta ida dauraye jikinta ba ta sauko daga bathtub din ta nufi kofar cikin 6arin jiki Kallon kofar take a tsorace tama kasa kai hannu ta bude saboda tsoro "Wai bazaki fitoba?!" Aka sake fadi cikin tsawa wanda har saida ta zabura Hannu na rawa ta zare sakatar kofar tana yin saitin gudu Banko kofar tayi da karfi itama tayo waje aguje tana callara ihu cikin zazzaqar muryarta Mummy datayi baya baya saboda bangajeta da Zainab tayi tayi saurin dafa wani qarfe dake gefe wanda ba don shi ba da tuni tajita qasa Zainab kau tana fitowa, waje tayi ido rufe tana sake fasa qara tana kiran sunan Daddy Bata damu da abinda ke jikinta ba ta sauka qasa da gudu hannu dafe da guntun towel din jikinta ta ratsa yan aikin dake falo suna karakaina Duk dakatawa da abinda suke sukayi suka juyo atsorace suka bi *MADAM* da kallo cike da alhinin meya biyota Basu qarasa tunanin zucinsu ba suka samu amsa don *HAJIYA* ce sukaga itama tayo qasa cikin gudu gudu sauri sauri, cable din chaza a hannunta tana kwala kiran Zainab ganin haka zata fita waje Saurin sunsukuya kai sukayi hartazo ta ratsasu itama tafice sannan suka dago suna girgiza kai na takaicin halin *ZAINAB* Zainab kau haka ta ratsa ma'aikata dake harabar gidan cikin gudunta wanda hakan yasa duk cinyoyinta suka fito waje, ma'aikatan sai binta da kallo suke amma ita ko ajikinta, itadai burinta ta cinma part din daddy kafin mummy ta kamata don tana jinta abayanta Ganin mummy ta fito yasa dukkan ma'aikatan dasuka bi Zainab da kallo saurin kame Kansu suna gaidata cikin girmamawa Babu wanda ta ko kalla sai nufar part din daddy datayi kamar zata tashi sama Zaune yake yayi balancing a kan wata lumtsetsiyar kujera yayi bake bake yana kallon abinda managern shi ke nuna mashi a laptop "Daddy! Wayyo Allah nashiga uku!" Suka tsinkayi muryar Zainab hakan yasa duk suka dago alokaci daya suna kallon kofar shigowa Banko kofar akayi, sai gata ta dirko kamar wacce aka tillo Kafin kiftawar ido harta qaraso gaban Daddy ta danneshi tana qara cikwikwiyeshi Iya rudewa Daddy ya rude don sosai take kurma ihu gashi taqi bari ma yatashi zaune bare ya tambayi abinda ke faruwa, tawani qanqameshi tana ihu kamar wacce ake yankawa Manager kau tsaye yayi agefe yana Kare mata kallo qasa qasa yana lasar le6e ganin yadda duk rabin fresh boobs dinta ke waje ga santala santalan jajjayen cinyoyi mallam Shigowar mummy yasashi saurin shiga taitayinshi yayi qasa da kai Ganin shigowar mummy yaqara volume din ihun Zainab tana qara maqalqaleshi cikin 6arin jiki Sai a sannan shima Daddy yasan meke faruwa hakan yasashi dagowa ya zubamata idanu cikin fushi Kallon da mummy tayiwa manager yasashi saurin daukar laptop din gaban Daddy ya rufe ya kwashe tarkacenshi yayi musu bankwana cikin girmamawa yayi waje Fitarshi keda wuya mummy tayo kansu Daddy gadan gadan wanda hakan yasa Zainab sakin wata mahaukaciyar qara ta cusa kanta a qirjin Daddy jikinta na rawa Ganin hakan yasa Daddy maidata bayanshi yayimata tsakani da mummy yana kallon mummy cikin huci Mummy kau mazuranshi da siracinshi be hanata qoqarin jawo Zainab dake la6e a bayanshi ba Qara kareta yayi yana riqo hannun mummy yafara magana cikin 6acin rai "Wai Maimuna meke damun kwalwarki ne?!" "Hauka ke damunta! Nace hauka nake, wlh yau babu mai hanani illata wannan shashashar anan!" Tafada tana qara yunkurin kamo Zainab dake bayan Daddy tana kuka sosai "Saiki illata ta din! Nace ki illatata! Wai Maimuna kanki daya kau? Kibiyo Yar qaramar yarinya da gudu da wannan lafcecciyar wayar a hannu, nufinki me to? Badai nufinki akanta zaki dora wannan tsinnaniyar wayar ba?" Yafada rai 6ace "Qaramar yarinya? Did you just called Zainab yarinya? Macen dake cikin shekara ta ashirin da daya? 21 ba 12 ba! Ace batasan daidai da rashin daidai ba? Bata iya ware fari da baqi? Kaikuma bakada aiki sai kareta? Bakada aiki sai lallata yarka da kanka!" Tafada cikin tsananin 6acin rai hawaye na kawomata "Yanzu me tayi kuma dazaki biyota dagudu kamar wata qaramar yarinya riqe da wannan uwar bulaliyar kamar ta bugun jakki? Anya kinada tausayi? Yanzu da kin samu riqeta da zubamata ita zakiyi ko? Don rashin imani irin naki, wlh ba don agida kika haihu ba kuma kuna kama da jewel da wlh nace ke ba uwarta bace, 'ya guda tilo da Allah yabamu duniya da lahira shine zaki kashemana ita? Inbanda abinki duka nawa take dazaki dinga addabar rayuwarta haka? To wlh baniso, banaso! Karki sake min haka don ban hada diyata da kowaba kuma zan iya yin komai akanta, idan ke baki sonta to ni inason abuna" ya qarashe yana huci sosai Mummy da tun lokacin daya fara zuba ta kafeshi da idanunta dake digar hawaye ta sa bayan hannunta ta share hawayenta ta saki wayar chazar dake hannunta ta juya tanufi hanyar fita afusace ta fita tana rufo qofar da qarfi Wata wawiyar Ajiyar zuciya suka sauke mai nauyi bayan sun rakata da kallo Komawa da baya Zainab tayi tafada kan kujera tana maida numfashi ahankali tareda furzo wata zazzafar iska daga baki Daddy da duk jikinshi yayi sanyi ganin yanayin da mummy ta fita ya nemi guri kusada Zainab ya zauna ya miqa hannu ya jawota jikinshi "Baby na, hope dai kina lfy?" Yafada cikin tsantsar kulawa Fizge jikinta tayi daga riqonshi sannan tafara magana cikeda tsiwa "Inafa lfy Dad? Ni wlh Allah yasani wannan Matar ba qaramin takurawa rayuwata tayi ba, can you imagine wai dukana zatayi? Yanzu data samu damar kamani fa dukana zatayi, am almost 21 amma ban girmi dukaba a gidanmu, imagine" taqarashe tana girgiza Kai fuska a yatsine Qara rungumota Daddy yayi cikin sigar rarrashi yace "Shiiii... Ya Isa haka, nayi maki alqawari zanyiwa tufkar hanci" Cikeda rashin kunya da tsantsar sangarta tace "Yaushe? Tun yaushe kake cewa haka amma abu ya gagara? Ni wlh haryanzu ban yarda wannan matar uwata ce ba, matarda kwata kwata bata qaunata? Ta tsani ta ganni cikin walwala da annushuwa, duk hanyar datasan zatabi domin daqile farincikina tasanshi, komai na duniyar nan idan nayi to ba daidai bane, tasamin ido tasamin hanci da baki, kai wlh nagaji, ace agidanku bakada freedom? A matsayina na diyar *Alh. Farouq Dan faranshi* diyarshi daya tilo ace banida freedom? Gasu kucakan friends dina wanda ko kwatan arziqinmu basu dashi suna life dinsu yadda sukaga dama, suna living free live babu takura, saini daddy? Saini the whole *ZAINAB FAROUQ DAN FARANSHI?*" ta qarashe zancen tana sakin kukan ta6ara Qara rungumeta yayi sosai yanajin kukanta na ta6a Mashi zuciya sosai "It ok Darling, Dan Allah ki daina kukan nan kar yajamaki wani ciwon, insha Allah zanyiwa tufkar hanci ok?" "Till when Dad? Nace ka kaini abroad na qarashe karatuna ka qiya, ka biye mata kun Sani a wannan Yar iskar makarantar da duk tarin yan jagaliya ke ciki, kai shikenan duk abinda mummy tace saika biyemata, da farko ka yarda zaka kaini UK karatu amma daga ta janyeka daki tayimaka karatu saika chanza magana, wai Umaru Musa Yar adu'a, wai kamar ni a UMYAU, mtcheew!" Taja tsaki cikeda rashin kunya Ajiyar zuciya Daddy ya sauke cikin rashin sanin tacewa saikuma can yace "Yanzu dai it ok, banason ganinki a 6acin rai wlh, hankalina tashi yake, and batun karatu abroad bawai don mummynki ta nuna batasoba yasa nafasa turaki canba, kawai baxan iya jurar zama na tsawon wasu lokutaba batareda na sanyaki a ido ba, Zainab kema kinsan ina qaunarki sosai banason ko quda ya ta6a min ke, kece rayuwata kece fitilata, ke kadai zan Kalla naji sanyi a zuciyata, be kamata kina tadamin hankali da fushinki ba, am sorry uhm? Insha Allah zan tabbatar kinsamu freedom dakike buqata, uhm?" Yafada yana qara tausa murya Zainab da tunda yafara magana tayo gaba da baki cikin sangarta tace "To daddy, yawuce amma please kayi warning dinta ta sakarmin mara nayi fitsari" Dariyar jindadi Daddy yayi yace "Ki kwantar da hankalin ki ok? Insha Allah zanwa tufkar hanci... Yanzu kije kisaka kaya kinga towel kawai ke jikinki, ga gashin ki ajiqe halan baki dade da fitowa daga wanka ba?" "To Ai daddy fitowar kenan, kawai ina cikin wanka naji ana bubbuga kofa kamar za'a 6alla, wai _Don ubanki bazaki fitaba_ inajin hakan nasan muguntar ta motso kenan shiyasa ina samu na bude na arto aguje" taqarashe tana kyalkyala dariya Shima daddy biyemata yayi shima yana kyakyata dariyar sannan yace "Maimuna? Ai halinta sai ita, yanzu dai rabu daita Babyna ki tashi kije kisa kaya kar sanyi ya kamamin ke" Kwalalo idanu tayi tana cewa "Inje ina insa kaya? Ca6! Sokake nakai kaina da kaina taji dadin farfesuna bare dama ka qara kunnata? Ca6!" Ta qarashe tana rungume hannayenta a qirji ta koma ta jingina da kujera tana karkada kaffafu "To yanzu ya za'ayi?" "Kawai kaimin shopping din kayan dazansa online don daga nanma school nayi don babu tsotsan dazai zaunar dani" Murmushi Daddy yayi yana girgiza kai sannan ya dauki daya daga cikin wayoyinshi dake kan stool din gefen kujerar dayake kai zaiyi yadda tace Fitt... Ta fige wayar daga hannunshi tana cewa "Ni zanyi, kana iya yimin wanda bemun ba" tafada hankalinta nakan wayar Maimakon yaji haushi saima murmushi daya saki yana girgiza kai Saida tagama danne dannenta sannan ta cilla wayar a dayar kujerar dake gefenta ta miqe daga ita sai guntun towel din tana miqa mai tafe da hamma babu ko kare baki🤦‍♀? "Daddy yunwa" tafada kamar zatayi kuka Tashi shima yayi yana cewa "Muje ga abinci can dining ba'ama dade da kawowaba ko budewa banyiba" Binshi tayi tana so6are baki Shi da kanshi yayi serving dinta ya dinga bata sai zubamashi shagwa6a da ta6ara take shikuma yana biyemata Koda suka kammala har an kawo kayan datayi shopping Ledar kayan daddy ya bata ta fizge tanufi sama da gudu gudu tsalle tsalle Binta da kallo yayi sannan ya girgiza kai yana murmushi, yarintar diyarshi na qara burgeshi😒 Saida yaga hayewarta saman sannan shima yajuya yafita don zuwa lalla6o Yar matarshi don yasan haryanzu tana can tana kumburi Saida tadauki fin awa asaman sannan tafito Kallo daya zakayi mata kafara tantamar anya musulmace? Sanye take da yellow din top ta roba mai dogon hannu rigar ta mugun lafe a fatarta har ana hango shatin bra dinta Ta cusa rigar cikin high waist red skinny trouser dinta taci zanzaro, wandon yayi mugun dameta gashi iyakarshi idon kafa Sai Ta Dora Farar After Mai Adon Red Stones Akai tasha baby shoes red sai dan siririn yalolon gyale shima jaa data yafama kai wanda ana hangen tulin gashinta ta gyallen don shara2 ne sosai Fuskarnan tasha heavy makeup sai shining take, hannunta daya rataye da wata guntuwar jar side bag dayan kuma riqeda faskekiyar wayarta _yes! Am the princess of the sacred kingdom who rule the life and deathhh_ _am the Queen of the ocean who shines through the rays_ _am the fairly girl in the fairly tale of wonderlandddd_ _so keep calm... Cos the ruling is mineee_ Da wannan waqar ta sauko qasa ta nufi hanyar waje, bata ko damu da rashin ganin daddynba a falon ta fice Tun kafin ta qaraso drivernta yataso da gudun tsiya yazo ya budemata kofa Da waqarta ta iso motar, bata amsa gaisuwar da Bala driver kemata ba sai antayen matsiyacin kallon datayi mashi ta shige motar Maidawa yayi yarufe ahankali sannan yazagaya dagudu ya bude mazauninshi Ganin hakan yasa security saurin wangale musu tangamemen gate din, suka so suka gittashi suka fice yana daga masu hannu...✍️ Ya kukaga kafcen😎 Yawan comments dinku zaiyi determine cigaban littafin, make me go gaga with your comments yadda zan zubomuku flows of updates💃 Ummin fasihu🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:31 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂️🙍🏻‍♂?* (The heartbreak💔) An amazing love story💘 Story written by Ashaanty love💖 *002* "Haba Maimuna? Be kamata akan qaramin abu kizo kina dacin rai ba, idan kika duba duka nawa Zainab din take? Kamata yayi ki dinga mata uzuri akan duk abinda take, nan gaba ko ance tayi baxatayi ba, kowa da kalar quruciyarshi, don Allah ki dinga dagama yarinyarnan qafa kinji?" Ya qarashe cikin sigar rarrashi Ajiyar zuciya mummy ta sauke bayan ta gama hadiyar qululun takaicin daya tokare mata wuya tace "Yanzu alhaji laifine don uwa ta kwa6i yarta? Karka manta fa Zainab macece, ko babu komai aure zatayi watarana, yanzu a tunaninka wa zai iya tolerating din nonsense dinta? Yarinya ace kwata kwata bataji? Koda yaushe abinda taga dama shi takeyi? Bata san daidai da akasinshi ba amma kai a matsayin wadda xaka tsawatar mata bakada aiki sai tunzurata? Wannan a tunaninka soyayya ce? Wannan ba soyayya bace ba alhaji, wannan salon sangarci ne da 6ata tarbiya, kai kullum gani kke kamar na tsaneta ne har cewa kake da ba gida na haihu ba da kace ba 'yata bace, yanzu tsawatarwa yaro yazama laifi. Idan banso Zainab ba amatsayin ta na 'ya talin qwal da Allah yabani was zanso? Inasonta kwatankwacin yadda kake ganin kana sonta koma fiye da hakan amma hakan baya nufin zan barta ta lallace kamar batada mafadi, karka manta bakin da karya kewa danta wasa dashi watarana dashi take cizonshi idan yayi ba daidai ba" Zama yayi kusada ita ya rungumo kafadarta yace "To shikenan zan kiyaye, ki saki fuskar hakanan, ni wlh tur6una fuskar ne baniso, indai baby ce zan mata magana bazata qaraba" Dan ta6e baki mummy kawai tayi batareda tace komaiba "Smile mana" yafada yana leqen fuskarta Dauke kai tayi saikuma ta tashi daga zaunen datake daga gefen gado tace "Yanzu muje kayi break din" tafada fuska babu walwala Tashi shima yayi yace "To da girman kujeranki, Ai yadda kika ce hakan za'ayi gimbiya" yafada yana dariya Itadai gaba tayi don she's not in the mood ****** Danno kai qossashiyar motarsu Zainab tayi cikin harabar makarantar. Tun shigowar motar yan tsirarun mutanen dake wajen suka karkatar da hankalinsu gareta don duk yadda kaso resisting din motar bazaka iyaba saboda daukar idon datake Ahankali ta qarasa inda ake parka sauran mottocin ta samu wuri itama ta parka Da sauri Bala ya bude murfin gefenshi ya sauko sannan ya zagaya ta dayan bangaren inda take yasa hannu ya bude mata murfin kofar Zaune take ta dora kafa daya kan daya tana daddana waya tana humming waqa ahankali Jin an bude kofar yasata tsayar da abinda take ta kalli driver dake tsaye still riqeda murfin ayatsine sannan ta watsar Saida ta mula tasha iska sannan ta dauki guntuwar bag dinta ta bude taciro wani bubble gum ta 6are ta jefa abaki sannan ta zaro sunglasses dinta ta toshe idanu sannan tafara yunkurin fitowa Ganin hakan yasa Bala qara ja baya sosai cikin girmamawa, ziro kafa daya tayi saida taja lokaci sannan ta ida biyota tafito cikin salon qasaita Kamar yadda sukayi tsammani ita dince don tun shigowar motar suka ayyana itace. Mafi yawa acikinsu tsaki sukaja suna kauda kai most especially yanmatan dake wajen don duk sadda ta 6illo sai sun raina Kansu da wankansu, duk yadda suka dau wanka na kece raini da jan hankalin mutane da tazo zata sirar masu dan guntun hayaqin Kansu, abin na matuqar 6atamusu rai most especially idan sunga yadda hankalin maxa ke karkata kacokam zuwa kanta Yanmata sunsha 6atawa da samarinsu akanta don data 6illo kowanne saurayi shagala yake da kallonta yama mance da yana tareda wata Gyara zaman yalolon gyalen kanta tayi ta miqama drivern jakkarta batareda ta kalleshi ba sannan tafara tafiya cikin salonta na catwalk tana taunar chewing gum din bakinta Nanfa idanu sukayi mata caa kamar zasu cinyeta, kowanne ya saki baki da hanci da idanu yana kallonta yayinda yawancin maxan wurin ke hadiyar Yawu ganin yadda albarkatun jikinta motsawa cikin tafiyarta Itakau ko ajikinta don tasaba and it gives her joy, babu abinda tafiso kamar ta dauki hankalin mutane, datazo waje asan tazo hakan yasa kullum da kalar shigar dazatayi don nunamasu eh fa wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa Duk abubbuwan dake faruwa akanta a school din tasani, tasan yadda yanmata ke fada da samarinsu akanta, tasan yadda ta tsone masu ido, tasan yadda take gwara kan students da lecturers da salonta Hakan ke qara fasa kanta taji tafi kowa kuma tana iya taka kowa Watanta hudu da joining din school din amma tayi sunan da ko yau kazo saika San da zamanta don ko shedanun shigarta besa kasanta xaka santa don rashin mutuncinta don ta qware a rashin mutunci da wulaqanci shiyasa kusan kowa ke shayinta don idan ta takaka ta taka banza don ubanta tsaye yake akanta sosai Daga nesa wasu yanmata hudu dasuma kowacce da shigar diban albarkan ta suka nufota suna dan sakarmata murmushi a yangace Dan yatsine fuska tayi tana daga girarta daya datasha shaped jagira ta sauke Saida suka qaraso sannan suka fara bata light hug daya bayan daya kowacce da abinda take fadi "Hey!" "Hyy!" "Hello!" "Xupp!" Saida suka gama sannan tadan motsa baki a yangance tace "How you?" Duk amsa mata sukayi da fine suna tambayarta ya ta kwana Juyawa tayi ta miqoma Bala dake bayanta riqeda jakkarta hannu Da sauri yabata yana mata kirari sannan ya gaida yanmatan wanda qawayene ga gogar taku suka amsa dakyar Da hannu tayi mashi nuni da zai iya tafiya hakan yasa yay musu bankwana sannan yajuya yatafi Rataya jakkar tayi a kafada sannan ta dago ta kalli friends dinta dasuma sai motsa baki suke kamar ita da alamu dai suma chewing gum din sukeci "Muje ko?" Tafada tana fara tafiya suma sai suka motsa suka jero su biyar suna tafe suna Yar firarsu da classic girls Duk binsu da na mujiya akayi, masu Allah wadai nayi masu kushewa nayi masu yabawa nayi, masu ji dama su nayi. "Kaiiii! Baabaa kalli can" inji wani yana qara kafesu da dissashin idanunshi Wanda aka kira da baabaa din dake zaune kan booth din wata baqar mota wanda kallo daya xaka Mashi kasan tattacen dan iskane shima, yace "Manta kawai, Ai na rigaka ganinsu yafada yana jan sigarin hannunshi idanunshi still akansu "Kai baabaa alqur'an babes dinnan akwai kayan ruwa, kullum saisun sa dau sautina ya dau sauti" inji wani mai qaton baki, le6en duk sun dafe don zuqe2 Na ukun yace "Ba doleba? Kajinne dagani zasuyi romo, wlh nima kullum sai sun kunnani" Na hudun yace "Babu kamar wancan mai yellow da red din, duk tafisu komai, Oga dakai kadai ta dace yasin" Wani kafirin murmushin gefen baki nakan motar yayi yana qara jan cigarette dinshi batareda yace komaiba saima kafama kugun Zainab idanu dayayi kasancewar harsun gittasu Na farkon yace "Oga nidai yau abani izini in tashi yanmatan nan hakanan, kwalelen yayi yawa" "Kana haukane Alex? Ka manta yadda take yaga duk wanda ya taremata gaba?" Inji na ukun "Ai gaba kuma da gabanta gandu, mu munfi qarfin yaga" Na biyun yace "Ga yamashi dai Alex yaga Ai mune nan zamu yagasu kai bama yagawa ba saidai mu farka mutum dan kaza kazanshi" yafada yana gatsine irinna qaurayen nan Alex ya kalli nakan motar wanda da alamu dai ogansu ne yace "Oga kabani izini na kawoma ita har makwancinka" Sai a sannan ogan ya dauke idanunshi daga Kansu zee dasukayi nisa ya kalli alex din sannan yadanyi wannan dan iskan murmushin na dazu da alamu dai shima miskilin kanshi ne sannan ya motsa baki dakyar yace "Nabaka" Kamar kau jira yake sai kawai ya nufesu cikin tafiyarshi ta bouncing suka bishi da idanu Su Zee basusan sunayiba suna tafe ne suna firarsu sai gani sukai ansha gabansu Hakan yasasu dakatawa suna kallonshi a dage Ganin abinda ke shirin faruwa yasa mutane fara dan matsowa most especially wadanda suke acan nesa don sunsan wani show din za'ayi yau don anma dan jima ba'ayi show ba don kowa tsoron tunkararta yake don sunsan hakan ba riba Gashi sunga daya daga cikin yaran MASTER ne wanda shima yayi qaurin suna a makarantar hakan yasasu qara matsowa don kashe kwalkwatar idanunsu "Yane chicks? Ya yau?" Yafada yana pocketing din hannayen shi tareda karkacewa gefe daya Anan ma babu wanda ya amsa mashi saidai da alama su qawayen zee sun dan sha jinin jikinsu sanin wanda ke gabansu itakau zee hankalinta nakan wayar hannunta tana taunar chewing gum tana qas qas dashi "So batareda 6atamuku lokaci ba kuma na 6ata nau, dama big boss ne dama yagani kuma ya kyasa, yakuma bani kwangilar kawo muku wannan gara6asar wanda ba kowa keda sa'ar samunta ba, hasalima yanmata ke kawo Kansu gareshi badai ya nema ba amma dayake Ku sipeshial (special) ne shiyasa ya turoni da kanshi don tashin Ku musanmman wannan sarauniyar kyau din" yafada yana kallon zee da da alamu bata Masan me yake cewa ba yana dan lasar bussashen lower lip dinshi "Ya? Mutafi ko? Gayacan yana jira, kunsan boss baya jira" yasake fada yana dake babbakewa yana dan jujjuyawa Har yanzu babu wanda yace komai, saima basarwa da suma qawayen sukayi ganin yadda itama boss dinsu tayi kamar batasan da wanzuwarshi ba Mutanen dake kallonsu sun dan qara yawa kasancewar wasu sun fito daga lecture ga gulmar daketa yawo hakan yasa wasu wadanda ma ba harabar makarantar suke ba garzayowa wajen don ganin qwam Ganin sunki motsawa bare suyi magana yasashi dan riqe tip din phone din hannun zee wanda tundazu idanunta na kai Hakan yasata dagowa tana kallonshi tacikin sunglasses dinta "Magana akemiki fa" yafada yana karkace baki Gira daya ta daga alamun me yake cewa? "Nace boss ne...." Maganar maqalewa tayi sanaddiyar wutar data kiftamashi a idanu Dagowa yayi agigice yana kallonta hannunshi dafe da kumatu yana kallonta baki bude Kingin yaran *Master* kamar yadda suke kiranshi sunyi yunkurin motsawa, Master din da har yanzu yana kan booth din motar ya daga masu hannu yana yima cigarette din hannunshi wawan zuqa idanunshi kansu zee din Suma yan ganin qwam sakin baki sukayi cikin mammaki suna ganin qarfin hali da tsantsar wautar da zee ta tafka "Kan bujinnan kayyasa! Ni kika mara?" Yafada unbelievably still dafe da kumatu Zare glasses din idanunta tayi tana aikamashi matsiyacin kallo tace "An mareka! Me zakayi?!" Cikin wani irin huci yayi kanta kamar zai maketa yaji Master ya kwalamashi kira wanda hakan yasashi tsayawa cak daga yunkurin dayayi Bata damuba ta nunashi da yatsa tacigaba dacewa "Kai waye dazakazo ka tareni a hanya? Waye kai? Waye ubanka a Katsina? Nace waye ubanka a Nigeria?!" Tafada cikin tsiwa "To bari kaji, nafi qarfin cakuri cici irinku, nafi qarfin jagaliyancinku, kaje ka gayawa wanda ya aikoka cewa mai wankemin toilet dinna ma tafi qarfinshi bare ni gabadaya, wutsiyar raqumi tayi Nisan nisa da qasa, yayi kadan don ko matsayin mai bawa flowers dinmu ruwa be kaiba and also ka gayamashi I don't mingle with riff-raffs don qaddara mace tasani attending din makarantar nan at the first place and duk randa wani dan iska yasake yunkurin tsallake limit dinshi I'll help him take him back to the lowest limitation" Tsaki taja tana bude murfin wayar hannunta a fusace, zare sim cards dinta tayi sannan tayi wurgi da wayar taja hannun na kusa da ita suka wuce bayan tasake jan wani dogon tsakin Duk binsu akayi da kallo yayinda qannanun murmurings keta tashi acikin mutanen yan kallo Daya daga cikin yaran Master din yazo inda Alex ke tsaye haryanzu yana hucin 6acin rai Bubbuga kafadarshi ta dama yayi sannan ya kama hannunshi suka nufi motar Tun kafin su iso Master ya diro daga saman motar ya kafa facing cap dinshi yana jefar da kingin tabar hannunshi tareda murjeta da qafa Daidai nan suka qaraso wajenshi, kallon Alex da fuskarshi haryanzu ke bayyana 6acin ran dayake ciki yayi sannan shima ya bubbuga kafadarshi alamun ya share kawai sannan ya zagaya yashiga motar suma suka shishiga aka rufe qoffofin sannan suka bata wuta suka fice daga makarantar aguje suna bade yan gulma da qura "Zee kin kau san suwaye wadannan mutanen?" Inji daya daga cikin friends dinta mai suna Nadeeya Ta6e baki tayi sannan tace "Ke Ai kin Sani ko?" "Honestly speaking abinda kikayi be dace ba, wannan ganganci ne, kinkau San hadarin gayun nan?" Inji Nadeeyar Tsaki zee taja cikin qosawa tace "Look, bansan suba bansan hadarinsuba, kamar yadda suma basu sanniba basusan hadarina ba, don haka ki kyaleni da maganar su karki qaramin 6acin rai akan wanda nake ciki ayanzu" tafada cikin Isa da tsiwa kamar yadda tasaba yimusu Shiru duk sukayi yayinda kusan dukansu maganarta tayimusu zafi, suna jin haushin yadda take treating dinsu tana nunamusu Isa saidai kwadayi ya hana suyi zuciya su kyaleta shiyasa kodayaushe basu iya musamata duk abinda tayi daidai ne koda beyimusuba, gwara gwara nadeeya ita tana dan magantuwa wani sa'in "Kema deeya ki kyaleta mana, mutanen nan fa su suka tsokalota sukazo har inda take, banda ma daqiqanci ma irin nasu ina sukaga munyi Kama da irinsu? Kwata kwata ba class dinmu bane su kinga kau duk abinda akayi musu su suka ja, ni wlh zee kinmin daidai don ko nice haka zanyi" inji wata mai suna Sumayya suna cemata sumee "Ai gwara Ku, suna iya tunkararku tunda dama zani ce ta tadda muje, meye banbancinku dasu? Amma tsabar ya rainama kanshi hankali yarasa wanda zai tunkara saini?" Taqarashe zancen tana nuna kanta a qasaice "Kodayake ba laifinsu bane, da ina UK da duk haka bata faruba, na yanzu ina can living a free and classic life, ina mingling da classic friends turawa ba irinku ba don Ku kam wlh managing nake daku don dai ba yadda zanyi ne" tafada tana yatsine face Dukkansu sunji haushin kalamanta sosai amma babu wacce ta gwada don idan da sabo sun saba da cin mutuncin datake musu akaikaice saidai sunkasa yin zuciya subarta saboda d'an abinda suke samu a wajenta don babu laifi zee badai bushasha ba "Yanzu dai komai yawuce, topic close. Ba girmanmu bane mu zauna muna discussing akan wadancan garorinba, muyi abinda zai fishemu kawai" inji ta ukun mai suna Nuratu suna cemata Nurr Tsaki kawai zee taja tana maida miqewa tsaye tareda sagale jakkarta tace "6acin rai upon 6acin rai, nagudo school saboda 6acin ran gida Ashe ban tsiraba, mtcheew! Muje please in chanza waya bana iya zaman diff" Duk tashi suma sukayi suna gyara zaman jakkarsu sumee nacewa "Aikaudai, Ai gwara da kika barmashi wancan, kiyi me daita baya ya ta6ata da dirty stained hannunshi? Muje mudawo dawuri don mudafa lecture" "Wane lecture?" Inji zee datayi gaba "Na mutuminki" inji sumee tana dariya Tsaki taja tace "Na manta ma, shiyasa fa yau nace ban zuwa mummy ta chaza min kai tasa dole nafito" Nurr dake dayan gefenta don tsakiya suka sata, sumee a gefen haggu nurr a na dama sai deeya da rukky dake bayansu Nurr tace "Ai naga bakwa shiri da mutuminnan" "Bashida mutunci Ai, shiyasa babu ruwana da lecture dinshi, text da exams dinshi kawai nakeyi shima don yazama wajibi" Su nadeeya dake baya kau kallon bayanta suke cikeda haushi sunajin kamar su maketa, sosai hassada ke dawainiya da zuciyarsu, komai ta hada ga kyau ga iya gayu ga kudi Badan abinda suke samuba awajenta da tuni anyi uwar watsi atsakanin su "Mtcheew, how I hate this girl" inji nadeeya "Hmm ke ke fadi anaji" inji rukky "Mtcheew ni wlh sumee tamafi bani haushi, sai wani zaqalqalewa take, cusa kai ba qwarjini kawai" inji deeya "Hmm Ai shiyasa kikaji ban tankaba, don wani abin takaicin hanaka magana yake amma ke naga alamun wulaqancin ta be damun ki don da kanki kike saye" inji rukky tana yin qas qas da chewing gum din bakinta Duk maganar dasuke ahankali sukeyi suna biyeda su zee din abaya "Hmm Ai wani abin kasa yin shiru nake saboda haushi, who did she think she is dazata mari yaron Master kamar Alex!" Wani makirin murmushi rukky tasaki na gefen lips tace "Nikuma dadi naji, gwara tafara ta6a wadanda zasuci ubanta, su maidota hayyacinta, wlh kinji na rantse kuma bazanyi kaffaraba, bazasu ta6a kyaleta ba, badai rawar kai da girida ba, zata gani, zata gane mummunar qaddararta yasata schooling a school dinnan ba UK din datake cikamana kunne dashiba, wlh Master saiya dauki mummunan mataki akanta don shirunsa ba alhairi bane kuma bazai ta6a zama alhairi ba, zatasan ta jangwaloma kanta" Itama deeya murmushin jindadi ya bayyana a face dinta tace "Kumafa hakane, Allah yasadai karya shafemu muma" Yar dariya rukky tayi daidai sun iso motar nurr kasancewar itama tanada ita don ba laifi suma sunada hali, tace "Karki damu, we're free" Dukda su zee sunji wannan Kalmar saidai basusan inda ta dosaba hakan yasa basu maida kai ba suka bude murfin motar, nurr a mazaunin driver zee a gefenta sai kingin dasuka shige baya. Tada motar nurr tayi sannan suka fice daga school din...✍️ Ummin fasihu🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:31 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂DEEN🙍🏻‍♂?* *003* Miqamashi ruwan gora mai sanyi Gandu yayi ya amsa ya 6alle murfin yashiga kwankwada Saida yakusan shanyewa sannan ya janye baki yana kwarama kanshi kingin ruwan "Hmm Ai na gayamaka, yarinyarnan idonta tsakar kai yake kaqi yarda, ga irinta nan ka zubarwa kanka mutunci a bainar jama'a" inji gandu Furzar da huci Alex yayi mai zafi kana yace "Wlh baxan bari taci bulus ba, sainayi gunduwa² daita, wlh saina sauyamata kammani yadda ko uwarta data haifeta bazata shedeta ba" yaqarashe zancen yana huci Dariya wani da ake kira t.j yayi yace "Daga baya kenan Ai, wannan Ai ihu bayan hari kakeyi, lokacin data wankeka yakamata kayi wannan burgar" Cikin jin haushi Alex yace "Wlh ba don Master ya dakatar daniba babu abinda zai hanani lallasa Yar iska, Kutt! Ni wlh sai yanzu abin ke qara bani haushi" yafada yana cizon yatsa Duk dariya suka fashe daita harda Master din wanda hakan yaqara qular da Alex din "Kai amma fa yarinyar nan tasha dakai, kawai sai gani nayi tayima fyal! Ta falleka da mari, yasin sautin Marin har inda muke tsaye" inji wani wai shi Bash Dariya suka qara saki wanda hakan ba qaramin kaishi bango yayiba "Wlh tlh na rantse da wanda ya busan numfashi saina rama, a tsakiyar school zanci mutuncin ta al-qur'an, wlh tajama kanta bala'i" "Kasan ko diyar waye?" Inji t.j cikin dariya "Ko diyar uban waye be shafeniba don ubanka, wlh sainajawa iyayenta asara" yafada cikin tada jijjiyoyin wuya Master ne ya tashi yaje ya zauna kusadashi yana murmushi ya dafa kafadarshi guda yace "Ya kakeji a zuciyarka yanzu?" Jin tambayar yayi kamar ma ta rainin hankali, ko makaho ya lalluba ai yasan ranshi a matuqar 6ace yake Hakan yasashi yin banza ya kyaleshi yacigaba da hucinshi "Karka damu, zaka rama. Da ace na barka a lokacin ka rama da tuni an wuce wurin ka sauke fushinka saidai Kaine da faduwa don bakasanta ba bakasan ubantaba, wlh ubanta na iyasawa a daureka har igiya tayi rara, yana iya sa a 6atar dakai amance da babinka kaga wa gari ya waya?" "Bayan wannan ma yanzu waya cemaka ana dukan mace? Wawa ke dukan mace, mace dakeda hanyoyi birjik na ramuwa marar gogewa a kwakwalwa? Duka abune mai zafi ga duka mutane biyun da abin yashafa Wato mai duka da wanda ake dukan, ta mareka, kai datayiwa Marin kaji zafi hakama itama datayi taji zafi amma a zuciya kaima idan ka rama haka zakaji, why not kayi ramuwar da ita zataji zafi, zafi marar misaltuwa, zafin gangar jiki da ruhi. Abangarenka kuma dadi zakaji, dadi marar misaltuwa, dadin gangar jiki da ruhi, ya kaji kafcen?" Alex da tunda master yafara magana ya kafeshi da mini minin idanunshi, bama shikadaiba harda sauran mutanen dakin suma sun bada hankalinsu kacokam gareshi suna saurarenshi "hakanma chakwai ne boss, wlh abinda ya dace daita kenan, kutt! Amma fah za'a kwashi kayan dadi anan" inji t.j yana kada kai Dan kama le6en qasa Alex yayi ya cije yana kada kai shima yana hasaso abin a qwalwarshi "amma fa bashi kadai ba yakamata ya ramaba master, yakamata mu tayashi ramuwar don nuna kishin ta6amana Dan uwa da akayi" ya qarashe cikin dariya ganin yadda Alex yadago yana watsamashi harara "ji Dan iska, wa aka mara wa ke kukan zafi? To kwalelenka, tawace ni kadai, wlh saita yabawa aya zaqin ta, b***a uba! Wlh ketata zanyi inyi yaga yaga daita, wlh saitafi wata bata iya zamaba, ca6! Zan tattakura inmata eh yane" yafada yana dunqula hannu yana wani wawwanashi Dariya duk suka sa gandu yace "kaji dan air, To wlh bakai kadaiba, muma saimun kwashi romonta mu shar6e mai gangarowa" yafada yana lasan lips Bash yace "ato gwara daka gayamashi, donmu ba itace bane dazamu barka da ita kai dayaba, harda mu wajen ramuwar yadda nan gaba bazata qara qaunar ganin namijiba, koya kace boss?" Murmushi master yayi yace "kwaret! Don nine nan zanfara shigewa sannan ku ku biyoni abaya, na dade ina tarata dama, tunda na dora idona kanta naji ko ana menene saina danata, saina jagula abinda take taqama dashi, dama kawai nake jira kuma tana gab da zuwa, zan kashe qishirwar da nadade ina tarawa akanta" yafada yana cizon baqin lower lip dinshi daya dusashe don zuqe2 "To yanzu master yaushe zamu far mata?" inji Alex cikin zaquwa "very soon, kawai dama zamu jira ta bayyana kanta saimuyi amfani daita, bawai gaggawa zamusa ba don aikin gaggawa na tareda danasani, ahankali zamu lalla6a harmu samu yadda mukeso, mu dasa mata mikin da baxai ta6a gogewaba a zuciyarta" Duk shewa sukayi irinna yan tashan nan sunama master din kirari yayunda shikuma ya jingina da kujera yana sakin wani munafikin Murmushi "Allah yakai damo ga harawa!" inji Alex da yanzu yake jinshi wasai duk wani fushin shi ya yaye Ameen dukkansu suka amsa dashi sannan suka cigaba da firarsu wanda duk na zainab ne *TUSHEN LABARI* Zainab diyace tallin kwal ga attajirin dan kasuwa Wato *Alhaji Farouq Dan faranshi* Alhaji Farouq mai kudi ne sosai kuma sannane ne a jahar katsina dama kewayenta. Matarshi daya mai suna *Maimuna Abdullahi* barumiya kyakyawa Diyarsu daya a duniya itama dakyar da sudin goshi suka sameta kasancewar tanada fragile womb duk cikin data dauka be kaiwa koina yake 6arewa, Dakyar suka samu cikin zainab ya tsaya shima sosai tasha wahalarshi don yasha yunqurin zubewa amma dayake Allah ya qaddarta zayazo duniya sai ta tsallake amma fa dakyar. Bayan haihuwar Zainab ma tayi 6ari sau uku, ganin haka yasa suka yanke shawarar suje ajuya mahaifar don Maimuna ta huta da wahalar hakanan Haka kau akayi, aka juya mahaifarta suka dawo suka maida hankalinsu kacokam akan gudan jininsu daya da Allah yabasu Soyyaya sosai suka dauka suka dorama zainab, riritata suke suna tattalinta kamar gwal, basa qaunar abinda zai ta6amasu sanyin idaniyarsu Zainab ta taso cikin gata da kulawa ta munsanman, tana samun gata ta kowane bangare, iyayenta basuda wani buri aduniya daya wuce su farantamata amatsayinta na diyarsu daya jall Ahaka tafara girma aka sata private school din boko dama islamiyya Makarantar datake zuwa na masu dashi ne sosai don idan kaji school fees din saika riqe baki Ahaka akaita rarrafawa tun zainab bata fahimtar gatar da ake mata har abin yafara shiga kanta Ahankali ahankali tafara tsiro halaye daban2, tafara sangarcewa tana yin abinda taga dama Tun abin be damun mummy(Maimuna) harya fara damun ta don sosai ta tsiro da halin wulaqanci ga na qasa dasu kai harma daidai dasu Tun mummy na kauda kai har abin yafara isarta tafara tsawatar mata Sosai take mata jan ido idan tayi abu ba daidai ba wani sa'in har ta hada da duka saidai daddy kwata2 beson haka don shi aganinshi yarinyace qarama quruciyace Hakan yasa suke yawan samun sa6ani dashi don ita acewarta bazata zuba ido yarinya ta sangarce ba Zainab kau duk da yadda mummy ke qoqarin tsawatar mata taga ta saitu ina? Yadda kasan tirata ake don abin sai qara gaba2 yake wanda Hakan yasamo asaline asanaddiyar goyon baya da daddy ke bata Wulaqanci har na saidawa take dashi, yan aikin gidansu sukafi tantance hakan don bata ragamasu ko kadan dukda ga lokacin bata wani girma ba Kuskure kadan mutum zaiyi ta wankeshi tass baruwanta da yawan shekarunka Akwai ranar da tasa wata yar aikinsu ta kawomata ruwa, garin miqamata hannunta ya kwa6e yazubarmata ajiki Batayi wata wata ba ta dauke mai aikin da mari wanda hakan yayi daidai da shigowar mummy falon Fadin tashin hankalin da akayi a ranar 6ata bakine don mummy liss tayimata ko daga kasawa tayi, shikuma daddy yana dawowa ya tarar da abinda yafaru yahau masifa Ta inda yake shiga batanan yake fita ba, ranshi yayi mugun 6aci munsanman dayaga yadda jikin zainab din yayi rudu2 jikinta yayi rau alamun zazza6i, abinka da yar hutu Duk banbamin dayayi qin tankamashi mummy tayi haryayi ya gaji, hakan ba qaramin sake 6atamashi rai yayi ba hakan yasashi korar yar aikin da abin yafaru saboda ita Wannan abun ba qaramin 6ata ran mummy yayiba amma saitaqi tankawa saidai tasa aranta babu gudu babu ja da baya duk sanda zainab tayi ba daidai ba saita tsawatar mata saidai duk abinda zai faru ya faru don bazata zuba ido diyarta kwara daya duniya da lahira ta lallaceba Tun daga lokacin zainab tafara tsoron mummy, duk rawar kanta bata yarda tayi gabanta, sosai taja baya daita hakan yasa babu irin Wannan shaquwar ta d'a da uwa atsakaninsu Hakan na damun mummy amma hakan take dannewa don tasan idan ta sake mata dayawa abin gaba zaici Haka rayuwa taita gangarawa har zainab tagama primary aka sata wata secondary itama ta masu kudi Shiganta secondary school yasake ta6ar6are al'ammura don a S.S1 ta hadu da wasu qawaye suma masu jida kudi da Wulaqanci Kan kace me? Suka qulle kasancewar duk kanwar jace kowacce na taqama da arziqi Awajensu qawayen ta koyi shigar banza wanda su a wajensu fashion ne Cikin dan qanqanin lokaci itama ta koya, tayi slim fitting din top din uniform dinta takuma gutsure skirt din yakoma guntun don dakyar yake rufe gwiyagu Takoma saka dammamun kaya acikin gida sa6anin gowns datake sawa ada Saida tajima tanayin haka sannan mummy ta ganota kasancewar duk abinda zatayi da taku takeyi saboda mummy yar da eyes don duk wani movement dinta tana qoqarin ganin tasani Amma dayake zainab 'A' ce saita gwadamata ita yar zamani ce Idan zata school saita sassauto da skirt din qasa yadda zai zama normal ta dora cardigan akan uniform din yadda baza'aga matsewar rigar ba, dataje school kuma ta cire cardigan din ta maida skirt din yadda yake, agida kuma bata yarda takamata da shigar diban albarkar datake idan tasan zasu hadu saita dora after dress Ranar da mummy tagano ba qaramin bugu taciba don Wannan karonma saida tayi mata liss dukda daddy nanan kasa qwatarta yayi, haka ta tisata gaba taje ta watso kayan closet dinta ta daukesu Wannan abin ba qaramin 6ata ran zainab yayi ba shiyasa taqara jan baya daita don aganinta bata sonta kullum burinta ta takuramata, bayan ba haka akema friends dinta ba don su asalin free life sukeyi babu takurawa dukda su sunada yayye da qanne ba kamar ita ba, gani take ita dake ita kadai Awajensu kamata yayi ace ita tasamu kwatankwaci koko fiyeda gatan dasuke samu Hakan yasata yankewa aranta cewa mummy bata qaunarta don itama wani sa'in tantanmar anya ita ta haifeta kau Dole tabar shigar banzan agida don anchanza mata closet inda aka tulamata gowns gowns masu kyau da tsada saidai ita bata ganin wani kyaunsu kawai sawa take, uniform ma mummy tasa aka dinka mata wasu kuma duk sadda zata fita zuwa school saita bincikata sannan ta tafi Ana haka har suka shiga S.S3, anan ne fa suka tsara wai su a qasar waje zasuyi higher institution. Tare da friends dinta suka yanke cewa uk zasu cigaba da karatu har suna cewa zainab acan zatafi sakewa tayi living free life dinta babu takurar mummy Jin haka Yasata Jin dadi sosai tana hasaso yadda zatayi rayuwarta mai cike da yanci Nan suka shiga tsare tsarensu suna planning yadda zasuyi rayuwarsu as classic ladies Koda zainab ta tunkari daddy da maganar kasa musawa yayi kamar yadda yasaba sabida gudun 6acin ranta Hakan yasa shi amince mata farat daya, sosai zainab taji dadi takuma qagara suyi final exams dinsu Wato w.a.e.c Alhamdullilah sunyi exam din cikin aminci sun gama inda suke saka ran samun results mai kyau don sosai suka dage a exams din musanmman zainab dake doqin wucewa abroad, batason result dinta yakawo mata cikas shi yasa ta dage gashi dama tubarkallah zee din badai kwalwa ba Koda result din yafito taji dadi sosai ganin yadda yayi kyau saidai murna ce takoma ciki jin daddy ya sauya maganarshi ta tafiyarta abroad Lokacin saida tayi dan qaramin hauka don rudewa tayi ta giggice banda kuka da ihu babu abinda takeyi Qarin abinda yabata haushi shine jin cewa mummy ce tasa daddy yafasa, baqinciki yasata kulle kanta a daki na kwana daya As usual daddy ne yashiga damuwa, yayi yayi ta bude kofar taqiya, haka shima yawuni bakin kofar ta yana rarrashi don shima hankalinshi be kwanta da tafiyar ba dama tun farko amsa mata yayi amma ansar bata kai ciki ba saigashi mummy tazo taqara zugeshi inda taita lissafomashi illolin dake tattare da barinta tafiyar A bangaren mummy kau ko ajikinta, tana ganin yadda daddy yaqi tsaye yaqi zaune sabida fushin zainab din tayi kamar batasan sunayi ba don acewarta wannan shirmen bada itaba Saida tagaji da fushin ta ta fito don dole jin yunwa zata kassarata, saidai tun Lokacin batada walwala kullum cikin qunci take Ahaka har Lokacin zana jamb yayi, don tabasu haushi taje taqiyin komai a jarabawar acewarta meye amfaninta bayan ba abroad zataba kuma ita Allah yasani batayin school anan Koda result yafito daddy beji dadi ba sam don ba haka yasoba itakau mummy tana ganin result din ta6e baki tayi tace idan bazatayi karatunba ai sai ayimata aure tunda ta ita, abu cikin sauqi Sosai ran zainab yaqara 6aci don dama don taba mummy haushi tayi amma taga alamun bata damuba saima sa6on datayi, wai aure Ca6! Aikau beyiwuwa, duka nawa take zatayi aure kuma ita ai haryanzu bataga wanda yayimata ba don haryanzu bataga taste dinta ba don ita yana daya daga cikin burikanta ta auri handsome multi-millionaira guy, mai ji da kyau da gayu dakuma naira wanda idan yashiga taro dolene asan da wanzuwarshi Wannan burin nata yasa bata sauraron kowa don kallon yan jagaliya take musu wadanda basukai level dinta ba Zainab tanada wani hali na downgrading din mutane musanmman na qasa da ita, tanada halin jin kai da taqama da isa shiyasa ba'a cika shigemata ba saboda halinta don samarin ma masu qarfin hali ke tunkararta wanda daga qarshe dai wulaqanci da cin fuska ke rabasu Ataqaice dai haka tayi wasting din wannan shekarar wajen xaman gida wanda sam bemata dadi ba saboda takurawar mummy don cikin shekara dayannan saida ta tilastamata iya girki don tisa qeyarta take su shiga kitchen tare Hakan yasa shekara na zagayowa ta kwantar da hankalinta ta zana jamb din dakyau don sosai mummy kemata barazana da kalmar aure kuma tasan halin mummy tana iya sawa ayimata din Sai gashi result din yafito mai kyau, daddy yaji dadi sosai, beyi wata2 ba ya sama mata gurbi a jami'ar Umar Musa Yar'adua Haka dai tafara zuwa school din badon tasoba sai don tasan shine kadai maslaha agareta Farkon zuwanta school din kamar tayi kuka don takaici, haka dai ta haqura tacigaba da zuwa saidai kwata2 bata qaunar school din Ba'a qulla wataba aka san da zamanta a school din, ko tsaddadun shigarta basu da shan qamshinta ba tsiwarta da wulaqancinta zaisa kasanta don bata ragama kowa cin mutunci awajenta ba komai bane Saida tayi wata uku batada qawa ko daya don bata buqata don aganinta duk ta wuce class dinsu, duk yadda yanmata keson cusa kansu gareta qin basu dama tayi don aganinta tawuce ajinsu Dakyar su nadeeya suka samu shiga suma don yan gayune sun iya gayu gasu 'ya'yan masu kudi dukda basukai zee ba Su ukune friends dinta da farko Wato *Nadeeya*, *Ruqayya* da *Nuratu* sai daga baya *Sumayya* tayi joining dinsu Suna abota sosai don Koda yaushe tare suke saidai hakan be hana tana musu wulaqanci ba saidai basu ta6a nuna sunajin haushi dukda kau suna ji kawai shanyewa suke don ko banza tasasu suma sunyi popular a school din Duk jikinsu tafi son sumee saboda tafi binta yadda yakamata shiyasa tafi dasawa da Ita saidai batasan dukkansu taciki na ciki Yanzu haka tana level 200 ne (sorry nayi mistake a page 2 nace watanta 4 da farawa, a min afuwa ina nufin shekararta cikin na biyu kenan) Tana karatun kadaran kadahar don ba laifi tanada kwalwa saidai duk cikin lectures dinsu tafi tsanar na lissafi plus basu shiri da lecturer din dake subject din he is a no nonsense man, yasha dizgata a aji da korata waje idan tayi laifi kuma cikin ikon Allah takasa maida martani don ba qaramin kwarjini yake mataba, hakan yasa tabar attending din lecture dinshi sai exam ko text daya zama dole shima duk yawanci take samun average dakyar don bata attending class dinshi kuma qawayen ta masu attending din duk masu qwalwar dusa ne Master kau irin wadannan student dinne marassa jin magana masu neme nemen magana da tada zaune tsaye a school Asalin sunanshi Murtala amma dayake beson sunan sai kawai ya radama kanshi master wanda yabishi don dayawa basusan ainahin sunanshi ba Iyayenshi talakawane futuk saidai shi yanada hali don har mota gareshi, mutane sun rasa koina yake samun kudinshi dayake bushasha a school, wasu har cewa suke qila fashi yake ko sata don dama yayi kama da wanda zai aikata saidai azahiri yana samun kudinshi ne ta hanyar huldar kayan chaji (maye) anan yake samun kudinshi kuma yakashe a banzace don beta6a taimakawa Iyayenshi ba dake fama da talauci Master ya dade a school din don karatun nashi kwan gaba kwan baya yake kasancewar beda man kai, hakan yasa duk aka sanshi a school din don yajima acikinta Tun farko farkon zuwan zainab school din ya kafa kwakwarshi akanta saidai beta6a tunkararta ba saboda yaga yanayinta yar ji dakai ce kuma zatayi wulaqanci, illai kuwa saigashi hasashenshi ya tabbata hakan yasa yaqi tunkararta amma a kullum da kwadayinta yake kwana yake tashi amma kasancewar shi tattacen dan bariki ne kuma ya dade acikinta yasashi qin tunkararta kai tsaye, shima Alex wanda ainahin sunanshi Aliyu yabashi dama ne kawai ya tunkareta don ganin abinda zatayi saigashi tayi abinda yake tsanmmani din kuma ya tabbata ko shine yaje haka zata mashi Aliyu (Alex), fahad (gandu), Tajudeen (t.j) da Bashir (bash) abokan jagaliyancin master ne, tare suke duk rashin jinsu shiyasa duk ake tsoransu a makarantar Ana shayin shiga gonarsu don sunsan fada da aljani ba riba, sai gashi yau zainab ta ta6o tsuliyar dodo.... ✍️ No editing 🙏🏻 Masu complaining bana turamasu a group dinsu bayan kuma ina ciki don Allah kuyi hqr, wahalar tayi yawa, shiyasa ma natura link din group din a duk groups danake ciki yadda ko yaya ne wasu members din group din zasuyi joining. Members din group dina please ku dinga sharing a groups din dakuke don Allah, basai nasha wahala bayan zaman typing inkuma dasa da sharing ba, please do this for me uhn? 🙍🏻‍♀? Thanks so much, nasan qauna ce tasaku complaining, nima i heart you so very much 😘 Ana together insha Allah 🤝🏻 Ummin fasihu🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:31 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* 004 *CIGABAN LABARI* Aranar dai basu koma school din ba don daga siyar wayar suka wuce yawon shopping kamar yadda suka saba yi duk lokacin da yan qalular school din yataso masu Sai can wajajen 3pm takira drivernta ta gayamashi inda suke yaje ya daukota suka rabu da friends dinta akan sai gobe idan Allah yakaisu Acan school kau yinin ranar rumours din abinda yafaru tsakanin zee da Alex yaita zagaye school din, inda duk wanda yaji saiya bayyana alhininshi da doqin sanin wane mataki su master zasu dauka akai, duk inda kaga mutane sunyi group suna magana to zancen suke, Allah Allah suke gobe tayi suga me zai biyo baya don sunsan team din master basa yafiya bare mantuwa. Zee kau Koda suka isa gida a d'ad'arce tashiga gidan tana zullumin yadda haduwarsu da mummy zai kaya Tadai san yanzu daddy bayanan bare ya taremata hakan yasata aro nutsuwa ta sa Da sallama tashiga main falo din gidan, sosai taji dadin rashin ganin mummy a falon hakan yasata yin wuff ta haye sama tashige daki Saida tayi wanka ta chanza kaya zuwa loose kaya nashan iska sannan ta gabatar da sallar asr da batayi ba sannan ta koma kan gado ta zauna tana jingina da kan gadon tareda miqe qaffafunta saman gadon Remote ta dauka taqara a.c din dakin tana dan jan tsaki Allah yasani batason irin weather nan ta zafi, jin zafin tsiya gareta kamar wata mai qiba, yanzu kuma lokacin shi ne don lokacin farko farkon damuna ne, ruwan basu sauko ba sosai don duka duka befi sau uku ba da akayi ruwa. Bata nemi abinci ba don dama saida suka cika cikinsu Awaje, da daddare kuma sawa tayi aka kawomata har dakinta kuma duk Wannan abin tana yine duk don karsu hade da mummy, abinda bata saniba shine mummy tariga ta wuce wajen don batada riqo sam, a lokacin da akayi abu take hawa da adan jima abin zai sire aranta koda zatayi reacting bazaikai yadda zatayi a lokacin da abin yafaru ba *WASHEGARI* Yau bata fita school ba dawuri kasancewar yau lecture din bayan sallar juma'a garesu kasancewar yau juma'a Sai wajajen 2:30pm tafito bayan taje ta gayawa mummy wanda ke qara jaddada mata cewa da angama takamo hanya suyo gida Da to kawai take amsawa don tasaba da irin Wannan kashedin nata, har mammaki take wani sa'in, yadda kasan tana magana da wata qaramar yarinya da batasan ciwon kanta ba, abin na bata takaici matuqa amma ya ta iya? Haka take binta Dole kodan gudun mazga Kamar jiya yauma bala ya budemata back seat tashiga ta zauna kamar bataso Zagayawa yayi ya bude front seat mazaunin driver ya zauna ya tada motar sannan sukazo suka fice Tafiya suke kan shimfidaddiyar kwalta cikin normal speed, bakajin motsin komai acikin motar Sai dan sautin motar da kuma alamun tafiya suke Tsaki taja tana dago kai daga wayar hannunta tana yatsine fuska, jitake komai baya mata dadi hakan yasata juya kanta ga window din motar tana kallon abubbuwan dake gudana waje ta tinted glass din motar Ana haka har suka qaraso school din, samun wuri bala yayi ya parka motar sannan yafito ya budemata murfin kofar Tun shigowar motar harabar school din idanuwa sukayi caa akanta, dama yawanci ita suke tsimaye don har yanzu sosuke suga yadda zata kaya tsakaninsu da master dukda tundazu suke raba ido suka ko daya daga cikin team din master amma basuganiba da alama dai yau bazasu zoba As usual saida tafara zuro kaffarta ta dama mai sanye da pink hill shoe mai madaurai, sosai takalmin yahau kafarta kasancewarta fara tass Saida taja yan daqiqu sannan ta ida fitowa bayan ta jefa chewing gum abaki kamar yadda tasaba Sosai aka qara yayyameta da ido saboda shigar datayi mai tafiya da imanin mutane Sanye take cikin peach english gowns mai adon pink stones agaba Rigar tabi jikinta ta zauna wanda hakan yasa shape dinta fitowa sosai, kanta yafe da siririn pink veil Sai purse pink da wayarta dake hannunta. Bata damu da kallon da mutane kemata ba ta dan kalli bala da wutsiyar ido tace "kaje kawai, zan nemeka but karkayi nisa" tafada kamar mai ciwon baki "ok, to afito lfy" bata sake bi takanshi ba tafara tafiya cikin takunta na catwalk wanda yazame mata jiki musanmman idan ta lura idanun mutane na kanta Batayi nisaba suka hade dasu sumee wadanda dama sun dan jima a school din Saida suka gaggaisa sannan suka wuce class kasancewar lokacin lecture din yayi Awa daya sukayi lecture din ya daukesu sannan suka fito, kai tsaye wurin dasuke zama idan suna free suka nufa Wajen bayan wasu classes ne, wurin is quiet gashi yanada shades din itattuwa hakan yasa wurin keda iska mai dadi ga mazauna wurin Zazzaunawa sukayi kowa na wash! Kamar wadanda sukayi aiki suka gaji "guys da alama dai bakusan abinda ke faruwa ba ko?" inji rukky Duk kallonta sukayi kowa nason jin mezata ce "Hmm to Mr Ibrahim dai ya tafka mana tsiya, wlh jiya attendance ya dauka na wadanda sukayi attending din lecture dinshi, wai kuma yace attendance din a matsayin 50% ne na exams dinshi" Duk wara idanu sukayi cikin tsagwaron mammakin maganar ta "dagaske? Waya fadamiki?" inji Nurr "Hmm zauna nan, wlh abinda yafaru kenan kije ki tambayi wadanda sukayi attending lecture dinshi kiji" inji rukky "but this is madness! Tayaya za'ayi attendance kawai yazama 50% din exams? Ina aka Ta6a Wannan?" inji Zee cikin tsagwaron mammaki "Hmm to ai gashi kinga anyi yanzu, ni wlh hankalina atashe yake" inji rukkyn tana buga tagumi da hannu daya Duk shiru sukayi suka kasa cewa komai, can sai sumee tace "kutt! Amma malaminnan akwai dan air, ji wata kalar bazata" Deeya tace "that means carryover for us don duk tsiyarmu bazamuci kingin 50% dinba kunga failing and carryover is the last option" "lallai kam, don ni babu abinda nake ganewa a lecture dinshi, kawai nasan yana rubutu yana kuma 6a6atu, nidama can na tsani calculations, bana ganewa sam" inji sumee "kece baki ganewa ko ni? Dama dakyar nake samun naci 20/60 a exam dinshi sai su assignment din da duk googling dinsu nake wanda yake hadawa da marks din cikin lissafi badon haka ba ai da tuni na fado, kawai dai na yarda soyake muyi carryover din don alamu sun nuna muguntarshi ce ta motsa" inji Nurr "ca6! Aikau baxai yiwuba wlh, wazai qara repeating 1year a Wannan yar iskar makarantar? Kunga kutashi muje musameshi don bamuga ta zama ba" inji zee tana yunqurin tashi "ina zaki? Kin manta baya zuwa school ranar friday? Kuma ma idan kinje me zakice mashi? Wannan mai baqar zuciyar kamar arnan farko kinsan ko mutuwa kike kina dawowa bazai chanza qudurinshi ba bare dama ga yadda alaqarku take dashi bakwa hada inuwa daya, kinsan ba sauraronki zayayi ba" inji rukky Komawa tayi tafasa tashin, ta dafe kai da hannu daya "wlh nasan saboda ni yayi Wannan abun, dama burinshi inyi failing, yaga duk hanyar dayabi saina 6ulle, ko yayane ina ququtawa insamu average shiyasa ya tsiro Wannan muguntar" inji Zee cikin dacin rai "wlh kam, ko shakka babu saboda ke yayi hakan don dama yana ciki dake na rashin attending din class dinshi da bakiyi" inji deeya "plus idan Kin ganshi bakya gaidashi kuma ya tsani rashin respect, yaga yabi ta kowacce hanya yakasa cinma burinshi shiyasa yabi ta Wannan hanyar gashi muma ta shafemu" inji sumee "Oh God! What am I gonna do? Banason carryover, I hate this school like mad! Na tsani school dinnan" tafada ashagwa6e tana yarfa hannu hawaye na taruwa a idanunta Duk shiru sukayi suna kallonta ganin dagaske hawayen take "Duk mummy tajamin Wannan abin, da yanzu inacan dasu Jidda muna karatunmu cikin kwanciyar hankali, Wannan ai immaturity ne, kawai don ya rasa yadda zaiyi sai yamin mugunta? Wlh nidai bazan yarda ba, gwarama asan abin yi don bazanyi wani carryover ba" tafada cikin 6acin rai still tana hawaye, dama haka take a zahiri kamar wata jan wuya saidai ruwa ruwa ce, abu kadan kuka Saurin matsowa kusada ita sumee tayi tana sharemata hawaye tana rarrashinta yayinda rukky da deeya suka kalli juna suka dan ta6e baki "haba dear, kibari mana don Allah, insha Allah bazamuyi carryover ba, back to sender, ki kwantar da hankalinki" inji Nurr itama tana matsowa kusada ita "tayaya zan kwantar da hankalina Nurr? This man hates me, kullum cikin son ganin ya wulaqantani yake, me nayi mashi? Why cant haters just leave me alone!" "Hmm ni aganina mafita yakamata mu nema ba Wannan ba let's just find solution to this" inji deeya "wane solution? Inbadai zuwa zamuyi muyi begging dinshi ba ya taimaka ya janye qudurinshi" inji rukky Dago watery eyes dinta da suka fara chanza launi tayi ta watsa mata kallo tace "beg him? Wani abu muka masa ne? Kawai confronting dinshi zamuyi yagayamana inda aka ta6a yin haka, don Allah yadorashi a wani matsayi saiyayi zalunci? Wannan ai zalunci ne" tafada cikin 6acin rai "Hmm ke kika san Wannan, kuma kinsan mr ibrahim baya tolerating din nonsense gwara ma mubishi ahankali don samun mafita wa kanmu" inji deeya tana dan ta6e baki Zee bata qara cewa komaiba sai sake dafe kai datayi tana kallon qasa Tana jinsu sunata shawarwarun yadda zasu 6illowa mr ibrahim, itadai kawai tana tareda sune amma hankalinta yayi wani wajen. Yanzu ya zatayi idan ta fadi? Kenan carryover din zatayi? Tasake maimaita year dinnan? Kai bazai yiwuba, over her dead body! Insha Allah hakan bazata faruba Sosai takejin zuciyarta na zafi don 6acin rai, jitayi zaman wurin ma ya isheta hakan yasata jan tsaki ta miqe tsaye tana duba time a tsaddadiyar wristwatch din hannunta Duk kallonta suke basuce komaiba, zaro wayarta tayi ta lallubo number bala ta danna mashi kira Ringing biyu tayi aka daga "kazo muwuce" tafada ataqaice ta yanke kiran batareda ta jira jin me zaice ba "badai tafiya zakiyi ba" inji nurr "mezan jira?" zee tafada batareda ta kalleta ba "kamata yayi mu zauna mu sama ma kanmu mafita" ta bata amsa "kudai sama ma kanku mafita, ni na riga na yanke on monday zanje insameshi duk yadda ta fanjama fanjam" tafada tana niyyar barin wajen Duk tashi suma sukayi suka maramata baya Tafiya suke saidai ita tana gabansu don yau ba irin tafiyarnan bace ta yanga, yau ranta a 6ace yake shiyasa bata tsaya Wannan catwalk din nata ba Tana cikin tafiya tana saqe saqen yadda zata 6illoma Wannan al'amarin, tasan dai ko ana manna mata garwashi a ido ne bazata iya yiwa mr ibrahim rashin kunya ba, yanada kwarjinin da bazata iya hada ido dashi na tsawon lokaci bare akai ga rashin kunya Duk fadin school din shine tafi shakka kuma tafi tsana don gwani ne wajen duzga mutum da kunyatashi Tun farkon zuwanta school din suke takun saqa dashi, be qaunarta kwata kwata saboda rawar kanta da rashin kunya, duk sadda yashigo class dinsu beda wanda ya tsone mashi ido kamar ita Duk tambayar dazai jefo to ita yake jefamawa, idan kuma bata amsa daidai ba yaimata tass a class din Yasha embarassing dinta a class hakan yasa tabar shiga class dinshi sai taga dama, wani sa'in ma idan tayi attending din class dinshi taga damar ya jefo mata tambaya tayi kunnen uwar shegu dashi, qarshe dai saidai ya korata waje Subject din da mr ibrahim ke koyawa yana daya daga cikin favourite Subjects dinta saidai kasancewar tasu batazo daya da mutumin ba yasa subject din siremata, taji yafita ranta, Tun tana jurewa tana zama Koda zai dizgata ne har tajima bata iya zaman lecture dinshi kwata kwata don Koda tana class yashigo tashi take tazo ta gifta ta gabanshi ta wuce, Wannan abin ba qaramin 6ata mashi rai yake ba shiyasa yaquduri anniyar koyamata hankali Saidai duk yadda yaso kadata bata faduwa don duk qumu saita ci average, hakan na bashi mammaki sosai kuma hakan na nunamashi tanada qwalwa kuma da zata zauna ayi lecturen tareda ita da taci fin haka kuma da tazamo daya daga cikin masu topping class din a subject din Amma girman kanta bazai barta ba, ita gani take tafi kowa kuma zata iya taka kowa, shikuma ya tsani mutum mai irin Wannan halin shiyasa basa ga maciji MR IBRAHIM ADAM magidancine kuma lecturer a jami'ar umaru musa yar adu'a Mutum ne na mutane wanda yayi suna kaff makarantar saboda dadewarshi acikinta dakuma kasancewar shike koyarda duka makarantar subject din mathematics Mutum ne adali kuma mai tsayin daka akan gaskiya shiyasa ko ana bribing din lecturers don samun marks to babu mai iya tunkararshi da hakan, shi mutum ne mai aiki da gaskiya abinda kaci shi zaibaka ba don haka ba yadda ya tsani zee da tuni ya kadata Mutum ne mai wasa da dariya amma fa da yazo bada darasi dinke fuskar yake dib donma kar akawo mashi wasa Yanada experience sosai na koyarwa yadda mutum zai fahimta duk daqiqancinshi saidai idan dama baka shirya koya bane Saidai kuma aduniya ya tsani raini da rashin kunya, duk yadda kuke dashi ka nemi kawomashi raini saiya nunamaka other side dinshi Asalin gabarsu da zee yafara ne lokacin farko farkon zuwanta makarantar Ranar tayi late kuma shi a dokarshi ba'a shiga aji idan yariga yashiga Itakau tana zuwa tashige sundum2 kamar sa ko gaisuwa Juyowa yayi daga rubutun dayake yana kallonta, ganin tana niyyar zama yasashi dakamata tsawa wanda ba qaramin kada hanjinta yayi ba don dama aduniya ta tsani tsawa "ke wacce daqiqiyace zaki shigoma mutane class babu neman permission?!" Bata amsaba sai yamutse fuskar datayi tana qoqarin daidaita nutsuwarta don ba kadan ba tsawarshi ta tsoratata "bakijina ne! Ko bakisan kinyi late ba kuma a dokana babu mai shigo min class idan narigashi shiga?!" Ga mammakin kowa sai gani sukayi ta gyara zaman handbag dinta tazo ta gifta ta gabanshi tawuce tana qass qass da chewing gum da taunarshi yariga yaxame mata jiki Duk binta sukayi da kallo baki sake har mr ibrahim, fadin 6acin ran da mr ibrahim ya tsinci kanshi aciki 6ata baki ne, jiyayi zuciyarshi na tafarfasa kamar zata faso qirjinshi Tunda yake ba'a ta6a wulaqantashi ba a bainar jama'ar dake ganin girmanshi ba irin na ranar, hakan yasa shima ya tattara takardunshi yafice don bejin zai iya cigaba da abinda yake. Ranar rumours yaita zagaye school don hakan na daya daga cikin abubbuwan dayasa aka santa Mr ibrahim bece komai ba don gani yake qaranta mane biyewa Wannan jaririyar yarinyar saidai labari na kaiwa ga kunnen school authority suka kirata Dukda sundan ji shayi dasukaji waye babbanta saidai hakan be hana sukai mata fadaba suka tisata gaba har office din mr ibrahim tabashi haquri Dukda yanuna ya haqura kuma dama shi abin be dameshi ba amma deep down yayi vowing saiya koyamata hankali shiyasa ya tsiro da salo salo na cin mutuncinta a class wanda hakan yaqara hura wutar gabarsu har zuwa Wannan ga6ar Fitt.... Taji an figemata dan yalolon gyalenta daga kanta wanda hakan yasata dawowa daga duniyar tunani data lula Waigawa tayi da sauri ganin wane dan iskan ne yayimata haka Turus tayi tana kallonshi dama su sumee dake bayanta Kanshi a sadde yake yana kiciniyar cire gyallen daya sarqaho mashi bracelet din hannunshi Tsayawa tayi tana kallonshi cikin rashin sanin abin yi Sumar Kanshi kawai take gani wanda yake rough ba gyara sai tip din hancinshi dakeda tsini sosai har kana hangenshi dukda kan a sadde yake Binshi da kallo take up & down Sanye yake cikin pure white jallabiya, it's so pure babu digon datti ko daya, kaffafuwanshi Sanye da baqin half cover shoes suma suna shinning da alamu sunsha polish sai hannunshi na dama dake sanye da agogo baqi mai matsakaicin kudi sai na haggun dake sanye da bracelet wanda shi gyallen zee ya tsarqaho Duk yadda yaso yacire kasawa yayi hakan yasashi sa baki yana amfani da haqoranshi wajen ganin ya cire amma still yakasa hakan yasashi jan gyallen afusace sai ji kake kyattttttt! Ya keceshi Zee da ta tsaya kallon ikon Allah tundazu ta wara manyan idanunta cikin tsakanin mammakin abinda yayi hakama su rukky Jefar da gyallen yayi qasa yana zare zarruruwan gyallen da suka maqale a bracelet din haryanzu yajuya batareda yanuna yamasan da tsayuwar wasu akanshi ba koko bema san dasuba oho? Ya cigaba da tafiyarshi yana cigaba da zare zarruruwan Ran zainab yaqara 6aci, dama yaya lfyar giwa? Hakan yasata saurin binshi tasha gabanshi Da sauri ya dago kamar ma atsorace jin kawai mutum a gabanshi Sauke hazal oily eyes dinshi yayi acikin nata large sexy eyes suka kafe juna dasu..... ✍️ Ummin fasihu🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:31 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *005* Wani irin abu taji ya tsirgamata daga tafin kafa har tsakar kanta Cigaba da kallon kwayar idanuwan nashi tayi wadanda suke farare tass sai wani maiko2 sukeyi Kasa janye idanuwanta tayi daga cikin nashi yadda kasan anyi magnetting dinsu Shima kallonta yake ta siraran gashin Kanshi dasuka biyo ta idonshi kasancewar sumar ganshi is rough amma kuma hakan ba qaramin style yabada ba. Kallonta yake cikeda nazari, ganin batada niyyar magana ko ta matsa mashi yawuce ya sashi ra6ata zai wuce Hakan yasata dawowa daga duniyar kallonshi tayi saurin qara tare gabanshi Jin ya sake zubamata wadannan idanun nashi yasata kawar dakai tace "what did you think you did?" Yamutsa fuska yayi yana mata kallon rashin fahimta hakan yasata nuna gyalenta dake yashe qasa abayansu tace "look at what you did to my veil!" Juyawa yayi yana kallon inda take nunawa nan yaga gyallen inda yake yashe Izuwa yanzu su sumee sun matso kusa suna kallonsu donma inda suke babu mutane da yanzu anfara taruwa don ganin kwam Dan wara oily eyes dinshi yayi alamun aiyo? Sannan maida kallonshi kan zee dake cike famm "ya.. Maqalomin bracelet ne" yafada cikin very cool voice mai gardi da jawo hankalin mai sauraro Izuwa ga mammalakiyarta Sosai muryar tashi tasake dulmiyar da Ita Izuwa duniyar kallonshi, she don't know what came over her kawai tsintar kanta tayi da sake kafeshi da large eyes dinta Ganin tayi shiru kamar dazu yasashi sake yunqurin wucewa Hakan kuma yaqara fargar daita tasake tareshi cikin fushin ganin yadda take wani shagala da kallonshi kamar yau tafara ganin namiji "Don ya maqaloma bracelet saika yagamin kaya ka jefar?!" tafada atsakankanin haqoranta Ganin ya tsaya yana kallonta beda niyyar cewa komai yasata qara fusata tace "ko bakaji ba!" atsawace Ga dinbim mammakinsu sai gani sukayi yayi saurin jada baya yana toshe kunnuwa da hannayenshi yana 6ata fuska "ouch! That's so scary" yafada cikin cool voice dinshi yana qara yamutse fuska still hannunshi dafe da kunnuwa Kallon juna zee dasu sumee sukayi sannan suka sake maida kallonsu Kanshi "babu kyau shouting, zai iya affecting kunnuwan mutane" yafada yana kallonta innocently "babu kyau me? Kayimin laifi kuma kanada gut din fadamin magana? Kasan koni wacece?!" tafada afusace "O'O! Kinji haushi ne?" yafada yana sakin hannayenshi daga dafe kunnuwan dayayi Kasa cemashi komai tayi tacigaba da kallonshi ganin yadda yayi maganar anarke Suma su deeya sakin baki da hanci sukayi suna kallon abu mafi al'ajabi a rayuwarsu "Don't worry, kakata tace idan mutum yaji haushi ya ja nannauyan numfashi ya fesar... duk numfashin dazaija yayi tasbihi idan zai fesar kuma yayi tahlil... idan kayi haka sau goma zaka nemi fushin ka rasa Kuma tace bakyau reacting nan take idan kana fushi, hakan zai iya zama cutuwa gareka, misali yanzu ke kinyi reacting cikin fushi ta hanyar yin tsawa, kinga zai iya zamo cutuwa gareki. nafarko maqogaronki yana iya yimiki ciwo nabiyu muryarki na iya shaqewa, kuma yana iya zama cutuwa ga mai sauraronki, nafarko yana iya affecting din kunnenshi na biyu yana iya tsorata kamar yadda nayi kuma ga duk lokacin da mutum ya tsorata hakan na affecting adrenaline hormones dinshi wanda zaiyi jerking dinshi yasashi yin abinda ya dara qarfinshi ko iyawarshi kinga idan mutum yacika tsorata To zai fada risk din yin abinda ya girmi hankalinshi har takai watarana yayi abinda zaizama cutuwa agareshi Kuma duk Wannan zai farune sanadin fushinki, kinga gwara first option din, inhale tasbih, exhale tahlil and stay safe" Baki, ido, hanci, kunnuwa suka saki suna kallonshi tunda yafara magana kamar sun samu majigi Ganin ba wanda ya motsa acikinsu kuma babu mai niyyar motsawa yasashi cewa "zan tafi, kakata nacan tana jirana" yafada cikin cool voice dinshi sannan ya ra6a yawuce suka bishi da kallo batareda wani daga cikinsu yayi yunqurin sake dakatar dashi ba Rakashi da kallo duk sukayi suna kallon yadda yake tafiyar tashi cikin sanyi da nutsuwa babu alamun sauri ko kadan aciki don tafiyar tafi Kama da ta qasaita ko sarauta Saida ya 6acemasu sannan suka maido kallonshi ga juna Fashewa da wata iriyar dariya deeya tayi harda dan duqewa yayunda kingin suka shiga tayata idan ka cire zee da tasake bin inda yabi da kallo "OMG! Kunkau ji abinda naji? Ko ni kadai naji?" tafada cikin dariya Rukky dake dariyar itama tace "like seriously anya kanshi daya kuwa?" Sumee tace "adai kammani he's ok amma a kwalwa ina tantanmar hakan" Dariya suka sake Fashewa dashi hakan yaqara qule zee "Wai meye abin Dariya anan? Ku bama ta matsalar damuka shiga ba kuke kun tsaya kula matsalar wasu, mtcheew this is immaturity kuna wani kware baki a tsakar santa and you still call yourselves classic girls, mtcheew" Hakan yasasu yin shiru amma ba qaramin zafi maganar ta tayimusu ba Guntun tsaki tasake ja sannan tawuce rai a matuqar 6ace, abubbuwa sun hademata goma da ashirin Binta da kallo sukayi ransu ba dadi, suna niyyar maramata baya sukaga Rukky tajuya zata tafi "ina zaki?" inji nurr Bata ko kalleta ba kuma bata tsayaba tace "class, ku kuma da bakuda zuciya saiku rakatan" tawuce tabarsu nan tsaye Jiki asanyaye suka juya sukabi bayan zee saidai suna zuwa sukaga har motarta tafice daga school din Suma rai a6ace suka watse kowa ya Kama hanyarshi. Yinin ranar qarasheshi tayi rai ajagule, abin duniya sun taru sunmata yawa ta rasa meke mata dadi hakan yasa takoma sukuku komai yinshi take kamar marar lakka Tsabar yadda tasa abin aranta saigashi itace harda su mafarkai wai a qarshen semester dinsu tasamu carryover din, mr ibrahim ya fiddota gaban jama'a yana dizgata itakau sai kuka take Da Wannan mummunar mafarkin ta tashi Addu'a tayi ta tofa a gefen haggunta sannan takoma ta jingina da kan gado tana qara tariyo mafarkin nata Tana ahaka taji bubbugar qofa, tasan mummy ce, dama tasaba duk asuba saita tadata tayi sallar Kauda kai tayi daga kallon qofar tana zu6ura baki, jitayi tana jin haushin mummyn don kome yafaru duk itace sila da tana uk da ba haka ba Jin still tana bugun kofar kuma ba barin bugun kofar zatayi ba saita tashi yasata janye bargon jikinta a fusace ta sauko sannan ta nufi kofar tana yan gunaguninta wanda ita kadai tasan abinda take cewa Saida tasaki fuska ta maida ta kalar wanda ya tashi daga barci be isheshi ba sannan ta bude kofar Mummy ta watsa mata harara tace "ke shikenan idan kin kwanta kamar mai barcin mutuwa baki ko motsawa" Dan turo baki tayi tace "mummy Allah banfa jiba" Tsaki mummy taja tace "dama yaza'ayi kiji kina Wannan barcin asarar, kiwuce kije kiyi alwalla gashican sai assalatu akeyi" Da To ta amsa sannan tajuya tawuce itama mummy tarufe kofar tawuce Alwalla ta dauro ta chanza zuwa wata brown jallabiya da dama ta wareta mainly for sallah sannan tazura hijab ta shimfida sallaya tahau kai tashiga gabatar da sallar Koda tagama komawa tayi ta jingina da gado sa6anin da da datagama take hayewa gado takoma barci Tunanin mafita take ga matsalar mr ibrahim, Allah yasani abin na ranta sosai kuma yana damunta, tasan kome zatayi bazata iya cinye kingin 50% dinba kuma samun qasa da 50% din yana daidai da faduwa koda 49% ne kuwa, gashi dama yaya lafiyar giwa? Daman cikin 100% take takarkarewa tasamu 60 ko 62% Shima saita hada da sleepless nights ta hana kanta barci tana karatu sannan zata take samu, gashi fa tana ganin tayi iya qoqarinta na karanta duk abinda aka koyar a class amma be zama kamar yadda zata dauka a class din idan anyi lecturen daita kuma dama abinda zaka dauka idan aka koyar dashi cikin aji yafi wanda zaka dauka idan ka ware kanka kai kadai da niyyar koyawa kanka Maida kanta tayi ta jingina da gadon tareda maida lower red lip dinta cikin baki tana tsotsa Yanzu meye mafita? Taje ta roqeshin kamar yadda taji su rukky nacewa? Idan ta roqeshi zai saurareta? Koko ma qara samun kafar wulaqantata zaiyi? To idan ma taje ya xatace? Bata ta6a roqon alfarma ba kuma batasan yadda akeyi ba, kuma batajin tana iya strooping so low ta roqi alfarma, rashin roqon kuma na iya chazamata wulaqanta ta qarshe amma kuma ai batada tabbacin roqon zaisa ya saurareta Cije lip din tayi tana lumshe ido cikin rashin samun mafita Fuskarshi yayimata gizo a idanunta hakan yasata bude idanun _inhale tasbih, exhale tahlil and stay safe_ maganar shi ta dawomata Tsaki taja tana cewa "phsyco kawai" under her breath Miqewa tayi daga kan sallayar ta ninke ta ajiye ta cire hijab dinta sannan takoma kan gadon ta kwanta tareda jan bargo da niyyar takoma barci saidai yaqi zuwa sai juyi kawai datake tana ta saqa da warwara Haka tayi spending din weekend din cikin zullumi da damuwa tana addu'ar Allah ya dorata akanshi ranar monday. *MONDAY* Tunda wuri tafara shiri don ko komawa barcin nan nata na bayan asuba batayiba, tana gama sallah tashiga shiryawa agurguje don tana son taje school din da wuri ayita taqare Saidai duk saurin datake saida tara takusa sannan tafita sakamakon ruwan da aka kece dashi wajajen qarfe bakwai Cikeda takaici takoma ta zauna Dole tajira ruwan ya dauke sannan ta fito Sanye take cikin riga da wando na pakistan mai irin bujen wandon nan, rigar kalar pink wandon kuma fari sai gyallen kayan Shima pink Kaffafuwanta kuma Sanye da fararen baby shoes sai side bag mai hannun sarqa pink Sosai tayi kyau, irin kyawunnan mai tafiya da imanin mutane, fuskarnan tasha heavy makeup don dawuya tayi simple makeup. Fitowa tayi tana duba agogon hannunta batareda ta kula ma'aikatan dake gaidata ba Ganin hakan yasa bala saurin tasowa yanufi motar dasu fita daita da aka lullu6e da rigar mota sbd ruwan da akayi Yayewa yayi sannan ya zagayo ya budemata kofar, fadawa tayi ciki tana cewa "dalla mallam kayi da jiki, am late" Saurin mayar da kofar yayi ya rufe sannan ya zagaya dagudu ya bude mazauninshi ya zauna, tada motar yayi sannan ya figeta cikin yan sakanni suka fice gidan suka halba kan titi *UMYU* Fitowa yayi bayan yagama daidaita parking din ya zagayo ya bude mata. Saida ta 6are bubble gum ta jefa abaki ta zaro shade dinta tasa sannan ta ziro qafa ta fito Caa akayi mata da idanu don yau mutanen dake harabar makarantar nada yawa saboda duk yanzu ake zuwa Bata damu da kallon ba as usual ta sallami bala tafara tafiyarta tana jin yadda iska mai dadi ke kadawa kasancewar ba'a dade da gama sheqa ruwaba Mutane kau kallon nasu nayau dabiyu don master be dade da wucewa ba Shima hakan yasasu ji ajikinsu cewa yau fa za'asha show inda yawanci addu'a suke Allah yasa aci uban yar iska suga ta fulaku Itadai batasan sunayi ba haka tazo tawuce cikin salon tafiyarta tawuce class direct. Tana niyyar shiga su sumee na niyyar Fitowa, ganin ta yasa suka juya suka shiga class din gabadaya suka wuce inda suke yawan zama idan ba lecture suke ba "yane?" inji zee tana dora jakkarta a cinyarta "Normal.." duk suka amsa sannan suka fara tambayarta ya weekend ta amsa da lfy Bin class din daya rude da hayaniya tayi sannan ta maida kallonta kansu tace "wai meke faruwa ne? Naga class ya burkice" Ajiyar zuciya suka sauke atare Sumee tace "ba Dole ya burkuce ba? Ai idan ma akwai fin burkucewa saiyayi" Gyara zama tayi tana kallonta tace "bani insha" Ajiyar zuciya sumee ta sauke tace "yawuce mutuminki?" Gabanta ne ya yanke ya fadi "mr ibrahim?" ta tambaya fuskarta na nuna alamun fargaba "shi fa, wlh yau naqara tabbatar da beda mutunci" inji Nurr "meya faru kuma?" inji zee "yanzu ya fattatakomu daga office dinshi" tabata amsa "ya fatattakoku? Zuwa ku kayi?" inji zee "bamu dade da shigowa class ba mukaji Ana shawarar zuwa wajenshi bada hqr, don fa mutane dayawa basuzo ranar ba, shine muma muka bisu mukaje, wai kinga wulaqancin dayayi mana? Hmm roqonshi muke amma yadda kikasan tirashi muke, ba arziqi muka fito bayan ya koromu" inji sumee Tunda tafara magana zee ke kallonta hankali tashe har takai aya "wlh mutuminnan wani sa'in beda m, kinga yadda ya fattatakemu kuwa?" inji deeya "Hmm aini dama nasan fa bazai yadda ba don magana daya yakeyi, yadai tabbata saimunyi carryover tunda ba digon imani aranshi" inji rukky Izuwa yanzu ran zainab yayi mummunan 6aci "wai me mutuminnan ke nufi damu ne? Ina ya ta6a jin anyi wannan zaluncin? Idan mutum lalura ta hanashi zuwa ranar fa? Shikenan sai a kadashi? Mtcheew!" taqarashe tana jan tsaki sannan ta miqe "Ina zaki???" suka fada har suna hada baki "wajenshi yau za'ayita taqare" tafada tana wucewa Deeya har zatayi magana rukky ta dakatar daita ta hanyar ruqo mata hannu tana wani makirin Murmushi. Direct office din mr ibrahim ta nufa zuciyarta na qara qarfafa mata gwiwa. Bata ja burki a koina ba sai a gaban kofar office dinshi inda aka rubuta sunanshi 6aro2 da manyan haruffa Tsayawa tayi tana kallon kofar tanajin dan qwarin gwiwarta na neman fecewa Saurin tattaroshi tayi ta saita kanta sannan tayi knocking Saida ta bubbuga sau biyu sannan taji yabata izini cikin husky voice dinshi nake nutsar da duk wani mai rawar kai Jitayi kamar ta juya saikuma ta daure ta tura kofar tashiga da sallama Ansawa yayi batareda ya dago daga tattara takardun dayake ba Zuciyarta ce tashiga racing tanajin kamar ma bazata iya bude baki tayi magana ba Jin shiru yasashi dagowa daga abinda yake don ganin wanene Turus yayi ganin itace saikuma slight Murmushi yayi forming agefen bakinshi ya dauke kai yana cewa "uhum? How may i help you?" yafada yana cigaba da hada takardun Qara gudu zuciyarta tayi Jin muryarshi akaro nabiyu sai yanzu tafara danasanin zuwanta ma Tattaro nutsuwarta tayi taqara matsowa ta tsaya bayan kujerar dake facing din table dinshi ta dafa chair din sannan tace "Good morning" "morning" ya amsa a taqaice batareda ya dagoba Dan gyara murya tayi sannan tace "amm... Dama maganar attendance daka dauka last week thursday ne wanda kace zaka ajiyeshi amatsayin 50% of your exam" shiru tayi ganin ya dago ya kalleta hakan yasata janye nata don bata iya jurar kallon cikin qwayar idonshi "Ehen? What about that?" yafada yana kafeta da idanu "am... Dama sonake naji ko hakane?" tafada still bata yarda sun hada ido ba "eh hakane" yabata amsa kai tsaye "but why?" tafada tana dagowa tana kallonshi "saboda na isa" yabata amsa yana komawa ya jingina da kujerarshi yana jujjuyawa "amma aganina Wannan be isa hujjaba kuma ina aka ta6a hakan?" tafada calmly tana kallonshi saidai ba directly a ido ba "gashi anfara anan, kuma inada ikon yin fiyeda hakan idan naga dama" yafada cikeda isa Qoqarin danne 6acin ranta tayi tace "amma sir baka ganin zai zama cutarwa ga wasu?" "wasu? Su wa?" inji mr ibrahim Hadiye wani abu tayi tana qara qarfafa ma kanta gwiwa "wadanda lalura ta hanasu zuwa ranar" "i dont care" yafada yana daga kafadu tareda sake jawo wasu files Jitayi zuciyarta na tafarfasa don takaici "but as a Good leader kamata yayi ka damu da damuwar na qasa dakai, akwai wadanda lalura zata hanasu zuwa kamar rashin lfy ko makamancin haka, idamma mataki zaka dauka bekamata kadau mai tsananin tsauri irin Wannan ba" Dagowa yayi akaro nabiyu yana kallonta sannan ya ajiye pen din hannunshi yayi interlocking din yatsunshi akan table din gabanshi yace "Good leader? Am i good?" Dan ta6e baki tayi ta kauda kai tana cewa "haka suke cewa" ahankali don karya ji amma saboda sharpness din kunnuwanshi saida yaji hakan kuma ba qaramin hasalashi yayi ba "naruga na yanke hukunci and there is no going back, so get out!" yafada yana zaro mata idanu "amma kasan Wannan ba adalci bane, How will you feel idan akayi wa 'ya'yanka haka? Suma students 'ya'yan wasu ne you should treat them How you treat yours" tafada muryarta nadan kyarma ga daci2 datake ji a maqoshinta "wait, are you talking on your behalf ne koko?" ya tambaya yana tsareta da ido don shi tunda tashigo beji ta furta kalmar ban haquri ba saima yi datake kamar bata cikin wadanda abin yashafa "Am talking on behalf of wadanda lalura ta hanasu attending, wadanda basu jiba basu ganiba" tafada hawaye na ciko idanunta Mammaki abin yabashi Wato ita tafi qarfin ta roqoshi kai tsaye saidai ta fake da wasu? "ke meye ruwanki tunda bakya cikinsu?" yafada yana Jin ranshi naqara 6aci "saboda nasan nice sila" tabashi amsa kai tsaye hawayenta na digowa wanda tayi Saurin sharcewa don bata buqatarsu yanzu "mene?" ya tambaya yana wara idanu Qara sharce wasu sabbin hawayen dasuka gangaro tayi tace "yes, saboda ni kayi hakan kuma nasani amma idan zakayi hakan be kamata ka hada da wasu ba, ni kadai zakayi mawa" "Are you insane!" yafada yana buga table da qarfi wanda saida ta miqe tsaye Jin yadda taji bugun har cikin kwalwa "nace kina hauka ne zaki shigo har office dina kiyimin shirme?!" yafada Shima yana tashi tsaye Zee dake hawaye sosai tace "idan da nikadai kayimawa bazaka ma ganin office din naka ba don hakan bazai iya yimin komai ba, bazai hanani tsallakewaba!..." sai kuma tafashe da kuka tasa taffukan hannunta ta rufe fuskarta tacigaba dayi Fadin 6acin ran da mr ibrahim yashiga 6ata bakine, shi sai yanzu yaqara tabbatarda yarinyar nan tantiriyace duk inda yake zaton takai ta wucenan "dakyau! Dakyau!! Dakyau!!!" yafada yana tafi saikuma ya tsuke fuska yace "ki tsallake to, albishirinki? Na safsafto hukunci na, attendance din ranar ya sauka daga 50% zuwa 30%, wadanda basuyi attending ba sunada damar neman 70% ciki harda ke.. Kuma qarin wani albishir... Acikin 70% zanbada gara6asar 20% a matsayin assignment, 50% kuma shine zaku ida samowa amatsayin exam, ki tsallake, nabaki wuri da babbar dama na tsallakewa, ki tsallake mugani... Kuma na rantse da mahallicina bazan ta6a yima kowa runton marks ba, kinsanni kuma kinsan abinda zan iya, bazan ta6a yiwa wani mahalluki rintoba a marks, da zanyi da tuni nayi hakan akanki don haka kitafi, Allah ba mai rabo sa'a" Share hawayenta tayi ta kalleshi da rinnanun idanunta ta rataye jakkarta dakyau sannan cikin rashin ta ido tace "sun gode, don ni ko ahakan aka tafi ba damuwata bace..." "out!!!" yafada a mugun tsawace Juyawa tayi tafice da dan gudu tana toshe bakinta Bugun desk din mr ibrahim yayi yana cize lip din qasa cikin mugun takaici Koda tafito dakatawa tayi da gudun tafara tafiya don kar agane yanayinta saidai ko ganin gabanta batayi sosai, 6acin rai da qunar rai sunsa batama gani sosai Jitayi ta bangaji mutum hakan yasata yin baya baya zata fadi taji an cha6e hannunta an ruqo Qara wara oily idanunshi yayi yana kallonta yanason ya sheda ina yata6a ganin Wannan fuskar Jin wanda ya ruqo hannunta beda niyyar dagota yasata bude ido ta kalleshi taga yawani yi sakato yana kallonta Batareda tama shedashi ba ta daka me tsawa cikin 6acin ran dake cinta tace "kai hamago!!!" Tsorata yayi wanda hakan yasashi sakin hannunta ba shiri tayi baya2 sai cha6all!! Tafada cikin chakwalon dake bayanta daya taru sanadin ruwan saman dazu... ✍️ Ga long page kusha yau da gobe, insha Allah duk ranar juma'a zamu dunga hutawa saboda falalar ranar kuma kasancewarta gajeriyar rana Juma'at mubaraq in advance🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:31 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *006* Runtse idanuwanta tayi gamm tana sakin qara, cha6all!!! Taji ta fada cikin wasu ruwa wanda sanyinsu ya ratsa ilahirin jikinta Daga inda take tana Jin gasping din mutane da yar hayaniya Bude idanuwan tashiga yi ahankali har suka bude tangaram Bin mutanen dasuka zagaye wurin tayi da kallo wasu baki a hamgame don mammaki wasu na qumshe baki don hana dariyarsu fitowa Da daya daya ta dinga binsu da kallo har idanuwanta suka sauka akanshi Sanye yake cikin qatuwar rigar sanyi baqa da wando jeans baqi sai hular sanyi dayasa wanda ta rufemashi kunnuwa itama baqa saidai anyi mata rubutu da farin zare a gaban hular, kasancewar shi fari sai shigar baqaqen kayan suka sake fiddoshi sosai Wara mata oily idanunshi yayi ganin ta kafeshi da ido "O'O! faduwa kikayi?" yafada yana dafe baki da tafin hannunshi yana qara wara idanu alamun al'ajabi Dariya mutanen dake kewaye da wajen suka Fashe dashi sosai wanda hakan yadawo daita daga duniyar kallonshi ta maida kallonta ga jikinta tana duba yadda koina nata ya 6aci da chakwali Rintse idanu tasake yi gamm sannan tafasa wata iriyar qarar takaici tana Fashewa da kuka Dariya masu kallonta suka qara sawa yayinda wasu har waya suke zarowa suna daukarta hoto, abinka da dama haushinta sukeji Shikau tun sadda tafasa qarar yaja baya atsorace yana cewa "O'O!" Su sumee ne suka kutso tacikin mutanen suka nufi inda take zaune rashe2 taci kwalliya da ta6o ga fuskarnan ta dauki combination din makeup dinta dana chakwali sai rizgar kuka take kamar zata shide Dagudu sukayi wajen ta suka kakkamata suka tadata tsaye still tana kuka idanuwanta arufe Yau wacce iriyar baqar ranace gareta, tunda take bata ta6a Jin ta muzanta ba irin na yau, jitake kamar qasa ta bude ta nitse ciki Kamata sukayi suka fara barin wurin da ita "yayi sarauniyar kyau! Wannan wanka ya wanku, gaskiya kin cancanci award mai taken mud queen!" wani acikin mutanen yafada Wurin sake daukar Dariya yayi nan kowa yashiga tofa albarkacin bakinshi Su sumee dai basu ko nuna sunsan dasuba suka wuce daita suna lalla6a ta cikin tausayawa saidai aqasan ransu fall yake da farinciki jisuke kamar su fiddo dariyar dake cikinsu suyi mai isarsu Motar nurr suka bude suka sakata ciki sannan sumee ta zauna kusada ita riqe da jakkarta rukky kuma kusada sumee sai deeya data shiga gaba itakuma nurr tashiga mazaunin driver, tada Motar tayi tabata wuta ta figeta suka fice daga makarantar gaba daya. Sukau students abin nema yasamu tuni school yakarade da labarin *mud queen* kamar yadda suka samata yanzu Wadanda basunan akayi sai cizon yatsa suke dukda yawanci an gwadamasu hotunan da aka dauketa, kowa Allah yaqara yake mata abinka dama da tayi baqin blood Awajensu kuma dama kowa haushinta yakeji. Suma su master dake bayan school cikin kangwaye inda suka saba zuwa su chake labari ya riskesu Zokaga dariyar qeta, duk acikinsu Alex yafi farinciki da abinda yafaru, sai cewa yake ai dama fada da aljani ba riba kadanma tagani. Zaune yake qarqashin wata bishiya yana cin chips hankali kwance, wasu students su uku suka zo wajenshi mace daya maza biyu. Shewa suka saki gabadaya suna qarasowa wajenshi Dago oily pure white eyes dinshi da zara zaran lashes sukaiwa qawanya yayi ya kallesu sannan yasaki Murmushi wanda ya lotsar da dimple dinshi na tsakiyar dan gemenshi ya matsa masu ganin zama zasuyi. "na wajen kaka! Na wajen kaka! Gaskiya yau ka farantamana rai fiyeda tunaninka" inji daya daga cikin mazan Murmushi kawai yayi ya saka chips din hannunshi baki sannan ya mimmiqa masu ledar chips din alamun bismillah "Ah! Ai dole muci *Deen*, Wannan farincikin daka samu yau dole muyi kodimo" inji macen cikinsu Duk daukan daddaya sukayi sannan suka daga sama sukace "murna!!!" sannan suka saka cikin baki suna ci suna dariya "Amma na wajen kaka yau kamin daidai, ashe baya ga qulluwa kanasa mutum farinciki" inji dayan mutumin Bece komai ba sai Murmushin dayayi yaqara saka wani chips din a baki "amma ka burgeni *deen* gwara daka jefa shegiya cikin chakwalon, ba ita yar iska ba?" inji na farkon "wlh, ai bakaji dadin danajiba, ina class aka kirani da gudu na iso wajen don baxan bari abani lbr ba" inji macen tana dariya "yo dama ai wanda bega show dinnan ba yayi rashi, duk fulakun dai yau itace dame2 cikin mud, dama ai ance qarshen alewa qasa" "O'O! Be kamata kuna cewa haka ba, idan kune bazaku so haka ba, kuma kakata tace Annabi (s. a. w) yace kasowa dan uwanka abinda zaka sowa kanka" yafada yana zaro wani chips din Dariya sukayi gabadaya sannan daya daga cikin mazan yace "idan hakane kai meyasa ka jefata chakwalin?" Saurin dagowa yayi ya kalleshi yace "ni?" "eh mana, bakai ka jefata ba?" "O'O! Ni ba jefata nayi ba, ita ta fada" ya amsa cikin son kare Kanshi "ita ta fada? To waya saki hannunta? Kai kanka kasan da baka saki hannunta ba da bazata fadaba" inji dayan yayinda kingin duk suka kada kai alamun haka zancen yake "O'O! Itace fa tayimin tsawa, sainaji tsoro na saketa.. kuma dama idan mutum ya Tsorata adrenaline hormones dinshi naqarayin sama hakan zaisa kayi abu cikin fitar hayyaci ko wanda ya girmi tunaninka, shiyasa bansan sadda na saketa ba. Kuma itama tsawar datayi tana iya zama cutuwa gareta, yana iya sa muryarta ta shaqe ko maqogaronta yayi zafi kuma..." "yanzu dai *Deen* ya isa haka kafin mukai magariba kana kwararo zance don nasan halinka, kuma aimu bacewa mukai kaine mai laifi ba, ai Allah ne ya kamata, wai kaga iskanci da take tsulawa a school dinnan kuwa? Ta raina kowa, gani take kowa trash ne shiyasa bata ganin kowa da gashi akai" Macen tace "ga girman kai, yadda take daukar kanta kamar irin diyar qarunnan nan, batasan shi arziqi Allah ke badawa ba ga wanda yaso kuma yana iya kwacewa a lokacin dayaso" "aikuma ta shiga uku don wlh saitayi danasanin zuwanta makarantar nan don yanzu tazama laughing stock, nan gaba zuwa school din saiya gaggareta" "O'O! Babu kyau rama sharri da sharri, kakata tace idan mutum yayi maka sharri kai ka rama da alhairi, bazaka fadiba saima kaci riba, kuma ai bata ta6a tanka muku ba kawai tana harkarta ne, jijji dakai da girman kai ra'ayinta ne, kuma arziqin da take taqama dashi nasune kubarta tayi mana tunda bata dai cutar dakuba, watarana idan babushi baxatayi ba... Kuma kakata tace Annabi (s. a. w) yace *laa dirara wala dirara* karka cuci wani kaima kuma karka bari acuceka, jijji dakanta da taqamarta bata cutar dakuba ta kowane siga meyasa kukuma zaku so cutar daita?" yafada innocently cikin muryarshi mai tsananin taushi da gardi. Kallon juna sukayi sannan suka fashe da dariya Macen tace "kai dama duk ta inda aka 6ullo maka saika gwalashe mutum" "ato bakiji takenshi bane, _na kaka hassala mahaqurci, tunzura mahaukaci, Fashe na kan wuya_" Duk dariya suka Fashe dashi shidai Murmushin nan nashi yayi yana shan ruwan pure water "matarka zatasha fama, wai! Kwamacala kenan" inji macen "saita nemi ayi harka sai kace kaka ta hana" inji dayan Duk dariya suka sake sawa macen na rufe bakinta da hannu alamun maganar tagirmeta dinnan "harkar me?" ya tambaya innocently Dariya suka qara tunzurewa dashi, macen ta tashi tana cewa bada ita za'ayi bankadar nan ba tawuce tana dariya Suma mazan tashi sukayi suna dariya, daya yace "au bakasan harkar ba kenan, bari kaka zata gayamaka idan lokacin yazo" yaqarashe yana dariya "wa? Bari a barshi daga shi sai ita kaga aiki da cikawa ai ire irensu sunfi jaraba alqur'an" inji dayan "au haba?" na farkon yafada yana bashi hannu Kashewa sukayi dayan na Cewa "am telling you" Shidai Deen kallonsu yake yakasa pointing finger akan abinda suke nufi "to na kaka, zamuyi sama" inji nafarkon "me zakuyi sama?" inji Deen Dariya suka qara kecewa daita dayan yace "kamo tattabaru, kaidai naga sadda zaka waye, muntafi da alamu dai bakada lecture ko? " Kada kai yayi yace" sai 1:00pm" "toko zaka rakamu kallon kwallo" inji na farkon cikin neman magana Girgiza kai yayi yace "A'a kakata tace..." "Allah sarki, Allah sarki, basai ka qarasa ba, nagane ai. Kai majeed mutafi" yafada yana kamo hannun wanda yakira majeed din suka wuce suna dariya Binsu da kallo yayi har suka 6acemashi sannan ya maida hankalinshi kan littafin hannunshi yashiga budewa A bangaren su zee kau kuka taita musu acikin mota dukda kau yadda suke bata hqr suna rarrashinta, jin zuciyarta take kamar a oven don zafi Abin yaxame mata biyu, ga cin mutuncin mr ibrahim ga na Wannan mutumin da batama san sunanshi ba Wai waye mutumin nan? Ranan ya fizge mata gyale ya yaga yau kuma ya jefata a ta6o "wlh Allah bazan yarda ba, wlh saiya gane ya ta6ani, sai yasan kowa ya wulaqanta daga shi har wancan immature ibrahim din, wlh saina koyamasu darasin lifetime!" saikuma taqara Fashewa da wani kukan Dukkansu qoqarin kumshe dariyarsu suke hakan yasa kowa kauda kai don idan ka ganta dole tabaka dariya tayi gaja2 kamar ba classic zee ba Rukky ce tayi qarfin halin cewa "Haba zee? Don Allah kibar kukannan hakanan kar yaja miki ciwon kai, kuma batun koya hankali ai dole ne don wlh saiya san ya ta6a classic girl kamarki" ta qarashe a siffar gaya magana Itadai bata ce komaiba saima cigaba da kukanta datake don data tuna taqara tunzura Babu abinda yafi 6ata mata rai kamar kalmarshi ta *faduwa kikayi?* idan ta tuni sai taji wani qululun takaici yasake danne zuciyarta Suma kingin haqurin suka shiga bata suna qara tirata akan karta kyaleshi wlh, ta banbance mashi tsakanin aya da tsakuwa Itadai kawai jinsu take saidai bata tanka masu ba sai kukanta data cigaba dayi Saida suka biya ta wani mall daya ta fita tasiyo after dress sannan suka dauki hanyar gida Koda suka isa budemasu gate akayi, ganin sune yasa hantar cikin bala kadawa don beyi tynanin ganin ta ba yanzu don tace dai da asr zaizo daukarta, To ko takirashi be saniba ne? Saurin bin bayan Motar yayi don karya qara laifi Rukky ce tafara fitowa hakan yasa ta sallameshi akan yatafi kawai babu komai Saida tazura after din acikin Motar sannan ta fito Bata qara kallonsu ba ta wuce ba gode bare nagode ta shigewarta ciki wanda zata tashi sama Ta6e baki sukayi suma suka koma cikin Motar nurr ta tada suka fice Sai anan suka samu damar amayar da dariyar dake cinsu tundazu, aikau sukaitayi kamar sabbin kamu. Tafiya yake cikin nutsuwa hannayenshi riqeda littatafai, komai nashi cikin sanyi yakeyinshi saidai akwai karsashi Idan ba sani kayi ba saikayi tunanin tafiyar qasaita yakeyi nan kau haka yake Tafiya naturally Wata mota tazo dagudu taja burki agabanshi wanda hakan yasashi dakatawa yana jan baya Sauke glass din Motar akayi wata kyakyawar budurwa ta bayyana "barka!" tafada tana daga mashi hannu fuskarta dauke da Murmushi Shima murmushin yasaki yana rungume littatafan a qirjinshi yace "barka dai ramla" "ina zakane?" Dan Wara idanu yayi sannan yace "gida" agajarce "ok shigo mutafi" tafada tana budemashi kofa Kallon inda ta bude yayi sannan ya girgiza kai yana Murmushi Dan hade rai tayi tace "meye hakan? Bazaka shigoba kake nufi?" Girgiza kai yayi yace "A'a ngd yanzu zan samu abin hawa" "nawa abin sauka ne halan?" tafada still bata saki fuska ba Murmushin nan mai qara qawata qawattaciyar fuskarshi yayi yace "A'a ina nufin adaidita" "itama Wannan tana daidaitawa ai, wai deen meyasa kake min haka? Bafa sayar dakai zanyi ba" tafada cikin sigar tsokana Qara fadada murmushin shi yayi yace "ai bakiyi kalarsu ma ba" "To kagani? Shigo mutafi kasa na tsaya kan hanya ko kaka ta hanaka shiga Motar mutane ne?" tafada cikin sigar tsokana tana Dariya Dagowa yayi ya watsa mata hararar wasa yana dan turo baki sannan ka shiga tareda maido kofar ya rufe "ato ai nasan halinka ne, komai kaka tace, kaka's boy" tafada cikin Dariya tana jan Motar Bece mata komaiba sai murmushin daya sakeyi don dama shi murmushin shi yafi maganarshi yawa dukda wani sa'in idan yafara magana sai kasamashi full stop don besan ya taqaita bayani ba, taqarqarewa yake tsakaninshi da Allah yayi qoqarin fahimtar dakai "ina ne unguwar tamu?" tafada tana dan satar kallonshi Juyowa yayi ya kalleta yace "unguwarku kuma? Ni tayaya za'ayi insani?" yafada yana dan Wara eyes Lumshe idanu tayi ta bude acikin nashi, tana bala'in son innocent look dinshi "To unguwarku nake nufi" tafada tana maida hankalinta kan kwalta Daga gira daya yayi alamun aiyo? Sannan yace "ke ina kika nufa?" Juyowa tayi tadan saci kallonshi tace "ina na nufa kuma? Kaike jana koni ke janka? Abeg mallam ina zan kaika don insan ko nawa zan chaza" Kallonta yayi a mammakince yace "dama kudi zaki amsa?" Dariya tafashe daita har tana dukan sterring tace "sannu dan son banza, nufinka kyauta zankaika? Ca6! Ai gwamnati ta hana aikin banza" Murmushi shima yayi kawai bece komaiba "inane?" tasake tambaya "kofar kwaya wajen A.T.C" ya bata amsa "wow hanyarmu daya Ni kofar saurii nike wajajen gidan sarki" ta amsa tana shan kwana Bece komaiba sai Murmushin dayayi, satar kallonshi tayi itama tana murmushin tana ayyana da Allah zai mallaka mata deen da yagama mata komai, komai nashi burgeta yake. Sanyi shi, muryarshi, murmushin shi, innocence dinshi, kai komai ma Motar ce ta dauki shiru na wani lokaci kafin tayi breaking silent din da "gaskiya fa dazu ka bada show, abinda kayi ya farantawa kowa" Juyowa yayi ya kalleta itama ta juyo ta kalleshi tana Murmushi tareda daga mashi gira daya Murmushi yayi shima sannan ya dauke kai cikin zuciyarshi yana mammakin yadda kowa kejin dadin abinda yafaru, dama haka kowa ya tsaneta? Sai jiyayi tabashi tausayi "gwara da ka jefar da hegiya ta6o, ai ta raina uban kowa, ba students ba ba lecturers ba, kamin daidai wlh" Shikau da be gajuya da kare Kanshi yace "O'O! Nifa ba jefata nayiba" yafada cikin Jin haushin yadda kowa ke tuhumarshi akan fadawarta ta6on, mutanen dasuka tareshi da Wannan maganar yau basuda iyaka don har abin yafara isarshi Ganin kamar ranshi ya 6aci yasata cewa "O'O! Nifa bacewa nayi kayi laifi ba ai hskanma dakayi daidai ne" itama tafada cikin salon maganarshi "ba daidai bane, Ni ban jefata ba, itace tayimin tsawa shine na saketa Batareda na sani ba saboda na tsorata kuma wanda ya tsorata adrenaline hormones dinshi ke hawa yayi abu cikin fitar hayyaci ko abinda ya girmi hankali shiyasa nima bansan na saketa ba" yafada cikin son kare kanshi, yagaji da yadda suke fassara abin, shi harga Allah bakin gaskiyarshi yake fadi don a duniyar nan ya tsani tsawa fiyeda yadda kuke zato don da anyimashi firgicewa yake ya rude "To ai shikenan tunda ba da gangan kayi ba, bakada laifi ai, Allah ya tsare gaba" tafada ganin fuskarshi ta nuna alamun rashin Jin dadi Da amin ya amsa ahankali daga nan kuma babu wanda yaqara cewa komai Cikin dan qanqanin lokaci suka isa unguwar tasu Daidai makarantar A.T.C din ya sauka, yana shirin fiddo kudin taja motarta tafece tabarshi sagale da baki Girgiza kai yayi yana wani slight Murmushi sannan yanufi wani mai saida yalo abakin titi ya sayi na hamsin sai agwalumar hamsin sanin kaka na sonta sosai ya bada kudin ya amsa bayan ansaka a leda sannan yayi hanyar gida cikeda doqin ganin kaka... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:31 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *007* Saboda 6acin rai ko knocking batayi ba bare ayi batun sallama ta murda handle din ta tura qofar tashiga Bata wani lura da mutum falo din ba tanufi stairs "ke!" maganar datasata Tsayawa cak kenan daga yunqurin hawan stairs din datayi Juyowa tayi tana kallon mummy dake bisa daya daga cikin kujerun falon, remote a hannunta Ajiyar zuciya ta sauke cikin ranta tana addu'ar Allah yasa karta qaramata wani zafin "mummy? Barka da gida" tafada still tana inda take Bata amsa gaisuwarta ba sai cewa tayi "ke yaushe zakiyi hankali zainab? Ki wani fadoma mutum daki ba knocking bare sallama? Which type of manner is this?" Zuciyarta taqara dagulewa hakan yasa tafara hawaye kamar an bude fanfo Sakin baki mummy tayi tana kallonta ganin tama zame qasa ta hada kai da gwiwa tana shesheka Tafa hannu mummy tashiga yi sannan ta riqe ha6a "zainab lfy qalau kuwa? Abin naki har yakai daga magana sai kuka?" Bata amsa mata ba kuma bata dagoba sai sheshekar data qarawa volume "wai badake nakeba!" inji mummy atsawace har saida zee ta zabura Fashewa da kuka taqarayi ta miqe tahaye sama dagudu cikin kuka Binta da kallo mummy tayi harta haye sannan ta girgiza kai tanama diyar tata fatan shiriya Koda tashiga dakin gado tanufa direct tafada akai tana cigaba da kukanta Jitake komai na duniyarnan beyimata dadi, Gani take babu mai sonta a duniyarnan, kowa burinshi ya cuzguna mata idan ka cire daddy mai son farincikinta Saida tayi mai isarta sannan ta tashi ta cire kayan jikinta cikeda kyankyami ta jefa a basket sannan tafada toilet ta sakarma kanta shower. *** Da sallama yashiga cikin soron gidansu, kasancewar akwai wani dan soro(zaure) saikabi taciki sannan kashiga ainahin cikin gidan Gida ne mai dauke da dakuna biyu sai kitchen dake daga bangaren dama sai kewaye dake daga can qarshen gidan sai tsakar gida mai dan yalwa, gidan dai kallo daya zakamashi kasan na masu rufin asiri ne Qara wata sallamar yayi bayan ya shigo cikin tsakar gidan don da alama ba'aji na farkon ba, kodayake ya za'ayi aji bayan yana magana ne kamar da Kanshi yake? Ko kadan be iya daga murya ba gashi muryar tanada taushi ba irin husky voice dinnan bane na maza Jin haryanzu shiru ba'a amsa ba yasashi nufar dan kitchen dinsu ganin hayaqi na fitowa daga ciki da alamu girki ake ciki A bakin kofa ya tsaya yana kallon wata tsohuwa dake duqe gaban murhu tana hura wutar da iskar bakinta don wutar tamutu sai uban hayaqin daya turnuke kitchen din 6ata fuska yayi yace "O'O!" Sai alokacin tsohuwar tasan da tsayuwarshi a wajen "A'a Kamal? Ashe ka dawo?" inji dattijuwar tana miqewa tsaye baki washe "O'O! Kaka ba nace kibar hura wuta da baki ba?" yafada yana 6ata fuska Dariya tayi tace "To Kamal taqi huruwa, ya zanyi?" Cikin tura baki yazo yawuce ta ya nufi murhun wutar ya ajiye littatafan shi gefe wanda yayi Daidai da daukesu da kakar tayi, ya dauki makwashin shara(parker) ya shiga fifita wutar, saida shima tabashi wahala sannan takama sai a sannan yatashi yabiyo kakar wanda tuni ta fita ya tarda tana ajiye mashi ruwan sanyi data debo daga tulu acikin wani kofin silba akan tabarmar data shimfida mashi Qarasowa yayi ya zauna still bakinshi a tunzure Kaka itama zama tayi kusadashi tasa hannu ta shafa tulin sumar Kanshi tana Murmushi sannan tace "waya ta6amin kyakyawa na?" Sake kumbura fuska yayi yace "O'O! Nidai A'a" Dariya tayi sannan tace "haba kyakyawa na? Idan kana fushi rage kyau kakeyi, ko kanaso ka koma mummuna kamar ni?" Saurin kallonta yayi sannan yasake 6ata fuska yace "O'O! Allah kinada kyau" Dariya maganar shi tabata tashiga yi tana cewa "A'a wlh, kaima kasani banida wani kyau, bakaga ni baqa bace?" Zamewa yayi ya dora Kanshi bisa cinyarta yana jujjuya kai bisa cinyarta cikin shagwaba wanda tayi bala'in yimashi kyau Itakau Dariya take mashi tana bashi hqr inda kamar qara tunzurashi take don sai qara shagwa6e mata yake "kai ka tashi kaji, yau abinda kafiso nayi maka" tafada tana Dariya Saurin miqewa zaune yayi yana dan Wara oily eyes dinshi "dagaske kaka?" ya tambaya cikin doqi "bari kagani" tafada tana yunqurawa ta miqe tawuce daya daga cikin dakunan gidan, can kuma tafito riqeda kwano mai murfi tareda plate din roba tazo gabanshi ta dire Saurin jawowa gabanshi yayi ya bude Lumshe idanu yayi cikin jindadi ya bude akan alalar dake ta tururi tayi jajur alamun taji taruggu kamar yadda yake sonta. Washe baki yayi wanda yaba jerrarun fararen haqoranshi damar fitowa yana nuna alamun jingina ga kaka Tallabe mashi keya kaka tayi tana cewa "ja'iri kawai, meye anan?" tafada tana daukar ledar gabanshi Be bata amsa ba sai 6are alalar dayake yi daga cikin leda Budewa tayi tana leqa ciki, Murmushi tayi tana qara Jin soyayyar jikan nata acikin ranta Tashi tayi taje ta daurayosu tadawo kusada Deen daya fara aika alalar shi Haka suka zauna sunaci suna fira cikeda nishadi da annushuwa, kallo daya zakamasu ka hango tsantsar shaquwar dake tsakaninsu Sai a lokacin nasamu damar qarewa kaka kallo Baqace kamar dai yadda tafada, don bazaka ida tantance baqa bace sai idan kaga sun jera da Deen da fatarshi ke tass irin wanda ake cewa saika wanke hannu kafin ka ta6a Batada muni hakama Batada kyau, kawai dai tanada dai tsaka tsaki wataqila harda tsufan datayi yasa baza'a iya tantancewa ba Kaka a qiyasce takai shekaru sittin da wani abu amma tanada qarfinta don tanayin komai datakeso da kanta, haka zalika akwai zuciyar nema don kullum sai tayi koko da qosai na siyarwa dasafe Da Wannan sana'ar take daukema kanta da dan jikanta nauyi dukda shima ba azaune yake ba, duk lokacin da babu school ko kuma beda lecture yana zuwa wajen wani carpentary shop dake qasan layinsu inda ake hada kayan furnitures Kama daga kujeru zuwa gadaje na amare. Ko kadan babu wata Kama tsakanin Deen da kaka don idan bawai sani kayi ba sai kayi mashi daukar balarabe Yana da kyau, irin kyawun nan mai tafiya da zuciya, komai nashi Daidai kamar shi ya hallici Kanshi, yanada cikar zati da qirar mazantaka don a kallon farko sai kayi tunanin wani jan wuya ne ko daya daga cikin ire iren jaruman nan na littatafan yaqi saidai a zahiri ba haka bane don wani irin mutum ne mai sanyin hali da mu'amala Beda hayaniya ko kadan, komai nashi yana yinshi ne asanyaye, ma'abocin Murmushi, gwanin ban Dariya uwa uba he's so innocent, beda matsala ko kadan. Ataqaice dai Deen is a cool handsome guy da kowacce mace ke muradin samu a matsayin abokin rayuwa na har abada Kaka... kaka ce komai na Deen don ko yanzu kuka fara haduwa dashi inhar zaka zauna na 10mins dashi saika fahimci kaka nada mutuqar muhinmmanci agareshi, beda wanda zai maye mashi gurbin kaka yayinda itakuma kaka ta maye mashi gurbin kowa. Uwa, uba, aboki duk kaka ce. Yana qaunarta fiyeda tunanin mai karatu hakan ma kaka bata da kowa bayan shi kuma batada wanda yafiyemata shi, Ataqaice dai kaka ce duniyar Deen itama shine duniyar ta Koda yagama harta sauke ruwan data dora a murhu ta sirka mashi takaimashi a bayi. Saida ya kauda kwanikan sannan yashiga dayan dakin da nake kyautata zaton nashi ne ya rage kayan jikinshi yafito daga shi sai vest da nicker Wow! Gaskiya Deen ya hadu takoina, ashe dazu kallon tsoro nayimashi? Sosai mazantakarshi taqara fitowa acikin Wannan shigar, ata cikin vest din kana iya hango broad kirjinshi da flat tommy dinshi mai dauke da packs Deen irin mutanen nanne masu gargasa wato masu gashi ajiki, hatta hannayenshi da kaffafu gashi ne kwanttace qawace dasu. Zura slippers yayi ya dauki kwandon wanka yawuce makewayin dake can daga qarshen gidan Makewayin ba rufi asama irin buddaden nan ne, shiga yayi bayan yayi addu'ar shiga toilet da kaka ta koyamashi ya rufo qofar. Kaka kau gyara inda sukaci abincin tayi sannan ta zubo ruwa abuta tayi alwallar sallar asr wanda aketa kira, koda tagama saita qara zuba ruwa aciki ta ajiye tashigewarta dakinta Kaka bata jima da shigewa ba yafito daga bayin riqeda bokitin qarfen wanka da kwandon soson sai qanqame jiki yake, saurin ajiyewa yayi yanufi dakinshi da sauri. Ba'ayi minti 3 ba yasake fitowa Sanye da jallabiya baqa, yanufi ruwan da kaka ta ajiye ya tsuggunna yashiga daura alwalla. Tashi yayi bayan yagama yaqara komawa dakinshi befi seconds goma ba yafito Kanshi Sanye da hular tashi da kwakwa fara sai counter dayake qoqarin sanyama yatsarshi Kaka ce tafito Sanye da hijabi ta kalleshi "kafayi sauri karka rasa sallar gashi can an kabbara" tafada tana miqamashi kudi Da to ya amsa sannan ya amshi kudin hannunta yafice bayan yayi mata saiya dawo, da addu'ar dawowa lfy tabishi sannan takoma daki itama Massalacin beda nisa da gidan su, koda ya isa har anyi ruqu'i hakan besashi zuwa aguje don karya rasa raka'arba, shiga yayi ya Daidaita sahu da wani sannan yatada kabbara lokacin har sun dago, haka yabisu har suka idar da sallar shikuma ya tashi ya kawo daya rasa Koda yagama komawa yayi ya zauna yana danna counter din hannunshi, saida yaqara mintuna kusan talatin ahaka sannan yayi daily du'a dinshi yashafa. Saida ya gaggaisa da yan tsirarun da suke cikin Massalacin sannan yafito, nan ma wasu ya iske waje suma saida ya gaida nasama dashi ta hanyar russunawa Daidai shi kuma ta hanyar musabaha, har rige rigen amsamshi dattijen keyi kowa na binshi da kallon sha'awa suma tsararrakinshi har rige rigen bashi hannu suke don su gaisa, saida suka gama gaisawa yajuya yanufi hanyar da zata sadashi da kasuwa don yiwa kaka siyayyar geron kokon jibi da waken qosan gobe idan Allah yakaisu A bangaren zee kau tunda tashige daki bata qara saukowa ba, ko abinci bata nemaba, dama can batada yawan ci sai gashi abin ya hade da rannan she's in a bad mood hakan yasata loosing apettite dinta taji bata marmarin cin komai. Zaune take kan gado jingine da kan gadon tana danne dannen waya saidai kallo daya zakamata kasan she's moody Kwankwasa kofar da'akayi yasata dan dakatawa daga abinda takeyi ta kalli kofar Batareda tace komaiba Sake Kwankwasa kofar akayi hakan yasata dan yamutsa fuska kafin tace "waye?" Ba'a amsa ba sai turo kofar da akayi aka shigo da sallama Ganin mummy ce yasata sakin fuskarta data daure tamm tana jiran ganin wanene Qarasowa mummy tayi fuska ba yabo ba fallasa ta zauna gefen gado don zainab ta gyara zama ta sauko kaffafuwanta qasa "sannu mummy" tafada kanta qasa tana jujjuya wayar hannunta cikin rashin sabo don kwata2 bata sakewa daita yadda yakamata 'ya ta sake da uwa "yauwa, kinyi sallah ne?" inji mummy tana kallonta "eh nayi" ta amsa mata "abinci fa.. Kinci?" "A'a mummy, banajin yunwa?" ta amsa tana dan yamutsa fuska "meyasa?" "hakanan, banada apettite ne" Ido mummy takuramata na wani lokaci wanda hakan yasa zainab Jinta atakure "meke damunki?" inji mummy Kallonta zee tayi sannan ta Girgiza kai tace "babu komai mummy" "meyasa kika dawo dawuri bayan kincemin 2:00pm zaki dawo?" Rolling idanu tayi afakaice acikin zuciyarta tana cewa 'da mummy yar jaridace da duk wanda ta tisa gaba da tambaya ya bani' "mummy banajin dadine" ta amsa asanyaye "meya sameki?" inji mummy tana kafeta da idanu "fever da headache" tafada tana kwa6e fuska Kai hannu mummy tayi ta ta6a wuyanta saidai babu zafi Janye hannun tayi ta tashi tana cewa "tashi mutafi kici abinci kisha magani" Zata musa taga mummy ta tamke fuska hakan yasata tashi badon tasoba tabi bayan mummy tana turo baki Tisata gaba mummy tayi saida taci abinci tasha magani sannan ta kyaleta takoma saman. Duk motsin da zatayi saita tuna abinda yafaru dazu kuma duk sadda ta tuna saita tsinci kanta cikin 6acin rai, yanzu shikenan mutuncinta yagama zubewa a idon wadancan kucakan yan school dinsu, tasan yau itace topic of discussion a school din, shikenan sunga wallenta. Haka taita juyi a daren ranar ta rasa abinda kemata dadi gashi barcin ma yaqi zuwa, babu abinda kemata gizo sai fuskar Wannan gayen, haduwarsu tabiyu kenan duk bata dadi ba, lallai Wannan karon saita mashi rashin mutuncin da bata ta6a yiwa wani mahaluki ba, saita tozartashi fiyeda yadda yayi mata, da wannan alwashin barci barawo ya saceta *DEEN* Suna zaune abisa tabarma suna tsintar waken da Deen yasiyo na qosan gobe yana bata labarin abinda yafaru school yau kamar yadda yasaba kullum sai yabata lbrin abinda yafaru dashi idan yafita, idan shawara zata bashi saita bashi, idan yayi ba daidai ba saitayimashi gyara idan kuma yayi daidai saita yabamashi Saida yagama labarta mata komai yadda yafaru sannan ya dago ya kalleta ta hasken wutar nepan dake akwai yace "wai kaka laifina ne?" ya tambaya yana turo baki Murmushi kaka tayi sannan tace "eh to, gaskiya tafika laifi saboda ita tayi maka tsawa harka saketa, tayiwu kuma batasan bakason tsawaba amma dukda hakan be kamata tayimaba daga taimako" Dadi yaji sosai cikin ranshi Jin ta goyi bayanshi hakan yasashi cewa "kuma fa kaka itace bata kallon gabanta, itace taita biyowa hanyata bayan sai kaucemata nake amma saida ta bagajeni" yaqarashe yana turo pink lips dinshi "Gaskiya bata kyautaba, kamata yayi ace tana kallon gabanta idan tana tafiya don koba yau ba tana iya zuwa ta fadawa wani abu dazai cutar daita kaga ina amfani?" Cafewa Deen da duk dadi yakamashi don kaka tanuna bashi da laifi yayi dacewa "kuma kaka kodayaushe a fusace take, itace fa Wannan dana cemiki tamin tsawa dana cire gyallen ta a bracelet dina, wancan karon ma haka tamin tsawa kuma na gayamata babu kyau zai cutar daita amma kuma taqara kuma fa na gayamata idan tana fushi tayi inhaling tasbih tayi exhaling tahlil amma kinga batayi ba... " Murmushi kaka tayi tana qara Jin qaunar shi acikin zuciyarta, he's so innocent, maganarshi ma irin ta yarace, idan mutum yaji maganarshi sai yayi tunanin irin wadanda basuda lafiyar kwakwalwa ne amma rass yake kawai halitarshi ce hakan, haka Allah yayishi shiyasa yake bata tausayi don tasan ba qaramin qalubale yake fuskanta awajen mutanen waje ba don suna iya cutar dashi cikin sauqi don Deen mutum ne da duk wanda ya washe mashi baki to masoyinshi ne, yanada sanyi fiyeda yadda akeso kuma tasan hakan ba qaramin raini zai jamashi awurin jama'a ba musanmman a school, qila ma shiyasa yarinyar tayimashi tsawa, wama yasan adadin masu yimashi tsawan? Wannan tunanin yakawo kwalla a idanunta tayi hanzarin maidasu don tasan daya gansu to an banu don barci na iya gagararshi tasan halinshi sarai, maida hankalinta tayi gareshi don tundazu zuba yake taji yana cewa "... Kuma idan adrenaline hormones din mutum yaqara gudu yana iya yin abu Batareda yasani ba ko yayi abinda ya girmi tunaninshi amma taqi ganewa" yafada yana 6ata fuska Murmushi kaka tayi tace "ai wasu dama basa ganewa, yanzu dai gobe idan Allah yakaimu idan kaje kuka hade kabata haquri kakuma yimata bayyanin kai bada gangan kayiba, kakuma gayamata bakason tsawa, Tsorata kakeyi saigaka ta fahimceka itama ta baka haquri wataqila batasan bakason tsawa bane" Kada kai yayi cikin gamsuwa yana cewa "insha Allah kaka" Haka sukaita firarsu har suka gama sukayi tatar qullun kokon gobe duk suka kai suka adana suka daura alwalla suka yiwa juna saida safe kaka na jaddada mashi yayi addua idan zai kwanta Kowannensu saida yayi shafa'i da wutri sannan ya kwanta bayan sunyi addu'ar barci *WASHEGARI* Tun bayan sallar asuba suka fito suka fara kiciniyar daura koko da qosai Deen ne ke hura wuta yayunda kaka ke surfa waken kosai Saida wutar takama sosai sannan ya dauko qatuwar tukunyar dasuke amfani daita wajen yin kokon ya dauraye ya dora yazuba ruwa aciki Itakuma kaka ta wanke waken ta cire duka hancin yayi tass, tasa a bokiti tasa watsa taruggu da albasa aciki taba Deen dake jiranta don yakai markade Kafin yadawo harta tsiyaya ruwan qullun ta daddama acikin bokitai plastic ta rurrufe sannan tashiga hura wutar qosai Wutar bata ida Kamawa ba yadawo, shi ya amshi hura wutar Itakuma tashiga hada qullun qosan. Saida wutar takama sannan ya dauko kaskon tuyar qosan ya dora ya bulbula mai aciki ya tsugguna tsakankanin wutan biyu yana gyara duk wadda ta ije Saida kaka tagama buga qullun qosan ya bugu sosai sannan ta dauki kujera yar tsugguno ta zauna gaban murhun qosai lokacin har man yayi zafi tashiga debar kullun da cokali tana sakawa a man Ruwan kokon na tafasa Deen ya maido bokitan plastic din kusa2 yasake motsasu da miciya wanda suke amfani daita sannan yashiga sheqa kokon. Izuwa yanzu har anfara shigowa saye, saida yagama ya maida wani ruwan sannan yazo yafara sallamar masu saye yana zubamasu kokon da qosan Tun masu sayen suna yan tsiraru har sukayi yawa sosai don da an tsame qosai zakaji yaran nata kiran sunanshi, "Yaya Deen na kaza! Yaya Deen ni za'aba! Yaya Deen nine kan layi!" Shidai saidai yaita Murmushi yana zubamasu kuma be runton layi, yana sane da wanda yariga wani Ahaka suka saida duka, lokacin har tara takusa, tare suka tsabtacce gidan yashiga wanka agurguje don yanada lecture 10:00am, atsaitsaye yayi break da kokon da suke diba su ajiye Tun tukunyar farko da qosai sannan yayi mata sallama yafice kaka na rakashi da addu'ar dawowa lfy. Bangaren zee kau qin zuwa school din tayi yau don batasan yadda zatayi facing school din yau ba bayan humuilation din jiya, tasan maidata zasuyi laughing stock susata jin ta muzanta hakan yasata fakewa da batajin dadi taqi zuwa. Sosai daddy yadamu da rashin lafiyar qaryanta don ranar yafe zuwa company yayi yatsaya ya kula da shalelenshi, itadai mummy zama yar kallo tayi don yabake komai shi keyimata. A school kau mutane dadama sunzo yau ne don su tunzura *mud queen* kamar yadda suka samata suna Wasu ma basuda lecture Aranar kawai abinda yakawosu kenan saigashi tabasu gula taqi zuwa makarantar hakan yasa suka fara cewa kunya ya hanata zuwa. Deen shima dayaje da niyyar bata hqr kamar yadda kaka tace mashi shima yasamu labarin rashin zuwanta, be damu da hakan ba ya cigaba da harkokin gabanshi A bangaren mr ibrahim kau shima labarin jiya ya riskeshi yadda yaji labarin yasashi sanin abin yafarune bayan fitowarta daga office dinshi, guntun Murmushi yayi acikin zuciyarshi yana cewa somin ta6i kenan, batama ga komai ba yayinda yashiga shiryama yadda zai 6ullomata ya nunamata kowa yaci tuwo dashi miya yasha. Suma su Alex sun so ganinta yau amma saiji sukayi bata xoba hakan be damesu ba saima cigaba da shiryamata tarkon dasukayi wanda suke fatan ya d'anu kuma tafada tazama prey dinsu (whoo zee baby mai farinjini 😆) Wasa2 duk kingin ranakun satin an baza idanu an baza kunnuwa babu zee babu alamunta, nanfa akayi concluding cewa taji tsorone wataqila ma bazata qara zuwa school din ba, kunya yasa bazata iya facing kowa ba. Sosai Alex ya tada hankalinshi dajin Wannan labarin don sosai ya kwallafa ranshi akanta, master ne ya kwantar masu da hankali cewa ko a qarqashin gadon uwarta ne ta 6uya saisun fiddota sunyi abinda sukayi niyya daita babu mahalukin daya isa ya hanasu. Bangaren zee kau tana gida duk ranakunnan ta fake da ciwon qarya taqi zuwa saidai duk abubbuwan dake faruwa a school din da magangganun da ake akanta tana sane dasu ta hanyar qawayenta Wato su sumee. Sosai ranta ya6aci, takuma sake daukar alwashin rama abinda gayen nan yayi mata gashi yanzu da mutuncinta da komai ya zubarmata dashi yaja school din ya gagareta zuwa. Ranar asabar su sumee sukazo har gidansu zee dubiyar qarya Zuwansu na uku kenan gidan, koda suka iso babu yabo ba fallasa mummy ta tarbesu don ita haryanzu basu kwanta mata ba dukda idan suna gabanta komawa suke salihan gaske amma kwata kwata basuyi mataba Zee ta sauko qasa ta tarbesu tawuce dasu dakinta daya jiqu da kayan more rayuwa Duk sadda zasuzo gidan nan sai hassadarta cikin ransu taqara farashi don ba qarya zee tayi dace, tanada komai da mutum zai buqata arayuwarnan shiyasa wani sa'in basa blaming dinta idan tana wani abin don yes ta isa tayi ne Haka suka baje dakin suka shiga koromata bayyanan abubbuwan daya faru a school da batazo ba harda qarin gishiri da maggi don abin yabada taste. Sosai abin yaqara bata haushi nan ta dauki alwashin saita basu mammaki, zata gwadamasu cewa kunya gaba tabata ba bayaba. Haka taita banbami suna tirata yayinda naciki ke cikinsu, basu sukabar gidan ba sai can goshin magrib, mummy ta hadasu da turraruka masu kyau da tsada ita kuma zee ta hadasu da kayan kwalama dake tile a dakinta suka jide suka tafi akan sai ran monday idan sun hadu a school. Bayan tafiyarsu zainab taita saqa da warwara akan yadda zata 6ullowa yan school din, sotake ta gwadamasu cewa tawuce duk inda suke tunaninta Haka ta qarar da weekend dinta wurin tsara yadda zata 6illowa kowanne dan air dayayi qoqarin kawomata wargi a school din. *MONDAY*..... ✍️ NO EDITING🙏🏻 ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:31 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN* *008* *MONDAY* Zaune suke suna labarin duniya kamar yadda suka saba, saidai bala nayi yana duba agogon hannunshi jefi2, ganin abin yayi yawa yasa security din cewa "yadai mallam bala? Naga sai wani duba agogo kake tundazu" Tsaki bala yaja yace "kaidai bari, wlh tundazu madam takirani akan infito tunda wuri zamu fita amma kalla yanzu kusan awata biyu da zuwa amma babu ita ba alamunta" ya qarashe maganar yana jan tsaki Dan guntun Murmushi security yayi yace "indai madam ce kaga fin haka, yanzu haka idan ance bata tashi daga barci ba ba'a gardama, kaidai kawai Allah ya cigaba da bamu haqurin zama da wadannan mutanen" Tsaki bala yasake ja yace "amin ai ina ganin rayuwa, wlh da badon ina samu sosai da sana'arnan ba wlh da tuni nabar dan iskan aikin, wlh nikadai nasan wulaqancin danake fuskanta a aikinnan" "Sai muyita haquri ai tunda Allah yariga ya qaddarta tanan zamu samu abinci kuma inda suke burgeni akwai fita haqqin ma'aikata don wlh nasan kafin kasamu inda ake biyan ma'aikata kamar mu sai kaci kwakwa, ga ci da sha mai kyau, kawai dai matsalar itace madam don Hajiya gaskiya babu ruwanta shima Alhaji sai an ta6amashi madam yake rashin mutunci" "kumafa da gaskiyarka don wlh suna biyanmu fiyeda yadda yakamata, shiyasa na liqe na nace nake shanye duk wulaqancin da akemin amma wlh wani sa'in yadda kasan mammaketa haka nakeji" inji bala Dariya sukasa security yace "ai ina ganin qoqarinka wani sa'in har tausayi kake bani idan naga ka rude kana rawar kafa wajen yimata abu" Dariya suka sake yi, bala yace "ba dole ba? Ai nikadai nasan tsiwarta da rashin mutuncinta, duk wanda yasani saidai yabiyo bayana" Kafin su sake wata maganar suka hango fitowarta, hakan yasa bala saurin miqewa yana cewa "To lambata ta fito" Dariya security yayi yace "aikaudai lambarka ta fito" Be qara sauraronshi ba yawuce wurin Motar dazai kaita da ita ya bude mata kofar baya tun kafin ma ta qaraso. Tafe take cikin tafiyar ta ta yanga tana taku daddaya Sanye take cikin baqar after mai igiyoyi a gaba duk ta daddauresu, kaffafuwanta Sanye da black hills masu tsinin gaske, kanta yafe da siririn veil baqi shima wanda tayi simple yafi dashi Sai black shade data toshe idanunta dashi, ta saqalo black handbag mai masiffafiyar kyau a hannu dayan kuma riqe da faskekiyar wayarta. Fadin haduwar datayi acikin Wannan shigar 6ata baki ne don baqi ne ya hadu da farar fata hakan yasata fitowa acikin shigar sosai. Kamar kullum, yau ma heavy makeup ne a fuskarta saidai glass din idanunta ya rufe kusan rabin fuskar baka hangen komai sai jan qaramin bakinta mai daukeda qananun soft lips wadanda suka qara jaa saboda janbakin dasuka sha. Zee is the real definition of beauty, tanada duk abinda mace ke muradin mallaka a bangaren hallita. Zee farace irin tass dinnan wanda harda gudunmawar hutu na irinna masu kudi wajen sa fatar yin tass da sheki Tanada round shaped face mai daukeda dara daran idanu dasuke farare tass sai dan madaidaicin hanci wanda yayi daidai da fuskarta. Bakinta yafi komai qanqanta a fuskarta wanda yake dauke da two little lips masu tafiya da mutane Bakinta da idanunta sunfi komai daukar hankali a fuskarta. A 6angaren structure kuma doguwace amma ba can ba Tanada diri mai tafiya da hankalin abokan hallitanmu Tanada madaidaicin boobs cikkaku kuma tsayayyu sai flat tommy dinta mai Kama da wanda ba'a zubama abinci wanda yaqara taimakawa wajen fiddo shape dinta sosai. Tanada hips sosai don yafi komai girma a jikinta. Daga wajen cikinta zuwa waist dinta a tsuke yake sai daga waist din zuwa cinyoyi daya bude yabada curve mai tada hankalin mai kallo. Tanada hips sosai wanda duk a jikinta yafi tafiya sa hankalin mutane, gashi ta iya sarrafashi yadda yakamata don idan tana tafiya ke dake mace saikin bita da kallo bare akaiga namiji. A taqaice dai Allah yayi mata baiwar kyau da diri da duk wata mace zatayi alfahari da samun irinshi. Koda ta qarasa ko kallon bala batayi ba bare ta amsa gaisuwarshi saima shigewa datayi cikin Motar a yangace tareda qamewa a bayan motar. Rufe kofar yayi yayi saurin zagayawa ya shige mazauninshi shima yarufe nashi kofar ya tada motar tareda janta Zuwa sukayi suka wuce security da tuni ya wangale musu gate suka fice daga gidan gabadaya. *UMYU* kasancewar safiya ce kuma safiyar ma ta monday hakan yasa dalibbai harma da mallaman school din kai kawo a harabar school din kowa na abinda yake gabanshi. Shigowa motarsu zee tayi cikin harabar school din. Babu wanda ya lura da ita don kowa harkar gabanshi yake kuma babu wanda yakawoma ranshi ita don tuni sunyi concluding tabar makarantar kunya bazai bari tazoba duba da duk kingin rannakun wancan week din batazo ba. "Bala... Kayi abinda zaijawo hankalin jama'a akanmu" tafada hankalinta na kan wayar hannunta datake daddanawa Satar kallonta yayi ta mirror kafin yace "angama madam" Kamar kau yadda ta buqata hakan yayi, da wani irin gudu mai tada qura ya qarasa parking space din wanda hakan yaja hankalin mafi akasarin mutanen dake harabar school din. Kowannensu dakatawa yayi da abinda yakeyi ya maido hankalinshi kacokam akan motar kowanne da tunanin dake mashi kai kawo a zuciya Murmushi tayi ganin duk taja ra'ayin mutane, hakan yasata ba bala umarnin yafita ya bude mata kofa Babu musu yafita acikin zuciyarshi yana nema mata shiriyar Allah Cire shade din fuskarta tayi tareda after dress din jikinta sannan ta ciro bubble gum ta jefa a baki. Tun fitowar bala mutane suka shiga tsantsar mammaki don sunganeshi sosai, shine drivern zee. Wow! Tagama 6oye 6oyen kenan? Tambayoyin da mutanen harabar sukayi kenan a zuciyoyinsu yayinda duk aka kafe motar da ido anason ganin fitowarta. Kamar kau tasan cike suke da doqin ganinta don saita ta mula tasha iska sannan ta zuro kafar dama mai dauke da hill mai shegen tsini sannan tabiyota abaya cikin wani irin slow motion Duk sakin baki sukayi suna kallonta dumpfounded Sanye take cikin royal blue t-shirt mai guntun hannu sai baqin straight skirt mai tsaga a baya wanda ya taimaka wajen bayyana fararan kaffafunta Agaban rigar daidai gefen saman boobs dinta na haggu akayi wani logo mai kyau da daukar ido mai daukeda zanen crown 👑, zagaye da logo din kuma aka rubuta *BORN TO RULE* A bayan rigar kuma aka rubuta *THE MUD QUEEN* Bude shade dinta tayi sannan ta qwamama fuska tana taunar chewing gum din bakinta ahankali sannan ta amshi handbag dinta daga hannun bala daya fitomata da ita ta sagala a hannu sannan tafara tafiya cikin takunta na sabon salo don Wannan salon yafi wanda tasaba zuwa dashi. Duk binta da kallo akayi baki sake ganin salon datazo dashi school din yau, babu wanda ya ta6a tunanin haka daga gareta don duk a tunaninsu bazata iya hada ido da kowaba don kunya amma saigashi ta shayar dasu ruwan mammaki ganin iskancinta ma gaba yaci ga sunan datayi printing a rigarta wanda yakamata su dinga amfani dashi wajen tsokanarta, alamun sunan yayi mata kuma bazai 6ata mata raiba. Babu wanda yayi yunqurin tankamata sai rakata da kallon dasukayi kowannensu dauke da yanayi mabanbanta. A class suka hade dasu rukky wadanda basu san ta iso bama. Wara idanu sukayi suna ganinta duk sukaje suka rungumeta cikeda murna inda suka zamo yan kallo ga mutanen class din. Nan suka fara tambayarta ya tabaro spain din? Kamar yadda suka tsara zasuyi ranar dasuka je gidansu Cikin shan qamshi take amsawa da alhamdullilah sun dawo Suma kuma gifts dinsu na can na jiransu. Shigowar lecturer class din yasa duk aka nutsu kowanne yanemi mazauni ya zauna aka shiga gabatar masu da darasin. Sai wajajen 10:30am suka fito daga lecture din, kai tsaye cafteria suka nufa inda duk inda suka gifta sai an dinga satar kallonsu musannman ma zee da labarin iskancin datazo dashi ya karade school din. Snacks kawai suka saya da drinks sannan suka wuce wajen usual mazauninsu dake bayan classes. "wow baby! Amma kinyi yaqa fa!" inji sumee Dan kalkada manyan idanunta tayi tace "haba?" Amasawa tayi da "na rantse, kinga kau yadda ake binki da eyes?" Murmushi kawai tayi batace komai ba sai sipping din drink din hannunta datayi "ba dole ba? Ai abinne yazomasu a bazata, basuyi expecting haka daga gareki ba, gaskiya Wannan salon yayi" inji Nurr ta mata jinjina👍🏻 "Hmm bar yan iska, ba dai taqamarsu iskanci ba? Zan gwadamasu na damesu na shanye a Wannan harkar, kadan ma suka gani, wlh ba'a isa a maidani laughing stock saidai na maida mutum wlh" ta qarashe tana crossing din kaffafu "aikaudai babe na, gashi yanzu duk cika bakin da iyayin sun kasa maki komai, dama duk rubace" inji deeya "To dama me suke iyawa? Nan gani nan bari wlh, duk wanda yaci tuwo damu miya yasha, kuma a sannu zamu koyawa duk mai kawomana wargi a harkarmu, mu bama shiga harkar wani haka zalika duk wanda yashiga harkarmu bazamu kyaleshi ba" inji rukky "wai waye gayen nan ne?" inji zee tana kallonsu "Hmm wama yasani? Nidai ban ta6a ganinshi ba sai ranar daya jefarmaki da gyale saikuma ranar da ya jefaki ta6o" inji deeya Tsaki taja don kalmar _ya jefaki ta6o_ din yabata haushi hakan yasata juyawa ga sauran tace "waye shi? Waye babanshi? Kuma meyake taqama dashi da har zai shiga gonata" tafada a gadarance "Gaskiya babu wanda yasan wayeshi acikinmu tunda muma ba saninshi mukayi ba amma fa da alamu dan manya ne idan akayi duba da yanayin gogewar fatarshi da mode of tafiyar shi sai inga Kamar dan manya ne" inji nurr "nikuma sai inga kamar ba kowa bane duba da yanayin dressing dinshi, yes yanada kyau da fata mai kyau amma hakan baya nufin dan manya ne don akwai qabilun dazakiga sunada kyau sosai da gogewar fata ba don arziqinsu ba sai don haka Allah ya hallicesu, gashi yana behaving somehow, ni sai inga kamar he's not normal" inji sumee "well, babu ruwana da normalness dinshi ko rashin normal dinshi, kamar yadda babu ruwana da arziqinsu da rashin shi, kawai abinda nasani shine yayi crossing limit dina kuma bazan barshi ba" tafada tana kalkada kafarta data dora kan dayar "Gaskiya ne, don kyaleshi kamar bude wata qaface ta raini agaremu, yakamata mu dauki mataki gaskiya" inji nurr "inane department dinshi?" inji zee "Banace ba amma ina yawan ganinshi abayan office din business admin. He's always lonely, is either ka ganshi yana karatu ko ka ganshi zaune shiru" inji deeya "kin tabbata?" inji zee "very sure" deeya tabata amsa "muje!" tafada tana miqewa tsaye. Duk miqewa sauran sukayi suma kowacce ta rataya jakkarta suka nufi inda deeya din tace Cikin sa'a kau suka hangoshi zaune a wajen shi kadai littafi a hannunshi yana dubawa. Sanye yake cikin farar shirt mai layi layin baqi sai baqin jeans trouser da baqaqen takalmi, sumar Kanshi a dan tuje as usual wanda hakan na faruwa ne ta dalilin yawan hargitsashi dayakeyi da yatsun hannunshi duk bayan lokaci lokaci Hankalinshi kacokam na kan littafin hannunshi yana nazari shiyasa bema lura da qarasowarsu wajenshi ba Fitt... Yaji an fizge littafin daga hannunshi hakan yasashi saurin dagowa don ganin waye Acikin manyan idanunta oily eyes dinshi suka sauka wanda hakan saida yasata Jin wani yarrr ajikinta Da daddaya yafara binsu da kallo kafin ya miqe tsaye yana cigaba da kallonsu Batareda yace komaiba "kai a tunaninka kana iya shiga gonarmu katafi scot free ne" inji nurr tana watsamashi harara Bece komaiba sai idanu daya kafamata wanda hakan yasata kauda nata saboda tsananin kaifinsu "kai kasan ko wacece Wannan agabanka kuwa?" inji sumee tana nuna zee da ke kallonshi still taqi magantuwa Maida kallonshi yayi akan zee din da sumee ta nuna still bece komaiba "To bari kaji, sunanta Zainab Farouq Dan faranshi, diya tilo ga shahararen mutumin nan Dan faranshi, duk fadin school dinnan babu mai arziqinsu, kowa shayinta yake a school dinnan shine zaka rasa abinda zatayi mata sai jefata a ta6o?" inji sumee tana Girgiza Dauke idonshi yayi daga kan zee ya kalli sumee yace "ni ban jefata ba, fadawa tayi" yafada cikin cool voice dinshi Sai a sannan zee ta motsa ta hanyar zaburomashi tace "ni na fada zakace?! Kawai hakanan zan fada cikin dirty ta6a saboda gani sabuwar kamu ko?!" ta qarasa a tsawace Saurin jada baya yayi yana dode kunnuwanshi yana cewa "O'O! Kinga kin fara kuma ko?" yafada yana yamutsa fuska "kakata tace in gayamaki banason tsawa kuma tace ai laifinki ne, da bakiyimin tsawaba da ban sakeki ba" yafada yana dan turo baki "ina ruwana da abinda kakar taka can tafada? Kuma tun farko waya kawoka hanyata da har ka bangajeni?!" tafada atsananin fysace, ga yarda ta shirya sotayi da sunzo tafara daukeshi da mari kamar yadda tasaba saidai tana zuwa taji takasa hakan, haka kawai wata zuciyar ke radamata fuskarshi ba'a yita don duka ba "O'O! Ni ban biyo hanyarki ba, kece kika fadomin a hanyata, nayi qoqarin kauce maki kika bangajeni cos you're too clumsy" Wara idanunta tayi tace "what? Ni kake cewa am clumsy?" Dan 6ata fuska yayi sannan yace "then why kika fadomin? Nayi qoqarin taimakonki kuma kiya yimin tsawa bayan na riga na gayamaki tsawa na Tsorata mutum kuma idan mutum ya tsorata adrenaline hormones dinshi..." "Adrenaline hormones din qaniya! Ina ruwana dashi! Kai kasan Wannan ni bansanshiba! Shin kasan ina iya sawa a kulle duka familynku?!" "harda kaka?" ya tambaya yana dan waro idanu "harda jika ma! Zan iya sawa a daure duka family dinku har igiya tayi rara kuma babu wanda ya isa ya amsheku" tafada tana nunashi da yatsa "ai nida kaka ce kawai babu sauran wasu" yafada Hankalinshi kwance Sosai abin yaqara tunzurata ganin yana son maidata wata 13 14 "kuma ma ai laifinki ne, daga taimako sai kiyimin tsawa? Kuma na fadamiki zai iya cutar dake, ko yasa muryarki tashake ko yajamiki sore throat" Rukky da tundazu keta faman danne dariyarta tace "mallam maimakon ka bata haquri har kanada bakin fada tana fada?" "inbata haquri?" ya tambaya yana maido kallonshi akan rukky din "Eh mana, ko bakasan tana iya sawa sojoji da yan sanda su kamaka ba?" tafada cikin sigar tsoratarwa Dan Wara idanu yayi yace "To ni menayi?" "na farko ka yagamata gyalle ka jefar, na biyu ka jefata a ta6o" Bata rai yayi yace "Ai gyalenta ya sarqaho min bracelet dina kuma nayi nayi incire yaqiya shiyasa naja" "To wayace kaja? Kasan tsadar gyallen kuwa, atleast sai kayi magana a ciremaka" Dan tsuke baki yayi yace "Ni bansan gyalenta neba ai, gani nayi yayi Kama da irin abin tatarmu" Dariyar dasuke qoqarin dannewa tundazu ya kufcemasu suka shiga yi banda zee data cika tayi famm "wai Wannan wane irin wukaqanci ne rukky zaki tsaya ki biyemashi kuna hauka?" tafada cikin 6acin rai sannan ta juya wajen Deen dake kallonta tace "you know what? Just know that you're doomed!" tana kaiwa nan tajuya zata wuce a fusace deeya tayi Saurin kamo hannunta sannan tajuya ga Deen dake kallonshi with his innocent face tace "kasan wani abu? Wannan dakake gani kawunta commander sojoji ne, baffanta kuma comissioner of police, yanzu haka zuwa zatayi ta kirasu azo a kamaka a tafi dakai can a kulle bazaka qara fitowa ba kuma bazaka qara ganin kaka ba" Bece komaiba but his look said it all don kallonsu yake cikin fargaba "idan aka tafi dakai bazaka qara dawowa ba, kaka bazata qara ganinka ba kaima bazaka qara ganinta ba and za'ayi maka horo sosai irinna sojoji" tafada threateningly Nan ma bece komaiba sai kallonsu dayake "kanason haka din?" Girgiza kai yayi Batareda yayi magana ba "then kayi abinda yakamata" tafada tana mashi nuni da zee naketa cika tana batsewa Kumbura fuska yayi sannan yace "Am sorry but kema nan gaba kibar yiwa mutane tsawa" Kallonshi tayi tana zaro mashi manyan idanunta tace "Sai nayi tsawan! Sai ka hanani idan kana iyawa!" tafada atsawace Fuskarshi still a kumbure yace "O'O! I don't like you!" "nima cemaka nayi I like you? Kuma ka kaddara nakira sojojin na gama" Su sumee me zasuyi banda Dariya "ba nayi apologising ba?" yafada yana rungume hura hanci "da kayi apologising sai kuma kabani sharadi? Harda wani I dont like you, ni gayamaka akayi I like you?" Kauda kai kawai yayi yana cigaba da kumburi Rukky dake Dariya sosai tace "kagani ko? Ka qara fusatata, she'll call the police" "but I apologised" yafada cikin kare Kanshi "yes and you insulted her after that" Wara idanu yayi yace "insult? Ni ban zageta ba, I just said I dont like her" "To ai kamar insult ne awajenta" "ok Am sorry, shikenan" yafada yana watsa hannaye "ba shikenan ba" inji Rukky "what again?" yafada cikin qosawa "zaka zama boy dinta" inji Rukky Atare zee da Deen suka waro idanu sukace "mene???" "yes! I mean zaka zama errand boy dinta".... ✍️ Wash! Gaskiya typing beyiba 🤕 idanuna har yaji yaji suke 🥺 Not edited 🙏🏻 Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:32 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *010* Ahaka Wannan satin yawucewa Deen cikin takurar zee, kodayaushe cikin takuramashi take Da sashi abubuwa musanmman aike Shidai Deen iyakarshi kumbure2 da fadin _I don't like her_ a zuciya A bangaren su rukky kau abin sai yazaman masu kamar comedy don kullum sai sunci Dariya saboda yadda Deen ke fusata zee, kullum da abinda zaiyi mata na quluwa gashi itakuma ba haquri nan da nan takeyin sama Saboda cin dariyar dasuke na dramar su yasa ko batayi niyyar kiranshi ba saisu matsa mata da tambayar akirashi? Har saitace akirashin, yawan takurawar tata yasa besamun lokacin ke6ewa yayi karatun shi kamar yadda yasaba don yadda kasan gadinshi suke dayazo ya zauna da niyyar karatu zasuzo kiranshi kuma babu yadda ya iya, hakan yake binsu ba don ranshi yasoba. Kamar kullum yau ma saida sukayi fada sannan yatafi siyomata abinda ta aikeshi, su sumee sai 6a66akar Dariya suke yayinda zee keta huci "Hhhh Deen mutumin mu, wlh dramar ku na mugun bani Dariya" inji nurr "Dole ai, wlh dama comedy kukeyi da kunyi kasuwa" inji sumee itama cikin Dariya "wlh kau, Wannan ko tom & jerry sun shafamaku lfy" inji deeya Tsaki zee taja tareda yin Kwafa sannan tace "hmm wlh dani yake zancen, bashi dan rainin sense ba?" "kema zee banga abin tada jijjiyoyin wuya anan ba, daga yace he dont like you shikenan? Sai kace wanda ya zaga?" inji nurr Qara zaburowa zee tayi a masifance tace "kar yayi liking dina mana, dama cewa nayi yayi liking dina? Wlh idan bebar cemin haka ba zan bashi mammaki, tom!" "ai zee Dole yace baya sonki don bayason tsawa ke kuma babu inda kikafi gwanancewa kamar yin tsawa" inji deeya "To idan ba tsawa ba me zanyi mashi, zabgegen mutum masha Allah kamar shi ba sense sai iya qule mutane" tafada tana jan tsaki "hhhh mudai yan kallo, iyaka ayi abin dariya muyi" inji sumee tana Dariya su nurr na tayata Tsaki taja sannan ta fuskanci deeya tace "wai ina rukky taje haka shiru?" "ohon mata, wai qawarta tabi ta amshi expo, kinsan fa gobe ake submiting din assignment din mutumin ki" inji deeya tana Dariya Tsaki zee taja tace "Duk tana aikin me ace har kamar yanzu batayi assignment din ba bayan tasan yace 20% ne na exam?" Ta6e baki nurr tayi tace "shiririta ko? Ni wlh mr ibrahim yabani mammaki, shida duk magiyar da mukayi mashi qin saurarenmu yayi saigashi rana tsaka ya chanza qudurinshi ya sassafto mana fiyeda yadda mukayi tsanmmani" "wlh nima abin yana dauremin kai, saidai fa ya sassafto be sassafto ba don Wannan assignment din yaci uban wanda yasaba bamu, ace questions yacika gaba da bayan fliscap? Nidai nayi iya yina na sallama sauran don Wannan ko a google danayi searching answers din duk rikitani sukayi Dole na tsintsinta nabar sauran" inji deeya Sumee tadan Wara idanu tace "cewa fa yayi idan ka duba google zai gane" Ta6e baki deeya tayi tace "ya dade be gano ba, nufinshi duk mu zamuyi Wannan uban aikin dakanmu kamar masu kwakwalen computer? Halan ke dakanki kikayi?" tafada tana kallon sumee sheqeqe Itama Ta6e baki tayi tace "ina? Kawai wani neighbour dinmu naba yayimin shima bana yake graduating, ni saida yagama na duba naga kamar ma duk shirme yayimin dama yafimin Kama da masu kwakwalen kifi masu zama bayan aji, Allah yasa ba shirme ya rubutamin ba don Koda nabashi dafarko yayi kamar be ganeba can kuma ya nuna ya gane" Dariya duk suka Fashe dashi banda zee data dan Ta6e baki tana jinsu tundazu taqi tankawa "yo ke kiduba kigani ko shirmen ne mana" inji nurr "induba inga me? Atleast shi ya iya rubuta shirmen ni ko shirmen ban iyawa gwara na lalla6a nayi submiting hakanan qila idan yaga yadda nacika takardu har biyu ya tausaya yabani maki" Dariya suka qara tuntsurewa daita deeya tace "Wato har paper biyu ya cikamiki kenan, Allah yasa ba lissafin bashishikan da ake binshi ba yayi miki a takardu" Harararta sumee tayi tace "shegiya yana dan masu kudin zaici bashi?" "To Allah yasa ba wanda yakebi ba ya lissafa maki a takardu ke kinanan kina jindadi an cikamiki takardu" inji nurr itama cikin Dariya Bugu sumee takai mata tayi Saurin kaucewa tana Dariya "ba bakinki ba, bakinki yasari danyen kashi mai wari, ai gwara ni da wadanda basuyiba kwata2" "su waye basuyiba? To ingayamaki tun washegarin ranar daya bada nayi abuna" inji nurr tana Harararta "wayayi miki?" inji sumee "wafa? Koko ance miki kowa mai kwalwar kifi ne irin ki?" tafada tana Harararta itama Ta6e baki sumee tayi tace "da dai ba'asan asalin balbela ba da saitace daga misra take, Allah yasa ba zero over kunnuwa zakici ba" "ba bakin mutum ba wlh, insha Allah saina linkaki maki" inji nurr itama tana Harararta Dariya duk sukayi sannan deeya ta kalli zee dake sauraronsu tundazu tace "kefa hajjaju? Kinyi?" Yatsine fuska tayi tace "tun shaidan na dan qauye? Ko yanzu akace kule cass zance don yanzu haka yana cikin jakkata" "kaji manya, Allah yasa kema be baki wahala ba" inji deeya tana dan Ta6e baki "Allah dai yasa asamu abinda akeso, batun bada wahala kam ai dolene tunda yasanyo mugunta aciki saidai kuma ta Allah bata mutum ba, mudin da akayi don mu sai munci Koda rabi ne saidai uwar diya taji kunya" tafada tana sake Yatsine fuska "To Allah yasa" inji nurr "amin dai" deeya ta amsa Sumee data hango rukky tafe tace "tofa? Da alamu dai andace Wannan zabga sauri haka?" tafada tana Dariya Suma duk kallonta sukayi suna Dariya qasa qasa. Qarasowa rukky tayi wajen tana sauke numfashi "yane? Halan ta samune" inji deeya tana Dariya Rukky dake sauke numfashi tace "tasamu a ina? Kuna nan hankalinku kwance ga dan mutane can za'a kashe" Gaban zee ya yanke ya fadi ta dafe qirji kamar yadda kingin sukayi "mene?" inji nurr tana waro idanu "wlh ga Deen can su tawagar master sun tareshi suna..." Zaburar da zee tayi ta miqe ya hanata idawa "mene? Deen? A ina?" ta jero tambayoyin ajere, bata kuma tsaya Jin amsa ba ta figi jakkarta tabar wajen hankali atashe Suma maramata baya sukayi da sauri kowanne hankalinshi tashe Sauri sauri gudu gudu ta qaraso inda taga dandazon mutane antaru Ana kallo Batareda magana ba tashiga kutsawa ta tsakanin mutane har tasamu ta qaraso gaba Wani tagani riqeda kwalar rigar Deen yana janshi yana Dariya Jitayi ranta ya sosu ganin yadda Deen keta qoqarin kwatar kanshi amma yakasa ga su can juice data aikoshi watse a qasa Batasan ya akayi ba Kawai sai ganinta tayi gaban mutumin tasa iya qarfinta ta tureshi Kasancewar T.j be shiryama haka ba sai yatafi yayi baya2 Alex dake bayanshi yayi saurin tareshi, nan aka shiga kallon kallo tsakanin zee dasu tawagar master Mutanen dake wajen yan kallo da duk aka rasa wanda zai ta6uka komai tundazu sukaji wani irin dadi ya ratsasu kasancewar dama kowa ranshi bemashi dadi da abinda ke faruwa, tsorone kawai ya hanasu motsawa, karon farko da zee tayi abinda students sukaji dadinshi "ku wadanne irin dabbobi ne da bakusan abinda kemuku ciwoba? Me yayi muku zaku tareshi a hanya kuna shaqoshi kamar kunsamu wani dan taure?!" tafada rai a matuqar 6ace "ke malama ki kiyaye abinda harshenki zai furta tun kafin in juyamaki fuska takoma baya yanzunnan" inji T.j da shima ranshi ya 6aci sosai "go ahead mana! Ka juya din, dama kayi Kama da arnan dajin qarnin farko, so dan kayi hakan ba komai bane, saidai zee tafi qarfin a ta6amata Koda tip din akaifa ne duk wanda yayi gigin haka ya shiryama baquntar lahira!" tafada tana nunasu da yatsa Alex da dama yana ciki daita ya hayyayako yace "ke eazy fa, acikinmu uban wa kikaga yayi Kama da tsararki anan?! Ko dan kinga Ana daga miki kikeson wuce makadi da rawa, To wlh kiyi gaggawar shiga taitayinki tun kafin na lahira yafiki jin dadi" yafada yana zazzare jajjayen idanunshi Ita yakewa warning amma mutanen wurin sukaji tsoro don sai zare idanu suke Wani kallon uku saura kwabo ta watsamashi tace "kai kuma daga ina? Person dey talk baboon dey answer, ko anan kaga masu irin siffarka ne?" Alex zai sake magana master da tunda aka fara abin yazama dan kallo yayi saurin dafa kafadarshi ya dan kalleshi fuskarshi dauke da wani munafikin Murmushi yace "Baaasar mana" Sannan yajuyo kan zee daketa watsamasu mugun kallo tana huci shikau Deen yana bayanta ba baka sai kunne Qarasowa yayi gabanta ya kwantar da murya yace "Baby.. Kiyi hqr, basusan dan uwanki bane, hakan bazai qara faruwa ba" Duk yan kallon wajen hangame baki sukayi cikin tsananin mammakin abinda yafito daga bakin master Itakau zee Yatsine fuska tayi tana mashi kallon sheqeqe tace "waye babyn? Kuma ba Dole sai dan uwana ba, su kingin mutanen basuda freedom akace muku? Bakuda aikin yi sai neman magana a school kun gagari kowa, kowa tsoronku yake and you're proud of that har kuna fitowa kuna nuna hakan, this school is for learning kuma saboda karatun Kowa anan ke zuwa, idan ku jagaliyanci kuka qware akai why not kutafi tasha da dandalin qauraye instead of coming here kuna harassing innocent souls" tafada kai tsaye babu ko digon tsoro a tattare daita Daga kallon mammaki ya sauya yakoma na tsoro a fuskar yan kallo suna ganin abin kamar almara wai wata ce ke tsaye gaban the whole Master tana gayamashi irin Wannan maganar Tare su Bash dasuka yunquro yayi da hannuwa yana Murmushi sannan yasake kallon zee dake binsu da disgusting look yace "kiyi hqr, hakan bazata sake faruwa ba, kuma ku bata hqr" yafada yana kallonsu Alex Alex zaiyi magana yayi mashi wani kallo yace "kubata hqr nace!!" yafada a tsawace har saida mutane suka Girgiza including zee da Deen dashima be qaunar tsawa ko kadan Ganin 6acin rai qarara a idanuwanshi yasasu Kama kansu suka juya ga zee dake qoqarin saita nutsuwarta daga firgicin da tsawar master ya sata suka bude baki kamar masu ciwon baki suka bata hqr zuciyarsu na tafarfasa Wannan embarassment din dame yayi Kama? Ace su kebada hqr ga yar tatsitsiyar yarinya a bainar jama'a? Maida kallonshi master yayi ga zee yace "kinji sun baki hqr, kiyi hqr hakan bazata qara faruwa ba" Yatsine fuska tayi tace "ni sukai wa laifi daxasu bani hqr? Shi da sukayi wa laifi shi zasu ba hqr" tafada tana nuna Deen dake bayanta still Kallon Deen master yayi sannan ya kalli su Alex yayi musu magana da ido akan suyi yadda tace Zuciyarsu kamar zata Fashe don takaici amma babu yadda suka iya Dole suka bashi haqurin Kafin ma su rufe baki sai ganin wani school authority sukayi tsulum cikinsu yafara tambayar ba'asi Kafin wani ya bude baki zee tayi caraff ta amshe da "sir yanzu abinda akeyi a school dinnan yadace kenan? Ace bakada freedom of walwala yadda kake so saboda tsirarun tsageru dasuka yiwa mutane karan tsaye suka yimusu shamaki da kwanciyar hankali?" "meya farune?" inji school authority din Cikin zaqalqalewa tace "sir, Wannan mutumin ne ke tafiya yadawo daga cafteria kawai besan hawa ba besan sauka ba suka tareshi suka watsar mashi da kayan da yasiyo, kalli ka gani..." tafada tana nuna juices dake watse a qasa "hakan be ishesu ba suka Kama mashi kwala suka shiga faffala mashi mari suna jijjigashi duk don sunsan babu mai iya takamasu burki a school din, yanzu don Allah Ahaka kukeso wasu suyi sha'awar shigowa school dinnan bayan sunajin labarin cin kashin da akewa students?" tafada cikin haqiqancewa Kafin school authority din yasamu damar amsawa sukaji Deen nacewa "O'O! Wannan ba gaskiya bane" Duk juyawa akayi gareshi Ana kallonshi baki sake Be damu da yadda akayi mashi caa da idanu ba ya cigaba dacewa "babu kyau qarya, kakata tace qarya haramun ne don Annabi Muhammad (s.a.w) yace *Iyakum wal kazziba, fa'inal kazziba yahdi ilal fujura, fa'inal fujura yahdi ilan-narr* Ma'ana *na haneku dayin qarya, domin ita qarya tana kaiwa ga ta6ewa, itakuma ta6ewa tana kaiwa ga wuta* don haka Mud queen kiji tsoron Allah ki daina qarya" Waro idanu tayi sosai 😳 tana kallonshi speechless Sauran yan kallon ma Wara nasu sukayi suna kallonshi baki hangame while wasu dasuka sanshi suka san halinshi suka dafe kai cikeda takaici 🤦🏻‍♂️🤦‍♀? "mene?" tafada cikin tsananin mammaki "cewa nayi qarya ne, basu mareni ba kuma basu jijjigani ba, kawai nine nataho ban gansu agabana ba na bangaje wancan baqin 👱🏿‍♂? wayarshi tafadi shine ya riqemin kwala yace wanene ni dazan bigeshi? Nace mashi nine Deen kuma ban sani ba na bigeshi shine yace saina biyashi wayarshi ko yayi tsirena, shine nace banida kudin biya shine ya riqemin kwala yace saina biyashi wancan mummunan 👩🏾‍🦲natayashi suna wata irin magana suna Dariya" yafada innocently cikin son kare su Alex data shirgama qarya Duk sakin baki akayi harsu Alex din Ana kallon ikon Allah yayinda ran zee yayi mummunan 6aci "kai ni zaka cewa maqaryaciya don na kareka?!" tafada cikin tsananin 6acin rai "ni banyi qarya ba, ba wani Marina dasukayi ki tambayi mutanen nan ai suna wajen keda kikazo daga baya ma?" yafada cikin son kare Kanshi "kai!!!" tafada a fusace tana yowa Kanshi Hakan yasashi saurin 6oyewa bayan master yana cewa "O'O!" Baki a tunzure Duk Dariya hakan yabasu hakan yasa suka shiga yinta harda authority din daya fuskanci komai Wato ita ta kareshi shikuma ya yarfata Ganin wurin ya kacame da hayaniya yasa authority din cewa "ya isa! Ya isa!!" Saida ya samu akayi shiru sannan yace "To yanzu koma dai menene Aliyu (Alex) baku kyauta ba tunda yace ba dagangan ya bigeku ba be kamata kuyi mashi hakaba ku dinga uzuri... Ke kuma kibar bada shaida akan abinda baki saniba, kince an mareshi an halbeshi shi yace a'a, kibari ayi abu agabanki sannan kibada shaida... Kai kuma ka dinga kallon gabanka idan kana tafiya ko ba yau ba watarana zaka iya fadama wani abin" Kada kai Deen yayi daga abayan master dayake leqe "To yanzu kowa ya watse, case closed, oya to your classes!" inji authority din Watsewa aka fara yi kowa na fadin albarkacin bakinshi hakan yasa wurin daukar hayaniya "malama kuma ku tafi, kaima wuce" yafada reffering to zee da Deen dake la6e still a bayan master Gyara zaman jakkarta tayi a kafada ta jefi Deen da wani mugun kallo wanda yasashi saurin komawa bayan master daga leqen dayake yana tura baki sannan tajuya itama tabar wajen a fusace Sai a sannan yafito daga bayan master din still yana turo baki ya tsintsince lemukanshi shima yaqara gaba akabar daga school authority din saisu master Kallonsu authority din yayi cikin kulawa yace "dan Allah ku dinga dagama yarannan qafa, yarane be kamata kuna shishige masu ba hakan zai iya jamuku raini" "basar kawai oga, guys mutafi" yafada yana yin gaba shima su Alex suka take mashi baya Binsu da kallo authority yayi a qasan ranshi yana musu fatan shiriya... ✍️ Tofah Deen ya 6allo ruwa🙆🏻‍♂? Zee ma ta 6allo ruwa🙆🏻‍♀? Wa ke aruwa kusada kada cikinsu 🐊🐊 Juma'at mubaraq in advance 💖 Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:32 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *009* Kallon juna zee da Deen sukayi sannan suka maida kallonsu akanta "ma'ana zaka dinga yin duk abinda tasakaka batareda musu ba har ta huce" rukky tafada tanawa zee wink 6ata rai yayi yace "but why? Haven't I apologize?" "you have, but it's not accepted, idan kuma kafison ta dauki mataki akai shikenan but remember sojijin sunada bindigu gashi kawunta yana sonta sosai be qaunar ata6a mashi ita gashi yanada saurin zuciya abu kadan zaisa akawomashi mutum ya harbeshi" inji rukky a yanayin tsoratarwa Pouting din mouth yayi 🙎🏻‍♂? bece komaiba "ya? Kanason tadau matakin koko ka yarda da sharadinta?" "yaushe zata huce din?" ya tambaya fuska a kumbure "ranar da na huce, now tell me are you ready or not?" tafada tana zaro mashi ido Kallonta yayi sannan ya kauda kai yace "ok" "me kace?" inji zee "I said fine!!" yafada cikin dan daga murya dukda bawani amo muryar tayi ba "hey, watch out am your boss karka qara yimin tsawa" tafada tana nunashi ta yatsa Dan kauda kai yayi cikin murya qasa qasa yace "I don't like her" "kalli nan" yaji tace hakan yasashi dagowa ya kalleta fuska still a tur6une Nuna logo din jikin rigarta tayi tace "meye nan? *Born to rule* I was born to rule everyone, am a princess, a queen so watch out!" tafada tana kwama shade dinta Shidai bece komaiba sai kallonta dayake acikin zuciyarshi sai nanata _I don't like her_ yake "mutafi" tafada masu rukky sannan ta juyo ta kalleshi ta nunashi tace "anytime I need you zan kiraka zakazo kayimin duk abinda nakeso, hope am clear" tafada tana jan kunnenta daya alamun gargadi Kauda kai yayi sannan ya kada kai ahankali "better" tafada tana wucewa Su kinginma bin bayanta sukayi suna qumshe Dariya bayan nurr tabashi littafinshi dasuka fizge Binsu yayi da kallo har saida sukayi nisa sosai sannan cikin kwala kira yace "Mud queen!!" Cak ta tsaya Batareda ta juyoba sai su rukky dasuka juya suna kallonshi "skirt dinki ya yage abaya! Duba kigani!" yafada cikin daga murya kasancewar sunyi nisa dashi don har saida yasa hannu yakare baki kamar yadda mai kiran sallah keyi don suji Takaicine yaqara qume zee hakan yasa bata ko juyoba taqara gaba tana jin yadda su sumee keta kakka6ar Dariya Ganin sun wuce yasashi daga kafadu yana mere baki 🤷🏻‍♂? sannan ya koma ya zauna yana duba lokaci a agogon hannunshi, guntun tsaki yaja ganin sun 6ata mashi lokaci sosai, maida hankalinshi yayi a littafin hannunshi yana nazari kafin lokacin dayan lecture dinsu yayi **** kallonsu tayi cikeda takaici tace "wai Wannan wane irin wulaqanci ne zaku tisani agaba kunata kakka6amin Dariya" tafada cikin jin haushi Dakyar deeya ta iya tsagaita dariyarta tace "I swear that guy is so funny, ko yanzu kasuwa ta watse dan koli yaci riba don he made my day" Rukky tace "wlh nima, the guy is soo funny shiyasa nayi Wannan dubarar ko banza munsha dariya" taqarashe cikin Dariya Guntun tsaki zee taja tace "ni kuma wlh banga abin ban Dariya ba anan, the guy is so annoying, very irritating" Sumee cikin Dariya tace "wai skirt dinki ya yage... Hhhhh guess be ta6a ganin straight skirt ba" "hakan na nuna alamun bayan hauka akwai qauyanci tattare dashi, ni am wondering ma yadda akayi yayi managing harya shiga Uni Wannan ai da kindergaten ya dace" inji zee "Hhhhh asarar kudi ko? Kinsan wasu iyayen da iyayi Dole sai 'ya'yansu sunyi karatu, basusan mu kanmu dake normal dakyar mukesha bare ayi maganar abnormal people" inji deeya "kedai bari, ai wasu iyayen dakwai daukar dala ba gammo musanmman ma talakawa, Wannan ai da psychiatric hptl yadace ba school ba" inji zee fuska a yatsine tana qoqarin fiddo dan memo dinta datake amfani dashi wajen jotting abubuwa masu amfani idan Ana lecture "saidai fa he's damn handsome, wlh tunda nake ban ta6a ganin namiji mai irin kyaunshi ba, Wannan da normal yake da anga miskilanci don daya fuskanci yanada kyau haka daddaga mana hanci zai dinga yi qila ma bazamu isheshi kallo ba" inji nurr Zee da tunda tafara magana ta tsaida abinda take tana watsama nurr wani irin kallo tace "dan Allah kibar irin wannan maganar idan kinsan ina kusa, ya dagawa wa hanci? Ki dinga tantancewa idan zakiyi magana kibar yin jimla, ni ai ba'ayi wanda zai dagamin hanci ba duk kyaunshi kuma duk dukiyarshi, ca6! God forbid badai ni zainab din ba, kuma ku kuke ganin wani kyaunshi, ina kyau anan? Mtcheew!" ta maida hankalinta akan memo din hannunta Duk dan ta6e baki sukayi, deeya da bata iya shiru tace "Gaskiya don kyau yanada kyau idan za'abi ta gaskiya, saidai kunsan abincin wani guban wani" "gwara da kika ce haka don mu ba kowanne abun dake burge kowaba ke burgemu, mu special people always want special things not cheap stuffs" tafada yana jujjuya idanunta cikin salo Duk sake ta6e baki sukayi qasan zuciyarsu cikeda haushinta don sosai jijji da kanta ke basu haushi saidai ba damar nunawa. Wata firar suka jawo suka shiga yi zee na dan tsoma masu baki jefi2 don kusan duka hankalinta nakan memo din hannunta tana nazarin abinda aka koyamusu dazun Sukau su sumee firarsu suke hankali kwance babu abinda yasha musu kai da yin koyi da abinda zee keyi sai firarsu suke suna Dariya hankalinsu a kwance Suna ahaka lokacin second lecture dinsu yayi suka tashi suka nufi aji don daukar darasin. Qarfe biyu Deen yafito daga second lecture dinsu, kai tsaye massalacin school din yanufa ya gabatar da sallar zuhr sannan ya wuce gida kasancewar bayada wani lecture din Su kau su zee sai 3pm suka fito daga last lecture dinsu inda kai tsaye itama motarta ta nufa don har bala yazo, tashige bayan sunyi bankwana dasu sumee suka fice daga school din. *** Cin abinci suke amma tana lura da yanayinshi, tunda ya dawo daga school dama taga kamar yanada damuwa don kadan kadan saiya turo baki ya hade gira "kyakyawa na..." Dagowa yayi ya kalleta yana dakatar da lomar dazaikai baki Murmushinta dake kwantar mashi da hankali tayi tace "yau baka bani labarin abinda yafaru a makaranta ba" Jin haka yasashi 6ata fuska tareda turo baki, hakan ya tabbatar da hasashenta na a can school din aka ta6oshi "meya faru kyakyawa na?" tafada cikin tsantsar kulawa Qara hade girarshi dake cike da gashi yayi yana kumburi yace "kaka bana sonta" Dan Wara idanu kaka tayi tace "wacece?" "Wannan Mud queen din mana" yafada yana qara cika "wacece hakan?" "Wannan wanda tayimin tsawa na saketa tafada chakwali" Qara wara idanu kaka tayi tace "tofah dama ba musulma bace naji sunanta wani iri?" "musulma ce mana, haka dai naga tasa a bayan rigarta, nidai bana sonta" yafada yana yatsine fuska "me kuma yafaru? Ba kabata haquri ba?" kaka tafada tana jin zafi a ranta don bata qaunar abinda zai ta6amata jikanta "ai tun ranar batazoba sai jiya, na gayamata banason tsawa amma sai taita qarawa kuma tace idan ban..." saikuma yayi saurin dafe baki yana mazurai don yariga ya manta da yace bazai gayawa kaka ba don yasan halinta tana iya jin haushi tace zata bishi har school din kuma Mud queen ranta yaqara 6aci tagayawa kawunta azo a tafi dashi "kayi shiru kuma, idan bakayi meba?" tafada tana tsareshi da ido 6ata fuska yayi yace "wai idan ban fita daga harkarta ba sai tasa an kamani" yafada cikin chanza abinda yayi niyyar fada da farko "yo dama kai harkarta kake shiga ne?" tafada cikin Jin haushi "A'a fa, ni babu ruwana da ita tunda na bata haquri ban qara tanka mataba" yafada yana kai loma baki Ganin kaka ta kafeshi da idanu yasashi sauke nashi yana rarrabasu a qasa yana taunar tuwon bakinshi "gayamin gaskiya, me tace maka?" tafada still tana kallonshi Bata fuska yayi yace "O'O! Nifa kaka gaskiya nake fadamiki" Tallabe mashi keya tayi tace "ja'iri! ahakan kake fadin gaskiyar sai rarraba idanu kake? Ko angayama zaka iya layyancemin ne? Koma dai menene karka qara shiga harkarta kuma duk sadda tasake ta tankamaka ka gayamin zan bika har school din inji dalili" "To" kawai yace yacigaba da cin abincinshi "kayi sauri kagama muyi tatarnan kar dare yayi mana kaga har tara saura" inji kaka tana miqewa don ita tuni tagama cin nata Da to ya amsa yana kallon inda suke rataye matacin qullun kokon yana tuna gyallen zee Be 6ata lokaci ba yagama ya kai kwanon kitchen dinsu ya dawo suka Kama da kaka suka fara tatar. Koda suka gama saida suka Kauda komai na rufewa suka rufe sannan suka daura alwalla kamar Koda yaushe suka shige dakunansu bayan sunyima juna saida safe. *WASHEGARI* kasancewar yau lecture din 12pm ke gareshi yasa sai 11am yabar gida. Koda yazo school din har sha daya da rabi takusa. Be zarce koina ba sai wajen zamanshi inda yasaba zama shikadai yayi karatun shi. Deen beda aboki ko guda, he's the type that cherish lonely life, baida hayaniya haka zalika bayason hayaniya shiyasa yaza6i yayi rayuwarshi shi kadai. Idan ka ganshi da mutum to lokacin lecture ne a aji ko sun hade a hanya kuma gaisuwace zata shiga tsakaninsu saidai ko su tsokaneshi yabisu da Murmushi idan kuma yaga abinda be mashi ba ya maganta Sanadin rashin son hayaniyarshi yasashi samun Wannan quiet wurin inda zai zauna shikadai yayi nazarin karatun shi, idan kaga yabar wajen to ko class zai shiga ko gida. Be dade da zama ba yaji ana cewa "Helloo" Dagowa yayi daga littafin dayake kallo ya sauke idanunshi akan deeya da rukky dake kallonshi shima fuskarsu dauke da Murmushi Bata rai yayi ya Kauda kai sannan cikin murya qasa2 yace "Hi" Kallon juna deeya da rukky sukayi Dariya marar sauti sannan suka maida kallonsu akanshi "ya? Karatu kake?" inji deeya Kada kai kawai yayi bece komaiba kuma be kallesu ba "amma yanzu kazo ko? Munzo dazu bakanan" inji rukky Dagowa yayi ya kallesu fuska ba walwala yace "eh" Qara satar kallon juna sukayi suna dagawa juna gira daya sannan rukky tace "To kazo inji zee" Dagowa yaqarayi yana musu kallon rashin fahimta yayunda can qasa kuma yana jin haushin yadda sukazo suna 6ata mashi lokaci "wanene haka?" ya tambaya yana hade girarshi "wanene haka ko wacece haka? To boss dinka nake nufi" tabashi amsa "boss kuma?" "eh, ko nufinka har ka manta? Hmm fatan dai baka manta da kawunta ba da sojojinshi?" Sake 6ata rai yayi yace "me kuma nayi yanzu?" "mefa? Kawai cewa tayi akiraka qila wani abin zaka mata ko ka manta da deal dinku ne?" "amma kunga ai karatu nake ko?" yafada yana nuna musu handout din hannunshi Dariya suka sa, deeya tace "haba? Ashe karatu kake? To me kake karantawa?" "me fa? Kawai bin rubutun yake da kallo wondering yaya akayi typing dinsu" Dariya suka sake sawa, ganin hakan yasashi ta6e baki ya maida ga handout din "kaifa muke jira" inji deeya "nace fa karatu nake kuma mun kusan shiga class" yafada cikin qosawa "class ko? Muje deeya, da rabon wani yajishi a cell yau" tafada tana kamo hannun deeya suka juya suka tafi Binsu da kallo yayi ganin sunyi nisa yasashi rufe handout din yana turo baki ya dauki kingin littatafan ya miqe yabi bayansu rai a6ace Tun daga nesa suka hangosu sun taho sai Deen dake bayansu yana cika yana batsewa "zee kalli mutuminki" inji sumee tana ta6ota while nurr tasa dariya Kallon wajen tayi ta dauke kai tana ta6e baki "ca6! Da alamu dai afusace yake ji yadda yake hura hanci" inji nurr tana Dariya "yo ba doleba, yaga ana neman takura mashi" "Hmm ai kadan ma yagani, I'll make sure I teach him a good lesson" inji zee tana qara Kauda kai ganin sun qaraso Zazzaunawa su rukky sukayi yayinda shikuma ya qame a tsaye yana mazurai Ganin babu mai niyyar tankamashi yasashi cewa "gani... What's it?" Banza tayi dashi don ko kallonshi batayi ba sai su rukky taketa xabga Murmushi suna jiran ganin yadda za'a kaya "Mud queen!" Saurin Juyowa tayi tana watsamashi mugun kallo tace "what did you just call me?" "Mud queen, isn't that your name?" yafada yana Kauda kai bakinshi agaba "kull! Kar inqara Jin Wannan sunan abakinka, my name is Zainab, call me zainab" tafada tana wani zazzare mashi manyan idanunta kamar irin tanama danta fada "O'O! Banason wadannan idanun!" yafada yana yamutse fuska Dan Wara idanu zee tayi tace "baka sonsu? To saika kwakulesu yadda zansan baka sonsu" tafada cikin quluwa Yamutse fuska yasakeyi yace "uhun, ni bazan iyaba besides idan na kwakule zaki koma skull with ugly forhead" Dariyar dasu sumee keta dannewa tundazu tafito fili suka shiga kyakyatawa "ni kake cewa ugly skull with forhead?!" tafada a qule Kauda kai yayi bece komaiba sai hura hanci dayakeyi Kwafa tayi tana kada kai Ganin bata qara tanka mashi ba yasashi cewa "intafi? Munada class in the next 15mins" yafada yana kallon yar agogonshi dake maqale da hannunshi "eh tafi din" tafada cikin gatse tana harararshi Dadi yaji ya kamashi yayi saurin juyawa zai tafi "au tafiyar zakayi?!" tafada a fusace Kasancewar tayi maganar a tsawace yasashi Saurin Juyowa a tsorace yana cewa "O'O!" "O'O! Nabi O'O dagudu, wai tsaya wama yasaka a university bayan ga kindergaten nan birjik a gari? Meye ma sunanka wai?" tafada tana Girgiza kasancewar ta tunda tafara ta miqe Banza yayi ya kyaleta yana kumburi "ok bazaka fadi ba? Sumee bani wayata inkira kawu" "Deen..." yafada a kumbure "mene?" tafada tana yatsina fuska "I said Deen!" ya fada da dan qarfi "kutt... Ni kakewa tsawa?" tafada tana nuna kanta cikin zare ido Banza yayi ya kyaleta sai hucin dayake "Dakyau! Amshi kaje ka siyomin ruwa" tafada tana miqa mashi 1k Juyowa yayi ya dan kalleta sannan ya amshi kudin yajuya yana cika da batsewa Su rukky da cikinsu harya fara ciwo don dariya ta kalla taja guntun tsaki sannan ta zauna tana huci "Allah dai zee, wlh you guys are so funny!" inji rukky "I swear, wlh kunfi tom & jerry ma" inji nurr itama cikin Dariya Tsaki tasake ja tace "kuke ganin funniness dinshi, mtcheew! he's so annoying" "Bawan Allah, I wonder how handsome guy kamar shi yake haka, gaskiya solu6ancinshi ba qaramin qwararshi yaiba" inji sumee "wlh kau, dama ance mutum tara yake be cika goma ba, shi nashi tawayan kenan" inji deeya Zee bata sake tankamasu ba tacigaba da danne dannenta a waya Deeya ce ta ta6o sumee tana gwada mata Deen daya taho kinkime da ledar pure wata daya Wara idanu sumee tayi tana toshe baki sannan ta ta6o nurr dake kusada ita ta gwada mata itama waro ido tayi tana qumshe Dariya, dama rukky tunda deeya ta ta6o sumee itama ta ankare Zee batasan wainar da ake toyawa ba don hankalinta nakan wayarta harya qaraso sai jitayi ya dire mata ledar pure water din agabanta yana miqomata chanji Bin ledar pure water din tayi da kallo sannan ta maido Kanshi cikin alamun rashin fahimta "ga chanjin" yafada yana miqamata Qara maida kallonta tayi ga ledar ruwan tace "meye Wannan?" "pure water din dakikace asiyo mana" yafada yana hade gira "ni nace ka siyomin Wannan? Wannan ne pure water? How is it pure kana ganin abu kamar ruwan toilet? Nufinka ni zansha Wannan?" injita tana kallon ruwan a wulaqance "but you said I should buy you water, wane ruwane kuma bayan Wannan" yafada cikin qosawa "ce maka akayi kowama nashan qazantar dakuke sha ne? Swan water nake nufi, dummy!" tafada tana harararshi Gani tayi beko motsaba hakan yasata qara cewa "kafa dauke Wannan abin daga gabana ka kawomin abinda nace" Bece komaiba sai duqawa dayayi ya dauki ledar ruwan ya wuce yana kumbura fuska Binshi da kallo sukayi suna Dariya qasa2 "ayyah? Ni wlh harya fara bani tausayi" inji nurr "nima wlh, the guy is so cool yanada hqr" inji deeya "karma yayi haqurin, ba ya iya jefa mutum Mud ba?" zee tafada tana kwafa "Allah sarki, gashinan ya dawo" inji sumee Duk Juyawa sukayi suka kalleshi suka ganshi ya taho ruqe da swan water daya Ta6e baki zee tayi ta Kauda kai tana taunar chewing gum din bakinta Koda yazo miqamata yayi yanzun ma yana turo baki Dagowa tayi tayi mashi kallon up & down sannan tace "meye Wannan kuma?" "ruwan" yafada yana dan Wara mata oily idanunshi "guda daya nacemaka kasiyo? Ko nikadai ke anan dazaka siyo guda koko cemaka sukayi azumi suke" tafada cikeda gadara tana enjoying moment din "zee mana" inji nurr tana kya6e fuska don honestly yafara bata tausayi Wani kallo tayimata ta dauke kai ta maida kan Deen dayake turo baki still "ko bakaji ba?" Sake cinno baki yayi yace "but you said swan water" yafada yana kallonta da innocent face dinshi "yes amma ai ba daya nace ba" "To nawa?" "mu nawa ne nan?" "5" "To 5 zaka siyo" "but munada lecture saura 5mins ashiga" yafada yana duba agogo "kaje ka dawo in 3mins sai katafi" Ba don ranshi yasoba yajuya yatafi qarowa a qasan zuciyarshi yana cewa _I don't like her_ Bayan tafiyarshi nurr tace "ayyah, zee adinga dai tausayawa" Dan harararta tayi tace "banason irin Wannan nurr, duka me nayi mashi? Shifa a ruwan chakwali ya jefani yasani nazama abin Dariya wanda a sannadiyar hakan yasani zaman gida na sati daya ina jinyar qarya, nikuma daga fara ramawa yau sai kice wani abu?" "kuma fa, kawai nidai yanayinshi kebani tausayi, he's so timid" inji nurr "shi ai be ba Kanshi tausayi, bakiji abinda yacemin dazu ba? Wai ugly skull with forhead" Dariya duk suka Fashe dashi sumee tace "ai ke kikace ya kwakule maki idanu shiyasa yagayamaki yadda zaki koma" "ba Dole ince ya kwakulesu ba tunda yace baya sonsu? Mtcheew dani yake zancan wlh" tafada tana maida kanta akan wayarta Cigaba da firarshi sukayi itadai zee bata qara tankamasu ba harya sake dawowa da robar ruwa hudu dik ya hada gumi saboda zirga2. Ajiye masu yayi duk suka dauki guda guda sannan ya miqama zee chanjinta yana kumburi Saida ta watsamashi harara sannan ta amsa tace yatafi zata nemeshi idan tana buqatarshi Cikin Jin dadi ya juya yafara tafiya da sauri don gab ake da shiga class sai jiyayi ankira sunanshi kuma Juyowa yayi yana 6ata rai alamun menene kuma? Nurr data kirashi ta nunamashi robar ruwan hannunta alamun yazo ya amsa Girgiza mata kai yayi kawai alamun baya buqata sannan yajuya yabar wajen da sauri don karma a qara tsaidashi Dariya duk suka sa rukky na cema Nurr maganinta kenan, Murmushi kawai tayi ta daga kafadu suka cigaba da firarsu. A bangaren mr ibrahim kau Kanshi ne yadau zafi, yarasa hanyar dazaibi wajen aiwatar da qudurinshi na kada zee Yasan idan ya tsaurara dayawa ba zee kadai ba zata fadi harda dayawa acikin class din wanda shi ba haka yakeso ba, ita kadai da unserious elements irin qawayenta yakeso su fadi amma tayaya? Yasan ba laifi kan zee na ja fiyeda wasu dake attending lecture dinshi, idan zai kadata ta hanyar tsaurara questions yasan dayawa cikin students dinshi suma zasu fadi tareda ita, To yanzu ina mafita??.... ✍️ No editing 🙏🏻 Kuyi hqr jiya ban samu chajiba sai da marece gashi ina azumi inajin wuyan typing, kar inje insaki layi🥴 Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:32 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *011* "zee kiyi hqr, nasan yadda kikeji ahalin yanzu, kiyi mashi uzuri da yanayinshi nasan da normal yake da beyi maki haka ba" inji nurr tana kallon zee dake zaune hannuwa harde da qirji lip dinta naqasa acikin bakinta tana tauna ahankali Kallo daya zakamata ka hango tsantsan 6acin ran datake ciki "Dole fa abin ya bada takaici, bansan solu6ancin gayen nan harya kai ya watsa ma mai kareshi qasa a ido ba, Wannan ai gaulanci ne" inji sumee Haka kawai nurr taji maganarta tamata zafi hakan yasata cemata "sumee karki manta kowanne dan adam da tawayar da Allah yayimashi don dukkanmu tara muke babu wanda yacika goma, ke da kike taqama kina normal idan an bincika akwai abubuwa da dama da wannan bawan Allahn yafiki dashi, kowanne dan adam da irin baiwar da Allah yabashi don haka a dinga sanin abinda za'ace don inhar kana raye To bazakace ka gama lfy ba" "ikon Allah, daga magana sai cibi yazama qari, wai nurr meye tsakaninki da guy dinnan? Naga sai wani zaqalqalewa kike akanshi, danace yana solu6anci ba solu6iyon bane? Gayamin! Inba hakaba wane normal mutum zai aikata abinda ya aikata? Dakuma kike cewa yafini, dame Wannan gaulan zai fini? Saidai da gaulancin amma babu abinda zai iya fina dashi" inji sumee tana harararta Ran nurr yasake 6aci tace "ai gwara shi, gaulancinshi abin so ne don baya cutarwa saidai a cutar dashi kuma gaulancinshi be hanashi Tsayawa akan gaskiyarshi ba duk dacinta kau, kuma gaulancinshi be sashi Jin tsoron mutane amadadin Jin tsoron mahallicimshi, tabbas be kyautaba daya dizgata a gaban jama'a amma idan aka duba za'aga akan gaskiyarshi yake, be iya qarya ba kuma tsoron mutum bazai sashi yafaraba, wasu fa? Haka zaka gansu sumi2 kamar na Allah, sululu kasau maciji sari ka noqe, wadanda tsoron mutum zaisa su take gaskiya don farantawa abokin hallitarshi" Sumee zatayi magana deeya ta katseta da "wai duk meye hakane? Meya jawo duk Wannan? Haba be kamata kuna behaving immaturely ba haka saboda wani can Deen, idan yayi fiyeda hakan ma ai ba abin mammaki bane tunda dan lokacin da mukayi atare ya isa ya nunamana waye shi, he's a straight-forward man, yana magana ne kai tsaye Batareda damuwa da abinda zai biyo bayaba, kawai zee hqr zakiyi tunda haka Allah yayishi saidai kawai atari gaba" tafada tana kallon zee da haryanzu bata ko daga kai ta kallesu ba tunda suka fara "aikau dai, kawai sharewa zakiyi kinga gaba idan yaqara shiga irin Wannan halin yaga wanda zai qara qoqarin taimakonshi" inji rukky "bama zai shiga ba Insha Allahu" inji nurr tana Kauda kai Hango Deen dasukayi ya nufo wajensu yana kukumbure fuska yasasu zubamashi ido banda zee da batama san da tahowarshi ba Qarasowa yayi gabansu yaja ya tsaya yana sake hade gira sannan ya miqoma zee ledar juices dinta yana cewa "gashi" Saurin dagowa zee da Batasan da isowarshi ba tayi sannan tayi Saurin Kauda kai tana lumshe manyan idanunta "gashi" yaqara fada yana sake miqomata ledar not minding her reaction "nurr kicemashi yabar nan kafin inyi something stupid" tafada cikin 6acin rai still bata kalleshi ba Dan jimm nurr tayi sannan tace "Deen bani nan" tafada tana miqomashi hannu Babu musu yaje ya miqamata juices din "Deen kasan abinda kayi baka kyautaba kuwa?" inji nurr tenderly Tura baki yayi yaqara hade gira yace "ni menayi kuma?" "abinda kayi yanzu mana, ka yarfa zee alhalin kai take taimako" inji nurr din "ni ban yarfata ba, cewa nayi abinda tafada ba gaskiya bane ba kuma babu kyau qarya shiyasa na gayamata" yafada cikin son kare Kanshi "amma saboda wa tayi qaryar? Saboda kai nefa, lokacin datazo mutane ne cike a wajen amma babu wanda ya iya cewa komai sai ita ta dauki risk din shigarmaka, kace qarya take basu mareka ba kanada tabbacin da bata tankaba daidai Wannan lokacin bazasu yima abinda yafi marinba? Atleast saikayi shiru kabari sai mun ke6e sannan kace qarya take amma ba gaban kowaba can, ka kunyatata gaban mutanen suji kamar su keda gaskiya" tafada cikin kulawa Shiru yayi kawai amma shima sai yaji badadi kuma yaji beyi daidai ba "sorry" yafada ahankali yana tura baki idanunshi aqasa "bani zaka cemawa ba, ita zakaje kaba hqrin" tafada tana nuna zee da tundazu taqi kallon 6arinsu Kallon zee din data nuna yayi ya 6ata fuska yace "she'll shout" "she'll not, just go apologize, shikenan" tafada affirmably Kamar bazai tafi din ba sai kuma yatafi yana qara 6ata fuska Agabanta yaja ya tsaya yana huhuro hanci da tura baki, ganin ko nuna tasan dashi batayiba yasashi qara 6ata rai yace "sorry" Bata ko motsaba bare ta dago hakan yasashi sake cewa "am sorry" Ganin kamar jine batayi ba don yanzu ma bata motsaba yasashi duqowa saitin kunnenta yace "I said am sorry!" da qarfi Dagowa tayi Saurin yi tana watsa mashi wani kallo hakan yasashi ja baya yana turo baki yace "O'O!" "Duk anubuwan da kayimin bai isheka ba saika hada da dodemin kunne?" tafada tana harararshi "O'O! Nazaci bakiji bane inata cewa sorry" yafada yana yamutse fuska "eh ga kurma ba? Ai dole kace banjiba... Kuma sorry din me zakayi mun? Ni ai na saya da kaina, ina zaman zamana rukky tazomana da zancen gaka can ankusan kashe ka, banma ida jiba na tashi kamar wata mahaukaciya na nufo wajen aguje, dama na sani da cewa nayi suqarama suyima liss" tafada cikin hargowa Dariya su sumee sukayi shikuma ya Kauda kai yana kumburi "dama Wannan ba shine na farko daka kunyatani ba, na farko ka jefani a Mud agaban mutane yanzu ma ka qara tsinkani agabansu daga taimako!" "yanzu dai kiyi hqr tunda yabaki hqr" inji nurr tana Dariya "hqrinshi na banza? Me xanci dashi? Kuma wlh ka qarawa kanka, da nafara hucewa amma yanzu ka da6a don haka yanzu muka fara wasan wlh" Bata fuska yayi yace "O'O! Ni menayi kuma?" "baka san abinda kayi ba? Zaka sanine, bari kaga.." tafada tana bude jakkar littatafan ta tana bincike Wani littafi ta zaro irin mai hard cover dinnan da handout daya ta miqamashi "Gashi, badai aiken ne bakaso ba? Fine, amshi nan" Amsa yayi yana jujjuya littatafan a hannu "wait ma ina littatafan ka inga ya jangos writing dinka yake?" tafada tana zaro daya daga cikin littatafan shi dake aje can gefe tafara dubawa Ajikin bangon littafin tafara cin karo da sunanshi daya rubuta cikin wani unique handwriting _*KAMALDEEN MUHAMMAD*_ dan tsurawa sunan ido tayi tana sake nanata sunan a zuciyarta, _dama Kamal sunanshi?_ abinda ta tambayi kanta kenan. Kauda tunanin tayi a ranta ta bude littafin Sake buda manyan idanunta tayi akan super unique handwriting din littafin wanda beyi kamada wanda hannu ya rubuta ba, Bin rubutun tayi da kallon shagala, ahankali ta cigaba da bude pages din littafin tana kallon the same unique handwriting wanda kallo daya zakamashi kaji ka kamu da sonshi Dagowa tayi ta kalleshi taga haryanzu kumburi yake _ya shi ya handwriting dinshi_ inji wani 6arin zuciyarta Saurin Kauda hakan tayi a ranta ta rufe littafin tana yatsune fuska tace "ba laifi, yanzu kaje da wannan littafin da handout dinnan kayi copying abin handout din daga page 15 inason zuwa gobe dazan amsa kayi pages biyar, understand? Thats your purnishment for embarassing me in public" tafada cikin isa kamar irin tana magana da danta ko qannenta Bece komaiba sai sake pouting din baki dayayi, nurr ce tace "haba zee, this is too much, ki dinga tausayawa condition dinshi mana" Kallon wutsiyar ido tayimata tace "atleast ya godewa Allah nama bashi aikin yi, da yayta zuwa school abanza yakoma a wofi" tafada tana juya idanu "aikaudai zee, nima ga nawa kinga idan yayi naki yau ni sai yaimun gobe" inji sumee Tare nurr da zee suka watsamata wani irin kallo "akan me? Nima ai da dalili nasashi afterall he's mine dama, baxaiyi ba ai ba Bawan kowa bane" inji zee cikin jin haushi Jin hakan yasa nurr dan sakin ranta don harga Allah batajin dadin abinda ake mashi kwata2 yanzu "you can go" tafada tana kallonshi Kallonta ya danyi sannan ya dauki littatafan shi ya hada da wadda tabashi ya wucewarshi. Duk binshi sukayi da kallo kowa da abinda yake saqawa a ranshi *MASTER* Dibar farar powder dake bisa takarda yayi da yatsu biyu manuniya da babbar yatsa yakai hancinshi ya shaqa. Girgiza kai yayi alamun abin ya shigeshi yana bubbuga kanshi da hannu sannan yakoma jagwab a kujera yana sake jujjuya kai Sudai su Alex na gefe suna kallonshi ba damar magana don ko mahaukaci ya lalluba yasan Wannan halin bana magana bane _*ku wadanne irin dabbobi ne!*_ Maganarta tasake dawo mashi a qwanya akaro na ba adadi _*idan ku a jagaliyanci kukafi qwarewa akai why not kutafi tasha ko dandalin qauraye!*_ _*dama kayi Kama da arnan dajin qarnin farko! So don kayi hakan ba wani abu bane*_ _*saidai zee tafi qarfin a ta6a mata koda tip of akaifanta ne, duk wanda yayi gigin yin haka ya shiryama baquntar lahira!*_ Buga table dinshi yayi da qarfi wanda hakan yasa duk suka miqe tsaye kamar dama akan qaya suke "master, master kabani izini yanzu yanzunnan inkawomaka ita gabanka, nikuma nayi maka alqawarin kawota har qasan kaffafuwanka boss" inji Alex yana numfarfashin masu nauyi Dago jajjayen idanunshi master yayi ya saukesu akansu na wani lokaci sannan yafashe da Dariya harda tuntsurawa Duk binshi da kallo sukayi sunaji ajikinsu ta zee taqare don duk wanda yaji Wannan Dariyar yasan bata alhairi bace Saida yayi mai isarshi sannan ya gimtse fuska kamar bashi ba yace "zan gwadamata mu dabbobinne! zan gwadamata mu arnan dajin qarnin farko ne! Zan gwadamata ba iya tip din akaifanta ba kadai zamu ta6a, harta rayuwarta saina tsiyayarmata dashi kuma inzauna lfy! Zan koyamata hankalin da idan ana dawowa duniya akaro na biyu idan ta dawo bazatayi sha'awar ganin kowanne namijiba bare harta daga kai ta kalleshi!" yafada cikin hargowa wanda saida nakusan sakin acawii saboda tsoro🥶 "muna bayanka master! Abinda ya kamata kenan yadda zata zama izina ga duk shege ko shegiyar datayi ko yayi niyyar yin koyi daita" inji gandu shima cikin zazzare idanu Kakkada kai master yayi yana zagaye la66anshi da harshe sannan ya cije lower lip dinshi da qarfi ya sake kallosu da rinnanun idanunshi "waye Wannan gayen?" yafada yana kallonsu still "Gaskiya bamu sanshi ba amma zamu bincikomaka idan kabamu umarnin hakan" inji Bash Kada kai yayi sannan yakoma ya jingina da kujera yace "nabaku, ku naimomin komai gameda shi, idan nace komai.. Ina nufin komai ciki harda alaqarsu da ita, banason ragin komai" "Angama boss!" suka fada atare cikin tabbatarwa "zamugani, zamu gani idan jarumta ta gaskiya ce, zamu gani idan zaki iya tserewa tarko na!" Wayyo zee 😭 *WASHEGARI* Tunda wuri tazo school yau kasancewar yau za'ayi submitting din assignment din mr ibrahim wanda yake amatsayin 20% na jimillan makinsu na subject din. Dama haka takeyi idan ya bada assignment da kanta zatayi submitting don bai amsar aike saidai tana bashi zata tashi tabar class din kuma be ta6a tankamata akan hakaba. Qarfe 9am daidai yace musu zai amsa, sanin beda african time ko kadan yasa students din zuwa da wuri don idan har ya rigaka shiga aji to ka lashe Tun 8:30am ta iso school, direct class ta nufa inda ta tarda aji duk ya hargitse, wadanda basu idaba sai jeka ka dawo suke na ganin sun ida kafin ya shigo. Bata dade da zamaba su sumee sukayi joining dinta banda rukky da itama tanacan tana faffutukar ganin ta kammala nata. Hira sukeyi sama2 rabin hankalinta akan yan class din, tana kallon yadda duk suka bi suka tada hankalinsu Tsaki taja arai, ina amfanin mugunta? Gashi don ita yayi amma gatanan zaune hankali kwance su students din nashi ke shan wuya Tasan itama ba lallai bane taci abin kirki ba amma tana kyautata zaton duk lallacewa dai ta tsira da rabin marks din Wato 10 saidai tanada tabbaci cikin so called students dinsu dawuya quatern cikinsu yakai goman nan, yanzu wa gari ya waya? Garin yiwa wasu mugunta ka afka naka aciki, kodayake yasan abinda ya taka don duk qumu duk yadda students din nashi zasu fadi a Wannan assignment din sunada 30marks dama so haka baxaiyi affecting dinsu ba sosai, dan sakin Murmushin takaici tayi tana Girgiza kai. Agogonta ta duba taga qarfe nawa don hayaniyar ajin ya isheta, gwara yazo ta miqamashi tsiyarshi ta fice Ganin tara saura mintuna sha biyar yasata jan karamin tsaki, tajawo jakkarta da niyyar ciro assignment din tayi going through abubbuwan datayi kafin yashigo. Saidai me? Takardar assignment din tace daukarni inda kika ajiye Tun bata dauki abin serious ba har abin yafara bata tsoro hakan yasata miqewa tareda zazzage dukan abinda ke cikin jakkar bisa desk dinta Batareda ta saurari su deeya dake ta tambayarta lfy? Da guda2 tafara daukar littatafan tana warwarewa tana zazzagewa ko zata ganta ta fado saidai harta gama babu ita ba alamun ta. Tashin hankali da ba'a samaka rana! Komawa tayi jagwab a kujera tana dafe saitin zuciyarta "wai zee lfy? Meke faruwa ne?" inji nurr suma duk hankalinsu ya tashi "innallilahi waina ilaihi rajiun! Nashiga uku ni zainab" tafada cikin Tashin hankali "wai menene zee? Kinafa tadamana hankali" inji sumee Itama cikin Tashin hankali "Assignment dina... Ban ganshiba"tafada cikin yanayin fitar hayyaci Galala sukayi suna kallonta speechless Can deeya tasamu fizgo maganar tace "kamar ya zee? Ina kika ajiye?" Kama kanta tayi da hannu bibbiyu tana nanata innallilahi "dan Allah zee kiyimana magana, ina kika saka assignment din?" inji nurr cikin rawar murya Nuna masu jakkarta tayi don tama kasa magana, bata fatan abinda ke shirin faruwa ya tabbata Dukkansu rufarma jakkar sukayi suka hau bincikata yayinda itakuma tayi suman zaune tana binsu da ido Saida suka bincika suna sakewa kusan sau uku sannan suma suka yarda bata cikin jakkar "ya sallam! Zee wa kika ba?" inji sumee kamar zatayi kuka Qara riqe kanta tayi cikin rudani da Tashin hankali Batareda ta iya furta komaiba "zee kiyi magana mana" inji deeya "wa zanba deeya? Wa zanba? Da hannuna fa na sakata a jakkarnan kuma ban qara budeta ba sai yanzu" zee tafada cikin rudani "To gaskiya da takardarnan na acikin jakkarnan da anganta, gaskiya bata nan, kidai qara tunawa ko kin mantata gida?" inji nurr Dafe kanta tayi da hannuwa biyu tareda lumshe idanu tana fitar da numfashi ahankali Rukky ta qaraso wajen cikin sauri, tana zuwa ta zauna jagwab tana maida numfashi "wai! Allah yayi" tafada tana maida numfashi Ganin dukkansu a moody state yasata dan shan jinin jikinta "yadai?" tafada tana binsu da kallo Duk shiru sukayi an rasa mai iya magana "wai lafiya? Meke faruwa ne?" tQara tambaya tana dan Wara idanu Deeya ta sauke ajiyar zuciya sannan tace "rukky assignment din zee ne ya 6ata" Kwalalo idanu rukky tayi cikin firgici tace "wane assignment?!" "wane bayan Wannan na mr ibrahim?" inji sumee "innalillahi waina ilaihi rajiun! Garin yaya? Ina kikasashi zee?" tafada tana maida akalar tambayar ga zee Kasa magana zee tayi sai qara tamke kanta datayi tana lumshe idanu "cewa tayi a jakka amma babu neman da bamuyiba amma babu shi" inji nurr Tashi itama rukky tayi ta zazzage komai na jakkar ta watsasu amma babu shi ba alamun shi Duk abinda sukeyi babu wanda ya lura dasu don kan kowa ya dau zafi kowa takanshi yake "innalillahi, zee wa kika ba? Ki tuna please" inji rukky cikin damuwa Watsa hannunta zee tayi alamun batasaniba don magana ma wuya take mata, ita kadai tasan yadda takeji "kiyi tunani sosai zee, ko kin barta agida ko wani wajen, kiyi tunani sosai" inji rukky Riqe kai tayi tana dan yamutsawa alamun tana son tunanowa "yauwa zee ki tunano tabbas ko tana gida ko kin ba wani" inji nurr Cigaba da yamutsa kanta tayi idanunta lumshe, can saita tsaya cak da abinda take ta bude idanunta da sauri "yaya???" suka hada baki suka tambaya cikin sauri "Oh my Goodness!!!" tafada tana komawa jikin kujera yaraf "menene? Halan gidan kika barota din" inji sumee Dagowa tayi da idanuwanta dasuka duri ruwa tace "da agida ne bada yafi sauqi ba atleast nasan kiran waya kawai zai biyamin buqatata amma Wannan banidama tabbacin yanzu akwaita" ta qarashe tana dafe kai "me kike nufi da hakan?" inji deeya "ya zanyi? Tana wajen wancan gayen" tafada cikin rawar murya alamun kukan na kusa "wane gaye?" suka hada baki wajen tambaya "Deen mana!" tafada tana bubbuga goshinta "DEEN!!!" suka hada baki a mugun mammakince Hawayen datake riqewa tundazu suka xubomata tace "takardar nacikin littafin dana bashi jiya yayimin note, am doomed!" tafada tana Hawaye sosai Galala sukayi suna kallonta sun kasa cewa komai "yanzu ya zanyi? Am perfect sure ya jefar daita cikin haukanshi ko ya yagata, Oh my God why am I so unlucky?" taqarashe tana Fashewa da kuka Hakan yaqara sanyaya jikinsu saidai kowanne yarasa me xaiyi ko zaice don tabbas idan har takardar nan na wurin Deen to tazama sheqaqa tuni "zee kibar kukannan haka nan please" inji nurr cikin sanyin murya "inbarfa kuka kikace, kinsan me hakan ke nufi? Hakan na nufi i've lost the 20% for good!" tafada cikin kuka "kar kice haka zee, tayiwu tana nan, kawai abinda yakamata shine muje mu sameshi da muzauna muna qara wasting time, kinga 9 saura minti 10 yanzu munada minti 10 left" inji nurr Kamar wadda aka tsikara tayi zumbur ta tashi tana cewa "muje please" Suma tashi sukayi suka maramata baya suka bar sumee na tattara abubuwan cikin jakkar zee dasuka watsar tana maidawa Direct wajen zamanshi sukayiwa tsinke amma babu ko alamun shi, class dinsu suka wuce kasancewar su deeya sunsan class dinsu saidai mutanen da suka iske a class din basufi goma ba, da suka tambaya sukace basu ganshi ba dakyar ma idan ya iso don yau lecture din 12pm garesu. Tashin sense! Yawo iya yawo sunyi, babu inda basu zagayaba a school din amma babu mai ko Kama dashi, zee banda dauke Hawaye babu abinda take, danasanin bashi aikin rubutun take sosai tanaji kamar ta maido hannun agogo baya saida suka gaji sosai sannan suka ja gefen wani class suka tsaya suna maida numfashi Kallon agogo deeya tayi "guys saura minti 4 fa" "yanzu ya za'ayi? Deen dai baya makarantar nan wlh" inji nurr "kawai mukoma class karya shigo bamunan" inji rukky "zee kiyi hqr kizo mutafi" inji sumee Share hawayen fuskarta tayi tace "inje ina? Idan naje me zanyi? Kawai ku tafi" "haba zee? Kitaho please, idan mukaje saikiyi mashi explaining" inji deeya Murmushin takaici tayi taqara share hawayenta tace "bazaku ganeba, ku tafi kawai" Shiru sukayi kuma suka kasa tafiya "kutafi karku 6ata lokacin ku a banza ayi biyu babu" tafada tana jin zuciyarta na suya sosai Badon ransu yasoba kodayake idan yaso ma ba ganewa za'ayi ba suka juya suka tafi jiki a sa6ule Zamewa tayi wajen ta tsugunna ta rungumo qaffafunta sannan ta cusa kanta a tsakankanin cinyoyinta tana kuka marar sauti... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:32 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *012* _hhhh mutane nata complain wai sanyin Deen yayi yawa, To ni bansan ya zanmaku ba, Wannan labarin na riga na tsarashi tun kafin nafara rubutashi, yadda tsarin yake haka nake bi dashi kuma karku manta akwai ire iren Deen a real life wadanda keda irin Wannan halayyar kuma suna fuskantar wulaqancin mutane babu yadda suka iya, so kuyi hqr afterall duka duka yaushe aka fara novel din? Wannan farko farko ne kuma bamuda tabbacin haka za'aita tafiya, so please exercise patience, I don't like the way you guys are complaining, idan kuma kunaso muyi rushing abinne, fine🤷🏻‍♀️_ Yanzu shikenan tayi loosing din 20% dinnan kenan? Dukda tasan ba duka zataciba amma tasan ko yayane dan mark din dazata samu zai dan taimaketa ko yayane, loosing dinshi is like a bad starting, alamu ne na faduwarta. "Deen where are you? Please show yourself" tafada under her breath tana sake cusa kanta a cinyoyinta "Mud queen!" taji anfada kamar daga sama Cak kukan datake marar sauti ya tsaya tana bude idonta dake cikin cinyoyinta "Mud queen!" Taqara jin anfada akaro na biyu Saurin dago kanta tayi idanunta suka sauka a nashi hakan yasata tashi azabure Yadda ta tashin ne yasashi dan ja baya yana kallonta Wani Murmushi yatahomata tareda hawaye "OMG Deen, ina ka shiga ka kusan sani hawan jini?!" tafada cikin yanayin fitar hayyaci Bece komaiba sai kallon daya kafeta dashi ganin hawaye a fuskarta, abinda be ta6a gani ba tunda yasanta "ina littatafaina?" tafada tana wartar littatafan hannunshi Batareda ta tsaya jiran amsarshi ba Cikin sa'a kau nata ke asama, jiki na rawa tashiga bubbude page pages din da sauri sauri jikinta sai 6ari yake kamar wacce ke a fridge, hakan yasa ta tsallake inda takardar take Batareda ta lura ba Koda tagama bubbudewa taga babu ta dauki handout din shima tashiga bubbudewa saidai shima babu takardar "as I feared!" tafada tana dafe kai wasu hawayen na zubomata "why are you crying?" taji yafada calmly yana kallonta da pure white eyes dinshi Dagowa tayi ta kalleshi da rinnanun idanunshi, jitake kamar taita kwala ihu Dakyar ta saita muryarta tace "ina ka yardamin takarda?" "wacce?" yafada yana Wara mata oily idanunshi "the damn paper I put here!" tafada cikin qaraji tana nuna littatafan ta Bata rai yayi yana kallonta Batareda yace komaiba "dakai fa nake!" tafada a qule "O'O! Must you shout?" yafada yana kumburi "me kake son nayi To?! Gabadaya ka lallatamin komai..." Ganin yabude littafin ya zaro wata paper a tsakiyar littafin yasa kingin maganar maqalewa "This?" ya tambaya yana miqamata Kwacewa tayi da sauri tareda warwarewa Sama sama tayi going through dinta taga itace hakan yasata gasping in excitement "OMG! Itace!" Saurin duba wristwatch dinta tayi, 1min to go Bata bi takan Deen ba kuma ta rataye jakkarta ta nufi class dinsu cikin sassarfa gabanta na dukan uku uku. Cikin sa'a kau bekai da zuwa ba hakan yasata saurin shiga tana saukar da ajiyar zuciya Su sumee sunyi mammakin ganin shigowarta saidai kafin suyi wani yunquri har mr ibrahim ya shigo Hakan yasa zee neman wuri ta zauna gaba gaba Batareda ta qarasa wajensu sumee ba Duk tashi akayi ana gaidashi including zee saidai ita tashin kawai tayi amma bakin ko motsi beyi ba. Cikin takun izza yafara takowa tsakiyar class din yanabin kowanne student da kallo, dayake yau da biyu ba lecture kawai za'ayi ba, class din yacika maqil Jin kamar ana kallonta yasata dagowa idanunta suka fada a nashi Saurin fizge nata idanun tayi ta saukesu qasa gabanta na tsinkewa haka kawai zuciyarta ta bata Wannan kallon ba normal kallo bane na tsana daya saba yimata, abayan Wannan ta hango wani wanda yayi kamada ta manufa "sit..." yafada cikin bada umarni Hakan yasa duk suka zazzauna, class din yasake daukan deadly silent "yeah... Today I noticed class dinmu yaqara cika, guess akwai reason behind this" yafada yana Murmushi Class din ya dauki qananun qananun surutai wanda baka iya sanin abinda ake cewa "silent!!" yafada authoratively don kawo shiru a class din, aikau nan da nan class din yadauki shiru Itadai zee batayi kwakwarar motsi ba tundazu burinta kawai ya buqaci takardar shi tabashi taqara gaba "well koma menene, we shall see" yafada yana zama kan desk din gaba yana facing dinsu "hope kowa na riqeda assignment dinshi?" yafada yana Bin kowa da kallo Wani mumuring din yasake tashi kamar dazu. Yanzu ma saida yakira order sannan akayi shiru "well, koma baku riqe ba ba tawa matsalar bace, just know that 20% of your exams marks ne sukabi iska" Nanma surutanne suka qara tashi saidai kafin yayi nisa yaqara takamusu burki sukayi tsit "is better you keep quiet and listen, meye na hayaniya, if you pass you pass hakan if you fail you fail, simple! You cant plant pepper and harvest onions, you reap what you sow, so kowa ya fiddo assignment nashi" Dumm.. Gaban zee yafadi daidai kalmar qarshe na mr ibrahim. Wani abu yashiga dawowa zee a kwalwa yana mata gizo. The handwriting... Yes! Tabbas taga handwriting din... Amma a ina? Lumshe idanunta tayi ta bude su cikin son tunano abinda ketayimata guje guje a kwalwa Handwriting din... The unique handwriting... Taganshi a wani wuri... Ina? Sake lumshe idanunta tayi _*ZAINAB FAROUQ DAN FARANSHI*_ cak! Brain dinta ya tsaya daga aiki na wucen gadi Yes, haka tagani anrubuta da unique handwriting din, sunanta aka rubuta _a ina?_ tambayar datayiwa kanta kenan Gabanta ne yasake yankewa ya fadi har saida tadan dafa chest dinta _No.. No.. No! It cant.. be_ abinda tafada a ranta kenan Saurin bude jakkarta tayi tareda zaro takardar da ta amso hannun Deen yanzu hannu na 6ari tashiga warwarewa tama manta a class suke Turus.. Tayi ganin abinda zuciyarta ke fargabar gani Handwriting dinshi ne, ba nata ba! Ya chanza mata rubutu, ya chanza! Going through din content din paper takeyi hankali tashe, komai ya chanza, kwata2 Wannan ba aikinta bane ba calculations dinta bane "now start submitting!" taji muryar mr ibrahim na cewa haka Dagowa tayi taga yana row din farko yana amsar takardun da guda guda Saramata kanta yashiga yi tanajin kamar roof din classroom din na jujjuya mata Fasalta maku halin data shiga a Wannan lokacin ba mai yiwuwa bane , ita kanta bazata iya misalta halin data tsinci kanta aciki ba Kawai dai azahiri zaune take kamar kowa paper a hannu amma ita kadai tasan abinda zuciyarta ke going through. Batasan tsawon lokacin data dauka ahaka ba sai jitayi daga sama ana cewa "yes? Your assignment miss" Dagowa tayi ta ganshi akanta fuskarnan murtuk Kallon gabanta tayi taga duk babu students din gabanta alamun duk sun bada sun fice Sai wadanda ke bayanta da ba'a kai wajensu "mallama you're wasting my time!!" inji mr ibrahim atsawace hakan yasa tayi Saurin jerking back to life Hannu na dan kyarma ta bashi takardar ya amsa yana jan guntun tsaki tareda yin gaba Jitayi classroom din na cigaba da juyamata hakan yasata Saurin miqewa ta jawo jakkarta ta nufi hanyar waje tana hada hanya. Suma su sumee saida sukayi submitting sannan duk suka fito waje. Waige2 suka shiga yi na neman inda zasu hangota, ganin basuga ko 6il6ishinta a wajen ba yasasu nufar usual mazauninsu dake bayan classes. Tun daga nesa suka hangota zaune kai hade da gwiwa, basu kawo komai aransu ba suka ida qarasowa wajen. Zazzaunawa sukayi nurr tace "ya dai? Kin samu Deen dinne halan?" Ko motsawa batayi ba bare ta dago "zee?" Nanma shiru "zee wai lfy?" inji sumee tana dago kanta Kwacewa tayi tasake maida kan akan gwiwowinta "she's crying fa" inji sumee tana kallon sauran Dawowa kusada ita duk sukayi suka sata tsakiya "zee wai lfy? Bakiga Deen dinbane?" inji deeya "To amma ai tayi submitting" inji rukky "da wannan yar iskar takardar danayi submitting ba gwara banyi exam dinba gabadaya ba?!" inji zee data dago afusace fuska jage2 da hawaye Duk Tsayawa sukayi suna kallonta sannan nurr tace "bamu ganeba" "dama tayaya za'ayi ku gane?! Wancan lunatic fring din ya chanzamin takarda ya jefar da wancan ya chanzamin da nashi dake cikeda hauka!" saikuma ta dafe kanta hawayenta na qara gudu "mene? Kiyimana gwari2 yadda zamu fahimta" inji rukky "bayan kun tafi na ganshi kuma na amshi takarda only to realised that he changed my paper at the deadly time! Nace mashi ya ta6amin takarda ne? Ko na bashi ajiya ne dazaiyimin tempering da ita, duk ya sauya calculations dina ya sanya nashi na hauka!" tafada cikin tsananin bakinciki "kutt! Kina nufin aikin Deen kikayi submitting?" inji rukky sai kuma tafashe da dariyar da bata shiryaba don can ta hango Deen ya zauna ya daddage yana mata lissafin hauka a paper Sosai dariyarta taqara tunzurata hakan yasata miqewa a fusace tace "yes, Dole kiyi Dariya mana tunda ba akanki abin yafaru ba, I won't blame you, am to be blamed most!" tafigi jakkarta tayi gaba fuuu Kallon rukky da tabar Dariya duk sukayi sannan suka ta6e baki suka marama zee baya leaving rukky behind, daga kafadu rukky tayi ta koma ta zauna saikuma tasa Dariya tana imagining face din mr ibrahim idan yana marking, he'll be like anya script dinnan bana psycho nake marking ba, hakan data hasaso yasata qara Fashewa da wata dariyar. Zee kau tafiya take amma kallo daya zakamata kasan cewa a mugun fusace take kuma bala'i na cin zuciyarta don fuskarnan dinke take d'ab, su sumee kau na bayanta suna binta amma sun kasa taddota kasancewar tafiyar tata ta fusattatu ne ba yanga aciki Tun a nesa suka hangoshi zaune a inda yasaba zama shikadai riqeda littafi yana dubawa sai lemun coke na can dayake dan korawa akai2 Bata ja burki a koina ba sai agabanshi, kafin ya dago ta fizge littafin hannunshi tayi flinging dinshi. Saurin miqewa tsaye yayi yana kallonta "kai wane irin daqiqi ne?! Nace kai wane irin daqiqi ne!!" Bata jira amsarshi ba ta fizgo can din coke dinshi, beyi auneba sai jin sanyi yayi ya ratsashi a qirji dama duk gaban jikinshi Jan wani irin wawan numfashi yayi Kanshi na saramashi a lokaci daya "zee!!!" nurr tayi exclaiming Bata saurareta sai cigaba da cewa "how dare you temper with my work? How dare you!!" Kanshi ne yaqara sarawa sosai, dagowa yayi ahankali ya sauke fararen idanunshi da izuwa yanzu sunyi jajur akanta "I said how dare you!" tafada tana daga hannu da niyyar marinshi Carraff taji an cha6e hannu ya maqale akan iska Kafin ta tantance komai taji an dauketa da wani bahaggon mari... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:32 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *013* Wani irin spark kanta yayi taga wuta ta gilma mata a idanu, baya baya tayi su sumee dake bayanta sukayi Saurin tareta. Dagowa sukayi baki sake suna kallonshi kowannensu ya kasa gasgata abinda yafaru yanzu Riqe Kanshi dake barazanar rabewa gida biyu yayi da hannu biyu yana groaning Dago rinnanun idanunshi dasukayi mugun runewa yayi ya watsamasu nan take jikin kowaccensu yafara 6ari Ganin ya nufosu gadan2 yasasu Saurin duqewa suna curewa wuri guda suna sakin qara Naushi yakaima iccen wurin yana sake wani gurnanin, nan da nan hannun yafara jini Sake dafe kai yayi da dayan hannun marar ciwo yanajin hajijiya na dibarshi, duk jijjiyoyinshi sun tashi rudu2 gasunan kana gani 6aro2. Dagowa zee tayi tana kallonshi tana maida numfashi da sauri2 Juyawa yayi yafara tafiya cikin hada hanya kamar dan maye, hannunshi kau izuwa yanzu yariga ya wanke da jini Beyi nisaba wani mugun jiri ya kwasheshi ya zube a wajen. Wata iriyar qara nurr ta kwala ta tashi ta nufeshi dagudu. Cikin kuka ta birkitoshi tana kwala kiranshi amma ko motsawa beyi ba "shikenan, kin kasheshi! Kin kasheshi da mugun halinki!" inji nurr cikin kuka Tana zaune a wajen takasa motsi sai kallonsu datake kamar doluwa, everything just happened so fast that takasa figuring a mafarki take ko zahiri. Tana nan inda take taga mutane sun taho wajenshi da alamu su sumee suka kirasu. Tana kallo aka daukeshi suka wuce dashi duk akabar wajen aka barta ita kadai in her sitting position kamar statue 💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖 "Daughter!!" taji hakan kamar daga sama ana girgizata Firgigit tayi ta dawo daga duniyar tunanin data lula ta dago tana kallon daddy dake kusada ita da alamu shine ya girgizata sai takuma maida kan mummy da itama tayimata quri tana kallo. "Wai lfyarki lau kuwa Daughter?" inji daddy yana kallonta keenly Lumshe idanu tayi ta bude kawai sannan ta dauki fork dinta data ajiye tundazu don tama manta a dining take tariga ta lula duniyar tunanin da tasaba a yan kwanakinnan. "magana fa ake miki" inji mummy tana kafeta da idanu Dagowa tasakeyi Wannan karon idanunta sun duri ruwa Ganin hakan yasa daddy Saurin kamo hannunta yana cewa "ya sallam! Wai Daughter meke damunki ne ko haryanzu jikin ne?" Dagamashi kai tayi ahankali hawaye na sakkomata "To gaskiya hospital zamu koma, ace fever haryanzu bata sauka ba? Tunfa ranar wednesday kika dawo haka amma haryanzu babu sauqi dukda magungunan da kikesha? Gaskiya we have to do something" yafada yana zaro wayarshi Sunajinshi ya kira family doctor dinsu yana mashi complaining akan haryanzu dai jiya iyau zee fa bata warwareba, basu ji me akace ba a dayan bangaren sukaji yace gobe kawai zasu zo tunda yanzu dare yayi yafison suje hospital din ayimata aune2 tunda treatment din gida yaqiya. Da haka sukayi sallama akan goben insha Allah suna nan tafe. Itadai zee zagaye abincinta take da fork tana saurarenshi hakama mummy wadda bata tofa komaiba don ita tasan Wannan ba fever bane akwai dai abinda ke damunta bayan Wannan. Cigaba da kwantarmata da hankali daddy yayi akan insha Allah gobe koma meke damunta za'a gano kuma za'a maganceshi insha Allah. Batace komaiba sai narkemashi datayi a kafada tana 6ata fuska ashagwa6e. Wurin barci ma yau kamar yan kwanakinnan neman barcin tayi ta rasa, juye juye kawai take tarasa abinda ke mata dadi. Abubbuwa ne suka taru sukayi mata cinkis a rai Nafarko baqincikin faduwar da zatayi a assignment wanda hakan na nufin ta rasa 50% na marks idan aka hada da wancan 30% din na attendance Na biyu 6acin ran Marin da Deen ya wankamata wancan ranar just because ta nunamashi 6acin ranta akan 6arnar da yayimata, a dakeka a hanaka kuka? Ita yayi mawa amma shi yafi reacting? Na qarshe kuma halin da aka tafi da Deen ranan, cikin wadannan Abubbuwan Wannan yafi yimata bake2 arai, badon tanajin laifinta ne ba Kawai haka kawai takejin abin ya tsayamata ya tsayamata a kwalwa takasa yakice hakan a kwalwar ta A cikin yan kwanakinnan, datayi jigim ta fada duniyar tunani to incident din take tunawa, batason ta yarda dacewa ta damu akan hakan, batason ta yarda cewa tanason sanin halinda yake ciki yanzu, dukda kau yadda zuciyarta ke azalzalarta akan haka, gani take ita yaiwa laifi why kuma zata damu dashi? Hakan ba qaramin sake dagula mata lissafi yake ba. Tashi tayi zaune ta jingina da jikin gadon tareda folding hannayenta a qirji, kafe waje guda tayi da kallo yayinda fuskar Deen a lokacin da ya burkuce tashiga yimata gizo. _meya faru dashi a Wannan lokacin?_ _fushi yayi? Dama ance masu sanyi basu iya fushi ba ko?_ _meya sashi fushin to? Zagin ko tsawar ko watsamashi coke din datayi?_ _koma wane ne aciki ai hakan be isa har yasa yayi collapsing ba_ _kuma ai duk laifinshi ne, da bai ta6amata kayaba da duk hakan be faruba_ _yanzu a wane hali yake ciki? Is he ok or not_ _meyasa tunaninshi yaqi barin brain dinta, meyasa?_ Haka taita karatun jakinta har barci yayi nasarar saceta can cikin dare. Washegari kamar yadda daddy yace haka yakaita hospital din dakanshi kasancewar ranar lahadi ne baya fita a ranar. Asibitin kudi ne data amsa sunanta don ga yanayin zubinta ma kasan bana qananun mutane bane. Kasancewar dama doctor yasan da zuwansu nan danan ya karbesu yashiga yimata aune2 kamar yadda daddy ya buqata don gano ainahin abinda ke damunta Duk gwaje2n dayayi be lallubo abu guda dake damunta ba hakan yasashi kawai rubuta musu wasu magunggunan na pain relieve yabasu dakuma basu tabbacin zata warware qila fever dinne be ida sakinta ba Koda suka fito daga hospital din maimakon suyo gida sai suka wuce yawo inda yaita yawatawa da ita parks parks da wajajen shaqatawa. Sosai hakan ya taimaka wajen lifting din mood dinta don sosai nauyin datakeji a qirjinta yaragu. Saida ya tabbatarda tadan warware sannan suka koma gida bayan sunyi sayayyar kayan zaqi dayawa daga parks din Aranar a kula da zee daddy ya lallace don tare sukayi yinin ranar yana debemata kewa, itadai mummy tazama yar kallo don tunda ta lura dakwai abinda ke damunta tayi2 ta gayamata ta qiya ta shareta. Ta lura zee bata sakin jiki daita kamar yadda 'ya takamata ta saki jiki da uwarta, hakan ba qaramin damunta ba yake amma tarasa yadda zatayi don zee din zumace saida wuta, koyaya ta sake mata zaqalqalewa take bayan haka kuma zee tariga ta Tsorata da ita duk yadda takeson ta dan jawota jiki sai tayi ta baya2 daita don sosai take shaqqarta wanda hakan yasamo asaline daga tsoron dukanta datakeyi don zee bata qaunar abinda zai ta6amata lfyar jiki hakan yasa take baya2 daita babu shakuwar nan ta uwa da 'ya atsakaninsu. *WASHEGARI* Yau monday kuma tayi shirin zuwa school wanda tun wancan wednesday din bata sake zuwaba Jiki a sanyaye tayi shirinta inda tunnanika kala2 ke kai kawo a brain dinta saidai wanda yafi kowanne rinjaye shine nashi, dukda batason gasgata hakan tasan babban dalilinta na zuwa school din shine azalzalarta da zuciyarta keyi nason sanin halinda Deen ke ciki. Abin har mammaki yake bata na yadda ta damu dashi dubada yadda takeda I don't care mana nata ta6a zaton zata ta6a damuwa da mutum irin Deen ba. Dakyar dai tasamu tagama shiryawa tafito tashiga dakin mummy don yimata bankwana Saida mummy ta tabbatar da taci abinci sannan tayimata addu'ar dawowa lfy bayan ta kashemata warning din data gama abinda takeyi ta kamo hanyar gida A harabar gidan ta iske bala wanda ganinta yasashi Saurin budemata kofa tazo tashiga yamaida yarufe sannan ya zagaya nashi mazaunin ya zauna, cikin yan sakkani motar ta halba kan kwalta. *** Fitowa tayi daga motar bayan yagama gyara tsayuwarshi a parking space din, sanya shade dinta tayi ta rataye handbag dinta sannan tabi hanyar dazai sadata da department dinta cikin tafiyar ta daya riga ya zamarmata jiki. Kasancewar sunada lecture din safe kuma sauran yan mintuna afara yasata nufar class direct. Koda tashiga students kadan ta iske kuma duk ciki babu wanda takema magana hakan yasata samun mazauni ta zauna. Zaro wayarta tayi tana danne2 saidai ko za'a shaqeta bazata iya fadin abinda takeyi da wayar ba don hankalinta kwata2 ba tareda ita yake ba yalula can inda yasaba lulawa a yan kwanakinnan. Ahakan ne taji an dafa kafadarta, dagowa tayi taga su sumee ne tsaitsaye kanta hakan yasata dan yatsine fuska irinta basarwa tana gyara zama Duk samun wuri sukayi kusada ita suka zazzauna sai alokacin ta lura da yadda class din yadan qara cika. "barka zee, yau agari inji maqi baqo" inji deeya Qara dan yatsine fuska tayi kamar bazatayi magana ba saikuma tace "humm" "kwana dayawa zee harmun fara tunanin zuwa duboki ga layyukanki duk basa shiga" inji sumee "uhm am not available ne" ganin yadda take amsamusu a daqile yasasu jan bakinsu sukayi shiru don sun lura yau yan wulaqancin na bisa kai Ita dama nurr bata tankaba don haryanzu tanajin zafin abinda zee tayiwa Deen dukda taso barin zee tafita daga cikinsu saikuma taji bata iyawa don zama da zee babban alhairi ne don zee din tayi ta fannuka da dama, barta da wulaqancin ta da rashin kunya amma a bangaren bude hannu da facaka da qawaye ba'a magana, gashi tarayya daita yasa ta chanza sosai ta koyi abubbuwa da dama na classic girls inda yanzu a unguwarsu batajin akwai wanda yafita gayu da suna, wadannan abubbuwan yasata jin bata iya rabuwa daita yanzu dukda kau mugun haushinta dake danqare a zuciyarta. Ba'a jimaba lecturer din dazaiyi basu darasi yashigo yafara abinda yakawoshi Saida sukayi 40mins a lecture din sannan suka fito kowanne yakama gabanshi yayinda su zee suka nufi mazauninsu. Tana jinsu sunata labaransu taqi tankawa kowa acikinsu dukda suna dan sanyota aciki, burinta kawai suyi magana akanshi ko zata dan samu haske akan abinda zuciyarta ke mintsininta akai, amma kamar sun sani babu wanda ya dauko zancenshi hakan yasata jin ranta yaqara jagulewa Ana haka taji deeya tace "zee bakizo ranar friday ba bayan kinsan ranar mutuminki zai raba assignment" Ranta ne yaqara 6aci saidai ko Dagowa batayi ba bare ta nuna alamun taji "To anraba saidai be bada nakiba wai idan kinzo kizo kisameshi a office" Sai a sannan ta dago ta kalleta, kamar zatayi magana saikuma tafasa ta maida kanta ga phone dinta datake huce haushi akanta ta hanyar danna. Ganin haka yasa suma suka fita batunta suka shiga discussing din marks dasuka samu inda duk babu wanda marks dinshi yakai goma dga mai 2 sai 5 sai 4, nurr cema tasamu 7. Nan sukaita labarin su suna zazzaginshi wai ai dama baso yake suciba shiyasa ya sakamasu mugunta don wlh ba don yahada da mugunta da sunci Itadai zee jinsu take yayinda take tunanin nata makomar, ko tantama babu gani yayi haukan yayi yawa shiyasa yakeson tazo har office dinshi yaci mata mutunci yadda yaga dama, yakuma yimata gori akan yadda tacika baki a wancan karon gashi ba'aje koina ba tafara sacewa. Ana haka wani saurayi yazo wajen yayi musu sallama. Saida sukayi mashi kallon up & down sannan suka amsa adage itakau zee ko Dagowa batayi ba abin da ya dameta ya dameta Saurayin da shima bada son ranshi ba yazo wajen yayi facing din zainab da haryanzu kanta ke kan wayarta yace "Zainab Farouq Dan faranshi, mr ibrahim yace nace kizo" Sai a sannan zee ta dago tana kallon saurayin a dage kamar yadda sauran sukayi mashi saikuma ta watsar "dake nake mallama" yafada yana jin haushin kallon dasuke binshi dashi, dama idan ba qaddaraba mexai kawoka majalissarsu duk abinda sukayi maka kai ka siya. "mallam tunda ka isar da saqonka ai sai kaqara gaba ko? Tajika ai" inji deeya tana yatsina Kallonta yayi yace "ai nasan da haka mallama, cewa yayi nazo qafata qafarta" Sai a sannan zee taqara Dagowa ta kalleshi, zatayi magana saikuma tafasa haka kawai yau taji magana ma wuya take mata don damuwa da baqin ciki dasuka taru sukayi mata katutu arai. Batace komaiba ta miqe ta rataya jakkarta sannan tayi gaba, ganin haka ya take mata baya don cika umarnin mr ibrahim. Rakasu da kallo sukayi sannan suka kalli juna suna ta6e baki "antafi amsar zero over kunnuwa" inji deeya tana Dariya "kedai bari, ai shiyasa tundazu take wani cicin magani, tasan abinda ta taka ai" inji rukky tana ta6e baki "ai dama Allah ba azzalumin kowa bane, gashi ta gina ramin mugunta ta zurma aciki, shiyasa akace ka kiyayi mutum especially ire iren Deen don baka ta6asu ka wanye lfy, gashi yanzu tafara gani ai" inji nurr "Zata dai fara gani, ai wlh naji dadin yadda Deen ya kashe yar banza da mari rannan, bawan Allah ko yaya jikinshi?" inji sumee "da sauqi ai ko yau kafin na shiga class saida nabiya department dinshi na tambayi Wannan friend din nashi yace min da sauqi sosai maybe ma cikin week dinnan yadawo school" inji nurr "To Allah ya sawwake kuma Allah yasaka mashi" inji deeya Da amin duk suka amsa haushin zee daqare da zuciyarsu, dama yaya lfyar giwa? Da sallama tashiga office din saurayin na biye daita. Amsawa yayi Batareda ya dago daga abinda yakeyi ba sannan ya sallami saurayin akan yana iya tafiya. Juyawa yayi ya fita hakan yasa mr ibrahim Dagowa ya kalleta sannan ya nuna mata seat alamun ta zauna. Kamar bazata zauna ba sai kuma taja kujerar tazauna a dosane tanajin kamar ta cire zuciyarta ta yar ta huta da nauyin datayi mata. "nasa agayamaki idan kinzo kizo ina nemanki, saqon ya isa gareta?" injishi yana yan rubuce2 Dagowa tayi ta kalleshi saikuma ta Kauda kai ganin shima na shirin Dagowa "A'a" tafada a taqaice Jingina kai yayi sannan ya turomata wata folded takarda a gabanta yana komawa ya jingina da kujera yana dan jujjuyawa Kallon takardar tayi sannan ta kalleshi zuciyarta na qara quntata Nuna mata takardar yayi da idanu alamun ta bude, ganin tayi jimm tana kallon takardar yasashi cewa "open mana" Hadiye wani yawu mai daci tayi sannan ta miqa hannu tafara warware takardar, zuciyarta na bugawa har wani jiri2 take gani, tasan ta fadi amma ganin abinda taci din ba qaramin affecting dinta zaiyi ba, taso kawai atafi ahaka Batareda tasan me taci dinba ko ba komai tayi preventing kanta from heart attack. Ida warware tayi cikin qarfin hali tana jan numfashi ahankali sannan ta kalli takardar. Ahankali manyan idanunta suka fara qara girma harta ida kwalalosu akan takardar tana kallon takardar with greatest shock rubuce a fuskarta. Dagowa tayi ta kalleshi sannan takuma maida akan takardar tana jin jikinta na tsuma don shock "waye yai miki?" taji muryar mr ibrahim kamar daga sama Hakan yasata qara Saurin dagowa tana kallonshi "yes, ni dake munsan ba ke kikayishi ba, tell me who helped you?" Kasa amsamashi tayi sai kafeshi da idanu datayi wanda azahiri batama san tayi ba, tunaninta ma tuni yayi qaura daga jikinta ya lula can "magana nake miss kin tsareni da idanu" yafada yana dan buga table Hakan yasa tadawo daga duniyar datake shirin dulmiyawa ta kalleshi "so ta Wannan hanyar kika biyo? Kince zaki iya amma kika nemi taimakon wani? I thought dakanki zaki iya din, Wannan ya nuna gazawarki qarara" yafada yana watsamata kallon raini Dafe kanta dake mugun saramata tayi ta gangaro da hannayen kan fuskarta ta rufe. _ya sallam! What have I done?_ _why.. Why.. Why_ Abinda ke yawo aranta kenan Shi mr ibrahim dayayi tunanin tashiga Wannan halin ne don ganotan dayayi yace "don haka this paper is on suspense, a qaida dama duk wanda yaci irin marks dinnan musanmman idan ana tantama akan marks din saiya sake yin wani don shafe tantanmar ko kuma ayi cancelling din abin gabadaya... Ke wanne yayi miki? Kin yarda zaki sakeyin wani agabana domin shafe tantama na ko kin yarda kinyi malpractice a cansile?" yafada yana kallonta Ta dade bata ko motsa ba kuma bata cire hannayenta daga fuska ba hakan yasashi qara cewa "mallama am talking!" Sai alokacin tacire hannayenta daga fuskarta, idanuwanta sunyi jawur saidai ko digon hawaye babu a fuskarta Kallonshi tayi da bloodshot eyes dinta sannan ta lumshe idanu ta bude Ahankali cikin cracking voice tace "fix the date, zan.. Chanza wani" Dama yasan amsar dazata bashi kenan don bata Saurin accepting defeat, ego dinta bazai bariba. Hakan yasashi cewa "next week monday, exactly irin wannan lokacin" yafada yana duba agogo "Thank you" tafada ahankali sannan ta miqe dakyar tanajin haryanzu kanta na sarawa. Hanyar waje tayi tana dan hada hanya hakan yasata rakata da kallo harta fice sannan ya ta6e baki yana daga kafadu ya cigaba da abinda yakeyi. Tafiya take Batareda tasan inda take tsoma qafarta ba, jin tafiyar na neman gagararta yasata samun wani icce ta jingina dashi sannan ta sulale ahankali ta zauna qasa. Ahankali taqara dago takardar tana binta da kallo, ahankali rubutun yafara yimata dishi2 sanadin ruwan daya taru a cikin idanunta, kifa takardar tayi a fuskarta daidai da 6allewar hawayenta... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:32 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *014* Batasan tsawon lokacin data dauka ba ahakan sai jitayi an dafata hakan yasata tsagaita kuka marar sautin datake ta dago ahankali. "ya sallam! Zee lfy?" inji su sumee dama jin shirun yayi yawa yasasu Bin sahu sai ganinta sukayi can jikin wani icce cure wuri guda "haba zee Wannan ai ba girmanki bane kuka in public ba, idan wani yaganki fa? Hakan ba qaramin zubda m bane" inji deeya tana kamota suka miqar daita tsaye "komai yayi zafi maganinsa Allah, menene don bakici Wannan ba? Insha Allah zaki fanshe a exam" inji rukky cikin yanayin tausayawa Dagowa tayi ta kallesu da rinnanun idanunta da sukayi ja sosai saboda kuka, ahankali ta motsa bakinta tace "ina.. Deen" Babu wanda yayi magana acikinsu sai kallonta da suke "tell me please" tafada tana lumshe idonta don ba hawayen dasuka taru damar sauka "me zakiyi mashi kuma? Kibari ya farfado daga wancan abin da kikayi mashi mana kafin kiyi tunanin dora mashi da wani" inji nurr da dama a wuya take daita akan abinda tayi mashi rannan Kallonta tayi ta hadiye wani yawu mai daci tace "where is he? Please" tafada tana kafeta da idanu Sumee dake bayanta taji tace "zee, rabon Deen da makarantar nan tun wancan ranar, ashe dama yanada pneumonia, coke din dakika watsamashi ya tado mashi ita, yanzu haka shekaran jiya akayi discharging dinshi daga asibiti kamar yadda mukaji labari" Juyowa tayi ta kafe sumee da ido tunda tafara magana, jitayi kamar ansa guduma an make mata kai. Babu abinda kemata kai kawo a kunnuwa sai _*ashe yanada pneumonia, coke din dakika watsamashi ya tado mashi ita*_ _*ashe yanada pneumonia, coke din dakika watsamashi ya tado mashi ita*_ 💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖 Ahankali wasu sabbin hawayen suka qara gangaromata wanda bataba kanta wahalar sharesu ba *"this?"* Cool voice dinshi tadawo mata lokacin daya miqomata takardar *"kai wane irin daqiqi ne? Nace kai wane irin daqiqi ne!!"* *"how dare you temper with my work?! How dare you!"* Waɗannan kalaman nata Suma suka shiga eoching a kunnenta Tunawa tayi da yadda yaja wani mugun numfashi lokacin da coke din mai mugun sanyi ya sauka a jikinshi Tunawa tayi da yadda yaja baya jikinshi na 6ari, yadda ya kama Kanshi da hannu bibbiyu, yadda yatafi taga2 yafadi Dago takardar tayi wanda tunda aka bata takasa ajiyeta, sake warwareta tayi tana binta da kallo Duk tadanyi jirwaye saboda ruwan hawayenta dake diga bisa ita duk lokacin datake kallonta, tarasa dalilin dayasa hawaye ke rige rigen zubomata aduk sadda take kallon takardar, dukda tanada Saurin kuka but this is too much Kallon unique handwriting dinshi take tana kallon neat calculations din sannan ta gangaro kan marks dinta *19%* She can't believe saboda Wannan ta tadoma mutum irin Wannan mugun ciwon pneumonia, She can't believe saboda shi ta kwantar da mutum jinya na kwana uku. Wannan tunanin ba qaramin qaramata nauyin zuciya yake ba, karo na farko datayi abu taji tana danasani sosai, taji tanajin kamar ta maido hannun agogo baya Jin kamar za'a bude kofa yasata Saurin share hawayenta ta cusa takardar qarqashin pillow sannan ta kwanta tana juyawa kofar baya. Mummy ce tashigo da kanta don tadota don yanzu ta aiko wata maid dinsu tace kofar arufe take kuma tayi knocking shiru Qarasowa tayi wajen gadon tana kallon zee daketa barci, kai hannunta tayi ga wuyanta domin feeling temperature dinta taji akwai dan zafi hakan yasata zama gefen gadon tashiga tadata. Saida tadan jima tana tadata sannan ta bude idanunta dasukayi ja cikin yanayin barci "tashi, wai haryanzu jikin?" inji mummy Tashi tayi zaune tana dan yatsine fuska sannan ta daga mata kai "kinsha maganinki na rana?" inji mummy Girgiza kai tayi ahankali "kin gani? Dama kina wasa da magani yaya za'ayi ki ida warwarewa? Yanzu tashi muje kici abinci saiki dawo kisha maganin" tafada tana miqewa tsaye Itama yaye bargon jikinta tayi ta sauko qaffafunta qasa sannan ta miqe tabi bayan mummy datayi gaba. Abincin ma tsatsakurarshi tayi badon yana mata dadi ba sannan mummy ta tsareta tasha maganin tadawo ta kwanta don dama dare yayi lokacin har 9 saura. Saidai koda ta kwanta din barcin qauracewa idanunta yayi ta sake lulawa duniyar tunani, yanzu ina zata ganshi? Yaushe zaizo school? Anya yama ida warwarewa kuwa? Inane gidansu? Wurin wa zata samu hint akanshi no matter how little it may be, kawai ita atunaninta tanajin guiltiness akan abinda tayi ne hakan yasata shiga damuwa sosai, bayan haka babu komai (to Allah yasa) Yau ma ta jima sosai kafin barci yayi nasarar yin gaba daita. *** Shiru master yayi yana sauraron Bash harya kai ayar zubar dayake tayi. Tsaki yaja yace "itakuma meye hadinta da trash irinshi? Ni nama yi tunanin wani dan qusa ne a qasar nan, wai koko da qosai, mtcheew!" yaqarashe yana jan wani tsakin "nima wlh boss musanmman idan ka lura da ajebo ne, nayi tunanin tsabar gata ya maida shi hakan ashe the reverse is the case" "Gaskiya ne, kawai Wannan ba wani amfanin dazaimana tunda bawani jituwama ke tsakankaninsu ba, kawai mu fiddashi a jadawali tunda mun samu daya daga makusantarta ta bamu hadin kai" "bama ceba, kawai mucigaba da samasu ido muna kuma samun information akanta daga ita makusanciyar tata, duk qumu baza'a qarashe Wannan semester dinba saina ja rayuwarta a ta6o na kacalcalata, that's a vow" inji master yana jan ciggarette din hannunshi "hakan ma yayi master! Dolene taji a jikinta, Dolene a gwadawa kowa babu wanda ya isa yajada master ya kwan lfy" inji Alex Murmushi master kawai yayi yacigaba da jan ciggarette dinshi yana ayyana abubbuwa da dama aranshi. 💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖 Washegari da dan qarfi2 ta tashi, qila harda maganin datasha yasata jin dan kuzari ajikinta, ba laifi zuciyarta ta rage Wannan nauyin datayi tadanji dama2 hakan yasa tayi shirinta cikin qanqanin lokaci tafito. Saida tayi breakfast sannan ta fito suka hau mota suka halba school. Yau duk yininta qarar dashi tayi cikin qunci, tarasa abinda ke mata dadi, tayi tunanin zaizo yau din tunda yanzu kwanakinshi 4 kenan da sallamoshi asibitin da akayi kamar yadda akace mata Gashi ko kadan taqi bayyana halin da take ciki ko a fuska ne don ko su friends dinta basu gane halin datake cikiba, gashi takardarta ta jiyama bata nunamusu ba, kawai hakanan taji bataso su fuskanci komai nata kuma don da da hali da zataso subata space don ba qaramin takuramata sukeyi ba yanzu Sosai takeson ta kadaice ko zata samu tayi tunaninta hankali kwance amma ba dama don duk inda tanufa suna nan maqale daita kamar bindi hakan yasa duk bataji dadin school ba ranar haka kawai ta daure suka ida lectures dinsu na ranar Batareda ta fahimci komai ba suka kamo hanya suka dawo gida. Wasa2 wednesday tazo tawuce babu Deen, thursday nanma haka har gashi yau friday babu shi babu mai Kama dashi. Ixuwa yanzu ko bakasan zee ba ada da ka zauna daita na wani lokaci saika gane tana cikin damuwa. Yanzu bata cika magana ba don mugun wuya take bata yanzu don ko maganar ake mata sai anci sa'a take amsawa dakyar Azahiri bata nuna damuwarta saidai ka gane hakan a hallayarta A bangarenta kau komai yabar yimata dadi, ta sukurkuce, school din yanzu ya ida fice mata arai saidai dukda hakan batason fashin ko rana guda gudun kar suyi sa6ani yazo ita bata zoba. Tarasa yadda zatayi placing yadda takeji, abin dai kamar damuwa da rashin sanin halin da yake ciki wanda koma wane halin yake ciki itace sila kamar kuma kewa, gata nan dai ita kanta bata ganema kanta ba. Kwata2 ma ta mance da deal dinsu da mr ibrahim na sake wani text din, gashi yau friday kuma ranar monday za'ayi amma kwata2 batashi takeba hasalima mantawa take da hakan Tsabar bashi ke gabanta ba Jin surutun dasukeyi yafara hawan mata kai yasata dagowa daga phone dinta datake jagulawa tundazu tadan kallesu taga firarsu kawai suke hankali kwance. Dan duba agogonta tayi taga haryanzu akwai sauran time kafin su shiga last lecture dinsu hakan yasata daukar jakkarta ta miqe Duk Dagowa sukayi suna kallonta da alamun tambaya "bari naje cafteria nadawo" tafada tana rataya jakkar "bari na rakaki" inji deeya tana niyyar tashi Saurin dakatar daita tayi ta hanyar cewa "no never mind, yanzu zan dawo ai" Bata sake jiran komaiba taqara gaba don dama surutunsu zata gujemawa idan ta biyota ai anyi ba'ayiba kenan. Cafteria din tanufa direct, burger kawai tasiya da freshyo na roba don dama idan ba gidaba da wuya taci abinci tafi ganema snacks dai Packaging dinsu akayi mata a leda tabiya kudi aka bata chanji sannan ta juyo da nufin tafiya. Idanunta ne suka sauka akan bayanshi dadai zai fice daga wajen. Kafin ta tantance shi dinne ko bashi ba harya fice. Da sauri ta saka abubbuwan data siyo cikin jakkarta tayi hanyar fita itama da sauri. Saidai koda ta fito babu shi babu alamunshi, waige waige tayita yi don ganin inda zata ga wulginshi saidai bataga ko mai Kama dashi ba Nufar inda yasaba zama tayi taga ko can yanufa saidai wurin wayam babu kowa kamar yadda wurin yake cikin yan kwanakinnan _to kodai bashi bane?_ tambayar datayiwa kanta kenan Girgiza kai tayi, tabbas shine dukda bayanshi tagani bata tunanin tana iya kasa ganeshi Dukda kallon yan sakkani tayimashi kafin ya fice taga komai gamedashi, tafiyarshi, structure dinshi, sanyinshi Department dinshi tawuce ko zata ganshi acan saidai wayam ma class din yake sai yan tsirarun mutane daketa kai kawo wajen Dafe kanta tayi tana furxar da iska _karfa ace gizo yayimata? Tunda ga lokacin data fito be isa ace ya 6acemata ba Koda kuwa sauri yake bare tasan yanayin tafiyarshi be iya sauri ba ko kadan. Juyowa tayi jiki a sanyaye tabar wajen. Ranta ne yaqara jagulewa taji duk ta sake quntata, sanin cewar idan takoma wajensu sumee ida jagula mata lissafi zasuyi da surutunsu yasa kawai ta nufi library don acan take saka ran ke6ancewa Batareda wani ya takuramata ba. As usual kamar yadda akasan library da shiru haka shima Wannan yake. Babu mutane dayawa aciki sa6anin yadda yake cika idan exams yakusa. Kamar yadda yake dabi'arta bata kalli kowa ba tanufi wani seat din dake empty wanda ke kusada window tayiwa kanta masauki anan Ajiye jakkarta tayi a kan desk din gabanta Tafiddo abubbuwan data saya don dama yunwa takeji don bata wani ci abincin kirki ba kafin tafito Kai burger din tayi abaki bayan tayi basmallah ta gutsira tafara tauna ahankali Cak ta tsaya da taunar lokacin da idanunta ya sarqe da oily hazal eyes dinshi... ✍️ Kuyi manage please, banida isashen chaji aradu😞 Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:32 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *015* Jitayi komai nata ya tsaya cak, kafeshi da idanu tayi cikin son tabbatar wa kanta yanzun ma ba gizo yayi mataba. Shi din dene, zauna daga can gaba yana facing dinta. Sanye yake cikin qananun kaya, wando jeans sai jar riga, kasancewar rigar mai guntun hannu ne hakan yaba damtsen hannunshi damar bayyana sosai Yaqara haske, lips dinshi sunqara pink sai gashinshi dake adan tuje as usual Batasan tayi missing dinshi har haka ba sai yanzu don jikinta har tsuma yake deep down datake kallonshi. Janye idanunshi yayi daga kanta ya maida kan book din dake kan desk yacigaba da rubutunshi, fuskarshi expressionless Itakau a bangarenta kasa janye nata tayi sai kallonshi take hoping zai qara dagowa. Tunda suke dashi yau tafara tsayawa tayi mashi kallon tsaf. Fuskarshi oval shaped ce, yanada wasu irin fararen idanu masu mugun daukar hankali, idanun basada irin girman nan haka zalika ba lumsassu bane, gasunan dai. Idanunshi irin masu maiko2 dinnan ne wanda hardasu suke taimakawa innocent look dinshi fitowa. Asaman idanun akwai girare dake cunkushe da gashi wanda har sunkusa hadewa don koyaya yadan yamutsa fuskarshi sai sun hade Yanada hanci mai tsayi sosai sai madaidaicin baki dake dauke da pink tausassan lips Yanada saje kwantattu dasuka qara qawata fuskarshi sai dan dimple dinshi dake tsakiyar gemushi wanda ko magana yake yana lotsawa Fari ne saidai yanayin fatarshi zai saka kokwanton ko dan nigeria ne don irin farin nan gareshi tass babu sirki ko kadan don idan ba sani kayi ba sai kayi mashi daukar balarabe kuma... Tashin dataga yayi ya dawo daita daga duniyar kallonshi Ganin ya juya zai fita yasata Saurin zabura itama ta tattara kayanta ta watsa a bag sannan itama ta tashi ta fito. Abin dariya sai alokacin ta tuna da burger din bakinta da tundazu tagaza taunewa. Furzar daita tayi tashiga bin Deen dake tafiya da dan sauri Ganin haka yasa itama qara pace, nan da nan ta taddoshi tasha gabanshi daidai wani silent wuri dake cikeda bishiyoyi. Tsayawa tayi gabanshi hannu riqeda kugu tana kallonshi Shima jan burki yayi ya tsaya yana kallonta fuskarshi babu walwala. "da kake neman guduwa cemaka akayi kana iya tseremin ne?" tafada tana dan Girgiza Kauda kai yayi still fuska ba walwala "kaii.." tafada tana kyakyafta mashi yatsu hakan yasa yajuyo yana kallonta "To gani, kabani haqurin" tafada tana Kauda kai gefe still hannunta Riqe da kugu Tsayawa yayi yana kallonta da alamun mammaki a fuska Jin shiru yasata sake waigowa gareshi tace "kabani haqurin mana, ba nemana kake don kabani haquri ba? Naji ance babu inda baka zagaye a fadin school dinnan don nemana ka bani haquri ba, yanzu gani na taqaita maka wahala, go ahead ina jinka" Ganin abin nata rainin hankali ne yasashi zagayeta da nufin tafiya taqara Saurin shan gabanshi Bude baki tayi zata qara magana yariga ta "what again? Me kuma zaki qara yimin? Am sorry amma ban ida warwarewa akan abinda kikayimin ba rannan, haquri kike son inbaki? To am sorry, sorry for everything, laifi nane dana ta6amaki kaya Batareda neman izininki ba, am sorry, hakan bazata qara faruwa ba, please free me.. Ki kyaleni hakan inyi rayuwata, please. Tsawon kwanakinnan nayi iya bakin kokari na don gujewa haduwarmu shiyasa banama bin hanyar da nasan zata hadamu, please leave me alone now, let me live my peaceful life again.. Please🙏🏻" ya qarashe yana hade hannu alamun roqo Tunda yafara taji kamar an zaremata lakka daga cikin jiki taji jikinta yayi lakwas Zagayeta yayi ya wucewarshi hakan yasa itama ta juya tana kallon bayanshi Yayi nisa ya tsinkayi muryarta "Deen!" Dakatawa yayi da tafiyar shi ya tsaya Batareda ya juyoba Share hawayen daya gangaromata tayi sannan ta tako zuwa kusa dashi "am.. Sorry" tafada ahankali tana kallon bayanshi Bece komaiba haka kuma be juyoba "I.. I don't know what came over me that day, I was mad and..." Sai kuma ta kasa qarasawa, idanunta ta rintse tareda kamo lower lip dinta ta cije wasu hawaye da batasan dasuba suka gangaro mata "am so sorry" tafada cikin rada still idanunta arufe Sai a sannan yajuyo ahankali ya fuskanceta, jin alamun ya juyo din yasata bude idanunta itama dasuke ajiqe suna kallon juna. 💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖 "... Wannan dalilin yasa nayi iyakar bakin qoqarina na ganin nasamu wani abu a assignment din don ko ba komai zai dan taimakamin daga barazanar carryover din da nake fuskanta, shiyasa lokacin da nagane ka chanzamin takarda naji hankalina ya tashi sosai kuma na fita hayyacina don aganina shikenan Wannan damar tariga ta kufcemin.... bansan kanada pneumonia ba, lokacin da labarin ya riskeni naji ba dadi sosai, ban ta6a tunanin reaction dina zai kai ga hakaba, am sorry" ta qarashe tana Dagowa ta kalli Deen dake zaune daura daita da shima ita yake kallo Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace "nima tsotsai yasa na ta6a takardar, bayan nakoma gida ranar, nafiddo littafin ki don inyi maki copy din saina tsinci takardar aciki, koda naduba sainaga assignment ne kuma kinyi, sai nayi going through din takardar naga duk akwai errors a calculations dinki, da farko naso inyi correcting dinshi a paper din sai naga zata 6aci shiyasa na samu wata sabuwa nayimaki ashe rabon kwanciya asibiti yasani yin hakan" yafada yana hade gira Maka mashi littafin hannunta tayi kadan tace "ba nace am sorry ba" Sosa inda ta makamashi littafin yayi yace "O'O!" Dariya tayi tace "wai kai idan baka ce O'O ba bakajin dadi?" tafada tana jin zuciyarta wasai yanzu Daga kafadunshi yayi yana ta6e baki sannan yace "yanzu ya assignment din? Nawa kikaci?" Yatsina fuska tayi tace "as I feared, zero over idanuwa" tafada tana gwale idanu Dan chuckling(Dariya marar sauti) yayi wanda yaba dimple din gemenshi damar lotsawa yace "O'O! They're big" "menene?" "wadannan" yafada yana nuna idanuwanta Hade rai tayi tace "ina ruwanka dasu? dama rannan kace baka sonsu" tafada tana qara zaro mashi su Rufe fuskarshi yayi yace "O'O! Kibari" "idan naqi fa? Mexakayi" tafada tana qara qwalalosu "mefa? Aini yanzu tsoronki nake" yafada yana maida fuskarshi kalar tsoro🤢 Dan Wara idanu tayi tace "tsorona kuma?" "eh mana, wancan karon kinyi landing dina hospital Wannan karon bansan inda zanyi landing ba" Bata fuska tayi tace "nida ka fallamin mari fa?" Shima dan Wara idanu yayi ya rufe bakinshi yana Dariya "O'O! Nidai babu ruwana" Yitayi kamar zata sake makamashi littafin tace "akwai ruwanka harda gwadogwadonka" Hakanan take jin kanta cikin nishadi, zuciyarta wasai kamar bata ta6a quntata ba "kece kika gigitani ai, bakiji ba sadda kika watsamin coke dinnan, kamar zan shid'e, the thing is so sudden and unexpected, sainaji kamar zan mutu" Jitayi tausayinshi duk ya lullu6eta, he's so innocent and simple, bayada matsala ko kadan "sharrin zuciya ne, alokacin am mad with anger shiyasa nayi duk abinda yazo min akai" tafada tana 6ata fuska "da ranki ya 6aci meyasa bakiyi inhaling tasbih kiyi exhaling tahlil ba? Nasha fada maki kakata tace idan ran mutum ya 6aci yayi inhaling tasbih yayi exhaling tahlil sannan kuma idan kashiga tashin hankali ko wani masifa ta tunkaroka Allah (s.w.t) yace " *wa basheeris- sabirina lathina iza asabathum musibatun qalu innalillahi waina ilaihi rajiun*°° *ula'ika alaihim salawaatun min rabihim wa rahmatun, wa ula'ika humul muhtaduun* Ma'ana : *kuma kayi bushara ga masu haquri wadanda idan muka jarabcesu da wata musiba suna cewa 'daga Allah muke kuma gareshi zamu koma'* °° *wadannan mutanen albarka da rahmar ubangijinsu zai tabbata agaresu, kuma wadannan mutanen sune abisa tafarkin gaskiya* Yin abu kai tsaye cikin fushi yana jawo aikin danasani, danasani marar amfani, kuma ambaton Allah a lokacin tsanani ko tashin hankali yana kawo rangwame ga mutum akan Wannan abin, don haka ki dinga kulawa" Zee daketa sauraronshi tundazu tace "hmm gaskiya ne alarrama Deen, shikenan daga yau zan dinga inhaling da exhaling din" "dama wadancan din" yafada cikin son tunamata "eh tabbas, dama wadancan din" tafada tana kada kai "yauwa, kingani idan kinayin haka bazaki dinga over reacting ba kuma Allah zai sauqaqamiki duk abinda yayimiki zafi" yafada in a serious tone Murmushi tayi don ita dariyama yake bata "hakane kam, shukran" Shima Murmushin yayi sannan ya dan karkace ya fiddo biscuit daga cikin aljihun wandonshi ya fasa sannan ya miqomata Murmushi tayi sannan ta zari guda tana cewa "biscuit kamar wani qaramin yaro?" Dan Wara idanu yayi yace "ni babba ne?" "qatoto ma" tafada tana nuna girman da hannu 6ata fuska yayi yace "O'O! Niba qatoto bane" Dariya tayi tana taunar biscuit din tace "To nufinka kai qarami ne? Ca6!" "eh din amma ai ba qatoto bane, qatoto fa babba ne sosai mai qiba da tunbi" Dariya tasakeyi sosai ganin yadda ya 6ata rai sosai shi adole beson acemashi qato "kaima kanada tumbin ai" Wara idanu yasakeyi "ni? Ina?" yafada yana qoqarin daga rigarshi don gani Saurin Kauda kai tayi tana Dariya tace "kaga dawasa nake maka bakada wani tumbi" "amma kika cemin qatoto" yafada yana sakin rigar "ai shine nace da wasa nake ko?" Harararta yayi yakoma ya jingina da iccen dake bayanshi yana cigaba dacin biscuit din hannunshi Bude jakka zee tayi itama taciro burger dinta da freshyo ta Ajiye tsakiya Shiru wajen ya dauka na wani lokaci ganin haka Yasata sake lalubar jakkar ta fiddo takardar assignment din ta miqomashi Kallon takardar yayi ya kuma kalleta yadan daga gira daya alamun meye? Daga kafadu kawai tayi tana qara miqomashi hakan yasashi amsa Warwarewa yayi ya duba saikuma yayi slight Murmushi yana Kauda kai "kaga zero over kunnuwa dakasa naci ko?" tafada tana antayamashi harara Murmushi kawai yasakeyi bece komaiba Sake duba takardar yayi sannan yace "meyasa ta jiqe haka?"yafada yana nuna jirwayen datayi Daga kafadu tayi tace "qila ruwa ya ta6ata" "hmm you're careless" yafada yana 6ata face "whatever" tafada tana juya idanu "yanzu nasan bakida fargabar carryover tunda nasan marks da zaki samu a exams idan aka hada da wannan zakiyi average" Duum! Gabanta yafadi ita sai yanzu ma ta tuna da yadda suka kaya da mr ibrahim "hmm, tukkuna dai, Wannan marks din basa cikin lissafi" tafada tana gutsirar burger kadan "why not?" ya tambaya yana kallonta "well, cewa yayi zan sake wani cos yana tantamar bani nayi wancan ba" "so what? Ba assignment bane? Idan yanaso Kuyi dakanku why beyimuku a class ba as test?" Watsa hannuwa tayi alamun oho ranta na qara jagulewa Shiru yadanyi kamar mai nazari sannan yace "yaushe zakuyi?" "monday" ta amsa a gajarce Dan Wara idanu yayi yace "Wannan coming monday din?" Kada mashi kai alamun eh tayi kawai "so hope kindai shirya" "shirin me zanyi? I'll just do my best and leave the rest" Dan Dariya yayi ganin tana magana a dan fusace "inhale and exhale, zakiji sauqi" yafada yana Murmushi Wata harara ta maka mashi ta Kauda kai "mutuminnan hates you" yafada yana still yana Murmushi "I know, and I hate him more" tafada ranta na qara 6aci Wani Murmushin yasakeyi yace "I'll help you" Sai a sannan ta juyo ta kalleshi Shiru tadanyi sannan tace "really?" Kadamata kai yayi yace "yes, I'll help you da dan abinda na iya" Jitayi farinciki ya lullu6eta "dade dayawa daka iya" tafada tana Murmushin jindadi "ni me na iya?" yafada yana warware takardar "komai ma, imagine Wannan uban aikin amma naci 19/20 kuma nasan duka naci kawai rage dayan yayi" Murmushi kawai yayi yana duba takardar "yanzu dai mufara da solving wadannan" yafada yana Ajiye takardar gabansu "bring out your writing materials" Hakan tayi ta fiffido kayan amfani cikin zumudi sannan tadan rage taxarar dake tsakaninsu "you know, mathematics subject ne dake buqatar aiki da brain, duk cikin subjects babu mai chaxa kwalwa kamar shi, idan kinaso ki qware akai to you have to be alerted always, ki dinga practicing din difficult difficult solving on your own Koda kuwa ba'a ta6a koya mukuba, kidinga karambani na solving din kome zaki gani Koda kuwa baxakici daidai ba, da haka da haka zaki ga kema kin gwanance" "kamar kai?" Harararta yayi ya Kauda kai Batareda yace komaiba "yanzu bari mufara da wadannan, shi mathematics steps of calculations gareshi, missing din step daya na iya 6atamiki aiki, bayan formula(s) abinda ya kamata ki laqaita sune steps, yanzu kamar Wannan..." Nan suka shiga solving din aikin, sosai zee ta maida hankalinta akan abinda sukeyi kuma sosai abin ke zama akanta. Saida suka shafe awa 1 da rabi ahaka don sosai yake fayyacemata komai shiyasa kafin su bar wani question sai sun dan jima don be bari su qara gaba sai ya tabbatar tagane Wannan sosai Ita sai alokacin ma take ganin simplicity din assignment din Saida suka gama tsaf sannan yace "and that's all about this" Wara idanu zee tayi tana tafi "wow! Gaskiya your gifted! Thanks so very mucch" Murmushi kawai yayi "amma a ido baka kama da genius, ca6 ashe ina tareda mathematician ban saniba, gaskiya kudos" Murmushi yayi yace "ba haka bane, mathematics is so simple.." "gareku genius ko?" Girgiza kai yayi yace "ga kowa ma, kawai s@i idan dai baka fahimta ba... And also kowanne subject dakika gani, idan kinaso ki qware akai Dole kiyi abu biyu, na farko kiso subject din koda yana wahalar dake, nabiyu kuma kiso teacher din subject din kuma yasoki to with that everything will go smoothly for you" Ta6e baki tadanyi tace "I'll like the subject but not the teacher" Daga kafadu yayi kawai "yanzu ai am fully ready, babu wanda ban Riqe ba anan" tafada cikin jindadi "To ce maki yayi the same questions zai qara baki" Dan bude ido tayi tace "ba the same bane?" Kallon uku saura kwabo yayi mata hakan yasa ta daga littafi zata makamashi. Curewa yayi yana cewa "wayyo kaka!" Dariya tayi tace "A'a jika" "Wannan kakar taka tana shan sangarta" inji zee Murmushi kawai yayi yana cije murfin biron hannunshi "yanzu to ya za'ayi? Ko mu dora da wani yanzu? Bari na ciroma littafin ka gani" Dakatar daita yayi dacewa "To amma fara dubamana qarfe nawa" Wayarta taciro daga jakka ta kunna Da missed calls din bala tafara cin karo hakan yasata wara idanu Agogon taduba taga 5 na marece saura "my goodness! Kaga driverna ma yakira banjiba ko? Dama vibration nasata" tafadi hakan tana dannamashi kira Ringing biyu aka daga "bala kana ina?" "ganinan kan hanyar komawa gida madam, nazo na nemeki dani da qawayenki bamu ganki ba kuma naita kira ba'a Dagawa" "To kayo kwana kawai ka dawo ina a school din library na shiga karatu" Bata jira amsarshi ba ta katse kiran "ka gani ashe yazoma yanata nemana be ganniba, duk kai kaja gashi kasa nayi loosing din last lecture dinmu" tafada tana 6allamashi harara Dariya yayi marar sauti yace "ai duk ke kikaja, kedama yanzu so kike mucigaba?" Marairaice fuska tayi tace "To ya na iya? The man is so wicked, bansan wane muguntar kuma zaimun ba, gwara na shirya ko yayane" "kina zuwa school gobe?" "gobe? Ni me zai kawoni school gobe saturday?" "akwai masu zuwa masu lecture" "really?" "yes, nima ina dan zuwa" "kuma kuna lecture ne ranar?" "A'a, kawai ina dan leqowa ne wani sa'in inyi karatu" Fuskarta ne ya washe "To ko nima inzo goben saimuyi?" "yes, idan kina iyawa" "yes! Perfect! Gobe zanzo very early" "no not early, bayan zuhr ake bude makarantar, students din lecture din marece garesu kinga saimu shiga as muma lecture din zamuyi sai mu wuce library kafin su gama" "Perfect! Hakan za'ayi" Daidai nan wayarta tayi Ringing "gashinan yazo" tafada tana daga wayar "ganinan" daga haka ta katse sannan ta miqe tsaye Shima tashi yayi ya kwashi littatafan shi itakuma ta rataye jakkarta "inane unguwar ku?" Murmushi yayi yace "kitafi kawai akwai abubbuwan da zanyi a library" "me kuma?" "akwai assignments dazan qarasa" "kabari kayi agida mana" "gida banida time, gwara inyishi nan" Tsayawa tayi tana kallonshi Wara mata oily idanunshi yayi yace "what?" "my mind is telling me bawani assignments dazakayi kawai bakaso muyi dropping dinka ne" Qara wara idanu yayi yace "then your mind is lying" Zata sake magana ya katseta da "he's waiting" Hakan yasata fara tafiya tana cewa "ok see you tommorrow" "see yah" yafada yana daga mata hannu Tsayawa yayi yana kallonta harta 6ace mashi Ajiyar zuciya ya sauke sannan yakoma library, saida yaja lokaci sosai wanda ya tabbatar su zee sun tafi sannan yafito shima. Saida yadan wahala sannan yasamu abin hawa ya shige suka shilla... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:32 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *016* Gaskiya inajin dadin yadda book dinnan ya samu qar6uwa a wurin ku fans, your comments always make me go gaga! Keep it flowing Wannan page din is dedicated to all members of *DEEN FANS GROUP* much love 💖 Washegari da ruwan sama aka tashi sosai, kasancewar damunan ya shigo sosai yasa yanzu akemusu ruwan saman akai2 An dade ana sheqa ruwan don tunda safe da aka fara sai wajen 12 ya dauke Sai garin yayi luff ya dauki sanyin damuna Sosai zee taji dadin daukewar ruwan don tunda akafara taketa zullumi don batason abinda zai 6atamata schedule dinta na yau. Tashi tayi ta zira guntuwar hijab akan doguwar rigarta ta nufi dakin mummy aqasan ranta tana addu'ar Allah ya dorata akanta don itace matsalar don idan ta daddy ne batada wata fargaba. Kwankwasa kofar tashigayi saida aka danja lokaci sannan aka bata izinin shigowa daga ciki. Murda handle din tayi daukeda sallama abaki sannan tashiga. Zaune ta tarda mummy Riqe da memo tana yan rubuce2 da alamu dai lissafe lissafenta na business takeyi Qarasowa ciki tayi a dan dadarce sannan ta samu wuri kan bedside locker ta zauna "mummy barka da rana" tafada tana kallonta Dagowa tayi daga rubutun datake tace "yauwa, barka, ya ruwa?" "alhamdullilah mummy" "masha Allah" tafada tana maida kallonta kan abinda take Shiru zee tayi tana practicing yadda zatayi convincing mummy aranta don tasan halin mummy tsaf ta hanata idan bata gamsu da bayyananta ba "erm.. Mummy" Sai a sannan mummy taqara Dagowa "mummy na mance jiya ban gayamaki ba.. Dama wani practical garemu a school yau, zamuyishi ne daga 2:30 zuwa 4pm, jiya na manta shaf ingayamiki sai yau dana tashi na tuna gashi practical din zai taimakemu sosai wlh" Tunda tafara magana mummy ke kallonta har takai aya, ganin still batabar kallonta ba yasata sunkuyar dakai tana wasa da yatsun hannunta "yau wace rana?" inji mummy Hadiye wani yawu zee tayi sannan tace "saturday" "dama ana zuwa school saturday ne?" Cikin qarfin gwiwa tace "eh mummy, akwai masuyi, mudai ne bamuyi amma kasancewar practical din is very important kuma zaiyi helping dinmu a exam daketa gabatowa yasashi fixing yau din, yadda zai kasance no disturbance tunda very few people ke zuwa school yau" Ganin yadda mummy ta tsatsareta da ido yasa gabanta cigaba da faduwa saidai bata yarda ta janye idanuwanta daga gareta ba don hakan alamu ne na qarya take wanda dashi mummy ke yawan kartota idan tayi qarfi" Janye idanunta mummy tayi ta maida ga memo din hannunta tace "practical din menene?" "biology" Kada kai tayi tace "yaushe kikace kuke gamawa?" "qarfe 4pm" Qara kada kai tayi tace "To amma bala zai jiraki harku gama sai ku kamo hanyar gida" Sosai farin ciki ke cinta kamar ta buga tsalle saita maze kawai don kwakwarar motsi na iya sawa ta chanza ra'ayi "To mummy" "and also idan kin dawo sai kin gwadamin abinda kukayi" Gabanta ne ya dan fadi saidai kuma Batareda ta nuna damuwar komaiba tace "To mummy" Maida hankalinta tayi akan abinda takeyi hakan yasa zee tashi tayi mata sallama sannan ta fita Dafe saitin zuciyarta tayi bayan ta fita tana sauke tagwayen ajiyar zuciya, mummy 🔥 Komawa dakinta tayi tashiga shiri a gurguje. Yau saboda sauri da kuma gudun kar ta tsaya 6ata lokaci mummy tafasa yasata kasa Tsayawa ta tsara makeup dinta hakan yasa tayi simple makeup ta gabatar da sallar zuhr kasancewar dama da alwallarta tafito bathroom Saida tagama tsaf sannan ta dauki abubbuwan amfani ta jefa a jakkarta ta fito. Dakin mummy tasake komawa don yimata bankwana can qasan zuciyarta kuma tana addu'ar Allah yasa ba rabon a hanata zai kaita ba. Shiga tayi bayan anbata izinin shiga sannan tace wa mummy ta tafi Dan jimm mummy tayi kamar mai nazari hakan yasa zee jin kamar taruga don fargaba "To Allah ya tsare, adai dunga kula da kai dakuma mutunci" "insha Allah mummy, saina dawo" Bata tsaya jiran komai ba kuma tafice tana duba agogo, qarfe 2:20pm. Tun daga nesa ta hangi bala zaune da security da alamu ita yake jira don yana hangota ya tashi ya nufi mota Gaisheta yayi yana bude mata kofa, bata amsaba as usual sai shigewa datayi cikin Motar tana cewa "muyi sauri am late" Hakan yasashi Saurin maidawa ya rufe sannan ya zagaya mazauninshi ya bude shima ya shige. Tada motar yayi yayo reverse sukazo suka wuce security daya wangale musu gate suka halba kwalta. *UMYAU* Kamar yadda yafada kau akwai few students a school din. Lokacin datazo lokacin wasu ma ke zuwa hakan yasa ta fito daga motar tawuce itama tabar bala anan yana jiran fitowarta. Direct library kamar yadda sukayi dashi ta nufa cikin doqi don tasan yana ciki yana jiranta. Saidai murnanta ne takoma ciki ganin babu shi cikin tsirarrun mutanen dake library din. Wucewa tayi seat din data zauna jiya ta zauna tana dora jakkarta akan cinya Duba agogon hannunta tayi taga 15mins to 3, hakan yasata buga tagumi da hannu biyu tareda kafe hanyar shigowa da ido, can kuma sai maganar Deen ta jiya ta fadomata *idan kinaso ki qware akai to you have to be alerted always, ki dinga practicing din difficult2 solvings on your own koda ba'a ta6a koya mukuba, ki dinga karambanin solving din kome zaki gani Koda kuwa bazakici daidai ba, da haka da haka zaki ga kema kin gwanance* Furzar da iska tadanyi sannan ta maido jakkarta saman desk din gabanta ta ciro duka materials din datazo dasu. Tashi tayi taje wajen shelves din library din tana neman textbook din mathematics da mr ibrahim ke amfani dashi, bata sha wahala ba tagani ta zaro daya tadawo wurinta ta zauna Batareda ta damu da kallon da yan library din kebinta dashi afakaice ba, idan da sabo tasaba besides ita kallon be dameta ba, be sata kuma be hana ta komai. Bubbudewa tashiga yi, da harta bude inda ba'ayi musuba da niyyar yin karambani kamar yadda yace saikuma ta chanza mind, gwara dai tayi wadanda akayi musu tunda test gareta ran monday, karambanin ya jira harta warware Wannan tukkunan. Bude wani topic wanda anyi musu shi amma yana mugun bata wuya tayi, tafara going through dinshi ta tattara dukan hankalinta akai sannan tafara solving difficult2 questions din topic din cikin kokwanton daidai takeyi ko ba daidai ba saidai hakan be sagemata gwiwa ba yi take tana making sure tana lura da steps of calculations din don gudun 6ata aikin ta. Tayi nisa da zurfi a abinda take har Batasan da zuwanshi ba Daidai tagama wani question wanda ya mugun wahalar daita ta ajiye pen ta dauki hanki dake kusada ita idanunta still a aikin datayi don making sure tayi daidai tashiga tsane zufar daya dan tsatsafo saman goshinta. Ajiyewa tayi bayan tagama ta dago sai sauke idanunta tayi cikin nashi a bazata. Hakan yasata Saurin yin baya cikin yanayin tsoro don ko kadan bata kawo ganinshi a gabanta ba. Dafe qirji tayi tana bude idanu tace "ya sallam! Deen? You scared me" Murmushi yayi wanda saida dimple din gemunshi ya lotsa yace "frightening kitten" Jawo littafin datake aiki dashi tayi ta rufe tayi kamar zata makamashi hakan yasashi Saurin yin baya shima yana Dariya Harara ta makamashi sannan ta ajiye littafin ta bude tayi fuska ta cigaba da abinda takeyi "so, me kikeyi haka har bakiga shigowa ta ba har zamana anan?" yafada da kingin Murmushi a cute face dinshi Dagowa tayi ta harareshi tace "ni Kama bar yimin magana, kazo ka shanyani nan kamar kayan shanya, you have no idea yadda nasamu dakyar mummy tabarni akan sharadin 4 nayi zan juyo amma shine ka shanyani sai yanzu kaga damar zuwa, duba time yanzu qarfe nawa? Is better ka koma inda kafito don babu ruwana dakai" tafada tana murguda mashi baki ta maida kanta kan littafin gabanta Daga gira daya yayi sannan yasa hannu ta saman hular Kanshi yana yamutsa tulin sumarshi yana Murmushi "you also have no idea yadda nima nazo nan, ba don namiki alqawariba da bazanzo ba" Sai Jitayi taji haushi, Wato indirectly nufin shi kawai taimaka mata yayi yazo don yamata alqawari, wato irin alfarmar nan yayimata Hakan yasa bata dago ba taji ma abin ya fita ranta, tana cikin shawarar abinda zatayi taji yace "da kamar bazanzo ba kuma nayi tunanin karki zo ke kuma kiyita jirana shiyasa na fito ba don haka ba yadda akayi ruwan nan da inacan under dozen of blankets, look at what am wearing amma dukda haka sanyi nakeji sosai, irin na cikin qashin nan" Sai a sannan ta dago ta kalleshi, ita sai yanzu ma talura da shigar shi. Sanye yake cikin qatuwar blue din rigar sanyi mai thick long wuya wanda ya rufe wuyarshi sai thick hular sanyin dake Kanshi wanda ya rufe mashi kunnuwa, hannunshi ma Sanye da gloves kuma ta tabbata kaffafunshi ma akwai safa sai face mask daya sauko dashi wajen qasan gemu tundazu. Sai Jitayi ya bata tausayi don ko ahakan rungume yake da hannuwa a qirji alamun still yana jin sanyin "To kodai mubar karatun tunda sanyi kakeji?" Murmushi yayi kawai yace "no, ai mathematics ne, akwai dumama jiki, before you know it mun jiqe da zufa kamar yadda kikayi dazu" yafada yana fizge littafin gabanta yana kallo "bari muga jangos din dakikeyi tundazu harda zufa" yafada yana kafe book din da oily eyes dinshi yayinda ita kuma ta kafeshi da nata Gani tayi yana Murmushi akai akai yana kada kai yana going through abinda take hakan yasa itama tayashi Murmushin Batareda tasan tanayiba. Dagowa yayi hakan yasa tayi gaggawar janye nata idanun cikin basarwa "wow! Nice move" yafada yana kada kai "Gaskiya you tried" yafada yana sake duban littafin yana Murmushi hakan yasa jin kanta ya fasu itama tashiga yin Murmushi "now bari nayi marking muyi corrections saimu dora" Kada mashi kai tayi tana qara dan motsawa tana leqa littafin "Pen?" Miqa mashi nata tayi tana cigaba da leqen abinda yakeyi, ganin bata gani sosai yasa ta tashi ta zagayo seat dinshi ta zauna tana dan ba Kansu tazara Bece komaiba sai cigaba da marking dayayi tana kallon yadda yake bin steps of calculations din, kowanne step da makin shi. Saida yagama duka sannan yayi calculating din marks din akan 16/20 Sosai taji dadi har hakan yakasa 6oyuwa a fuskarta. "ga scores dinki" yafada yana nunamata Blushing ☺️ kawai tayi tareda Kauda kai "yanzu bari muyi corrections" "na bari" tafada ta buga tagumi da hannu biyu Kallonta yayi sai sukayiwa juna Murmushi sannan yafara Tana kallon duk abinda yake da mistakes din datayi dakuma yadda yakamata tayi, hakan be daukesu wani lokaci ba suka gama, ya cigaba dacewa "you know, maths is very simple, kawai teachers din kesawa yayi looking difficult, sai kiga yazo yabaku aiki yayi muku amfani da formula kuga abin very simple saidai daya baku aiki duk saiku daburce kuga kamar ba'a ta6a yimuku shi ba, what they do here is rikita calculations din dasuke yi don su chaza muku qwalwa, mai yiwuwa a very simple example yayimuku saidai wajen baku aiki saiya baku mai wuya har kufara tantanmar anya abinda ya koyamuku ne don wani sa'in ma saikuga kamar ma babu yadda za'ayi amfani da formula din a qyestion din, hakan na faruwa right?" Zee dake sauraronshi tundazu tace "right" tana kada kai don ita kanta tana yawan tsintar kanta a Wannan halin "so the solution shine, bayan sanin formula ki kuma san yadda zakiyi amfani daita ta kowacce siga, ya kasance ko tawane siga qyestion yazo miki zaki iya tackling dinshi, kuma wajen yin haka sai ansa nutsuwa sosai an fara sanin what the question is all about yadda xakisan yadda zaki 6ullomata, yanzu saboda qarancin lokaci bari mudauki wani topic din yadda kafin mutafi munqara two more" yafada yana bude note book din saikuma yabata yace ta bude wadanda sukafi bata wuya Babu musu ta amsa ta budomashi wadanda ke mugun bata wuya nan suka shiga yi Sai gashi maganar Deen ta tabbata don tuni kai yafara daukan chaji suka fara hada gumi. Sai gashi kafin 4pm sunyi covering abubbuwa da dama don Deen is slow amma a bangaren karatu he's so fast and talented don yasan yadda zai fayyacema mutum abu nan da nan ya dauke gashi kuma anci sa'a kan mutumiyar taku naja sosai Alarm din wayarta ya katsesu hakan yasasu Dagowa tare "what's that?" inji Deen Fuska a tur6une don bataso su tsaya yanzu ba tace "Alarm nasa don karmu wuce lokaci mummy tayi farfesu na, mtcheew I swear I don't want to go now" tafada tana qara 6ata fuska Murmushi Deen dake kallonta yayi yace "but you have to, worry not ai zaki ida a gida, tomorrow ma saikiyi trying wasu abubbuwan idan muka hade monday sai inyi checking" Shiru tayi cikin zuciyarta tana cewa kokuma ta amshi phone number dinshi idan tasamu matsala ta kirashi? Saikuma wata zuciyar tace no, ba ajinta bane ta tambayi number shi ba shi be tambaya ba, Wannan zubar da class ne Hakan yasata miqewa tsaye tana cewa "ok, thanks so much, ya na iya?" Shima miqewa yayi yana kallon yadda take tattara stuffs dinta Tattaro wasu yayi yabata hakan yasa ta dago ta kalleshi, Murmushi yayi mata itama ta maida mashi martani sannan ta amsa ta cusa a jakka cikin zuciyarta tana gulmar yadda Murmushi keyi mashi kyau Saida tagama tsaf ta rataye jakkar ta dago ta kalleshi taga yana maida mask dinshi. Tare suka fito yana qara gayamata logics da dabarun mathematics Awaje ma students keta tafiya da alamu Suma sun gama, duk yadda zee taso yabisu qi yayi, ganin yanata kawo mata excuses duk na zamewa ga binsu yasata kyaleshi don dama bata wani qware wajen naci ba, haka tashiga motar da bala ya budemata ta zauna tana kallonshi ta window Tsaye yayi shima yana kallonta hannunshi rungume aqirjinshi fuskarshi dauke da guntun Murmushi Saida bala ya tada motar sannan ya shiga daga mata hannu yana Murmushi Ganin haka yasa ta dagamashi yatsu itama tana Murmushi har suka fice Bin motar yayi da kallo har saida ta fice daga school din sannan ya sauke ajiyar zuciya ya maida hannayenshi cikin aljihunan rigar yana sake qanqame jiki shima yanufi hanyar fita Yau yafi jiya shan wahala kafin yasamu abin hawa suka shilla suma. *** Koda zee ta isa gida saida tafara biyawa dakin mummy ta gwadamata takardar practical din, dama tun kafin ta fita ta zari wata takarda wanda sukayi practical aciki saita rubuta date din ranar asama yadda abin zai qara armashi shiyasa mummy na dubawa ta yarda ta maida mata abinta ta sallameta. Shikau a bangaren Deen yana komawa gida ya duqunqune cikin bargo yana makarkatar sanyi, dama qaqa lfyar giwa? Haka kaka taita mita akan ai dama ta hanashi fita ya nace ai ga irinta nan, shidai jinta kawai yake amma ko uffan bece ba Hura wuta kaka tayi tasamu garwashi sosai tasa cikin wani abu kamar irin borner dinnan na qasa saidai Wannan yafi shi girma ta cikoshi takawoshi dakin sannan ta tado din dakyar yazo ya tsaya kusada garwashin don dumama jiki, be tashi daga gaban garwashin ba saida aka fara kiraye2n magrib sannan ya tashi yayi alwalla da ruwan dumi da kaka ta dumama mashi sannan yayi sallarshi agida don ga yadda yake ji dinnan bazai iya fita yashawo iskar waje ba Yana zaune har akayi isha'i itama ya tashi ya miqata sannan yasha shayin da kaka tayimashi yadanci tuwo sannan ya kwanta, yau saidai kaka tayi aikin tatarta ita kadai. Zee kau kusan raba dare tayi tana karatu, saida taga idanunta sun fara yimata yaji sannan ta hqr ta kwanta Washegari ma yini tayi garden dinsu tana karatu, sallah kawai ke tadata, akwai wurare dayawa da duk bata fahimta ba hakan yasa take ticking ☑️ wajen akan idan sun hade dashi gobe saiya gwadamata Abinci ma sai mummy ta mata magana take tunawa dashi, yau ma saida taji kanta na neman darewa gida biyu sannan ta shafawa kanta lfy ta hqr ta kwanta *MONDAY*... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:33 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *017* *MONDAY* Kasancewar jiya bada wuri ta kwanta ba yasata makara wajen tashi don tunda ta tashi dakyar tayi sallar asuba takoma bata tashi ba sai 8 da mintuna A gaggauce tayi shirinta sannan ta sauko ta cuccusa breakfast don tasan halin mummy bazata barta ta tafi ba idan bataci ba Saida tagama komai tsaf sannan tayiwa mummy bankwana, daddy dama tun shekaran jiya yayi tafiya. Babu 6ata lokaci ta isa parking space inda bala yake yana jiranta, suka shishige motar yabata wuta suka fice daga gidan. *UMYAU* Direct library ta nufa tanayi tana duba wristwatch dinta, 9 harta gota hakan yasata qara pace dinta. Wata ajiyar zuciya ta sauke data shiga library din saboda hangoshi datayi can qarshen library din Dukda Kanshi a kife yake kan desk hakan be hanata ganeshi ba, hakan yasata nufar seat dinshi direct. Saida taja kujera ta zauna sannan tadan bubbuga desk din ganin ko motsawa beyi ba. Ganin yadda yadanyi kyarma lokacin da take bugun desk din yasata sanin be san da ita dinba, wataqila ma barci yake Dagowa yayi daga kwancen dayayi ya sauke idanunshi dasuka danyi surkin ja akanta Dan Wara idanu tayi tace "subhanallilah! Baka lfy ne?" Dan Murmushi yayi sannan ya zauna sosai ya bude baki yace "you're late" Jin muryarshi tadan dashe yasata cewa "yakuma naji muryarka haka? Are you ok?" Ganin damuwa a fuskarta yasashi jin dadi, koba komai ta damu dashi kuma ta gano he's not ok Gyaran murya yadanyi don maqogwaronshi yayi clearing yace "am ok, kawai slight mura ne" Maida fuskarta tayi kalar tausayi tace "ayyah, hope kasha magani" Daga mata kai yayi kawai yana Murmushi "Allah ya sawwaqe" tafada tana kallonshi cike da tausayawa don yanzu mugun tausayi yake bata Da amin ya amsa, ganin irin kallon datake mashi yasashi cewa "ya weekend? Hope anyi abin kirki" yafada yana kallonta a dage Hakan yasa ta watsamashi harara tace "cemaka akayi ni lazy ce kamar kai?" Bata fuska yayi "O'O! Ni ba lazy bane" "O'O! Kai lazy ne" ta kwakwayeshi Dariya sukayi gaba daya sannan yace "how's the weekend? Hope kidanyi wani abu" "yeah, bari kagani" tafada tana doro jakkarta saman desk "saidai fa there are lot da bangane ba amma nayi musu alama so that I'll show it to you" tasake fada tana fiffido littatafan Bude mashi tayi ta tura gabanshi shikuma ya dauka yana Dubawa Saida yagama duba duka sannan ya dago ya kalleta yaga itama shi take kallo Dagamashi gira daya tayi alamun ya? Sai yayi mata Murmushi yana hade yatsu babba da manuniya 👌 yace "fabulous! Gaskiya kinyi qoqari sosai, banyi tunanin zakiyi covering duk wadannan ba" Murmushi kawai tayi "To yanzu lets go straight to the lesson you see yanzu to 10 gashi inada lecture at 10:30 and I guess kuma kunada na safe ko?"yafada yana wasu yan rubuce2 "yeah, amma mu sai 11" Kada kai yayi kawai yana cigaba da rubutun saida yagama sannan suka shiga karatun gadan2. Kamar yadda yace 10:30 nayi suka dakata bawai don sun gamaba saidai ba laifi sunyi abin kirki sosai. Barinta yayi anan yawuce class itakuma ta cigaba har saida taga 11am takusa sannan itama ta tashi tanufi class Koda tashiga class har anfara taruwa, can ta hangi su sumee wurin zamansu suma duk sun zubamata ido hakan yasata qarasawa wajensu fuska ba yabo ba fallasa Matsa mata sukayi ta zauna tana cewa "hello babes" Duk amsawa sukayi da "hyy dear!!" Sai deeya ta dora da "yar halak, yanzu muka gama maganar ki" Daga gira daya tayi tace "really?" Sumee ta amsa da "yes, tundazu muketa zuba ido muga ta ina zaki 6illo amma shiru kakeji wai mallam yaci shurwa" Murmushi tadanyi tace "am late ne yau, ban fito da wuri ba" "ayyah, harmun fara zullumi don kinga ranar friday ma saidai muka nemeki muka rasa, bala ma yazo mukaita nemanki dashi, qarshe dai muka hqr muka barshi, wai ina kika shiga ranar?" Zee da tunda rukky ke magana hankalinta ke kan memo din hannunta tace "gida na wuce, banajin dadin jikina ne lokacin" "ayyah, To how are you feeling now?" inji nurr "am feeling better" kafin ma ta ida rufe baki lecturer din lecturen dasuka dashi ya shigo hakan yasa duk aka nutsu 40mins suka dauka a lecture din sannan suka fito Direct usual wajen zamansu suka nufa badon ran zee yasoba don ita wurin Deen taso wucewa saidai tasan wadannan pest din bazasu bari ba, kafarta kafarsu. Ita yanzu da sunsani da sundan ja baya da ita don yanzu bata cika son hulda dasuba ba, She really want a space from them amma basa ganewa don kullum qara likemata suke kamar snail and it shell Suna zaune su sumee nata hirrarakinsu suna Dariya itakau zee jinsu kawai take saidai hankalinta ba anan yakeba, duk ya karkata yakoma ga aikin dazatayi a office din mr ibrahim, hakanan take jinta so nervous tana addu'ar Allah yasa karya 6ullomata ta hanyar da bazata iya sha ba. Sosai takeson taqara nazari akan wasu abubbuwa kafin lokacin yayi saidai surutunsu ya hana, abin ban haushin ma surutan duk marar Ma'ana sukeyi don ba qaruwa ko kadan aciki Haka dai taita hqr har 12 saura mintuna 10 Ganin ta tashi tsaye tana rataye jakka yasa duk suka dago suna kallonta "ya dai?" inji rukky "daidai" zee ta amsa a gajarce "wani wuri zaki ne?" inji rukky again "eh zani office din mr ibrahim ne" tafada absentmindly Duk Wara idanu sukayi "mr ibrahim? Hope komai dai lafiya" "lfy, kawai chanza Wannan assignment din zanyi" Duk sai yanayin fuskarsu ta chanza na yan seconds snn sukayi Saurin daidaita fuskarsu "To? Kice Allah ya doraki akanshi kenan, lallai yau sai anyi ruwa harda qanqara, wai yau mr ibrahim keyin alfarma kuma wa ke" inji deeya in mixed feeling Itadai zee batace komai ba sai gyara rolling din gyalenta datayi tace "bari natafi, 12 zamu fara, see yah" ta qarashe tana dagamusu yatsu "see you!!" suma suka amsa suna daga mata yatsu suma Duk rakata sukayi da ido harta 6acewa ganinsu "kutt.. Wai kunji abinda naji kuwa koko ni ke ciwon kunne?" inji rukky "nima that's what am doubting, mr ibrahim da yimata alfarma? Ko zaiwa kowa alfarma ai sai inga banda ita yadda ya tsaneta dinnan" inji deeya "lallai kam, kodayake qila kuka tayita mashi tana gamashi da Allah da annabi akan ya taimaka ta chanza wani wancan ba ita tayiba, kinsan class din datake taqama dashi duk rubace, bakuga yadda muka isketa ba sadda muka taddata chan ba?" inji nurr "ba shakka! Qila kukan tayita yimashi tunda ai shi muka tadda tanayi amma girma ya fadi wlh" inji sumee "hmm Allah yasa ga kukan kawai aka tsaya, kinsan mutum idan yanason abu yana iya komai don samun biyan buqatarshi" inji rukky "kamar ya fa?" inji nurr "She can give what She have to get what She want" inji rukky "kai, nanfa daya, kinsan zee kema saidai idan fadin son ranki zakiyi amma kinsan bazata iya Wannan ba" inji sumee "ko zata iya mr ibrahim bazai bata hadin kai ba, kinsanshi ai" inji nurr Ta6e baki deeya tayi tace "kudai ba'a shaidar dan adam" Rukky ma ta kyabe baki tace "ato" Haka dai suka cigaba da hirarta don kowa Wannan abin beyi mashi dadi ba, so suke atafi ahakan a yimata amfani da mark din assignment din don sufa haryanzu basuga takardar ba, duk a tunaninsu zero din taci don harsun fara sata a list din yan carryover na bana (Allah ka rabamu da abokai masu fuska biyu 🤲🏻) Saida tayi knocking sau uku sannan aka bata izinin shiga Duba agogonta tayi taga 12 dot sannan ta tura kofar tashiga bakinta dauke da sallama Dashi da wani saurayi tagani a office din don amsar saurayin taji yayinda mr ibrahim keta rubuce rubucenshi na fama Qarasowa tayi cikin office din tana gyara zaman jakkarta "good afternoon sir" tafada tana kallon wani wajen Idan kun amsa to shima ya amsa, hakan kuma ba qaramin 6ata mata rai yayiba amma saita fuske tacigaba da tsayuwarta Saida ya mula yasha iska sannan ya dago ya kalli saurayin dake zaune can gefe sannan ya kalleta Kauda kai yayi sannan ya miqe tsaye riqeda wata takarda yana cewa "are you guys ready?" Hakan dataji yasa tasan da ita da wannan saurayin zasuyi tare, To shikuma meye tashi matsalar? Oho Saurayin kadai ya amsa da "yes sir" Kada kai yayi sannan ya wuce wajen wani chalk board dake daga gefen office dinshi yana cewa "kowanne ya zauna bisa different chair" Jin haka yasata Juyowa ta kalli saurayin taga shima ita ya kalla saita Kauda kai ta wuce wurin wata kujera nesa dashi ta zauna "drop your bag on my desk" ta sake tsinkayar muryarshi yana fadin haka Batareda ya juyoba Ba musu ta tashi tawuce desk dinshi ta dora jakkar akai tadawo ta zauna daga ita sai pen sai calculator Shiru office din ya dauka bakajin komai sai motsin chalk akan board din Kasancewar ya tare board din yasa bata ganin komai sai motsin da bayanshi keyi sanadin rubutun dayake. Shiru sukayi suna jiran yagama kowanne da saqe saqen dayake. Yakusan 15mins sannan ya gama ya ba kowanne plain paper yana umartarsu akan answer kawai yake buqata a takardar Duk amsa sukayi kowanne da addu'ar dayakeyi a ranshi sannan mr ibrahim ya koma mazauninshi ya zauna yana lura dasu Da daddaya tafara bin questions din da kallo har takai qarshe Wani slight Murmushi yayi forming a gefen bakinta don rabi da kwatan questions din shine karatun dasukayi da Deen ranar saturday Babu 6ata lokaci ta zaro bironta ta budeshi ta dorashi a takarda tana basmallah Aikin ya daukesu 40mins sannan saurayin yafara zuwa yayi submitting, yana ajiyewa mr ibrahim yayimashi izinin tafiya Tafiyarshi da minti goma itama ta gama ta tashi itama takaimashi Amsa yayi itama tareda bata izinin tafiyar, bata qara 6ata lokaci ba a office din tafice tanajin kamar taita tsallen murna Da farko library tanufa saikuma ta duba agogo taga 1 tadan gota hakan yasata fasawa don tasan yanzu haka yana class don sunada lecturen qarfe daya Wucewa tayi wajen da suke zama ta tarda wajen wayam babu su sumee Hakan yayi mata dadi sosai don haka tayi zamanta tana ciro wata takarda tashiga rubuta questions din datake iya riqewa acikin wadanda sukayi yanzu don ba Deen yayi solving taga ko tayi daidai 1:30pm nayi ta rufe littafin ta tashi tanufi masjid din school din don yin sallah Koda tafito wucewa class tayi a gaggauce saboda lecture dasuke dashi hakan yasa sukayi sa6ani da Deen don shikuma a daidai lokacin suka fito lecture Shima masjid ya wuce ya gabatar da sallar zuhr sannan ya wuce gida don sosai murar ke nuqurqusarshi Basu zee suka fito ba sai wajajen 3pm Library tayi ko zata ganshi amma baya nan hakan yasa tanufi department dinshi taga duk sai tsiraru hakan data gani ne yasata tabbatar da yatafi gida, dawowa tayi class dinsu ta kira bala awaya akan yataho kawai don dama ita tace mashi yau sai 4 zaizo daukarta don da nufinta suyi karatun 1hr da Deen kafin sutafi gida. Babu 6ata lokaci sai ga bala ya qaraso ya kirata ta fito suka wuce. *WASHEGARI* Kasancewar duk sunada morning lesson yasa basu hadu ba sai wajajen 11:30am Zaune suke a wani silent cool wuri inda mutane basu fiye zurga2 awajen ba Zee keta zuba yayinda Deen ya maidata t.v sai zabga Murmushi yake "... Bakaji yadda naji haushi ba wlh, na tsani na gaida mutum yaqi amsawa, at that instant zan fara regretting gaisuwar, wai sai can ya tashi yana tafiya with that double crooked yams he called legs ya wuce gaban board yana muzurai kamar wanda ya hadiye gari, sannan cikin frog-like voice dinshi yace 'kowanne ya zauna bisa different chair' I was like 'dakace hakan, da bisa cinyarshi nace zan zauna?'" Dariyar Deen data fito fili ya dakatar da ita "haka kikace mashi?" inji Deen cikin Dariya Harararshi tayi tace "ya za'ayi incemishi haka? Cikin zuciyata nace hakan, all thanks to Allah dayasa ba'a gane abinda mutum ke fadi a zuciya da duniyar nan takoma war ground" tafada tana sipping juice din hannunta Dariyar da Deen keyi yadan tsagaita yace "but sai inga kamar zaifi idan ana hangen komai dake zuciyar mutum, kinga ko qarya mutum yayimaka zaka iya hangowa directly from the heart" Dan Wara idanu zee tayi tace "no, gwara dai da ba'a gani don some people dole saidai a zuciya zaka maida masu martani kamar dai Wannan mr frog din" Murmushi yayi yace "hmm but still gwara adinga gani, saboda wasu a waje they'll smile to you amma aciki they hate you kuma Kana tareda su always bazaka ta6a sanin whats on their mind ba amma idan ana gani kinga no more pretending" Daga kafadu tayi tace "that's their problem, so far hateness dinsu bazai yi affecting dina ba, To can su gane, ni bazan iya pretending inason mutum ba bayan ba haka bane har cikin zuciya, if I don't like you, To I don't like you ne and I don't care what people think about me, I just dont care" Murmushi Deen yayi yace "that's why mutane dayawa don't like you" Dagowa tayi ta kalleshi tace "mene?" Shima kallonta yayi yana dan qara wara idanu yace "yes, your I don't care manner yasa mutane dayawa basa sonki a school dinnan" "harda kai ko?" Dan zaro ido yayi yace "ni?" "yes, sau nawa kake cemun you dont like me? You hate me" tafada tana fuming Qara wara idanu yayi yace "O'O! Ni bance I hate you ba, kawai nace I don't like you ne kuma saboda lokacin you're harsh ne amma yanzu.." Sai kuma ya daga kafadu "amma yanzu me?" tafada kamar zata makeshi Dan gaucewa yayi yana Dariya sannan yace "amma yanzu you're nice" Daga gira daya tayi tace "really?" "yes, amma kadan fa, you're a little bit nice, kamar haka" yafada yana nunamata daidai saman qaramin yatsunshi "ba haka ba?" tafada tana wara hannu tana mai nuni da tsayin tsakankanin hannun nata "A'a, bekai hakaba tukkuna" yafada yana Dariya ganin yadda ta 6ata fuska Ta6e baki tayi tace "well, me I don't care idan mutane basasona, mutane baka iya musu gwara kayi living life dinka ka sharesu" "yes, sometimes gwara hakan amma kuma shaidar mutane akanka ba qaramin tasiri ke gareta ba, yes karka biye akan saika iyawa mutane amma kuma kar hakan yasa kuma kasa su dinga yimaka wani kallo daban, care about what people say about you sai ka tsinta aciki, idan akwai inda ake buqatar gyara saika gyara idan kuma babu saika share amma nuna halin ko in kula ga abubbuwan da mutane ke tunani akanmu yanada illa ko babu komai bamusan sadda zamu mutu ba and idan ka mutu, the same mutanen da baka damu dasu ba su zasu fara fadin abinda suka sani gameda kai, for instant idan na kirki ne kuma mutumin is nice to them sai kiji anfara yabonshi ana jimamin rashi da akayi amma idan sa6anin haka ne saikiji ana magangannu marassa kyau gameda mamacin kuma ana nan ana daukar record amma they dont care wasu ma don aqara maka kan abinda zaka tarar zasu dinga yi dakai din kinga ai that's not proper bayan haka kuma mutane ganin su kike amma bakisan baiwar da Allah yayi musuba, wani kambun baka gareshi duk abinda ya fada akanki yana iya binki, akwai masu haka dayawa Batareda suma sunsan sunada shiba, kinga gwara ka kiyaye kuma kabi a sannu don ko ba haka ba ma, kasancewar mutumin mutane yafi dadi akan mutum yazamana kowa baya sonshi only few does" Tunda yafara maganar ta kafeshi da idanu harya kai aya, mammaki ne sosai aranta, ina duk yasan Wannan? Mutumin datake yiwa kallon sha uku sha hudu shi yasan duk wadannan? Ganin batace komaiba sai yacigaba dacewa "and also rashin kunya ga nagaba dakai babu kyau, komai abinda zaiyimaka kau, Koda yayi maka wani abu marar kyau to yaci albarkacin girme maka dayayi kayi hqr ka kyaleshi shi da Kanshi idan ya nutsu daga baya zaigane yayi ba daidai ba kuma koba komai yasan kanada issashiyar tarbiya bazai kuka dakai akan hakan ba Yanzu misali mr ibrahim, idan kika duba babban mutum ne, yanada 'ya'ya qilama yakusan haihuwar ki, he's well respected man, mutane na yabonshi saboda kyawawan hallayenshi, yes ke yana nuna miki baya sonki amma kin ta6a tambayar kanki meyasa? Kin ta6a lura da yanayin mu'amallarshi da sauran dallibai sannan ki duba da naki? Meyasa yake son kingin dalliban ke yake nuna maki akasin haka? Ke zaki bawa kanki amsa And also ki dinga dora kanki a mizanin wasu, idan kece yaro dan 10yrs yayi maki rashin kunya Koda kuwa laifinki ne ya zakiji? Am sure idan bakiyi mashi duka ba saikin mareshi, so goes with mr ibrahim, shi bazai dakeki ba don kin wuce duka a wajenshi amma abinda kikeyi dake qonamashi rai zaisa ya dauki mataki ta wata hanyar kamar yadda yake shirin yi yanzu don ko kece hakan zakiyi saboda abinda zakiyi tunani akai shine yaya zakiji idan mutum tsaranki ya yarfaki agaban wadanda ke ganin mutuncin ki? To bare ace kin girmeshi nesa ba kusaba Bayan haka kuma mallamai sunada matuqar muhinmmanci agaremu don Allah ma na amsar addu'ar su akanmu, To idan hakane sai kiyi tunani tsinuwarsu agaremu baxaiyi tasiri akanmu ba kuwa? Ni aganina mr ibrahim bashida laifi a Wannan gabar taku idan ma yanadashi kiyimashi uzuri da shekarunsa ku shirya, am telling you zakiji dadin subject dinshi fiyeda yadda kike zato... Amma fa shawara ce" yafada yana daga kafadu yana kallonta da innocent eyes dinshi Zee da tundazu ta maida shi t.v takasa cewa komai ta Kauda kai tana jan numfashi Hakan yasashi tsarguwa sai yace "sorry idan magangannuna sun 6ata miki rai, am just trying to.." Ringing din wayarta ta katseshi hakan yasa yayi shiru yana kallonta Cirota tayi daga jakkarta ta daga ta kara a kunne tana kallonshi Shiru tadanyi sannan can tace "am around the school, menene?" Bamuji abinda akace ba sai cewa tayi "ok ganinan, am coming" Daga haka ta katse kiran sannan ta dago ta kalleshi taga shima ita yake kallo Murmushi tayimashi shima ya maida nata martani "bari naje Deen" tafada tana maida wayarta a jakka Kamar zai tambayeta ina? Saikuma yayi shiru Ganin hakan yasata yin Murmushi ta miqe tsaye tana rataye jakkar tace "wajen mr ibrahim, guess result din zan amsa, sumee tabugo wai yana nemana" Murmushi yayi mata yace "ok good luck" "thanks, zan dawo in tardaka anan?" "no, library zan koma, iskar nan wajen yafara yawa, idan kuma 1 tayi zan wuce class" "ok see ya, ai bazan kai 1 dinba tunda nasan result din kawai zai bani, saina dawo" "To, adawo lfy" Batace komaiba ta juya ta wuce shikuma yabita da kallo harta 6ace mashi Ajiyar zuciya ya sauke yana daga kafadu sannan shima ya tashi ya tattara littatafan shi yanufi library don iskar dake kadawa harya fara mashi yawa gashi dama mura yake dukda da sauqi sosai... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:33 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *018* Tafiya take amma magangganun Deen ne keta dawomata a kwanya Tarasa dalilin dayasa magangganun suka tsaya mata sosai a rai har tanajin tasirinsu ajikinta Da Wannan tunanin ta qarasa kofar office din mr ibrahim Knocking yayi, saida yabata izinin shigowa sannan ta tura qofar tashiga Abin mammaki sai jitayi ta tsargu ga wata uwar kunya data lullu6eta kamar ta nitse lokacin da yadago suka hada ido hakan yasata janye nata da sauri ta ida Qarasowa cikin office din "good afrernoon sir.." tafada a hamgame Batareda ta kalleshi ba "afternoon" ya amsa a taqaice shima Batareda ya kalleta ba Saida yagama abinda yakeyi sannan ya dago yasake kallonta saikuma ya Kauda kai yana zaro wata takarda "here.." Dagowa tayi taga miqomata yake, hakan yasata qarasawa sai samun kanta tayi da amsa hannu biyu Dan kallonta yayi saikuma ya Kauda kai yajawo wani aikin Ganin still tana atsaye yasashi cewa "zaki iya tafiya" Kada kai tayi sannan tajuya tabar office din Binta da kallo mr ibrahim yayi harta fita sannan yakoma ya jingina da kujera yana cije lip din qasa Sosai scores din dataci yabashi mammaki, tunma yana marking yake mammakin yanayin aikin nata, da ba agabanshi tayi ba da saiyace ba ita tayi aikinnan da kanta ba Hakan ba qaramin 6ata mashi rai yayi ba don yaga alamun duk inda ya 6ullomata saita sha, yarasa hanyar dazaibi ya rama wulaqancin datake mashi, yarasa yadda zaiyi daita. Koda zee tafito saikuma taji batason komawa wajen Deen Wucewa tayi inda tasan su sumee suke As usual, fira ta tadda sunayi ana shewa Ganinta yasa duk suka maida hankalinsu kanta "hey guys!" tafada tana Qarasowa wajensu "hey!!!" Duk suka amsa mata dashi "yane?" tafada tana zama cikinsu "normal, ya? Kin kau je kiran mr ibrahim kuwa?" inji sumee Kada kai kawai tayi alamun eh tana komawa ta jingina da bishiyar bayanta "To ya kuka qare? Hope dai kina tafe da good news" inji deeya cikin zaquwa "well, ban saniba nima don ban ma bude ba" tafada tana nunamasu takardar a hannunta Har rige rigen fizgewa suke a hannunta suka shiga warwarewa cikin doqi Shiru tayi kawai tana kallonsu Batareda tace uffan ba Sosai score dinta ya Girgiza zuciyarsu don ba haka sukayi expecting ba Saida suka dan ja lokaci suna Bin takardar da kallo sannan sumee tayi qarfin halin cewa "wow! Masha Allah, gaskiya abu yayi kyau" Sai a sannan kingin ma suka hau yaqe suna yaba score din nata Itadai batace komaiba sai dan Murmushin datayi kawai "kai amma abu yayi, gaskiya mungodewa Allah dayasa mr ibrahim ya tausaya yabarki kikayi wani, kinga yanzu no more fargabar carryover" inji rukky wanda da zaka bibbiya yadda zuciyarta take akan hakan dakasha mammaki "aikau dai Allah ya sanya alhairi, ya taimaka kam" inji nurr tana maida mata takardar Amsa tayi tana cewa "thanks" ta maida a jakka Batareda ta duba ba Firar tasu yanzu ta rage armashi don kowa da abinda yakeji a zuciya na rashin Jindadin abinda yafaru ga zee Sai anan kowacce tafara fargabar carryover din wa kanta don da su bata tasu suke ba, itan dai data tsaremasu wuri suka sama ido Ganin zaman ya isheta wajen yasa ta tashi tace masu bari taje library tayi karatu Duk da to suka amsamata don dama suna buqatar space su tattauna akan Wannan mummunan abin da yafaru agaresu Duba agogo tayi taga 1 tadan wuce, tasan baya library din yanzu, yana class Illai kuwa data shiga bata tardashi ba, bata damuba ta wuce ta zauna ta dora jakkarta saman desk din ta buga tagumi da hannu bibbiyu Shiru tayi yayinda tashiga yiwa magangganun Deen na dazu fashin baqi Tabbas idan bazata sanyo san zuciya a lamarinnan ba tasan Deen nada gaskiya a Wannan fannin Itace cause din gabarsu da mr ibrahim, don tun farko ita ta taqaleshi Ta shigo class Batareda izininshi ba yayimata magana maimakon tayi apologizing tazo tawuceshi ta fice Tabbas kowa akayiwa haka saiyaji haushi kuma saiya dauki mataki akai wataqila shiyasa ya addabeta a lokacin tazama abin dizgawarshi a class inda daga baya dataga bazata iya cigaba da dauka ba tabar attending lecture din nashi Tabbas idan za'a bibiyi gaskiya ita keda laifi saidai ga lokacin, tunanin cewa tafi qarfin kowa dakuma qiyayyar datakema school din yasata take gaskiya ta cigaba a hakan Ciro takardar tayi ta warwareta itama tana kallo *17%* Saidai abin mammaki bata tsinci kanta cikin farin cikin da take tunanin zata tsinci kanta ba Haka kawai takejin zuciyarta a cinkushe tun bayan maganarsu da Deen. Tunda take dasu sumee basu ta6a nunamata abubbuwan datake ba daidai bane saima turata dasukeyi, duk abinda tayi daidai ne a wajensu saigashi yau tasamu wanda ya nusar daita abubbuwan datakeyi ba daidai bane dakuma hujjoji wanda ta gamsu dasu Tunanin dayafi tsayamata a qwalwa shine, yau idan ta fadi tamutu me yan school dinnan zasuce akanta? Me mr ibrahim zaice? Wa zaiyi jimami akan haka? Bayan qwatarta (su sumee) wazaiyi jimamin rashin ta har ya bude baki da sunan yimata addu'ar jin qai awajen Allah? _babu_ dayan zuciyar tabata amsa _dadi ma zasuji sun rabu da alaqaqai_ dayar zuciyar ta fada mata Cukwikwiye takardar tayi ta damqeta a hannu sannan ta kifa kanta a desk din gabanta tana lumshe idanu, ita kanta Batasan yadda zata misalta yadda takeji a zuciya ba, kawai jin ranta take a matuqar jagule, jagulewa marar misaltuwa. Batasan iya lokacin data dauka ba ahakan sai jin cool voice dinshi tayi sama2 Jitayi an bubbuga desk din ana cewa "hey, get up!" Sai alokacin ta bude idonta sannan ta dago ahankali Tsaye taganshi akanta da dan guntun Murmushi a fuskarshi Zama yayi yana cewa "sleepy skull, kin karya dokar library" Murmushi tayi tana zama daidai tace "harkun gama?" "yes, dazu nayita jira shiru, saura kadan nayi missing lecture" Murmushi tadanyi wanda yafi kama da na yaqe tace "be sallameniba da wuri ne" "ok, hope dai an dace" yafada yana dan wara idanu Ganin kallon dayake mata yasata Murmushi sannan ta bude hannunta dake damqe da takardar still tabashi Qara wara idanu yayi yace "O'O! Wannan ce takardar kuma kikayi squeezing dinta haka" Daga kafadu kawai tayi ta koma ta jingina da kujera "pheew! You're careless" yafada yana zaro mata idanu "whatever!" itama ta fada tana maida kanta akan desk kamar dai dazu Harararta yayi sannan ya warware takarda zuciyarshi na gayamashi ko She failed ne shiyasa duk tayi haka Ganin score dinta yasashi waro idanu "wow! You passed!" taji yafada, hakan yasata danyin Murmushi daga kwance "look you scored 17" yafada yana nunamata cikin murna "I know' tafada a taqaice "amma meyasa bakya murna?" yafada murnanshi na dan komawa ciki "just" taqara amsawa a taqaice Tsayawa yayi yana kallonta "are you ok?" yafada asanyaye Hakan yasata dan dago idanu ta kalleshi daga kwancen "yes, kawai banajin dadine" ta amsa tana tashi zaune Bata fuska yayi kamar zaiyi kuka yace "sorry" Kada mashi kai kawai tayi tana dan Murmushi "ko muje school clinic abaki magani?" inji Deen cikin damuwa "no, dont worry dana je gida zansha nawa" Daga haka basu qara cewa komaiba, ita ta maida kanta a jikin kujera tareda lumshe idanu shikuma ya fiddo littafi yana dubawa yana yi yana Dagowa ya kalleta akai2 Kiran sallah ya fiddasu library din, ita tawuce masjid din mata shi yawuce na maza Koda suka fito bankwana sukayi don wucewa Deen zaiyi gida ita kuma sunada lecture yanzu, hakan yasa suka rabu anan akan sai gobe idan Allah yakaisu inda yake qara jaddadamata tafa sha magani idan taje gida. Lecture din dai rabi da rabi ta fuskanta don mind dinta baya wajen Saida sukayi 30mins sannan suka fito Direct parking space ta nufa don bala yariga yazo Babu 6ata lokaci tashiga yaja suka fice *** Ranar haka ta qarashe yinin cikin rashin kuzari. Magangganun Deen sun kasa barin ta ta sarara, duk motsin da zatayi saita tunasu kuma saitayi zurfi atunani akansu *WASHEGARI* Daga takardar yayi don hanata gani yace "kibar kallo haan?" Dariya tayi tana qara tantado dan gani tana cewa "To menene idan na kalla haan?" Maida takardar yayi bayanshi yace "idan teacher na marking dama student na zuwa ya kalla ne?" yafada yana hade gira "Sai afara akanka" tafada tana Dariya Saka takardar yayi a aljihu yace "To shikenan, nafasa marking din sai naje gida sai nabaki gobe" Wara manyan idanunta tayi tace "gobe kuma? To shikenan yi abinka nabar leqowa" Kauda kai yayi yana hade rai yace "no, sai naje gida" 6ata fuska tayi tace "O'O! Sokake in kasa barci yau?" "me zai hanaki barcin" "zullumin marks da zanci mana" "To ba ke ke leqowa ba?" "To nabari, kaga ma ba kallonka ba nake" tafada tana kallon gefe Saida ya gallamata harara sannan yaciro takardar yacigaba da marking yana yi yana satar kallonta yaga ko zata juyo Bata juyo dinba amma tana satan kallonshi shima ta wutsiyar ido har yayi ya gama. "To juyo" inji shi Juyowa tayi ta gallamashi harara "mutum da abinshi a hanashi kallo ai gashi yanzu zaka gwadamin duk 6oyon.." Ganin yana linkewa alamun yayi zuciya be bada wa yasata Saurin Wara idanu tana cewa "laa, wasa fa nake maka kai bakasan wasaba?" ta qarashe tana fizge takardar ta tashi tsaye tana warwareta da sauri Ganin abinda taci yasata dan yin qarar murna "yeeee!" saikuma tayi mashi gwalo 🤪 Kwafa yayi kawai yana jinjina kai Komawa tayi ta zauna tana cewa "dama dan kaga naci duka shiyasa kake jamin rai ko" Harararta yayi yace "stop talking to me ni babu ruwana dake" "Sai nayi, sai nayi!!!" ta qarashe da qarfi Saurin dode kunnuwa yayi yace "O'O! Why are you shouting?" "I'll keep shouting indai bakace da ruwanka dani ba" tafada tana yin ready din yin wani qarar "To, ok naji! Da ruwana dake, shikenan!" yafada da dan qarfi sannan ya juya mata qeya Dariya tayi tana cewa "Allah ya taimakeka to" tafada tana qara duba takardar aikin daya bata yanzu ta cinye duka Sosai haduwa da Deen ya chanzata cikin yan kwanakinnan, yanzu she's more happy and lively A kullum idan tazo school burinta ayi agama ta Kama gabanta ta koma inda tafito amma yanzu har qagara take gari yawaye taje school duk don su hade dashi Tunda take bata ta6a sakin jiki da namiji kamar yadda tayi da Deen yanzu ba, kai ko mace babu wacce ta ta6a sakin jiki daita kamar yadda tayiwa Deen, lafiya lau suke wasa da dariyarsu, idan tana gabanshi itama komawa take mashiririciya kamar shi, daga abokin fada yakoma aboki yanzu kuma bestie duk acikin yan kwanaki. Sosai takeson tarraya dashi don he's fun to be with Kallonshi tayi taga yana gyara setting agogon hannunshi Shiru tadanyi tana taunar qasan bironta sannan ta janye tace "Deen?" Dagowa yayi ya kalleta "inaso muyi magana dakai ne" Jin haka yasashi maida dukkan hankalinshi akanta Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace "akan maganar damukayi jiya ne... You know, nima banason gabar dake tsakanina da mr ibrahim but.. Bazaka ganeba, mr ibrahim mugun dan dizgi ne, dama abinda yafara hadamu kenan, duzga mutane, yanzu ina iya zuwa inbashi hqr ya yarfani, I know him very well" tafada tana 6ata rai Shiru Deen yadanyi sannan yace "kinaso ku shirya ne?" Itama shiru tayi kamar mai nazari can kuma ta daga kafadu tace "maybe" Murmushi yayi yace "bazai duzga ki ba, I bet you" "no ni kadai nasan halinshi, bana sone wajen gyara a 6ata gabadaya don idan ya dizgani zuciya na iya dibana nayi mashi rashin kunya and I don't want that to happen" Shiru Deen yasakeyi na wani lokaci kamar mai nazari sannan ya kalleta yace "To, why not muyi haka? Karki tareshi directly kibashi hqr, kibi indirectly" "how?" tafada cikin yanayin rashin fahimta "first step shine kifara attending class dinshi ma'ana daga yanzu no more missing din lecture dinshi" "tayaya hakan zai taimaka?" ta tambaya cikin rashin fahimta "ta hanyoyi da dama, kinga na farko abin zai bashi mammaki, he'll be like anya kuwa kece? Na biyu hakan zai dan sauko dashi daga fushin dayake dake, idan kika tunkareshi daga baya baxaiyi bursting ba zaiyi considering dinki" "hmm idan ya koreni daga class din fa?" "bazai koraki ba, da farko zaiyi mammakin ganinki a class dinshi, sai kuma ya kyaleki yaga dame kikazo dashi, ke kuma alokacin sai kiyita neman kusanci dashi ta hanyoyi daban2 kamar amsa tambaya idan yajefo, tambayarshi abinda baki ganeba, kodama kin gane ki dinga tambaya, yadai kasance kuna communicating ko yaya ne, da haka da haka har muga perfect time daya kamata kibashi hqr" Shiru tayi tana nazarin maganganunshi can tace "To students fa? Me zasu ce gameda hakan? Baka ganin class dina zai zube?" saikuma tayi Saurin matse bakinta don zancen zuci ne yafito fili Murmushi yayi yace "kefa kikace bakya damuwa da abinda mutane ke cewa akanki, you see mutane baka iya musu, so far kinsan abinda kikeyi shine daidai to ki rabu da magangannunsu saidai idan abinda kikeyi dinne ba daidai ba Wannan saiki gyara, so dont think about what they'll say just act as if you dont care" Shiru tasake yi tana nazari sosai, duk abinda yafada gaskiya ne, to amma tana iyawa kuwa? Ko babu komai akwai kunya, tayaya zatayi mursisi ta zauna a lecture dinshi bayan abubbuwan datasha yimashi "please dont think negatively about this, Wannan shine daidai duk wani tunanin da zai zomaki daga baya to daga shaidan ne, dont give the devil a chance, act strong, show him you're stronger" yafada cikin qarfafa mata gwiwa Kada kai tayi tana cewa "ok" a sanyaye Dadi yaji "that means zakiji din?" "yes.. Zan jaraba, amma fa da sharadi" "meye sharadin?" "idan yasaki ya dizgani akanka zan rama, zuwa zanyi saitin kunnenka da speaker inyita kwalamaka ihu harsai eardrum dinka ya Fashe" Dariya yayi sosai sannan yace "deal" Kada kai tayi itama tana Murmushi tace "kadai rubuta ka ajiye" "no p, yanzu yaushe zaki fara?" "gobe insha Allah, gobe thursday munada lecture dinshi har double period" ta amsa acikin zuciyarta tana tantanmar anya tana iyawa? "good! Please try your best, na miki alqawari ke Kanki sai kinji dadin rayuwarki don dakun shirya jizakiyi kamar an dauke miki qaton dutse ne a qirji, zakijiki very free" "dont worry zanyi insha Allah" tafada in affirmation "To Allah ya yarda" Da amin ta amsa suka cigaba da firarsu wanda kallo daya zakayi ka hango tsantsar shaquwa atsakaninsu yadda kasan sunyi shekaru tare ***** "guys nifa na kasa ganema Wannan matar, tare zamu fito class daita amma the next minute mu nemeta mu rasa?" inji nurr "hmm nima fa abinda ke daure min kai kenan kwana biyunnan, yanzu kwata2 ta rage hulda damu, bama ganinta ma sai lokacin lecture kuma da anfito mu nemeta mu rasa" inji deeya "To ko wasu qawayen ta chanza?" inji sumee "qawaye kuma? Kai I dont think so, kinsanta da shegen d'agin kai muma tayaya muka cika, kawai dai da abinda take 6oyemana nake tunani idan ba haka ba meye na janyemana haka?" "Gaskiya nima abinda nake tunani kenan, tabbas akwai lauje cikin nadi, akwai abinda takeyi wanda batason musani kuma Dole musani" inji rukky "Gaskiya kam, Dolene musamata ido, mu dinga lura da kowanne movement dinta" inji deeya "Gaskiya, hakan xamuyi bazai yiwu ta maidamu shashashai ba" inji sumee Haka sukaita firarsu duk akan yadda zasuyi monitoring dinta har sugano inda take zuwa a 6oye (Allah ka rabamu da mutanen da basa facing din tasu damuwar saita wani🤲🏻 Allah ka tsaremu daga sharrin duk mai sharri (Ameen)... ✍️ Manage please 🙏🏻 yanzu ba lallai bane ku dinga samun long page don haihuwa akayimana bansamun zama amma zan dinga yin yadda ta kama, da babu gwara babu yawa Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:33 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *019* *THURSDAY* Tundazu takejin so nervous, jitake kamar bazata iyaba, kamar ta tashi ta fita. Su sumee basu kawo komai aransu ba ganin rubutu take, atunaninsu da mr ibrahim yashigo zata fita tunda tasaba yin haka idan ya ritsata a class din Shiru class din da aketa hayaniya yayi lokaci guda wanda hakan ke tabbatar da shigowar mr ibrahim. Yan cikinta ne suka kada dataji kawo na tashi tsaye suna hada baki wajen gaisheshi. Dakyar itama ta tattaro sauran kuzarinta tamiqe tsaye kamar sauran saidai takasa dago kanta dake a sunkuye Tsitt class din ya dauka, shi be amsa gaisuwarsu ba kuma be basu izinin zama ba don shi nan jira yake ta fita kamar yadda tasaba yafara gudanar da abinda yakawoshi Daga tsayen datake kanta a qasa takejin yawon idanu akanta wanda hakan yaqara mata restlessness din datake ji, sosai zuciyarta ke bugawa tana danasanin zama a class din tun farko "sit!" ta tsinkayi muryarshi na cewa haka Duk zama aka shigayi ga dunbin mammakinshi wai harda ita a masu xaman Kauda mammakinshi yayi ya ajiye takardunshi acikin zuciyarshi kuma yana tambayar kanshi yau kuma dame tazo? Gyaran murya yayi wanda saida zee tadan firgita don dama Duk a tsorace take kamar wanda za'acema kyatt ta ruga Ta riga tagama sadaqarwa yau ta kawo kanta don bazai ragamata, cin mutunci zaiyi mata harna innanaha "na'am, how are you guys?" yafada yana satar kallon zee qasa2 wondering ko yau buguwa tayi ne shiyasa bata tantance komai Duk amsa mashi sukayi da they're fine "good what was our last topic?" yafada yana bude handout din gabanshi Dayake Duk ansan dabi'arshi na kafin ya dora wani darasi saiya bibiyi wanda sukayi na qarshe harma yayi musu tambayoyi akai, hakan yasa suke shiryama hakan don tsoron a cankoka ka kasa kata6us Tare suka hada baki suka bashi amsa ta hanyar fadin topic din da sukayi qarshe Tambayoyi yafara jefamusu akan topic din kamar yadda yake a al'adarshi suna amsawa Duk abinda ake zee bata dagoba, tana nan dai zaune kanta aqasa saidai kallo daya zakayimata ka gano tana cikin takura matuqa A bangaren su sumee kau suma sosai sukasha mammakinta, they can't believe yau zee ce zaune lecture din mr ibrahim, sosai gulma ke cinsu amma ba damar yi dole suka danne suna satar kallonta ta wutsiyar ido kamar yadda mafi akasarin Yan class din keyi suma. Saida yagama tambayoyinshi tsaf sannan yasa kowa ya fiddo handout dinshi domin dorawa daga inda suka tsaya Duk ciroshi sukayi including zee suka bude daidai inda yace, nan aka shiga karatun gadan2 Sosai tayi qoqarin saita kanta don ganin tayi yadda Deen yace saidai ko kadan takasa samun courage din yin tambaya kamar yadda yace ko ta amsa tambayoyin Dayake jefowa jefi2 Dukda tasan amsoshinsu 1hr lecture din ya daukesu wanda zee jinshi tayi kamar shekara daya, tsabar daburcewa ko rubutun kasa yi tayi Saida yagama tsaf sannan ya kwashi tarkacenshi yaqara gaba, zuciyarshi fal mammakin abinda zee tayi yau Fitarshi a class din yayi daidai da fitar wani nannauyan numfashi daga huhunta wanda yafi kama da na 'Dakyar nasha' Class dinne yafara daukar hayaniya irin wanda yasaba dauka idan babu lecturer aciki Saurin mayar da handout din tayi ta rufe ta jefa a jakka sannan ta miqe still tanajin idanu akanta Bata damuba ta ciro baqin shade dinta ta toshe idanu dashi ta rataya jakkar tayi waje Ganin haka yasasu suma Saurin miqewa suka maramata baya batareda sun bari ta lura dasuba Tafiya take a nitse a zahiri amma a badini aqagare take taganta gabanshi, jikinta har tsumuwa yake, tanajin kamar ta ruga aguje taje ta sameshi ta amayarmashi abinda ke ranta. Tun daga nesa ta hangoshi zaune yabata baya, kanshi a qasa wanda bata raba dayan biyu tasan duba littafi yake Ganinshi yasata rage tafiyarta harta kaiga ta tsaya batareda ta ida qarasawa ba tana kallonshi Su sumee ma da suka iso wajen suka samu ma6oya suka tsaya kallonsu ta ma6oyarsu wondering wanene gayen don suma bayanshi suke gani Jin alamun ana kallon shi dayayi yasashi dan juyowa Ganinta yayi tsaye a dan nesa dashi ta kafeshi da idanu wadanda ke qyalli sanadin hawayen dasuka taru aciki Ganin haka yasashi saurin miqewa tsaye shima yana kallonta wanda hakan yayi daidai da warowar idanun su sumee cikin kaduwa "DEEN!" duk sukayi exclaiming cikin zuciyarsu Takowa yayi cikin tafiyarshi ta nutsuwa yazo gabanta yana rarraba idanu a fuskarta Nurr saurin dafe saitin qirjinta tayi jin zuciyarta na baraxanar tarwatsewa by their mere sight Dago idanunta dake salqi haryanzu da hawayen dataqi ba damar gangarowa tayi tana kallonshi itama Ganin hawayen yasashi rudewa harya kamo hannunta batareda ya saniba don duk a tunaninshi wani abun mr ibrahim yayi mata Tsakanin shock din da zee da Nurr sukaji bansan wanda yafi wani ba Don sosai hakan yayi tasiri akansu su biyun saidai ta fanni daban2 Fitowa Nurr tayi niyyar yi daga ma6oyarsu taje wajensu ido rufe allah ya taimaka su deeya sukayi saurin kamota Qoqarin fizgewa take cikin jin wani mahaukacin kishi na tasomata saidai sunqi sakinta saima janyeta da sukayi daga wajen ma gabadaya suka bar wajen suna rufemata baki don karta tonasu Fizge hannunta zee tayi da sauri tana watsamashi wani kallo hakan yasashi dan ja baya yana dan wara ido "am.. Sorry, I..." wuceshi datayi taje ta zauna inda ya tashi yasa kingin maganar maqalewa ya bita da kallo Jiki asanyaye shima ya tako zuwa inda take zaune shima ya zauna dan nesa da ita yana kallonta Tabbas abinda yake gudu yafaru, dole mr ibrahim yayimata wani abun, qilama dizgin datake gudun yayimata Tunawa yayi da yadda yayi ta convincing dinta yau da safe kafin ta yarda zatayi attending lecture din don dafarko cewa tayi tafasa don ita gaskiya tsoro takeji Haka yaita lalla6ata yana yimata alqawarin babu abinda zaicemata qarshema ya nuna yayi fushi kuma babu ruwanshi da ita harya miqe zai tafi saboda dama yau saboda ita yazo don baida lecture yau, Ganin Hakan yasata yarda zatayi, gashi yanzu abinda ya biyo baya Hadiye wasu yawu dasuka taru a bakinshi yayi yana kallonta cikin yin fiki2 da idanu kamar marar gaskiya yace "erm .. Are you ok?" yafada yana rarraba idanu Gani yayi ko kallonshi batayiba "amm.. Mud queen oop!.." ya dafe baki don tunawa da yayi batason sunan ga wani kallo na musanmman data juyo tana watsamashi Bata fuska yayi yace "O'O! Ni menayi kuma?" Zaro mashi idanu tayi a masifance tace "me kayi? Me kayi ma zakace? Ka turani can kai kananan hankali kwance? Bari kagani" tafada tana rarumo wani dutsi na kusada ita tanufeshi gadan2 Ganin Hakan yasashi saurin runtse ido yana qanqame jiki cikin jiran tsanmmani Shiru yaji babu abinda yasameshi can kuma yaji sautin dariyarta tanayi ahankali Ido daya yafara budewa ahankali sannan ya bude dayan ya waresu akanta yana kallon yadda take dariyar ga hawayen dasuka taru a idanunta sun gangaro Sakin baki yayi yana kallonta yayinda itakuma yadda yake kallonta din ke qara Bata dariya "Are you crying or laughing?" yafada yana kallonta cikin mammaki don shi beta6a ganin inda ake dariya da hawaye lokaci daya Qara volume din dariyarta tayi harda dafe ciki "ya kamata kaga fuskarka a mirror yanzu" tafada tana nuna fuskarshi cikin dariya "ko kuma ke ba? Ke ke buqatar mirror, kuka fa kike da dariya" yafada cikin al'ajabi Dariyar tacigaba dayi tace "Hakan ake kira mixed feeling" tafada cikin dariya Buga tagumi yayi yana kallonta yace "to, nidai am i safe" Dariya tayi ta dauki littafi tayi kamar zata kwalamashi tana cewa "gaka kusada mahaukaciya ba?" Kaucewa shima yayi yana dariya "da farko nayi tunanin mr ibrahim ne, ashe..." saiyayi mata nuni da alamun mental problem Littafin da Bata makamashi ba dazu ta makamashi yanzu tace "nice mahaukaciyar?" Dariya yayi yana sosa kanshi inda ta kwalamashi yace "kinga laifina, laughing and crying altogether? Ca6 ban ta6a ganiba" "gashi Ka Gani yau" tafada tana share tears dinta dasuka gangaro mata "to ya? Tell me duk abinda yafaru" yafada cikin zaquwa Harara ta gallamashi tace "amebo! Ashe maza ma sun iya gulma?" Dariya yayi yace "whatever, nidai gayamin" Murmushi tayi tace "becemin komai ba kuma be dizgani dinba" Washe baki deen yayi yace "I told you ai" Murmushi taqarayi tace "amma fa baka ganiba, kamar na sume na dawo don tsoro, danaji zaiyi magana sai inji kamar zan sume don sai inta ganin dani zaiyi, wuhh! Na sha dakyar" tafada tana dafe kai Dariya so sai deen yashiga yimata "matsoraciya kawai!" "eh ba komai" tafada tana Murmushi "yanzu Are you still in ko zaki janye?" yafada cikin Murmushi "am in! In!! In!!!" tafada sunayin dariya tare "nayi tunanin tsoro bazai qara Bari kiyi ba" yafada cikin dariyar jindadi "tsoro your head! Ni cema akayi kaine" "who? Don't even compare me to you don nafiki jarumta" Daga gira daya tace "haba? Ahakan" Huro hanci yashiga yi yana cewa "kina tantama ne" Dariya tayi tana rufe baki tace "sunan wata unguwa" tafada tana nuna hancinshi dayake hurowa "wai ita?" yafada yana qara hura hancin "qofar marusa" tafada cikin Dariya sosai Hade gira yayi ya dauki Littafi shima zai kwalamata tayi saurin tashi tareda fizge jakkarta tayimashi gwalo tajuya ta tafi cikin sauri tana waiwayenshi tana mashi Dariya ganin haryanzu fuskar ahade take *NURR* "wai nurr meke damunki ne haka? Kuka fa kike?" inji deeya Kasa cewa komai nurr tayi kamar yadda takasa tsaida hawayenta, hoton her hot crush wato Deen kawai take hange riqeda hannun zee Bata ta6a tunanin tanada irin wannan kishin ba sai yau don yadda ziciyarta ke tafasa da tasan yadda za'ayi ta cirota ta jefar da tayi ko ta rage jin radadin datake ji "hmm aini ba tun yauba na karto jirginta ba, dama tun lokacin data fara xaqalqalewa akan al'amurranshi nasan sonshi take, bakiga yadda take mayar min da magana ba ranarda su master suka tareshi, kamar irin na ta6a qanin innansu? Tun anan nasan da walakin goro a miya, hmm aikau aiki ya ganki don inhar zee ce to ki qaddara kin rasashi kin gama don duk abinda tasa agaba to saita mallakeshi gwara ki tashi tsaye da wuri kisan nayi" inji sumee tana rungume hannaye a qirji tana girgiza qaffafu "amma zee tacika baqar munafuka, dama ashe duk 6oye 6oyen datake tasan abinda take qullawa, wai yaushe ma Deen yadawo school din bamuda labari?" inji rukky cikin alhini "ai dama ire iren zee su akecewa poisonious snake, maciji sari ka noqe, fuska musa zuciya fir'auna" inji sumee "ai dama kun ta6a ganin tabarmu mun samu abun kanmu? Koda yaushe sotake ya kasance itace agaba muna abaya muna take mata baya, a kullum sotake muzama fadawanta shiyasa take qoqarin ganin ta mallake komai ta gaje duka, wataqila lura tayi kina sonshi shiyasa ta biyomiki ta bayan qasa don ta mallakeshi inba haka ba dama shiri suke? Mutumin da ta tsana take wulaqantawa?" inji deeya "nima fa abinda ke bani mammaki kenan, Mutumin da tayi sanaddiyar kwanciyarshi gadon asibiti harna kwana uku shi zata dawo yanzu tace tana so? Wlh ba sonshi take ba kawai tsabar mugunta ce kawai, lura tayi nurr na sonshi shiyasa tabi ta wannan hanyar don kuntata mata takuma gwadamata tafita matsayi da iko ta koina, allah sarki bawan allah, na tabbata dadin baki tayimashi shikuma tunda ba cikakken hankali gareshi ba ya fada tarkonta, kawai nurr ki haqura kawai don fada da aljani ba riba, tunda tasanyo muguntarta kawai mu haqura ya muka iya?" inji rukky tana marairaice fuska Aikau kamar jira nurr take ta zaburo tana cewa "wlh bazata yiwuba! Deen nawa ne! Nawa ni kadai! Ba yar kaza kazan data isa ta rabani dashi, akanshi zan iya komai ma! Idan nace komai ina nufin KOMAI!!" sai kuma taqara fashewa dawani kukan mai cin rai "aikau ina bayan ki nurr, lokaci yayi da zamu nunama zee muma da zuciya a qirjinmu, lokaci yayi da zamu nunamata bafa tsorontaba akeji, Shiru Shiru ai ba hauka bane" inji deeya cikin fushi "aikau dai, lokacin daukar action yayi, lokacin da zamu nunamata ita ba kowan kowa bace, dolene mu dusasar da tauraruwarta mu hada qarfi da qarfe mu kwato soyayyarki, dole muje musameta muyi mata tass!" inji rukkyy cikin bala'i Wani makirin murmushi sumee tayi tana cewa "anzo wajen.. Guys albishirinku, nasamo mana hanya mafi sauqi wajen cin ubanta hankali kwance batareda mun tadawa kanmu hankali ba, tauraruwarta zata dishe, rayuwarta zata tarwatse, dukiya da kyau da duk abinda take taqama dashi bazasu amfaneta da komai ba, zatayi mutuwar tsaye inda saita gwammaci mutuwa da rayuwarta, are you Guys ready? Kun shirya bada hadin kai domin kwatar yancinmu?" inji sumee tana kallonsu da daddaya "na shirya! Indai Hakan zaisa na mallaki deen to ashirye nake" inji nurr "muma mun shirya! Mun gaji da mulkin mallakan da ake mana, ki fadamana koma menene ashirye muke mu bada hadin kai" inji deeya, rukkyy na kada kai itama alamun goyon baya Wani makirin murmushi sumee tayi sannan tace "to ku matso kuji" Nan duk suka matso suka zagayeta tashiga radamasu mummunan qullin da suke hadawa zee... ✍️ _ashe makashinka yana nan tare dakai, duk inda kake ya bika_😭 Allah ka tsaremu Daga sharrin masu sharri 🤲🏻 Ummin fasihu🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:33 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *020* Kamar yadda kau zee tace haka tayi, tun daga ranar bata qara missing din lecture din mr ibrahim ba Tun tana d'ari2 akan zaiyi mata harta dan saki jiki Ganin Hakan yasata fara yin qoqarin zama active a class din ta hanyar daga hannu idan akayi tambayar da tasani Saidai ko kallon gefenta beyi bare yanuna yasan abinda takeyi. Da farko jikinta yayi sanyi har Hakan yaso ya sanyaya mata gwiwa amma da taimakon Deen dake qarfafa mata gwiwa ta cigaba batareda ta sare ba Duk lokacin daya jefo tambaya wanda mafi akasari Duk ta sansu don haryanzu suna karatu da Deen ahalin yanzu ma they're ahead of the class don Duk abinda mr ibrahim zai koyar a class kamar revision ne agareta don sun riga sunyi da Deen, Hakan kesa karatun kezomata da sauqi sosai Duk lokacin daya jefo tambaya saita daga hannu dukda tasan bazai ko kalleta ba, tun tana d'ari2 harta ware da kallon da yan class ke yawan binta dashi Ana haka watarana mr ibrahim ya jefo wata tambaya wanda Duk aka rasa wanda zai amsata a class din sai zee don ita kadai ta daga hannu A bangaren zee kau batasan ita kadai ta daga hannu ba don tasaba akwai masu kwalwa a bayanta don sau dayawa yana cankosu su bada amsa Tsit class din yayi students din suka zubamasu ido don ganin mezai faru next Mr ibrahim beda option tunda ita kadai ta daga hannu, rashin bata damar maganar na iya zama wani abun daban ga students din shiyasa ya cije ya fuske ya nunata yana cewa "yes? Say it" Zee batasan da Ita yake ba don ita harta saba daga hannu kawai take amma bata amsawa ganin duk an kallota yasata tsarguwa, ta juya bayanta taga babu kowa mai hannu sama ita daya dece Hakan yasata jin cikinta ya murda don kwata2 bata shiryama hakaba, da tasan babu wanda ya iya da itama bata daga hannu ba Ganin tana neman bada kanta yasata tattaro sauran nutsuwarta ta miqe tsaye, cikin confident data rasa daga ina yazo tashiga bashi amsar tambayar tashi dalla2 Tunda tafara yake kallonta yana mammakin wane irin brain ke ga yarinyar nan don har abinda be ambata masu ba ta ambata wanda Hakan ba qaramin faranta mashi yayi ba don shima kamar kowanne teacher yana bala'in son student mai sharp brain "a round of applause for her" yafada bayan tagama zayyano amsoshin Class dinne ya kaure da tafi wanda Hakan yasata jinta on top of the world Umarni yabata akan ta zauna takoma ta zauna haryanzu tana jin yadda zuciyarta ke tsalle Har aka qarashe lecture din bata qara gigin daga hannu domin amsa wata tambayar ba don harga lokaci takasa komawa normal Bayan lecture din daje tasamu Deen ta karanta mashi komai daya faru a ajin cikin tsananin murna, tana ta nannata wai yau ita mr ibrahim yacema ayiwa tafi Deen dai Dariya yayita mata yana cemata ba sabon ba yayinda take cewa eh babu komai Tofa tun daga ranar zee tafara zama active student a class din mr ibrahim Yanzu koda cikin mutane dayawa ta daga hannu yakan cankota jefi2, hakan kuma ba qaramin qara mata popularity yayi ba a class don a hasashen kowa yanzu kamar duk acikin class din ita ke topping din class din a subject din don wani sa'in ita kadai ke iya amsa wata tambayar Hakan yafara jamata farinjini a class din (kundai san yadda akema maqwara a fanni maths kallon manyan qwari😜) Sai yazamana tana qara burge yan class din, tana ba kowanne sha'awa donma sanin halinta na wulaqanci yasa duk ake shayin zuwa wajenta amma yadda tayi sunan nan da lafiya lafiya da taga yadda ake tururuwar zuwa koyon karatu awajenta. Su sumee kau a bangaren su wannan sabon cigaban na zee ba qaramin qara masu kiyyayarta yayi ba, sosai hassadarsu da baqinciki akanta yaqara farashi don sun lura akoda yaushe cigaba take samu ba ci bayaba Hakan ba qaramin rura wutar abinda suke shiryamata yayi ba azuciyarsu Saidai dayake munafukaine masu 2face ko kadan basu ta6a nunamata komai ba a fuska saima qara jawota jiki dasuke kuma koda wasa babu wanda ya tadamata maganar Deen acikin su saima yi dasukayi ma kamar ma sun manta dawani hallita Deen bayan a badini koda yaushe suna nan suna yimasu la6el either a library ko a sabon wurin zamansu, koda yaushe saisun je sunganosu wanda yanayin da suke tardasu yake qara hura wutar kishin nurr tarasa meke mata dadi a duniya. A bangaren zee da Deen kau wani sabon fejin shaquwa ne ya bude a tsakaninsu, ada akwai ranakun da basada lecture wanda hakan kesa basa zuwa ranar, amma a yanzu basa fashin ko wace rana, kullum sai sunzo kuma inhar ba lecture suke ba to suna tare Suna dan zuwa school din ranar saturday don yin karatu duba da yadda exams keta qarasowa, hakan yasa suka dage kowannensu ya maida hankali fiyeda da a karatu Abin mammaki yanzu idan ba tare suke karatu ba basa jin dadin karatun, kuma be cika zama ba ma Sau da dama idan suna gida suka dauki Littafi da niyyar karatu sai suji abin dai gashi nan, karatun duk bawani dadi Amma idan suna tare koda kuwa kowa da littafinshi a hannu yana karatunshi shikadai sai suji sunfi jindadi kuma yafi zama, wannan abin ba qaramin mammaki yake basu ba hakan kuma yaqara donqon shaquwarsu, yaqarawa Abin armahi👌 Yau ma kamar koda yaushe suna zaune a sabon wajen zamansu, kowannensu riqeda Littafi a hannu sun juyawa kansu bawa kowa na abinda ke gabanshi Jin kanta na neman fashewa don nauyin dayayi mata yasata maida littafin ta rufe tana dafe kan tana matse idanu Duk abinda take Deen besan tanayiba don sosai yayi nisa a duniyar karatu Juyowa tayi taga kanshi na kan Littafi bema san abinda ke faruwa ba hakan yasata dan 6ata rai tasa hannu ta fizge littafin hannunshi Firgigit yayi ya waigo don abin yazomashi a bazata, Ganin tayi saurin maida littafin bayanta yasashi shima 6ata rai "O'O! Give me my book" Maqe kafada tayi tace "anqi din, kai baka gajiya? Ni yanzu haka jin kaina nake kamar zai dare gida biyu" Daga kafadu yayi yace "then? Aike keji ba niba ko? Bani littafina" yafada yana neman amsa Maida littafin tayi bayanta tana Dariya Duk yadda yaso ya amsa qi tayi hakan yasashi hqr ba don yaso ba yace "now tell me, me zamuyi bayan karatun?" "komai ma Amma banda karatun, nagaji" tafada tana yatsine fuska "komai kamar me?" "komai dai, kamar labari da dai sauransu" "Ni ai ban iya labari ba" "wa din?" tafada tana eyeing dinshi "Ni din" yafada shima yana Dariya "hmm, gwara dakaba kanka Dariya" tafada tana harararshi "nidai ai gaskiya nafadi" yafada yana cigaba da Dariya Harararshi tayi kawai can kuma tace "ka Bani lbr, na komai ma, ko naka, kona family dinka, komai ma, qila inji sauqin nauyin kwalwa ta" Murmushi yadanyi sannan ya gyara zama yace "to bari nabaki na Ni da family dina" Itama gyara zama tayi cikin jindadi tace "yauwa, to inaji" tafada tana buga tagumi da hannu daya Murmushi yayi ganin yadda tawani nutsu ita dadi labari sai yace "Nidai sunana Deen kamar yadda mutane including you ke kirana, Amma my real name is _*KAMALDEEN MUHAMMAD*_ Amma kakata nace min _Kyakyawa na_🙈" ya qarashe yana rufe fuska alamun jin kunya Dariya zee tayi wanda hakan yasashi leqota ta tsakankanin yatsun dake fuskarshi "waye Kyakyawan? Cemaka akayi kanada kyau ne? Ca6! Tana fada ne kawai don kaji dadi Amma dont let that get into your skull ok?" Cire hannunshi yayi daga fuska yana kumburi "cigaba" Maqe kafada yayi alamun beyi "meye kuma?" "kin Cemin am ugly" yafada yana hade gira Wara idanu tayi tace "yaushe nace hakan? Kaji tsoron allah" "ba yanzu kikace ba?" "nace you're ugly? Cewa nayi bakada kyau" "what's the difference?" "difference din shine, ugly yana nufin mummuna, marar kyau kuma yana nufin marar kyau" Yamutse fuska yayi yace "me I see no difference in these" "ni naga difference din, so cigaba" Qara Maqe kafada yayi Bata fuska tayi tace "why na?" "sai kince inada kyau" yafada yana turo baki Dan Wara ido tayi sannan tace "to shikenan kanada d'an kyau" Juya idanu yayi yace "eh babu komai, aidai inada shi ko? Keda bakidashi kwata2 fa" Harara ta gallamashi "me din?" "kyau din" ya amsa yana mata gwalo Yitayi kamar zata makamashi Littafi yayi saurin jada baya yana Dariya Kwafa tayi tana jinjina kai "in cigaba?" ya tambaya yana dan leqota Hararshi tayi tace "cigaba ba don halinka ba amma" Dariya sukayi gabadaya sannan Deen yacigaba dacewa "yauwa as I was saying, kakata na kirana kyakyawarta nikuma ina kiranta kakata.. Kakata itace komai na, my life, my happiness, my komai Tana sona sosai, komai nata is kyakyawarta, haka nima komai nawa itace Tana yin komai don ganin ta faranta mani, tana yin komai don taga ta inganta rayuwata mudin hakan be sa6awa shari'a ba We are not rich but alhamdullilah bamu rasa komai ba. Kakata na sana'ar koko da qosai da safe nikuma ina zuwa wani workshop anytime am free, ina koyon aikin furnitures a qasan layinmu. With that muke living happily the way We can" ya qarashe yana murmushi Itama murmushi tayi cikin sha'awar simple life dinshi "mama da baba fa? Tunda muke dakai ban ta6ajin ka ambacesu ba" tafada tana kallonshi Dan jimm yayi, sai kuma yayi murmushi mai ciwo yace "basa nan, tunda na bude idanuna duniya kaka nasani, itace mamata itace babana itace komai na, amma ga yadda kaka tace accident sukayi suka rasu kuma dama nikadai suka haifa shiyasa banida siblings, kaka kuma babana ne kadai danta shiyasa we're all alone, daga ni sai ita" Tunda yafara take kallonshi cikin tausayawa, ashe maraya ne gaba da baya? Allah sarki "am.. So sorry, ban sani bane, Allah yajiqansu yayi musu gafara" tafada asanyaye Murmushi yayi mata cikin jindadin addu'ar tata yace "amin ya rabb" Shiru ya ratsa wajen inda zee tashiga saqe2, to ina dangin mamanshi? Ina dangin kaka? Yakamata ace basu kadai bane kamar yadda yace, koba komai Yakamata yayi maganar dangin mamanshi "kefa? Saura ke kibani lbrin ki" yafada shima yana buga tagumi yadda tayi dazu Dariya tadanyi tace "nawa tarihin is not as special as yours" "eh dukda haka abani" yafada yana kada kai Slight murmushi tayi tace "ni sunana zainab.. Zainab Farouq" ta tsinci kanta da kasa qarasa sunan "Dan faranshi?" inji Deen yana daga mata gira Kallonshi tayi da dan mammaki "how did you know?" Qara dage gira daya yayi yace "the paper, ko har kin manta" Dariya tayi tace "to haka yake, nima ni kadai ce ga iyayena, babana bahaushe ne, mamata kuma barumiya" "menene barumiya?" yafada cikin rashin fahimta Yar Dariya tayi "tribe ne, kai bakasan Rumawa ba? Masu tsagu biyu2 a gefen kunne?" Girgiza kai yayi alamun a'a yace "no, ban ta6a jiba" "ai dama ya za'ayi ka sani? Kai dama kifin cikin rigiya ne" tafada tana Dariya ahankali Ta6e baki yayi yace "eh babu komai, yanzu ita mum dinki ce rome din?" Dariya tayi tace "ba rome ba, Rumawa nace" "to Rumawa, amma itama tanada marks din?" "yes, kuma yana Masu kyau sosai don yawancinsu farare ne kuma kyawawa sai kuma tsagar taqara fiddosu" "wow! Kema Rumawa ce ko? Tunda Kema fara ce" yafada yana mata murmushi still be janye tagumin ba Harararshi tayi tace "barumiya zakace, mutane dayawa ne Rumawa, dummy!" Daga kafadu yayi yace "whatever" "nima barumiya ce Tunda mamata barumiya ce hakama bahaushiya ce Tunda dad dina bahaushe ne, ruwa biyu kenan" tafada tana kashe mashi ido daya Murmushi yayi yace "bawani, ke ba barumiya bace Tunda bakida marks" Xaro ido tayi tace "marks? Ca6 allah ya sawwaqe, ni dama banaso a jikina nafi sonshi a na wasu shiyasa ma naji dadi da ba'ayimin ba" "nikuma Inaso, i wish muma tribe dinmu anayi da kinga yanga" yafada yana juya eyes Dariya tayi tace "sai kuma gashi ba'ayi taar🤪" "eh babu komai" yafada yana Hade gira "to ku wadanne tribe ne?" "hausa mana" "hausa kuma? Kana nufin kai bahaushe ne" tafada tana mashi kallon uku saura kwabo "yes, dafa?" "and you want me to believe?" tafada cikin rashin yarda "allah dagaske fa nake" Harararshi tayi bata ce komai ba "allah, wlh kinjima na rantse" yafada cikin son gamsar daita "to amma babu either of your parent ko mama ko baba dasuka hada jini da Arab?" Girgiza kai yayi alamun babu "shuwa Arab?" Nan ma Girgiza kai yayi "allah mai iko, buzaye fa ko fulani dukda bakayi kalarsu ba" Qara Girgiza kai yayi snn yace "I told you ni bahaushe ne, mutane dayawa na tambayar kaka kuma haka take cewa, both mum da dad dina duk hausawa ne" yafada innocently Kada kai tayi tana kallonshi bawai don ta gamsu ba tace "kuma fa, amma nayi mammaki amma kuma ba abin mammaki bane, ikon allah kenan" Murmushi yayi kawai suka cigaba da firarsu cikin jindadi wanda sosai yadan ragemasu nauyin da kansu yayi Saida lokacin tafiya gida yayi suka rabu, ita zee tahau motarsu shikuma ya tari adaidaita _guys are you ready for the next chapter?_ _to ku tanadi hanki 🤧 domin zaiyi yaji 🌶? irin sosai dinnan_ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:33 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *021* 😆😆😆 jiya nace ku tanadi hanki mutane sun gigice, O'O!🙍🏻‍♀️Kudai bakusan wasaba, to wasa nake muku 🤗 Ku kwantar da hankalinku kamar kunyi baqo ya sheqa🙄 Haka lokaci yayi ta wucewa, exams nata qaratowa Kan kowa ya dauki chaji da masu qoqarin da mashiriritan duk aka komawa allah aka rungumi Littafi Alokacin library yakoma kamar bashi ba saboda cika, duk wanda ya rungumo guntun littafinshi to library yanufa Hakan yasa su Deen chanza wurin zama suka dawo silent place dinnan bakidaya Izuwa yanzu bama ce su mr ibrahim da zee sun shirya ba Saidai babu wannan yar tsamar dake tsakaninsu ada, yanzu lafiya lau suke mu'amallantan juna irin mu'amalar tsakanin malami da dalibi, abin nasu safa safa ba yabo ba fallasa Da farko zee taso tabashi hqr a lokacin sai kuma taga zaifi tabari sugama exam don karma yayi tunanin taimakonta takeson yayi a exam din😏 Hakan yasa ta qudurta cewa dasun gama exams zata bashi hqr komai ya wuce a tsakaninsu Tsakaninta dasu sumee babu yabo ba fallasa don tunda exams ya qarato kai yadau chaji haduwarsu tayi wuya, dama haka yake yawan faruwa don tun kafin ma zee tasan Deen da exams ya gabato take ajiye shiririta ciki hardasu tayi facing karatun ta don tasan idan ta biye musu ita hau zai hau don kwata2 babu ruwansu da karatu koda kuwa irin wannan lokacin ne na gabatowar exam don sunfi damqa imaninsu ga expo(satar amsa) Ita kuma dayake bata iyaba yasa duk lokacin gabatowar exam haduwarsu ke dan wuya don lokacin busy take karatu sukuma busy suke da shashanci dayaimasu yawa a brain shiyasa irin wannan lokacin basu cika hadewa ba sai ta waya ko idan an Hade a makarantar a gaisa tsaitsaye awuce To Hakan ta kasance yanzu ma, basa yawan hadewa saita waya wanda mafi yawanci su ke kiranta su gaisa, wannan kulawar dataga suna bata yasata qara jin sonsu don ita tana masu so na tsakani da allah kuma kamar yadda tace ita bata iya pretending ba, idan tanason abu to tanasonshi idan kuma beyi mata ba to 6aro2 zata nuna beyi matan ba bata tsoron bayyana Hakan Tun suna lissafin exams saura sattitika harya koma saura kwanaki har yazo ma gabadaya Sosai school din yaqara daukar serious atmosphere don wannan exam din na chanza aji ne babu mai fatan yayi repeating Hakan yasa kowa ke iya bakin qoqarinshi don ganin ya tsallake Su zee sun riga su Deen fara exam kasancewar daman ba course daya suke karanta ba kuma dama yafita da shekara daya, ita tana level 200 zata shiga 300 shikuma yana level 300 zai shiga 400 level Sosai zee ta baje kwalwarta sosai wajen jarabawar sai gashi wannan karin maganar ta turawa na _how you spread your bed that's how you lay on it_ wato _yadda kayi shinfidarka haka zaka kwanta akai_ Sosai exams din sukazo mata da sauqi fiyeda kowane semester don tafi shirya mashi a wannan semester din fiyeda kowane Har yanzu tare suke karatu da Deen, duk wanda lokacin shiga ajinshi yayi saiya tashi yabar dayan yaje ya zana ya dawo A bangaren su sumee kau bana kasuwa batayimusu dadi ba don bana an tsamar tsaro sosai dakyar suke samu sudanyi satar amsa wanda ahakan ne aka kama rukky har Sau biyu inda duk inda aka kamata tofa tayi loosing din jarabawar don yake papern akeyi kuma bazata sake wata ba, daga baya ma sai aka wareta daga cikin students aka kawo mata kujera da desk gaban class inda ba damar satar amsa, wurin yazama wurin zamanta duk in zasuyi exam, Hakan yasa komai yaqara dagule mata don kwalwar fankoce babu komai a ciki sai dusa Suma su sumee ba'a barsu abaya ba don duk watsasu akayi a class din, kowanne da mazauninshi gashi ba damar satar amsa saboda idon da aka samasu Hakan yasa basa ta6uka komai a duk jarabawar dazasu zana, wata jarabawar ma Saidai su rubuta sunayensu su sake copying din questions din aciki suje suyi submitting hakanan Sosai suka shiga damuwa da baqinciki don fa bana ba sauqi sai wajen allah, qarin baqincikin su shine idan suka hango zee ta sadda kai tanata rubutu ko dagowa batasonyi sai suji wani qululun baqinciki ya tokaremasu maqwalato suji kamar suyi tsuntsuwa sugansu gabanta su fizge shegiyar takardar su yayyaga, oho batasan sunayi ba don abinda ke gabanta takeyi su tabari da harara cikin duhu😡 Jarabawar mr ibrahim itace kusan ta tsakiya, duk cikin Jarabawar babu wanda akafi zullumi kamar ita, wadanda basuyi barci ba ranar daren Jarabawar sunfi yawa Ciki harda mutumiyar taku wanda a lokacin Saidai Deen ya ajiye nashi karatun sukayi nata tare Kuma Hakan ba qaramin taimaka mata yayi ba don sosai sukayi covering abubbuwa da dama Dayake Jarabawar monday ce sai suka hadu ranar saturday a school inda ranar ma wata Jarabawa sukayi on their own don ranar tambayoyi Deen yayta rubuta mata tana amsasu kuma tayi qoqari sosai don ta ciye rabi da kwata, kingin kuma suka farmasu harta fahimta Ranar sunday kuma kwana ta kusan yi zaune saboda karatu Hakan yasa ta tashi washegari da ciwon kai Saidai cikin amincin allah tana shan magani taji dama2 Kamar yadda kowa ya chanfa Jarabawar mr ibrahim da mugun wuya a kowanne semester haka kuma yafaru a wannan ma don wasu suna tozali da question paper din zufa yafara ketomusu Kunsan *goyon goyo?* to haka questions din suke, kowanne tambaya da goyon datayi itama goyon da nata goyon shima goyon da nashi don a question daya kana iya bata long sheet gaba da baya kodayake ga yan wahala yake Hakan don su yan baiwa (su nurr) ko gaban long sheet daya basu cika ba ga dukkan questions din tsabar gwanancewa 😆 (ouch! Waya jefeni 🥺) An saba duk wuyan exam iyakar gudun tsiya kayi 1hr kana yi amma wannan saida akafi awa biyu kafin afara fita Qarin gishiri cikin ciwo kuma harda mr ibrahim cikin invigilators din Hakan yasa abin yafi daukan Zokaga rikicewar students ranar Mafi yawa a cikin students din kuka sukaitayi wasu na jama mr ibrahim allah ya isa kamar yadda suka saba duk Jarabawa Sukau mutanenku sai suka zama yan kallo don su aganinsu ma kuka ai rahamane, tunda har suka samu sukayi kukan to matsalar tasu bata kai matsala ba A bangaren zee ma sosai Jarabawar ta jigatar da ita dukda dai tana saka ran samun abin kirki don ita kanta tasan tayi qoqari Haka tadawo wajen Deen gajiye ti6is Deen sai Dariya yake mata Kingin exams din ma sukazo suka wuce, inda students sukayisu cikin jindadi don dama zaffafan su suka fara zuwa Kingin kau duk yan tagajan2 ne Su zee sun riga su Deen gama Exam don dama sun rigasu farawa Lokacin da su zee suka gama su Deen saura paper uku sugama Hakan yasa take ta shan hutunta tabarshi da wahala Acikin haka ta yanke shawarar bama mr ibrahim haquri Saidai ta rasa ta wace hanya Itadai tasan bazata iya samunshi face 2 face ba hakan yasata yanke shawarar yin haka a rubuce Wata zungureriyar takarda tasamu fara tass ta zauna tafara tsara kalaman ban haquri Saida ta cika gaba da baya sannan ta linke neatly Sai a sannan kuma tafara tunanin ya za'ayi takardar takai mashi don gaskiya tana tsoron taje da kanta Haka taita saqa da warwara daga baya dole Deen ta nema don yabata shawarar yadda zatayi kuma kamar yadda yasaba samo mata mafita a matsalolinta wannan karon ma haka yayi Tare dashi sukaje parking space din malamai inda mottocinsu ne a parke a wajen Wajen motar mr ibrahim suka nufa cikin sa'a kuma sukaga daya daga cikin glass din windown motar be ida rufewa ruf ba Tanan suka lalla6a suka zura takardar tafada seat din mai zaman banza Suna ganin haka sukabar wajen da sauri kowanne zuciyarsu fall murna Mr ibrahim betashi ganin takardar ba saida ya isa gida, dauka yayi yana jujjuyata sannan ya warwareta Ganin rubutun dayawa yasashi maida wa ya ninke akan saiya nutsu sannan ya karanto Sosai yasha mammaki bayan yagama karance takardar kodayake dama yaga alamu daga gareta tun lokacin data fara zama class dinshi Saidai beyi tunanin yadda take nuna jinkai dinnan zata iya bashi haquri akan abubbuwan da duk tayimashi Maida takardar yayi ya ninke ya adanata Zee tayi tunanin zai nemeta amma Shiru takeji, data gayawa Deen yace mata ta kyaleshi kawai yanzu dama ba lallai bane yayi saurin haqura kawai tabari atafi hutu adawo saita sameshi a mutum taqara bashi haqurin Sosai ta gamsu da wannan shawarar Hakan yasa tayi amfani daita ta kyaleshi A bangaren su sumee kau sosai yanzu suke hadewa da zee don Mafi yawancin lokuta suna tare musanmman yanzu da ba komai take ba ga Deen yana busy don basu gama tasu Jarabawar ba hakan yasa suka koma suka jone kamar da dukda suna yawan hadewa da Deen din shima anytime he's free *BAQAR RANA* Yau laraba kuma yau su Deen ke qarasa paper dinsu ta qarshe Sosai ake kwala rana yau ga zafi harna innanaha Hakan yasa duk inda zaka gitta a school din Saidai kaga students qarqashin bishiyoyi suna shan iska don idan ba dole ba babu abinda zai saka zaman class Dayake duk yawancin departments sun gama Jarabawarsu sai school din yarage jama'a sosai don sai tsirarun masu Jarabawa saikuma ire irensu zee wadanda dalili kawosu Tare suke da Deen har saida lokacin shiga final paper dinsu yayi sannan suka rabu bayan yafada mata inda zasu hadu idan yafito Ta dan jima nan zaune ita kadai tana yan danne dannenta a waya Zaman kadaicinne ya dameta Hakan yasata miqewa ta sa6i jakkarta da niyyar zuwa wajensu sumee koba komai sunyi fira to whine time away Koda taje mazauninsu saita iske wajen wayam, tana niyyar juyawa taji muryar sumee a bayanta Juyawa tayi ta hangota ta taho tana daga mata hannu Hakan yasata yimata guntun murmushi ta tsaya don jiran qarasowarta Qarasowa tayi wajen tana dan sauke numfashi "keda wa kiketa sauke numfashi kamar wanda aka biyo?" inji zee Tsaki sumee taja tace "kede bari, wlh saqo naje amsowa na tararda mai kawowan ma bai isoba shiyasa na dawo har zan wuce naga wata kamar ke shine fa na biyo ki" "to? To where are others? Naga wurin wayam ko yau basu zo bane?" inji zee "sunzo mana, wazai zauna anan kina ganin yadda ray din rana ke reflecting ta koina? Wani cool waje muka samu daga bayan school, bakiji wurin ba so cool kamar karka tashi, nima dan iskan saqonnan danaje amsowa ne ya tadoni abin ban haushi kuma ashe be qaraso ba" tafada cikin nuna jin haushi Ta6e baki zee tayi tace "yanzu dai muje wajen dan allah, na gaji ga rana na kwalata i need some breeze" "ai dole, gaskiya yau ana rana, qila ruwa xa'ayimana dama andan daga mana qafa kwanan nan" inji sumee suna tafiya Tafiya suke suna firarsu suka nufi bayan school inda tunda zee take a school din bata ta6a zuwa wajen ba Saidai bata kawo komai a ranta ba don babu wata alama da zai janyo ta zargi wani abu Suna cikin Tafiya wayar sumee tayi ringing Cirota tayi ta kara a kunne bayan ta tsaya Hakan yasa itama zee tsayawa tana kallonta "wai fatima wannan wanne irin wulaqanci ne? Kince min kinzo naje na tararda bakya nan, naita jira Shiru kin shanyani cikin rana kamar yar iska" tafada a masifance Jimm tadanyi alamun magana akeyi acan bangaren can kuma taja Tsaki tace "haba wannan ai wulaqanci ne wlh, kawai saiki sani zuwa da dawowa kamar marar aikinyi bayan kinga yadda ake kwala wannan ranar? Mtcheew! Ganinan zuwa idan kuma kinga dama karki tsaya inda zanyi saurin ganinki, Mtcheew!" ta katse kiran a fusace Dagowa tayi ta kalli zee dake sauraronta Tundazu "wai kinji don wulaqanci sai yanzu taga damar zuwa, ni wlh badon saqonnan nada muhinmmaci ba da babu abinda zai sani wannan wahalar" tafada cikin fushi Dan Ta6e baki zee tayi tace "to ya kika iya? Tunda yanada muhinmmaci dolenki kau kije ki amso, ehe!" ta qarashe tana mata Dariya ganin yadda take cika tana batsewa Tsaki sumee taja tana girgiza kai tace "ko zaki rakani please" tafada tana narke fuska Harara ta gallamata tace "ca6! Wazai qara wannan uwar tafiyar yadawo? Nikam saikin dawo, ni wlh ma bansan abinda yasa kukazo nan ba, zafi kanku farau zaku shigo nan inda babu wulgin kowa? Ni tunda nake a school dinnan ban ta6a zuwa nan arear ba" inji zee tana qarewa environment din kallo "hmm wlh duk aikin su deeya ne, nima dafarko nayi wannan mitan amma danaje naji coolness din wajen kamar naita barci donma wannan yar banzar fatiman ta kofsa min" "haba wajen yayi nisa sosai, ga wurin so quiet ku bakwa tsoro?" inji zee "kede ke ganin haka, sai kinje wurin zakiga acike yake don duk can students suka ruga shiyasa kikaga basuda yawa acan cikin school din" tafada cikin son convincing dinta "to nidai bari na qarasa ranar nan tafara gasamin forehead, kije ki amshi saqon kin shanyata itama" "kyaleta itama ta dandana ai" tafada tana Dariya Wucewa zee tayi tana cewa "badai kyau mugunta" Dariya sumee tayi tajuya itama tana cewa "saina iso" ta wuce Cigaba da tafiya zee tayi hoping ta hango su deeya din amma sai qara nausawa take babu su babu alamun su don ko wulgin mutum bata ganiba Gajiya tayi ta ja ta tsaya tana riqe kugu Izuwa yanzu wani iska iska akeyi mai shige da na hadari don dama kamar yadda sumee tace wannan zafin na yau da walakin Tsaki zee taja cikin quluwa, in banda ma hauka mezai kawoka nan duk da sunan shan iska? Wayarta ta ciro daga cikin jakka tashiga lalubar number su Saidai babu ta wanda ke shiga, Hakan ba qaramin qara quleta ba yayi Hakan yasa tayi kwafa ta kashe wayar tajuyo da niyyar tafiya sai jitayi ta bangaji abu har wayar hannunta na faduwa Baya2 tayi tasamu dakyar tayi regaining din balance dinta sannan ta dago don ganin menene ta bangaje Gabanta ne ya yanke ya fadi ganin wani tsaye agabanta ciggarete a hannunshi yana aikamata wani dan iskan kallo da jajjayen idanunta Dan jada baya tayi Saidai motsin dataji a bayanta yasata saurin Juyawa nanma taga wani Da guda guda taga sunata fitowa har suka gama fitowa suka zagayeta ya zamana tana tsakiyarsu Da guda guda tafara binsu da kallo gabanta na faduwa, gabanta ne yayi wani mummunan bugawa datayi tozali da master dayayi pocketing din hannunshi yana kallonta da jajjayen idanunshi dan guntun murmushi dauke a gefe bakinshi Cigaba tayi da kallonsu da daidaya zuciyarta na mugun bugawa, dakyar ta tattaro yawun bakinta ta hadiye sannan tayi qoqarin aro nutsuwa ta yafa ta duqa da niyyar daukar Wayarta sai gani tayi na kusada ita ya taketa har saida tayi qarar fashewa sannan yayi ball daita tafada can cikin wasu ciyayi Dagowa tayi gabanta na cigaba da racing tana kallon wadda ya take wayar, cikin qarfin hali tace "wai malamai lfy? Ku su waye?" tafada cikin muryar dataji kamar ba nata ba Wata mahaukaciyar Dariya suka kece daita wanda Hakan yaqara farashin tsoronta don wannan Dariyar daga jinta ta tsantsar mugunta ce "baa baa! Kaji wai qarin bayyani takeso" inji gandu yana qara fashewa da Dariya "wai dagaske kike baki ganemu ba? Harda nima" inji T.J yana nuna kanshi yana Dariya "haba baby? Kin iya mari amma baki iya tantance mutane ba?" inji Alex dake gefen damarta shima yana Dariya Gabanta ne yayi mummunan bugawa da jin haka _ya ilahi! What am I into_ tafada a cikin zuciyarta "ya isa!!" inji master yana daga hannu wanda hakan yayi daidai da daukewar dariyarsu "baby bata ganeku ba, qilama bata sanku ba tana neman qarin bayani, koba haka ba baby?" yafada yana kallonta tareda kashe mata ido daya Kasa magantuwa tayi sai kallonshi datake speechless "karki damu, ni zan fahimtar dake, ai ke ranki shi dade ce dole sai ana hadawa da tuni" yafada yana tunkarota Bugun zuciyarta ne yaqara qaruwa tafara ja da baya cikin tsananin tsoro shikuma yana tunkarota haryanzu dauke da wannan murmushin Duk takunshi daya na tunkararta daidai yake da nata daya na ja da baya, haka sukaitayi har tajita gab da bash dake bayanta, saurin Juyawa tayi tana kalleshi ta kuma kalli master dake daff daita, cikin kidima tasa hannu da niyyar ture master daya kusan Hade jiki da ita ta gudu Saidai caraff ya cafke hannun, kafin ta tantance komai taji an dauketa da wani giggitaccen mari... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:34 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *022* *DEEN* Yana fitowa daga exam hall yanufi inda sukayi da zee zasu hadu Be tarar daita ba wajen Hakan yasashi zama don jiranta yasan qila wani abu tajeyi ko taje saye Fiddo wata takarda yayi yana sake dubata Form ne da wani maqocinsu ya samo mashi na aiki a wani company Ga yadda maqocin nasu ya gayamashi yace suna daukar mutum da kowanne mataki na karatu kai hatta wanda iyakar shi primary suna dauka Saidai kawai banbancin albashi da za'a samu tsakaninsu Tun jiya yabashi akan zai amsa yau idan ya cike, sosai shima Deen din yaji yana son aikin don dama yanzu hutu zasuyi gashi aikin furniture dinsu yanzu ba'a cika samu ba kasancewar yanzu damuna ce kowa ta kanshi yake duk ba'a fara fitar da amfanin gona ba bare kudi su yawaita har afara maganar aure2, dakuma ya zauna hakanan ai gwara ya jaraba wannan din ko allah zaisa a dace Ciro pen yayi yashiga cike takarda cikin nutsuwa making extra sure beyi mistake ba ko guda Saida yagama cikewa tsaf sannan yatsaya yana sake dubawa don tabbatar da beyi kuskure ba ko daya, Ganin komai daidai ne yasashi bude tsakiyar wani Littafi ya saqa takardar ciki ya maida ya rufe Daga kai yayi yana kallon sararin samaniya ya hangi yadda hadari ke neman haduwa ga iska iskar daketa kadawa yanzu Duba wristwatch dinshi yayi yaga 3 saura, yanzu aqalla yafi 30mins da zama _to ina ta shiga ne haka?_ tambayar dayayiwa kanshi kenan Komawa yayi jikin kujerar ya harde hamnayenshi a qirji ya cigaba da jiran tsanmmani *ZEE* Wani dum taji kanta yayi tayi baya baya ta zube qasa Dafe kumatunta da takeji kamar ba nataba tayi tana jan numfashi cikin fitar hayyaci Rankwafowa Master yayi gabanta yana cigaba da wannan dan iskan murmushin "da kika wani yunquro, nima marina zakiyi? Eh?" yafada yana leqa fuskarta data farayin jajajaja Dagowa tayi ta kalleshi da idanunta dasuka farayin ja hannunta still Dafe da inda ya mareta tana jan numfashi haryanzu "gayamin, nace nima marina zakiyi?" yafada yana kai hannunshi saitin qirjinta Bige hannun tayi tana ja da baya dakyar Kamo hannunta yaso qarayi taqara Bige hannun tana qara ja baya tana nishi "Go away, you brat!" tafada tana dibar qasa ta watsamashi still tana ja da baya Saurin kauda kai yayi ganin qasar ta nufo fuskarshi Hakan yasa ta sauka a jikinshi Sake juyowa yayi ya kalleta "brat? Nine brat? Wato bakinki bai mutuwa ko? Dont worry, zan kashe maki shi ayau, now and forever!" yafada yana nufota Ganin Hakan yasata saurin miqewa a gigice tayi niyyar guduwa sai kawai taji bash dake bayanta ya cafketa Qara tasaki tashiga qoqarin kwace kanta a hannunshi amma takasa, batayi wata wataba tasa kafarta atsakiyar kaffafunshi ta dago gwiwarta Wani mahaukacin qara bash yasaki tareda sakinta ba shiri, ya fadi yana billayi Faduwa tayi itama daya saketa amma ko second daya batayi ba ta miqe tafara gudu cikin son ku6uta daga garesu "kubita! Karku sake ta gudu!" inji master cikin qaraji Da gudu su alex suka bita yayinda shikuma master din ya zube gaban bash daketa ihu haryanzu hannayenshi damqe da gabanshi ya dagoshi yana kallo Gudu take cikin fitar hayyaci batareda tasan hanyar da takebi ba, ga wani iska mai qarfi daya taso mai tafeda duhun hadari Iya gigicewa ta gigice don kawai jefa kafarta take inda tasamu gashi bata ganin gabanta sosai saboda iska, qarin tashin hankalinta kuma shine sautin gudunsu dataji yana qara kusantota sosai Kafin ma tayi wani nisa suka cimmata gandu yasamata kafa tayi tuntu6e ta fadi Jan kugu tashigayi da baya baya tana numfarfashi Nufota suka ta cigaba da jan kugu tana girgiza kai cikin tsantsar tashin hankali, tsabar rudewa ma takasa jawo kowacce addu'a sai 6ari da duk ilahirin jikinta keyi Take kafarta T.J yayi wanda hakan yasata sakin qarar azaba, bata gama tantance zafin wannan ba taji an damqi gashinta anfara janta qiiiii! Ihu ta cigaba da kwallawa tana Iya qoqarinta na ganin ta qwace amma takasa, be tsayar da ita koina ba sai a gabansu master dake duqe still gaban bash daya galabaita Iya galabaita don ba qarya ya bugu Jefar daita yayi ta zube gabansu master tana haqi Afusace master ya damqi gashinta har saida tayi qara ya dago kanta saitin fuskarshi yana kallonta da jajjayen idanunshi Qalato yawu tayi ta tofamashi a fuska cikin qarfin hali Kauda kai yayi yana rintse ido saboda yawun daya sauka akan fuskarshi, Afusace yasake juyowa ya dauketa da marin dayafi na dazu ratsa jiki Wata wahallaliyar qara tasake fasawa ta zube awajen tana numfashi sama2 Jitayi kunnenta nayimata dumm dumm ga idanuwanta da suka fara ganin dishi2 Bayan hannu yasa ya goge yawun fuskarshi yana huci sannan ya qara nufarta ya sake damqo gashinta ya tadota zaune Rintse idanuwanta tayi gamm, tsabagen damqa har jijjiyoyin gashinta ana gani "ni zaki tofawa yawu a fuska? Eh?" yafada yana qara dauketa da wani marin wanda yaqara sata zubewa Cusa fuskarta tayi cikin ciyayin wajen tana jan numfashi dakyar Qara damqo gashinta yayi ya dagota again yana saita fuskarta saitin fuskarshi ya nufi bakinta da niyyar sumbata Datse bakinta tayi gamm ta hanyar maida la66anta ciki ta danne tana numfarfashi masu nauyi Cikeda mugunta yasa dayan hannun ya Kamo kumatunta ya lotsa yatsunshi a kowanne gefe cikin mugunta har saida bakin ya bude Qara nufar bakin yayi da niyyar kiss ta dago hannunta daya dakyar ta rufe mashi fuska tana turashi Kauda kai yake cikin son kaucema ture fuskarshi datakeyi amma taqi bari Hakan yasa ya saki gashinta da haryanzu ke a damqe a hannunshi ya Kamo hannun nata data tare mashi fuska dashi dago dayan hannun tayi shima ya cafkeshi ya hadesu a baya ya riqesu da hannu guda yasake dago fuskar da tsiya yasake nufar bakin *DEEN* Qara duba agogon hannunshi yayi a karo na ba adadi, wai ina ta tsaya haka? Koko ta tafi ne? Amma ai basuyi daita cewa tafiya zatayi ba, gashi kuma beson tafiya kuma ace tananan tazo ta nemeshi batanan Kallon sama da hadari keta qara haduwa yayi ga iska daya fara qarfi Miqewa tsaye yayi yana rungume littatafanshi a qirji yana qara kallon yadda hadarin ke qara haduwa Ina ta shiga to? Sai yanzu yake jin haushin rashin number wayarta da bedashi daba yanzu yakira yaji ko ta tafi ba? Ga hadari sai qara haduwa yake, yasan rufin asirinshi shine yabar school dinnan Tun yanzu kafin ruwa ya 6alle saboda yanayinshi don yanzu haka ma iskar dake kadawa yafara affecting dinshi _maybe ta tafi gida itama_ _yes na tabbata ta tafi_ yafada ma kanshi cikin qwarin gwiwa Da wannan tunanin yasa ya fito daga inda yake yana qara qanqame littatafanshi a qirji ya fara tafiya don barin school din. Wani iska mai qarfin gaske yaqara tasowa wanda saida Deen yaqara qanqame jikinshi, gashi dama daga shi sai wata yar farar t-shirt mai gajeran hannu, kasancewar yau da zafi aka tashi yasashi sanyota don ko kadan be ta6a kawoma kanshi za'ayi ruwa ba Qara saurin tafiyarshi yayi cikin zuciyarshi yana addu'ar allah ya daga ruwan nan harya kai gida don bazai manta da gargadin Dr ba a wancan attack din na ciwonshi inda ya gargadeshi sosai akan ya kiyayi shiga ruwa saboda condition dinshi don koyaya ya shiga ruwa matsala za'a samu Wani iska mai hadeda gugguwa yasake tasowa wanda saida yakai hannunshi yakare fuskarshi ganin yadda gugguwar qasar ta nufoshi Yanajin zubewar wasu daga cikin littatafan hannunshi amma be bude idanunshi ba saima addu'o'i daya shiga karantowa a zuciyarshi har gugguwar tawuce Sauke hamnayenshi yayi Bayan ta wuce yayi saurin duqawa don tattare littatafanshi Iska ake sosai wanda Hakan yasa littatafan suka bashi wuya wajen tattarosu don iskan sosai yake kadawa har littatafan na bubbudewa da kansu Cikin hakane wani Littafi ya bude iska yashiga bubbude pages din da sauri sauri har yakai page din daya saka takardar shi na form din daya cike Fitt! Iska ya figeta tayi sama tafara shawagi acikin iskan "O'O!" yafada yana kallon yadda takardar ke sama ke qasa acikin iskan Saurin ida tattara kingin littatafan yayi sannan ya miqe yafara bin takardar don kamota Saidai kwata2 yakasa don the more yake tunkarar takardar the more iska ke qara yin gaba daita Haka yaita binta da gudu2 sauri2 trying all his best na ganin ya kamota amma a banza *ZEE* Duk yadda taso qwatar hannayenta daya riqe a bayanta kasawa tayi don ba qaramin riqo yayimusu ba gashi qarfi ba daya ba Duk yadda yaso ya lallubo bakinta kasawa yayi don sosai take amfani da iyakar qarfinta na ganin ta kwace wanda Hakan yasa taqi tsayawa wuri guda bare yasamu damar lallubo bakin Su alex na nan still tsaye kansu suna kallon artabun da sukeyi Tundazu, suna son su shiga suma a faffata dasu amma sanin halin master yasa suka jinkirta don ga dukkan alamu shi da kanshi yakeson yafara ladaftata kafin suma su biyo sahu Gajiya yayi da kokowar tasu Hakan yasa yakai hannunshi yakamo gaban rigarta, batayi auneba sai jitayi kyattttttt yaja yana ketata Wani giggitaccen qara tasaki cikin dimaucewa wanda saida yayi amsa kuwa ta koina Ido rufe ta rarumo hannunshi na dama takaimashi cafka da haqoranta ta datsa cikin cicin qarfi Wata qarar azaba yasaki ya tureta da sauri yana yarfe hannunshi cikin azaba Jada baya tashigayi cikin jan kugu tana kakkare qirjinta da suke awaje saboda yagan da akayiwa rigar "help!!! Somebody help me!!.... Deen!!!" Tashi tayi da niyyar sake guduwa Saidai samata qafa da wani yayi wanda bazata tantance fuskarshi ba saboda biji bijin da take gani yasata qara zubewa awajen tana sakin wata qarar mai qarfi "help!!! Deen!!! Sumee!!! Somebody help me!!" *DEEN* Sosai ya jigata wajen qoqarin kamo takardar, gashi hadari sai qara haduwa yake Saidai yakasa haqura daita don muhommmacinta agareshi yasashi jin be iya barinta tabi iska hakanan Dakyar yasamu ta tsaya wani wuri inda ta maqale cikin wasu qayoyi Saurin qarasawa yayi wajen ya duqa ya daukota Ajiyar zuciya ya sauke ganin batayi komai ba yashiga linketa neatly ya sakata aljihunshi Qarar dayajiyo daga dan nesa da wajen yasashi waigawa da sauri Shiru yayi ya kasa kunne amma tsit beqarajin komai ba Ajiyar zuciya yasake saukewa har yajuya zai tafi yaqara jin wata qarar wanda tafi wancan don wannan ma kamar ta namiji ne Sake waigawa yayi yana kallon saitin inda qarar ke tahowa Jin wata qarar yakuma yi kamar ma magana ake Saidai bazai iya tantance abinda ake fadi ba Shiru yayi yana kallon saitin inda qarar ke fitowa saikuma ya kalli sararin samaniya yaga yadda hadari ke qara hadewa Wata qarar yaqara ji sama2 kuma kamar muryar mace Tunani yafara yi, to idan ma mace ce me zai kawota nan? Hankalinshi ne yakasu kashi biyu, daya a inda yake jin qarar dayan kuma gida Yasan idan ruwan saman nan ya sauko to ya kade har ganyenshi Saidai kuma yarasa dalilin dayasa zuciyarshi tafi karkata ga inda yakejin qarar Qara kasa kunne yayi yaji ko zaiji wani abin sai yaji tsit, ya dan jima yana sauraren ko zaiji wani abin Saidai beji komai ba hakan yasa ya yanke shawarar tafiya wata qila kunnuwanshi ne basu jiyemashi daidai ba Qara rungume littatafanshi yayi yafara takawa zai tafi Wata qarar yaji wanda tafi dazu wanda Hakan yasashi qara waigowa da sauri Tabbas wannan qarar mutum ne kuma mace Me mace keyi anan cikin wannan gungurmin hadarin? Ko 6acewa tayi? Babu mai amsamashi Hakan yasashi fara bin inda yakejin qarar yana qara rungume takardunshi The more yake qara nausawa the more yakejin muryar clearly "Daddy!!! Mummy!!! Help!!! Taimako!!! Please Help!!!" Jin Hakan yasashi qara sauri yana dan hadawa da gudu yana bin muryar harya bayyana a scene din Sakin littatafan hannunshi yayi yana qara wara oily eyes dinshi ganin yadda mace ke kokowa dawani namiji bakin rai bakin fama Macen ce akasa namiji akanta suna kokowa sai ihu Macen keyi Besan yadda akayi ba sai kawai ganinshi yayi a wajen ya cakumo namijin ta baya ya dagoshi ya wurgar gefe sannan ya ranqwafa ya dago Macen da sauri Qanqameshi zee tayi cikin fitar hayyaci still tana sabbatun neman taimako Duk yadda yaso ya 6an6areta daga jikinshi kasawa yayi don Qanqameshi tayi gamm kamar her life depends on him Babu zato yaji abu ya tunkudashi ta baya wanda Hakan yasa yayi gaba ya fadi dashi da zee din dake jikinshi Lumshe idanunshi yayi ya budesu akan fuskarta da sai yanzu ya samu damar ganinta Qara wara idanun yayi ganin the shock of his life _*zainab!*_ zuciyarshi tayi exclaiming Saurin mirginawa yayi gefe ya tashi zaune still yana kallonta da madaukakin mammaki a fuskarshi Itakau curewa tayi wuri guda ta rungumo qaffafunta ajikinta tana kuka mai cin rai jikinta babu inda be 6ari "kai!!!" qarajin master ya dawo da Deen daga duniyar kallon zee Dagowa yayi ya fara binsu da kallo daya bayan daya sun jera agabansu suna kallonshi shima sai huci suke "kai waye dazaka shigo gonarmu har ka nemi takamana burki?! Ko bakasan ko mu su wayeba?!!" inji T.J cikin qaraji Dode kunnuwanshi yayi yana yatsine fuska "O'O! Meyasa kake tsawa to?" inji Deen still hannunshi dode da kunnuwan _*O'O!*_ Kamar kunnuwanta abinda suka jiyemata kenan, duk duniya mutum daya tasan yana cewa haka _*DEEN*_ "tambaya ma kake meya sani tsawa? Wato bakama ji tsoro ba saima rainin hankali dakake neman yi?" "ni ban raina maka hankali ba, babu kyau tsawa ne saboda Hakan yana da illa sosai, gareka dakuma mai saurarenka. Idan kayi tsawa hakan yana iya cutar dakai domin..." "DEEN!!!!" zee ta katseshi da fadin hakan ta rarrafo cikin sassarfa ta fada jikinshi Wani irin kuka mai tsuma kuka tafashe dashi tana qara Qanqameshi "wayyo Deen! Deen ina katafi ka barni? Please Help me Deen, take me out of here, zasu kasheni..." tafada cikin fitar hayyaci jikinta na rawa sosai Dago fuskarta yayi cikin taffukan hannunshi yana bin fuskarta da kallo "Zainab, look fuskarki ta kumbura and this.." yafada yana dangwalo jinin dake gefen bakinta ya nunamata "meya sameki?" yafada cikin raunin murya Fashewa tayi da wani kukan tana sake komawa jikinshi ta Qanqameshi, kafin zuwanshi tariga ta saddaqar rayuwarta tazo qarshe amma yanzu ganinshi yasama mata hope, hope na cigaba da shaqar numfashi da fitarwa, kasancewarta a jikinshi kawai ya samata jin sense of security, yasamata hope na tsira daga wadannan shaidanun "oho? Sai yanzu na ganeka, wannan gayen ne master" inji alex yana Fashewa da Dariya Su kingin ma Fashewa sukayi da Dariya banda master da fuskarnan ke a murtuke, ga hannunshi dayake jini sanadin mugun cizon da zee tayimashi, radadi duk ya isheshi "silent!!" injishi cikin quluwa don shi bega abin Dariya ba anan Tsit wajen yayi zee kau qara shigewa jikin Deen dake kallon master tayi tana rufe idanu Takowa master yayi ya nufosu Ganin Hakan yasa Deen miqewa tsaye da zee dake jikinshi still ganin master ya tunkarosu yasata saurin komawa bayan Deen ta lafe zuciyarta na cigaba da bugawa Qarasowa yayi gabanshi nan aka shiga kallon kallo tsakaninsu Qara lafewa bayanshi zee tayi tana kwantar da kanta bisa bayanshi "kai! Maza kama gabanka" inji master kamar irin yana ma dan shekara 4 magana Shiru Deen yayi be amsa ba kuma beyi abinda yace ba "ko bakaji ba!" yafada atsawace yana zazzaromashi idanu Dan jada baya yayi don sosai tsawar ta daki kunnenshi gashi idanun master beda kyan gani, sun wani rune kamar garwashi "O'O! Meyasa kaima kake shouting? It's not good for your health kuma ka daina kallona da wadannan idanun, bana sonsu" yafada yana yamutse fuska Sheshekar zee ce ta tsaya cak Sai yanzu ta tuna da waye Deen, sai yanzu ta tuna da waye ta la6e a bayanshi a matsayin garkuwa Deen ne, the timid guy, tambayar anan shine shi zai kareta daga su ko ita zata kareshi? "kai! Kalleni dakyau kagani kaga wasa a idona? The best option for you shine ka 6acemun anan tun kafin nahada dakai da mental problem din naka nayi kaca2 daku" yafada cikin zazzaremashi idanu Shiru Deen yayi yana kallonshi batareda yace komaiba "baka jiba?" 6ata fuska yayi yace "Meyasa ka daketa? Bakaga ita macece ba kuma yarinya? Abinda kayi bashida kyau" yafada cikin son nusar dashi gaskiya "yarinya? Yarinya ce amma ta iya tsokano manya? Wannan yana nufin tana jinta daidai da manyan ne don haka ta tsokanoma kanta, saita banbance tsakanin aya da tsaguwa yau" injishi cikin huci "kayi hqr to idan laifi tamaka amma ai ba girmanka bane ka biye mata, kai kana gaba da ita, ka dauketa a matsayin qanwarka" yafada cikin son convincing dinshi Qara matsowa master yayi gaban Deen har suna iya shaqar numfashin juna cikin husky voice yace "look, ni banida case dakai ko daya, da ita nakeda so karka bari nasamu case din dakai, ka miqomin ita katafi salin alin tunkafin in burkita maka wannan fuskar!" yafada yana kamo gemun Deen din yajawo fuskarshi har gab da tashi sannan ya turashi baya wanda Hakan yasa sukayi baya baya shi da zee suka fadi Be qara bi takan Deen ba ya wuce wajen zee dake jada baya ya damqo hannunta ya miqar daita tsaye yafara janta Qara ta kwala tana tirjewa "Deen! Help! Please!" Jin hakan yasa Deen saurin miqewa tsaye yayi saurin binsu Master besan dashi ba saiji yayi an fizge hannun zee din daga hannunshi Hakan yasashi juyowa yana kallon Deen dake riqe da zee din ta wani lafe a qirjinshi Zuciyarshi ce taqara harzuqa Hakan yasashi kaima Deen naushi a gefen kumatu wanda yasashi fadawa can gefe Qara zee tasaki a gigice tana binshi inda ya fada din tayi saurin duqawa gabanshi "Deen!!" tafada agigice tana qoqarin dagoshi Dagowa zaune Deen yayi dakyar yanajin gefen kumatunshi kamar ba nashi ba Qara damqo hannunta master yayi da niyyar sake dagota, tirjewa tashigayi tana kuka sosai tana ruqo rigar Deen da dayan hannun Qara fusata master yayi ganin yadda suke 6ata mashi lokaci Jawota yayi da qarfi har saida rigar Deen data damqe da dayan hannun ta yage guntun kyallen yabiyota Tirjewa tashigayi tana kuka sosai tana miqoma Deen da keta yunqurin tashi hannu Dakyar Deen ya taso yaqara nufarsu yanajin inda master yakaimashi naushi na yin nauyi Qara fizge hannunta yayi daga na master ya Jawota jikinshi ya rungumeta yana jada baya yana kallon master daya juyo shima yana kallonshi Riqe kugu master yayi yana kallon Deen cikin rashin sanin abinda yakamata yayi mashi "ka.. Kyaleta, please" inji Deen yana maida numfashi ahankali Cigaba da kallonshi master yayi cikin takaici sannan ya kalli su alex dake kallon duk abinda ke faruwa Tundazu "ku takaitamin shi" yafada yana maida kallonshi akan Deen din Kamar kau jira suke suka nufi Deen gadan2 Damqe hannun Deen zee tayi jikinta na 6ari "Deen mu gudu, they'll kill us" tafada cikin rawar murya Kamar kau shawarar ta yake jira sai shima yaqara damqe hannunta suka juya suka fara gudu "kai! Mubisu karku saki su tsere!" inji master din yana binsu suma suka maramashi baya Gudu suke da dukkan qarfinsu suna jefa kafarsu duk inda suka samu Sosai iskan dake kadawa yanzu da qarfi yake kawomusu tirjiya a gudun nasu don kadowa yake saitinsu sai jisuke kamar zai maidasu baya Sosai Deen kejin effect din iskan ajikinshi don qirjinshi a bude yake sanadiyar yagan da rigar ta samu dazun Haka dai yake daurewa suke gudun da dukkanin qarfinsu batareda sunsan inda suka dosa ba Cikin wasu ciyayi suka samu suka lafe suna maida numfashi "Zainab... Ruwa" yafada cikin maida numfashi Saurin rufemashi baki tayi jikinta na rawa sannan cikin muryar rada tace "ka rufamana asiri gasunan karsu jimu, kabari musamu mu ku6uta saimu samo ruwan" Janye hannunta yayi daga bakinshi yana cigaba da maida numfashi "ruwa...ruwan sama, yafara sauka" Sai a lokacin zee ta lurada anfara yayyafi "shhh it ok, please karka bari sujimu" tafada tana qara qamewa waje guda jin tafiyar su master gab "no, doctor yace karna shiga ruwa... Mubar nan, am sick already" yafada yana rintse idanunshi yanajin yadda sanyi ke shigarshi har cikin qashi Cak zee ta tsaya tana binshi da kallo cikin tashin hankali, ita harga Allah ta manta shaf da lalurar Deen 'innalillahi waina ilaihi rajiun' tafada cikin zuciyarta tana kallon yadda jikinshi ke dan 6ari, jijjiyoyin kanshi na bayyana Saurin kama damtsen hannunshi tayi tana kiran sunanshi ahankali hankali tashe Bude idanunshi yayi ahankali ya kalleta Gani tayi idanun sunfara chanza launi zuwa ja ga siraran jajjayen jijjiyoyin dasuka fiffito a farin qwayar idanun "Deen are you ok?" tafada cikin tashin hankali Lumshe idanu yayi ya sake budesu yanajin yadda yayyafin da yanzu yaqara qarfi ke sauka ajikinshi "mu... Barnan, please" yafada yana cije haqoranshi gamm Ganin haka yasa ta kama hannunshi ta riqe gamm "kana iya gudu?" tafada cikin rawar murya Qara tamke idanunshi yayi ya bude yanajin jiri2 Kada mata kai yayi cikin qarfin hali Qara tamke hannunshi tayi sannan ta taimaka mashi suka tashi suka fara gudu Su master daketa bulayin nemansu Suka jiyo motsi a bayansu Hakan yasasun saurin juyawa Su Deen suka Gani suna gudu Hakan yasa suma suka maramasu baya a tamanin Gudu suke sosai da duk qarfinsu Tun suna ganin gabansu har takai basa gani saboda qarfin da ruwan saman yayi Kawai gudu suke suna saka qafarsu inda suka gani Suna cikin gudu Deen ya fadi jagwab awajen Hakan yasa zee jan burki itama "Deen! Deen! Katashi don Allah, you can do it! Please gasunan" tafada tana girgizashi cikin fitar hayyaci jikinta sai digar ruwa yake don sun jiqe jagab Cije lower lip dinshi yayi jikinshi na rawa sosai Yunqurawa yayi dakyar ya miqe yana jin kamar zai sake kifewa Saurin kama hannunshi tayi tana qara damqewa suka cigaba da gudun Saidai kana ganin Deen zaka gane baya cikin hayyacinshi kwata2 Basuyi nisaba yasake yankan jiki yafadi yana maida numfashi dakyar Durkushewa gabanshi zee tayi tana kuka sosai "Deen! Deen!! Get up, are you ok?" Rintse idanunshi yayi yana sauraron yadda ruwa ke bugunshi yana tuna gargadin da Dr yayi mashi shi da kaka _*"yakamata ku kula sosai, a wannan condition din nashi idan yaqara samun wani attack din am sorry to say komai yana iya faruwa, ciki harda rasashi, ya kiyayi abinda zai tadomashi ciwon komai qanqantarshi, ya kiyayi wanka da ruwan sanyi, idan ana sanyi sanyi ya tabbatar ya kare jikinshi gareshi ta hanyar sa kayan sanyi, idan ana ruwan sama karya sake ya fita, yanzu damuna ce don allah a kiyaye, a kiyaye duk abinda zai qara tadamashi ciwon nan, please*_ Lumshe idanunshi yayi ya qara budewa yana jin yadda numfashinshi keyin sama sama Sama sama yakejin kukan zee da sunanshi datake kira can kuma yaji motsinsu master dasuka qaraso wajen Sake maida idanun yayi ya rufe yana numfashi ahankali Zagayesu sukayi suna kallo kowanne na maida numfashin gudun dasuka sha Kifa kanta tayi ajikinshi tana cigaba da kukanta ahankali Takawa master yayi gabansu ya fizgo zee Qanqame Deen tayi gamm tana kuka sosai Janta yake amma yakasa 6an6areta hakan yaqara fusata shi ya dauketa da mari Qara tasaki tana fadawa kan Deen, qara jawo hannunta yayi da qarfi saigashi ta taho batareda tirjiya ba Saidai bata ida miqewa ba Deen da idanunshi ke rufe ruff ya riqo dayan hannunta Ja master yaqarayi amma ya riqe gamm yaqi saki saima motsi da idanunshi keyi alamun soyake ya budesu Afusace master ya fizgeta da qarfi daga riqon Deen din sannan ya kalli su alex cikin bada umarni yace "ku gama mun dashi!" Nufar Deen da har yanzu ke qoqarin tashi zaune amma yakasa sukayi alex ya cakumoshi ya miqar dashi tsaye "No! Dan Allah karku mashi komai baida lfy, please!" inji zee dake riqe a hannun master Wani naushi alex yakaima Deen wanda saida yazube acikin ruwan daya taru qasa Rufar mashi suka suna dukanshi takoina Ihu sosai zee takeyi tana roqonsu su kyaleshi Saidai kamar zugasu take, bugu suke kaimashi takoina, tun yana iya yunqurin karewa harya kasa Saida sukayi mashi laga2 sannan suka gyaleshi suka ja gefe suna maida numfashi Sakinta master yayi Hakan yasa ta ruga da gudu wajen shi inda yake kwance jina2 ta durqushe agabanshi Rufe bakinta tayi tana gunjin kuka ganin yadda sukayi mashi, jini duk ya 6atamashi kyakyawar fuskarshi "innalillahi waina ilaihi rajiun" abinda tayita maimaitawa kenan tana kallon Deen dake kwance kamar gawa ruwa sai bugunshi yake Qarasowa master yayi ya tsugunna gefenta shima yana kallon Deen din dake kwance shame2 "shi yajama kanshi ai, nagayamashi ya fita gonata yaqi, wannan itace sakayar data cancanceshi, ayau ke tawace, tamu ce duk wanda yayi yunqurin shiga tsakaninmu da cikar burinmu akanki saimun kaudashi ko wanene! Saboda mun dade muna jiran wannan ranar, mun dade muna cin burin wannan ranar, na dade ina kwadayinki, tun ranar da na dora idanuna akanki nasama raina ko ana menene saina sameki sainayi yadda nakeso dake, yanzu ina mai taimakon ki kuma? Waye zai qara fitowa don taimakon ki! Waye?! Babu! Babu! Yau ce, yau ce baqar ranar dana dade ina tanadar maki Yau zamu sauke duk wani 6acin rai dakika ta6a qunsamana, yau zamu sauke maki komai. Duk abinda kike taqama dashi yau saimun sauke makishi, kina ji kuma kina gani zamuyi amfani dake mu duka biyar daya bayan daya, again and again and again! Harsai mun tabbatar babu sauran numfashi dake fita daga huhunki sannan mu daukeki a yadda kike mu watsar abakin titi yadda komai zaki zama karin kumallon kowanne qafar sada zumunta da labarai Naked hotonki zai yawata yazama abin fadin kowa, babanki zai qara shahara shaharan da yafi na yanzu, mai muni Classic zee mai jida kudi da gayu da wulaqanci zata zama abin yad'awa a social media, naked and raped brutally by 5 mens, thats your fate!!" Tsagaitawa yayi yana maida numfashi yana kallon yadda take gunjin kuka jikinta na rawa takoina "ba mu kika kira dabbobi ba? Zakiga dabbanci and one more thing.. Nasan haryanzu bakisan yadda akayi mukayi trapping dinki ba kokuma ince wadanda suka bada gudunmawar trapping dinki You're so dull that kin kasa gane dawa kike tare dasu, kin kasa banbance masoyanki da maqiyanki, tayaya zaki iya Hakan bayan babu abinda kikasa gaba sai pride? To ki bude kunnuwanki kijini dakyau Bakowane ya taimaka mana wajen trapping dinki illah qawayenki" Dagowa tayi tana kallonsu da jajjayen idanunta in shock "yes, da taimakon qawayenki muka samu cikar muradinmu har aka kai ga haka, tsabar daqiqanci bakisan kina tareda maqiyanki ba masu son ganin bayanki, don kinga suna washe maki baki Hakan na nufin har a zuci ne? No! Sun tsaneki to the extent da har suka nemi mu kasheki bayan mun cimma burinmu, ada naso abin ya tsaya a iya rape amma tun sadda kikace babu wanda ya isa ya ta6a koda tip din akaifanki ya wanye lfy naji ina kwadayin ta6aki din, naji ta6a mutuncinki kadai bazai wadatar ba sai na hada da rayuwarki, mutuwarki ita kadai zata sani hucewa daga 6acin ranki dake raina, mutuwar wulaqanci! Babu mai cetonki, you scream and scream and scream har muryarki ta disashe, Zakiyita kokowa da numfashin ki har ki kasa jawowa, haka kina ji kina gani zaki mutu mutuwar wulaqanci, sannan kuma kizama breaking news din komai a kowanne qafar watsa labarai and that's the end, *YOUR END!!*, are you ready?" yafada yana miqewa tsaye Jada baya tashigayi tana kuka sosai "No please, karkuyimin haka, idan zaku kasheni ku kasheni amma bata wannan hanyar ba, iyayena bazasu iya jurar haka ba, mutuwa zasuyi, don Allah, Don Allah" tafada tana Hade hannayenta cikin kuka Basuce komai ba basu kuma fasa binta ba itama bata fasa jan kugu ba tana ja da baya tana roqonsu cikin kuka Saidai sam basaji sunyi nisa, kallo daya zaka masu kasan sun shawu don saida suka cika kwalwarsu da hodar iblis sannan suka zonan don haka komai nasu a toshe yake, cikar burinsu shine a gabansu Haryanzu ruwa akeyi kamar da bakin qwarya, koina na jikinsu ya jiqe sharaf musanmman zee wanda duk kayanta sun mammane mata ajiki wanda Hakan yaba surar jikinta damar fitowa sosai gashi dama gaban rigarta a yage yake Hakan yaqara sa lantarkinsu qara ja, wutar sha'awarta naqara ruruwa a zuqatansu Tun tana ja da baya har takai takasa ta tsaya ba don taso Hakan ba sai don batada kingin qarfin motsawa kuma "iyakar gudun kenan? To ai shikenan, let the game start" yafada yana qarasawa gabanta Ganin ya rankwafo da niyyar ta6ata yasata curewa awuri guda tana tamke idanunta gamm Qara taji an fasa wanda saida yayi amsa kuwa akoina Kafin ta tantance ta wanene taji an fadomata ajiki Hakan yasata zabura tana matsawa gefe tana hankada wanda yafadomata Jin Tsit yasata tafara dagowa ahankali atsorace Abinda tagani ne yasata ida dagowa ba shiri tana kallonshi Deen ne tsaye yana tangadi riqe da wani qaton icce a hannu Gefenta ta kalla taga master ne a kwance ruf da ciki qeyarshi ta fashe sai 6ul6ular da jini take Qara Jada baya tayi tana rufe bakinta da taffukan hannayenta tana qara wara idanu Deen da ke tsaye yana layi kamar dan giya yaqara riqe iccen da hannayenshi daketa 6ari yace "ku kyaleta... Or... I kill you.. Dukanku" yafada cikin rawar murya kai daji kasan mugun qarfin hali yakeyi don ko iya bude idanunshi sosai be iyawa Ganin abinda yayi wa ogansu yasasu yin kukan kura suka nufoshi Biji biji yake gani Hakan yasa yagansu sun rarrabe mashi dayawa, qara riqe iccen dake neman silalewa daga hannunshi yayi yana jan numfashi dakyar Tunma kafin suzo yafara wurwura iccen wuraren dayaga dama don ba ganinsu yakeba sosai Cikin sa'a kau yasamu alex a goshi yafadi yana qarar azaba tareda dafe wajen yana tarbe jinin daya 6allemashi Ganin kawai wurwura iccen yake batareda yasan inda yake kai iccen ba yasa kingin dakatawa suna saitin yadda zasu cafkeshi Basu sha wata wahala ba suka samu bash ya damqeshi ta baya Kokowar qwacewa Deen yashiga yi cikin fitar hayyaci amma yakasa don beda kingin wani qarfi numfashi ma dakyar yake janshi Kwace iccen t.j yayi daga hannunshi zai kwalamashi yaji saukar wani abu mai shegen nauyi akanshi Ba shiri yasaki iccen yafadi riqe da kanshi Binshi qasan zee tayi ta cigaba da makamashi katakon cikin fitar hayyaci Jitayi an cafki hannunta an fizgota har Hakan yasa katakon hannunta faduwa Mari Gandu ya dauketa dashi ta fadi yasake nufota Dagota yasake yi ya daga hannu zai qara kaimata mari ta daga gwiwarta a tsakanin kaffafunshi kamar yadda tayiwa bash dazu Wata mahaukaciyar qara yasaki, yasake ta ba shiri yafadi yana kama wajen Ganin haka yasa bash sakin Deen ya fadi sannan yanufi zee dake duqe qasa tana haki Cikin qarfin hali Deen yafara jan jiki zuwa wajen iccen da t.j yasaki ya dauka hannunshi na rawa Daidai bash ya duqa zai kamo zee yaji saukar nashi kason iccen a qeya Kama wajen yayi yana sakin qara yayi gaba zai fadama zee tayi saurin kaucewa yafadi qasa Binshi zee tayi da kallo sannan ta dago ta kalli Deen dashima yazube awajen yana jan numfashi jini duk ya 6ata jikinshi Tashi tayi da sauri kamar zata nufeshi sai kuma tadawo ta dauki katakon dazu ta bisu da daddaya tana sake kwalamasu Duk wanda ta sake kwalamawa saiya saki qarar azaba don katakon badai girma ba Sakin katakon tayi bayan ta tabbata babu mai iya tashi yanzu ta nufi Deen dake kwance babu alamun rai ajikinshi "Deen! Deen!! Wake up, Deen!!" Saidai ko motsi beyiba Tashi tayi cikin qarfin hali tana qoqarin dagoshi Saidai yamata nauyi, bata haqura ba tasake dagoshi Saidai basu ida miqewa suka koma suka zube Bata daddara ba taqara tashi tana dagoshi dakyar don burinta subar wajen donsu master na iya farfadowa akowane lokaci. Dakyar tasamu ta riqoshi tabaya ta saman cikinshi tashiga tafiya tana janshi Haka taita janshi tana nishi tana numfarfashi harta samu sukayi nisa sosai. Hango wani fassashen wuri a bangon da aka zagaya school din dashi yasata nufar wurin dashi tana cigaba da janshi Kafin su isa wurin saida suka fadi sau uku sannan suka samu suka isa. Kasancewar fassashen wurin nada girma don mutum ma na iya bi tawurin yasata fara turashi, tana nishi tana komai harta samu ta turashi waje sannan itama tafito wajen Qara kamoshi tayi ta cigaba da janshi har suka zo bakin titin dake qwal kamar anyi shara Faduwa tayi a galabaice ta jawoshi jikinta ta qanqameshi Duba gabas da yamma tayi taga babu alamun mutum ko daya bare abin hawa, titin yadda kasan an shareshi qwal, dama yaya lfiyar giwa? Dama irin titin nan ne wanda kafin abin hawa ya wuce sai anci kwakwa Saidai idan lokacin tafiyar students gidane zakaga masu abin hawa na dan shigowa saboda mutanen da basu hawan school bus din makarantar To dama su kesawa titin yadan zama busy to yanzu sai ahankali tunda majority din students suka gama exams, uwa uba ga ruwan saman da ake sheqawa Hakan yasa titin yayi tsit babu mai wucewa Wani irin kuka taqara Fashewa dashi "taimako!! Wani ya taimaka mana!! Please!!!" tafada cikin qaraji tana qara qanqame Deen dake jikinta kwance kamar gawa. Jikinshi duk ya 6aci da jini ga babu alamar numfashi ko kadan ajikinshi "Allah ka kawomana dauki! Allahumma ajirni fi musibati, ya Allah ka kawo mana dauki!" tafada tana qara qanqameshi tana kuka sosai .... ✍️ 10 Read more 🙆🏻‍♀? Gaskiya ni bata wasa bace😎 Ina masu cewa ahada masu na ranar alhamis, juma'a da asabar? To gashinan harda na lahadi na hada muku don ma karku sarai gobe, ehe😏 Don gobe ina can zaman makokin alarrama Deen, an za6eni cikin masu rabon masa, wannan karramawar har ina, kunga bekamata na watsamasu qasa a idoba 😋 Wadanda ke jiran alarrama Deen yakoma jetli, ai ba film din china bane ko india😕, wannan hausa ne ko kun ta6a ganin Ali nuhu na sama na qasa yana *qishaa🤜🏻* Saidai tingaran gajam 🤭 Yo ai hikenan 🙄 saimun hadu gidan kaka zaman makoki, aradu kuzo dawuri idan kunason samun masa don kar mutum yaje besamu ba yadawo group yana gulmata, atoh nidai babu ruwana🤥 Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:34 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *023* Batasan iya adadin lokacin da suka dauka a wajen ba don tun ana ruwan harya tsagaita har harya koma yayyafi daga baya ma ya dauke dab sai iskar sanyi irin wanda akeyi bayan angama ruwan sama Tun tana kuka har hawayen suka gaji da fitowa, muryar kuma tashaqe Rungume take da Deen haryanzu dake kwance kamar gawa ta dora kanta bisa jiqqaqiyar sumarshi Sosai sanyi ke surarta don har wani kyarma2 takeyi na sanyi Agefe wayar Deen ne data lalubo a aljihunshi dazun Saidai koda ta fiddota jiqe take jagab saima digar ruwan datake, a Hakan taso tayi amfani daita amma ko alamun kamawa batayi ba shiyasa kawai ta ajiyeta gefe Batasan ko karfe nawa ba a lokacin amma tasan dare yafara duba da duhun daren daya fara kunno kai Sake rungumo kanshi tayi tana qara cusa fuskarta cikin jiqaqqen gashinshi tana sauke numfashi ahankali tana jin yadda sanyi ke barazanar hallakata Can kamar a mafarki taji an haske mata fuska daga nesa Hakan yasa ta bude idanun ta dasuka qanqance don wahala Biji2 tafara hango hasken naqara kusanto su Hakan yasa taqara bude gajiyayyun idanunta tana kallon wajen Saidai hasken ya matso gab sannan ta gane abin hawa ne, qara wara gajiyayyun idanunta tayi don tabbatarwa ba mafarki take ba Saurin sauke kan Deen qasa tayi ta miqe jiki na bari Tsakiyar titin ta hau kamar wata sabuwar kamu tana daga hannuwa "ka tsaya! Taimako! Dan Allah ka taimaka mana!" tafada cikin dashashen muryarta tana daga hannu Daga cikin adaidaitan mutumin ke qara gwala idanu don tabbatar da idanunshi ba qarya suke gwadamashi ba Wanene wannan a irin wannan wuri a irin wannan lokacin kuma? Saida ya qara kusantowa sannan ya gane macece Gabanshi ne yafadi lokacin da zuciyarshi ta darsamashi ko aljanace Hakan yasa ya fara yin slow yana qara gwala idanu yana hangota Gani yayi tanata qara dago hannuwa alamun ya tsaya Tunani yafara yi yana shawarar ko ya juya, dama tsotsai yasashi tahowa yanzu ya biyo ta wannan hanyar, yana batsari aka kece da ruwa duk yadda yaso yataho kasawa yayi saboda qarfin ruwan haka dole ya haqura ya fake har saida ruwan ya tsagaita Da farko mutanen wajen sunso yabari sai gobe yataho amma shi hankalinshi duk yayi gida, yasan iyalanshi nacan hankalinsu atashe suna ta duban hanya Addu'o'i yafara jerowa acikin zuciyarshi yana qara rage gudun abin hawanshi har yaja ya tsaya dan nesa daita Da gudu ta qaraso wajen tana riqe gaban rigarta india ya yage Tana zuwa ta zube awajen wanda Hakan yasa mai adaidaitan yaja baya yana kallonta atsorace don harya be ida yarda mutum ce ba "Dan Allah ka taimaka mana bawan Allah, zai mutu, zamu mutu" saikuma tafashe da kuka Jin tayi magana yasa hankalinshi dan kwanciya Hadiye yawun tsoro yayi dakyar sannan yace "baiwar Allah, me kikeyi anan cikin wannan sanyin daren?" Kasa cewa komai tayi sai kukan datake "to... To kishigo na ajiyeki cikin gari" yafada yana kallonta don haryanzu bata ida kwanta mashi ba Jin Hakan yasata saurin dagowa "yana can, dan Allah ka taimaka karya ida mutuwa, yana can" tafada tana nuna inda ta ajiye Deen Bïñ inda take nunawa yayi da kallo, kana ganinshi kasan a tsorace yake Qara Hadiye yawun tsoro yayi sannan yace "wa.. Waye acan din?" "dan uwa na ne, baida lfy, don Allah ka taimaka karya mutu" tafada cikin kuka tana jin yadda kanta ke saramata Cikin sadaqarwa ya sauko Addu'o'i fall zuciyarshi Ganin Hakan yasata saurin miqewa ta nufi wajen Deen dake yashe awajen dagudu Binta mai adaidaitan yayi shima yana dan qanqame jiki saboda sanyin da ake surawa Ida qarasowa yayi wajen da sauri ganin mutum a sheme wajen "ya sallam! Meya sameshi?" be tsaya jiran amsa ba ya duqa ya dago Deen Itadai zee na baya tana kuka hannu dafe da baki "kije ki bude kofar bari na daukoshi" batama bari ya idaba ta wuce da sauri tayi yadda yace Dakyar ya cicci6oshi yanufo adaidaitan dashi Kaucewa tayi ya sakashi ciki itama ta shiga ya rufemasu qofar sannan shima ya zagaya da gudu ya shige mazauninshi Tada napep din yayi ya halbata titi Qara rungumo kanshi tayi tana kuka sosai cikin dashashen muryarta tanajin yadda jikinta ke rawar sanyi Saida sukayi tafiyar da Batasan adadinta ba sannan taji napep din ta tsaya Bude rinnanun idanunta tayi ta dago tana kallon haraban wurin Bata ida tantance wurin ba mai adaidaitan ya zagayo wajen su ya leqo yana cewa "ku jira bari nasamo nurses suzo sukama" Bejira cewarta ba ya shige cikin asibitin da gudu Maida kanta tayi bisa nashi tana cigaba da kuka marar sauti Ba'a dadeba sai gashi yafito tareda nurses dake jaye da gadon marassa lfy mai tayoyi Ganin Hakan yasa ta sauke kanshi itama ta sauko Da taimakon su nurses din aka fiddoshi aka dorashi saman gadon aka shiga turashi da sauri aka shiga cikin hospital din Binsu abaya mai adaidaitan da zee sukayi da gudu gudu sauri sauri suma Daidai bakin ward din aka dakatar dasu shikuma Deen aka shigar dashi ciki Komawa zee tayi jikin bango ta jingina sannan ta zame qasa ta cure wuri guda ta hada kai da gwiwa tana cigaba da kukan da yabar fitowa ma yanzu Kallonta mai adaidaitan yayi yaga kamar ma rawar sanyi take Hakan yasa ya fice daga wajen don samomata wasu kayan dazata chanza don koshi dake sanye da rigar sanyi yana jin sanyi inaga ita dake sanye da jiqqaqun kaya? Batasan da tafiyar shi ba sai jitayi ana mata magana bisa kai Hakan yasata saurin dagowa tana kallon mai maganar Wata nurse ce tsaye tana Binta da kallon up & down Saurin miqewa tayi tsaye tana qara riqe gaban rigarta tace "nurse ya yake? Don Allah kicemin ya farka" tafada cikin dashashen muryarta "be farka ba" inji nurse din kai tsaye "ina wanda ya kawo shi?" tafada tana sake mata kallon up and down Waiwaigawa tayi sai taga wayam babu mai adaidaita _yaushe ya tafi?_ tambayar datayiwa kanta kenan "mallama magana nake" inji nurse din tana yatsina "nice na kawoshi, ki gayamin ya ake ciki" tafada tana kallonta tana jin zafin kallon wulaqancin da nurse din kemata Qara yatsine fuska tayi sannan tace "saiki biyoni dama Dr ya buqaci ganin wanda ya kawoshi" tafada tana qarawa gaba Bin bayanta zee tayi saurin yi Saidai batayi taku uku ba taji ana magana ta bayanta "baiwar Allah! Baiwar Allah!" Dakatawa zee tayi tareda juyowa Mai adaidaitan ya qaraso wurin cikin sauri hannunshi ruqeda leda "ya ake ciki ne?" yafada yana miqamata ledar hannunshi Kallon ledar tayi takuma kalleshi da alamun tambaya a fuskarta Dan sosa qeya yayi sannan yace "erm.. Kaya ne, ki chanza wadannan sun jiqe" Shiru tayi tanajin wasu hawaye na kawomata, yau itace ake ba kyautar Kaya Amsa tayi tana hadiye hawayenta "nagode" tafada a sanyaye Kafin su qara motsi nurse din dazun tadawo tana kallon zee cikin masifa "wannan wane irin wulaqancine? Nazo kiranki kin wani koma" tafada a masifance Mai adaidaitan yayi saurin cewa "kiyi hqr sister, nine na tsaidata bansani bane" Tsaki taja sannan tajuya tana cewa "idan kinga dama kitaho, haka kawai bani na kar zomonba za'a huce akaina" ta wucewarta Binta zee zatayi mai adaidaitan yayi saurin dakatar daita "ki.. Fara chanzawa tukunna, kinga sanyi ake bari ni naje" be jira me zatace ba shima yayi gaba Shiru tayi tana nuna binshi da kallo harya wuce sannan ta maida kallonta ga ledar Budewa tayi ta leqa ta hango kayane aciki sai jitayi sanyin yaqara suromata taji babu abinda takeso kamar chanza kayan Wucewa tayi tana neman inda zata chanza kayan, dakyar tagano wani restroom tashiga Duk kyankyaminta haka ta daure tacire kayan jikinta ta Fiddo nacikin ledar ta warwaresu taga gown ce mai sauqin kudi sai hijab three qauter Zura rigar tayi ta daure madauran dake baya sannan ta saka wanda rabonta da ita har mantuwar ta mance Sosai taji sauqin sanyin da takeji dukda ba duka yatafi ba Sai tsintar kanta tayi da tunanin ko Deen shima ya chanza Kaya? Hakan yasa tayi saurin saka wadanda tacire cikin ledar tafito Waste bin datagani wurin ta jefa ledar sannan ta nufi inda suka tsaya dazu da sauri "wannan wane irin sakaci ne ko ince ganganci?! Ace mutum mai irin wannan ciwon za'a bari yashiga ruwa? Look at his clothes, kalla yadda kayanshi suke, mai pneumonia sanye da jiqqaqun kaya?" inji Dr daketa balbale mai adaidaita da bala'i Tundazu "ayi hqr don Allah..." "haka zakace ai, haka zakace tunda ba kai keda ciwon ba, mutane basusan muhinmmacin lafiyarsu ba, Sai abu yafaru sannan suzo suyita baza idanu, banda hauka ko lafiyarka lau ai shiga ruwa is not good for the health bare mai irin wannan lalular kuma a irin wannan matakin dayake" Shidai mai adaidaita Shiru yayi Dr ta cigaba da balbaleshi akan abinda besan hawa ba bare sauka Ahaka zee tashigo tasamesu Dagowa Dr tayi afusace tana mata kallon 'ke kuma fa?' Wuri2 tayi da idanu tana kallon Dr sannan ta maida ga mai adaidaitan Ganin zee yasa mai adaidaitan cewa "yauwa, ga wanda suke tarenan, qaraso baiwar Allah" Qarasowa tayi tana kalle2 a office din "Dr ya jikinshi? Dan Allah kicemin ya farfado" tafada cikin rawar murya Haushi yaqara qume Dr basira, dama gata masifaffa abu kadan ke hassalata "tayaya zai farfado bayan kun so ku kasheshi ne?" Dagowa tayi da sauri ta kalli likitan "A'a Dr, dan Allah ki taimaka mana karya mutu, idan yamutu bazan iya yafewa kaina ba" tafada hawaye na kawomata "to dama wake take? Kima roqi Allah ya yafemiki kafin akai ga kankin, dama kuna sonshi kuka bari Hakan tafaru dashi? Zakizo kina ma mutane kukan munafurci? Wai tukunna ma ina iyayenku ko wani babba mai hankali? Ku suwanene nashi?" Izuwa yanzu mai adaidaita yafara quluwa "Don Allah Don annabi Dr ki kyalemu hakan ki kulamana dashi, idan be mutun ba a dalilin sakacinmu ai yanzu sakacinki na iya sawa ya qarasa" Sakin baki Dr tayi tana kallonshi "rashin kunya zakamun? A haife ban haifeka ba?" inji matar cikin masifa Ganin Hakan yasa zee daketa hawaye Tundazu ga kanta dake saramata kamar zai rabe gida biyu tace "don Allah kiyi hqr Dr, kiyi hqr wlh tsotsai ne, dan allah ki dubamana shi karya mut..." saikuma ta rufe baki tana shesheqa Ganin Hakan yasa Dr basira tadan sauko ta antayama mai adaidaita daya juyar dakai ganin ta kalloshi harara sannan takoma ta zauna taciro wata paper tahau rubuce2 Saida tagama sannan ta miqama zee fuska a daure Da sauri ta amsa tana share hawayenta "kuje ku samo wannan, kuma dole sai an qaramashi jini don nashi ya zuba sosai" tafada tana harararsu qasa2 don ita a duniya ta tsani masu sakaci da lfy Zee daketa amsamata da to tayi saurin Juyawa zata tafi saikuma ta tuna da wani abu saita qara juyowa ta fuskanci Dr data fara rubuce2 "amm... Dr don Allah.. An chanza mashi.. Kaya" tafada a rarrabe ganin kallon da Dr din ke jifanta dashi "A'a a tsirara yake" tafada cikin quluwa Jin Hakan yasata saurin Juyawa zata tafi tana cewa "kiyi hqr na dauka..." "yanzu ai saiki sauke " ta katseta da Hakan tana binsu da harara har suka fice Tsaki taja sannan ta cigaba da abinda take rai 6ace Kai tsaye wajen masu saida kati suka nufa don sayen kati Koda aka buqaci sunan majinyacin zee ce tabada full name din Deen. Haka sukaita zirga2 har suka samu aka bude mashi file Daga nan kuma suka wuce blood bank don siyan jini Saidai an duba kaf babu irin nashi kasancewar 'O' group yake mai wuyar samu Dawowa sukayi wajen Dr din suka gayamata Cemasu tayi to agwada acikinsu agani ko akwai meshi idan kuma babu su nemo ko cikin yan uwa, yanzu zata faramashi qarin ruwa, takuma gargadesu akan suyi sauri don jininshi yayi qasa sosai idan ba so suke ya sheqa ba Haka suka fito kuma suka wuce lab inda ake gwajin jini dukda dukkansu sunsan ba 'O' group ne jininsu ba Saidai kowanne na fatan ace dayan na cikin group din Sosai zee ke qarfin hali wajen zirga2 nan, don ita kanta da za'a aunata da anbata gado Saida aka aunasu akaga duk jininsu beyi sannan suka fito jiki a mace Juyowa mai adaidaitan yayi ya kalli zee dake dauke hawayenta da gefen hijabinta, fuskarta tayi fayau daka ganta saita baka tausayi Shiru yadanyi sannan yace "yanzu ya xa'ayi?" Shiru tayi cikin rashin sanin abin yi don kwalwarta ta toshe "ko kinada number wani daga cikin yan gidanku sai a kira" Dagowa tayi ta kalleshi, ita sai yanzu ma ta tuna da kira tsabar yadda kanta yahau chaji "eh amma banida waya ta fadi" tafada cikin sauri Zura hannu yayi cikin aljihu ya Fiddo tashi "ga wannan ki kira daita" yafada yana miqamata Saurin amsa tayi hannu na rawa tashiga loda number daddy kaida gani tana cikin zaquwa Dialing din number tayi ta kara a kunne idanunta na durar ruwa _line busy_ akace mata Hakan yasa tayi Dialing din number mummy Bugu biyu aka daga mummy tayi sallama cikin nutsuwa Jin muryar mummy yasata fadawa cikin shauqi kukan datake dannewa Tundazu yafito "subhanallilah! Zainab? Zainab kece? Hello?" inji mummy a rude Duk yadda taso tsaida kukan saita kasa sai shesheqa take takasa magana Can taji muryar daddy qasa qasa da alamu da mummy yake magana can kuma taji muryarshi yana kiran sunanta shima da alamu amsar wayar yayi "daughter? Please talk to me, is that you?" yafada cikin tsananin damuwa Dakyar ta tsaida kukan tasamu ta bude baki "Daddy na.." saikuma ta fashe da kuka Mai adaidaita yana gefe sai kallonta yake cikeda tausayawa "ya ilahi! Daughter ina kika shiga? Gamunan hankalinmu duk ya tashi babu inda bamu jeba amma babu ke? Ina kike? Why are you crying?" yafada kamar shima zaiyi kukan Jan majina tayi sannan tace "Daddy muna asibiti, zai mutu. Haryanzu ban ganshi ba, be tashi ba" tafada cikin kuka sosai "subhanallilah! Hospital? Meya sameki? Wazai mutu? Wane asibiti kuke?" ya jero mata tambayoyin lokaci guda Kukan datake yasa takasa amsawa Hakan yasa mai adaidaitan amsar wayar hannunta ya kara a kunne yayi sallama "wslm, bawan allah meke faruwa dan allah? Meya samu daughter? Wane asibiti kuke?" inji daddy hankali tashe "amm.. Asibitin qwararu (medical centre) kuma jiki da sauqi amma so samu kuzo" yafada calmly "to.. To.. Gamunan, Gamunan yanzu yanzunan, Gamunan..." Kitt... Aka yanke kiran Juyawa yayi wurin zee data sulale ta zauna kan wata kujera sannan ya qaraso shima ya zauna daga dan nesa da ita Kallonta yasake yi yana neman kalmar da zaiyi amfani daita wurin rarrashinta "dan allah kibar kukan nan haka, insha allah allah zai tashi kafadunshi, a halin yanzu yafi buqatar addu'armu fiyeda komai, kiyi hqr allah baya dorawa bawa abinda bazai iyaba" yafada cikin rarrashi Hakan ya dan taimaka don ta rage kukan sai shesheqa datakeyi akai2 jin kanta take kamar ba nata ba, kamar ta cire ta jefar ko zata huta Shiru wajen ya dauka kowa da saqe saqen dayake duk suna jiran tsanmmani yayinda hankalin mai adaidaita duk yayi gida yasan matarshi nacan hankalinta atashe, sake duba agogon wayarshi yayi yaga 11 takusa gashi batada waya bare ya kirata ya gayamata halin da ake ciki Gashi ita kadai ke gidan kasancewar duka2 watansu bakwai da aure yanzu haka ciki gareta na wata biyar Hakan yasa yaji duk hankalinshi yayi gida don yasan duk inda take hankalinta a tashe yake shi gudu ma yake kar tace zata fita cikin daren nan don yasan halinta qaramin aikinta ne tace zata tafi nemanshi gidansu, gashi Tundazu yake neman wayar qannenshi bata shiga Komawa yayi ya jingina da kujerar ya harde hannayenshi a qirji yana karkada kafaffu, allah allah kawai yake mutumin dasukayi waya dashi yanzu din ya qaraso ko zai samu shima yatafi don bazai iya barinsu ba a wannan halin... ✍️ Manage👏 Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:34 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *024* Zaune suke Shiru na wani lokaci, can ringing wayar mutumin ta dawo da kowanne daga duniyar tunaninshi Duba wayar yayi yaga daddy ne Dagowa yayi ya kalli zee dake kallonshi itama "shine, qila sun qaraso" yafada yana dan yimata murmushi sannan ya daga "assalamu alaikum" "wslm, d'ana gamunan mun qaraso kuna ina ne?" "ok bari nazo reception sai nataho daku" inji mai adaidaitan sannan ya katse kiran Kallon zee dake suraronsu Tundazu yayi "bari naje na taho dasu" Kada mashi kai kawai tayi ya tashi ya tafi Lumshe idanu tayi tana jin yadda kanta ke sara haryanzu Koda mai adaidaitan yaje reception waige2 yashigayi don ganin inda zai hango mutumin Yana cikin haka yaji an dafashi saurin juyowa yayi saiyaci karo da wasu yan sanda biyu, daya hannunshi riqe da waya yana kira yayinda daidai lokacin wayar mai adaidaitan tafara ringing "shine" inji mai kiran yana sauke wayar daga kunne Binsu da kallo mai adawo keyi gabanshi na faduwa, shine wa? Meye kuma nashi da yan sanda? Kamar sun karanci tsoronshi don haka daya yace "karka damu abokina, ni sunana A.s.p Jamal Qaseem, muna tareda mahaifin wannan yarinyar, fatan kaine mukayi waya dashi dazu" Kada masu kai kawai yayi don shi bega abin tattago yan sanda ba a wannan case din "ok muje, gasucan ku gana" inji dayan yana gwadamashi hanya Ba musu yawuce suka takemashi baya har suka isa parking space daga gefe inda wata dalleliyar mota ke a parke securities takoina Qarasowarsu wajen yasa A.s.p Jamal yawuce wajen motar ya kwankwasa Mai adaidaitan besan ko me yace ba sai gani yayi an bybbude back seat din an fito Wani mutum yagani wanda kallo daya zaka mashi ka gane ba qaramin mutum bane saboda cikar haiba da qwarjini irinna masu arziqi sai macen da kallo daya zaka mata kasan jinin zee ce saboda matsananciyar kama dasukeyi Cikin nutsuwa suka qaraso wajensu mai adaidaitan, daddy na kafeshi da kallo Sauke kanshi yayi cikin jin nauyin daddyn ya shiga gaidasu yana dan russunawa cikin zuciyarshi yana gulmar wai ashe masu kudine wadanda ya taimaka? Amsawa sukayi atare sannan daddy yace "bawan Allah kaine mukayi waya dakai yanzu?" Qara dan duqar dakai yayi yace "eh alhaji nine" Ajiyar zuciya daddy ya sauke na jindadi yace "to ina take? Ina daughter? Hope babu abinda ya sameta" yafada cikin damuwa Kada kai mai adaidaitan yayi yace "babu abinda ya sameta insha Allah, muje ku ganta" yafada yana basu hanya "yauwa muje" Nan suka shiga asibitin bisa jagorancin mai adaidaitan Zee dake zaune haryanzu Saidai yanzu ta hada kai da gwiwa tayi shiru taji alamun tafiyar mutane na kusantota Hakan yasata dagowa da jajjayen idanun ta Su daddy da mummy ta hango tafe da wasu mutane da bata wani tsaya tantancesu ba Tashi tayi azabure ta nufi daddy da gudu Fadawa jikinshi tayi ta kankameshi tana sake Fashewa da kukan da yanzu yabar zuwa da hawaye don suma idanun izuwa yanzu sun gaji da zubda kwalar Maida hannuwa shima daddy yayi a bayanta ya rungumeta yana sauke ajiyar zuciya Dagota yayi yayi cupping fuskarta a taffukan hannunshi yana bin fuskarta da kallo "are you ok daughter? What happened? Meya samu fuskarki?" yafada yana bin fuskarta da duk sahun yatsun marukan datasha suka fito sukayi jajur abinka da farar fata kuma ta hutu Batace komai ba sai qara komawa jikinshi datayi tana cigaba da kukan Janta yayi wajen kujerar data taso ya zaunar daita shima ya zauna ya cigaba da rarrashinta A dayan bangaren kuma mai adaidaita wanda yace sunanshi Ahmad yake bawa yan sandan bayyanin yadda suka hadu dasu dakuma inda yagansu Saida suka gama sauraron dukkan bayaninshi sannan ya nemi su barshi yatafi gida don yabaro iyalinshi ga kuma halin datake aciki Basu qi ba Saidai sun amshi number wayarshi sannan mummy tayita mashi godiya da fatan gamawa da duniya lafiya Saida zai tafi sannan daddy shima yataso daga wajen zee dake narke jikinshi yana ta rarrashi Tundazu yazo shima yaita yimashi godiya yakuma debo kudade masu yawa yabashi, dafarko yaqi amsa amma ganin ya nace yasa ya amsa ba don yasoba ya tafi da alqawarin zai shigo gobe insha allah yaga mai jiki Daga nan office din Dr Basira suka nufa don zee ta nace akan itadai Deen, karya mutu Sosai Dr tayi mammakin ganin babban mutum kamar Alhaji Farouq a office dinta Tarba tayi masu na mutunci sannan sukayi mata bayyani Tayi mammaki sosai ganin cewa ashe diyar dan faranshi tayima haka, Hakan yasa ta tashi tafara rawar jiki wajen ganin an kula da Deen yadda ya kamata sannan ta qara gayamasu ana buqatar jini cikin gaggawa don nashi yayi qasa kuma gashi babu irin nashi a hospital din Abunka da manya waya kawai Alhaji yayi wa family doctor dinsu ya fadamashi buqatar shi, cikin qanqanin lokaci saigashi a hospital din da jinin nan aka shiga qaramashi ana bashi taimakon gaggawa wanda za'a samu adan shawo kanshi kafin gobe da safe da za'a basu transfer sukoma wata asibitin Zee ma daga baya kwantar daita akayi saboda wani zazzafan zazza6ine ya lullu6eta itama, Hakan yasa aka bata gado itama aka duqufa akan su biyun don ganin an shawo kan matsalarsu. *KAKA* Tunda aka fara iska iskar hadari hankalin kaka yaqi kwanciya Sai duban hanya take taga ta inda Deen zai 6ullo amma Shiru kakeji Hankalinta ne ya ida tashi lokacin da aka kece da ruwa, idan ta tuna da kayan daya fita dasu sai hankalinta yaqara tashi Haka ta zauna bakin kofar dakinta ta buga tagumi tana hango qofar shigowa cikin jiran tsanmmani amma Shiru kakeji wai mallam yaci shurwa Tun tana daukar abin wasa har abin yafara bata tsoro, tun tana jiran agama ruwan har taji bata iya wannan haqurin. Hakan yasa tafito cikin ruwan tareda yar lemar ta (umbrella) ta nufi gidan maqofcinsu wanda ya samomashi form din company dinnan Ta dade tana bubbugawa sannan aka bude gidan Sosai maqofcin wato mallam Nasiru yayi mammakin ganin kaka cikin wannan ruwan da ake tsugawa Iso yayi mata ta shigo ciki nan tashiga gayamashi abinda ke faruwa cikin matsar qwalla Kwantar mata da hankali mallam Nasiru da matarshi suka yi da cewa wataqila fakewa yayi har ruwan ya dan tsagaita sannan yataho tunda shima yasan da lalurarshi bazai yarda yashiga ruwan ba Da wannan hankalin kaka ya dan kwanta Saidai still takasa komawa daidai, bini bini ta kalli agogo zuciyarta na qara tsunduma cikin fargaba Haka dai matar mallam Nasiru ta zauna da ita suna jiran tsanmmani Ganin har magrib ta gabato babu Deen ba alamunshi yasa hankalinta ida dugunzuma Kuka kawai takeyi tana cewa itadai makarantar nan zata tafi, tana ji aranta duk inda Kamal yake ba lafiya ba Tun Mallam Nasiru na rarrashinta akan tabari ruwan ya tsagaita har ya haqura yaje yasamo mai adaidaita na cikin unguwa suka shiga dashi da kakar mai adaidaitan yajasu zuwa makarantar Kafin su isa makarantar ruwa ya tsagaita sosai don harya koma yayyafi A bakin gate din makarantar suka sauka sukaje nufi wajen mai gadi Sosai mai gadin yayi mammaki jin wai wani suka zo nema nan yace musu gaskiya baya tunanin akwai sauran student ko daya a school din don tun hadarin nafara taruwa suka fito dama ba yawa garesu ba yan qallilan ne dake qarasa Jarabawarsu yau kuma suna fitowa motar school ta kwashesu ta tafi dasu don kosun tsaya ba samun abin hawa zasuyi ba Dukda haka kaka tayi insisting akan itadai a duba wataqila shi be fitoba Babu yadda suka iya haka suka shiga makarantar aka fara nemanshi Every nook and cranny saida suka duba babu Deen babu alamunshi, kuka kau kaka ta shashi harta godewa allah Dakyar aka rarrasheta akan su koma gida sugani qila yakoma, wataqila harda shi aka shiga bus din saiya fake cikin unguwa kafin ruwan ya tsagaita Haka suka fita suka shiga napep din kaka nata kuka suka nufi gida kowa na addu'ar allah yasa su taddashi gidan Fitarsu kaka daga school din keda wuya motarsu daddy ma tashigo Suma the same story ne da kaka don ruwan saman ya hana bala zuwa daukanta sai yanzu suka samu yadan tsagaita suka taho Saidai suma the same amsa mai gadin yafada masu Suma basu yarda ba suka shiga school din suka duba koina babu ita ba alamunta Saidai duk nemansu babu wanda ranshi yabashi su duba can bayan school din don basu ta6a kawoma ransu ba don school din nada girma da fadi kuma can bayan school din duk jejine bazasu ta6a kawo ma ransu zasu nufi wajen ba Suma haka suka haqura suka tafi Wasa wasa abu qarami yazama babba don koda su kaka suka dawo gida babu Deen Hakan yasa hankalin kaka yayi qololuwar tashi, kuka take tana fadin dan allah a nemomata dan marayanta, bashi da kowa sai ita itama batada kowa sai shi Cikin qanqanin lokaci labari ya kewaye unguwa, Deen din kaka ya 6ata Saigashi cikin daren nan gungun mazan unguwar, matasa da dattijawa suka bazama neman Deen yayinda mata sukaita shigowa gidan kaka suka zauna daita anata rarrashi da jaje A bangaren su daddy kau koda labari ya riskeshi akan ba'a ganta a school ba hankalin shi ne ya tashi, gashi anata neman number ta bata shiga Hakan yasa shima fitowa aka shiga neman dashi Dafarko police station suka nufa inda daga nan aka qara komawa school din don qara bincikawa Agefe kuma aka kira school authority din aka gayamashi abinda ke faruwa Hankali tashe shima yakira wasu manyan school din suka dunguma sukayi school din Sosai aka shiga nema again ana chaje koina na school din Saidai babu ita. Hankalin daddy yatashi sosai Hakan yasa ya baza jami'an tsaro akoina don nemo mashi tilon diyarshi Itama mummy hankalinta ya tashi sosai, tsakanin uwa da 'ya sai allah saigashi sai dauke hawaye take akai2, addu'arta kawai allah ya karemata diyarta a duk inda take Sai wajajen shadaya ne kira yashigo wayar mummy, tana ganin kiran taji ajikinta cewa kiran nada alaqa da Zainab Hakan yasa tayi saurin dagawa Jin kukan Zainab yasata yin sallalami takira sunanta wanda Hakan yaja hankalin daddy dake gefe baya zaune baya tsaye yana amsar kira takoina To shine fa yazo ya amshe wayar hannun mummy inda anan sukaji ainahin inda zee din take. A bangaren kaka kau kwanan zaune tayi akan sallaya don wajajen shabiyu tawagar neman Deen suka dawo basu ganshi ba amma sun aje akan gobe da angama sallar asuba zasu qara bazama nemanshi dukda sunkai rahoto a station din unguwar Abinda zai burgeka shine yadda kowa ke jajjantawa al'amarin dakuma yadda kowa ya damu don masha allah Deen mutumin mutane ne bayada matsala ko kadan Duk wanda ya budi bakinshi a wajen sai kaji yanata kwararo yabone akanshi Dakyar dai matan suka samu suka lalla6a kaka tabar kuka sannan dayawa suka koma gida suna fatan allah ya bayyanashi inda wasu kamar su matar mallam Nasiru da wata dattijuwa tsarar kaka wanda suke amintaka sosai da ita suka tayata kwana Yadda kaka taga rana haka taga dare don kwana tayi zaune akan sallaya tana kwararo ma Deen addu'o'in tsari a duk inda yake *WASHEGARI* Alhamdulillah zee taji sauqi sosai don yanzu babu wani zazza6i a jikinta sai murar datake dakuma yan ciwukkan dataji da akayi treating dinsu Da safen akayiwa Deen da har yanzu bai farkaba transfer daga wannan asibitin zuwa asibitin kudi inda family doctor dinsu yake Duk yadda akaso zee tabi mummy su koma gida don itama ta huta qi tayi da taga za'a matsamata ma saita sa kuka Hakan yasa daddy yace abarta don idan akwai abinda ya tsana to kukan shalelenshi ne Acan private hospital din yan sandan jiya wato su A.s.p Jamal suka iskesu, lokacin har anyi admitting din Deen likitoci sun duqufa akanshi suna baje kolin basirarsu ta wannan fannin Zee suka samu suka nemi ta gayamasu duk abinda yafaru Bata 6oyemusu komai ba ta warware masu duk abinda yafaru tana kuka Ran Alhaji farouq ya 6aci sosai yabada umarnin aje akamo masu sa hannu a wannan abin duk inda suke sannan a dayan 6angaren kuma a nemo dangin Deen don yasan suma sunacan cikin tashin hankali Amsawa sukayi da angama suna bashi tabbacin cika aikinsu yadda ya kamata *UMYAU* School ne ya rikice lokacin da labarin abinda yafaru jiya ya riski yan tsirarun mutanen dasuka zo school din Abin be ida rikicewa ba saida yan sanda suka dira school din Can bayan school din kamar yadda zee tayimasu bayani suka nufa inda anan suka tsinci littatafan Deen dasuka jiqe suka 6aci da cha6i sai jakkar zee da gyallenta sai agogon daya daga cikinsu master Sosai hankalin mallaman makarantar yatashi jin abinda yafaru a bakin polisawan Nan da nan aka fifiddo files dinsu master dasu sumee na makarantar don bincike Babu 6ata lokaci aka watsa yan sanda don kamo mutanen da ake zargi Cikin sauqi aka ritsa dasu sumee kowacce a gidansu Zokaga tashin hankali wajen wadannan ahali dasu kansu su sumee Abin yazo masu mugun bazata don ko kusa basu ta6a tunanin abin zai juye masu haka ba tunda su aganinsu an riga an gama daita babu yadda za'ayi a zargesu Duk hada kansu akayi akayi station dasu aka garqame A bangaren su master kau, anyi neman duniyan nan ba'a gansu ba don kowannensu babu wanda iyayensu ko danginsu suka san inda suke, wasu ma rabon da susasu dansu a idanu mantuwar harta manta musanmman ma iyayen master wadanda sun tsufa ga talauci daya qarawa tsufan tsanani Abin tausayi haka aka kama uban kowanne aka riqe akan idan aka ganosu za'a sakesu Zokaga kuka a wajen wadannan ahali musanmman na master, uwar tayi kuka kamar zata shide, fadi take allah ya isa tsakaninta da murtala, bazata ta6a yafemashi ba kuma tayi danasanin haihuwarshi datayi Abu dai ba dadi, sai bayan an kukkulesu ne sannan aka samu wani yazo yafadama yan sandan gidan da su mastern suke kwana amma koda sukaje babu su babu alamunsu donma ga yadda suka iske dakin a hargitse wardrobe dinsu babu komai ya tabbatar musu sun gudu. Hakan yasa aka baza matakan tsaro akoina harda tashoshin motoci da airport don kama wadannan shaidanun *KAKA* Kamar yadda mutanen unguwa sukayi alqawari saigashi suna gama sallar asuba suka sake taruwa don fita nemanshi Kasa kansu sukayi kashi2 inda kowa da inda ya nufa yadda abin zaifi zuwa da sauqi sannan suka bazama Kaka kau kallo daya zakamata tabaka tausayi saboda har ramar dare daya saida tayi Kan kace me? Gida yafara cika da mata yan jaje, a unguwa duk inda ka wuce sai kaji ana labarin 6acewar Deen din Kaka mai koko. Wajajen qarfe tara saura yansanda suka dira kofar gidansu Deen. Nan suka nemi iso cikin gidan sannan suka shiga Haka aka rakasu dakin Kaka inda take zaune ba uhm ba uhm uhm sai yar charbinta datake ja Ganin yansandan hankalinta yaqara tashi jin maganar Deen ce takawosu Saida suka kwantar mata da hankali sosai sannan suka sanar daita Deen na asibiti dukda basu fadamata halin dayake ciki ba Nan take gida ya kaure da koke koke, Kaka nayi mutane nayi, yan kadan ne masu rarrashi Haka Kaka tafito tana shar6ar kuka da ita da matar mallam Nasiru da Baaba Abu aminiyarta suka bi yansandan bayan kowacce mace tafito an rufe gidan A motar ne matar mallam Nasiru ta bugawa mallam Nasirun waya akan anga Deen yana asibiti takuma fadamashi sunan asibitin Su zee na zaune a waiting room tareda daddy su Kaka suka iso Sosai Kaka ke kuka akan abari ta ganshi Haquri akaita bata akan tayi Haquri likitoci ke ciki tabari sugama aikinsu Dukda Hakan batayi Shiru ba sai kuka take tana su taimaka mata shi kadai gareta Haquri duk akaita bata akan ta kwantar da hankalinta insha allah komai zaizo da sauki Dakyar aka samu ta zaune tayi shiru Saidai kwata2 hawayenta sunqi tsayawa Zuwansu Kaka ba qaramin sake dagulama zee lissafi yayi ba don itama kukan nata da akasamu yayi sauqi ta cigaba dayi, tanajin cewa duk itace silar komai, idan wani abu yafaru da Deen tasan bazata ta6a yafewa kanta ba Ana haka su mallam Nasiru da kingin yan tawagar neman Deen din suka qaraso, nan aka hadu aka tsaya jiran tsanmmani... ✍️ Manage 👏 babu dai editing, mugun wuya yake mun aradu☹️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:34 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *025* Sun jima anan sosai sannan likitocin suka fito daga dakin da aka kwantar da Deen din Mutanen na kyalla ido suka ga fitowarsu duk sai suka tashi kowa cikin jiran jin abinda likitocin zasu ce Matsowa kaka tayi gabansu likitocin cikin hawaye tace "Likita ya ake ciki? Ina jikana? Meya sameshi?" Shima daddy ya taso ya matso wajensu, zee a gefenshi itama cikin zaquwar tasan halin da Deen din ke ciki "Dr how is he now?" inji daddyn Family Dr dinsu dake kan gaba a kula da Deen din yace "Alhamdulillah, ku kwantar da hankalinku. Insha allah zaiji sauqi kai yama ji sauqi insha allah, yanzu dai Alhaji muje office akwai bayyanan da zan maku gamedashi acan" Caraff kaka tace "harda ni za'aiwa bayanin, ni kakarsa ce bayada kowa saini nima banida kowa saishi ku taimaka ku fadamin wani hali yake ciki, ku kaini wajenshi don Allah" ta qarashe tana rufe fuska da gefen zani Dafa kafadarta Baaba Abu tayi cikin sigar rarrashi itama tana matsar kwalla "eh, ita grandma dinshi ce, i think itama tanada ikon jin abinda ke faruwa tunda itama makusanciyarshi ce" inji daddy "ba damuwa, muje office din" inji Dr din yana yin gaba Juyawa daddy yayi ga zee datake tsane idanunta da farin hankin hannunta yayi cupping din fuskarta "dear, bari muje uhm? Kijiramu anan ok?" yafada a tausashe Ahankali ta Kada kai, kiss ya mannamata a goshi sannan ya nemi wani acikin maxan yazo shima, nan mallam Nasiru yazo suka wuce tare, ita kau kaka tuni tayi gaba Binsu da kallo zee tayi har suka shige sannan ta maida kallonta kan kofar dakin da Deen din yake ta kafeta da ido, jitake kamar taje ta bude tashige ta ganshi ko zataji sanyi sanyi a ranta Komawa tayi ta zauna ta jingina da jikin kujerar tareda lumshe gajiyayun idanunta tana jiran fitowarsu daddy *OFFICE* Tunda Dr yafara bayyani kaka keta kuka harya kai aya "innalillahi waina ilaihi rajiun, innalillahi waina ilaihi rajiun. Dama haka wancan Likitan na Janaral (General) yace, sosai ya gargademu akan kar ya shiga ruwa, ko iska ake sosai yace karya sake yafita babu kayan sanyi, yanzu idan Kamal yatafi yabarni ya zanyi? Ya zanyi da rayuwata ni Ma'u?" taqara Fashewa da kuka tana rufe fuska da gefen zane "Hajiya kiyi hqr, insha Allah Allah zai tashi kafadunshi, insha allah zai samu lafiya" inji Daddy cikin sigar rarrashi Dan kallonshi tayi ta gefen ido ta kauda kai tana cewa "ai dama haka za'ace, dama ai wanda aka cuta ake ba haquri, yaro besan hawaba besan sauka ba anjamashi jinya, yaron daba ruwanshi da kowa, harkar gabanshi kawai yake yanzu gashi anjamashi shiga halin rai ko mutuwa, wannan abu da me yayi kama?" saikuma taqara Fashewa da wani kukan Kasa cewa komai daddy yayi sai mallam Nasiru dayayi saurin cewa "haba kaka? Komai fa muqaddarine daga allah, Duk abinda kike ganin yafaru da mutum to allah yariga da ya qaddara Hakan zai faru dashi don Allah kiyi hqr insha allah Deen dinmu zai tashi akan kafafunshi nan kusa" Bata sake cewa komai ba sai kukan data cigaba dayi "yanzu Dr zamu iya ganinshi?" inji mallam Nasiru "A'a Gaskiya don a halin Yanzu baya buqatar hayaniya ko kadan.." "Dan Allah likita kubari naganshi, wlh bazanyi hayaniya ba, yadda na shiga haka zan fito ko kwakwarar motsi bazanyi ba, Don Allah" inji kaka cikin muryar kuka "kaka bawai hanaki nayi ganinshi ba, wlh dokace idan mutum na a wannan condition din ba'a barin ashiga dakin, kiyi hqr" inji Dr "Nidai Don Allah kayi hqr inganshi, bakasan yadda nakeji a zuciyata bane da kasani daka bari na ganshi, don Allah Alhaji kacemashi yabarni na ganshi, shine kadai sanyin idanuna, sanin halin dayake ciki zaisani jin sauqin abinda nakeji a raina, don Allah" tafada tana kallon daddy pleadingly Kallon Dr daddy yayi yace "Dr please do something, abarta ta ganshi ko daga nesa ne" Shiru Dr din yayi na wani lokaci cikin nazari sannan yace "ok, Gaskiya Saidai ta cctv don it's a strict law patients dake cikin irin wannan condition din babu mai shiga wajensu sai likitoci, wannan dokace akowanne hospital ba a wannan kadai ba Amma tunda ta nace zamu kaita recording room saita ganshi ta cctv, wannan shine iya taimakon dazamu iya yimata Gaskiya" "eh babu komai, akaini rekodin din, naji akaini" tafada tana share hawayenta da ha6ar zane Tashi Dr din yayi yace "to bismillah" Duk tashi suma sukayi Dr yayi gaba suka maramashi baya Jin tafiyar su yasa zee bude idanunta ta dago tana kallonsu Ganin zasu nufi wata hanyar yasata saurin tashi ta nufo daddy Ba musu ya miqamata hannu ta kama suka cigaba da bin Dr Recording room din suka shiga inda duk zirga zirgan da akeyi a hospital din ana ganinshi a wani qaton majigi Dr din ne yayi ma mutumin dake in charge of wajen magana akan ayimasu zooming din room 12 Yadda yace din haka mutumin yayi, yayi zooming din abinda ke faruwa a dakin da Deen ke kwance Gasping both kaka da zee sukayi suna rufe baki cikin tashin hankali Deen ne kwance kan gado sanye da blue kayan asibiti da akewasa marassa lfy Kanshi nannade da bandage, hancinshi sanye da abin oxygen dake taimakawa wajen jawo numfashi sai hannunshi dakeda cannula anamashi qarin ruwa Zamewa kaka tayi zata fadi zaune mallam Nasiru yayi saurin kamata ya zaunar daita kan wata kujera Kafe Deen din cikin majigin tayi da kallo idanunta na tsiyayar hawaye, ganinshi a wannan condition din ba qaramin ta6amata zuciya yayi ba hakan yasa tashiga yin kuka kamar zata shide Zee kau Fadawa jikin daddy tayi ta rintse idanunta gamm Bazata iya jurar kallon Deen a wannan halin ba hakan yasa taqara rintse idanunta gamm tana shesheka Shafa bayanta daddy keyi cikin sigar rarrashi idanunshi na kan Deen din cikin majigi Dole duk mai imani idan yaga Deen a halin dayake aciki ya tausayamashi "Dr please do everything you can to save him, please" inji daddy "insha allah sir, ku kwantar da hankalinku insha allah zai tashi zai koma kamar be ta6a kwanciyaba insha allah" inji Dr din cikin son qarfafa musu gwiwa Dakyar aka samu aka rarrashi kaka tareda yimata nasihohi sannan suka fito Alhaji ne yabiya duka bill din treatment din Deen din Saida suka qara tattaunawa da Dr inda aka fadama kingin yan unguwansu Deen dake wajen halin da ake ciki, sosai kowa ya jajjanta tareda yimashi addu'ar samun sauqi Nan mazan duk suka tafi da tabbacin zasu dawo anjima da marece aka bar kaka da matar Nasiru da baaba abu sai daddy da zee Basu dade da tafiya ba motar gidansu zee tashigo hospital din Wata dattijuwa cikin ma'aikatan gidansu zee ta tafito ita da bala driver daya kawota Hannunta dauke da basket din abinci wanda mummy tasa akawo musu Saida suka gagaisa da kowa sunamasu ya jiki sannan daddy da zee suka tashi akan zasubi bala ya ajiyesu gida, ita kuma dattijuwar mai aikin saita tsaya dasu Godiya su matar mallam Nasiru da baaba abu suka shiga yimashi saboda sosai ya nuna hallaci duba da yadda ya tsaya akansu sosai batareda yayi la'akari da matsayinshi ba na babban mutum Itakau kaka batama san da tafiyarsu ba don tunda tadawo ta zauna ta buga tagumi ba tace komaiba sai Kafe waje guda da ido datayi Bayan tafiyarsu daddy ne dattijuwar yar aikin mai suna Inna Binta ta gabatar masu abincin datazo dashi, duk sunci sai kaka da sukayi juyin duniyar akan taci amma taqiya haka suka haqura suka kyaleta A bangaren zee kau koda suka isa gida mummy ce ta tisata gaba tayi wanka da ruwan masu dumi sosai ta gaggasa jikinta sannan ta tilasta mata taci abinci dukda bada wani yawa taciba sannan tabata maggugunanta tasha tasata ta kwanta Ko minti biyar ba'ayiba da kwanciyarta barcin gajiya ya saceta Tasha barci sosai wanda ke cike da mafarkan Deen kala2 wanda tana tashi duk ta mance mafi yawa a cikinsu Sosai taji dadin jikinta yanzu duk wata gajiya ta tafi sai dan abinda ba'a rasaba saikuma murar datake fama daita haryanzu Miqewa tayi tashiga toilet ta dauro alwalla sannan tazo ta gabatar da zuhr daya wuceta ta dora da asr da ake cikin lokacinta yanzu Ta dade tana yima Deen addu'ar samun lafiya sannan ta nemi sakayyar allah akansu nurr dasuka ci amanarta da su master dasuka nufeta da sharri Saida tagama sannan takoma kan gado ta zauna ta lula duniyar tunani Ahaka wata maid tashigo kiranta inji mummy Tashi tayi bayan ta yafa veil din gown dinta ta bita Kamar yadda ta hasaso abinci mummy zata sata ci Saida ta gaidata mummy ta amsa tana mata ya jiki ta amsa da da sauki sannan mummy ta zubamata farfesun kan rago wanda yaji kayan yaji sosai ta turamata a gabanta Babu musu tashiga sha don itama tana buqatar abinda zai dan warware mata toshewar hanci datake fama dashi sai gashi kuma ya taimaka sosai don taji dadin jikinta bayan tasha Haka taita kasa kunne taji ance ta taso su koma asibiti amma shiru Gashi batada waya yanzu bare takira daddy ta narkemashi yasa akaita gakuma batason ta tambayi mummy, haka taita jira amma shiru Daga baya ma saita daure taje tasamu mummyn da maganar sai cemata tayi ba yanzu ba Abin ya 6ata mata rai sosai Hakan yasa takoma daki ta kulle taita kuka Sai bayan isha'i mummy ta aika agayamata ta shirya suwuce hospital din Tuni ta mance da zuciyar datake tayi saurin chanzawa tana addu'ar allah yasa su tararda ya farka Da ita da mummy dawata maid dinsu suka tafi wannan karon ma da abinci a basket A asibitin taga daddy Hakan yasa tawuce wajenshi da sauri ta Rungumeshi tana tura baki Dagota dadi yayi yajamata hanci yana tsokanarta yana kiranta cry cry baby ita kuma sai qara zunbura baki take Binsu mummy dasukayi gaba suma sukayi suka shiga dakin dasu kaka suke Saida su mummy suka gama gaisawa dasu kaka sannan itama zee ta gaidata cikin jin kunya kuma ba kunyar komai bace saina tasan tanamata kallon itace silar rashin lfyar jikanta Amsawa kaka da yanzu ta dan kwantar da hankalinta tayi tana tambayar ta ya jikinta, Amsawa tayi da dasauqi sannan itama ta tambayi lafiyar mai jiki itama ta amsa da dasauqi daga nan kowa yayi shiru Mummy ce ta gabatar musu da abinci, amsa sukayi suna godiya suka ajiye ko don anjima don basu dade dacin abincin da matar mallam Nasiru takoma gida tayi musuba Sosai mummy tasaki jiki dasu sukaita fira kamar dama sunsan juna, yadda mummy tasaki fuska tanata fara'a yasa suma suka saki jiki daita sunata hira harda kaka dake tofa nata akai akai Zee kau tun bayan gaisuwarnan bata qara cewa komai ba saima sadda kai datayi tana wasa da zoben hannunta tana sauraronsu Hankalinta gabadaya baya tareda su kawai dai tana wajen ne amma ko wuqa za'asa mata bazata iya recalling kalma daya a abinda suke cewa ba Hankalinta gabadaya na kan Deen, idan akwai abinda tafiso yanzu to sanyashi a ido ne Sun dan jima a Hakan sannan tadan dago taga haryanzu firarsu suke hankali kwanta Dan Hadiye yawun bakinta tayi sannan tayi gyarar murya wanda Hakan yasa duk suka kallota, sai kuma taji ta takura da kallon amma saita basar tace "zan dan je wajen daddy" tafada tana qirqirar wani busashen murmushi Da to saita dawo su baaba abu suka amsamata suna kallonta yayinda mummy batace komai ba sai kauda kai datayi Tashi tayi tana dan satar kallon mummy sannan tanufi hanyar fita ta fice Duk binta da kallo sukayi harta fice sannan baaba abu tayi fuska kalar tausayi tace "baiwar Allah, kai allah ka cigaba da karemu da zuri'armu wannan abu da me yayi kama? Yarinya nitsatsa amma anason wargazamata rayuwa, allah kacigaba dayimana katangar tsari da ire iren wadannan azzaluman bayin naka" Duk da amin aka amsa banda mummy da tadanyi murmushi kawai Wai nitsatsa, Yarinyar da shegen rawar kai yayima yawa wataqila garin Hakan taje ta tsokano ma kanta su don ita haryanzu bata yarda haka kawai zasu nemi wargazamata rayuwa ba Nan akalar hirar tasu takoma kansu, inda suketa addu'ar tonuwar asirin su master da kuma yin allah wadai dasu sumee dakuma fatan waraka wa Deen *ZEE* Ajiyar zuciya ta sauke bayan tafito tana dan juya manyan idanunta Wawaigawa tayi don ganin inda zata hango su daddyn amma bata gansu ba Har tayi hanyar office din Dr dinsu saikuma tafasa Dawowa tayi ta nufi recording room dasuka shiga dazun dasafe Saida tayi knocking sau hudu sannan aka bude kofar mutumin wata mata ta bayyana Dan murmushi matar tayimata tace "hi" Itama maida mata murmushin tayi tace "hy" "how may I help you miss?" inji matar tana kallonta Rasa abinda zatace tayi Hakan yasata fara kame2 Ganin Hakan yasata cewa tashigo ciki sai suyi maganar Shiga zee tayi tana wondering ina wancan mutumin yake na dazun? Saida ta zauna sannan matar tace "yes miss? How may I help you?" inji matar tana folding hannunta tana kallonta Taking deep breath tayi sannan tace "amm.. Dama sonake ayiman viewing wani dake kwance a room 12 ne please, patient ne amma anhana shiga ganinshi shine nakeso please kiyimin viewing dinshi" Shiru matar tayi tana kallonta na dan wani lokaci sannan tace "am sorry, amma ba'a zuwa ganin mutum anan, kiyi hqr kijira har abaku izinin shiga ku ganshi Hakan ma zaifi" Shiru zee tadanyi tana kallon zoben hannunta sannan tasake dagowa ga matar "please, kawai ganinshi zanyi koda flashing dinshi zakiyimin nadan ganshi ki kashe, I want to know how he is please" tafada pleadingly "idan kinason sanin yadda yake likitanshi zakije ki nema ba nan ba, am sorry but it's strictly against the law, da ana yin haka da kowa ma nan zaizo don ganin nashi, kiyi hqr please ki jira har lokacin da za'a baku izinin shiga ganinshi, am sorry" Kada kai zee tayi a sanyaye tana qoqarin maida hawayenta sannan ta miqe tsaye "thank you" tafada ta nufi kofa Binta da kallo matar tayi har Saida tadora hannu akan handle zata murda "wane ward yake?" zee ta tsinkayi muryar matar Juyowa zee tayi da sauri kamar dama jira take tace "12... Ward 12" Murmushi matar tayi tace "ok zo kiganshi na seconds biyar kiwuce kafin azo akamamu anan babu ruwana" tafada tana operating din mouse din hannunta Da sauri zee tadawo ta zauna tana murmushin jindadi dabatasan tanayiba Kunnomata matar tayi tayi mata zooming dinshi sannan ta kaucemata don tagani Tsayawa zee tayi tana kallonshi Kwance yake kamar dazu haryanzu abin oxygen a hancinshi Saidai yanzu babu qarin ruwa a hannunshi da alamu an cire "Don.. Allah ma, kidanyimin zooming face dinshi" tafada cikin sanyayar murya Murmushi matar tayi tayi yadda tace, nan take fuskar Deen yafito daro2 a screen din majigin Kafeshi tayi da idanu tanajin zuciyarta na kumbura don shauqi Dukda abin oxygen din ya kare kaso mai yawa na fuskar Hakan be hanata ganin yanda fuskar tayi fayau ba Idanunshi a lumshe sai lashes dinshi dasukayi zara zara suka hade dajuna sanadiyar lumshe idanun dayayi, ga girarenshi masu cika da baqi dasuka kusan hadewa Maida kallonta tayi akan ciwon dake akanshi wanda aka nannade da banda sannan akan tulin lallausan sumarshi dake tuje as usual Kafeshi da idanu tayi bako kyaftawa tanajin kamar zai bude idanu at any moment Batasan iya lokacin data dauka a haka ba sai jitayi an dafa kafadarta hakan yadawo da ita daga duniyar kallonshi Dariya matar tayi tace "haba madam? Daga ganin marar lafiya saikuma a bige da kuka?" Sai a sannan tasan ashe kuka takeyi Hanki din hannunta tasa tana tsane fuskarta tana murmushin jin kunya "to ai kiganshi yanzu, 5 seconds na neman zama 5 minutes, allah yabashi lfy insha allah very soon za'a barku kushiga wajenshi kiyita ganinshi babu mai takura maki" tafada tana Dariya Dan murmushin kunya tayi tana tashi "thank you very much" tafada tana murmushi "Don't mention.. Amm, nace dan uwanki ne?" tafada tana qumshe Dariya Kada kai kawai zee tayi sannan ta nufi hanyar fita tana mata sai anjima Cikin Dariya matar tace "to allah yaqara donqon zuminci, allah kuma yaqaro afuwa" Itadai zee fitowa tayi murmushi a fuskarta Tana fitowa daidai su mummy ma na fitowa da niyyar tafiya gida Hakan yasa suka wuce bayan itama zee din tayimasu kaka sallama suka shige mota harda daddy suka wuce gida *BAYAN KWANA UKU* Cikin kwanakin nan abubbuwa da dama sunfaru ciki harda nasarar damqe su master da akayi a gidan wani abokin huldar kayan mayensu inda wani dan leqen asiri yakawoma yan sandan rahoto sukuma basuyi wata wata ba suka yiwa wajen tsinke inda sukayi ramm da dukkansu aka kwashesu sai magarqama Ciki kuma harda sauqin da Deen yasamu dukda ba farfadowa yayi ba Amma an chanza mashi daki inda ana iya shiga aganoshi Saidai kwata2 ba'ason ayi hayaniya Tsakanin zee da kaka saina rasa wanda yafi farinciki da wannan cigaban dukda ita zee nata farincikin be bayyana ba kamar na kaka amma a badini tafi kaka murna da Hakan Kullum sai sunje asibitin Sau biyu, dasafe da kuma bayan isha'i Sosai su daddy ke hidimtamasu kaka wajen abin da yashafi lafiyar Deen don haryanzu ko sisin kaka beyi ciwon kai ba da sunan maganin Deen Hakan yasa kaka ke ganin girmansu sosai don ita kaka dama batada babban masoyin da yawuce mai nunawa dan jikallenta qauna A bangaren zee kau duk lokacin dasuka zo daga gaisuwa da tambayar mai jiki bata qara cewa komai sai kallon Deen da zata cigaba da yi Su kaka da mummy sunsha kamata ta kafeshi da ido dukda yadda take kallon a fakaice Izuwa yanzu babu wannan abin oxygen din a hancinshi Hakan yasa fuskar shi ke afili Saidai tayi fayau taqara haske lips dinshi kuma sunqara pink sosai Yau sunyi baqi yan dubiya sosai ciki harda yan makarantarsu dama mallamai, Cikin mallaman harda mr ibrahim Rasa inda zata sa kanta tayi don kunya lokacin da mr ibrahim ya yimata jaje da fatan Allah ya tsare gaba Haka dai ta amsa da amin batareda ta iya hada idanu da ko daya daga cikin su ba Haka akaita zuwa ganinshi, a yan kwanakin nan tasan Deen mutumin mutane ne don sai zuwa dubanshi ake takoina kuma duk wanda yazo da kalar yabon da zaimashi na kyawawan hallayenshi Hakan yasa taji ya qara burgeta akan nada kuma take kwadayin itama watarana tasamu mutane masu yaba hallayenta, wadanda zasu nuna damuwarsu sosai idan wani abu ya sameta Ahmad mai adaidaita ma yazo dashi da matarshi ganin din, Saidai lokacin dasukazo su zee basukai ga zuwa ba saida sukazo sannan aka gayamasu Zaune suke suna dan fira jefi jefi Kaka ce da baaba abu sai mummy da zee a dakin Can su ukun ke firarsu yayinda zee ke gefe tana yan danne dannenta a sabuwar wayar da daddy ya siyamata tanayi tana dagowa tana kallon Deen lokaci bayan lokaci Dagowa tasakeyi ta dan kalleshi saitaga kamar yatsun hannunshi sun dan motsa Qara dan waro idanunta tayi tana kallon hannun sannan ta maida kallon ga fuskarshi amma bataga yakuma motsin ba Bata Janye idanun ba akanshi ta cigaba da kallonshi babu ko blinking don idan idonta ba qarya sukayi mata ba tabbas taga yatsunshi sun motsa Qara girma idanunta sukayi ganin idanunshi sunfara motsi a runtsen dasuke Cigaba da kallonshi tayi idanu a ware bata ko kyaftawa don gani take idan ta kyaftasu zataga akasin abinda take gani yanzu Cigaba na motsi idanun sukayi da alama soyake ya budesu Can eyelids din suka fara rabawa idanun suka shiga budewa ahankali Biji2 yafara gani Hakan yasa yashiga kyafkyafta idanun Ahankali ganin nashi yafara clearing tun yana ganin abubbuwa blurring har ganin nashi yadawo clearly Be sauke idanunshi koina sai cikin nata large pure white eyes din... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:35 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *026* Cak komai nata ya tsaya ta kafeshi da idanu kamar yadda shima nashi ke kafe da ita Sotake ta tashi tayi ihun murna ta nufeshi ta kamo hannunshi tayi mashi magana amma duk ta kasa, ko kyafta idanu batasonyi don gani take data kyafta ta bude zataga idanunshi a rufe kamar kullum Mummy ce kema Zainab magana akan ta miqo ledar kusada ita amma shiru ko motsawa batayi ba "bakiji ba?" inji mummy tana kallonta bama ita kadai ba harda su kaka Still bata motsaba ko ta nuna alamun taji don bama lallai ne intaji dinba Ganin ta zaune ta kafe wuri guda da ido yasa suma bin inda take kallo da ido Atare duk suka miqe kowa bakinshi bude "Deen!!" Duk suka fada atare Kaka ce farkon qarasowa gabanshi tana riqo hannunshi cikin tsananin farinciki Sai a lokacin ya janye idanunshi da basu ida washewa ba daga kan zee ya maidasu kan kaka dake kuka da Dariya lokaci guda "kyakyawa na, katashi? Alhamdullilah! Alhamdullilah! Allah mun gode maka, allah mun gode maka" tafada tana Rungumeshi qamm Lumshe oily idanunshi dasuka dan dishe yayi ya bude yana qara narkewa a wuyan kaka Dago idanunshi yayi a hankali ya saukesu akan zee da yanzu take tsaye tana kallonshi itama idanun na kyallin hawayen dasuka taru aciki "wai bazaki tafi ki kira Dr din bane?" inji mummy ganin tayi tsaye taqi gaba taqi baya Magana mummy ya dawo da zee daga duniyar kallon Deen tayi saurin Juyawa ta nufi kofa Binta da kallo Deen dake rungume still ajikin kaka yayi kamar yau yafara ganinta Harta dora hannu a handle din kofar saikuma taqara juyowa ta kalleshi Lumshe idanu yayi ya qara budesu akanta wani slight murmushi wanda yayi mugun tsayawa aran zee ya su6ucemashi Saurin bude kofar tayi tafita ta rufo Saidai maimakon tayi gaba saita koma ta jingina da kofar ta Lumshe idanu wanda Hakan yaba hawayen dasuka taru a idanunta damar gangarowa Ahankali ta silale awajen tana dafa saitin zuciyarta datakeji tana kumbura da sacewa Hawaye sosai take wanda ita kanta batasan na meye ba yayinda murmushin Deen na yanzu yaqi 6acemata a idanu Rabashi kaka tayi da jikinta ta dago fuskarshi tana shafawa tana murmushi da hawaye a lokaci guda Shima mayar mata da martanin murmushin yayi yana Lumshe idanu tareda budewa Suma su mummy qarasowa sukayi cikin farinciki suna miqa godiya ga Allah (s.w.t) daya tasheshi "sannu son, ya jikin?" inji mummy tana kallonshi tana kuma qara hango zallar qaunar da kaka kemashi Dan kafeta da idanu yayi saikuma ya Lumshe idanu ya bude alamun da sauqi Itakau baaba abu cewa tayi "Allah mun godemaka, raggon maza an leqo lahira an dawo, to ya hanya?" tafada cikin sigar tsokana don dama haka takemashi Itama murmushi yadanyi mata sannan ya maida kallonshi kan kaka da haryanzu ta tisashi gaba tana kallo kamar tasamu t.v Murmushi yasake mata Hakan yasa takai hannunta a kumatun haggunshi tana shafawa, Lumshe idanu yayi ya sake budesu yana son dago hannu ya dora akan nata dake dafe da kumatunshi amma yakasa don kwata2 beda wani qarfi ajikinshi "kyakyawa na, nayi zaton tafiya zatayi ka barni, nayi zaton barina zakayi ni kadai a duniyar nan, da katafi ka barni da bansan yadda zan kuma cigaba da rayuwa babu kai ba, rayuwa batareda kai ba rayuwar kunci ce Hade da dawwamammiyar kewa" Girgiza mata kai yayi ahankali alamun ta daina kuka Hakan yasa taqara rungumeshi tanajin farinciki na huda zuciyarta takoina Share qwalla mummy da baaba abu sukayi na tausayinsu, mummy na qara jingina soyayyar dake tsakanin wannan kakar da jikan Jin shirun yafara yawa yasa mummy cewa "bari naje na dubo likitan narasa abinda yasa basu qarasoba Tundazu" Bata jira komai ba tanufi kofa Murda handle din tayi ta tura sai taji abu ya tokare kofar cikin mammaki taqara turawa taji har lokacin atokare Cikin mammaki tace "ikon allah" taqara turawa wannan karon da qarfi Firgigit zee ta dago daga hada kanta da gwiwa datayi Jin ana turo kofa tabayanta yasata saurin miqewa tana ja baya Gani tayi an bude kofar mummy ta leqo Wara idanunta zee tayi don sai yanzu ta tuna abinda ya fiddota Saurin yin u-turn tayi ta nufi hanyar dazata sadata da office din Dr din Binta da kallo mummy tayi baki sake sannan ta ida fitowa itama ta nufi hanyar office din Dr din don bazata qara jiran gawon shanu ba Tana shawo kwanar dazata sadata da office din Dr din sukayi kici6us da Drn da zee Batabi takan zee ba tace ma Drn "yauwa Dr, yafarka yanzu yanzunnan" "ok muje mugani" inji Drn Nan tajuya suka koma ta hanyar dasuka taho zee a bayansu Shigowarsu yasasu duk dagowa suna kallonsu Qarasowa Drn yayi ciki fuska a washe "masha allah, alhamdullilah! You're back" yafada yana dan dafa goshinshi Murmushi kawai Deen yayi kamar yadda yake tun lokacin daya tashi Ciro abin wuyanshi Dr din yayi yasa a kunne sannan ya dora a qirjinshi yana feeling heartbeat dinshi Duk tsit akayi a dakin ana kallonsu kowa fuska bayyane da farinciki Saida likitan yagama duka gwaje gwajenshi sannan juyo gasu kaka, kaka bakinnan kamar gonar auduga "to kaka ina tayamu murna, yatashi kuma alhamdullilah jiki da sauqi sosai sai dan abinda ba'a rasaba, yanzu ayimashi brush asamar mashi abu mai dan ruwa ruwa da zafi zafi yasama cikinshi Ayanzu beda qwarin jiki sai ahankali qarfinshi zai dawo kuma don Allah banda hayaniya, please" Duk amsa mashi sukayi da insha allah Yan rubuce rubuce yayi a memo din hannunshi sannan yace "abashi wani abin yasa a cikinshi kafin indawo mashi da maggungunan dazai dinga sha, Allah yaqaro afuwa" Duk da amin suka sake amsawa sannan yafita Waya mummy ta dauka bayan fitar Dr itama tafita don kiran daddy Ita kuma kaka ta shige toilet don tarar ruwa itakuma baaba abu tafita sai dakin ya rage daga zee dai Deen Kafe juna da ido sukayi expressionless Ahankali Deen ya dago hannunshi ya miqomata yana dan murmushi Hakan yaqara tsumata tayi saurin qarasawa wajenshi ta kama hannun ta damke gaam takifa fuskarta akai tana shesheka Binta kawai yake da kallo not saying anything Saida tayi mai isarta sannan ta dago da watery eyes dinta ta kalleshi taga shima ita yake kallo "am so sorry.. Am sorry for everything, nina jawo komai, nakusan sanadin rayuwarka, daka tafi da bansan yadda zanyiba don bazan ta6a yafewa kaina ba, am sorry for causing you pain upon pain, forgive me.. Please" ta qarashe tana lumshe idanu hawayenta na gangarowa Dora dayan hannun yayi akan nasu dake wuri guda sannan ya girgiza mata kai yana murmushi saikuma ya bude baki kamar zaiyi magana amma taqi fitowa Ganin Hakan yasata cewa "menene? Baka iya magana ne?" Murmushi yayi ganin yadda take tambayar cikin damuwa saikuma ya nunamata cikinshi yana yamutsa fuska Ganin Hakan yasata saurin tashi tana raba hannunsu tanufi wani flask dake kan wata locker wanda dama ana ajiyeta ne da ruwa ciki incase ya farfado don dama Dr yariga ya fadamasu zai iya farfadowa a kowanne lokaci Tana cikin fiddo cups din kaka tafito hannunta riqeda bowl da dogon kofi dake dauke da ruwa Daidai nan baaba abu tadawo ita da mummy dasuka Hade a waje Maclean din da baaba tasiyo ta matsa a sabon brush data siyo ta miqama kaka da zatayi mashi brush Daukan cups din zee tayi taje ta daurayo sannan ta dawo ta jawo flask din da kayan shayin dake cikin leda tashiga hadawa Sosai tasa ginger powder aciki tayimashi hadin mai citta Deen da kaka kema brush sai 6ata fuska yayi kaka nata qara lalla6ashi har aka samu aka gama brush din Daidai nan zee tagama hada tea din taba kaka Cikin jindadi tashiga sama zee albarka sannan tazo tafara ba Deen din shayin Ana haka daddy yashigo tareda Dr Tashi zee tayi tanufi daddy da sauri ta fada jikinshi cikin tsananin farinciki Shima daddy riqeta yayi fuskarshi awashe suka ida qarasowa ciki Deen tunda zee ta ruga wajen daddy yake binsu da kallo harsuka qaraso wajenshi, yama bar amsar shayin hankalin yakoma can "masha allah, sannu kaji?" inji daddy cikin kulawa Kada mashi kai Deen yayi yana dan murmushi sannan ya kalli zee da itama murmushi yaqi barin face dinta "Allah ya sauwaqe ya qara lafiya, allah yakuma kiyaye gaba" inji daddyn Duk da amin suka amsa banda Deen din dayayi murmushi kawai "Gaskiya kayi mana hallacin dabazamu iya sakamaka da komai ba, ba don kai ba da yanzu wani zancen ake, babu abinda zamuce illah allah yasaka da alhairinsa" inji mummy tana murmushi "hakane kam, babu abinda zamuce face allah ya sakamaka da alhairi, ka ceci rayuwarmu don rayuwar Zainab tamuce idan muka rasata komai na iya faruwa, words can't express how gratefull we are kuma insha allah saimun tabbatar an hukunta wadannan shaidanun daidai da abinda suka aikata don yanzu haka magana takai kotu on monday za'a fara zama" inji daddy "Allah yakaimu, ai abinda yakamata kenan dama, yaran yanzu ka haifesu ne baka haifi halinsu ba, kuduba qannanun yara irin wadannan sun iya munafurci ni Zainabu, kuma wai qawayenta ne na qut da qut, duniya ina zaki damu? Idan wadanda ka yarda dasu suna maka zagon qasa ta bayan fage dawa zaka yarda ni Abu?" inji baaba Abu tana riqe ha6a "shiyasa ai qawayen basuda wata amfani, ni dama basuyi minba tunda nafara ganinsu nakuma yimata magana amma taqi rabuwa dasu ai ga irin abubbuwan danake guje miki nan kinfara gani" inji mummy tana eyeing dinta "wlh kam, qawayen yanzu ko bam (bomb)? Ke kina nan kin saki jiki dasu kina zama dasu da zuciya daya amma su basuda maqiyi daya wuce ke kuma basuda burin daya wuce suka bayan ki, ai da akayi abota ba wannan zamanin ba" inji kaka tana ajiye kofin shayin ganin besha "To allah ya kyauta, yaranma naji ance cocaine dealers ne suna safarar miyyagun qwayoyi da hodar iblis yanzu haka da akaje gidan da aka kamasu akayi bincike saigasu nan birjik anata zaqulosu yanzu kunga abin yaqara tsawo ga wannan ga wancan" inji daddy Riqe ha6a baaba abu tayi tace "danqari! Ashe yan kwaya ne? Ca6 aikau sun aikata tunda dasun shawu suka bugu tafara gayamasu qarya kome yazo kansu yi zasuyi" "To allah dai yashiryasu idan masu shiryuwa ne" inji kaka "fatan kenan" inji mummy tana Kada kai Dr ne yaqara duba Deen sannan yabasu maggungunan shi bayan ya gayamasu yadda qa'idar shan yake Da zasu tafi zee jitayi kamar karta tafi kamar tayita zama anan Don dole tabisu daddy tana waigen Deen dashima yake kallonta yanajin kamar karta tafi Ranar nan zee ta dade batayi barci ba, duk motsin da zatayi saiya fado mata arai duk kuma lokacin daya fadomata a rai saita tsinci kanta da murmusawa Barci 6arawo ne ya sadado batareda ta farga ba ya saceta A bangaren Deen kuwa saida ya rama sallolin da ake binshi cikin daren nan sannan yasha maggungunanshi wanda Dakyar aka samu ya hadiyesu don dama shi kwata2 beson magani duk lokacin dazaisha magani sai kaka tata fama dashi don daya saka maganin abaki zaita kakari kamar zaiyi amai Dakyar ake samu ya hadiye Yana gama sha ba dadewa barci ya daukeshi don dama cikin maggungunan harda na barci Su kaka kau ranar sun dade kafin suyi barci, firarsu kawai sukesha cike da annushuwa kallo daya zaka masu kasan yau rana ta musanmman ce agaresu don farincikin dasuke aciki a bayyane yake a fuskokinsu Suma sai can cikin dare barcin ya sacesu suka 6ingire *WASHEGARI* Tunda ta tashi bata komaba tana gama sallar asuba ta sauko tashige kitchen Maid biyu ta iske cikin kitchen din suna hidimar dora breakfast Sunyi mammakin ganinta by this time kuma a kitchen, shanye mammakinsu sukayi suka shiga gaidata Amsawa tayi tana nufar abubbuwan dasuka dora tana bubbudewa Saida tagama sannan ta rurrufe ta juyo garesu "Akwai cow leg?" ta tambayi daya daga Maid din "eh madam Akwai a Deep freezer, shi kikeson ci ne?" inji maid din cikin ladabi "ciromin shi farfesu zanyi" tafada tana wucewa wajen tukwane ta dauki wata yar madaidaiciya Yin yadda tace maid din tayi tana mammakin zee a zuciyarta don da wuya ka ganta kitchen da sunan girki sai idan mummy ta tilastata bakuma wai don bata iyaba ne kawai dai qiwuya ce da son jiki irin nata na yar hutu Cikin qanqanin lokaci tafara hada farfesun qafar sa dinta wanda yaji citta sosai da kayan qamshi kamshi Kan kace me? Har kitchen din dama gidan baki daya ya garame da qamshin girkinta Koda tagama yar warmer tasamu tajuye aciki ta fita daga kitchen din tabar maids din da gulma ke cinsu a zuciya Koda tashiga dakinta ajiyewa tayi kan mirror tayi tafada bathroom don freshen up Kamar kullum yau ma qarfe 10 suka bar gidan don zuwa hospital din Duk sammakon zee da zumudin dole saida tajira har lokacin da mummy tafito Haka suka fito zuwa mota tanata cin magani don taso taje dawuri ya kasance farfesun da tayi mashi zai fara sha amma yanzu ai tasan ya riga ya karya Haka tashiga front seat ta zauna ta dora yar warmer dinta a cinya tana cigaba da kumburi while itakuma mummy tashige baya ta zauna batama san wainar da zee ke toyawa ba *HOSPITAL* Mutane sosai suka tadda a dakin wadanda duk mazane yan unguwarsu Da sallama suka shigo dakin amma kasancewar mutanen dakin nada yawa shiyasa ba duka suka lura da shigowarsu ba Zaune taganshi bayanshi jingine da pillow hannunshi riqe da dan mug din shayi yana kur6a ahankali Fuskarshi dauke da wannan murmushin mai karamashi kyau yana sauraron wani daga cikin matasan dasuka kewayeshi yana bashi labarin irin wahalar dasuka sha wajen nemanshi aranar da abin yafaru Dauke idanunta tayi daga kanshi ta qarasa wajensu kaka dake masu sannu da zuwa Wuri tasamu ta zauna tana gaidasu sannan ta tambayi lafiyar mai jiki Duk amsa gaisuwarta sukayi kaka na tambayarta ya gajiyar jiya Murmushi kawai tayi batace komai ba Jin sun cigaba da magana dasu mummy yasa ta daga kai da niyyar satar kallonshi Caraff suka hada ido dashi don tunda kunnuwanshi suka jiyomashi muryarta lokacin dasuke gaisawa dasu kaka ya maido hankalinshi kanta Ganin ya tsareta da ido expressionless yasata dan yimashi murmushi Kamar jira yake sai shima murmushin ya su6uce mashi Dauke kai tayi daga gareshi fuskarta still da murmushi ta maida kan kaka da aka dage sai labari ake badawa baki washe kamar ba ita bace so moody a yan kwanakinnan ba Bata qara kallon sashin Deen ba Amma tanajin idanun shi akanta Hakan kesa murmushi ke su6uce mata akai2 tana kauda kanta duk lokacin da ya su6uce mata cikin basarwa Ba'a jimaba mutanen dakin suka fara ragewa don dama duk mazane yan dubiyan inda yawancinsu daga nan wajajen sana'arsu suka nufa Matan dake dakin daga kaka sai matar mallam Nasiru sai mummy sai zee, baaba Abu ankoma gida dazu sai anjima zata dawo da kingin matan unguwa masu zuwa dubiya Saida duk suka fice sannan ta dago ta kalli saitinshi Hada ido suka qara yi don dama ita yake kallo Harara ta gallamashi tana qara kauda kai Dan wara idanunshi dasuka qara dan washewa yayi yana kallonta saikuma ya 6ata fuska Kaka ce ta dago taganshi ahaka "Ohni ma'u, wai haryanzu baka shanye shayin ba kasha maganin koko sai lokacin shan yawuce sannan?" Maida kallonshi yayi akan kakan sai yaqara kumbura fuska Dariya mummy tayi tace "besha maganin bane?" "hmm wannan me shegen tsoron maganin? Tundazu nake mashi magana yawani fake da shan shayi don inmance, to kar nake kallonka ka gama kwalailaitar saika shashi" Dariya duk sukayi zee kuma ta dago ta kalleshi tana murmushi taga sai yamutsa fuska yake "ko bejin dadin shayin? Gashi naga Tundazu yake hannunshi wataqila ma ya huce" inji mummy "ai har wuce hucewa ma yana iyawa don tun kafin kusaran zaku zo aka bashi yayi yasha abashi maganin amma yaita jujjuyashi a hannu, da anyi magana saiya kai baki kamar shan gaske yakeyi" inji matar mallam Nasiru tana gallamashi hararar wasa "A'a kubarshi, wataqila ba shayin yakesoba, bari mugani azubamashi kunun gyada ko zai iya sha kinsan idan mutum yatashi daga rashin lafiya bakin sai ahankali sai anringayi ana daurewa Caraff zee tace "mummy gama wani farfesu nan, sai inga kamar zaifi sonshi, ko?" tafada tana maida akalar tambayar ga Deen Shiru Deen din yadanyi sannan ya Kada kai alamun eh "to? To ai saiki zubamashi yasha yayi yasha maganin tun kafin lokacin shan yawuce inba sokake muyimaka duraba" inji matar mallam Nasiru tana Dariya Qara hade cikakkun girarshi yayi yana kauda kai Tashi zee tayi tana murmushi ta Fiddo wani dan bowl dake cikin yar ledar warmer din sannan ta Fiddo warmer din ta bude ta zuba acikin bowl din ta miqama kaka "A'a kai mashi tunda yanzu yana iya komai da hannunshi sai yasha, wazai biyewa shiriritar tsantsaninshi?" inji kaka Tashi zee tayi tawuce wajen Deen taja kujera ta zauna sannan tabashi Saida ya harareta sannan ya amsa ahankali yana bin farfesun ciki da kallo "kasha ko nakira wancan matar tayimaka dura yanzu" tafada qasa qasa yadda shikadai zaiji Dagowa yayi daga kallon farfesun ya gallamata harara ta daga kafadu tana murmushi Daukar spoon din yayi ya diba yakai bakinshi Lumshe idanunshi yayi kunnenshi daya na motsi don dadi Bude idanun yayi ya kalleta yaga itama shi take kallo, daga mashi gira daya tayi alamun 'ya?' Murmushi kawai yayi ya kuma diban farfesun yana hadawa da naman wanda aka yankasu qananu qananu daidai ci yakai baki yana tauna ahankali Acan bangaren su kaka mummy ce tace "ya naga kamar baya magana? Naga Tundazu beyi magana ba" "hmm ai haka yake idan ciwon ya tashi, kai ko sanyi yadan bugeshi yanzu zakiji muryarshi ta chanza ta shaqe bare mai gabadaya, wancan atak (attack) din ma saida yayi kwana uku muryarshi bata fita lokacin a makaranta ma ne yasamu atak din wai wata shegiyar yarinya ta watsamashi abu mai sanyi ajiki, wlh bakiga yadda ya burkuce ba. Lokacin ina gida nagama dan wanki na akashigo aka cemin ga Kamal can asibiti, hankali tashe naje na taddashi a wani yanayi numfashi ma kanshi Dakyar yake ja, kai allah dai yakawomana qarshen wannan ciwon don wlh yana wahalar dashi, yanzu sai ahankali ahankali muryar zata dawo" inji kaka Tunda kaka tafara magana murmushin fuskar zee yafara daukewa harya dauke dab Bata qara fuskantar kingin magangganunsu ba saima kalmar _wai wata shegiyar yarinya ta watsamashi abu mai sanyi_ dayaita eoching a kunnenta Wacece yarinyar? _*ni?*_ tabaiwa kanta amsa Citayi zuciyarta ta quntata Bawai don taji haushin kalaman kaka ba don Gaskiya tafada, the bitter truth Kalaman kaka sun tunasar daita cewa ta ta6a kwantar da Deen gadon jinya akan dalilin da haryanzu idan ta tuna saita ji kunya Yamata alhairi ita kuma ta sakamashi da sharri, ta sakamashi da kwanciya jinya Halau kuma taqara da6awa, taqara kwantar dashi, ta tadomashi ciwonshi tadowar datafi wancan Halau a dalilin taimakonta, is she that wicked? Deen da tun lokacin da yanayin fuskarta ya chanza ya kafeta da ido babu ko kyaftawa Yasan abinda takeji, yasan abinda take tunani shima duk sai yaji ba dadi Ahankali yakai hannunshi ya dora akan nata dake kan hannun kujerar datake akai Bata dagoba kamar yadda yakeso kuma bata motsaba Dan damqar hannun yayi yana son yayi magana amma yakasa Wani abu taji ya tsirgamata ajiki Hakan yasa tayi saurin zame hannunta daga nashi ta miqe tsaye Wucewa tayi ta nufi kofa da sauri zata fita taji mummy na tambayarta ina zata Daga mata wayar hannunta kawai tayi alamun zata amsa waya ta maida wayar ta kara a kunne tafice Binta da kallo Deen yayi harta fice Maida kallonshi yayi kan farfesun gabanshi cikin wani yanayi, shiru yayi yana kallon bowl din kamar yana ganin wani abu aciki saikuma yadanyi slight murmushi ya sake daukan spoon din ya cigaba dasha Yasha sosai sannan ya ajiye, Ganin Hakan yasa kaka tasowa da ledar magani a hannunta tana wani cin magani don ma karya kawomata wasa Kamar yadda yasaba yanzu ma Dakyar ya iya Hadiye maggungunan sai wani kakari yake Komawa yayi ya kwanta yana maida numfashin shan maganin dayayi yanajin matar mallam Nasiru namashi tsiya Maida idanu yayi ya rufe Saidai ba barci ba yake Shiru zee bata dawoba tun mummy na jiran dawowarta don su tafi harta Fiddo waya ta kirata Basu dade da gama wayarba ta dawo dakin Bude idanu Deen yayi jin ta dawo ya cigaba da Binta da kallo Saidai ko kadan taqi yarda su hada ido bama dashi kadai ba da duk yan dakin Tashi mummy tayi tayimasu sallama akan sai anjima insha allah sannan taqara yima Deen fatan warwarewa Daukan basket din abincin jiya daddadare dasuka kawo zee tayi itama tayimasu sallama tafito batareda ta yarda ta kalli side din Deen ba dukda kau yadda takejin idanunshi akanta. Maida idanun Deen yayi ya lumshe bayan fitarsu yana jin ba dadi sosai, ahaka har wani barcin yasake daukanshi... ✍️ Juma'at mubaraq in advance✨? Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:35 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *027* Wunin ranar haka ta qarasheshi rai a jagule Kwata2 batada walwala aranar tabi ta tsagwami kanta ga sense of guiltiness datake ji duk lokacin da ta tuna Da daddare da mummy ta aiko akan tafito sutafi dojewa tayi ta hanyar kawo qabali da ba'adi Hakan yasa mummy tayi tafiyarta ita kadai A bangaren su Deen kau haka sukayi Wunin yau da shige da ficen yan dubiya Mutane sunzo sosai most especially yan unguwarsu Duk wanda zaka gani da farinciki a fuskarshi yana yimasu barka da arziqi Kaka yau baki be hutaba, wuni tayi 6a66atu saboda yan dubiya Saidai Hakan sam be dameta ba don sosai taji dadin yadda aka damu da dan kyakyawanta ana nuna mashi kulawa don har riqe wadanda sukazo takeyi a kwanya tana lissafin wadanda basuzo ba kuma tana zuba ido taga ko zasu zo don Gaskiya wanda bezo yaga dan jikallenta ba yayi mata barka ba to zata qullaceshi akan Hakan don aganinta abin azo aimata barka ne dan jikanta ya leqo lahira ya dawo A bangaren Deen kau yau yini yayi murmushi don haryanzu muryar shi sai a slow Fara'ar nan tashi mai qaramashi kyau yawuni daita, yana tarbar kowanne daita Saidai a qasan zuciyarshi tunaninta ne maqale a wajen Shi besan metayi ba, fushi tayi koko jin badadi akan abinda kaka tace Yasan dole taji ba dadi Amma ai Gaskiya kaka tafadi kuma Batasan itace ba da bazata fadi agabanta ba, kodayake beda tabbacin idan tasan itace zata cigaba da washemata 36 dinta don duk wanda ya ta6ashi batayin wata2 wajen jefashi blacklist dinta Tunawa yayi da yadda yasamu Dakyar yashawo kanta wajen haqura da zancen wancan karon don ita da a dole saita bishi makarantar taga wace hegiyar gorar take niyyar sheqemata jika, Dakyar yasamu ta haqura da Hakan bayan ya laftamata qaryar shi bema iya ganeta don dama karo sukayi abin hannunta mai sanyi ya zubarmashi ajiki Hakan yasa ta haqura ba don taso ba takuma gargadeshi akan ya dinga kulawa Haka suka cinye Wunin yanata looking forward to dare don yaganta Saidai me? Sai gani yayi mummy ce kawai tazo Yanajin kaka na tambayarta ina aminiyar tata don haka take cemata wani sa'in kasancewar takwarar baaba Abu ce Mummy ta amsa da yau batajin dadi ne shiyasa batazo ba Nuna alhini kaka tayi takuma yimata fatan samun sauqi tana cewa ai tanama qoqari, wannan zirga zirgan ita kanta tana iya jawo wani abin gwara ta huta Sosai ran Deen yaqara jagulewa, sai duk zumudinshi na ganinta yakoma ciki Hakan na tabbatar da dagaske fushin tayi, to amma fushin me? Shi bega abin fushi anan ba Har lokacin tafiyar mummy yayi ta tafi ranshi a jagule yake. Yauma saida kaka ta tilasta mashi maganin yasha Dakyar sannan yakoma ya kwanta ba don yana jin barcin ba Ya dade idanunshi biyu kafin can barcin ya sadado ya daukeshi A bangaren zee kau sai bayan tafiyar mummy taji kuma tana danasanin rashin Binta Haka kawai taji babu abinda take son gani kamar shi Haka taita daurewa tayi wanka ta kwanta da niyyar yin barci amma takasa Idanunta biyu lokacin da mummy tadawo don shigowar motarsu a kunnenta taji Tashi tayi daga kwancen datake Tundazu ta leqa ta window tana hangen mummy data fito tayo gaba bala na biye daita da basket din abincin safe da suka kai Sakin labulen tayi bayan shigewarsu ta dawo kan gadon ta zauna tana jingina da jikin gadon Haka kawai takejin haushin rashin zuwan datayi don jitake ajikinta kamar tayi missing din wani abu Itama ta dade tana karatun jaki sannan itama barci ya sadado ya dauketa *WASHEGARI* Yau Deen ya tashi da qwarin jiki sosai don da kanshi ma yashiga toilet din ward din yayi freshening up Sosai farinciki ya kama kaka na cigaban da akasamu don har magana yana dan yi dukda muryar ba fita take sosai ba Yau ma yan dubiyan da basu samu zuwa jiya ba sukaita zuwa Tun Deen na baza ido don ganin ta inda su zee zasu 6illo har yakai da tambayar kaka ganin har sha biyun rana tayi shiru Dariya kaka tayi tace ai dama bada wuri suke zuwa ba ranar juma'a sai nan da bayan antaso sallar juma'a zuwa la'asar zasu zo Kada kai kawai yayi yayi shiru yana jin komai bemashi dadi *4:30pm* Zaune yake kan gadonshi ya zuro qaffafu qasa hannunshi riqe da plate din faten doya yana diba da cokalin hannunshi yana ci cikin sanyinshi Agefe kuma kaka ce da wasu mata zazzaune ana maida yadda akayi Knocking din kofar d'a kayi ya katse firarsu kaka Murda kofar akayi aka shigo da sallama Dakatar da spoon din abincin da yayi niyyar kaiwa baki yayi jin muryoyin da yayi Dagowa yayi ya kallo kofar sai idanunshi suka sauka ana zee dake bayan mummy riqe da basket din abinci Ga mammakin zee sai taga ya kauda kai ya cigaba da cin abincinshi Sai jitayi wani abu marar dadi ya tsirgamata a zuciya, ba haka tayi tsanmmani daga gareshi, tasaba da kallonshi ta kuma sanshi da kallo don rabin communicating dinshi da idanu yakeyi saikuma murmushi Yadda taji tana missing dinshi dinnan tayi tunanin yafita, tayi tunanin idan yaganta zai kafeta da idanu kamar yadda yasaba babu ko kyaftawa "Aminiya, jiki yayi sauqi kenan?" inji kaka Murmushi tadanyi tana ida qarasowa wajensu "aikaudai kaka, ina yini? Ina yininku?" tafada tana kallon kingin matan dakin bayan ta gaida kaka Duk amsawa sukayi da lafiya lau kaka na dorawa da "ya jikin kuma? Mamanki tace bakiji dadi ba" Murmushi tayi cikin jin kunya, ta rasa dalilin dayasa tun farkon haduwarsu da kaka taji tana jin kunyarta "alhamdullilah kaka, ya mai jiki?" tafada tana dan satan kallon Deen daketa aika abincinshi kamar ma besan abinda akeyi ba "kai ai jiki alhamdullilah, jiki sai qara kyau yake don yau dakanshi yaje yayi alwala yakumayi sallar asuba atsaye gakuma magana anfara kinga kau ai ana samun sauqi" Jin kaka tace yana magana yasa ta dago ta kalleshi shima daidai ya kallota Suna hade ido yaqara kauda kai yana hade gira "kai masha allah! Haka akeso ai allah yaqaro sauqi, naji dadi sosai wlh" inji mummy cikin farinciki Itama zee kauda kai tayi daga kanshi ta kalli kaka da murmushi a fuskarta tace "masha allah, Allah yaqara sauqi" Kaka da duk dadi ya isheta ganin yadda suma sukayi farinciki da Hakan tace "amin amin, ai dole mu godewa allah da ni'imarsa dayaimana, da haka da haka zakuga ya warke tass kamar beyi ciwoba" "to allah ya amince ai muma fatan mu kenan, allah yaqaro afuwa" inji mummy Duk amsawa mutanen dakin sukayi da amin Sai a sannan kaka ta dago ta kalli Deen daketa cin abincinshi hankali kwance "kyakyawa na, bakaga su Zainabu sunzo ba? Kaida Tundazu ka dameni da yaushe zasu zo kuma yanzu kayi kamar bakasan sunzo ba" Dago kai yayi yana dan kumburi "O'O! Ni ban tambayeki itaba mummy na tambaya" yafada cikin muryarshi dabata fita sosai Duk Dariya mutanen dakin sukayi kaka tace "ikon allah, yo da ita da mummyn ba duk daya bane? Nima ai dama ba ita nace ba, su nace" Kauda kai yayi yana qara hade gira sannan ya kalli mummy dake kallonshi tana murmushi yace "mummy ina wuni?" Cikin fara'a tace "lfy qalau son, ya jikin? Jiki yayi sauqi ko?" Murmushin nan nashi dake lo6ar da tsakiyar gemunshi yayi yace "eh mummy, alhamdullilah" "to allah yaqaro sauqi, ana dai shan magani ko?" tafada cikin sigar tsokana 6ata fuska yadanyi jin an ambaci maqiyinshi Hakan yasa duk mutanen dakin suka sa Dariya banda zee dake murmushi Tundazu "wannan din? Ai yau ma saida muku sha fama, wai mutum yasan fa maganin amfanin kanshi ne amma yaita wulaqanci, wlh da don tashi ne da Saidai ya dawwama ahakan besha" Daya daga cikin matan dakin tace "haba kai kuwa? Kamar ba namiji ba? Ai mata aka sani da tsoron magani da allura" "hmm to kindai gani, gwara gwara ma allurar bejin tsoronta amma magani? Dama an ambaceshi zakiga ya 6ata rai irin an ambaci maqiyinshi dinnan, don dai ma ni jar wuyace duk abinshi haka zan tusashi gaba saiya shanyesu, yo to idan na kyaleshi haka za'a tafi bazai shaba, kuma ina akaga sauqi ba'a shan magani, in don ta shine haka zamu dawwama a asibitin bayada asara" inji kaka Duk Dariya suka sakeyi wannan karon harda zee datayi chuckling tana dan rufe baki tana kallon yadda Deen keta cika yana batsewa "A'a yanada asara tunda ai jikinshi ne zai gayamashi" inji wata mata cikin matan dakin "ba sai yasan ciwon jikinshi ba din? Daya sani ai bazai kawo wasa kwata2 akan harkar samun lafiyarshi, ni kuma fa? Allah kadai yasan cinikin da ya wuce ni cikin yan kwanakinnan" ta qarashe tana buga tagumi cikin jimami Dariya dakin ya sake dauka "aikuwa kamar kinsan kullum sai anta zirga2 gidanki dasafe, duk mun saba dake kwata2 bama jin dadin saye wani Wurin" inji dayan matar "yo to nima ai ba dadin ba nakeji, ina dadi a zama waje guda ba shige da ficen 'yan aninnai? Amma ahakan ja'irin ke neman qara zaunar damu" tafada tana hararar Deen dake kumburi Tundazu "A'a kaka, yafa isheku haka, yaya zaku tisa d'ana agaba kuna mashi tsiya? Da kanshi zaiji ko surutunku? Kedai kawai kice rashin shige da ficen yan aninnan naki ne damuwarki bawai rashin shan maganin ba kuma ai Son jarumi ne tunda gashi cikin kwana biyu sauqi yafara samuwa sosai don haka abar takuramana hakanan" inji mummy cikin sigar wasa Wani dadi Deen yaji Hakan yasashi murmusawa ya kalli kaka yayi mata gwalo Hakan yasa duk aka qara kecewa da Dariya Cigaba dayimashi tsiya kaka tayi mummy na kareshi Wannan dramar yasa duk damuwarsu ta yaye sunata Dariya Dagowa Deen yayi ya kalli zee daketa Dariyar dramar su kaka Samun kanshi yayi da kasa daina kallonta don sosai Dariyar ta dace da fuskarta Sai jiyayi shima farinciki ya mamaye zuciyarshi ya shiga murmushin da besan yanayi ba idanunshi still kanta Kamar ance ta kalloshi saikau suka hada ido Tsuke fuska yayi ya kauda kai irin na fushin nan Murmushi tayi kawai ta cije lower lip dinta tana cigaba da kallonshi Sake juyowa yayi da niyyar satar kallonta suka sake hada ido Harararta yayi Hakan yasa zee dan waro idanu, ta nuna kanta alamun da ita yake? Kada mata kai yayi yana sake Harararta, sosai hararar tashi tabata Dariya amma saita danne ta kauda kai tana 6ata fuska tana ta6e baki kamar mai shirin kuka Sake juyowa tayi ta kalleshi still fuskar a kwa6e sai taga shima ita yake kallo Ganin ta kalloshi yasashi qara hade gira ya kauda kai yana satar kallonta da wutsiyar ido Qara ta6e baki tayi tana kallonshi ☹️ Qara juyowa yayi ya kalleta sai gani yayi ta dagomashi yatsarta ta qarshe 🤙🏻 alamun su shirya Dan kauda kai yayi yana Rungume hannuwa a qirji yana fuming😠 Qara daga mashi yatsar tayi tana qara kwa6e fuska Dan maqe kafada yayi yana qara Rungume hannuwa a qirji Dariya yake bata sosai amma batasonyi Hakan yasa take dannewa, abin mammaki sai jitayi kamar sunawa juna magana da zuciya Idan yana body language dinshi saitaji kamar tana jin muryarshi a zuciyarta Sauke idanu tayi qasa tayi kalar tausayi 😔 Murmushi yadanyi yana kallonta yana jiran ta dago Kamar ta sani saita dago tadan kalleshi Dan huro hanci yayi sannan shima ya daga yatsarshi ta qarshe alamun 'to mu shirya' Harararshi tayi tareda murguda mashi baki ta kauda kai acikin zuciyarta tana cewa _it's my turn nima , zakaga jan aji_ Dan wara idanu yayi ganin murguden datayi mashi saikuma yakai hannunshi yana dan yamutsa sumarshi Tana jin idanunshi akanta amma taqi kallonshi tayi kamar su kaka take sauraro saida ta wajigashi sannan ta dago ta kalleshi Kamar kau jira yake yayi saurin dago yatsarshi yana marairaice fuska Duk yadda taso danne dariyarta saida ta murmusa Hakan yasa shima murmusawa yana qara dago yatsar Saida tadan harareshi sannan tashiga dago yatsar nata kamar zatayi kamar kuma zata chanza shawara Hakan yasashi kafeta da idanu ba kyaftawa Yamutsa fuska tayi ta kalleshi tadan turo baki sannan ta dago mashi Cikin jindadi yaqara dago nashi sukayi kamar sun qulla Deen na raba tsakiya Saikuma suka bawa kansu Dariya zee tashiga qumshe tata yayinda Deen yasaki murmushi mai sauti wanda yasa su kaka juyowa suna kallonshi Saurin maida hankalinshi yayi ga abincin gaban shi da sai yanzu ya tuna dashi yashiga ci batareda murmushin yabar fuskarshi ba Haka suka qare zamansu yayinda su kaka ke firarsu acan gefe kuma zee da Deen ke nasu firar ta kurame wanda idan ba sa ido kayi ba baka ta6a ganewa, fuskarsu sai tashin murmushi suke Ahaka har lokacin komawansu gida yayi Ba don sun so ba suka rabu dukda zee bata nuna a fuska ba kamar shi Saidai acan qasan zuciyarta jitake kamar su dawwama ahakan Haka sukayi sallama dasu suka fito Har suka kawo gida akwai kingin murmushi a fuskarta dakuma ta tuna wani abin saita rufe bakinta tana qumshe Dariya Haka ta qarashe wannan yinin ashiririce ga yawan murmushin da takeyi every now and then Shima Deen Hakan take a bangarenshi, kallo daya zaka mashi kasan yau he's very lively don fara'ar yau tasha banban data kullum, annurin dake fita a fuskarshi yau na dabanne Saturday and sunday sunzo sun wuce lfy, Deen jiki sai qara kyau yake don masha allah yanzu sosai yake recovering speedly A bangaren alaqarsu da zee kuwa sai abinda yaci gaba Sosai suke jin dadin kasancewa tare don har aqage suke suga juna Da lokacin Zuwansu yayi haka zakaga yana daga kai yana duban agogon dakin akai2, hankalinshi be kwanciya sai yaga shigowarsu Itama a 6angarenta dataga lokaci yakusa zataita zumudi, bata qaunar abinda zai 6atamasu lokaci ko yaya ne Saidai duk zumudin son ganin junan maganar dake shiga tsakaninsu idan suka hadun be wuce ta tambayeshi ya jikin ba shikuma ya amsa daga nan zasu ja bakinsu su tsuke sai body language ko kallon kallo *MONDAY* Yau ake fara zaman kotu akan case dinsu master da zee Qarfe 10:00am ake fara zaman amma su zee suna wajen tun 9 Saida 10 takusan da yan mintuna sannan aka fara shiga kotun ana zazzaunawa 10am daidai alkali yashigo dakin shara'ar wanda ya dauki shiru tun bayan sanarwar isowarshi Miqewa duk mutanen kotun sukayi bayan mai buga guduma ya buga Saida alkali ya zauna sannan duk suka koma suka zauna Mai gabatar da qara ya tashi ya gabatar da qarar daza'ayi a lokacin sannan ya miqa takardun ga mai girma mai shara'a Shiru dakin yayi Saida alkalin yagama yan dube dubenshi sannan ya dago ga jama'ar wajen yace "kotu zataso lauyoyin 6angarorin biyu su bayyana kansu" Lauyan su zee ya tashi yafara gabatar dakanshi sannan mai kare su master shima ta gabatar dakanshi Saida yaqara yan rubuce rubuce sannan ya dago yana bawa Lauyan su zee damar farawa Lauyan ne ya buqaci su master da zee su fito Daddy dake gefen zee ya dafa kafadarta cikin qarfafa gwiwa don ganin yadda tabi ta takura kanta, sannan yayi mata nuni da ta tafi Tashi tayi jiki a sanyaye tanajin idanun mutane akanta ta nufi bayan dan akwatinan ta tsaya inda suma su master da sukayi wujiga wujiga dasu suka tsaya bayan dayan akwatin dake dayan gefen Saida aka sasu gabatar da kansu suka kuma yi rantsuwa akan fadin Gaskiya sannan aka fara Gyara zaman rigarshi ta lauyoyi Lauyan su zee yayi sannan ya kalli alkalin yana neman izinin abashi damar yiwa su master tambayoyi Bashi daman alkalin yayi Hakan yasa ya wuce wajensu master daketa muzurai kamar zasu ci babu Master yayi facing yace "zaka iya fadamin yaya sunanka?" Wani kallon sheqeqe yayi wa Lauyan sannan yace "dazu toshe kunnuwanka kayi da auduga halan shiyasa bakajiba?" Buga guduma alkali yayi sannan ya gargadeshi akan ya iya kallamanshi nan kotu ce ba wajen wasan yaraba Kauda kai yayi yana Gyara tsayuwarshi irin ta tattatun yan tashan nan marassa tsoro, duk jikinsu tabon ciwone don ba qarya yan kwanakinnan dasukayi a cell sun jibgu don iskancinsu ya zarta tunani Hakan yasa duk sadda suka kawo masu iskanci jibgarsu ake kamar kayan wanki kuma Hakan be hanasu fasawa saima abinda yaci gaba shiyasa polisawan ma ke allah allah afara zaman kotun Ayi a yankemasu hukunci sutafi ko sa huta Lauyan yasake cewa "Ana tuhumarka kaida tawagarka akan neman yiwa Zainab Farouq Dan Faranshi fyade, meye zakace akan Hakan?" Gyara tsayuwa yasake yi yana qara babbakewa harda pocketing din hannuwa a aljihu yace "me fa?" "ina nufin haka ne ko kanada ja?" inji Lauyan Yanzun ma Saida yaqara Gyara tsayuwa sannan yace "inada ja..." Dagowa zee tayi tana kallonshi bama ita kadai ba harda kingin mahalarta kotun "ba yunqurin yimata fyade ba kawai mukayi harda ma kisa don da munci nasara da bazamu barta da numfashi ba, kuma ko ayau muka qara samun dama saimun aiwata nufinmu don babu wanda ya isa ya jada master ya zauna lfy" yafada yana qara babbakewa yana muzurai Qananu qananun magangganu suka shiga tashi a dakin har Saida alkali ya buga guduma sannan aka nutsu Lauyan ne yaqara cewa "kenan kun amsa laifinku akan Hakan?" "da alamu dai kunnuwanka na buqatar likita" ya bashi amsa ataqaice Qara buga guduma alkali yayi wannan karon a fusace yaqara bigemashi warning akan ya kiyayi harshenshi Kauda kai kawai yayi bece komai ba Dan murmushi Lauyan yayi sannan yaqara cewa "zaka iya fadamana dasa hannun wa wajen taimaka muku don ganin kun cimma burinku?" "eh zan iya" ya amsa a taqaice "to muna jinka" inji Lauyan "qawayenta ne" "su wa kenan?" Kamar bazaiyi magana ba saikuma yace "su sumee take ko wa?" "sumee da wa da wa?" "ban riqe sunan sauran ba" ya bada amsa a taqaice Maida kallonshi Lauyan yayi ga alkali yace "ya mai girma mai shara'a, zanso kotu tabani dama wajen gayyato qawayensu Zainab don amsa wasu yan tambayoyi" yafada yana dan russunawa Dago kai alkalin yayi daga rubutun dayake yace "kotu ta baka dama" Nan kau aka kirasu gaban akwatin tambayar suka fito suka tsaya kusada su master kowacce na matsar qwallar danasani Tunda suka fito zee ke binsu da kallo tana hawayen da batasan tanayi ba, zafi take ji sosai a rsnta don da ciwo wanda ka yarda dashi ya munafurceka Suma Saida sukayi rantsuwa akan fadin Gaskiya sannan yafara masu tambayoyi Suma b@su ba shara'a wahala ba suka shiga fadin Gaskiya suna fadin yadda suke zaune da zee a munafurce dakuma dalilin dayasa suka hada kai dasu master akan ganin bayanta Sosai zee tashiga matsananciyar mammaki jin saboda Deen suka shiryamata wannan qullin, wai don tana sonshi, wai _*so*_ Jin ta bakin zee akayi itama inda itama ta warwaremasu yadda suke tareda su sumee, ta kuma nuna ita babu wata alaqa ta soyayya a tsakaninsu da Deen kawai abotace kuma ta karatu sannan kuma ta gayamasu abinda ke tsakaninta dasu master ta qarashe da gayamasu makircin da sumee tayi mata ranar da abin yafaru wanda Hakan yayi sanadiyar Fadawa tarkonsu Saida aka maida akalar tambayar gasu sumee dasu master akan suna da ja akan abinda zee tafada suka nuna basuda ja duk abinda tafada haka yake Kasancewar babu wanda yaba shara'a wahala a kowanne bangare yasa shara'ar tazo da sauki sosai inda Lauyan ya rufe jawabanshi da ambatar wanda ya taimaki zee wato Deen dakuma halin jinyar dayake ciki yanzu, sannan yayi Godiya yakoma mazauninshi ya zauna Tsit dakin ya dauka kowa hankalinshi akan mai shara'ar daketa rubuce rubucenshi na fama ana jiran jin me zai yanke, a gefe guda kuma ahalin wadanda ake tuhuma wato su sumee dasu master harsun fara matsar kwalla ta baqinciki tunma kafin a zartar da hukunci Saida yagama sannan ya dago ya kalli Lauya mai karesu sumee dayayi tsamo2 kamar zakaran da aka tsoma a ruwa yace "Lauya mai kare wadanda ake da zargi, ko kanada abinda zaka dora dashi?" Me zece? Bayan duk kowa ya amsa laifinshi, wannan ai tozarci ne agareshi. Dama sunsan saurin miqa wuya zasuyi suka jajiboshi? Koda su keda laifi ai yakamata su dan ja bawai suyi saurin miqa wuya ba irin haka Tashi yayi cikin jin haushi, yadan russuna yace "banida tacewa ya mai shara'a" Dan rubutu alkali yayi sannan yabashi izinin zama yadan qara rubutun sannan ya dago yana gyaran murya Duk qara nutsuwa akayi don sauraron abinda zaya zartar "Abisa hujjoji da aka gabatar dakuma miqa wuya da wadanda ake tuhuma sukayi batareda sunba shara'a wahala ba, zamu yanke hukunci kamar yadda constitution ta gindayar" Shiru yayi Hakan yasa dakin yaqara daukar deadly silent "abisa hujjoji dakuma amsa laifikansu dasu summaya Abdallah, nadeeya umar, nuratu shehu da ruqayya muhammad sukayi na munafurci da cin dunduniyar wacce ta yarda dasu dakuma hada kai da wasu don ganin bayanta an yankewa kowaccensu zama gidan yari na tsawon shekaru bibbiyu da tarar naira dubu dari biyar ga kowacce kamar yadda dokar constitution ta...... Da........ ta tanadar" Dakin shara'ar ne ya dauki hayaniya yayinda su sumee suka fashe da kuka wiwi suna dora hannu akai Yanzu ma Saida alkali yabuga guduma sannan dakin yadawo normal Qara gyaran murya yayi don fara karanto hukuncinsu master Hakan yasa dakin qara daukar deadly silent "A sakamakon hujjoji da kuma amsar laifin dasu Murtala lawal, Aliyu hassan, täjudeen garba, bashiru Ahmad da isma'il muntari sukayi na yunqurin yiwa Zainab Farouq Dan Faranshi fyade da kisa, Hakan yasa aka yankemasu hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru goma goma tareda aiki mai tsanani" Dakin ne ya kaure da hayaniya wanda Saida alkalin yayi dagaske sannan yasamu akayi shiru Ya cigaba dacewa "abisa kuma kalaman barazana dayayi na ko yanzu suka samu dama saisun aikata abinda sukayi niyya an yankemasu zaman gidan yari na shekaru biyar tareda aiki mai tsanani dakuma yarjejeniyar duk abinda ya sameta na ta6a lafiyarta zamuyi holding dinsu responsible sannan suma kowanne zai biya tara na naira dubu dari biyar na tadowa bawan allah ciwon shi mai mugun hadari, idan aka hada da wancan yazama zama gidan yari na shekaru 15 tareda aiki mai tsanani sai tarar kudi naira dubu dari biyar biyar kowannensu, idan akwai wanda wannan hukuncin beyi mashi ba yana iya daukaka qara a supreme court" Yana gama fadin Hakan ya bubbuga guduma Sau uku sannan ya miqe Duk miqewa kowa yayi suna hada baki wajen cewa court!!! Sosai zee ke hawaye tana kallon su sumee daketa rusar kuka kamar zasu shide Saidai su master ko gezau saima muzuran dasuke kamar basu ji hukuncin da aka yankemasu Dakyau ba Saida alkali yafita sannan duk aka fara fita bayan an tasa qeyar su sumee gaba su master kau polisawa na zagaye dasu don bayan mintuna 30 za'a qara gabatar da shara'arsu na kayan mayen dasuke huldarsu Sosai wuri ya kaure da hayaniya, masu kuka nayi masu murna nayi haka dai daddy da mummy suka kama zee suka ficewarsu daga kotun gabadaya yayinda sukuma su sumee aka tusa qeyarsu cikin motar gidan yari suna kuka danginsu nayi aka fice dasu daga harabar kotun Dayawa basu tafi ba saida aka gabatar da dayan shara'ar tasu master inda anan ma an yanke masu hukuncin zaman gidan yari na shekaru goma goma wanda idan aka hada da wadancan sun zama shekaru 25 kenan Zokaga kuka ga ahalinsu Saidai su ko gezau don sun dake ko a fuska basu nuna wata dakuma ba dukda kowanne taciki na ciki Haka aka tusa qeyarsu suma cikin motar gidan yari akayi gaba dasu akabar danginsu daketa faman ganin kuka... ✍️ 😭wayyo ina team dinsu master dasu sumee? Kufito mutayasu kuka 😭 don yau baqar ranarsu ce Allah sarki zamuyi missing dinku 😭😫 Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:35 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *028* Wunin ranar zee yinshi tayi a kasalance, she can't believe su sumee zasu zama prisioners na tsawon shekaru biyu Dukda ita suka munafunta sai kuma taji tana tausayinsu, yanzu shikenan sun tafi prison suda fitowa sai nan da shekara biyu Sunyi wasting din karatunsu sunyi tarnishing din mutuncin gidansu Wannan tunanin yasa ta qarashe yininta a sanyaye tanajin komai baya mata dadi Da daddare mummy tashigo dakinta ta zaunar daita tashiga yimata nasiha mai ratsa zuciya tana nunamata illar hulda da qawayen banza saboda gudun irin haka, yanzu da allah ya basu nasara akanta da yanzu wani zancen ake Ta dade tana mata nasihohin kamar yadda tasaba yimata akai akai, abin mammaki sai ji taji nasihohin sun shigeta sosai sa6anin da datake ganin duk salon takura ce irin ta mummy Saida tagama mata nasihohin sannan ta rufe da addu'a sannan ta umarceta ta tashi ta sauko suci abinci Tashi tayi jiki a matuqar sanyaye don sosai nasihohin mummy suka qara saukarmata da kasala tabi bayanta suka fita Koda ta kwanta ma barcin qin zuwa yayi dawuri, sosai nasihohin mummy suka qi barin brain dinta tanata jujjuyasu tana hango tsantsan gaskiyarta aciki Ahaka barci ya dauketa can cikin dare batareda ta shirya ba. *WASHEGARI* Zaune yake a kan gadonshi na asibiti, ya jingina da pillow qaffafunshi a miqe hannunshi riqe da dan qaramin littafin hisnul muslim yana karantawa A gefe daya kuma kaka ce zaune kan sallaya tana can charbi don gama sallar walha dinta kenan Duk sunyi nisa a abubbuwan dasuke akayi knocking din kofa Tare suka dago suka kalli kofa sannan suka kalli juna Ganin kaka na niyyar tashi yasashi cewa "bari naje kaka" Yasan gardama zatayi mashi Hakan yasashi saurin saukowa kafin tayi magana ya nufi kofar Daidai za'a murda handle din tawaje shima ya murda ya jawo kofar Kasancewar na wajen be shiryama Hakan ba yasashi yowa gaba Hakan yasa Deen saurin tareshi Gasping tayi cikin rintse ido cikeda tsoro Jin an tarota yasa ta bude idanu ahankali nata yafada cikin nashi Dan wara nata tayi cikin nashi tana saurin janyewa tanajin wani abu na tsirgamata a duk ilahirin jikinta Shima dan jada baya yayi shima kamar a tsorace yana cewa "oh... Sorry" "wai ya naji shiru kamal?" sukaji muryar kaka daga ciki Hakan yasa Deen kallon ciki dukda ba hangen kakan zai iyayi ba "A'a dama nabude ne saita fado..." qara yasaki sanadin take mashi qafa da zee tayi saurin yi ganin zai saki layi "kyakyawana?!" inji kaka tana saurin miqewa tsaye jin qararshi Saurin qarasowa wajen tayi taganshi duqe yana kama kafar da hannu guda yana yarfa hannu sai zee datake duqe itama tana jeramashi sannu a rude don ita batama san sadda ta tareshi da qarfi ba Haka "subhanallilah! Lfy kuwa?" inji kaka tana duqawa itama tana taya Deen din kama kafar a rude Hakan yasa zee sake daburcewa "eh... Dama... Kawai turo qofar nayi.. Ashe yana kusa sai ya buge kafar" tafada tana zazzare idanu irin na marassa Gaskiyarnan 6ata fuska yayi yace "O'O! Ba Haka bane" Dan waro idanu tayi kafin tayi magana yace "ba kofa ta bugeni ba" yafada yana cije le6e alamun zafi "h.. Hakane mana" inji zee tanajin zuciyarta na jumping tana tuna abinda yafaru ranar da ta tareshi daga su master "A'a ba Haka bane" yafada yana qara tamke idanu alamun zafi "to garin yaya? Kaida kasan ba cikakken lafiya ke gareka ba, tashi muje ka zauna tukunnan" Zee data sure Tundazu tayi saurin cewa "eh.. Eh, tashi muje ka zauna.. Sorry" Taimaka mashi sukayi ya tashi yana dangyasawa kamar gaske Dariya na cinshi ganin yadda zee tabi ta rude Har gadon suka kaishi ya zauna yana nishi yana sauraron zee daketa jeramashi sannu kamar ma ba a hayyacinta ba Zee kau a bangarenta a rude take, tasan halin Deen yana iya cemata ita ta takashi idan ta tambayi dalili kuma yace don tayo gaba zata fadi ya tareta Ina zata da wannan kunyar? Gashi ita yanzu tsoro ma takeji wani abu yasamu Deen ata dalilinta ganin yadda kaka bata wasa da abinda yashafeshi, afili take nuna qaunarshi tana nuna batason abinda zai ta6ashi Hakan yasa take tsoron wani abu yasake samun shi a sanadin ta gudun ata dalilin ma allura ta tono galma tasan itace wannan yarinyar data watsamashi abu mai sanyi, tasan idan tasan Hakan qila farfesunta zatayi Kaka ce ke dan matsamashi kafar tana mitan ai dama kicihi yasashi tashi yaje bude kofar, banda gulma meye na zuwa bude kofa a matsayinshi na majinyaci? Ai ga irinta nan Zee dai anyi tsuru2 tana ta zare idanu tama kasa zama 6ata fuska Deen yayi yace "O'O! Nifa kaka ba koface ta bigeni ba" Jin Hakan yasa zee wara idanu sai tayi saurin katsesu da "kaka ina kwana ya mai jiki? Kinga mummy batazo ba ko? Wlh yau unguwa zataje shiyasa bata samu zuwa ba Amma tace in gaidaki" ta qarashe tana qaqalo murmushi Jin Hakan yasa kaka sakin wancan zancen tayi murmushi tace "Allah sarki, mummy ko mutumiyar kirki? Wlh babu komai, ai tana ma qoqari wlh, samun irinta acikin masu kudin yanzu sai an tona, wlh babu komai allah ya saka da alhairi yajiqan mahaifa" Yaqe zee tayi tana cewa amin tana satar kallon Deen dake 6ata fuska haryanzu Ganin zaiyi magana yasata qara saurin katseshi da cewa "ga wannan kaka inji mummy, kuma tace a gaida mai jiki" tafada tana ajiyemata basket din abincin agabanta, da kaka ta lura daita sosai data gane a matuqar daburce take "ohni ma'u🤔 wannan abu babu ko gajiya, kullum saikun aiko na rana daban na dare daban? Allah dai yasaka da alhairi ya jiqan mahaifa" tafada muryarta na rauni tana jawo ha6ar zani tana rufe fuska Ganin Hakan yasa tayi saurin kallon Deen dake kallon ta itama Hade rai tayi tana zaromashi idanu tareda cije haqoranta 😬 Ganin Hakan yasa ya 6ata fuska yana kallonta gira ahade Ganin kaka ta dago daga kukan kicihinta yasa tayi saurin gyara yanayin fuskarta tana qaqaro murmushi "zauna mana aminiya, kinyita tsayuwa?" Sai a lokacin ta tuna da zama Hakan yasa tayi saurin jawo kujerar dake gefe ta zauna tana qara fadada yaqen fuskarta Don dole zee taita jan kaka da fira don kawar da hankalinta daga kan Deen daketa 6ata 6atan rai don atambayeshi wanda she's very sure idan aka tambayeshin abinda take gudun zai fada Hakan yasa ta dage suna fira da kakar tama mance dawata kunyarta datake ji A bangaren kaka kau abin nema ne yasamu nan sukayita firarsu abinsu Deen kau sosai Dariya ke cinshi ganin yadda zee ta dage sai zubo zance take wai duk don karya fadi Hakan ba qaramin Dariya yake bashi ba Saidai yana qoqarin dannewa yana sauraronsu, dayaga tafara relaxing irin tana tunanin ya mance dinnan saiya 6ata fuska yana ta6a kafarshi yayi kamar zaiyi magana Hakan sai yasa taqara saurin jawo wata firar Sai gashi harda labarin akun gidansu dasuke kiwatawa take bata bayan labarin school dinsu kala2 databata, dama labarin abinda yafaru a kotu jiya shine farko farko da labaran suka qare ne tafara bada duk wanda yazo kanta kawai muddin dai Hakan zai kawar da wancan zancen Haka Deen yakoma yayi relaxing yana sauraronsu yana ta kyalkyala Dariya cikin zuciyarshi (kai Deen muna maka kallon ustaz🤭) Saida ya wajigata son ranshi sannan yaqara 6ata fuska yace "ouch!!" Duk juyowa sukayi suka kalleshi, kaka na saurin miqewa tana tambayarshi menene yayinda zee tashiga fargaba sosai Hade gira yayi yace "ni kaffafuwana sunyi dayi, nidai zan dan fita na dan yawata" "yawo kuma? Idan ka kamu da sanyi fa?" "bafa iska ba ake kaka, bakiga zafi ba ake? Danaji iskan yafara isata saina dawo" "to kai ina kasani a asibitin nan da zaka yawata? Idan ka 6ace fa?" inji kaka kamar irin allurar nan, wai zai 6ace 🙄 "ai ga Zainab, ita tasan hospital din sosai, nidai wlh nagaji da zama wuri guda" yafada yana narke fuska Shiru tayi kamar mai nazari sai kuma tace "to yan dubiya fa? Idan sukazo bakanan fa?" tafada da alamu dai batason yatafi Shiru yayi kawai amma kana ganin yadda ya maida fuskar baby face kasan kawai haqura yayi ba don yaso ba Ganin Hakan yasa kaka cewa "to ai shikenan, amma fa karku dade... Aminiya ai kina iya rakashi ko?" tafada tana maida akalar tambayar ga zee dake sauraronsu Tundazu Murmushi zee tayi tace "sosai ma kaka" tafada tana niyyar tashi Ganin Hakan yasa shima Deen saukowa daga kan gadon cikin jindadi Saida kaka ta gargadesu akan karfa su dade sannan suka fice Fitowa sukayi daga dakin zee agaba Deen biye daita sukaita tafiya har suka sha wata kwana da babu mutane sosai Hakan yasata juyowa ta tsaya tana kallonshi hannuwa riqeda kugu fuska a Hade Jan burki shima yayi yana kallonta trying so hard wajen controlling dariyarshi "menene?" ya tambaya innocently "menene? Menene ma zaka tambayeni?" tafada cikin tada jijjiyoyin wuya "O'O!" "O'O! Nabi O'O da gudu, kai kenan ba'a sirri dakai, daka bude baki, da nufinka gayamata komai zakayi? Ansamu ta manta amma saboda shegen naci saika tuna mata?" Yadda ta haqiqice tanata bala'in yasa dariyar dayake dannewa Tundazu taqi dannuwa yashiga kyalkyala abinshi Sakin baki tayi tana kallonshi saikuma ta jinjina kai ta juya tafara tafiya Ganin Hakan yasashi saurin binta yana cigaba da dariyar "look, it's not what you're thinking.. Listen" yafada cikin Dariya yana cigaba da binta Banza tayi dashi ta cigaba da tafiyarta kamar zata tashi sama don haushi "hey... Listen mana, please" yasaka fada cikin Dariya yana Binta cikin qoqarin ganin ya taddota Ganin taqi sauraronshi yasashi yi kamar yayi tuntu6e ya duqe yana Sakin yar qara Zee dake gaba tana tafiya cikin fushi tayi saurin juyowa ta kalleshi Ganin shi a duqe ya riqe qafa yana runtse idanunshi yasata waro nata tareda komowa wajenshi da sauri "hey, are you ok?" Ta tambaya tana tayashi duba qafar "wash! Zafi" yafada yana yarfe hannu "a ina? Ina ne wajen?" tafada tana qara duba qafan tana son gano inda ya bige din Jin shiru yasata dagowa sai gani tayi kallonta yake fuska dauke da murmushi Tsuke fuska tayi ta tashi cike da jin haushi tawuce, Ganin Hakan yasa shima saurin miqewa yabita yanata mata magana amma taqi sauraronshi saida suka zo wani wuri inda ba jama'a sosai tasamu karkashin wata bishiya ta zauna Shima zama yayi dan nesa da ita yana maida numfashin biyo tan dayayi Dagowa yayi ya kalleta yaga danne danne ma take a wayarta "O'O! Ni menayi to? Why are you strong-headed?" Ganin yadda ta dago tana gallomashi harara yasashi dan daga hannuwa in surrender yace "ok, ok. Am sorry, shikenan?" Bata kalleshi ba kuma bata tankamashi ba "O'O! Banace sorry ba? What did you want me to do again?" Harararshi tasake yi bata ce komai ba "honestly, niba gayamata fa zanyi ba, ke kike ganin haka, i was just kidding you" Sai a lokacin ta kalloshi tace "kidding? Ka kusan sa zuciyata ta buga saboda fargaba shine zaka kira Hakan da wasa? Sai gashi nazama ru66a6iyar redio ta qarfi da yaji" Dariya Deen keyi tunda tafara har takai aya "but why? Are you that scared of her?" "fiyeda tunaninka, yadda batason komai ya sameka dinnan idan tasan takeka nayi ai babu kanta" Murmushi yayi yace "kibar tsoro babu abinda zatamaki, kakata nada kirki" "dama aiba kirki nace batadashi ba, Saidai cikin few days dinnan na karanci yadda take sonka kuma bata qaunar abinda zai ta6aka" "meyasa kikace haka?" "saboda haka ne, just imagine idan tasan nice na watsamaka coke kwanakin baya, me kake tunanin zai faru?" Murmushi yayi yace "babu komai, ai tsautsayi ne kuma kowa yasan tsautsayi" "no ba tsausayi bane ganganci ne, ni dakai munsan Hakan, ya kake ganin zatayi reacting? Ga kalamanta na ranan nasan reaction dinta won't be good" "shine dalilin dayasa kikayi fushi?" "fushi? Cema akayi nayi fushi?" "A'a kawai ni nasani" "to baka canka daidai ba" tafada tana harararshi "to amma meyasa baki zoba ranar da daddare kamar yadda kika saba?" "saboda banajin dadi ko ba Haka mummy tace ba" "haka tace kuma tace Hakan ne don haka kika gayamata amma kuma a zahirin Gaskiya ba Haka bane, kinqi zuwa ne saboda abinda kaka tace" "eh naqi zuwa ne saboda abinda kaka tace amma ba a sigar daka fahimta ba, ni banyi fushi ba, why on earth ma zanyi fushi? Me zaisa inyi Hakan bayan ni keda laifi? Kawai jinkaina nayi very guilty a lokacin naji kamar duk nice silar wahalhallun dakuke sha daga kai har kaka a sanadiyar ciwon nan naka daya tashi Sau biyu duk ta dalili na, abinda yasa nace wahalhallun dakukasha bance da kasha ba don itama kakar zan iya cewa banbancinka daita alokacin shine kai kana kwance unconcious ita kuma she's concious Saidai physically ba emotionally ba Tinawa nayi da yadda ta damu matuqa, ta yini kuka, every now and then tana dauke hawayen dake sakkomata, a fuskarta naga tsoro, tsoron rasaka wanda kallo daya zaka mata kasan idan wani abu yasameka akwai matsala, ban ta6a sanin tanada surutu ba don da farko ko magana sai takama dole takeyi ko fira ake bata cika sa baki ba Amma kana samun lfy tazama talkative, labari harna saidawa A lokacin nakama tunanin qila yadda tayi a lokacin dakake a kwance haka tayi wancan karon da na tadomaka ciwon, nasan ga lokacin ma tayi dararen dabata rintsaba Tunanin halin dazata shiga da wanda kaima yashiga yasa naji guiltiness atattare dani, idan kuma na tuna silar faruwan komai sai inji narasa inda zan saka kaina don guiltiness, shiyasa... Shiyasa ranar naji bana iya zuwa, bana iya zuwa naganta ko naganka don zuciyata tayi nauyi sosai, i can't face you guys" Deen dake Sauraronta keenly Tundazu yayi murmushi yace "kibar wannan tunanin, kibar jin guiltiness akan abinda yafaru a ranar, rashin sanine, gashi kina cikin fushi, fushin kuma mai dalili don honestly ko nine akayiwa haka I'll get mad In 6ata lokaci na inyi important assignment irin wannan wanda shizai zame mani tsani wajen hayewata a wannan subject din, in baje kwalwata inzuba komai wato inyi maqurar qoqari akanshi sannan wani wanda ban tabbatar da ya iyaba yazo ya yaga ya chanza dawani nashi without my permission? Konine zan fusata matuqa kuma komai na iya faruwa, so ni banga laifinki ba kuma koda kaka zataji bazataga laifinki ba don koba komai akwai rashin sani aciki don am perfect sure da kinsan inada pneumonia bazakiyi Hakan ba, so kibar tsangwamar kanki akan Hakan don bakida laifi koda kaka taji barema bazata jiba Saidai idan ke zaki fadamata" Murmushi zee dake kallonshi Tundazu tayi, wani lokacin idan yana magana kamar bashi ba, idan yaga dama ya dinga abu maturely idan yaga dama ya dinga abin yara, ta rasa gane kanshi "wa? Rufamin asiri, Saidai ko kai zaka fadamata, yadda take nuna sonka dinnan bana fatan na 6atamata rai ta wannan bangaren" Dariya sosai yayi ganin yadda tayi da fuska "waya gayamiki? Kaka nasona kamar yadda kowa keson nashi" "A'a, na kaka ya zarta" "be zarta ba" "ya zarta!" Murmushi yayi yace "how? You know, bake kadai bace ke ganin haka ba, dayawa mutane na ganin haka, wasu ma sai suga soyyayar datake nunamin yayi yawa tana overpampering dina Abinda mutane basu ganeba shine, ita qauna daya ce Saidai kowa da yadda yake nuna tashi Akwai masu iya 6oyewa ma'ana masu kawaici akan nasu Akwai masu bayyana nasu afili kamar dai kaka To irin haka ne sai aga kamar yayi yawa bayan da za'a gwada wannan soyyayar tasu data wannan mai kawaicin da wata qila aga ko kama qafar ta mai kawaicin batayi ba Kakata bata nuna kawaici akaina, she loves me openly batareda damuwa da abinda mutane zasuce ba Bana mantawa lokacin da nake qarami kusan kullum sai kaka tayi hayaniya da mace akaina Bawai jawo magana ba nake, A'a ni ake ja itakuma bata iya kyalewa most especially idan tasan ni keda Gaskiya, kaka bata ta6a kawaici idan taga za'a kwareni saita tsaya mun batareda damuwa da abinda mutane zasu ce akan Hakan, Hakan yasa mutane ke ganin soyyayar datake nunamin tayi yawa bayan ba Haka bane Idan ma Hakan ne banga laifinta ba don tana taking role din mutane uku ne agareni Uwa, uba da kaka. Shiyasa soyyayar tayi yawa don tana min soyyayar dazan buqata a wajen wadannan mutanen wato mahaifiyata, mahaifi na da kaka ta Shiyasa bana missing iyayena ta fannin nuna qauna da kulawa don kaka tayimin komai, tana sona kuma nine komai nata kamar yadda nima nake sonta kuma itace komai nawa Duk duniya banida babbar masoyiya kamar kaka daga ita sai mai sonta sai mai son mai sonta sai mai son wadda taso wanda ke sonta" Dariya sukayi atare saboda yadda hausarshi ta qarshe take so confusing "to aku mai bakin magana, wai mai son wadda taso mai sonta, wannan love chain din fa?" inji zee tana Dariya Murmushi yayi yace "wai don ki gane" "tayaya za'ayi ingane wannan doguwar hausar? Gaka ba bahaushe ba sai fihili" 6ata rai yayi "nine ba bahaushe ba?" Dan bude idanu tayi tace "oh ashe bahaushe ne, mantawa nayi" tafada tana ta6e baki don ita haryanzu bata yarda shi bahaushe bane Akwai dai abinda yake 6oyemata "yanzu ai kin tuna" yafada yana harararta Qara ta6e baki tayi tace "aikau dai na tuna bawai don na yarda ba" Ta6e baki shima yayi yana daga kafadu sannan yace "dazu naji kina ba kaka labarin yadda akayi da qawayenki jiya" Mood dinta ne ya chanza, Ganin Hakan yasa yace "Allah ya tsare gaba, allah yasa kuma Hakan yazama silar shiryuwarsu, 2yrs kamar 2days ne insha allah" Kada kai tayi sai kuma ta dago ta kalleshi tana tuna abinda sukace shine dalilinsu na juyamata baya _*son Deen*_ Jitayi zuciyarta ta buga da qarfi Hakan yasa tayi saurin kauda kai daga kallonshi zuciyarta na beating fast Tasan kwata2 maganarsu ba Gaskiya bace amma tarasa dalilin dayasa daga jiya zuwa yau data tuna Da wannan kalmar sai zuciyarta taqara gudu musanmman ma yanzu datake tare dashi Haka ta danne abinda zuciyarta keyimata ta cigaba da sauraronshi suka cigaba da firarsu Basu qara jimawa ba suka tashi don komawa don kar kaka taita jira shiru Daga nesa daka hango yadda suke tafe suna hira kowanne da murmushi a fuskarshi sai sun burgeka don sosai sukayi matching dajuna ta kowanne fanni... ✍️ Tofa, munfara tsunduma cikin main labarin, muje zuwa 💃 yanzu ma za'a fara wasan😍 Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:35 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *029* Saida tadan qara jimawa hospital din sannan tawuce gida Tun daga ranar abin nema yasamu, duk lokacin dasu zee suka zo saisun fita da ita dashi wai miqe kafa wanda Dr ne yaqara qarfafa abin don acewarshi ya dinga yawatawa din Hakan na cikin abinda zai ida sawa yaji sauqi sosai Haka kullum zasu fita susamu quiet wuri inda ba'a cika zirga zirga ba suyi zamansu susha firarsu, sai sun gaji sannan zasu koma Acikin yan kwanakinnan wata muguwar shaquwace ta shiga tsakaninsu wacce tafi ta da Har takai idan basa tare sai sudinga jinsu empty kamar akwai abinda ke missing a rayuwarsu Sosai Deen yake samun sauqi don ba qarya yana samun kulawa na sosai da sosai, abinka da private hospital inda ake tarairayar patients sosai da sosai Gashi kuma patient din Alhaji farouq ne wanda yana daya daga cikin wadanda suke darrajawa sosai saboda gudunmawar dasuke ba asibitin shiyasa yake samun special treatment Ranar daren da za'a sallamesu ake amsar result a school Hakan yasa zee bata samu zuwa hospital din ba Koda ta isa school din saitaji komai na ranar nan na komamata sabo Duk inda tawuce sai an bita da kallo wanda tasan Hakan baya rasa nasaba da abinda yafaru dakuma makomarsu master Kamar yadda tasaba kallon be dameta ba harkar gabanta kawai take Wucewa tayi wurin da aka liqa nasu ta duba, babu abinda tafara nema sai subject din mr ibrahim Wani farinciki ya ziyarceta lokacin dataga abinda tasamu *57/100%* Hakan na nufin a exams taci 40% idan kuma aka jona da score dinta 17% na assignment dinnan saiya bada 57% Sosai taji dadi kuma ta godewa allah akan Hakan sannan tabi sauran subjects din wanda suma duk tayi qoqari acikinsu Koda tagama kamar ta tafi saikuma wata zuciyar tace mata ta dub a nasu nurr mana Dubawa tayi Saidai results dinsu ba kyan gani don duk tarin carryover(s) ne, bataji dadi ba sam don haryanzu suna ranta dukda kuwa abinda sukayimata don ita idan zata so mutum to da dukkan zuciya takesonshi babu algus Daga nan wucewa tayi department dinsu Deen don ta dubomashi shima As expected, shima yayi passing in flying colours don result dinshi is so amazing Ciro wayarta tayi tashiga snapping din daidai nashi murmushi a fuskarta Saida tagama komai sannan tawuce cafteria ta siya snacks da drink ta wuce wurin zamansu don jiran qarasowar bala Ga mammakinta tana zama wajen sai jitayi tana kewarsu sumee, sai tafara tunanin ko me sukeyi a yanzu? Da sunanan da yanzu suna tare ana maida yadda akayi Kawar da tunaninsu tayi tafara cin snacks dinta silently Tunanin Deen ne yafadomata, ko me yakeyi yanzu shima? Tambayar da tayiwa kanta kenan, tasan da yau ta tafi asibitin da yanzu suna tare suna firarsu mai dadi mai sa nishadi Sai jitayi tayi missing dinshi shima, murmushi kawai tayi ta cigaba da cin abin hannunta tana saqa da warwara ita kadai har bala ya qaraso Babu 6ata lokaci ta tashi tawuce parking space din tashiga mota suka fice daga harabar school din *WASHEGARI* Yau ce ranar sallamar Deen daga hospital, ya warke garau kamar be ta6a kwanciya jinya ba saima wani qara fresh dayayi da kyau Kaka yau baki be rufuwa, sai kai kawo take wajen ganin ta kammala kayyayakinsu waje guda Wajajen 12 su zee da mummy suka duro asibitin suma daddy kau dama yayi tafiya tun washegarin ranar da akayi zaman kotu, dama abinda ya tsaidashi kenan Koda suka iso sai tarar da kaka sukayi tagama kammala komai wuri guda jira kawai take a sallamesu su qara gaba don zaman asibitin ya isheta, sati biyu ba wasa ba Mummy ce tashiga tsokanar kaka akan zumudin datake wai kodai don taje ta cigaba da samun yan anninnan ta yasa take wannan zumudin? Dariya sukayi baki daya kaka nacewa ashe dai ta gano Kallon Deen zee tayi taga ya sakarmata murmushi Itama maida mashi martani tayi tana kauda kai tashiga gsida kaka itama Cikin fara'arta kaka ke amsawa tana tambayar ta ya sakamakon dataje dubowa jiya Murmushi tayi tace "Alhamdullilah kaka, sakamako yayi kyau sosai" "masha allah, ai haka akeso. Ai ina ganinki nasan zakiyi qwanya kamar dai kyakyawa na, allah sarki, kowa zaije ya dubomashi shi? Inajin nizanje in dubomashi bari dai komai ya lafa" Dariya duk sukayi jin abinda tace, Deen yace "to kaka ke ya za'a yi ki iya? Tayaya zaki iya gano sunana cikin jerin sunayen dake manne a wajen? Kuma ma Dariya zasuyi miki wlh, suga tsohuwa tazo duba result" yafada yana Dariya Daquwa ta watsamashi tace "ungo nan don qaniyarka, nice tsohuwa?" Dariya duk suka sake dauka "Ato, maganar shi dai na kan hanya" inji mummy tana Dariya "ba wata kan hanyar datake zaki wani goyi bayan shi, kubar ganin na haka to tsohuwa ce mai ran qarfe don abinda mai ji da quruciya bata iyayi ina iyawa, ko aminiya?" Murmushi zee tayi tace "kyalesu kaka, ai fadi ma 6ata baki kuma bama sai kin wahalar da kanki ba na dubomashi, bari kigani" tafada tana zaro wayarta ta lalubo result din ta nuna ma kaka, aikau ta amshe wayar tana dubawa baki washe kamar irin tasan abinda ke ciki dinnan "kai masha allah! Bana gayamaku ba, dan jikallen nawa ba dai qwanya ba, kalli wani dan abu abu nan nasan na masu qoqarine ko?" tafada tana nunama zee dake Dariya bama itaba duk mutanen dakin "eh kaka ai yayi qoqari sosai" inji zee tana kallon wayar "snapping dinshi kikayi?" inji Deen yana kallon zee Kada mashi kai kawai tayi alamun eh "mugani kaka" yafada yana miqa hannunshi Janyewa tayi tana cewa "tsaya mugani, meye wannan abin shikuma?" "ko an fadamaki ba ganewa ba zakiyi kaka, kidai bani ingani" Harararshi tayi tasake gwadawa zee Saida tagayamata ko menene sannan ta bashi tana jinjina kai alamun ta fahimta amma a zahiri babu abinda ta fahimta Amsa Deen yayi cikin zumudi yana dubawa Wani kyakyawan murmushi yayi yana maida pink lip dinshi na qasa ciki yana taunawa Batasan itama shi take kalloba tana murmushin da Batasan tanayi ba Saida ya dago suka hada ido Saurin janye idanun ta tayi cikin basarwa still murmushin a fuskarta "mugani son" inji mummy Miqamata yayi ta amsa itama tana dubawa "kai masha allah! Gaskiya result yayi kyau sosai" Cikin jindadin abinda tace kaka tace "kede bari, ai dan naki badai qwanya ba. Yo to Allah na tuba yadda yake raba dare yana karatunnan ai dole ma yaci, ko lokacin dayake firamari shi ke dauko na daya, duk lokacin hutu saiya dawo da kyauta, abashi a makaranta abashi a hanyar dawowa gida, duk wanda ya gamu dashi a hanya ya amshi takardar ya duba saiya bashi wani abu, tun sannan nasan yaron naki dan baiwa ne ba irin wasu ba masu kwalwar dusa, kullum Saidai a matse jakka a hammata azo amsar kudin tara, ja'irai dama kudin ke kaisu sudai abasu sutafi sukul din sukasosu sudawo suna zare idanu, ranar hutu kuma sunfi uban kowa kukan an kaddasu a jarabawa Haka kyakyawana yaita fama dasu, duk lokacin da aka bashi takardarshi sukaji yayo na daya sai suyita jin haushinshi wani sa'in ma su tareshi a hanya suyimashi duka su yaga takardar, dayake raggo ne babu abinda ya iya shiyasa suka bi suka rainashi Haka zai dawomin hurtutu idanu jajjaye ga yagaggiyar takarda, Saida na tashi tsaye sosai suka shafamashi lfy don bana jin kunyar kowa idan danki ya daki jikana har gida zan biyoshi na rama mashi, babu ruwana Sunyi surutun sunyi surutun amma ban fasaba don ko qarqashin gado yashuge saina zaquloshi na rama mashi saigashi sun daina ko kallon Banza ma basa mashi Ato idan kace ka nuna sanya sai a raina maka hankali..." Haka kaka taita zuba Sukau sai sauraronta suke suna murmushi, wani wurin kuma mummy tasa baki Suna haka akafara kiraye kirayen sallar azahar Duk tashi sukayi suka gabatar daita Basu dade da gamawa ba Dr yashigo Saida yaqara duba shi yaga komai normal sannan ya rubuta masu sallama bayan ya basu maggungunan Deen dazai cigaba dasha yakuma gargadesu su dinga kulawa abar barin sanyi na bugunshi Babu 6ata lokaci suka gama kimtse kimtsensu suka fito Motarsu mummy suka shiga mummy ce ke tuqi sai zee gefenta, abaya kuma Deen ne da kaka suka fice daga asibitin suka shilla Da kwatancen kaka suka qaraso unguwarsu Deen Zee sai kallon unguwar take tana ganin yadda aketa kai kawo jefi jefi A gaban wani dan gida kaka tasasu tsayawa Fitowa duk sukayi gabadaya suna maida koffofin suna rufewa Bïñ arear zee take da kallo tana kallon yadda yanayin gidajen unguwar suke Wucewa tayi wajensu kaka daketa qoqarin lalubo makullin gidan shikuma Deen rungume da qullin komatsansu Bude kofar kaka tayi tana cewa "to bismillah, kuyi hqr gidan dai gashi nan dan kuqut" Deen ne ke bayanta sai zee dake riqe da nad'ad'iyar tabarmarsu wanda kaka ke amfani daita a asibitin sai mummy Da sallama duk suka shiga gidan dake tass yasha shara don dama tun jiya matar mallam Nasiru taje ta amshi makulli tasa yaranta suka gyara gidan fess don tasan agajiye zasu dawo gashi dama gidan ya dade bega gyara ba "maraba damu, kai yaushe rabo? Nasan gidannan ma yayi kewarmu" inji kaka tana qarasawa kofar dakinta Murmushi duk sukayi sai mummy tace "ai dole, sati biyu fa?" Kaka data shige dakin tace "sati biyu amma jinshi nake kamar shekara biyu" Tafito hannunta da wata tabarmar ta shinfida masu tana cewa "bismillah, ku xauna munshawo rana, kamal tashi kasamomana pure water mai sanyi ko ma jiqa maqoshi" Tashi Deen da dama zamanshi kenan yayi ya amsa yawuce Binshi da kallo zee da mummy sukayi cikin sha'awa Sai ji mummy tayi yaqara kwanta mata don a duniya tana bala ' in son d'a ko 'ya mai biyyaya kuma a yan kwanakinnan datayi dasu kaka ta lura Deen akwai biyyaya ga sanyi bayada hayaniya ko kadan abinda take buri ga diyarta amma Saidai ba Haka take ba ko dayake taga acikin kwanakinnan kamar tafara dan hankali hankali Suna zaune suna dan fira Deen yadawo da rabin ledar pure water masu sanyi yawuce dasu kitchen can kuma yafito dasu bisa unbreakable plate mai dan fadi kamar yadda suka saba yiwa baqi yazo ya ajiye tsakiyarsu dan murmushi a fuskarshi Kaka da kejin kishi sosai tafara dauka tana cemasu ga ruwa su dauka Babu musu suka dauka zee na raka Deen daya nufi wani daki da kallon qasan ido Mummy ce tafasa tadan sha ba laifi itakau zee dauka kawai tayi badon tasha ba don bata iya shan wannan ruwan inba sotake cikinta ya rikice ba hakan yasa ta riqeshi a hannu kawai Saida suka qara dan jimawa sannan suka tashi da niyyar tafiya Tashi itama kaka tayi tanata kwarara masu Godiya da samasu albarka da addu'o'i suna amsawa, kiran Deen tayi don suyi bankwana Saida suka rakasu har kofar gida suka tsaya suna jiran ganin wucewarsu sai gani sukayi mummy ta tafi bayan booth ta bude sannan ta yafito Deen da hannu alamun yazo Babu musu ya qaraso wajen cikin nutsuwa Gwadamashi booth din tayi tace "ya za'ayi a sauko dasu ko wasu za'a samu su taimaka?" Dan wara idanu Deen yayi ganin abinda take gwadamashi "na menene wadannan din?" "naku ne and banason wani qorafi, maza samo masu dauka" Ganin yadda ta Hade rai yasashi kasa musawa sai kawai ya fara nade hannun shirt dinshi yace "bari na dauka zan iya ai" Zee na gefe tana kallonsu har suka gama fidda kayayyakin daga booth din Kaka tariga takoma ciki so Batasan wainar da ake toyawa ba Rufe booth din mummy tayi tana cewa "to mu zamu tafi amma insha allah zamu dinga dan leqowa tunda munga gidan, allah yaqara sauki" tafada tana kallon smiling face dinshi "to mummy mun gode qwarai, jazakillah bil-jannah" yafada cikin ladabi Wani kayattacen murmushi tasaki tana cewa amin sannan tawuce bangaren driver Kallon zee dake tsaye gefen kofar mai zaman Banza yayi yaga itama shi take kallo Murmushi yayi mata itama ta maida mashi martani slightly sannan tajuya ta bude kofar tashiga ta zauna maida ta rufe, mummy ma rufe nata tayi bayan tashiga tana daura seat belt Juyowa zee tayi ta kalleshi ta window taga shima still yana tsaye yana kallonta itama Tsayawa sukayi suna kallon juna kamar suna karanta wani abu a fuskar junansu Tada motar mummy tayi tafara reversing ahankali Ahankali Deen yaga zee ta dago hannunta sannan tayimashi waving murmushi nadan forming a fuskarta Shima dago hannun yayi yafara daga masu hannu fuska dauke da murmushi har suka bar layin Bïñ motar datayi nisa yayi da kallo yanajinshi awani yanayi dabazai iya pointing finger akai ba Saida ta 6acema ganinshi sannan ya sauke ajiyar zuciya yadawo da kallonshi akan kayayyakin dake gefe ajiye Wani yaro dan babba2 yazo wucewa ya kirashi yace ya taimaka mashi shigar da kayan ciki Tare sukaita shiga da kayan ciki har suka qare sannan Deen yaba yaron naira 20 yanamashi Godiya sannan yadawo cikin gidan inda kaka ta tisa kayan gaba tana binsu da kallon mammaki Shigowar Deen din yasa ta maida kallonta akanshi cikin ayar tambaya Hakan yasa yadan 6ata fuska yace "wlh kaka Saida nace a'a saita fara fushi wai saina amsa" "ita wa?" "mummy mana, zanyi magana ta hanani wai Batason qorafi" Shiru kaka tayi tana kallon kayan wanda duk kayan abinci ne, su cartons din taliya, macaroni, couscous, gallon din mai da manja, packs din maggigika sai wasu abbubuwa a leda wanda ahaka bazasu iya gane meke ciki ba saisun buda Ajiyar zuciya kaka tayi tace "kuma shine kabari ta tafi ko Godiya?" "ina gama saukewa ta tafi ai" Ajiyar zuciya kaka tasake yi tace "to allah yasaka masu da alhairi, allah ya biyamasu dukkan buqatunsu na alhairi, gashi ko unguwarsu bamu saniba bare muje Godiya, allah dai yaqara budi, sun taimaka sosai wlh kaga zasu riqe mu nawasu lokaci kafin mu maro, allah dai ya biya" Da amin Deen ya amsa, cemashi tayi yakama su shiga dasu ciki kafin afara Shigowa Da taimakon shi suka kwashesu duka suka kai dakin kaka suka adana sannan suka daura alwalar sallar asr don har anfara kiraye kiraye Wucewa masjid yayi ita kuma kaka tawuce d'aka *** Tunda suka kamo hanya take kallonshi ta side mirror din motar harya 6acema ganinta, sai jitayi kamar ta taho tabar wani abu nata acan Lumshe idanu tayi ta koma ta lafe a kujera tayi shiru tanajin yadda suke tafiya akan titi Basu wani dade ba suka qaraso gida Horn biyu mummy tayi aka wangalemasu gate din gidan suka shige Saida tayi parking sannan duk suka fito zee na jinta very empty Wucewa sukayi ciki suka haye sama kowa yayi sashenshi don gabatar da sallar asr da aketa kira *** Koda aka gama sallah gagaisawa Deen yashiga yi da mutanen cikin massalacin kamar yadda yasaba sunata tayashi murnar sauqin dayaji Koda yafito ma zai tafi gida haka yaita gamuwa da mutane sunata mashi barka yana amsawa da murmushi harya samu ya qaraso gida A gidan ma yan tsirarun mata ya iske wadanda suka shigo yima kaka barka Gaidasu yayi a ladabce duk suka amsa suna mashi ya jiki ya amsa masu sannan yatashi yashiga dakinshi Be dade ba ya fito yazo wajensu yaqara gaida wadannan suka sake Shigowa bayan shigarshi daki sannan yace ma kaka zai dan fita wajen aikinsu Fatan dawowa lfy tayimashi tana cewa kar yakai magrib Da to ya amsa ya tashi yayi sallama da mutanen yafita Direct wajen workshop dinsu yawuce inda ya ishesu suna dan ta6a aiki don yanzu sai ahankali abunka da damuna Duk sunyi murnar ganinshi Hakan yasa suka shiga gagaisawa cikin fara'a Suna tambayar shi ya jiki yana amsa masu da ya warware Haka ya zauna cikinsu anata fira wanda becika sa baki ba Saidai da anyi abin Dariya yayi murmushi kawai Be baro wajen ba sai wajajen magrib Saida yafara gabatar daita sannan yashiga gida inda ya iske duk matan sun tafi sai kaka dake daki bisa sallaya ita kadai Saida yayi mata barka da gida sannan yawuce dakinshi Be sake fitowa ba sai lokacin isha'i yawuce massalaci don dama da alwalarshi Koda aka gama ya dan jima awaje sannan ya dawo gida Abinci kawai sukaci suka kwanta saboda dama a matuqar gajiye suke shiyasa suna kwanciya barci yayi awon gaba da kowanne A bangaren zee kau yau Dakyar tayi barci, wani irin kewa takeji sosai musanmman da lokacin Zuwansu asibiti na dare yayi Haka taita juyi a gado don kwata2 babu barci a idanunta Ganin Hakan yasa tajawo wayar ta tana yan danne danne amma a Banza don Hakan bewani hanata jin abinda takeji ba Haka taita fama har tasamu Dakyar barci yayi gaba daita can wajajen 12 dare... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:35 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *031* "Are you ok?" yafada yana tsareta da ido Kauda kai tadanyi gefe tana hadiye qululun takaicin daya tokaremata maqoshi Kallonshi tayi tadanyi murmushi irin na takaici tace "am fine, kawo nasa maka" Amsa tayi tana jin kamar ta kwalata da qasa amma tayi qoqarin controlling emotion dinta Saboda tsabar yadda takeji har wani dishi dishi take ganin screen din wayar Dakyar tasamu ta daddana nambobin mummy data riga ta riqe ta offhand sannan ta miqamashi Ganin be amsa ba yasa ta dago ta kalleshi taga ita shima yake kallo Sake miqamashi wayar tayi batareda tace komai ba Amsa yayi ahankali sannan yace "Are you sure you're ok?" "more than you are" tabashi amsar tana juyawa kwalin wayar a hannunta Kafin yasake wata maganar harta fice daga zauren ta nufi Motarsu Dayake a fusace take ko jira a bude mata motar batayi ba ta bude abinta dakanta tashige Tsayawa Deen daya biyo ta shima yayi a bakin kofar gidan yana kallon motar dukda baya iya hangota taciki saboda tinted glass dinta Da sauri bala ya zatayi ta bangaren mai tuqi yashiga shima yarufo qofa Yana tsaye yaji qarar tashin motar sannan tafara yin reverse tana barin layin Bin motar yayi da kallo abubbuwa da dama na kai kawo a zuciyarshi Tabbas she's not ok, ya hangi wani abu a fuskarta dukda 6oyemashi datayi qoqarin yi, kamar fushi kamar takaici bazai dai iya pointing finger akai ba To idan ma fushin ne meye silar? Tunda yashigo gidan ya lura da wannan expression din a fuskarta Duk sai yaji ba dadi, satinsu daya rabonsu da juna and he's longing and waiting for the day they'll meet, a tunaninshi bayan wannan lokacin da sukayi basu ga juna ba haduwarsu zaya zama very memo ranar one, zasu dade suna firar yaushe gamo amma yaga akasin haka saima qin Sakin jiki da fuska data sabayi Ya dade nan tsaye sannan ya juya ya koma ciki a sanyaye Idan ran zee ya kai dubu to duk sun 6aci Tama kasa fasalta abinda takeji a ranta wannan lokacin She's totally and totally dissapointed with him Tayi sati tana kewarshi tana begen ganinshi tana looking forward to ranar haduwarsu cikin zumudi amma sai gashi babu abinda ta kwasa a ranar datake zumudin sai kayan haushi da takaici It hurts idan kadamu da mutum harya kasance koyaya ka motsa saiya fadomaka a rai amma at the end of the day ka gano cewa bakai ke gabanshi ba Koda bala yayi parking bata tsaya ya budemata kofa ba kamar dazu ta bude ya fita tayi gaba Zagayowa bala yayi ya rufe kofar data bari bude cikin ranshi yana gulmarta wai dama idan tafito mota dakanta to ranta a 6ace yake Da sallama ciki2 tashiga falon, babu kowa falon hakan yasa tayi sama direct Kamar tashiga dakin mummy sai kuma tafara bude dakinta ta tilla ledar wayar hannunta saman gadonta sannan ta rufe tawuce kofar mummy tashiga knocking Saida aka bata izinin shiga sannan ta tura kofar tashiga tana kokarin saita fuskarta Mummy daketa lissafe2 ta dago tana kallon zee data shigo dakin Qarasawa zee tayi ta samu wuri ta zauna tana yiwa mummy sannu da aiki "yauwa, harkun dawo?" Kada mata kai tayi tace "eh mummy, tana gaidaki sosai tamace zata kiraki nabata number ki" "masha allah, me jiki fa? Hope ya warware" Wani abu taji ya tsayamata a qasan maqoshi jin anyi maganar Deen "eh da sauqi" ta amsa non-chalantly "to allah ya kyauta gaba dama haka muke fatan ji" Shiru yadan ratsa dakin can zee ta tashi da niyyar tafiya "kunyi waya da daddy?" inji mummy tana dakatar daita "A'a, duk yau bamuyi ba Saidai jiya munyi da daddare" ta amsa "wani abu yafaru ne mummy?" tafada cikin curiosity Murmushi tadanyi tace "ohon muku, ai kunfi kusa, cemin yayi yana kiranki bata shiga wai idan kin dawo ki kirashi" Murmushi tayi tana jin kaso kadan daga cikin 6acin ranta na tafiya "ok zan kirashi yanzu insha allah" Daga haka tayi mata sallama tafita Dakinta tawuce direct Gyallen kanta tafara warwarewa ta cire sannan ta zauna gefen gado tana scrolling din wayar ta Foreign number daddy ta lalubo ta antayamashi kira Bugu biyu ya daga ya dauka yana sallama Shagwa6e fuska tayi lokacin dataji muryar daddynta "daddy na" Murmushi mai sauti daddy yayi daga can bangaren yana cewa "my jewel! Har kun dawo" Komawa tayi da baya ta kwanta tana lumshe ido tana jin sanyi na ratsa zuciyarta "eh daddy na, nidai daddy na yaushe zaka dawo, i missed you sooo muchhhh" Dariya daddy yayi daga dayan bangaren yace "missed you more and more darling, wannan satin naso dawowa amma allah beyiba inajin sai kuma next week qila" "kai daddy, next week is too far, i can't wait" tafada a Shagwa6e Dariya yasakeyi yace "then bari nabaro komai nadawo tunda sweetheart dina bata iya jira" "but daddy kingin aikin fa?" "that can wait i guess" Murmushi tayi tace "kai daddy" "yes, ina iya barin komai nazo na ganki inhar Hakan zai farantamiki" "no daddy tunda ka kusa kabari saika gama sannan kadawo" "no, bayan kin tadomun tsumin son ganinki? Gobe zaku ganin daga sama, don't tell your mummy about this" Tashi tayi zaune tana dan wara idanu tace "wai dad da gaske kake? Daddy am joking please karka taho saika gama abinda yakai ka" "Sai kiyi, am done talking" Sai gashi ita takoma bashi haquri yabari saiya kammala abinda yakaishi sannan ya dawo don tasan qaramin aikinshi ne ya taho din muddin Hakan zai sata farinciki Dama haka yake koda yaushe farincikinta shine nashi, yasha yin abu don farincikinta koda kuwa Hakan na nufin sadaukar da nashi farincikin ne, that's daddy for you Dakyar tasamu ya yarda zai zauna din yana mitan zata hanashi ganinta, nan tace indai don ganinta ne suyi video call ba shikenan ba? Haka kau akayi, nan take sukayi switching din kiran zuwa video call Sun jima sosai suna wayar sannan sukayi sallama kowanne murmushi a fuskarshi Izuwa yanzu kaso mafi rinjaye cikin 6acin ranta yabi iska tareda firarsu da daddy Tashi tayi ta shiga toilet can ta fito hannunta da fuskarta Duk ajiqe Idanuwanta ne suka sauka akan ledar wayar dake a tsakiyar gadon Yarfe hannunta tayi ta dawo gefen gadon ta zauna tajawo ledar ta bude ta Fiddo kwalin tana jin ranta na qara 6aci Bude kwalin tayi taga wayar gatanan kamar ma ba'a ta6a ta6ata ba Cirota tayi tana jujjuyata a hannunta cikin zuciyarta tana tambayar kanta kodai ya raina wayar ne? Inba haka ba wa za'a ba this kind of kyauta ya mayar? Kodai besan ko nawa take ba? Ko ba kalarta yakeso ba? Ko... Ko... Ko.. Tama rasa abinda zata hasaso again Danna power din wayar yayi tafara booting Saida tajira ta bude dakanta sannan tayi swiping "wow!" tafada ganin tana preparing apps din wanda Hakan ke nufin ko ta6a kunnata beyi ba Kada kai tayi cikin qunar rai tana dan murmushin takaici Tarasa dalilin dayasa abin yake 6ata mata rai har haka Ko don bata ta6a yiwa wani kyauta ba ya maido mata? Tunawa tayi dasu sumee wadanda kamar dama jira suke, data basu abu zasu amshe suta murna, ta tabbata da daya daga cikinsu taba wannan kyautar da tun ranar inbox dinta zai cika da sms din Godiya harma da kiraye kiraye amma wai shi ko kunnata beyiba _*mun gode qwarai amma bazan iya amfani da wannan ba, nama riga na chanza wata so no need to worry*_ Maganarshi ta dazu ta fadomata arai Wai ya chanza wata, badai wannan calculator din yake kira waya ba Badai akanta yayi rejecting nata ba Wai kuma to top it all yaqi tambayarta number wayarta Ita abin ma mammaki yake bata, mutum ba kowan kowa ba sai shegen jin kai da nuna halin ko in kula Ta tabbata da wani ne tun farko farkon haduwarsu zai nemi digits dinta amma shi be nema ba kuma beda niyyar nema gashi ta bashi a 6agas ko sanin ta bashin beyi ba Kwafa tayi cikin zuciyarta tana cewa "you'll come and beg for it, I promised" 💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖 Deen haka ya qarashe Wunin a sanyaye shikuma Duk iya hasashenshi ya rasa what went wrong, abu daya dayake iya pointing finger akai shine mayar mata da wayan dayayi To amma shi bega abin fushi akai ba kuma ma kafin ya maida mata ya lura da yadda taqi sake mashi don yaga ko kallonshi ma bata sonyi Idan ma maida wayar ce shi bega abin fushi anan ba To be honest bazai iya amfani da waya worth #50,000, waye shi? Dan gidan waye? And also beson alfarma ko kyauta, yafison yayi amfani da abinshi don yama fi sakewa yayi amfani da abu idan yasan nashi ne amma idan akasin hakane duk saiya ji yakasa sakewa yayi yadda yakeso dashi Haka ya qarasa ranar cikin rashin jin dadin komai, komai nashi a sanyaye yake yinshi kamar marar lakka dama qaqa lafiyar giwa? **** Kamar yadda tayiwa kanta alqawari haka take qoqarin yi Sosai take qoqari wajen ganin ta cire Deen daga cikin tunaninta ta ajiye Saidai fa abin gaba gaba yakeyi yadda kasan qara mata akeyi don kodayaushe abin qaruwa yake with every passing seconds Abin harya kai ko barci ta kwanta sai tayi mafarkinsu shi da ita in a romantic mood suna fira cikin annushuwa Tun tana daukar abin wasa har yafara bata tsoro don haka kawai zata zauna tayi zugum ita kadai Wani sa'in tafara rairo baitin waqa gamedashi batareda ta sani ba Sosai wannan abin ke damunta don the more take son yakiceshi a zuciyarta the more yake qara mannewa a zuciyar Kwance take akan gado rigingine idanunta bisa p.o.p ta kafeshi da idanu Kewa takeji sosai, everything seems boring to her Ga bata fita don dama Mafi yawancin fitarta school ne to yanzu suna hutu Ga ba qawaye, no more su sumee gashi babu daddy agida dazai dan debemata Kewa, mummy ce kuma ita sai ahankali The worst part of it kuma tunani da kewar wanda be damu da itaba daya maqalemata a zuciya yaqi barinta sukuni, fushi take dashi amma kuma idan da abinda tafi son yin arba dashi to shine Sau biyu mummy na gayamata sunyi waya da kaka harma da Deen din amma ko sau daya be ta6a cewa abashi itaba koba komai atleast su gaisa Dama haka yake? Tasan yanada ban haushi amma wannan is freeky more annoying Wani sa'in ma har mammaki take ba kanta idan tashiga irin wannan yanayin na tunaninshi, har tambayar kanta take wai meye ma dslilin liqemashi har haka? The last time she checked ita mace ce da bata cika damuwa da abu ba, abin ma wai namiji Ita irin matannan ne masu i don't care manner wanda class dinta ma baya bari kagane if she really cares din amma wannan yana neman gagararta Tsaki taja tana maida jan lower lip dinta ciki tareda cijewa _Am a big big girl_ _in a big big world_ _it's not a big big thing_ _if you leave me_ _but i do do know_ _that i do do will.._ _miss you much_ _miss you much 😔_ Lumshe idanunta tayi sai ganinshi tayi a idanunta yana wannan murmushin nashi mai fito da innocence dinshi _murmushi.. Kyauta ce_ _murmushi.. Baiwa ce_ _murmushi.. tsani ce_ _kyawu nee!_ _mai qarawa kyawu kyawuu!_ _Haske ne.. mai qarawa fuska annurii!_ _me matso da tazara yai kusa_ _mai zabura duk mai nakkasa_ _mai yad'a manufofi akusa_ _mai matso da nesa taxam kusa_ _somewhere.._ _somewhere.._ _there's someone who dreams of your smiling..._ Bude idanunta dasukayi ja tayi ahankali tana kallon p.o.p din, saikuma tayi murgina tayi ruff da ciki tana rungume pillow a qirjinta *meke damuna ne?* *kodai nafara hauka ne?* *am running mad* *am crazy* Ahankali tashiga raira wata waqar _what's wrong.. With the calmly me?_ _what's wrong with the classy me?_ _what's wrong with the rude me_ _why am i crazy over him?_ _I miss your smile but I miss my own even more._ _am waiting.. Am still waiting_ _Nothing hurts more than waiting since I don’t even know what I’m waiting for anymore._ _I’m not gonna miss you, I’m just going to wait_ _till you realize your mistake._... ✍️ Please kuyi Manage, mura ta addabeni 😤 naso page din yafi haka. Amun addu'a👏 Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:35 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *030* Da sallama yashigo gidan hannunshi riqe da leda mai layi layi guda biyu kowacce a hannu guda Qara sallamar yayi lokacin daya ida Shigowa tsakar gidan don yasan ba'aji na farkon ba don dama qaida ne idan zai shigo gidan sai yayi sallama sau biyu ko uku saboda yadda muryarshi take, sai yana kusa akeji Amsa sallamar kaka tayi daga cikin daki Hakan yasa yanufi dakin shima Sallama yasakeyi sannan ya shiga dakin Amsawa kaka tayi tana dagowa daga abinda takeyi "yauwa kyakyawa na har ka dawo amma kayi sauri" Zama yayi yana ajiye ledojin yana cewa "ai sama nadawo shiyasa, nagaji nasha yawo akasuwa ashe geron ya tashi duk inda naje haka suke cemun shiyasa kawai na haqura na siya sai kawai na auno waken tiya daya da rabi maimakon biyu" yafada yana tura mata ledojin Jawo ledojin tayi tana dubawa tana cewa "ohni ma'u, yanzu kuma qara mashi kudi akayi, ya akeso tallaka yayi don Allah? Yanzu mun siyoshi haka ya sukeso mu Saida bayan mun sarrafashi? Dama bawata ribar kirki akeci ba ina ga yanzu" Deen dai bece komai ba don baida tacewa Maida ledojin tayi bayanta tana cewa allah ya kyauta Sai kuma tamiqe tsaye tana cewa "yauwa, dama kai nake jira tundazu, bayan tafiyarka na bubbude kayyayakin nan nasu mummy, bari kaga abinda nagani" tafada tana dauko wata baqar leda ta dawo ta zauna sannan ta turamashi gabanshi tace "bude kaga ikon allah" Gyara zama yayi sannan yajawo ledar shima ya budeta ya leqa ciki Dan waro idanu yayi yana kallon abin cikin ledar sannan ya dago ya kalli kaka dake kallonshi itama "Kaka, ina kika samu wannan?" "ina fa bayan cikin kayan wadannan mutanen, nima ina gani na maida na ajiye nace saika dawo zan gwadamaka" inji kaka Fiddo kwalin yayi daga cikin ledar yana qara Bïñ sunan wayar dake rubuce 6aro2 a kwalin da kallo *Spark 8* Bude kwalin yayi yaciro wayar sabuwa gadagau sai shining take kalar dark blue sai bluetooth dinta da charger sai script dinta dake daga qasan kwalin Jujjuya wayar daketa daukar ido yayi tayi a hannu yana kallonta haka kawai zuciyarshi tabashi wannan aikin zee ne "kayi shiru bakace komai ba" inji kaka "me zance kaka? Kinsan ko nawa wannan wayar take?" "nawa" "dubu hamsin da takwas fa" Qwalalo idanu kaka tayi kamar zasu faddo daga raminsu tace "iyyee?? Dubu nawa?" "dubu hamsin da takwas shima banida tabbaci ko be qara ba abinda yasa ma nasani don kwanaki dana raka sanusi siyan waya kasuwar tsaitsaye muka tadda wani na cinikin second dinta wai dubu 30 amma mai ita yaqi bari anan ne ma naji yana fadamashi ainahin kudin sabuwarta" Kaka da Tundazu tayi kasaqe tana jinshi tace "to kodai dubu biyar da dari takwas yace kaine bakaji ba?" "kai kaka, ya za'ayi asamu irin wannan wayar dubu biyar? Ko vivo akwai wanda tafi hakan" Tafa hannuwa kaka tashiga yi sannan ta riqe ha6a "ni ma'u naga abinda yafi zare tsayi, dubu hamsin! Akan waya shegiya da kawai kira zakayi a kiraka?" Shiru Deen yayi yana qara Jujjuya wayar "ca6! Masu kudi na sha'aninsu, dubu hamsin da takwas! Ni ko ta takwas din saman ma ina iya saye? Wlh bazan iyaba koda kuwa filo nakeyi da kudi, waya idan tawuce dubu biyu to akai kasuwa, meye amfaninta? Ka kira a kiraka ne fa, abinda wannan zatayi shine rakani kashi zatayi to meye banbancin? Amma tsabar almubazzaranci shine za'a Fidda dubu hamsin harda takwas a siya wannan yar iskar wayar wanda da yatsu biyu ma ina iya riqeta, yo nabada dubu hamsin ai wlh Saidai abani wanda sai anyi kama kama za'a iya daukarta Ana babu kudi babu kudi ashe akwai su inda suke, yanzu fa wadannan kudaden tarin wani ne na shekara biyu amma a wofi anba yan danfara sun hadasu da molaqaqen qarfe, banda shirme ma aini banga abin burgewa ba a wayar nan, wayar kutare? Don fa su akayota saboda basuda yatsun dazasu latsa yar latse amma tsabar rashin sanin ciwon kai shikenan sai kowa yabi ayari, mutum da lafiyarshi ya maida kanshi kuturun qarfi da yaji, ni wlh masu ita basu burgeni, idan na gansu yadda kasan na kashesu da mari wlh, mtcheew wlh wasu mutanen basa ta6a wayewa" tafada tana maida numfashin maganar datayi Shidai Deen be tanka ba kamar yadda ya saba sai bin wayar daya cigaba dayi da kallo "yanzu ya kake ganin za'ayi?" inji kaka Ajiye wayar yayi saman kwalin yayi yace "Kaka kamata yayi a maida masu, Gaskiya abin yayi yawa, koko?" Shiru kaka tadanyi tace "kuma fa, amma mu ina muka san inda zamu qara ganin su?" "ai mummyn tace min zasu dinga dan zagayowa" "idan basu zagayo bafa?" "saina ajiyeta har mukoma school sai inba Zainab ta maida masu" "kuma fa hakane, Gaskiya gwara a maida masu din, abin ai yayi yawa ga wannan ga wannan, inma kyautarce zasu yimaka bada saisu baka kudin ba kayi wani abin mai amfani dasu ba?" "A'a kaka, bama buqata, abinda sukayi mana ma ya isa, ai sunmana hallaci" "kuma fa, tunda kaga dukkan zaman mu asibitin nan ko kwandala bamu kasheba da sunan jinyarka, Gaskiya sunyi mana hallaci don ba qaramin zuga kudi sukeba Asibitin kudi? Ca6 taci sunanta ai don komai na kudi ne, har wannan washe bakin dasuke mana da kulawa duk biyansu akayi, da ba'a biyasu ba basuyi ba, munafukai duk kar nake kallonsu, da zuwa mukayi bamuda ko sisi ko kallo bazamu ishesu ba, harda wannan baqar nass din mai fihilin tsiya kallonta kawai nake dashi kanshi daftan mai sanqo, wannan sanqon duk na son kudi ne, tsabagen munafurci har wani a kula sosai yake kamar irin yafini sonka dinnan, inbanda tsautsayi dama wazakagani a asibiti? Mtcheew Ai saika je ka ajiye da sunzo abasu tsiyarsu dama ba don Allah sukayi ba, don dai sunsan sune silar komai shiyasa suke wani nan nan damu don mu haqura, yo to dama ai sukeda alhakin biyan kudin asibitin tunda ta dalilin diyarsu abin yafaru. Mtcheew, bari naje na jiqa geron, kaima katashi kaje ka dauki abincinka yana kicin, babu kyau zama da yunwa rabonka da abinci tun shayin safe, kar qwalsa tazo ta kamaka in shiga uku" tafada tana ficewa daga dakin Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya mamaida komai cikin kwalin yasaka cikin ledar yana jin ba dadi Shi jima yake wama yasashi amsar kayan jiya din? Shi idan akwai abinda beso to shine alfarma, inba dole ba be amsa yafison yayi amfani da abinda allah ya horemashi, kuma jiyan ma don mummy ta sauya fuska yasa ya amsa don sosai take mashi kwarjini shiyasa tana Hade fuska yaji be iya yimata musu Adana wayar yayi sannan ya fito yawuce kitchen kamar yadda tace ya dauki kwanon abincinshi yawuce dakin shi *BAYAN SATI DAYA* Zee Batasan komeye kalmar *kewa* ba sai a cikin kwanakinnan Sosai takejin kewar da har abin yafara bata tsoro Batada damar yin wani kwakwarar motsi saiya fadomata arai Tasha tana abu amma ta shagala da tunaninshi ta manta da abinda takeyi Yanzu har tsoron saukowa cin abinci da mummy take saboda mafi yawancin lokuta Saidai taji mummy ta girgizata tayi sauri ta dawo daga duniyar tunaninshi sai taga ashe dining take Kokuma haka kawai taita murmushi kamar sabuwar kamu Mummy tayi maganar tayi fadan akan tafada mata idan wani abu ke damunta amma kodayaushe amsarta dayace, *babu komai* Kiran wayarshi kau datake tsanmmanin shigowarshi tun ranar dasuka rabu haryanzu shiru Tayi tunanin tun a ranar daddadare zai kirata don Saida ta samashi sim card har biyu a wayar kuma tayi mashi saving number ta amma shiru Dafarko tayi tunanin ko aranar be dubaba Hakan yasa ta yanke shawarar jira zuwa washegari sai gashi har aka wuni aka kwana shiru har zuwa yanzu da akayi sati daya Abinda bata fahimta ba anan shine, saqonne beje mashi ba koko yaje kawai sharewa yayi? Sau da dama saita dauki waya tashiga contact din ta tsaya tayiwa number quri taji kamar takira amma jin kanta da class dinta ya hana sai jima tayi taji haushin saya tun farko karde ace don tayimashi Hakan yayi wani tunanin daban ko ya raina class dinta Koyaya wayarta tayi beeping sai tayi sauri ta dauka hoping shine amma to her dissappointment data duba sai taga bashi bane Tun tana mashi uzuri dazai kira har abin yafara bata haushi Rannan saboda yadda kanta ya dau chaji da tunaninshi Batasan sadda ta goge number tashi ba cikeda haushi, jitake kamar ta bigi kanta don takaici Saidai ta goge number ne a wayarta amma tana nan daram a kwakwalwarta Wani sa'in idan tana latse latsenta awaya bata sanin lokacin da take rubuta number shi Saidai kawai taga ta rubuta, gabadaya duk tabi ta susuce ta rasa meke mata dadi Yanzu ma zaune take kan dining suna lunch tareda mummy Saidai kawai cin abincin take ba don dadi ba kawai komai ma yanzu haushi yake bata, tarasa meke mata dadi Dagowa mummy tayi ta kalli zee dake sipping ruwa dake cikin glass cup tace "kiyi da jiki kigama zaku fita da bala" Ajiye cup din hannunta tayi tace "to mummy" "kuma kafin kuje zaku biya supermarket kudan yimasu sayayya, naso ace dani za'a amma am busy don yau order na zai iso, kice duk ina gaidasu, kicema kaka insha allah zanshigo kwanan nan" Cokalin da tayi niyyar kaiwa baki ta dakatar ta dago tana kallon mummy ido waje Kallonta mummy tayi itama tace "ya dai?" "mummy, gidan... Kaka zani?" ta tambaya cikin son gasgata abinda kunnuwanta suka jiyemata "eh, ko da wani abu ne?" inji mummy tana kafeta da ido Saurin girgiza kai tayi ta maida kanta kan abincin dake gabanta Saidai turawa kawai take batareda halshenta na banbance mata taste din ba Tarasa me takeji, dadi ko akasin haka Jitake kamar karta je don shima shareta yayi dukda yanada hanyar dazai sameta amma kuma qasan zuciyarta cike take da dokin ganinshi, dokin ganin cute innocent face dinshi. *** Saida ta 6ata lokaci sosai wajen shiri kamar yadda ta saba don ita bata iya simple makeup dinnan ba, tafison ta gyara fuskar tafito fess kamar ka hadiye don kyau Fitowa tayi daga dakinta ta fara taka stairs tana saukowa qasa Takunta yasa mummy dake falo riqe da remote ta dago tana kallonta Sanye take cikin Arabian gown bubu style tasha adon pink agaba sai gyalen gown din pink data yafa akai ta maida jelolin abaya Hannunta na dama sanye da tsaddadiyar pink agogo sai qaffafunshi dake sanye da pink hill shoes sai yar jaka pink kamar an roqo mai shegen daukar ido irin ta goyawarnan mai dogon hannu ta goyata ta tsayamata daidai tsakiyar baya sai wayarta dake hannunta Dauke kai mummy tayi daga kanta acikin ranta tana tasbihi ga ubangiji daya hallici wannan baiwar tashi yayi mata komai daidai kamar ita tayiwa kanta Sosai take alfahari da diyar tata don duk inda mace mai jida kyau da aji takai itama takai, komai nata acan acan kamar ita tayiwa kanta Qarasowa wajenta tayi ta zauna bisa kujerar dake facing dinta "mummy am ready" inji zee Dagowa tayi ta kalleta sai kuma ta dauke kai tana cewa ta miqomata purse dinta dake kan centre table Tashi tayi ta dauko ta miqamata ta amsa Bude jakkar tayi ta fiddo wasu kudade tabata tana cewa "ki siyo fruits haka da drinks kafin ku wuce, extend my greetings to her kice nima zan leqo insha allah" Amsa zee tayi tana cewa "ok mummy" "karku dade, kinayin abinda yakai ki kujuyo, hope am clear" "to mummy" "Allah ya tsare" "amin mummy tafada tana miqewa tsaye ta dan sauko jakkar bayanta ta bude ta cusa kudin ciki sannan ta maida ta goye "saimun dawo mummy" "to allah ya kiyaye" Da amin ta amsa tana ficewa A harabar gidan ta hango bala wanda dama jiran fitowarta yake Da sauri yataso ya qaraso motar dazasuyi amfani daita ya bude mata back seat yana mata sannu da fitowa Amsawa tayi kamar yadda takeyi a yan kwanakinnan sannan tashige cikin motar tana gyara zaman bluetooth dinta ta cikin gyalenta Maida mata kofar yayi ya rufe sannan ya xagaya shima yashiga motar ya rufo kofar sannan ya tadata yafara reverse Kamo waqar datakeso tayi ta kunna tanaji ta bluetooth din kunnenta takoma cikin kujerar motar ta lafe tana saurare Dama haka take, sauraron waqa na daya daga hubby dinta musanmman cool music shiyasa tsabar sonsu datake har qirqirar nata takeyi wani lokacin, da zata shiga studio da ba qaramar fasaha zata zuba ba Saidai bashi ne gabanta ba kawai tana yine for fun Fita motar tayi daga gidan suka halba saman kwalta Kamar yadda mummy tace musu Saida suka biya supermarket sukayi musu siyayya sannan suka dauki hanyar unguwarsu Deen. 💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖 Tunda suka shigo unguwar taji zuciyarta ta chanza bugu Kalle kalle tashiga yi ta tinted window din motar kamar mai son hango wani abu Jin motar ta tsaya ne yasa zuciyarta ta qara gudu fiyeda kima "madam bari na d'an tambaya kar ace mun wuto wajen" inji bala cikin ladabi Kada mashi kai kawai tayi trying so hard to control her heartbeat Tana jinshi ya bude murfin kofar ya fita ya maido ya rufe Komawa tayi jikin kujerar motar tana lumshe idanu _ya sallam! Meke damuna ne? Meyasa zuciyata ke bugawa da sauri_ Tambayar da tayiwa kanta kenan Anya zuwan nan nata bazai jamata raini ba? Ta bashi waya da number ta aciki da tsanmmanin jin kira daga gareshi amma beyiba gashi kuma ta biyoshi har gida? Wannan ba zubda class bane? _ai ba zuwanshi kikayi ba, mummy ce ta aiko ki wajen kaka_ Wata zuciyar ta gayamata Hakan Kada kai tayi, yes mummy ce ta aikota kuma ba wajenshi tazo ba sai kuma ta furzar da iska takoma ta lafe a kujerar Bude kofar mazaunin drivern akayi Hakan yasa tadan dago idanu ta kalli bala dake qoqarin Shigowa "madam na gano, ashe ma mun dan wuto layin amma yanzu zamu koma" Bata ce komai ba sai maida idanunta datayi ta rufe tana jin yana sake tada motar Basuyi wata tafiya mai nisa ba taji motar ta tsaya Hakan yasa taji zuciyarta ta tsinke ta fadi Fita bala yayi daga motar ya zagaya ya bude mata kofar Saida ta hadiye wasu yawu dasuka taru a maqoshinta sannan ta zuro kafarta tafara fitowa Wani sanyayar iska ce ta bigi fuskarta Hakan yasa ta lumshe idanu ta sake budesu Kallon kofar gidan take, tabbass gidan ne don bazai iya 6acemata ba dukda Zuwansu daya "ina jin nan ne gidan, amma bari mu tambaya" inji bala Dakatar dashi tayi da "eh nan ne basai ka tambaya ba" Dan kallon wasu samari biyu masu wucewa sun wani sakarmata na mujiya tayi sannan ta dauke kai ta nufi kofar gidan bala na binta a baya da ledar kayan da suka siyo Da sallama suka shiga gidan amma shiru Hakan yasa suka qarasa ciki zee na qara sallama Jitayi ana amsawa daga cikin daki kuma ta shaida muryar kaka ce Shiru tayi zuciyarta na cigaba da gudu tana jiran taga ta inda za'a bullo "maraba!!" suka sake jin muryar kaka tana daga labule ta fito Jan burki kaka tayi tana qwalalo idanu ganin Hakan yasa zee maida nata qasa tana dan murmushi "wa zan gani kamar Zainabu?" tafada mammaki a fuskarta Murmushi zee tasakeyi tace "mune kaka" "lale lale da baqin ogas, yaushe rabo? Gaskiya yau muna da manyan baqi" tafada tana shigewa daki can kuma ta fito hannunta riqe da tabarma ta baza masu tana cewa "daki zafi nima sallah takaini ciki kunsan yanzu sirkawa akeyi ga zafi ga ruwa" Zama zee data cire takalminta tayi tana murmushi tace "ai ana zafi sosai... Ina wuni kaka" "lfy qalau lumi aminiya, kwana dayawa" Murmushi kawai tayi bata ce komai ba Shima bala gaidata yayi sannan ya ajiye ledar hannunshi kusada zee yace bari yaje ya jirata waje, Kada mashi kai kawai tayi ya juya ya fice Tashi kaka tayi tana cigaba dayi mata maraba tashiga kitchen can tafito da kofin silba mai murfi ta ajiye mata agaba tace "ga ruwa Zainabu abu mai tagwayen suna, kun shawo hanya dole maqoshi ya bushe" Murmushi tayi tadan ja kofin gabanta Saidai bata bude ba tace "Kaka mun sameku lfy? Ya mai jiki?" "wlh duk lfy qalau yar nan. Ya bayan rabuwa kuma? Mu bamu san inda kuke ba gashi baku sake zuwaba, munga kaya rannan amma ba hanyar Godiya tunda cikinmu babu wanda yasan ta inda zamu sameku" _shi jikan naki ya sani ai_ tafada a zuciyarta amma a zahiri murmushi kawai tayi "yasu mamar taki?" "wlh lafiya lau kaka, tana gaida ki tama so zuwa amma allah beyi ba" "ai ba komai wlh, kunga Deen kwarai mace mai kirki, kai allah dai yasaka da alhairi, bari na zubomiki abinci" tafada tana niyyar tashi Saurin Dakatar da ita zee tayi da "A'a kaka, alhamdullilah azumi ma nake" Dan waro idanu kaka tayi tana komawa ta zauna tace "azumi? Ca6 shiyasa baki sha ruwan ba ashe, amma duk mai azumi yau sai yaji a jikinshi wannan kwala rana haka masha allahu" Murmushi tasakeyi Firarsu suka cigaba dayi wanda kaka ce keyin kusan rabi da kwata zee sai murmushi take don sosai takejin dadin firar tata Suna ahaka sukaji sallamarshi wanda ke daidai da bugawar zuciyar zee Saurin kauda kai tayi daga kofar Shigowa ta maida kan jakkarta dake gabanta ajiye tana jin kaka na amsa mashi Jimm aka dan yi sai kuma taji kaka na cewa "qaraso mana, ita ce din dai" Sai a lokacin ta dago bata sauke idanun a koina ba sai cikin nashi Saurin Janye nata tayi tana runtse su gam _ya sallam!_ ta fada a zuciya Bata ta6a sanin tayi missing dinshi har haka ba sai yanzu, jitake zuciyarta na kumbura tana sacewa don shauqi Qarasowa Deen daya kafeta da idanu yayi kamar meson gasgata abinda idanunshi ke gani "wlh itace, ina sallame sallah naji sallamarsu bama su dade da zuwa ba" inji kaka Ida Qarasowa yayi ya cire takalminshi ya zauna kan tabarmar still idanunshi kanta Be ta6a jin ya ta6a missing wata hallita ba kamar ita, ganinta kuma yau ba qaramin tado mashi tsumin kewar yayi ba Dukda bashi take kallo ba tasan ita yake kallo don tana jin idanuwanshi akanta Hakan yasa taqi dagowa ta cigaba da kallon qasa tana wasa da zoben yatsarta Cool voice dinshi taji yana cewa "Kaka yaushe tazo?" Lumshe idanu tayi ta bude, ya Allah! Tayi missing komai gameda gayen nan, har muryar "basu jimaba wlh, nima abin yazo mun a bazata wlh kuma naji dadi sosai" Maida kallonshi yayi akan zee din dataqi sake kallonshi can kuma yace "yasu mummy?" Dan dagowa tayi ta kalleshi saikuma ta kauda kai tana dan murmushi "tana lfy, ya qarfin jiki?" tafada trying so hard wajen controlling muryarta "Alhamdullilah, longest time" Dan kallonshi kawai tayi sai kuma ta kauda kai tana jin takaicin maganar shi Wai longest time, da yaso da ya kirata ko gaisawa sunayi amma ya share amma har yanada bakin cewa longest time Haka kawai taji rashin kiran nashi na cimata rai, batama san tun ranar daya ajiye wayar be qara waiwayarta ba "to kaka bari mutafi" inji zee din tana kallon kaka avoiding Deen's gaze "haba badai tun yanzu ba Zainabu" Qoqarin miqewa tsaye zee keyi tana cewa "wlh kaka, mummy tace karmu dade ne" Tashi itama kakan tayi da zee da Tundazu yakasa janye idanunta akanshi "to ai mungode qwarai ma wlh, gashi dama azumi kike, to allah yasa asha ruwa lfy, kice ina gaida mamar taku sosai da sosai, ya kamata kyakyawana ka amshi lambar su yadda zamu dinga gaisawa" inji kaka Kada kai Deen yayi alamun to saikuma yajuya yashige dakin kaka Da kallon qasan ido ta rakashi sannan ta dauke kai ta duqa ta dauko ledar dasuka shigo daita ta ajiye gaban kaka tace "gashinan kaka ba yawa" "meye din? A'a wlh abin ai saiyayi yawa ga wancan ga wannan?" "Kaka dan allah ki amsa ba yawa kawai kayan marmari ne" Da farko qiyawa tayi amma daga baya saboda nacin zee ta amsa tana Godiya "dan allah ki miqamin godiyata gareta idan kin koma, insha allah zan kira ma da kaina mu gaisa kibashi lambar ki" Da to ta amsa kawai tana murmushi sannan tayi mata sallama ta nufi hanyar fita Daidai nan Deen yafito daga dakin kaka yaga ta danyi nisa ma "Kaka ina zuwa" Da to kaka tabishi tana kallonshi ganin ya nufeta Dukda tanajin alamun binta dayake Hakan besa ta nuna tasani ba bare ta tsaya Daidai tashiga zaurensu taji muryar shi na cewa "Zainab!.." Cak ta tsaya ba don ta shirya ba sai don tasirin da kiran yayi agareta sosai Qarasowa yayi ya tsaya bayanta yana dan basu tazara "Tafiya zakuyi?" yafada yana kallon bayanta don bata juyoba Ahankali ta juyo ta kalleshi suka kafe junansu da idanu without saying anything Ahankali zee ta motsa baki tace "eh, ko kanada matsala da Hakan ne?" Murmushi ya dan saki yace "A'a... Ga wannan" yafada yana miqamata wata baqar leda Kallon ledar tayi saikuma ta kalleshi da ayar tambaya Qara miqo mata yayi murmushi a fuskarshi Hakan yasa ta amsa ta bude tana leqawa Kanta ne ya sara ganin kwalin wayar data siyomashi ce Dagowa tayi ahankali tana kallonshi still da ayar tambaya "ki maidama mummy kice mun gode qwarai amma bazan iya amsa ba, dawainiyar da kukayi akanmu ta isa, muna Godiya. Dama tun ranar dana ganta na maidata na adana akan idan kuka zo kamar yadda mummy tace ko muka hade a school inbaki, mun gode qwarai amma bazan iya amfani da wannan ba, yanzu haka ma nayi wata so no need na damuwa, kinga saiki samin number mummyn don su dinga gaisawa kamar yadda tace and also na warware please ku daina mana dawainiya haka nan, the one you did is appreciated and we'll continue to appreciate it..." Saka hannu yayi a aljihu don lalubo wayarshi batareda ya lura da irin kallon da zee ta kafeshi dashi ba Zaro yar qaramar wayarshi keypad qirar itel yayi ya miqamata yana cewa "here, samun number" Kallon nata ne ta janye daga kanshi ta maida akan yar ficikar wayar hannunshi tana feelings din da bata ta6a jin irin shi ba kuma ta rasa taqamaimai me takeji Haushi? Takaici? Dana sani ko embarassment? Ashe duk haukan ma datakeyi na jiran kiran shi ita kadai keyi? Ko ta6a budewa beyi ba, wai ya adana ta don ya maida mata? And qarin gishiri a ciwo wai tabashi number mummy don su dinga gaisawa da kaka bama tabashi tata ba A'a ta mummy wato ita kadai ke haukanta he Don't care a bit about her Wani abu mai daci2 taji ya ziyarci maqoshinta tana jin kamar ta dora hannu aka taita ihu Ganin tayi tsaye tana kallonshi dakuma irin kallon datake mashi yasashi dan wara mata oily eyes dinshi yana cewa "are you ok?".... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:35 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *032* *BAYAN KWANA BIYU* Shiru zee tayi takasa cewa komai sai ma wasa datake da zoben hannunta "am talking to you Zainab" "mummy babu komai fa" "babu komai kika koma haka? Just look at yourself amma kice babu komai? Ke kanki kinsan you're lying" Sauke idanunta tayi tana kallon yatsun hannunta cikin rashin ta cewa Dawowa mummy tayi ta zauna kusada ita tana kallonta "Zainab..." Dagowa zee tayi ta kalleta da idanunta dasuka fara salqin hawaye "meke damunki? Are you sick?" Girgiza kai tayi ahankali tana maida kanta kasa, ita kanta da tasan abinda ke damunta datafi kowa murna "Zainab am your mother kuma bakida kamar ni.. Bakida wanda zaki fadawa matsalar ki kamar ni don haka karki 6oyemin komai, ki gayamin komai I can understand" Yadda mummyn tayi magana tenderly yasa zuciyarta qara tsuma kan kace me sai hawaye Kamo hannunta guda mummy tayi tana murzawa ahankali cikin sigar rarrashi wanda ta rabu dayi mata Hakan yasa zee kwantowa a kafadarta tana cigaba da hawayen Hannu mummy tasa around her tayi mata side hug wanda Hakan yasa taqara narke mata "tell me" inji mummy Sniffing tayi sannan tace "mummy am bored, am lonely. Banajin dadin komai, ina kadaici sosai" Shiru mummy tayi can kuma tace "shiyasa kika takurawa kanki har haka? Duka yanzu kwana nawa ya rage kuyi resuming school?" "dukda haka mummy, am very lonely banida wanda zamu dinga hira, am always bored" Ajiyar zuciya mummy tayi sai kuma tace "ok, yanzu ya za'ayi? Kina son insamo miki training class, kona girki ko kwalliya or something like that?" _no i want to see Deen_ Abinda tafada a zuciyarta kenan amma azahiri tace "no mummy, I want to travel" "travel? Ina?" Dagowa zee tayi daga jikin mummyn sannan ta marairaice fuska "Ruma, don Allah mummy kibari intafi" Sakin baki mummy tayi tana kallonta "ke kecewa zaki Ruma da kanki yau? Wonder shall never end" Dan tura baki zee tayi tace "mummy nafa rabu da zuwa" "kin rabu da zuwa amma wancan zuwan qarshen ya kikace? Cewa fa kika yi baki qara zuwa kuma ma bazan bari kije ki takurawa mutane da daukar maganarki ba, never" Sake marairaicewa tayi don sosai takeson tafiyar ko zata manta da wannan annoying fring din "mummy please, nafa shiryu baki gani ba" Sosai maganar zee taba mummy Dariya amma sai tayi dan murmushi tace "kin dai shiryu and also duka yanzu saura kwana nawa kuyi resuming? Da zuwan ne ai da tun farkon hutun ya kamata kije amma yanzu kije hutu be kai sati biyu zai qare ba wannan zuwa hutu ne?" "mummy ko sati daya ba sai nayi ba na dawo? I promised mum baxanyi komai ba nafa shiryu mummy na daina abubbuwa marar kyau" Harararta mummy tayi ta tashi ta nufi closet dinta "kinji mummy? Please.." Batareda mummy ta juyo ba tace "kije zan gayawa daddy duk yadda yace shikenan" Dadi ne ya ziyarci zuciyarta taji kamar tayi ihun murna don tasan idan daddy ne batada case dashi amma sanin halin mummy abu kadan zaisa ta chanza ra'ayi yasa ta danne tace "to mummy, allah yasa ya yarda" Juyowa mummy tayi ta gallamata harara "kamar duka kenan, salan kije ki kallalameshi kafin na gayamashi kiga idan ban soke tafiyar ba" Daga hannu zee tayi tace "A'a ni bazan kirashi ba, how dare me" Ta6e baki mummy tayi ta cigaba da abinda take Tashi zee tayi taimata sallama ta fita cikin zumidin tafiyar tanajin atlast zata rabu da kadaici bare har tunanin Deen ya samu gurbi a zuciyarta don ita duk tunaninta kadaici ke jawo tunanin nashi Tana shiga daki ta murza key ta nufi bedside locker dinta ta dauki phone dinta ta zauna can qarshen gado ta lalubo number daddy ta dannamashi kira Ba'a daga ba har Saida ta yanke tana qoqarin sake kira kiranshi yashigo Cikin zumudi ta dauka ta kara akunne "daddy na!"tafada cikin tsananin murna Dariya daddy yayi daga can 6angaren yace "na'am daughter din daddynta" Murmushi tayi tace "daddy I missed you!" "missed you more and more jewel, amma alhamdullilah am coming back soon, me zan miki tsaraba?" "komai ma daddy don kafini sanin abinda zai sani farinciki" "really? To angama I'll make you happy insha allah" "Allah ya yarda daddy" Sai kuma tadanyi Jimm sannan cikin shagwa6e murya tace "daddy?" "yes? Daddy's pet" "daddy am lonely, banajin dadin komai kullum kasa barci nake har kuka nake yi ma" tafada cikin narke fuska "subhanallilah, but why?" "am lonely, every thing seems boring gashi babu school kullum zaman gida na gaji" tafada kamar zatayi kuka "oh please kar Kiyi kuka kinji? Ba gashi na kusan dawowa ba? Idan nadawo kullum saimun fita shaqatawa, idan bazaki iya jira bama gobe balarabe ya fita dake duk inda kikeso Kiyi shopping and every other thing that will make you happy uhm? Nakusan dawowa everything will be ok" 6ata fuska tayi don ba abinda takeso ba kenan "Nidai daddy duk wadannan baxasuyi ba, na gaji ne da komai da garin, I want to go to Ruma, please" "Ruma kuma daughter?" "yes dad, please! Kaga na rabu dazuwa" "to yaushe zaki dawo idan kika tafi yanzu, and kun kusa resuming ai" "daddy yanzu saura kwana 12 muyi resuming, Kaga sai inyi 1 week acan kuma dama naji ance aunty Feenah tadawo kaga zamu ga juna dama rabona da ita tun kafin ta tafi a waya ma bamu cika magana ba, please kabarni naje daddy just 1 week zanyi nadawo, zanji dadi sosai zanyi farinciki" inji zee don tasan idan akwai abinda yakeso to farincikin ta ne Ajiyar zuciya taji ya sauke daga can 6angaren yace "Alright then, kin gayawa mummyn ki?" Cikin zumudi tace "eh daddy, tace ma zata kira ka ta gayamaka" "ok idan takira zance mata tabarki kawai, yaushe kikeson zuwa?" Ihun murnar da batayi ba dazu tayi tana cewa "yes! Thank you my sweet daddy" Murmushi mai sauti daddy yayi yace "you're welcome, nace yaushe kikeson zuwa?" "dad ko zuwa gobe haka, please kace tabarni natafi gobe" "to shikenan an gama princess" "yauwa daddy kuma fa karka cemata munyi maganar dakai don Saida tayimin warning akan Hakan, kawai kayi pretending bakasan da maganar ba if not she'll slaughter me" Dariya daddy yayi sosai a dayan 6angaren sannan yace "to angama dear, sai kuma me?" "shikenan sweet daddy" "to shikenan, I'll pretend bansan da maganar ba and also zanmiki transferring din sum amount sai ayiwa mutanen Ruma tsaraba" Cikin jindadi sosai tace "thank you so much daddy, muah! I love you" Cikin Dariya yace "love you more sweetie" Da haka sukayi sallama ta koma ta jingina da gado beaming with smiles tanajin atlast zata rabu da qaya Duk a tunaninta zama lonely ke kawo tunaninshi shiyasa ta yanke wannan shawarar na tafiya Ruma tasan ko yaya ne she'll feel better from what she's feeling now Da wannan tunanin ta kwana ta tashi, haka taita baza kunnuwa taji me mummy zatace gameda tafiyar amma shiru Tun tana jira harta sire don har magrib shiru batace mata komai ba Sai bayan isha'i suna tsaka da dinner mummy tace mata ta shirya gobe zasu wuce Ruman Dukda da farko fushin sharetan da mummy tayi take Hakan be hanata yin murna ba A cikin daren ta harhada kayanta wadanda zasu isheta na zaman sati da tarkacen kayan amfani na yau da kullum Medium trolley guda tacika ta ajiye gefe sannan ta kwanta tana Allah Allah gobe tayi ta shilla *WASHEGARI* Sai wajajen 12 rana suka bar gidan a motar da bala ke ja suka nufi garin Ruma dake qaramar hukumar batsari bayan mummy ta gama cikasu da tsarabobi da zata kaiwa yan uwanta mutanen Ruma Tunda suka kamo hanya zee keta sauke Ajiyar zuciya tana fatan Hakan zai ragemata abinda takeji acan din Bluetooth ta maqalawa kunnenta wanda cool music ke tashi a cikinshi ta dawo kusada window ta jingina tana kallon yadda suke wuce dajika da gudu, sosai abin ya nishadantar da ita don koina luff yake da ciyawu sunyi green abin sha'awa abunka da damuna wannan scene din ya mantar da ita abubbuwan dake damunta a zuciya ta kama jinta wasai Anata sallar azahar suka isa cikin garin. Direct gidansu mummy suka wuce wanda keda girma ba laifi kallo daya zakayi mashi kasan na masu rufin asirine sosai Saida yayi horn sau uku sannan aka bude qaramar kofar gate din aka leqo sai kuma aka koma can aka shiga bude dan madaidaicin gate din Shigar da motar bala yayi, yayi parking a parking space din wajen da beda girma sosai sannan ya fito ya zagayo ya budemata Saka bluetooth din data ciro daga kunnenta tayi cikin jakka sannan ta zuro kafarta tafito daga cikin motar Shaqar iskar garin tayi sannan ta fesar tana jin wani dadi har cikin zuciyarta Rataya jakkarta tayi a kafada ta saka siririn spec dinta sannan ta nufi cikin gidan yayinda bala da maigadi da shima ya qaraso wajen ke qaqaniyar ciro kayanta dake booth Knocking tayi a main door sannan ta murda handle din ta bude tashiga bakinta dauke da sallama Da farko tayi tunanin babu kowa a falon Saida ta qarasa shigowa ciki sannan taga wata budurwa kwance cikin kujera waya kare a kunnenta tana kallon zee din data shigo Murmushi zee tayi mata itama ta dan maida mata martani sannan tace "I'll call you back" Daga nan ta katse kiran Qara dagowa tayi ta kalli zee dake kallonta itama fuska dauke da murmushi "mutanen katsina ne a wannan tsakar ranan?" tafada cikin maqaqqiyar murya datafi kama data mage Qarasowa zee tayi ta zauna a kujerar dake facing dinta "yeah, hope mun sameku lfy" "lfy lau" inji budurwar sai kuma ta maida kanta kan wayar ta Bata damu ba don tasan wacece Feenah da hallayenta kuma wai nan don ma suna d'asawa da zee saboda halinsu daya kusan zuwa daya yasa ta tsaya ta tankamata haka Feenah itace autarsu mummy, mace mai shegen yanga da jin kai Ga tsiwa don bata ragawa kowa, duk cikin 'ya'yan *Umma* wato kakar zee babu wanda ya kaita kyau Tanada kyau irin na asalin rumawa ga jiki dan d'as daidai ita. Feenah irin classic ladies dinnan ne masu ji da wayewa don tama lunka zee ta shanye a wannan fannin. Tanada fada sosai ga batason raini kwata2 shiyasa basa shiri da 'ya'yan yayyanta dasuke a matsayin 'ya'yanta itama sai zee da halinsu yakusan zuwa daya don dama kowa cewa yake ita ta gado a halin jin kai da yanga da gayu Feenah yar gayu ce ta qarshe mai jida wayewa, yanzu haka ko sati batayiba da dawowa daga france inda take karatu wanda dawowar ta din din din ce don ta riga ta kammala karatun "kunyi graduating, allah ya sanya alhairi" Dagowa Feenah tayi ta watsamata wata harara tace "Sai yanzu zaki yimin allah sanya alhairi? Kwana na nawa da dawowa amma ko kira bayan am very sure kinsan da dawowata" "kai Aunty Feenah! Shiyasa fa na taso takanas nazo don nayimiki, ai kinfi qarfin nayimiki ta waya shiyasa na shiryo na taho" Wata hararar Feenah taqara watsamata tace "eh, maidani shashasha wacce batasan abinda take ba, yarinya gaba na aka haifeki tun kafin kisan kanki nasan basaja, ehe" Dariya zee tadanyi tace "haba uwas! Kar kisa ajimu aimana Dariya, ni da uwata haka muke🤞🏻babu mai jinmu" Wani kallon sheqeqe tayi mata tace "ku nawa kuke Hakan 🤞🏻? Keda waya ma Dakyar kike kirana sau daya a wata kuma ki kirani da uwa? Ina kika ta6ajin haka?" "yanzu dai komai yawuce aunty Feenah, allah ya huci zuciyarki ai tsakanin uwa da diya sai allah, shiyasa ma nazo takanas don na goge laifina" Harararta Feenah tayi ta kauda kai Dariya zee tayi tace "tuba nake ran uwata ya dade" Dan ta6e baki tayi a yangace sannan tace "ya wuce.. How's your studies?" "Alhamdullilah aunty, hutu ma muke amma zamuyi resuming very soon" "Ayyah, allah ya taimaka" "amin... Ina hajiya granny?" "hmm tana can dakinta yanzu ta koroni da chazbi" Tashi zee tayi tana Dariya "kin ta6ota kenan?" "wai don nayiwa wannan qazamin yaron sultan tsawa shine ta koroni ita mai jika" Dariya zee tayi ta nufi hanyar dazai sadata da cikin main gidan tana cewa "Allah dai granny nayi missing dinta ai" "ai gaki gata wannan karon ma da fada zaku rabu i bet you" Dariya Kawai zee tayi ta shige itakuma Feenah ta maida hankalinta kan wayar ta Direct part din Umma ta wuce cikeda dokin ganin ta Da sallama tashiga falon umman tana cewa "granny! Granny! Am back!" Jin shiru yasata ajiye jakkarta a sofa tana qara cewa "granny! Wai ina kike..." Bayyanar umman ya katseta saitayi wajenta aguje ta rungumeta tana Dariya Qoqarin kwace kanta take daga riqon zee tana cewa "wai wace yar malfar uba ce wannan?" Dagowa zee tayi tana Dariya "kai Umma, nice yar malfar uba?" "yo banda shaqiyanci saiki shigo min gida ba sallama ba komai sai iface iface, shegiya mai kama da uwarta ta falo, dama yanzu itama nagama zaneta saura ke wlh" "haba dai, ai muda duka sai ruwan sama kiji ingayamaki, don ma kinsamu anzo ana murnar ganinki? To nafasa murnar ma" tafada tana komawa kan kujera ta zauna ta rungume hannaye a qirji tana kumburi "kanki akeji" inji Umma tana qarasowa itama ta zauna "wai yama naga qaffafunki a gidan nan? Jinake ke da kanki kikace ke da nan har illa masha allahu" "yo dama in don takece wazai zo? Ni wajensu kawu nazo da Aunty Feenah" "haka fa, ai kin aikata, tunda ga uwarki dakikayo gadon komai nata ta dawo ai dole kema kizo yadda zaku taru ku samun ciwon kai, to wlh kubi a sannu, yanzu ba da bace yanzu kana yimin abinda bemun ba zan zane mutum radam da wannan charbin" tafada tana daga mata chazbahar hannunta "inyee! Su granny an qaro wulaqanci, to bari na kama kaina, nama fasa zama dakinki dakin Aunty Feenah zan sauka, kar kin tashi cikin dare kin kasa barci ki juya kiga ina nawa cikin kwanciyar hankali kiji haushi kihau zugamun ita" tafada tana miqewa tsaye tana wucewa dakin Feenah dake kusada dakin Umma tana cewa "mutum yayo tafiyayya yazo ganinka ko sannu da zuwa bare Ayi maganar ruwa saima maganar charbi da aka tareshi dashi, kai wannan grannyn her wahala is too much" tafada tana shigewa dakin "eh zaggani dakyau kinji? Ja'ira mai zubin mami water idan abin Gaskiya ne Kiyi yaren dazan gane mana kuma anqi ayimiki sannu da zuwan, dake da sannu da zuwan na hada ku nayi muku qumuss, dama zuwa na kika yi da zan wani fara yimaki maraba, kijuya ki koma inda kika fitomana kiga wazai damu, aikin banja kawai" tafada tana tashi ta koma dakinta itama tana cigaba da surutai Bata dade da shiga ba Feenah ta shigo ta tararda zee tafito daga toilet daure da alwala Bata cemata komai ba sai wucewar datayi kan gado ta zauna Qarasowa cikin dakin zee tayi tana gyara yafin gyalenta "Aunty Feenah, ba'a shigo da kayana bane?" "suna falo" inji Feenah "kai Aunty Feenah, shine ko ki taimaka ki qarasomin dasu" Wani kallon up and down tayi mata ta kamar dakai batareda tace komai ba Wucewa zee tayi closet dinta ta zaro daya daga cikin hijjabin Feenah da sallaya tana cewa "baqonka dai annabinka Aunty" Ta6e baki Feenah tayi tace "su ru6e a falon indai ni zan qaraso miki dasu ciki" Zee bata qara cewa komai ba ta kabbara sallar zuhr daya riskesu kan hanya Lokacin da tagama Feenah bata dakin Hakan yasa ta miqe ta cire hijab din ta linke ta maida da sallayar sannan ta yafa gyalenta ta zauna gefen gado ta dannama mummy kira don fadamata isarsu Saida tagama wayar daita sannan ta bugama daddy shima ta fada mashi sun dan dade suna fira sannan sukayi sallama ta tashi ta fita Falon farko tafara komawa ta dauko kayanta ta kawosu dakin Feenah sannan ta bude jakkar tsarabobin datayi ta warewa kowa nashi sannan ta tashi ta fita da nasu kawunnanta Gidan dama part uku ne, na farko na kawu yusuf yayan mummy yanada mata daya da 'ya'ya hudu Na biyu na kawu Umar qanin mummy mai bimata yanada mata shima da 'ya'ya biyu Sai na ukun part din Umma wato mahaifiyarsu mummy inda take zaune da Feenah don dama' ya'yanta hudu rayyayu mijinta kuma tun Feenah na qarama allah yayi mashi rasuwa Part din kawu yusuf tafara zuwa Tun daga bakin qofa yaran suka tareta sunata tsallen murna Itama zee rungume su tayi tana Dariya don Allah yayi ta da son 'ya'ya sa6anin Feenah da bata son 'ya'ya sam shiyasa yaran su kawun basa shigemata don sunsan sauran Tare suka qarasa cikin falon sunata tsallen murna suna ina tsarabarsu Zama tayi tana dora sultan akan cinyarta tana Dariyar musun da sukeyi akan wa za'a fara ba tsarabar Ahaka mamansu tafito ta taddasu, riqe baki tayi cikin mammakin ganin ganin zee kamar daga sama Qarasowa tayi tana tsawatarwa yaran akan su rufewa mutane baki sun bi sun cika mutane da surutu Duk shiru sukayi kowanne na turo baki gaba "A'a Aunty Raliya, kawai sai ki hana yara taryar yayarsu, kai kowa yazo, line up according to your age sai na baku" Kamar jira suke sai suka taso cikin zumudi sukayi layi kowa fuska washe Nan tashiga ciro tsarabar su tana basu daya bayan daya kowanne murna da Godiya Sai da tagama basu sannan Aunty Raliya ta kada kansu ta korasu dakin su ko kunnensu zasu huta sannan ta juyo kan Zainab "zee baby! Saukar yaushe? Har angama fushin? Ina alwashin kuma?" Dariya tayi tace "hmm kedai bari Aunty ai haryanzu alwashin na nan daram dam yanzu ma ai ba zuwanku nayi ba zuwan Aunty Feenah ce" "to? Muma ai bamu gayya, can ku qarata daga ke har Feenar dama ina ciki daita dazu ta gigitomin auta to wlh ki gayamata ta kiyayi haduwarmu" Tashi zee tayi tace "A'a nan fa daya, gwara ki sameta da kanki don waqa a bakin me ita tafi dadi, ina uncle?" "ana wajen aiki, yasu Aunty maimunar?" "tana can lafiya lau tana gaidaku ga wannan bari nawuce part din kawu umar" "to? Harda mu tsarabar? Gaskiya mun gode qwarai allah yasaka da alhairi" Da amin ta amsa tana ficewa daga dakin tabar part din tawuce dayan part din na kawu umar Suma a falo yaran suke suna homework Jin sallamarta yasa duk suka dago Kamar yaran kawu yusuf suma da gudu suka tashi suka taryeta cikin murna Mamansu ma murmushi take na farincikin ganinta tana cewa "yau agari inji maqi baqo?" Qarasowa zee tayi ta zauna tana murmushi Gaidata yaran suka shiga yi don sunfi yaran kawu yusuf nutsuwa ko hayaniya basu cika ba Amsawa tayi tana shafa kansu tana tambayar su karatunsu duk suka amsa da alhamdullilah sannan suka koma suka dauki littafinsu dasuke homework suka shige ciki don dama mamansu ta saba musu da sunga baqi to su shige ciki bayan gaisuwa Nan suka shiga gaisawa da mamansu da zee takira da Aunty maijidda Kwata2 batada surutu kamar Aunty Raliya Hakan yasa bata jima ba sosai part din tafito bayan ta basu tsarabar su suma Part din Umma takoma ta tarda tana sallar asr da aketa kira Itama wucewa toilet tayi tai alwalla sannan tazo kusada ita ta gabatar da tata Daga nan suka shiga fira inda yawanci fadan jika da kaka ne Anan ta shiririce har magrib, dama bala tun bayan asr yayi sallama dasu ya juya A dakin Feenah takoma tayi magrib Da isha'i sannan tafito riqeda tsarabar Umma takai mata nan ma da fada aka rabu sannan tafito daga part din ta shi shiga part din kawunanta don su gaisa kasancewar sun dawo Anan duk ta shiririce sai can wajajen 9pm takoma part din Umma Dakin Feenah takoma inda ta tarar daita lafe kan gado rungume da pillow tana waya cikin muryar da ba'aji bare ka tantance me take cewa Kallonta tayi taga sai wani lumshe idanu take murmushi yaqi barin fuskarta Tayi mammaki sosai da Hakan don Aunty Feenah ba ma'abociyar murmushi bace da wuya ka ganta tana fara'a don koda yaushe a wuya take jira take qiris ka ta6ota ta sauke maka kwandon bala'i batada haquri sam yadda kasan zawo Qarasowa tayi ciki ta bude closet ta ciri towel ta rage kayan jikinta ta daura sannan tawuce toilet Tadan jima sannan tafito tana makyarkyatar sanyi don garin yau da iska sosai gashi dama su cikin damuna ana yawan yimasu ruwa ba kamar cikin katsina ba shiyasa weather dinsu yafi nacan sanyi Saida tagama shafe2nta sannan ta saka thick night gown ta hawo gadon ta kwanta Har a lokacin waya Feenah keyi cikin qasa qasa da murya sai sakin siririyar Dariya take every now and then Deen ne yafadomata arai, dama kuma yana ranta don yau ma wuni tayi dashi arai don ba taqi ba zuciyarta damar tsayawa tunaninshi shiyasa taqi zama bata nan bata can don da tadan nutsu zai fadomata arai Qara qudundunewa tayi cikin bargon tanajin kewarshi na dawo mata sabuwa, babu abinda ya chanza a abinda take ji game dashi saima abinda ya qaru Tana ahaka har Feenah tagama wayar ta ta gyara kwanciya ta kwanta Shiru koina ya dauka don dare yayi sosai Saidai ko alamun barci babu a idanun zee, wannan dai tunanin nashi ya addabi kwalwarta kamar yadda yasabayi duk dare Ta dade ahakan jin bazata iya jurewa ba yasata kiran sunan Feenah Shiru, tasake kira hoping batayi barci ba Juyowa Feenah tayi tana fuskantarta tana kallonta da idanunta dasuka fara jin barci "ya akayi ne? Dama bakiyi barci ba?" "eh Aunty, please magana zamuyi" tafada not sure idan ya kamata ta gayawa wani amma ai taji ana cewa problem shared is problem solved wata qila zata bata haske akan yadda zatayi ta rabu da abinda ke damunta Kallonta Feenah ta tsaya yi na wani lokaci sannan ta muskuta ta tashi zaune ta jingina da jikin gado ta harde hannayenta a qirji tace "yes? Inaji" Itama tashi tayi ta zauna tana fuskantarta amma takasa cewa komai "idan bazaki iya magana ba inkoma in kwanta banson wulaqanci" inji Feenah tana hade rai Ajiyar zuciya zee ta sauke sannan tace "dama Aunty, tambayarki zaniyi. Dan allah idan mutum ya kasance koda yaushe yana tunanin abu duk motsinshi saiya tuna da abin har ya hana shi barci wani sa'in, me Hakan ke nufi kuma tayaya mutum zai iya yakice tunanin a ranshi?" Shiru Feenah dake sauraronta Tundazu tayi tana Kallonta irin kallon tuhuma sannan itama ta sauke Ajiyar zuciya itama tace "Wani abu, shi abin menene? Mutum ne koko?" Shiru zee tadanyi sannan tace "eh asa mutum dinne" Harararta Feenah tayi tace "munafuka, gwara kifito kimin gwari2 yadda zan gane, mutum dan tatsitsi dashi sai gulma, mtcheew" 6ata fuska zee tayi tace "kai Aunty, munafurcin me nayi?" "kin fini sani ai, to bari kiji koma menene abin sonshi kikeyi, koma waye mutumin you're in love with him kuma babu yadda za'ayi ki yakiceshi a zuciyarki, the more kike qoqarin yakiceshi the more zai qara liqewa don haka the best solution is Kiyi accepting soyyayarshi" Tunda Feenah tafara magana taja dabaya tana Kallonta baki bude "w.. What?" tafada unbelievably "yes, sonshi kike koma wanene, that's one of the symptoms of love, you're in love Zainab" Qara jada baya tayi tana girgiza kai "no.. No.. It can't be"... ✍️ Juma'at mubaraq in advance ? 🌜 Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:35 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *033* "No, it can't be. Haba Aunty ya zakice haka? So fa? This is totally impossible" tafada cikin qaryata zancen Tayaya xa'ace tana son Deen? Deen fa, of all people ta rasa abin so sai Deen? Impossible! Tsayawa Feenah tayi tana kallonta sannan tace "bari kiji, nothing is impossible indai love is involve, shi so babu ruwanshi da wanda ya cancanta da wanda be cancanta ba kawai daya tashi kama mutum kama shi yake batareda duba cancanta ba, zee you're in love ko kinqi ko kinso don gayanan rubuce vividly a idanunki so zaifi maki kidawo hayyacinki tunda wuri kibar yaudarar kanki" "Aunty Feenah, baki san fa wa muke magana akai ba, da kinsani da kema kin qaryata Hakan da kanki, how on earth zan fada soyyayar Deen? Kinsan shi kuwa? Kwata2 beyi matching qualities danake nema a namijin da zanso qarasa rayuwata dashi ba, that annoying being? That timid mouse? How? When? Why?" Dariya Feenah tayi tace "kalli yadda kika firgice akan wannan yar maganar" "har haukacewa ina iya yi akanta Aunty, kinsan ko dawa kike dangantani kuwa?" "ban saniba kuma banson sani, abinda nasani shine you're in love with koma waye mutumin, gashinan rubuce 6aro2 a fuskarki kuma abubbuwan da kika fadamin early na daya daga cikin alamomin fadawa soyyaya, bari kiji kadan daga alamomin Soyyaya tana zuwa ma mutum ta siga daban2 Na farko if you're in love with someone koda yaushe zai kasance maqale a cikin zuciyarki, idan wani abu kike zaki dinga wondering shi me yakeyi, kiji kamar a hasko maki shi ki ganshi, abin nufi anan koda yaushe yana maqale da zuciyarki dashi zaki dinga kwana kina tashi Na biyu kunya, wasu yana zuwa masu da kunya, kiji bazaki iya hada idanu dashi ba and if you do bazaki iya jurar kallonshi eye-eye na tsawon lokaci ba Zai kasance duk lokacin da kuke tare zakiji kamar ku kadai kuka rage a duniyar babu sauran wasu inma akwai kin manta da wanzuwarsu haka zalika idan bakwa tare zakijiki so empty kamar kin rasa wani muhinmmin abu na sashenki Zakiji kina tausayamashi fiyeda qima, bakya qaunar wani abu ya sameshi idan kuma ya sameshi kiji kamar ke abin yasama koma kifishi jin radadin abin kiji kamar ki cire abin daga jikinshi ki maido naki Akwai changing of heartbeat ma, idan akwai soyayya duk lokacin da kuka kusanci juna ko kuke tare sai bugun zuciyarki ta chanza Duk damuwar da kike ciki arba dashi batareda ma kunyi magana ba zakiji kamar bakida sauran damuwa a duniyar nan Komai nashi burgeki zaiyi koda ba abin burgewa bane Shaquwa ta sosai da sosai zata shiga tsakaninku inda rabuwa a lokacin will hurt you both physically and emotionally... Ke signs din soyayya are so much to be mention, so very much don idan natsaya lissafa miki sai mu kwana a zaune ni kuma barci nakeji' Zee data maidata t.v Tundazu takasa magantuwa don kamar mai duba, maganganunta sunyi matching da abinda takeji sosai amma still this is impossible Tayaya za'ayi ace tana son Deen? Classic girl kamar ta ta bige da son Deen Deen beda qualities din datake bid'a tattare da namiji Zata iya cewa daya kawai yake dashi cikin siffofin namijin datake fatan aura shine KYAU Yes yanada kyau, a wannan ga6ar bazata ja ba don duk kushen mai kushe bazai iya kushe kyawunshi ba Yana da kyau mai sanyi da tafiya da zuciya farat daya Tana son namiji mai kyau amma ba kyawun kadai ba Tana son namiji mai jida kyau da naira, jarumi mai jida kanshi, very Classic handsome guy abin nuni ga kowa Yadda take Classic dinnan itama tana son Classic guy irin ta dan kwalisa mai ji da gayu da qasaita Acikin abubbuwan data lissafo abu daya Deen ke dashi wato kyau amma duk kingin bedasu then how on earth za'ace tana sonshi "Aunty Feenah, wataqila kinyiwa abin bahaguwar fahimta ne, Yes ni dashi friends ne kuma akwai Shaquwa sosai a tsakaninmu wataqila shiyasa nake missing dinshi amma tayaya Hakan zai zamo soyayya? Beda qualities din my dream man kwata2 so kima bar kawo batun soyayya aciki" Tunda tafara Feenah ke mata kallon up and down fuska a yatsine sannan taja tsaki tace "banda ke shashasha ce ina kika ta6a ganin an qulla abota tsakanin namiji da mace an wanye lfy? Babu wata alaqa dake tsakanin namiji da mace da babu soyayya aciki muddin ba muharraman juna bane Kosu duka basu kamu da son juna ba daya zai kamu kamar yadda nake zargin ke kadai kika kamu a naku alaqar Bari kiji duk namijin dakika gani yana abota da mace to ki bincika is either suna son juna ko daya na son daya aciki don a jadawalin alaqa dake tsakanin namiji da mace babu abota, ba yadda za'ayi ayi abota zalla tsakanin mace da namiji that's impossible Dan haka ki nutsu Kiyi tunani dakyau ki banbancema kanki abinda kike ji a zuciyarki don the earlier the better, soyyaya muguwar abu ce wanda idan ta juyamaka other side dinta sai kayi nadamar zuwanka duniyar baki daya, ina magana ne akan experience bawai kara zube ba, nasan soyayya ciki da bai, na dandani kowanne side dinta, da mai dadin da mai dacin Fatana dai ace shima yaso ki, karkiyi son maso wani don wannan sashen yafi kowanne daci a soyyaya" Tana kaiwa nan ta juya ta kwanta tareda lullu6e jikinta har saman kai ta qudundune Da kallo zee tabita na mammaki don tana iya rantsewa taga kyallin hawaye a idanun Feenah Hakan ba qaramin qara sanyaya mata jiki yayi ba, sai gashi ita dake ganin zata samu mafita abin ya qara dagule mata Komawa tayi ta jingina da frame din gadon ta rungume hannuwa a qirjinta Rasa tunanin da zatayi tayi Hakan yasa ta lumshe idanu tana sauke numfashi ahankali tana dauko magangganun Aunty Feenah da daddaya tana warwaresu tana masu fashin baqi daidai fahimtarta. *WASHEGARI* Sukuku ta tashi yau, idanunta sunyi ja sunyi nauyi saboda rashin isashen barcin jiya Sallar asuba kawai tayi ta koma kan gado wani barcin yasake yin gaba daita Bata farka ba sai wajajen 10am shima Feenah ce ta tadata don kar breakfast dinta yayi sanyi Dakyar ta tashi tashiga bayi tayi freshen up tafito Haryanzu maggungunan dasukayi da Feenah daren jiya keta kai kawo a kwalwarta, maggungunan dasuka liqema kwalwarta suka hanata sukuni Daga ita har Feenahr babu wanda ya tadama juna maganar jiya don daga baya ma Feenah barin gidan tayi ta tafi unguwa Sama2 tayi break din ta fita Parts din kawunnanta tashishiga suka gaisa sannan ta dawo dakin Umma Tunda suka gaisa ta haye bisa gadonta na qarfe ta lumshe idanu Duk zazzage zazzagen da Umma keyi mata akan ta sauko mata daga gado bata tanka ba hasalima ko bude idanu batayi ba bare ta nuna alamun tasan abinda take Gajiya Umma tayi ta kyaleta ta fice daga dakin ma gabadaya Sai a lokacin zee ta samu damar tunanin nata dakyau Meyasa kowa ke danganta alaqarta da Deen a matsayin soyayya? Haka su Nurr ma sukayi gashi Feenah itama tabi sahu, meyasa? Da gaske ne babu wata alaqa tsakanin mace da namiji da baza'a rasa soyayya ba? Idan Gaskiya ne to cikin shi da ita wa keson wani? Waya damu da wani? Wake kewar wani? _ni?_ _no, never! Insha allah ba so bane.. Insha allah_ _kai bama so bane, tayaya zanso Deen? He's just a friend shima ada, yanzu he's no more, abotanmu ta yanke tun ranar da ya maidomin wayata, Hakan ya nuna be daukeni yadda na daukeshi ba, it's over and over and over!_ Haka ta wuni ranar daga kwanciya sai kwanciya Idan kaga ta tashi to abinci zataci ko sallah, dakuma tagama zata koma ta nade Tun Umma na mita har tafara xargin ko batajin dadi ne Hakan yasa ta tsareta da tambaya dole tayi qaryan kanta ke ciwo Tana ji tana gani Umma ta tilasta mata shan maganin da bazai amfaneta da komai ba na ciwonta Da daddadare ma haka tayita juye juye, ta juya 6angaren dama ta juya haggu amma sam barci yaqi zuwa, haka ta kusan raba dare idanunta biyu sannan allah ya taimaketa barcin ya dauketa can cikin dare *** Haka ta cigaba da zaman garin amma kwata2 batada walwala Ita da taje don ragema kanta abinda takeji sai gashi abin yaxama gwara baraa da bana Haka kawai zaka ganta zaune ta kafe wuri guda da ido tayi shiru Tun Umma bata dauki abin da muhimmmanci ba har abin yafara damunta Sai tayi tunanin ko kewar gida take Hakan yasa takira Feenah tasata suje tareda zee su yawata dangi ko zataji dama dama Feenah da tasan dawon garin ta ta6e baki kawai don tasan babu wanda zaiyi maganin abinda ke damunta sai mutumin Washegari wanda yayi daidai da kwanakinta hudu a garin suka fara zaga dangi da zee da Feenah dake tuqi dakanta Babu laifi tadanji dama daman abinda takeji aranta amma still abin yaqi fita ranta ta rasa yadda zatayi Har suka qaraci yawonsu suka dawo babu wanda ya tadawa dan uwanshi maganar Saidai acan cikin zuciya kowa da abinda yake saqawa Yau ma da daddare batayi barci ba, tanajin Feenah na waya, har tayi ta qarashe idanunta biyu tanajin sadda Feenahr ta gyara kwanciya ta kwanta ta rufe jikinta Sai jitayi dama ita, dama ita keda peace of mind din kwanciya haka tayi barci Tayi nisa a tunaninta taji muryar Feenah kamar daga sama tana cewa "ba tunani ko takura kai ne mafita ba, mafita shine ki ajiye komai ki fuskanci Gaskiya" Juyowa tayi ta kalli Feenahr dake lullu6e haryanzu wanda ita tamayi tunanin tayi barci Kamar bazata amsa ba sai kuma tace "kamar ya? Sai a lokacin Feenah ta yaye lulli6in tana kallon ta "ina nufin ki ajiye duk wani tunaninki na qualities or whatsoever dakike ganin be kai ba na wanda yakamata kiso don shi so babu ruwanshi, so mahaukaci, real mahaukaci don yana iya yin hadi da hadin da kwakwalwa ma bazata dauka ba, muddin dai mutumin kirki ne then kibi abinda zuciyarki keso, karki yaudari kanki" Tashi zaune zee tayi "wai Aunty waya gayamiki sonshi nake? Ni idan kina furta kalmar so dinnan bakiji yadda nakeji ba" Murmushi Feenah tayi sannan ta tashi zaune itama tana kallon zee da hawaye suka taru a idanunta "to meye na kuka kuma?" Dauke kai zee tayi hawayen na gangarowa dama mai neman kuka aka jefa da ledar kashi Murmushi Feenah tasakeyi tace "ke kanki you're confused zee, kin fada soyayya amma baki yarda kin fadaba to tayaya za'a fara maganar mafita bayan ke kanki baki yarda akwai matsalar ba? Dole sai idan da matsala ake neman mafita amma ke yanzu kinma qi yarda da matsalar bare akai ga batun neman mafita" Dafe kanta kawai zee tayi hawayenta na cigaba da diga Murmushi Feenah tayi ta dafa kafadarta "Nima na ta6a cikin wannan yanayin zee, nasan yadda kikeji don na shiga yanayin dayafi naki ciwo, ke ki godewa allah abokinki ne nikau babu abinda yahadamu zan iya cewa ma besan da wanzuwata a duniyar nan haryanzu, so is better kidawo hayyacinki ki fuskanci me kike ciki yadda zaki shawo kan matsalar kafin komai ya kwa6e miki" Tana kaiwa nan ta juya ta gyara kwanciyarta Dagowa zee tayi tana Binta da kallo da jiqqaqun idanunta zuciyarta na qara dagulewa A halin yanzu ma ta rasa mema zatayi? Komai sai qara kwa6emata yakeyi ta rasa tunanin da zatayi. Washegari da ciwon kai ta tashi ga idanunta dasuka kumbura alamun kuka da rashin barci Sosai hankalin umma ya tashi ta tusata gaba tana tambayar meke damunta, da aka takura mata ma sai tasa kuka don ita kanta idan tace ga abinda ke damunta to tayi qarya Ganin Hakan yasa hankalin umma ya ida tashi tasa aka kira kawunnanta aka suka zo suka tusata gaba da rarrashi akan tafada masu abinda ke damunta amma ba amsa don batasan abinda zatace masu ba Duk abinda ake Feenah na gefe tana kallonsu gefe guda kuma tana charting da saurayinta da akayi masu baiko dashi don befi saura wata uku ba auren dama tana shiga final level aka turo neman auren ta akasa bikin gabadaya Ganin sun dameta yasata cewa ita gida zata koma tana kewar daddy Ganin dagaske ta tubure gida takeson komawa yasa aka bata hqr tabari zuwa jibi sai ta tafi, Dakyar aka samu ta yarda sai jan zuciya take Ranar a dakin umma ta kwana don bata buqatar sake jin abinda zai qara dagulamata lissafi Kingin ranakun kawai idasu tayi a darare burinta kawai tabar garin Sai a lokacin ma take danasanin zuwa garin, gashi garin neman qiba taje ta kwaso rama Ranar dazata koma kawu umar dakanshi ya maidata bayan sun cikata da tsarabobi Dayake tafiyar safe ce basu wani jima ba suka isa Sosai daddy da mummy suka tarbi kawu umar inda anan daddy ya riqeshi har bayan la'asar sannan ya juya *STRANGE WORLD💗* Sosai zee ta chanza cikin yan kwanakinnan, takoma wata silent da ita batada walwala ko kadan, ga saurin kuka abu kadan sai hawaye Sosai abin ke damun su daddy musanmman ma shi daddyn da damuwarshi tafito qarara Tambayar duniyar nan yayimata akan tafada mashi meke damunta amma babu amsa sai kuka idan aka matsa mata Yawan shaqatawa da shopping kullum sai sun fita don dai ta warware amma a banza don babu abinda ya chanza, kodayaushe she's moody batada walwala Ganin Hakan yasa suka danganta Hakan da missing din school don dama tun farko abinda ta ambata kenan shiyasa sukaita allah allah Ayi resuming qila takoma her normal self Saura kwana biyu suyi resuming daddy yafita daita shopping din school resumption Kaya sosai ta loda na zuwa school da kingin tarkacen datake ganin tana buqata Cikin kwanaki biyun nan sai tarasa me takeji, doqin komawarsu school take ko doqin sake ganinshi *MONDAY* Tunda ta tashi da asuba bata koma ba, shirye2 take na resuming school yau Duk yadda taso qaryata abin dole ta yarda tana doqin komawarsu makaranta, doqin da bata ta6ayi ba duk hutun baya Sosai tayi shiga ta kece raini kamar yadda tasaba Sanye take da less 'yan ubansu mai shegen kyau Lace din kalar baqi sai yarfi yarfin jaa ajiki Anmata dinkin riga fitted da skirt pieces wanda ya zauna a kugunta d'ass Tayi daurin dan kwalin zahra buhari sannan ta yafa jan siririn kyalenta a kafada Kaffafuwanta sanye suke da jajjayen hill shoes sai jar jakkarta mai daukar ido dake hannunta da faskekiyar wayarta a dayan hannun Kamar koda yaushe fuskarta tasha kwalliya guntun bakinta yaqara yin jajur gwanin sha'awa Sosai shigar baqi da jaa din suka amsheta tayi wani irin kyau mai tafiya da numfashi Ahankali take tako stairs din cikin tafiyarta mai kamada ta sarauniyar kyau A dining tagansu daddy namata murmushi Itama murmushin ta maida masu ta qaraso wajensu "wow princess kinyi kyau sosai" inji daddy yayinda mummy ko dagowa batayiba Dan Kada idanu zee tayi murmushi a fuskarta tace "thanks dad" tafada tana jan kujerar kusadashi ta zauna "mummy ina kwana?" tafada tana kallon mummyn dake cin abincinta "lfy lau" ta amsa a taqaice "daddy good morning" "morning dear, wannan fara'a haka ashe daman ciwonki school? Ai gashi nan ankoma mun huta da koke2" Dariya tayi tana rufe fuska Abinci tadan zuba shima saboda mummy ba don haka ba da wucewarta zatayi idan taje school tasamu snacks Bataci dayawa ba ta tayi wiping bakinta tana niyyar tashi "ba dai har kin qoshi ba" inji daddy Dan 6ata fuska tayi tana shafa cikinta "eh daddy zai Fashe" Murmushi mai sauti daddy yayi yace "Daga cin abinci sai ciki yafashe? To tashi hakanan ai baxanso yafashe ba" Tashi tayi tana satar kallon mummy data wani hada rai, daman idan tayi Hakan to dawani abu aqasa Illai kuwa tana tashi mummy ta dago tana harararta "idan bazaki iya yafa gyallen ba kije ki sanyo hijab" Kafin ma takai aya tayi saurin warware gyallen ta yafa don akace tasama kayannan hijab an cuceta Murmushi daddy yayi kawai sannan ya miqomata hannu Kama hannun tayi tana yiwa mummy saita dawo mummyn nacewa allah ya tsare Tare suka fito da daddy hannu cikin hannu Bala na ganinsu yayi sauri ya taso yana kwasan gaisuwa sannan yawuce motar dazasuyi amfani daita ya bude mata Saida tagama shagwa6arta daddy na biyemata sannan tashiga motar daddy ya maida ya rufemata Da sauri Bala ya zagaya dayan bangaren ya bude mazauninshi ya shige ya zauna sannan ya rufo Ana tada motar daddy yaja da baya yana daga mata hannu itama tana daga mashi Bala yaja motar suka bar gidan *UMYU* A parking space Bala shima ya ra6a tashi motar yayi parking sannan ya sakko ya zagayo ya bude mata kofa Gyara zaman gyallen data maido kafadarta tayi sannan taciro siririn spec fari tasa a idanunta Ahankali ta ziro qafarta ta fito tana shaqar iskar da tarabu da shaqa na makarantar Lumshe idanu tayi ta bude tana kallon harabar makarantar abubbuwa da dama na dawomata a qwanya Daga farkon fara zuwanta makarantar nan zuwa yanzu abubbuwa da dama sun faru amma wancan semester din yafi abubbuwan tunawa abubbuwan da bazata ta6a mantawa dasu ba, abubbuwan da zasu dora daga inda suka tsaya a wannan semester din Sagale jakkarta tayi a hannu tafara tafiya ahankali tana analysing din makarantar da bata wani cika ba kasancewar yau ne ranar farko na dawowa Dama masu doqi irin ta ne ke dawowa farko farkon dawowa wadanda suka ci suka gyare kuma sai next week Cikin tafiyarta take tafiya tana jin yadda daidaikun idanu ke Binta da kallo Bata damu ba ta cigaba da tafiyarta harta bar harabar ta sha wata corner don wucewa tsohuwar department dinsu Tunda ta karya corner taji gabanta ya tsinke ya fadi Hakan yasa tafara slowing din tafiyarta Wani iri tashiga ji, feeling din is familiar, tasaba jinshi, amma a ina? Kallonta akeyi, yes kallonta akeyi, kuma wannan feeling din tana jinshi ne idan mutum daya na kallonta... "Zainabbb..." Cak Kaffafuwanta suka tsaya daga tafiyar dasuke lokacin da wannan cool voice din nashi mai gardi ta ziyarci kunnenta... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:36 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *034* "Zainab..." taqara jin an ambata daga bayanta tana jin takunshi na qara kusantota Runtse idanu tayi ahankali battling with her heartbeat _*akwai changing of heartbeat ma, idan akwai soyayya duk lokacin da kuka kusanci juna ko kuna tare sai bugun zuciyarki ta chanza*_ Maganar Aunty Feenah ta rannan tashiga dawomata a qwanya Qarasowarshi dakuma kiran sunanta da datakejin kiran har cikin zuciyarta yasa ta bude idanunta ta saukesu tarr akan fuskarshi Fuskar da batasan haka tayi missing dinta ba sai yanzu Saidai duk kwadayin zuciyarta nason kallon fuskar to the fullest kasawa tayi saboda haske da kaifin idanunshi bazasu bari ba hakan yasata kauda nata _*Na biyu kunya, wasu yana zuwa masu da kunya, kiji bazaki iya hada idanu dashi ba and ko kinyi bazaki iya jurar kallonshi eye-eye na tsawon lokaci ba*_ Maganar Feenah tasake dawomata Deen dake sauke numfashin saurin dayayi ya kalleta yana murmushi, murmushin nan nashi mai tafiya da zuciya "Zainab, is this you?" Nan take taji kaso 80% na damuwarta yabi iska, jitayi kamar anyi lifting wani qaton dutse daga qirjinta _*duk damuwar da kike ciki da kinyi arba dashi batareda ma kunyi magana ba zakiji kamar bakida sauran damuwa a duniyar nan*_ Sake dago idanunta tayi ta zubasu a fuskarshi A take zuciyarta ta amince mata da maganar Feenah Wata murya acikin kanta tafara cemata _*you're in love Zainab!*_ _*you're in love Zainab!!*_ _*you're in love Zainab!!!*_ Saurin toshe kunnuwanta tayi da hannuwanta biyu tana runtse idanunta gamm Deen dake magana ya dakata ganin reaction dinta Kallonta ya tsaya yi da oily eyes dinshi cikeda ayar tambaya "Zainab are you ok?" Shiru kuma bata bude idanunta ba "Zainab.." dakatawa yayi ganin ta bude idanunta ahankali tana kallonshi kallon daya sanyaya jikinshi nan take Batareda tace komai yaga tazo tabi ta gefenshi ta zagayeshi ta wuce Juyawa yayi yana kallonta da mammaki sai kuma yayi saurin Binta abaya "Zainab.." "Zainab!" Jin muryar shi da takunshi a bayanta yasata sanin biyota yayi Hakan yasata qara pace Ganin Hakan yasa shima qara sauri don sosai hankalinshi ya tashi ganinta a yanayin da be ta6a ganinta ba nan take duk sai murna da doqin ganinta suka koma ciki Dakyar yasamu ya taddota daidai wata kwana yayi saurin shan gabanta Yin gefe tayi zata wuce shima yayi saurin yin gefen ya tare tasake yin wani gefen nanma ya tare "Zainab listen to me, are you ok?" Dakyar ta iya bude bakinta datake jinshi a kafe tace "ka bani hanya" Beyi yadda tace ba sai qara matsowa dayayi gabanta yana cewa "Zainab.." "ka bani hanya nace!!!" tafada a mugun tsawace wanda yasashi ja baya atsorace Dagowa tayi ta sauke idanunta cikin nashi dasuke kallonta a mammakince "I Said go away can't you get it?! I don’t want to see you, I don’t want to talk to you, just go.. Go!" Yadda tayi maganar yaqara kayarmashi da gaba don kwata2 kamar bata a hayyacinta Dan qara matsowa yayi yace "Zainab, please.." Dafe kai tayi ta juya tabi hanyar data fito da sauri Binta da kallo yayi harta sha kwana sannan shima yayi saurin bin bayanta zuciyarshi na rayamashi duk yadda akayi ba lafiya ba, bazai ce be ta6a ganinta a wannan yanayin ba Amma ya dade rabon da yaganta a irin wannan yanayin, tun lokacin da case din assignment dinta ya hadasu, Hakan yasashi zargin duk yadda akayi yauma ba lafiya Koda yashawo kwanar harta kusan kaiwa gate Hakan yasa ya qara sauri dukda be iya tafiyar sauri ba, yana kallon sadda ta fita gate Hakan yasashi qara sauri dukda he's exhausted already Yana isowa bakin gate yaga wucewar wata adaidaita Be bi takanta ba yashiga waige waigen inda zai ganta amma babu ita babu alamunta, nan take kwakwalwarshi tabashi tana cikin adaidaitan nan Juyawa yayi yabi adaidaitan data fara 6acemashi agani da kallo yana jin zuciyarshi na wani irin daci da nauyi 💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖 Mai adaidaitan yaqara juyowa karo na biyu yace "baiwar allah nace ina zan kaiki?" Dagowa tayi ahankali da idanunta dasuka fara chanza launi ta kalleshi sai kuma tadanyi jimm na tunanin ina zatace akaita "any closest restaurant" "Na'am?" inji mai adaidaitan da alamu be gane turancin nata ba "nace gidan abincin dake kusa kusa da nan" "oh to" yafada yana cigaba da jan napep din ita kuma ta maida idanunta ta lumshe Tana jin yadda napep din ke slowing down harta tsaya amma bata bude idanun ba "hajiya mun qaraso" Sai a lokacin ta bude idanunta ahankali tana dan leqa inda suke Jakkarta ta sagala sannan ta sauko daga napep din tayi zipping din jakkar #500 taciro tabashi ya amsa yana shirin bude dan abin dasuke ajiye kudi don ciromata chanji yaga taqara gaba Dan leqowa yayi yana "hajiya chanjin fa?!... Hajiya!" Ko nuna alamun ta jishi batayi ba tashige restaurant din Daga kafadu mai adaidaitan yayi sannan yaima napep din key yaja shima yaqara gaba. Cikin restaurant din is very quiet don daidaiku ne customers din wajen sai ma'aikatan dake kai kawo jefi jefi sai cool music dake tashi ta background din wajen Wani table dake a dan kusurwa ta nufa taja daya daga cikin kujerun dake kewaye dashi ta zauna tana dora jakkarta kan cinyarta sannan tayi interlocking yatsun hannayenta bisa table din ta dora fuskarta akai Bata dade ahaka ba taji muryar wata waiter na yimata sannu da zuwa Dago fuskarta tayi ta kalli yarinyar da bazata wuce sa'arta ba Amma kallo daya zakamata kasan ba bahausa bace duba da yanayin shigarta da gashin kanta Kada mata kai kawai ta iya yi tana sauke idanunta daga kanta "me kike so akawo miki?" tafada a cikin hausarta da bata ida zama abakinta ba Shiru tadanyi sai kuma tadan yamutsa fuska tace "something chill, maybe softdrink" "wane iri ma'am" Dan dafe kanta zee tayi don idan akwai abinda bataso yanzu to magana ne "something milky haka" "ok ma'am" inji yarinyar tana Juyawa Bata dade da tafiya ba ta dawo dauke da tray dake dauke da hollandia yoghurt sai glass cups biyu a gefe Ajiyewa tayi ganin batace komai ba saita juya ta tafiya Ganin ta tafi yasata dan gyara zama ta jawo kwalin hollandia din ta bude murfin ta zuba a daya daga cikin glass cups din ta maida ta rufe ta ajiye sannan ta dauki na kofin takai baki tafara kur6a ahankali _*A jadawalin alaqa dake tsakanin mace da namiji babu abota, babu yadda za'ayi ayi abota zalla tsakanin mace da namiji batareda so yashiga ciki ba, is either suso junansu ko daya yaso daya*_ Maganar Feenah tasake dawomata _*So mahaukaci ne, real mahaukaci don yana iya hadin da kwakwalwa ma bazata dauka ba*_ _*is better kidawo hayyacinki ki fuskanci me kike ciki yadda zaki shawo kan matsalar kafin komai ya kwa6e miki*_ Lumshe idanunta kawai tayi tana nanata innallilahi waina ilaihi rajiun a ranta Yaushe wannan abin yafaru? Tayaya? Yaushe? Meyasa? Meyasa zuciyarta zataso Deen? Yaushe tafara sonshi ma? Tayaya tafara sonshi Wani irin abu zuciyarta keyimata wanda bazata iya musaltawa ba hakan yasa taqara interlocking hannunta ta dora fuskarta akai tana sauraron cool music din dake tashi a background din restaurant din mai taken _did you believe in love ❤️_ *DEEN* Ya dade nan tsaye yana bin inda suka bi da kallo kamar mai sa ran ganin sun sake 6illowa Da yafara gajiya da tsayuwar ne saiya juya ahankali jiki a sanyaye yakoma cikin school din Tambayoyi dayawa ne keta battling a zuciyarshi _meya faru kuma?_ _meyasa ta fusata?_ _dama batayi missing dinshi ba?_ _yayi tunanin tayi kewarshi kwatankwacin yadda yayi mata, amma alamu ma sun nuna bama ta tashi ba take_ Tunawa yayi yadda tun saura kwana uku Ayi resuming yake ta doqin zuwan ranar badon komai ba sai don ya ganta Yayi kewarta, kewa ta haqiqa don a tsawon rayuwarshi be ta6a yin aboki ko qawa ba sai akanta, bayan kaka babu wanda yakeji aranshi kamar ita wannan hutun ma hakanan yayi shi a darare kullum lissafin kwanakin dasuka rage suyi resuming yake ba don komai ba sai don ya ganta A tunaninshi itama tana can tana doqin ganinshi A tunaninshi zasu yi farinciki marar musaltawa na ganin juna bayan kusan wata daya rabon da suga juna ko suji muryar juna Amma sai yaga akasin haka, abinda be ta6a kawo ma ranshi zai faru ba Samun wuri yayi ya zauna kan dakalin wani office inda yake iya hango gate daga nan idanunshi akan gate din hoping zaiga 6illowarta akoda yaushe amma shiru Tunani yafara yi a zuciyarshi akan reaction dinta Meyayi zafi haka? Waya fusatata? Meyasa takoma bayan yanzu tazo? Ina ta tafi? Wane hali take ciki yanzu? Tambayoyin da yaita yima kanshi kenan wanda babu mai bashi amsarsu *ZEE* Batasan iya adadin lokacin data dauka ahaka ba Amma tasan ta dade sosai Hollandian data zuba a cup din ma ko rabi bata sha ba Tunani kau tayi shi har tafara jin kwalwarta na neman fashewa amma har lokacin abu daya ta iya tsayawa akanshi shine tabbas tana son Deen How? When and why? Shine bata saniba Dama ana soyayya batareda wani dalili ba? Tambayar data kasa samun amsarta kenan Jin ta gaji da zaman yasata duba agogon wayarta 01:15pm ta gani Hakan yasa ta sauke Ajiyar zuciya tayi swiping din screen din wayar ta lalubo number bala ta dannamashi kira Ce mashi tayi yazo ya dauketa sannan ta fadamashi inda take ta katse wayar takoma jikin kujerar ta jingina ta kafe wuri guda da kallo tayi shiru. Ba'ayi 30mins ba saiga kiranshi wanda yabata tabbacin zuwanshi, bata daga ba ta tashi tareda daukar jakkarta ta rataya tawuce wurin biyan bill tabiya sannan tafito Tana fitowa ta hangi motar daga can gefen titi Hakan yasa itama ta nufi wurin tana tafiya kamar wanda kwai ya Fashemawa aciki Bude back seat din tayi ta shiga ta rufo sannan takoma cikin kujerar motar ta lafe tana lumshe gajiyayyun idanunta tana cigaba da sauraron yadda zuciyarta ke tsira takoina. *DEEN* Ganin lokacin zuhr yayi yasashi tashi daga bisa dakalin dayake akai Tundazu Ahankali yafara takawa zuwa hanyar dazata sadashi masjid din school din don gabatar da sallar Koda aka gama sake dawowa inda yatashi yayi don duk a tunaninshi zata dawo tunda dole nan drivernta zaizo daukarta Amma shiru har lokacin asr yayi, tashi yasakeyi yanufi masjid ya sauke farali sannan ya fito He has no option than yatafi shima Hakan yasa yanufo gate din cikin sanyi yanajin zuciyarshi na qara jagulewa Koda yafito ma tsayawa yayi a gefen hanya ya kafe titi da idanu yayi shiru tunanika kala2 na kai kawo a zuciyarshi Ya dan jima sannan wata adaidaita ta gitta ya tsaidata Cikin sa'a yana gayamashi inda zaya yace yashigo suka bar wajen. *** Yinin ranar haka suka qarasheshi cikin rashin walwala musanmman zee Sanin cewa ta kamu da sonshi ba qaramin daga mata hankali yake ba gashi da alamu dai kamar yadda Aunty Feenah ta fada qila ita kadai ke haukanta Meyasa to? Meyasa zuciyarta zata yimata haka? Ya zatayi da son nashi? Tadai san ko mutuwa takeyi tana dawowa bazata iya bayyanamashi halin da zuciyarta ke ciki gameda shi ba, yama zatayi wajen yin Hakan? Sam bazata iyaba Sosai zuciyarta ta shiga damuwa, damuwar makomarta don tasan idan zataso abu bata iya sonshi ba kamar yadda bata iya qin abu ba Idan taso abu da dukkan zuciyarta take sonshi haka ba idan ta tsani abu ta tsaneshi kenan ko me za'ayi abin baya ta6a burgeta Dole ne, dole ne tayi gaggawar takawa zuciyarta burki, ta yakiceshi daga ciki da qarfin tsiya Koda Hakan zai illatata Saidai ta yaya? Yanzu haka idan da abinda take son gani to shine Sau biyu ta kalleshi dazun amma sai gizo fuskarshi ke mata Kunnuwanta babu abinda suke son ji kamar muryarshi Babu abinda takeso yanzu sai kasancewa tare dashi, to tayaya zata iya abinda ta quduri yi? *WASHEGARI* Sa6anin jiya, yau sukuku ta tashi tana jin idanunta na mata wani nauyi2 sanadiyar barcin da be ishesu ba Da farko tayi niyyar yin zamanta agida kawai basai taje school ba Saidai kuma sanin cewa zaman bazai wani amfaneta da komai ba inbanda qarin damuwa ba yasa ta fasa Bayan haka kuma zuciyarta na son ganinshi itace ma ke ingizata akan taje din koba komai zata ganshi wanda Hakan zai sanyaya mata rai ko yayane Dama tasani, Dakyar zata iya controlling zuciyarta a wannan ga6ar don zuciyarta is very fragile and sticky, idan ta damqi abu Dakyar take iya saki musanmman ma a wannan ga6ar da takejin abinda bata ta6a ji ba akan abu Bazata iya musaltawa yadda takeji ba Saidai kawai tasan shine maganin matsalar ta, ganinshi zai yayemata damuwarta, murmushin shi zai sanyaya mata zuciya, muryarshi kuma zata sakata a shauqi sosai Dayake komai yinshi takeyi kamar lakka Hakan yasa taita jan jiki har 9 tawuce sannan ta fito Wajen motar dazasu fita dasu ta wuce tana tafiya a hankali Koda tazo dama bala yariga ya bude mata kofa Hakan yasata shigewa kawai Zagayawa bala yayi shima ya bude mazauninshi ya shige sannan suka fice daga gidan *UMYU* Jin qarar budewar kofa yasata bude idanunta data lumshe tunda suka Kamo hanyar tahowa Sotake ta taso ta fito amma takasa Hakan yasa ta maida idanunta taqara lumshewa Takusan mintuna biyu ahakan sannan tasake bude idanunta ta yunqura dakyar tafara niyyar fitowa Qara matsawa baya bala dake tsaye Tundazu yayi ta fito sannan ya sunkuya ya dauko mata jakkarta da tabaro aciki ya miqamata Saida tagama gyara yafin gyallenta sannan ta amshi jakkar tana ratayeta kasancewar side bag ne Bata qara bi takanshi ba ta juya tafara tafiya ahankali Yau ta lura makarantar tafi jiya cika Ba abin mammaki bane don dama da kadan kadan za'aita dawowa har zuwa next week da makarantar zata cike Wannan karon sabon department dinsu ta nufa Saidai Koda taje Wurin daidaikun mutane tagani kuma duk maza Hakan yasa tayi kwana ta koma inda tafito Tsaki taja a zuciyarta tana jin qunci da kadaici sosai tama rasa inda zata nufa kuma Zuciyarta ce ta yanke mata ta wuce tsohon mazauninsu inda suke zama dasu sumee Can din tanufa tana jin kanta na mata nauyi saboda rashin isashen barci Akwai qura sosai akan bench din dasuke zama amma kasancewarta agajiye yasa tasa hanki dinta ta kakka6e inda zata zauna kawai ta zauna tana maido jakkar akan cinyarta sannan jingina kanta da bishiyar bayanta ta lumshe idanu Ta dan jima a wajen a Hakan idanunta still a rufe sai jitayi zuciyarta tafara chanza bugu Wannan feeling din datake ji duk lokacin da yake kallonta ya biyo baya Zuciyarta ce tayi motsi da qarfi wanda Hakan yasa ta bude idanunta ta dago bashiri bata saukesu a koina ba sai akan kamillaliyar fuskarshi Batasan ko ya akayi ba sai jitayi takasa Janye idanunta akanshi duk yadda taso Janyewa kuwa yadda kasan anyi magnetting din idanunta akan fuskarshi Zuciyarta tashiga narkewa ahankali cikin shauqin ganinshi Shima Deen dake jingine da bishiyar dake facing dinta Tundazu ita yake kallo yana son karantar abubbuwa da dama a fuskarta amma it's blank baya iya hango komai Dagowa yayi daga jinginen dayayi da bishiyar yafara takowa ahankali batareda ya bar kallonta ba harya kawo gabanta yana dan basu tazara a tsakaninsu Ahankali ya rage tsawo ya daidaita tsawonsu ta hanyar duqawa wanda Hakan yasa itama tabiyoshi qasa da idanunta Cigaba da kallon juna sukayi aka rasa wanda zai magantu Lumshe idanu tayi akan fuskarshi tasake budewa tana jin yadda emotions ke building up a kowacce kusurwa ta zuciyarta Hakan yasa hawaye suka fara taruwa a idanunta "Zainab.." Maida idanun tayi ta lumshe tana kallon gefe Ita kadai tasan yanayin da muryarshi ta jefa ta, jitake kamar tana yawo a gajimare "Zainab meke faruwa? Meke damunki?" Qara tamke idanunta tayi trying so hard wajen controlling emotion dinta "Zainab.." Saurin miqewa tayi tsaye tayi wanda yayi daidai da miqewarshi tsaye shima Juyawa zatayi ta tafi yayi saurin shan gabanta 6ata fuska yayi yadda yasaba yana cewa "O'O! Please say something Zainab" Sake kauda kai tayi tana jin yadda shagwa6ar tashi tayi tasiri akanta sosai "please Zainab kiyi magana, am so worried, jiya ma haka kika tafi naita jiranki baki dawo ba kuma yanzu zaki sake tafiya, don Allah ki fadamin, are you angry with me? Wani laifi nayimiki? Please tell me and I promise to apologize, zan baki haquri" Jin hawayen datake ta maqalewa na neman sakkomata yasa tayi saurin kauda kai ta chanza hanya zata bi Ganin Hakan yasashi saurin tarewa again Bata kulashi ba ta chanza wani yasake bi ya tareta Hakan yasata dagowa a fusace tace "wai menene haka?! I said leave me alone can't you get that?!" Dan jada baya yayi yana kallonta cikin rashin sanin abinda zaice ganin Hakan yasa ta ra6a gefe zata wuce don jitake kamar zuciyarta zata Fashe saboda bugun datakeyi "Zainab, saboda kyautar da na maido miki kike fushi?" Tambayarshi ta dakatar daita daga tafiyar data fara Ganin ta tsaya yasashi dan takowa yadan rage tazarar dake tsakaninsu "am sorry amma ni bada wata manufarba nayi Hakan, na lura tun ranar ranki ya 6aci akan Hakan amma ni banyi Hakan da nufin 6ata miki rai ba, am sorry babu kyau gaba" Hawayen ne suka silalo mata ahankali Hakan yasata cigaba da tafiyarta da sauri don bata buqatar yagansu Binta da kallo yayi jiki a sanyaye batareda yasake yunqurin binta ba, yana ganin kamar ba Zainab din daya sani bace, kamar an sauyota... ✍️ Love in the air💃 Wannan labarin is all about love ❤️ a very emotional love story wanda zai antaya ma karanta da dama cikin shauqi har yakawo qwalla a idanun masu raunin cikinsu It's all about true love, sadaukarwa da heartbreak. stay tuned insha allah wannan book din zai zama one of your favourite book ever 🧚🏻‍♀? Ashaanty love 💖 8/2/21, 9:36 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *035* *2 DAYS AFTER* Kwance take a tsakiyar gadonta ruff da ciki ta cusa fuskarta a pillow qaffafunta a sama tana ta dan wuwullawa Yau kwana biyu kenan rabonta da school Tun ranar da ta tafi tabar Deen tsaye a inda yasameta Daga ranar bata qara zuwa school ba saboda gudun haduwarsu don bata fatan sake jin abubbuwan dataji gameda shi ranar shiyasa ta yanke shawarar qin zuwa school din duk don tasamu sauqi ashe Hakan ba sauqi bane ba Bata gane Hakan ba sai cikin kwanakinnan biyu Halin data shiga a cikin kwanakinnan biyu ya sake tabbatar mata cewa ba qaramin nutso tayi ba a kogin soyayyar Deen ba kuma ya tabbatar mata cewa qaurace mashi ba mafita bace agareta ba don a cikin kwanaki biyun nan tashiga halin da taji gwara ta dinga ganinshi din ko babu komai zataji sanyi a zuciya A cikin kwanakinnan ta gano cewa rayuwa batareda Deen ba kamar rashin gishiri ne a abinci, bazakayi saurin lura da kasantuwarshi ba bare alfanunshi sai idan babu shi Taji kuma ta gane cewa rayuwa bataredashi ba rayuwa ce mai cike da qunci da azabtuwar ruhi Batasan sadda tafara sonshi ba kuma bata tunanin akwai lokacin da zata daina don a cikin kwanakinnan ta gano abubbuwa da dama gameda yadda takeji gamedashi Da farko gani take nisantarshi zai zamemata mafita yadda zata manta dashi gradually amma a cikin yan kwanakinnan ta qaryata Hakan don tun kafin akai koina tafara wahala Takoma gatanan dai kullum soo moody komai baya mata dadi a duniyar nan A cikin kwanakin is either kaganta zaune shiru tayi nisa cikin duniyar tunani, ko kuma kaji tafara rairo wani baiti wanda yayi daidai da abinda take ji a lokacin Ko wanne mutum da irin baiwar da allah yabashi, both ta 6oye data bayyane Wasu har su koma ga mahallicinsu basu gane baiwar da allah yayi musu Wasu suna ganewa amma basa ta6a amfani da baiwar a aikace Daidaiku ne masu bayyana baiwar su ga jama'a suyi amfani daita ta kuma zama garkuwa agaresu Zee nada baiwa guda wanda bata san dashi ba, ko tasani to bata maida kai akanshi ba *WAQA* Allah ya yimata baiwar iya tsara baiti a nan take kuma kaji yahau yayi dadi kamar wanda aka zauna akayi nazari sosai aka tsarashi Tun tana qaramarta takeda habit din qirqirar waqa datayi daidai da yanayin datake ciki walau farinciki ko akasin haka Saidai ko kadan bata ta6a maida hankali akan haka ba don abin kawai yazama kamar cikin jininta yake bata ganinshi a matsayin wani abu daban daya kamata ta fiddoshi fili ba mutane su sani harma tayi tunanin zama wani abu da Hakan Ahankali ta dago fuskarta daga ciki filon ta dora ha6arta akan hannuwanta dake bisa juna kan pillon suma ta kafe mirrornta da idanu _my heart beats_ _echoes into the cold streets_ _where nightmares and darkness.._ _begin to meet!!_ _how?_ _how did I fell in?_ _how did I fall for.._ _the cold hand of LOVE_ _I have always been so afraid_ _of losing people I love_ _but sometimes I keep asking myself_ _is there anyone out there_ _anyone out there_ _who’s afraid of losing me too_ _sometimes one hello_ _makes you never want to say goodbye_ _SO_ _dadin fada a baki ne dashi_ _amma a zuciya in yayo dashe ..._ _zance ya lalace!_ _yaushe ne nafara?_ _yaushe zani gama?_ _yaushe zanji rahma?_ _rahama da sallamar ruhi_ _I want to push you_ _push you out of my heart_ _but every breath I take_ _proves I can't live without you_ Saukar abu mai dumi dataji a kumatunta yasata tasan kuka take again Kukan da ba yanzu tafara shiba kuma ba yanzu zata gama shiba _I wish_ _I wish_ _I wish... Am wishing_ _and wishing_ _but I don’t know what to wish_ _to have you or to leave_ _cos when my brain said NO.._ _my heart says YES!_ Lumshe idanu tayi wasu hawayen suka sake gangaromata _Ina ma.. Ina ma_ _zuciya idan tasamu rauni_ _za'a iya yanke daidai raunin_ _ina ma.. Ina ma_ _za'a iya numfashi ba zuciya... da na bada nau kyauta_ _ina ma.. Ina ma_ _za'a iya maida hannun agogo baya... Dana tsallake haduwarmu dakai_ _ina ma_ _ina ma..._ Saita kasa idawa ta maida kanta ta cusa cikin pillow tana shesheqa ahankali Ita kadai tasan abinda takeji babu kuma wanda zai san abinda takeji sai wanda ya tsinci kanshi acikin irin wannan yanayin Ace ka kamu da soyayyar wanda har abada bakajin kana iya furta Hakan gareshi Ba soyayyar bace illah, barinta a zuciyar tafi komai illah Domin fitowarta tafi linketa a zuciya Amma tayaya zata bayyanata? Tayaya? Allah ya hallici mace da kunya da kawaici wanda Hakan tamkar ado ne agareta Duk macen da batada su to ta tashi daga mace ta koma wani abin daban Yaya zatayi? Cigaba zatayi da qumshe abinda takeji a zuciya? Koko ajiye wannan adon nata a matsayin ta na mace zatayi ta fitar da abinda ke ranta? Yaya zatayi? She's damn confused. _*it's better kidawo hayyacinki, ki fuskanci me kike ciki yadda zaki shawo kan matsalar kafin komai ya kwa6e miki*_ Maganar Aunty Feenah ta rannan tadawo mata a kwanya Yanzu ta fuskanta, meye mafitar Wani abu yayi clinging a brain dinta hakan yasata saurin tashi zaune ta jawo wayarta dake kan bedside locker tashiga contact ta lalubo number Aunty Feenah Har zata danna dail botton sai kuma takasa Yanzu idan ma ta kirata me zata cemata? Ta ina zata fara? Hakan yasata chanza shawara tafita daga contact din ta kunna data connection dinta ta shiga whatsapp app dinta Messages suka fara Shigowa Hakan yasa ta tsaya har Saida suka gama Shigowa sannan tashiga contact ta lalubo number Aunty Feenah Gani tayi batafi awa da sauka ba hakan yasa tashiga keyboard tafara typing kamar haka _*Barka da wuni Aunty, ya mutanen Ruma? Yasu umma?*_ _*Please Aunty I need your help.. Na fuskanci matsalar, meye mafitar?*_ Saida ta tsaya taqara karantawa sannan ta danna send botton ya shiga Shiru tayi tana kallon message din data tura hoping Aunty Feenah zata samarmata mafitar dazata sauqaqa mata abinda takeji Saida ta gaji don kanta sannan ta rufe datarta ta sauka hoping lokacin dazata sake hawa zata tararda amsar mafitar ta 💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖 "wai haryanzu baka gamaba kyakyawa na?" inji kaka data leqo dakin nashi a karo na uku Dagowa yayi daga zagaye abincin dayake da cokali ya kalli kaka dake bakin kofa tana kallonshi shima "Kaka nidai allah na qoshi" yafada yana 6ata fuska Sakin labulen tayi tana ida Qarasowa ciki "bangane ka qoshi ba? Abincin da kafi so fane, ka duba da kyau, ko wani abu ne beji ba?" tafada tana amsar cokalin hannunshi tayi tasting taji komai daidai "Kaka komai yaji kuma yayi dadi sosai kawai na qoshi ne" "kyakyawa na, ko wani abu na damunka ne? Nina kasa gane kanka tun shekaranjiya wacan, ka koma wani iri gakanan abinci ma kanshi baka ci, sokake qwalsa ta kamaka mushiga uku?" Murmushi Deen yayi ganin yadda take maganar cikin damuwa "Kaka ulcer ce ba qwalsa ba" Tallabe mashi qeya tayi tace "kajimin ja'iri ana maganar qwarai yana sanyo wasa aciki, ina ruwana da koma mecece? Tunda dai ka gane ba shikenan ba?" Shafa qeyarshi yake yana kumbura fuska alamun yaji zafi Tsaki taja tace "yanzu zaka fadamin abinda ke damunka din ko kuwa?" Zamewa yayi ya dora kanshi bisa cinyarta ya lumshe idanu "Kaka banajin dadi, kaina na ciwo kuma bakina babu taste" Nan take kaka ta rude "dagaske? Tun yaushe? Meyasa baka gayaminba? Maza tashi indauko maka paracetamol kasha, waya gayamaka ana zama da ciwo?" Sai a lokacin qaryar dayayi ta dawo mashi, cewa yayi beda lfy ko? Innallilahi! Meyasa yace haka? Yanzu shan magani farilla. Dama Dakyar yasamu tabar bashi wadancan don ko bayan warwarewarshi tilasta mashi take saiya sha Dakyar yasamu ta yarda ta kyaleshi gashi yasake jama kanshi Saurin tashi yayi daga kan cinyarta yace "Kaka dama shekaranjiya kan ke ciwo kuma nasha magani tun a school, tun ranar ma na warke yanzu lafiya lau nake, Allah" yafada yana 6ata fuska ganin kallon datake binshi dashi "hmm daga baya kenan, magani ne sai kasha, ashe dama bakajin dadi ne shine daka fadi gwara kaita zama da ciwon saboda rashin son magani? To allah ya matsi bakinka kuma babu abinda zai hanaka sha don bazan zuba maka idanu kayi ta zama da ciwo ba" Tana kaiwa nan ta tashi ta nufi kofar fita tanata sababi ita kadai Binta da kallo yayi harta fita sannan ya dafe kai tareda lumshe idanu cikin rashin sanin abin yi Babu abinda yafi tsaya mashi arai kamar zee, yakasa sukuni kwata2 akanta Jiya da yau haka yakusan wuni a makaranta cikin saka ran ganin ta amma ko mai kama daita be gani ba Sosai abin ya dameshi don haka kawai yaji beson loosing dinta a matsayin qawa ko don be ta6ayin abokin da sukayi shaquwa kwatankwacin wanda sukayi da ita? Yana nan zaune kaka tadawo da sachet din magani da ruwa a kofi Ganin yadda ta tamke fuska yasa yasan ko me zayayi sai yasha Hakan yasa be ba shara'a wahala ba ya amsa sadda ta miqomashi yanajin kamar yayi saboda warin maganin daya bugi hancinshi Kamar dai yadda yasaba wannan ma Dakyar ya hadiyesu sannan yakoma ya kwanta yana maida numfashi kaka nata jeramashi sannu Tattare abincin da beciba tayi ta fita dasu sannan tadawo ta rufeshi da bargo har iya wuya sannan ta shafa sumarshi tana cewa yayi barci qila kafin yatashi ciwon kan ya lafa Kada mata kai kawai yayi ya maida idanun ya rufe yana sauke Ajiyar zuciya ahankali Ta dade tana qaremashi kallo tanajin wani irin tausayinshi na ratsa mata zuciya Addu'a tayi mashi ta tofeshi dashi sannan ta tashi ta fita tana share hawaye ta jamashi kofa Ahankali ya bude idanunshi bayan fitarta yayi juyi a gadon yana qara qudundunewa a bargon yasake lumshe idanu yayi luff kamar mai barci amma ba barcin ba yake ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ Sake hawa tayi a karo na uku, still babu amsa amma ga alamun an karanta nan yafito amsar ce dai ba'a bada ba To me Hakan ke nufi? Tambayar data yiwa kanta kenan Dubawa tayi taga she's still online kawai batayi niyyar tankamata bane Haushi taji amma ya ta iya? Ita ke nema dole tayi haquri Sake typing tayi _*Aunty Feenah baki bani amsa ba, am waiting please*_ Tasake sandawa Saida aka kusan mintuna biyu da turawa sannan taga alamun an karanta Saidai tajira har tsawon mintuna goma shiru ba amsa babu kuma alamun typing ake Ranta ne yaqara 6aci, tasan wulaqanci kawai Aunty Feenah keyimata don gashi nan sarai ta gani kawai amsarce batayi niyyar badawa ba Hakan yasa ta kirata video call ta whatsapp din Saida takusan katsewa sannan aka daga, nan take Feenah ta bayyana kwance akan gado kanta sanye da hular net ta barci "ya?" inji Feenah cikin halin ko in kula da so6are so6aren da zee keyi "haba Aunty, nayi maki magana kin shareni alhalin kin gani, haba Aunty" tafada kamar zatayi kuka "a ina kikayi Magana?" inji Feenah "anan mana, kuma kin karanta kikayi ignoring dina" "a ina wai, sai wani anan kike, ina ne nan din?" tafada cikin masifa daya riga ya zamemata jiki Turo baki zee tayi kamar zata fasa kuka tace "ba texting dinki nayi ba via whatsapp? Kuma ai kingani" "naga me? Naga waiting dai, waiting for the message yasa ni banga komai ba" Dan murmushi zee tayi don tasan tabbas ta gani kawai rainin hankali ne irin nata "to bari nasake turomiki.." "kinga idan bazaki fada min yanzu ba karki kuskura ki sake damuna, yanzu bakinki ciwo yakeyi da bazaki fadaba sai na tsaya jira kinyi typing? If you're not serious zan kashe wayata yar rainin hankali kai" Zee data turo baki tun sadda tafara ta qara 6ata fuska, dama tasani tagani sarai kawai sotake ta furta da bakinta "dama.. Dama maganar rannan ce.. Shine nace na gano matsalar meye mafitar?" Dariya sosai taba Feenah a dayan 6angaren Saidai ta dake taqiyi a cikin zuciyarta tana cewa 'yaro man kaza" A zahiri kuma tace "matsala? Matsalar me kuma ana zaman lfy?" Kukan shagwa6a zee ta fashe dashi tana cewa "kai Aunty Feenah, kinfa san komai kawai pretending kike" Tsaki Feenah taja tace "bakida aikin yi" tana shirin katse kiran Hakan yasata saurin cewa "maganar Deen din damukayi Aunty wanda kika ce am in love with him na qaryata shine nace na gano matsalar ki fadamin mafitar" Tafada kamar tayi kuka "meye matsalar to?" Fashewa da wani kukan shagwa6ar tayi tace "kai Aunty, kinfa sani, ina sonshi mana" Sai a lokacin Feenah tashiga yin dariyar da taketa dannewa Tundazu harda kyakyatawa, iya cika zee ta cika famm sai kumburi takeyi "shashasha! Dama nace ina nan ke da kanki zaki nemeni ba ke yar rainin sense ba? Ana so ana kaiwa market? Kadan kika gani yarinya" tafada tana yin kwafa "nidai yanzu tunda kinsani fada a taimaka min abani mafitar" inji zee tana kwa6e fuska "yaushe kikayi realising haka?" "ranar damukayi resuming school, ina dora idanuna akanshi nayi realising na afka" tafada tana rufe face🙈 Dariya Feenah tayi tace "awwn! Love in the air 😘 sai kikayi yaya? Badai gayamashi kikayi ba" "kai Aunty, tayaya ma zan fara? Never and ever" "to yanzu ya ake ciki?" "Aunty tun lokacin danayi realising Hakan sai naja baya dashi, bana yarda magana ta hadamu amma sai ya cigaba da nacemin duk inda nayi saiya bini Hakan yasa kwana biyu kenan rabona da zuwa school saboda shi duk don incireshi a rai kafin abin yayi nisa amma wani abin mammaki Aunty bakiji yadda naji a kwanaki biyun nan ba, kamar ana sake huramin wutar sonshi, am helpless, na rasa yadda zanyi, yanzu haka babu abinda nakeson gani kamar shi" Tsaki Feenah taja "banda ke shashasha ce dama angayamaki yin nesa dashi mafita ce? Da mafita ce da tuni kin shawo kan lamarin tun a hutun ku tunda ba hadewa ba kuke, abinda muke magana a yanzu shine what your heart wants, zuciyarki na sonshi kekuma kina nisantata dashi dama ina za'aga zaman lafiya?" Zee dake jinta Tundazu tace "to Aunty meye mafita? Ni gudu nake kar muna tare abin yaita gaba gaba har yakai stage din da bazan iya controlling dinshi ba kuma ba sona yake ba" "shi yace miki baya sonki? Meyasa zaki yanke cewa baya sonki tun yanzu" "da yana sona ai da ya nuna min Aunty" "wawuya, to kika sani ko shima beyi realising yana sonki ba? Duka kema yaushe kikasani? Kika sani ko shima yana sonki sani ne beyi ba? Baki tsaya kikayi tunani ba kika yanke shawarar nisantarshi" Shiru zee tayi tana calculating din maganar Feenah "tayiwu shi ma is in love with you besaniba ko kuma yasani amma yakasa samun courage din fadamiki koko kinyi it's very easy to say I Love You? Idan da da sauqi ai da kema kin furta Wataqila yana can shima yana tunanin ta hanyar dazai fadamiki amma kuma kike neman nesanta kanki dashi wanda Hakan ba komai zaiyi ba sai sagar mashi da gwiwar da zaiyi yakasa furtawa ku biyun ku cigaba da wahala Kinga ita soyayya idan an shigeta anshigeta ne babu batun backing off don indai ta Gaskiya ce jada bayan bazai amfaneku da komai ba saima qarin wahala dazaku jama kanku, so karki kuskura Kiyi wannan mistake din, stick on ku koma yadda kuke da zai furta maki am assuring you" Zee datayi tsit Tundazu tana sauraronta cikin gamsuwa ta sauke Ajiyar zuciya tace "to idan muka koma yadda muke da din shaquwarmu ta linka da daga baya nagane ni kadai ke hauka na fa?" "think positively zee, insha allah Hakan ma bazata faruba, kina da komai da namiji zai soki dashi, baki rasa komai ba zee, bayan haka akwai hanyoyi da dama da mace zata nuna alamomin soyayyar ta ga namiji ta dasa mashi tata a zuciyarshi batareda ta furta ba Ciki akwai kyautatawa, zuciya ko wacce iri ce tana son mai kyautata mata kema kin sani Iya wannan ya isa and am telling you zaki samu zuciyarshi, zaki shige ciki Kiyi bake2 am telling you" Murmushi zee tadanyi saikuma ta kalli Feenah dake cikin screen din wayar tace "amma Aunty Feenah naji kince kema kin ta6a tsintar kanki a wannan yanayin, waye mutumin? Yaya Auwal?" Yanayin Feenah ne yadan chanza sai tace "A'a na gayamaki wancan ko sanina beyi ba ko kin manta?" "eh hakane, to waye shi? Kuma ya akayi kema bakiyi amfani da abinda kika cemin ba wajen ganin yasoki" Shiru Feenah tadanyi sai kuma tadanyi murmushi wanda yafi kama da na takaici tace "I told you be sanni ba, besan fa wanzuwata ba tayaya zanyi yadda na gayamaki? Wannan sai idan akwai sannaya ko yayane kamar dai naku amma wannan Saidai na ganshi a hanya ko sunan shi ban ta6a sani ba har kawo yanzu Kuma bazan iya cusa kaina gareshi ba that's not perfect a matsayina na mace dukda kuwa nayi qoqarin lurar dashi yasan dani amma be saniba ko don banje directly ba? Yes nace maki ki kyautata mashi bawai ina nufin kiyita rawar kai ba, maza basason mai rawar kai sunfison mai aji kamar dai ke dinnan, karki chanza mashi in anyway har yagane kina mashi rawar qafa amma ki cigaba da bayyana mashi kyawawan hallayenki a kaikaice da duk abinda zaisa ya dinga ganin mutuncin ki ki kuma dinga burgeshi ciki harda son family dinshi, kowanne namiji yana matuqar alfahari da mai son family dinshi, mai nuna damuwa da kulawa akanshi dama sauransu So bawai rawar kai zakiyi ba, no, ki cigaba da zama classic girl dinki don class adon mace ce dukda ba'ason yayi yawa, insha allah zakiga komai yazo miki cikin sauqi, insha allah" Sosai zee ta gamsu da bayyanan Feenah Hakan yasa taji zuciyarta ta rage nauyi ga wani qwarin gwiwa datakeji tasamu sosai Saidai kamar taga yanayin Feenah ya chanza tun lokacin da ta ambato mata wancan mutumin "bye, am sleepy ki gaidamin yaya da daddy" inji Feenah Zatayi magana taji qiit an katse wayar Bïñ wayar tayi da kallo taga tama sauka Hakan yasa itama ta sauka ta ajiye wayar gefe tayi folding din hannunta a qirji tashiga dauko magangganun Aunty Feenah da daddaya tana masu filla filla *WASHEGARI* Yau juma'a kuma yau ta tashi da qudurin zuwa school, jiya ta dade idanunta biyu tana nazarin magangganunsu da Feenah takuma yanke shawarar zata gwada tagani Hakan yasa ta yanke shawarar zuwa school yau Kamar yadda tasaba duk ranar juma'a yau ma bata fito da wuri ba sai bayan sallar juma'a Sanye take cikin shadda dark purple buba wanda tasha aiki mai kyau daga daman rigar har qasa Kanta yafe da farin siririn gyale, takalminta farare haka ma jakkarta da agogonta Motarsu tanufa tana zuge zip din jakkarta data fiddo waya daga ciki Koda ta qaraso har bala ya budemata kofa Hakan yasa ta shige ya rufo ya zagaya shima ya shige suka fice daga gidan *UMYU* Tunda suka shigo harabar makarantar zuciyarta tafara qara gudu Bata san meyasa ba sai jitayi tana fargaba, fargabar yin amfani da shawarar Feenah nan gaba abu ya kwa6e mata Batayi nisa a dan guntun tunanin data fara ba taji an budemata kofa Hakan yasa ta lumshe idanu ta bude sannan taja nannauyan numfashi sannan tafara yunqurin saukowa Iskar dake kadawa ya bugi fuskarta Hakan yasa ta lumshe idanu tasake budewa tana shaqar sanyayar iskar dake kadawa Rataye jakkarta tayi a hannu tafara tafiya tana dan kallon harabar da daidaikun mutane keta kai kawo Tasan yau mutane qalilan ne suka zo don dama ko anyi resuming fully mutanen dake zuwa ranar friday basada yawa bare yanzu da ba'a ida resuming ba Ahankali ta cigaba da takawa a cikin zuciyarta tana tunanin anya kau yau zasu hade da Deen? Tasan ba lallai bane su Hade ba don ba lallai bane yazo yau ba Amma still tana sa ran ganinshi Tunawa tayi da kalmarshi ta rannan Wai ko fushi take saboda ya maido mata wayarta? Wato yasan abin da ban haushi kenan, yasani dagangan yayi mata Saikuma wani tunani ya bijiromata a kwakwalwa Wane tunani zaizo mashi bayan tafiyar ta a ranar? Qila ya dinga yimata kallon mai riqo marar saurin yafiya tunda har haquri yabata amma taqi sauraronshi Tunawa tayi da lokacin da tabashi hqr akan watsamashi coke datayi yakuma haqura nan take batareda ya qullaceta ba Saita auna abubbuwan biyu a mizani sai taga idan ma qullatar ne shi yafi cancanta ya qullaceta a lokacin ba itaba saboda shi yanada right din amsar abinda yayi mashi yakuma maida abinda beyi mashi ba dukda ba dadi maida kyauta hannun kyauta baya Yanzu tasan kallon mai riqo da rashin saurin yafiya zai dinga yimata kuma bataga laifin shi ba don kusan haka ne tunda ga lokacin takasa tsayawa ta saurareshi dukda iyakar bakin qoqarin shi dayayi na ganin tayi Hakan Ahankali bugun zuciyarta yafara qaruwa sannan wannan feeling din data saba ji idan yana kallonta tafara jinshi Dago kai tayi tafara dan waige waige ahankali don ganin inda zata ganshi Daga can jikin wani office mai facing dinta ta ganshi jingine da bango hannuwanshi harde a qirjinshi Ja tayi ta tsaya itama tana kallonshi kamar yadda shima yakeyi Ganinshi a yanzu yasata samun daya daga cikin Tambayoyin datakewa kanta Yaushe? Yaushe tafara sonshi? Ganinshi datayi yau da shigar dake ajikinshi yabata amsarta Tafara sonshi ne ranar data fara ganinshi Rana mai kamar ta yau, sanye da shiga irin ta yau Ranar da bracelet din hannunshi ya sarqaho mata gyallenta Sai yanzu tagane ma'anar Hakan, wato Hakan na nufin bond ne tsakaninsu tunma kafin susan juna Bracelet dinshi ya sarqaho gyallenta ne don akwai alaqa mai qarfi dazai qullu tsakanin mammalakin bracelet din da mammalakiyar gyallen Haka kwakwalwarta ta bata, hakane! Kasa dauke ido akan juna sukayi suka cigaba da kallon juna kowanne da irin kibiyar dake fitowa a idon dan uwanshi yana fadawa nashi A hankali murmushi yafara forming a fuskarta tana cigaba da kallonshi Dukda bata ganin fuskarta amma tasan this is the sweetest smile ever data ta6a yiwa wani Gani tayi yayi blinking idanu sau biyu kamar na mai son tabbatar da abinda yake gani can kuma ya miqe daga jinginen dayake da bangon yana cigaba da kallonta kamar mai son tabbatar da wani abu A hankali shima fuskarshi tafara washewa, murmushi yafara gauraya fuskar, wannan cool murmushin nashi mai tafiya da zuciyarta... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:36 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *036* "Am happy kinzo Zainab, jiya da shekaranjiya haka na wuni a school dinnan amma ko sign of you ban ganiba, am damn worried" inji Deen cikin cool voice dinshi fuskarshi dauke da murmushi Zee dake kallonshi shima tadanyi murmushi ta dora jakkarta akan desk din library din ta dora hannunta kan desk ta buga tagumi "and why are you worried?" tafada tana kallonshi Murmushi yasake saki ya dan kauda kai sannan yasake kallonta "saboda yanayin da muka rabu rannan, it's not normal shiyasa nashiga damuwa" "damuwa akan me?" tasake Tambayar shi "damuwa akan halin dazaki shiga" "meyasa ka damu to?" "saboda nasan nine sila" Dan daga gira daya tayi "really?" Kada mata kai yayi yace "yeah, and I begged you amma kinqi saurarena" Kauda idanunta tayi akanshi tana jinta a wani yanayi jin yace _*i begged you*_ He's so innocent, beda matsala ko kadan, beda girman kai irinna wasu samarin, yayi ta koina. Jin tayi shiru yadan qara matsowa jikin desk din data raba tsakaninsu yace "am sorry, qila lokacin banyi explaining kaina ba yadda ya kamata shiyasa kikaji haushi but the truth is banyi haka don kiji haushi ba, Swears" Murmushi tadanyi, ba na komai ba saina tausayin kanta, soyayyarshi a zuciyarta qara qaruwa take da duk wani kalma tashi She's confused, tarasa gane wannan abu Lokacin data qaurace mashi zuciyarta ta azabtu yanzu kuma dasuke tare zuciyar qara dulmiyawa take tana qara yin nisan nisa a sonshi, Tambayar anan itace dama haka so yake? Koko nata yazo da hakan? "kinyi shiru" inji Deen yana kallonta Itama kallonshi take, idan yana wani abin kamar shima sonta yakeyi, koko shima sonta yakeyi? Koko da Gaskiyar Aunty Feenah shima yana sonta bedai gano bane? Koko ya gano bazai iya fadi ba? koko hakanan yake wannan abin babu sonta a ranshi? She's confused Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace "ok duk naji amma ban huceba" 6ata fuska yayi yace "O'O! Meyasa? Haven't I apologize?" "you have amma it's not accepted" Shiru yayi yana kallon na wani lokaci sannan yace "then tell me what to do" Gyara zamanta tayi ta kalleshi taga ya buga tagumi shima yana kallonta alamun yana jinta ga murmushin dayaqi barin fuskarshi Tundazu Itama murmushin tayi sannan tace "idan kanason in huce saika amsa" Dan 6ata fuska yayi yace "O'O! Please mubar maganarta haka nan mana" Daga kafadu tayi tace "yes zamu bari, idan ka amsa kenan... Look na bakane ba don komai ba sai don kyautatawa dakuma tunanin danayi mun zama daya, we're friends.. Good friends so banyi tunanin idan nayi maka abu zakayi rejecting ba kamar yadda nima idan kayimin bazanyi rejecting ba, that's what real friends are, amma Hakan dakayi yasani tantama akan Hakan kuma nima bazai bari nazama very free da kai da abinka ba" Ajiyar zuciya ya sauke batareda yace komai ba "what did you say?" tafada tana kallonshi ita kanta tarasa dalilin dayasa ta nace ma Hakan akan dole saiya amsa Ajiyar zuciya ya sake saukewa sannan yace "Alright... Thank you so very much!" Wani murmushi da batasan dashi ba ya su6uce mata sai kuma ta jawo jakkarta tashiga zugewa Tsayawa yayi yana kallonta feeling very happy ganinta itama in a happy mood Gani yayi ta zaro wayarta ta qara dagowa ta kalleshi sai yaimata murmushi itama ta maida mashi martani sannan tashiga yan danne danne aciki can ta ajiye itama tana sauke Ajiyar zuciya "me kikayi?" inji Deen "ina ruwanka?" tafada tana harararshi Dan Hade gira yayi yace "I'll tell kaka" Dan Dariya tayi saikuma ta tuna da maganar Feenah na taso family dinshi takuma dinga nuna damuwa akansu Saikuma ta tuna abinda ya ta6a cewa a hospital _*duk duniya banida masoyiya kamar kaka, daga ita sai mai sonta, sai mai son mai sonta sai wadda taso mai son wadda tasota*_ "Allah sarki kakata, please how is she?" Kallonta yayi sai taga ya saki murmushi "she's fine amma tawace ba taki ba" ya qarashe yana harararta Itama harararshi take tace "inji wa? Kai yanzu tsohon yayene, ni kaka ke yaye yanzu" "ba wani nan, ni ake yaye kuma ni za'a cigaba da yaye" "in your wildest dream ba, tambayi kaka kasha labari, nan gaba kaka tarkatoka zatayi ta watso waje ni nakoma ciki inyaso sai katafi wajen mummy kema" "mummy? Yes I like her, indai wajenta zani babu damuwa atleast zan huta da durar magani da kaka kemini" Yar Dariya zee tayi, a halin yanzu jinta take wasai kamar bata ta6a shiga damuwa Hakan yakuma qara tabbatar mata cewa farincikinta yana tareda Deen "har yanzu baka bar tsoron maganin ba?" "har gobe.. What's Good about magani? I hate it ko warinshi banaso sai inji cikina na rumbling" Murmushi tayi tace "aikau kanada aiki don itama mummy ba sauqi gareta ba, bari ganin tana washe maka 36" Murmushi shima yayi yana jin dadin wannan moment din, kasancewa da ita ahaka ba qaramin nishadi yake sashi ba "babu komai, dukda Hakan nabarmiki kakan abarmin mummy" "hmm idan mummy ce gaka ga ita, abu mai sauqi?" Murmushi sukayi atare sai shiru yadan gitta a tsakaninsu Jin shirun yasata dan dagowa ta kalleshi taga shima ita yake kallo Murmushi ya sakarmata yace "tell me" Gabanta ne yadan fadi sai ta dake tace "me?" Tagumi yasake bugawa yace "yadda kikayi spending holiday dinki" Dauke kai tayi tana sauke Ajiyar zuciya, cikin zuciyarta tace 'wannan holiday din ai shine worst holiday dina, duk a burkuce nayishi kuma kaine sila' A zahiri kuma tace "well the holiday is so amazing, kaga the first week a hospital nayishi kafin a sallameku sai nasake wani agida doing nothing sai hutawa daga baya kuma nayi tafiya zuwa garinsu mamanmu" "wow! Interesting, ina ne?" "Ruma" "Ruma? State ne?" "No gari ne a 6atagarawa local government" "wow! I love travelling" yafada yana murmushi still da tagumi "yeah travelling yana da dadi sosai, kaga zakaje wani wuri ka xauna da mutanen Wurin for a while, you'll learn something From them therefore adding to your experience" Kada kai yayi cikin gamsuwa "nima zanso watarana nayi tafiya wani wuri" "baka ta6a ba?" "I don’t think so don da wayauna ban ta6a tafiya ba qila sannan ina qarami" Shiru tayi saikuma tace "karka damu ai watarana nasan zakayi, ko wajen dangin mamanku ko wasu naku haka, ko duk cikin garinnan suke?" Shiru shima yadanyi sannan yace "maybe" Itama shiru tayi tana kallonshi, da alamu wani tunani yayi crossing zuciyarshi gameda danginshi Ita dai tana mammakin yadda za'ayi ace mutum beda wani dangi bayan kakarshi Koda mamanshi da babanshi sun rasu ina danginsu? Ina dangin uwa? Ina na uban? Ina na kakar itama? Abinda ya dade yana qullemata kai kenan don ko a kwanciyarsu asibiti yan unguwarsu kawai ke zuwa babu danginsu ko daya Ganin kamar shima yafara nisa a nashi tunanin sai tace "kaifa? How did you spend yours" Murmushin daya fara tafiya daga fuskarshi yadawo sannan ya gyara zama shima ita kuma ta buga tagumi kamar yadda yayi dazu yashiga bata labarin yadda ya cinye lokacin hutunsu wanda yawancin wajen aiki yake zuwa ya dawo ya taya kaka aikin sana'arta kamar dai yadda yasaba Sun jima sosai suna firarsu mai cikeda nishadi har mancewa ma suke da tafiya gida Suna ahaka kiran wayar bala tashigo wayarta sai a sannan suka farga da tsawon lokacin da suka dauka tare Daga wayar tayi yafada mata ya iso Tambayarshi tayi ya amso mata saqo a wajen maid dinsu? Da eh ya amsa yana cewa gashi nan ma hannunshi Kwatancen inda zai taddasu tayi mashi tace ya kawo mata sannan ta kashe wayar Ba'a jima ba kau sai gashi ya qaraso gaban library din Waya yaqara buga mata ya sanar daita ya iso Hakan yasata tashi tafito Amsar saqon tayi tace mashi ya jirata yanzu zata fito Komawa tayi cikin library din tana zuwa ta ajiye ledar agabanshi Ko be duba ba yasan meke ciki Hakan yasashi yin murmushi yana jin wani iri Jawo ledar yayi ya dan bude ta ya leqa saikuma ya dago ya kalleta "thank you so very much, jazakillah khairan" Lumshe idanu tayi ta bude tareda yimashi murmushi batareda ta amsa ba ta tashi ta dauki handbag dinta ta rataya "ni zan wuce, he's waiting for me outside" Shima tashi yayi yace "ok, sai monday ko?" "yeah" "to ki gaidamin mummy na" Wani dadi ya ratsa zuciyarta jin abinda yace "insha allah, kai fa? Ba yanzu zaka tafi ba?" Dan yamutsa gashin kanshi yayi yace "yes.. Sai anjima kadan, akwai abinda zanyi ne" Tasan qarya ne kawai beson suyi mashi tayin rage mashi hanya ne amma saita share tace "ok, see yah" Ta juya tafara tafiya tana jin idanunshi akanta itama tana jin kamar ta juyo ta sake kallonshi amma ta maze Har takai bakin kofa zata fita taji ya kira sunanta wanda taji kiran har cikin zuciyarta Dakatawa tayi sannan ta juyo ahankali tana kallonshi Shima takowa yashiga yi ahankali harya qaraso gabanta ya tsaya suka shiga kallon kallo Ahankali ya dago hannunshi ya miqamata Maida kallonta tayi a hannunshi taga yar qaramar wayarshi ce yake miqomata Bata amsa ba sai sake maida kallonta datayi a kanshi cikin ayar tambaya "your digits.. Please" Dan wara idanunta tayi cikin tsananin mammaki, _finally.. Finally!_ Saurin gyara yanayinta tayi sannan ta dan yamutsa fuska "ban gane ba" "number ki zaki samun.. Please" _OMG! Sai Yanzu? Why are you so slow?_ Abinda tafada a zuciyarta kenan A zahiri kuma tace "Why? I thought kanada number mummy" "yes, yanzu taki nakeso so that zamu dinga gaisawa musanmman on weekends zamu kuma dinga sanar da juna some important stuffs idan sun taso bama tare" yafada calmly Murmushi tayi cikin zuciyarta, kai mutumin nan yacika gara mutane, sai yanzu yasan duk da wadannan? Tun yaushe take expecting haka amma sai yanzu data gama fidda rai sannan Jitayi tana son qara jamashi aji amma kuma tana gudun karya tsinke😝 Hakan yasa ta amshi wayar ba yabo ba fallasa amma deep down tsallen murna take Number ta ta sakamashi sannan ta miqa mashi ta juya tana cewa "bye.." "bye!" taji ya amsa mata gab da zata fita Koda ta fito babu bala Hakan yasa ta nufi parking space tanajin kamar tana tafiya kan iska don dadi, jitake kamar tayi ta tsallen murna tana ihu Dakyar dai takai kanta bakin motar tashige ciki fuskarta a washe Komawa tayi cikin kujerar motar ta lafe ta dora hannayenta saitin zuciya tana sauke numfashi ahankali Ita kadai tasan yadda takeji, farinciki takeji marar musaltawa, farincikin da rabon da taji irin shi harta manta Lumshe idanunta tayi broad smile shimfide a fuskarta Deen nayi mata gizo a idanu Tanajin tashin Motarsu dakuma fara tafiyar ta, ahankali ta bude bakinta cikin rada tace _bye ruhii❤️_ Saida ya tabbatar sun tafi sannan shima ya tashi ya hada tarkacenshi shima yafito Cikin sa'a yana fitowa wata napep tazo wucewa ya tareta sukayi ciniki ya hau suma suka lula 💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝 _first let me tell you_ _I cannot wait to see you 👀_ _you're the treasure? I've been waiting for 💃💃_ _Did you know? Did you know?_ _how much I really need you?_ _I dey pray for the day when_ _I can finally kiss 💋 you 🙈_ _you know say everyday I dey pray 🤲🏻 for you 😭_ _in my heart oh there's a permanent place for you 👉🏻❤️_ _that's why my heart dey beat like.._ _duduke 💓 *du💓* *du 💓* *ke💓*_ _cos na you I choose oh_ _Ayonfemi 👩‍❤️‍💋‍? ayonfe😘_ Waqar datake bi kenan na simi mai taken _Duduke_ tana tsane gashinta kasancewar bata dade da gama wanka ba don wani irin zafi ake garin yau Da rawar fairy ta isa gaban closet dinta tana cigaba da bin waqar ta bude shi tana duban kayanta tana shawarar wanne ya kamata tasa Wata blue black armless gown ta ciro marar nauyi da farar hula takuma koma gaban mirrornta da rawar data taho Kallo daya zakayi mata kasan yau fa take sallah a wajen ta don farincikin datake ciki be 6oyuwa kwata2 Saka kayan tayi sannan taja kujerar gaban dressing mirror din tana busar da gashinta Saida tagama sannan ta dan shafa powder sama sama tasaka kwalli kadai a idanun sannan tayi amfani da roll on mai sanyin qamshi a duk kusurwar jikinta sannan ta feshe kayanta da turare shima marar hayaniya don dama duk yawancin turarrikanta sai kana gab daita zakaji qamshinsu bata cika son wanda da kaje wuri ba turarenka zai fara tonaka Kashe disc din dake waqar tayi ta bude kofa ta fice A dining ta tardasu har sun fara cin abincin "daddy na!" tafada da yar qara sannan tayi wajenshi tabashi side hug Dariya daddy yayi yace "daughter na!" cikin yanayin da tayi magana Dariya sukayi gabadaya mummy ma tadanyi murmushi tana cigaba da cin abincinta Ja mata kujerar kusadashi daddy yayi ta zauna fuska fall murmushi sannan ta kalli mummy tace "mummy ina wuni?" Dagowa mummy tayi ta harareta saita sunne kai tana sosa kai Dariya daddy yayi yace "kyaleta, kishi take don baki fara yimata magana ba, me zakici? Tundazu na aika akiraki shiru" "daddy wanka nake shiyasa" tafada tana daukar spoon tasaka a plate din daddyn alamun tare zasu ci "guess yau tsintuwa kikayi, wannan fara'ar haka? To Gaskiya raba daidai za'ayi" Rufe fuskarta tayi da tafuka tana Dariya tace "kai daddy" "eh mana, naga yau farinciki akeyi, kwananan you're so moody amma yau shar" Murmushi tayi cikin zuciyarta tace 'bazaka ganeba daddy' Azahiri kuma tace "mood swing ne daddy" Cigaba da cin abincin sukayi suna firarsu da daddy mummy na dan samasu baki jefi jefi, kallo daya zaka su burgewa don they are small example of a Happy family 💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜 Bude kwalin yayi ya ciro wayar dake kwance carefully yana jujjuyata a hannunshi Wayar ta hadu iya haduwa, he can't believe shi zai dinga amfani da wannan wayar Jin alamun za'a bude kofa da muryar kaka yasa yayi saurin ajiye wayar bayanshi Saidai he's too late don taga alamun ya 6oye abu "hmm me ake 6oyemin?" tafada tana qarasowa Dan kumbura fuska yayi yace "ashe kece nayi tunanin 6era ne" "eh 6era ce mai qaffafu biyu" tafada tana gallamashi harara Murmushi yayi sannan ya fiddo wayar daga bayanshi ya miqamata yana cewa "kalla kaka" Dan wara idanu kaka tayi ta zauna kusadashi ta amshi wayar itama tana jujjuyata "wannan ba wannan wayar bace?" inji kaka tana qara jujjuyata a hannu "itace kaka" "to ba kace ka mayar ba? Ya akayi kuma na ganka daita?" "itace ta maidomin kuma" "wa? Mummyn?" Sai a lokacin ya tuna ashe kaka batasan zee ce mai kyautar ba "A'a Zainab ta aiko" Tagumi kaka tayi tace "ni ma'u, dukda an maida Saida suka maido? Yanzu ya kake ganin za'ayi" Shiru yadanyi sannan yace "Kaka mu amsa kawai tunda babu dadi aqara maidawa Saidai bazamu qara abu hannunsu ba, koko?" "kuma fa, ka kawo shawara kawai mu amsa tunda sun nace ya zamuyi?" Murmushi yayi yace "tanada kyau ko kaka?" Dan yamutse fuska kaka tayi tace "ni ai kasan ban cika ganin kyan irin wadannan wayoyin ba, dadai irin tamuce" Murmushi kawai Deen yayi ya ciro tashi qaramar wayar ya budeta yafara zaro sim card da memory card dinshi "to amma badai riqeta ba zakayi, sayar da ita zakayi ko?" Dakatawa yayi daga abinda yake yace "meyasa?" "tayaya zaka riqe wayar dubu hamsin? Wannan ai almubazzaranci ne, zaifi maka ka Saida kasamu wani abu mai muhinmmanci kayi dasu wannan ta hannunka ta isheka" Dan jimm yayi sai kuma yace "kuma fa, insha allah haka xa'ayi" Cikin jindadi kaka tace "yauwa kyakyawa na, kaga sai muyi wani abu dashi ko jari yadda zamu dinga samun kudi ta wata hanyar bayaga namu ko?" Kada mata kai yayi alamun eh yana murmushi amma deep down yasan tatsuniyace don babu abinda zai sashi siyarda wayar, yasan idan zee tasani to daidai yake da yankewar alaqarsu "yauwa to yanzu maza ka shirya katafi" "A'a kaka yanzu marece yayi, mubari sai gobe idan ba Haka ba tayin wulaqanci zasuyi mana" "kuma fa, to shikenan a bari sai goben sai kutafi da salmanu don naga yafika baki idan katafi kai kadai qwararka za'ayi" Murmushi kawai yayi bece komai ba Tashi tayi ta nufi kofa tana cewa "bari naje naduba abinda yake kan wuta karyayi kamu, kai amma mun gode wannan aka bamu kudinta ai mun warware" Saida ya rakata da kallo harta fita sannan ya sauke Ajiyar zuciya ya maida hankalinshi kan wayar hannunshi yana ida zuramata sim din da t-card sannan ya kunnata 'wow!' yafada under is breath ya shiga daddanata yana shige da fice a wurare dayawa cikin ta yana jin wani irin nishadi a ranshi 💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖 Tun dazu waya ke hannunta tana danne danne Saidai a zahiri ba danne dannen take ba, wani abu take jira Kira take jira, kiranshi amma haryanzu shiru Tunda tadawo daga school take kasa kunne da baza idanun ganin kiranshi amma shiru wai mallam yaci shirwa Da tagaji da jira saita kunna datar ta tashiga whatsapp dinta Gani tayi Aunty Feenah na online Hakan yasa tayi mata sallama Bayan minti daya ta amsa mata nan suka shiga fira both typing da voice note inda Feenah ke Tambayar ta ya ake ciki ita kuma ta gayamata sun hade yau har sun koma sun jone kamar da tana kuma gayamata yadda yake nuna damuwarshi akanta kamar yana sonta shima din Qarfin gwiwa Feenah taqara mata na karta sare kuma ta dinga yawaita addu'a dakuma neman za6in allah Sun dade suna fira Feenah nata bata shawarwari yadda kasan yaya da qanwa sannan daga baya Feenah tace insha allah kwanan nan zata shigo katsinan itama zee tayi ta murna tana cewa allah yakaisu lokacin Da haka sukayi sallama duk suka sauka Duba lokaci tayi na saman wayar taga har 12 na dare Haushi taji ya turnuqe ta Wannan wane irin slow mutum ne mai ban haushi? Dama yasan ba kiranta zaiyi ba ya amshi number ta? Koko duk salon jan rai ne daya saba? Wannan idan aka tafi a haka ga yadda take ganin alamu Koda sonta yake saita kusan zarewa sannan zai bayyanamata Kashe wayar tayi cikin jin haushi ta tillar daita can tsakiyar gado taja bargo har kai tana jan tsaki A ranar ta dade barci bai dauketa ba sai juyin datake tayi, tsaki kau tajashi yafi cikin kwando, daga baya dai tasamu barcin ya sadado ya dauketa *WASHEGARI* *02:40pm* Zaune suke ita da mummy Kadai a dining suna lunch Bakajin komai a Wurin sai qarar cokali sai kau maganar t.v dake dan kawomusu anan Zee sai tsatsakurar abincin take don dole don kwata2 batada appetite Yau haka ta tashi zuciya a cunkushe komai ma bata haushi yake shiyasa batada walwala sosai Mummy data lura da Hakan taita mammaki don kwanan nan zee takoma kamar wata mai aljannu, yanzu zaka ganta cikin farinciki anjima kuma ka rasa gane kanta Yanzu dai kamar jiya haka fa tayita washe baki kamar wacce aka biyawa hajji amma yau kwata2 babu wannan fara'ar saima kumbure2 data lura tana yi Tundazu Ringing din wayar zee ne ya katse shirun Wurin wanda Hakan yayi daidai da dakatar da cokalin da zee tayi niyyar kaiwa a baki Kallon screen din take ganin sabuwar number ce zuciyarta na qara gudu Dagowa tayi ta kalli mummy taga itama ita take kallo "ki daga mana" inji mummy ganin wayar takusan tsinkewa Kamar dama umarnin mummyn take jira saita dauki wayar ta daga kiran ta karata a kunne batareda tace komai ba "Assalamu alaiki..." Luu... Tayi baya baya ta jingina da kujerar datake akai kamar marar lakka tana lumshe idanu ta bude daidai lokacin da muryar tashi ta daki dodon kunnenta... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:36 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *037* _jiya nayi mistake, *Ruma* cikin qaramar hukumar *BATSARI* take ba *6atagarawa* ba. Afuwan👏_ "Hello?" Muryarshi taqara ratsa dodon kunnenta dama zuciyarta baki daya Ahankali ta bude lumssasun idanunta ta saukesu akan na mummy dake kallonta itama Saurin zabura tayi zaune don ita harga allah ma manta a inda take zaune "hello" tafada tana miqewa tsaye "excuse me mummy" tafada tana wucewa hanyar stairs da sauri Mummy ba tace komai ba sai Binta datayi da idanu "hello?" Deen yaqara cewa a karo na uku "hy" zee ta amsa daidai tashiga daki ta maido kofa ta rufe Sautin murmushin shi taji wanda ba qaramin tasiri yayi a gareta ba "aslm alaiki" Zamewa tayi ta zauna gefen gadonta tana shaqar numfashi ta fesar ahankali tana jin yadda 6acin ran data wuni dashi na fecewa ahankali yana bin iska "wslm.." Sai shiru ya biyo baya Jin shirun na neman yin yawa yasata cewa "yes? Who’s this?" Sautin murmushin shi taqara ji sannan taji yace "Kamal ne" Itama murmushin tayi amma marar sauti tace "Kamal?" tafadi sunan cikin wani salo da Saida Deen yakoma ya jingina da bangon dakinshi ya lumshe idanu Jiyayi tasake cewa "wane Kamal din?" Murmushi yayi wanda tajishi sarai yace "like seriously baki gane muryata ba? Deen ne fa" Murmushi tayi cikin zuciyarta tace 'ko cikin muryoyi dubu naji muryarka saina tantanceta" A zahiri kuma tace "Oops! Deen? Dama naji muryar sounds familiar ashe kaine?" Murmushi yasakeyi yace "eh nine, good afternoon" "afternoon, how you? Ina kakata?" "lfy lau, kakarki na nan lfy lau ina mummy na?" "mummy tana dakinta" Murmushi taji yasake yi sai jitayi dama tana ganinshi taga smiling face din "just call to say hello" Murmushi itama tayi mai sauti tace "thank you so much, how's weekend?" "weekend alhamdullilah, zaki zo school on monday?" "why not?" tafada tana jawo pillow tana rungumewa a qirji "ok saimun hadu monday din" inji Deen a dayan bangaren Ba haka tasoba don ita nan gyara zaman susha firarsu tayi amma ya ta iya? "ok allah ya kaimu" tafada ahankali "bye ki gaida min mummy" "zataji nima ka gaida kaka" "ok bye" "bye" Kittt... Taji an katse wayar Lumshe idanu tayi ta Janye wayar daga kunnenta ahankali tana sauke wani nannauyan numfashi Wani kayattacen murmushi ya su6uce mata tayi wani juyi a kan gadon wanda yakaita tsakiyar gadon ta kwanta rigingine still pillon a qirjinta Number daya kirata dashi ta shiga kallo fuskarta dauke da murmushi Latsa wajen adding contact tayi tayi saving din number shi da _*D❤️*_ Sannan ta maida wayar ta rungume a qirji ta maida manyan idanunta ta rufe. *** "kyakyawa na! Kyakyawa na!!" Kiran da kaka keyi mashi yasashi ajiye wayar ya tashi ya fito "kakata?" yafada yana qarasawa kitchen din datake "maza ga abincinka nan ka dauka ka cinye ka kawo na qara maka"tafada tana nuna mashi kwanon abincin Waro idanu yayi yace "aqara kuma? Kaka wannan ai yayi yawa" Dan harararshi tayi tace "kuma saika cinyeshi ba, maza dauka bari na shinfida mana tabarma waje" tafada tana fita daga kitchen din Tabarma ta fiddo ta shinfida daidai Deen yafito da abincinshi dana kaka Zama sukayi kowa yaja abincinshi gabanshi sukayi bismillah suka fara ci Can kaka ta dago tace "yau za'a Saida wayar nan ko?" Dago idanu Deen yayi ya kalleta sannan ya kada kai kawai "yauwa ai gwara ayi a saidata ko mun samu jari, jiya kusan raba dare nayi ina tunanin yadda zamuyi dasu harna samu na yanke shawara Idan aka samu kudinnan zan qara jarin kokon nan don dama sau dayawa ba isa yake ba kafin takwas ya kare azo kuma aita nema babu, kaga saimu qara yadda zamu dinga samu da dan kwari ko?" Kada kai Deen dake aikin sauraronta yayi alamun gamsuwa "Sai kuma wata shawarar dana yanke, mezai hana nafara siyarda dambu?" Dagowa Deen yayi ya kalleta "Dambu kuma kaka?" "eh dambu, kaga da hantsi wajajen 12 haka zuwa azahar zanyi kuma naga babu masu yi anan unguwar sai inga kamar za'a samu alhairi, koko?" "to kaka muda bamu ga kudin ba tukkuna" "ai zamu gani ko? Ba yau za'a siyar daita ba?" "eh" "to? Ina wannan lissafin ne yadda komai zai qara zo mana da sauqi, kaga yanzu ba aiki kuke samu ba can wajen aikinku sai wannan yar sana'ar tawa ta koko ita ke dan taimaka mana ga kudin makarantarka don ma aski yazo gaban goshi kaga ya kamata mu qara himma ko kuwa?" Deen dake sauraronta Tundazu ya kada kai ahankali zuciyarshi fall tunani kala2 Yasan tanada Gaskiya don yanzu sunfi raja'a akan abinda ake samu a sana'ar ta na koko da qosai don ba aiki suke samu ba sosai yanzu yawanci yan gyare gyare ne da kudinsu basu taka kara suka karya ba, ga kudin makaranta Gaskiya so samu a siyarda wayar don zata taimaka sosai amma kuma bejin yana iyawa bawai don yana kwadayin riqeta ba don gayu ko wani abu, A'a kawai jiyake bazai iya siyarda kyautar da akayi mashi ba, kyautar kuma ta zee "yauwa kayi da jiki ka gama kaga idan ka fita siyan geron gobe sai ku wuce kasuwar tsaitsayen ku sayar" Da to ya amsa mata ya cigaba da cin abincin cikin sanyi, zuciyarshi fall tunani Atare suka gama cin abincin ya kwashe kwanikan yakai kitchen din yadawo ya xauna kusada kaka dake qilga kudin dazata bashi yayi sayayyar Saida tagama sannan ta bashi ya amsa ya tashi ya shiga daki ya dauki wayar yafito yayi mata saiya dawo ita kuma tabishi da adawo lfy Koda yafito hanyar gidansu salmanu yayi Saidai kafin ya qarasa yaci karo da qannen salmanun nan yake Tambayar shi ina salmanun sai yace bayanan yafita Hakan yayi ma Deen dadi sosai sai kawai yayi tafiyarshi kasuwa don yiwa kaka sayayya Koda yadawo da batun wayar ta tareshi nan ya gayamata ai be samu salmanun ba shiyasa basuje ba Bataji dadi ba Amma saita haqura akan ai akwai gobe, sai aje siyarwa goben Deen kawai jinta yake amma bayajin zai iya Hakan don he valued the phone kamar yadda yake value mai ita Da daddare bayan sun fito sallar isha'i Deen ya tari salmanu yayi convincing dinshi akan Koda kaka tayimashi maganar siyarda waya yasan abinda zai gayamata Dayake salman dan maqocinsu ne kuma sunzo tsararraki da Deen kuma ba laifi suna mutunci sosai Hakan yasa ya amince bayan yagama tsokanarshi akan to ya tanaji kudin dazai biyashi na qaryar da zaiyi don buhari ya hana aikin banza Shidai Deen Dariya kawai yayi sukayi musabaha ya wuto gida Washegari ma haka yaita raina ma kaka hankali akan bega salmanu ba can dai taje gidan da kanta tabada sallahun idan salmanu yadawo yazo tana nemanshi Dayake shima yasan kiran ko na menene be tashi zuwa ba sai bayan isha'i, sanin cewa babu halin zuwa lokacin saita cemashi yatafi yadawo gobe da marece zai raka Deen kasuwa Da to kawai ya amsa ya tashi yayi tafiyar shi. A bangaren zee kau yau ma haka taita jiran kiran Deen Saidai bata qwalaffa rai ba irinna shekaranjiya Saidai har dare babu kira babu alamun shi Bata wani damuba don tasan gobe zasu Hade school Hakan yasata kwanciyarta hankali kwance wani barci mai shegen dadi yayi gaba daita *MONDAY* Tafiya take ahankali cikin tafiyarta data zame mata jiki Bïñ harabar school din take da kallo ganin yadda yacika sosai yau don dama kowa wannan monday din ne harinshi Qara gyara zaman gyallenta da iska ya saukoshi daga kafada tayi tana cigaba da tafiyarta "Zainab..." Taji an kirata daga baya wanda ko bata juyaba tasan mai kiran Yitayi kamar batajiba ta cigaba da tafiyarta tana murmushi slightly "Hey! Zainab.." taqara jin muryarshi na qara kusantota Wani murmushin tasake saki tana dan daga gira daya sama batareda ta tsayaba "Zainabbb!" taji a kusa kusa da ita da alama yana gab da ita Sai a lokacin tafara slowing down ta juyo ahankali cikin son ganin wa ke kiranta Deen din ne, sanye cikin baqin wandon jeans sai farar t-shirt mai zanen baqi a gaba, as usual sumarshi a dan tuje take dan akwai zirin dama ya biyo mashi ta fuska Ganin shine yasata tsayawa tana kallon yadda yake ida qarasowa yana dan yatsine fuska "my goodness Zainab, are you deaf?" yafada yana sauke numfashin saurin dayayi Dan daga gira daya tayi cikin alamun tambaya shikuma daidai ya qaraso "tun daga bakin gate nake kiranki amma bakiji, are you sure Kunnuwanta lafiya lau suke?" Harararshi tadanyi suka cigaba da tafiya tace "kokuma kaine za'ayi ma wannan Tambayar ba? Are you sure maqoshinka lfy lau yake? Dama tayaya zani jika da wannan voice din naka?" "Allah da qarfi nake kiranki, cewa nake Zainab! Zainab!! But unknown to me ashe kurma ce" Juyowa tayi tayimashi mugun kallo shikuma yadan matsa gefe yana Dariya "Allah, gashi energy dina ya qare Wurin shouting" "dama kanada energy din ne? Lazy bone" tafada tana dan Harararshi "O'O! Am not lazy" "O'O! You are" ta kwaikwayeshi Kafin wani yasake magana a cikinsu sukaji daga bayansu ance "hey! Ku biyunnan kuzo" Atare suka juya daidai wanda ya kirasu din shima ya kallesu sai kuma ya dauke kai yana cigaba da Fiddo abubbuwan dayake fiddowa a booth din motarshi daya wuto da ita ciki sosai yadda kayan zasuyi dadin kaiwa office. Kallon juna Deen da zee sukayi saikuma suka qarasa wajenshi kamar yadda yace Deen ne cikin ladabi yafara cewa "Good morning sir" Amsawa mr ibrahim yayi batareda ya dagoba sai sannan itama zee ta gaidashi itama ya amsa mata batareda ya kalleta ba Suna nan tsaye a bayanshi har yagama fiddo kwalayen daga booth sannan ya rufe ya juyo ya fuskancesu "help me with these" yafada yana nuna masu kwalayen "ok sir" inji Deen yana wucewa don daukar daya Itama zee wucewa tayi Wurin qaramin cikinsu ta dauka sai jitayi ashe babu nauyi ma da alamu takardune ciki ko littatafai "ga key, ka bude kushiga dasu ciki saiku dawo mu ida kwashewa" inji mr ibrahim yana miqama Deen key din office din Amsa yayi sannan suka jera da zee suka wuce don kaiwa Saida sukayi nisa sannan Deen cikin muryar rada yace "mutuminki" Kallonshi tayi tana dan Harararshi tace "Amebo" itama cikin rada Murmushi mai sauti yayi yace "eh din" Ajiye nashi kwalin yayi bayan sun qarasa ya bude office din zee tashige sannan shima yadawo ya dauki kwalin shima yashiga Ajiyewa duk sukayi a qasa sannan suka fito yasake rufe kofar sannan sukayo hanyar dawowa "guess ya haqura" inji Deen yanzu ma cikin rada dukda basuma shawo kwanar da zasu hangi mr ibrahim din ba Daga kafadu zee tayi tace "may be, maybe not" "gashi nan ya kiramu" "ai besan mune ba, bakaga reaction dinshi ba dayayi realizing nice" "ni ban gani ba" "dama ya xa'ayi ka gani da wadannan small small eyes din naka kamar na cinnaka🐜" Dan 6ata rai yayi yace "kekuma da naki big big eyes kamar na kwado🐸" Dan wara idanun tayi "nidin?" "exactly" Yitayi kamar zatazo wajenshi yayi saurin matsawa yana Dariya Kwafa tayi tana murmushi suka shawo kwanar da zasu dinga hango mr ibrahim suka hangoshi tsaye yana magana da wani lecturern shima Cikin rada zee tace "yaushe kake ganin ya kamata na sake samunshi? Now?" "No not Now, kibari zamuyi magana but not Now" yafada daidai sun qaraso wajensu mr ibrahim din Gaida dayan lecturern sukayi sannan suka sake daukar kwali guda guda ya rage saura daya sukayo gaba Kafin ma ya bude kofa sukaga shima mr ibrahim yataho da kwalin qarshe Kafin ya qaraso har sun shiga sun ajiye yana isowa shima ya shigo ya ajiye yayi masu Godiya sannan ya sallamesu suka fito "yanzu ina zaki?" inji Deen "Sabon department dinmu ofcourse" "kinje copying timetable?" "No kaifa?" "nima yanzu zanije" "ok muje, Hakan ma yakamata nafara ko?" "nima haka nagani" Daga nan sai suka sha kwana suka kama hanyar inda ake liqa timetable suna tafe suna fira gwanin sha'awa Tare sukayi copying din timetable din anan suka ga ashe duk basuda class yanzu Zee sai 12pm saikuma na 2:30pm shikuma yanada na 1pm shima da 2:30pm. Ganin Hakan yasa suka wuce library don a lokacin duka qarfe 10 da yan mintuna Anan sukayi zamansu sunata fira har lokacin shiga lecture din zee yayi ta tashi tabarshi anan Ganin Hakan yasashi daukar wani Littafi yana karantawa to wine time away, lokacin shigarshi class nayi shima ya tashi ya fice ya nufi sabon department dinsu Zee tarigashi fitowa Hakan yasa tawuce cafteria ta siyamusu snacks ta dawo library din Bata dade ba sai gashi shima yayi joining dinta Tare sukaci abinda ta siyo din suna duba lecture din da suka dauka yau Sai wajajen 2pm suka tashi suka nufi masjid gabadaya shi yayi bangaren maza ita tayi na mata Koda suka fito classes dinsu duk suka wuce don duk sunada lecture a daidai lokacin A kusan tare suka fito inda a lokacin har Motarsu zee ta qaraso As usual sallama sukayi don Deen cewa yayi akwai abinda zaiyi ba yanzu zai tafi ba Bata damuba itama sukayi sallama tashige mota bala yaja suka fice tanajin kanta cikin nishadi marar musaltawa Haka ranaku sukaita tafiya masu, kodayaushe zaka gansu a school atare Saidai idan daya ya shiga class yabar daya, sosai wata iriyar shaquwa datafi tada tasake shiga tsakaninsu Agefe daya kuma wutar soyayyar Deen tana cigaba da balbala a zuciyar zee Yanzu yana dan kiranta don wani sa'in yana kiranta sau daya a rana wani sa'in kuma sai bayan kwana biyu yake kiranta, itama tana dan kiran shi amma ba sosai ba kuma yasha bata kaka su gaisa ta waya Duk yadda takejin soyayyar shi a zuciyarta tana iya bakin qoqarinta na dannewa tayi acting normal musanmman ma a gaban shi dukda wani sa'in Dakyar take iya controlling din emotion dinta Sosai soyayyar shi ke qara hauhawa a duk kowacce daqiqa a zuciyarta abin har tsoro yake bata don wani sa'in har kuka take tana fargabar kar allah ya jarabceta ta wannan fannin don tasan ba qaramar wuya zatasha ba A gida ma mummy tayi noticing chanji sosai daga gareta Don yanzu kusan kodayaushe indai tana gida to batada Wurin zama kamar garden, can zataje ta xauna shiru ko ta buga tagumi tana kallon waje guda tana murmushi kamar ta6a66a Wani sa'in ko a dining suke haka kawai sai takama murmushi tun abin na ba mummy mammaki har abin yafara damunta A bangaren Deen kau haryanzu be furta soyayyar shi ga zee ba Saidai yana bata kulawar dake sata tantamar anya babu sonta a ranshi kuwa? Saidai kuma data tuna waye Deen da abinda yake iyawa sai ta bar wannan tunanin don ba qaramin aikinshi bane ace duk kulawar nan babu sonta ko daya a ranshi kawai abota ce Yanzu haka satinsu uku da komawa school, komai yana tafiya masu daidai a karatunsu musanmman ma zee don sosai Deen ke warware mata abubbuwan dasuka shigemata Gashi sun shirya da mr ibrahim don taje ta sameshi personally tabashi hqr dukda Saida Deen yasha fama kafin ta yarda taje don sau uku ana saka rana sai ranar tazo taji bata iya zuwa daga qarshe dai Dakyar ya iya convincing dinta taje sai gashi mr ibrahim din ne gwasaleta ba kamar yadda take gudu yayi accepting apology dinta yakuma yimata nasiha Hakan ba qaramin dadi yayi mata ba don jitayi kamar anyi lifting wani abu mai nauyi daga saman qirjinta *** Yau friday, dawowarta daga makaranta kenan tashigo falon tana sallama qasa qasa tana jan qaffafu irin a gajiye dinnan Saidai wanda tayi tozali dashi yasata warwarewa nan take "Aunty Feenah!!!" tafada cikin wara idanu sannan ta nufi Feenah da gudu ta fada jikinta tana dariyar murna Itama Feenah riqeta tayi cikin Dariya tana cewa "ji yar rainin hankali zata qaryani, ni abokiyar wasarki ce?" Mummy dake gefe zaune tace "hmm ai indan wannan ce kadan ma kika gani" Dagowa zee tayi still tana Dariya tace "wai dama yau zakizo shine baki gayamin ba? Gaskiya banji dadi ba" tafada tana so6ara baki "to idan ma gayamiki wani abu zaki yimin? Kema ba daga sama ba naga kin fado gidanmu ba?" "oh ramawa kikayi kenan?" "qwarai kuwa" Dariya tayi tace "babu komai ai, tsakanin uwa da 'ya sai allah, ina kayan ki nashigar miki dasu ciki dukda ni ba'a shigarmin da nau ba" Yi Feenah tayi kamar zata maketa tayi saurin miqewa ta nufi stairs tana Dariya Kwafa Feenah tayi tana cewa "zanyi maganinki ai tunda naga kin maisheni kakarki" "ai kunfi kusa, dama zani ce ta tarda muje don kaff babu abinda tabari a halin ki" inji mummy "kai yaya, wlh nafi Zainab hankali" inji Feenah tana turo baki "kindai fita" mummy ta amsa tana Dariya *10:30pm* Sake dagowa tayi daga wayarta datake danne danne daita ta sake kallon Aunty Feenah data juya mata baya tana waya cikin yin qasa da murya sosai don ko zee dake kwance kusada ita bata jin abinda take cewa Sai jitayi ta bata sha'awa har itama tana hasaso kanta tana waya da Deen dinta Tunawa tayi da yadda suke waya, sunyi gudun tsiya suyi 5mins suna waya amma Tundazu take duban agogo awon Aunty Feenah daya da kusan rabi suna waya _ko me suke cewa?_ abinda ta tambayi kanta kenan saikuma ta ta6e baki ta cigaba da danne dannenta Saida Feenah taqara daukar 15mins kafin suyi sallama da saurayin nata ta juyo ta kalli zee datayi nisa a wayarta tana downloading wata waqar hamisu breaker Fizge wayar Feenah tayi tana cewa "dawa ake charting?" Tashi zee tayi zaune da sauri tana cewa "wayyo Aunty dan allah karki datsemin yakusan Shigowa" Jada baya Feenah tayi tana Dariya ganin tana qoqarin amsa ta daga wayar sama tana dubawa "Yadda kunne yaji? Menene wannan?" inji Feenah tana yatsine fuska "Wata sabuwar waqar hamisu breaker ne, naga gajeriyar video dinta a status dazu sai naji ta burgeni shiyasa nake downloading" "mtcheew! Ni dalla amsa, namayi tunanin dashi kike charting" Amsa tayi tana Dariya "da wa?" "bansaniba yar rainin sense" Dariya zee taqara yi "wai Deen? Bana tunanin yana charting" "why?" Daga kafadu zee tayi "qila ra'ayi" Ta6e baki Feenah tayi "to Saidai waya kadai kuke yi?" "itama ba sosai ba" "why?" "hmm kema fa kinsani Aunty, wayar ma duka yaushe muka fara? The guy is so slow in everything qila saina haukace sannan zai bayyana min zuciyarshi" tafada tana maida fuskarta kalar tausayi Murmushi Feenah tayi tace "karki damu zee, ana slowing a komai amma banda soyayya, insha allah zai bayyana miki ba kince kina ganin signs ba?" "sosai ma, amma yaqi furtawa. Kuma ni tsoro nakeji karna sakankance dayawa abin yazo ya juye ba yadda naso ba in shiga uku" Dariya sosai Feenah tayi ganin yadda ta qarashe maganar 6ata fuska zee tayi tace "kai Aunty, Dariya ma nabaki?" "dole kibani Dariya mana, wai ki shiga uku" "ato Aunty har tara ina iya shiga wlh don bakisan yadda nakeji a zuciyata bane" Murmushi Feenah tayi tace "nasan yadda kikeji zee don na fiki dandana dacin soyayya" Zee tadanyi jimm saikuma tace "Aunty dan allah kibani labarin wadda kike so din, rannan kince ba yaya auwal bane, to waye?" Shiru Feenah da mood dinta ya chanza tayi sannan tadanyi murmushi tace "Wani ne" Sai kuma tasake yin shiru Zee ba tace daita komai ba Haka ma bata bar kallonta ba "A france muka hadu... Haduwar da bazata ta6a mancewa ba qila har namutu" Sai kuma tasake yin shiru Ganin Haka zee tayi kasadar cewa "a school?" Nan ma shiru sai kuma taga ta kauda kai gefe ta dauke hawayen dake shirin gangaro mata Hakan yasa jikin zee yayi sanyi qalau "A'a.. Ba a school ba, a supermarket... Ranar na raka wata course mate dina siyayya, asali ma siyan pad ya fiddamu don lokacin period dinta ya matso don harta fara jin alamu. Da farko badani za'aje ba don cewa nayi bani zuwa can dai suka lalla6ani harna yarda zan bisu, ashe qaddarar so ke kirana" Sosai jikin zee yaqara yin laqwas ganin yadda Aunty Feenah of all people take hawaye sosai dukda qoqarin datake na sharewa amma tana sharewa wasu na zubowa Hakan yasa itama taji idanun nata na durar ruwa "harmun gama siyayyarmu mun fito saina lalluba naga banga bangles dina ba wanda najire wajen gwada wata agogo dana siya Saina koma don daukota Koda naje na tarar dashi inda na ajiyeshi saina dauki abuna na juyo ina maidawa kawai sai naji na gwara kaina da abu mai zafi" Shiru tasakeyi tana hadiyar zuciya itakau zee sai kallonta take tana hawaye "ashe shine, kallo daya na yimashi nasan tawa ta qare daga nan, kallo daya" "kallon ma irin briefly dinnan don ko tsayawa ya kalleni ko yaga wanda ya buge beyiba sai dan daga hannu dayayimin alamun sorry ya wuce yana cigaba da amsa wayar dake kare a kunnenshi, kallon danayi mashi befi na daqiqu biyu zuwa uku ba amma kwakwalwata tayi capturing dinshi, ba ita kadai ba.. Harda zuciyata" Share wasu hawayen dasuka gangaro mata tayi tana sniffing "bansan iya tsawon lokacin dana dauka tsaye anan ba kamar an dasani Saidai jinayi daya daga cikin qawayena da mukazo tare tana girgiza kafadata, sannan nadawo. Nadawo daga duniyar da bansanta ba" "Tambayoyi taita jeramin na lfy? Amma ban iya amsa mata ko daya ba na kama hanya kamar wacce bata cikin hayyacinta nafito tabiyoni itama da sauri abaya" Dagowa tayi ta kalli zee dake hawaye itama cikin muryar kuka tace "zee, bana fatan ko maqiyina ya tsinci kanshi a irin halin dana shiga a lokacin, na zauce zee, zaucewa na haqiqa. Kullum... Kullum saina je wajen nan.. Don nasake ganinshi.. Koda brief kallo zan mashi irin na wancan, Koda bekai wancan ba. Kullum saina je, na tsaya waje ina jiran shi, ina jiran wanda ko sunan shi ban saniba. Tun qawayena na daukar abin wasa har abin yafara basu tsoro, bana kuka Saidai na xauna shiru, idanuwa jawur ina kallon waje daya, cikin dare bana barcin kirki konayi shi ke addabata a mafarki" "nazo na daina gane komai a makaranta, hankali na baya jikina, ko attending class ban cika yiba ina can.. Ina can ina jiranshi.. Ina jiran wanda bansaniba, bansan sunan shi ba, bansan addininshi ba... It hurt zee, akwai ciwo sosai, ciwon da bazan iya musalta mikiba, ciwon da babu wanda zai iya ganewa sai wanda ya dandani abinda na dandana" "haka zan wuni acan, Saidai in dinga chanza position don kar a lura dani afara zargin meke kawoni, haka zan wuni jira amma bazan ganshi ba na Kamo hanya kuma nadawo, idanuwana jajur don ban ta6a kuka ba don duk yadda naso yinshi baya zuwa, Saidai su qawayena suyita yi, suyita yimin kuka.. Ni kuma ina kallonsu ina ji azuciyata inama nice su, nima in iya kukan ko zanji sassaucin abinda nakeji" Kuka sosai zee takeyi kamar zata shide, Ganin Feenah tana kuka ba qaramin tadamata hankali yayi ba "Saida nayi kwana sha tara daidai sannan nasake ganinshi... Ganin da shima bazai ta6a gogemin a zuciya da kwakwalwa ba" "A ranar nayi kukan da nake roqon allah yabani damar yi don inji sassaucin zuciyata, nayi kuka zee kukan da ban ta6a yiba.. Kukan da ya tashi hankalin dukkan yan hostel dinmu, kukan da nasan farkon shi amma bansan qarshen shi ba" "na ganshi.. Shi da matarshi... Da 'ya'yanshi biyu.. Suna..." kasa idawa tayi saita hada kanta da gwiwa kawai Saurin rarrafowa zee dake kuka sosai tayi ta rungumeta gamm suka cigaba da rera kukan tare 😭 Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:36 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *038* "A lokacin nayi tunanin mutuwa zanyi Zainab... I never thought I will survive it, gashi ni kadai naje ranar. Ina zaune inda nake kamar statue har suka shiga suka fito. Na kallesu dakyau naga bayyananiyar farinciki da shauqin juna a tare dasu da alamu su basuda wata damuwa a duniyar nan" "kamar yadda suka shigo a gaban idona haka suka fice a gaban idona" "bansan tsawon lokacin dana dauka ba a wajen, nadai san kamar qawayena suka dawo dani gida.. Koko ni nadawo? Bana ce ba.. Nadai kawai ganni a dakin mu qawayena zagaye dani suna kuka.. Sama sama naji suna girgizani suna cewa inyi kuka ko zanji sauqi" "da farko kasawa nayi amma ahankali ahankali sai yafara zuwa.. Sai nayi" "ganin cewa allah yabani damar kukan yasa banyi wasa da damar ba, naitayi.. Naitayi zee.. Nayi tayi bakin iyawa na duk don in amayar da radadin zuciyata" "bansan me yasake faruwa daga nan ba na farka a gadon asibiti daga nan sai gida" "a lokacin kina secondary school, wataqila zaki tuna Da wata rashin lafiyar danayi don har Saida kukazo... A sanadiyar naqara repeating shekara daya a makaranta don a shekarar babu abinda nayi a school." "na dade ina jinya both physically and emotionally sannan nadan warware nakoma school" Dagowa tayi daga rungume juna dasukayi Tundazu tana kallon zee da fuskarta yayi jajur saboda kuka da rinnanun idanunta "tun a lokacin ban qara ganinshi ba, yatafi.. Wataqila har abada.. Ya tafi ya barni da tabon da qila dashi zan mutu" Sake rungumeta zee tayi tana lumshe ido wasu hawayen na silalowa "Kiyi hqr Aunty Feenah, am so sorry" Qara rungumeta Feenah Tayi itama ta lumshe idanu "Don't be zee, don't be" Shiru ya ratsa dakin bakajin komai sai qarar naurar a.c Sun jima a Hakan sannan Aunty Feenah taqara breaking rungumarsu takoma jikin gado ta jingina tana share hawayenta "amma dukda Hakan na godewa allah daya musanyamin da Auwal, dama abinda kakeso wani sa'in becika zama alhairi a gareka ba, alhamdullilah yanzu na wuce wajen, na samu mai sona.. Auwal" "amma shima kina sonshi?" inji zee tana kallonta da jiqqaqun idanunta Dan murmushi tayi "it doesn't matter" "kamar yaya?" inji zee cikin alamun tambaya Dan murmushi Feenah tayi tace "so dayane zee, kuma nariga na baiwa wancan mutumin" "to yaya Auwal din fa? Kina nufin bakya sonshi?" "it doesn't makes sense ko?" Shiru zee tayi takasa amsawa "yeah, banace bana sonshi ba kamar yadda bazan ce ina sonshi ba. Amma shi yana sona... Sosai Kinga banida damuwa" "kamar yaya?" "zee, Koda ace nasamu mutumin nan yasan abinda nake ciki gameda shi yayi deciding ya aureni saboda sonshi danake bawai don shima yana sona ba, bazan ta6a auranshi ba" "meyasa?" inji zee cikin mammaki Ajiyar zuciya Feenah ta sauke tace "saboda wahala zansha, kinsan illar auran mijin da baya sonka kuwa? Baki sani ba Amma ni nasani... Babu komai cikin auren da mata tafi son miji bayan azabtarwa da wulaqanci. Da Hakan gwara ki auri mai sonki Koda kuwa bakya sonshi muddin nagarttace ne, zakiji dadin rayuwar aure fiyeda tunaninki" "Auwal na sona, makauniyar soyayya. farincikina shine nashi Koda kuwa zai cutar dashi, baya qaunar abinda zai 6ata min rai, kullum cikin tattalani da kulawa dani yake kamar kwai, idan na aureshi na more" "Zainab, da mace ta auri wanda takeso baya sonta ko kuma soyayyar dayake mata bata kai tata ba gwara ta auri mai sonta wlh don rayuwar aure rayuwace mai zurfi da tarin qalubale idan har mijinki na sonki, so na Gaskiya bazaki ta6a wulaqanta ba" "zan auri Auwal badon soyayya ba saidon nasan zan samu farinciki wanda shine muradin kowacce mace agidan mijinta.. Wataqila.. Wataqila farincikin dazai sani ya goge min wancan araina, wataqila watarana shima nasoshi.. Wataqila" 💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖 Da magangganunsu dasukayi jiya da daddare zee ta kwana ta tashi. Sosai jikinta yayi laqwas matuqa da kalar soyayyar Aunty Feenah No wonder, shiyasa take mata kallon shashasha lokacin da take denying din soyayyar Deen Sosai taji tausayin Aunty Feenah dama kanta don itama batasan wace qaddara zata fadamata ba, fatan ta dai kar ya shafi soyayyar Deen don Hakan ba qaramin tashin hankali bane agareta. Feenah kau tashi tayi garau kamar babu abinda yafaru, yanda take zirga zirganta freely yaba zee mammaki sosai don yadda kasan ba ita kebada labari jiya ba tana kuka Ganin Hakan yasa itama dan warwarewa, sukayi komai tare sannan suka shirya suka shiga zaga gari kamar yadda Aunty Feenah ta buqata Sosai yawon nasu ya ragema zee cinkushewar zuciya harda ma Feenah dake qoqarin 6oye nata damuwar Basu dawo ba sai yamma liqis lode da kayan qwalama da zaqi Washegari kau shopping suka tafi don ranar monday zata juya dama kwana uku tazo yimasu Zee bataji dadi ba sam don sosai takejin dadin dan zaman nan da Feenah dukda zafinta, Saidai masu iya magana na cewa idan kasan halin mutum sai kaci maganin zama dashi Sosai zee ta laqaici halayen Feenah shiyasa tafi kowa sanin yadda zata xauna daita shiyasa ma suke jituwa sosai don duk cikin dangi sunfi jituwa daita Daddy ne mai daure gindin zuwa shopping din A.T.M yabasu akan suje su dauki duk abinda sukeso a zara ta atm din Aikau sunyi siyayya harta hauka inda yawanci duk na mayyuka ne na gyaran fata wanda duk yawanci Feenah ce tasansu don wasu ko ta6a ganin su zee batayi ba Itama zee batayi wata wata ba tashiga daukar duk wanda taga ta dauka itama wai zata jaraba A taqaice dai Saida sukayi shopping son ransu sannan suka kamo hanya suka dawo gida Koda suka iso gida mummy riqe baki tayi ganin uban shopping din dasukayi, zatayi magana daddy yace babu ruwanta ba shi yabasu go ahead ba? Ranar ma da daddare sunsha fira inda zee taita roqon Feenah idan zasu tafi su biyo school taga Deen Da farko qin yarda tayi tace ita batason abinda zai jawomata raini wajen mutum, saida zee taita roqonta tana cemata Deen babu ruwanshi, beda matsala ko kadan sannan tasamu dakyar ta yarda. A bangaren Deen kau tun kaka na maganar siyar da wayar harta haqura don kullum da kalar karatun dasuke kawomata musanmman salmanu don yafi Deen baki Daga qarshe ma cewa sukayi sunje anyi musu tayin wulaqanci wai dubu 15, wai yanzu babu kudi Nan suka lalla6ata akan tabari sai anshiga kaka lokacin kudi sun wadata sai a siyar Babu yadda kaka ta iya haka ta haqura da sharadin da kaka tayi za'a siyar suka ce sun yarda. *MONDAY* Zaune take inda suka saba zama duk lokacin da sukayi sha'awar zama waje ba library ba Memo ne bisa cinyarta sai pen a hannunta tana rubutu tana waqa ahankali Ita kadai ce zaune don batada class shikuma Deen yana class Tundazu don sunada lecture Tayi nisa a abinda take har batasan da Qarasowarshi ba Dan nesa daita ya tsaya ya rungume littatafanshi a qirji yana kallon bayanta _da rai lafiya take amfanuwa_ _da lafiya ake more rayuwa_ _a rayuwa so na kauda damuwa_ _da damuwa akan rasa rayuwa_ _soyayya ce da ba'a yin kwatance_ _in kayi dace hankalinka kwance_ _idan ta 6aci sai tasa a xauce_ _mafita ce, addu'a a taqaice_ _dakai na dace_ _a soyayya banda yakai_ _har abada dani dakai_ _da'iman! Da'iman!!_ Jin alamun kamar ana kallonta yasata saurin juyowa saita ganshi tsaye bayanta rungume da littatafai yana kallonta Kunya taji ya kamata sai tayi saurin Juyawa kawai dana dan matse ido Qarasowa ya ida yi ya xauna daga can gefenta yana murmushi "wow! Waqar tayi dadi" Murmushi kawai tayi bata dago daga rubutun da take ba "dama kina waqa?" Dan daga kafadu tayi "Wani sa'in" "tayi dadi, you have a melodious voice" Blushing tayi tana kauda kai dadi na lullu6e zuciyarta "inason waqa" taji yasake fada Dagowa tayi ta kalleshi tace "kanason waqa ko kanason ka dinga yin waqa?" "duka" ya amsa yana ajiye littatafanshi akan cinya "kuma zaka iya, your voice is sweet idan kayi waqar zatayi dadi" saikuma taji kunya tace Muryarshi nada dadi Hakan yasa ta qara kauda kai ta cigaba da rubutun ta "really? To amma ni ban iyaba, as in how zan qirqiri waqar da kaina?" Dagowa tayi daga rubutun datake ta kalleshi tace "waqa directly daga zuciya take, duk abinda yake zuciyarka kana iya furtashi ta sigar waqa, it's so simple kuma yafi dadi ma saboda you're singing with the whole of your heart, pouring out your mind" "how? Nayi tunanin koyo akeyi" inji Deen Gyara zama zee tayi tace "eh ana koya akwai kuma masu basira ta wanda they can form their song nan take, zasuyi amfani da abinda sukeji at exactly lokacin suyi forming din waqa kuma sai kaji yayi dadi sosai yafi na wadanda suka koya din ma" "but tayaya Hakan zai yiwu? Kawai daga tunani sai waqa? Kowa ma na iyawa kenan" Murmushi tayi tace "kusan Hakan don abin baiwace, idan har ka iya lanqwashe harshenka ka iya juya maganar yadda kasan zatayi dadi to shikenan.. Yanzu misali kai wane abu ke ranka ko yanayin dakake aciki?" "yanayin danake ciki?" Sai yayi shiru alamun mai tunani can yace "am happy" Murmushi tayi "to kayi kalma da farincikin dakake dakuma abinda yasaka farincikin" Shiru yasake yi alamun tunani can kuma yace "sitting beside a friend and feeling the pleasant atmosphere make me happy" ya qarashe yana daga gira alamun yayi Kada kai tayi tace "to yanzu bari muyi forming waqa da kalaman" Sai tadanyi gyaran murya tafara _Happiness is the best gift of the nature that exist_ _smiling is the cutest gift of the cutest that exist_ _friends are the best thing that happen to human that exist_ _cool weather, the best atmosphere that exist_ _joining them together gives you the best moments that exist_ _the best feeling comes when all these exist_ _the best feeling and moments which made the word HAPPINESS_ Deen daya saki baki Tundazu yana kallonta yayi blinking din idanunshi sau biyu "OMG!" Sai kuma ya hau tafi "wlh tayi dadi, soo much!" Murmushi kawai tayi "to amma tayaya kika iya yin haka?" "saboda ina iyawa" "to wa ya koyamiki?" "babu, kawai gani nayi na iya" "wonderful! Kudos" Murmushi tayi kawai "to nima na Jaraba?" "eh jaraba" "ok kema kiyi wata kalma amma mai sauqi fa" Murmushi tayi tace "ok.. I love travelling alot" tafada sanin cewa shi ya ta6a amfani da kalmar kuma daga zuciyarshi take Gyara zama yayi yana gyarar murya _l love travelling, because travelling is good. You'll see lot of people and know their culture, therefore adding to your experience and also..._ Dariyar zee ce ta katseshi ya dakata daga zubar da yakeyi Ganin Dariya take mashi sosai tana nuna shi ya 6ata rai "O'O! Meyasa kike min Dariya?" Bata amsa ba saima Dariyar data cigaba dayi, Hakan yaqara kular dashi ya cika yayi famm "like seriously, wannan waqa ce ko magana?" Sai kuma taqara Fashewa da Dariya "kafara abu babu full stop babu comma kamar mai rapping ko numfasawa bakayi?" Deen dake kumburi yace "kema ai haka kikayi" "wa? Ni bakaji baiti baiti nake kawowa ba?" "nima ai baiti baiti zan kawo" "a ina? Kaida tunda kafara baka tsaya ba" "ai bankai baitin farko ba ai" Qara wara idanu tayi sai tasake daukar Dariya "wato wadannan duk cikin baiti daya ne? Hhhh🤣 wayyo cikina" Qara cika yayi sai huro hanci yakeyi "to qarasa baitin" tafada Dariya na cinta Harararta kawai yayi ya dauke kai Duqar dakai tayi tayi Dariya marar sauti sannan tasake cewa "ka cigaba mana" "don kinga ban iyaba kike yimin Dariya?" yafada yana kauda kai gefe "ok, ok sorry, ni bansan Dariyar tazo ba ma, yanzu dai sorry, qarasa baitin" tafada tana danne dariyarta "saboda kiji dadin yimin Dariya ko?" "A'a bazanyi ba" "promise?" "yes" Sai yakuma gyara zama ya gyara murya sosai Zee kallonshi kawai take tana iyakar kokarinta na ganin ta riqe dariyarta _kuma zanga gari naita yawo aciki, ina lura da banbance banbancen al'adarmu, idan sunada yare nima saina koyaaa yadda idan nadawo gida naita yiwa kaka amma bata ganewaaa_ Kallon zee yayi data hada kai da gwiwa Tundazu, dan yamutse fuska yayi cikin ayar tambaya yace "hey.. Hey!" Qin dagowa tayi "hey, are you ok?" yafada yana dan leqo fuskarta ta qasa sai a lokacin ta dago fuskarta idanunta sun duri hawaye Kafin yayi magana ta fashe da dariyar da Tundazu take yinta a ciki tasake maida kanta bisa gwiwa tana yi Sosai Tsayawa yayi yana kallonta kawai har tayi ta gaji sannan tasake dagowa ta ciro hanki dinta ta dan tsane hawayenta Cikin muryar Dariya tace "tau saura baiti na uku" Kauda kai kawai yayi bece komai ba "kaji? Saura na uku" Juyowa yayi ya Harareta ya kauda kai Murmushi tayi sannan cikin danne dariyarta tace "you know what? Matsalar waqarka shine kana jan baitin da tsawo.. Hhh... Kuma kamar ba waqa ba.. Baka fidda karin waqa.. Hhh" "wannan da a cinema aka daukeka waqa da kafin ka kai baiti daya zaka fara jin ruwan duwatsu😆" Be tanka mata ba kuma be juyo ya kalleta ba Saida tagama yimashi shaqiyanci sannan tace "yanzu bari kaji, idan zakayi waqa, anaso ka taqaita tsawon baitin yadda ba zaiyi sounding boring ba misali _kuma zanga gari naita yawo aciki_ Kana iya barinshi daidai nan sai kasake wani baitin Misali _kuma zanga gari naita yawo aciki_ _na dinga lura da al'adun ciki_ _nakoyi yaren dasuke aciki_ _nai jama'a da mutanen dake ciki_" "akwai wani abu da ake kira kafiya a waqa, shine ya kasance duk baitin waqarka ya dira lafiya lau, so samu ma ace duki kalmar qarshe tazo daya na wadannan baitikan misali a wadancan baitikan dana kawo kaga duk (ciki) shine kalmar qarshe, yana iya zama (ki) din qarshe ma duk ana iya yin Hakan saboda waqar tatafi a tsari takuma bada taste" (duk inda nayi kuskure a wajen bayanin waqa acan sama👆🏻 ayimin afuwa. Qarfin hali ne kawai na marubuci, babu abinda nasani a waqa ☹️ kawai dai hasashe na ne kuma saboda labarin ya ta'alaqa dashi shiyasa na sakoshi ciki, so mawaqa Ayi hqr 👏 na shiga gonar da batawa ba😝 waqar ma Dakyar nake hadata 😆 donma a rubuce na, da na saurarone da babu kanta🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀?) Deen da tunda tafara bayanin ya juyo yana sauraronta harta kai aya ya Kada kai yace "ok, bari nasake gwadawa" "ok gwada" inji zee dake readyn cin Dariya Qara gyaran murya yayi yace _saina siyawa kaka tsaraba dayaWA_ _ciki harda ku6eWA_ _harda alaWA_ _sai na hau abin haWA_ _nadawo gida ina.._ Shiru yayi ganin baitin bazai qare da WA ba Saiya sake cewa _nadawo gida ina riqeda ledar ku6eWAR_ Atare suka shiga yin Dariyar wannan karon don shi kanshi yasan he sounds so funny Suna cikin haka wayar zee tayi ringing Zaro wayar tayi ta duba mai kiran taga Aunty Feenah ce Dan wara idanu tayi don ita shaf tama manta yadda sukayi daita Daga wayar tayi ta kara a kunne tayi sallama cikin muryar da Dariya bata gama saki ba "gamunan waje karki 6atamin lokaci" taji Feenah tace daga dayan 6angaren "to Aunty, gamunan zuwa" Kittt suka katse wayar Atare Kallon Deen dake kallonta shima tayi "kaga na manta ko?" "menene?" "Wata Aunty ta ta Ruma tazo tun ranar friday, to a schedule dinta gobe zata koma amma saboda wani abu daya taso cikin gaggawa shine tafiyar tadawo yau, ni kaina ban sani ba don Saida nazo school sannan ta kirani ta gayamin shine nace bazata tafiba sai tazo munyi bankwana, kaga har tazo ma" "ayyah" yafada a gajarce yana murmushi "muje muyi mata bankwanan" Dan wara idanu yayi yace "ni kuma? No kije zan jiraki" 6ata fuska tayi "why? Yanzu fa zamu dawo" "but.." "shikenan kawai" tafada tana tashi alamun ranta ya 6aci ta dauki jakkarta ta rataya Ganin Hakan yasashi tashi shima don kwata2 beson 6acin ranta, ko yaya yanayin fuskarta ya chanza sai yashiga damuwa Dama tasan idan yaga tayi fushi zai taso Hakan yasa ta danyi murmushi a cikin zuciyarta "ok mutafi a gaisuwa ce ko?" Kada kai kawai tayi "ok muje" yafada shima yana rungume littatafanshi a qirji Tare suka jera suna tafe suna fira gwanin sha'awa kowanne da murmushi a fuskarshi Saida suka fita wajen gate don motar na waje Motar suka hanga daga gefen titi na dama, dukda zee tayi mammakin ganin ba tasu bace haka suka nufeta don ganin ko sune. Tun kafin su qaraso murfin bangaren driver ya bude wani kyakyawan Saurayi yafito daga ciki Dan wara idanu tayi "Yaya Auwal?" Murmushi saurayin yayi yace "na'am diyarmu?" Daidai nan itama Feenah ta Fito daga bangaren mai zaman banza "Ina wuni yaya Auwal" "lfy qalau lumi yar daughter mu, kin ganni kamar daga sama ko?" Kada kai tayi tana murmushi "zuwa mukayi daukar gimbiyar, mun samu Dakyar an sahale mana muzo" inji saurayin wanda ga dukkan alamu yanada faran2 sosai Dan hararar shi Feenah tayi tana dan 6ata fuska cikin salo Murmushi zee tayi tace "aikau dai yaya, kuma dama kun rabu da shigowa k.t kunga har zuminci sai ayi" "ashe kin gane, yar daughter mu" injishi yana Dariya "ya karatu?" "alhamdullilah yaya, ya aiki" "gashinan munata fama wlh, wannan abokin nawa fa?" yafada yana kallon Deen dake baya yana sauraronsu Sai a lokacin Deen ya dago fuskarta dauke da murmushi yayi musu sallama Atare suka amsa suna maida mashi martanin murmushin "Yaya Auwal, Aunty Feenah meet my course mate Deen, Deen wannan itace Aunty ta sai yayana" Fuska dauke da murmushi ya gaidasu calmly sukuma suka amsa suma murmushi a fuskarsu sai kallonshi suke "ya karatu, fatan za'a qara tighting belt" "insha allah brother" inji Deen "to allah ya taimaka, daughter mu zamu wuce" inji Auwal yana dan sunkuyawa ya ciro ledar dayayi mata siyayya ya miqo mata "gashi Ayi manage" "kai yaya, harda hidima? Thanks so much" inji zee tana amsa "Don't mention" yafada yana komawa cikin motar "to sai munyi waya ko?" inji Feenah tana dan kashe mata ido alamun akwai labari "to Aunty a gaida kowa da kowa, ace nayi missing dinsu" "eh, tunda ni yar aikenki ce ba?" tafada itama tana shigewa ta zauna "pleeease" tafada cikin marairaicewa "ok amma ba don halinki ba" tafada tana harararta "eh babu komai" inji zee tana maida mata kofar ta rufe Tada motar Auwal yayi nan suka shiga daga ma juna hannu harda Deen, Auwal yaja motar suka tafi Ajiyar zuciya zee ta sauke sannan tajuyo ta kalli Deen "how was that?" "nice, they're so nice" Murmushi kawai tayi suka juya suka koma ciki Sallah duk suka wuce suka farayi sannan dik suka shiga class kasancewar suna da lecture a lokacin Saida suka fito sannan suka zauna suka ci kayan da Auwal ya ba zee dukda Deen be wani ci sosai ba Suna haka akazo daukar zee sukayi sallama ta tafi sannan shima ya fito ya samu abin hawa shima ya tafi *** *10:15pm* Kwance zee take kan gado wayarta a hannunta tana danne danne sai murmushi take akai akai da alamun abinda takeyi da ita na bata sugar "hmm Aunty Feenah, wannan rudewa haka?" ta tura Can sai message yashigo kamar haka "wlh zee gayen yayi 👌🏻 wai kinga sadda kuka jero? Yadda kikasan romeo and his juliet😍" "😆😆 dama kin sansu a kammani ashe?" "baki da labari ashe 🤨" "banida ☹️" "to saiki sani tun yau 😏 ashe dai dama da walakin goro a miya 🤔 haba dole ai ki rude ki gigice, taga dan fari kyakyawa 😒" "kai Aunty, duk kyawunshi ya kaini😟" "😳wa? Ke? 🤮🤮🤮" "😩😩😩" "kyaji dashi 😒, Gaskiya maganar Gaskiya kun dace, ya kamata kuyi ku daidaita junanku hakanan, Ca6 you'll make a perfect match, na so naga 'ya'yanku🥰" "kai Aunty 🙈🙈🙈" "munafuka, anaso ana kaiwa market 🙄" "kai Aunty 😫" "yanzu dai kuyi ku daidaita junanku musha biki💃💃" "kai Aunty 😟 nifa yarinya ce haryanzu 😔" "sannu jaririya 😕 ai naga ko yayeki ba'ayi ba" "😁😁😁" "yar rainin sense kawai, ki gaida yaya da daddy, ni zan sauka, barci 🥱" "tun yanzu 😳 yau babu wayar 👉🏻❤️ ne?" "ungo nan 🖐🏻😡" Dariya zee tayi a zahiri ta turamata "🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀" Sannan ta rufe datarta ta koma ta kwanta rigingine ta jawo pillow ta rungume Tunawa tayi da dramarsu ta dazu na koyan waqa Murmushi mai sauti tayi ta murgina tsakiyar gadon ta rungume pillon gamm a jikinta _*DEEN*_ tafada cikin shauqi da begen mammalakin sunan... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:36 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *039* *SIRRIN ZUCIYA ❤️* Akwana a tashi gashi har su zee sun qulla wata kusan biyu da resuming school Komai yana tafiya masu daidai kuma sosai suka maida hankalinsu akan karatunsu musanmman ma Deen dake final year Yana da burika dayawa dayake son cikawa a duniya ciki harda inganta rayuwarsu shi da kaka, most especially ma kaka saboda ita ta tsaya mashi kai da fata wajen karatunshi don kusan dik abinda tasamu nan suke tafiya saboda ta yarda karatu shine gatan mutum kuma ko ba dade ko ba jima zasuci gajiyar shi shiyasa bata wasa da abinda ya shafi karatunshi komai tana iya badawa muddin akan karatunshi ne Shiyasa shima a nashi bangaren be sanyo wasa ko shiririta a bangaren karatunshi Yanada burin zama wani abu a duniya ta dalilinshi yadda zai tallafi rayuwar kaka kamar yadda ta tallafi nashi A 6angaren zee kuwa jiya-i-yau. Haryanzu tana nan tana dakon soyayyar shi a zuciyarta Kullum sonshi qara hauhawa yakeyi a zuciyarta kamar yadda kullum shaquwarsu ke qara qarfi Sosai take azabtuwa da soyayyar shi datayi mata bake bake a zuciya Saidai haryanzu shiru a ta bangaren Deen Saidai akwai signs da symptoms na soyayyarta dayake nunawa amma that wasn't enough, so take ya furta mata, abinda taga bashi da niyyar yi kwata2. A bangaren Feenah kau biki sai qara gabatowa yake don yanzu bekai wata daya ba, ata kowanne bangare shirye shiryen bikin akeyi musanmman ma bangaren Amaryar kasancewar itace auta shiyasa ata koina ake nuna mata gata. *** Yau asabar, babu school don haka yini tayi a gida tana hutu Fitowa tayi daga dakinta dauke da wani dan bowl din tangaran wanda tagama shan fruit salad cikinshi ta fara tako stairs don sauka qasa ta maida Muryar mummy da daddy taji suna magana da alamu fira sukeyi Murmushi tayi ta cigaba da saukowa Saidai maganar dataji mummy tayi yasa tafara slowing tafiyarta "Gaskiya ne, nima dama nayi wannan tunanin, kaga Feenah tun tana makaranta ta tsaida miji, gab da zata gama kuma akasaka rana kaga yanzu duka watanta biyu da gamawa nan da yan satittika asha biki, me yafi wannan? Wlh zaman ba yi bane gwara da angama Ayi auren don shine mutuncin ko wacce 'ya mace dama namiji ma Kuma idan akace sai an gama karatun sannan za'a samu mijin yaushe za'ayi kenan? Gwara tun yanzu asa sanwar abin bare kai dama ita kenan daya, kowa ya dauko idanu ya zuba maka yaga yadda zakayi Ni sai inga Hakan shi yafi kawai" Tsayawa zee tayi takasa qarasowa tana jujjuya maganar mummy cikin son gane inda ta dosa Daddy taji yana cewa "nima haka nagani wlh Maimuna, gwara afara tun yanzu. Gashi yaron yanada tarbiyya don nasanshi sosai, muna Yawan hadewa idan naje gidansu ko kuma wasu lokutan idan sunzo tare da baban. Kuma bayan wannan kinga zumunci zai qara qulluwa, amintarmu da babanshi zai qara qarfi kuma bazanyi fargabar wani abu yasamu diyata ba don ko babu ni a duniya nasan Alhaji Abubakar mai iya riqe amanar iyalaina ne" Kan zee yaqara kullewa Tabbas tasan Alhaji Abubakar, babban aminin daddy ne kuma abokin kasuwancinshi. Sau dayawa shida iyalanshi suna zuwa nan ziyara suma suna zuwa gidanshi Saidai zee bata cika son zuwa ba don yaran gidan mugun yan zafin kai ne, girman kansu yayi over shiyasa basa shiri don kamar yadda suke jinsu su wasu ne haka itama ke jin kanta shiyasa basa shiri sam "wlh kam, to yanzu yakusan dawowa ne?" inji mummy "eh, ga yadda muka tattauna dashi Alhaji Abubakar din cewa yayi yagama komai kawai sai yan ide ide, nan da wata daya nasan yadawo, to kinga me ake jira? Aiki dama akwai shi available shi dama yake jira, kinga a lokacin saisu fahimci juna da tashiga level 400 din sai asaka rana tana gamawa sai asha biki, ko yaya kika gani?" "Gaskiya Hakan yayi Alhaji, kaga zamu sauke dukkan nauyinta akanmu, ga ilimi mun bata kuma mun aurar daita a lokacin daya dace, dama ni na matsu naga anyi Hakan saboda ita 'ya mace ce kuma duk inda hankalin iyayen 'ya mace yake to bazai ta6a kwantawa ba sai sunga sun rabu daita lafiya ta hanyar aurar daita. Allah yasa Hakan shi yafi alhairi kuma allah ya daidaita su kasan diyar taga yar tutsu ce wani sa'in" Dariya daddy yayi "ai karki damu, insha allah zaiyi mata 100%, nifa nasan taste din diyata, nasan abinda zataso da abinda bazata so ba kuma am betting you, zaki gani. Da hannu bibbiyu zata amshi tayin bari dai lokacin yayi" "to allah yasa, ka dai san ba'a shaidar 'ya'yan yanzu, bare wannan diyar taka mai shegen ruwan ido, kana ganin yadda masu neman ta ke zuwa take musu wulaqanci, duk wanda yazo saita nemi makusanshi ta kushe, nayi fadan nayi nasihar a banza" Dariya daddy yasake yi "ai jewel din kenan, ita allura ce cikin ruwa, mai rabo ka dauka kuma *Asad* shine mai rabon don dama don shi taqi sauraron kowa, nasan diyata kuma nasan abinda takeso don hakama yasa nasan da Asad zasu dace, kuma zaki gani" "to allah ya tabbatar da alhairi ai haka akeso" inji mummy cikin farinciki "hmm kaji su Hajiya Maimuna an kusa zama in-law" inji Alhaji cikin tsokana Dariya tayi tana juya idanu wanda a wurinta zee ta gado nata "Ato, kana black stomach ne?" "A'a, namafi kowa white stomach" yafada shima yana kwaikwayon juya idanun datayi Dariya duk sukayi mummy na cewa "to allah dai ya tabbatar mana da alhairi" "Amin summa amin" inji daddy Ahankali zee ta juya tafara taka stairs din don komawa batareda tayi motsin dazasu lura daita ba Bude kofar ta tayi ta shiga sannan ta rufo ta taho ahankali kamar marar lakka ta ajiye bowl din hannunta saman bedside locker ta zauna ahankali gefen gadonta Shiru tayi tana kallon Kaffafuwanta dake bisa dan carpet din dake gaban gadon kamar anan zataga amsoshin tambayoyin dake tsere a kwalwarta *kinga a lokacin saisu fahimci juna, da tashiga level 400 sai asaka rana tana gamawa asha biki* Maganar daddy ce tadawo mata a qwanya *nasan abinda takeso don hakama yasa nasan da Asad zasu dace* Wai wa yake magana akai? Waye kuma Asad? Wacece zasu dace dashi? Hadiye wasu yawu dasuka taru a maqoshinta tayi Me suke nufi? Tadai san basuda wata 'ya bayan ita kuma taji suna maganar sauke nauyi ta hanyar aurar da 'yar su _Ni kenan?_ Sai kuma ta girgiza kai _no this is impossible!_ _it can't be_ Waye wani Asad kuma? Suna ko gishiri babu. Ca6 dasake wlh, yanzu yanzu ba sai anjima ba zataje tagayawa daddy don karma ya wahalar da d'an mutane wajen zuwa don Hakan bazai ta6a yiwuwa ba don tanada wanda takeso Zumbur tayi tasake tashi ta nufi kofa Harta dora hannu akan handle saita kuma dakata Idan taje me zatace mashi? "daddy Gaskiya ni banason wannan Asad din, inada wanda nakeso" Sai yace "waye?" Me zatace? Deen? Deen zata ambata? Mutumin da har yanzu batasan matsayinta ba a gareshi? Idan tace Deen din ne yakuma nemi ya ganshi me zatace? Cewa zatayi ita ke sonshi? Ko cewa zatayi jiranshi take taji matsayinta a wajenshi? Ahankali ta saki handle din Tabbas tasan daddy, takuma san idan yayi farinciki to yaga tayi ne Idan tace mashi bata sonshi bazai gardama mata ba don tasan bazai ta6a yimata dole ba Amma shi wanda zatayi Hakan akanshi tanada tabbaci akanshi? Tanada tabbacin yana sonta? Ahankali takoma da baya2 ta lulubi stool din dressing mirror dinta ta zauna akai Tasan idan tace bata son wanda suke magana akai zasu nemi sanin wa takeso, idan tace babu bazasu yarda ba musanmman mummy da dama burinta taga tayi aure kuma ga yadda taga ta nuna amincewarta sosai akan wannan maganar da wuya ta barta ta tafi a iska Idan kuma tace tana da wanda takeso zasu so sanin ko waye, idan ta ambaci Deen zasu so jin ta bakinshi, idan kuma sukaji cewa bema san da maganar ba me kenan? Hannuwa takai bisa kanta ta cusa yatsunta cikin lallausan gashinta tana maidasu baya sannan tayi interlocking din yatsunta bisa wuya Anzo wajen! Anzo ga6ar da take gudu Lumshe idanuwanta tayi ahankali tana jin baqinciki na mammaye zuciyarta Har zuwa yaushe? Har zuwa yaushe zata cigaba da jiran shi? Har zuwa yaushe zata cigaba da dakon soyayyarshi? Har zuwa yaushe zata cigaba da wahala Ranta taji ya 6aci, zuciyarta ta dagule, jitayi kamar taita ihu don takaici. Dama tasani, wannan slowness din nashi wahala zai bata, dama tasan saita fara zaucewa sannan zai bayyana mata sirrin zuciyarshi. Haka ta qarashe Wunin ranar rai a matuqar dagule Baqinciki, 6acin rai, takaici duk sun taru sun tokaremata qirji wanda Hakan yasa taji babu abinda keyimata dadi a duniyar nan Haka ta qarashe weekend din wannan satin cikin cinkushewar zuciya, sosai takejin haushin Deen har cikin zuciya, jitake kamar ta sameshi taita duka ko zata huce shiyasa Koda yakirata da marece ranar lahadi kamar yadda yasaba sai bata daga ba sai tasa number shi yadda idan ya bugo zaiga line busy Da daddare ma ta dade batayi barci ba kamar yadda yake a al'adarta indai akwai abu a ranta yakan hanata barcin kirki Haka taita juyi kafin tasamu dakyar wani barci marar dadi ya dauketa *WASHEGARI* Zaune take a library wani qaton textbook a gabanta tana budewa ahankali page by page A zahiri sai kayi tunanin wani abin kirki takeyi amma maganar Gaskiya ita kanta batasan me take dubawa ba, hankalinta da tunaninta yayi wani wuri daban Deen ne yashigo library din, waige waige yadan farayi na ganin inda zai ganta sai ya hango ta can qarshen dakin Murmushi yayi sannan ya nufo inda take cikin tafiyarshi ta nutsuwa Tunda yashigo ta ganshi amma tayi kamar bata ganshi ba, haushin shi takeji kamar me? Jitake kamar ta tashi taita zazzagamashi abinda ke cin ranta Tanajin Qarasowarshi amma bata dago ba harya ja kujerar dake facing dinta ya zauna Sa hannu yayi ya rufe littafin data kafama idanu kamar mai karatun gaske, yana cewa "hey... Book worm" Sai a lokacin ta dago ta kalleshi da alamun bazata a fuskarta "oh! You scared me" Yar Dariya yayi yace "ai kece hankalinki na kan Littafi baki jin ko motsin mutane, meye kike karantawa?" yafada yana juyo da littafin gaban shi yadda zai gani Dan daga kafadu zee tayi tace "just going through topic da mukayi jiya" Kada kai yayi yana maida mata littafin shima ya doro nashi littatafan a sama "good, how's your weekend?" "Alhamdullilah" ta amsa a gajarce tana sake jawo littafin daya maido mata gabanta tana cigaba da dubawa "meya samu phone dinki jiya?" yafada shima yana zaro wani littafi a tsakiyar littatafanshi Zee da maganar nan ma datake yi duk dauriyace don ita tasan me takeji a zuciyarta ta dago ta kalleshi sannan ta daga kafadu "babu" "but nayita kira bata Shigowa saima line busy dayaita nunawa" Qara daga kafadu tayi batareda ta dagoba tace "qila lokacin waya nake" "amma fa na dade ina kira tana rubuta Hakan har da daddare ma" Qara daga kafadu tayi in an I don't care manner tace "yeah, ina waya ne" "wow! Da wa? Irin wannan dadewa haka?" Dagowa tayi tadan yimashi murmushi "kayi mammaki ne?" "sosai ma" Murmushi taqara yimashi tace "to ka daina" Shiru yadanyi yana kallonta "and who is that if I may ask" yafada yana dan bubbude littafin daya ciro *"my man"* Cak ya tsaya da bubbude pages din dayake kamar wanda aka tsaida da remote Saikuma ya dago ahankali ya kalleta yaga ita hankalinta ma na kan textbook din gabanta "Your man?" yafada yana tsareta da ido Dagowa tayi itama tana kallonshi and she can swear taga wani abu mai shigen da kishi a idanunshi saikuma taga yayi saurin sauke idanu Hakan yasata amsawa cikin fara'a "yes, sorry ban ta6a discussing dinshi da kai ba, he's my cousin, he's very nice insha allah zanyi introducing dinku wa juna watarana" Tunda tafara maganar ya sake dagowa yana kallonta har takai aya Wani dry murmushi yayi sannan ya maida kanshi akan littafin gaban shi ya cigaba da budewa Itama bata qara cewa komai ba ta maida hankalinta kan littafin dake gabanta Sai wajen ya dauki wani unusual silent da basu saba dashi ba don muddin suna tare babu yadda za'ayi su dauki tsawon lokaci kamar haka batareda sunyi exchanging Koda kalma daya ne Suna ahaka har lokacin shigar zee class yayi Hakan yasa ta maida littafin ta rufe ta dago ta kalleshi taga idanunshi kafe suke akan littafin gabanshi shima Tashi tsaye tayi wanda Hakan yasa shima ya dago for the first time bayan maganarsu ta dazu yana kallonta Maida textbook din tayi a shelve din library din inda ta zaroshi sannan ta dawo ta dauki jakkarta dake kan desk pretending bata lura da kallon dayake binta dashi ba Rataya jakkar tayi sannan ta kalleshi "Bari natafi kar na makara Deen, see you" tafada tana dan daga mashi yatsu Murmushi kawai yayi ya kada mata kai tawuce yabita da kallo harta fice _*my man*_ kalmar ta ta dazu tadawo mashi a kwanya Ahankali ya lumshe idanu ya bude yana jan wani nannauyan numfashi Me Hakan ke nufi? Me take nufi da *her man?* Koma dai me Hakan yake nufi beyi sounding good to him ba Haka kawai yaji zuciyarshi ta quntata tayi mashi nauyi ga wani daci daci dayake ji maqoshinshi Maida littafin gaban shi yayi ya rufe shima ya tashi ya kwashi littafanshi ya rungume ya fice daga library din Wani quiet wuri yasamu ya zauna don haryanzu akwai kingin lokaci kafin yashiga class Duk yadda yaso ya maida hankalinshi akan littafin daya kuma zarowa kasawa yayi Kalmarta kawai take mashi kai kawo a zuciya *sorry ban ta6a discussing dinshi da kai ba, he's my cousin, he's very nice insha allah zanyi introducing dinku wa juna watarana* Jiyayi zuciyarshi taqara quntata, yaji ya tsani mutumin tun kafin ma ya ganshi Haka yaita zama shikadai cikin quncin zuciya har lokacin lecture dinsu yayi ya tashi ya wuce class Saidai me? A class din ma babu abinda ya fahimta, yadai ga lecturer din nata 6a66atu amma bazai iya riqe kalma daya daya fada ba Har akayi lecture din aka gama be fahimci komai ba, haka shima ya taso yabiyo ayarin masu fitowa daga class din yafito Kasancewar anfara kiraye kirayen sallah yasa yawuce masjid din school din don yin sallah Koda yafito be bi takan inda zasu hadu ba yawuce class ya zauna dukda saura mintuna talatin afara lecture din, haka kawai yaji beson zuwa wajen ta yanzu saboda yadda zuciyarshi kemashi zafi duk in yatuna da kalmarta Haka ya zauna ya rungume hannayenshi a qirjinshi ya kafe wuri guda da kallo abubbuwa kala2 na kai kawo a qwanyarshi Ahankali ahankali class din yafara cika har lecturern dazai yimasu darasin shima yashigo Abin mammaki wannan karon ma babu abinda ya tsinta a abubbuwan da akeyi a class din Gangar jikinshi ke zaune a class din amma hankalinshi da tunaninshi sunyi nisa, be ankaraba yaga anfara fita daga class din alamun har angama lecture din Agogon hannunshi ya duba yaga har 4pm saura Hakan yasa shima ya tashi jiki a sanyaye yafito Koda yazo inda suke zama be ganta ba hakan yasashi wucewa library nan ma babu ita sai ya wuce department dinsu don ganin ko tana can amma canma babu ita don babu ma mutane sosai Wurin Hakan yasashi sanin ta tafiyarta Sai yaji zuciyarshi taqara quntata, ranshi yaqara dagulewa yaji wani abu ya tokaremashi qirji Juyowa yayi kawai yanufi hanyar fita school din Cikin sa'a yana fitowa yaga wata napep ta sauke wadansu sai ya qarasa yayiwa mai napep din magana suka daidaita yashige suka wuce A bangaren zee kau tun daga reaction dinshi na farko data gani tafara tabbatar da hasashenta Kamar yadda Deen yayi attending class batareda ya fuskanci komai ba Haka itama tayi Itama kawai zama tayi a class din amma bata fahimci komai ba, gabadaya hankalinta da tunaninta nakan reaction din Deen na dazu. Tabbas ta hango wani abu mai shigen kishi a qwayar idanunshi and then sai yarage kuzari, yama qi magana harta taso tabar wajen Dukda yayi qoqarin 6oye expression din fuskarshi tana iya hango bitterness din fuskar, tabbas maganar ta ta dakeshi don taga alamun Hakan Cije lip dinta na qasa tayi sosai tana jin yadda zuciyarta ke bugu sosai. Tama rasa tunanin da zatayi. Koda suka fito lecture din itama masjid ta nufa tayi sallah, tana fitowa kuma ta hangoshi shima ya fito ya nufi hanyar barin wajen, kamar tayimashi magana kuma saita fasa tabi tafiyar dayakeyi a sanyaye da kallo, tabbas muddin ka sanshi sosai kallo daya zakamashi ka gane ba lau Wani dan murmushi ya su6uce mata tana wani calculating a zuciya sannan ta dan ciji qasan lip dinta itama tafito daga wajen Koda tafito daga next lecture din nasu bata tsaya jiran shi ba kamar yadda tasaba kawai tashige mota suka fice tana jin wani yaqini a zuciyarta *** A bangaren Deen haka ya qarasa ranar cikin rashin walwala, ko kaka ma tasan yau ba lau ba Tambayar duniyar nan tayimashi amma amsar daya ce "babu komai" Hakan yasa tayi tunanin ko bejin dadi ne shiyasa yake tsoron gayamata saboda shan magani Hakan yasa taje ta dauko magani tabashi akan yasha Ga mammakinta sai gani tayi ya amsa babu ko gardama ya watsa a baki ya kora da ruwa ya tamke idanu yana hadiyewa don shima abinda zai sauqaqa mashi abinda yakeji a zuciya yake nema shiyasa beko yimata gardama ba ya amsa yana ganin inhar zai sauqaqa mashi abinda yakeji babu abinda zai sashi yaqi sha Komawa yayi ya jingina da bangon dakinshi yana maida numfashi Jiki a sanyaye kaka ke mashi sannu Saidai ko bude idanunshi beyi ba Ce mashi tayi ya kwanta ya dan rintsa qila kafin ya farka zaiji sauqi Babu musu ya zame ya kwanta yaqara tamke idanu yana jin yadda zuciyarshi ke tashi kamar zaiyi aman maganin dayasha Saida yaji fitarta sannan ya bude idanu ahankali ya kalli kofar data rufomashi Qara maida idanun yayi ya rufe yayi shiru *my man* muryarta taqara yimashi amsa kuwa a kunnenshi *he's very nice* Bude idanun yasakeyi sannan ya miqe zaune ahankali Wayarshi ya lalubo ya danna power botton takawo haske Time ya duba yaga 10 saura na dare Haka kawai sai gani yayi ya shiga contact ya fara scrolling sunayen ciki Daidai sunanta dayayi saving da *bestie* ya tsaya Ya dade yana kallon number sannan ahankali kamar mai tsoro ya dannama number kira _the number you dial is busy with another call, please hold on or try again later_ Abinda yaji baturiyarnan ta m.t.n tafada kenan sannan ta cigaba da ringing Harta katse bata dagaba Hakan kuma be hana yasake kiraba yanajin zuciyarshi na wani irin zafi kamar a oven Tambayar dake kai kawo a qwalwarshi itace dawa take wayar? Yayinda zuciyarshi ke hasasomashi qila da so called *man* dinta take wayar Saida ya jeramata kira uku duk babu wanda ta daga she's busy on another call, qarshe sai tayi sending sms na _*am busy, please call later*_ Besan ya akayi ba sai gani yayi ya wurgar da wayar ta daki bango ta fado qasa Be bi takanta ba ya koma ya kwanta kan gadon ya jawo bargo ya rufe jikinshi har kai dukda uban zafin da akeyi Ya runtse idanunshi Gamm yanajin zuciyarshi na suya kamar a kasko... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:37 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *040* *THE CONFESSION💗* Koda gari ya waye Dakyar kaka ta iya tadashi yafita sallar asuba don dama sai gab da asuban yasamu barcin ya dan daukeshi Kallo daya zaka yima yanayinshi kayi tunanin beda lfy duba da yadda yaqaro sanyi ya hada da ainahin sanyinshi Ba'a dade da gama sallar ba yadawo yana jin kamar yayi shigewarshi daki yayi barcinshi amma bazai iya barin kaka da wadannan tulin aikin ba ita kadai Gaisawa sukayi da kaka kamar yadda suka saba tana Tambayar jikinshi yace mata da sauki ya wuce Domin hura wutar koko Be wani sha wahala ba takama kasancewar dama ya saba da hurin wutar amma maimakon ya tashi ya dora tukunyar saiya tsaya a tsugunnen dayake ya qurawa jar wutar dakeci ido Kaka batasan yana yiba har Saida tagama wanke waken data surfa takawomashi don yakai markade sai ta ganshi tsugunne gaban murhun ya qurawa wutar ido kamar mai karantar wani abu jikinta Magana tayi mashi amma beji ba don yayi nisa sosai Saida ta dan ta6ashi sannan yayi saurin dagowa sai kuma ya kalli wutar yayi saurin tashi yawuce don dauko tukunyar kokon kaka na binshi da kallo Saida ya dora ruwan sannan ya amshi bokitin waken yafita yo markaden Kasancewar ya dan makara da zuwa markaden sai ya tararda jira har mijin mai markaden na tsokanarshi wai ko yau ranar barci sukayi Shidai bayan murmushi babu abinda yake Waje ya koma don jira yasamu dakalin kofar gidan Shiru yayi ya kafe santar tasu da ido yana dorawa daga inda ya tsaya a tunaninshi yana kuma tunano mafarkan dayayi nata a yar kwanciyar nan dayayi Wanda yafi daga mashi hankali cikinsu shine wanda yayi daga baya bayannan wanda yana cikin yinshi ne kaka ta tadashi Wai a cikin mafarkin yaga zee zaune da so called cousin din nata suna fira dukda be iya ganin fuskar mutumin ba sosai Fira suke sosai suna Dariya, kawai sai gashi kamar an jefoshi a wajen Be nufi kowaba sai saurayin yafara yimashi qarajin ya tashi yabar wajen Qin tashi mutumin yayi kuma yaqi kallonshi hasalima kamar basu masan dashi ba don firarsu suka cigaba dayi cikin nishadi Haushi yaji saiya ture mutumin daga kujerar dayake akai ya fadi Jiyayi zee tayi qara kamar ita ya ture sannan ta tashi tana hayyayako mashi akan meyasa ya ture "man" dinta shikuma ambatar man dinnan yaqara qular dashi sai ya juyo kanta yafara magana cikin hayyayakowa shima, Saidai shi kanshi besan abinda yake cewa ba, kamar ma maganar bata fita don jin maqoshinshi yayi tamau kamar an shaqe amma ahaka yake fizgar magangganun yana gayamata, magangganun ma ko sauti babu Yana cikin haka yaga ta tureshi gefe taje zata tada wancan wanda ke kasa har lokacin sai ya cafko hannunta ya fizgota ta fado jikinshi beyi wata wata ba ya Hade bakinsu Waje daya Mutsu mutsun qwacewa tashiga yi amma yaqi bata dama saima farma le66unanta dayayi kamar maye yasamu nama, ahaka yaji ana janshi a baya ana jijjigashi, can yaji muryar kaka na cewa "kyakyawa ka tashi, kyakyawa na! Kyakyawa! Ka tashi karda ka rasa jam'i" Sai a lokacin yafara bude idanunshi ahankali har suka bude tarr yaga kaka sunkuye akanshi tana cigaba da tadashi, dan Juyawa yayi saiya fuskanci ashe ma kan katifarshi yake, ashe mafarki yake. Saida ya tabbatar Yana da tsarkin jiki sannan ya lalla6a ya taso yafito jiki a mace Jin a dan bubbugi kafadarshi yasashi qara yin firgigit ya dago yadawo daga duniyar tunanin daya sake lulawa Wani yaro yagani tsaye akanshi bokitin markaden Deen a gefe "yaya Deen wai ance ga markaden" inji yaron Miqewa Deen din yayi ya lalubi kudi yaba yaron yace yakai sannan ya dauki markaden yayo gida cikin dan sauri sauri ganin yadda gari yayi fau yayi haske yasan ma kaka nacan tana tunanin lafiya Illai kuwa yana shiga sukaci karo da kaka datake shirin fitowa jin shirun yayi yawa Tambayar shi tayi ya akayi ya dade haka yace mata jira ke akwai Suka dawo ciki tare yaga harta sheqa tukunyar farko ta maida wasu Murhun qosai yanufa yafara hurawa ita kuma kaka tashiga hada kullun qosan Cikin dan qanqanin lokaci suka gama kaka tafara tuya izuwa lokacin har yara sunfara Shigowa Haka dai Deen ya daure yayi attending customers din har suka samu yaqare duka Lokacin har tara da rabi Hakan yasa kawai yafada bandaki yayi wanka sannan ya fito ya hau shirin school Har daki kaka ta kawomashi nashi kokon don ya karya Saida tagama sannan ta miqa mashi magani akan yasha taga haryanzu kamar jikin be warware ba Kamar zaiyi kuka yake cemata shifa ya warke amma bata kulashi ba Saida yashasu yana kakari yana komai Sannan ta sallameshi yafito daga gidan lokacin har goma ta wuce yasamu aca6a suka daidaita yahau suka lula *UMYU* Koda ya iso school din be nemeta ba don yasan tana class kasancewar yau morning lecture gareta sai kawai yayi wucewarshi inda suka saba zama idan basa library yayi zamanshi can ya dora karatun jakinshi daga inda ya tsaya Students suke ta fita daga class din. Ida rubuta abinda take rubutawa tayi sannan ta maida littafin ta rufe ta bude jakkarta ta saka aciki Itama tashi tayi tabi ayarin masu fita itama tafito Fiddo wayarta tayi ta duba time taga 11:52am Hakan yasa tasan is either yana library ko wurin da suka saba zama don yau lecture din 1pm gareshi, dama duk sunyi cramming lokacin lectures dinsu aka Library tafara nufa dukda tasan mawuyacine ace yana can duba da zafin da akeyi a garin don yanzu damuna ta wuce ana zafin gasa dawa Bata tarar dashi ba wurin kamar yadda tayi hasashe saita juya ta nufi inda suke zama din don tasan tabbas yana can Daga nesa ta hangoshi zaune bisa benci ya sunkuya qasa amma batasan abinda yakeyi ba Ida qarasowa tayi, jin motsinta yasa Deen saurin sa kafa ya baje rubutun dayakeyi da dan kara a qasa sannan ya dago yana kallonta, looking so beautiful as ever Harta qaraso wajenshi be Janye idanunshi akanta ba har Saida ta kyafkyafta mashi yatsu a fuska sannan yadanyi blinking sai kuma ya sauke idanunshi qasa Zama tayi kan dutsen dake facing dinshi tana cewa "wannan kallon saikaja inyi tuntu6e" Bece komai ba kuma be dago ba "Saida naje library na tarda baka nan, how's my kaka?" Sai a lokacin ya dago ya kalleta sai kuma ya motsa baki kamar mai ciwon baki yace "she's fine" Ganin yanayin dayayi mata magana kamar anyi forcing dinshi yasa bata qara ce mashi komai ba ta zaro wani Littafi ta shiga budewa "I called jiya baki dagaba" yafada yana kafeta da ido "yes I was on another call kuma I tried to reach you later amma bata shiga" tafada hankali Kwance batareda ta dago daga bude littafin datake ba "you're busy with another call, da wa?" Kafin ta bude baki ta amsa ya tari numfashinta da *"Your man?"* Dakatar da bude littafin datake tayi ta dago ta kalleshi and for the first time taga a very serious expression a fuskarshi, tunda take bata ta6a ganinshi in seriousness kamar yau ba, babu alamun wasa ko kadan a fuskarshi Daga kafadu tayi ta maida hankalinta akan littafin hannunta tace "yeah, ka canka daidai, I was busy with him" Jin maganar tata yayi kamar saukar mashi a qahon zuciyarshi, bugun zuciyarshi yashiga gudu sosai Dukda taji yadda hasken idanunshi ke reflecting a fuskarta bata dago ba saima cigaba da bude littafinta take wanda a zahiri tama wuce inda take son budowa Hadiye wani yawu mai daci Deen yayi sannan ahankali yace "Zainab.." Sosai kiran yashigeta don yayishi ne in a very cool manner Dagowa tayi ta kalleshi batareda tace komai ba sai zuciyarta dake qara gudu Kamar bazai ce komai ba sai kuma yaqara tattaro wani yawun ya hadiye sannan yace "please ina neman wata alfarma wajenki" Shiru tayi takasa cewa komai saboda yadda zuciyarta ta tsananta bugu jitake kamar data bude bakin zuciyarta zata biyo ta wajen ta fito Ganin batace komai ba kuma bata bar kallonshi ba yasashi cewa "please, karki qara... Kulashi" ya qarashe yana kallonta da wani expression mai wuyar ganewa a fuskarshi Batace komai ba sai kallonshi datake still "please... Don Allah" yasake fada murya a matuqar sanyaye Cikin danne abinda ke taso mata a zuciya ta yamutsa fuska "I don’t get you" Ajiyar zuciya ya sauke yadan ciji lower lip dinshi yasaki sannan yace "I mean, your... Cousin, please kibar kulashi" "why?" tafada tana mashi wani kallo "because... I think... I don’t like him, please just stay away From him kuma kibar picking call dinshi... Please, do this for me... Please" Sai kuma ya dafe kanshi yana jin yadda zuciyarshi ke zillo "what? Kasan abinda kake fada kuwa? Kasan matsayin wanda kake magana akai aguna, you just Said it, he's my cousin" Janye hannunshi daya dafa kanshi dashi yayi yace "am.. Sorry, nasan family dinki ne but... Just let it remain like that, babu qari babu ragi. Please kibar kiran shi your man kuma kibar waya dashi like that" yafada shi kanshi yasan he sound so stupid "me? Meye aciki don nayi waya dashi?" "ba wayan dashi ne matsalar ba, what you guys are discussing ne" "me muke discussing?" inji zee tana kallonshi kamar yau tafara ganinshi don sosai yakoma kamar bashi ba yawani burkuce "I don’t know also amma koma menene it doesn't sound good to me, nasan qila kunyi awa kuna wayar.. And also dare ne, kamata yayi ace barci kike a lokacin" "kamata yayi ace barci nake a lokacin kuma kai ka kira?" "na kirane don nayi confirming kinyi barcin ne and also Koda kin daga bewuci mu gaisa ba inyi miki good night muyi hanging call amma shifa? Heaven knows what he's saying to you kuma allah kadai yasan lokacin da kuka gama wayar" Tunda Deen yafara take kallonshi cikin mammaki deep down kuma farincikine kesata jin kamar ta taka rawa Ganin wanda kake tunanin kai kadai ke haukanka akanshi na kishinka ba qaramin abu bane mai antaya mutum cikin farinciki, wanda ya tsinci kanshi a wannan yanayin kadai zai iya ganewa "well ni banga abinda zai dameka ba akan haka" "but am your friend, dole na damu dake" "and he's my man, my boyfriend.." "damn it!" yafada yana qara dafe kai cike da takaici "wai Deen are you sure you're ok?" Dagowa yasake yi wannan karon idanunshi sun fara chanza launi "Nace maki kibar kiranshi your man and you're now calling him your boyfriend" "wai Deen meke damunka ne? Meye matsalarka dashi" "I don’t know, I just hate him, can't you get that?!" yafada cikin dan daga murya yana jin kamar yaita ihu don takaici "you hate him? My boy friend?" "oh my God! For Heaven's sake kibar kiranshi haka?" yafada jijjiyoyin wuyan shi na tashi Dukda taji tsoron yanayin shi amma bata fasa cewa "why? He's my boy friend, he loves me who are you to tell me not to love him back" tafada tana miqewa tsaye tana mashi wani kallo Shima miqewa tsaye yayi "No! Qarya ne, wlh ba sonki yake ba, yaudararki zaiyi, he never loved you" yafada yana maida numfashi ahankali "what?" tafada tana dan ja baya "yes, he doesn't, I swear, kawai he want to play your heart ne, he want to use and dump your heart, ki yarda dani" yafada yana dan matsota "Deen, are you sure you're ok?" tafada tana qara jada baya ganin kamar ma ba a hayyacinshi ba yake "yes.. Yes, yes Zainab, am ok, ki yarda dani, he doesn't love you, baya sonki, nike sonki Zainab, nike sonki..." Tsit wajen yayi Dafe kai yayi yana jan numfashi ahankali yayinda zee data qame kamar statue takasa Janye idanunta akanshi Dagowa yasake yi ya kalleta da idanunshi dasukayi ja "am... Sorry Zainab, am..." saikuma yaqara dafe kanshi, yakoma wani zararren qarfi da yaji lokaci guda Sake Dagowa yayi "Don Allah.. Kiyi hqr, bansani bane, bansan sadda nace haka ba... Amma kuma Gaskiya ce I.. Love..you, Kiyi hqr amma that's it, the truth Na dade ina ajiye wannan kalmar a zuciyata, na dade ina juriya wajen ganin na barta iya cikina amma not any more, bazan iya ba kuma. Am sorry.. Am sorry" yafada yana Hade hannayenshi Ahankali zee da haryanzu idanunta ke kafe akanshi tafara takawa da baya baya Ganin Hakan yasa yafara Binta shima ahankali "nasani.. Nasan na wuce iyakata amma don Allah Kiyi hqr, wlh nima bansani ba, bansan sadda nafara sonki ba, please don't leave, please" Haryanzu batace komai ba kuma bata bar kallonshi ba kuma bata bar tafiya da baya baya ba "please Zainab, stop moving, say something but please don't leave me, nima nasan I was stupid to think of doing that but I swear nima bansani ba, bansan yadda akayi ba nafara ba, I swear ban saniba" yafada still yana Binta Juyawa tayi da sauri tafara tafiya da sauri sauri don barin Wurin Ganin Hakan yasa shima Binta da sauri, Ganin Hakan yasata fara gudu shima yasa gudu yabita Saidai cikin tsautsayi yayi tuntu6e da wani dutse a gabanshi yayi saurin duqawa yana kama kafar Sake Dagowa yayi yaga takusan shanye kwana Hakan yasa shima yacije ya tashi dukda radadin da qafarshi kemashi yabiyota Saida Koda shima ya shawo kwanar babu ita babu alamunta Cigaba da tafiya yake yana waige waige, yadai san bata isa takai gate ba don akwai tazara sosai da nan wajen dole ya hangota, dole Saidai idan wani Wurin ta 6oye "Zainab? Zainab!!" yafada yana dudduba Wurin amma babu ita Hakan yasashi qarawa gaba yana nemanta amma ba ita ba labarin ta, Hakan yasa yadawo yanufi department dinsu yaga ko can tayi Daga inda take la6e ta hangi shigewarshi kwanar da zata sadashi da department dinshi Hakan yasata fitowa tana share hawayenta ta nufi hanyar gate da sauri sauri tana yi tana waige harta samu tafito daga school din Wasu adaidaita biyu tagani sunzo wucewa tashiga tsaida na farkon Saida tazo gab taga ashe cike take Saita koma tana tsaida na biyun Cikin sa'a babu kowa ciki, fadawa ciki kawai tayi tana cema mai adaidaitan sutafi tana leqen gate din school din Babu musu mai adaidaitan yaja napep din suka bar wajen Babu inda be duba ba a department dinsu amma babu ita yasake dawowa inda ta 6oye dazu batanan ya wuce library nan ma haka "ya sallam!" Yafada yana zama kan daya daga cikin kujerun library din ya dafe kanshi "my goodness! Tayaya ma nayi wannan su6ul da bakan" yafada yana rufe fuskarshi da taffukan hannunshi yana furzar da huci Yes he's in love with zee kuma ya dade da sanin haka Saidai bayada courage din tunkararta da Hakan Tayaya talaka kamar shi wanda bayan allah da annabinsa beda kowa sai kakarshi zai tunkari mace kamar zee, yarinya yar masu kudi, wanda babanta sannane ne a katsina dama nigeria gabadaya? Tayaya? Bazai iya tunkararta da hakan ba, gani zatayi yama raina ajinta, gani zatayi don yaga tayi strooping tana abota dashi shine yasa zai wuce makadi da rawa wajen cewa yana sonta Tabbas yasan zee tafi qarfinshi ata koina, asali, arziqi, class, komai ma Yanayi ne ma da qaddara yasa suka Hade a school dinnan don yasan tafi qarfin zuwa school din Tun sadda ya fahimci halin da zuciyarshi ke ciki gameda ita yasa yafara kafa kafa da ita wajen barin Hakan iya zuciyarshi batareda ya barshi ya fito ba Ya gano Hakan ne tun kwanciyarshi a hospital, yaso yayi denying Hakan amma ita zuciya batasan wannan ba, abinda takeso shi takeso ko kai mai zuciyar kaqi ko kaso Lokacin da aka sallamesu daga hospital he's very sad Dik majinyaci farinciki yake a lokacin da aka bashi sallama amma shi akasin haka ne a wajenshi don yasan Hakan na nufin yin nisa da juna, dan ganin ta dayakeyi sau biyu a ranar zai zama tarihi Hakan yasa lokacin dazasu tafi yakasa tafiya ya tsaya yana kallonta yana jin kamar ya hanata tafiya amma haka ya daure yanaji yana gani ta tafi tabarshi feeling very empty kamar ta tafi mashi da abu mai matuqar muhinmmanci kodayake ta tafi din da abin nashi mai muhinmmanci, zuciya ❤️ Tun daga lokacin yake jin tsananin kewarta da begenta, kullum cikin tunaninta yakeyi da mararin ganinta amma yasan ba hali wataqila shida ganinta sai sunyi resuming Kwatsam sai gata sati daya da sallamarshi Lokacin daya shigo ya ganta jiyayi kamar a mafarki don be ta6a kawo Hakan a ranshi ba Murza idanunshi yashiga yi don tabbatar da ita din ce sai yaji kaka na cewa "qaraso mana, ita din dai ce" Qarasowa yayi cikin doqin ganinta Saidai me? Saiya lura ita kamar bata doqin ganinshi don kallo daya tayimashi ta sauke idanunta qasa Hakan yayi matuqar sanyaya mashi jiki amma ya daure yayi mata magana yana tambayarta yasu mummy Babu yabo ba fallasa ta amsa mashi saikuma ta tashi wai zata tafi Beji dadi ba sam don ba Haka yaso ba, so yayi tayi zamanta susha firarsu yayita kallonta yana jin dadi Ganin dagaske tafiyar zatayi harta miqe yasashi shima tashi ya shiga dakin kaka ya dauko wayar data bashi don maida mata Koda yafito har takai zaure yayi saurin Binta Kiranta yayi ta tsaya amma bata juyoba Tambayar ta yayi tafiya zatayi sai ta juyo tace eh ko yanada matsala da Hakan ne? Beji dadin amsar ba Amma ya amsa da A'a sannan ya maida mata wayarta, da farko be lura da kallon datake mashi ba sai daga baya lokacin daya miqa mata wayar hannunshi don ta samashi number mummy Kallon datake mashi lokacin yakuma sanyaya jikinshi sai yaji yakasa yimata dayar maganar wato tasamashi numberta su dinga gaisawa Ganin taqi barin kallonshi yasashi tambayarta lfy kau? Sai yaga ta kauda kai saikuma tasake juyowa ta amsa da lfy ta amshi wayar tayi yan danne danne ta miqomashi Qin amsa yayi yana kallonta trying to read her expression amma Abu daya ya iya ganewa, tana fushi Hakan yasa yakasa qara tambayarta number ta sai ya amshi wayar kawai yana cewa "Are you sure you're ok?" Sai gani yayi ta juya tana cewa "more than you are" ta fice Binta da kallo yayi yana jin ba dadi, tsawon satin dayayi batareda yasata a idanunta yasa yayi missing dinta sosai yayi tunanin itama Hakan yake a wajen ta yayi tunanin duk lokacinda suka sake ganin juna Dakyar zasu rabu Fitowa yayi ya tsaya bakin kofar gidansu yana kallonta ta cikin mota dukda baya iya hangota saboda tinted glass din motar, yana ji yana gani aka ja motar aka tafi aka barshi nan Daga lokacin duk sai jikinshi yayi sanyi, ya kasance kodayaushe cikin tunaninta yake Bayan kwana biyu da tafiyarta ya matsa ma kaka ta bugama mummy tayi mata godiyar datace zata yimata Haka yaje yasanyo kati na #200 a lokacin ita kenan ma gareshi duk don yaji lfyar zee in so samu ne ma yaji muryarta Saidai Koda suka gaisa din kaka ta tambayi zee tace ina take tace mata lfy lau tana dakinta, jiyayi kamar yace ma kaka tace a kai mata amma babu dama haka shima ya amshi wayar suka gaisa sukayi sallama da juna ba don yaso ba Bayan kwana biyu again yasake tusa kaka gaba akan tasake kira, shima wannan lokacin zee batanan tashiga wanka wai, Hakan ba qaramin sake dagulamashi lissafi yayi ba A kira na uku ne yaji mummy na gayama kaka zee tayi tafiya zuwa garinsu mummyn, Hakan ba qaramin sake dagulamashi lissafi yayi ba don Hakan ya tabbatar mashi cewa shi da ganinta ko jin muryarta kuma sai sunyi resuming Haka ya hqr don dole ya cigaba da looking forward na resuming dinsu, kullum cikin qirgar ranakun dasuka rage yake Ranar daren dazasu koma ko isashen barci beyi ba saboda doqi Ranar dazasu koma kuma safko ya buga saboda doqi, yaci kwalliyarshi ciki kayanshi na qure daka yatafi Saidai me? Wannan karon ma tarbar dabeyi tunani ba tayi mashi Yana shiga gate din school din yaganta kuma kallo daya yaimata ya gane itace dukda bayanta yagani, Hakan yasa yafara sauri yana kiran sunanta Saida yakusan taddota sannan yaga ta tsaya alamun tajishi amma bata juyo ba Da sauri ya qarasa yana maida numfashin saurin dayayi Zagayowa yayi gabanta yana kallonta cikin so da shauqin ganinta "Zainab is this you?" yafada cikin tsananin shauqi da jindadin ganinta Sai gani yayi ta dago ta kalleshi tayi shiru kamar mai karanta wani abu a face dinshi "Zainab, are you ok?" yafada ganin yadda ta kafe shi da ido Still babu amsa kuma batabar kallonshi ba "Zainab..." Sai yaga tasa hannu ta toshe duka Kunnuwanta ta runtse idanunta gamm Ganin Hakan yasashi rudewa, qara kiran sunanta yayi sai yaga tayi saurin Zagayeshi ta wuce Hakan yasashi binta ya sha gabanta Cikin matsanancin damuwa yasake tambayarta lfy amma saita qara ra6awa zata wuce yasake tareta da sauri yana sake kiran sunanta Tsawa tayi mashi wanda yajishi har cikin ranshi wanda Hakan Saida yasa yadanja baya "I said leave me alone, can you get that?!" tafada again a tsawace Dukda tsoron tsawar dayake Hakan be hana yadan qara matsowa ba yasake kiran sunanta, sai ta dafe kai tajuya takoma ta inda ta fito Da farko kasa Binta yayi saikuma yabita amma yana zuwa yaga wucewar adaidaita ashe itace a ciki Sosai jikinshi yayi sanyi yaji kamar yaita kuka, ya dade tsaye a wajen harya gaji yakoma Koda yakoma ma wuri yasamu kan dakalin wani office ya zauna inda zai dinga hango gate yadda data shigo zai ganta Amma shiru babu ita babu alamunta har lokacin zuhr yayi dole ya tashi yaje yayi sallah yakuma dawo ya dasa jiranta daga inda ya tsaya Saidai har asr bata dawo ba hakan yasa ya tashi yayi sallah yawuce gida zuciyarshi a matuqar sanyaye Ranar beyi wani barcin kirki ba saboda damuwa Washegari ma Hakan take don ranar tun Shigowarta ya ganta kasancewar ranar ma dawuri yaje school din Yana kallonta har tazo ta wuce sannan shima ya lalla6a yabita har inda tasamu ta zauna Tsayawa yayi jikin wata bishiya mai facing dinta ya rungume hannayenshi a qirji yana kallonta Abin mammaki Saida yadan jima ahakan kafin ta farga dashi kuma tana ganinshi ta sake kafeshi da ido irin jiya Qarasowa yayi gabanta ya tsugunna yafara qoqarin yimata magana tăsake tashi zata tafi Shan gabanta yayi yana mata magiyar ta gayamashi ko fushi take dashi amma taqi sauraronshi saima tsawar datayi mashi, Ganin Hakan yasashi barinta ta wuce, har tayi nisa ya tsaidata ta hanyar tambayarta ko saboda ya maido mata wayarta take fushi, idan ma don hakane tayi hqr shi bada niyyar ya 6ata mata rai ba yayi Hakan Bata ko juyo ba tawuce ta barshi nan tsaye Sai yaji zuciyarshi taqara quntata, sai jiyayi duk murnarshi ta Ayi resuming school yaganta duk ta koma ciki, damuwa ta maye gurbinta Washegari yazo har yatafi bega 6il6ishinta ba, Hakama Washegari nan ma ko mai kama daita be ganiba Hakan kuma ba qaramin qara tsundumashi kogin tunani da damuwa yayi ba Ranar juma'a kamar bazai ceba saikuma ya shirya jiki a sanyaye yaje don daya zauna gida yaita tunani gwara yaje can Koda bazai ganta ba atleast zai samu damar tunaninta batareda takurawar kaka ba Usual inda yasaba zama cikin yan kwanakinnan wato dakalin wannan office din inda ake iya hango gate daga nan ya tsaya ya jingina da bango Be dade ba kamar a mafarki kawai yaga Shigowar motarta Be motsa ba hakan zalika be kyafta idonta ba akanta har aka bude mata kofa tafito Sosai tayi mashi kyau cikin shigar shaddar datayi Hakan yasa ya shawara da kallonta Kawai sai gani yayi tafara waige waige, sai zuciyarshi tabashi ya 6oye kar ganinshi yasa tasake Juyawa ta koma yau ma Saidai kafin yayi wani yunkuri harta juyo sun hada ido Gani yayi ta kafeshi da ido shima sai yakasa Janye nashi akanta yana kallonta zuciyarshi nata zallo kamar zata fito waje Ga mammakinshi sai yaga ta sakarmashi murmushin da be ta6a ganin wanda ya ta6a yimata kyau irinshi ba Tashi yayi daga jinginen dayayi yana jin nauyin zuciyarshi na raguwa ahankali Blinking idanu yayi don ganin ko idanunshi ke gayamashi qarya Sai yaga dagaske ne, zee daice tsaye tana mashi murmushi Besan sadda shima yafara murmushi ba harda yar Dariya sannan ya qaraso wajenta da sauri Murmushi tasake yimashi sannan ta wuce shi ta nufi hanyar library ganin Hakan yasa shima yabita da sauri feeling so happy, baqincikin zuciyarshi na yayewa To a lokacin ne suka shirya, ranar yayi farincikin daya rabu dayi kuma a ranar bebari damarshi taqara su6uce mashi ba ya amshi number ta kuma ya amshi wayarta data mashi kyautarta Yaso ya kirata tun ranar amma gudun karya takura mata ko taqara botsare mashi yasa yafasa ya haqura har Washegari, da yaso yabari ya haqura har dare amma yakasa sai ya bugamata a lokacin Yaji dadin samunta dayayi da kuma dagawar datayi a kira na farko don yadda yasanta da ajinnan yayi tunanin bazata daga ba, kuma ajinta na daya daga cikin abubbuwan dayasa ya kware mata sai kyawawan dabi'unta wanda idan ba saninta kayi ba sosai bazaka ta6a sanin tanada su ba, she's classic but simple, very simple and nice A ranar badan yaso ba yayi mata ban kwana dawuri ba saidon karya takura mata gashi daman lalla6ata yake yi karta qara yin fushi dashi don yasan shi zaisha wahala don bazai iya yin zuciya ya barta ba don zuciyar bazata bada hadin kai ba, gwara dai ya lalla6a Ahaka har suka kwashe wadannan lokacin kullum da sonta yake kwana yake tashi don jiyake ma kamar qara huramashi wutar sonta a zuciyarshi Hakan kesa wani sa'in har tausayin kanshi yake don yasan abinda bazai yiwubane yake qwallafawa ranshi akai, amma ya ya iya? Shi kanshi da yasan yadda zaiyi ya cire sonta a zuciyarshi da yayi Hakan amma baya iyawa Hakan yasa yabar abinshi a zuciya dukda wani sa'in Dakyar yake controlling emotion dinshi, gudu yake kar Hakan yasa yayi biyu babu ba soyayyar takuma warware abotarsu, gwara ya tsaya da daya, da babu gwara ba dadi Saidai kalmar ta na *my man* yazo ya ruguje tsarinshi, besan yanada kishi ba sai jiya, jiyayi kamar garwashin wuta ta watsa mashi a lokacin, Ganin idan yace zaiyi magana zai saki layi yasashi hadiye wa Dakyar yayi controlling emotion dinshi amma na yau is so unbearable Jiyayi kamar yaita hauka lokacin da take kiran wani her man wai harda boy friend, Hakan yasa yakasa controlling kanshi harya furta abinda ya dade yana 6oye wa a zuciyarshi Shikenan ya rushe komai, ya lallata komai, ya rasata har abada, bazata qara kulashi ba, he can't imagine rayuwa batareda ita ba, yasan shikenan watan wahalarshi ta kama Sauke taffukanshi daya rufe fuskarshi yayi ya hadesu daidai saman bakinshi yana jin kamar yayi kuka Shi kenan, shi kenan. Abinda yaita nanatawa a zuciyarshi kenan Dan karkatawa yayi ya zaro qaramar wayarshi don dama baya fitowa da babbar yayi saurin shiga call log ya lalubo numberta dake sama don dama tun bayan Kiranta dayayi jiya be qara waya ba Dialing number yayi yana hadiye wasu yawu a bakinshi Ringing take amma har tayi ta tsinke ba'a daga ba, qara danna wani kiran yayi nan ba babu response be gaji ba yasake danna wani kiran itama harta yanke ba'a daga ba. Sake kira a karo na hudu yayi amma sai yaji yar baturiyarnan mai ban haushi na cewa _the number you dial is switch off, please try again later_ Cike da jin haushi yau ma ya jefar da wayar kamar na jiya yasa hannu bibbiyu ya dafe kanshi dake barazanar rabewa gida biyu... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:37 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *041* *IS LOVE REALLY BLIND? 🖤* "madam ina muka nufa?" Sa bayan hannunta tayi ta goge wasu sabbin hawayen dasuka qara zubomata "New Layout" ta amsa ahankali "kudinki #250 ne" inji mai adaidaitan "muje" tafada tana qara share wasu hawayen dasuka qara gangarowa Sunqi tsayawa, kuma dama batayi qoqarin dakatar dasuba, bata damuba suyi ta zuba, suyi ta zuba bazata gaji da sharesu ba Zuciyarta ta cinkushe, a halin yanzu ita kanta batasan a yanayin da take ciki ba Farinciki ko baqinciki? Dadi? Haushi? Takaici? Batasaniba, batajin komai She's emotionless, batajin komai, dama ana haka? Qara share wasu da suka sake gangarowa tayi *Saboda ni ke sonki Zainab, nike sonki...* "Ya allah!" Tafada tana rufe fuskarta da taffukan hannunta tana shesheka Mai adaidaita yadan waigo ya kalleta jin kamar kuka take don sheshekar nata mai sauti ne Maida kallonshi yayi ga titi cikin zuciyarshi yana cewa "aifa! Ita wannan ko me tayi? Idan kaga yanmata na kuka to ta 6aci, sun sufka tsiyar. Allah ya kyauta, dama yan jami'a ai sai ahankali tunda har baraka ta iya haka ai kowama zai iya, allah ya kyauta" Itadai zee batasan yana yi ba don tayi nisa a kukan datake sai jitayi wayarta na ringing Bata dago ta duba ba har kiran farko ya katse, sai a kira na biyu ta dago ta duba wayar taga shine Bata daga ba kuma bata bar kallon wayar ba har ta tsinke Tana tsinkewa kira na uku yasake shigowa kuma still shine "madam kamar fa kira ake" inji mai adaidaita Ko kallonshi batayi ba bare ta nuna tajishi Kiran na katsewa ta danna power botton ta kashe wayar gabadaya ta jefata a jakka sannan takoma ta jingina da jikin kujerar ta lumshe idanu Tanajin yadda zuciyarta ke qara cinkushewa wuri guda. Da kwatancenta suka isa qofar tangamemen gate din gidansu Tsane fuskarta tayi ta ciro google dinta na cikin jakka ta kwama ma fuska sannan ta sauko #500 ta ciro miqaqa tabashi Shima kafin yayi yunqurin bata canji har tayi gaba "hajiya chanjin fa?" inji dan adaidaitan yana leqowa Hannu kawai ta daga mashi alamun yabarshi batareda ta juyoba ta qarasa gaban gate din tafara knocking "to angode, Allah yabiya!" inji mai adaidaitan cikin daga murya yadda zataji Ko nuna alamun taji batayi ba ta cigaba da knocking gate din wannan karon a dan fusace, Ganin bata kulashi ba yasa yaja yar napep dinshi yayi gaba Qaramar kofar jikin gate aka bude security ya leqo fuska a daure yana readyn yin bala'i amma ganinta yasa yadan wara ido sai yayi saurin ida bude kofar yana mata barka da dawowa Ko kallonshi batayi ba tazo ta shige "wai wanene naji kayi shir... " ganin Zainab ya sa bala kasa ida Maganarshi yayi saurin tashi tsaye "subhanallilah, madam? Sai naji kamar kince sai qarfe uku zanzo" inji bala yana rarraba idanu Ko iskar data deboshi bata kalla ba ta wucewarta ta nufi cikin gidan tanajin zatayi breaking down at any time, babu abinda takeso kamar ta fada kan gado ta jawo pillow ta rungume ta rintse idanunta gamm Security ya qaraso wajen bala dake tsaye yana bin zee datayi nisa da kallo "ya akayi to tadawo dakanta yau?" "wama yasani, ni wlh 3pm tace nadawo" inji bala "to qila kawai taga damar tahowa ne, tunda kaga bata cemaka komai ba ai saika share" inji security din yana komawa ya zauna Shima bala zaman yayi amma kana gani kasan jikinshi a sanyaye yake Luckily lokacin data shigo babu kowa a falon, dama tasan mawuyaci ne ta tararda mummy don dama tasan zata fita, zataje gidan wata qawarta Hajiya Kubra mai kayan qamshi, zatayiwa Feenah yan siyayya na kayan kamshi Sama ta haye tayi dakinta direct Tana shiga ta maido kofar ta rufe sannan tawuce wajen gadon da Tundazu take muradin ganinshi ta fada kanshi tajawo pillow ta rungumeshi qaqaam a qirjinta tana sauke numfashi ahankali *I.. Love.. You, Kiyi hqr amma that's it.. the truth* Qara rungume pillon tayi wasu hawayen nasake sauko mata *Na dade ina ajiye wannan kalmar a zuciyata* *na dade ina juriya wajen ganin na bar Hakan iya cikina..* *... But not anymore* Cusa fuskarta tayi cikin pillow *Nike sonki Zainab... Nike sonki* *I.. Love.. You* Kuka take sosai tanajin kamar ana melting din zuciyarta Bata ta6a tunanin haka zatayi reacting a irin wannan ranar A tunaninta duk ranar da Deen ya bude baki yace yana sonta yini zatayi rawar murna A tunaninta yini zatayi washe baki Amma saigashi Hakan ya faru, mafarkin data dade datayi ya faru, burin daya dade a zuciyarta ya cika Amma kuma ta rasa abinda zatayi sai kuka? Kuka? To kukan menene? Meya sata kuka, dadi? Dama wannan ake kira kukan dadi? Inkau shine yaci sunanshi kukan dadi Don kukan takeyi amma dadi yake mata, bata saniba ko kukan keda dadi ko dadi yasa kukan yayi dadi Kawai abinda tasani shine tanaso tayi kuka, tayi kuka har yazamo babu sauran hawayen zubarwa. *DEEN* Gajiya yayi da zaman library din ya tashi jiki a matuqar sanyaye Jiyake kamar an zuqe mashi dukkan lakkar dake jikinshi Inda ya yasar da wayar yaje ya tsinceta don har battery yayi nashi wajen, don ma allah yaso qaramar ce mai ran qarfe da faduwar datayi jiya da yau ya jawo mata matsala don jiya ma da ya wurgata har Saida wani wuri yadan 6alle Maida batteryn yayi ya rufe murfinta sannan ya kunnata Saida yabari ta kunnu sannan ya qara shiga call log ya sake danna kiranta Saidai yanzun ma amsar daya ce, switch off Saka wayar yayi a aljihunshi yafita daga library din Be nufi koina ba sai inda suka zauna dazu Littatafanshi daya bari wajen ya tattara ya rungume a qirji sannan ya nufo hanyar fita daga school din gabadaya yama manta dawani lecture dayake dashi Koda yafito titin qwal yake sai private cars dake wucewa jefi jefi Tafiya yafarayi ta gefen titi yana jin kanshi na wani irin saramashi Haka yaita tafiya kai a qasa batareda yaqara Dagowa da niyyar tsaida abin hawa ba dukda yanda suke Wucewa jifa jifa Saidai ko lura dasu beyi don yayi zurfi a tunani Yaci tafiya sosai sannan yaji ana mashi magana kamar daga sama Saurin dagowa yayi ya waigo sai yaga ashe dan express(aca6a) ne ke mashi magana "tafiya ne?" Sai lokacin ya tuna ashe abin hawa zai hau Kada mashi kai yayi yace "eh" "ok muje, ina ka nufa?" Zagayowa Deen da yakejin kanshi kamar zai tsage yayi yace "kofar kwaya bayan A.T.C" "dari da hamsin" inji dan express din Bece mashi komai na ya hau sannan yace "muje" Tada mashin din dan express din yayi yaja suka wuce A kofar gidansu aka saukeshi, saka hannu yayi a aljihu ya zaro kudi yaba mai express din #200 yabashi chanjin #50 sannan yaja mashin dinshi yaqara gaba Ahankali Deen yanufi kofar gidansu feeling very empty Da sallama yashiga gidan Saidai shiru, sake kutsawa yayi yana sake sallamar nanma babu amsa kuma yasan Hakan baya rasa nasaba da yadda Muryarshi take bare kuma yanzu taqara sanyi Qarasawa yayi bakin kofar kaka ya sake sallamar batareda ya shiga ba Kaka dake zaune kan sallaya bata dade da gama sallar zuhr ba ta dago "wslm, wa nake ji kamar kyakyawa na?" Bece komai ba sai shiga dakin dayayi looking so weak Kaka dake yunqurin tashi ta koma ganin ya shigo "kyakyawa na, kace Saida la'asar zaka dawo" tafada tana kallonshi Bece komai ba sai Qarasawa dayayi wajen ta ya kwanta ya dora kanshi a kan cinyarta ya lumshe idanu Gaban kaka yafadi ganin yadda yayi "Kamal lfy? Meke damunka wai?" Shiru "Kamal?" Bude idanu yadanyi sai kuma ya maida yarufe cikin sanyin murya yace "Kaka banida lfy, kibani magani" Hankalin kaka ne ya tashi, yau Deen ke neman magani? "Innallilahi waina ilaihi rajiun, bakada lfy meya sameka? Tashi muje asibiti, banga tazamaba ni ma'u, tashi tashi" Sake bude idanunshi dasukayi mashi nauyi yayi sai kuma ya maida ya lumshe yace "kaina ke ciwo, kibani magani nasha na kwanta zai daina" "A'a kyakyawa na katashi mutafi asibiti wannan abu bana zama bane, banga ta zama ba" Yiyayi kamar zaiyi kuka "nidai kaka kibani bakisan yadda nake ji bane, jinake kamar kan zai tsage" Jin Hakan yasa ta daga kanshi ta dora carefully akan pillon data jawo daga saman gadon qarfenta Sannan ta miqe tashiga neman magani acikin wata yar locker Fiddo maganin tayi sannan tayi sauri tafita ta debo ruwa tadawo wajenshi Dakyar tasamu ya tashi zaune jikinshi harya fara daukan zafi Maganin tabashi ya amsa ya watsa a baki yana danne yunqurin aman dake son tasomishi ya amshi kofin hannun kaka da sauri ya kora ruwan yasamu ya hadiye Dakyar Maida kanshi yayi saman filo yana sauke numfashi ahankali Kaka keta jeramashi sannu, jitake kamar taita kuka Dakyar ta lalla6ashi ya tashi ya koma kan gadonta ya kwanta sannan taja abin rufa ta rufeshi tana jin kamar taita kuka don tausayinshi Lamo yayi kan gadon ya lumshe idanu kamar mai barci amma ba barcin yakeyi ba Tunannika kala2 kawai ke zarya a kwalwarshi ga saran da kan kemashi yanajin kamar ya cire kan ya yar ya huta Yana nan Kwance kamar wanda dannau ya danneshi don kwata2 yakasa tashi don wata iriyar kasala ke nuqurqusarshi Jin kiran sallar la'asar ya fargar dashi zuhr din da beyi ba hakan yasa ya tashi Dakyar feeling so weak Kaka data shigo daidai lokacin tayi saurin qarasowa wajenshi "yaya? Me zakayi?" "sallah" yafada ahankali "to bari na zubamaka ruwa, kana iyayin alwala da ruwan sanyi ko a zazzafa?" Girgiza kai yayi sannan yace "ina iyawa" "to ka jirani ina zuwa" ficewa tayi don hada mashi ruwan Can sai gata ta dawo dakin tace yafito yayi alwalar Tashi ya sakeyi trying very hard to be stronger Fita yayi wajen yayi alwalar sannan ya shiga dakin kaka ya gabatar da zuhr lokacin har an kabbara asr Hakan yasa yafito ya nufi massalacin wanda ana iya jin sallarsu ma daga gidansu Deen din Koda ya isa massalacin har sun dago daga ruqu'i na raka'ar farko Niyyar bin Liman yayi yayi kabbara sannan yayi joining dinsu Koda suka sallame shi tashi yayi ya kawo nashi raqa'a dayan daya rasa sannan shima ya sallame Ya dade nan zaune yana addu'o'i sannan ya shafa a fuska Dan waiwaigawa massalacin yayi mutanen dake ciki yan tsiraru ne Ja gefe yayi ya jingina da bango yana sauke Ajiyar zuciya Jin zuciyarshi yake kamar wanda aka dauke wani dutse mai nauyi akanta Dukda fargabar dayake na rasata gabadaya Hakan be hanashi jin sallamar rabuwa da abinda kullum dashi yake kwana yake tashi dashi ba Furta mata abinda ya dade cinkushe a zuciyarshi ba qaramin sassauta mashi abinda yakeji a zuciyarshi yayi ba, he feel very relieve dukda acan qasan zuciyarshi tsoron rabuwa da ita yakeyi don yasan rabuwa daita daidai yake da rabuwa da farincikinshi Karkatawa yadanyi ya zaro wayar shi ya danja gefe ya jingina da bango Kunnata yayi yashiga call log yatsaya yana kallon number ta Lumshe idanu yayi ya bude sannan ya danna mata kira badon yasa ran zata shiga ba Jin tafara ringing yasa yadan wara idanu sannan ya kasa kunne yana jiran a daga Saidai harta yanke ba'a dagaba, qara bugawa yayi itama harta tsinke ba'a dagaba Hakan yasa ya maida akalar kiran zuwa sms Typing yafara *Zainab am so sorry.. Please pick my call.. Please* Ya tura Saida yadan jira na yan mintuna sannan yasake bugawa Saidai harta tsinke bata daga ba hakan yasa yasan ko me zaiyi bazata daga ba hakan yasa ya cigaba da text din *zăinab nasan yanzu haka ranki a 6ace yake kuma nasan ni naja amma please listen to me, I can explain* *yes abinda nafada dazu is nothing but the truth, Ina sonki zee, na dade ina dakon soyayyarki a zuciyata, na dade ina 6oyonta a zuciyata dukda wahalar dani datake, I know haushi kikeji yanzu haka da kike karantawa amma that's it, that's the truth* *nasan bankai matsayin inyi soyayya dake ba zee and that's why nake 6oyewa* *kullum qoqari nake wajen danne zuciyata akanki, kullum qoqarin controlling emotion dina nake akanki, kullum qoqarin pretending am ok nake while am not... Kinsan meyasa?* "meyasa?" inji zee dake karanta text din acan bangaren ta Ko minti daya ba'a qaraba wani text din yashigo *Because I don’t want to loose you* *banason narasaki a matsayin qawa agareni, banason ki juyamun baya, idan kikayi Hakan zan shiga matsanancin damuwa, it will break my heart more than your expectation* *please don't leave* *pretend as if Hakan be faru ba* *Kiyi pretending kamar ban fadamiki Hakan ba, please* *muci gaba da abotarmu kamar komai be faruba* *pleaseeee🙏* "shashasha aini abinda kafada din nakeso amma saboda kana maloho kaqi ganewa, mtcheew" tafada ita kadai cikin jin haushi Wai tayi pretending kamar bece komai ba, tayaya? Bayan abinda ta shafe lokaci mai tsawo kenan tana jira, mtcheew Kashe wayar tasakeyi don yafara bata haushi, wai maimakon ya cigaba da nacewa akan eh sonta yake no matter what amma wai shi burinshi ma ta manta da yafadi Hakan saboda wata banzar abota "Aboto! Nabi abota da gudu, idiot" Takoma ta jingina da frame din gado tareda lumshe idanu Sai kuma ta tuna yadda ya rikicemata jiya don ta ambaci wani da boy friend *damn it!* *Oh my God, For heaven's sake kibar kiranshi da haka* Wani kayattacen murmushi ya su6uce mata ta lumshe idanu ta sake budesu *I.. Love... You* Maganarshi tasake dawo mata Pillon kusada ita ta dauka ta rungume a qirjinta ta dora ha6arta akai tasake Lumshe idanu murmushi a fuskarta Cikin sanyin murya tafara waqa : _oh you what you did?_ _what you did to me?_ _it's a feel and it stole my heart away_ _mr deputy oh come to my aid_ _cos I don’t know how I got this way_ Wurgar da pillon tayi ta tashi tsaye kan gadon ta zare ribbon din kanta ta girgiza kanta gashinta duk suka barbaje ta cigaba da waqar tana rawa _the thing dey do me tininny🤩_ _this kind love is amazing 😍_ _boy you let me feel everyday like am abiding_ _I can't deny am feeling it💃_ _I wanna call you baby🥰_ _baby.. Butterfly🦋🦋_ _boy you give me butterfly🧚🏻‍♀️_ _you be thief.. I know sey you be thief oh💃_ _and you know sey.. You don steal my heart oh❤️_ _you be thief... I know sey you be thief oh💃_ _oh boy you get my.._ _you get my heart away... You be thief💃_ (waqar simi ~you be thief~) Murnar daya kamata tayi Tundazu takeyi yanzu Tsalle kawai take kan gadon tana wurwurga gashinta tako ina tana cigaba da waqar Jin zuciyarta take wasai babu kingin damuwa ko kadan saima farincikin daya maye gurbin damuwar Murnar datake hasaso ma kanta zatayi a irin wannan ranar saigashi tanayin finshi Saukowa tayi daga kan gadon tafara stripping kayanta still tana rawar waqar datakeyi Saida ya rage saura bra da pant sannan ta jawo towel ta daura ta nufi toilet still tana lalauyewa kamar macijiya, gashin kan nan yayi kaca duk sun zubomata a fuska Tana shiga ta cire towel din ta wurgar ta ida stripping sannan ta tsaya qasan shower ta sakarma kanta ruwa Runtse idanu tayi tana jin saukar ruwan bisa kanta Dago kanta tayi ta tara fuskarta a ruwan tana murmushi ruwan na dukkan fuskarta _*ina sonki zee*_ _*na dade ina dakon soyayyarki soyayyar a zuciyata*_ Qara fadada murmushinta tayi tana zaro halshe ruwan shower din na dukanshi Farinciki takeji kamar tayi hauka, bazata iya musalta yadda takeji ba don duk yadda zata musalta mai karatu bazai gane ba don gane irin wannan sai wanda ya ta6a tsintar kanshi a halin datake aciki Yayinda zee a bangarenta take celebrating shikuma Deen a bangarenshi yana can zuciya a cinkushe Ranar haka ya qarasa Wunin a sanyaye, da daddare ma haka ya kwanta yayi barci rabi da rabi sai yawan farkawa dayake yaga ko gari ya waye sai yaga still darene Daren ranar yazamo mashi Mafi tsayin dare don bemashi gudu kwata2, sai gab da asuba sannan barci na sosai da sosai ya daukeshi *WASHEGARI* Yau safkon zuwa school yayi da 8:00am dukda beda lecture ma kwata2 ranar Bayada burin daya wuce yaga zee yakuma san matsayinshi a wajen ta yanzu don da Hakan ya wuni jiya ya kwana Aikau yasha jira don zee bata shigo school din ba sai wajajen 12pm Yana zaune kan dakalin office dinnan dake facing din gate ya qurawa hanyar Shigowa ido kawai kamar a mafarki yaga shigowar motar ta Wani dadi ya ziyarci zuciyarshi har yana Sakin wani qayattacen murmushi Tashi tsaye yayi yana kallon motar data tsaya zuciyarshi na racing Bala yaga yafito ya zagayo side din da zee take sannan ya bude mata kofa Kafe ta inda zata fito Deen yayi ko kyaftawa babu Ahankali ta zuro kafarta dake sanye da farin takalmi mai dan tudu sannan gangar jikin suka biyo baya Lumshe idanu yayi ya bude akanta yana jin wani sabon shauqin sonta na huhhuda zuciyarshi takoina Sanye take cikin farar arabian gown mai adon stones masu walwali agaba ta yane kanta irinna larabawan nan, fuskarta tayi fess sai sheqin makeup take Rataya white side bag dinta tayi sannan ta sallami bala tafara tafiya Sosai Deen ya shagala da kallonta don sosai shigar fararen kayi ya hauta Ganin takusan qarasowa ta inda yake yasashi shima tahowa wajenta "Zainab.." Dan kallonshi tayi ta kauda kai ta cigaba da tafiyarta "Zainab please let me explain, please" "shiyasa nazo ai, but not here" tafada tana qara dan kallonshi sannan tayi gaba shima ya maramata baya Library ta nufa Hakan yasashi shima Binta kamar raqumi da akala Koda suka shiga shi yayi saurin jamata kujera don ta zauna Dan kallonshi tayi sai kuma tadan kauda kai tana dan murmushi sannan ta zauna shima yaja mai facing dinta ya zauna sai Wurin ya dauki shiru Ganin shirun yafara yawa gashi ita ko ajikinta don danne dannen waya takeyi ma hankalinta Kwance Hakan yasa ya hadiye wasu yawu sannan ya bude baki yace "Zainab, please let me explain everything to you" Sai a sannan ta dago ta kalleshi sai taga yanayin fargaba a tattare da fuskar, fargabar kar ya rasata, irin fargabar datasha shiga a kwanakin baya Murmushi tayi a zuciyarta tana cewa _sha kuruminka dan saurayina, ni takace kai kadai_ A zahiri kuma ta ajiye wayar ta koma jikin kujera ta rungume hannuwa a qirji tace "inaji" Ajiyar zuciya ya sauke saikuma ya rasa ta inda zai fara Saida yaqama kame kamenshi sannan ya fara cewa "Zainab, I don’t know when it started amma inaji ajikina a lokacin da na jefaki a chakwali ne" "bayan incident din sai mutane sukaita zuwa wajena suna yabona akan jefaki danayi a ta6o dukda kuwa ina gayamasu bada gangan bane amma sai suce su ai Hakan yayi musu daidai sunata maganganu marar dadi akanki" "da farko ban dauki abin wani serious ba Amma ganin yadda mutane ke tururuwar zuwa ganin wanda ya jefaki a ta6o yabani mammaki kuma duk wanda zaiso kalmar allah kara yake furtawa dakuma bayyana dadin da abin yayi musu Anan ne nafara tunani, nafara tunanin meyasa haka? Meyasa naga kamar duk basa sonki, kowa da kalar furucin da zaiyi akanki marar dadi, maimakon ayimiki jaje sai allah kara? Sai naji kin bani tausayi, sai kuma naji ba dadi kasancewar nine silar Hakan A ranar danaje na gayawa kaka saita cemun idan nazo school washegari nabaki hqr Da qudurin Hakan nazo school din amma bakizo ba Washegari ma haka, Washegari ma haka. Sai naji banji dadi ba da tunanin qila nine silar rashin zuwanki din Kwatsam ranar monday ina zaune ina karatu naganku kamar daga sama keda qawayenki Na tashi ina kallonki ganin yadda kike bina dawani irin kallo, duk sai naji badadi don nasan dole kiji haushi na Naso baki hqr a lokacin sainaga a matuqar fusace kike kuma kinqi bani damar magana sai tsawar da banso kike yimin Hakan yasa nafara gano dalilan dayasa mutane basa sonki, bakida kirki Qawayenki sunyimin barazanar ko nazama errand boy dinki ko kisa akamani wai kawunki commander sojane uncle dinki kuma commissioner of police A lokacin na yarda da Hakan ne ba don tsoro ba A'a sai don nabaki damar hucewa" "qawayenki dama ke kanki kunamin kallon psycho nikuma saina biku ahaka dukdon mu rabu lafiya A cikin kwanakin dakika maidani errand boy dinki da ida gano dalilan dayasa mutane basa sonki Ranar da kika watsamin coke kuma ya ida tabbatar min da bakida kirki Amma kuma saina kasa gayawa kaka ainahin abinda yafaru kawai nabar abin a matsayin tsautsayi nakuma yi alqawarin fita daga hanyarki gabadaya Saidai kuma a qasan zuciyata Koda yaushe kina fadomin a rai in dinga wondering ya kike, banji haushin abinda kika yimin ba a lokacin don ke kallon mahaukaci kikemin tayaya zaki yarda da abinda na rubuta? Saina maida laifin kaina saboda nasan da ban ta6a miki kayaba da duk Hakan be faru ba" "saina yanke shawarar fita harkarki kwata2 wanda Hakan yasa Koda nadawo school nabar zama mazauni na nafara zaman library, nayi kwana uku da dawowa, Kwatsam sai gaki kin shigo library din kema Naso intashi inbar wajen amma saina kasa sai naita kallon ki inajin wani feeling da bansan kona menene ba, inajin wata kewa taki wanda bansan dama inayi ba Sai kema kika dago idanu muka hada ido Hakan yasa gabana yafadi Sai naga kema kin kafeni da kallo Hakan yasani jin uneasiness saina tashi na fita Bansan kin biyoni ba sai gani nayi ansha gabana Gabana yasake faduwa saboda bansan dame kika zo dashi ba kuma a lokacin saboda nariga tayi entitled dinki a matsayin marar kirki Amma jin kina bani hqr yayi matuqar bani mammaki Ban ta6a zaton Hakan ba don nayi tunanin wata tijarar zakiyimin sai naga akasin haka, kika bani hqr kuma fuskarki ta nuna you're sorry din har cikin zuciyarki Sai naji kin burgeni, saina qaryata daya daga cikin magangganun da mutane keyi akanki, Girman kai. Saina qaryata Hakan don da kinada girman kai bazaki ta6a bani hqr ba Saina hqr muka zauna muka fara magana, a lokacin kuma saina lura you are so simple don dukda a lokacin bansan ko ke wacece ba na fahimci ke yar manya ce amma kuma kika saki jikinki dani Anan kika gayamin abinda ke tsakaninku da mr ibrahim Tun anan Naso na nuna miki kuskurenki na gaba da malami amma kuma saina fasa saboda ba lallai bane ki fahimceni Sainaji inason taimakonki a subject din don naga kamar kina fargabar faduwa sai nayi maki tayin Hakan kuma kika kar6a hannu bibbiyu, anan kuma naqara tabbatar da rashin girman kanki" "ahankali ahankali naita fuskantar halayenki wanda sai nakusa dake kawai zai san su saina fuskanci kyawawan halayenki sunfi marasa kyan yawa Daga baya kuma na fuskanci ashe rashin qawayen kirki yasa kike wasu abubbuwan ganin daga baki shawara akan gabarki da mr ibrahim kika nuna damuwarki kema akai kika kuma nuna kinason ku shirya, Hakan ya tabbatar min cewa eh daga qawayen ne don a dan lokacin damukayi tare naga kamar su babu ruwansu da karatu, they're not serious at all shiyasa nima na kawar da hankalinki daga kansu ta hanyar baki lokacina da gudunmawa gwargwadon ikona don ganin kinyi nasara" Dakatawa yayi ya dago yana kallonta yaga itama shi take kallo babu ko kyaftawa "Bansan sadda nafara sonki ba, abinda nasani shine kina burgeni amma bansan sadda Hakan ya rikide zuwa so ba. Na fuskanci Hakan ne a zamanmu na asibiti, a lokacin nasan na kamu da makauniyar sonki, a lokacin da aka sallamemu Sainaji kamar Kada a sallamemu kamar muyi ta zamanmu a asibitin muddin zaki dinga zuwa sau biyun nan ina ganin ki, ranar da aka sallamemu sosai jikina yayi sanyi, najini so empty kamar wanda kika tafi mashi da wani abu mai matuqar muhinmmanci...." Cigaba yayi da bata labarin yadda yayi missing dinta kamar yadda nakawo a last page har kawo ranar datazo gidansu da yadda beji dadin yanayin datazo dashi ba da kuma fasa niyyar amsar number ta dayayi, ya gangaro zuwa kiran dayasa kaka taita yiwa mummy don yaji muryarta har zuwa lokacin da akace tayi tafiya har zuwa lokacin resuming dinsu da abinda yafaru har zuwa kawo yanzu dasuke zaune. Shiru yadanyi saikuma ya saki Ajiyar zuciya "Zainab, am not begging love From you, nasan bazan ta6a samuba saboda bankai matsayin Hakan ba, Kiyi hqr naci amanar abota, kin riqeni a matsayin aboki nikuma na chanza tawa manufar gareki" "meyasa kake ganin bakakai matsayin ba?" inji zee karo na farko tunda suka zauna "saboda ta koina akwai banbanci atsakanina dake" "meye banbancin?" inji zee again "zee, ke diyar masu kudi ce, you're born with a sliver spoon in your mouth, nifa?" Dan murmushi tayi sai ta kada kai tace "bayan wannan fa?" Shiru yayi yana tunani saikuma yace "family, kinada families masu sonki sosai, nifa? Kaka ce kawai" "kakan ba family bace? Kaka kawai ce? Soyayyar kaka ba soyayya bace?" Shiru yayi yana kallonta Ajiyar zuciya ta sauke tace "tunda muka zauna nan kake fadamin dalilan dayasa kafara sona mun dauki kusan 30mins kana lissafosu dakuma bayyana yadda kakeji aranka game dani amma dakazo akan dalilan da zaisa ka haqura dani sai naga ko minti daya bakayi ba, hasalima duka dalilai ne guda biyu kacal, marassa tushe" Shiru yayi still yana kallonta batareda ya iya cewa komai ba "miye banbanci na dakai? Meye banbancin mai kudi da talaka, atsakaninmu mu yan Adam ke akwai banbanci amma a wajen Allah fa?" Girgiza kai yayi sannan ahankali yace "babu... Sai wanda yafi tsoron allah" Murmushi tayi sannan tace "families kuma, dama kasan wasu families dinane banida labari? A tunanina mummy da daddy kawai ka sani koko don kai bakadasu kake jin kamar bakadasu? Daga sama ka fado? Kaima dole kanada baba da mama kuma sun rasu, ba Haka kaceba? Yakuma za'ayi kace bakadasu? Ina kaka? Ita ba family bace? Ko bata kai matsayin a kirata da Hakan ba?" Shiru yayi nan ma yana jin zuciyarshi na wani iri "soyayya babu ruwanta da mai kudi, marar kudi, mai kyau, marar kyau, yare, qabila, addini... Babu ruwanta Makauniyace, marar dan jagora duk abinda tasamu kaimashi wafta take ta damqe gamm Mai so na asali bazaiyi fargaba akan banbancin komai ba tsakaninshi da abinda yake so zai soshi ne yakuma tsaya tsayin daka akan Hakan no matter what Amma tunda abotarmu ne bakason ya wargaje, fine mu tafi a Hakan, Abokai" tafada tana murmushi Saita fara yunqurin tashi, saurin rigarta tashi yayi yana cewa "yes, yes nagane, nagane Hakan Zainab, I was so stupid to think of that, a lokacin babu abinda nake hasasowa idan na tunkareki sai rabuwa, rabuwa na har abada kuma Hakan shine abu na qarshe da zanso yafaru damu because... I LOVE YOU" Dagowa tayi tana kallonshi "yes I love you, I love you! I love you!! Please give me a chance, give me a space no matter how tiny it is in your heart, please love me back, give me a chance... Please" Tunda yafara take kallonshi babu kyaftawa tanajin zuciyarta na kumburi don shauqi Kallon pleading face dinshi tayi data koma abin tausayi saita miqe ta dauki jakkarta da wayarta ta rataye jakkar Binta da kallo yayi tayi zuciyarshi na bugawa da qarfin gaske Dagowa tayi ta kalleshi taga shima ita yake kallo babu kyaftawa "idan ban baka space ba a zuciyar tawa fa?" "zan roqi kibani dama nayi jaraba kutsawa har nasamu nasarar yin Hakan watarana" yafada ahankali "idan nabaka kuma fa?" "zanfi kowa farinciki a duniya" yafada still yana kallonta zuciyarshi kuma bata bar bugu ba Wani kayattacen murmushi tayi sannan tace "Go ahead, kafi kowa farinciki a duniya" Saita juya ta nufi hanyar fita Dan yamutsa fuska yayi cikin rashin fahimta Yafi kowa farinciki kuma? Wani abu ya gifta mashi a qwalwa Yace zaifi kowa farinciki a duniya idan ta amince dashi Kuma tace yafi kowa farincikin Kenan? Ta amince? Dagowa yayi saurin yi saigani yayi harta fice "OMG! Ta amince! Ta amince!!!"... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:37 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *042* *DEEZEEN💞* Saurin tashi yayi ya fita Saidai ya waiga ta koina babu ita. Duba agogon hannunshi yayi sai yaga har 1pm ta dan gota kuma dama tanada lecture qarfe 1 Murmushi yayi ya saka hannu yana dan yamutsa gashin kanshi ya nufi hanyar department dinsu. Tun daga nesa ya hango alamun class din karatu ake amma dukda Hakan be hqr ba ya zagaya ta dayan side din class din yafara bin bango ahankali kamar wani qwararren dan F 😒 Koda yazo wajen window saiya leqo ta gefe ahankali yana scanning din iya inda yake iya hangowa amma be ga ko wulginta ba Hakan yasashi yin qasa ya rarrafa don kar aganshi ta window yawuce dayan windown sannan ya miqe ahankali ya jingina da bango yasake leqawa ahankali ta gefen windown Qara bin iya inda zai iya gani da ido amma be ganta ba Har zai qara gaba sai kuma yaga windown gaba ai na masu zama baya ne kuma ya tabbata Zainab bata zama baya Hakan yasa yaqara dan leqawa yana dan wurwurga idanu ta koina Saikau gashi ya ganta a row din tsakiya zaune Littafi kan desk dinta ta buga tagumi da hannu daya tana taunar gindin biron hannunta hankalinta akan lecturer din Murmushi ne ya su6uce mashi saiya qara gyara tsayuwa yana cigaba da leqenta Jin wannan feeling din tayi wanda takeji idan yana kallonta Saidai bata wani maida hankali akai ba don tasan bayanan Tunani tayi ko ya gane hausarta dazu? Sai kuma tayi murmushi tana cigaba da taunar biron hannunta, allah yasani yau tana cikin farinciki, farinciki marar musaltawa Kamar ance ta waigo ta windown gefen damarta sai taga kamar abu na leqowa yana komawa Hakan yasa ta kurawa wajen ido Shikuma ganin ta kallo wajen yasashi dan qara leqowa sosai yadda zata ganshi Wara idanu tayi ganin shine sai kuma tayi saurin kauda kai tana kallon lecturern dake koyar dasu Lallai ma Deen, baya tsoron ko aganshi ma? Tambayar da tayiwa kanta kenan Haka aka cigaba da lecture din rabin hankalinta akan lecturer rabi kuma akan Deen Duk lokacin da zata juyo ta kalloshi sai taga yamata murmushi ya daga mata hannu saita kauda kai kuma Ahaka har lecture din ya qare lecturern ya fita Ganin Hakan yasashi zagayowa da sauri shima don tarbonta Zee daketa sauri ta fito itama taci karo dashi a waje "har kun gama?" yafada yana qarasowa yana mata murmushi Murmushi kawai itama tayi mashi tana lura da yadda wasu ke kallonsu "kai zan tambaya, harka gama la6en?" tafada tana nufar hanyar fita Shima Binta yayi suka jera yana cewa "eh, amma fa nasha wuya, bayana ciwo" yafada yana 6ata rai Ta6e baki zee data kasa hada ido dashi tun dazu tayi tace "dakyau" "hakama zakice?" yafada yana marairaicewa Murmushi kawai tayi ta kauda kai, shi bemasan kunyarshi take jiba Tare suka nufi masjid don har ankusan kabbarawa Kowa nashi nashen yayi, basu dade da shiga ba aka tada iqama Kusan tare suka fito don Deen na fitowa itama tana fitowa Tare sukaje cafteria sukayi siyayyar abinda zasu dan ci kowa daidai aljihunshi sannan suka wuce usual Wurin zamansu idan basa library Zama sukayi Deen yafara bude masu ledar chips dinshi suka shiga ci tare Shiru wajen ya dauka na wani lokaci bakajin komai sai sanyayar iska dake kadawa sai kukan tsintsaye dake kai kawo Deen daga kai yayi yana kallon wasu balbelu dasuka zo suka wuce ta gabansu "look" yafada yana nuna mata da yatsa Bïñsu da kallo itama tayi "suna tayamu murna suma" yafada yana murmushi Itama saita tsinci kanta da murmusawa "the birds are also singing, suma suna tayamu murna... Kalli can" Bïñ inda ya nuna tayi da kallo sai taga yan moli moli ne guda biyu mace da namiji bisa kan wani reshen bishiya "A good example of us, right?" yafada yana kallonsu yana murmushi Itama su take kallo fuskarta dauke da murmushi, ahankali tace "so beautiful" "yes, love is beautiful and amazing" yafada sannan ya maido kallonshi akanta Hakan itama yasa ta juyo tana kallonshi shima "Nagode Zainab, Nagode da kika bani damar jan ragamar zuciyarki, I promised you bazaki ta6a danasaniba. Zan jagora agareki, jagora dazai jagoranceki zuwa duniyar farinciki, zan iya sadaukar da komai akanki zee na, komai" "promise" inji zee ahankali "promise you'll never let me down, no matter what" tafada tana kallonshi tanajin hawaye na neman taruwa a idanunta Kama hannunta yayi cikin nashi ya matse "nayi, nayi alqawari my zee, I'll never let you down insha allah don letting you down is equal to letting myself down, down to grave" " If I could chose between loving you and breathing I would use my last breathe to say I LOVE YOU." Sai kuma yayi interlocking din yatsunshi da nata ya dago hannun yana kallo Itama kallonsu tayi dukda tasan be dace ba Amma takasa hanashi Murmushi yayi ya kalleta, itama shi ta kalla not saying anything "yanzu nagane dalilin space dake a tsakanin yatsu na da naki Anyisu ne don yatsunmu su maye gurbinsu, kamar haka" yafada yana dan daga hannayen nasu Murmushi tayi sosai tanajin wani dadi na ratsa zuciyarta, Gaskiya soyayya dadi gareta musanmman kaso aka soka, wayyo dadi 😍 Zame yatsunta tayi daga nashi ta duqa zata dauki juice din gabanta Saurin riganta yayi ya dauko mata ya miqamata "ki dinga fadamin duk abinda kike so idan ina kusa, kibar wahalar da kanki, feel free wajen sakani komai, dama ni errand boy dinki ne" Murmushi tayi kawai ta amsa ta dan kur6a don harya bude mata Haka sukaita zama wajen Deen nata tarairayarta, wasu abubbuwan ma har mammaki yake bata don batasan ya sansu ba, a ganin ta babu abinda ya iya a faggen love, batasan yan shiru shiru dinnan akwai iya buga love🥰 Suna ahaka har drivernta yazo Saida ya rakota har motar, kafin bala yama zagayo shi ya bude mata kofa, babu abinda ya dameshi ko lura da kallon da daidaikun mutane ke masu beyi ba Shiga zee tayi ya sunkuya ya maida mata yar jelar rigarta da bata ida shigewa ba sannan ya rufo mata kofar ahankali Bala daya saki baki yana kallon ikon allah ya lalla6a yakoma cikin motar gulma fall ranshi Sunkuyowa yayi jikin glass din Hakan yasata wining din glass din qasa Murmushi suka yima juna "bye.. Ki kulamin da zuciyata" Murmushi tayi sannan tace "nima haka" "kema me?" Blushing tayi tana dauke kai tace "yadda kace" Murmushi yayi "to shikenan, qila maganar ke miki wuya amma na gane ai, zan kula miki daita sosai and please.. A taimaka a daga wayata yau.. Please" Kallonshi tayi taga yadda yawani marairaice Murmushi kawai tayi tafara wining din glass din motar sama tace "bye" "bye.. Godiya nake" Jin an tada motar yasa yadanja da baya yana kallonta dukda baya hangenta amma yasan itama shi take kallo Ganin xa'aja motar yasashi fara daga mata hannu yana murmushi har motar ta daga ta nufi hanyar gate Bebar daga hannun ba har Saida suka fita daga school din Ajiyar zuciya ya sauke yana jin zuciyarshi sakwat kamar an rabashi da wani mai nauyi aka, tabbas ya yarda zee ce farincikinshi kuma idan yana tareda ita zaiji dadi da sallamar zuciya da ruhi. Ajiyar zuciya itama zee tayi sai takoma jikin kujerar motar ta lafe tana murmushi, murmushin dayaqi barin fuskarta tun jiya Wani irin dadi takeji marar musaltawa, she can't believe yau ita Deen ke furtawa kalaman soyayya, she can't believe yanzu Deen natane Dama kenan shima yana sonta tuntuni shine baya gwadawa kwata2? Kai amma ya gama daita, duk wannan sleepless nights din da damuwa ashe wanda takeyi don shi shima tana can a ranshi? Dakau tasan da Hakan da ba zata ta6a damun kanta ba irin haka, amma nevertheless yanzu ma alhamdullilah, ta godewa allah daya kawomata abin da sauqi, dama wannan itace babbar matsalar wato kaso aqi sonka amma muddin soyayyar ta kowacce bangare ce to duk abinda zai biyo baya mai sauqi ne. Ahankali ta dago hannunta tana kallo _*yanzu nagane dalilin space dake tsakanin yatsu na da naki*_ _*anyisu ne don yatsunmu su maye gurbinsu, kamar haka*_ Murmushi tayi tareda runtse hannun ta lumshe idanunta cikin jindadi A bangaren Deen ma bata dade da tafiya ba shima yafito feeling himself on top of the world Be dade ba yasamu abin hawa suma suka shilla Koda ya dawo gida kaka tayi mammaki sosai ganin yadda kai kawo cikin nishadi, murmushi yaqi barin fuskarshi sa6anin dasafe daya fita kamar yayi kuka yana komai sumi sumi Koda ta tambayeshi lfy? Ko tsintuwa yayi? Sai yakama Dariya kawai yana cewa eh tsintuwa yayi, a zuciyarshi kuma yace *Tsintuwar soyayya ba* Haka wadannan bayin allahn suka qarasa Wunin su cikin nishadi da annushuwa kowanne Saida aka ganemashi a gida don fara'ar yau ta dabance 💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖 "wow! Wow!! Wow!! Dole na kwaso shokiii💃💃💃" inji saqon Feenah via whatsapp Dariya zee tayi afili sannan tayi typing "kai Aunty, yaushe kika zama motar yansanda?😆" "har tarakta ma ina iya zama, wayyo dadi 💃 amma na tayaki murna 🥰" Murmushi zee tayi sannan tace "thanks Aunty 😍" "shikenan kuka yaqare ko 😏" "dama wani ke kuka 🤨" "qaniyarki, shegiya kin manta lokacin da kike kuka hawaye da majina kina wlh Aunty idan be soni ba mutuwa zanyi😩 yar rainin hankali kawai 😒" "😳kai Aunty yaushe akayi haka? Wlh adai dinga tsoron allah 😫" "kyaji dashi... Yanzu shikenan harkin amince? Bawani jan aji ba komai?😒" "shi ajin wani kalan abinci ne 🙄" "😦 kinci bashi yarinya 😠" "babu komai na biya idan muka hadu😜 ina alarrama yaya Auwal?" "waya bashi muqamin alarramancin 😒" "ai basai anbashi ba, alarrama ne 😆 alarrama ango ba🤣🤣" "kutt! Ni tsarar wasanki ce 😬" "😝😝😝" "zaki gane bakida wayau ne 😠" "👏👏tuba nake uwata ta kaina" "zamu Hade ne zaki fadamin yaushe muka fara wasan jika da kaka dake 😠" "haba Aunty ta ta kaina, ai babu mai jin kanmu insha allah🥰" "😒😒ayi kema azo a aurar dake don naga wani tashen balaga kikeji kwanan nan" "can't wait 😁💃💃" "😳marar kunya?" "🙈🙈🙈😄" "😞Allah ya shirya" "Amin summa amin Aunty ta 😜" Kira taga ya shigo wayarta *D❤️* taga ansa Hakan yasata dan murmusawa Daidai nan message din Aunty Feenah yasake Shigowa "ai yanzu tunda hankali ya kwanta dole ki nunama kowa kin qoshi" Murmushi tayi sannan tayi saurin typing "eh babu komai😜, Saida safe" "tun yanzu?" "shine yakira🙈" "yar isss lamiya😒" Dariya tayi ta kashe datarta lokacin har kiran ya tsinke amman nan take wani kiran ya shigo Murmushi tayi Saida takusan tsinkewa sannan ta daga, saita tsinci kanta da kashe murya wajen yin sallama Wata nannauyar Ajiyar zuciya Deen ya sauke daga dayan bangaren sannan ya amsa sallamarta sannan ya dora da "nayi tunanin har kinyi barci wlh" Murmushi tayi "kamar kaza?" "who knows" Murmushi tayi ta janyo pillow qirjinta ta rungume tace "ina kaka ta?" "tayi barci nasan takai kaduna yanzu" Yar Dariya tayi tace "bakada kirki, a gaban aminiyar tata kake fadin haka?" "oh haka ne fa ashe ku aminan juna ne" "sosai ma" inji zee Murmushi taji yayi sannan yace "banida lfy, ko ki kira kiji ya nake" ga yanayin dayayi magana tasan kumbura fuska yayi Dan wara idanu tayi tace "bakada lfy? Meke damunka?" "kewa" Dan daga gira tayi sannan tace "kewa? Kewar wa?" "Kewar wa? Banda ke" Murmushi tayi "duka yaushe muka rabu" "duka yaushe ma zakice? Tunfa 3" "3 din, duka awa nawa?" "O'O! Kenan ni bakiyi missing dina ba" yafada a marairaice Yar siririyar Dariya tayi tace "nayi amma kadan" "babu komai, what matters shine kinyi, zan taimaka miki nazo school gobe dawuri don ki ganni kiji sanyi a ranki" yafada cikin sigar tsokana "wasa ma kenan, dani dakai wa zai ga wani yaji sanyi?" "dani dake" Sai sukayi Dariya atare Hira suka shiga yi mai cikeda nishadi da raha Sai gashi wasa wasa har sukafi mintuna talatin sai anan kudin Deen suka kare Bugamashi zee tayi ita kuma don Saida firar ta dauko sugar katinshi ya qare Sai gashi sune har 12 dare suna fira kwata2 sunma mance a wace duniyar suke kawai basa tunawa da kowa da komai sai kansu Tun zee na iya qoqarin bude idanunta idan suna rurrufewa alamun barci har barcin ya saceta batareda ta farga ba Jin saukar numfashinta yasashi sanin tayi barci Saidai kuma yaqi kashe wayar saima ya danna recording yana daukar saukar numfashi a zuciyarshi kuma yana hasasota tana barcin, yasan barci zai mata mugun kyau, zaiso ganinta idanunta Lumshe bata komai sai sauke numfashi ahankali, yasan sosai fuskarta zata qara Fiddo cuteness dinta Katse kiran yayi ba don ya gaji ba sai don tunawa dayayi kudinta ne ke qonewa a banza Koda ya katse kiran kasa barcin yayi sai juye juye yakeyi Firarsu yake sake yin bitarshi a zuciyarshi yana jin wani shauqin sonta na qara fizgar zuciyarshi Ahaka har shima barcin ya daukeshi batareda ya shirya ba. ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ Soyayya sukeyi tsaftattaciya wanda ya kunshi kulawa da tarairaya a kowanne bangare Zee bata bar soyayyar ta zama boring ba ta hanyar yin dunkum, itama tana nuna mashi kulawa da soyayya tsantsa dukda ba wai rawar kai takeyi ba, komai tana yinshi ne stylishly da kuma class. A school tun ana zargin soyayya suke har suka tabbatar da Hakan don a relationship dinsu babu batun wani 6oyo ko kunya, don wani lokacin ma zee ce ke dan jin kunya amma shi baya kunyar nuna mata kulawa a koma inane. Duk inda kaga daya to dayan na wajen except idan daya yashiga class yabar dayan Idan suna tafiya Deen ne ke Rataya jakkar zee ita kuma ta rungume littatafanshi Da farko daya fara amsa jakkarta hanawa take don cewa take tayaya zai daukar mata jakka kamar wata mijin Hajiya Amma nacinshi dakuma cewan dayake dama ai mijin hajiyan zai zama yasata dinga bashi itakuma saita amshi littatafanshi ta rungume A fannin waya kau ba dama Bata ta6a tunanin Deen ya iya waya ba sai a dan wannan lokacin don sa6anin da da idan sunyi gudun tsiya suyi wayar five minutes to yanzu wayar awanni suke kuma su rabu bawai don firar ta ishesu ba Deen ke fara bugowa sai sun cinye katinshi sannan ita ta bugo su ida wayar. A fannin text messages kau zee har tasan lokutan shigowar text dinshi a wayarta Idan ta farka da asuba da text dinshi take fara tozali, idan ranar akwai school kafin ta fito sai yayimata na fatan isowa lfy, idan kuma suka rabu daga school saiya daidaici sun isa gida zai mata na fatan sauka lfy, da daddare ma haka Itama tana yimashi Saidai ba kamar nashi ba barkatai, tana yimashi daya kowacce safiya, sai ranar juma'a kuma tayimashi na barka da juma'a bayan an taso daga sallar juma'a Zee bata yarda da yin dunkum ba a soyayya kamar yadda Mafi yawan yanmata keyi Idan be kira ba ita tana kiranshi, idan suna fira tana co-operating itama batayi mashi shiru Daga eh sai A'a sai hmm Tana Sakin jiki suyi labari na raha Saidai kuma tana matuqar kama kanta sosai wajen ganin bata bar wata 6araka tashigo a soyayyarsu ba Akwana a tashi saigashi bikin Feenah sai qara matsowa yake, kowanne bangare an shiga hidima ka'in da na'in Amarya sai shan gyara take ciki da bai taqara fitowa tass fess kamar ka wanke hannu kafin ka ta6ata Mummy da zee sai biki saura kwana hudu suka wuce Ruma Anan zee taita santin kyaun da Feenah tayi tana tsokanarta da itama wacce tayi mata gyaran zatamata itakuma saita hau masifar ta rainata ta maidata kakarta Bikin ba'ayi wani bidi'a ba sai dinner daza'ayi ranar daurin aure da daddare Washegarin ranar da suka isa zee da qawayen Feenah data shige cikinsu tsamo tsamo dukda duk sun girme mata suka wuce saloon Idan ka ganta cikinsu sai kayi zaton tsararraki ne don kusan babu mai girman jiki sosai cikinsu gashi ta iya mu'amalla da mutane musanmman yan gayu irinta shiyasa suma suka jiki sosai daita don tun a ganin farko yanayinta da gayunta yayi musu Daga saloon suka wuce shopping bags da shoes dazasuyi amfani dashi da yan abubbuwan da ba'a rasaba. Daga nan suka dawo gida Ranar daren biki kuma masu qunshi sukazo gidan inda aka yini ana yin qunshi, ita amarya dama mai qunshinta ta musanmman ce don ita kadai dama zatayi mawa Haka aka xauna a garejin gidan kasancewar yanada girma sosai aka baje anama amarya da qawayen amarya qunshi sai fira ake ana shewa na irin wayyayun mata Qawayen Feenah kau sai tsiya suke mata ganin yadda Auwal ya addabeta da kira, bini bini sai ya kira Hakan yasa wata qawarta ta amshe wayar daya sake bugowa cikin barkwanci tace allah idan yasake damunsu saisu fasa bashi amaryar su riqe abinsu Dariya yayi yana cewa tuba yake kanshi abisa wuya, idan suka hanashi ita ai Hakan daidai yake da hanashi numfashin shaqa, ya tuba bazai qara ba sannan yace to don Allah abata yaqara jin muryarta yayi alqawarin daga wannan bazai qara takura musu ba Dariya dik sukayi sannan qawar tata ta karama Feenah da duk ke jinsu wayar a kunne kasancewar hannunta duk qunshi ne Suka danyi magana wanda babu wanda yaji abinda suke cewa Saidai dariyar datake ahankali sannan sukayi sallama ya katse kiran Zee daga inda take zaune ana zana mata na qafa jaa take kallon dramarsu cikin burgewa Sai yanzu taqara gano hikimar Feenah na amincewa da Auwal don ko yanzu ka santa dashi to saika lura da tsananin so da kulawar dayake nunamata kuma tana ji ajikinta insha allah zata soshi don yana kyautata mata kuma zuciya kowacce iri ce tana tsananin qauna da ganin girman mai kyautata mata Hakan yasa ta tuna da Deen dinta, basu dade da gama waya ba yana complaining shi ta tafi tabar shi cikin kewarta tana mashi Dariya akan cewa ba gobe zaizo ba (dayake ta gayacceshi daurin aure, Aunty Feenah da kanta tabada katin I.v din abashi don tsakani da allah mutumin yayi mata kuma muddin kaji Feenah ta yabi abu to karka bincika abin yayi 💯) Dakyar tasamu sukayi sallama bayan ta fadamashi qunshi za'ayi mata Basu suka gama qunshin ba gabadaya sai can da marece liss kowanne sai santin nashi qunshin yake don ba qarya masu qunshin qwararru ne *WASHEGARI* Rana bata qarya... 💃 Yau su Hajiya Feenah za'a amarce Gida ya cika maqil ya cinkushe takoina, duk wanda zaka gani is very busy musanmman su mummy da matan kawunnan zee. Su Umma ana bedroom dinta an qame bisa gado tasha dakakkiyar shaddarta dataji aiki ajiki ga daurin dan kwalin da zee ta dotsana mata mai kyau, anci gayu ansha lalle tsohuwa ta fada kwata, kukau bikin auta guda? 😆 A bangaren Amarya kau tana dakinta dake cike da qawayenta da yanuwa yanmata Kowa sai shiri yake don an kusan daura auren Amarya ana gefen gado taci kwalliyarta itama cikin ankon bikinta, fuskar nan tasha makeup ga wani dauri mai shegen kyau da aka murzamata sai hasketa masu daukarta hotuna keyi da flasher. Zee ce tashigo dakin cikin hijab iya gwiwa sai daurin gaba datayi da zane aciki wanda ana iya hango zanen ta qasan hijab Fuskarta da hannayenta duk a jiqe suke da alama daga wanka tafito "wai ke ina kika shiga Tundazu kinbar waya anata kira?" inji wata cousin dinta Qarasowa tayi tana yamutsa fuska "wanka najeyi part din Aunty Raliya I can't use toilet din dakinnan" Harararta yarinyar tayi tana cewa "sannu tsafttatu, nidai dalla amshi abinki an wani cika mana kunne da kira" Itama Harararta tayi sannan ta amsa tana cewa "waye?" "saiki duba ai da kanki" inji yarinyar tana kauda kai ta maida gasu Feenah dake can suna dimi bama susan abinda suke ba *D❤️* tagani Murmushi tayi sannan ta juya tafita daga dakin saboda hayaniya ta zagaya can bayan gidan inda babu hayaniya sosai tayi dialing number Ringing biyu aka daga amma sai akayi shiru "Baiby.." tafada cikin sigar tsokana "babu wani nan, don't baby me mun 6ata" Dan wara idanu tayi murmushi a fuskarta "6atawa? Meyasa?" "kinsan kira nawa nayimiki?" "yakai dari?" ta Tambaya cikin sigar jan fada "Haka ma zakice?" Dariya kawai tayi "mun sake 6atawa, hang the phone banason yin wayar dake kuma" Dariya tasake yi tace "kai kayi hanging din mana" "ai ke kika kira ke ya kamata Kiyi hanging up" "then we die here" Dariya sukayi gabadaya "gist me, kun taho?" "yanzu muka gama Gaisawa da suruki na" "suruki kuma?" "yes, ashe zai iya ganeni? Rabonmu da juna tun hospital kafin a sallameni amma tsaf ya ganeni, muka gaisa amma naji kunya 🙈" "wow! Nufinka har kun qaraso?" tafada cikin doki "yes? Gashi nanma ana shirin daura aure" injishi "wow! Ashe dai kakar tabari" "zauna nan... Bari in katse gashinan za'a fara" "na bari... Tare zaka biyo su daddy ku dawo nan?" "tambaya ma kike? Me zan tsaya yi acan?" "tsayawa Wurin anguna" "meye kuma anguna? Dama shi ya kawoni? I came to see my missing princess" Zatayi magana ya sake katseta da "gashi nan za'a fara, bye.. See you" Kittt.. Ya katse kiran Ajiyar zuciya tayi tana rollling manyan idanunta sannan tayi hanyar cikin gidan da sauri don shiryawa Koda tashigo dakin saita tararda anama Feenah wani daurin dan kwalin don harta chanza kaya zuwa wani royal blue materials Bata tsaya wani kalle kalle ba tawuce bude wardrobe din Feenah taciro kayanta dake cikin leda tafice daga dakin again Part din Aunty Raliya taqara komawa don achan ne kadai babu mutane ta bude falon da makullin hannunta tashiga ta rufo Saida tafara gabatar da sallar xuhr don dama da alwalarta tafito wanka dazu Sannan itama tafara shiri shap2 don kar Deen yazo bata gama ba Angon bikin ne tasa Atamfa mai shegen kyau taji dinkin doguwar riga wanda yayi mata dass ajiki Sannan ta zauna ta tsara makeup dinta daya dace sosai da fuskarta sannan tafara daurin dan kwali Tana cikin daurin taji hayaniya daga waje sai kuma 6uda dake tashi a can cikin gidan Murmushi zee tayi ta cigaba da daurinta acikin zuciyarta tana masu addu'ar zama lafiya. Saida tagama ta tashi ta feffeshe jikinta da turare mai sanyin qamshi sannan ta yafa yalolon gyalenta stylishly a kafada Linke kayan data cire tayi ta zuba a leda ta ajiye dakin yara sannan tafito da sauri don hayaniyar gidan sai qara sama sama take. Rufe mata gidan tayi sannan tafito tana tafiyarta kamar yadda tasaba tana duba wayarta dake vibrating "Hajiya Zainab!" Taji an kira sunanta abaya Juyowa tayi sai taga wani cousin dinta ne ke kiranta Kauda kai tayi kawai bata amsa ba tana qoqarin sake dialing number Deen don shi yakira "haba Aunty zee, meya kawo fada babu gaba? Magana fa nake maki" "don kana min magana sai akace dole saina saurareka?" tafada tana qoqarin dialing number still tana cigaba da tafiya Saurin shan gabanta yayi yana cewa "tuba nake ranki ya dade, haba sisi nifa yayanki ne be kamata kina yarfani ba" Wani kallon ta makamashi na wasa tace "kaine yayan wa?" "yayanki, idan kina gardama muje mu tambayi mummy" "A'a daddy zamu tambaya ba mummy ba" tafada tana qara dialing number Deen don ba'a daga wancan kiran ba "eh muje a tambayeshi daddyn, zakiji abinda zaice. Yarinya bar ganinki haka kin wani zabge to har naman sunanki Saida naci wlh da wayau na aka haifeki" Sauke wayar tayi daga kunnenta ganin ba'a daga ba again sannan ta kalli cousin din nata tace "inyee, congratulations tunda kaci naman sunana sai kaje ka rattaba Hakan cikin littafin tarihinka Saidai ko me zakayi bazai chanza ni yayarka bace, haka kowama kecewa" tafada tana mashi gwalo "marassa hankali ba, don sun ganni da dan jiki? Su kalli fuskata dakyau zasu ga bata yau bace wlh, wadannan tamoji tamojin kadai ya ishesu amsa" Dariya tayi tace "ai alarrama anbar duba fuska yanzu, tsawo ake dubawa mallam don haka kazo mu taimaka mu sanmma tsawo" tafada tana mashi Dariya "Kutt.. Amma fa kin qoshi saura ki dora da juice, wato ni kike ma shairin tsawo ko?" yafada cikin jin haushi Juyawa tayi tafara tafiya tana cewa "niba sharri nayimaka ba, Gaski... " Maganarta ce ta maqale lokacin dasuka hada idanu dashi daga can jikin gini ya jingina da bango ya harde hannayenshi a qirji ya zubamata idanu... ✍️ Kuyi hqr jiya kunjini shiru, jiya bananan ne shiyasa ban samu zaman typing ba 👏 Ummin fasihu 8/2/21, 9:37 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *043* *THE PROPOSAL* Jitayi numfashinta yakusan daukewa saboda yadda ya tafi da imaninta Sanye yake cikin farar shadda riga da wando irin na samarin nan wanda zakaga rigar da kadan ta wuce gwiwa, anyiwa wuyan rigar siririn aiki da dark blue din zare a wuya dakuma tsakankanin qirji sai kuma saman aljihu Kanshi sanye da hular dara kalar aikin kayan sai takalmi farare sai usual agogonshi data sanshi dashi daure a hannunshi Karo na farko data fara ganinshi da manyan kaya kenan sai taji dama su yake sawa don sosai yafito acikinsu yayi wani irin breathtaking kyau "waye shi din?" taji muryar cousin din nata kamar daga sama Hakan yasa tayi saurin dawowa daga duniyar kallon Deen ta kalleshi sai kuma tasake kallon inda Deen yake "muje.. He's a friend" tafada tana wucewa Dan Jimm cousin din yayi sannan yabi bayanta suka nufi Deen din da haryanzu be Janye idanunshi ba daga kanta Qarasawa tayi gabanshi cikin murmushi, sai yaji kaso mai yawa cikin 6acin ran dayake ciki yabi iska "hey.. " tafada tana dan daga mashi yatsu Dagowa yayi daga jinginen dayake yana murmushi " hyy" "ashe kana nan, inata kiranka no response" tafada hankalinta Kwance "oops na manta ban fiddata daga silent bane, nasata a silent ne dazamu shiga masjid" yafada yana kallon cousin din zee da shima shi yake kallo kowa da irin expression dinshi a fuska Ganin wanda yake kallo yasa ta juya ga cousin dinta "Umar meet Deen.. Kamaldeen, a friend" Murmushi Umar yayi mashi dryly yana miqa mashi hannu Miqa mashi nashi Deen yayi shima suka shiga yin musabaha "Deen, this is Umar.. My cousin" Dan murmushi yayi na gefen baki sannan yace "ashe shine? The guy.. Nice to meet you" yafada yana yiwa Umar murmushi Shima dan murmushin yayi yace "you're welcome" Sai suka sauke hannunsu gabadaya Umar ne yajuya ya kalli zee datayi kamar wanda ruwa ya cinye don sarai tasan inda maganar Deen ta dosa "ok sisi, bari natafi, see you" inji Umar Dan murmushi zee tayi mashi tana cewa "yeah, see you" Besake kallon Deen ba yayi gaba ya barsu anan Binshi da kallo Deen yayi yana jin zuciyarshi na mashi zafi sannan yajuyo ya kalli zee Cikin basarwa zee tace "you're welcome to Ruma, so ya kaga garin?" "Amazing" yafada simply still yana kallonta Murmushi tayi tace "to muje ciki ku gaisa dasu mummy ko?" "is that necessary?" yafada still babu irin wannan walwalar tashi attatare dashi "yeah, ba kace kun gaisa da daddy ba? Bazata ji dadi ba idan taji kazo bakaje kuka gaisa ba" Kada kai yayi sai yace "muje to" Tare suka jera suka nufi cikin gidan Saidai babu mai magana acikinsu Zee ta lura fushi yake but he's trying wajen 6oye Hakan Ita Dariya ma yabata, ita wlh tama manta da wani batun cousin dinta data ta6a yimashi don dama qarya ce kawai don tabashi haushi lokacin yasa tafadi Hakan ashe shi be manta ba Da ta tuna Da ko introduction din ba zatayi ba Amma kuma a qasan zuciyarta dadi taji ganin yadda yake kishinta, tana son mutum mai kishin abinshi wanda beson wani abu ya ra6eshi ko yaya ne Hakan na daya daga signs of qauna. Wani wuri inda babu jama'a sosai suka tsaya "bari nayiwa mummyn magana" Kada mata kai kawai yayi ta juya ta wuce yabita da kallo Hannu yasa ya cire hular kanshi yadan yamutsa lallausan gashinshi sannan ya maida hular ya sake harde hannayenshi a qirji Ganinta da wani ya 6ata mashi mood sosai, kafin lokacin murna yake da doqin Ganinta amma kuma ganinta da wani har tana mashi Dariya yasa duka murnar komawa ciki yaji ya rage kuzari sosai Cigaba da jiranta yayi yana dan kalle kalle Can sai ya hangosu sun taho da mummy da zee dake dauke da sultan d'an Aunty Raliya. Ganin mummy yasa Deen qara gyara tsayuwa murmushi yana forming a fuskarshi Qarasowa su mummy sukayi, mummy na cewa "wai patient ne haka?" Cikin fara'a Murmushi Deen yayi har Saida dimple dinshi na gemu ya losta sannan ya tsugguna yana gaida mummy Sai mummy taji kanta yaqara girma "haba tashi mana kamal, yasu kaka?" Tashi yayi yana murmushi yace "Tana lfy lau mummy, tana gaidaku ma" yafada yana kasa hada ido daita Murmushi mummy tayi tace "Allah sarki, muna amsawa. Munyi rashin kirki bamu tura mata I.v ba" Murmushi kawai Deen yayi yarasa abinda zaice "to idan katashi tafiya ayimin magana please, bari nakoma na ida abinda nakeyi" inji mummy Dan russunawa Deen yayi yana cewa "to mummy, afito lfy" Murmushi kawai tayi ta juya ta tafi Saida yaga ta tafi sannan ya dago ya kalli zee dake kallonshi murmushi a fuskarta Hade rai yayi ya kauda kai gefe Dariya ne ya kufce mata ta rufe bakinta da tafin hannu tanayi, sultan din hannunta ganin tanayi sai shima ya kwaikwayeta ya rufe baki da hannu shima yana Dariya Hakan yasa Deen murmusawa sannan ya miqoma sultan din hannu Da gudu yatafi don dama shi beda kiwuya ko kadan, daka miqomashi hannu zai taho yana 6angale baki Amsarshi Deen yayi yana lakutarmashi hanci ya Hade goshinsu yana girgiza kai yana mashi Dariya shima sultan din na 6angalar Dariya Zee dake kallonsu cikin sha'awa takama murmushi acikin zuciyarta tana hasko Deen dauke da baby dinsu yana mashi/mata wasa Yatsa sultan yasa a kwarin gemunshi yana cigaba da Dariya Murmushi Deen yayi mashi yana jin qaunar yaron har cikin ranshi don shima allah ya yishi da mugun son yara ko don shima shi kadai ne? Dagowa yayi ya kalli zee dake kallonsu itama murmushi a fuskarta Harararta yadanyi sannan yasake kauda kai Murmushi tadanyi tana dan girgiza kai sannan tace "let's go" Dagowa yayi ya kalleta kamar zaiyi magana saikuma yafasa yabita suka fara tafiya sultan sai gwaranci yara yake mashi shikuma yana biyemashi Part din Aunty Raliya suka wuce, a balgony ta ajiye musu kujeru biyu farare sai tashiga ciki ta dauko daya daga stools dake gefe gefen kujerun Aunty Raliya ta fito Zuwa tayi zata ajiye yayi saurin amsar mata ya ajiye inda yaga zata ajiye yana wani qara hade cikakkun girarshi Murmushi tayi kawai. Daidai nan wata yarinya tashigo gidan bazata wuce yar shekara 13 ba, itama tasha ankonta na bikin Da sallama yarinyar tashigo hannunta dauke da tray an rufeshi da wani white clean sheet Amsawa sukayi gabadaya suna kallonta Gaidasu duk tayi suka amsa sannan tazo ta dora tray din bisa stool din zee na taimaka mata Miqama sultan dake bisa kafan Deen hannu yarinyar tayi Saurin lafewa yaron yayi ajikin Deen yana 6ata fuska Dariya Deen da yarinyar sukayi zee kuma tayi murmushi "shikenan, zamu hade ne, zaka gane ni kayiwa kiwuya" inji yarinyar tana Juyawa ta tafi Bayan fitarta zee ta yaye farin kyallen tray din saiga snacks da drinks sun bayyana Dago glass cups dake kife tayi ta bude drink din ta tsiyaya masu ta ajiye mashi nashi gabanshi ita kuma ta dauki nata tafara sipping ahankali Shiru ya biyo baya idan ka cire gwarancin sultan daketa yima Deen qiriniya akan qafa sai tumurmusa mashi shadda yake shikau Deen ko ajikinshi saima murmushin dayake mashi. Dagowa yayi ya kalli zee yaga drink dinta take sipping ahankali idonta akan waya "kinyi kyau" yafada ahankali Dagowa tayi daga wayar hannunta ta kalleshi taga still fuskarshi babu walwala kamar ma bashi yayi maganar ba "thanks, kaima haka" tafada tana qara kai kofin a baki "nima me?" yafada yana kallonta "yadda kace" tafada tana juya ido Dan murmushi yayi "ni ai Gaskiya nafada bawai nafada ne kawai don kiji dadi ba" "nikuma don kaji dadi na fada? Nima Gaskiya nafada" "haba dai, kina nufin nayi kyau?" Murmushi tadanyi mai sauti sannan ta Kada kai kawai Daga kafadu yayi yace "amma ai ban kaishi haduwa ba" yafada yana dan ta6e baki Dagowa tayi ta kalleshi "wa kenan?" "kin fini sani... *your man*" yafada yana qara ta6e baki Murmushi kawai tayi batace komai ba shikuma ba abinda yakeso ba kenan soyake tafadi wani abu dazai dan sanyaya mashi zuciya daga zafin kishin dayakeji a zuciya "shi ai naga har Dariya kike mashi nikau sai shan qamshi kike min" yasake fada yana kauda kai Dariya yabata sosai Hakan yasata yin murmushi mai sauti kawai batace komai ba, Hakan yasake quleshi "kuma wajen introducing dina wajenshi wai *my friend* amma shi kin iya kiranshi *my boyfriend*, adai dinga tsoron allah" yafada yana daukar cup din gabanshi a fusace yana sha Sauke kai qasa zee tayi tana Dariya marar sauti "ko banza nafishi tsawo, wani dunqul dashi" Dariyar zee ce tafito fili tashiga yi Babu kakkautawa Qara tamke fuska yayi ya kauda kai yana sipping din juice din cikin kofin "am smelling something here... Jealousy" tafada tana Dariya Harararta yayi "it's not funny" "it is, jealousy!" "babu komai, ai so ke kawo kishi amma ni na lura ma ni kadai ke haukana babu wani sona dakike" yafada yana kumburi Murmushi tayi tace "haka dai kace" "haka dai ne, ba gashi ba kina kula wani babu ruwanki da halin da zan shiga" yafada yana kauda kai don sosai abin yayi mashi zafi don dai shi ba gwanin fushi bane koma gwanin fushin ne bejin yana iya yimata "dan uwana ne fa" "kuma boy friend dinki ba" "wai wa ya gayamaka shine? Bashi bane wannan" "wato haryanzu akwai wancan din kenan kuma haryanzu boy friend din naki ne" "my goodness! Dama haka kake?" "nafi Hakan ma Indai akanki ne " yafada yana kauda kai Murmushi kawai tayi tace "nidai banida wani boy friend, inka yarda Amma" Saurin juyowa yayi ya kalleta ya marairaice "kice wlh, wlh bakiji yadda zuciyata ke zafi ba" Dariya tayi "wlh ba abin Dariya bane, wlh bakiji yadda naji ba danaga kina washe mashi baki" Dariya tasakeyi tace "he's only my cousin, sokake naita zare mashi idanu? Afterall me zanyi da guntu bayan inada iroko tree" Harya fara washe baki Amma jin tace iroko tree saiya tsuke fuska "nine iroko din?" Dariya tashiga yi tana rufe baki da hannu "tsawon iroko ai marar kyau ne, ni banaso" "to ai naga irin tsawon gareka?" "wa? Ni? God forbid, kinsan yadda iroko tree yake kuwa, siriri sai mugun tsawo? Allah ya kiyaye" Murmushi mai sauti kawai tayi "nidai don Allah ki fita harkar shi please, ba don ni ba please" yafada yana sake marairaicewa "ai na gayamaka, me zanyi da gajere?" "babu, wlh ko guntu ne ga hancinshi kamar gajeren wando, qofofin hancin kamar kofar durbi, with that tiny tiny eyes nashi kamar na yan china" Dariya sosai zee keyi ganin yadda ya daddage yana kushe bawan allah, imagining take da agabanshi yake fadin haka da kau sun kwashi yan kallo "Allah Gaskiya nake fadamiki, Is better you choose wisely karki za6i wanda zai saki haihuwar masu zubin emmanuella" Dariya tasakeyi tana girgiza kai "Allah Deen bakajin magana" "Gaskiya na fadamiki ai, ato" Murmushi tayi sannan ta nuna mashi snacks din da be ko ta6a ba "Sai kince kin daina kula kowa sannan" "dama ai ba kula kowa nake ba kaidai ke ganin haka Afterall da wane zuciyar zan so wani bayan ni kaina banida iko daita sai yadda akayi daita" tafada tana ta6e fuska Wani farinciki ya ratsa zuciyarshi nan take murmushi ya gauraye fuskar "dagaske?" Murmushi kawai tayi tasake turamashi snacks din gabanshi batareda tace komai ba Daukar daya daga cookies din gabanshi yayi ya dan gutsira still yana murmushi "thank you" yafada yana mata winking Kauda kai tayi tana murmushi kawai Cigaba sukayi da firarsu kamar babu abinda yafaru kowanne fuskarshi da annushuwa shikau sultan wasanshi kawai yakeyi abinshi Sosai Deen yaci snacks din don shi dama bejin kunyar cin abinci ko a ina ne, idan dai kaga yaqi Sakin jiki yaci abinci sosai to be yarda da tsaftar abincin bane shiyasa ko a school yafi mu'amala da snacks, biscuit, chips e.t.c Basu sake jimawa ba suka tashi don tafiya yace zaiyi don 4 saura kuma kaka tariga tayi warning dinshi akan kar yayi dare Tare suka qara jerowa Deen riqe da sultan dake barci a kafadarshi Duk inda suka bi sai anbisu da ido ana wondering waye wannan tareda zee A inda yajira dazu tayima mummy magana yasake tsayawa Amsar sultan din zee tayi Deen nacewa tabi ahankali kar taji ciwo don jiyake da yana iya shiga daya kai mata shi har cikin gidan Batace mashi komai ba tajuya ta wuce cikin gidan Can ba'a jima ba sosai yaga mummy da zee sun fito Sauke idanunshi yayi qasa yana dan murmushi har suka qaraso wajen "Kamal har zaku tafi?" Cikin girmamawa yace "eh mummy naga marecen yafara kuma kakata tace karna kai dare" "aikau dai babu kyau tafiyar dare, to bari na kira rabi'u yazo ya kaika" "laa mummy, da kin barshi zan dan biya kasuwa ne sannan na wuce tasha saina hau motar acan" "to basai ya biya dakai ba? Zai Mafi sauqi" Shiru yayi don besan abinda zaice kuma ba " ga wannan ka kaima kaka, kace ina gaidata" Nauyin ta dayakeji yasa ya amsa yana mata Godiya don yasan ko yaqiya saita tilastashi Cema zee tayi ta hada shi da rabi'un saiya wuce dashi sannan sukayi sallama mummy ta koma ciki Kallon juna sukayi sukayi murmushi sannan suka taho "muje ka gaisa da amarya?" Wara idanu yayi yace "No please, please mutafi mutane sunyi yawa Wurin" Daga kafadu tayi suka wuce Basu sha wahala ba sukaga rabi'u kuma dama mummy takirashi ta gayamashi so babu 6ata lokaci kawai suka wuce mota. "yaushe zaki dawo?" "Nan da just 1 week" Wara idanu yayi yace "one week! Lokacin na mutu da kewarki kenan" "daidai kenan" "nidai please yaushe zaki dawo kinga ga school you'll miss alot" "zan dawo very soon insha allah tunda ai anyi abinda ya kawomu sai yan ide iden da ba'a rasaba" Bude murfin gaba yayi amma be shiga ba yace "ok allah ya maidoku lfy and please, don Allah karki kula kowa, please" Murmushi tayi "insha allah" "inso samu ne ma karki je dinner nan" "saifa naje" "to kije but please karki kula kowa please" Rolling idanunta tayi tace "to" "promise?" "promise" Murmushi yayi mata sannan ya shiga motar yaja murfin ya rufo Ganin Hakan yasa rabi'u dake cikin mota Tundazu tada motar Dagama juna hannu suka shiga yi Alamu yayi mata da saisun yi waya ita kuma tayi murmushi kawai, rabi'u yaja suka fice daga gidan Ajiyar zuciya ta sauke bayan taga firarsu daga gidan sannan ta dawo ciki. Lokacin data sake komawa dakin da amarya take Saita iske Aunty Feenah ma bata ciki sai yanmatan amarya daketa maida yadda akayi wasu kuma nata sallar asr Ganinta yasa sukayi mata caa suna tambayarta waye suka ganta tare dashi Qin basu amsa tayi saima biyemasu datayi sunata chafta kafin daga baya ma ta baro masu dakin takoma can part din Aunty Raliyar tayi ta kauda abubbuwan dasukayi amfani dasu dazu ta dauro alwala itama ta gabatar da sallar asr Tana zaune bisa sallaya bayan tagama sallar ta Fiddo wayarta ta kunna tashiga gallery, tashiga wani folder nan take hotunan Deen cikin shigarshi ta dazu suka bayyana Murmushi tayi tafara binsu daya bayan daya tana kallo Dik aciki babu wanda ya nuna alamar yasan an daukeshi Duk yawancinsu hankalinshi nakan sultan dake hannunshi suna Dariya sosai Bïñ hotunan taitayi da kallo don ba qarya sun dauku dukda a sace akayi daukar kuma duk babu na banza aciki Murmushi tayi sannan tafita daga gallery din tashiga message tayi mashi short safe journey sms ta tura mashi sannan ta tashi ta fita *7:30pm* Gida fa ya hargitse duk inda kayi hayaniya ce kawai na mutane yan zuwa dinner. Duk wanda zaka gani cikin shigar anko din dinner zaka ganshi pink and blue Koina ya cakude motoci sai daukar mutane suke zuwa dinner Can na hango zee tafito tana zuge wata guntuwar jakkarta mai shape din heart pink colour, itama taci adonta cikin doguwar rigarta ta anko din gyalenta a sagale da hannu, kan nan yasha daurin head. Saurin qarasawa jikin wata mota tayi don dama ita kadai suke jira ta bude back seat tana basu hqrin bata masu lokacin datayi ta shiga ta zauna sannan ta rufo, nan da nan aka tada motar suma sukabi ayarin motocin dake fita daga gidan zuwa dinner Dinner tayi dinner, ansha shagali sosai a dinner ba qarya inda amarya da ango suka fito suka zama taurari acikin tarin al'umman wajen. Zee kau samari ne suka yimata caa kowa burinshi yasamu shiga amma kamar yadda tayiwa Deen alqawari babu wanda ta kula acikinsu haka sukayi suka gaji suka barta Ba'a wani dade sosai ba a dinner don 10:00pm nayi aka tashi, motoci suka shiga jigilar mutane zuwa gida Itama amarya gida aka maidota badon ran Auwal yaso ba don shi da so samune abashi amaryar shi a lokacin suyi tafiyarsu amma ya ya iya dole ya hqr tunda da yau da gobe duk daya ne. Washegari ranar kai amarya dakinta Sai wajajen 5pm motocin daukar amarya suka iso Saiga amarya daketa cika bakin ba zatayi kuka ba da kuka sha6e sha6e, dakyar aka 6an6areta daga jikin Umma dake hawaye itama aka fita daita su kawunnanta sukayi mata fada sannan aka shiga daita mota Su zee dama an riga an shishige mota fitowar amarya kawai ake jira Ajere motocin suka fita suka wuce gidan amarya. Masha allah, gidan amarya yayi kyau sosai, ba wani babban gida bane sosai amma an tsarashi gwanin burgewa ga jeren Aunty Feenah ya mugun dacewa da sanfarin gidan Hakan yasa gidan yaqara badawa Saida su zee suka gama zagayen gida suna santi sannan tabi su Aunty Raliya suka dawo gida duk kuwa da yadda Feenah tayi tayi daita tabari sutaho da qawayenta dake jiran zuwan ango amma taqi, tabi su Aunty Raliya tana Dariyar Feenah dake cewa zasu Hade ne zatasan ita tayiwa rashin mutunci. To amarya fatan mu dai allah yabada zaman lfy yakawo dattin daki. Saida su zee suka qara kwana biyu a garin sannan suka dawo gida. Zokaga murna wajen Deen don dama duk lokacin da sukayi waya sai yayi mata complain din ta tafi ta barshi cikin kewa. Dawowar zee yasake bude wani fage na soyayyarsu da Deen Soyayya suke nunama juna tsantsarta suna jin idan babu daya daga cikinsu dayan bazai iya rayuwa ba. Ana haka suka shiga watan masoya wato february na watan bature inda aciki ke akwai ranar masoya wato VALENTINE DAY Tunda aka shiga watan kowanne masoya suka shiga tanadi wa wannan ranar ciki hardasu Deen, wadanda basu ta6a celebrating din ranar ba sai a wannan karon. Kowa shirye shirye yake wa ranar suna looking forward to ranar cikin doqi. *14th FEBRUARY 20...* Yau takama ranar laraba, ranar da duk wasu masoya ke dakon zuwanta. Ranar da kowanne keson gwadama masoyiyarshi ko masoyinta matsayinshi ko matsayinta a zuciyarsu. Hakan take a wajen su Deen ma Zaune suke a usual Wurin zamansu dake very quiet sai tsuntsayen daketa kai kawo a wajen Zaune suke suna facing din juna kowanne sanye cikin kaya jaa da fari Zee na sanye cikin wata english gown A shape wanda akayi slashing */* gaba rigar, bangaren dama kalar fari na haggu kuma jaa sai gyalen data yafa a kanta fari, takalmi ma Hakan. Shikuma Deen sanye yake da farin jeans trouser ya dora top jaa takalmi ma jaa Sosai sukayi kyau acikin wannan shigar kamar ka sacesu Zaune suke sun jejjera kwalaben drinks a gabansu sai cards na kalaman soyayya da suka mimmiqar dasu tsaye a gefe gefen kwalaben sai wani kwalin chocolate da chocolate candy ke aciki duk qananu masu shape din heart suna dauka da daddaya suna ci suna fira suna Dariya cikin nishadi. Kallo daya zaka masu kagane suna cikin farinciki sosai, farincikin da zasuso dawwama aciki har abada. Ana haka, Deen ya dago ya kalli zee dake sipping din drink din hannunta. Ganin ya kafeta da idanu yasata ajiye kofin hannunta itama tana kallonshi murmushi a fuskarta "Zainab, you're the best thing that ever happened to my life, shigowarki rayuwata tasa ta dad'a kyawun kammani, jinake kamar mu kasance ahaka har abada, daga ni saike sai tsuntsayennan, zaune haka muna kallon juna, har abada" Murmushi zee tayi sannan tace "kai fitila ne, aguna. Na dade ina tunanin dalilin dayasa burina na karatu awaje be cikaba, ina wondering meyasa qaddara takawoni nan ba inda zuciyata ke muradi ba. Ashe haske ne, wani haske ne dake qoqarin haskaka mani rayuwata ya hana faruwar Hakan, kuma ba kowa ne wannan hasken ba face kai Ka haskaka mani rayuwata, ka cetoni daga halaka, ka taimaka wajen bidani hanya miqaqiya, ka nusar dani meye soyayya ta Gaskiya and finally I was glad mummy ta hanani fita waje karatu don data barni da banyi gamo da wannan hasken ba, da haryanzu ina cikin duhu ina lalube" Murmushi Deen yayi sosai wanda ya lotsar mashi da dimple dinshi "inasonki Zainab, yanzu, da'iman abadan" "nima ina sonka, ada, Ayanzu, da'iman, abadan, abada" Dariya sukayi tare cikin jindadi suna jin wani irin farinciki na huda zuciyarsu "one minute" inji Deen Saiya karkata ya zaro wani dan qaramin red box dake cikin aljihunshi Dagowa yayi ya kalleta yaga itama shi take kallo Murmushi yayi mata sai taga ya tashi tsaye sannan yayi mata alamar itama ta tashi Tashi itama tayi ahankali tana jin yadda zuciyarta ke bugawa sosai Ahankali taga yafara rage tsayi har yakai kan gwiyagunshi Runtse idanunta tayi gam tanajin wasu irin emotions na building a zuciyarta "will you marry me?" taji muryashi tace haka a tausashe Bude idanunta tayi ta kalleshi still on his knees, box din abude tana hango kyakyawan zoben ciki. Sake kallonshi tayi takasa cewa komai sai hawayen dake forming a idanunta Ahankali ya ciro zoben dake cikin box din sannan ya dago yana kallonta "marry me, please" Yanayin yadda yafadi a marairaice yasata yin Dariya hawaye na saukowa a idanunta ta miqamashi hannunta ahankali tana share hawayen dasuka sauko mata still murmushi a fuskarta Ahankali ya tallabo tafin hannunta cikin nashi sannan ya zuramata zoben a yatsarta na biyun qarshe Jitayi qaffafuwanta bazasu iya daukarta ba Hakan yasata xamowa itama tayi kneeling ta rufe fuskarta da taffukan hannunta tana shesheka ahankali Shima kallonta yakeyi yanajin zuciyarshi na raunana, yanajin kamar ya rungumota a qirjinshi ko zaiji sauqin abinda zuciyarshi ke mashi Haka kawai su biyu kejin kamar wannan shine happy moment dinsu na qarshe, dalilin da yasa zuciyoyinsu ke basu Hakan ne basu saniba "I love you" yayi maganar kusan cikin rada Dago fuskarta tayi daga tafukan hannunta ta kalleshi da bloodshot idanunta "please don't leave me, no matter what" itama tafada cikin karyewar zuciya "never, I will never" yafada yana jin kamar shima yayi hawayen, idanunshi shima sun Kada Share hawayen fuskarta tayi sannan ta jawo jakkarta ta bude taciro wani box itama jaa Saidai yafi na Deen girma Dagowa tayi ta kalleshi taga shima ita yake kallo Murmushi tayi mashi daidai saukar wani hawayen saikuma tayi saurin sharewa da bayan hannu sannan ta bude box din carefully Dagowa tayi taga shima kallon abinda ke cikin box din yake sannan ya dago ya kalleta Bands ne guda biyu aciki jere jajjaye, daga tsakiyar band din akwai wani heart shaped bud Ahankali ta cirosu tana nuna mashi murmushi a fuskarta Kallonsu yayi sannan ya kalleta shima murmushi na forming a fuskarshi Ajiye daya tayi ta riqe daya ta lalubi wani botton ajikin bud din band din nan take tsakiyar band din take kamar fuskar agogon hannu yashiga bada wuta yana bada rubutun _*Deezeen*_ Idan kuma ya dauke yasake dawowa sai yabada _*together forever*_ "wow!" Deen yayi exclaiming yana kallon band din cikin sha'awa Nuni tayi mashi ya miqo hannunshi Miqawa yayi yana murmushi Ahankali ta daura mashi a wrist dinshi saigashi yayi mashi d'ass a hannu gwanin kyau Shima duqawa yayi ya dauko dayan dayan ta miqamashi hannunta itama ya daura mata ahankali Murmushi sukayi ma juna sannan suka jera hannayen nasu mai band din kusada juna suka danna dan qaramin botton din nan take haske yakawo da rubutun _*DEEZEEN 💞*_ Da _*TOGETHER FOREVER❤️*_ .... ✍️ UMMIN FASIHU 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:38 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *044* *ASAAD* Kwance take kan gado ruff da ciki kaffafunta asama tana dan wasa dasu Ring din yatsarta ta qurama ido wanda yawancin lokuta irin haka idan tana zaune bata komai saita tisa zoben agaba tana kallo tana jin wani shauqi na musanmman na tasomata Kwantar da kanta tayi akan filo tayi lamo tareda qure waje guda da ido ita kadai tasan abinda ke kai kawo a kwakwalwarta Knocking da akayi a kofa ya dawo daita daga guntun tunaninta. Kallon kofar tayi sannan ta miqe zaune "yes?" Turo kofar akayi aka shigo sai taga ashe mummy ce Sauko da kaffafunta tayi qasa tana cewa "mummy?" "ki shirya kinyi baqo yana falon baqi" inji mummy Dan daga girarenta zee tayi tace "baqo kuma?" "eh, Kiyi maza karki 6atawa mutane lokaci " inji mummy tana Juyawa zata tafi Binta da kallo zee tayi harta fita tana wondering wane irin baqo kuma da daren nan Duba agogon bangon dakin tayi taga 8:30pm sai kuma ta tashi don yin yadda mummy tace After dress baqa kawai ta dora kan kayan jikinta ta yafa gyale sannan tadan gyara fuskarta tayi spraying turare a jikinta sannan ta dauki wayarta ta fita A qasa ta tarar da mummy "yauwa dauki wadannan kitafi dasu" inji mummy tana nuna wani tray dake kan centre table din falon Tsayawa zee tayi tana kallon tray din dake dauke da kayan motsa baki cikin mammaki "ko bakiji ba" inji mummy tana hade rai Wucewa zee tayi wajen tray din not saying anything ta dauki tray din ta nufi hanyar fita "behave yourself ok? Karki saki ki 6atamin rai" taji mummy na fadin Hakan a bayanta "to" kawai tace ta ida ficewa tana jin wani haushi a zuciyarta Ko ba'a fadamata ba tasan wani ne yazo wurinta don dama ansaba hakan donma sundan ja baya yan kwanakinnan saboda bata kulasu ko sunzo din, da kenan da batada Deen bare yanzu. Ta6e baki tayi ta qarasa guest room din tayi knocking ahankali sannan ta tura kofar tana sallama Ahankali taji an amsa cikin masculine voice Qarasa Shigowa falon tayi batareda ta kalli gefen da mutumin ke zaune ba ta qarasa centre table din dakin ta ajiye tray din sannan ta nemi kujera dan nesa dashi ta zauna Sai a sannan ta dago tadan kalleshi sama sama ta kauda kai "Sannu" tafada ahankali tana gyara zamanta Sai a lokacin shima gayen ya Janye idanunshi daga kan wayar hannunshi ya kalleta itama sama2 ya kauda kai yana cewa "sannu" Wani abu taji ya tsayamata a maqoshi amma saita hadiye ta koma itama ta jingina da kujerarta tafara latse latse a wayarta Shiru dakin yasake dauka banda qarar a.c babu abinda ke tashi dakin Sun kusan minti 20 ahakan wayar zee tafara ringing cikin low tone Ko bata duba ba tasan ko wanene don dama shi kadai keda wannan ringing tone din Dan murmushi tayi Saida takusan katsewa sannan ta daga ta kara akunne "Ranki ya dade" taji cool voice din Deen na fadin Hakan tacikin wayar Murmushi tayi sannan tace "tareda naka" Shima murmushin taji yayi yace "barka da daren juma'a" "barkanmu dai, where is my kaka?" "Your kaka tana dakinta Dakyar nasamu na faki idonta nafito" Dan wara manyan idanunta tayi "kafito? Katafi ina?" "ina kofar gidanmu, inason jin muryarki ne kuma dataga na shiga daki zata biyoni taga ko menene so I decided gwara na gudo waje" Dariya zee tayi ahankali tace "kai ko? Allah yasa ta leqo ta ganka wajen to" "babu ko wuya Indai kaka ce, ni wlh nagaji yakamata ta dinga kyaleni Hakan tunda na girma amma kullum cikin samin ido take kamar qaramin yaro" ya qarashe a dayan bangaren yana kumbura fuska Dariya tasakeyi ahankali sannan tace "wulaqanci? Yanzu kaka kake cewa tana samaka ido?" "to, ai Gaskiya ne, am very sure da cikin gida nake da yanzu tabiyo sahu tana _kyakyawana? Lfy ka qunqume daki?_" yafada yana kwaikwayon maganar kaka Rufe bakinta zee tayi tana Dariya ahankali sannan tace "ka qaddara kayi a gabanta, takanas zanzo gidan na fadamata" Shima dariyar yayi yace "dakau kin ja ta zaneni radam" Wara idanu tayi "dagaske? Tana iya dukanka?" "sosai ma, ai haryanzu kallon dan 5yrs takemin, tsaf zata zaneni nikuma naita kuka 😭" ya qarashe maganar da muryar kuka Murmushi mai sauti tayi tace "nikuma naita Dariya ba? ina maka waqar mai kukan banza" Kumbura fuska yayi "hakama zakice?" "eh mana, bayan haka ba har videoing dinka zanyi na dora a social media with caption *crying kaka's boy*" Sake hada gira yayi "ashe dai bakya sona" "Sai yanzu ka sani?" "sadly yes" Murmushi tayi "am glad yanzu kasani" "hmm marar M... Wai kinsan wani abu?" "A'a saika fada" "dazu nayi composing wata waqa, bakijita ba, very muah!" Yafada cikin doqi Dariya marar sauti tayi "har kasan tayi dadi?" "bani nayita ba?" "don kai kayita ai bakai zaka yabeta ba sai kabari wadanda suka jita su yabeta" "to ai shiyasa zanyimiki kijita" "to shikenan, ina saurare" Gyaran murya taji yashiga yi Hakan yasata fara Dariya marar sauti, kamar kau yasani sai yace "to ai ina iya farawa kuma kiyita yimin Dariya" Dariyarta ce tafito fili "hmm there you go" inji Deen yana hada rai "ni Dariya nayi, bafa Dariya nayi ba" "ba Dariya ba kikayi? Ni kurma ne?" "to sorry, inaji" Jitayi yaqara gyaran murya ita kuma taqara kasa kunne murmushi a fuskarta "to ai kuma kina iya cewa baitin is so long" "ni yaushe nacema zance Hakan?" "na sani ne ai, kina iya kushemin abuna duk yadda nakeji daita kau" Dariya tasakeyi sai taga kamar inuwa inuwa a gabanta Hakan yasata dago idanu sai taga mutumin ne ya miqe tsaye Dan wara idanu tayi don ita harga allah ma ta manta da akwai wani a dakin Ganin zaiyi magana yasata saurin cewa Deen "excuse me Deen, I'll call you later" tafada tana katse kiran batareda ta tsaya jin Amsarshi ba Saurayin dake kan wuya akan wulaqancin datayi mashi yace "zan tafi, thanks" "thanks too, agaida gida" Kada kai yayi kawai yana cizon lower lip dinshi sannan yafita a fusace leaving the door open Binshi da kallo tayi harya fita sannan ta sauke Ajiyar zuciya tana rolling idanunta sannan itama ta tashi ta nufi tray data ajiye wanda ko ta6ashi ba'ayi ba ta dauke tana ta6e baki tafito ta maido kofar ta rufe. Luckily bata tarda mummy falon ba hakan yasa tawuce da tray din kitchen taba daya daga cikin maids din ciki tafito Tana fitowa taci karo da mummy dake sakkowa daga stairs Hakan yasa gabanta yadan fadi "harya tafi?" inji mummy tana kafeta da idanu "eh, yatafi yanzu yanzunnan" inji zee tana rarraba idanu kamar marar gaskiya Mummy bata sake cewa komai ba tazo ta wuce ta tashige kitchen Hakan yasa zee sauke Ajiyar zuciya sannan itama ta nufi sama Saida tagama shirin barcinta sannan ta haye gado bayan ta qure a.c din dakin Wayarta ta dauka ta lalubo number Deen takira kamar yadda tace mashi Kamar kau jira yake a ringing na biyu ya dauka yana sallama Lumshe idanu tayi ahankali ta bude sannan ta gyara kwanciyarta tana amsa sallamar ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ Dagowa daddy yayi yana kallon zee data zauna yanzu murmushi a fuskarta. "daughter ta" yafada shima yana mata murmushi "na'am daddy na" tafada cikin shagwa6a "ya weekend?" "alhamdullilah daddy na" tafada tana murmushi "kinsan abinda yasa nayi kiranki?" "A'a daddy" Gyara zama daddy yayi Yayinda mummy haryanzu bata dago ta qara kallonta ba Tun amsa gaisuwarta datayi, ita gani ma tayi kamar fushi take "jiya wani yazo wurinki ko?" Jimm zee tadanyi fara'ar fuskarta na dan tafiya "eh daddy" tafada ahankali "masha allah, ya fadamaki ko wanene?" inji daddy again Shiru tadanyi sai kuma ta girgiza kai ahankali "To sunanshi ASAAD, d'a ga babban aminina kuma abokin kasuwancina Alhaji Abubakar" Dagowa tayi ahankali ta kalli daddy, ita sai yanzu ma ta tuna Da maganar data ta6a ji daddy nayi da mummy akan d'an Alhaji Abubakar din No wonder, dama tasansu tasan halinsu na jin kai, shiyasa ma jiya qila yafara daddaga mata kai besan idan dagin kai ne gidanshi ne yazo. "yau da safe ya kirani yana gayamin abinda yafaru a tsakaninku, banji dadi ba Amma kuma laifina ne da ban sanar dake zuwanshi ba dakuma gayamaki ko shi waye, I think duk Hakan yajawo matsalar tun farko. Shiyasa nace bari na kiraki nayimiki bayanin komai dalla dalla yadda zaki fahimta" Shiru dakin ya dauka babu mai cewa komai Hakan yasa daddy cigaba da cewa "kamar yadda na fadamaki sunanshi Asad, First born din Alhaji Abubakar. Yaro ne haziqi don Yanzu haka yagama masters dinshi ne a qasar india ko sati biyu beyi da dawowa ba kuma insha allah next week zai fara aiki a daya daga cikin manyan companies din babbanshi a matsayin mai jagorantar kamfanin Asad yana da komai da kikeso bama ke kadai komai da kowacce mace zata so shiyasa nama fara tunkararki da wannan maganar Bayan haka kuma faruwar Hakan zai qara qulluwar zumincinmu dake tsakanina da Alhaji Abubakar kuma zamu qara girma da qima a idanun juna Nasan jiya rashin sani ne yasa kika qi kulashi Hakan ma nagayama Alhaji Abubakar din amma zai qara dawowa yau sai ku fuskanci juna dakyau" Shiru dakin yasake dauka zee bata dagoba kuma ba tace komai ba "baki ce komai ba dear" Sai a sannan ta dago ta kalleshi sannan tace "Dad... I think basai yasake dawowa ba" Shiru daddy yayi yana kallonta sai kuma yace "basai yasake dawowa ba kamar yaya?" "saboda ko yasake dawowa din bazamu fuskanci juna ba" Shiru dakin yasake dauka, haryanzu mummy batayi magana ba Saidai wani kallo datake jifan zee dashi, zee na ankare da kallon amma taqi kallon gefen mummyn don karma tarasa qwarin gwiwarta "meyasa?" inji daddy yana kallonta yanayin rashin jindadi na bayyana a fuskarshi "saboda bana sonshi Dad..." "ke!! Wato haryanzu bakida hankali ban saniba? Ina maki kallon wacce tafara hankali ashe haryanzu da saura?!" inji mummy a matuqar fusace Sauke idanunta zee tayi tana dan qara shigewa kusada daddy "ya isa maimuna" inji daddy Ahankali "ya isa din me? Yarinya shikenan bazata ta6a hankali ba, don gidanku ke kika haifemu ko mu muka haifeki dazaki maidamu shashashai? Duk wanda yazo da abinda zakice? Dama ina ganin dawowarki jiya nasan ba lau ba ke kenan Duk wanda yazo beyi miki ba? Me kika dauki kanki? Ko atunaninki cigaba zakiyi da zama damu har abada!" Daddy ne yaqara katseta da "haba Maimuna, ya isa Hakan mana, daga fadin ra'ayinta saiki hauta da fada?" "haka ma zakace Alhaji? Yarinya shikenan sai abarta tayita abinda taga dama babu kwa6a? Dama kai ka lallatata ai, idan ba Haka ba tsabar wulaqanci duk wanda yazo sai tace bata sonshi, sotake mu tisata gaba muyita kallo kenan har ta tsofe a gida? To bari kiji, diya mace qa'idattacen lokaci gareta, wlh tun kinada sauran damar ki ki rufama kanki asiri ki za6i miji tun kafin yazamo ke ke neman ayi za6i dake" inji mummy cikin mugun 6acin rai Shima daddy da ranshi yafara 6aci yace "haba Maimuna? Wannan meye to kike mata? Baki ne ko me dazakice zata zama ita za'ayi za6i daita? Wannan maganar kwata2 be dace ta fito daga bakinki ba a matsayinki na Uwa" Kauda kai kawai mummy tayi tana huci itakau zee banda hawaye babu abinda takeyi Juyowa daddy yayi Wurin zee daketa dauke hawayenta cikin sassauta murya yace "daughter?" Dagowa tayi ahankali ta kalleshi da watery eyes dinta "bakya sonshi ko kika ce?" Ahankali ta gyada kanta avoiding mummy's gaze "to masha allah, Zainab ni mahaifinki ne kuma mai son farincikinki, bazan ta6a yimaki dole ba, na riga da na dauki alqawarin auramaki muradinki ba don komai ba sai don dorewar farincikinki wanda nima shine nawa So karki wani damu, ni bazan yimiki bakin ki tsofe agida ba kuma bazan miki bakin kizama za6in wasu ba, insha allah saikin za6a kin darje da kanki kin kawoshi da kanki nikuma na cika miki burinki ta hanyar auramaki shi" Farinciki ne ya mamaye zuciyar zee Yayinda mummy kuma ta kauda kai cikin tsananin takaici "Thank you so much daddy... Kuma.. Dama ni yanzu akwai wanda.. Nakeso" tafada ahankali Ba daddy kadai ba har mummy Saida ta waigo ta kalleta sai kuma suka kalli juna sannan suka maida kanta again "menene?" inji daddy unbelievably Murmushi kawai tayi ta Kada mashi kai tana sunne kai, karo na farko data fara jin kunyar daddy Washe baki daddy yayi "masha allah, to kingani ko? Kinga abinda nake fadamaki, baki bari yarinya tagama fadin abinda zata fadaba kinyi jumping to conclusion" daddy yafada yana kallon mummy data qara kauda kai Cikin farinciki yajuyo gun Zainab dataji wani sanyi na ratsa zuciyarta yace "wanene shi to? Gayamin everything about him" Murmushi zee taqarayi a kunyace tana jin wani yaqini a zuciyarta "Daddy kaima ka sanshi ai" Dan wara idanu yayi "dagaske? Tofa, to wayeshi din?" "School mate dinane, Sunanshi DEEN" Tsittt dakin yayi Kallon kallo aka shigayi tsakanin mummy da daddy Saidai kowa da kalar kallonshi Daddy kallon rashin fahimta mummy kuma kallon mammaki "Kina nufin Kamaldeen?" inji mummy a mammakince Bata dago ta kalleta ba ta kada kai alamun eh Sake kallon juna mummy da daddy sukayi "wai wanene Hakan?" inji daddy in confusion Shiru mummy tayi tama kasa cewa komai "daku fa nake" "ta fadamaka mana, tunda itace mai maganar" inji mummyn tana kallon zee Maida kallonshi yayi akan zee din dake kallonsu itama "daughter na, kiyimin bayani, ni banganeba haryanzu" Zee da jikinta yafara sanyi tadan tattaro kingin kuzarinta sannan tace "Kamaldeen, wanda yayi rescue dina a wajensu Master, wanda ya kwanta hospital ta dalilin incident din" Diff... Wutar daddy ta dauke na wucin gadi "What?!" Yafada in shock... ✍️ *please Manage 👏, yau Dakyar nasamu nayi wannan biki garemu kuma jiya ma ban samu zaman yiba, sanin cewa kuna nan kunata jira yasa nadanyi wannan don jiya ma ba'ayi ba Ayi hqr, da babu gwara babu yawa Natafi cin shinkafar biki 🚴🏻‍♂️🚴🏻‍♂️🚴🏻‍♂️🚴🏻‍♂? Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:38 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *045* *THE CHALLENGE* Dagowa zee tayi tana kallon daddy jin yadda yayi magana sai gani tayi shock ne written all over his face, sai taji jikinta yayi sanyi "I.. Don't get you" inji daddy yana kallonta cikin son gasgata abinda kunnuwanshi suka jiye mashi Shiru tayi takasa cewa komai "wa kike nufi, I don’t get you" daddy yasake fada Hadiye wani abu daya tattaru a maqoshinta tayi sannan tace "wannan Deen din wanda keda pneumonia wanda aka kwantar dashi asibiti dalilin attempt dinsu master akaina" Ganin yayi shiru yana kallonta yasata yin tunanin ko haryanzu be gane bane Hakan yasata qara cewa "yace kunma Hade a wajen daurin auren Aunty Feenah Har kuka gaisa ma, wannan mai grandmom din?" "daughter are you ok?" inji daddy yana Binta da kallon mammaki Itama kallon rashin fahimta tashiga yimashi "ki rasa wanda zakice kina so sai wannan yaron?" inji daddy still cikin mammaki Gaban zee yashiga harbawa ahankali ta cigaba da kallon daddy batareda tasan na cewa ba "wai maimuna bakiji abinda muke cewa bane kikayi shiru? Wai kinsan wa take nufi? Wannan yaron? Wannan poor yaron? Yaron wannan tsohuwar? Shi wai take so" Bugun zuciyar zee yashiga qaruwa tana zuciyarta na dan fara nauyi "haba Zainab, haba Zainab, da kyanki da matsayinki da arziqinki ki rasa wanda zakice kina so sai wannan flirty poor guy?" Dagowa zee tayi ta kalli daddy tana jin zuciyarta na Bugun daya kusan faso qirji "Duk masu kudin dake zuwa nemanki? Duk masu matsayin dake zuwa nemanki, duk freaking rich, classic guys nake sonki ki rasa wanda zakice kina so sai wannan?" "b..but daddy, meye aibunshi?" inji zee cikin rawar murya Sake Binta da kallon mammaki daddy yayi not believing what he's hearing "mene? Meye aibunshi kikace? Wai daughter when did you change? Yaushe kika chanza? Magangganunki sam basuyi kama da naki ba" Itadai mummy kasa cewa komai tayi sai kallonsu kawai datakeyi "daddy ni aganina what matters is Good characters not wealth" inji zee dakeji kamar tayi kuka "wai yaushe kika chanza daughter? Ni dake munsan qualities din dakike buqata a namiji, wanda kike ambata min yanzu bana tunanin yanada ko daya" "that was then daddy, wancan tunanin na da ne, yanzu na gane ba duk kyalekyali keda amfani ba, what matters most is Good heart" Shiru daddy yayi kawai yana kallonta, this is the least he has expected Ajiyar zuciya daddy ya sauke sannan yace "kije ki sake tunani Daughter, amma wannan ba za6i bane" Yana kaiwa nan ya miqe ya shige quryarshi Binshi da kallo both zee da mummy da Tundazu takasa magana sukayi harya shige ya rufo kofar Mummy ce ta maido dubanta kan zee Hakan yasata sunkuyar dakai tanajin wasu hawaye na taruwa a idanunta Mummy batace komai ba itama ta tashi tabi bayan daddy suka barta zaune nan ita kadai Bin mummyn tayi da kallo itama harta shige Kafe kofar dasuka rufo tayi da idanu zuciyarta na lugude Koda wasa bata ta6a kawoma ranta soyayyarsu zata samu matsala ta wannan sigar ba She thought ko mahaukaci takawoma daddy a matsayin wanda takeso zai auramata shi don farincikinta, bata ta6a tsanmmanin wannan reaction dinba daga gareshi Ahankali ta miqe itama tajuya ta nufi kofar fita daga falon tana share fuskarta da bayan hannu. *** "nifa sai inga wannan abin duk bekai na tashin hankali har haka ba" inji mummy tana kallon daddy dake zaune Tundazu rai a jagule Dagowa yayi ya kalleta "bekai na tashin hankaliba kikace? Kinsan meke shirin faruwa kuwa? My only daughter in love with a mere street guy? Kema kinsan Hakan ba mai yiwuwa bane" "Alhaji please calm down, wannan abin ahankali yakamata abishi bada zafi zafi ba, kamata yayi a zauna ayi tattaunawa ta fahimta akanshi" Wani kallo yayima mummy "wane tattaunawa? Kema kinsan ko me za'ayi diyata bazata auri irin wannan mutumin ba. The whole diyar Dan Faranshi? Diyarshi tallin qwall? Ina?" Shiru mummy tayi takasa cewa komai, she's confused also, itama burinta Zainab ta auri wani ko dan wani wanda Hakan daidai yake da qarin qima da mutuncinsu na masu arziqi amma ambatar suna Deen da zee tayi yasa zuciyarta tafara rawa akan wannan ra'ayin nata, Hakan yasa yanzu ita kanta batasan wanda take goyon baya ba, Zainab ko Daddy. "ni ina nan ina jiran takawo za6inta, I thought it will be the best, ashe am mistaken? A tunanina duk wandanda ta kora mafiyinsu zata kawo ashe ba Haka bane? Taje can an huremata kunne, am very sure wannan ba ra'ayin ta bane wlh, wannan harda zuga da hurin kunne, ai nasan diyata ciki da bai. Babu yadda za'ayi ace wannan shine za6inta, babu. Wannan kawai hurin kunnene irin na maza and I will never tolerate it, zan koyama mutum hankali ne koma wanene, babu ruwana" yafada cikin tsananin 6acin rai Ajiyar zuciya mummy datayi zugum Tundazu tayi tace "to allah ya kyauta" Beko kalleta ba ya tashi ya nufi toilet din dakin. Cikin sanyin jiki tafito daga part din daddy takoma part dinsu Ahankali tashiga hawan matattakalan benen harta qarasa sama Dakinta ta nufa Direct ta bude tashige ciki ta maido ta rufe sannan ta nufi gadonta ta zauna a gefenshi Shiru tayi ta qurawa waje guda idanu, zuciyarta keson kawomata wani tunani amma taqi bata damar Hakan, taqi yarda taba kowanne irin tunani damar yin tasiri a ranta Abu daya kawai ke qarfafa mata gwiwa Shine Farincikinta shine na daddy itakuma batada wani farinciki daya wuce Deen Hakan na nufin dole daddy yayi accepting din Deen idan har yanason dorewar farincikinta kuma a wannan ga6ar ne batada tantama akai, daddy na iya sadaukar da komai akan farincikinta ciki harda farincikinshi, Hakan ne yaqara qarfafa mata gwiwa akan Deen Amma kuma ta rasa dalilin dayasa kuma zuciyarta ke rawa akan haka, tarasa dalilin dayasa take fargaba dukda tabbacin datake dashi, ta rasa meyasa takeji ajikinta wani abu marar dadi zai faru daita, dasu, ita da Deen. Ringing din wayarta yasata sauke wata Ajiyar zuciya tana lumshe idanu tareda budewa Shine, ko bata duba ba tasan shine. A halin yanzu babu muryar wanda take buqatar ji kamar tashi haka zalika kuma babu wanda bata fatan yaji muryarta ahalin yanzu kamar shi Jin Muryarshi zai kawo sauqi wa zuciyarta shikuma jin muryarta zai jawo fargaba da rashin kwanciyar hankali gareshi Kiran farko ne ya katse, ba'a jima ba wani yasake Shigowa Cigaba da kallon wayar take tana bin sunanshi dake motsi a screen din da kallo batareda ta Ko motsaba har itama ta katse Daukar wayar tayi dafarko kamar ta kashe sai kuma ta chanza shawara ta sata a silent ta ajiyeta kan bedside locker itakuma ta zame ta jingina da frame din gadon Idan akwai abinda bataso to tashin hankalin Deen ne don haka dole ta hadiye kwadayin jin muryar tashi ta zauna da nata damuwar ita kadai don tasan dayaji muryarta zaisan babu lafiya kuma zaiso tilasta mata ta fadamashi abinda ke faruwa wanda ita a ganin ta bashi da amfani don abune da bazaiyi wuyar warwarewa ba, tasan daddynta so batada case. This is just a minor challenge. *08:35pm* Kwance take kan gadonta tana danne dannen wayarta tana iyakar qoqarinta na ganin ta kauda duk wani damuwa dake son yin tasiri a zuciyarta Saidai dannar wayar kawai take amma ita kanta bata gane me takeyi da wayar ba Knocking din kofarta taji anyi Dago kai tayi ta kalli kofar batareda tace komai ba Gani tayi an murda handle din anshigo dakin Mummy ce Sauke kai tayi cikin zuciyarta tana cewa itafa bata jin yinwa ko an tilastata bawani abin kirki zataci ba "dress into something decent ki sauko kinyi baqo" inji mummy babu alamun wasa Saurin dagowa tayi ta kalli mummy "baqo kuma mummy?" "eh baqo kuma" "but I thought..." "look karki 6atawa mutane lokaci, Kiyi abinda nace yanzu!" Saurin sauko da kaffafunta tayi daga kan gadon don tasan halin mummy idan ranta ya 6ace "nabaki 5 mins Kiyi ki fito tun kafin ranki ya 6aci" inji mummy sannan tajuya ta fita Binta da kallo zee tayi harta fita ganin Hakan yasa tafara dirje dirjen kaffafu aqasa tana kukan ta6ara "ni ya kukeson nayi ne nace banasonshi banasonshi inada wanda nakeso, haan!" tafada tana hucin kukan datakeyi Sai kuma ta tashi a fusace tanufi wardrobe ta budeshi da qarfi taciro wata baqar gown ta dorama nightie din jikinta ta yafa gyale tadan fesa turare sannan ta fita looking so angry. A falon ta tarda mummy ba ita kadai ba harda daddy zaune bisa kujerar dake facing stairs Bata kalli ko daya daga cikinsu ba tawuce centre table din dake akwai tray mai dauke da kayan motsa baki sama ta dauka ta fice batareda ta yarda ta kalli gefensu ba. Binta da kallo duk sukayi sannan suka sauke Ajiyar zuciya "Alhaji baka ganin kamar dolen dakace baxaka yimata ba shi kake niyyar yimata?" inji mummy Shiru daddy da ranshi ke duk a jagule yayi can sai yace "haryanzu ba dolen zanyi mata ba, idan basu daidaita ba still zan bata damar samo wani amma ba wannan yaron ba ko makamancinshi, ta nemo miji gidan manya gidan mutunci ba inda zan kaita ba inkasa cin abinci ba saboda tunanin ko ita tasamu abin sakawa aciki" Ajiyar zuciya mummy ta sauke not knowing what to say don haryanzu batada ra'ayi acikin wadannan ra'ayoyin biyu wato na daddy da na Zainab, Itadai fatanta dai allah ya tabbatar da wanda yafi alhairi *** Da sallama tashiga guest room din ma wannan karon The same voice daya amsa sallamarta ta jiya ta amsa yau ma Bata yarda ta kallo gefen dayake ba ta nufi centre table din Wurin ta ajiye tray din datake jin kamar ta sakeshi Tundazu Kujerar da ta zauna akai jiya tasake akai yau tayi crossing kaffafunta tafara dannar wayarta Tunda tashigo yake Binta da kallon qasan ido ganin yau batada niyyar tankamashi yasashi cewa "sannu" kamar mai ciwon baki Ahankali ta dago ta kalleshi saikuma ta maida kallonta akan wayarta "yauwa" tafada itama kamar wanda aka tilasta Shiru yaqara biyo bayan haka. Ita hankalinta na kan waya shikuma hankalinshi na kanta yana studying dinta Sun kusa minti 15 ahakan sannan Asaad ya gyara zamanshi a kujerar dayake akai "Am Asaad Abubakar Dikko by name, ni d'a ne ga Alhaji Abubakar Dikko, a graduate with masters certificate a fannin business, and you?" yafada yana tsareta da madaidaitan idanunshi Sai a lokacin tasake Dagowa ta kalleshi sama sama tasake Janye idanunta "Am Zainab.. Zainab Dan faranshi" tafada a taqaice Kada kai yayi "Good, hope kinsan dalilin zuwa na nan?" "zan sanine bayan ka sanar dani" Dan murmushi yayi na gefen baki sannan ya kada kai yana dan mere baki "well, ni nasani kuma zan sanar dake dukda nasan kema kin sani" Dan daga kafadu cikin qara ta6e baki yace "I was sent here by my Dad, akwai abinda suke son qullawa tsakanina dake for their benefits don Hakan zai qara zumuncinsu da amincinsu kamar yadda sukace, shiyasa aka turoni don wai mu fahimci juna which I think bazai yiwuba don ni atsarina mata Africans basuyimin ba kwata2, primary dina kawai nayi a Africa, secondary dina nayishi ne a france, nayi first degree dina a uk and yanzu na qarqare masters a India A duk cikin qasashennan babu baqaqen fata duk jajjayene wataqila shiyasa kwata2 bana ra'ayinsu, babban burina shine auren one of those jajjayen ba baqaqen Africans ba dukda ke naga you're not that black" ya qarashe yana dan ta6e baki Zee tunda yafara ta maida hankalinta kanshi tana kallonshi dumpfounded "so nazo nan ne ba don mu fuskanci a sigar da tsoffafinmu keso ba sai don mu fuskanci juna na ainahi wato sanin ra'ayin juna akanmu, ni kinji ra'ayi na, so samu kiyi co-operating mu samawa kanmu mafita" Wani murmushi ya su6ucema zee tadan kauda kai tanayi Bece komai ba sai cigaba da kallonta dayake yana jiran jin me zatace Dagowa tayi taqara kallonshi sannan ahankali tafara magana "A ganina a smart guy with sharp brain tun zuwanshi na farko a wajen budurwa zai gane yasamu kar6uwa ko be samuba. Me haja shike buqatar talla. Gaskiya ra'ayinmu yazo daya don nima ban cika ganin mutuncin desperate African a qasashen masu jajjayen fata ba. Wadanda basa kishin kansu bare akai ga kare martabar asalinsu, bana masu kallon mutane at all saboda a qasarsu sunfita sahun mutane saboda basa kishinta a can inda suke marari kuma ba'ayimusu kallon mutane. Nayi primary school dina a Nigeria, Secondary school ma haka, and now nakusan graduating still a beloved qasata Nigeria and after that ko zanyi aiki I'll proudly reject kowanne offer na kowane qasashe musanmman na jajjayen and proudly stick to my beloved country Nigeria kuma ko zan fita din it will be within Africa din not outside. So inajin there's no need of worrying tunda ra'ayi yazo daya and am glad it does don ni dama ba kowanne namiji nake ma kallon namiji ba" tafada itama tana dage kafadu kamar yadda yayi dazu. Tsit dakin yayi Kallonta yake babu kyaftawa, yama rasa mai zaice ko zaiyi. Ganin shirun yayi yawa kuma baida niyyar cewa komai ko motsawa yasata sake dagowa ta kalleshi "mr.... Yama sunan? Well, whatever. I think tunda mungama fuskantar juna yakamata musan inda dare yaimana ko? As you can see am sleepy already, ko da wata maganar ne?" Cije lower lip dinshi kawai yayi ya Janye idanunshi akanta "No, I don’t think so" yafada saikuma yatashi tsaye yana pocketing hannayenshi "Good night" "yeah, mu kwana lfy" tafada itama batareda ta kalleshi ba Zuwa yayi ya wuce ya bude kofa ya fita ya maidota da qarfi har Saida zee tadan dode Kunnuwanta "stupid fool!" tafada tana bin kofar da harara tareda jan dogon tsaki Sai kuma tahau Dariya, wai jajjaye yakeso gashi shi kamar gawayi, saikuma ta cigaba da Dariya tana tunanin yan wahala fa yawa garesu a duniya, ita ko dauramata shi akayi a qafa saita kwanceshi ta yar don babu abinda zatayi dashi Tsaki tasake ja sannan ta miqe tafito itama daga dakin ta nufi cikin gida Luckily babu kowa falon Hakan yasata hayewarta sama ta maido dakinta ta rufe ta cire gown din saman nightie dinta ta qure a.c ta baje tana fesar da iska daga bakinta. Bata dadeba ahakan barci yayi gaba daita saboda dadin iskar dake shigarta *WASHEGARI* Zaune take tana waya da Deen daketa yimata mita wai jiya yaita kiranta bata dagawa har hakan yaja yakasa samun isashen barci itakuma tana yimashi Dariya Jitayi anyi knocking din kofarta aka bude aka shigo Ganin daddy ne yasata saurin katse wayar batareda ta shirya ba ganin yanayin daddyn "Daddy?" "Why? Meyasa zaki yimashi haka? Yes nasan bakya sonshi amma abin har yakai kicimashi mutunci? Beci yaci arziqin mahaifinshi ba Zainab?" Gaban zee ne yafadi Hakan yasa ta saukar da kaffafunta qasa ta miqe tsaye "Dad meke faruwa ne?" "look, karma ki fara, nasan ki nasan halinki, tsaf zaki iya finma abinda yace" "daddy ni me nace? Shi be fadamaku abinda yace ba? Wai he hate Africans wai bayason baqar mace? "koma me yace be kamata ki kirashi da dabba ba ko don albarkacin amincin dake tsakaninmu da mahaifinshi" "dabba? Ni yaushe na kirashi dabba daddy?" "kin fini sani tunda ke kika fada don nasani tsaf zaki fadi fin haka amma ko babu komai ya kamata ko beci darajar mahaifinsa ba ni yaci daraja ta tunda ni na gayyatoshi" "daddy.." tafada cikin rawar murya idanunta na kawo kwalla "ba komai ai, laifinane, kinriga kince bakya sonshi nikuma na saki kije wajenshi dukda Hakan, babu komai, tunda baki sonshi fine, bazan tilasta miki shi ba, kije ki samo wani na aura miki amma banda wannan yaron, kin dai jini ko? Banda wannan yaron ko wani talaka irin shi don bazai ta6a yiwuwa ba, so ko shi ke zugaki that won't change anything bazan ta6a hada zuri'a da tallaka ba wlh, tsakanina dasu sai kyautatawa da taimako idan naga dama amma bana alaqa ta surukantaka, never!" Yana kaiwa nan yajuya yabar dakin a fusace Binshi da kallo zee tayi harya fice ya maido mata kofarta Ahankali tayi baya baya ta zauna jagwab kan gadonta tana sauke numfashi ahankali _meke shirin faruwa daita ne?_ _meyasa wannan case din data raina keson girmama?_ _what went wrong?_ Hannu tasa ta shafo kanta zuwa baya cikin tsananin damuwa Tanaji tana ganin wayarta nata ringing da tone din Deen Amma takasa dagawa... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:38 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* Hhh yau ga post din dare, Gaskiya yau typing ya wahalar dani 🥺 *046* *THE CHALLENGE 2* Wunin ranar haka ta qarasheshi rai a jagule, kwata2 tarasa abinda ke mata dadi. Sosai fushin daddy da alwashinshi ya tsoratar da ita abinka da bata saba ganin haka ba Da mummy ce tazo tayi mata wannan hargagin bazaiyi tasiri a ranta ba kamar yadda na daddy keyimata yanzu don ita mummy dama ta saba da ganin Hakan agareta amma daddy zata iya cewa tunda tayi wayau bazata iya tuna ranar da ya ta6a yimata fada ba shiyasa yanzu abin ya dameta fiyeda zatonta Yinin ranar haka tayishi a dakinta ko abinci akazo akayi mata Maganarshi Saidai tace a hauro mata dashi sama kuma cikin sa'a mummy bata tankamata ba akan hakan, qila itama fushin takeyi Wayarta kau kasheta tayi don tasan Deen bazai barta ta numfasa ba da kiraye kirayenshi gashi ita bata cikin mood din Waya dashi kwata2 don batama son ya fuskanci wani abu gameda abinda ke faruwa Da daddare bayan wajajen 9:14pm tafito daga dakinta, tasan yanzu daddy na can yana kallon news while mummy na dakinta tana shiri Dama wannan lokacin ta ware don tasamu daddy suyi magana takuma bashi hqr akan abinda yafaru. Saukowa qasa tayi ta fita daga part din gabadaya ta nufi part dinshi tana saqa da warwara akan abubbuwan data shirya zata cemashi. Doorbell ta latsa sau biyu a na ukun ne taji muryar daddy ta cikin dakin yana bada izinin Shigowa Saida taja numfashi ta fesar sannan ta murda handle din ta tura kofar ta shiga da sallama. Dagowa daddy yayi daga kallon labarai da yake a t.v yana amsa sallamarta Ahankali ta qaraso cikin dakin cikin sanyin jiki tana jin hawaye na kawomata Daddy kau kafeta da idanu yayi harta qaraso tsakiyar dakin Hakan yasa ya miqamata hannu alamun tazo ganin Hakan yasata da saurin qarasawa ta riqe hannunshi ya zaunar daita gefenshi Dora kanta tayi a kafadarshi tafara sheshekar kuka ahankali Hakan yasashi dan rungumota a jikinshi yana rarrashinta ahankali Saida ta dan tsagaita kukan nata sannan daddy yace "am sorry shaleleta, nine ko?" Ahankali ta girgiza kai "nice daddy" "bake bace, nine. I shouldn't have yell at you" yafada yana shafa kanta ahankali cikin sigar rarrashi "A'a daddy, duk ni naja ai, da ban biyemashi ba Amma naji haushi ne dayace wai beson Africans bayan shima African din ne Shiyasa nikuma nace mashi bana son wanda baya kishin kansa bare asalinsa don ni bana masu kallon mutane, shikenan fa abinda nace" tafada cikin muryar kuka Murmushi daddy yayi ya sake rungumota a jikinshi "na yarda dake daughter don baki yimin qarya, I know you amma kuma shima ai ba qarya yayi ba, baki fito fili kika kirashi da dabban ba amma shi ya gane abinda kike nufi tunda ba qaramin yaro bane, idan bakayima mutum kallon mutum ba To kallon dabba zakayi mashi cikin dayan biyu amma babu komai, karki damu nima dazu don raina ya 6aci ne shiyasa kikaga nayi reacting haka amma kar Hakan ya dameki, komai ya wuce, shima Alhaji Abubakar din be dauki abin da zafi ba tunda ko dazu muna tare dashi, so no need to worry" Dagowa tayi ta kalleshi da watery eyes dinta fuska a marairaice tace "daddy ka yafe min?" Dariya daddy yayi "ni dama ai bakiyimin komai ba, kima bar damun kanki kinji, pretend nothing happened" Murmushi tayi cikin jindadi taqara kwantar da kanta akan kafadarshi tana lumshe idanu shikuma yayi mata kiss a tsakiyar kai sannan ya maida hankalinshi ga kallon dayakeyi Shiru dakin ya dauka na wani lokaci babu abinda ke tashi dakin sai muryar yar jaridar dake karanto labaran duniya cikin t.v din. Daddy hankalinshi kacokam yana kan news din itakuma zee saqa da warwara take akan yadda zata tado maganar Deen Amma takasa sanin ta ina zata fara Haka sukaita zama har Saida aka gama news din Ganin dai wannan shine daidai lokacin daya kamata ta tado maganar don mummy na iya Shigowa a kowanne lokaci yasata dan muskutawa ta daga kanta daga kafadarshi "yadai? Barci ko?" inji daddy cikin kulawa Murmushi kawai tayi sannan ta kuma sauke idanunta qasa tana wasa da yatsunta ta Wani yi kalar tausayi Ganin Hakan yasa daddy riqo hannunta datake wasa dashi din yace "tell me, wani abu ke damun ki?" Shiru tayi kuma bata dagoba Qara squeezing hannunta yayi "tell me" yafada a tausashe Hadiye wasu yawu ahankali sannan tace "daddy, dama...maganar Deen ne.... Please daddy.." "I thought mun riga munyi closing wannan chapter dake" daddy ya katseta da fadin Hakan "daddy, wlh Deen beda matsala ko kadan, he's very nice and innocent, gashi yanada ilimi both boko da Arabic and he loves me so much more than I did to him" "so? Don duk yanada wadannan abubbuwan Hakan na nufin zai iya riqeki? Anacin ilimi ne? Ko ana saka kyawawan hali? Meye aikinshi? Nawa yake samu a wata? Sune abubbuwan daya kamata ki gayamin" "daddy he's still under-graduate wannan shine last year dinshi a school kuma yace min yana practicing carpentry work irin na funitures yana dan samu anan kuma ai kafin lokacin yagama school nasan ma yasamu aiki" "carpentry? Nufin ki kafinta zaki aura? Diyar dan faranshi a matsayin matar kafinta?" "daddy I told you zai samu aiki kafin lokacin" tafada kamar tayi kuka "yaushe? A wannan Nigeria din kikeda yaqinin samun aikinshi da wuri? Masu kwallin degree har masters nawa ne ke kan titi Suna yawo kullum don neman aiki? Wasunsu sunfi shekaru biyar suna buga bugar neman aikin haryanzu basu samuba, ahaka zakiyita jiranshi har saiya samu aikin wanda allah kadai yasan lokacin?" "Daddy, kana da companies dayawa, yanzu haka akwai dayawa dakake ginawa, kullum cikin daukan ma'aikata kake, a ganina samun aiki bazai yima wanda nakawo wajenka a matsayin wanda nakeso wuya ba don ko wasu nakawo Koda bansansu ba kawai nayi niyyar taimakonsu nakawosu wurinka gani nake zaka iya sama masu aiki a cikin kanfanoninka bare wannan" Murmushin manya daddy yayi "yanzu na gano komai, kuma na tabbatar da abinda nake zargi. Wato dama don kudinki yake sonki, don yasan ke diyar wani ce wanda idan ya ra6a yasan zai kwashi arziqi, tunda harya fara sanya maki tunanin ni zan samomashi aiki" "haba daddy" zee tafada hawaye na kawomata "wlh daddy, kaji na rantse? Bamu ta6a wannan maganar dashi ba hasalima bayada kwadayi ko kadan wlh, abin hannun mutum be cika damunshi ba" "haka zai nunamaki ai amma a zuciyarshi akwai wata manufa ta daban, auran jari yakeson yi dake yadda shima zai ra6i arziqi, nawa akayi? Nasha ganin irin case dinnan a wurare da dama, sai yaro yazo ya hurema diyarka kunne ya kasance ta aminta dashi dari bisa dari, ta nace sai an aura mata shi sai angama sannan tazama itace abin wulaqantawa na farko a Wurin shi sannan kuma yafara planning yadda zai handame komai nata yadawo qarqashinshi, that's it, that's their aim" Hawaye sosai zee keyi tunda yafara maganar "haba daddy, why zaka siffantashi da wadannan munnanan aiyukan? Don baka sanshi bane, da kasanshi da bazaka ta6a fadin haka akanshi ba" tafada cikin kuka "kema ai iya abinda yakeso kisani gameda halinshi yabari kika sani, dama bari zaiyi kisan qudurinshi? Koko cemaki akayi hali a fuska ake ganewa, Zainab you're too young, bakisan komai ba a rayuwarnan. Ni nasan duniya kuma nasan mutanen cikinta, huldata ta yau da kullum yasa nasan mabanbantan halayen yan Adam Ba kowanne murmushi ke amsa suna murmushi ba, wani murmushin na mugunta ne, don mutum yayi looking innocent ba hakan na nufin he's innocent din har cikin zuciyarshi ba Kin riga kin makance a soyayya, ya riga ya burkita tunaninki, bazaki iya gane komai ba yanzu don bakya a hayyacinki amma ni ina a hayyacina kuma bazan ta6a folding hannayena ina kallonki ki fada halaka ba, never! Don Haka ma mubar wannan maganar don rayyuka ne kawai zasu 6aci don abune da bazai ta6a yiwuwa ba" Kuka sosai zee keyi, tama rasa abinda zatace Bata ta6a sanin haka akeji ba idan akaqi fahimtarka, bata ta6a sanin haka akeji ba idan aka soki masoyinka ba aka laqamashi abinda kasan bazai ta6a iyawa ba Wai Deen daddy ke cewa saboda kudi yake sonta, yaudararta kawai yakeyi saboda kudinta, how? Mutumin da abin duniya basa gabanshi? Be damu da abin hannun mutum ba? Tayaya? Shigowar mummy da sallamar ta yasa duk suka dago suka kallo kofar Mummy tadanyi Jimm ganin expression din fuskokinsu, zee idanu jajur ga hawaye a fuskarta shikuma daddy alamun 6acin rai a fuskarshi Qarasowa tayi cikin dakin Hakan yasa zee miqewa tsaye "Saida safenku" tafada idanunta a qasa sannan ta juya ta fice dakin Binta da kallo duk sukayi harta fita Maida kallonta mummy tayi akan daddy Saidai ko damar yin magana be bata ba shima ya tashi ya nufi bedroom dinshi rai 6ace. Da gudu ta nufi gadonta ta fada akai ta cigaba da kukan datake Tarasa meyasa daddy bazai tsaya ya fahimceta, tarasa meyasa daddy yayi ma abin mummunar fahimta. A ranar barci rabi da rabi tayi sai can gab da asuba wani barci mai dadi ya dauketa Hakan yasa Saida mummy tasha wahala kafin tasamu ta tashi sallar asuba. Koda tagama komawarta barci tayi bata farkaba sai wajajen 8:30am shima don mummy ce ta sake tadata. Wanka tashiga tayi sharp sharp tafito ta shirya ta tsara makeup dinta sannan tafito cikin shirin school ta sauko qasa A falo ta tarar da mummy, gaidata tayi ta amsa sannan ta nuna mata dining area tace taje tayi break Babu musu tawuce don tasan dole tayi inba haka ba ranta ne kawai zai 6aci a banza Tadan ci babu laifi sannan ta taso tazo tayiwa mummy sallama sannan tafice. *UMYU* Qarfe 9 da yan mintuna suka isa makarantar Tana jin anyi parking ta bude lumssasun idanunta ta dan kalli waje sannan ta miqe zaune daga jinginen datake da kujerar motar ta tsaida waqar datake ji ta bluetooth din kunnenta Jitayi an bude mata kofa Hakan yasata daukar jakkarta tafara yunqurin fitowa. Dago kan da zatayi sai taga ashe Deen ne ma ya bude kofar, yana tsaye riqe da murfin motar yana kallonta Dan wara idanunta tayi alamun dama kaine Shikuma yayi mata murmushi tareda ja da baya yana bata hanya don saukowa Ahankali ta sauko tana kallon smiling face dinshi tana jin damuwarta na yayewa a hankali. Saida ta ida fitowa sannan ya maida kofar ya rufe sannan ya juyo wajen ta yana mata murmushi yace "Good morning" Murmushi kawai tayi mashi sannan tace "ya weekend?" "Bad.. That's the most boring weekend I've ever had" Dan wara idanu tayi "dagaske? Meyasa kace haka?" "zan gayamiki, but first mutafi tukkuna" Hannu ya miqamata yana dan russunawa "may I?" Tasan abinda yake nufi Hakan yasa tabashi jakkarta itama ta miqamashi hannu ya doro mata littatafanshi akai Murmushi sukayima juna sannan suka nufi cikin school din. Basu yada zango a koina ba sai library don dama yau sunyi zasu dan ta6a karatu Kwana biyu soyayya ta hanasu karatu, da sun zauna sai su bige da firar soyayya before you know it lokaci ya tafi hakan yasa suka yanke shawarar fidda ma kansu timetable din karatu inda zasuyi scheduling komai yadda ya kamata. Usual seat dinsu suka zauna kowa na ajiye abin hannunshi bisa desk "Tundazu nake jiran zuwanki" "to? Amma ai am not late ko?" "you're not late amma son ganinki ne yasa naga kamar kinyi late din" Murmushi zee tayi batace komai ba "how's your weekend?" "cool.. Kaifa?" "not that cool" yafada yana yatsine fuska "why not?" "I was missing you, most especially muryarki, wai me yasamu wayarki?" "kajita kashe jiya?" "yes, tunda mukayi wayar nan da safe naketa neman wayarki amma shiru, what's wrong?" "matsala tadan samu shiyasa, muna cikin waya ta dauke sai screen din yabar kawo haske sai kawai na badata aka gyaromin" tafada tana daukar jakkarta dake gabanshi ta fara zuge zip din "ayyah, I thought as much. But are you sure you're ok?" Dagowa tayi daga bude jakkar datake "Me ka gani?" Daga kafadu yayi "kawai naga kamar you're not ok ne, kinmin wani iri" Murmushi kawai tayi ta cigaba da leqa jakkarta "then idanunka sun fara ciwo" tafada cikin tsokana Murmushi shima yayi yace "babu mammaki" Ciro handout da wani littafin tayi tana cewa "yanzu dai mufara, karka shagalar damu da surutunka" Harararta yayi yafara Ciro Littafi shima "ni dake wa yafi surutu?" "ni dakai" Dariya sukayi atare sannan duk suka bude Littatafan suka fara duddubawa Sun dan jima ahakan kafin lokacin shiga lecture din zee yayi ta wuce ta barshi anan shima yana duba nashi Littatafan kafin shima lokacin shiga class din nashi yayi shima ya tashi. Babu laifi zuwanta school a yau ya ragemata damuwarta sosai kuma ta cigaba da iya qoqarinta wajen 6oye damuwarta don ganin Deen be fahimci komai ba dukda dai yini yayi yana mata mitar shidai sai yaga kamar she's not ok Abin na bata mammaki don sosai take qoqarin pretending komai is ok amma sai yace tayi wani iri kamar something is wrong, idan yace Hakan saita tsokaneshi akan qila idanun ke buqatar doctor sai suyi Dariya Hakan kuma bazai hana yasake yimata maganar ba idan yasake kallon fuskarta. Sai wajajen 3pm bala yazo daukar zee Har motar Deen ya rakota kamar yadda suka saba tun bayan fara soyayyarsu Shi ya bude mata kofar tashiga sannan ya rufo mata yana cemata sai sunyi waya Kada mashi kai kawai tayi tana murmushi Dage tinted glass din motar tayi takoma ta jingina da kujera tana kallonshi Jin an tada motar yasa Deen dake waje fara daga mata hannu dukda baya hangenta Bïñ hannun tayi da kallo tana kallon band din data dauramashi ranar valentine Saita maido kallonta kan nata itama Ahankali ta danna dan botton din fuskar abin yakawo wuta _*DEEZEEN 💞*_ tasake dannawa _*TOGETHER FOREVER ❤️*_ Murmushi tadanyi ta dago tana kallon Deen jin motar tafara tafiya Har a lokacin daga mata hannu yakeyi har Saida suka fita daga school din Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya maida hannayenshi cikin aljihu yana cigaba da bin inda suka bi suka fita da kallo kafin daga baya yajuya yakoma inda yafito. Tun daga ranar da sukayi magana da daddy tashiga wasan 6uya dashi Idan tasan yana wuri bata yarda tafito wurin haka ma idan ya ritsata gaisuwa ce kawai a tsakaninsu babu irin wannan wasan nasu Da farko tayi tunanin itace ta dauke mashi wuta sai daga baya taga ashe shima Hakan take a wajenshi don maimakon ya damu kamar yadda yasaba yi duk lokacin da take fushi akan abu sai taga tayi biris daita kamar ma besan tana yi ba wanda Hakan na nuna alamun babu gudu babu ja da baya a Maganarshi. Hakan yaqara sakata cikin damuwa, don tasan muddin aka rabata da Deen to rayuwarta ta tagayyara don Deen shine farincikinta, idan babu shi zata qarasa rayuwarta ne babu ko digon farinciki. Ta rasa yadda zata 6illowa daddy ya fahimceta yakuma fahimci Deen don taga alamun ma kwata2 Deen be yimashi ba don ko Maganarshi bayason ana tadawa a gidan. Rannan data rasa yadda zatayi saita yanke shawarar samun mummy da maganar Batasan ra'ayin mummy akan wannan case din ba amma sai taga kamar mummy na son za6inta duba da yadda bata nuna rashin amincewa ba akan Hakan kamar yadda daddy yayi. Ranar Saida tagama sallar asr sannan ta tashi bayan tagama bitar abubbuwan dazata gayawa mummy din Direct dakinta ta nufa don bataji fitowarta ba Tun bayan shigarta sallah Ahankali tafara knocking acikin zuciyarta kau tana addu'ar samun nasara Tasan idan har mummy ta goyi bayanta to abin zaizo da mugun sauqi don zatasan yadda zatayi convincing din daddy kamar yadda tasaba a abbubuwa da dama. Saida tayi knocking uku sannan aka bata izinin shigowa Ahankali ta murda handle din ta tura kofar tashiga da sallama a bakinta Mummy dake ninke sallayarta ta dago ta kalleta ta amsa sallamarta sannan ta cigaba da ninkinta ta ajiye a ma'ajiyarta. Qarasowa zee tayi jiki a sanyaye kamar ta allah sannan ta zauna bisa sofa dake dakin Zama itama mummyn tayi a gefen gadonta tana kallonta, kallo daya zakayimata kasan tana cikin damuwa "yes? Meya faru ne?" inji mummy a tausashe Hakan yasa taji zuciyarta na raunana Shiru tadanyi tana jujjuya abinda zatace sannan ta dago ta kalli mummyn "mummy... Dama akan.. Maganar Deen ne.." saikuma tayi shiru Itama mummy shiru tayi tana kallon ta kawai "mummy, daddy kwata2 yaqi fahimta ta, wai saboda kudi Deen kesona kuma wlh ba Haka bane hasalima shi bema damu da abin mutum ba, idan ma ka bashi baya son amsa. Deen na sona sosai mummy, bazai ta6a yaudarata ba kamar yadda daddy ke cewa saboda bema san yadda ake yaudarar ba Babu ruwanshi, he's so innocent, shine silar gyaruwan wasu daga halayena marassa kyau, shi yafara saitani a hanya mai kyau batareda nasan saitanin yake ba. He's always there for me, yana taimakona a karatu sosai mummy, sosai. Shi yafara sona tsakaninshi da allah tun kafin ma yasan sona yake. A school babu mai sona harta wadanda nakema daukar qawaye, duk kowa qina yake sai shi kadai dukda abubbuwan danayi mashi marassa kyau" Saita fara bata labarin farkon haduwarta dashi dakuma haduwarsu ta biyu da abinda yafaru Ta cigaba da bata labarin yadda ta maida shi errand boy dinta har zuwa lokacin da case din assignment dinta ya hadasu da kwanciyar asibiti data jamashi Ta gangaro zuwa yadda suka shirya dakuma yadda yafara nunamata kuskuren da takeyi har ta gangarowa zuwa ranar da abinnan yafaru tsakaninta da master. Labarin take badawa tana kukan da batama san tanayi ba Ta cigaba da cewa "mummy har waya na siyamashi lokacin da za'a sallameshi ganin bayada waya tashi ta fadi a wancan ranar amma yaqi amsa Saida nayi fushi sosai sannan ya amsa kuma bama amfani yake daita ba don tun daga ranar ban qara ganinshi da ita ba Be ta6a roqona yar biyar ba, kuma bayaso nabashi, ko tashi mukayi daga makaranta Saidai yayi min karyar akwai abubbuwan dazai tsaya yi a makarantar duk don kar nace yazo mu rage mashi hanya. Mummy tayaya za'ace saboda kudina yake sona? Wlh ni nasani soyayyar Gaskiya yakemin mummy, idan narasa shi bazan ta6a samun wanda zai soni ko rabin son da yakemin. Please mummy kisa baki, kema ai kinsan halinshi, he's very nice and obedient. Aunty Feenah ma tasan shi da ita da yaya Auwal suma duk sunce yanada kyawawan halaye don su sukama gayyaceshi a bikin su kima tambayesu kiji, wlh babu ruwanshi, bazai ta6a yaudarata ba mummy" Tunda tafara maganar mummy ke kallonta Lallai Zainab, ba qaramin kamu soyayyar Deen tayimata ba, ji yadda tabi ta rikice Ita dama tun a hospital tafara zargin Hakan amma sanin halin zee na high taste dinta akan namiji shiyasa bata ta6a kawoma ranta soyayyar ce dagaske Ajiyar zuciya mummy ta sauke sannan ahankali tace "Zainab, nima nasani, Deen bazai yaudareki ba Amma abinda nakeso kisani shine, baka kwallafawa ranka abu kace dole dole sai abin don Mafi yawancin abubbuwan da mukeso baya zama alhairi agaremu shiyasa allah ke musanya mana da wani abin, idan mukayi hqr sai kiga munci ribar haqurin. Zanyi mashi magana kamar yadda kika buqata amma kuma inason kisa a zuciyarki koma menene idan har Kamal mijinki ne to saikin aureshi idan kuma ba mijinki bane ko duniyar nan zaki gayyato suyima daddyn magana Hakan bazai faru ba Abinda nakeso ki dinga yi shine addu'a, ki dinga addu'ar allah ya za6amiki abinda yafi alhairi bawai ki nace Lallai lallai sai shi ba, idan shine yafi alhairi allah ya za6amiki shi idan kuma bashi bane to allah ya musanya miki da wanda ya fishi, kinji ko? Kada kai tayi ahankali acikin zuciyarta tana cewa insha allah shine ma wanda yafi alhairin Cigaba da yimata nasiha mummy tayi mai kwantar da hankali wanda Hakan ya rage mata kaso Mafi yawa na damuwar ta kafin daga baya ta sallameta akan zata sameshi tayi mashi maganar, kawai tayi addu'ar allah yasa ya gane don ita tana maraba dashi a matsayin suruki don hallayarshi ta dade tana burgeta. Da wannan zee taqara samun qwarin gwiwa, tashiga addu'ar allah yasa qarshen case dinnan kenan, allah yasa ya fahimta. *** Suna Kwance suna dan fira irin na kafin barcin nan cikin nishadi Mummy nata son yimashi maganar su Deen Amma tarasa ta ina zata fara don a kwana biyun nan ta fuskanci idan akwai maganar wanda ke 6ata mashi rai to na Deen ne "jiya ma munyi waya da Ummu batool ai tace tana gaisheka wai ta nemi number ka bata shiga" inji mummy "ita ta nemi number ta Ko ni na nemi number ta? Tunfa shekaranjiya nake neman number ta bata shiga" inji daddy "nima haka nace mata don nima na nemeta ban samu ba wai ashe layi ta chanza, jiya ma da sabuwar number ta kira" "ayyah to duk ya suke? Yasu batool?" "Duk suna lfy lau ai har gaisawa mukayi da batool shi yayan nata ne bayanan yana wajen aiki" "ai wadannan yaran naso naga lokacin da zasu dinga zuwa nigeria frequently musanmman babban, rabonshi da nigeria ai za'ayi shekara biyar ko?" "ko fi ma, ai kasan halin aikinsu they're always busy gwara gwara batool ita ana dan zuwa daita dukda itama wani sa'in school na hanata zuwa" "ai babu komai, insha allah lokaci zan fidda mu kwasa dukanmu muyimusu zuwan bazata" Yar Dariya mummy tayi tace "dakau mun kyauta, ai yakamata a dinga tunawa da zuminci ko yaya ne bawai business ba kowanne lokaci" "to? Dani ake kenan?" Yar Dariya taqara tace "ni bance ba Saidai idan tsarguwa kayi" "har tsarguwar ma nayi tunda nasan dani ake" Dariya sukayi sakeyi atare Shiru yadan biyo baya "diyarka fa nacan, kodayaushe very moody, abinci ma saina tilasta mata takeci, na rasa gane kanta" Nan take mood din daddy ya chanza "ai dole kiga Hakan tunda tana can kullum wancan yaron na zigeta" "Yana zigeta kamar ya?" "hmm, ai duk motsinsu yanzu akan kunne na yake don tun ranar da mukayi maganar qarshe akanshi daita nasamu balarabe nayi mashi Tambayoyi akansu yace min shidai ada lafiya lau take huldarta ita daya amma daga baya ya dinga ganin yaron na liqemata wai har budemata mota yake idan zata shiga ma Hakan wai harda riqe mata jakka. Bayan naji daga gareshi na sallameshi na kuma samu wani akan ya dinga samin ido akansu a school din and the same amsa dasamu dana bala harda ma qari wai duk inda zataje yana maqale daita har hotunansu ma Saida ya daukomin don su zama evidence. Gabadaya ya shiga rayuwarta kullum da irin zugar da yake mata yana huremata kunne yana nuna mata wai sonta yake itakuma dayake she's dull takasa ganewa, mataki zan dauka akai tsatsaura kau, lokaci kawai nake jira" yafada cikin 6acin rai Kan mummy ya kulle "ni sai inga kamar wannan duk misunderstanding ne, yaron is very calm and quiet, kamar bazai iya Hakan ba" "hmm wai ke kenan da kike babba bare ita da take qarama, kice inbar ganin laifinta don bata gane abinda nake nusar daita ba tunda kema gaki kin gaza ganewa" "ba Haka bane Alhaji, Zainab ta sameni tagayamin komai kuma da gamsu dasu, wlh daddy a kallo daya idan kayima yaron zakasan yanada nutsuwa sosai, bakaga Zainab ta chanza ba taqara hankali a yan kwanakinnan? Tafada min duk shine sila bayan Hakan ga siyarda rayuwarshi dayayi wajen cetonta a wannan incident din nasu a school, da ba don shi ba da wani labarin mukeyi daban yanzu" Daddy dayayi sakato Tundazu yana jinta ya girgiza kai cikin takaici "ansha fadamin mata basuda hankali amma ban ida yarda ba sai yanzu. Wato ta nan kuma ya 6illo? Dama ai shi tallaka be ta6a taimako don Allah ba, dole don ribar kanshi yakeyi Yayinda mu kuma sukeso mu kyautata masu don Allah To idan maganar taimakon ta dayayi ne yazo yayi naming price dinshi ko nawa yakeso zan bashi, ladar taimakonta dayayi, ba shikenan ba? Yazo ya fadamin ko nawa yakeso zan bashi amma wlh diyata tafi qarfinshi, diyata matar manya ce! Kuma shiriya ta allah ce idan baki sani ba, dama can nasha gayamiki yarinta ke damun ta zata bari kece baki yarda ba shine kuma yanzu da shiriryar tazo zaki alaqanta ta da wani can, dama mutum ke shirya mutum ba allah ba?" Mummy da duk ranta ya jagule akan magangganun da daddy ke fadi tace "Alhaji ba Haka bane..." "to yaya ne? Yaro yabi ya kallalameku da qarya da komai kun yarda dashi? Nifa matafiyine mai shiga jama'a daban daban mai kuma hulda da juma'a masu mabanbantan hallaya. Na fiku sanin me duniya take ciki. Ke kanki kinsan case din Alhaji Hassan da surukinshi wanda haryanzu abu yaqi ci yaqi cinyewa Shima ba ta wannan sigar yazo ba ya kwantar dakai ya ruda diyar mutane aka bashi ita Yanzu kullum gasucan hanyar court suna sintiri ya danne duka dukiyarta yasa ta chanza komai nata da sunanshi ya handame komai, ko zakice baki san da Hakan ba?" yafada cikin hayayyakowa Shiru mummy tayi takasa cewa komai "shifa tallaka a duniya bayada babban maqiyi kamar mai arziqi don gani yake be kamata shi a hanashi ba wasu kuma abashi besan komai ikon allah ne ba muma bamu mukayi wa kanmu ba. Kullum burinshi tayaya zai ra6emu ya kwashi na kwasa ya gudu Babu wata soyayya a tsakanin tallaka da mai kudi duk qarya ce don kowacce qwarya da abokin ragayarta. Idan har kikaga Hakan to akwai cuta aciki musanmman irin wannan case din da ita macen itace mai kudin, dama ace namijin shine mai kudin da da sauki don ana saran zai iya controlling dinta amma a wannan case din fa? Ita kanta kacokam a qarqashinshi take inaga maganar dukiyarta? Saboda haka na riga na ajiye magana kuma ta ajiyu Tunda kika ga nayi burus daita dukda nasan halin datake aciki Hakan ya isa ya nuna miki babu gudu babu jada baya a wannan maganar don bazan ta6a barin inzama silar cutar da diyata daya da allah yabani ba. Don haka taje taita nema, ni ba matsa mata zanyi ta kawo miji dawuri ba, she should take her time wajen Fiddo wani responsible one bazan damu da tsawo lokacin dazai dauka ba Amma batun wannan yaron abu ne da bazai yiwuba wlh. Kuma shima zan sameshi, zan bashi damar rabuwa daita ta lallama idan kuma yaqi zan gwadamashi true colour dina, zai gane ba kowanne mai kudi ake jadashi a wanye lfy ba" Yana kaiwa nan ya juya ya gyara kwanciyarshi ya rufe jikinshi har kai ranshi na qara 6aci yana kuma qara jin tsanar Deen a zuciyarshi Shiru mummy tayi takasa cewa komai, sosai ranta ya jagule taji komai ya sake kwa6e mata, batasan daddy yayi nisa har haka ba, nisan da bazai ta6a jin kiraba inba wani iko daga allah ba. Gyara kwanciyarta itama tayi ta lumshe idanunta batareda ta qara cewa komai ba ta cigaba da saqa da warwarar wannan rikittacen al'amarin a zuciyarta... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:38 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *047* *THE PROMISE* Washegari Zee tayi ta jiran feedback daga wajen mummy amma shiru don ko makamanciyar maganar mummy bata tadomata ba Haka ta haqura ta wuce school ranar tana tunanin qila bata kaida yimashi maganar ba, haka ta haqura a zuciyarta tana fatan koma da yaushe zata mashi maganar allah ya dorasu a kanshi. A school ma ranar tare suka wuni da Deen wanda bayada lecture ma kwata2 a ranar kawai zuwa yayi don ita. Sunyi karatu sosai don yanzu sun koma kamar da karatu suke babu kama hannun yaro don exam is at the corner dukda da dan saura ga lokacin. Sai bayan zuhr sukayo gida inda su zee ne suka fara tafiya sannan shima daga baya yafito yasamu abin hawa shima ya wuce unguwarsu. Deen hankalinshi Kwance yake gudanar da al'amuranshi don ko kadan besan abinda ke faruwa ba a 6angarensu zee ba. He never saw anything like that coming shiyasa yake gudanar da al'amuranshi hankali Kwance. Ya dade yana daily addu'o'in shi daya saba duk bayan kowacce sallah sannan ya shafa. Saida ya dan qara yin Jimm a masallacin kafin daga baya ya tashi ya fito. Babu mutane sosai a wajen masallacin Hakan yasa ya zura takalminshi kawai ya fito daga masallacin don komawa gida don dama shi daga masallaci sai gida, salmanu yasha tsokanarshi wai kamar mace ko irin fitowa wajen mai shayi beyi yadan rage dare yafison daya gama sallar isha'i yakoma ya qunqume gida kamar matar kulle Shidai be ta6a tanka mashi ba Saidai yayi Dariya kawai a wuce wajen don shi bejin zai iya wannan zaman na majallisar mai shayi duba da yadda kodayaushe wurin ke cike da matasa anata hayaniyar cafta irin nasu na maza, shi idan yaje ma ai ciwon kai zai jama kanshi a banza saboda hayaniyar wajen, gwara shi salmanun dayaga zai iya yayi. Tun daga nesa ya hangi wata mota parke a daga dayan gefen santarsu daidai gaban gidan Mallam Nasiru Be kawo ma ranshi komai ba ya cigaba da tahowa kai a qasa yanata lissafe lissafe a zuciyarshi Daidai yayi hanyar shiga gidansu yaga an dallareshi da hasken motar Dan juyowa yayi yana kallon motar yana dan kare fuskarshi saboda yadda hasken yayi reflecting din fuskarshi Kamar kau mai motar ya sani sai gani yayi an kashe hasken Sake Juyawa yayi zai wuce aka qara dallaro hasken wannan karon harda dan horn Hakan yasa ya qara tsayawa ya juyo yana kallon motar. Gani yayi an bude murfin mazaunin driver wani ya fito. Tsayawa yayi yana kallonshi har ya tsallako 6angarenshi ya qaraso wajenshi sai a sannan ya lura da fuskar mutumin, bala ne drivern zee. Qarasowa bala yayi wajenshi cikin fara'a ya miqa mashi hannu shima Deen ya miqa mashi hannu yana murmushi suka gaisa "Tundazu muke nan muna jiranka, wani yaro yace mana kana masallaci" Murmushi kawai Deen yayi tareda Kada kai alamun haka ne "lafiya dai ko?" inji Deen yana kallon motar dake can gefen titin parke "lfy qalau wlh, kawai Alhaji ne keson ganinka, mu qarasa idan babu damuwa yana ciki" yafada yana nuni da motar Qara bin motar Deen yayi da kallo sannan ya kalli bala yayi mashi dan murmushi yace "ba damuwa, muje" Atare suka sake tsallakawa dayan barin da motar take suka nufi inda motar ke a parke Saida suka qaraso sannan bala yayi saurin Qarasowa ya bude back seat saiga daddy ya bayyana a zaune takardar jarida a hannunshi yana dubawa Jin an bude kofar yasashi Dagowa daga kallon jaridar dayake ya kallesu. "Gashi nan Alhaji" inji bala yana komawa daga baya yadda Deen zai bayyana ga Alhajin Ganin daddy yasa Deen jin kunya don be ta6a tunanin shine ba Fuska dauke da murmushi Deen ya zame qasa ya tsugunna yana gaida daddy cikin girmamawa. Sai ji daddy yayi wani iri don rabon da ayimashi irin wannan gaisuwar harya mance Sai kuma yayi saurin kawar da zancen a kanshi yana tuna tattaunawar da sukayi da Alhaji Abubakar dazu har yana cemashi talaka babu abinda bazaiyi ba na kwantar da kai duk don yasamu shiga domin suna iyayin komai don cikar burinsu. Kawar da wannan tunanin yayi yashiga amsa ma Deen cikin fara'a yana cemashi ya tashi. Tashin Deen yayi cikin sunkuyar dakai don shi harga allah kunyar daddy yakeji sosai "zagayo abokina, zuwa nayi mu tattauna" inji daddy cikin fara'a Gaban Deen yadan fadi da jin Hakan, badai yasan komai ba? Wayyo ya zaiyi da kunya? Haka dai ya zagayo din kamar yadda ya buqata, ya bude kofar dayan gefen ya shigo ya zauna a darare yana dan wasa da band din hannunshi kamar irin amaryar nan idan ana siyan baki duk yabi ya takura. Ajiye jaridar hannunshi daddy yayi ya gyara zama ya juyo yana kallonshi yana kallon yadda yakasa sakewa kwata2, sai yadanyi murmushi "Kamal ko?" inji daddy yana kafeshi da idanu Dagowa Deen yayi ya dan kalleshi sai kuma yayi murmushin tabbatar da Hakan "Ina wuni Alhaji" yasake gaidashi a karo na biyu Dan murmushi daddy yayi yace "lfy lau, ya mutanen gida?" "Duk suna lfy lau "ya school? Ana dai maida hankali sosai ko?" Murmushi Deen yayi yace "insha allah daddy" Shima daddyn murmushin yayi yana Kada kai "to allah ya taimaka" Da amin Deen ya amsa trying so hard wajen controlling nervousness dinshi "dama wata yar magana ce takawoni wajen ka ko ince alfarma" Dagowa Deen yayi ya kalleshi in surprise sai kuma ya maida kanshi qasa bece komai ba "naji ance kai abokin yarinyata ne sosai kodayaushe ma kuna tare ko?" Sake Dagowa yayi ya kalleshi again sai kuma ya sake sauke idanunshi "eh daddy" "dakyau, dama wata alfarma nazo nema awajenka akanta nasan kai kadai zaka iya yimin Hakan" Shiru Deen yayi be kuma dagoba saima jin maganar daddy dayake wani banbarakwai, wai alfarma, ina shi ina yiwa mutum irin wannan alfarma? "Dama akan Zainab ne, kwanan nan narasa gane kanta gabadaya, ta tsiro wasu hallaye da ba nata ba, bansan inda matsalar take ba ko itace ta chanza ko chanzata akayi oho?" Qara Dagowa Deen yayi ya kalli daddy saikuma ya sauke idanunshi "Wani abu takeyi ne?" "Abubbuwa ma kai, lokaci daya yarinya ta chanza? babu irin wannan biyayyar ta da da jin magana ta, tabar saurarona ma bare tabi abinda nake nunamata" Hankalin Deen ne yafara tashi kuma Hakan ya nuna a fuskarshi "ya sallam! To meyasa?" "nima shine ban sani ba Amma nafi kyautata zaton huremata kunne akeyi don ada ba Haka take ba. Munyi maganar wani yaro daita, ita tama kawoshi da kanta tace tana so nakuma aminta da Hakan saboda yaron nagarttace ne sosai, yanada kyawawan hallaye ga tarbiya, yana sonta sosai itama tana qaunarshi Lafiya lau muka tsaida magana da manyanshi akan idan tagama school za'a aura mashi ita Amma kwatsam lokaci daya Abubbuwa suka fara chanzawa, bata saurararshi yanzu, bata bashi damar ganinta ko yin waya daita. Tabi ta chanza a yan kwanakinnan duk mun rasa gane kanta, bata sauraron maganarmu sam bare tayi amfani daita kuma da ba Haka take ba, Zainab yarinya ce mai sauraron maganar iyayenta most especially ni amma yanzu ta chanza tayi fatali da duk tarbiyar da muka bata. Mun rasa yadda zamuyi mata don sosai yaron yake cikin damuwa saboda yana sonta sosai amma duk yadda mukaso ta fahimcemu ko ta fahimtar damu meye matsalar taqiya. Shiyasa danaji ance kai abokinta ne sosai kusan ma kullum tare kuke yasa na yanke shawarar zuwa wajenka wataqila ka iya abinda ke neman gagararmu" Tunda Daddy yafara magana wutar Deen ta dauke diff, kanshi yafara jujjuya mashi ahankali, fadin tashin hankalin da zuciyarshi ta fada 6ata baki ne, jin magangganun daddyn yakeji kamar a mafarki "shiyasa nazo wajen ka, please ka jawo ra'ayinta akan Hakan tunda naji ance kai abokinta ne, kana iya yin abinda mu muka gagara yi, ka kuma samata ido kaga ko wani ke zugata don ni nafi tunanin Hakan, ta yiwu wani ko wata ke zugata yana dorata a keken 6era da nufin kaita yabaro. Please do this for me, kaji d'ana?" yafada yana kafeshi da idanu cikin son karanto yanayin dake fuskarshi kuma yasamu abinda yake nema don tsagwaron tashin hankaline rubuce all over fuskarshi "bakace komai ba kamal" inji daddyn still yana kafeshi da idanu Sai a lokacin Deen yadan qaqaro murmushin yaqe yahau yi "insha allah daddy.. I'll try my best" Murmushi sosai daddy yayi cikin nuna farinciki sosai "yauwa d'ana, naji dadi sosai, allah yayi maka albarka, don Allah ka kulamin daita sosai, ka nusar daita sosai idan ma kaga alamun zugata akeyi to let me know, sai na tabbatar na koyawa munafukin hankali don na tsani munafurci kana gani na nan, duk yadda muke da mutum daya munafurceni to wlh nagama dashi kuma zamu sanya kafar wando daya ne dani dashi" Kasa dago kai Deen yayi don jiyayi kamar ma dashi yake, gudu sosai zuciyarshi take acikin zuciyarshi yana lissafa cewa kenan shine mai huremata kunnen, da daddy yasan da Hakan da da wane ido kuma zai kalleshi? Hakan yasashi jin duk ya takura, a zahiri sauraronshi yake amma a badini duk bayama gane abinda yake cewa. Dakyar dai yasamu yagama magangganun shi yana kuma qara jaddada mashi ya taimaka mashi wajen ganin sun shawo kan matsalar. Da insha allah kawai Deen ke amsawa batareda ya iya hada idanu dashi ba Godiya sosai daddy yayi mashi yana Tambayar kaka shikuma yana amsa mashi da tana cikin gida "to my regards to her" Sai kuma ya karkata gefe ya shiga lalubar aljihunshi Shidai Deen besan yana yi ba don kanshi na qasa haryanzu yana sake jujjuya magangganun daddy a ranshi "ga wannan babu yawa" yaji daddy na fada Dan Dagowa yayi sai yaga ashe kudi yake miqomashi Dan murmushi yayi sannan ya girgiza kai ahankali "A'a daddy, ngd qwarai" "haba ka amsa mana" inji daddy "don Allah daddy kabarsu" "meyasa? Ko sun maka kadan ne?" Sake Dagowa yayi ya dan kalleshi sai kuma ya sauke idanunshi "ba Haka bane daddy, kaka batason haka, zatayi fada kayi hqr" Dan ta6e baki daddy yayi ya maida kudin a aljihunshi "to shikenan ai, babu damuwa, ngd kaji, please kayimin qoqari akan Hakan" "insha allah daddy" "bari mu wuce, dare sai qara yi yake" "to" inji Deen yana fitowa daga motar dama bai rufe kofar ba Maido mashi kofar yayi ahankali ya rufe yana mashi sallama da fatan isa gida lfy shikuma daddy ya daga mashi hannu kawai yana murmushi bala yaja motar sukayi gaba Bïñ motar yayi da kallo harta fice daga layin nasu Lumshe idanu yayi ahankali ya bude yana jin kanshi na wani irin saramashi. Meke shirin faruwa ne? Wanene Zainab keso har aka tsaida maganarsu? Wake huremata kunne? Bayada wanda zai bashi duk wadannan amsoshin Hakan yasashi Juyawa jiki a sanyaye yashige cikin gida. Koda ya shiga Saida kaka ta tambayeshi dalilin dadewarshi awaje yau sai cemata yayi suna dan fira ne da salmanu. Duk yadda yaso 6oye yanayinshi ga kaka Saida ta gano sauyin yanayinshi Hakan yasata Tambayar shi meke damunshi, babu komai yace mata ganin zata matsa mashi yasashi cewa barci yakeji sosai jikinshi duk ciwo yake mashi. Jin Hakan yasata gabatar mashi da abinci da sashi yadanci ba laifi sannan ta rakashi har daki ya kwanta bisa katifarshi tana jera mashi sannu. Saida taga barci ya daukeshi sannan ta taso ta fito daga dakin ta cigaba da yan qananun aikace aikacenta don Allah ya taimaketa tunda marece sukayi tatar qullin kokonsu. Saida tagama duk diminiyarta sannan ta daura alwalla tashige nata dakin itama ta rufo kyaure. A bangaren Deen kau barci qauracewa idanunshi yayi, dama pretending yayi kamar yayi barcin don kaka ta kyaleshi tana fita ya bude idanu ahankali ya tsurama saman rufin dakin ido. Ya rasa meke mashi dadi a zuciyarshi, ya kuma rasa yadda zai fassara magangganun daddy. Dama zee tanada wanda takeso aka har aka tsaida magana dashi kafin yashigo da tashi manufar akanta? Koko dai za6amata akayi daga baya? Zainab na son mutumin dagaske kamar yadda daddy yace? Koko shi take so? Meyasa bata ta6a yimashi magana makamanciyar wannan ba? Meyasa bata ta6a cemashi an tsaida maganar ta da wani ba? Daren ranar Deen kasa rintsawa yayi saboda damuwa Yarasa me keyimashi dadi, ya kasa Kamo bakin xaren al'amarin, yadda yaga rana haka yaga dare. *WASHEGARI* Still haryanzu mummy bata yimata maganarsu ba dukda kau kasa kunnen datake tayi tun jiya, abinda bata saniba shine bata kaiga gayamashi bane koko ta gayamashin Itadai ce bata bata feedback ba? Tana son Tambayarta kuma tanajin tsoro Hakan yasata haqura ta cigaba da kasa kunne da jiran tsanmmani. Shirin school tayi a gagauce don yau tanada morning lecture Koda ta sauko breakfast tayi sama sama ta tashi tayi sallama da mummy tafito, babu 6ata lokaci suka shige mota ita da bala suka fice daga gidan. *UMYU* Koda ta isa school saura minti biyar su shiga aji Hakan yasa tayi ma ajin tsinke Direct Mintuna 40 lecture din ya daukesu sannan suka fito daga class din Rataya jakkarta tayi itama ta biyo ayarin masu fita daga class din itama tafito. Direct wajen zamansu tanufa tana tafiya a gajiye tana tare goshinta da wani littafin saboda hasken rana dake reflecting goshin nata. Tun daga nesa ta hangeshi zaune ya juya mata baya Ahankali ta qaraso wajen tana kallon bayanshi tana jin soyayyar shi a kowane magudanar jininta Ganin kamar besan da isowarta ba yasa ta qarasa bayanshi cikin sand'a ta dan duqa saitin kunnenshi tayi tafi da qarfi Aikau firgigit yayi yayi saurin waigowa Hakan yasa tashiga yimashi Dariya tana toshe bakinta Dan murmushi yayi sai kuma ya juya ya cigaba da kallon inda yake kallo Qarasowa tayi ta zauna itama tana dan basu space tace "scary mouse, har kaji tsoro ko?" Kallonta yasakeyi ya danyi murmushi sai kuma ya qara dauke kai "tunanin me kakeyi harna qaraso baka jini ba?" Girgiza kai yayi batareda ya kalleta ba bece komai ba "yaushe ka iso school? Juyowa yayi ya kalleta again, ahankali ya bude baki yace "dazu" a takaice Tsayawa itama tayi tana kallonshi don sosai kallonshi yabata mammaki Babu wannan fara'ar babu murmushi babu sakewa dukda fuskar ba adaure take ba but look dinshi is very formal. "ya dai?" tafada tana kallonshi cikin ayar tambaya kauda idanunshi yayi daga kanta yana cewa "daidai" "what's wrong?" tasake tambaya Juyowa yayi yasake kallonta, kallon da yasa hanjinta dan kadawa don kallon yana dauke da ma'anoni daban daban "babu, wani abu kika gani?" ya Tambaya yana cigaba da yimata irin kallon Shiru tayi da farko saikuma tace "kamar you're not alright" Wani slight murmushi yayi sannan ya dauke kanshi, shima kamar bazaiyi magana ba sai yace "am alright, kawai na gano wani abu ne" "Wani abu? Wane abu?" Yan tsakuwa ya tsinta a gabanshi qwara biyu ya tilla daya can nesa "abinda ake 6oyemin" yafada yana tilla dayan ma Shiru tayi tana kallonshi kawai takasa cewa komai Qara tsinto daya yayi ya riqe yana kafeshi da idanu kamar mai karanta wani abu jikinshi sai kuma ya danyi murmushi "yanzu nasan komai, na daina lalube" yafada yana tillashi shima Jikin zee ne yadanyi sanyi kamar bazata iya cewa komai ba sai kuma tace "wai meke faruwa ne Deen? Are you ok?" Juyowa yayi ya kalleta da idanunshi dasuka fara kadawa "nayi kama da wanda ke ok? Am not" "then.. What's wrong? Sai magana kake marassa ma'ana aguna, meke faruwa ne?" "kin fini sani Zainab, kinsan komai and that's what hurts me more, 6oyemin dakikayi" Kallon idanunshi datake yasa nata ma kadawa tanajin yadda zuciyarta ke bugawa sosai "mena 6oyemaka?" tafada cikin rawar murya "da ace baki sani ba da bazan ji komai wajen gayamiki ba Amma kinsani Zainab, kinsani. Kuma barina a duhun da kikayi yafi komai yimin ciwo" Hawaye ne suka taru a idanunta "waya gayamaka?" Dan murmushi yayi mai ciwo tareda kauda kai "sanin Hakan beda muhinmmancin" "don Allah ka gayamin, please" tafada tana qoqarin danne hawayenta "it doesn't matter Zainab, bayada wani fa'ida" yafada yana qara kauda kanshi yana jin zuciyarshi na zafi sosai Sauke idanunta tayi qasa Hakan yaba hawayenta damar digowa kan skirt dinta "nayi Hakan ne don karka shiga damuwa, nayi tunanin zan iya solving abin ne ni kadai" tafada ahankali batareda ta dago ba "amma ai abin nima ya shafeni, nima inada right din sanin kome ke faruwa Koda abin zai bugarmin da zuciya" yafada shima batareda ya juyo ya kalleta ba Ahankali ta tsane idanunta sannan ta dago ta kalleshi "am sorry, kamar yadda nafada dazu nayi Hakan ne don karka shiga damuwa" Shima juyowa yayi ya kalleta "ni idan ban shiga damuwa ba shi wanda kika bari da broken heart ya zaiyi da rayuwarshi?" Kallon rashin fahimta tayi mashi "wa kenan?" Murmushin takaici yayi "da kinsani da kinbar pretending saboda nariga nasan komai, everything" "pretending kuma? Ni bansan abinda kake magana akai ba" "really? Kenan kin manta da wanda aka ajiye maganarku dashi tare?" "mene? Aka ajiye maganar me?" tafada in confusion "maganar aurenku, kina sonshi, keda kanki kika kawoshi wajen dad dinki aka kuma ajiye magana akanku, ko shima kin manta" yafada zuciyarshi na quna "what? This is crazy! Yaushe aka badani bansaniba? Murmushin takaici kawai yayi ya kauda kai "Tambayarka nakeyi Deen, waya gayamaka haka?" "wanda bazai ta6a yimiki qarya ba, so is better kibar pretending" yafada cikin qunar zuciya "Daddy?" Juyowa yayi ya kalleta da idanunshi da haryanzu basu washe ba saikuma ya kauda kai Dafe goshi zee tayi kawai tayi shiru Saikuma ta dago ta kalleshi "dame dame ya gayamaka?" "dama akwai wasu abubbuwan da be gayamin ba?" yafada cikin qaryewar zuciya yana kallonta kamar zaiyi kuka Jin tayi shiru batace komai ba Saima kallonshi datake itama yasa yace "don Allah ki gayamin, zanfi son inji daga bakinki bawai daga wani wajeba, qila zafin bazai kai yadda zanji ba idan nayi discovering Hakan a bakin wani" Sosai yabata tausayi Hakan yasa wasu hawayen sake taruwa a idanunta "dagaske ne kina sonshi kuma an tsaida maganar ku? Yaushe ne Hakan ya faru? Kafin muhadu ko kafin mufara soyayya ko bayan Hakan? Don Allah ki bani wadannan amsoshin ko zan samu rintsawa yau" Kauda kai tayi tana dauke hawayenta dasuka kusan gangarowa "ba Gaskiya bane, tunda nake ban ta6a soyayya ba sai akanka kuma bazan ta6a sharing soyayyar ka da wani ba" Dukda be yarda ba Amma kuma yaji sanyi, yaji zafin zuciyarshi ta dan ragu "amma ai bazai yimiki qarya ba" "zai iya komai don ya rabamu" Kallonta yayi cikin tashin hankali "ya rabamu, dama yasan da maganar mu" Dagowa tayi ta kalleshi "yasani, sosai ma bama shikadai ba, harda mummy" Shiru yayi yana kallonta da mammaki _*shiyasa nazo wajen ka, please ka jawo ra'ayinta akan Hakan tunda naji ance kai abokinta ne, kana iya abinda ya gagaremu ka kuma samata ido kaga ko wani ke zugata don ni nafi tunanin Hakan*_ Girgiza kai Deen yayi bayan ya gama tuno wadannan kalaman na daddy "anya Zainab daddy yasani kuwa? I don’t think so" yafada yana girgiza kai Dan murmushi tayi sannan tace "meya fadamaka? Ka gayamin" Shiru yayi kamar bazai gayamata ba sai kuma ya sauke Ajiyar zuciya ya shiga labarta mata yadda sukayi da daddy jiya daddadare Dan murmushi zee tayi mai ciwo sannan tace "kasan abinda yayi?" Girgiza kai Deen yayi ahankali batareda yace komai ba "warning dinka yayi indirectly akan ka rabu dani" Tsayawa yayi kawai yana kallonta yana jujjuya maganar ta "Deen daddy beson tarayyarmu, duk hanyar danasan zanbi na fahimtar dashi nabi amma yaqi fahimta ta, I tried and am still trying amma banganin alamun nasara, bansan ya zanyi ba kuma" tafada qara tsane idanunta "naqi fada maka ne don banaso hankalinka yatashi, a ganina komai zai zama daidai kafin ka ankara, bansan zaije yasameka ba" "don Allah ki fadamin abinda ke faruwa, komai. Karki ragemin komai, don Allah" inji Deen Shiru tayi hawaye na cigaba da sauko mata batareda tace komai ba "Zainab ki tuna wannan abin mu biyu ya shafa, be kamata ace daya na cikin duhu ba, don Allah ki taimaka ki gayamin" yafada pleadingly Cije lower lip dinta tadanyi sannan tafara bashi labarin duk abinda yafaru, daga zuwan Asaad har zuwa rashin amincewar daddy akan za6inta da dalilin haka, tiryan tiryan tabashi labarin komai har zuwa yanzu dasuke zaune Shiru wajen ya dauka na wani lokaci _*ka nusar daita sosai, idan ma kaga alamun zugata akeyi let me know, sai na tabbatar na koyawa munafukin hankali don na tsani munafurci kana gani na nan, duk yadda muke da mutum daya munafurceni to wlh nagama dashi kuma zamu sanya kafar wando daya ne dani dashi*_ _*ta yiwu wani ko wata ke zugata yana dorata a keken 6era da nufin kaita yabaro*_ Ajiyar zuciya Deen ya sauke, sai yanzu duk ya gane inda magangganun daddy suka dosa Tabbas warning ne, warning yake mashi indirectly amma shi yakasa ganewa, to dama tayaya zai gane bayan besan komai ba gameda abinda yake faruwa? Babu makawa shine daddy ke nufi da yana zugata yana huremata kunne yana so yakaita ya baro. "Deen kar Hakan ya dameka, wannan abin duk yayisu ne don be fahimceka ba, amma ina ji ajikina watarana zai fahimta, very soon" Dagowa yayi ya kalleta "Zainab daddy yanada Gaskiya, yafimu hangen nesa tunda gashi ya hango abinda duk bamu hango ba, Ya hango future dinmu. Zainab akwai banbanci sosai a yanayin rayuwar da taki, ke kinsaba da akwai, kin saba da wadata a kodayaushe Yayinda ni a nawa bangaren ba Haka bane, mu abu biyu muka saba dashi, samu da rashi" "Deen kaima kasani, ni kai nakeso ba abinda ka mallaka ba ko zaka mallaka, kaine farinciki na, farinciki yafi gold and sliver" "Zainab, abin saukin fada gareshi a baki Amma wuya a experience, ina sonki zee, soyayyar da babu sirki ko kadan aciki, ba don komai naki ba Zainab kuma ina iyayin komai don na faranta miki amma Tambayar anan shine zaki samu farinciki a duniya ta? Duniyar da babu bushasha babu ababen more rayuwa kamar wanda kika taso aciki? Zaki iya zama a irin gidan danake zama? Zaki iya cin irin cimarmu, zaki iya shan ruwanmu? Zaki iyasa irin suturarmu? Zaki iya?" "Zan iya, kuma fa mutane ne kuma kuna rayuwa da duk abubbuwan daka lissafomani naku cikin farinciki. Rayuwa a kango tareda kai kamar rayuwa ne acikin mansion mai cikeda kayan more rayuwa Rayuwa batareda kai ba a mansion kamar rayuwane acikin kango Deen. Ina sonka a yadda kake kuma zan iyayin komai a dalilin son ka, zan ci cimarku zansha ruwanku nakuma saka suturarku don wata rana ba kasancewa zanyi babu ci babu sha Saidai ni nazama cima ga wasu hallitun, namana yazama abincin wasu qannanun dabbobin, suturata kuma daya ce ta Gaskiya wannan farin kyallen, so why zance bazan iya Hakan ba Tun a duniya, idan ban iya yiba a duniya zanyi don dole idan na mutu" Kallonta yakeyi yana jin qaunarta na hudamashi koina na zuciyarshi "nidai kawai sonake kayi min alqawari cewa baxaka ta6a barina ba no matter what, kowanne abu yanada qalubalenshi, wannan yana daga cikin qalubalen soyayyar mu kuma zamu tsallake da taimakon juna" "Zainab bazan ta6a barinki ba duk rintsi, zan jajirce a soyayyarki babu gudu babu ja da baya, insha allah zamu tsallake wannan qalubalen dama duk wanda zaizo a gaba dukda bama fatan Hakan" Bude hannu tayi ta miqo mashi tana kallonshi "promise me, promise you'll never break my heart" Kallon hannun nata yayi sannan shima ya dora nashi hannun asama suka damqe najuna Shima yana kallonta cikin ido yace "I promised, I promised I'll never break your heart, never!"... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:38 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *048* *THE PROMISE 2* Sun dade suna tattauna yadda zasu 6illowa al'amarin, da yadda zasu samu shawo kan dukkan muhinmman mutanen da zasu buqaci amincewarsu a wannan tafiyar tasu. Sai a sannan zee ta yarda da wannan karin maganar ta bature na *a problem shared is a problem solved* Sai gashi abin yayi juye yazama mai sauqi agaresu, ita datake 6oyewa don karya shiga damuwa sai gashi saninshi yakawo masu mafita Basu tashi school din ba sai wajajen 3pm kuma kamar yadda yasaba shi ya rakota mota yakuma bude mata kofa tashiga. Yana jin idanun bala akanshi yana kuma lura da kallon dayake binshi dashi amma ya share don he's ready for everything. Yana tsaye yana kallon motar yana daga mata hannu har suka fice daga school din. Ajiyar zuciya ya sauke yana jin wani qwarin gwiwa a zuciyarshi, yes he'll fight for his love, insha allah bazai gaza ba. Shima fita yayi ya samu abin hawa yahau shima ya kama hanyar unguwarsu. *** Da sallama yashigo gidan hannunshi riqe da cazbaha, forehead dinshi kuma da alamar qasa alamun daga sallah yake Kaka dake zaune a tsakar gida bisa tabarma saboda zafin da akeyi ta amsa sallamar shi Qarasowa yayi ya cire takalminshi shima ya zauna gefen kaka yana sauke Ajiyar zuciya "ya dai?" inji kaka "na gaji" yafada yana yatsine fuska "kamar wanda yayi wani aiki?" Murmushi kawai yayi bece komai ba Shiru Wurin ya dauka sai kuma ya matso gaban kaka yana tayata tsintar waken datakeyi "Kaka?" Dagowa tayi ta kalleshi "na'am" Sai kuma yayi shiru yarasa ta ina zai fara "ya kuma kayi shiru? Wani abu?" inji kaka tana kallonshi cikin kulawa Murmushi yayi saikuma ya rufe fuskarshi da taffukan hannunshi "Tofa? Meye kuma haka kakeyi kamar wata amaryar qauye?" Dariya Deen yayi yana cewa "kai kaka" Itama dariyar tayi tace "ai Gaskiya ne, kana wani rufe fuska kamar gaban surukarka" Murmushi yayi yace "kika sani ko gwada yadda zanyi agaban surukar tawa na keyi?" Dariya kaka tayi "kuma fa, to ai sai kabari kafara yin surukar sannan" Murmushi yasakeyi "Kika sani ko nayi din" "Me din?" "surukar" Wani kallo tayimashi ta cigaba da abin take tana cewa "ahakan?" Gyara zama yayi cikin zumudi yace "Allah kaka" "Allah me?" Sai kuma ya sake rufe fuskarshi "nayi maki suruka" Tsayawa tayi tana kallonshi babu kyaftawa Jin shiru yasa yadan leqo a tsakankanin yatsun dake fuskarshi Janye hannun yayi daga fuska ya kalleta "bakice komai ba" "yo aini ban gane ma inda ka dosa ba" tafada still tana kallonshi Yar Dariya yayi sannan yace "to kawo kunnenki kiji" Da sauri kau ta miqa tana murmushi Rada yashiga yimata a kunne sai naga idanun kaka sun qara budewa "iyee! Wai dagaske!" tafada unbelievably Sake rufe fuska yayi yana Dariya Tashi tayi babu shiri tana rangada gud'a "Ayiririririririririririririririririiiiiii! Kai amma allah na gode maka, kace me?" tafada cikin tsananin farinciki "kai kaka Kiyi ahankali kar ajimu a waje" "a jimu a wajen, Ayiririririririririririririririririiiiiii!! Wannan ai abin son kowa yajine, abin alhairi? Kai amma allah na gode maka, iyee! Kai dole ma nayi sujjadar Godiya ga allah " Sai tayi qasa ta kai goshinta qasa Deen dai kallonta yake kawai fuskarshi beaming with smile Saida ta dago sannan ta cigaba "Allah ya tabbatar da alhairi kyakyawana, kyakyawana zaiyi aure, kyakyawana yasamu wacce yakeso, kyakyawana ya girma, ashe da rabon zanga bikinka kyakyawana, da rabon qila zanga 'ya'yanka" Sai kuma ta fashe da kuka tana rufe fuskarta da ha6ar zaninta Dariya Deen yayi "kai kaka, kuka kuma?" Dagowa tayi ta kalleshi cikin kukan tace "dole nayi kuka, dole ne 😭" Dariya yasake yi don shi Dariya ma ta bashi Saida tayi mai isarta sannan ta koma ta zauna ta fuskanceshi dakyau tana maida tray din waken dasuke gyarawa baya tace "to yanzu gayamin wacece surukar tawa? Wace yar albarkar ce mai sa'ar kyakyawan sardidin jikan nawa" Dariya yaqara yi zuciyarshi qall "kai kaka" "eh mana, ai duk macen datayi sa'ar samunka to tagama dace a duniya saikuma ta nemi lahira, ba cika baki ba jikana namiji ne daya tamkar dubu, ga kyawun hali ga kyawun fuska Kamalele kamala, kamaladini mai kamala takoina, fari mai farin aniya! Gayamin dan sardidin kyakyawana Wace santaleliyar tayi sa'ar duniya wajen za6enka?" Dariya Deen keyi sosai tunda tafara maganar don yana jin dadi idan kaka na mashi kirari "wannan kirarin duk nikadai kaka?" "ai ka cancanci fin haka dan kyakyawana, Gayamin wacece?" "ai kinma santa kaka?" "to? Ba mammaki kau amma dai gwara ka fadamin nasan ko ainahin wacece" Murmushi Deen yayi "Aminiyarki ce kaka" "Aminiyata kuma?" tafada cikin rashin fahimta "eh, Zainab" "Zainab.. Zainab.. Zainab" tafada cikin son tunano mai sunan "kai kaka Gaskiya kinfara tsufa wannan mantuwa haka? To Zainab yar makarantarmu dinnan, diyar mummy wadanda muka zauna asibiti dasu" Wara idanu kaka tayi "wacece? Kana nufin wannan Zainab din?" tafada tana waro idanu Murmushi yasake yi "Ashe kin gano? To ita" Ahankali fara'ar kaka tafara ragewa a fuskarta mammaki ya maye gurbin murnar Ganin wannan chanjin yasa shima fara'arshi ragewa "yadai kaka?" "bakada hankali ne? Wace yarinya kake nufi? Wannan diyar masu kudin?" ta tambaya still a mammakince "eh kaka ita din" "a wane duniyar mahaukatan Hakan zai yiwu? Ko kai bakasan kosu waye ba?" Murmushi yayi yace "Kaka nasan kosu waye mana, ai ba wannan ne abin dubawa ba hallarcin Hakan za'a duba" Sakato tayi tana kallonshi "to don kai kana sonta cemaka akayi zata soka ne?" Murmushi Deen yaqara yi sannan ya matso kusa ya kama hannayen kaka ya riqe "mezai hana taso ni kaka? Maganar ma damuke yanzu su daddy da mummy duk sunsan da zancen" Sakin baki kaka tayi tana kallonshi kamar yau tafara ganinshi tama kasa cewa komai Sakin hannunta daya yayi yadanyi waving a fuskarta "kinyi shiru kaka" "dole inyi shiru kyakyawana, ka tabbatar da abinda kake cewa kuwa" "wlh kau kaka na tabbatar, wlh duk sunsan da maganar" yafada cikin zumudi "ikon allah" inji kaka cikin mammaki saikuma taji kaso sittin na cikin murnarta yabi iska Qara ruqo hannayenta Deen yayi sosai yace "to kaka ya naga baki murna kuma?" "ai kyakyawana abin ne yazo min wani iri, anya kau baka debo da zafi ba?" Qara damqe hannunta yayi "haba kaka, komai mai yiwuwa ne muddin allah be haramta ba" "hakane, amma sai inga kamar yarinyar tafi qarfin ka, bakaga daga gidan data fitoba? Ya zakayi daita?" Dan murmushi yayi "kamar ya yaya zanyi daita kaka?" "Ato ai dole nace haka, yarinya tasaba da akwai, ga cima mai rai da lafiya kullum cikin wadata take ya zakayi daita idan ka aureta? Wai ita ma tace maka ta amince dakai ko kuwa?" "eh kaka, nima tana sona kuma ta amince ta zauna dani akowanne hali, tana sona sosai tsakani da allah" Shiru kaka tasake yi sai kuma tace "to iyayenta fa? Sun amince suma?" "eh mana kaka, duk sun amince, duk sun yarda" Yafada yana murmushi yana kallonta yanason yaga fara'arta ta dazu tadawo "ikon allah, to allah yaza6a Mafi alhairi, allah ya tabbatar da alhairi" tafada incheerfully "to amma kaka yanaga bakya murna irin na dazu?" yafada yana 6ata fuska "ina murna mana, ina murna sosai, kawai dai ina fargabane kar muna zaman zamanmu mujawoma kanmu matsala" tafada tana jawo tray din waken ta cigaba da tsinta "insha allah kaka babu wata matsala, ki tayamu da addu'a kawai" yafada shima yana saka hannu a tsintar "to allah ya tabbatar da alhairi, ai addu'a muna yimuku kullum kuma zamu cigaba dayi" "yauwa kaka ta" yafada suna cigaba da tsintar yana cigaba dayi mata firar zee Itadai sauraronshi kawai take amma kwata2 hankalinta yaqi kwanciya da za6in nashi, ba don batayi mata ba sai don fargabar faruwar abinda bata shirya mashi ba kuma bata fatan ya lokacin ya riskesu nan kusa har abada. *ZEE* A bangaren zee kuwa sai bayan dinner taje tasamu mummy har daki don yanzu don dole mummy tazama makusanciyarta saboda ra'ayinsu dayazo daya. Anan ne tasamu mummyn ta zauna ta fadamata duk yadda sukayi da Deen da safe dakuma yadda daddy yaje wajenshi jiya. Ajiyar zuciya mummy ta sauke sannan ta kalli zee tace "Zainab, Gaskiya wannan maganar tawuce duk yadda kike tunani, ni aganina gwara kawai ku haqura da juna saboda Gaskiya daddy bada wasa ya dauki maganar nan ba" Gaban zee ne yafadi "mummy... Na haqura dashi kikace?" tafada cikin rawar murya "qwarai Zainab saboda Gaskiya wannan al'amarin ba qaramin al'amari bane, dukda daddy be fahimci wasu abubbuwan ba shima ta Wani bangaren yanada Gaskiyarshi akan wannan al'amarin don idan kika tsaya kika natsu kika duba zakiga duk wannan abin dayakeyi duk saboda ke yake yinsu, he's making sure kar ayi abinda baza'azo ana regretting nan gaba ba. Shi aure babban al'amari ne idan babu sanyawar albarka daga daya daga cikin iyayen both macen da namijin abin na iya juyewa yazama something else don haka Kiyi hqr kiyita addu'a idan kamal dinne mafi alhairi a wurinki to allah ya ganar da daddy idan kuma bashi bane allah ya za6a maki Mafi alhairi, insha allah zaki samu mai sonki sosai wanda zai Mafi kamal din sonki" Tashin hankali!! Kuka zee tafashe dashi sai gata on her knees "Mummy please, karki ce haka. Ke kadai ce last hope dina please karki karaya, karki karya min gwiwa please. Wlh Deen shine Mafi alhairi gareni please don't say that" Sakin baki mummy tayi ganin yadda ta rude lokaci guda "meye haka Zainab?" tafada a mammakince "mummy don Allah karki bar bayana, please... We can do it, we can convince daddy, don Allah karki ce na haqura da Deen, bazan iya ba" saikuma ta zauna ta Hade kanta da gwiwa ta cigaba dayin kuka, idan mummy ta bar bayanta ya zatayi? She's her last hope. "haba Zainab, saboda namiji zaki zauna kina irin wannan abin kina kuka? Inji dai bake ke forcing kanki agareshi ba?" Dagowa zee tayi fuska sha6e2 da hawaye "mummy wlh A'a, shima yana sona, bani ke cusa kaina ba, he loves me more than I do to him" "then sai Kiyi hqr ki tsaya kiga yadda allah zaiyi daku, idan da rabon ku mallaki junanku zakuyi Hakan idan kuma babu babu yadda kuka iya dole ku hqr da juna. Shi musulmin qwarai da tawakkali aka sanshi da kuma daukar qaddara" Kasa cewa komai tayi sai cigaba da sobbing datayi "kije ki cigaba da addu'ar za6i na alhairi don kuka won't change anything da yanayi da mutane da dama bazaki gansu da damuwar komai ba. So is better ki riqe du'as don shikadai zai taimakeki nima zan tayaki kuma zan sake yimashi magana nima bawai na karaya bane kawai dai sonake na fahimtar dake ba kowanne abu da ka qwallafawa rai kake samu ba, kinji ko?" Kada kai kawai tayi ahankali cikin matsar hawaye "Good, yanzu tashi ki tafi and wipe your tears don basuda amfani, what matters most is du'a" Qara Kada mata kai tayi sannan tashare hawayenta ta tashi tana jin kamar jiri zai kwasheta "Don't worry kinji zan sake mashi magana insha allah zai fahimta" tafada cikin son qara kwantar mata da hankali Qara kadamata kai zee tayi sannan tayi mata sallama ta fita Binta da kallo mummy tayi cikin tausayawa saikuma ta girgiza kai ahankali ta cigaba da abinda takeyi. Tana shiga dakin tayi wajen gadonta da gudu ta fada akai. Sauran kukan da bata ida a dakin Mummy ba ta cigaba dayi Jitayi kamar ta riga ta rasa Deen din ma Wannan wane irin abu ne? Ko kadan bata ta6a kawoma ranta zata samu matsala irin wannan a soyayyarsu ba Tariga ta dogara da maganar daddy na bazai mata dole ba duk wanda takawo zai kar6a hannu bibbiyu, bata ta6a tunanin banda talaka ba ko dayake ita kanta idan aka gayamata zata so talaka a lokacin qaryatawa zatayi, kawai lokaci daya ta makance a soyayyarshi makantar da bata tunanin zata ta6a bude ido nan kusa. Aunty Feenah ce tafado mata arai, sotake ta kirata ta gayamata komai ko zataji sauqin abinda takeji ko kuma tabata shawarwaru kamar yadda tasaba Amma saita tuna basama qasar, tun bayan wata daya da auren suka shilla honeymoon gashi batada number ta tacan kuma Koda tanada ita bekamata ta kirata ba a irin wannan lokacin ba, be kamata ta takura masu ba Suna tsaka da cin amarcinsu. Ringing din wayarta ya katse ta daga tunane tunanen datakeyi Wani sanyi taji a zuciyarta tun kafin ma ta duba mai kiran. Ganin zata tsinke yasata saurin dauka ta daga kiran ta kara phone din a kunne bayan tayi iya qoqarinta na gyara yanayin ta don batason ya fuskanci halin datake ciki ko kadan batason ta saremashi gwiwa shima. Saida suka gaisa sannan Deen cikin zumudi yashiga gayama zee yadda sukayi da kaka da amincewarta 💯 harda qarin maggi da gishiri a labarin don yaqara bada armashi. Nan take zee taji duk damuwar ta ta yaye itama tashiga murna Sun dade suna firarsu kamar basuda wani problem a rayuwa sannan suka rabu dakyar ba don sun so ba sai don barcin daya addabi idanun kowannensu Sallama sukayiwa juna akan sai gobe idan sun hade a makaranta sannan suka katse kiran kowanne zuciyarshi wasai Babu dadewa duk barci ya kwashesu mai cike da mafarkan juna Kingin ranakun dasuka biyo baya sunzo very smoothly for the two lovers Kwata2 sun manta da damuwarsu sun dauki damuwarsu sun ajiyeta a gefe sun cigaba da gudanar da soyayyarsu tsabtataciyar cikin salo na burgewa da ban sha'awa. Soyayya suke bugawa wacce tafi ma tada, irin soyayyar nan mai tsayawa a rai kamar zane akan dutse wanda baya ta6a goguwa. Basuda damuwar komai idan ma suna da ita to qila sun manta da ita don kwata2 basama kawota a jadawalinsu sam, rayuwarsu sukeyi kamar dama subiyu ke a duniyar basa tunawa da komai da kowa. A bangaren iyayen kau abin dai babu yabo ba fallasa za'ace, haryanzu daddy shiru yayima biris da zancen Haka ma mummy bata qara tada zancen ba Kaka ma ba laifi amma bawai ida Sakin jiki tayiba da wannan relationship din nasu ba don haryanzu hankalinta be ida kwanciya dashi ba Taso ace Deen yasamo daidai shi ko don kaucewa matsala anan gaba, matsalar da basusan iyakar ta ba Amma ganin yadda Deen ya saki jikinshi dakuma yadda yake nuna tsananin qauna akan Hakan yasata 6oye damuwar ta ta cigaba da binsu da addu'ar za6i na alhairi. Everything was going smoothly kwatsam wata rana zee na Kwance daki waya a kunnenta taji an banko kofa anshigo a fusace. Saurin juyowa tayi cikin mammaki sai ganin daddy tayi kamar an jefoshi dakin sai suraci yake. Saurin tashi zaune tayi zumbur batareda tama tuna Da katse kiran dasukeyi ba. "daddy?" tafada ahankali tana kallonshi da kuma mummy datake bayanshi daga bakin kofa Da yatsa daddy ya nuna zee "wato ke bakya jin magana ko? Duk abinda nake gayamaki ta kunnen dama yake shiga yafita na haggu ko? Dama bakida hankali bansaniba?! Ina nunamaki hanya kina rufe ido! Kinje kina biyewa wancan dan iskan yaron ya huremaki kunne ya bushe maki idanu bakya ganin kowa da mutunci ko?!! Eh! Kullum kinacan banda qara liqemashi babu abinda kikeyi ko? And itama Good for nothing uwarki babu abinda takeyi sai goyon bayan ki ko?!!" Sosai zee ke kuka ganin yadda daddy ya burkuce mata sai tsawa yake mata abinda be ta6a ba "daddy don Allah kayi hqr wlh ina sonsh.." "will you shut that your dirty mouth up! Are you stupid! Ina maki magana kina yimin zancen banza zancen wofi!!" Yadda ya hayyayaqomata kamar zai maketa yasata saurin yin baya ta zauna kan gado tana shigewa jikin frame din gadon tana wani irin kuka cike da tashin hankali. "harni zaki fadawa soyayya?! Ni zaki fadawa kina sonshi! Soyayyar banza soyayyar wofi?! Soyayyar dakike mashi yakai wacce nake maki ne! Soyayyar da yake maki takai kwatar wanda nake miki?! Wato ni kuka maida shashasha ma ashe, ni inacan ina haukana ku kunacan kuna abinda kuka ga dama babu abinda ya dameku" "am disappointed in you Zainab, very disappointed. A tunanina Koda ban kawo maki hujjar komai ba na hanaki kula wannan yaron haka kawai zaki rabu dashi ko don farincikina kamar yadda nasha sadauqarda farincikina saboda naki. Amma da hujjata da komai kuma duk abinda nakeyi akanki nakeyi don kar rayuwarki ta tagayyara amma shine zaki debo qasa ki 6ullamin a idanu, kin mance da soyayyar danake miki kin manta da qaunar danake miki kin fita harkata duk saboda wannan kwadayayyan yaron, duk saboda dadin bakin dayayi miki ko!!" Kada kai yayi yana murmushin takaici "to wlh bazai yiwuba, zan dauki mataki, mummuna kuwa akanshi, tunda nabishi ta girma da arziqi bejiba, I'll have to show him my true colour, don haka daga yau karki qara fita daga gidannan kije koina, ko school na hana, zanyi maganinku ne wlh, shashashan banza!!" Yana kaiwa nan ya kada babbar rigarshi ya fice daga dakin kamar zai tashi sama itama mummy ba don tayi saurin matsawa ba da yayi gaba daita. Bin bayanshi mummy tayi da kallo harya fita yamaido masu kofar da qarfi. Maida kallonta tayi kan zee dake takure akan gadon haryanzu tanata kuka kamar zata shide Ajiyar zuciya ta sauke cikin rashin sanin abin yi sannan itama ta nufi kofa ta bude ta fita Qara fashewa da wani kukan tayi tana Hade kanta da gwiwa, sosai takejin wani zafi na ratsa kowanne lungu da saqon zuciyarta tana jin yadda take fidda hucin zafi. Zamewa tayi ta kwanta tana cigaba da kukan da tasan shi zai sata jin sauqin abinda takeji a zuciyarta. Bata san iya tsawon lokacin data dauka ahaka ba sai jitayi anfara kiraye kirayen sallar magrib Dakyar tasamu ta tashi tayi alwala ta gabatar da sallar Tana nan zaune aka fara kiraye kirayen isha'i nan ma ta tashi ta kawota tayi addu'o'i sosai akan allah yakawo masu mafita sannan ta tashi ta koma kan gado ta kwanta tana jin yadda kanta ke saramata. Duk yadda taso yin barci kasawa tayi don kwata2 barcin ya qauracewa idanunta ga wani irin ciwo da kanta ke mata na kukan datasha. Wayarta ta laluba ta kunna sai taga duration din wayar dasukayi da Deen ke samar screen din wayar. Lissafi tayi da lokacin dasuke wayar da lokacin da daddy yashigo saita ga ashe ma bata katse kiran ba bayan shigowarshi, Saida aka qara 10mins kafin kiran ya tsinke wanda cikin dayan biyu ne, ko shi ya katse ko kuma kudinta ne suka qare, idan haka ne that means yaji duk yadda sukayi da daddy? Rasa mai bata amsar tayi sai kawai ta dannama number shi kira Saidai tun kafin aje ko ina taji ana cewa number datake kira bata shiga Qara bugawa tayi bayan wancan ya katse nan ma amsa daya ce, the number is not reachable. Kashe wayar gabadaya tayi ta tura qarqashin pillow ta koma ta kwanta tana cigaba da kukan zuci. Wannan wane irin abu ne da maimakon yaci baya sai qara cigaba yake? She can't believe yau ita daddy ya tsaya yayi ma tass haka, kuma ta tabbata da ta tsaya jayyaya dashi babu abinda zai hana ya wanka mata mari saboda yanayinshi kawai ya nuna yakai maqurar qurewa a 6acin ranshi Sosai fadanshi da barazanar shi na daukan mummunan mataki akan Deen ya tsaya mata arai, Hakan yasa bata wani samu isashen barci ba a ranar duk rabi da rabi tayi kuma marassa dadi. Washegari ta tashi da zazza6i, yau lahadi babu school gashi ta tashi da menstrual cramps wanda ke nuna alamun zata samu menstrual flow dinta a kowanne lokaci. Bayan ta samu tayi sallar asuba dakyar takoma kan gado ta kwanta ba don tana jin barci ba sai don she's too weak har a lokacin. Ta dade ahaka lamo kan gado can taji an bude kofar dakinta an shigo. Batasan ko wanene ba kuma bata bude idanu ba don ganin waye Jitayi anzo bakin gadon ta kuma ji alamun zama bisa bedside locker din wajen Dumin hannu taji a wuyanta Hakan yasa ta sauke Ajiyar zuciya ta bude gajiyayyun idanunta tana kallon mummy dake ta6a wuyanta "Are you sick?" inji mummy tana qara feeling temperature dinta Lumshe idanu kawai zee tayi batareda tace komai ba "tashi muje kici abinci kisha magani" Yamutsa fuska tayi zatayi magana mummy ta girgiza mata kai alamun karta fara saikuma taqara cewa "tashi mutafi" Babu yadda ta iya haka ta tashi dakyar tanajin kamar taita kuka. Saida tafara yin brush sannan ta dawo ta zauna don daga baya ma sama aka kawomata abincin. Ta danci da dan yawa bisa takurawar mummy sannan tabata maggunguna tasha harda na period dinta saboda ta mata complain din ciwon cikin. Saida ta shanyesu duka sannan takoma ta kwanta tana jin yadda kanta har lokacin ke harbawa Bata dade da kwanciyar ba barcin da bata samu yiba tun jiya ya dauketa. Lokacin da ta tashi har menstrual flow dinta yazo Hakan yasa ta tashi ta shige toilet don babu laifi tadan ji qarfi qarfin jikinta tayi wanka tayi packaging kanta sosai sannan ta dawo ta zauna gefen gado. Wayarta dake kashe tun jiya ta lalubo ta kunnata tashiga call log taqara buga number shi Saidai this time around sai sukace tana switch off. Komawa tayi ta jingina da frame din gadon ta lumshe idanu tana jin daci a ranta, this is the toughest time in her life. Aranar ko kofar dakinta bata fita ba abinci Saidai a biyo ta dashi daki kuma dole taci don mummy ke tsareta sai taci. Har dare number Deen bata shiga abinda be ta6a faruwa ba hakan yasa taji hankalinta yaqi kwanciya babu abinda ke fadomata arai sai kalmar daddy na saiya dauki mataki akai mummuna, Hakan ba qaramin samata fargaba yakeba a zuciya A daddafe dai tasamu gari ya waye. Tunda wuri tayi shiri don babban burinta shine taje ta ganshi a school ta tabbatar da lafiyarshi don jiya dashi ta kwana a ranta Saidai me Koda ta sauko saita nemi bala ta rasa Koda ta tambayi security sai cewa yayi be isoba har lokacin Komawa cikin gida tayi ta zauna a falo tashiga neman number bala amma bata shiga, tafi awa nan tana zaman jira amma shiru gashi ita bata iya driving ba. Ganin abin na neman zama rainin hankali sai ta tashi ta sake fita da niyyar samun adaidaita kawai tayi tafiyarta Saidai me firr security yaqi bude mata gidan wai daddy yabashi umarnin kar yabari ta fita. Sosai abin ya quleta Hakan yasa tashiga zazzaga mashi bala'i akan ya bude mata gidan tafita gidan na ubanshi ne? Saidai dik masifarta da hayaniyarta ko gezau securityn beyiba dama ta dameshi saiya shige dan dakinshi ya rufo kofa. Juyawa itama zee tayi tashiga cikin tana kuka sosai, Direct dakin Mummy ta nufa taje ta tardata tana yan lissafe lissafenta Fadawa tayi jikinta tana kuka sosai tana roqonta tazo tasa security ya bude mata gida Ajiyar zuciya mummy tayi tace "Zainab, bakiji abinda daddyn naki yace bane? Cewa yayi bazaki qara fita daga gidan nan ba Koda kuwa school zaki, Kiyi hqr kawai harya sauko" Kuka zee ta cigaba dayi "mummy am scared, tun shekaranjiya number Deen bata shiga, kar ace daddy yayi mashi wani abin" "babu abinda zaiyi mashi insha allah, kawai shawarar dazan baki yanzu itace kibar batun Deen for now, muddin kinason zaman lfy don daddynki ya dauki abin da zafi fiyeda tunaninki" Da wannan kalmar zee ta tashi ta koma dakinta ta kwanta ta tattakure waje daya kamar marainiya. Tun daga ranar farinciki ya kaura a rayuwar Zainab, tun tana attempting fita daga gidan ana hanata har ta haqura ta bar ma fitowa kwata2 daga dakinta. Kullum yini take cikin dakinta tana kuka babu abinda yafi daga mata hankali kamar jin Deen shiru har lokacin, yanzu sati daya kenan da faruwar Hakan amma haryanzu number shi is switch off, sosai Hakan ke daga mata hankali. Cikin wannan kwanakin sai gashi tayi wata ramar dole, sai acikin kwanakin taqara tabbatar da bazata iya rayuwa batare dashi ba don ita kadai tasan yadda takeji a yan kwanakinnan da bata sanyashi a ido ba kuma bataji muryashi ba. Ana haka ranar data cika kwana goma da faruwar komai tana zaune waya a hannunta ta lalubo number Deen ta tsaya ta kuramata idanu kawai tana kallo Kamar da wasa ta dannama number kira batareda sa ran zata shiga ba Kamar a mafarki kawai sai taji tafara ringing Wara idanunta tayi cikin mammaki bugun zuciyarta na qara gudu Saidai harta tsinke ba'a daga ba Hannu na rawa taqara bugawa tana miqewa tana jin kamar zuciyarta zata tsinke saboda bugawar datake Saida ta jera kira uku, ata hudun ne taji an daga Kasa cewa komai tayi sai rarraba idanun datake zuciyarta na mugun gudu "Zainab..." cool voice dinshi ta ratsa kunnenta Rufe bakinta tayi da tafin hannunta takoma ta zauna bisa gadon da6as "Hello? Zainab?" tasake jin Muryarshi nacewa Hakan Hawayene suka shiga taruwa a idanunta still takasa cewa komai "Zainab is this you? Please say something" Lumshe idanu tayi tana ba hawayen idanunta damar gangarowa "Deeen..." Sai kuma tashiga yin sheshekan kukan da batasan yazo mata ba "Zainab, are you crying? Please kibari kinji? Kar zuciyata ta buga, am ok kinji" taji yafada shima a cikin wani irin murya mai matuqar rauni "Deen ina ka shiga? Nakusan mutuwa saboda fargaba, meya faru da wayarka?" tafada cikin kuka "am ok zee, babu abinda yasameta kawai babu charge ne" yafada cikin son kwantar mata da hankali Girgiza kai tayi "No Deen, you're not ok, gayamin meya faru me daddy yayi maka" "babu komai Zainab, babu abinda yayi min, I love you and I'll never back off, no matter w..." Sai kuma taji shiru "hello? Hello! Deen! Kana jina?" tafada tana sake miqewa hankali tashe "eh yana jinki, mallama me kuma kike nema da jika na? Me kuma yasaki nemanshi?" Baki na rawa zee tace "k.. Kaka?" "eh nice, kaka ce. Nagode ma allah da kika gane Hakan, meye kuma kike nemanshi bayan duk abinda kukai mashi? Eh!" Kasa cewa komai tayi sai bakinta dake rawa amma takasa furta komai "to ahir dinki wlh, karki qara kiran yarona a waya, kifita harkar shi wlh don shima yariga ya gama dake dama ai qarfin hali ne irin nashi banda Hakan ai ke ba kalar matar dazai aura bace.." Muryar Deen taji daka can baya yana kiran sunan kaka Muryar kaka taji tana cigaba da cewa "menene? Menene kake hanani magana? Kabari nayi mata wonin Kina jina? Wlh ki fita harkar jikana kina jina ko? Mu ba kowan kowa bane bamuda wadanda zasu tsaya mana idan kika jefamu a chakwakiya, muna zamanmu ne cikin rufin asirinmu da wadatar zuciya, muna zamanmu cikin farinciki don Allah karki tarwatsa mana shi, don Allah ki kyalemin yaro kije kema allah ya hada ki daidai ku masu kudi muma haka, mun gode da duk dawainiyar dakukayi mana da qaunar da kuka gwadamana amma dan allah karki sake nemanmu, ba don mu ba don Allah" Kittt.... Taji an katse kiran Ahankali ta Saki wayar hannunta ta fadi sannan itama ta zame ta zauna kan bedside locker tana kafe waje guda da ido... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:38 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *049* *THE ACCEPTANCE* Maida kanta tayi baya ta jinginashi da bangon bayanta tareda lumshe idanunta Ita kadai tasan abinda cikin, duk yadda zata musaltashi bazai misaltu ba. Ta dade sosai ahakan sannan ta bude idanun ahankali ta qurawa saman p.o.p. Din dakin idanu. Batasan iya lokacin data dauka ahaka ba sai jitayi ana bubbuga kofar dakin Maida idanun tayi again ta lumshe batareda ta Ko motsa ba. Bude kofar akayi mummy tashigo Ganinta zaune akan bedside tana kallon sama yasata ida Qarasowa dakin "Zainab?" Bata motsa ba bare ta nuna alamun taji Ida Qarasowa tayi tadan bubbuga mata kafada "ke Zainab?" Sai a lokacin ta bude idanunta dasukayi jawur sannan ta sauke kanta qasa tana cije lower lip dinta "lfy?" inji mummy tana kallonta Girgiza kai kawai tayi ahankali batace komai ba "ki bude baki kiyimin magana mana" Ahankali ta bude bakin cikin muryar da ita kanta batasan tanada ita ba tace "lfy lau" Tsayawa mummy tayi tana kallonta, sosai take bata tausayi amma ya ta iya? Ita kanta daddy fushi yake daita bayama mata magana bare ace zata iya wani abu akai "kinci abinci?" ta tambayeta a tausashe Kada kai tayi saikuma ta qara bude baki tace "eh" "Good yanzu ki tashi kiyi sallah kinga anfara kiraye kiraye" "to" tafada ahankali "tashi to" inji mummy tana dan ja baya don bata damar tashi Ahankali ta dafa gefen bedside locker din ta tashi tsaye saikuma tayi baya zata zube mummy tayi saurin tarota "subhanallilah! Are you ok? Jiri kikeji?" Qoqarin miqewa tsaye tayi tana girgiza kai ahankali Saidai ta kasa tsayawa "zauna, zauna anan" inji mummy tana kaita gefen gado Zama tayi takoma ta jingina da gadon tana sauke Ajiyar zuciya "bakida lfy ne Zainab?" Idanunta a lumshe ta girgiza kai tana sauke numfashi ahankali "jiri kikeji?" Ahankali ta Kada kai "sannu, bari naje na hadomiki tea kisha saikisha magani ki kwanta anjima kyayi sallar" tafada cikin tausayawa Itadai zee batace komai ba kuma bata bude idanun ba sai sauke numfashin data cigaba dayi ahankali. Ahaka taji alamun fitar mummy Wasu hawaye ne suka kufto daga rufaffun idanun suka gangaro, batayi qoqarin hanasu gangarowa ba don itama tana da buqatar zubdasu Hakan yasa tabasu damar zuba iya son ransu. Bata san dawowar mummy ba sai jitayi an dafa kafadarta Bude jajjayen idanun tayi ahankali ta kalli mummy taga itama mummyn kallonta take "menene kuma Zainab?" Sauke idanunta tayi a qasa sannan ta girgiza kai ahankali "Wani abu yafaru kuma?" Sake girgiza kai tayi ahankali wasu hawayen nasake zubowa Ajiyar zuciya mummy ta sauke sai ta ajiye mug din tea din hannunta ta zauna kusada ita "Zainab komai yayi zafi maganinsa allah, don Allah kibar takurawa kanki haka, insha allah komai zai warware, komai zai zama tarihi" tafada cikin sigar rarrashi Itadai batace komai ba kuma batayi motsiba "ki zama mai daukar kaddara Zainab walau mai kyau ko akasin haka, kibar sama kanki damuwa arai Hakan na iya affecting lafiyar ki, Kiyi hqr kinji? Insha allah idan kamal mijinki ne babu abinda zai hana ki aureshi amma idan kika cigaba da sama kanki damuwa komai ma na iya faruwa" Haka taita yimata nasiha, Itadai zee nata saurare batace komai ba har tayi ta gama Tea din tabata tasha sannan ta bata magungguna suma ta sha sannan tasata kwanciya yadda maganin zaiyi aikinshi yadda anjima zata tashi da qwari qwarin jiki. Kwanciyar tayi Saidai ko kadan barci be nufo idanunta ba Haka taita kwanciya har mummy tasake dawowa dakin Da taimakonta ta tashi tayi alwala tayi sallah sannan ta sake tilasta mata tadanci abinci sannan ta koma ta kwanta. Haka ta qarasa Wunin nan rabi a Kwance, sosai jikinta ya saki tanajin batada qarfi ko kadan. Da daddare ma Dakyar tasamu wani barci marar dadi ya dauketa can cikin dare. Washegari da wani zazzafan zazza6i ta tashi, jikinta yayi ringis sai fidda hucin zafi yake. Lokacin da mummy tashigo don tadata rikicewa tayi ganin halin da ta tararda Zainab. Babu shiri tafita ta nufi part din daddy gudu gudu sauri sauri. A falo ta tarar dashi zaune sanye da brown jallabiya yana qoqarin Kamo tasha Ganin yadda tashigo a rikice yasashi dakatar da abinda yakeyi yana kallonta da ayar tambaya "Alhaji zoka gani, Zokaga halin da Zainab ke ciki" Gaban daddy yafadi Hakan yasa yayi saurin miqewa tsaye yana Sakin remote din hannunshi "meya faru? Meya sameta?" yafada yana yin gaba batareda ya tsaya jin amsoshin tambayoyinshi ba Maramashi baya itama tayi suka fito daga part din Kusan lokaci daya suka sake Shigowa dakin nata inda take Kwance yadda mummy tabarta. Da sauri daddy yayi bakin gadon ya zauna yana kamo hannun Zainab din Jinshi rauu da zafi yasashi wara idanu a rikice shima "Daughter? Daughter! Innallilahi waina ilaihi rajiun" yafada yana dorota jikinshi Kallon mummy dake tsaye itama gefe hankali tashe yayi yace "wai meke faruwa ne? Meya sameta?" Jitayi Tambayar ma tabata takaici sai tace "ka fini sanin meke faruwa, idan kayi sanadin rasa yar dayar da allah yabamu ai sai kowama ya huta" tafada hawaye na cicciko idanunta Maida kallonshi yayi akan zee dake sauke numfashi mai zafi ahankali tama kasa bude idanu tsabar yadda takejin jiki Wayarshi yayi saurin lalubowa a aljihu yashiga kiran family doctor dinsu Ba'a daga ba a kira na farko ba sai ana biyu Sallama Dr yayi daga dayan bangaren "Dr ba lfy, ga daughter na nan in a critical condition, I badly need your help" Cikin rikicewa shima Dr a dayan bangaren yace "innallilahi waina ilaihi rajiun! Meya sameta? Ganinan zuwa yanzu" "No, bari muzo, bazamu iya jira ba muhade a hospital kawai" "ok.. Ok sir, nima yanzu zan kamo hanya saikun iso" Katse kiran daddy yayi ya kalli mummy "maza dauko mata hijab dinta" Da sauri Mummy ta bude closet dinta ta ciro mata yar madaidaiciyar hijab dinta da taimakonta dana daddy suka samata sannan daddy ya tashi daita ajiki ta tallabeta kamar ya dauki jaririya. Daddy ne agaba mummy abaya kallo daya zakayi musu kasan a mugun rikice suke A back seat ya shimfidar daita mummy tashiga itama ta dora kanta a cinyarta sai daddy yakoma mazaunin driver ya bude yashiga yana danna uban horn tun kafin ma ya ida zama sosai A rikice security yafito, Ganin an tada mota yasa ya tsaya yana kallon motar dazata juyo don ganin su wanene Hango daddy dayayi a mazaunin driver dakuma nuni dayake mashi na ya bude masu gate yasashi rugawa da gudu ya shiga wangale masu gate din. Da gudu daddy yaja motar suka zo suka fice suka halba titi. Sosai daddy ke tsula gudun tsiya akan titi donma gari be ida wayewa ba babu motoci sosai akan titin Cikin dan qanqanin lokaci suka isa inda kusan shigowarsu tareda Dr din. Da sauri Dr yafito daga motarshi yanufo tasu da gudu daidai shima daddy ya fito "Alhaji meke faruwa ne?" "Tana ciki" inji daddy yana bude seat din baya Leqawa Dr din yayi saikuma yayi cikin hospital din da sauri Da taimakon mummy aka fiddota daga cikin motar daidai nan Dr yadawo da wasu nurses jaye da gadon gurgura marassa lfy Ahankali aka dorata akai sannan aka shiga gurgurata zuwa cikin asibitin mummy da daddy biyedasu cikin tashin hankali. A wajen ward dinda aka shiga suka ja burki kowa yayi cirko cirko cikin tashin hankali Da taimakon nurses din aka maida ta kan gadon cikin ward din sannan Dr din yashiga bata taimakon gaggawa don sosai jikinta yayi mugun rauu kamar a oven. Zainab najin duk abinda akeyi amma she's too weak don ko bude idanunta ma takasa, jin kanta take kamar ta cireshi ta jefar ko zataji sauqin abinda takeji Sun kusan awa akanta sannan suka samu daidaita temperature dinta aka kuma daura mata drip. Saida Dr yagama komai Sannan ya juya da niyyar fita yasamu su daddy dayasan suna can cikin tashin hankali Jiyayi an kama ha6ar rigar shi Hakan yasashi saurin juyowa. Zee ce riqe da rigar amma still idanunta gamm a rufe Saurin dawowa wajenta yayi yana cewa "Zainab, menene? Gayamin how are you feeling? Ina ke miki ciwo?" Hawaye ne suka gangaro daga ruffafun idanunta "sorry ok, zaki samu sauqi, ko nakira daddy?" Ahankali ta girgiza kanta still idanunta a rufe sai kuma tashiga motsi da baki Hakan yasa yayi saurin duqowa don yaji me zatace "z..zan mutu" "bazaki mutu ba Zainab, insha zakiji sauqi, kinji?" Girgiza kanta tayi ahankali wasu hawayen nasake gangarowa "zan mutu ne, zan mutu idan baka taimaka min ba" tafada cikin dashashiyar muryarta "zan taimaka miki, kinga ma gashi nan ina taimaka miki ko? Kiyi hqr zakiji sauqi, be strong" Sai a lokacin ta bude jajjayen gajiyyayun idanunta da har lokacin ke zubda hawaye "zan rayu ne idan ka taimaka min, ina neman alfarma awajenka Dr, please" Tsayawa Dr din yayi yana kallonta na wani lokaci sannan yace "Alfarmar me Zainab" Hadiye wasu yawu tayi ahankali sannan tace "kacemasu daddy jinina ya hau, hawan da zai iya bugar da zuciyata, kacemasu zan rasa rayuwata, kacemasu zuciyata takusan bugawa, kace muddin basu bani abinda nake so ba zasu rasani" Sai kuma tafashe da kuka Tsayawa Dr yayi yana kallonta kawai yakasa cewa komai "Duk wadannan abubbuwan dana lissafa zasu faru dani soon Dr, zan iya rasa rayuwata soon, ba hakan nakeji ba, wahalar dazani sha nake tsoro, don Allah ka taimakeni, ka ceci rayuwata, ka fadamasu Hakan ko zasu tausaya min su bani abinda nake so" Sosai jikin Dr yayi laqwas sai kallonta yake cikin tausayawa Qara kallonshi tayi "don Allah kar kace A'a Dr, don Allah" ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ Safa da marwa daddy ketayi tsakanin farkon ward din zuwa qarshen shi Yayinda mummy ke zaune kamar akan qaya ta buga tagumi kowannensu jini akan akaifa. Jin budewar kofa yasasu saurin dagowa gabadaya Ganin fitowar Dr yasasu saurin tahowa wajenshi da sauri "Dr ya? Ya take yanzu?" inji daddy cikin rikicewa "karku damu, calm down please, komai zai tafi normal" inji Dr cikin sigar kwantar masu da hankali "yanzu yaya take aciki Dr, don Allah ka gayamana" "zan gayamaku yanzu ma kuwa, but mutafi office tukkuna" yafada yana nuna musu hanya nan duk suka rankaya suka nufi office dinshi Zama yayi a kujerar shi suma suka zazzauna a kujerun dake facing desk dinshi suka zuba mashi idanu cikin neman qarin bayani Gyaran murya Dr yayi sannan ya zare glasses din idanunta yana kallonsu "meke damun Zainab ne?" inji Dr Kallon juna mummy da daddy sukayi sannan suka sake kallonshi "kamar yaya? Abinda ke damunta ai kai zamu tambaya tunda kai ka dubata" inji mummy Ajiyar zuciya Dr ya sauke sannan ya koma ya jingina da kujera yace "abinda yasa na tambayi Hakan saboda naga alamun tana tattare da damuwa ne sosai wanda Hakan ke barazana ga lafiyarta" "Me Hakan ke nufi Dr?" Tasowa Dr yayi yayo gaba ya dora hannuwa akan desk dinshi yace "am sorry amma diyarku tana cikin tsananin damuwa wanda Hakan ya ta6a lafiyarta sosai don a halin yanzu jininta ya hau fiyeda qima wanda Hakan barazana ce ga lafiyarta sosai, zuciyarta na cikin matsala don ba don kun kawota dawuri ba da komai na iya faruwa" Rufe baki mummy tayi da hannu tana gasping Yayinda daddy yaita maimaita kalmar innallilahi Ganin yadda suka rikice yasashi cigaba da cewa "yanzu haka Dakyar nasamu nashawo kan al'amarin, yanzu nayimata allurar barci don tasamu peace of mind yadda zamu samu jinin ya dan sauka" "innallilahi waina ilaihi rajiun"inji daddy cikin tashin hankali "ka gani ko? Kaga irin ta Ko? Ai shikenan, saika kasheta kowama ya huta" inji mummy cikin kuka sai kuma ta tashi ta fice daga dakin da sauri Binta da kallo duk sukayi sai kuma daddy ya dafe kai yana sake ambaton sunan allah Shidai Dr cigaba da bashi hqr yayi da kwantar mashi da hankali. Dagowa daddy yayi da idanunshi dasuka Kada ya kalli Dr yace "meye mafita Dr? Banason rasata, she's the only child I got" inji daddy cikin tsananin damuwa "ka kwantar da hankalinka Alhaji, insha allah bazamu rasata ba, insha allah zata warke sumul kamar bata ta6a ciwo ba Amma fa kuma Saida taimakon ku, idan har ana son komai ya daidaita jininta ya sauka dole sai an magance matsalar Dake damunta don damuwa da tunani duk suka jawo wannan abin, dole a guji abinda zai qara sata damuwa har hakan yasake tasiri a zuciyarta don akwai matsala sosai" Furzar da huci daddy yayi daga bakinshi yana lumshe idanu Ya dade ahakan batareda yace komai ba sai kuma can ya miqe tsaye yana cewa "shikenan Dr, muna iya ganinta?" Shima Dr miqewa yayi "sure, amma kamar yadda nace maka nayimata allurar barci yanzu haka ma barcin take" "ok babu matsala muje mu ganta din" Atare suka fito suka sake nufar ward din da zee ke Kwance. Iske mummy sukayi aciki zaune gefen gadon da zee ke Kwance ta riqe hannunta daya tana kallonta Tunda tajuyo tayimasu kallo daya bata qara kallonsu ba. Qarasowa sukayi suma bakin gadon suka tsaya Kallon zee da idanunta ke arufe daddy yayi cikin wani yanayi yana hango ramar datayi acikin yan kwanakinnan. Sun dade a tsaye babu mai cewa uffan acikinsu can sai daddy ya juya ga Dr din yace "Dr please take care of her, abata duk kulawar datake buqata" "insha allah Alhaji, it's my duty though" Kada kai daddy yayi sukayi musabaha sannan yajuya yafita. Saida Dr yaqara dubata ya duba yadda drip din ke tafiya yaga komai normal sannan ya juyo kan mummy dake zaune jigum Tundazu Rarrashinta da kwantar mata da hankali yaitayi yana assuring dinta komai zai daidaita sannan yafita yabarta da zee din a dakin. Tunda daddy ya fita be sake dawowa ba sai wajajen 1 na rana kuma har lokacin bata farka ba. Wannan karon ma ko gefen daddy mummy bata kalla ba har yagaji da tsayuwarshi yasake fita. Wajajen 2pm wata maid takawo masu abinci asibitin bisa umarnin mummy. Wajajen uku saura mummy na zaune gefen gadon zee tayi nisa a tunani sai jitayi kamar ana motsi Saurin maida kallonta tayi ga zee taga itace ke motsin sai qoqarin bude idanunta takeyi Saurin matsowa kusa mummy tayi tana Kamo hannunta "daughter?" tafada cikin doqi Ahankali zee taita kyafta idon gabadaya kafin daga bisani ta ida budesu ahankali Ganin mummy tayi akanta tana kallonta tana murmushin murna "Zainab kin farka?" Batace komai ba sai lumshe idanunta datayi tasake budewa tanajin jikinta so weak "bari na kira Dr kinji? 1 minute" Daga haka saita juya ta fice daga ward din Sake maida idanun tayi ta lumshe tana inhaling da exhaling ahankali. Ba jimawa mummy tadawo tareda doctor Babu 6ata lokaci yashiga duddubata Saida yayi making sure komai is ok sannan ya kalli mummy yace tayi mata brush abata liquid abu mai dumi sai tasha magani. Da to mummy ta amsa ta tashi shikuma Dr yafita Da taimakon mummy zee tayi brush sannan tadawo ta hada mata kakkauran tea tana bata cikin kulawa Sosai zee taji sanyi ganin yadda mummy ke nuna kulawa sosai gareta abinda ta manta rabon da tayi mata ko dayake bata Sakin jiki daita bare tasamu kulawar kullum daddy daddy ko mummy tayi yunqurin yin wani abin sai taqi Sakin jikinta kamar tana tareda wata bare amma yanzu gashi da aka 6ata da daddyn dole aka dawomata. Saida tashanye tea din sannan mummy tasake kiran doctor din don yabata maganin Tana cikin shan maganin daddy yashigo dakin. Tunda taji muryashi ta sunkuyar dakai takasa dagowa ta kalleshi dukda wani feeling datakeji na daban ajikinta Qarasowa daddy yayi cikin murna yanata hamdala dakuma godewa Dr sannan ya matso kusada zee da har lokacin kanta na a sunkuye "daughter na?" ya kirata a tausashe Sai jitayi hawaye sun kawomata a idanu She missed him, so very much, batasan dahaka ba sai yanzu "ya jikin?" yafada yana dafa kanta Kada kai kawai tayi alamun da sauqi batareda ta dago ba don batason yaga hawayenta Zama daddy yayi gefen gadon shima yana facing dinta ya kafeta da idanu while ita kuma ta kafe yatsun hannunta da idanu Kamo hannun nata yayi ya riqe yace "daughter na? Fushi kike da daddyn ki?" Hawayen datake ta riqewa ne suka 6alle mata batareda ta shirya ba Jawota yayi jikinshi ya rungumeta Hakan yasa tafara shesheka "am sorry, am so sorry kinji, am sorry I hurt you, please forgive me" yafada yana patting bayanta itakuma tana cigaba da kukanta Dago fuskarta yayi yayi kissing goshinta "ina sonki daughter, bazan iya gangancin dazai sa na rasaki ba don idan narasaki kamar nima na rasa kaina ne, zan qara wata sadaukarwar daughter, zan sadaukar da farincikina Domin naki kamar yadda nasaba. Na amince, na amince daughter, you can have Deen, allah yasa Hakan shiyafi alhairi" Batasan lokacin da ta kwace kanta daga rungumar da daddy yayi mata ba tana kallonshi mouth agape Itama mummy kallon daddy take idanu waje kamar zasu fado daga socket dinsu Kada mata kai daddy yayi yana murmushi sweetly sannan ya kamo hannunta ya riqe "ina iya bayar da komai saboda ke amma bazan iya bada ke ba saboda koma menene. Bazan ta6a yafewa kaina ba idan na rasaki ta dalilin selfishness dina Bazan ta6a rayuwa cikin farinciki idan babu ke acikinta ba Kiyi hqr my daughter, I was selfish, I hurted you fiyeda tunani na Nida ya kamata na kareki daga cutarwa da dukkan rayuwata saiya kasance nike cutar dake, am sorry, forgive your daddy" Fadawa jikinshi zee tayi tana kuka sosai tana girgiza kai, she can't believe abinda Kunnuwanta ke jiyemata, kodai mafarki takeyi? Bubbuga bayanta daddy yashiga yi yana rarrashinta sannan ya dagota yayi cupping fuskarta "ya isa hakanan zee, Deen is now yours" yafada cikin murmushi "D..dagaske?" "bari kigani" Saiya kalli kofa yace "son!! Bismillah son!" Duk maida kallonsu sukayi ga bakin kofar zee na jin yadda zuciyarta ke bugawa kamar zata faso qirji Gani sukayi an murda handle din daga waje sai aka fara turo kofar ahankali "Assalamu alaikum..." taji cool voice dinshi ya daki Kunnuwanta Lumshe idanu tayi tasake budewa daidai shima ya ida Shigowa Idanunta ne suka fada cikin oily bright eyes dinshi dake shining as ever.... ✍️ Juma'at mubaraq in advance ? 🌜 Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:38 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *050* *THE INTRODUCTION* Kasa ko kyafta idanu tayi akanshi kamar yadda shima Hakan yake a wajenshi. Basusan sunyi missing juna ba har haka Saida sukayi arba da juna 11days, kwana shadaya rabonsu dasa juna a ido abinda be ta6a faruwa ba Tun bayan fara soyayyarsu. Hakan yasa yanzu dasukayi arba da juna suka kasa Janye idanunsu akan juna Ahankali ya tako still idanunshi akanta har ya iso bakin gadon shima daga bayan daddy. Janye idanunshi yayi daga kanta sannan ya duqa ya gaida mummy Cikin fara'a mummy ta amsa mashi tana sakejin qaunarshi har cikin zuciyarta Miqewa yakeyi yana Tambayar mummy ya me jiki tana amsawa da da sauqi sannan suka gaisa da Dr yana tsokanarshi wai badai patient dinshi bane ya murmuje haka Shidai murmushi kawai yayi yana sunkuyar dakai yana dan satan kallon zee da itama ta sunkuyar dakai ta wutsiyar ido. Da daddaya suka fara barin ward din har yarage daga Deen sai zee Dagowa yayi ya kalleta sai yaga haryanzu kanta a sunkuye yake sai yadanyi murmushi sannan yaja kujerar da mummy ta tashi akai ya zauna. Tana jin yadda idanunshi ke piercing din fuskarta amma taqi Dagowa saima jujjuya Ring dinshi dake yatsarta datake yi "ya jiki?" taji yafada ahankali Ahankali ta Kada mashi kai batareda ta dago ba "I missed you" taji yaqara fada Ahankali ta dago itama ta kalleshi Saidai batace komai ba sai cigaba da kallonshi datayi "kin rame" yasake fada ahankali Hakan dayace yasa itama ta hango nashi ramar "you too" tafada ahankali itama Murmushi yayi "dole na rame, kwana na 11 banga abincin ruhi na ba" Dan murmushi tayi tana sadda kai tanajin duk wata damuwarta na fecewa daya bayan daya. "am sorry for what kaka said, naso na dakatar daita amma taqi yin shiru" yafada yana kwa6e face Dagowa tayi ta kalleshi "da Gaskiyarta ai, wataqila wani abin daddy yayi muku" Girgiza kai Deen yayi "babu abinda yayimana kawai rudun tsufar kaka ne, daddy is very nice" Dan murmushi zee tayi "ka fadamin Gaskiya" "na ta6a miki qarya?" Shiru tayi don ta tunano ko ya ta6a din saiya katse mata tunanin da "hankalina ya tashi sosai lokacin da kuka gama wayar da kaka, gashi inason miki magana amma kaka ta cire layin ta karya dole nafita wani shagon kati na ari wata wayar nakira but ba'a dagawa tun lokacin hankalina ya ida tashi don zuciyata na fadamin ba lfy. Jiya ko barci banyi ba" Murmushi kawai tayi tana kallonshi not saying anything "am glad you're ok now and am glad baxamu qara yin nisa da juna ba, daddy ya amince" yafada cikin doqi Fadada murmushin ta itama zee tayi sai kuma ta dan 6ata fuska "what?" inji Deen yana dan daga mata gira "Kaka fa" tafada tana marairaice fuska Dariya yayi "Kaka too is ok with everything" "dagaske? "yes, sunyi magana da daddy dama duk rudun tsufa ne" yafada yana Dariya "to don Allah me daddy yayi muku, naji tafadi Hakan jiya" "babu komai fa nace miki" "please tell me" tafada a marairaice "please stop asking" Shima yafada yana karya wuya "is it really bad?" Daga kafadunshi yayi yace "not that bad" Zata sake magana ya katse ta ta hanyar cewa "shhh, Kiyi shiru ba'ason marar lfy yana surutu" Harararshi tayi zata sake magana yace "shhh, Kiyi shiru, ni zanyi maganar kekuma sauraro ne naki, ok?" yafada yana dan Hade gira Murmushi tayi ta kauda kai Jin shiru yasa tasake juyowa ta kalleshi sai taga shima ita yake kallo Daga gira daya tayi alamun ya? Sai yayi mata murmushi "I love you" yafada in whisper Sauke idanunta tayi tana murmushi "I love your face, your smile, your everything, don Allah ki warke dawuri mukoma school yadda zamu dinga hadewa kullum, kewarki nason kasheni" Murmushi tasakeyi "ni zan warkar da kaina?" Girgiza kai yayi sai kuma ya bude taffukan hannunshi cikin sigar addu'a yace "ya rabb kaba wannan baiwar taka lfy yadda zamu dinga zuwa school muna ganin juna kullum Allah kasa ta maida qibarta karta tsaya haka kamar sugar cane" Wara idanu zee dake sauraronshi Tundazu tayi tace "kutt.. Nice sugar cane" Jada baya yayi da kujerar yana Dariya "sorry, to kamar fish bone" Qara Wara idanun tayi shikuma ya cigaba da yimata Dariya. Sun dade ahakan suna fira suna Dariya har mummy tashigo ta iskesu Sosai mummy tayi mammakin ganin yadda ta gyagije kamar ba ita ba, fuskarta beaming in smile, sai a lokacin itama taqara jinjina soyayyarsu takuma qara tabbatar wa Deen shine farincikinta Deen be qara dadewa ba yayi musu sallama yatafi don tareda yimusu alqawarin zasu dawo da kaka anjima Ji Zainab tayi kamar tace mashi kar yatafi shima jiyake kamar kar ya tafi haka dai sukayi sallama rai babu dadi yatafi. Sai a lokacin ta tashi tayi alwalla ta rama sallolinta na asuba dabatayi ba da zuhr sannan ta hada da asr da ake cikin yi lokacin. Tana gamawa mummy ta gabatar mata abinci kuma taci sosai tasha magunggunanta Kallo daya zaka mata ka fuskanci tana cikin farinciki dukda haryanzu zuciyarta na dar dar akan wannan al'amarin musanmman ma a 6angaren kaka da bata tabbatar da nata amincewar ba. Sai wajajen biyar daddy yasake dawowa hospital din da siyyayar abubbuwan dayasan tanaso wanda mostly duk fruits ne, ya shaqo babbar leda dasu. Sosai daddy yashiga tarairayarta fiyeda yadda yake mata ma da, tun bata ida Sakin jikinta dashi ba har ta gyagije suka koma yadda suke Yana taredasu har magrib sannan ya tashi ya fita Sai bayan isha'i yadawo tareda Deen da kaka dasuka Hade a waje Tunda zee tayi ido hudu da kaka ta maida kanta qasa tanajin yadda gabanta ke faduwa don ita tunda ta fahimci kaka bata shiri da wanda ya ta6a mata Deen take taka tsantsan daita don ga dukkan alamu zatayi masifa Saidai ga mammakinta sai taga akasin abinda tayi tunanin gani don lfy lau aka gaisa tayi mata ya jiki cikin fara'arta data saba yimata don harda guzurin kayan fruits datayo mata Ganin Hakan yasa ta dan saki jikinta itama Fita daddy yasake yi don yin magana da Dr don Gaskiya beson su kwana asibitin tunda taji sauqi gwara su koma gida duk yan ide iden da ba'ayi ba Dr yabiyosu har gida a ida. Hira sosai kaka da mummy keyi kamar babu abinda ya faru, kwata2 babu wanda ya tada maganar misunderstanding din daya faru tsakaninsu saima firar duniya dasuke tayi abinsu Sukau mutanenku yan saurare ne kawai, sun kasa kunne sai sauraron hirarsu mai cike da ban Dariya suke idan akayi abin ban Dariya sai su kalli juna suyi murmushi Sun dan jima ahakan daddy yasake Shigowa tareda Dr Saida aka sake gagaisawa sannan Dr yaqara dubata yaga komai normal sannan ya rubuta masu sallama bayan ya basu maggungunanta Daga zee har Deen babu wanda yaji dadin sallamar don that means su da haduwa sai a school kuma Sai wajajen 10 saura duk suka fito lokacin har daddy yasa an kawo wata motar dazata sauke su kaka gida. Cikin farinciki da aminci suka rabu su kaka suka hau motar da bala zaija sukuma su daddy suka hau dayar motar inda daddy ne zai jasu sannan suka fito daga asibitin gabadaya kowa ya dauki hanyarshi. Da kanshi daddy ya raka zee har dakinta yana lalla6ata kamar wata kwai Saida ya zauna suka qara dan fira sannan ya tashi ya fita bayan sun yima juna Saida safe Saida tayi wanka tayi shirin barci sannan ta haye gado ta kwanta don dama tariga taci abinci a can haka asibitin tasha maganinta. Kwanciya tayi shiru idanunta akan p.o.p. Takasa yarda haryanzu wai daddy ya amince da Deen. Just like that? Saikuma ta tuna irin qaunar da daddy ke mata tabbas bazai ta6a barin ya rasata ba muddin yana da yadda zaiyi ya ceci rayuwarta Murmushi tadanyi, da tasan da Hakan da duk ba'a kai yanzu ba, da tuntuni zatayi faking sickness din amma dukda haka alhamdullilah, what matters is ya amince din don haka bata tunanin tanada wata matsala a rayuwa. Tunawa tayi da wayarta Hakan yasa ta miqe zaune tana waige waigen inda zata ganta Can qasan gado ta hango ta tafiddo ta. Danna power botton tayi sai taga takawo haske amma charge dinta yayi low 5 missed calls tagani a gaban screen din Swiping tayi ta shiga call log sai taga baquwar number ce mai kiran Har tafara tunanin waya kirata saita tuna Da Deen yace ya nemeta da wata wayar da ya aro, tabbas shine kenan. Danna ma ainahin number Deen din kira tayi dukda taji yace kaka ta karya layin Kamar kau yadda ta zata bata shiga ba hakan yasa ta kashe wayar gabadaya ta jonata a chaji takoma ta kwanta tana jin zuciyarta wasai Bata wani jima ba barci ya sadado yayi gaba daita Washegari garas zee ta tashi sai dan abinda ba'a rasaba. Har daki daddy yazo dubata yakuma sata taci abinci yabata maggungunanta tasha. Sosai yake kulawa daita kamar kwai Yana nan zaune daita har wajajen 9am lokacin da Dr yashigo Domin duba lafiyar ta Saida ya duddubata yaga komai normal sannan ya qara jaddadamasu akan ta cigaba da shan maganin akan lokaci insha allah zata ida warwarewa. Tare da Drn daddy yafita don dama shi yake jira yazo ya duba mashi diyarshi kafin ya fita aiki. Sai a sannan zee tasamu damar fitowa daga dakin itama tafara biyawa dakin Mummy suka gaisa sannan tadawo falon qasa ta zauna. Tana ahakan wajajen 12pm kira yashigo wayarta Dubawa tayi taga baquwar number ce Kamar karta daga saikuma wani tunani yazo mata saita daga aikuwa hasashenta ne yazamo Gaskiya don Deen din ne "patient" Murmushi tayi "waye Hakan?" "kinfini sani, yaya jikin?" "alhamdullilah, naji sauqi sosai" Sautin murmushin shi taji "masha allah, allah yaqaro sauqi" "Amin ya allah" ta amsa tana yin filo da hannun kujerar datake akai "yasu mummy?" "mummy lfy lau, ina my kaka?" "Your kaka tana nan lfy lau tana gaidaki da jiki" Murmushi tayi "ina amsawa sosai, nima ina gaida ta" "to zataji... Baki tambayeni ba" Dan daga gira tayi "Me?" "this strange number" Murmushi tayi "yanzun ma aro kayi?" "nop, siyan wani layin nayi so you better save it" Yadda yaqarashe maganar bossily yasata Dariya "yes boss!" tafada tana Dariya Shima dariyar yayi "yaushe zakiyi resuming school?" Daga kafadu tayi "Don't know, qila saina ji sauqi" "O'O! Ba kinji ba?" "O'O! Ban ida warwarewa ba" tafada cikin kwaikwayon Maganarshi Ko bata ganshi ba tasan 6ata fuska yayi "please get well soon, am missing you badly" Murmushi tayi kawai amma gani take duk missing dinta dayake bekai wanda takeyi ba "insha allah" tafada tana murmushi "kinga exams nata matsowa, we have alot to cover" "yeah, insha allah ai Dr ma yace naji sauqi sosai saura strenght dina ya dawo" Jitayi yace "Ya rabb kadawo mata da strenght dinta ta tashi tajita da qarfi kamar super man" Dariya tayi tace "da kaine punching bag dina na farko" Wara idanu yayi daga can 6angaren "Ca6 baxaki iya ba" "why not?" "saboda fuskata ba don punching akayita ba, bazaki iya dora ko yatsa daya akanta ba da sunan duka bare naushi" "Me zai hana?" "kyawun ta mana" Dan wara idanu tayi "fahari ko?" "No, Gaskiya ce ai" "tayaya to kasan tanada kyau" "nasani mana, ba ina duba mirror ba" Dariya ya bata amma batayi ba "haba? Namiji dama na duba mirror?" "baya dubawa dama?" "haka nazata" "to nidai ina dubawa" "to kuma yaya akai ka gane kyawun?" "ba nagani a mirror ba?" Dan gasping tayi cikin mammaki 😱 "dama mutum idan ya kalli kanshi a mirror yana gane kyawunshi?" Cikin confusion yace "ke idan kika kalli mirror bakya ganin kyawunki?" Dariya tayi marar sauti sannan tace "A'a ni ban ta6a gani ba" "to me kike gani?" ya tambaya confused "kawai dai nasan nice, thats all" "bakya kallon large white eyes dinki, da pointed hancinki da qaramin red lips dinki da cute kumatunki da long lashes dinki, duk bakya tsayawa kallo?" Dariya taqara yi tana rufe bakinta don karya ji "ni duk bana gani kawai nadaisan nice kawai and the moment na ajiye mirrorn saina mance yadda fuskar take" Wara idanu yayi "yanzu bakya gane fuskarki without mirror" "ko kadan, kai kana ganewa ne?" tafada tana qumshe Dariya jin ya dauki abin serious "Are you kidding me? Tayaya za'ayi na mance fuskata? Nine fa?" "abin mammaki, kenan kana iya gane kanka? Tayaya zaka iya riqe fuskarka ba Saidai wani ya riqemaka ba tunda ba ganin kanka kake ba?" Qara shiga confusion yayi yace "to Saidai idan bakida lfy amma tayaya za'ayi ki kasa gane fuskarki?" Dariyar datake riqewa Tundazu ya kuce mata tashiga yi Ajiyar zuciya ya sauke Cigaba da Dariyar tayi "Gaskiya yakamata Dr yaqara duba ki, I wonder yadda ma akayi na yarda da maganar ki tunfarko bayan nasan bakida lfy" Wara idanu tayi still tana Dariya "nice banida lafiyar?" "ga zahiri?" Shima yafada yana Dariya Haka sukaita firarsu Saida yan kudin da Deen yasa suka qone sannan. Bata sake bugamashi ba ta tashi ta haye sama don tasan idan ta bugamashi kuma sai allah yayi don ita ko awa zasuyi kudin bazasu qare ba gashi idan suna waya basu iya taqaita ta ba don dasun fara mancewa da komai suke sai kansu kadai *fast forward* A cikin kwanaki uku zee ta warke sumul kamar bata ta6a ciwo ba Sosai take samun kulawa a wajen iyayen nata musanmman daddy dayake riritata fiyeda yadda yakeyi ada. A bangarenta da Deen kau sai abinda yayi gaba don kodayaushe suna maqale awaya suna firarnan tasu mai antaya kowannensu acikin nishadi. Ata koina komai tafiya yake masu so smoothly sun mance da wata aba wai damuwa. A ranar da yakama kwana biyar da kwanciyar zee hospital wanda yayi daidai da ranar asabar da daddare lokacin kwanciyar su mummy. Suna Kwance suna firarsu kamar yadda suka saba Daddy ne ya qara fuskantar mummy sannan yace "ya kika ga daughter na yanzu? Very cheerful and lively" Murmushi mummy tayi "hmm kaidai bari, ai yaran zamanin kenan, baka yimasu dole idan kuma kayi kai zaka fara ganin sakamakkon shiyasa muddin kasan abinda sukeso mai kyau ne kawai ka miqa wuya" "ai naso nayi ganganci maimuna, dana rasata ai shikenan na shiga uku" Dariya mummy tayi ganin yanayin daya fadi ya shiga ukun. "Ato ai kaine wani sa'in baka jin shawara, wlh ni tunda ta ambaci sunan yaron nan naji hadin yayi min don Gaskiya yaron yanada wata baiwa da ba kowanne keda ita ba, ga nutsuwa uwa uba ladabi. Wlh tun a asibiti halayyar yaron nan ke burgeni Gaskiya kaka tayi qoqari" Murmushi daddy yayi "ai nima naso tafka babban kuskure, don nagartar yaron na tabbatar da nagartar shi kawai selfishness ne dakuma burin dana dauka na dorawa auren daughter na ne, I thought hamshaqin mai kudi zata kawo shiyasa data kawo wannan naji nakasa yarda" "ai kudi ba shine farinciki ba, yara nawa suke auren masu kudin amma kaga babu kwanciyar hankali? Kaga sai bushewa suke a tsaye bayan akwai komai na more rayuwa a gidan, kawai fatan miji nagari shiya dace ga kowacce diya mace ba bawai kudi ba don wasu ga kudin amma rashin kwanciyar hankali ya hana sucisu cikin jindadi" inji mummy "ai duk na gane Hakan yanzu, na zauna nayi karatun ta nutsu nagano money is not everything kuma nayi bincike akan hallayarshi nasamu nagarttatun result, shiyasa na yanke shawarar gayamashi ya turo ranar laraba idan allah ya kaimu" A mammakince mummy ta juyo tana kallonshi "turowa kuma?" "yes, yaturo ayi Introduction" "but why the rush?" inji mummy still cikin mammaki "hmm ke baki san halin da ake aciki bane Allah yayiwa diyarki farinjinin masoya, mutanen dake tunkarata da son abasu ita ko wa 'ya'yansu ko wa kansu basuda iyaka, kullum cikin atracking dina suke akan maganarta amma saboda nayi alqawarin bazan yimata dole bane yasa duk bana maida hankali akai Saidai nace suje su tunkareta idan ta amince dasu to ni banida matsala Dukda Hakan ban tsiraba kullum cikin zarya ake wajena shiyasa na yanke shawarar kawai sawa zanyi yaron datake so ya turo a daidaita magana kinga duk wanda yaji an badata bazai qara damuna ba" Shiru mummy tayi sai kuma ta Kada kai "kuma fa hakane, amma sai inga yayi wuri dayawa abari takusan gama school mana" "ai ba auren za'a daura ba bakuma sa biki za'ayi ba kawai introduction ne, ma'ana suzo neman auren ta ya kasance an tsayar da magana, kinga idan shi yayi graduating yafara service sai asa bikin lokacin dazai gama service sai a daura auren dama kuma nariga na fidda post dazan bashi a daya daga cikin companies dina kinga sai suyi settle down ga mata ga aiki, ko yaya kika gani?" Tuni mummy tahau fara'a batasan sanda ma tayi mai half hug ba "perfect! Hakan yayi sosai wlh, kai amma naji dadi" Murmushi daddy yayi ganin yadda mummyn ke murna sai yace "kinga basai acemashi ya turo wannan larabar ba, basai sun takura kansu ba da kawo kudi yanzu duk mun zama daya kawai fatanmu allah yasama abin albarka" "Amin ya allah Alhaji, Gaskiya bansan yadda zan iya musalta maka farincikin danake ciki ba, am supper happy, at last nafara jiyo qamshin auren diyata" Dariya daddy yayi ganin yadda ta rikice don murna sai yace "wayaga uwar amarya" Jujjuya idanu tayi "hmm za'ayi abu" tafada cikin cin buri Dariya daddy yasake yi yace "to yanzu sai agayama su mutanen Ruma ko sai asamu kosu yusuf suzo" "har saisun zo?" "yo ba diyarsu bace? Ni nan kinsan banida yayye ko qanne maza sai only qanwata JAMILA(ummu batool) kuma ba anan qasar suke ba bare nace mijinta ya wakilceta Kinga idan daya daga cikin kawunnan nata na Ruman suka zo sai nasamu aboki ko daya nima ayi zaman tunda kawai introduction ne basai anyi wani gayya ba" "hakane wlh, Gaskiya tsarin yayi, allah ya taimaka yasa ayi taro lfy a watse lfy" "Amin amin Hajiya ta, insha allah bikinnan zai zama one in town, zamu jijjiga Katsina" "Allah Alhaji na" tafada cikin tsananin jindadi "Allah hajiyata" Da wannan firar suka kwanta a ranar kowa zuciyarshi fess. Washegari ummu batool ce ta fashe kwan wa zee don ita batasan anayi ba Saida ummu batool din ta kirata tana kodata tana cewa tun saura wata biki zasuzo nigeria su tare don sune amara qirjin bikin Tace ba don daddy ya hana ba da dasu za'ayi introduction din Itadai zee haka taita biyemata da Dariya ba don ta fahimci zancen nata ba Saidai kawai tadanyi Dariya cikin wayancewa Saida suka gama Gaisawa da ummu batool din sannan taba batool din itama suka gaisa da zee inda itama take tsokanar ta da sunan amarya Ahaka dai tasamu a daddafe tagama wayar sannan ta tashi da gudu tayi dakin Mummy A rikice take gayama mummy yadda sukayi dasu ummu batool tana Tambayar me suke nufi Murmushi mummy tayi na manya sannan ta fadamata abinda ke shirin faruwa. Zee was so shocked, dumpfounded, Happy, tama rasa wanda ya rinjayi wani a feelings din Tambayar mummy tayi tace tun yanzu? Sai mummy tayi mata bayanin da daddy yayi mata itama jiya. Murna a wajen zee ba'a magana don Tsalle tayi ta rungume mummy tana ihun murna babu ko kunya Tureta mummy tayi daga jikinta sannan ta fattatakota waje wai tafitar mata a daki tunda batada kunya Dakinta zee takoma tana cigaba da tsallen murna, she can't believe wai Deen zaizo neman aurenta ne Dafarko harta dauki waya zata kirashi saikuma ta tuna ba ita ya kamata tafara breaking din news din ba atsakaninsu shi ya kamata yafara Hakan yasa ta maida wayar ta ajiye ta cigaba da murnarta Koda daddy yadawo da marece har daki tabi shi Domin bayyana mashi farincikin datake ciki don dama ita bawani kunyarshi takeji ba Sosai daddy shima yaji dadin ganin irin murnar datayi yana kuma alfahari da kanshi ganin ya wanke mata zuciya tass. Sai daddadare tasamu kiran Deen wanda dama wayar na hannunta tana kallonta every now and then don ganin ta inda kiran zai shigo. Duk yadda tayi tunanin Deen zaiyi murna Saida ya wuce nan don har abin Saida yasata shauqi Sosai yake bayyana murnarshi yana cewa yana jin kamar ya jawo ranar tazo ko zai huta don bayada tabbacin zai samu isassun barci cikin dararren nan na kafin ranar Itadai zee Dariya Kawai take mashi tana sauraron sambatun nashi tana kamar babu wanda yakaita farinciki a duniya. Yan Ruma labari yakai musu, sosai sukayi murna da wannan al'amarin don sai bugowa ake tayi ana allah ya sanya alhairi dukda bawai bikin za'asa ba sai aka wakilci kawu yusuf don yaje don dayan bayama garin. Shiri akeyi sosai na ranar a gidan su zee, kowanne ka gani kasan cikin farinciki yake don ace labarin zuciya a tambayi fuska, kallo daya zaka ma ahalin gidan suna cikin jubilation A bangaren zee da Deen wata sabuwar soyayya ce suke shimfidawa ta waya Koda yaushe maganar Deen bata wuce ya qagara ranar tazo, jiyake kamar ya tariye ranakun azo daidai ranar Itadai Saidai tayi ta yimashi Dariya tace ya cika zumudi. *WEDNESDAY* Tunda safe aka fara shirye shiryen tarbar baqi Sosai aka gyara gidan musanmman can 6angaren baqi don anan za'ayi zaman wanda aka fidda za'ayi qarfe 3:00pm A kitchen kuma kayan snacks ake hadawa na musanmman saboda baqi Tun 12pm Kawu yusuf ya qaraso daga Ruma. Yasamu tarba mai kyau wajen mummy da daddy Anan aka kira mashi Zainab da tazo tanata wani sunne sunnen kai wai ita kunya Tsokanarta kawu yusuf yashiga yi su daddy nayimata Dariya itakau Saidai ta sunne kai tana murmushi Saida sukaci abinci sannan daddy da kawu yusuf suka fita sallar zuhr Lokacin dasuka dawo yayi daidai da lokacin da abokan daddy suka iso duk manyan mutane, da Alhaji Abubakar (baban Asaad) da wani Alhaji bello. Wucewa sukayi bangaren daddy suka zauna sunata firarsu na manyan maza ana raha an cika masu gabansu da kayan motsa baki Suna ci suna fira suna jiran isowar mutanen Deen. *03:15pm* Zaune zee take gaban dressing mirror tana qarasa daurin dankwalin kanta tana humming waqa ahankali cikin nishadi Jitayi an murda kofa an turo Hakan yasa tadan dakata tajuyo tana kallon mai shirin Shigowa Mummy ce Hakan yasa tayi saurin sadda kai don kunyarta takeji sosai Qarasowa mummy tayi wurinta ta tsaya "mummy welcome" tafada cikin jin kunya "yauwa, nace kunyi waya dashi ne?" inji mummy fuska babu walwala Cikin rashin fahimta tace "waye?" "Kamal mana, yabar mutane Tundazu sunata jira shiru ko besan lokacin da akayi fixing bane?" Gaban zee ne ya yanke ya fadi "b.. Basu zoba?" inji zee cikin dan rawar murya "da sunzo da kin ganni anan? C'mmon bugamashi kiji lfy suka tsaida mutane haka?" Saurin tashi tayi jiki na dan rawa ta jawo wayarta dake kan gado tashiga laluben number shi wanda last call dinsu jiya daddadare ne Dakyar ma suka rabu a wayar don qin bari yayi su ajiye wayar dukda yadda wayar shi ke mashi low battery daga qarshe ma kiran katsewa tayi wanda bata raba dayan biyu chajin ne ya ida qarewa ta mutu Danna ma number kira tayi amma aka bata amsar _switch off_ Dagowa tayi ta kalli mummy taga itama ita take kallo "ya dai?" inji mummy "wai akashe" inji zee "akashe? Why zai kashe wayar shi a irin wannan ranar?" inji mummy wanda Alamu sun nuna tafara fusata "wlh ban sani ba Amma jiya damuke waya yayi min complain wayar babu chaji don sai warning suke mashi, qila mutuwa tayi" tafada tana jin zuciyarta na gudu har lokacin "ta mutu kuma shine bazaisa charge ko yakai a samashi ba? Mutanen nan tun after 2 suke anan zaune amma ace haryanzu shiru? Uku kusan da rabi?" "bari na sake gwadawa" tafada tana qara danna mashi kiran amma the same amsa ne _switch off_ Daidai nan daddy shima yashigo dakin cikin shigarshi ta alfarma da yayi musanmman domin ranar "wai ya haka? Daga aikoki kema shiru?" inji daddy yana kallon mummy "hmm gamunan munata neman number yaron muji lfy mukaji shiru amma wai switch off?" "number tashi?" inji daddy "eh mana" inji mummy cikin takaici "muga number daughter" yafada yana qarasawa wajen zee daketa faman sake re-trying number Shima kira yayi amma amsar dayace, akashe take. "to babu number wani nashi dakuka sani? Ko kaka?" "Kaka batada waya" inji zee cikin sanyin jiki "muga number" inji mummy Kallon number tashiga yi "wannan ai ba number bace ba" inji mummyn "ai ya chanza layine wancan ya fadi" inji zee dake jin kamar tayi kuka Ajiyar zuciya daddy ya sauke sannan ya duba agogon hannunshi "yanzu 3:40pm bari mushiga sallar asr qila kafin mufito sun iso maybe wani abu ya tsaidasu, allah yasa lafiya" Duk shiru sukayi jigum babu mai amsawa "ku saki ranku mana, insha allah they're on their way, kuma kuje kuyi sallan kafin mugama zasu iso" Da Hakan ya juya ya fita. Kallon juna zee da mummy sukayi saikuma zee ta sauke kanta qasa Ajiyar zuciya itama mummy tayi tace "kije kiyi sallar gashi kin 6ata fuskar da kwalliya sai kije ki wanke" "ai inada alwallata" inji zee a sanyaye Ta6e baki mummy tayi ta fice itama Komawa zee tayi ta zauna gefen gado tana tunanin meyasa haryanzu mutanen Deen basu qaraso ba? Bata daddara ba taqara dago wayar hannunta taqara dannama number shi kira amma still *switch off*..... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:38 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *051* *THE LETTER✉️* Sauke wayar daga kunnenta cikin damuwa To ya akayi haka? Ita a tunaninta ma su mutanen Deen din su zasuyi jira basu za'a jiraba duba da yadda Deen ke zumudin abin. Meyasa wayar shi take a kashe? Koda jiyan ta mutu ai yaci ace yanzu yasamu charge koma ina ne. Anya kau lfy? Ta jima tana wadannan tunane tunanen sai kuma ta tashi tashige toilet ta wanke makeup dinta sannan ta daura wata alwallar tafito tana jin zuciyarta babu dadi Shimfida sallaya tayi ta hau kai ta tada sallah. Tun kafin ta ida mummy tasake Shigowa dakin ta zauna gefen gado tana jiranta. Sallame sallar tayi sannan ta juyo ahankali ta kalli mummy Expression din fuskar mummy kadai ya isa yabata amsarta "wai what's all these ne? Yanzu 4:10pm amma haryanzu basu qaraso ba, qarin har awa daya da Mintuna? Kamata yayi ace Koda matsala aka samu su bugo sufadi atleast Hakan zai fidda zuciyoyinmu daga wasiwasi" inji mummy Cikin 6acin rai Sadda kanta kawai zee tayi qasa tana jin hawaye na kawo mata, tama rasa wane tunani zatayi Ringing wayar mummy ta dauka Hakan yasa taja Tsakin takaici kafin ta ciro wayar ta duba mai kiranta Daddy ne Dagawa tayi ta qara a kunne "ya ake ciki yanzu?" inji daddy a wancan bangaren "hmm nima bansaniba, wannan ai wulaqanci ne a tara manyan mutane a shanyasu? Idan sunsan basu shirya ba ai kamata yayi su sanar tun wuri a daga ranar" "yanzu dai calm down maimuna, bari na aika bala yaje ya gano ko lfy?" "haba Alhaji, kamar muna neman kai daita? Ina aka ta6a haka? Kawai a kyalesu ka sallamesu" "A'a maimuna, ta yiwu wani abin yafaru wanda dole Hakan ya tsaidasu kuma basuda hanyar reaching dinmu bare su bugo su gayamana, muyi musu uzuri, shima balan ai ba shiga zaiyi ba, kawai zuwa zaiyi as C.I.D ya gano me gidan yake aciki" Shiru mummy tayi amma allah yasani ranta a mugun 6ace yake "bari nasan abinda zan gayamasu baqin don Gaskiya suma sun fara qosawa da wannan al'amarin kafin nan bala yadawo sai muji daga gareshi" "to shikenan" inji mummy Cikin cinkushewar rai sannan suka katse wayar atare Kallon zee da haryanzu kanta ke a sadde tayi sai kuma ta tashi ta fita daga dakin Dagowa zee tayi tabi mummy da kallo da watery eyes dinta don tunda ta sadda kai take hawaye. Tashi tayi daga kan sallayar ta ninketa ta ajiye sannan taqara daukar wayarta taje daidai bakin window inda ake iya hangen harabar gidan daga nan ta yaye labulen tana kallon harabar tanan Daddy taga yana magana da bala sannan taga balan yanufi parking space shikuma daddy yakomo cikin gida Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta maida hankalinta akan wayar hannunta ta cigaba da kiran number Deen din amma shiru. Wasa wasa har qarfe 5pm shiru babu mutanen Deen babu alamun su Zainab tana tsaye still a bakin windown tana kallon harabar gidan kamar mai son ganin ta inda zasu 6illo. Jitayi anyi horn a gate din Hakan yasata zabura ta qara yaye labulen tareda zubama gate din idanu zuciyarta na bugu sosai Hango security tayi ya fito da gudu ya nufi gate yafara qoqarin budewa Babu addu'ar da batayi ba a zuciyarta na allah yasa su ne amma sai me? Sai gani tayi motar da bala yafita daita ne tadawo. Qurawa motar idanu tayi in utmost disappointment tana jin kamar zuciyarta zata fashe. Bala ne taga yafito daga motar sannan taga ya dan yi danne danne a wayar shi ya kara a kunne Be dade yana magana ba ya sauke wayar ya cigaba da tsayuwa a inda yake Can jimm kadan saiga daddy yafito yazo ya tarda bala din inda yake tsaye Gani tayi suna magana, dukda batajin abinda suke cewa tasan koma menene ba alhairi bane duba da yanayin fuskar daddy. Gani tayi daddy ya dafe kai yayi shiru saikuma ya cigaba da magana kamar ma a 6acin rai yana yi kamar zai make balan shidai balan kansa a qasa yake bece komai ba Can kuma daddy ya juyo a fusace ya nufo hanyar cikin gida Sakin labulen tayi ta dawo ahankali kamar wanda kwai ya fashe mawa aciki ta xauna gefen gado tayi wa waje guda quriii. Ba'a jima ba taji an bude kofar dakinta an shigo Dagowa tayi ahankali tana kallon daddy daya shigo din "daughter wai what's going on ne?" Cigaba da kallon daddyn tayi don ita kanta Tambayar da taso yimashi kenan "na aika bala gidansu amma yadawo ya fadamin wai gidan a rufe da kwado wai ya tambayi mutane sunce suma basusan whereabout dinsu ba, meke faruwa ne?" inji daddy Kasa ko kyafta idanu akan fuskar daddy tayi _kofa arufe da kwado? Me kenan?_ "am talking to you Zainab kinyi shiru kin quramin ido, yaushe rabon da kuyi waya?" Cikin wata murya da ita kanta bata tantance ko tata bace tace "jiya... Jiya da daddare" Daidai nan mummy tashigo dakin "wai ya ake ciki ne?" inji mummy tana kallonsu Ignoring dinta daddy yayi ya cigaba da yima zee magana "da kukayi wayar be fadamiki wani abu ba, something concerning taron yau?" Tunawa tayi da kadan daga cikin magangganunshi na jiya _gobe ne ko?_ Murmushi tayi kawai batace komai ba _gobe ne ranar, wannan daren zai kasance daya daga cikin tarihin rayuwarmu, dare mai tsayi, mai duhu mai cike da jira. Nasan wannan daren zai kasance mafi tsayi agareni, zan qarara gari ya waye ko zai yaye min duhu da damuwar zuciyata amma zaiqi wayewa sai nayi jira jiran da bansan adadin shi ba_ Murmushi tasakeyi tace _karka damu duk nisan dare ai gari zai waye, duk jiran dazakayi mashi kasa a ranka a kowanne passing seconds ragewa yake safiya kuma na kusantowa, fatan mu anan shine allah yakai mu da rai da lfy_ Sai yace _amin Zainab, amin zanso yayi saurin wayewa Zainab, zanso yayi saurin wayewa kafin zuciyata ta gaza hqr ta buga_ Dariya tayi mashi sannan tace _bazata ma buga ba baban zumudi_ Murmushi mai sauti taji yayi sai yace _I LOVE YOU_ "wannan wane salon wulaqanci ne ana miki magana kinyi shiru?" inji mummy a fusace "A'a maimuna ki kyaleta babu ruwanki, dani da ita muke magana" inji daddy sannan yasake maida hankali kanta "inaji daughter, kunyi wata magana data shafi yau" Girgiza kai tayi ahankali sannan tace "A'a saima zumudin dayake yi wai he can't wait gari ya waye" Duk shiru dakin ya dauka "wai Alhaji balan yadawo ne?" inji mummy "eh amma wani abu wai ya tarda gidan arufe wai kuma ya tantambaya wai suma haka suka wayi gari sukaga gidan" Shiru dakin yasake dauka babu mai cewa komai. Sun dan jima ahakan daddy ya saki Ajiyar zuciya sannan ya kalli agogon hannunshi "6 saura minti biyar" "Alhaji kawai ka sallami mutanen nan, ba zuwa zasuyi ba" inji mummy Cikin dacin rai Shiru dakin yasake dauka "innallilahi waina ilaihi rajiun, yanzu ta ina zan fara musu bayani ma?" inji daddy cikin tsananin damuwa Zee kanta na sadda takasa controlling din hawayenta "ya zamuyi kawai afadamasu meke faruwa babu wani 6oye 6oye, sun dai maida mu qanannun mutane kawai" inji mummy Cikin dacin rai Jigum suka sakeyi kowa rai babu dadi saikuma daddy ya juya "bari naje na barosu su kadai" Saiya juya ya fita Itama mummyn Jigum tayi tana kallon wuri guda saikuma itama ta bude kofar tafita. Baya zee tayi ta kwanta kan gadon ta kafe p.o.p din saman, tama rasa tunanin da zatayi A bangaren daddy kau zuciya ba dadi yayi musu bayanin komai nan take suka shiga jajantawa duk zuciya babu dadi inda suke Fatan allah yasa dai lfy. Haquri daddy yayi ta basu akan zaman jiran gawon shanun da sukayita yi sukuma suna nuna babu komai ai Indai lfy tau alhamdullilah kuma idan suka dawo aka sake fixing rana a sanar dasu zasu dawo insha allah. Da Alhaji Abubakar da Alhaji Bello suka wuce shikuma Kawu Yusuf don dole daddy ya riqeshi akan yabari sai gobe yatafi tunda har magrib tayi, haka ya haqura ba don yaso ba. Tare suka wuce masjid don yin sallar magrib suna tafe suna firar dalilin dayasa mutanen Deen basu zo ba Suna fatan allah yasa dai komai lfy. A bangaren zee kau sosai abin ya tsaya mata a zuciya takasa komai Ta rasa aciki me yafi damunta, rashin Zuwansu mutanen Deen ko rashin sanin halin da yake ciki. Banda hawaye babu abinda takeyi Dakyar tasamu itama ta tashi tayi sallar magrib ta kuma zauna anan tayi nisa a tunani har akayi sallar isha'i taje ta chanza alwalla tadawo ta miqata itama. Komawa tayi saman gado ta zauna jigum waya a hannunta har lokacin bata haqura da neman number tashi ba. Tana ahaka maid tashigo dakin akan ta sauko dinner is ready Cemata tayi ta tafi batajin yunwa Jin haka yasa daddy zuwa dakin nata da kanshi ya lalla6ota dakyar yasamu ta fito dining din. Saida ta gaida mutanen wajen cikin dashashen muryarta sannan ta zauna a kujerar da daddy yaja mata baya Zuba mata abincin daddy yashiga yi yana cewa "daughter please ki saki ranki, ki tuna da problem dinki, kibar saka abin arai sosai insha allah komai will be ok, kinji?" inji daddy Ahankali cikin sigar rarrashi Batace komai ba sai riqe fork din datayi tana dan motsa abincin ahankali Kawu Yusuf yace "Gaskiya ne diyata, karki bari abin ya dameki kinji? Insha allah zamu ji daga garesu soon" Itadai mummy ko dagowa batayi bare ta Ko kalli gefenta, abincinta kawai takeci amma ita kadai tasan irin 6acin ran datake aciki yau. "amma fa abin da daure kai, ina zasuje haka daxaisa suyi watsi da abu mai matuqar muhinmmanci irin wannan?" inji daddy "nima abinda ya daure min kai kenan Alhaji, koma menene kamata yayi su sanar sai ayimusu uzuri da lamunin daga ranar zuwa wani lokacin amma ai ba Haka akeyi ba ka tara mutane ka koma gefe kayi shiru ka barsu a shanye ba" "hmm to mudai fatanmu allah yasa lfy, duk wani abu dazai biyo bayan wannan mai sauqi ne" inji daddy "Amin fa Alhaji, fatanmu kenan" inji Kawu Yusuf din. Haka suka qaraci firarsu da daddy da Kawu Yusuf su mummy iyakarsu sauraro don babu wanda ya iya tankawa cikinsu, su kadai sukasan abinda sukeji a zuciyoyinsu. A daren ranar kasa isashen barci zee tayi, banda juyi daga farkon gado zuwa qarshenshi babu abinda takeyi Kwata2 takasa samun kwanciyar hankali bare salamar ruhi, ranar Saidai tayi barci rabi da rabi tasamu gari ya waye a daddafe. *WASHEGARI* Saida Kawu Yusuf yakai har 12 rana don jiran jin ko zasu samu wani feedback daga family dinsu Deen Amma shiru Hakan yasa yayi musu sallama ya kama hanyarshi ta komawa yana cewa duk yadda akayi sun gayamashi ta waya. Ranar ma haka ahalin gidan suka wuni cikin baqinciki don kwata2 babu alamun su Deen nada niyyar zuwa ko kira aji yaya ake ciki taqamaimai. Izuwa yanzu hankalin zee yafara tashi don ita yanzu ba rashin zuwan nasu ne yafi damunta ba rashin sanin halin da suke ciki yafi damunta gashi haryanzu numbershi bata shiga kwata2, daga jiya zuwa yau amsa dayace duk lokacin data buga wayar, switch off Tun tana daurewa tabar abin iya cikinta har takasa ta tunkari daddy da maganar don ko giyar wake tasha bazata ta6a nufar mummy da wannan maganar ba don haryanzu mummy bata sauka daga 6acin ran datake aciki ba Koda ta fadama daddy abinda ke damunta dakuma fargabar kar ace ba lafiya ba sai shima ya damu yana jin Gaskiya ya kamata a bincika Hakan yasa ya qara aika bala unguwar tasu Deen don ganin ko sun dawo gidan Amma daya dawo amsa daya ce haryanzu, gidan a kulle yake still da kwado kamar dai yadda ya ganshi jiya. Sosai hankalin zee yaqara tashi. To meya faru? Ina suke? Yaushe zasu dawo? Dama sauran tambayoyi da dama keta kai kawo a qwalwarta wanda duk babu mai bata amsoshinsu. Ganin yadda ta tashi hankalinta yasa shima daddy shiga damuwa sosai don shi yanzu baya qaunar abinda zai sakata a damuwa saboda maganar Dr dayayi akan a kiyayi barinta cikin damuwa, he can't afford to loose his only daughter just like that Hakan yasa yaita rarrashinta da kalamai na kwantar da hankali yana assuring dinta insha allah gobe zaije shima da kanshi yagani da kanshi. Hakan yadan kwantar mata da hankali har tadan samu taci abinci kadan wanda shima tutturawa kawai tayi bawai don dadi ba don kwata2 rasa abinda ke mata dadi a duniya tayi ga wani fargaba ta musanmman data addabi zuciyarta Mummy kau duk abinda suke ko kallo basu isheta ba don ita tun jiya zuciyarta ke cinkushe. Tarasa ma a wane siga zata kalli wannan al'amarin Qin zuwa sukayi da gangan koko akwai dai abinda ke faruwa? Sosai ranta ke a dagule saboda wannan abin daya faru Saidai kuma haryanzu takasa dora laifin akan Deen ta kuma kasa yarda da abinda zuciyarta ke saqamata na kodai Deen yaudarar zee yake dama bawai auranta yake so yayi ba? Da wannan tunanin yazo mata sai tayi saurin kawar dashi tana girgiza kai don Gaskiya Deen beyi kama da mayaudari ba kuma tana hangen soyayyar zee a idanunshi tsantsarta, to a ina matsalar take? Tabbas akwai lauje cikin nadi. Washegari kamar yadda daddy yayi ma zee alqawari wajajen bayan 12pm na rana ya shirya tsaf don zuwa dubowa shima don tunda gari ya waye zee ta matsa mashi akan Hakan Itadai mummy haryanzu batace uffan ba akan komai ba, yima takeyi kamar batasan sunayi ba. Har parking space ta raka daddy din tana jin kamar tace zata bishi itama suje su dubo tare. Saida taga fitarshi daga gidan sannan ta juyo a sanyaye tadawo falo ta zauna a kujerar da take facing kofar Shigowa ta raku6e ta zubama kofar idanu tana jiran ganin ta inda daddy zai dawo. A lokacin idan kaga Zainab dole tabaka tausayi, tawani yi laushi ta sururuce, kallo daya zaka mata kasan tana cikin damuwa sosai. Ta dade anan zaune tana counting down din seconds daya gota ma agogo tana jiran ganin dawowar daddy, deep down kuma addu'a kawai takeyi allah yasa adace don yanzu idan akwai labarin da zaisata cikin matuqar farinciki to na ganin Deen ne, kawai ita dai burinta aganshi a tabbatar da lafiyarshi lau. Har 2pm ta gota daddy be dawo ba hakan yasa ta tashi don dole ta wuce sama don yin sallar zuhr. Tana zaune akan sallaya ta gama sallah taji horn din mota a bakin gate Aikau babu shiri ta tashi tsaye tanufi windon nan da sauri ta yaye labulen Motar daddy ta hanga tashiga parking space. Sakin labulen tayi ta juyo tanufi kofa da sauri. Budewa tayi ta fita ta sauko stairs din tana tsallakesu da bibbiyu harta samu ta ida saukowa. Daidai takai hannu a handle aka murda handle din daga waje aka turo kofar. Jan burki daddy yayi da farko ganinta a bakin kofar saikuma ya Kamo hannunta ya maida kofar ya rufe ya shigo falon still jaye da hannunta "daddy ka ganshi? Daddy sun dawo? Are they ok?" abinda take fada kenan tana Binshi har suka qaraso wajen wata kujera mai daukar mutum biyu ya zaunar daita. "daddy ya akayi ka dade? Sun dawo ne? Nasan sun dawo ko?" "shhh ya isa hakannan sweetheart kinji? Ya isa, now shaqi numfashi..." Shaqa tayi yadda yace "to fesar... Yauwa to qara Shaqa... To fesar... Yauwa daughter na, ki daina magana babu ko sayawa numfashi kinji, it's not Good for the health" "daddy... Deen" yadda tayi maganar yasa yaji jikinshi yayi sanyi sosai "daddy please say something, ka gansu ko?" taqara fada tana kallonshi da gajiyayyun idanunta wadanda sukayi jaa sosai bawai don kuka ba sai don tashin hankali da rashin isashen barci Cupping fuskarta daddy yayi a hannunshi Hakan yasa zee zubamashi idanu itama tana kallonshi "dear, please calm down, banaso kina tada hankalinki" Tunda yafara maganar tashiga Kada kai yana gamawa tace "to daddy, to nabari, please tell me, where is he?" Tausayinta yasake lullu6e daddy ganin kamar ma ba'a hayyacinta take ba. Dagowa yayi ya kalli mummy da itama saukowarta kenan ta tsaya daidai bakin stairs itama tana kallonsu. Maida kallonta yayi akan Zainab din daketa kallonshi itama tama kasa hadiye miyau don fargaba Sake Cupping din fuskarta yayi ahankali sannan yace "Zainab karki tashi hankalinki kinji? Please" Banda Kada kai babu abinda takeyi cikin sauri tana kallonshi "dear haryanzu basu dawo ba, gidan arufe da padlock kuma babu wanda yasan inda suka tafi da lokacin da suka tafi kawai wayan gari sukayi sukaga babu su a gidan, har mai gidan daya basu haya Saida aka hada ni dashi amma shima cewa yayi besan komai gameda tafiyarsu ba don bawai kudinsu ne yaqare ba Suna da kingin kudi harna wata 3 a wajenshi. Abin dai da daure kai, bansaniba qila travelling sukayi garinsu ko something like that" _wow! I love travelling!_ _nima zanso watarana nayi tafiya wani wuri_ Tunawa tayi da maganarsu ta kwanaki To amma ina zasu tafi yanzu ana school, lokacin da ma exams keta matsowa? "Daddy please ina zuwa, nima zanje nagani" tafada pleadingly "Me zaki gani?" inji daddy "gidan nasu, please bazan samu rest of mind ba idan ban gani ba" "kina hauka ne?! Ina kika ta6a ganin anyi haka? Ace saurayi ya turo magabatanshi yaqi turowa kuma don rashin sanin ciwon kai sai budurwar tabi shi har gida?" inji mummy tana qarasowa dakin Sadda kanta zee kawai tayi qasa not saying anything Saidai ita kadai tasan abinda zuciyarta keyimata "kawai a kyalesu aga iya gudun ruwansu, ai zasu dawo kuma am betting you zasu zo har nan su fadamana komai" inji mummyn tana zama itama kan kujerar kusa dasu Ganin yanayin zee yasa daddy cewa "tashi ki shirya mutafi" Saurin dagowa zee tayi ta kalleshi trying to believe what she heard "haba Alhaji, ya zakace haka kuma?" inji mummy "maimuna kinsan condition din yarinyar nan tunda dake akayi mana bayani, why zan bari najama kaina bala'i? Idan zuwan zai saka hankalinta ya kwanta, fine" "to amma saboda allah Alhaji wannan ai xubar da qima ne" Kallon zee da murnarta tafara komawa ciki daddy yayi yace "jeki shirya ki sauko mutafi" Aikau kamar akan qaya take dama tayi saurin miqewa ta wuce sama da sauri Daddy ne ya kalli mummy "please maimuna kabari taje tagani for herself, Hakan zaisa hankalinta kwanciya" "amma Alhaji idan kukaje akayi daidaitoni sun dawo fa? Sai kawai suga kunje nemansu, suruki da budurwar da za'azo neman aurenta aka fasa sun biyo saurayi har gida? Wannan ai xubar da mutunci ne" Dan murmushi daddy yayi sannan yace "ni lafiyar diyata ta fiyemin komai, ina iyayin fiyeda Hakan ma saboda ita" Daidai nan zee ta sauko daga sama ta chanza kayan jikinta zuwa blue black jallabiya Tashi daddy yayi shima ya miqo mata hannu ta taho ta kama hannun tana avoiding idanun mummy Tasan abinda takeyi ba girmanta bane kuma ba ajinta bane amma ya ta iya? Abinda zuciyarta ke ingixata tayi kenan kuma a halin yanzu batada wani za6i sai na bin umarnin zuciyar tata don kwata2 a wannan fannin bata iya controlling dinta. Ficewa sukayi daga falon mummy na binsu da kallo. Parking space daddy ya nufa riqe da hannunta Hakan yasa bala dake can wajen security rugowa da gudu ya rigasu isa motar ya bude masu backseat. Da daddy yaso yayi driving din sai kuma yafasa ganin balan duk sai suka shige backseat din ya rufo musu kofar sannan shima ya zagaya mazaunin driver ya bude yashiga. Tada motar yayi sannan yayi reverse ya kama hanyar gate din da security yariga ya wangale musu suka fice daga gidan. Tafe suke cikin normal speed motar tayi tsit bakajin komai sai alamun tana tafiya da zakaji Zee a bangarenta a matuqar darare take, a qagare take su iso unguwar dukda yadda zuciyarta ke qara gudun bugu duk kusancinsu da unguwarsu Deen din. Daddy daya lura da uneasiness dinta ya damqe hannunta acikin nashi Hakan yasa ta juyo ta kalleshi Kada mata kai yayi alamun ta kwantar da hankalinta Dry murmushi tadan yimashi tareda Kada mashi kai shima ta Janye idanunta ta maida kan glass din gefenta. Basu qara jimawa suna tafiya ba suka qaraso unguwar tasu. Bugun da zuciyarta keyi sai ya linka na dazu Tanaji bala ya sauko daga motar sannan ya zagayo ya bude masu Daddy shi yafara fita sannan ya miqo mata hannu. Cikin sanyi itama ta miqa hannun nata ta kama nashi sannan tafito da taimakonshi. Ganin Hakan yasa bala maida kofar ya rufe ya matsa gefe. Dagowa zee tayi ta kalli kofar gidansu Deen din wanda kamar yadda masu zuwan ke fadi rufe take da qaton kwado Qurawa kofar idanu tayi ko kyaftawa babu tana jin yadda zuciyarta ke bugawa sosai "basu nan, tun wancan jiya din muma munzo siyan koko basunan" suka tsinkayi muryar yar yarinya tana fadin haka Duk juyowa sukayi suka kalleta Hakan yasa yarinyar tasha jinin jikinta Kafin wani cikinsu yayi magana harta juya ta arta a guje. Binta da kallo duk sukayi ahakan sukaji muryar wani mutum nacewa "A'a Alhaji, sake dawowa kayi?" Sake juyowa sukayi kan mutumin (mallam Nasiru) daddy yace "wlh kau ka ganmu munsake dawowa? Dawowa mukayi muga ko za'a dace da sun dawo" "wlh kau Alhaji kaga dai basu dawo ba, abin da matuqar daure kai don wlh ranar daren da zamu wayi gari muga gidan a kulle tareda Deen din muka fito daga massalaci bayan sallar isha'i kuma Koda wasa be gayamin zasuyi tafiya ba bare inda zasu din abinda basu ta6a yiba don wlh kamar yan uwan juna haka muke komai namu sun sani suma haka, bansan ya akayi ba wannan karon" inji mallam Nasiru "to ko wajen wasu danginsu suka je ko yan uwa haka? Kasan inda wasu nasu haka suke?" inji daddy Girgiza kai mallam Nasiru yayi "Gaskiya A'a don tun Zuwansu nan unguwar duk kusancinmu bata ta6a nuna mana wani nasu ba ko yan uwansu bare akai ga maganar inda suke kuma bamu ta6a ganin wasu nasu sun kawo masu ziyara ba" Shiru wajen ya dan dauka "to sun kai shekaru nawa da dawowa nan?" inji daddy "Ca6! Gaskiya sun dade sosai don aqalla sunkai shekaru goma sha biyu a nan lokacin tun banma dade da aure ba" "kuma ace duk lokacin babu wani nasu daya ta6a zuwa masu?" inji daddy cikin alhini "to banace ba Alhaji tunda qila suna zuwa ko su sukan je mune bamu sani ba Amma dai bata ta6a gwadamana wani ko wata a matsayin yan uwansu ba" Daidai nan wani saurayi ya qaraso wajen yana masu sallama Duk juyowa sukayi wajenshi suna amsa sallamar "A'a salmanu kaine?" inji mallam Nasiru Cikin murmushi ya amsa da eh sannan yashiga gaidasu sukuma suna amsawa "dama yanzu ina gida zan fita qanwata rahma tashigo gida aguje wai ga wasu masu mota can kofar gidansu Deen shine nace bari nazo qila kune wadanda nake nema" Duk maida hankalinsu sukayi akanshi gabadaya Kallon zee salmanu yayi yace "kece Zainab?" Gaban zee ne ya fadi Kasa amsawa zee tayi sai kallon daddy datayi tasake maido kallonta akan salmanun "eh itace dan samari, fatan dai lfy?" inji daddy "eh lafiya lau, dama Deen ne yabani saqo wai idan wata Zainab tazo inbata" Gaban zee yaqara yankewa ya fadi tanajin zuciyarta na qara speed Karkatawa yayi ya zura hannu aljihu yana cewa "wlh ranar talata da daddare yabani bayan mun fito daga massalaci wai don Allah wata Zainab zatazo wai inbata dana tambayeshi shi me zai hana yabata sai cewa yayi ai tana iya zuwa shikuma a lokacin yatafi school gashi saqon nada matuqar muhinmmanci bazai yiwu taje ta dawo ba To tun lokacin na amsa sai kuma aka wayi gari gidansu a kulle. Haka na wuni ranar ko aiki banje ba don gudun kar natafi yarinyar kuma tazo gashi yace saqon nada matuqar muhinmmanci, to amma shiru har dare banga wulgin kowa anan ba To shine naketa ajiya kuma ina dan zagayowa ina kuma sa qannena suna dubamin ko wata zatazo nemanshi. To yanzu ma na dawo gida ne naci abinci ina shirin fita rahma tashigo aguje wai ga wasu masu mota can kofar gidansu Deen shine nace bari nazo nagani ko za'a dace" ya qarashe zancen yana Miqama zee wani brown envelope daya zaro daga aljihun wandonshi "ki duba kigani ko naki dinne" yafada yana sake miqa mata Kasa amsa tayi sai kafe envelope din datayi da idanu Tanajin kamar zuciyarta zata faso qirji saboda bugu "dear ki amsa ki duba" inji daddy cikin sanya qwarin gwiwa Kallon daddyn tayi sannan taqara kallon wasiqar, sannan ahankali ta dago hannunta dake rawa rawa ta amshi envelope din. Jujjuya envelope din take a hannunta tana fargabar budewa Dafa kafadarta daddy yayi Hakan yasa taqara Dagowa ta kalleshi Kada mata kai yayi cikin qarfafa gwiwa Hakan yasa ta sauke wata nannauyar Ajiyar zuciya sannan ahankali hannu na rawa ta farke envelope din taga wata ninkakkiyar farar takarda ta bayyana Gabanta ne yasake tsinkewa Duk ita mutanen wajen suka zubama ido in curiosity suma Zare takarda tayi tasaki yagaggen envelope din aqasa Ahankali ta shiga warware takardar hannunta hannunta na rawa, zuciyarta na rawa kai komai ma nata rawa yakeyi da za'a auna jininta a lokacin da ta tabbatar da za'a ga yakai maqurar hawa. Unique handwriting din da shikadai tasani dashi yafara yima idanuwanta maraba Ahankali tafara bin abinda yake cikin takardar tana karantawa _*Nasan lokacin da wannan takardar zatazo miki na riga nayi nisa.*_ _*Bansan me zance maki ba, bansan ta ina zanfara ba, bansan da wadanne kalamai zanyi amfani dasu ba*_ _*daren ranar danake rubuta wannan takardar shine mafarin duhun rayuwata, Koda gari ya waye wa kowa ni bazai waye min ba, ba yanzu ba kuma bana jin lokacin zai ta6a zuwa*_ _*zan cigaba da kasancewa a duhun ne qila har ahada, Domin nariga nayi nisa da hasken dazai haskaka min rayuwata*_ _*ina sonki*_ _*nasan yanzu ba lallai bane ki yarda da Hakan ba kuma nima ban cancanci na fadamiki Hakan ba*_ _*amma that's the pure truth.. Ina sonki, zan cigaba da sonki, wataqila ma sonki ne ajali na*_ _*am sorry... For every thing.. Da abubbuwan danasaki fuskanta da wanda zan saki fuskanta*_ _*kin dauki zuciyarki dunqullala kin bani amana nikuma na raratsata ta zuba a plate na maido miki*_ _*ban cancanci yafiyarki ba zee, ban cancanci gafararki ba Amma Hakan bazai hanani neman gafararki ba*_ _*ki yafemin Zainab... Don Allah.. Ba don niba.. Don girman allah👏😭*_ _*natafi.. Am gone.. Maybe forever maybe not*_ _*I LOVE YOU*_ Ahankali takardar ta sulale daga hannunta "daughter!!" taji muryar daddy na cewa haka da qarfi sai kuma taji an riqota gamm "innallilahi waina ilaihi rajiun! Zainab! Ki bude idanunki ki kalleni, please don't do this" tasake jin muryar daddy sama sama ana dan bubbuga mata kumatu Amma the more takeson bude idanun the more yake qara rufewa "Zainab!! Innallilahi waina ilaihi rajiun! Jama'a ku taimaka min! Zainab!!" "DEEN..." Kalmarta ta qarshe kenan idanun suka rufe ruff... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:39 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *052* *HEARTBREAK 💔* _jiya kasa yiwa kowa reply nayi_ _Everyone is saying why? Why? Why?_ _that's destiny kuma komai yanada reason na faruwarshi kuma idan akasa hqr ahankali ahankali komai zai warware_ _dama tun farko nariga na fada cewa wannan story din ya qumshi, true love, heartbreak da sadaukarwa. Don haka sai kuyi hqr don yanzu muka fara zuwa inda na dade inason muzo, insha allah komai zai warware and Gaskiya zatayi halinta sooner or later_ _sorry for the heartbreak 😞_ _Hajiya am'ash mai jiran sai komai ya warware sannan ta cigaba da karatu, comgratulations, qila sai munzo semi-final zakiyi joining dinmu 😆_ Dagudu security din gate din asibitin ya qarasa gate din ya shiga wangale masu gate din. A tsiyace motar tashigo harabar asibitin, maimakon tayi parking space sai tayi hanyar entrance din hospital din ta tsaya few feet da tudunkar entrance din. Already su likitoci da nurses duk sun fito nurses din riqe da dan gadon nan na gurgura marassa lafiya Kofar baya aka bude sannan daddy yafara qoqarin tattarota ya dauketa amma yakasa saboda rawar da jikinshi yakeyi Ganin Hakan yasa su likitoci matsowa suma da taimakonsu aka fiddo zee da komai nata yasaki kamar gawa don idan bama lura kayi ba sai kace ma bata numfashi kwata2 Akan gadon aka dorata sannan duk aka shiga turata dagudu aka nufi cikin hospital din Duk inda suka wuce sai mutanen dake kai kawo wajen sun tsaya suna kallonsu don ganin yadda ake gurguro gadon da mutanen dake Binshi dagudu ya isa ya nuna cewa koma wa ke saman gadon yana cikin very critical condition. Emergency room suka nufa, tun kafin su qaraso aka bude masu kofa kuma suna shiga aka rufo kofar wanda Hakan yasa su daddy da bala jan burki bakin kofar. Dafe kanshi daddy yayi ya juya yashiga yin safa da marwa cikin mugun tashin hankali. Shima bala was restless, shima tashin hankaline rubuce koina a fuskarshi. Acan kau a wani daki aka shigar daita akayi transferring dinta daga gadon mai taya zuwa na cikin dakin. Nan take likitocin guda uku suka rufa akanta suka fara baje basirarsu wajen ganin sun shawo kan matsalar Na farko numfashinta dayayi mugun qasa suka shiga qoqarin jawoshi su daidaitashi. Sosai suke aikin babu kama hannun yaro suna iya bakin qoqarinsu na ganin sunyi saving life dinta don ahalin yanzu tana cikin very critical condition. Daddy kau kasa tsayawa wuri guda yayi, safa da marwa kawai yakeyi cikin tsananin tashin hankali, idan ya kalli kofar da aka shiga da zee sai yaji kamar yaje ya 6allata yashiga yaga wane hali take ciki. Babban tsoronshi shine kar ciwon ta ya tashi wanda Dr yafada musu wancan karon, he's scared, bazai iya musalta rayuwa babu sanyin idanunshi Zainab "Hasbunallah wa ni'imal waqeel! Innallilahi waina ilaihi rajiun! Innallilahi waina ilaihi rajiun! Ya allah help me, don’t take her away From me now, not now please, I can't take it" yafada cikin tsananin tashin hankali still yana zirga zirganshi "Alhaji kayi hqr, insha allah zata tashi, insha allah allah zai tashi kafadunta" inji bala cikin tausayawa da son qarfafa mashi gwiwa Ko kallo be isheshi ba ya cigaba da zirga zirganshi yana cigaba da sambatunshi Sosai likitocin suka jigatu kafin su samu su daidaita numfashinta don dole suka maqalamata abin oxygen a hanci wanda zai taimaka mata wajen numfashi Sosai jikin family Dr dinsu yayi sanyi liqis don qaryar dasukayi wancan karon itace ta tabbata Jinin zee yayi mugun hawa, hawan da ba'aso saboda hadarinshi. Saida suka shafe fin awa sannan suka samu komai yadawo daidai suka fito kowannensu na sharce zufa Daddy na ganin sun fito ya nufosu da sauri kamar zai kifa qasa "Dr ya ake ciki? How's my daughter?" yafada ajere Daya daga cikin doctors din yace "calm down Alhaji, komai yadawo normal yanzu insha allah" "to muje naganta, I want to see her" yafada zaiyi hanyar dakin da aka kwantar da ita din Taroshi ainahin Dr dinsu yayi yana cewa "A'a sir, not now yanzu ba'ason kowa yashiga wurinta, ka kwantar da hankalinka insha allah she's safe now, muje office mu tattauna" Dakyar suka samu ya haqura da shiga din yabisu office din don tattaunawar kamar yadda sukace. *** "inajinku Dr(s), don Allah karku fadi abinda zai bugarmin da zuciya" inji daddy da kallo daya zakamashi kasan yana cikin tension sosai Daya daga cikin likitocin ya sauke Ajiyar zuciya yace "Alhaji ka kwantar da hankalinka kuma kasa aranka dik abinda yasamu mutum jarabtace daga allah, da lafiya da rashinta dik na allah ne..." "Duk nasan da wadannan Dr, basu na tambaya ba, lafiyar diyata nakeson ji" inji daddy cikin qosawa Dayan likitan yace "alhamdullilah Alhaji, yanzu mun samu mun shawo kan komai, dama jininta ne yayi mugun hawa, hawan lokaci daya wanda Hakan keda matuqar hadari don a wasu unlucky case din sai kaga mutum ya fadi sanadiyar Hakan ya tashi da mutuwar 6arin jiki amma alhamdullilah nata yazo da matuqar sauki plus ankawota asibiti da wuri an takama abin burki cikin gaggawa, saikuma numfashinta dayayi qasa sosai yana neman seizing shima mun samu shawo kan Hakan yanzu Hakan tanacan maqale da abin oxygen wanda ke taimaka mata wajen daidaita mata numfashinta" Dafe kai daddy yayi yana kallon saman desk din gabanshi not saying anything, shi kadai yasan halin dayake ciki "kayi hqr Alhaji, insha allah all will be well" inji wanda yagama bayanin yanzu "to yanzu ina iya ganinta please" inji daddy "No Alhaji, kayi hqr don Hakan sa6ama doka ne, tana intensive care yanzu babu mai shiga wajenta yanzu sai doctors" "Koda ba ciki ba, Koda tawaje zan hango ta ina dai son ganin halin datake aciki ne" inji daddy Kallon juna likitocin sukayi sai family Dr dinsu yayi Ajiyar zuciya yace "muje Alhaji" Jin Hakan yasa Alhaji miqewa da sauri Dr din yayi gaba shikuma Alhajin yabishi abaya suka fice daga office din Kamar yadda sukayi lokacin da aka kwantar da Deen a asibitin haka akayi wannan karon ma Recording room suka wuce inda anan aka haskoma daddy dakin da zee ke Kwance Ganin zee Kwance kamar bata numfashi maqale da wannan abin a hanci ba qaramin girgiza zuciyar daddy yayi ba Qurawa Mafi soyuwar diyarshi ido yayi yana jin kamar ya dauke mata ciwon ya maido jikinshi. Idanunshi daya quramata sun kada sosai zuciyarshi banda zafi babu abinda takeyi Juyawa yayi don bazai jure kallonta a wannan halin for a long time ba Bude kofar wajen yayi ya fita. Bala dake zaune Tundazu ganin daddy ya fito yana tafiya kamar wanda zai tashi sama yasashi saurin miqewa tsaye Ganin waje ya nufa yasa shima yin saurin take mashi baya. Dagudu ya rigashi isa motar ya budemashi. Shigewa yayi batareda ya kalleshi ba yana daddana wayarshi at the same time. Rufo mashi bala yayi ya zagaya dagudu gaban motar ya bude yashige shima Tada motar yayi daidai lokacin dayaji daddy na cewa "wlh bazan bar yaronnan ba, duk inda yashiga sai an nemoshi kuma wlh wani abu yasaki yasamu diyata just hold yourself responsible tunda harda hadin bakinki wajen cutar ta!" Kana jin yanayin yadda yake magana zakasan ranshi a matuqar 6ace yake "just shut up! Duk ba ke kikafi bada gudunmawa a komai ba?! Dama ni tun farko ban yarda dashi ba Amma kika nace, kuka nace! To gatacan ya kasheta, ga gawarta can hospital saiki zuba ruwa qasa kisha, dama ai ba sonta kike ba! Mtcheew" Ya katse kiran cikin qunar zuciya yana huci Kallon bala dake driving yayi sai ya daka mashi tsawar da yakusan sawa ya saki sterring din "gidan ubanwa zaka kaini! C'mmon kaini police station! wlh zai san ya ta6a jinina! Saisan Jinin dan faranshi ya ta6a!" Shidai bala daya samu ya iya ruqo sterring din daga kufcewar dayaso yi yayi u-turn ya kama hanyar nearest police station kamar yadda ya buqata Sosai hankalin mummy ya dugunzuma ya tashi Babu abinda ta fahimta a magangganunshi sai gatacan ya kasheta, ga gawarta can hospital Gawar wa? _wa suka fita tareda shi?_ zuciyarta ta tambayeta _Zainab?!_ Babu shiri ta bude daya daga cikin locker dinta ta zari makullai ta Ciro na mota aciki ta figi gyallenta ta yafa ta fice daga dakin hankali tashe Saukowa tayi qasa ta wuce kofar fita cikin sauri ta bude ta fita ta maido ta rufo Parking space ta nufa ta danna remote din car key din don rikicewa ma ta hana tasan makullin wace mota ta dauko Motar dataji tayi tsuwa ta nufa ta bude mazaunin driver tashiga sannan ta maida ta rufe sannan ta tada motar tafito daga parking space din tazo tawuce security din daya bude mata gate din ta fice in speed. A bangaren daddy kau suna isa police station ya sauko ya shiga ciki kamar zai tashi sama Kasancewarshi na babban mutum kuma shahararre yasa babu 6ata lokaci aka hada shi da d.p.o kamar yadda ya buqata. Anan ne yayi stating qarar Deen daya kawo ya hada da qarya da Gaskiya ya fada aka rubuta Sannan yasa a nemoshi duk fadin Katsina dama kewayenta yakuma yimasu albishir din kyauta mai tsoka muddin suka samo mashi shi. Abinka da abin manya nan da nan aka bazama neman Deen, aka bugamashi tambarin *WANTED.* Ganin komai ya tafi yadda yakeso saiya baro police station din yadawo asibitin Suna yin parking ya bude kofar motar yafito batareda ya jira bala ya zagayo ya budemashi ba. Direct emergency ya nufa ya kama hanyar ward din zee. Tun daga nesa ya hango mummy zaune akan bencin dake kofar ward din Ranshi ne yaqara 6aci Hakan yasa ya qara tamke fuskar kamar hadari Dagowa mummy tayi da idanunta dasukayi jajur wanda da alama itama kukan tayi ta kalli daddy daya qaraso wajen. Kasa yimata masifar dayayi niyyar yimata yayi sai kawai ya cigaba da binta da mugun kallo mai cike da haushi da takaici Sauke kanta tayi qasa itama tana share hawayen dasuka sake gangaromata. Juyawa yayi kawai ya kalli gefe yana jin 6acin rai har lokacin Haka yaita tsayuwa yana kallon gefe itakuma tana zaune kanta a qasa babu mai cewa uffan Can dai daya gaji da tsayuwar saiya wuce ya kama hanyar dazata sadashi da office din Dr din nasu. Cikin gari kau neman Deen ake takoina, bincike akeyi babu kama hannun yaro yadda kasan wani kasurgumin 6arawon daya kufce suke nema. Har school Saida yansandan sukaje bincike aka dauko masu file dinshi inda anan dinma basu samu wani gamsashen information dazai basu hint din inda yake Acan unguwarsu ma akwai yansandan da aka tura can Inda anan aka kirawo mai gidan da suke zaman hayan gidanshi Tambayoyi harna innanaha Saida sukayi ma mutumin sai abinma yayi kamar zai juye kanshi don sai tuhumarshi suke wai ya za'ayi yaba wadanda besaniba kuma besan kowa nasu ba haya? Haka aka taru a kofar gidansu Deen din anata abu guda inda shima mallam Nasiru akaso shafa mashi shima wai ai shima yanada kusanci sosai dasu don haka dole yasan wani abu gameda guduwansu. Abu dai ya cakule ya rikice don tuni unguwar ta dauki shelar ashe su Deen yan danfara ne? Danfara sukayi suka gudu gashi anzo ana nemansu ruwa ajallo Kan kace me? Maganar tayi spreading kamar gobara a busassun ciyayi, inda Mafi yawancin mutane suka yarda suna allah wadai dasu, qalilan kuma basu yarda ba Suna cewa sharri ne ciki harda baaba abu data yini kuka. Daga baya dai 6alle kofar akayi aka shiga gidan aka bincikeshi kaff Komai na gidan na nan except kayan sawansu Hakan yasa aka maida aka kulle akan zasu dinga dawowa akai akai don bincike suka kuma sanar duk wanda yaga wulginsu yayi maza ya sanar dasu don cafkesu. Sosai jikin mallam Nasiru yayi sanyi dama mutanen unguwar gabaki daya. Matar mallam Nasiru kau itama kuka taitayi tana rantse rantse akan wlh qazafi ake musu babu yadda xa'ayi Deen ya iya danfaran mutum. Haka dai unguwar nan ta Wuni da zancen bayin allah nan a bakunan mutanen unguwar, abu dai babu dadi A bangaren zee kau har dare bata farfado ba Da farko likitocin cewa sukayi suna iya tafiya basai an kwanan mata ba Amma cikin daddy da mummy aka rasa wanda zai yi yadda suka ce din Anyi rarrashi anyi komai amma ko motsawa daga inda suke basuyi ba hakan yasa aka kyalesu kawai aka basu wani ward din dake gefen na zee don suyi spending dare aciki. Haka suka kwana a asibitin ko kalma daya bata shiga tsakanin mummy da daddy ba. Shi daddy najin haushin mummy don gani yake duk itace silar komai itakuma mummy damuwar datake cikima ya isheta kaya. Haka sukayi kwanan zaune duk babu wanda ya iya barcin kirki ita mummy daga baya ma wajajen 4am ta tashi tafara nafilfilu har asuba tayi ta dora da sallar asuba shikuma daddy ya fice massallaci. A taqaice dai Saida zee ta kwana biyu a wannan dakin da ba'a shiga ganinta a kwana na uku aka chanza mata ward inda lafiya lau ana iya zuwa ganinta Saidai shima banda hayaniya izuwa lokacin anriga ancire mata abin oxygen din hancinta don tana iya breathing da kanta Izuwa lokacin duk yan uwa da abokan arziqin su mummy da daddy sun sani Yan Ruma dama yan uban su daddy labari yakai musu Hakan yasa sai tururuwar zuwa ganinta akeyi. Daddy su biyu mahaifiyarshi ta haifa dashi da qanwarshi Ummu batool sannan tafita daga gidan inda anan tabar daddy wanda yasha wahalar matar uba da yaranta sosai. Be samu sauqinsu ba Saida yashiga secondary school aka sakashi boarding, to tun lokacin yaja baya Sosai da yan uban nashi dama gidan uban nashi gabadaya don ko hutu akayi gidan da mahaifiyarshi ke aure nan yake zuwa ko kuma yayi hutunshi a school din. Ana haka allah yayiwa babbansu rasuwa lokacin yana S.S 2 To rashin mahaifin nashi a gidan yasa ya ida qauracewa gidan don Koda aka raba gado ya tsira da daki daya acikin gidan siyarwa yayi ga babban wansu don a lokacin idan akwai abinda ya tsana to gidan ne da ahalin ciki. To ahaka daddy ya cigaba da karatunshi mahaifiyarshi na taimaka mashi da mijinta shima kuma yana yan buga buganshi har yasamu ya qare secondary school din ya shiga jami'a inda yashiga course din business saikuma ya hada karatun da zuwa kasuwa inda ya kasance yaron shagon wani babban dan kasuwa a kasuwar garin nasu. Ahaka ahaka har yayi graduating lokacin ya goge sosai a harkar business shiyasa Koda shima yafara cikin qanqanin lokaci abin ya bunqasa allah yasamashi albarka a harkar, abin yaita gaba gaba har yakai matsayin dayake aciki yanzu. Shekara daya da yin auren daddy da mummy allah yayiwa mahaifiyar daddy da mijinta rasuwa a wani hadarin mota dasukayi a lokacin zasu kai ziyara garinsu mijin. Shiyasa yanzu bayada dan uwa makusanci sosai kamar Ummu batool wanda ke aure Dubai tanada 'ya'ya biyu, namiji da mace Namijin mai suna Abubakar sadeeq amma kasancewar sunan uban mijin Ummu batool ne dashi sai aka sakaya sunan ana kiranshi da *Aymaan* ita kuma macen sunanta Fatima amma itama ana kiranta da *Batool* Tsakanin daddy da yan ubanshi babu yabo babu fallasa ana dan zuminci sama sama kuma dama suma mahaifiyarsu ta dade da rasuwa kuma duk yawancinsu ba agarin suke ba musanmman matan wadanda aure ya kaisu wasu wuraren. Bama cika sanin halin da junansu suke cikiba inba ta kama ba don sosai zumincinsu keda rauni bama zaka ta6a cewa sun hada uba ba. To a wannan case din yarasa wanda ya gayamasu ma don shidai be gayamasu ba Saidai kawai yaga wasunsu sunzo dubiya. A bangaren abokan aikinshi ma duk sun zozzo inda amininshi baban asaad shine gaba akan komai don shima sosai ya nuna damuwarshi akan hakan don yama kusan fin daddy nuna damuwa. Suma yan Ruma sun zozzo ganinta inda duk yawancin wanda yaji labarin abinda yafaru sai ya jajanta inda mafiyancinsu ke xagin Deen dama yima samari gabadaya kudin goro acewarsu dama samarin yanzu duk tarin mayaudara ne da wuya kasamu mai so don Allah A bangaren yansanda kau haryanzu neman Deen suke Saidai cikin kwanakinnan ko mai kama dashi basu gani ba kuma har lokacin basu samu wani kwakwaron hint ba na inda zasu ganshi Kwanan zee biyar a asibitin a daren kwana na biyar din ta farka. Lokacin mummy nakan sallaya ta idar da sallar isha'i kenan kamar ance ta juyo sai gani tayi tanata marr marr da idanu alamun sotake ta budesu Ganin Hakan yasa ta tashi da sauri tazo bakin gadon tana kallonta. "Zainab" ta kira sunanta Cigaba da qoqarin bude idanun zee tayi Hakan yasa mummy ta juya ta fita daga dakin don kiran doctor Fitar mummy keda wuya idanunta suka bude ahankali. Hasken dakin daya haske mata idanu yasa taqara maidasu ta rufe can kuma taqara budesu ahankali tana jin yadda sukeyi mata wani yaji yaji. Ahankali take wurwurga idanun nata don tantance inda take. Bata ida tantancewa ba mummy da doctorn dataje kirawowa suka shige shigo dakin. Saurin Qarasowa bakin gadon sukayi gabadaya suna kallonta itama tana kallonsu kamar mai son karantar wani abu a fuskokinsu Babu 6ata lokaci Dr yashiga dubata ita kuma zee ta maida idanunta ta rufe trying very hard wajen son tuno abinda yafaru _gobe ne_ Ta tuna Maganarshi ta last call dinsu dasukayi a daren ranar introduction _I LOVE YOU_ ta tuno kalmar qarshe data karanta a wannan takardar _natafi... Am gone... Maybe forever.. Maybe not_ Ahankali ta bude idanunta lokaci guda dukkanin abubbuwan dasuka faru suna rushing back a kwalwarta _I LOVE YOU_ itace kalmar qarshe data karanta daga haka batasan abinda yasake faruwa ba sai yanzu data bude idanunta And then she realize, she realize cewa yafadi Gaskiya.. Yafadi Gaskiya dayace ya rarratsa zuciyarta into pieces don yanzu haka abinda takeji kenan Jin zuciyarta take kamar glass din da ake rarratsewa into tiny tiny particles Zuciyarta taji rauni, mummunar rauni don yanzu haka bleeding take, unstoppable bleeding Kuma the worst thing shine wanda duk duniya tafi so tafi bama yarda shine silar wannan raunin Shine ya luma mata kaikaifan wuqa a qahon zuciya ya barta aciki yayi tafiyarshi _*DEEN*_.... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:39 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *053* *INCOMPLETE* Ahankali ta maida idanun ta lumshe tana hadiye yawu ahankali. Zafi takeji, zafi mai mugun radadi a zuciyarta, jitake kamar ana gasa mata zuciyar ne a oven kuma ana tarfa mata narkakkiyar darma. Abinda takeji bazai iya musaltuwa ba koda zata musalta bazaka ganeba inba kaima tsintar kanka kayi aciki irin halin datake ciki kayi ba wanda bata fatan ko maqiyinta yashiga irin halin data shiga "sannu Zainab" inji Dr yana kallonta Bata bude idanunta ba Haka ma bata motsa ba bare asa ran zata amsa "Me kike ji yanzu? Kina jin wani ciwo?" inji Dr din again yana kallonta keenly Nan ma ko motsawa batayi ba "Zainab.." taji tender voice din mummy Ahankali ta bude lumssasun idanun nata ta dagasu ta zubama mummy din Wani irin tausayinta ya tsirgama mummy ganin irin kallon datake mata, a very painful look Sanin abinda tafi buqata yanzu yasata Qarasowa ta zauna gefen gadon ta kama hannun zee dake daure sa cannula tana kallonta Itama zee ita take kallo babu ko kyaftawa Ahankali mummy ta jawota jikinta tabata warmly mother's hug wanda ta rabu da yimata Wani nannauyan Ajiyar zuciya zee ta sauke tana qara cusa kanta a wuyan mummy Lumshe soyayyun idanunta tayi tasake budewa Da ada ne da yanzu tafara hawaye ko kuka amma yanzu shiru kakeji, sotake tayi amma ya gagara, idanunta sun bushe, zuciyarta ta soye, kukan is nowhere to be found Dagota mummy tasakeyi tana kallonta, lumshe idanu zee taqarayi ta bude su akan fuskarta itama "Are you ok dear?" inji mummy tana kallonta cikin kulawa Wani dan murmushi ya kufce mata wanda kallo daya zakamashi kasan murmushi ne mai ciwo Ji mummy tayi kamar tayi mata kuka, dukda bazata iya cewa tasan exactly abinda zee keji a zuciya ba Amma tasan dole yanzu she's in pain "meke yimaki ciwo? Kifada kinga sai Dr ya dubaki" inji mummy tenderly Kama hannun mummy zee tayi ahankali sannan ta dora saitin zuciyarta daketa halbawa in speed Saurin kauda kai Mummy tayi sanadiyar hawayen dasuka kuftomata sai kuma tajuyo tajawo Zainab a jiki ta rungume qamm Qara cusa kanta zee tayi a wuyan mummy ta maida idanunta ta lumshe tana sauraron sheshekar mummy tana jin dama ita allah zaiba damar yin irin wannan kukan ko ba komai zata hawayen zai wanko kadan daga cikin raunin dake zuciyarta Dr din ma kallonsu yake cikin tsananin tausayawa, jikinshi duk yayi sanyi Saida mummy ta share hawayenta ta bayan zee sannan ta dago fuskarta dago zee daga jikinta tayi cupping fuskarta "Kiyi hqr kinji? Allah na tareda masu hqr, insha allah komai zai wuce maki kamar be ta6a faruwa ba, be strong and move on. Dama tun tasowarki badashi kike rayuwa ba, daga baya ne yashigo rayuwarki yanzu kuma ya tafi, ki dauki Hakan kamar haduwar hadarin kaka ne, ya hada kuma ya baje ya 6ace 6att kamar ba'ayi ba Ki dauki naki case dinma Hakan, ki dauka baki ta6a rayuwa dashi ba, karki bari abinda yayimiki yayi tasiri aranki da har zaiyi pinning dinki down, fight Zainab! Fight the feelings and move on!" Mummy batasan hawaye take ba Saida taga zee takai hannu tana sharemata Hakan yasa ta sake jawota a jikinta tasake rungumeta Lumshe idanu zee tasakeyi tana jin inama inama Inama abubbuwan da mummy ke lissafowa yanzu suna da sauqin yi Inama tana iya yakiceshi kamar yadda tace ta cigaba da gudanar da rayuwarta kamar da, inama inama 😭 Ahankali ta bude idanunta sai suka sauka acikin na daddy sake tsaye bakin kofa Tundazu basusan shigowarshi ba He looked very sad and disturbed, idanunshi shima sun Kada sosai yana kallon diyar tashi with pain all over his face Tashi tayi daga kafadar mummy tana cigaba da kallon daddy. Hakan yasa mummy Juyawa inda take kallo taga ashe daddy ne Ahankali daddy shima ya qaraso bakin gadon ya zauna shima kusada mummy ya Kamo hannunta guda "daughter" yafada a matuqar sanyaye Cigaba da kallonshi shima tayi kamar mai karantar wani abu A fuskarshi "come dear, come" yafada yana miqomata hannayenshi duka biyun Ahankali ta matso ta shige cikinsu a sanyaye daddy ya rufesu a bayanta Rasa da wadanne kalamai zaiyi amfani dasu wajen rarrashinta yayi Hakan yasashi cewa "Am sorry daughter, am so sorry!" Qara narkemashi ajiki tayi tana qara rufe idanunta Sun dan jima ahakan sannan sukayi breaking hug din suka ba Dr din damar dubata dakyau Saida yagama dubata yayi mata Tambayoyi wanda mostly duk qin amsawa tayi Saidai idan yace meke yimata ciwo ta nunamashi saitin zuciyarta kawai don ita kadai kemata radadi jitake kamar a ciremata ita ta huta. Cewa Dr yayi ahada mata tea a bata tasha kafin yadawo yaqara yimata allurar barci don sosai zata taimaka mata wajen ragemata damuwa wanda itace sanadin ciwon zuciyar datake complaining din Yadda yace din akayi Kakkauran tea aka hada mata daddy ya amsa yana bata a baki tanasha har Saida yafi rabi sannan ta kauda kai alamun ta qoshi Ganin Hakan yasa daddy kiran Dr din yazo ya harhada alluran dazaimata yayi mata su Ba'a qara minti biyar ba wani barcin yazo yaqara yin awon gaba daita. A lokacin ne daddy yasamu damar kiran yan uwa da abokan arziqi yana masu albishir farkawarta, sai washe baki yake cikin farinciki *WASHEGARI* Tunda garin allah ya waye mutane keta tururuwar zuwa ganin zee Daddy baki be rufuwa baya zaune baya tsaye kodayaushe yana kan hanyar rako yan dubiyan ganinta ko kuma raka masu tafiya waje Sosai manyan mutane keta ziyarta asibitin don Saida kowa yasan da Hakan yau ga sadakar da mummy tasa akayita yima mutane patients na take away din jollof da swan water dukda dai suma patients din ba baya ba don saika tara kake iya zuwa irin wannan asibitin. Zee kau haryanzu babu uhm ba uhm uhm, duk wanda yazo dubanta Saidai tabishi da idanu, idan kuma ana yimata ya jiki Saidai ta amsa ta hanyar lumshe idanu ta bude kawai Kayan dubiya kau tashasu qumshi qumshi don duk wanda yazo ganinta saiya ajiye mata qatuwar ledar kayan dubiyan shi Acikin masu zuwa dubata harda Asaad da qannenshi biyu mata Yanmatan sai wani daddage hanci sukeyi kamar yadda suka saba, Asaad mane ke da dan sauqi sauqi don shi ya nutsu sai kallon zee da duk basu isheta kallo ba yakeyi kamar zai hadiyeta. Haka suma suka qaraci zamansu har lokacin tafiyarsu yayi inda anan Asaad ya ajiye mata damin kudi a gefenta sannan shima yabi bayan masu fita Yadda bata kalli kudaden ba Haka shima wanda ya ajiyesu din bata kalleshi saima maida idanu datayi ta lumshe tana sauraron yadda daddy keta yabon kirki da hankalin Asaad. Haka dai suka qarasa Wunin ranar cikin yin baqin yan dubiya don da wasu sun shigo sai wasu su fita haka sukaitayi har dare sannan abin ya lafa itakuma zee sai a lokacin tasamu nutsuwar yin tunaninta dakyau. Saidai bata dade dafara tunanin ba Dr yasake dawowa yayi mata allurar barci don tunanin ne ba'ason tafiye yi a wannan condition din shiyasa akama bari yan dubiyan sukaita zuwa ko sun Janye hankalinta daga tunanin yanzu kuma da babu su sai akayi mata allurar don tayi barci tasamu rest of mind. Washegari kau baqi yan Ruma ne suka sake dawowa ciki harda Umma Sosai Zuwansu yadan debe mata kewa musanmman ma da akazo da yaran Haka taita wasa da sultan da aka doromata shi saman gadonta kamar yadda ta buqata tanayi tana sauraron su mummy da su Aunty raliya daketa firarrakinsu Duk lokacin da ta kalli sultan sai ta tuna Da ranar da Deen ke wasa dashi acan Ruma lokacin bikin Aunty Feenah The smile, the dimple, fararen haqoran, the pink lips da kwantaccen sajenshi, dukkansu sai flashing sukeyi a idanunta Ahankali ta hada goshinta dana sultan kamar yadda Deen yayi wancan karon Bangalewa sultan yayi da Dariya kamar yadda yayi wancan lokacin, itama tsintar kanta tayi tana murmushi Ahankali yadda ita kadai zata iya jin abinda take cewa tafara magana "Bansan abinda yasa ake kiranshi karayar zuciya ba(heartbreak) Jinake kamar wani sashe na jikina ma ya karye" Qara bangale mata baki sultan da besan abinda take cewa ba yayi, itama murmushi mai ciwo tayi sannan ta cigaba da cewa " Wasu na cewa da ciwo ka jira wani Wasu na cewa da ciwo ka manta da wani Amma Mafi ciwo aciki shine karasa abinda zakayi aciki Ka jira? ko ka manta?" " Ka yimin rauni fiyeda yadda na cancanta, dama haka kakeda mugunta? Naso ka fiyeda yadda ka cancanta Dama haka shashanci na yakai?" Hannu sultan ya dago ya dora akan bakinta ita kuma ta bude bakin ta dan yimashi cizon wasa Saurin zare yatsarshi yayi daga bakin nata yana dan 6ata fuska dukda ba sosai ba ta ciza "The worst feeling is not being lonely, it's being forgotten by the one you'll never forget" taqara fada cikin rada tana kallon puppy face din sultan Fashewa sultan din yayi da kuka hakan yasa hankalin mutanen dakin dawowa kansu "oh ni sultan ka cika rigima wlh, kawoshi karya dameki" inji Aunty Raliya tana zuwa wajenta ta daukeshi Zee batace komai ba sai komawa datayi ta jingina da jikin gadon ta lumshe idanunta tana cigaba da sauraron firarrakinsu. Yau kasancewar surukar daddy na asibitin Hakan yasa yau ba'a zauna asibitin ba wai saboda kunya Saidai kiran dayaitayi ma mummy dik lokacin da yaso jin muryar zee sai ta bata su gaisa dukda ba magana take ba sosai don daga farkawarta zuwa yanzu za'a iya qirga magangganunta datayi Sai can da marece wajajen 5pm su Umma sukayi shirin tafiya inda kafin sutafi Saida kowanne yaita yimata nasiha da rarrashinta akan tayi qoqari ta manta dashi tayi moving on Jinsu kawai take amma a zuciyarta tasan Hakan da kamar wuya don a dare guda zaka iya kamuwa da son mutum amma zaka iya 6ata shekarun rayuwarka batareda ka iya mantawa dashi ba *MANTUWA* kalmace mai sauqi wajen fada a baki Amma mai matuqar wuya a aikace. Washegari da zee ta cika kwana takwas a asibitin Ummu batool ta dira Nigeria Sosai su daddy sukayi mammakin zuwan nata don bata sanar dasu zatazo ba saboda sanin halin daddy yana iya cewa basai tazoba itakuma bazata iya ba don gashi dama ta dade rabonta da Nigeria kuma ga rashin lafiyar zee wanda take jinta kamar ita ta tsungunna ta haifeta shiyasa Koda ya fadamasu tafara shirye shiryen tahowa Nigeria din batareda yasani ba. Sosai ta tausayawa zee data ganta don acikin yan kwanakinnan ta chanza sosai She's no more that active Zainab din ta koma wata silent and dull daita, ga ramar datayi acikin yan kwanakinnan wanda ya bayyana sosai Sosai Ummu batool ta tausaya mata don harda kukanta tana cewa sai allah yasaka mata shima kuma haka Itadai zee bata cewa komai kamar yadda ta saba a kwanakinnan Saidai deep down tanajin zafi idan aka soki Deen ko aka zageshi, ta rasa meyasa Saida suka qara kwana biyu a asibitin kafin a sallamesu Cikin kwana biyun nan Saida asaad yasake zuwa dubata kuma kamar wancan karon ya tisata gaba yanata kallo ko me yake kallo a jikin baqar African oho? Haka ma babanshi Alhaji Abubakar, kusan kodayaushe tare suke tareda Alhaji Farouq don duk cikin ma abokan daddy Alhaji Abubakar yafi tsayawa taredashi a wannan halin shiyasa daddy ke qara jin qaunarshi a cikin zuciyarshi yakuma qara aminta dashi ganin yadda dukda butulcin da diyarshi tayimashi Hakan be hanashi tsayawa a side dinshi ba a lokacin buqata, da wani ne da gefe zai koma yana yimasu Dariya. A ranar dasuka cika kwanaki goma sha daya aka sallamesu daga asibitin, lokacin zee ta murmure sosai physically Saidai ciwon da ba'a iya gani wato na zuciya. A ranar saboda murna Saida daddy ya shirya yar kwarya kwaryar party na welcoming dinta home duk don ya faranta mata Haka ma'aikatan gidan suma sukaita zuwa yimata barka da dawowa Ita dai iyakarta dan murmushi daga kuma Hakan zata maida fuskarta yadda take. Da daddare ma Ummu batool biyota tayi dakinta acewarta itama nan zata kwana wanda tayi Hakan ne a hikimance don kar abarta ita kadai har tasamu damar fara wannan tunanin da ba'aso din Saidai abinda basu saniba shine shi abu idan yana a rai ko kasamu nutsuwa ko baka samu ba yana ranka kuma dole ka tunashi a kowanne motsin da zakayi Kuma rashin ba zuciya damar nutsuwa tayi tunanin abinda ke qumshe a cikin ta shike jawo ta cinkushe ka rasa me keyima dadi a duniya Zee ta chanza sosai, idan nace sosai ina nufin sosai da sosai Ta tashi daga wannan zee din mai tsiwa, classic mai yawan ado da kwalliya takoma so silent, moody and simple Rabon da ta zauna da niyyar yin kwalliya Koda simple makeup ne tun ranar introduction dinsu da za'ayi Yanzu dai data samu tayi wanka ta zura duk abinda ya tari gabanta shikenan sai takoma ta nade a gado ko kuma ta zauna tayi shiru kamar kurma. Sosai take ba su daddy tausayi shiyasa duk suke iya qoqarinsu wajen ganin sunyi cheering dinta up. Haka kawai daddy zai kwashesu da zee da mummy da Ummu batool su fita park ko shopping ko cinema duk don cheering dinta up. Mummy ma yanzu babu batun daure dauren fuska don wani sa'in ma Sai kazo ka taddata zaune tanata bata labari kala kala duk nasa nishadi Haka ma Ummu batool wanda haryanzu tare suke kwana dakinta, itama tana iyakar bakin qoqarinta wajen ganin ta debemata kewa takuma sanyata nishadi Saidai abinda basu saniba shine gangar jikinta ne kawai taredasu, ainahin ruhinta na taredashi ya tafi dashi Without Deen she's incomplete and she'll never be complete. *** Zaune suke a falo dukkansu ana kallo ana fira, zee a kwance tayi pillow da cinyar Ummu batool idanunta a lumshe dukda ba barcin take ba Dagowa Ummu batool tayi ta kalli daddy da mummy tace "Yaya da matar yaya, akwai wata magana dake son fadamaku amma ban saniba ko zakuyi maraba daita ba" Duk maida hankalinsu sukayi akanta, mummy tace "haba in-law kifadi koma menene mana, kinsan kinfi qarfin komai a wajen mu" Murmushi Ummu batool tayi sannan tasa hannu ta shafa kan zee da idanunta ke a lumshe har lokacin "mezai hana idan natashi komawa Dubai natafi da daughter ta? Aganina idan ta cira daga nan zataji sauqin abin sosai kuma zatayi saurin mantawa" Duk shiru sukayi babu wanda yace komai, ganin Hakan yasata cigaba dacewa "kuma kunga acan bazata kasance lonely ba, ga batool ga aymaan duk zasu debemata kewa, sai inga yafi taita zama anan, zuciyarta bazata yi saurin healing ba kamar idan tabar nan din" Shiru wajen yasake dauka can sai daddy yace "to banqi ta taki ba sister, amma karatunta fa? She's in 300level yanzu, baki ganin tafiyarta ba kamar watsarda wadannan shekarun data diba tana karatun bane?" Murmushi Ummu batool tayi "yaya kenan, to kai kanada tabbaci zata iya cigaba da karatun yanzu? Kuma a the same makarantar? Kufa kukace acan suka hadu kuma acan ne wajen haduwarsu kusan kodayaushe, bakwa ganin Koda taso manta komai zuwanta makarantar zai dinga dawo mata da memories din baya?" Nan ma shiru sukayi Sai ta cigaba dacewa "amma idan can ne zamu sama mata wata makarantar Koda school of nursing ce, kuma zatayi saurin moving on acan don can garine dayasha banban da nan kuma haka ma mutanen ciki ba na nan bane, zatayi saurin manta past dinta, ga kuma batool zata debemata kewa sosai amma nan fa? Batada wani sublings ita kadai ce ko wannan ma kadai ya isheta" Duk shiru suka sakeyi suna jujjuya maganar kuma suna hango tsantsar Gaskiyarta aciki, tabbas idan Zainab ta cirama qasarnan komai zaifi zomata da sauqi kuma zatayi saurin mancewa da past dinta. Daddy ne yasake cewa "hakane lil sis, abinda kika fada haka yake kuma muma zamuso tayi moving on, mun gaji da ganinta ahakan amma matsalar anan shine ita, anya zata yarda kuwa?" "eh daddy" inji zee dake bisa cinyar Ummu batool still idanunta arufe Duk juyowa sukayi suka kalleta itama daidai nan ta bude idanunta sannan ahankali ta miqe zaune tana kallonsu "daddy na amince, zanbi Ummy (haka dama take kiran Ummu batool), inason nayi nisa da nan, inason intafi wani wajen, Hakan zaisa naji sauqin abinda nakeji. Daddy, mummy please ku yarda, ku yarda ta tafi dani, please" tafada a sanyaye tana kallonsu da lumssasun idanunta da haryanzu haskensu be dawoba bawai don kuka ba A'a sai don rashin kukan don tunda abin yafaru bata zubar da ko digon hawaye ba da sunan kuka. Ajiyar zuciya daddy ya sauke sannan yace "Hakan zaisaki farinciki?" Da sauri zee ta kadamashi kai cikin doqin da rabonsu da ganin irinshi a fuskarta har sun manta Kallon juna daddy da mummy sukayi sukayi murmushi Daddy yace "shikenan, as you wish princess. Allah yasa Hakan shiyafi alhairi" Ga mammakinsu sai sukaga wani qayattacen murmushi ya su6uce mata wanda rabon da su ga irinshi a fuskarta harsun manta... ✍️ Kwana biyun nan Saidai kuyi hqr dani, bana samun yin typing da wuri am kinda busy these days Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:39 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *054* *DUBAI 🌇* Cikin dan qanqanin lokaci su Ummu batool da Zainab suka fara shirin juyawa Dubai Sosai Zainab ke zumudin zuwa qasar don koyaya take moody idan ka tado mata maganar tafiyar sai kaga tadan washe ba kuma ke jawo haka ba sai ganin datake databar qasar barinta zatayi da duk wani damuwanta Siyayya sosai sukayi na tafiyar a bangaren daddy kuma yaje yayi musu settling komai na tafiyar. Ranar da saura kwana biyu tafiyar sukaje zaga dangi don zee tayi bankwana dasu ciki harda yan uban daddy dake garin, su mutanen Ruma kau Saidai sukayi bankwana ta waya don lokacin yariga da ya qure bare suje kuma dama ai yan Ruman basu dade dazuwa ba. Ranar daren dazasu bar qasar kasa barci zee tayi. Ranar kwana tayi kuka, kukan da batayi ba tun faruwar wannan abin. Toilet tashige ta kunna shower tashiga ciki tayita kukanta har Saida muryarta ta disashe Ko daddare ma kasa rintsawa tayi, tana Kwance lamo kamar mai barci amma ba barcin take ba Rayuwar dasukayi da Deen kawai take tariyowa a kwalwarta From A-Z Tayi kukan da bata ta6a yiba a wannan daren shiyasa koda ta tashi washegari idanunta sukayi suntum suka kumbura Su mummy basuyi mammakin haka ba don sunsan kukanta mai dalili ne, gwara ma tayi ta wanko abinda ke zuciyarta da ta barshi a daskare a wajen. Jirgin qarfe 12pm zasu bi Hakan yasa sukabar gida Tun qarfe 11:15am suka dauki hanyar airport. Tafiya suke sunata fira cikin raha ana Dariya banda zee da idanunta ke kafe akan glass din motar na gefenta tana kallon masu wucewa, tana yiwa Nigeria kallon qarshe don ta qudura a ranta ita da Nigeria kuma sai wani ikon allah 11:30am dot suka shigo filin jirgin saman Parking daddy yayi a parking space sannan duk suka bubbude koffofin motar suka shiga fitowa. Zee ce qarshen fitowa. Wani iska ne ya bugi fuskarta Hakan yasa ta lumshe idanunta tana shaqar iskar sannan tasake budesu Su daddy ke fiddo trolley dinsu daga cikin motar Yayinda itakuma ke bin harabar airport din da kallo ba wai na qauyanci, A'a na bankwana, tana bankwana da her beloved country Nigeria inda zata tabar mutane masu matuqar muhinmmanci acikinta wanda bata jin zasu qara haduwa nan kusa Saidai idan su zasu bita can. she's gone too, maybe forever, maybe not. 12 saura minti goma su Ummu batool da Zainab sukayi bankwana dasu daddy Rungume zee su mummy sukayi in turn duk suna iya qoqarin ganin basu bayyana rauninsu ba ta hanyar xubar da hawayen dake forming a idanunsu. Itadai zee barin nata tayi suka gangaro don bataga amfanin riqesu ba Saida sukaji ana qara sanarwa sannan suka haqura da bankwanan suka juya Ummu batool riqe da hannun zee suka fara tafiya Tunda suka fara tafiya zee bata qara waigowa ba har Saida suka kai daidai kofar dazasu shiga cikin inda passengers din keta shiga sannan ta waigo Su mummy da daddy ta hanga can nesa tsaye still suna kallonta, dan murmushi tayi musu dukda batada tabbacin zasu gani saboda nisan dasuka yima juna sannan ta juya suka ida shigewa. Mummy ce ta dora fuskarta akan kafadar daddy hawayenta na gangaro mata Dafe bayanta daddy yayi idanunshi akan kofar da suka shige shima yana trying very hard don ganin yayi controlling emotion dinshi. Ahankali zee kebin Ummu batool dake riqe da hannunta still suka isa inda ake tantancewa aka tantancesu suma sannan suka shige ta inda zasu bi su 6illa filin da jirgin da zasu hau yake. Babu 6ata lokaci suka shiga jirgin suka nemi seat number dinsu suka zauna, zee na daga ciki daidai window Ummu batool na kusada ita. Tunda ta zauna ta maida kanta baya ta jinginashi da kujerar datake akai ta lumshe idanunta _*Xainab bazan ta6a barinki ba duk rintsi, zan jajirce a soyayyarki babu gudu babu ja da baya*_ _*I promised, I promised I'll never break your heart, never!*_ Jitayi anfara announcing akan a daura seatbelt jirgin na shirin tashi Tana jin Ummu batool ta jawo belt din seat din nata tana dauramata Hakan yasa taki bude idanun _*Zainab ina sonki, yanzu, da'iman, abadan*_ _*please marry me*_ _*am sorry... For everything*_ _*natafi.. Am gone.. Maybe forever.. Maybe not*_ Jin Sautin tashin jirgin ne yasata bude jajjayen idanunta Ahankali Kallon window din gefenta tayi tana hangen waje ta nan Dagawa jirgin yafarayi har ya ida barin qasa Kurawa waje ido tayi tana ganin yadda suke qara yiwa qasa nisa "bye.." tafada ahankali daidai da gangarowar wasu hawaye masu zafi "Natafi... Maybe har abada.. Maybe not" _safe journey ✈️_ ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ *DUBAI (Abu dhabi)* Tafiyar awa bakwai sukayi kafin su iso Qasar Gamayyan Larabawa wato Dubai, a birnin tarayyar qasar wato Abu dhabi. Agajiye suka fito daga jirgin don ba qarya sun zaunu Dare ne a qasar don lokacin har 10 ta dan gota Saidai garin tarr yake da hasken fitilun streetlights kamar da rana, mutane sai hada hada akeyi wanda mostly Larabawa ne Amsar trolley dinta zee tayi hannun Ummu batool dake Miqamata ta Fiddo abin ja din tashiga ja tana bin bayan Ummu batool datayi gaba waya kare a kunnenta Tafiya take tana dan qarema Wurin kallo a fakaice tana hango tarin banbancin dake tsananin nan da qasarta Nigeria Gashi duk wanda zakaji ya bude baki yayi magana to larabci ce ziryan ta Cigaba da bin Ummu batool tayi har suka ida fita daga airport din wanda Hakan yayi daidai da gama wayar Ummu batool Juyowa tayi ga zee tayi mata murmushi "marhaban biki bintii! Welcome to Dubai, qasar farincikin ki" Murmushi zee tayi tana Kada kai kawai "muje can mujirasu, sunce suna dab da isowa" inji Ummy tana nufar wata rumfa daga gefensu na dama Itama zee jan akwai ta tayi tabita abaya kamar raqumi da akala Gwadama zee inda zata zauna Ummy tayi ta zauna sannan itama ta zauna kusada ita tana qara daddana wayarta Karawa a kunne Ummy tasakeyi da alamu kira take Magana tafarayi da larabci tana dan sirkawa da hausa Hausar datake dan jefawa aciki yasa zee gane ashe kwatancen inda suke takema wanda take wayar dashi Can sai ga wata baqar mota tazo ta paka daga dayan side din Ummu batool na ganin motar ta gyara yafin gyalenta tana cema zee ta tashi su Abbu sun iso Wayar Ummy tasake daukan qara Hakan yasa ta daga tana kama trolley dinta itama tayi gaba zee da itama ta miqe tsaye tabi bayanta Tsallakawa dayan gefen sukayi suka nufi baqar motar Kafin su qarasa aka 6alle murfin kofar mai zaman banza wata budurwa wanda bazata wuce tsarar zee tafito sanye da arabian jallabiya ta yane kanta da veil din rigar irin yanin Larabawa Bangaren driver kuma wani babban mutum ne yafito shima sanye cikin farar jallabiya da hula tashi da qwaqwa a kanshi Kallo daya zee tayi musu ta shaidasu, Abbu ne da batool. Da sauri batool ta taresu ta rungume Ummy tana tsuwar murnar dawowarta tana Dariya Ummy ma na tayata Abbu ne ya qaraso wajen shima fuska fall murmushi yana yima batool magana da larabci da alamun tsokanarta yake don nan da nan ta cinno baki Ummy kuma na cigaba da yimata Dariya Maida kallonshi yay akan zee dake kallonsu tundazu cikin fara'a yace "lale marhaban yayata" Murmushi zee tayi don dama hakan yake kiranta kasancewar sunan yayarshi gareta Dan russunawa zee tayi tana gaidashi cikin murmushin yaqe shikuma yana amsawa da fara'a yana tambayarta ya suka baro su daddy tana amsawa da lfy lau Batool ce tasaki Ummy ta nufi zee cikin murna ta rungumeta itama tana dan tsallen murna Dan murmushi kawai zee tayi batace komai ba Dagowa batool tayi daga rungumarta datayi "ashe da gaske dake za'azo? Wlh dafarko ban yarda ba na zaci jana akeyi" inji batool din cikin hausarta dake radam don dukda anan aka haifesu iyayensu basuyi sake sun bari yarensu ya kufce masu ba. Murmushi zee kawai tasake yi batace komai ba "to ai yanzu da kika ga zahiri kin yarda ko?" inji Ummy tana yin gaba da kayanta Saurin amsar trolley din hannun zee batool tayi da hannu guda takuma sarqaho hannun zee da dayan suma suka shiga bin su Abbu dasukayi gaba tana cewa "eh Ummy na! Yau yaya zaisha haushi, nasamu wacce zamu dinga hademashi kai" tafada tana Dariya "ko wacce zasu dinga hademaki kai ba" inji Abbu dake saka trolley din a booth Dan kumbura fuska batool tayi saita juyo ta kalli zee dake sauraronsu tace "wai ukhty zee? Aini zaki za6a ko? Akhie bayada kirki ko kadan" Murmushi kawai zee tayi tana jin Ummy na bata amsa da "ai ke kinada kirkin ko? Ni ki kyalemin diya tasha gajiya kina damunta da surutu, babu abinda zatayi cikinku, ku dai da kuka saba sai kuyita fama" Tura baki batool tayi tana cewa "kai Ummy, ke dama da kin samu wata saiki mance da ni yar gaban goshinki ce" tafada tana shigewa shiga bayan motar bayan zee Tariga ta shiga "yaushe? Aini tuni na mayar dake bayan qeya dake da yayan naki, ga yar gaban goshi na nan" tafada tana nuna zee daketa murmushin dramarsu 6ata fuska batool tasakeyi sannan ta kalli Abbu dake qoqarin tada motar "Abbie, kaji ko?" Dariya Abbu yayi yana cewa "kyaleta, Aini ko me za'ayi auta ta itace da muqamin kujeran goshi na, itace ta gaban goshi na always" yafada yana tada motar Dariyar jindadi batool ta fashe dashi sannan ta juyo wajen zee dake kallonta tayimata gwalo wanda Hakan yasa murmushi qara su6uce mata dama tuni ba Tun yau ba tasan halin batool, drama Queen ce ta gidan gaba "to kinji kibar wani jin dadi, nima akwai masu sona" tafada tana gwalemata idanu Dariya duk mutanen motar sukayi banda zee datayi murmushi kawai, Abbu yaja motar suka bar harabar Airport din Tafiyar da batakai ta minti tallatin ba sukayi suka qaraso gidansu Horn Abbu ya danna a bakin gate din gidan nasu Ba'ayi seconds 20 ba aka wangale masu gate din Danna hancin motar Abbu yayi cikin gidan suka shige Direct parking space Abbu ya nufa yayi parking a kusada wata mota dake a wajen Bubbude koffofin motar sukayi duk suka firffito Kallon parking space din ummy tayi sannan tace "Aymaan bayanan ko? Naga banga motarshi na" "hmm yana hospital, wai yau night garesu" inji batool dake gyara gyalenta Girgiza kai ummy tayi "workaholic kenan, ni ban ta6a ganin wanda ya tattara dukkan imaninshi yaba aiki ba kamar Aymaan" "to yaya kikeson yayi? Yaita zaman gida kamar mace? Karki manta yadda aikin likitanci yake musanmman irin wannan bangaren nashi na gynecology, ceton rayyuka yakeyi kuma dukda albashinshi nasan yanada lada awajen allah" inji Abbu yana ciro kayan bayan booth "dukda haka Abbu, abin yayi yawa, gana fa gani wani lokacin ba lokacin aikinshi bane amma kuma a kirashi yakuma je, wani sa'in ma baida taqamaimai lokacin kanshi idan ba weekend ba" inji ummy tana kama hannun zee suka nufi cikin gida gabadaya "ai saboda qwarewarshi tasa ake yawan nemanshi har haka, ke ba abin murnar ki bane ace danki is a professional doctor wanda ake jidashi a daya daga cikin shaharrarun asibitocin dubai?" Dan ta6e baki ummy tayi tace "dama ai kai ke daure mashi gindi shiyasa yake abinda yakeyi din, ku kuka sani ai, like father like son" Murmushi duk sukayi daidai lokacin da suka qarasa shiga cikin gidan. Dayake a gajiye suke kuma dare yayi basu wani tsaya jan zance ba ummy tasa batool ta wuce da zee dakinta da yanzu zai zama nasu su biyu akan cewa za'a biyo su da dinnersu sama. Bankwana sukayima juna batool tayi gaba jaye da trolley din zee itakuma zee na take mata baya Yayinda ita kuma ummy tawuce tareda Abbu part dinshi Sama suka hau inda anan sukaci karo da dakuna uku ajere "kinga dakin ummy nan" batool tafada tana nuna dakin farko Wucewa sukayi zuwa na tsakiya "kinga dakinmu nan" Sannan ta nuna na qarshe "kinga dakin akhie, dayake farin kura ne saboda tsoro saiya za6i abarmashi na quryar yadda duk abinda zai faru saiya fara taddamu kafin ya taddoshi besan mu damuke kusa kusa da stairs ba munfi samun opportunity din guduwa idan ma abin tsoron yazo shi kafin ya 6a66aka ma mun bar layin unguwar" Murmushi mai sauti zee tayi batareda tace komai ba Bude kofar dakin tayi ta tura ta sannan ta koma gefe tana cewa "welcome to the princess chamber" tafada tana bowing dramatically Shigowa dakin zee tayi still murmushi a fuskarta tana yan kalle a dakin. Komai na dakin pink ne yayi kyau sosai dukda bekai nata na Nigeria girma da tsari ba "to ya kika gani?" inji batool tana daga gira daya "fabulous" inji zee tana wuceta taje ta zauna gefen gado tadan jinginar da kanta a frame din gadon cikin gajiya "yes! Dama nasan you'll like it, bari allah ya kaimu gobe na gwada miki na akhie sai ki tantance mana wanda yafi kyau da tsari, kullum cikin rigimar muke babu mai raba mana gardama to yau ga raba gardama nan tazo" Zee da duk ta qoshi da surutunta ta dago daga jinginen datake tace "where's the toilet?" "there, me zakiyi?" tafada tana nuna mata kofar toilet din Tashi zee tayi tsaye tana warware gyalen kanta tace "wanka, am tired and sleepy" "ok bari na hadamiki ruwan" inji batool tana nufar hanyar toilet din "No please, zan hada basai kin wahalar da kanki ba" inji zee "Karki damu, nima na baqunta zan miki don kice am nice amma kina ganina nan shegen san jiki gareni, gwara kibari nayi maki yau din don wata rana da kudinki ba zaki nemi nahada miki naqiya" tafada tana shigewa toilet din Dan murmushi tayi tana ta6e baki sannan ta cigaba da rage kayanta Closet din batool din ta bude ta dudduba can ta hango towel din datake nema ta dauka ta daura daidai lokacin da batool tafito daga toilet din Bata cemata komai ba tawuce toilet din don sosai take buqatar wankan ga barcin dake idonta sosai shima Cikin yan Mintuna tayi wankan ta fito saita tararda batool har tayi shirin barci glass cup din fresh milk a hannunta tana kur6a Qarasowa tayi tana niyyar jawo trolley dinta ta ciro kayan barci batool ta nuna mata nata data riga ta ciro mata Godiya tayi mata ta daukesu ta saka tayi amfani da roll on din batool sannan itama tazo ta dauki nata glass of milk din ta zauna gefen batool tashiga sha Tasha fin rabi sannan ta ajiye lokacin batool ta fita Bata tsaya jiran komai ba ta dauki remote din dakin ta qure a.c din sannan ta haye gadon ta jawo bargo ta lullu6e tana sauke Ajiyar zuciya Lokacin da batool tadawo har barci yayi awon gaba daita don dama agajiye take liss Daukar remote din batool tayi ta rage sanyin a.c din sannan itama tahau gadon ta kwanta batareda ta rufa ba, itama cikin qanqanin lokaci barci yayi gaba daita. *WASHEGARI* Sosai zee taji dadin barcinta na jiya don tun bayan abinda yafaru bata qara barci irin na jiya mai dadi ba, shiyasa da safe ta tashi garass Suna gama sallar asuba batool tajata suka sauka qasa don hada breakfast Sosai Hakan ya burge zee don agidan basuda yar aiki ko guda sai maigadi kawai Komai su sukeyi da kansu. Hada breakfast din suke batool nata zuba kamar radio itakuma zee na aikin sauraronta Cikin dan qanqanin lokaci suka gama suka kuma jeresu a dining Komawa sukayi sama sukayi taking turn Wurin yin wanka da brush sannan suka shirya 8:00am daidai suka sauko qasa don yin breakfast kamar yadda yake a al'adarsu Lokacin suma su ummy da Abbu sun fito suma cikin shirinsu Hakan yasa duk suka hallara dining area din Batool ce tayi serving dinsu gabadaya Itadai zee duk cikin kayan shayi kawai ta iya sha da toast bread tabar musu kingin kayansu na larabawa Sosai taji dadin zaman yin breakfast din don sosai suka nishadantar daita da firarsu Itadai murmushi ne nata idan akayi abin Dariya bata tsoma bakinta sai an sakota a zance kuma Koda an sakota a taqaice take bada amsar Ahaka suka gama breakfast din su ummy suka dawo falon sukuma su zee din sukayi clearing din table din suka dawo sukayi joining iyayen a falon aka dasa firar Sai can wajajen 9am Abbu ya tashi don zuwa shirin fita ummy tabi bayanshi saiya rage saura batool da zee Cigaba da ba zee labaranta da basu qarewa batool tayi zee na sauraronta can batool tayi excusing kanta wai ta manto wayarta sama zataje ta dauko tadawo Kadamata kai kawai zee tayi tanajin dadi atleast kunnuwanta zasu huta kafin ta dawo Ajiyar zuciya ta sauke bayan wucewar batool tana mammakin yadda komai yafaru so fast qaddara takawota nan bawai da niyyar ziyara ba ko komawa nan kusaba sai don zama na adadin lokacin da itama bata sani ba Ajiyar zuciya ta sake saukewa sannan ta miqa hannu ta dauki wani daily magazine dake kan centre table tafara budewa tana going through dinshi. A gajiye ya turo kofar falon yana tafe yana jan qafa alamun gajiya Lapcoat dinshi matse a qasan hannunshi na dama briefcase kuma riqe a hannunshi na haggu Sallama yayi ciki ciki yana yayatsine fuska alamun liss yake ya ida Qarasowa cikin falon Hangota yayi zaune hankalinta gabadaya akan littafin dake hannunta bama tasan da shigowarshi ba Ajiye briefcase din hannunshi yayi ya tsaya ya riqe kugu yana kallon bayanta don baya dama ta juya mashi Cije lip din qasa yayi sannan ya ajiye Lap coat dinshi yafara tahowa cikin sanda ta bayanta Zee batasan wainar da ake toyawa ba sai kawai jitayi fitt an fige magazine din hannunta ta baya Kafin tayi motsi kuma aka rufe mata idanu duka biyun da hannuwa ta baya Qara tasaki don sosai abin yazo mata so sudden takuma tsorata sosai Duk yadda taso cire hannunshi daga idanunta kasawa tayi don ya hanata yin Hakan Hannunta tafara miqawa tasama don lalubawa taji ko wanene, tasan dai bai wuce batool amma data kawo hannu saiya zame yana qumshe Dariya Daidai nan batool ta fito daga daki tanufo qasa Abinda tagani yasata Wara idanu kamar zasu fado "Akhie!" tafada cikin tsantsar mammaki Saurin dagowa yayi ya kalli inda yajiyo muryar batool ya ganta can tsakiyar stairs tana kallonshi baki bude Gabanshi ne yafadi, idan wancan batool ce to wacece wannan? Abinda qwalwarshi ta tambayeshi kenan Babu shiri yayi saurin cire hannunshi daga face din zee yaja baya yana kallonta Kyafkyafta idanu zee tashiga tana miqewa itama tsaye Hannu tasa ta murza idanunta yadda ganinta zai dawo sannan ta bude idanun ta juyo ta inda aka rufemata idanun Turuss tayi ganin wanda bata ta6a expecting ba Dan Wara idanu tayi tana kallon yadda shima ya Wara idanu yana kallonta sai kuma ta maida kallonta ga batool da itama haryanzu tana a inda take tana kallonsu... ✍️ Manage 👏 Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:39 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *055* *DR AYMAAN* Janye idanunta tayi daga kan batool tasake maidowa akanshi Cikin daburcewa yafara bata hqr cikin harshen larabci Dariyar batool ce ta dakatar dashi "batajin larabci akhie, she's hausa" inji batool tana Qarasa saukowa tana Dariya Sake kallon zee yayi yace "ohh, please kiyi hqr, nayi tunanin wancan ce am sorry" Sauke idanunta kawai zee tayi batace komai ba Batool ce ta qaraso tana cigaba da Dariya "shiyasa akace idan zaka gina ramin mugunta ka ginashi gaj..." Bata qarasa ba ya fincikota ya kama kunnenta "ni tsaranki ne?" yafada cikin larabci yana qara murda mata kunnen Qara batool tasa tana matse ido cikin jin zafi "wayyo akhie kunnena!" Qara twisting din kunnen yayi yana cewa "bani kike gayawa magana ba?" Qara da tsuwa batool taita yi tana qoqarin qwace kunnenta amma takasa Zee tunda suka fara take jinta uncomfortable, ga qarar batool datake ji har cikin dodon kunnenta "amm... please leave her mana" inji zee tana kallonsu Jin abinda tace yasa ya dakatar da murdawar dayake yiwa kunnen ya tsaya yana kallonta batareda ya saki kunnen ba Ganin Hakan yasata dauke kanta gefe "ka sakeni mana tunda tace ka kyaleni" inji batool tana 6ata fuska Sakinta din yayi bayan ya gallamata harara yace "ta ceceki da yau saina cire kunnen" Yafada yana qara satar kallon zee da bata qara kallon gefensu ba Saima zamanta datayi Da idanu Aymaan yayiwa batool nuni da wacece wannan? Dariya batool tayi ta koma daga gefen zee din tace "wai kinji uktie wai gulmarki yake da idanu" Wara idanu Aymaan yayi sai ya nufota Hakan yasa ta qara Sakin qara ta ruga shima yabita suka fara zagayen falon Tsayawa zee tayi ta saki baki tana kallon ikon allah don ita abin nasu ma mammaki yake bata "afuwan akhie, afwan!" inji batool tana tana zillewa "wlh yau zaki gane kurenki, yaushe nayi gulmarta?" yafada yana qoqarin tarota "wlh bakai bane, bakai bane" tafada tana qara zillewa Suna haka su ummy da Abbu suka shigo falon, Abbu cikin shigarshi na suit da alamun aiki zai fita "ya subhanallilah! Meye haka?" inji ummy Hakan yasa suka dakata daga abinda suke "wlh ummy kiyimashi magana" inji batool kamar zatayi kuka "Kun fara ko? Wai yaushe ma kadawo Aymaan?" inji Ummy Hade gira Aymaan yayi "yanzu yanzunnan kuma wai daga zuwana saita jamun sharri Wurin wannan" yafada yana nuna zee da haryanzu ke kallonsu Tsaki ummy taja ta qaraso falon "Allah ya shirya ku agaban baquwarma saikun saida halin, kun girma bakusan kun girma ba" tafada tana wucewa Wurin zee Sosa lallausar sumarshi Aymaan yayi "baquwa mukayi ne ummy?" Dago zee ummy tayi sannan ta juyo ta gallamashi harara "ba baquwa bace yar gidace kana ganinta nan don yanzu tama fiku iko da gidan" "haba dai ummy, wannan wasane ko akhie?" inji batool Gallamata harara Aymaan yayi yace "ni meye hadina dake da zaki tambayeni? Tafiki iko da gidan, me zakiyi?" Kumbura fuska tayi kamar zatayi kuka Dariya Abbu dake sauraronsu Tundazu yayi yace "Allah ya shirya ku, nidai karku koyawa yayata wannan halin naku, tana yar saliharta itama ta koma burkakka" Dariya duk sukayi itakuma zee ta sauke kai tana dan murmusawa Matsowa Aymaan yayi kusada Abbu cikin rada yace "Abbu wai wacece?" Murmushi Abbu yayi yace "ai dole ka tambaya, kaida bakasan kusan mafi yawa cikin danginka ba. To Zainab ce ta gidan daddy, daddyn Nigeria" Wara idanu Aymaan yayi saikuma ya qara kallon zee da bashi take kallo ba "you mean diyar Daddyn Nigeria?" Kada mashi kai Abbu yayi in affirmation "wannan yar yarinyar? Yaushe ta girma haka?" inji Aymaan cikin mammaki Dagowa zee tayi jin abinda yace sai suka hada ido Hararar da batasan tayi ba ta gallamashi don sosai taji haushin kiranta da yar yarinya dayayi Ganin Hakan yasashi kauda kai yana Sosa qeya bakinshi dauke da murmushi Dariya duk aka dauka falon ummy tace "ba dole kayi mammaki ba? Yaushe rabonka da Nigeria? Almost 6years ba dole ta chanza maka ba?" Qara satar kallonta yayi yaga bama gefen shi take kallo ba "hmm ai zanje kwanan nan" yafada yana wucewa dining "kamar duka kenan" inji ummy "Allah kau ummy, bari aiki ya dan lafa, zan baku mammaki" yafada yana jan kujera daya ya zauna "hmm allah yasa" inji ummy "Amin dai ummy" batool ta amsa Dagowa Aymaan yayi ya watsamata mugun kallo "ba na hanaki sakamin baki a magana ba?" Turo baki tayi ta koma bayan ummy "bazaki zo Kiyi serving dina ba?" yasake fada yana huro hanci Qara turo baki tayi sannan tazo ta wuce kitchen Binta da kallo yayi sannan yayi kwafa ya juyo sai caraff suka hada idanu da zee, da sauri ta kauda kanta tana dan ta6e baki "Daga zuwa sai cin abinci baka freshening up" inji ummy da tayi gaba jaye da hannun zee "zanyi idan nagama, darabanil ju'i" yafada yana shafa cikinshi fuska a marairaice "acici" inji ummy tana jan hannun zee suka nufi wajen Abbu "muje mu raka Abbu kinji 'yata" "to ni natafi, ma'asallama" inji Abbu Fatan tsari Aymaan yayi mashi sannan suka fice gaba daya, Abbu a gaba ummy da zee abaya Binsu da kallo yayi har suka fice sannan yadan daga kafadu Batool ce tafito da kayan break wanda dama an fidda mashi nashi an ajiye incase idan yadawo Zuwa tayi tana jerawa still fuskarta a kumbure "tazo nan hutu ne?" inji Aymaan "wa?" "baquwar" ya amsa yana kallonta Daga kafadu tayi tace "kusan haka amma zata dan jima kadan" Daga girarenshi yayi yace "masha allah, kice mun qara yawa amma naga kamar bata magana, meyasa?" "bari tadawo na tambayar maka ita" Yiyayi kamar zai maketa tayi saurin ja baya da serving spoon a hannunta tana Dariya Kwafa yayi kawai yajawo abincinshi yayi basmallah yafara ci Acan waje kau har mota su ummy suka raka Abbu Sallama sukayi da zee tana mashi fatan dawowa lafiya sannan ta juyo ta dawo ciki tabar ummy can tareda Abbu suna magana Da sallama tasake Shigowa falon Dago kai Aymaan da yanzu saura shikadai a falon yayi yana kallonta ya amsa Kallonshi itama sukayi suka hada ido saita kauda kai Stairs tanufa batareda ta yarda ta qara kallon gefenshi ba dukda yadda takejin idanunshi akanta Binta da kallo yayi harta haye saman sannan yasake daga girarenshi biyu ya kada kai ya cigaba da cin abincinshi A daki zee ta tararda batool Kwance tana waya cikin harshen larabci Zama tayi gefen gadon tana sauraron batool din absentmindedly Idanunta ne suka sauka akan Ring din yatsarta dake sheqi sanadin hasken rana dayayi reflecting akanshi ta window din bayanta Qurama zoben idanu tayi tunanuka kala kala na kai kawo a kwalwarta Yanzu Deen na ina? Me yakeyi? Yana tunawa da ita kau? Koko ya riga ya shafe babinta a tarihinshi? Yana cikin farinciki koko akasin haka? Yana kewarta? Koko bayayi? Ta yarda ta biyo Ummu batool nan ne don aganinta zata iya mancewa dashi with time, amma daga jiya zuwa yau tafara tantamar yiwuwar Hakan Don duk motsin da zatayi saiya fadomata arai, duk blinking idanun da zatayi sai yayi mata gizo a idanu Anya zata iya mantawa dashi? Anya? She doubt it, tana tantama sosai akan haka, don Deen acikin zuciyarta yake, yariga yabi Jinin jikinta, mantawa dashi daidai yake da musanya zuciyarta da wata wanda babu Deen aciki kokuma musanya jininta da wani wanda babu shi a gudanuwarshi Jitayi an dafa kafadarta Hakan yasa ta dawo daga duniyar tunanin data lula Batool ce zaune kusada ita tana mata murmushi Kamo hannunta batool tayi tana kallon zoben yatsarta itama "shi yabaki?" inji batool tana kallon Ring din Dago idanunta zee tayi ta kalleta batareda tace komai ba Itama batool ta dago tana kallonta sai tadanyi murmushi "yanada kyau sosai" tafada tana dan Kada kai Nan ma batace komai ba "sister, wani lokacin you have to let go abinda kake matuqar so sosai, ba wai don son ranka ba sai don Hakan shi zai fiyemaka alhairi. Wani sa'in abubbuwa masu kyau basu cika zama masu amfani ba, misali wannan zoben dake hannunki Kina Ajiyarshi ne bayan kinsan bazai amfaneki da komai ba Saima ya jefaki a wani hali idan kika kalleshi, why not ki cireshi tunda kema sanin kanki ne be cancanci zama a yatsarkiba yanzu" Dan murmushi zee dake kallonta Tundazu tayi saikuma ta maida kallonta akan zoben "a tunaninki cireshin zai sauya wani abin ne?" Saita girgiza kai "babu abinda zai chanza, babu. Rashin shi ne ma zai jawo wani abin" Kallon zoben tasakeyi "idan na kalli Ring din sai natuna da ranar, ranar dayake gabana, zube a gwiyagunshi begging me to marry him. The love, affection, seriousness dana gani a qwayar idanunshi a ranar yana sani tantamar abinda nagani a takardar da yabani, yana sani tunanin anya shi ya rubuta takardar, da hannunshi? But sadly shine, shine, dalili kuma shine ban sani ba, abinda yafi komai tsayamin arai kenan. Meyasa zai tafi batareda gayamin atleast dalili qwara daya ba? Meyasa? Atleast yafada min Koda kuwa zuciyata ce zata buga, Koda qarya zaiyi min yayimin amma bawai yatafi hakannan ba, leaving me like a lost cat in the jungle" Batasan hawaye takeyi ba Saida batool ta jawo ta ajikinta tana share mata su "it ok zee, nasan yadda kikeji.." "baki saniba batool, kuma bazaki ta6a sani ba sai idan kin tsinci kanki a wannan halin, nikuma bana maki fatan haka" Qara rungumeta sidely batool tayi sannan tace "ki gayamin, ki gayamin tarihin soyayyarku" Girgiza kai zee tayi "A'a, nima da nasan abinda zanyi inmanta da tuni nayi Hakan" "unfortunately baki sani ba, amma kuma idan kikayi sharing dinshi da wani zakiji sauqi. Tunda abin yafaru kin ta6a zaunar da wani kinyi pouring out abinda ke a zuciyar ki?" Ahankali zee ta girgiza kanta "you see? Fadama wani damuwarka ma yana rage damuwa. Problem shared is Problem solved. Idan kin fadamin zaki samu abu daya zuwa biyu Nafarko zuciyarki zata rage nauyi saboda kinyi pouring out abinda ke cinkushe a cikinta wanda ke hanaki saqat Na biyu kuma, who knows wataqila ina iya hango maki wani abu a soyayyar taku ko kuma na sama muku solution, bawai don am perfect ba saidon kowa da irin nashi baiwar da hangen" Murmushi mai ciwo zee tayi tace "zan fadamiki saboda dalili na farko da kika fada, wato don naji sauqin abinda nakeji a zuciyata Amma batun samun solution ba be tasoba, sai idan akwai Problem ake samun solution, anan babu wani Problem idan ma akwai to bansaniba, tayaya za'a samu solution din?" Ajiyar zuciya batool tayi tace "to shikenan, ki fadamin din, am all ears" Itama zee Ajiyar zuciya ta sauke sannan ahankali ta maida kallonta akan zoben hannunta "Sunanshi DEEN... KAMALDEEN MUHAMMAD...." **** Ummy ce tashigo falon bayan taga tafiyar Abbu A dining din ta iske Aymaan yanata aika abincinshi hankali kwance Qarasowa wajenshi tayi taja kujera itama ta zauna "Likita bokan turai" inji ummy cikin tsokana Murmushi yayi sannan ya dauki glass cup din gabanshi yayi sipping ruwa "Umminmu! Ashe jiya zaki dawo da nasani da banje aiki ba" Harara ta gallamashi "kamar duka kenan" Dariya yayi "Allah ummy jiya munshiga busy sosai, surgery hudu nayi da daddaren nan" Girgiza kai Ummy tayi "Allah sarki, ai mata na shan wuya, haihuwa yaqin mata, allah yasa kowacce tagamata lfy" Sipping ruwa yasake yi sannan ya amsa da amin "kaga qanwarka ko?" inji ummy tana kallonshi "baquwa?" Harararshi tasakeyi "sunanta kenan?" "I don’t know her name ai" "shame on you, ace bakasan sunan cousin dinka ba" Sosa kai yayi yana dan 6ata fuska "kai ummy" "to ai Gaskiya ce, to sunanta Zainab" "oh kinga kina fadi na tuna, ai na santa lokacin danaje Nigeria last ai naganta lokacin yar qarama ce nasan bazata wuce 15 ba kuma she's a talkative tana magana sosai gashi batajin magana amma yanzu ta chanza sosai, naga ko magana batayi, ko haka girman yazo mata?" Murmushi ummy tayi "eh to, kasan ana qara girma ana qara nutsuwa, tabbas ta nutsu Saidai wannan nutsuwar haka bata lafiya bace don kamar yadda kace magana ma wuya take mata gata always moody" Ajiye spoon din hannunshi yayi "to meya faru? Meya maidata haka to?" Ajiyar zuciya ummy tasakeyi tace "she's heartbroken" "heartbroken?" inji Aymaan yana kafe maman tashi da hazal eyes dinshi "yes, wanda takeso ne ya yaudareta, kwanan nan ba kaji muna maganar introduction daza'ayi a Nigeria ba?" "yes, naji kuna discussing dinshi da Abbu" "to itace, yaron asalinshi dan talakawa ne don koko da qosai suke saidawa for living Sun hadu da Zainab dinne a school and they both fell in love Amma da maganar tazo wajen daddy saiyaqi yarda saboda yaron ba Dan masu hali bane plus yana gudun ace ba sonta ba yake kawai yaudararta yake yana sonta saboda kudin da mahaifinta kedashi Daddy yayi iya qoqarinshi don ya rabasu amma a banza don she's deeply in love with the guy don a sanadin haka ta kamu da hawan jini saboda damuwa. Ganin babu sarki sai allah yasa kawai ya yarda yakuma cema yaron ya turo magabatanshi suzo ayi introduction idan dagaske yake. Lafiya lau aka fidda ranar introduction din har ya bugomin nan munata murna Saidai ranar da aka fidda don yin introduction din babu yaron babu magabatan nashi babu alamunsu. An jira anjira shiru gashi wayar yaron bata shiga Ganin Hakan yasa daddy aika drivernshi don ganowa ko lfy? Wai dayaje saiya iske gida garqame da kwado Aranar dai Saidai aka watse ba'ayi introduction din ba Washegari shiru, babu su babu alamar su Hankalin Zainab ya tashi don tana sonshi Sosai fiyeda tunaninka Ganin ta tashi hankalinta yasa daddy shiryawa washegari yaje yagano da kanshi and the same story ya tarar still gidan kulle Zainab dai taqi yarda ta nuna tanaso taje tagani da kanta Koda sukaje din saita tarar da abinda suka tarar suma, suna ahaka wani abokin yaron yazo wajen da shar6e6iyar envelope wai gashi inji yaron da sukaje nema And could you believe what she saw inside? Letter ne ya rubuta yana magangganu marassa kan gado wai he's gone wai tayi haquri wai he's gone forever" "what? But why?" inji Aymaan Watsa hannuwa ummy tayi "oho, beyi stating dalili qwara daya ba nayin Hakan, kawai wai he's gone. Anan take tayi collapsing a wajen daga nan aka kwasheta sai hospital Saida tayi kwana uku kafin ta farfado, blood pressure dinta yayi high ga difficulty in breathing. Dakyar aka shawo kanta a kwana na uku ta farfado kuma daga ranar takoma haka, babu uhm babu uhm uhm, yanzu ma fa wai da dan sauqi ne ma tunda idan akayi magana tana amsawa da kau bata magana Saidai tayi smiling painfully. Ganin Hakan yasa kawai na yanke shawarar tahowa daita nan don am very sure zatafi saurin healing nan bisa ga can, don ko babu komai ta chanza environment. Shiyasa kaga na taho daita har lokacin da zata warware kamar babu abinda yafaru" Sosai jikin Aymaan yayi sanyi, nan take yaji abincin gabanshi ya fita ranshi "so sad" yafada ahankali "very sad indeed wlh, donma kamar yadda nafada maka ta dan warware da lokacin danaje Nigeriar ne da sai kayimata qwalla" Wani zafi Aymaan yaji ya ziyarci zuciyarshi nan take yaji ya tsani koma waye wannan mayaudarin "amma wannan ya cika butulu wanda besan alhairi ba, ko babu komai ko don soyayyar Gaskiya data nunamashi be kamata ya badamata qasa a idoba" "hmm ai kai kasan da Hakan shi besaniba" Shiru yayi ya cigaba da huci, yana jin ranshi na 6aci sosai "shiyasa nazo daita nan don tasamu sallama, Aymaan wannan aikin tareda ku zamuyishi, help her, help her forget her past, mu Hade qarfi wajen ganin mun mantar daita past dinta, tayi moving on kamar babu abinda yafaru" Dagowa Aymaan yayi ya kalli ummy "yes ummy, we'll do everything, everything wajen ganin mun mantar da ita past dinta, I assure you, insha allah zata yi farinciki fiyeda da" Murmushi ummy tayi cikin jindadi "barakallahu fika Aymaan, allah yayi muku albarka gabadaya, idan kukayimin haka kun biyani wlh" Wani qayattacen murmushi Aymaan yayi yace "karki damu ummy, wataqila dama basu daceba, wataqila ba alhairi bane agareta shiyasa allah ya kawar dashi, insha allah zata samu wanda ya dace daita, insha allah zatace gwara da akayi hakan, shikuma zaiyi nadama har qarshen rayuwarshi" Murmushi jindadi ummy tasakeyi "Alhamdullilah! Allah yasa Hakan Aymaan, allah ya tabbatar mana da alhairinsa" Da amin Aymaan ya amsa yana daukar ruwan gabanshi yakai baki "bari naje sama ok? Kayi sauri ka qarasa abincin karya huce" tafada cikin yanayin farinciki Kadamata kai yayi kawai yasake jawo abincin gabanshi Ganin Hakan yasa ummy wucewa tana jin wani madaukakin farinciki a ranta, tabbas da alamu haqanta zai cimma ruwa, taga alamun abinda takeso zai faru, idan kau Hakan yafaru sai tafi kowa murna a duniya. Aymaan kau tana wucewa ya ture abincin gabanshi ya koma ya jingina da kujerar bayanshi ya harde hannayenshi a qirji Fuskarta tayi mashi gizo a idanu, yes! She's in pain, yaga Hakan a fuskarta, to amma wane asarrare ne marar hankali da zai rasa wanda zaiyi hurting sai damsel irin wannan Wani kayattacen murmushi ya su6uce mashi Lallai, to koma waye yayi sakaci, sakacin dazai qare rayuwarshi yana cizon yatsa, har qarshen rayuwarshi, he'll make sure he did that.... ✍️ _wasa farin girki🤸🏻‍♀️_ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:39 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *056* *KADDARAR SO ❤️* Kuka sosai Batool keyi lokacin da zee takai aya a labarin soyayyarsu da Deen datake bata Jawota tayi jikinta suka rungume juna suna cigaba da kukan atare. Sun dan jima ahakan sannan sukayi breaking hug din "Am sorry" inji batool tana kallon zee idanunta jiqe da hawaye Girgiza kai zee tayi tace "Don't be" "labarinku is so touching, rabuwarku is so disheartening" inji batool Kada kai kawai zee ta iya yi tana share hawayenta da bayan hannu "Inaji ajikina ba laifinshi bane zee, inajin koma menene ba da son ranshi ba ya barki" Dan murmushi zee kawai tayi tace "nima Hakan nake tunani don na yarda da soyayyarshi agareni amma koma menene yakamata ya gayamin, who knows muna iya working together musama ma kanmu mafita, koma menene be kamata ya karya alqawurranshi da yayi min ba" Kada kai batool tayi tace "Kiyi hqr zee, nasan duk inda yake shima yana can yana kewarki kamar yadda kike kewarshi" Girgiza kai zee tasake yi "I don’t miss him, I miss who I thought he is" "kibar fadin haka zee, insha allah watarana qaddarar data rabaku zata qara hadaku and at that time zai fayyacemiki komai" "babu qaddarar dazata sake hadamu batool, mun riga mun gama da juna a duniyar nan, shi yana Nigeria ni ina nan, bazan koma Nigeria ba kamar yadda shima bazai ta6a zuwa nanba, tell me, tayaya qaddarar zata hadamu" "zee kenan, qaddara ta wuce tunaninki musanmman qaddarar so, you dont know what allah have in stock for you dahar ya rabaku, wataqila ba alhairi bane agareki ko kuma akwai wata manufa akan Hakan" Daga kafadu kawai zee tayi tace "mubar maganar haka, atleast na danji sauqin zuciyata danayi sharing damuwata, nagode" Murmushi batool tayi "never mind, amma idan bazaki damu ba zan dan nemi alfarma awajenki" Komawa Zee tayi ta jingina da frame din gadon tace "Inaji" "please idan kinada picture din gayen ki gwada min inason ganinshi" Shiru zee tayi "please.." inji batool pleadingly Dan murmushi tayi sannan ta nuna mata wayarta dake kan mirror Da sauri batool ta tashi ta dauko wayar ta miqa mata Girgiza mata kai tayi tayimata nuni da ta bude Swiping wayar kawai tayi ta bude don dama ita bata sakawa waya security "ki shiga gallery" Yin yadda tace tayi "shiga folder mai suna DEEN" dubawa tayi saita ga folder saita danna ya bude Hotuna tagani masu yawa duk sun bubbude Na farkon ta danna nan take smiling face din Deen ya mammaye screen din wayar Dan Wara idanu batool tayi tana gasping "woooow!" tafada ahankali tana qarema fuskarshi kallo Itadai zee mayar da idanunta tayi ta rufe kawai tana sauraronta Wuce hoton na farko tayi na biyun ya bayyana nanma Saida tayi gasping Haka taita bin hotunan daya bayan daya wanda duk hotunan fuskarnan dauke take da wannan murmushin nashi mai tafiya da zuciyar mutane kuma ga dukkan Alamu ma babu hoton da aka dauka da saninshi, wani Wurin yana magana ne, wani Wurin idanunshi nakan littafin dake hannunshi, babu wanda yafi burgeta sai wanda akayi mashi yana dauke da sultan suna Dariya. Saida tagama going through duka sannan ta dago ta kalli zee da haryanzu idanunta ke a lumshe "wow sis, Gaskiya guy dinnan ya hadu, dole rashinshi yasa ki shiga hali" inji batool cikin santi Bude idanunta zee tayi ta gallamata wata muguwar harara sannan ta maida idanunta ta rufe Dariya batool tayi tace "Allah kau karki ji wasa sis, wannan na sameshi ai tusashi gaba zanyi ina kallo inajin dadi, ko laifi yayi min dana kalli fuskarshi zan huce, wayyo allah amma ya hadu dama ana samun ire iren hot guys dinnan a Nigeria?" Banza zee tayi ta kyaleta kawai "wayyo, aikau Ahmed nafasa sonka, Nigeria zani! Wayyo hot Nigerian guys inanan tafe" Dan murmushi ya su6uce ma zee, sosai shirmen batool ke bata Dariya, haka taita sauraronta tayita zuba ita kadai ko gajiya batayi. *AYMAAN* Aymaan kau da maganar zee ya yini ya kwana ya kuma tashi Sosai abin ya tsaya mashi arai. Ga wani gizo da fuskarta keyi mashi duk lokacin daya motsa. Tunawa yayi jiya a wajen dinner Kasa concentrating yayi akan abincinshi banda satar kallonta every now and then babu abinda yakeyi Itakau batama san yana yi ba don bayan Gaisawar dasukayi sama sama ko gefen shi bata qara kallo. Koda ya dawo sallar asuba shirin fita asibiti ya hau yi don yau aikin safe garesu. Qarfe 8:00am yafito daga dakinshi cikin shigarshi ta qanannun kaya, baqin dogon wando da farar shirt yaci zanzaro ga lapcoat dinshi dake sagale da hannunshi sai briefcase riqe da dayan hannun. Yayi kyau sosai a shigar ga wani irin cool qamshi dake tashi a jikinshi Fara saukowa yayi daga stairs din Waya kare a kunnenshi yana amsa kira har ya ida sauka. Dago idanunshi yayi sai suka sauka akan zee dake jejjera flask akan dining table Kafeta da idanu yayi yana kallon every movement dinta Yayinda can qasan zuciyarshi yake jin wani feeling da bazai tantance kona menene ba Zee dake aikinta hankali kwance tadan dakata jin kamar ana kallonta Ahankali ta dago sai caraff suka hada ido dashi tsaye a inda yake yana kallonta itama Ahankali yadan sakarmata wani cool murmushi Dauke kai tayi kawai ta cigaba da abinda takeyi Hakan yasa ya qara fadada murmushin shi sannan ya nufo dining area din Jan kujera dake facing dinta yayi bayan Qarasowarshi ya zauna still yana kallonta Bata dago ba ta kalleshi haka kuma bata dakatar da abinda takeyi ba "sabahal khair ukhtie" yafada jovially Sai a sannan ta dan dago ta kalleshi, kamar bazata yi magana ba sai kuma ta motsa bakinta ahankali tace "sabahan-nurr" Dan Wara idanunshi yayi jin ta maido mashi da larabcin "dama kinajin arabic?" ya tambaya yana kallonta "No" tafada tareda Juyawa tabar wajen Binta da kallo yayi harta shige kitchen din, daga girarenshi yayi sannan ya danyi murmushi ya kada kai sannan ya sa hannu yajawo abubbuwan kan table din yana bubbudewa don serving kanshi. Yana cikin cin abincin ne suka sake fitowa daga kitchen din da zee da batool Dagowa yayi daga shayin dayake sipping yana kallonsu har suka qaraso "sabahal khair Akhie" inji batool cikin fara'a "sabahan-nurr" yafada yana dan satar kallon zee dake dora tray din hannunta kan table din "yau kuma tunda safe zaka fita?" inji batool tana taya zee jejjera abubbuwan dasuka kawo "ga zahiri?" yafada a taqaice yana sipping shayinshi ahankali yana satar kallon zee ta saman kofin "da ace yau lecture din safe gareni da kayi dropping dina" Dagowa yayi ya gallamata harara yace "ke da wa?" Dariya tayi "Don't even try that, rannan ma dakikaga na kaiki don ummy tayi magana ne shiyasa amma wlh kika qara yimin Hakan zan daukeki ne naje na watsar gefen titi babu ruwana" Dariya batool tasakeyi tace "babu komai saina tashi na nemi cab ya qarasa dani school din, what matters shine kadai tuqani" Dagowa yayi ya gallamata harara Hakan yasa ta koma bayan zee datayi kamar batasan sunayi ba tana Dariya Kwafa yayi sannan ya turama zee plate dinshi "zubamin wannan kadan ukhtie" Kallon plate din tayi saikuma ta dan jawoshi tashiga zubamashi Saida yaga yakai daidai yadda yakeso yace "yauwa ukhtie, shukran. Ke kuma ki koyi yadda ake girmama na gaba kamar dai ita" yafada yana nuna zee Ta6e baki batool tayi tace "nima ai inayi, Ganine ba'ayi" "a ina kike yi? Kin maidani abokin wasanki, shi yaya girmama shi akeyi sosai, don babban wa uba ne, koba haka ake cewa ba ukhtie?" yafada yana maida kallonshi kan zee "yes" tafada simply sannan tajuya ta bar dining din ta nufi stairs Binta da kallo duk sukayi sannan suka kalli juna Qumshe Dariya batool tayi tana rufe bakinta da tafin hannunta Wani kallo ya watsamata yace "bar nan" Da sauri tabar wajen tana cigaba da qumshe dariyarta tabi bayan zee Kwafa yayi sannan ya maida hankalinshi akan abincin gabanshi ya cigaba da ci Bai qara 6ata lokaci ba ya tashi ya fice daga gidan. Tunda yashigo hospital din aketa gaidashi, duk inda ya gitta sai an gaidashi shikuma yana amsawa cikin fara'a Aymaan kenan, kyakyawan namiji mai cikar haiba da kamala, mutum ne faran faran ga yawan wasa da sakewa wanda Hakan yasa yakeda farinjinin mutane sosai Aymaan ba fari bane haka zalika ba baqi bane, he's chocolate in complexion, chocolate dinma irin mai sheqin nan. Dr Aymaan qwararren likitan mata ne wanda ake jidashi a daya daga cikin manyan asibitocin dubai saboda qwarewarshi da hazaqa da allah yayi mashi Yayi suna sosai a asibitin dama sauran asibitocin qasar don sosai kingin asibitocin ke kwadayin samunshi a asibitinsu suma kuma sunsha kawo mashi tayin yadawo asibitin su akan farashi mai tsoka amma yayi turning down request dinshi politely don idan akwai abinda ya tsana to cin amana ne? Ko patients sunfi son Dr Aymaan ya dubasu saboda qwarewarshi wajen aiki dakuma iya mu'amallantar patients dayayi, gashi qwaro ne a fannin aikinshi don wani lokacin idan wasu likitocin suka kakare to shi ake kira kuma cikin ikon allah da yazo komai zai warware. Shiyasa mafi yawancin lokuta ma bayada timetable na kanshi na aiki don ko lokacin aikinshi bane ana iya kiranshi at anytime kuma yatafi batareda gardama ba Aymaan allah yayishi da tausayi musanmman akan mata. Yana matuqar tausaya masu kuma beson abinda zai ta6asu don idan akwai abinda beso to kukan mace ne idan kuma akwai wanda ya tsana to mai sa mace kuka ne, duk wanda yasan Aymaan yasanshi da wannan tausayin na mata ko don shi likitansu ne kuma yasan matsalolin da suke fama dasu? Akwai lokacin daya ta6a yiwa wata mata aiki dazata haihu don takasa haihuwar da kanta, haihuwar matar tabiyu kenan Cikin sa'a akayi aikin lafiya aka gama lafiya don har Saida ya gwadama matar diyar daya Ciro yana Tambayarta me tasamu dayake aikin na ido biyu akayi. Lafiya lau ta amsa mashi da mace aka samu Hakan yasa yabada diyar akaje wajen gyarata shikuma yafita yima ahalin matar albishir din yin aikin successfully. Sosai ahalin sukaita murna suna godewa allah shikuma suna sanya mashi albarka. Da farinciki ya dawo dakin da take Saidai me? Sai ya tarar matar nata kokowa da numfashi nurses nata qoqarin bata taimakon gaggawa. A rude shima ya shiga iya qoqarin shi wajen ganin numfashinta ya daidaita Saidai kana naka allah na nashi don ko minti biyar bata qara ba a duniya ta rasu Sosai mutuwar ta girgiza Aymaan a lokacin. Sunfi Mintuna 10 ahaka dashi da nurses din dakin dasukayi cirko cirko cikin rashin sanin abin yi Daga baya Dakyar ya iya summoning courage yafita Domin sanar da ahalin nata Saidai ganinsu sunata daukar jaririyar anata murnar qaruwa Sosai gwiwarshi ta sage yaji zuciyarshi ta karye Koda sukaga Hakan sai suka fara Tambayar shi lfy? Dakyar ya iya danne abinda yakeji yayi breaking din labarin mutuwar matar garesu Dayake ba masu qarfin imani bane sai suka hau koke2 da iface iface har wata ma ta sha qwalarshi tana cewa qarya yakeyi ba yanzu yazo ya sanar dasu lafiyarta lau ba Nan fa akazo aka taru mutane nata rarrashin ahalin mamaciyar suna yimusu tuni da qaddara. Aymaan kau be cewa komai sai hawayen dayake wanda ba komai ya jawo Hakan ba sai kukan da jaririyar keta tsanyarawa. Sosai jaririyar tabashi tausayi don bilhaqqi da Gaskiya take kukan kamar tasan abinda yafaru Ganin Dr Aymaan na hawaye yasa duk jikin mutanen wajen yin sanyi suna kallon yadda ya dauki jinjirar yana kallo yana hawaye. Saida ya dauki kwanaki sosai kafin abin yasakeshi kamar yadda yasaba dik lokacin da patient ya mutu a hannunshi. Babu wanda besan wannan halin nashi na tausayi ba a fadin asibitin Hakan yasa Koda yaji labarin zee sai yaji ta mugun bashi tausayi kuma yaji ya tsani wanda yaudareta don shi aganinshi mata hallitu ne na musanmman wanda ya kamata ayi treating dinsu specially don a gurinshi mata sune gift of life. Aymaan yanada abokai wadanda shi kansa besan iyakarsu ba Amma acikinsu akwai babban amininshi wanda alaqarsu tawuce abota kadai ta koma kamar ta yan uwantaka. Sunan aminin nashi AHMAD JUNAID, dan kasuwa kuma P.A a companin babanshi Tare suka taso tun suna yara kuma tare sukayi karatu a makaranta daya sai course dinsu kawai daya banbanta Sosai suke abota mai tsafta wanda Hakan yasa tun suna qananu suka qulla zuminci tsakanin iyayensu suma don sosai iyayen Aymaan da Ahmed ke zuminci Zuminci yaqara karko ne lokacin da Ahmad da batool suka fara soyayya. Babu wanda beyi farinciki ba da Hakan don ko babu komai Hakan zai qara qarfafa zumuncinsu kuma zai qara girmama abotar dake tsakanin Aymaan din dashi Ahmad din, Wannan kenan. Sai da marece sosai sannan yabaro asibitin Akan hanya ya tsaya yasayi kayan maqulashe da fruits sannan ya wuce gida. Parking yayi a parking space sannan ya bude motar yafito Kamar kullum lapcoat din na sagale a hannunshi ya riqo briefcase dinshi da dayan hannun Rufe kofar yayi sannan ya zagaya ta dayan bangaren ya bude back seat ya Fiddo ledar tsarabar daya siyo yasake maida kofar ya rufe ya kulle motar gabadaya da key din hannunshi sannan ya juya ya nufi cikin gida Da sallama yashiga falon, babu kowa aciki Hakan yasashi nufar stairs kawai yanufi sama Yana qarasa hawa saman itakuma ta fito daga dakin Turus tayi ganinshi haka unexpected Murmushi yayi mata, bata mayar mashi da martani ba Haka kuma batayi magana ba sai kauda kai datayi. "hyy, slm alaiki" yafada cikin murmushi Qara Dagowa tayi tadan kalleshi saikuma ta dauke kai "wa'alaika sallam" ta amsa tana shirin wucewa "here" yafada yana miqa mata ledar hannunshi Kallon ledar tayi takuma kalleshi da alamun tambaya Murmushi yasake yimata "tsarabarku ce, ke da batool" Kamar bazata amsa ba sai kuma ta miqa hannu ta amsa "thanks" "afwan, haza wajibi" yafada yana mata murmushi Juyawa tayi batareda taqara cemashi komai ba takoma dakin Murmushi yasake yi ya dan shafa lallausar sumarshi sannan shima ya wuce dakinshi. A dinner ma yau haka yabi ya takura mata da kallo donma kallo bemata komai Tariga ta saba dashi shiyasa bata maida hankaliba kanshi. Duk abinda yasan zai jawo suyi musayar magana shi yakeyi don ko yaya ne sai yayi yadda yayi ya sanyota cikin Maganarshi Haka ya cigaba dayi acikin kwanakin dasuka biyo baya. Sosai yake qoqarin janta ajiki by behaving freely around her amma kwata2 taqi bashi hadin kai, magana ce idan yayi mata ta amsa a taqaice daga haka kuma zataja bakinta tayi gumm Saidai Hakan be sanyaya mashi gwiwa ba ko kadan kuma besa yafasa janta ajiki ba, everyday idan zai dawo saiya dawo masu da tsaraba, wani sa'in kuma ya kwashesu da ita da batool sufita outing ko shopping wanda acewar batool albarkacin zee take ci don da don ta itace Saidai ta ru6e bata fita shopping ba Indai shi zai kaita Ahankali ahankali tadan fara sabawa dashi don Aymaan mutum ne matuqar iya zama da mutum komai baudadden halinshi, idan ya lura da yadda kake to baya damuwa da duk abinda zakayi zai bika ne a yadda kake har ku fahimci juna. Ahankali zee tafara dan Sakin jiki dashi don wani sa'in suna dan fira sama sama. Ga packs packs daya saba mata da zuwa duk lokacin da yake free Sosai Aymaan yasan takan gari kuma yasan wuraren shaqatawa masu sanya nishadi wanda duk idan ya kaisu sai zee ta nemi damuwarta tarasa. Hakan yasa har qagara take taji yayi masu magana akan su shirya suje yawo. Kasancewar lokacin da zee tazo dubai duk higher institution sunyi nisa a semester dinsu don gab ake da zana exams Hakan yasa aka bari sai anyi hutu an koma sannan a sama mata replacement itama. Cikin yan kwanakinnan zee ta dan warware, yanzu lafiya lau za'a zauna ayi fira da ita harda dariyarta, tasaba da wannan ahalin sosai musanmman batool data koma mata kamar wata bestie don bata jin komai wajen sharing damuwar ta da ita Aymaan kuma haryanzu dai bata ida Sakin jiki dashi ba don basu yan tsokane tsokane yadda yakeyi da batool don koya tsokaneta Saidai tayi murmushi kawai ta kauda kai Shikau Aymaan Hakan baya damunshi don ko gwasaleshi tayi baya nuna yaji haushi haka zai bita yadda takeso don a zauna lfy Ahmed ma yasan da zaman zee a gidan don gidan Wurin zuwanshi ne sosai kamar yadda shima Aymaan ke zuwa gidansu Ahmad din sosai Sau biyu suka ta6a ganin juna amma kusa kullum da kalar labarinta da Aymaan zai bashi Shidai nashi saurare idan kuma yagama yaita yimashi Dariya yana tsokanarshi akan koya afka ne, duk lokacin dayace Hakan Saidai Aymaan yayi mashi kallon uku saura kwabo ya watsar batareda yace mashi uffan ba. *1 MONTH LATER* "nifa zan tafi Allah" inji zee dake bakin kofa tana kallon batool fuska a tsuke "haba habibty, don Allah Kiyi hqr saura kadan fa, idan kika fita wlh tafiyarshi zaiyi bazai tsayani ba" tafada tana cigaba da kiciniyar daure igiyoyin takalminta "kema mugun nawa gareki wlh, tun yaushe kike abu guda kin kasa gamawa anbar bawan allah yanata jira" Tashi batool tayi bayan ta ida gyara takalmin tace "kice dai kawai zumudi kike mutafi bawani an tsaida bawan allah mu mukace muna zuwa? Shi yace muje mu shirya mutafi" Kwafa zee tayi ta juya ta bude kofar ta fita. Saurin feffesama jikinta turaren hannunta batool tayi ta ajiye ta maramata baya da sauri Qara duba agogon hannunshi Aymaan yayi a karo na ba adadi yana wondering wane irin shiri ne Hakan sukeyi haryanzu basu fitoba Sanye yake cikin farin wando da sky blue din riga mai ratsin fari sai takalma farare, yar sumar kanshi tasha gyara sai salqi take Jin taku a stairs yasashi Dagowa ya kalli wajen Lumshe idanu yayi akanta yasake budewa cikin zuciyarshi yana fadin "masha allah" Sanye take cikin dark blue arabian gown da duk jikinta stones ne sai gaban rigar da stones din yafi yin da6a da6a, rigar mai irin faffaden hannun nan ne mai jela sai gyalen rigar data yana akai irin na larabawa wanda sukeyi harda saman ha6a Purse fara ce a hannunta sai takalmi suma farare wanda bakama hangensu sosai sai idan tana tafiya saboda tsawon rigar Besan kallonta yakeyi ba har Saida yaji muryar batool na cewa "Akhie!! Ko mun fasa fitar ne" Da sauri ya dawo duniyar kallonta daya shiga ya juyo ya kalli batool dake tsaye riqeda qugu tana kallonshi Harararta yayi sannan ya miqe tsaye yana cewa "ni tsaranki ne? Kin gama tsaida mutane kuma shine yanzu zaki ishesu da ihu?" Dan Wara idanu batool tayi "na tsaida mutane ko ta tsaida mutane, Tundazu ita nake jira tagama Tambayarta kaji" Juyowa zee tayi tana kallonta a mammakince jin yadda ta laftamata qarya qiri qiri Ganin Hakan yasa Aymaan yayi kamar zai maketa yana cewa "munafuka, sharri zakiyi mata ko? To wlh kibi ahankali kar nace banda ke a tafiyar nan" Turo baki batool tayi "nidai dama nasan ba'a sona" "gwara da kika san Hakan, ukhtie mutafi kinji?" yafadawa zee Saida zee ta danyi mata gwalo a fakaice sannan ta taho suka wuce da Aymaan Binsu da kallo batool data cika famm tayi saikuma tayi Kwafa tabi bayansu, da tana iya zuciya da tayi tafasa binsu amma tasan ko tayi ita keda asara ba suba Awaje ta taddasu zee harta shiga bangaren mai zaman banza Aymaan ya maida kofar ya rufe gently Qara kumbura fuska tayi sannan tazo sumi sumi ta bude back seat ta shiga Ta6e baki Aymaan yayi shima ya zagaya mazaunin driver ya shiga ya tada motar sannan suka fice daga gidan. Tafiya suke babu mai cewa komai a motan daman batool itace aku mai bakin magana cikinsu to yau kuma fushi akeyi shiyasa Aymaan ya kunna wani disc na waqar maheer zain jin yadda motar ta dauki shiru. Basu jima ba suka iso wani babban pack Tun daga waje zaka gane pack din ya hadu kuma bana qanannun mutane bane. Parking space Aymaan ya nufa ya nemar ma motarshi Wurin parking ya pakata sannan duk suka firfito Sosai zee taji farinciki ya lullu6eta don ko ba'a fadaba tasan pack din ya hadu. Wajen siyan tickets suka nufa ya siya masu sannan suka wuce ciki Saida suka babbada tickets din sannan suka wuce ciki. Sosai farinciki yasake lullu6e zee don suna shiga taji Wurin yayi bala'in yimata Har mammaki take na yadda Aymaan yasan wuraren shaqatawa masu qayatarwa irin haka. Batool dake fushi tuni itama ta warsaqe suka shiga yawonsu. Sosai sukayi enjoying lokacinsu don sun yayyawata sosai don pack din babba ne yana Hade da zoo da restaurant ma, ga beach daga can qarshen Wurin. Saida suka sha yawo suka gaji sannan suka samu wuri kusada beach din suka zauna shikuma Aymaan yawuce don samarmasu ice cream da sukace suna so. Labari zee da batool suka cigaba dayi cikin nishadi suna kallon ruwan gabansu suna jiran dawowarshi Dan shiru zee tayi kamar mai tunani Ganin Hakan yasa batool cewa "ya dai?" "wlh dazu dazamu shigo daidai wajen wasan yarannan naga ana siyarda burger, ina son burger sosai wlh, kallo daya nayimata ta biya raina don rabona daita tun a Nigeria" "shine kuma bakiyi magana ba muka tsaya muka siya?" Dan yatsina fuska tayi "banson tsaidamu ne amma bari kigani kafin yadawo zanje nasiyomana" tafada tana yunqurin tashi "A'a kibari yadawo saiki fadamashi saiya siyamana" inji batool Harararta zee tayi tace "tunda gashi bawa ko? Nidai natafi I'll be back in a jiffy" tafada tana wucewa "ok saikin dawo" batool ta amsa sannan ta maida hankalinta kan ruwan gabanta ta cigaba da kallo. Dakyar zee ta iya gano inda taga burger dazu saboda girman wajen donma tana bin signboard suna nuna mata hanya Burger manya biyar tasa akayi mata wrapping sannan taciro kudi tabiya aka bata Chanjinta aka bata ta amsa tajuyo tana zura kudin a cikin purse dinta Batayi auneba taji tayi qaro da abu wanda Hakan yasa ledar burger dinta faduwa "ya sallam!" tafada ahankali tana kallon burger dasuka watse a qasa Juyawa tayi ta kalli mutumin da sukayi karo dashi wanda yaqara gaba kamar ba mutum ya buge ba. Ganin yayi nisa yasa ta buga Tsaki cikin jin haushi ta duqa tafara tattara burgern ta Cak ta tsaya da tsintar datakeyi lokacin da wani abu yayi crossing qwalwarta Ahankali ta tariyo abinda yafaru yanzu a kwalwarta. Koda sukaci karo ta dan kalli fuskarshi sama sama kafin ta maida a kan burgern ta dake watse a qasa Wani irin bugu zuciyarta tayi Zumbur ta miqe tsaye tayi saurin Juyawa Saidai babu shi babu alamunshi. Cikin fitan hayyaci ta shiga ratsa mutane da gudu gudu sauri sauri tana waiwaigawa don ganin ta inda zataga koda wulginshi ne Saidai babu shi babu 6il6ishinshi. Haka ta cigaba da ratsa mutane wasu ma bangajesu takeyi bata saniba, zagi kau tashashi Saidai a banza don batasan sunayi ba, Kunnuwanta sun dode, idanunta sun rufe, hankalinta yayi qololuwar tashi, babu abinda take gani a idanunta sai fuskarshi... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:39 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *057* *DEEN 😱* Tun daga nesa Aymaan ya hangi batool ita kadai zaune inda yabarsu. Qarasawa yayi cikin zuciyarshi yana wondering ina Zainab "hey" yafada yana zama gefenta Juyowa batool tayi ta kalleshi sai tayi murmushi "laa harka dawo?" "eh, ina Zainab din kuma?" "wlh wai burger takeso tagani a playground din yara dazu dazamu shigo shine taje saye" "Amma meyasa bata gayaminba? Da nataho mata dashi ai" Daga kafadu batool tayi alamun oho? Shima dan daga kafadun yayi sannan ya miqa n Mata nata robar ice cream din shima ya bude nashi suka shiga sha suna fira jefi jefi. Sun kusan minti ashirin ahakan amma har lokacin babu alamun dawowarta "wai tun yaushe ta tafi ne? Shirun yafara yawa ga ice cream dinta yafara narkewa" inji Aymaan "wlh Akhie nima naji Shirun Yayi yawa, tun fa baka dade da tafiya ba ta tafi" "kema meyasa zaki barta ta tafi ita kadai? Ita da ba yar gari ba? Maimakon kisa ta jirani indawo in saimata kokuma kuje tare" "wlh nace mata tabari kadawo ka siyamata amma ta qiya tace ai kafin ka dawoma zata dawo" Shiru Aymaan yayi sai kuma ya miqe tsaye "bari naje naduba" Itama batool miqewa tayi "nima zan bika" Be amsa mata ba yayi gaba itama ta ta take mashi baya Wajen playground din yaran suka fara zuwa Saidai ko mai kama da ita basu gani ba hakan yasa suka nufi wajen balaraben dake siyar da burger din Cikin harshen larabci Aymaan ya gaida mutumin sannan ya tambayeshi wata tazo nan siyan burger yanzu? Cewa yayi ai masu sayen dayawa bazai iya riqe wadanda suka zo ba Kwatancen zee din Aymaan yashiga yima mutumin da kayan dake jikinta nan take mutumin ya gane ta Yace eh tazo ta siya amma fa Tundazu, tana kuma siya ta tafi. Godiya Aymaan yayi mashi sannan yace ma batool su koma inda suka fito qila sa6a hanya sukayi Saidai ko da suka koma still batanan. Wasa wasa tun suna nemanta batareda sun kawo komai aransu ba har hankalinsu yafara tashi don babu inda basu zagaya ba a fadin pack din amma ko me kama daita Basu ganiba. Hankalinsu ne ya tashi suna tsoron kar ace 6acewa tayi Nanfa Aymaan ya rufe batool da fada yana cewa duk laifinta ne data barta ta tafi ita kadai yanzu ga irinta nan Itadai batool batada ta cewa, fatan ta dai kawai aganta din. Dole sukaje wajen securities din wajen sukayi masu magana Jin Hakan yasa suma suka gayawa manajojin wajen nan take aka ce a aika su Aymaan din can wajensu. Tareda jagorancin wasu securities din biyu suka tafi can babban ofishin masu managing wajen. Shiga dasu akayi recording room kamar yadda suka saba idan wani ya 6ace a wajen nan aka shiga tambayarsu tun yaushe ta tafi Batool ce ta fada masu lokacin dakuma inda taje Nan take aka Maida cctv din wajen playground din zuwa daidai lokacin da batool ta bada Tsayawa dik sukayi suna kallon masu shige da ficen wajen ta cikin majigin ga mai burgern nan shima yanata harkar gabanshi Can kawai sukaga shigowar zee wajen "yauwa gatanan, wannan ce" inji Aymaan yana nuna masu zee data nufi mai burger din Duk nutsuwa suka sakeyi suna kallon yadda take magana da mai burgern da lokacin daya samata a leda yabata da lokacin data Fiddo kudi tabashi yabata chanji Sai tajuyo tana saka kudin a purse, kawai sukaga tayi kan wani dake tahowa sukayi karo ledar hannunta ta watse a qasa. Mutumin be tsaya ba ya cigaba da tafiyarshi sai sukaga ta bi mutumin da kallo sai kuma ta duqa tafara tsintar burger dinta dasuka watse qasa Sai sukaga ta tsaya Cak da abinda takeyi kamar an tsaida ta da remote Saikuma tayi saurin miqewa tana waige waige. Can tabar wajen da sauri tanata ratsa mutane har tabar playground din. Hankalin su Aymaan yasake tashi Shugaban Wurin yaba mai operating din computer umarnin duk ya maido daukar koina na pack din zuwa daidai lokacin da zee tafita daga playground din Haka kau yayi ya maido daukar daidai lokacin yayi playing record din Duk nutsuwa sukayi suna baza idanu a kashi kashin recording din dake gaban majigin "gatacan!" inji Aymaan yana nuna zee datayi hanyar fita Zooming Wurin akayi akaga har lokacin tafiya takeyi tana waige waige harta fita daga gate. Shiru sukayi duk kansu akulle, can kuma sukaga tasake Shigowa pack din wannan karon ta nufi zoo. Zooming din mai dauka zoo sukayi sukaga nan ma neme neme take tana magana kamar ma bata a hayyacinta Can kuma ta dauki hanyar restaurant nan ma taci nemanta sannan ta dawo ainahin playground din ta cigaba da tafiya tana waige waige kamar marar hankali. Shiru duk sukayi suna kallonta ta majigin duk inda tashiga sai ayi Zooming wajen har akazo daidai wannan lokacin sukaga ta zauna kan wata kujerar yara mai zagaye ta kife kanta bisa qarfen kujerar "gatanan, muje kai kuma ka cigaba da monitoring dinta data tashi ka sanar dani" Managern ya gayama mai operating din computer Da Managern da Aymaan da batool suka fito suka nufi inda suka ganta ta cikin majigin cikin sauri Cikin lokaci qanqani suka isa wajen kuma suka hango ta tun daga nesa a position dasuka ganta a majigin kanta Hade da qarfen kujerar haryanzu Saurin ida qarasawa wajenta sukayi Batool ce ta zauna kusada ita tareda dafata Hakan yasata saurin dagowa Yadda batool taga idanunta sunyi jajur yasa gabanta faduwa "meya faru ukhtie? Menene?" Shiru tayi batace komai ba Saima kafeta da jajjayen idanunta datayi "talk to me sister, what happened?" taqara fada Saidai nan ma shiru Hakan yasa shima Aymaan matsowa kusa "Zee, meya faru? Meyasa kike kuka?" Wasu hawayen ne suka qara gangaro mata Sosai Hakan yaqara tada hankalinsu Hakan yasa batool riqo hannunta gam cikin nata tana cewa "Kiyi magana don Allah zee, what happened?" Saurin fadawa jikin batool din tayi ta rungumeta gamm tana kuka sosai Sosai Hakan yasake hargiza tunaninsu Hakan yasa nan da nan itama batool tafara hawaye "sister.. Don Allah ki fadamin" inji batool cikin muryar kuka itama "na ganshi batool, naganshi.. Wlh" Dagota batool tayi daga jikinta tana kallonta "kinga wa?" "DEEN dina, na ganshi da idanuna wlh.. A playgroud, wlh shine.. Deen dina" Cikin mammaki Aymaan da batool suka hada baki Suna cewa "Deen?" Cikin sauri zee da duk jikinta ke rawa ta kadamasu kai sannan tace "eh.. Eh wlh, naganshi. Naga Deen dina.. A playground, ya bangajeni.. Ya zubarmin da burger yatafi, nasan be ganni bane, bega fuskata ba, be ganeni ba Amma ni na ganshi, naganshi wlh. My Deen is back batool I can't believe it" tafada cikin kuka sosai Rungumota batool tayi ganin yadda jikinta ke rawa kamar mazari itama tana hawaye "waye Deen batool?" inji Aymaan da duk yakasa gane kan maganarta Share hawayenta batool tayi still zee na jikinta tana shesheka "her boyfriend" inji batool ahankali Wani abu Aymaan yaji ya soki zuciyarshi nan take "boyfriend?" injishi yana kallon batool cikin wani yanayi Kada kai tayi tace "wannan wanda ya tafi ya barta" Maida kallonshi yayi akan zee dake shesheka haryanzu kanta kife a jikin batool "but Zainab ba yana Nigeria ba?" Dagowa tayi ta kalleshi wasu hawayen na sake gangaromata "na ganshi, dazu.. Da idanuna" Hadiye abinda ya tsaya mashi a wuya yayi cikin tausasa Murya yace "Zainab, calm down please.. Wataqila wani kika gani kikayi mistaken dinshi dashi, wataqila ko yanayi yayi dashi amma ai wancan Nigeria yake kuma he's gone, mezai kawoshi nan?" "bansaniba, bansan abinda ya kawoshi nan ba, all I know is shine" "to idan shine ina yake? Wataqila gizo yayi maki" "ba gizo yayi min ba Aymaan, na ganshi da idanuna, I took a glimpse of him and before I could turn back again to confirm he's gone" "that's means definitely gizon yayi miki, kince kafin ki sake juyowa he's gone, bakya ganin dama babu shi din kawai imagination din idanunki ne? Idan shine zaki ganshi immediately you turned back, Koda ba a kusa ba zaki hangeshi" "meyasa zaimin gizo yanzu? Meyasa tun baya be yimin gizo din ba sai yanzu? Am telling you shi nagani, shi nagani, you guys have to believe me, nasan shi, bazan iya mistaken dinshi da wani ba, nasanshi fiyeda shi kanshi, why zaku maidani mahaukaciya" ta qarashe cikin dan daga murya Ajiyar zuciya Aymaan yayi yace "shikenan, yanzu ya kike son ayi?" "mu nemeshi please, tayiwu ni yake nema shima, tayiwu yaje gidane akace na dawo nan shiyasa shima ya biyo ni, please ku tayani nemanshi" tafada tana Hade hannuwa cikin kuka Sosai zuciyar Aymaan ke zafi, who on earth is this guy? Is he this heartless? Ji yadda ya maida yar mutane zarrariyar qarfi da yaji. Maida lower lip dinshi yayi ciki ya cije yana imagining haduwarsu da gayen and how he'll make him pay for all he did Kallon zee yasake yi yana jin kukan nata har cikin zuciyarshi "muje" yafada yana kallonta Dagowa tayi saurin yi ta kalleshi "Akhie, kaima ka yarda shi din tagani?" inji batool Kauda kai yayi "idan muka duba din zamuyi comfirming ko shi dinne ko bashi ba" yafada yana miqewa tsaye Gabadaya mood dinshi ya chanza, gabadaya wannan al'amarin yayi ruining day dinshi Itama zee tashi tayi cikin sauri tana share hawayenta "inane kika ganshi?" inji Aymaan trying so hard to control himself "A playground wajen mai burger" tafada cikin sauri "ok muje" yafada saikuma ya juya wajen mutanen dasuka taho dasu nemanta wadanda duk basu fahimci me suke cewa ba kasancewar hausa sukeyi Abinda ya faru ya gayamasu briefly sannan yayi musu Godiya yace karsu damu zasuyi handling din kingin Da haka suka rabu Aymaan yayima zee nuni da hanya ta shiga gaba don kaisu inda taganshi din Playground din suka sake komawa ta gwada masu inda sukaci karo din sannan ta nuna masu hanyar dayabi ya tafi, sai suka bi hanyar suma suka shiga nemanshi Babu inda basu shiga ba a park din ba, Saida suka duba every nook and cranny din park din, wani Wurin ba basusan dashi ba Amma ko mai kama dashi basu gani ba Saidai dukda Hakan zee bata haqura ba sai qara jansu take suna komawa wuraren dasuka wuto don sake dubawa. Sosai Batool ta gaji da yawon Saidai taga su ko ajikinsu, ga Aymaan daya biyemata duk inda tayi Binta yake batareda nuna any single sign na gajiya ba Hakan yasa itama daurewa kawai ta cigaba da binsu amma harga allah ta gaji sosai da yawon Haka sukaita zagaye park din har zee din ta gaji don kanta ta haqura ta zame ta zauna bisa grass carpet din wajen ta Hade kai da gwiwa Hawaye ta cigaba dayi tana sobbing ahankali tana jin raunin zuciyarta daya fara qamewa tadawo sabo kamar yanzu tajishi Kallonta Aymaan da batool suka tsaya yi Babu mai cewa komai sai ma tausayinta daya qara samun muhalli a zuqatansu. Ahankali Aymaan ya duqa gabanta ya tsaya yana kallonta kawai Lumshe idanu yayi ya bude, shi kadai yasan abinda yakeji a zuciyarshi "Zainab.." ya kira sunanta gently Bata amsa ba kuma bata dago ba "kibar kukan nan haka Zainab,please. Wanda kike zubdama hawayen nan be cancancesu ba" Dagowa tayi fuska sha6e2 da hawaye ta kalleshi tace "ban damu da ya cancancesu ko be cancancesu ba, abinda nasani shine na cancanci in zubdasu akan abubbuwan dake faruwa dani" "Zainab hawaye bazasuyi miki maganin komai ba, da sunayi da sunyimiki tuntuni, abinda zaifi miki shine haquri, Kiyi hqr kikuma rungumi qaddararki, and pray hard to move on, but not wasting your tears ga wanda beyi worthing dinsu ba" yafada zuciyarshi na zafi sosai "Tears are not a sign of weakness Aymaan, but of courage. Hiding your emotions is self destructive and will never allow you to heal" "No guy is worth your tears Zainab and when you find one that is, he won’t make you cry" inji Aymaan cikin qunar zuciya Banza kawai tayi dashi ta kyaleshi don bazai ta6a ganewa ba. Yanzu idan akwai abinda tafi buqata shine kukan, shine kawai zai sata jin sauqin abinda takeji. A yan kwanakinnan tayi tunanin she has moved on, tayi tunanin tariga ta maida past dinta behind her ta cigaba Amma ganin Deen yau ya maido ta at the very beginning, yajawota zuwa level 0 datayi tunanin tuni ta wuce wajen. Shiru wajen ya dauka na wani lokaci sannan batool ta qaraso itama wajensu ta tsugunna ta kalli zee da haryanzu kanta ke kife da gwiwa saikuma ta maido kallonta ga Aymaan dake kallon zee din shima Dafa kafadarta batool tayi tace "it ok sister, Kiyi hqr ki tashi mutafi kinga dare nayi, idan ma shine zaku qara haduwa insha allah, idan allah ya qaddara zaki sake ganinshi zaki ganshi, put that faith in your mind, let's go home." 💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙 Haka sukayi tafiyar komawa gida silently, motar tayi shiru kowanne da abinda ke kai kawo a ranshi, sai gashi suda suka fita outing don samun nishadi sun dawo rai a dagule. Koda sukayi parking zee ce farkon fita daga motar ta nufi cikin gida. Duk binta sukayi da kallo harta shige. Ajiyar zuciya batool ta sauke sannan itama ta sauka zata wuce Aymaan ya dakatar daita da "karki sake ki tadomata maganar, just behave kamar babu abinda yafaru, ok?" Kada mashi kai kawai tayi sannan ta wuce Binta itama yayi da kallo harta shige sannan ya maida kanshi a kujera ya lumshe idanu. Ya jima ahakan sannan ya fito ba don ya shirya ba sai don kiraye kirayen sallar magrib da aka fara Haka suka qarasa ranar ransu a jagule musanmman zee da Aymaan Ko wajen dinner Aymaan na lure da zee kuma kallo daya yayimata ya gane tayi kuka ba Dan kadan ba hakan yasashi jin ranshi ya ida dagulewa, idan ya tuna cewa yanzu haka wanda yasakata a wannan halin yana can hankalinshi a Kwance sai yaji ranshi ya qara 6aci, sai yaji inama zai ganshi face-to-face da saiya tabbatar ya hadamashi jini da majina, saiya mashi illan da bazai qara moruwa ba Batool kau kamar yadda Aymaan ya fada mata haka tayi, kwata2 nunawa tayima kamar ta mance da abinda yafaru, haka taita harkokinta tana kuma sako zee data koma kamar ba ita ba Cikin shirmenta Da daddare kasa barcin kirki zee tayi, banda juyi babu abinda takeyi, daga baya dataga barcin ya gagara saita miqe taje tayi alwalla tafara nafilfillu Ta dade tana addu'a akan idan har dagaske Deen ne tagani a pack yau allah yasake bayyana mata shi, idan kuma ba shi bane allah ya sassauta mata abinda takeji a zuciyarta Sai can cikin dare tasamu barcin ya sadado yayi awon gaba daita. *WASHEGARI* Yau asabar kuma weekend so yau ranar hutu ce ga mutane da dama musanmman ma'aikata Ciki harda Aymaan da dama ranakkun weekend ne kawai yake samun hutawa sosai. Koda ya sauko yin breakfast qasa sai ya tarar su harsunyi abinsu sun koma sama, Hakan yasa ya zauna shikadai yayi serving kanshi yafara ci _Deen dina_ Maganar zee ta jiya ta fado mashi a rai a karo na ba adadi Ya rasa dalilin dayasa yakasa cire wannan kalmar a ranshi kuma duk lokacin daya tunata sai yaji kamar ana gasa mashi zuciya Jiya shima beyi isashen barci ba, da tunanin abinda yafaru ya kwana, he can't believe duk abinda gayen nan yayima zee zata iya koda yimashi kallon tsiya ne bare na arziqi A tunaninshi koda tururuwa akayi tayi ana Shigowa ana cewa tafito gashi can waje ko kallo masu kiran bazasu isheta ba, a tunaninshi ta tsaneshi tsanar da bata misaltuwa amma sai yaga sa6anin Hakan Daga yimata gizo ta gigice ta rikice, wannan da dagaske ne fa to? Dama haka soyayya take? Mutum yayi maka laifi, ya cuceka amma ka kasa haqura dashi, ka kasa zuciya dashi, dama haka soyayya take koko tata ce Hakan? Da wannan tunane tunanen yagama cin abincin sannan yakoma sama yashige dakinshi yasake kwanciya ya qure a.c ya kwanta rigingine ya lumshe idanunshi abubbuwa dadama na kaikawo a qwalwarshi Besan sadda barci ya daukeshi ba sai jiyayi ana bubbuga kofarshi cikin barci Juyi yayi zuwa dayan gefen gadon yana qara tattare jikinshi wuri guda saboda sanyin a.c din dakin daya fara mashi yawa Jiyayi an cigaba da bubbuga dakin, wannan karon da dan qarfi Duk yadda yaso ignoring bubbugawar kasawa yayi don bugun kofar akeyi non-stop Hakan yasashi tashi Dakyar ya miqe zaune. Agogon bangon dakin ya duba yaga 1 saura Tsaki yaja yana jin wani irin haushi ya mammaye zuciyarshi Jin an sake bubbuga kofar yasa ya tashi a fusace ya nufi kofar Murda handle din yayi ya bude kofar da qarfi wanda Hakan yasata dan ja baya a tsorace Ganinta yasa nan take expression din dake fuskarshi na fushi yayi saurin chanzawa yafara murmushin yaqe "ukhtie? Kece ashe?" yafada yana fadada murmushinshi Sauke idanuwanta tayi qasa kawai tayi sakamakon arba datayi da broad chest dinshi da packs dinshi ta cikin singlet dinshi don dama daga shi sai dogon wando sai singlet "erm.. You need something?" Girgiza kai tayi ahankali batareda ta dago ta kalleshi ba Ganin uneasiness dinta yasashi gane abinda yasata yin Hakan sai yace "ok, you want to talk to me right? Ina zuwa, just a minute" da haka saiya koma ciki Ko seconds talatin beyi ba yasake bude kofar wannan karon sanye da jallabiya ash ta maza Fitowa yayi daga dakin ya jingina da kofar sannan ya kalleta yana murmushi "ya yau?" Still bata dago ta kalleshi ba tace "alhamdullilah" Shiru yadan ratsa wajen, jin Hakan yasata dagowa sai taga shima ita yake kallo sai tayi saurin sauke idanunta qasa "tell me, menene?" yafada tenderly Sake dagowa tayi ta kalleshi sai kuma ta saukar da kanta qasa ahankali kamar mai ciwon baki tace "park din da mukaje jiya" Dan shiru Aymaan yayi saikuma yace "yes? What about that?" "sunanshi.. Nakeson ka gayamin" tafada still idanunta a qasa Tsayawa yayi yana kallonta for some moments Jin shiru yasa ta qara Dagowa ta kalleshi da shining eyes dinta dake glittering saboda dan ruwan daya taru aciki "please" tafada ahankali tana kallonshi "meyasa kike son sanin sunan?" inji Aymaan still yana kallonta kamar mai son karantar wani abu a fuskarta "babu, just tell me" "zan gayamiki amma saikin fadamin dalili" yafada still idanunshi akanta "please.." tafada ahankali sai kuma ta sauke idanunta wanda yayi daidai da digar hawayenta qasa Cigaba da kallonta yakeyi yana jin zuciyarshi kamar ana melting dinta "ki fadamin me zakiyi da sunan and I'll tell you" yasake fada "babu ruwanka, just tell me" tafada cikin cracking voice, a inda yake tsaye yana hango diddigar hawayenta "da ruwana saboda ke sister ta ce, idan batool ce tazo ta tambayeni itama haka zan cemata, ke da batool daya ne a wajena" Ba don bata iya zuciya ba da babu abinda zai qara tsaidata a gabanshi, Hakan yasata cewa "inason.. Naje ne" "Wani abu kikeso? Ki fadamin koma menene zanje nasiyo miki" inji Aymaan din "babu abinda zan siyo, nidai ka fadamin.. Don Allah" Sai kuma ta rufe fuskarta da taffukan hannayenta ta shiga sobbing ahankali Lumshe idanu Aymaan yayi cikin quncin zuciya sannan yasake budesu suna kadawa ya kalleta dasu "Me zakiyi acan?" yasake tambaya Muryarshi na chanzawa Cikin kuka zee tafara magana "I know I may sound ridiculous ko ayimin kallon mahaukaciya, I don’t care. Zuwa zanyi nemanshi, bazan iya jure abinda zuciyata keyimin ba, I can't Zuciyata na gayamin yana can, yana nemana, Inason inqi zuwa amma bazan iya ba, bazan iya cigaba da jure azabar datake minba, nayi qoqarin jurewa daga jiya zuwa yau but not anymore. Ka fadamin sunan wajen, ko cab ne sai yayi dropping dina Idan kuma bazaka fadamin ba zan tafi, zan tafi naita nema harna gane" Tunda tafara maganar Aymaan ke kallonta batareda yayi qoqarin katse mata hanzari ba har Saida takai aya. Dan murmushi yayi wannan yafi kama da mai ciwo sannan yace "to meye na kukan? Why the tears? Da Alamu dai beneath that eyes akwai qoramun ruwa shiyasa abu kadan sai sharr hawaye. Meye aciki to? Ni bakiyi sounding ridiculous to me ba, thats what your heart wants and so be it. Jeki shirya na kaiki" Dagowa tayi ta kalleshi da wet eyes dinta Kada mata kai yayi "yes, ki shirya zan kaiki basai kin hau cab ba" Girgiza kai tayi tace "A'a nidai kawai ka fadamin sunan, thats all" Shima girgiza kai yayi yace "naqi din, go and dress up bari nima na shirya saimu tafi" Be bata damar qara magana ba ya bude kofar dakin nashi ya shige ya rufo Bïñ kofar tayi da kallo sai kuma ta share hawayenta ta juya ta koma daki tana jiran fitowarshi don ita dama a shirye take. Kujerar dake facing din gadonshi ya samu ya zauna akai tareda dafe goshinshi Shi kadai yasan abinda yakeji a zuciyarshi, musaltashi kuma 6ata lokaci ne don bazai misaltu ba Ya kusan Mintuna goma ahakan sannan ya miqe ya zare jallabiyar jikinshi sannan ya nufi toilet. Zaune take kan stool din gaban mirror tana daga kai tana kallon agogon dakin akai akai Tunda tashigo ko gefen batool bata sake kallo ba don haryanzu haushinta takeji na qin gayamata sunan Wurin datayi wanda Hakan ma yasa taje tasamu Aymaan din Itakau batool bata damu ba sai cigaba da harkan gabanta da itama tayi batareda ta kulata ba. Suna Hakan zee tajiyo budewar kofar dakin Aymaan Jitayi kamar ta miqe ta fita amma tasamu ta danyi controlling kanta kadan ta cigaba da jira Kwankwasa kofa yayi Hakan yasa tayi zumbur ta miqe tsaye ta nufi kofar Dakatar da abinda takeyi batool tayi tana kallon kofar don ganin wa ke bubbuga kofar Bude kofar zee tayi sai sai idanunta sukaci karo da Aymaan da ya chanza shiga zuwa manyan kaya irin namu na hausawa farare sunyi bala'in amsarshi Murmushi yayi mata "sorry na tsaidaki ko?" Batace komai ba sai sauke kai qasa datayi "oya muje" yafada yana kaucemata a hanya Dama abinda takeson ji kenan Hakan yasa ta ida fitowa tafara tafiya shikuma ya biyo bayanta "Akhie!!" muryar batool ta tsaidasu dga tafiyar dasuka fara Juyowa sukayi suna kallonta Yayinda itakuma ta qaraso bakin kofa tana ma Aymaan kallon mammaki "Akhie, badai wajen nan zaku ba?" ta tambaya a mammakince "eh can ne ko kinada saqo?" inji Aymaan "but Akhie.." "baki dashi kenan, sai mun dawo" yayi gaba abunshi Zee ta sauke sigh of relieve sannan itama ta bi bayanshi batareda tabi takan batool dake binsu da kallo cikeda mammaki ba A parking space ta tarar dashi harya budemata Front seat kamar yadda yasaba Zuwa tayi ta shiga sannan ya maida kofar ya rufe ahankali sannan ya zagaya yashige shima ya rufo kofar sannan ya tada motar yayi reverse sukazo suka fice daga gidan. Tafiya suke silently babu mai cewa komai acikinsu har suka qarasa park din jiya. Fitowa sukayi gabadaya suka rurrufe kofar sannan suka fara tafiya, Aymaan a gaba zee a bayanshi Saida suka fara sayen ticket sannan suka shiga ciki Kamar dai jiya yau ma wajen acike yake da mutane sunata kai kawo Zee ce agaba yanzu Aymaan a bayanta suka shiga bin ko ina suna dubawa kamar dai jiya. Duk namijin da zasu hadu dashi sai zee ta kalli fuskarshi Koda baya ya juyamata saita san yadda zata shawo gabanshi taga fuskarshi Haka sukaita zagayen park din kamar dai jiya Gajiya iya gajiya sunyi amma Aymaan ko kadan be nuna ba Binta kawai yakeyi yadda takeso Saida taji daga kafa na neman gagararta sannan ta nemi wani kujerar swing ta zauna yana sauke numfashi ahankali Cikin kulawa Aymaan ya dan duqo yana kallonta "Are you ok?" yafada ahankali Kada mashi kai tayi sai kuma ta share hawayen daya sulalo mata "don Allah mu jirashi, nasan qila bekai da zuwa bane, Inaji ajikina zaizo don Allah mu zauna mu jirashi, kaji Yaya Aymaan?" Murmushi ya su6uce mashi, wai yaya Aymaan, dama yaushe tafara kiranshi yaya? "haba karki damu sister, mu jirashi din nima Inaji ajikina zaizo, no p kinji?" yafada still yana murmushi Dadi taji ya kamata, dama haka gayen nan keda sauqin kai? Shima zama yayi a kujerar dake kusada ita yayi folding hannu a qirjinshi yana kallon masu kai kawo kamar yadda takeyi itama This is crazy! Anya kau wannan yarinyar soyayya bata haukatata ba? Tayaya zata sa su tsaya jiran gawon shanu? Mutumin da batada ma tabbacin ta ganshi din Amma dayake Aymaan mutum ne matuqar haquri da kuma saukin kai plus yadda yake jinta a zuciyarshi sosai yasa yaqi nuna komai suka cigaba da jira. Wasa wasa sune har bayan asr zaune suna jira sallah kawai ke tadasu, a inda suke suna iya hango gate so duk masu shige da fice a kan idonsu Dukda Aymaan be duba wayarshi ba yasan akwai tarin missed calls dayawa dama Saida ya maidata silent tun a gida don kar kira yayi distracting dinshi Ya riga yasa a ranshi yadda ita tasa suka zo nan to komawar ma saita nemi sukoma din zasu koma don shi mutum ne me bama mutum damar gano bullewar hanyar daya dauko da kansa kamar yadda yanzu yake son tagano haukanta da kanta Maida kanta tayi kan gwiyagunta jin anfara kiraye kirayen sallar magrib Sosai zuciyarta ke mata suya kamar ana soyata a tafasashen mai Ta dan jima ahakan sannan ta dago batareda ta kalli Aymaan ba tace "mutafi" Yi yayi kamar bejita ba hakan yasata qara cewa "ka maidani gida" Sai a lokacin ya dago ya kalleta "tun yanzu?" yafada yana kallonta Miqewa tsaye tayi ahankali tana Rataya jakkarta "eh mutafi" "ok, mufara sallah tukkuna" yafada yana miqewa tsaye shima Saida suka wuce masjid akayi sallar dasu sannan suka fito daga wajen suka hau mota suka kama hanyar gida. Kamar yadda suka zo yanzu ma silently suka koma babu mai cewa komai kowa da abinda yake sakawa a zuciyarshi Yana iya ganin yadda take dauke hawayenta akai akai ta gefen idonshi, Ajiyar zuciya ya dan sauke yana dan girgiza kanshi ranshi a mugun jagule. Koda suka isa gida sai suka tararda su ummy tsaitsaye hankula a tashe Zee dai tana zuwa tayi sama dagudu cikin kumshe kukan dake neman kufcemata Hakan yasa suka maida hankalinsu akan Aymaan Fada sosai suka shiga yimashi akan meyasa zai biyemata sutafi suyi wannan zaman bayan yasan ba lallai bane ace da gaske shi din tagani ba, mezai kawoshi dubai mutumin dake Nigeria Beyi mammakin yadda akayi suka san da zancen ba don yasan batool ce zata gayamasu Hakan yasa yayi shiru suka qaraci fadansu suka gama ya basu haquri sannan ya wuce sama yashige dakinshi shima. A ranar babu wanda yafito dinner da zee da Aymaan din Kowannensu is in a very sad mood Saidai za'a iya cewa na Aymaan yafi don zee ita ke wahalar amma yafita jin zafin abin, jiyake kamar yayi me don takaici. Ranar dai da daddare barci Saidai sukayi rabi da rabi shima marar dadi Washegari ma haka suka tashi so moody don dukkansu ransu a cinkushe yake musanmman zee, shi Aymaan ma yana gama abinda zaiyi a gidan ya fice ya wuce gidansu abokinshi Ahmad Junaid A bangaren zee kuma haka ta wuni cikin rashin walwala, duk yadda batool taso sata feeling better Saidai ta haqura ta kyaleta itama. Ahankali Zainab takoma gidan jiya, always moody, magana inba takama dole ba batayi, Dariya kuma rabonta dayi tun ranar kafin abin yafaru Sosai wannan chanjin ya damu su ummy dasuka fara murnar warwarewarta da farko. Wani sa'in haka zasu zaunar daita suyita yimata nasiha da rarrashinta amma a banza, kwata2 takasa komawa normal self dinta kuma Aymaan kau shima yana cikin damuwa tunda abin yafaru musanmman daya lura da halin datake aciki yanzu amma dayake gwanin iya 6oye damuwa ne babu wanda yasan abinda yake ciki don Kodayaushe idan ka kalli fuskarnan zaka ganta da qayattacen murmushi akai. *AFTER TWO WEEKS* Haryanzu zee bata ida komawa daidai ba Saidai tarage moodiness dinta sosai Yanzu takan zauna ayi fira daita amma ba mai tsayi ba don haryanzu bata ida healing daga famin datayi ba na raunin zuciyarta Yau saturday, babu aiki don haka a gida Aymaan ya wuni Batool bata gida taje ganin wata classmate dinta da batada lafiya Babu yadda batayi da zee akan ta rakata ba taqiya dole ta tafi ita kadai. Suna zaune falo da ummy da zee suna dan fira Aymaan ya sauko daga sama cikin shirin shi na fita Qarasowa yayi falon cikin fara'arshi ya zauna suka dan qara labarin dashi sannan ya miqe yana cewa ummy zaije wajen aikin Abbu amso saqo, shi ya kirashi yaje Adawo lfy ummy tayimashi itakuma zee takama kallonshi kamar tace zata bishi don itama zaman gidan yafara isarta don jitake wama yace taqi bin batool Ganin kallon datake mashi yasashi yimata tayin ko zata rakashi? Da sauri ta Kada kai kamar dama jira take sai kuma ta kalli ummy ta sadda kai Murmushi ummy tayi tace to ta tashi su shirya sutafi ko babu komai taga gari zata kuma ga ma'aikatarsu Abbu. Cikin zumudi ta tashi ta haye sama don chanzawa suka bita da kallo fuska dauke da murmushi Cigaba da firarsu su ummy sukayi harta sake saukowa cikin shirin ta. Ganin Hakan yasa Aymaan tashi daga zaunen dayake sukayi sallama yayi gaba zee tabishi a baya Motar Aymaan suka shiga shi a mazaunin driver ita a gefen shi suka fice daga gidan. Ma'aikatar su Abbu din suka shiga, Aymaan yafita yabarta a motar yashige ciki Be dade ba sai gashi sun fito tareda Abbu Qarasowa sukayi wajen motar Hakan yasa zee fitowa suka gaisa da abbu yana tsokanarta kamar yadda yasaba. Saida suka dan jima ahakan sannan sukayi sallama da juna, Abbu yakoma ciki sukuma suka Kamo hanyar dawowa Tafiya suke cikin shiru babu mai magana sai waqar dake tashi a background din motar ahankali Can sai Aymaan yadan juyo ya kalleta sai kuma ya maida kallonshi akan titi "muje shopping?" Juyowa itama tayi ta kalleshi Daga mata girarenshi yayi sannan yayi murmushi yana sake maida hankalinshi akan titi "No" tafada ahankali "why? Bazamu dade ba ai, kawai zamu siya some stuffs ne saimu juya, ni akwai abubbuwan danake buqata ne nasan kema bazaki rasa ba" Shiru tayi kawai bata ce komai ba "I'll take your silent for yes" yafada tareda karya kan motar ya dauki corner da zata kaishi supermarket na kusa kusa. Parking yayi a parking space din supermarket din sannan ya fito ya zagayo ya bude mata itama ta fito Rufe motar yayi sannan suka nufi cikin shopping mall din atare. Zuwa yayi inda ake daukan shopping basket ya dauki biyu ya bata daya shima ya riqe dayan "zan shiga session din maza, idan kin rigani gamawa ki jirani anan" inji Aymaan Kada kai tayi kawai Hakan yasashi Juyawa ya wuce ya barta nan Ta dan jima a tsaye saikuma ta sauke Ajiyar zuciya sannan itama ta wuce session din mata Yan sayayya tayi wanda bata kai ta kawo ba wanda mostly turarrika ne masu kyau da tsada sai yan kayan maqulashe da ba'a rasaba. Ta rigashi gamawa shiyasa tazo ta tsaya inda yace din riqe da basket dinta tana jiran shi Wayarta dake jakkarta ta dauki ruri Hakan yasa ta ajiye basket din agabanta ta bude jakkar ta fiddo wayar _*sis batool* taga na yawo a screen din. Dan murmushi tayi sannan ta daga ta kara a kunne Dagowar da zatayi sai ta sauke idanunta akanshi Zuciyarta tayi wata muguwar wuntsilawa Wara manyan idanunta tayi sosai a kanshi kamar zasu fado daga socket dinsu "hello.. Hello" taji anayi a kunnenta amma ina? Batama san meye kare a kunnen nata ba, hankalinta ya tafi, ya tafi gabadaya Ahankali ta rintse idanunta ta bude amma still yana nan, tsaye hannunshi daya zube a aljihun wando daya riqe da waya yana daddanata wani na yimashi magana Kafeshi tayi da idanu kamar wata hallita take gani daban ba mutum ba irin ta Sanye yake da black american suit idanunshi toshe cikin da baqin shade, lallausar baqar sumarshi s gyare sai salqi take Ahankali taga yafara motsa bakinshi yana magana still kanshi hankalinshi akan wayar hannunshi saikuma ya dago ya kalli mutumin dake gefenshi yanata Kada kai cikin girmamawa ga dik abinda yace Wata maganar yasakeyi sannan ya amshi wata takarda a hannun mutumin ya duba ya miqa hannu baya, wani dake bayanshi shima sanye da suit yayi saurin bashi pen Dan rubutu yayi a takardar mai kama da file sannan ya rufe ya miqama mutumin Cikin russunawa mutumin ya amsa yanata washe baki yana qara russuna mashi yana magana wanda bazata iya jin abinda yake cewa ba daga inda take Sai gani tayi ya juya batareda yabi takan mutumin ba ya nufi hanyar waje cikin wani taku Hakan yasata dawowa firgigit daga duniyar kallonshi data lula Sakin wayar da haryanzu ke kare a kunnenta tayi batareda ta saniba "DEEN!!!" tafada da qarfi tana nufar shi da sauri "Zainab!" inji Aymaan da yakusan qarasowa inda take amma ina bataji ba hartayi gaba Saurin ida Qarasowa inda ta jefar da wayar yayi ya dauka saikuma shima yayo hanyar waje Fitowa zee tayi a gigice tafara waige waige cikin fitar hayyaci can ta hangeshi sun nufi wata mota waya kare a kunnenshi "DEEN!!!" ta qara qwalamashi kira sannan tayi wajen da sauri sauri gudu gudu. Bude mashi kofar baya akayi still yana making call Ahankali ya duqa zai shiga yaji an kamo mashi gefen suit dinshi da qarfi Dakatawa yayi daga yunqurin shigar dayayi batareda ya juyo ba Itama zee data damqo gefen rigar kallonshi take tana sauke numfashi mai nauyi Guards din wajen kau shock ya hanasu ta6uka komai sai tsayawa dasukayi suna kallonta baki bude "Deen??" tafada cikin wata iriyar karyayar murya Ahankali kamar wanda ake controlling da remote yashiga juyowa harya qarasa juyowa ya fuskanceta Kallon kallo suka shiga yima juna dukda shi nashi idanun na lullu6e da shade "Deen.." tasake fada cikin sarqewar murya tana jin numfashinta na qara yimata nauyi... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:40 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *058* *WHO IS WHO?* Ahankali yasa hannu ya cire shade din dake manne da idanunshi, oily eyes dinshi suka bayyana. Sauke idanunshi yayi kan hannunta dake riqeda gefen suit dinshi haryanzu sannan yasake Dagowa yana Binta da wani irin kallo Sosai kallon dayake binta dashi ya sake hautsina mata ciki hakan yasa batasan sadda tasaki rigar ba "Deen? Baka ganeni ba?" tafada tana kallonshi babu kyaftawa Kafin ya ko motsa Guards dinshi sukayo gaba zasu taso mata Daga masu hannu yayi, still idanunshi akan zee da itama takasa dauke nata akanshi, ba komai yasa Hakan ba sai irin kallon dayake binta dashi wanda bata ta6a sanin Deen dinta dashi ba Duk tsayawa sukayi Cak sanadin dakatar dasu da yayi Ahankali ya shiga zame suit dinshi na sama a qyamace still idanunshi cikin nata, ganin Hakan yasa wani guard dinshi Qarasowa bayanshi yana taimaka mashi har suka sa6ula rigar Batayi aune ba taji saukar rigar a fuskarta Wani masculine qamshi dake jikin rigar ya bugi hancinta Hakan yasa ta lumshe idanunta ta bude sannan tasa hannu ta Janye rigar daga fuskarta Ahankali Gani tayi ya juya yana niyyar shiga motar again Hakan yasa ta cafki hannunshi tana tsaida shi daga yunqurin shiga again "Deen.." tasake fada muryarta na rawa sosai Wani qololon abu ya tsaya mashi a wuya. How dare her! How dare her zata ta6ashi da wannan dirty hannun nata Juyowa yayi again yana mata kallon da yasata jin kamar ta narke don tsoro amma dukda Hakan taqi Sakin hannun "Deen? Meyasa kake min wannan kallon? Nice fa, zee.. Your Zainab" tafada cikin rawar murya sosai Cikin quluwa ya fizge hannunshi daga riqonta wanda Hakan yasa tadanyi loosing balance tayi kamar zata fadi Saidai bata fadin ba Sudai Guards dinshi nasu ido don tunda ya dakatar dasu dazu idan bashi yabasu umarnin yin wani abu ba bazasu yi gigin yin wani abin ba Juyawa yasakeyi zai shiga taqara Kamo hannunshi ido rufe "No Deen, please don't do this, don’t reject me for the second time, I can't take it, i'll die" tafada cikin kuka sosai hankalinta a matuqar tashe A matuqar fusace ya sake juyowa, beyi wata wata ba ya daga hannu da niyyar shararawa fuskar mari sai yaji an cafe hannun a iska da qarfi Zee data tamke idanunta gamm tana sauraron saukar marin taji shiru Hakan yasa ta bude idanun ahankali Aymaan tagani tsaye gefenta riqe da hannun Deen a iska suna bin juna da fierce kallon kallo Saurin qarasawa wajen Aymaan tayi "Aymaan ka kyaleshi, Deen ne fa, shine. Please ka sakeshi kar yayi fushi" tafada tana riqo hannun Aymaan daya riqe hannun Deen dashi Juyowa yayi ya kalleta cikin matuqar quluwa "zaki saki hannuna kosai na fasamaki baki?!" Yafada cikin qaraji, fuskarshi na bayyana tsantsar 6acin ran dayake ciki Sosai zee ta girgiza da yanayin Aymaan wanda bata ta6a saninshi dashi ba Amma so ya riga ya rufe mata ido Hakan yasa taqi saki "naji, ka fasamin kai ma idan ka tashi just leave him, ina ruwanka da rayuwata!!" itama tafada cikin daga murya Idanunshi dasukayi mugun kadawa ya kafeta dasu saikuma ya saki hannun Deen din ahankali Ganin Hakan yasata qara saurin nufar Deen din "Deen am sorry, besan ko waye kai ba, am very sorry" tafada tana niyyar sake kama hannunshi Hakan yasashi Janye hannun sannan ya turata baya a fusace Baya baya tasakeyi tana gasping don tasan wannan karon dole takai qasa kuma idan takai qasa saitaji jiki Jitayi an tareta ta baya an tsaidata daga faduwar A tsorace tasake bude idanun sai tayi arba da fuskar Aymaan dake kallonta da rinnanun idanunshi Bata iya cewa komai ba sai kallonshi itama datake numfashinta na qara yin nauyi Miqar da ita yayi tsaye sannan ya saketa yayi wajen Deen dake tsaye fuskarshi tayi jaa don fushi Guards ne sukayi saurin tareshi suna kakkama hannunshi Zuciyarshi ce ta qara harzuqa Hakan yasa ya wuntsilar dasu da iya qarfinshi duk suka sakeshi batareda sun shirya ba sukayi baya baya "you dog!" Yafada yana shaqo kwalar Deen qirjinshi sai sama da qasa yakeyi alamun zuciyar yan mazan ta tashi Bïñ hannun da Aymaan ya shaqi kwalarshi Deen yayi da kallo suprisingly sannan ya dago yana kallonshi shima jijjiyoyin jikinshi na tashi Cikin harshen larabci Aymaan yafara magana "waye kai?! Waye kai da zaka dora hannu akanta?!!" Afusace Deen yasa hannu ya kwa6ar da hannun Aymaan daga qwalar rigar tashi, kafin Aymaan yayi recovering daga haka yaji saukar naushi a gefen kumatunshi Qara Zee tasa tana kiran sunan Aymaan Baya baya Aymaan yayi saikuma ya dakatar da kanshi daga faduwar dayaso yi Hannu yasa ya taba gefen bakinshi ya duba sai yaga jini Sake kallon Deen dake huci yayi sai yayi kukan kura ya nufeshi Saidai tun kafin ya qarasa gunshi guards dinshi suka tareshi, basuyi wata wata ba suka tarar mashi suka shiga jibga. Qara Zee tasake saki tana rufe baki hankali a mugun tashe, kuka takeyi kamar zata shide jikinta na wani mugun 6ari Gaskiyar hausawa dasuka ce sarkin yawa yafi sarkin qarfi don tun Aymaan na iya maida martanin har yakoma kare kanshi har daga baya ma yakasa kare kanshi din. Ganin Hakan yasa zee nufar Deen dake tsaye yana kallonsu ta Kamo hannunshi "Deen na roqeqa, kace subari zasu kasheshi" Wani irin fizge hannunshi yayi wanda har Saida takai qasa Juyawa yayi zai wuce wajen motar shi tayi saurin rarumo qafarshi daya "Deen! No! Karka tafi zan mutu!" tafada tana rungume qafar da dukkan qarfinta A matuqar hasale ya fizge kafar itama yana ja baya yana kallonta da bloodshot idanunta sannan yana nuna ta da yatsarshi datake karkarwa saboda yadda jikinshi ke tsuma don 6acin rai Sai kuma ya juya ya bude kofar baya na motar ya bude wani akwati ido rufe ya fiffido wrappers din kudinsu nacan ya farka wrappers din yashiga watsamata kudadden ajiki, tsayawa tayi Cak da kukan tana kallon yadda yake warwatsa nata kudadden akai, da wani yaqare Sai ya farka wani har Saida ya qarar da wrappers biyar akanta "Go away, you brat!!" Yafada cikin hargowa sannan ya juya ya shige motar ya rufo da qarfi. Ganin Hakan yasa guards din kyale Aymaan da suka yima lilis suka rugo wajen mottocin suka shishiga suka tayar suka bar wajen a 360 suna badesu da qura Ahankali Aymaan ya bude idanunshi dasukayi mashi mugun nauyi yabi motocin dasuka fita a harabar wajen da kallo sannan ya maido kallonshi akan zee dake zaune har lokacin bata ko motsi Maida idanunshi yayi ya lumshe cikin azaba yana kiran sunan allah under his breath. Saida yayi yunqurin tashi sau biyu ya kasa, ana uku yasamu ya tashi zaune Dakyar yana cije lip dinshi na qasa Koina na jikinshi ciwo yakeyi kamar ana dandaqarsu ga bruises a jikinshi sunyi jaa abinka da fatar hutu dama Ahankali yasake bude ido ya sake kallon zee dake a sitting position dinta har lokacin Bude bakinshi yayi Dakyar yafara magana "kin gani.. Ko? Kinga.. Abinda kika jawo ko?" Shiru Shaqar numfashi yayi sannan ya fesar yafara yunqurin tashi, sosai jikinshi yayi laqwas don babu qarya ya jibgu don shi tunda yayi wayau bazai iya recalling lokacin da aka ta6a yimashi irin wannan dukan ba Ganin bazai iya tashin ba yasa ya qara Dagowa ya kalleta yaga still wuri guda take kallo sai jiyayi ranshi ya kuma 6aci "ki tashi mutafi" yafada yana kallonta but still bata motsa ba "Zainab! Am talking" Nanma shiru Shima shiru yayi ya tsaya yana kallonta yana qoqarin gano wani abu Abinka da medical doctor nan take ya gano Wara idanunshi dasuka tattaso yayi sannan yayi saurin rarrafawa gabanta "Zainab" yakira sunanta yana waving a gaban fuskarta amma bata ko kyafta idoba "zee?" yafada yana dan ta6ata kawai sai yaga tayi baya baya Ba don yayi saurin tarota ba da tasha qasa "Zainab! Zainab!!" Yafada yana jijjigata amma shiru Tara yatsarshi yayi a hancinta sannan ya dora kunnen shi daidai zuciyarta yana feeling heartbeat dinta A rikice ya dago ya karkata ya zaro wayar shi dake aljihunshi still tana jikinshi Lalubo number Ahmad yayi ya danna mashi kira Saida takusan katsewa sannan aka daga "hey!" inji Ahmad daga wancan bangaren "Ahmed kana ina?" "lafiya?" inji Ahmad jin muryar Aymaan wani iri "answer the damn question!" inji Aymaan yana qara jijjiga zee dake sheme ajikinshi "ina gida, meya faru naji voice dinka wani iri?" "kazo Ni'ima shopping mall, urgently please" Daga Hakan ya katse kiran ya maida hankalinshi kanta "Zainab! Zainab!! Wake up zee!" Yafada yana dan marin fuskarta amma shiru Waige waige yafara, kasancewar babu mutane sosai a wajen ga kuma motoci dayawa dasuka kakkaresu shiyasa tunma lokacin dasu Deen ke nan ba'a gansu ba. Ahankali ya maida ta ya kwantar daita sannan ya tashi Dakyar yafara dangyasawa ya fito fili Waige waige yafara can ya hangi securities, daya na bude gate daya na a zaune Da dingishi ya qarasa wajensu, tun daga nesa dasuka hangoshi suka fara kallonshi harya qaraso gabansu Dakyar I.D card dinshi yafara nunamasu, Ganin ko waye yasasu saurin tashi suna tambayarshi lfy suka ganshi haka Briefly yayi musu bayanin he's attacked By some thugs shi da sister shi dake can unconscious sannan ya gayamasu abinda yake buqata don yimata taimakon gaggawa. Cikin sa'a aka samu most abubbuwan daya lissafo suka koma wajen zee dake sheme har lokacin Dukda yadda yakejin kamar kanshi zai rabe gida biyu don sarawa haka ya daure yafara bata taimakon gaggawa Suna haka Ahmad ya iso supermarket din. Kasancewar Aymaan dama yariga ya fadamasu wani nanan tafe wajensu yasa yana isowa aka rakoshi wajensu Sosai hankalin Ahmad ya tashi ganin halin dayaga Aymaan dama zee dake unconscious har lokacin Cikin qarfin hali Aymaan yace ma Ahmad ya kaisu hospital Da taimakon Ahmad aka saka zee back seat sannan sukuma suka dawo gaban seat, Ahmad ya tada motar yayi reverse suka fice daga supermarket din. Asibitin da Aymaan ke aiki suka zarce. Tun kafin su iso Aymaan ya bugama wani colleague dinshi waya ya sanar dashi Zuwansu shiyasa Koda suka isa akayi saurin kar6ar zee aka shige daita Da farko Aymaan qin yarda yayi ayi treating ciwukkanshi har Saida ya tabbatar da sun ceto rayuwar Zainab from danger sannan Dakyar su Ahmad suka samu suka lalla6ashi ya yarda. *** Kwance yake bayan angama treating dinshi idanunshi a lumshe kamar mai barci amma ba barcin ba yake Shi kadai ne dakin don tunda nurse tagama treating dinshi suka fita suka bashi wuri don ya huta sosai Qarar bude kofa yaji amma Hakan besa ya bude lumssasun idanunshi ba "bismillah ummy" yaji Ahmad na cewa Hakan, Hakan yasashi bude idanun babu shiri ya juyo yana kallon saitin kofar Ummy yagani agaba sai batool a bayanta sai Abbu a bayansu Yunqurin tashi zaune yafara sai ummy tayi saurin Qarasowa tana taimaka mashi ya ida tashi zaune ta karamashi pillow a baya Dagowa yayi yana kallonsu sai yaga suma shi suke kallo cikin tausayawa "sannu Akhie" inji batool kamar zatayi kuka Dan murmushi yayi mata sannan ya kalli su ummy "ummy, waya gayamaku?" "Ahmad ne habiby, muna can hankalinmu Kwance ashe babu lafiya" Dagowa yayi ya watsama Ahmad mugun kallo shikuma yayi murmushi yana daga kafadarshi "sannu son, allah ya kyauta gaba amma nayi mammaki ace thugs a supermarket, how come?" Shiru Aymaan yadanyi sai kuma ya sauke Ajiyar zuciya "Abbu nidai bansan ya Hakan yafaru ba, kawai nagama siyayya ta nafuto saina hangeta inda nace ta jirani Amma kafin na qaraso sai naji qarar faduwar abu daga hannunta sai kuma naga tayi wajensu dagudu Na kwalamata kira amma bata saurareni ba shiyasa nima na qaraso wajen da sauri sai naga ashe wayarta ce ta saki Saina dauketa na tashi nabita lokacin harta fita waje Nima saina bita Saidai Koda nafita ban ganta ba don har titi saina nakai amma banga wulginta ba Dawowa nasake yi da niyyar komawa ciki again sainaji kamar magana a ta parking space din wajen Saina zagaya, kawai saina hangeta daidai wani ya tureta I thought faduwa zatayi amma sainaga bata fadi ba, sai nayi saurin nufar wajen Ina qarasawa wajen ya daga hannu zai mareta saina dakatar dashi..." Duk tsit mutanen dakin sukayi ya cigaba da basu labarin har kawo yanzu dasuke asibitin nan Duk salati suka shiga yi cikin tsantsar mammaki da alhini "innallilahi waina ilaihi rajiun, to shi mutumin waye? Kawai daga ganin mutum sai tace shine Deen? Haka fa tayi muku a park rannan ko?" Ajiyar zuciya kawai Aymaan ya sauke don shi kadai yasan abinda yakeji a zuciyarshi "to Gaskiya ya kamata nakira yaya na fadamashi, idan aka tafi Hakan akwai matsala, ace duk wanda tagani tace Deen ne, idan ta qara gamuwa da muggai kamar na yau fa babu wani dazai iya taimakonta a kusa fa?" "A'a, be kamata a kirasu ba, hankalinsu ne zai tashi sosai, kawai mu nemo mafita da kanmu" inji Abbu "nima Gaskiya am scared Abbu, gwara asan yadda za'ayi don nima abubbuwan datake yi sunfara bani tsoro, haka fa rannan ta dage akan ita dole shi tagani tasamu mukaita zagaye a banza" inji batool "kai, amma dai yaron nan ya cuceta wlh, cutar da dole sai allah ya sakamata, daga wannan sai wannan? Sai abu yayi kamar yafara warwarewa sai kuma yaqara ta6ar6arewa, kullum abu beci baya sai gaba?" inji ummy hawaye na taruwa a idanunta "Addu'a yakamata mu dinga tayata dashi Abbu, allah ya kawo mata rangwame a halin datake ciki" inji Ahmad da Tundazu bece komai ba Kada kai kawai duk sukayi cikin amincewa da Maganarshi Shidai Aymaan bece komai ba sai kafe waje guda dayayi da ido kawai, allah kadai yasan meke kai kawo a qwalwarshi Ranar aka sallamesu suka koma gida Zee ta farfado and she's ok physically amma karka bincika zuciyarta Zuciyar tata data samu ta lilliqeta da gum tun bayan rarratsata da Deen yayi tasake Fashewa, fasuwar da mawuyacine taqara iya yimata paci kamar yadda tayimata da farko Tun daga ranar ta chanza, chanzawar da tafi duk na baya Bata cin abinci sai an tsareta an tilasta mata to anan zataci kadan Kuma ko zaka yini kanta kana magana bazata cemaka komai ba har ka gaji don kanka ka kyaleta Daga baya kuma saita fara zazza6i, irin zazza6innan mai zafi sosai Dr Aymaan ne kullum mai treating dinta, yana iya qoqarin shi na ganin ya bata dukkanin kulawar datake buqata amma a banza, kullum cikin ciwo take ga wani bushewa datakeyi a tsaye Sosai wannan ahalin suka sake shiga damuwa mai tsanani Suna son su sanar dasu daddy na Nigeria amma Aymaan ya hana yana cewa it's not proper gwara suyi iya qoqarinsu akanta basai sun sanar dasu halin da ake ciki ba. Haka Aymaan dama sauran ahalin gidan sukaita iya bakin kokarinsu akanta Duk safiya bayan sallar asuba zasu shigo dakinsu zee din su zauna tilawar alqur'ani kowa da nashi a hannu itama a bata nata tana dubawa while su suna karantawa Sosai Hakan yayi tasiri sosai akanta don duk lokacin da suke wannan karatun takan tsinci kanta cikin nutsuwa, zuciyarta ta ragemata zugin data keyi Da rana kau wuni suke garden da batool wanda zataita iya qoqarinta wajen sanyata nishadi Da daddare kuma Aymaan zaizo ya fara karanta mata littatafai masu dadi masu sanya nishadi Haka sukaita iyakar bakin qoqarinsu akanta suna kuma hada mata da addu'a don tabbas lamarinnan sai an hada da addu'a Wata rana jikinta yasake tashi, zazza6i mai mugun zafi ya rufe ta. Ranar kowa na gidan beyi barcin kirki ba Haka suka tare wajenta Aymaan na iya bakin qoqarinshi akanta a matsayinshi na qwararren likita Dakyar suka samu jikin ya lafa tasamu barci drip maqale da hannunta Su ummy da batool sai dauke hawaye sukeyi akai akai shikuma Aymaan idanunshi sun Kada sosai, jiyake da shima zai iya kuka da yayi mata Haka yafita dakin ya barta dasu ummy da anan zasu kwana wajenta A ranar besamu rintsawa ba, haka ya zauna ya kafe waje guda da ido Tunanuka kala2 ke kai kawo akanshi Ko yatafi Nigeria neman Deen? Ko yaje a chanza mashi fuska irinta Deen? Me zaiyi? Me zaiyi dazai dauke ma zee abinda takeji? Shi da yasan yadda zai dauke mata abinda takeji a zuciya shiya dinga ji da yayi Hakan, daya jure kowanne irin wahalar da zaisha muddin zai dauke mata wahalar Yadda yaga rana haka yaga dare, asuba nayi ya miqe ya fice massalaci Koda ya dawo dakinsu yafara shiga ya tarar da har lokacin barci take Sake dubata yayi sannan ya cire mata qarin ruwan don yaqare sannan yafita A gaggauce yayi shirin asibiti ya fita don dama kwana biyu be cika zaman asibitin ba saboda tattara hankalinshi dayayi akan zee Yauma wani emergency aka kawo wanda lallai ana buqatarshi a aikin shiyasa ya shirya a gaggauce yayi sallama da mutanen gidan yatafi Bashi ya fito daga asibitin ba sai wajajen 3pm Hakan yasa ya wuce gida kawai don duk hankalinshi yayi gida kuma yanason yaje yaga wane hali zee din ke ciki Koda ya shigo gidan parking space yashiga yayi parking sannan ya fito Kamar kullum yau ma lapcoat dinshi riqe take a hannunshi ya fito ya rufe qofar sannan ya fito daga parking space din Hangen batool yayi ta fito daga garden tayi hanyar cikin gida batareda ta lura dashi ba Ganin Hakan ya tabbatar mashi cewa zee tana garden din itama don Mafi yawancin lokaci irin wannan can suke zama don sudan debe kewa. Hakan yasa ya chanza akalar tafiyar tashi zuwa garden din don dama babu wanda yakeson gani kamar ita yanzu Cikin takunshi ta nutsuwa ya taka zuwa garden din Tun daga nesa ya hangota zaune bisa wata yar doguwar kujerar garden din ta juya mashi baya so be ganin fuskarta itama kuma batasan da shigowarshi ba garden din Wasu yan moli moli take kallo dake tsaye a kan wani reshen bishiya suna dan tsuwarsu suna ra6ar juna _*look*_ Ta tuna abinda Deen yace wancan ranar da suka gansu a school _*A Good example of us, ko?*_ Lumshe idanu tayi akansu ta bude sannan ahankali tafara waqa _the word around town.._ _is that you're back in town_ _and I tried not to think about you_ _I tried_ _but it's been so long.._ _and I thought I moved on.._ _but now I really doubt it_ _I do_ _I wonder why you even come_ _it's almost like you're having fun with me_ _and though if I set my eyes on you, it's on avoidable_ _how come oh boy?_ _I thought you've gone for good_ _so how do you!.._ _have to pull me back!" _I thought you said, you won't be coming back_ _then why did you?!_ _this is really bad!_ _I thought you said you're gone for Good_ Dakatawa Aymaan yayi daga tafiyar dayakeyi yana kallonta cikin wani irin yanayi _what you did is wrong_ _cos you know all along am doing ok without you_ _you don't want me to.._ _try to move on.. Try oh_ _the heart is too strong_ _can't be with you and can't be without you_ _the truth is that I.._ _wonder why you even come_ _is almost that you're having fun with me_ _and though if I set my eyes on you, it's unavoidable_ _how come oh boy?_ _I thought you've gone for good_ _so why did you?!_ _have to pull me back?!_ _I thought you said, you won't be coming back_ _then why did you?_ _this is really bad!_ _I thought you said you're gone for Good_ Ahankali yafara takawa da baya baya still idanunshi akanta making sure be ankarar daita dashi ba Saida yayi nisa sannan ya juya yayi saurin barin garden din Saboda rufewar idanunshi baya ma ganin gabanshi clearly wanda Hakan yasa yaci karo da batool a bakin kofar shiga falo Daga mata hannu kawai yayi ya wuce don ga yadda yakeji dinnan yasan ko yayi maganar bazata fito ba Binshi da kallon mammaki batool tayi, kamar ta bishi sai kuma tafasa don wataqila 6ata mashi rai akayi kuma tasanshi idan yana cikin 6acin rai beson kowa ya ra6eshi, Hakan yasata juyowa kawai ta koma garden din. A daddafe Aymaan yasamu ya haye saman ya qarasa dakinshi ya bude yashiga ya maido ya rufe Jingina yayi da kofar ya saki lapcoat din hannunshi qasa yana sauke wani irin numfashi mai nauyi idanunshi a lumshe Kamar da wasa sai jiyayi wani abu na silalowa daga idanunshi zuwa kan kumatunshi Ahankali ya bude idanunshi sannan ya kai hannu ya dangwalo ya duba Hawaye? Kuka yake? Sake maida idanun yayi ya lumshe wasu nasake gangarowa. Jingina kanshi yayi da kofar yana maida lower lip dinshi aciki ya datse da haqora Besan iya lokacin daya dauka ba ahakan Saida yagaji da tsayuwar sannan ya dago daga kan kofar ya wuce wajen gadonshi ya zauna gefenshi ya dafe kanshi da hannaye bibbiyu yana kallon qasa Ya jima ahakan yanata saqa da warwara sannan ya Janye hannayen daga dafe kan dayayi ya karkata ya zaro farin hanki dinshi a aljihunshi na wando yashiga wiping fuskarshi Qara cije lip dinshi na qasa yayi yana kafe waje guda da idanunshi dasukayi ja sai kuma yasake karkatawa ya ciro wayar shi ya kunna ya lalubo number batool ya bugamata Ringing biyu aka daga "Akhie?" yaji tafada a can bangaren "ki riqe wayarki a hannunki zanyi miki sms, it's privacy" Be jira cewarta ba ya tsinke kiran Batool acan gefen jin ya katse mata hanzari ta hanyar kashe wayar ta sauke wayar cikin mammaki tana kallonta, itakau zee hankalinta ma ba kanta yake ba, tayi nisa as usual Ko minti biyu ba'ayi ba text message yashigo wayar tata Saurin budewa tayi sai taga yasa _*kisan yadda zakiyi ki dauki phone din Zainab ki kawomin yanzu, it's urgent*_ Shiru tayi tana qara karanta text din Me zaiyi da wayar zee kuma? Dagowa tayi ta kalli zee dake zaune har lokacin ta kafe waje guda da ido batama san me takeyi ba. Ba'ayi Mintuna uku ba yaji an kwankwasa mashi kofa Hakan yasashi saurin tashi kamar dama kan qaya yake ya nufi kofar Budewa yayi sai ga batool ta bayyana "yauwa, bani" yafada yana miqomata hannu "Akhie? Meya sameka?" tafada tana kallon yadda idanunshi sukayi jajur Be amsa mata ba sai jan hannunta dayayi suka shiga dakin ya rufo kofa "the phone" yafada cikin kosawa Dagota tayi ta gwadamashi Amsa yayi da sauri ya kunna yayi sliding sai yaga ta bude Direct contact yashiga yayi searching 'Deen' amma babu result saiya tuna ashe wannan sabon layine ma ashe don dama tunda tazo nan ta chanza layi irin na qasar Shiru yadanyi kamar mai tunani, Itadai batool Binshi kawai take da idanu Dagowa yasake yi ya kalleta "ta ta6a nuna miki hotonshi?" "wa?" "wannan mayaudarin" yafada kai tsaye Tasan wanda yake nufi don haka sai tace "eh, folder daya gareshi ma sunkutukum" Miqa mata phone din yayi "gwadamin shi" Amsa tayi ta shiga inda tashiga rannan nan da nan ta shiga cikin hotunan Daya tafara shiga sannan ta miqama Aymaan din dake kallonta hannaye rungume da qirji Amsa yayi ya juyo wayar sannan ya sauke idanunshi akan photon Idanunshi ne suka fara warawa akan hoton yana kallonshi a mammakince Ganin yana kallon hoton hankali a tashe yasa itama batool tazama so curious "Akhie, menene?" Dagowa yayi ya kalleta "Are you sure wannan gayen ne Deen?" yafada yana qara nunomata hoton Sake dubawa tayi itama sai ta Kada kai tace "eh Akhie, kaga nan a library din school dinsu ne.." Saita wuce ga wani hoton "wannan kuma ma a school ne.. Wannan kuma a garinsu mamansu zee din lokacin daurin auren nan na sister din mummyn, to shima yaje daurin auren, nan zaune suke dashi ta daukeshi" Aymaan sai baza idanu yake da kunnuwa yana sauraron batool Qara kallon hoton yake, ba fuskar kowa yake gani ba sai fuskar wannan gayen na supermarket Kenan ba haukan zee bane? Kenan dagaske wannan gayen Deen ne? Kenan ba gizo fuskarshi yake mata ba kamar yadda suka zata? Kenan Deen ne wannan gayen da yakusan marin zee? "unbelievable!!" Yafada in total shock "yaya wai menene? Ka sanshi ne?" inji confused batool Dagowa yayi ya kalleta saikuma yasake kallon hoton "shine" yafada yana kallon smiling face din Deen na cikin wayar "shine wa?" inji batool cikin rashin fahimta "shine gayen da muka gani a supermarket" yafada yana kallonta Wara idanu batool tayi in out most shock "mene?" "shine, kenan dagaske shine? Tabbas wannan fuskar ce, bazan ta6a mancewa ba. Kenan dama Deen ne wannan gayen?" "Are you kidding me Akhie? Kana nufin wannan gayen na cikin wayar nan kuka gani?" tafada zuciyarta na bugu sosai "shine batool, tabbas shine, ya sallam!" Yafada yana dafe goshi in confusion To kodai shima yafara zaucewan ne? Kodai shima idanunshi sun fara gayamashi qarya ne kamar dai zee? "but Akhie meya kawo Deen dubai?" inji batool cikin confusion Shiru yayi yana kafe hoton da idanu hoping zaiga fuskar ta chanza zuwa wani, hoping idanunshi ne ke mashi qarya "zanje na gayawa ummy, I can't believe this!" inji batool tayi hanyar waje Saurin dakatar daita yayi ta hanyar riqo hannunta Juyowa tayi ta kalleshi Girgiza mata kai yayi sai kuma ya sauke Ajiyar zuciya "No, ba yanzu ba. Karki sake ki fadawa kowa, zanyi confirming, kibari mu tabbatar sannan" Batool bataso Hakan ba Amma ya ta iya Wayarshi dake kan bedside locker ya dauko yashiga xender ya tura pics din Deen din biyu daga wayar zee din zuwa tashi sannan ya miqama batool din wayar "jeki, zanyi confirming and also karki bari kowa yaji wannan zancen kinji?" Kada mashi kai tayi sannan ta fita jiki a sanyaye Komawa yayi ya zauna yana tunani, be ta6a kawowa ranshi ya bincika ko dagaske wannan gayen Deen ne don shi duk a tunaninshi kawai haukace irin ta soyayya, to amma abin da kulle kai, Tunawa yayi da yadda ya daga hannu zai kifamata mari wanda da badon yayi saurin qarasawa wajen ba da babu abinda zai hanashi marin ta din, Tunawa yayi da kallon kyamar da yake Binta dashi, kamar ma beta6a sanin ta ba a duniyar nan Abin Tambayar anan shine dama can soyayya sukeyi koko dai ita ke sonshi tana liqemashi don shidai bega alamun so ko sannaya ba a qwayar idon wannan gayen ba Idan ma shine yaushe yazo dubai? Yaushe yayi kudi? Mutumin da ummy tace koko da kosai sukeyi for living, yaushe yayi kudi haka harda bodyguards? Hannu yasa yana scratching kanshi in confusion, kanshi a mugun kulle Batool ma dai kasa komawa daidai tayi tunda tafito daga dakin Aymaan She can't believe Deen din zee ne dagaske suka gani anan Daba Aymaan yafada ba da ta qaryata, meke faruwa to? Haka Itama ta qarashe wunin cikin tunanin wannan rudaden al'amarin. Aymaan da shirinshi yafito sallar isha'i Saida yafara biyawa dakinsu batool inda ya tadda zee zaune kan sallaya da alamun itama jiran afara kiran isha'i take tayi, batool kuma na linke wasu kayan su data Fiddo Jin batool na yiwa Aymaan sannu da zuwa yasa zee Dagowa Tsaye taganshi idanunshi akanta Sanye yake cikin lallausan milk din yadi mai kyau anyi kayan aikin dark brown A dan zaman nan datayi dasu ta lura Aymaan masoyin manyan kayane don yana sasu sosai kuma suna mashi kyau sosai suna sake fito da cikar kamalarshi Sauke idanunta tayi daga kanshi ta maida kan sallayar gabanta Ahankali ya qaraso wajenta ya tsugunna "patient" yafada yana kallonta yana murmushi Dagowa tayi ta kalleshi batareda tace komai ba "ya jiki?" yafada ahankali Kadamashi kai kawai tayi ahankali sai ta maida kanta qasa Binta da kallo ya cigaba dayi yana imagining pain dinta Na farko wanda take bala'in so ya karya mata zuciya ta hanyar gujemata batareda wani dalili ba Na biyu ta sake ganinshi amma kuma bata gabanshi sam Na uku mutanen daya kamata su fuskanceta wanda a wajensu zata dan ji sanyi sanyi suna mata kallon zautatta, basa yarda da duk abinda take cewa sai suyita mata kallon mahaukaciya wacce so ya haukata How painful is that? _very painful_ Ajiyar zuciya ya sauke yana maida lower lip dinshi aciki ya danne Tabbas shikuma yayi alqawarin kawo farinciki a rayuwarta, zai sake maido mata lost murmushinta a fuska, zaiyi koma menene don wanzar da farinciki a rayuwarta, saiya maida mata komai tarihi insha allah Dagowa yayi ya kalli batool yaga itama shi take kallo Dan murmushin gefen baki yayi saiya miqe tsaye "Allah ya sawwaqe, batool make sure tasha magani data ci abinci, zan fita" "insha allah Akhie allah ya tsare" inji batool Qara duqawa yayi wajen zee din "natafi dear" yafada ahankali Dagowa tayi ta kalleshi jin abinda ya kirata _Dear?_ Kada mashi kai tayi sannan ta bude baki ahankali tace "Allah ya kiyaye" Murmushi yayi mata "Amin dear" yafada sannan ya miqe tsaye yajuya ya fita Duk Binshi da kallo sukayi atare harya fice. Saida yayi sallama da ummy sannan yafice cikin motarshi Saida ya tsaya yafara yin sallar isha'i sannan ya wuce gidansu Ahmad don dama sunyi waya yace mashi yana gida Gidansu Ahmad shima babba ne don yafi nasu Aymaan ma don sunfisu kudi dama. Parking yayi sannan ya fito yana dan wurwura keys dinshi Saida yafara shiga suka gaisa da maman Ahmad din sannan ya fito yawuce part din Ahmad din don dama shi part dinshi daban a gidan Cikin fara'a suka gaisa "Dr! Dr!! Ganinka yanzu sai an cika form" inji Ahmad cikin tsokana Harararshi Aymaan yayi ya wuce wajen dan fridge din dakin ya bude ya ciro ruwan faro yakoma ya zauna yana cewa "lallai ma, har business man nada bakin yima doctor gori?" "ai wlh gwara mu daku, kufa har tsakar dare aiki kuke idan ta kama, mu fa?" "muma ai sai ta kama, kuma ai ba kodayaushe bane" "dukda Hakan dai kunfimu, haka matarka zataita fama, nidai batool dina ta huta don tun 6 na marece idan nadawo na rufe fita Saidai ko qila fita sallah" Pillon kujerar kusadashi Aymaan ya jefeshi dashi yana cewa "ko kunyata bakaji?" Karewa Ahmad yayi yana Dariya Kwafa kawai yayi ya chanza cigaba da shan ruwan hannunshi Saida yagama ya ajiye sannan yakoma jikin kujera yayi balancing "ya? Miye labari?" inji Ahmad dake qoqarin kunna t.v Dan shiru Aymaan yayi sai kuma ya dan karkata ya ciro Wayarshi ya shiga gallery yashiga hotunan Deen daya tura dazu saiya miqa mashi Amsa Ahmad yayi ya koma ya zauna ya kalla Wara idanu yaga yayi yana kallon hoton "ya dai?" inji Aymaan Kallonshi Ahmad yayi "dama gayen nan yasan kalmar murmushi? Unbelievable" Cikin rashin fahimta Aymaan yace "ban gane ba" "A'a mammaki nake kawai, ban ta6a sanin gayen nan yasan yadda ake murmushi ba, amma kalli nan ma Dariya yake, ina kasamu pics dinnan?" Cikin mammaki Aymaan yace "ka sanshi ne?" Wani kallon uku saura kwabo Ahmad yayi mashi "mene? Are you kidding me? Waye besan gayen nan ba? Kaima kasanshi Saidai ko kaqi saninshi a fuska amma ina ne sunanshi beyi trending ba?" Kan Aymaan yasake kullewa "waye shi din?" Gyara zama Ahmad yayi "kasan *NURUL HAQQ PLAZA*, *NURUL HAQQ PARK*, *NURUL HAQQ INVESTMENT*, *GIDAJEN MAN NURUL HAQQ*, *MAKARANTUN NURUL HAQQ* da asibitoci?" Kada kai Aymaan yayi don babu mahalukin dazai ce be sansu ba duk fadin Abu dhabi kai dubai din ma gabadaya, ko yaro ka tambaya yasani. Nuna Deen din cikin waya Ahmad yayi yace "to kaga mai su nan" Wani irin zaro idanu Aymaan yayi "what!!" Yafada shocked "Ca6! Wlh shine, idan kaji ana cewa _*MUSADDIQ AL-HASSAN*_ to wannan gayen ne" Qara zabura Aymaan yayi "what!!! Wannan din?!" Dariya Ahmad yayi ganin yadda ya rude yace "dole kayi mammaki ai, shi mutum ne da bakowa yasanshi ba saboda bai cika bayyana kanshi ba sai ire irenmu business man. Kana ganinshi haka business tycoon ne, qwaro a harkar business Sau daya na ta6a ganinshi face - face shima ranar Saida na raina kaina Ya wuce duk tunaninka wannan gayen, baya Dariya ko kadan, ni namayi mammakin ganin Dariyar shi anan don wlh cewa akeyi baya ko murmushi ashe yana yi mune bamu saniba" Zufa ne sosai ke keto ma Aymaan a goshi ya kafe Ahmad da kallo yanata zuba kamar kanya Saida yakai aya sannan yace "yanzu kana nufin park din NURUL HAQQ na wannan gayen ne?" "sosai ma, kaga duk zurfinshi da fadinshi dinnan shine mammalakinshi, Ca6! Multi-billionaire nefa wannan gayen, ya wuce duk tunaninka" Shiru Aymaan yayi yana kallonshi in shock Kenan park din dasuka je na wannan ne? Park din da zee tace taga Deen? Waye wannan gayen? Waye shi? Ahmad da duk be lura da halin da Aymaan ya shiga ba yace "amma kai ina kasamu pics dinnan, wlh sunyi kyau, dole natura na gwadama colleague dina nace masu to _*MUSADDIQ AL-HASSAN*_ dai na murmushi harda Dariya ma" yafada yana jawo Wayarshi zai tura "a wayar zee na tura" inji Aymaan yana kallonshi "really? Yo ita dataxo daga baya baya ina tasamu irin wannan pics din nashi?" inji Ahmad cikin mammaki "ita ta daukeshi" inji Aymaan Wani irin waro idanu Ahmad yayi "mene? Ita ta daukeshi? A ina?" "A Nigeria" Sake qwalalo idanu yayi "Nigeria?" "eh.. Wannan shine Deen dinta, her boyfriend" Wani irin zabura Ahmad yayi ya miqe tsaye "what!!" Shima Aymaan tashi tsayen yayi "yes, boyfriend dinta ne, wanda ya tafi ya barta a can Nigeria" "what!!!" Ahmad yasake fada in outmost shock... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:40 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *059* *WHO IS WHO ? 2* "I don’t get you" inji Ahmad yana kallon Aymaan unbelievably Ajiyar zuciya Aymaan shima ya sauke yakoma ya zauna yana cewa "nima am confused wlh" Dawowa Ahmad yayi ya zauna kusada shi yace "ina kasamu pics din?" "a wayar ta" "kuma saita cemaka shine Deen din?" "yes, batool ta gwadamawa itakuma ta gwadamin" "this is crazy! Yaushe sir Musaddiq yazama Deen?" inji Ahmad a mammakince Shiru Aymaan yayi duk kanshi ya kulle "idan da cewa kayi ta ganshi a Nigeria zan yarda don business babu inda bekai mutum amma batun shine Deen kwata2 qarya ce, babu yadda za'ayi Musaddiq yazama Deen" "kuma fa ummy cewa tayi koko da qosai sukayi for living a can Nigeria" Wara idanu Ahmad yayi sai kuma ya fashe da Dariya "kutt! Wlh you're very funny" yafada yana Dariya sosai don shi kawai hango sir Musaddiq yayi yana dama koko "mtcheew, kaifa wani sa'in banza ne, what's funny here?" inji Aymaan a qule "meye ma ba funny ba, sir Musaddiq dayin koko da qosai for living, hhhh idan ka bibiya ma besan meye kokon ba, kuma ya kamata kubar yarda da duk abinda yarinyar nan tace, she's heartbroken, tana iya ganin fuskar saurayin nata a fuskar kowa ma, ba Haka tayi ba a supermarket rannan? Tajamaka dukan tsiya" Cikin quluwa Aymaan yace "ai yanzu ma ba ita na tambaya ba, prove ne nagani a wayarta kuma gayen dakake cewa mun Hade a supermarket din ai shi dinne" "shi wa?" "na cikin wayar hannunka" ya amsa mashi kai tsaye "ban gane ba" inji Ahmad yana kallon Aymaan babu kyaftawa "mtcheew! Kar allah yasa ka gane mana, ai abinda yasa na yarda da zancen Zainab din kenan don the same guy na cikin wayar hannunka muka hadu dashi a supermarket din, Saidai abinda yafi kulle kai shine wannan da alamu he's rich don harda wasu kartin bodyguards" Qara qwalalo idanu Ahmad yayi "kana nufin dashi kukayi wannan fadan?" "yes?" yafada yana eyeing dinshi "Omg! Badai da sir Musaddiq kukayi fada ba" yafada in shock "look I don’t care koma sir wanene, all I knew shine yayi crossing limit dina kuma ni bana barin Hakan" Sakin baki Ahmad yayi ya cigaba da kallonshi in shock "wai meye Haka?"inji Aymaan da yaga kallon yayi yawa "you're unbelievable" inji Ahmad "so?" inji Aymaan yana daga kafadarshi in an I don’t care manner "wlh kabar daukar abin wasa, Musaddiq ya wuce duk tunaninka, I wonder ma yadda ya kyaleka a ranar be kulleka ba" Wani mugun kallo Aymaan ya antaya mashi "ya kulle wa? Ai wargi ma wuri gareshi, shi kanshi yasan ba sa'ar yina bane shi, nafi qarfinshi wlh" Ahmad tsayawa yayi yana kallon Aymaan cikin mammaki "Aymaan you're crazy, very crazy! Kai ban ta6a ganin crazy being ba irinka" "Sai yanzu kasani? Look let's drop that man's topic don tun gani na farko da nayi mashi naji na tsaneshi, let's get back to business" inji Aymaan wanda kallo daya zakayi mashi kagane he mean what he's saying Ajiyar zuciya Ahmad ya sauke yace "alright, ina jinka" Ajiyar zuciya Aymaan ya sauke "Deen.. Huhh! Inaji ana cewa sai mutum na zaman zamanshi cikin kwanciyar hankali.. boom!! sai problem din wani yataso yayi maka kane kane a rayuwa Da farko ban yarda da Hakan ba sai yanzu, yanzu banida wata matsalar data wuce ta zee, I don’t know but na tsani ganinta a yanayin datake aciki, na tsani gani pain a idanunta, ina kwadayin ganin farincikinta, ina kwadayin ganin fara'arta, I want her to live freely and happily kamar kowa amma Hakan ya gagara, kuma babu mai mata katanga da Hakan sai wannan gayen" Ajiyar zuciya Ahmad yayi yana qara kallon hoton Deen na cikin wayar "yanzu me kake so?" inji Ahmad "nima ban sani ba, bansan me zanyi ba, bansan ta yadda zan 6illowa komai ba, shiyasa nazo gurinka don neman shawara, gashi komai na neman qara cha6ewa" Qara kallon hoton Ahmad yayi sai yace "Allah mai iko, wallahil azeem haryanzu nakasa yarda wannan musaddiq bane, this is so confusing" "nima abin ya mugun dauremin kai, don wanda muka hadu dashi supermarket din is freaking rich, kaga kayan jikinshi? Kaga motocinshi? Lokacin datace shine Deen I thought she's out of her sense sai yau danaga pics dinnan sannan" "kai Aymaan, anya ba editing pics dinnan akayi ba, saifa kaga musaddiq din kodayake ka ganshi ai, ni sai naga akwai inda akasamu mistake" Amsar wayar Aymaan yayi ya qurawa pics din idanu shima "Ahmad this is real, duba kagani, dukda a pics ne kana ganin surrounding dinnan kasan ba qasarnan bace, bayan haka dubi kayan jikinshi, very cheap clothes, this is real" Shiru confused Ahmad yayi "to idan wannan ba musaddiq bane wanene? Meye alaqarshi da musaddiq har yayi mugun kama dashi?" "abinda yafi daure kai kenan Ahmad" Shiru Ahmad yayi kamar mai nazari can kuma yace "shi wannan waye iyayenshi?" "nima bansaniba, abu daya nasani shine talakawane kuma Nigerians ne, that's all" Shiru Ahmad ya sakeyi yana kallon pics din Deen daya kasa dauke idanunshi akai Yace "Gaskiya akwai rudani a wannan al'amarin, Indai dagaske mutanen nan biyu ne to akwai wani qullalen al'amari a tsakaninsu, haba kammanin yayi yawa, dole akwai wani abin da bamu sani ba" "nima haka nake tunani Ahmad, abin da matuqar kulle kai" Shiru yasake ratsa dakin kafin Ahmad ya dafa kafadar Aymaan "you know what? Abinda ya kamata muyi anan shine kowannensu mu binciko asalinsu da komai gameda rayuwarsu sai muyi comparing dinsu mugani" Kada kai Aymaan yayi "perfect, nima ina ganin Hakan zaifi" "yes, yanzu kai kaje kasamu zee din ta gayamaka komai gameda shi wannan din, nikuma zan samo mana komai gameda mussadiq" "perfect! Insha allah Hakan za'ayi, zan qoqarta nasamu dukkan bayaninshi a wajenta" Haka suka cigaba da shawarwarunsu har Saida Aymaan yaga dare nasonyi sosai sannan ya tashi suka fito sukayi sallama akan sai sun hadu, sannan yabar gidan Da wannan firar tasu Aymaan ya kwana a rai Haka maganar nan taita cinshi a rai a kingin kwanakin dasuka biyo baya, kodayaushe cikin son tunkarar zee da maganar yake amma be samun damar Hakan Ana haka har watarana yasamu opportunity din ganawar daita lokacin ya sauko qasa ne daga stairs ya taddata ita kadai zaune a dining Cikin jindadin Hakan ya tunkari dining room din yana jujjuya maganar dazai mata din. "aslm alaiki ya ukhtie" yafada yana jan kujera ya zauna Dagowa tayi daga abincin gabanta sai tadanyi yaqe "wlsm" tafada a taqaice "Me akeci ne babu ko tayi?" yafada yana dan leqa plate din Murmushi tasakeyi sannan ta tura mashi plate din tana cewa "bismillah" Turo mata plate din yayi shima yana cewa "alhamdullilah, am joking, kici ki qoshi ko kin qara qiba don naga Alamu batool wani Gani gani take mana kwanan nan, baki ga shiyasa nima na dage da cin abinci ba? Wannan yarinyar idan ta rainaka ka banu gwara kema ki dau mataki tun wuri" Murmushi tasakeyi kawai tana jinjina barkwanci irin na wannan ahalin, kusan dik haka suke, zaiyi wuya ka xauna dasu basu saka Dariya ba Shima dadi yaji, Ganin irin wannan murmushin a fuskarta ba qaramin sanyashi nishadi yake ba Cigaba da cin abincinta tayi slowly tana jin idanunshi akanta, bata dago ba Bata kuma nuna tasan yana yi ba har Saida tadan qaraci da dan yawa sannan ta tura plate din gefe ta dauki cup din ruwa tadanyi sipping ruwan sannan ta ajiye Dagowa tayi ta kamashi yana kallonta kamar yadda tayi zato Daga mata girarenshi yayi dan murmushi a lip dinshi Kauda kai tayi itama tana dan murmushi sannan taja kujerar ta baya tana niyyar tashi "badai har kin qoshi ba?" Kada mashi kai tayi tana ida tashi "erm.. Please sit, magana zamuyi.. Idan babu damuwa" yafada yana kallonta Dan Jimm tayi saikuma ta koma ta zauna tayi still tana saurarenshi Furzar da iska yayi ahankali daga bakinshi sannan ya gyara zamanshi looking very serious "Deen..." Dagowa tayi tana kallonshi yanayinta na chanzawa "I want to know everything about him" yafada yana kafeta da idanu kamar yadda itama ta kafeshi da nata Qara jan kujerarta tayi baya ta miqe tsaye Hakan yasa shima ya miqe "please Zainab, ki tsaya muyi wannan maganar tanada matuqar muhinmmanci" "agareka ba? Ni aguna batada, please spare me" tafada tana niyyar tafiya "Zainab Hakan nada matuqar muhinmmanci, shi zaisa abubbuwa da dama su warware mana, ciki harda asalin Deen" "ni nasan waye shi don haka bana buqatar sanin komai gameda shi again, for me Deen is as Good as dead" tafada cikin qunar zuciya "why? Meyasa zaki yanke wannan hukunci" "I don’t own anyone any explanation, banason labarinshi, kai ko sunanshi banason naji an ambata, labarinshi dana sani dinma da nasan yadda zan goge shi a qwalwata da tuni nayi Hakan" tafara yunqurin barin wurin "Koda kuwa ace bashi kika ganiba a supermarket?" maganar Aymaan ta dakatar da ita Dan murmushin takaici tayi sannan ta juyo ta kalleshi "dama ai ku baku ta6a yarda shi nake gani ba, kallon zauttaciya kuke min" Ahankali Aymaan ya tako har yazo gabanta "eh ada kallon zauttaciya nake maki, mai ganin fuskar saurayinta a fuskar kowa amma yanzu na fahimta, tabbas Deen ne kika gani, a park da supermarket Saidai bashi bane, kammaninsu ne daya amma bashi bane" Kallon rashin fahimta tayimashi "ban gane ba" "meyasa baki tambayi kanki tayaya Deen yazo dubai ba? Tayaya yazama mai kudi a lokaci guda? Baki lura da motarshi ba? Harda bodyguards? Tayaya yazama haka a lokaci daya?" Shiru tayi kawai tana kallonshi don ya soso mata inda ke mata kaikayi ne, wadannan Tambayoyin dasu take kwana take tashi a ranta. "wannan ba Deen bane, sunanshi MUSADDIQ AL HASSAN" "MUSADDIQ AL HASSAN?" inji zee cikin rashin fahimta Kada kai Aymaan yayi "yes, mu zauna na fadamaki komai" yafada yana nuna mata kujera Kamar bazata yi yadda yace din ba, saikuma ta tafi tajawo kujerar ta zauna tareda sunkuyar da kai abin tausayi Shima komawa yayi yaja kujerar daya zauna akai dazu ya zauna "Zainab, Deen qaddararki ne.." "nasani, mummunar qaddarata, am cursing the day I met him" ta katse shi da Hakan cikin muryar kuka Ajiyar zuciya Aymaan ya sauke cikin quncin rai shima yace "shiyasa nayi qoqarin taimaka miki da abinda zan iya don replacing Koda ba duka ba na farinciki dakika rasa a dalilinshi, nasan bazaki ta6a mantawa dashi ba so no need of making you forget him shiyasa nayi tunanin gano waye wannan Deen din dakuma nemoshi duk inda yake dukda ni kaina bansan abinda zanyi mashi ba ko abinda zai yimun. Sai nasa batool ta satomin wayarki don samun wani hint ko kadan ne akanshi Saidai Koda na duba babu number wayar shi a wayarki saima na tuna bada layin Nigeria kike amfani ba don haka saina chanza akalar binciken nawa zuwa ga Hotuna sai naji inason sanin kammanin wannan mutumin da sunanshi kawai nakeji har lokacin Abin mammaki da girgizarwa shine lokacin da nayi arba da fuskar mutumin da muka Hade a supermarket Honestly kafin lokacin kallon zauttaciya kawai nake miki ganin a park kin nuna kinga Deen a supermarket ma daga ganin mutum kince shine, ko ba niba ko wani ne haka zaiyi tunani don kowa yasan wanda ake magana akai a Nigeria yake, yaushe yazo dubai kuma karki manta duk bamusan kammaninshi ba" "Amma ganin wannan na cikin wayarki yasa kaina ya kulle, nace muddin wannan shine Deen to shine muka gani a supermarket Hakan yasa kaina yasake kullewa, meya kawo Deen dubai? Ganin kwalwata nason bursting saboda tunani saina yanke shawarar samun aboki kuma aminina da muka saba zama mu warware matsalolinmu atare wato Ahmad Saidai me? Ina gwadamashi pics din Deen saiya fara wata maganar daban mai matuqar rikita qwalwa..." Nan yashiga bata labarin yadda sukayi da Ahmad ranar be 6oyemata komai ba har kawo shawarar dasuka yanke don 6illowa matsalar Tunda yafara magana zee ta kafeshi da idanu tama kasa ko blinking Yayinda kwalwarta duk ta rikice itama "kana nufin ba Deen bane muka gani ba a supermarket, kana nufin bayan Deen akwai wani mai sak kammaninshi?" Ajiyar zuciya Aymaan ya sauke "bazan iya concluding ba yanzu sainaji waye Deen don tabbatar da hasashena... Zainab waye Deen? Su waye iyayenshi?" Girgiza kai zee tayi "bayada iyaye" tafada ahankali "kamar yaya?" inji Aymaan cikin rashin fahimta Goge hawayenta tayi da bayan hannu sannan tace "according to him wai duk sun rasu a hadarin mota, shi bema sansu ba don yana qarami a lokacin, kakarshi kawai ya bude ido yasani" Shiru Aymaan yayi yana lissafa magangganunta a qwalwarshi "to iyayen nashi wadanne tribe ne?" "wai hausawa ne" inji zee "ok, su kingin danginshi suna ina?" "kamar yadda nafada maka besan kowa nashi ba sai wannan kakar tashi, besan kowa ba sai ita" Cikin mammaki Aymaan yace "but how come? Tayaya za'ayi yaqi sanin danginshi? Ina yan uwan mahaifiyarshi da mahaifinshi?" "nima Hakan ya dade yana kulle min kai, koni nasha mammakin Hakan, kwata2 besan danginshi ba, daga shi sai kakar tashi ke rayuwarsu" Shiru Aymaan yayi yana kallonta na wani lokaci sai kuma ya sauke Ajiyar zuciya yana sauke idanunshi "then cikin dayan biyu ne" Maida hankalinta zee tayi sosai kanshi don jin abinda zaice "ko dai wannan kakar tashi na 6oyemashi wani abu gameda shi ne ko kuma shi ke 6oyemaki wani abu gameda shi" Cikin rashin fahimta tace "kamar yaya?" Dan cizon lower lip dinshi yayi yana kallon table din gabanshi sai kuma ya saki lip din ya kalleta yace "kodai kakarshi tana 6oyemashi wani abu na asalinshi ne ko kuma kawai yayi framing up story ne gareki" Gaban zee yafadi "kamar..ya?" tafada cikin rawar murya "tayiwu they are all fake, tayiwu ba kakarshi bace shima ba Deen din bane, tayiwu kawai framing story sukayi don Shigowa rayuwarki ya wargaza ya tafi. Cikin dayan biyu, ko dai dagaske bayan mussadiq al-hassan akwai Deen ko kuma mussadiq al-hassan shine Deen, yashigo rayuwarki ne da manufa yakuma fita bayan cikar burin shi" Saurin dafe zuciyarta zee tayi dataji kamar zata buga saboda wani mugun bugu datayi "No.. This can't be" tafada hankali a tashe Ganin yadda hankalinta ya tashi yasashi realizing mistake dinshi na fadamata Hakan kai tsaye bayan ga halin datake aciki "look zee, ni bance hakane ba, kawai hasashe ne kuma insha allah ba Haka bane" "kenan he did that purposely? Me nayi mashi dana cancanci Hakan" tafada cikin fitan hayyaci To fa, abu kadan ya girmama, duk inda hankalin Aymaan yakai Saida ya tashi ganin yadda zee ta burkuce lokaci guda, kuka kawai take cikin fitar hayyaci tana fadin metayi ma Deen dazai sakamata da Hakan. Nan take kingin mutanen gidan da basusan abinda ke faruwa ba suka sani, Aymaan yayi mugun danasanin fadin wannan maganar don besan zatayi affecting dinta haka ba don shi kawai hasashe yayi Koda su Abbu sukaji abinda ke faruwa sunyi mammaki sosai sunkuma dorawa Aymaan laifin tada mata hankali da furucinshi suna cewa be yakai shi fadin Hakan bayan yasan halin da dama take ciki Shidai kasa cewa komai yayi sai tarin nadamar data sauko mashi, da kyar dai aka samu aka kwantar mata da hankali akan tabari suji ta bakin Ahmad kafin su yanke hukunci Dakyar suka samu suka shawo kanta ta dan kwantar da hankalinta Hakan yasa Aymaan takurawa Ahmad da har lokacin be gama tara bayyanan Mussadiq al-hassan ba, kasancewar shi babban mutum kuma mai murdadden hali na rashin bayyana kanshi ko sirrinshi yasa tattara bayananshi yayi wahala don shi mutum ne da idan ba saninshi kayi ba baka ta6a sanin shine mai amsa sunan don be yarda da baza sirrinshi ba irin yadda sannanu keyi shiyasa wani lokacin harya shiga wuri yafita baza'a ta6a sanin dashi ba, gashi he's not a social media fan, baya komai sai whatsapp shima ba sosai ba don yana iya wata beyi ba, gashi baya pics ya watsa, idan kaga pics dinshi to daukarshi akayi bada saninshi ba don bayaso kwata2 Dakyar dai Ahmad yasamu ya tattara bayanai akanshi ya kira Aymaan ya sanar dashi Ranar da Ahmad zaizo gidansu Aymaan din da bayanan kowa Saida jininshi yazo kan akaifa musanmman Aymaan da oganniya zee Ita zee fargabar ta shine kar ace hasashen Aymaan yazamo Gaskiya shikuma fargabar shi tashin hankalin zee Sai bayan la'asar Ahmad ya diro gidan Ganinshi yasa gaban mutane da dama acikinsu faduwa A falo duk suka zauna aka gaisa sama kowa hankalinshi ba akwance ba Murmushi Ahmad yayi ganin Hakan saiya bude briefcase dinshi daya zo dashi ya Fiddo wani file ya dagoshi "to alhamdullilah, wannan file din yana qunshe ne da komai na Mussadiq al-hassan" Tsit falon yasake dauka kowa na kallon file din Hakan yasa ya bude shi yafara zazzaro takardun ciki ya barbaxasu a centre table din da aka maido gabansu Ahmad yafara da "sunan babanshi *AL-HASSAN* haifafen garin madina a qasar saudiya. Su biyar ne a family dinsu kamar yadda bayanin yazo yanada yayye biyu sai shi da twin dinshi *AL-HUSSAIN* Sai gambonsu wanda itace auta, duk ba'a kawo sunansu ba and I think it doesn't matter. Sunan mahaifiyarshi *ZAINAB BINT ABUBAKAR* haifaffiyar qasar Misra (egypt). Sunyi aure ne a shekarar 1*** Tareda AL-HUSSAIN shima da matarshi yar madina itama Ga hotunan su nan... Wannan shine Al-hassan.. Ga dan uwanshi Hussaini" yafada yana nuna masu hotunan "wannan kuma matar Al-hassan ce wato Zainab wannan kuma matar Al-hussain" Nan ma bin Hotunan sukayi da kallo inda nan take zee ta hango tsantsar kammanin Deen da matar Al-hassan wato Zainab bint Abubakar. "bayan shekaru biyar sa auren sai Zainab matar Al-hassan ta haihu, lokacin matar hussain haihuwarta biyu ma A lokacin ne Zainab ta haifo yan biyunta kyawawa, gasunan" Ya gwadamasu pics din jarirrai biyu cikin kayan sanyi dukda hoton yayi dishi dishi sosai "Ranar suna aka radawa yaran suna *MUSADDIQ* da *MUJAHEED*" "bayan haihuwarsu da shekara kusan hudu kuma sai aka haifi gambonsu mai suna *AYSHATUL HUMAIRA* a lokacin ma Al-hassan wato mahaifinsu Mussadiq be dade da rasuwa ba, itama ga hotonta nan datake yarinya dakuma yanzu data girma" yafada yana nunamusu hotuna biyu, daya na yar yarinya da batafi 3yrs ba na biyu kuma budurwa kamar dai sa'ar batool "Al-hassan dama dan kasuwane kuma babu laifi yanada arziqi bakin gwargwado, bayan rasuwarshi ne al-hussain ya riqe masu mussadiq dukiyarsu har mussadiq ya girma yayi karatu yakai munzalin amsar dukiyarsu sannan ya amsa yafara kasuwanci kamar dai babanshi, cikin ikon allah sai gashi allah yasama abin albarka har suka baro madina suka dawo nan dubai ya cigaba da kasuwancinshi har allah yakai shi a matakin dayake aciki yanzu" Tsit falon yayi bakajin qarar komai don tsab idan alura tafadi a wajen aji qararta kan kowannensu ya kulle gamm "to kunji gajeran labarin Mussadiq Al-hassan" inji Ahmad yana kallonsu Shiru dakin ya dauka sai can Aymaan yace "to twin din mussadiq fa? Mujaheed kace ko me? Ina yake? Ya akayi daga baya baka sanyo Maganarshi ba a labarin?" Duk Kada kai sukayi kingin mutanen dakin da alamun abinda ke ransu ya fada "ya rasu!" Qwalalo idanu dik sukayi suna kallonshi "ya rasu???" Duk suka hada baki wajen fadin Hakan Kada kai Ahmad yayi "eh, shekararsu uku uku, Mujaheed al-hassan ya rasu babu jimawa mahaifinsu wato al-hassan yabishi lokacin Zainab bint Abubakar nada matashin cikin Ayshatul Humaira" Kowa sai yakoma dumbfounded, kansu yaqara kullewa "ta..yaya ya mutu" inji zee cikin rawar murya Kallon zee Ahmad yayi yace "wannan ne haryanzu bamu saniba, nayi nayi nasamu information ko kadan ne akai amma babu duk hanyar danabi a toshe take, kawai dai ansan Mujaheed ya rasu amma ba'asan sila ma" Hankalin mutanen dakin yasake tashi Cikin rawar murya batool tace "k..kenan? D..Deen shine.. Mujaheed?" Kowa kallon Ahmad yake zuciyoyinsu na bugawa da qarfi Ahankali Ahmad ya kada kai "Tabbas! *DEEN* shine *MUJAHEED*".... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:40 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *060* *IN TROUBLE* _jiya bansamu posting ba don bansamu typing ba saboda baqin da nayi, kamar yadda nayi tunani kuna nan kuna cigiya sai naga cigiyar ma tafi yadda nayi tunani, wasu suna Deeeeen 🗣️🗣️🗣? wasu zeeeeeeee 🗣️🗣️🗣️🗣️ wasu Aymaaaaan 🗣️🗣️🗣️🗣️ amma anrasa mai cewa Ashaaaaanty 🗣️🗣️🗣️🗣️😕, babu komai nasan matsayina a wajenku 😞_ Dukkansu mutuwar zaune sukayi jin abinda Ahmad yace "yes, idan mukayi duba da tarihinsu inda Deen yatashi beda kowa besan kowa nashi ba sai wannan wanda yake kira kakarshi Hakan ya isa ya tabbatar da hasashenmu, tabbas Deen twin din mussadiq ne, shine wanda akace ya mutu lokacin da basu wuce shekaru uku uku ba, Saidai silar mutuwar da yadda akayi yaje Nigeria shine abu Mafi daure kai aciki, Tambayar anan itace wacece kaka? Meye alaqarta dashi? Tabbas ita kadai zatafi warware mana wannan qullin" "innallilahi waina ilaihi rajiun" Zainab tafada ahankali tana dafa goshi. She can't believe this, Deen.. Deen ashe ba Dan Nigeria bane? Deen ashe yanada uwa a duniya? Deen ashe yanada yan uwa? Deen twins ne? Nan da nan hawaye suka shiga sintiri a kumatunta abinka da ruwa ruwa dama _*banida kowa sai kaka, itama batada kowa sai ni. Nice duniyarta itace tawa*_ Wasu sabbin hawayen suka sake gangaromata tuna wannan maganar ta Deen datayi Itama batool hawayen take, abin dai kamar al'mara kamar a shirin film, wani irin tausayin Deen taji ya kamata, she's just imagining kanta ace tarabu da Ummy tun batasan kanta ba takuma rayu a wani wuri tareda wacce basuda alaqa kwata2 daita, a rabata da ummy, Abbu, dan uwanta dama family dinsu gabadaya, akaita wata duniya daban inda batasan kowa ba sai mai riqonta. This is touching, so touching. Shima Aymaan jikinshi yayi laqwass yayi sanyi, shi kanshi tausayin Deen ke dawainiya dashi, tunaninshi a yanzu shine ina yake? Ina kaka tasake kaishi? "Tabbas hakane, kaka kawai zata iya warware mana komai, amma ina take? Ina zamu nemeta a duniyar nan? Ni jikina na bani ita ta gudu dashi, wataqila gani tayi asirinta zai tonu wajen introduction din tunda basuda kowa kuma za'ayi bincike kuma taga Gaskiya na iya fitowa shiyasa ta gudu dashi" inji Abbu "nima haka nake tunani Abbu, tabbas akwai abinda kaka ke 6oyewa, wataqila saceshi tayi ta gudu dashi Nigeria, yanzu kuma ganin asirinta zai tonu saita qara guduwa" inji ummy "to amma abin daure kai anan ummy shine, meyasa akace mutuwa yayi? Meyasa ba'ace saceshi ba akayi? There's something fishy here" inji Aymaan "yes, nima ina wannan tunanin Aymaan, meyasa aka rufe details din mutuwar? Ya za'ayi mutum ya mutu shekara da shekaru kuma a ganshi a wata qasar? Definitely akwai wani qullalen al'amari tattare da wannan abin" inji Ahmad Shiru dakin ya sakeyi kowa yayi zurfi a tunani, kan kowa ya kulle tamau Can dai Ahmad yace "yanzu meye mafita?" yafada yana kallon dukkan mutanen dakin Dakin ya dauka sannan Abbu yace "kamar yadda kafada dazu dole mu nemo kaka, kaka ce kawai zata iya warware mana wannan chakwakiyar" "to amma Abbu ina zamu fara nemanta? Babu mammaki ma yanzu ta chanza qasa, qila bata Nigeria kwata2" inji ummy Duk Kada kai sukayi cikin gamsuwa da maganarta "ni a ganina kawai muje mu samesu, mufada musu cewa mujaheed be mutu ba yana Nigeria tareda wata, wataqila Hakan zai taimaka, suna iya ma taimakawa wajen ganota" inji batool Girgiza kai Ahmad yayi "idan baka iya kama 6arawo ba barawo saiya kamaka, tayaya zamu tunkaresu haka kai tsaye batareda wata hujjaba qwaqwara? Na farko babu Deen din kuma bamusan inda yake ba, Nabiyu babu kaka itama we can't tell inda take, gashi dama bamusan silar barin Deen din gidan ba, aiki kawai zamu 6allowa kanmu don karkiyi mammaki idan abin yajuye kanmu aka fara zarginmu akan komai" Kada kai duk sukayi cikin amuncewa da maganarshi shima Shiru dakin yasake dauka sannan can Aymaan yace "A ganina task biyu ke agabanmu yanzu Nafarko sanin Gaskiyar abinda yafaru da Deen koko nace mujaheed a wancan lokacin Nabiyu kuma nemansu kaka. Sanin ainahin abinda yafaru da Deen a wancan lokacin zai iya sauqaqa mana ko kuma yabamu haske akan abubbuwa da dama dake lullu6e agaremu, tunkararsu family din mussadiq a yanzu kamar yadda Ahmad yafada gangancine sosai, so samu musamu every proof and evidence kafin Hakan, amma Tambayar anan shine tayaya? Tayaya zamu iya samo information akan mutuwar tashi?" "da kamar wuya Aymaan, wadannan information din ma don bakusan baqar wuyar da akasha ba kafin asamosu, kwata2 gayen baya barin any space na bayyanar sirrinshi wanda ya shafeshi ko wanda yashafe rayuwar ahalinsu, wadannan ma mafi yawancinsu ta hanyar Aysha muka samesu, kaga abu ne mai matuqar wuya" Shiru dakin yasake dauka Zee ce ta dago ta kalli Ahmad, akaro na farko tun fara muhawararsu tace "kafada mana komai akan Aysha" Dan daga kafadu Ahmad yayi yace "well, kamar yadda nafada maku dazu Aysha itace gambonsu kuma autarsu, a halin yanzu tana gab da cika shekara 21, tana karatu ne a jami'ar ANNUR ISLAMIC UNIVERSITY inda zata shiga 300level bana, bayan Hakan kuma tanada bakeries da yayanta ya bude mata da sunanta inda take siyar da kayan snacks kala kala, I think that's all" inji Ahmad Shiru duk sukayi suna kallon zee da ga dukkan Alamu tayi zurfi a wani tunani nata ne "ANNUR ISLAMIC UNIVERSITY! Can nakeso ayi register dina" tafada tana kallonsu Dik kallon rashin fahimta sukayi mata "meyasa? Ba makarantarsu batool zaki shiga ba?" inji ummy "eh ummy, yanzu nafasa, zanje ANNUR din, anan zanyi accomplish din first mission dinmu na gano ainahin meya faru da Deen a shekarun baya ta hanyar shigema Aysha inda zan zama friend dinta if possible ma nazama aminiyarta, da Hakan zan samu na shiga jikinta sosai har nasamo mana information din da muke buqata" "No way! Tayaya zakiyi Hakan? What if suka ganoki? No Gaskiya bazai yiwuba" inji Aymaan Kallon Aymaan din tayi "haba Aymaan, it gonna be easy, kawai zanyi duk yadda zanyi ne nazama qawarta daga nan saina san yadda zanyi nasan komai, that's all, I will be very careful" "bazai yiwuba Zainab! Wannan abin yanada sauqin fada ne abaki amma wuya a aikace so kima bar maganar nan" inji Aymaan firmly "but..." "No but malama, that's final!" inji Aymaan cikin hade fuska Gani tayi yayi mata wani mugun kwarjini daya Hade fuskar Hakan yasa ta sauke idanunta hawaye na kawomata Ganin Hakan yasa ummy cewa "Amma Aymaan..." "ummy please, kema kinsan abinda take shirin yi is very dangerous, zamu samu wata hanyar mu cika mission dinmu but not this, please" Shiru duk suka sake yi Ahankali Zainab ta share hawayen dasuka digo mata sai ta tashi batareda ta kalli kowa ba "excuse me please" tafada sannan ta wuce Duk Binta da kallo sukayi harta haye sama Ajiyar zuciya duk suka sauke "Aymaan, meyasa kake son hanata bayan bamuda wani idea na 6illowa wannan al'amarin bayan nata?" "Ahmad this is very dangerous, tayaya xa'ayi muyi risking dinta akan wannan al'amarin?" "do we have any option other than that? Maganar risking kuma kamar yadda tace, we'll be very careful kuma allah yaga zuciyarmu yaga niyyar mu, bamuda niyyar cutar kowa saima taimako, ko don haka zai qaremu." Shiru Aymaan yayi da alamu maganar Ahmad tafara shigarshi Hakan yasa ya cigaba da cewa "bayan wannan hanyar ni bansan wane hanya zamubi ba Cikin sauqi mu cimma burinmu. Aysha itace the easiest way to our mission Bayan ita bansan wata hanyar ba don mussadiq kamar yadda nasha fadamaka ya wuce tunanin mai tunanin He's a very smart guy wanda yake amfani da qwalwa kuma qwalwarshi na ja sosai Ya wuce duk yadda zanyi maka bayani don haka bi ta hanyar shi is out of question don tsaf zai gano komai kafin muyi nisa So Aysha dinnan dai itace last hope dinmu kuma da ita zamuyi amfani muyi accomplish mission dinmu kuma babu ta sigar daya kamata aje mata kamar na wanda zee tafada, wannan is the easiest kuma ba za'ayi saurin zargin komai ba. Idan lafiyarta kakeji ka kwantar da hankalinka, inada mutane a school din don da taimakonsu nasamu wadannan informations din ma Zasu kulamana daita muma zamu kula daita, insha allah babu abinda zai faru sai alhairi" inji Ahmad in affirmation Shiru falon ya sakeyi kowa idonshi akan Aymaan dake jujjuya magangganun Ahmad a zuciya "Akhie don Allah ka yarda, mutumin nan yasha wuya, imagine shekaru 20 plus baka tareda ainahin iyayenka, baka tareda kowa naka, bakama sansu ba, how will you feel? Don Allah ka yarda Akhie, insha allah everything will go smoothly" Har lokacin Aymaan be dago ba kuma bece komai ba hakan yasa ummy itama saka baki "Aymaan Ahmad nada Gaskiya, we have no other way na cimma wannan burin namu na sada lost son da family dinshi sai wannan, kawai mu tayata da addu'a dakuma fatan nasara" Kada kai Abbu yayi "hakane Aymaan, let's give it a try, idan muka ga Hakan zai jawo wata matsala sai muyi quitting dinshi mu nemi wata hanyar" Shiru dakin yasake dauka kowa na kallon Aymaan din Jiyayi dik sun daureshi da jijiyoyyin jikinshi, yes yasan wannan hanyar itace the most easiest way na cimma burinsu amma ya rasa dalilin da yasa Hakan yaqi kwanta mashi, haka kawai yaji baya son taje school din Ajiyar zuciya ya sauke "alright, amma fa dole ne musaka mata ido kar mubarta ita Kadai don wannan abin is very risky, dole ne mu dinga bibiyar halin datake aciki don karta fada danger batareda saninmu ba" "yes, insha allah ai we're into this together, babu yadda za'ayi mubarta ita Kadai babu tsaro" inji Ahmad Kada kai sannan ahankali kamar beso yace "shikenan" Dadi duk suka ji, batool harda yar qarar murna "yauwa alhamdullilah, to allah ya bamu ikon gama komai sucessfully, Ya kamata a kira yan Nigeria a gayamasu ko?" inji ummy Saurin girgiza kai Aymaan yayi "A'a ummy, ni sai naga da kawai mun barsu for now har sai munfara shawo kan abin ko yaya kuka gani?" yafada yana kallonsu Ahmad Kada kai sukayi Ahmad yace "Gaskiya kam, kawai a kyalesu tunda ko afadamasu dai babu abinda zasuyi daga can kawai a kyalesu har mushawo kan al'amarin tukkuna" Duk Kada kai suka sakeyi, nan suka cigaba da yan shawarce shawarcensu atsakaninsu *ZEE* Tunda tashigo dakin ta haye kan gado ruff da ciki ta jawo pillow ta cusa kanta aciki tana cigaba da hawayenta Abin mammaki wai yau ita mutum kamar Aymaan ya hana abu kuma takasa musawa Abin yayi matuqar bata mammaki ne saboda sanin halinta datayi na idan taso abu babu mai taka mata burki ko ya hanata cikin sauqi Tunawa tayi yadda ada mummy kadai ke iya hanata ta hanu itama sai tasha wuya Yes don chanzawa tasan ta chanza amma batayi tunanin chanji harya kai mutum kamar Aymaan, mai irin shekarunshi wanda tsaf ta iya gayawa magana son ranta wai ya hanata abinda ranta keso kuma takasa musawa Meyasa? Meyasa takasa musawa? Meyasa takejin batason 6atamashi rai ta hanyar jan maganar dashi? Meyasa yana hada fuska takasa cewa komai kuma? _Respect_ Ta bawa kanta amsa Yes, Respect din datake mashi ne ya hanata Hakan Tun lokacin data fuskanceshi na yadda yakeda matuqar sauqin kai agareta, taga baya jin wuyar yin abu Domin faranta mata, kuma baya qaunar tashin hankalinta, tun lokacin taji yanada wani qima a idonta. Bayan haka a dalilinshi tasake ganin Deen kuma ta dalilinshi asalin Deen ya bayyana saboda yadda ya dauki problem dinta fiyeda yadda take jinshi, wannan kadai ya isa ta dinga ganin girmanshi har abada. Kuma tana iya haqura da komai itama ko don ta faranta mashi itama kamar yadda shima yasha sadaukar da abubbuwa don farincikinta Jitayi an bude kofar dakin ahankali an shigo Bata damu ta juyo ba don tayi tunanin batool ce amma jin dakin ya chanza da scent din turarenshi yasata saurin dagowa daga Kwancen datake ta juyo Ganinshi tayi jingine da kofa ya harde hannayenshi a qirji yana kallonta Hakan yasata kauda kai tana share hawayenta stylishly Dagowa yayi daga jinginen dayayi ya qaraso ahankali har gabanta Sauke idanunta tayi qasa tana kallon zoben yatsarta tana jujjuyashi ahankali Duqawa yayi ahankali gabanta making sure ya dan basu tazara a tsakaninsu sannan ya kafeta da idanu "Are you angry?" yafada ahankali Dagowa tayi ta kalleshi saikuma ta sauke idanunta qasa tana girgiza kai "you are" yafada still akanshi Qara girgiza kai tayi sannan ta dago ta kalleshi "am not, why will I?" "saboda na hanaki abinda kike so" yabata amsa Sake girgiza kai tayi tace "nasan wataqila Hakan ba alhairi bane agaremu shiyasa ka hana, don haka fushin me zanyi?" Murmushi yadanyi "amma ai fuskarki ta nuna fushin kikeyi, ga idanunki so wet alamun kinyi kuka" Sake saurin sa bayan hannunta tayi tana goge fuskarta tana cewa "Allah A'a, ni ba kuka ba nake" Murmushi yasake yi "ki gayawa wanda be sanki ba, cry cry baby kawai" Dan turo bakinta tayi tana Hade girarenta sannan ta kauda kai Murmushi yasake yi ganin Hakan sannan yace "I think zan bari kije din, allah yasa Hakan shiyafi alhairi" Saurin juyowa tayi ta kalleshi tana wara idanu saikuma ta kwa6e fuska "meyasa? Nidai A'a tunda bakaso nima banaso, allah ba fushi nake ba" Qara murmusawa yayi ganin sigar datayi maganar dashi a shagwa6e "nima ba don kinyi fushi ba yasa na amince, kawai nayi nazari ne naga Hakan zaifi" Dan Wara mashi idanu tayi "dagaske?" Kada mata kai yayi ahankali yana mata murmushi still "dagaske" Dadi taji Hakan kuma ya bayyana sosai a fuskarta "thank you so much" tafada cikin washe baki Dariya shima yayi ganin yadda take murna, haka kawai yaji he's proud of himself By making her happy "amma da sharadi" yafada yana kallonta Dan daga girarenta tayi saikuma tace "miye sharadin?" "da sharadin you'll have to be very careful kuma karki yi rushing abin By approaching her desperately, kawai kibi komai ahankali and muma zamu dinga kulawa iyakar yinmu" Dadi taqara ji "insha allah Akhie, zanyi yadda kace" tafada cikin jindadi Dan tsayawa yayi yana kallonta har tadan tsargu ta sauke idanunta qasa "Me kika kirani yanzu?" taji ya tambaya Kunya ce ta kamata Hakan yasa ta rufe fuskarta da taffukan hannunta "Allah saikin maimaita kokuma ni kadai nasan abinda zan miki" Turo bakinta tayi ta cikin taffukan hannun datasa ta rufe fuskarta "cewa nayi insha allah zanyi yadda kace" "nasan wannan ai, sunan da kika kirani nakeso ki maimaita" Qara tura baki tayi ta cikin taffukan "ba kaji ba?" "banji ba sosai ai" Qara Hade gira tayi sai kuma ahankali tace "Akhie.." saita qara rufe fuskarta Dariya yashiga yi sosai wanda Hakan yasa taqara jin kunya saita hada kanta da gwiwa ta cusa fuskarta a cinyarta Saida yayi mai isarshi sannan yace "very nice, yanzu na ida tabbatarwa inada qanne biyu, da alamu anyi accepting dina as yaya kenan, Happy me" Murmushi tayi fuskarta still a cinyarta "Good, bari natafi tunda tsabar ba'ason ganina har rufe fuska ake" Nan ma batace komai ba sai murmushin data sakeyi Tana jinshi ya miqe yayi mata sallama sannan yafita, sau a sannan ta dago kai tabi kofar daya rufo da kallo Dan ihun murna tayi takoma ta kwanta ta rungume pillow gamn cikin jindadi, ko babu komai zata samu kusanci da daya daga cikin yan uwan Deen wanda shi besamu damar yin Hakan ba Takuma quduri cewa insha allah, zatayi iyakar bakin qoqarinta na taimaka mashi wajen ida bayyanar asalinshi dukda he doesn't really deserve that, amma ta quduri anuyar rama sharri da alhairi ko don darajar soyayyar datake mashi wanda haryanzu batayi Koda gezau bane a Zuciyarta Gadan Gadan suka shiga aiwatar da shirinsu cikin tsari Dayake dama lokacin registration ne sai suka shiga nema mata admission a school din Da taimakon Ahmad da wadanda yasani a school din tasamu admission din dukda Saida sukaci kwakwa kuma sun kashe kudade sosai don ba qarya makarantar ta manya ne don sai dan wane da wane ke iya zuwanta Basuji komai ba wajen narkar da kudinsu a wajen samamata admission din ba Haka suka saki aljihu har suka samu sukayi clearing komai Nan fa aka shiga shiri gadan Gadan na resuming school, sosai sukeyin sayayya na school din musanmman kayan sakawa na fita school Batool kau wani sa'in har mita takeyi wai itama da ana transfer daga wata makarantar zuwa wata makarantar batareda an dawo baya a karatu ba da wlh sai anyi mata transfer, wai itama wlh Annur takeso Itadai zee Saidai tayimata Dariyar shaqiyanci tana cemata bakin alqallami ya bushe sai ta rungumi sorry Yayinda suke shurye shiryen resuming school din a gefe guda kuma sai qara bata hints ake akan Aysha ana fadamata abubbuwa dazasu amfaneta a tarrayarsu gameda ita dakuma shawarwaru na yadda zata 6illomata cikin sauqi Haka rannaku sukaita tafiya suna cigaba da shirye shiryensu na resuming school din ga Aymaan ya sakarmata aljihu sai siyayya take na school yadda taga dama a gefe daya kuma she's very eager sufara zuwa school din Yau ma sun fito zasuje shopping mall suje su ida sayayyarsu ta fama wanda da alamu be qarewa Dakyar ummy tabarsu suka fito don taga alamun siyayyarnan bata qarewa Saida sukayi ta gamata da allah suna cewa daga yau shikenan kafin ta kyalesu, suma abinda yasa suka fita din wata latest jakkace tafito mai mugun kyau sukaji idan basu yita ba hankalinsu bazai ta6a kwanciya ba shiyasa suka takura zasuje din don latest design ce bata dade da Shigowa ba. Haka suka fito cikin jindadin barinsu da akayi, batool tashiga mazaunin driver zee tashiga gefenta don har lokacin bata iya tuqiba, suka tada motar sukaja suka bar gidan Cikin harabar wani qayattacen mall sukayi parking. Bubbude koffofin motar sukayi sannan suka fito atare Rurrufewa sukayi batool ta dannama motar remote sannan ta zagayo ta bangaren zee suka nufi hanyar kofar mall din suna tafe suna firarsu Koda suka shiga ciki dan qaramin basket suka dauka sannan suka nufi 6angaren bags and shoes. Layi layin bags din suke bi don neman irin design din dasuke so Saidai babu ita gashi kuma a magazine the shopping mall din sukaga jakkar harta burgesu Sake dawowa baya sukayi suna bin jakkukunan daya bayan daya da kallo wai ko qila dazu sun wuceta basu saniba saidai har suka gama babu ita Riqe qugu batool tayi "to? Sunsan basuda ita sukasa hoton a magazine? Wannan ai wulaqanci ne" "hmm I wonder too sister, gashi dai duk munbi layikan jakkukunan babu mai kama daita" "kutt! Aikau bazamuyi fitowar banza ba, bari naje nayi masu magana" inji batool "kice masu me?" "gwadamasu hoton jakkar zanyi ai gashi nan allah yaso da magazine din nazo, sai nace ita nakeso wataqila akwai basu fiddota bane" Kada kai zee tayi tana ta6e baki "to saikin dawo" Har batool zata tafi wayarta tafara ringing. Dakatawa tayi ta zaro wayar ta duba "wayyo" tafada ahankali "menene?" inji zee "kirana ake wlh, please ukhtie ko zakije kiyi musu complain din ni nasamu na daga wayar?" Wani kallon uku saura kwabo zee tayi mata "ki mutu baki Daga ba" tafada tana kauda kai "haba ukhtie, please please 👏 kinga kirana akeyi ki taimaka" "shi mai kiran naki bazai iya jiraba kigama abinda kikeyi ba? Just tell him you're busy or better still kigama wayar saiki tafi, nikam babu inda zani" Cigaba da roqonta tayi akan ta taimaka taje har Saida tasamu dakyar ta yarda don batool idan ta nacema abu to saita samu Fizge magazine din hannun batool din tayi ta gallamata harara sannan tawuce Dariya batool tayi tana cewa "eh babu komai" sannan ta maida hankalinta a wayar hannunta Cikin jin haushi zee ta taho wajen inda ake biyan kudin kaya idan ka siya Complain tayi cikin harshen turanci akan sunzo sayan jakka amma babu irin wanda suka gani a magazine din Dubawa mutumin yayi saikuma ya dauki telephone yayi kira Batasan me yake Cewa ba don da larabci suke maganar Saida yagama sannan ya ajiye wayar yajuyo gareta Farawa yayi da bata haquri akan Hakan sannan yace tana iya zuwa sama tayima Manager magana yace akwai jakkar saukota ne ba'akai dayi ba Kwatancen hanyar dazatabi yayi mata tayi mashi Godiya tabar wajen. Inda yace zatabi tabi tana tafiya ahankali Shopping mall din babbane mai hanyoyi daban daban wanda Indai kai baqon wajen ne nan da nan zaka 6ace Hakan take ga zee, sai gashi tayi missing Kwatancen dayayi mata tabi wata hanyar daban Haka taita tafiya tun batasan ta 6ace ba harta gane ta sa6a hanya. Dawowa tayi ta inda ta biyo don ganin ko zata gane Saidai idan tabi wani passage da inda zai 6illa daita, sai ta zama very confused tama kasa gano hanyar komawa inda tafito Wayarta ce tazaro ta lalubo number batool ta danna mata kira amma wai busy Haushi taji taja wani gajeren tsaki ta cigaba da tafiyar amma still takasa gano hanyar Sake dannama batool kira tayi yanzu ma busy sai taji ranta ya 6aci sosai Wannan wane irin wulaqanci ne? Dukda she's busy ai tasan dole taga kiran nata meyasa bazata daga ba atleast taji ko me zata fada? Maida wayar tayi cikin jakka ta cigaba da tafiya ranta na suya taga wani passage kamar ta wuce saikuma tabi ta passage din tana addu'ar allah yasa ta gane ita Koda waje ne hanyar ta fiddata Wurin is so silent and she wonder why Ahankali tashiga bin passage din tana dan waiwaigawa har tazo tawuce wata kofa Cak ta dakata daga tafiyar data keyi tadawo ahankali kamar mai sanda daidai wajen kofar Kofar normal koface amma akwai glass siriri daga tsakiyarta inda ana iya hangen na ciki tanan Ahankali ta la6e ta inda ba glass bane sannan ta sunkuyo ta leqo ta glass din Tsaye yake amma yajuyama kofar baya waya kare da kunnenshi Kallon bayanshi take tana wondering wanene? Sai wata zuciyar tabata shawarar ta bubbuga mashi tagayamashi 6acewa yayi qila ya iya fiddata Da wannan shawarar tazo miqewa daga leqen datake yimashi shikuma daidai ya juyo fuskarshi yana facing din kofar Wara manyan idanunta tayi akan fuskarshi sai tayi saurin rufe bakinta don hana ihun datayi niyyar yi fitowa Shine! Deen! No, Mussadiq! Rufe bakinta tayi gamm takoma gefe tana sauke numfashi, Tabbas mussadiq ne, me yakeyi anan? Ahankali tasake duqowa don ta leqa saita hango ya nufo kofar Hakan yasata saurin tashi tashige yar kusurwar dake kusada ita ta mannema bangon wajen jiki na 6ari Jitayi an bude kofar an fito an maida an rufe Riqe numfashinta tayi tana jin yadda zuciyarta ke bugawa kamar zata faso qirjinta Luckily maimakon yayo bangarenta sai yayi wancan 6angaren yashiga tafiya don barin wajen yana cigaba da wayarshi Jin takunshi yadanyi nisa daita yasa tadan leqo saita hangi bayanshi yayi nisa sai Maganarshi datakeji faintly Batasan yaya akayi ba sai kawai ta tsinci kanta da Binshi a baya cikin sand'a da bin bango Da taga alamun zai juyo saita la6e a jikin bango kuma gashi tabashi tazara sosai babu yadda za'ayi ya lura daita Wata kwana yasha ganin Hakan yasa tayi saurin Qarasowa daidai kwanar don karya 6ace mata, tana kawowa ta hangeshi yana qoqarin shan wata guntuwar kwanar Takalminta ta cire ta riqe a hannu saboda tsaro don suna dan making sound idan tana tafiya. Haka taita Binshi a baya cikin sand'a, duk inda yayi saitabi tana making extra sure be lura daita ba. abin mammaki saigashi duk kwanonin dasuke sha har lokacin ba sukai inda zaya ba, sunsha kwana tafi goma don tun tana qilga harta manta da qilgar Wata kwana yasha itama tabishi cikin sand'a feeling exhausted Tanashan kwanar itama ta nemeshi ta rasa Hanhangawa tayi amma bata ga ko wulginshi ba ga passage din da mugun tsawo be isa ya shanyeta ba A tsorace tafara biyo passage din tana waige waigen inda zata hangoshi Daidai tazo tsakiyar passage din babu zato taji an chafki hannunta From nowhere an jata wani lungu A mugun gigice ta bude baki zata fasa qara taji an dademata baki an kuma mannamata wani abu a gefen ciki "if you move, I'll shoot" taji anfada cikin husky voice ana qara mannamata abinda yanzu tagane bindiga ce a gefen ciki... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:40 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *061* *MUSSADIQ AL-HASSAN* _Godiya agareku yan Deen fans group ❤️_ _nagode qwarai da addu'o'inku, allah ya saka da alhairi ya bar zuminci 🤲🏻_ _Manage this, da babu gwara babu yawa_ Still tayi tana jin numfashinta na neman daukewa Mutumin na bayanta hannunshi daya still dade da bakinta dayan kuma riqe da bindigar daya saita mata a gefen ciki Wani masculine qamshi ke fita daga soft hannunshi dake dade da bakinta yana dakarmata koffofin hanci Rarraba idanu takeyi babu damar ihu The thought of wai bindiga ce a gefen cikinta kadai yasata jin tanason suma amma suman yaqi zuwa, sai yanzu tagane ashe idan aka suma tashin hankalin bekai tashin hankali ba "who are you?" taji cool husky voice din directly a kunnenta kasancewar dama bakinshi nada kusanci da kunnen Kasa amsawa tayi saboda dademata baki dayayi Hakan yasata cigaba da raba idanu zuciyarta na qara racing "Speak!!" Yafada da qarfi at the same time yana qara turamata bakin bindigar a kwarin ciki Jikinta yaqara daukar kyarma tanajin kamar tasaki fitsari a tsaye Mumbling tafara yi cikin tafin hannun dake dade da bakinta hawaye na kawo mata "Your hands up, up!!" Babu shiri ta daga hannayenta sama jiki na 6ari "if you move, I'll shoot" yaqara fada in a very serious tone Tamke idanunta tayi gam tanajin wane tsotsai ma yasata fita yau? Ahankali taji yafara dauke hannunshi a bakinta takuma ji yafara raba jikinshi da nata Hakan yasata bude idanunta "I repeat, if you move, I'll burst your brain, try me" yafada daringly Daga jin tone dinshi tasa zai aikata shima shiyasa ta maida idanun ta rufe tayi still harya ida Sakinta yayi saurin zagayowa gabanta yana aiming dinta da qaramar bindigar hannunta Kallonta ya tsaya yi still bindigar na nunata "Open your eyes!" Yafada da qarfi Hakan yasa tayi saurin bude idanunta dasuka kawo ruwa ta kalleshi Zuciyarta ce ta buga sosai sanadin arba datayi da fuskarshi Deen No mussadiq A zahiri ba Deen bane amma agareta kamar Deen ne a gabanta Komai da komai irin na Deen dinta, oily idanun, pointed nose din, pink lips din, komai Kamar harta 6aci kawai banbancin shine tunda take da Deen bata ta6a ganin yasha kunu kamar yadda na gabanta keyi ba yanzu, kodayaushe fuskarshi a washe take Koda ba murmushi ba yake, haka allah yayishi da very friendly face "who are you?" yafada murya a kausashe still yana nunata da bindigar Bude baki tayi tana son yin magana amma maganar taqi fitowa "speak! Man anti??!" Yafada cikin tsawa again yana Binta da wani mugun kallo mai tsoratarwa "D.. Dan allah kayi hqr, ni..." "shut up! Use English language or Arab, speak!" Yafada again yana kai dan yatsarshi wajen kunamar bindigar Cikin harshen turanci tashiga cewa "Am sorry, 6atan hanya nayi, am sorry" Shima cikin turanci yace "yimin shiru! Ke yar leqen asiri ce ko? Waya aikoki? Zakiyi magana ko saina tarwatsa kanki da wannan bindigar?!" Yafada yana sake yi kamar zai danna kunamar Wara idanu zee tayi jin ya kirata da yar leqen asiri "No, wlh tlh 6atan hanya nayi, cashier ne yayi directing dina nan yace na nazo office din Manager saina 6ace, wlh am not a spy" tafada tana jin kamar ta narke don tsoro "shut up! Kin 6ace shine kike leqen mutane ta kofa? Kuma nafito kike bina a baya kamar 6arauniya, da 6acewa kikayi fitowa Zakiyi ki tambayeni na nuna miki hanya amma sai kikaita bina idan nayi kamar zan juyo sai kiyi saurin la6ewa, gayamin wacce ta 6ace haka ya kamata tayi!!" Wara idanu tayi kawai da dropped jaw tana kallonshi Dama duk yana sane da ita tun lokacin datake leqen shi? Shikenan takawo kanta "zaki fadamin wadanda suka aikoki din ko saina tsiyayar miki da kwalwa din?!" yasake dakamata tsawa Baki na rawa tafara motsashi zatayi magana saiya katseta da "ni kamar ma nasan fuskar nan" yafada yana qure ta da oily eyes dinshi Jitayi cikin ta ya Murda, shikenan dama ajalinta ya kawota nan "fadamin, ina na ta6a ganinki?" yafada yana qara saita ta da bindigar Saurin girgiza kai tayi a rude "babu.. Babu" Shiru yadanyi yana kallonta kamar mai son tunano wani abu can kuma saiya daga cikkaken girarshi daya "yes, the beggar" Itama kallon rashin fahimta tayi mashi fuska sha6e2 da hawayen da tuntuni tafarasu "the beggar?" itama tafada cikin rashin fahimta "yes, kece almajirar dakikayi attacking dina keda wani mahaukaci a supermarket ko? Tun lokacin ya kamata nasan ke yar leqen asiri ce" "ni ba almajira bace kuma ba yar leqen asiri bace" tafada cikin qunar zuciya "Zakiyi min shiru kosaina alburusheki!" Yafada yana qara saitata "speak up, wa kike ma aiki" Wasu hawayen suka sake zubomata, tunda take bata ta6a ganin an saita wani da bindiga ba bare ita, jitake kamar ta sume musanmman idan ta kalli dan yatsarshi dake bisa kunamar bindigar, mistake daya idan akayi ya Latsa kunamar Saidai wata ba ita ba "don Allah kabar nunani da bindigar, ni bansan komai ba" Kamar cewa tayi ya qara nunata da bindigar saiya qara saitata yace "ba nunaki da bindiga ba, har harsashe saina sa na huda kanki idan bakiyi co-operating ba" "ni na fadamaka bakin Gaskiya ta, ni ba yar leqen asiri bace, 6acewa nayi" tafada cikin kuka "then?" yafada yana mata kallon tama rainashi "then saina ganka... Saina... Saina..." "Sai kika yanke shawarar bina a baya cikin sanda har na fiddaki ko?" yafada yana mata kallon sheqeqe Saurin Kada kai tayi "Eh.. Eh hakane" "saiki bari saikin samu gara sannan Kiyi mashi irin wannan karatun, wadanda suka turoki basu gayamaki ko ni wanene ba? Kodayake ba lallai bane idan su kansu sun sanni bare susan hadari na, da kinsan hadarina da tun farko baki yarda kin amshi wannan aikin na bibbiyata ba, dakuma kinsan hadari na da nan take zaki fadamin wadanda suka aikoki batareda gargada ba, amma tunda Kin za6i kiyi taurin kai, fine. Now say goodbye to the world" yafada yana sake dora yatsarshi bisa kunamar bindigar Ahankali zee ta rufe idanunta tana numfashi sama sama, shikenan dama ashe yau zata mutu, ashe dama ajalinta ke kiranta Ringing din da wayarta ta dauka yasata sake tamke idanu don tayi tunanin qarar bindigar ce, jin ba taji komai ba yasa ta bude idanu ahankali ta kalleshi taga jakkar kafadarta yake kallo "Don't move!" Yafada a tsawace saikuma ya sa hannu ya fizge jakkar daga kafadarta With one hand still aiming at her yasa dayan hannun ya zuge zip din jakkar ya zazzageta a qasa Lokacin har kiran ya tsinke Still aiming at her ya duqa yana sa dayan free hannun yana barbaza kayan daya watsar qasa don son samun abu Koda daya ne dazai samu glue akan cewa bibiyarshi din take Besamu ba don banda kudadden dake ciki sai waya Sake kira akayi Hakan yasashi daukar wayar ya miqe tsaye still pointing the gun at her Duba screen din yayi yaga ansa *B sis* Juya screen din yayi a fuskarta yadda zata gani sannan yace "who?" Ganin sunan Batool a screen din wayar yasata jin dadi, atleast qila ta ceceta daga wannan beast din, Is he a beast? Yes, a handsome arab beast "who!!" yasake fada wannan karon a tsawace "Batool.. She's my sister tare mukazo nan" tafada da sauri Duk maganar dasuke da turanci ne don mussadiq bayajin hausa, turancin ma nashi mai irin slang din larabawa ne Daga kiran yayi yasa hands free "oh my lovely ukhtie don Allah Kiyi hqr, wlh naga kiranki amma lokacin muna tsakiya da magana mai muhinmmancine,Kiyi hqr. yanzu kina ina nazo wajen cashier yace Tundazu yayi directing dinki wajen manager naje kuma bakya nan, badai tafiya kikayi ba?" Shiru zee tayi takasa amsawa sai rarraba idanun datake tsakanin wayar da mussadiq daya kasa kunne yana sauraron batool attentively kamar yasan abinda take cewa "hello? Hello zee? Kinaji?" Dagowa mussadiq yayi ya kalleta sannan ya katse kiran "wacece?" yafada yana kallonta "my sister, tare mukazo, nemana take" "tare kukazo leqen asirin?" Qara dan wara idanu tayi "A'a, bakaji tace tanata nemana ba har wajen cashier?" "banji ba, banajin jagwalgwalon yarenku so ban yarda ba, sai nayi confirming" yafada yana saka hannunshi a aljihu dayan hannun har lokacin yana sai tata da bindigar Yan danne danne yayi a wayar ya kara a kunne ya dago yana kallonta Daga wayar akayi daga can 6angaren Bataji me akace ba sai jitayi yafara magana cikin harshen larabci wanda itama bata ganewa saboda dan larabcin data iya bekai ya kawo ba dukda duk tadan qara sanin wasu a zaman datayi a dubai din Magana yake da nakan wayar amma idanunshi na akanta yana yawo dasu a fuskarta kamar mai neman wani abu Saitaji ta takura da kallon taji kamar idanun nashi na piercing cikin hudojjin fuskarta Hakan yasa ta sauke nata idanun tana sauraron maganar dayakeyi "meye sunanki?" taji ya fada cikin muryar da sak ta Deen, banbancin kawai wannan tanada dan kaushi ta Deen kuma tafi taushi "Zainab" tafada ahankali Jimm yayi yana kallonta jin sunan data ambata sai kuma ya cigaba da magana a wayar taji ya sako sunanta cikin Maganarshi Saida suka qara exchanging few words a wayar sannan ya katse kiran sannan to her outmost relieve taga ya sauke bindigar hannunshi daga nunata daita dayakeyi Wata iriyar nannauyar Ajiyar zuciya ta sauke har tana lumshe idanu ganin at last yabar nunata da bindigar "hands down" yafada still yana kallonta Ahankali ta sauke hannunta da dama sunfara sagemata "pack these" yafada yana nuna mata kayanta daya watsar Babu musu ta duqa tafara tattare kudaddenta ta cusa su a jakkar sannan ta zuge ta miqe tsaye Wayarta ya miqomata batareda ya kalleta ba Amsa tayi itama ta sakata cikin jakkar "you're lucky today, karki qara barin tsautsayi yasa ki qara shiga hanyata" Yana rufe baki taji muryar batool tana qwalamata kira Saurin juyowa tayi sai taga batool dince tareda wasu mutane uku sun taho Sake juyowa tayi gareshi taga hankalinshi yanzu yana kan wayar hannunshi Yayinda bindigar hannunshi kuma batanan yanzu "Zainab ina kika shig..." maganarta ta maqale lokacin da idanunta sukayi arba da mussadiq wanda shima Dagowa yayi a daidai lokacin jin ana kiramashi sunan uwa gatse gatse Saurin Janye idanunta batool tayi gabanta na faduwa Wayyo allah, itama tagani, taga mai kama da Deen! Magana mutanen dasuka zo tareda batool wadanda cashier dinne da Manager din wajen suka shiga yimashi wanda tafi kama da ban hqr da rarrashi. Be tanka musu ba har suka gama hasalima hankalinshi nakan wayar hannunshi ne Suma ganin Hakan yasa sukayi shiru suka nutsu suna jiran yaga damar tankamasu Saida yagama danne dannenshi sannan ya dago oily eyes dinshi be sauke su akoina ba sai acikin large eyes dinta don itama shi take kallo Atare suka Janye idanun daga na juna sannan ya kalli cashier din da manajan, magana yadan yimasu da larabci yana saka wayar shi a aljihu Duk magana daya idan yayi sai sun Kada kai da sauri cikin girmamawa suna dan russunawa Koda ya gama Saida ya qara juyowa ya kalleta itama daidai ta kalleshi suka sake hada ido Wani kallo mai wuyar fassara yayi mata sannan yajuya yafara tafiya manajan na saurin take mashi baya Binshi da kallo daga zee har batool sukayi suna kallon yadda yake tafiya majestically Sai tafiyarshi ta tuna mata da ta Deen Shima irin wannan tafiyar yakeyi Saidai shi nashi akwai sanyi tattare daita, shi wannan yana yine da kuzari "am so sorry ma'am, I should have ask someone to escort you, am sorry please" inji cashier din cikin ban hqr Janye idanunta tayi daga kan su mussadiq dasukayi nisa ta maido kan cashier din sannan ta daga mashi kai kawai Hanya ya nuna masu alamun suje, yayi gaba suka take mashi baya suma Tunda suka fito daga supermarket din batool keta zuba kamar ru6a66iyar radio kuma duk akan mussadiq Ta Wani koma zarrariyar qarfi da yaji, wai ita wlh duk fadin kamanninsu da akeyi bata ta6a sanin ya kai haka ba, sak mutumin data gani a wayar zee Itadai zee jinta kawai take abinda ya dameta ya dameta, ita wai data ga Deen kenan a pics, ita datayi rayuwa dashi fa? Tace me? Sai taji ranta ya jagule, ina Deen? Me yakeyi yanzu? Yana cikin farinciki ko akasinshi? Me sukeyi yanzu su samu abinci? Ga yan uwanshi nan cikin daula suna birkida aciki shi yana can allah kadai yasan wane hali yake ciki Wani irin feelings ke tasomata a zuciya wanda takeyi duk lokacin da ta tuna shi, wani irin tausayinshi takeji a kowanne kusurwar zuciyarta Yes, yatafi ya barta a lokacin datafi buqatar shi, ya karya alqawurran dayayi mata, ya badamata qasa a idanu, yayi breaking din zuciyarta Amma Hakan be rage ko kaso 00.001 na soyayyarshi dake cikin zuciyarta ba, saima hauhawa datakeyi ga kuma qarin tausayinshi dake dawainiya da ita tun lokacin data gano asalinshi. Da gaskiyar batool datace wataqila akwai dalilin rabuwarsu, akwai abinda allah ya tsara masu shiyasa ya hadasu a lokacin da basu shirya ba yakuma rabasu a lokacin da basuyi tsanmmani ba Qaddarar so ta kawota dubai, gashi yanzu ta hadata da mutane Mafi muhinmmaci a rayuwar masoyinta Me kuma zai faru nan gaba? Bata saniba, time will tell, komai dama tsararre ne a wajen allah mune kawai muke haukanmu Fatan ta dai allah yabasu ikon kammala abinda suka fara lafiya, allah ya gwadamata ranar da Deen zai sadu da lost family dinshi. Share hawayen dasuka gangaromata tayi da sauri kafin wancan akun ta lura Komawa tayi jikin kujerar motar ta lafe ta lumshe idanunta Insha allah zata jajirce, zatayi trying all her best wajen ganin tasamu abinda takeso a wajen Aysha, insha allah sai komai ya warware very soon Amma matsalar ta anan shine Mussadiq Yasanta, yasan fuskarta and kuma ya zargeta da yar leqen asiri Idan yaganta da Aysha anya komai bazai kwa6e ba? Hakan na nufin she have to be extra careful da duk move da zatayi har tasamu ta cimma burinta Batasan sun iso gidaba Saida taji sunyi parking Saurin Kamo hannun batool dake kyarmar fita tayi Hakan yasata dakatawa ta juyo ta kalleta "batool please karki gayawa kowa munga Mussadiq" Zumudin fuskar batool ya rage don dama abinda take kyarmar taje tayi kenan "meyasa?" "Hakan na iya 6ata komai, musanmman idan yaya Aymaan yaji, yana iya yiwa abin wata fassara daban kokuma ya hanani zuwa school din don dama shawarar bawai kwanta mashi a rai tayi ba, please let this be between me and you" Shiru batool tadanyi cikin naxari saikuma ta Kada kai "ok, insha allah" "yauwa, thanks" tafada tana sakin hannunta sai suka fito tare suka rurrufe koffofin motar suka shige ciki tare Kingin rannakun sunzo very fast suka wuce, har yau ranar da zata fara zuwa school. Tunda wuri ta shirya don tare zasu fita da Aymaan don shi zaiyi dropping dinta Ahankali take saukowa daga stairs din cikin shigarta na atamfa riga da skirt mai pattern fari sai manyan zanen flawowi ja akai Saita dora jar afterdress asama ta yane kanta da gyalen afterdress din. A dining ta iske Aymaan dashima ke cikin shirinshi na asibiti Saidai kamar kullum be dora lapcoat din ba, tana gefen table din Shi kadai ne a dining din riqe da mug din shayinshi daketa tururi Tunda ya hangota daga nesa ya kafeta da idanu harta qaraso dining din "sabahal khair Akhie" tafada tanayi kamar bata lura da kallon dayake mata ba "sabahan-nurr ya ukhtie, kaifa naumiki?" yafada cikin kulawa "alhamdullilah" tafada a taqaice tana jan kujera itama ta zauna Shirin daukar mug take itama ta hada nata shayin saiya rigata Hakan yasa ta fasa takoma ta zauna tana kallon yadda yake hada mata Saida ya hada mata sannan ya turamata a gabanta "shukran" tafada tana murmushi Shima murmushin kawai yayi ya cigaba da shan shayinshi Itama daukar nata tayi suka cigaba da sha cikin shiru Basu jima ba duk suka gama suka tashi Shiga kitchen zee tayi da mugs din ta daurayesu sannan ta ajiyesu ma'ajinsu tafito Koda tafito saita tardashi tsaye hannunshi daya rataye da jakkarta dayan kuma riqe da briefcase dinshi sai rigar likitocin shi dake bisa kafadarshi Ganinshi rataye da jakkarta ya tunamata da Deen dinta hakan yasa ta danyi murmushi Duk yadda taso yabata jakkarta qiyawa yayi itakuma tana jin kunyar amsar nashi briefcase din Haka dai ba don taso ba suka fita zuwa wajen mota Shiya bude mata tashiga sannan ya miqo mata jakkarta ta amsa sannan ya rufe kofar shima ya zagaya nashi side din yashiga ya rufo kofar Reverse yayi da motar suka fito daga parking space din sannan suka nufi gate wanda aka riga aka wangale masu, suka zo suka wuce suka fice daga gidan... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:41 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *062* *AYSHA AL-HASSAN* Tun shigarsu gate din farko take bin school din da kallo har suka ida shiga cikin qatuwar qayattaciyar makarantar Bïñ harabar school din ta cigaba dayi cikin sha'awa, she can't help but got fascinate with the school Kallo daya tayima yanayin school din taji ta kamu da sonta Har Aymaan yayi parking yafita bata saniba sai jitayi an bude kofar gefenta wanda Hakan ya dawo daita daga duniyar kallon school din Dagowa tayi ta kalleshi sai taga shima ita yake kallo fuskarshi na fidda siririn murmushi Sauke idanunta tayi sannan ahankali tafara yunqurin saukowa Ganin Hakan yasashi matsawa gefe don bata damar fitowar Ahankali ta ida fitowa sannan ta daga kai tana qara samun clear view din harabar makarantar inda mutane keta kai kawo aciki akai akai Tayi nisa wajen kalle kallenta taji muryashi akusa daita yana cewa "did you love it?" Saurin juyowa tayi ta kalleshi saikuma tayi murmushin kunya sannan ta daga kanta ahankali "Good, dama it's a unique school for unique people like you" Sake Dagowa tayi ta kalleshi "muje, ko sai kingama kallon?" Sakeyin murmushi kunya tayi sannan ta gyara zaman jakkarta alamun she's ready Hakan yasa Aymaan nunamata hanya Babu yadda ta iya haka tayi gaba shima yazo ya jera daita suka fara tafiya cikin nutsuwa Tafiya suke suna gamuwa da mutane kala kala, mostly Arabs ne sai few qabilu The more suke nitsawa cikin school din the more take qara jin shauqinta This is her dream school, ta dade tana burin fita karatu qasar waje a irin wadannan qayattatun school din, sai gashi allah ya cika mata burin ta a lokacin da batayi tsanmmani ba Haka sukaita ratsa wajen suna qara shiga ciki An riga an kammala duk wani registration nata kawai saura tafara attending lecture Signboard suka wuce tareda Aymaan inda anan ma sun tarar da mutane ba laifi mostly suna jotting out timetable dinsu Shima Aymaan fiddo wani dan memo yayi daga aljihunshi da pen yashiga yima zee jotting din nata Kallon yadda yake daga kai ya hango abinda ke rubuce yakuma maida hankalinshi akan memo ya rubuta takeyi Sai yatuna mata da Deen, ya tuna mata memories dinta da Deen sunje kwafe timetable dinsu Wai yaushe komai zai bar tuna mata da Deen ne? Duk abinda zai faru baya zama new thing to her Saidai yazamo kamar tuni agareta Hakan na nufin duk abinda mutum zaiyi mata bazai zama saboba Saidai yazamo kamar tuni agareta? Meyasa? "Here" taji anfada Hakan yasata dagowa ta kalli Aymaan dake miqa mata memo din Kallon memo din tayi sannan tasa hannu ta amsa ahankali "gashinan, komai na rubuce anan, Hakan zai sauqaqa miki, all you have to do shine ki duba zakiga duk lokacin dakukeda lecture" Murmushi tayi tana Kada kai "thanks so much" Shima murmushin yayi mata "my pleasure" "yanzu kinga nan da 30mins kunada lecture, ya kamata kishiga class tun yanzu" Sake Kada mashi kai tayi batace komai ba "muje na rakaki" yafada yana nuna mata hanya Babu musu ta wuce suka nufi department dinta Har class Saida ya rakata ya samarmata Wurin zama daga farko farkon ajin Akwai few mutane a ajin Saidai kowa harkar gabanshi yake babu wanda ma ya lura dasu Saida ta zauna sannan ta ajiye jakkarta akan desk din sannan yafara yimata sallama "zan tafi, please take care, idan akwai wata matsala call me" yafada cikin kulawa, dama tanada numbershi don tuni sukayi exchanging digits "insha allah" tafada tana murmushi "Good, yanzu bari natafi, zan dawo around 3pm na daukeki ai naga 2:30pm kuke gama duk lectures din yau ko?" Kada kai tayi tana kallon memo din hannunta "Good zan dawo, insha allah zan nema miki driver dazai dinga kawoki yana maidoki kafin na koyamiki tuqi" Slight murmushi kawai tayi batace komai ba "to natafi" yafada yana gyara zaman tie dinshi "Allah ya tsare" tafada ahankali "Amin ya rabb habibty" yafada cikin jindadi sannan ya juya yafara tafiya Binshi da kallo tayi harya kai bakin kofar fita sannan ya juyo shima ya kalleta sai suka hada idanu Murmushi yayi mata mai kyau itama ta maida mashi martani Daga mata hannu yayi alamun bye itakuma saita qara fadada murmushinta tana kada mashi kai Tana kallonshi harya ida ficewa ya wuce, sauke numfashi tayi sannan ta koma ta jingina da kujerar datake akai Bïñ class din da kallo take da mutanen ciki, duk yawanci new comers ne Suma don mostly mutum shikadai zaka gani zaune yana raba idanu cikin baqunta kafin nan da few days lokacin da sabo zai shiga tsakanin juna kowa yayi aboki amma ita ta qudura a zuciyarta cewa bazata ta6a yin qawa ko daya ba kuma a school Su Deeya sun koyamata hankali, sun nunamata ba duk mai washe maka baki bane masoyinka Saita tsinci kanta da tunanin ko a wanne hali suke ciki yanzu? Yanzu dai sun kusa yin shekara a garqame wanda Hakan ke nufin sun kusa rabin zaman dazasuyi a jail, sai taji tausayinsu kamar yadda takeji duk lokacin da suka fadomata arai Tunawa tayi dasu master, wadanda ma bama sufara sa sanwar zama gidan yarin ba don a zaman dazasuyi a gidan ko kaso daya acikin 100 basuyi ba Suma fatan shiriya tayi musu da fatan allah yasa Hakan yazama silar shiryuwarsu Tunaninta ya katse ne lokacin da lecturer yashigo class din Sai a lokacin ta lura da yadda class din yaqara cika Tashi sukayi gabadaya suka gaidashi ya amsa yabasu izinin zama sannan duk suka koma suka zauna Nan take lecture din yafara Saidai ba lesson din suka shiga ba gadan Gadan, introduction kawai ne kamar yadda most lecturers keyiwa sabbin shiga 40mins sukayi a class din kafin lecturer din yafito Bayan fitarshi suma students din suka fara fita daga class din Tashi itama zee tayi ta dauki handbag dinta ta rataye sannan tafito daga class din itama Binging wayarta tayi Hakan yasa ta dagota daman tana hannunta ta duba Text message ne Hakan yasa tayi sliding wayar tashiga saqon _*In milk silky Abaya, in the cafeteria*_ Haka aka rubuta a text din Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta karanta sannan ta dago daga kallon wayar tana qara bin harabar school din da kallo _inane cafeteria din?_ Tambayar datayiwa kanta kenan Ajiyar zuciya tasake saukewa sannan tafara tafiya tana barin gaban class din Bata sha wahala wajen locating din cafeteria din ba don ba'a yishi inda mutum zaisha wahala kafin ya gano ba Cikin cafeteria din tashiga wanda yayi mugun shan banban da cafeteria dinsu na UMYU Wannan ya hadu iya haduwa, ga varieties din abubbuwan da zaka buqata ko wane iri ne, ga wajen very clean and quiet Ahankali take taka tiled floor din wajen tana dan wurwurga idanunta ta cikin shade din data saka ma idanunta kafin ta shigo wajen tana son ganota Bata sha wahala ba wajen ganinta ba don kwatancen kayan jikinta da akayi mata ya taimaka wajen spotting dinta da wuri Tana gaban wani glass da apples ke jere aciki da alama saye take Kasancewar ta juyamata baya yasa zee bata ga fuskarta Hakan yasata wucewa inda drinks ke jere inda tanan tana iya hango duk wani motsin ta Yitayi kamar tana son za6ar drink din dazaiyi mata Yayinda a zahiri idanunta na kanta Saidai shade din idanunta bazai ba mutane damar gane Hakan ba Ta inda take tana iya hangenta harta gama selecting apples din da sukayi mata sannan ta hada ruwan gora daya sannan ta wuce inda ake biyan kudin ta bude tsadaddiyar side bag dinta mai kalar kayan jikinta ta Fiddo A.t.m sannan ta miqa ma mai amsar kudin Ganin Hakan yasa zee maida hankalinta akan abinda takeyi tayi taza6i drink biyu sannan itama ta juya ta nufi inda ake biya lokacin har an cire kudin Aysha daga A.t.m din an maido mata Zee na isa wajen Aysha na Juyawa zata bar wajen, da wutsiyar ido zee tabita da kallo harta wuce sannan itama ta maida hankalinta kan cashier din Babu 6ata lokaci ta biya yayi mata packaging din kayan yabata tayi saurin fita don karta 6ace mata Cikin sa'a kau tana fitowa itakuma Aysha daidai zata sha wata corner Hakan yasata bin bayanta itama Koda itama ta shawo corner sai taganta zata shiga kofar wani office Saida ta qaraso wajen sannan ta lura ashe library ne Saida tadan ja lokaci sannan itama tashiga library din Tana shiga ta hangeta can row na biyu a gefen haggu na library din tana duba wani Littafi data bude a gabanta tana gutsirar apple din hannunta Janye idanunta zee tayi ta qarasa Shigowa ta nufi can bayan library din ta samarma kanta mazauni ta zauna Few people ke library din shiyasa wajen ya dauki shiru fiyeda yadda library dinsu na UMYU keyi Zama tayi ta zaro Littafi itama tana kallo sama sama Yayinda hankalinta ke kan Aysha da batama san daita ba Tayi deciding ba yanzu zata fara tunkarar Aysha ba har saita gama lura da duk moves dinta Batason sanyo gaggawa acikin aikinta don she believe duk abinda aka sanya gaggawa aciki baya lasting, Hakan yasa ta yanke shawarar cigaba da monitoring dinta har lokacin dataga its the perfect time ta tunkareta Tana nan zaune still monitoring her tana son ganin lokacin da zata tashi amma har lokacin second lecture dinsu yayi bata tashi ba, kuma batada alamun tashi don da alamu tayi nisa a naxarin littafin datake Hakan yasa zee maida littafin ta a jakka ta tashi ta nufi hanyar fita daga library din Second lecture din ma kamar na farkon ne, shima just introduction wanda Hakan kamar revision ne ga zee don tuni ta wuce wannan Wurin back in Nigeria amma dukda Hakan saita nutsu har akayi aka gama Sa6anin dazu yanzu ta lura yawancin wadanda suke zaune alone a lecture din farko yanzu suna tare da partner wataqila har sunfara sabawa wanda nan gaba sabon zai juye yakoma abota Ta6e bakinta tayi don ba wannan ke gabanta ba, idan ma abota zatayi to da mutum daya zatayi wato AYSHA AL-HASSAN itama din da dalilin yin Hakan, Hakan yasa taqi Sakin fuskarta a class din har suka gama abinda suke a class din ta biyo ayarin masu fitowa daga class din ta fito itama Library din ta nufa dukda tasan ba lallai bane ta isketa ba Illai kuwa bata ciki hakan yasa tajuyo kawai ta nemi wani quiet shady wuri ta zauna ita kadai har lokacin wani lecture din yayi Shima Saida suka dauki 30mins suna yi sannan suka fito Agogon hannunta ta kalla taga 2:40pm Tasan Aymaan nakan hanyar dawowa daukarta yanzu tunda yace 3pm zai zo Ganin akwai sauran free 20mins yasa ta yanke shawarar sake ganinta kafin ta tafi Number data turo mata text dazu ta turama guntun text kamar haka _*where?*_ Bayan minti daya saqo yashigo mata _*gone*_ Ajiyar zuciya ta sauke bayan taga reply din saita maida wayar a jakka takoma library don jiran isowar Aymaan Babu jimawa wayarta tafara ringing Cirota tayi ta duba Aymaan ne kamar yadda tayi tsanmmani Dagawa tayi ta kara a kunne tana sallama Acan bangaren taji ance "wslm student, hope kin gama komai" Kada kai tayi sannan tace "yes" "ok ina wajen danayi parking dazu" "ok ganinan zuwa" "to a iso lfy" Katse kiran tayi sannan ta miqe ta dauki jakkarta ta Rataya ta fito Inda yace mata din ta taddashi, yafito ya jingina da motar kanshi sunkuye yana danne danne a waya Besan isowarta ba Saida yaji motsin ta Dagowa yayi daga wayar ya kalleta sai ya sakarmata murmushi Itama dan murmusawa tayi tana Janye idanunta akanshi "Good afternoon" tafada ahankali "how are you? Ya makarantar?" "very nice" ta amsa tana dan kare goshinta da hannunta saboda hasken ranar dake dallota Ganin Hakan yasashi cewa "ok muje" Bude kofar tayi shima ya bude ta gefen shi suka shiga atare sannan suka maido koffofin suka rufe Tada motar Aymaan yayi ya jata suka dauki hanyar fita daga school din Suna kan hanya bayan sunyi nisa daga school din Aymaan yadan kalleta sannan ya maida hankalinshi akan titi yace "so ya kikaga school din?" "tayi sosai, every thing in order" ta amsa "lecturers fa? Is anyone hard on you?" Dan murmushi tayi sannan ta girgiza kai tace "not at all" Kada kai yayi "Good, karki dai manta, idan kikaga ko sign din matsala ne let me know please, kinji?" yafada cikin kulawa "insha allah" tafada a gajarce idanunta akan gashi gashin jikin jakkarta datake wasa dashi "kin ganta?" Kallonshi tayi sannan ta Kada kai "eh na ganta?" "wow! Kunyi magana?" "A'a, nayi deciding ba yanzu ba, be kamata nayi jumping to her ba batareda nasan komai gameda ita ba, kawai ina monitoring dinta ne yanzu kafin opportunity din Magana ya hada mu" Kada kai Aymaan yayi cikin gamsuwa "Good, Saidai dukda Hakan ki kula please da kinga something is going wrong ki sanar dani, banason wani abu ya sameki" Yadda yayi magana yasata dan sunkuyar da kanta tana dan murmushi Sai taji yaqara cewa "kinsan ko meyasa?" Dagowa tayi ahankali ta kalleshi saikuma ta girgiza kai alamun A'a Shima daga kafadu yayi "nima haka, amma zanyi qoqarin gano dalilin" Kauda kai kawai tayi batace komai ba Ta rasa dalilin da yasa haryanzu takasa sakewa dashi, ba Haka take ba, tanada saurin sabo amma a case dinshi abin ya chanza Gwara idan tare suke da batool tafi sakewa amma idan daga ita sai shi ne sai taita jinta wani iri, taji ta qagara tabar wajen kamar yadda yanzu ma ta qagara su isa gida ta samu ta sulale Haka suka cigaba da firar jefi jefi inda duk Aymaan keyin rabi da kwatan ta don zee tana amsawa ne where necessary wani wuri kuma tayi murmushi kawai Koda suka isa gida ma da Tambayar taga Aysha duk suka tarbeta Kamar yadda taba Aymaan amsa haka suma tabasu kuma sukayi na'am suma da shawarar tata. Washegari ma haka zee tayi, daga nesa nesa take lura da Aysha tana kuma monitoring moves dinta kuma batasha wahalar ganota ba don wanda yabata information jiya yabata yau ma wanda duk aikin Ahmad ne don shi yayi assigning wadanda zasu dinga lurarmashi da Aysha din yakuma basu number zee akan su dinga sanar daita akai akai Hakan ba qaramin sauqaqawa zee yayi ba don nan da nan take ganota duk inda take saboda information dinsu Ahaka suka cinye satin farko har aka shiga na biyu shima Acikin kwanakin nan zee ta samu abubbuwa da dama gameda Aysha Kama daga mutanen da take mu'amala dasu, yanayin mu'amalarta da mutane, wuraren datafi zama ddss Ranar wata juma'a Zee ta yanke shawarar tunkarar Aysha Cafteria tashiga bayan ta tabbatar da shigar Aysha aciki Hangenta tayi usual spot dinta wato wajen apples tana selecting wadanda takeso Itakuma zee tawuce wajen kayan snacks wadanda ke opposite din inda Aysha take itama tana za6ar wadanda sukayi mata Ganin Aysha ta juyo zata taho yasa itama juyowa riqe da abubbuwan data dauka Tahowa sukayi suna fuskantar juna Yayinda zee ke targeting din yadda zata aiwatar da plan dinta Suna kawowa tsakiya sukaci karo da juna wanda Hakan yasa kayan hannunsu watsewa "ya Ilahi!" inji Aysha cikin daddadar muryarta "ya sallam!" inji zee itama tana Wara idanu akan kayyayakinsu dasuka watse a wajen Atare suka duqa suka shiga tsintsintosu sannan suka miqe "am very sorry, ban kula bane" inji zee cikin harshen turanci tana kallonta cikin yanayin ban haquri karo na farko dazasuyi face - face kuma taga fuskarta tarr ba kamar yadda tasaba hangenta daga nesa a yan kwanakinnan ba Aysha batayi irin kamar nan ba da mussadiq da Deen sukayi, ita kammaninta daban, tafi kama da babbansu amma kallo daya zaka mata kasan jininsu ce don ko babu kama ta fuska akwai ta jini Itama farace irin fatt dinnan, yanayin fatarta na shige da fatar kajin turawa, tanada yar madaidaiciyar round face mai dauke da dara daran idanu sai dan siririn hanci da madaidaicin baki She's beautiful in her own way kuma kallo daya zaka mata ka hango tarin nutsuwar dake tattare daita "oh, never mind, ai karo mukaci, it's not intentional" inji Aysha cikin turanci itama mai karin larabawa irin dai na mussadiq Murmushi zee tayi tana miqoma ta daya daga cikin apples dinta data tsinto mata "thanks for your understanding" Itama murmushin tayi mata tana amsar apple din "thanks too" Wani abu yayi knocking kan zee, wani abu Aysha tayi yanzu takoma mata sak Deen Saidai abin yazo ya wuce in a flash that takasa pointing finger akai "here" inji Aysha tana miqamata sausage roll dinta da itama ta tsinto mata Amsa tayi tana murmushin yaqe tana kallonta don son ganin abinda tagani dazu "thanks" zee taqara fadi ahankali "yeah, take care" tafada tana sake sakarmata murmushi sannan tayi gaba And then sai lokacin zee ta gano abinda tagani dazu Murmushinta A'a ba Murmushinta ba Abinda yafito ta sanadin murmushin Dimple Dimple din tsakiyar gemu Lumshe idanu tayi ta bude su cikin shauqi Bata ta6a sanin tayi missing din murmushin Deen ba sai yanzu Bata ta6a sanin tayi kewar Dimple dinshi ba sai Yanzu Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi tana maida lower lip dinta ciki tareda cijewa Tadan jima ahakan kafin itama ta fara yunqurin barin wajen amma abinda witsuyar idanunta ya hango mata ya hanata wucewa din Kafe wajen da idanu tayi sannan ahankali ta qarasa wajen ta duqa ta dauki abin Gabanta ne ya fadi Dago abin tayi a hannu tana jujjuyawa tana ganin kammaninshi sak da wanda tasaba gani Bracelet ne Irin wanda take ganin Deen dashi kullum a hannunshi, wanda wani lokacin har tunanin amfanin me yake mashi take ganin kullum yana maqale a hannunshi Bracelet din da shi ya hadata da Deen ta hanyar sarqahoshi datayi da gyallenta Tashi tayi tsaye tana cigaba da jujjuyawashi a hannu abubbuwa da dama na yawo a zuciyarta... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:41 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *063* _sorry for the late post, yanzu Dakyar nake samun typing, bear, bear, bear with me👏_ Damqe Bracelet din tayi a hannunta sannan itama ta bar wajen da niyyar zuwa maida ma Aysha Saidai Koda tafito bata nan Wajen cashier ta wuce ta biya kudin abinda ta siya sannan ta fito waje Nan ma ta hanhanga bata ganta ba Tasan wuraren da zata iya ganinta a daidai wannan lokacin Hakan yasa ta dauki hanyar inda takeda tabbacin tana wajen yanzu Harta fara tafiya wata idea tayi stucking qwalwarta Sake kallon Bracelet din tayi Duk yadda akayi wannan abin mai matuqar muhinmmanci ne ga wadannan ahalin Idan ta fuskanci ya 6ata hankalinta zai tashi kuma zata shiga nemanshi Yanzu batada tabbacin tama san da faduwarshi so idan takaimata ba zatayi wani murna ba Kamata yayi tabari ta nemeshi ta jigatu a nemanshi har tafara fidda rai da ganinshi a sannan itakuma ta bata, Hakan zai sata murna sosai kuma qila daga nan abinda take burin ya qullu a tsakaninsu ya qullu Ajiyar zuciya ta sauke, yes this makes sense, bazata bataba yanzu, sai monday. Da wannan shawarar ta bude jakkarta ta jefa Bracelet din aciki ta juya ta dauki hanyar class dinsu Ba lokacin lecture bane amma haka ta shige class din ta zauna Jitayi duk babu abinda ke mata dadi, she's very lonely gashi babu abokin fira Buga tagumi tayi da hannu daya datayi supporting da desk dinta tana kallon masu shige da fice a class din Tunawa tayi da Good old days dinta inda kullum burinta gari ya waye ta shirya ta tafi school ba don komai ba sai don haduwa dashi Tunawa tayi da yadda suke zama a either library ko wurin zamansu suna karatu Tunawa tayi da yadda yake haquri daita akan calculations yaita fahimtar daita har saita dauka, idan kuma bata dauka ba bazaiyi gaba ba dole sai yayi ensuring ta iya wannan sannan duk kuwa tsawon lokacin da Hakan zai daukesu Tunawa tayi da yadda suke fira, firar da haryanzu takasa samun mai mata mai dadi irin nashi kuma haryanzu takasa samun wanda zata saki jiki sosai suyi fira da Dariya kamar shi Tunawa tayi yadda takeyi kamar zata makeshi da littafi idan yayimata laifi ko yafadi wani abu da bemata ba, Tunawa tayi da yadda yake curewa wuri guda idan tayi Hakan ko yayi baya yana Dariya Tunawa tayi da yadda yake Hade cikkakun girarenshi idan yana fushi da yadda yake kumbura cute face dinshi Batasan murmushi take ba, shes lost in his thoughts as always Lokacin datayi realizing Hakan sai taga few students ma kallonta suke, tasan tunani zasu dinga yi ko wancan lfy? Bude jakkarta tayi ta ciro wani plain sheet da pen ta ajiye a gabanta ta qara buga tagumi da hannu guda, dayan kuma tafara rubutu _I heard someone whisper your name, but when I turned around to see who it was, I was alone. Then I realized that it was my heart telling me that I miss you._ _Sometimes, I sit and think of all the memories I’ve made and smile. Then I smile even more at the thought of memories yet to be made._ _I still miss him, I miss him, I’m missing him._ _I miss the old days,the old you, the old us.._ Kasa cigaba da rubutun tayi saboda yadda hannunta yakasa riqe pen din sosai saboda rawa rawar dayake Kafe rubutun tayi da idanunta tana ganinsu biji biji sanadiyar hawayen dasuka taru a idanunta Ahankali ta dauke takardar ta cukwikwiyeta ta Runtse ta a hannu Yaushe Deen zai bar zuciyarta ta huta? Yaushe zata yini ta kwana batayi tunaninshi ba? Yaushe zata yini ta kwana bata zubda kwala ba akanshi? When will all these end? **** Weekend yazo ya tafi very fast inda zee ke qagare monday tayi don sake fuskantar Aysha Tasan izuwa yanzu taci nema harta gaji, tasan izuwa yanzu tana cikin damuwar rashin shi kuma samunshi a wannan lokacin ba qaramin dadi zaiyi mata Haka hassashen zee yake don a bangaren Aysha bata lura da babu Bracelet din a hannunta ba sai lokacin tafiyarta gida Hankalinta yatashi sosai dataga baya daure a tsintsiyar hannunta, Hakan yasa tashiga nemanshi Duk inda taje ranar Saida ta koma ta dudduba amma babu shi Har cafeteria din Saida taje ta dudduba har inda suka ci karo da zee amma babu abu mai kama da Bracelet dinta Kamar bazata tafi ba ranar amma haka ta haqura tabi driver suka koma gida tana jin kamar taita kuka Koda ta isa gida haka ta tisa umminta gaba da maganar 6acewar Bracelet din Sosai ta damu kanta akan Hakan ganin Hakan yasa umminsu lallashinta tana assuring dinta zata ganshi insha allah Da Hakan ta dan kwantar da hankalinta itama tana looking forward to monday don qara komawa school ta duba ko zataci sa'ar ganinshi ko kuma cleaners din school din sun tsintar mata *MONDAY* Tunda wuri ta shirya suka sauko tareda batool da itama tayi shirin zuwa makaranta Suna zaune kan dining suna karyawa Aymaan shima ya sauko cikin shirinshi na fita asibiti Shima babu 6ata lokaci yayi joining dinsu suka karya tare sannan suka tashi suka fito gabadaya suna musun wa zee zatabi Shi Aymaan yace shi zatabi yayi dropping dinta itakuma batool tace bata yarda ba don atare ai yazo ya iskesu qasa Indai yanason tabishi Saidai idan su biyu zaiyi dropping Shikuma yace bazata shigar mashi mota ba shi zee kawai zai dauka Itadai zee tana gefe tana kallon dramarsu Wani sa'in idan suna wannan chaftar tasu kamar ba wa da qanwa ba, ta lura akwai wasa sosai a tsakaninsu ba kamar wasu siblings din ba da zakaga babu yan wasa tsakaninsu Ganin abin nasu bana qarewa bane kuma lokaci wucewa yake yasa ta dakatar dasu ta hanyar cewa to bari ayi yar chankal duk wanda abin ya fada mawa to shi zatabi Qin yarda Aymaan yayi yace shi be yarda ba tana iya cheating Saidai idan coin za'a jefa Haka kau akayi, Aymaan ya Fiddo wani kwandala ya nuna ma batool akan ta za6i side daya Saida tagama ruwan ido sannan ta za6i side din da zanen mutum ke ajiki shikuma Aymaan aka barshi da plain side din Zaya jefa batool tace bata yarda ba Saidai aba zee ta jefa Zee na Dariya ta amshi kwandalar ta jujjuyata a hannu sannan ta jefata sama tayi tumbulan sau uku asama kafin ta fado qasa Duk tahowa sukayi don ganin wayaci, sai gani sukayi side mai zanen ke sama Ihun murna batool tayi ta kama hannun zee tajata zuwa motarta suna yiwa Aymaan daya tsaya Hannu riqeda qugu yana binsu da kallo Dariya Bude mata passenger seat tayi ta shiga sannan itama ta zagaya seat din driver tana cigaba da yimashi Dariyar mugunta Saida tayimashi gwalo sannan tayi saurin shigewa ta rufo kofar ganin yayi kamar zai nufosu Saurin tada motar tayi tajata aguje suka fice daga gidan suna cigaba da dariyarsu Kwafa Aymaan yayi sannan shima ya nufi motarshi murmushi a fuskarshi yashiga ya tada shima yabar gidan Har cikin school din batool ta kaita tayi parking suka fito tare Yau zee taji dadin ride din zuwa school din don firarsu sukaitayi suna Dariya har suka iso bata saniba sa6anin idan tareda Aymaan take don jitake ta qagara su iso don she always feels nervous around him kuma tarasa dalili Aymaan nada fara'a ga wasa da Dariya amma tarasa meyasa take jin kunyar shi, kwata2 bata iya sakewa freely idan suna atare, tarasa dalili Tareda batool suka wuce cikin school din don cewa tayi sai taga class dinta Babu musu zee tayi leading dinta har class din inda duk inda suka gitta sai batool tayi santi tana jin dama school dinsu ne Daga baya ma saita fara fushi wai kishi take da zee don school dinsu yafi nasu kyau Itadai zee Saidai tayimata Dariya tana mata gwalo don qara tunzurata Ahakan ta rakota inda tayi parking motar ta tashiga ta tadata sannan sukayi sallama taja motar tayi gaba Ganin Hakan yasa zee Juyawa takoma class don lokacin first lecture dinsu yakusa Bayan 40mins zee tafito daga class kamar yadda kingin students din ke fitowa Wayarta ta fiddo tashiga number dake bata information akan Aysha *_where?_* Ta turawa number Bayan wani lokaci akayi reply da *_cafeteria_* Maida wayar tayi cikin jakkarta sannan ta nufi hanyar cafeteria din Daga nesa ta hango ta tafito daga cafeteria din ta dauki hanyar komawa department dinsu Sanye take cikin wata tsadaddiyar blue Arabian gown mai kwalliya a gaba tayi rolling gyallenta yadda larabawa keyi, side bag bisa kafadarta mai matching din kayan jikinta Tunda ta hangota tasan babu lafiya don fuskarta dauke take da yanayin damuwa wanda bata raba dayan biyu rashin abin hannunta yajawo Hakan Gyara nutsuwarta zee tayi ta nufi hanyar cafeteria itama Saida taje gab da kofa sannan tajuya ta kalli Aysha da har tayi nisa Cikin dan daga murya zee tace "hey!" Bataji ba don tayi nisa a tunanin datake gashi da dan tazara a tsakaninsu Hakan yasa zee biyo bayanta "hey! Sister! Ukhtie!" Cikin tunani Aysha taji kamar ana mata magana saita dan dakata sannan ta juya ahankali Zee ta hango tana daga mata hannu tana nufota murmushi a fuskarta Tsayawa tayi tana kallonta harta iso tana qoqarin son tuno inda tasan face dinta Qarasowa zee tayi tana dan panting saboda dan saurin datayi Murmushi Aysha tadanyi mata tana cewa "Aslm alaiki" Ajiyar zuciya zee tayi sannan tace "wslm warahmatullah, tun dazu nake miki magana bakiji ba" tafada cikin turanci Dan dafa goshi Aysha tayi "oh Afuwan, banji bane" Murmushi zee tayi tace "nice wannan wanda mukayi clashing a cafeteria ranar juma'a?" tafada cikin sigar son tuna mata Kada kai Aysha tayi tana murmushin da yasa dimple dinta lotsawa tace "na tuna, ya kike? Ya yau?" Da lfy lau zee ta amsa saikuma ta fara qoqarin bude jakkarta tana cewa "ranar bayan tafiyarki naga wani abu, bansaniba ko nakine" tafada tana laluben jakkar Zubama jakkar idanu itama Aysha tayi tana jin bugun zuciyarta na qaruwa, fatanta dai ace abinda take nema ne Bayan yan lalube lalubenta ta Ciro Bracelet din ta nunama Aysha din tana cewa "naki ne? Rufe bakinta Aysha tayi cikin tsananin murna sannan tayi saurin amsa tana jujjuyawa a hannu "ya rahman! Nawane, ina kika ganshi?" tafada cikin tsananin murna Murmushi zee tayi mata "a cafeteria bayan kin tafi, qila faduwa yayi" "kai amma nagode qwarai yar uwa, you have no idea yadda na damu da banganshi ba" Murmushi zee tayi tana Kada kai "babu komai yar uwa" Sake jujjuya shi tayi kamar mai son ganin ko shi dinne Yayinda zuciyarta ta washe tayi wasai tana jin wani irin farinciki a zuciyarta Sake Dagowa tayi ta kalleta cikin farinciki tana cewa "shukran aidaan ukhtie, naji dadi sosai, jazakillah bil-jannah" Murmushi zee tayi don ita banda murmushinta babu abinda take kallo "ohh babu komai, just take care next time" tafada tana mata murmushi Kada kai Aysha tayi tana sake damqe Bracelet din a hannunta tana cewa "insha allah sweet ukhtie" Yar Dariya zee tayi tace "Zainab, ki kirani da Zainab" Dan Wara idanu Aysha tayi "Ashe ummie ce? Zan dai kiraki da ummie saboda sunan Umminmu gareki" Dan Wara idanu itama zee tayi cikin mammaki "wow, kice ni Umminki ce" tafada cikin tsokana Dariya Aysha tayi tana Kada kai "Na'am, ke Umminmu ce kinga dole daga yau mu dinga biyayya" Itama dariyar tayi tace "kefa, ya sunanki?" "Aysha.. Aysha Hassan" "wow! Nice name" "thanks ummie" Murmushi zee tayi cikin jindadin nasarar da tasamu tace "zan tafi, kafin lokacin lecture yayi, see you" "yeah, see you" tafada itama tana daga mata hannu Saida taga wucewarta sannan ta maida hankalinta kan Bracelet din hannunta tadanyi ihun murna tasake rintseshi a hannu sannan itama ta wuce department dinsu Da farinciki zee ta qarashe Wunin ranar ganin yadda plans dinta ke working out successfully, saikuma tafara planning what's next don Batason tayi fuck up ko yaya ne a wannan mission din nata Washegari Zee bata yarda suka sake haduwa da Aysha ba sai washegari Ranar ma Saida tayi timing lokacin shigarta library sai ta rigata shiga ta zauna daga tsakiyar library din yadda data shigo zata hangota Tana zaune pretending kamar karatu take Aysha tashigo library din Da farko bata lura da zee ba Saida ta ida Shigowa library din Dan Wara manyan idanunta tayi tana cewa "Ummie!" Zee jitayi kamar ta dago nan take Saidai ta cije taqi Dagowa Hakan yasa Aysha qarasawa wajenta "Ummie" taqara fada tana dafata Saurin dagowa zee tayi da alamun tsorata a fuskarta ta kalli Aysha Dariya Aysha tafara tana rufe bakinta "sorry, na baki tsoro" Ajiyar zuciya zee ta sauke tana dafe saitin zuciya "Gaskiya kam, kin bani tsoro" "sorry, I was calling you amma hankalin na can" tafada tana nuna littafin gaban zee Murmushi zee tayi "wlh kau, hankalin yatafi, please have a seat" tafada tana matsa mata Babu musu ta zauna tana murmushi tareda daukar littafin gaban zee tana cewa "Me kikeyi?" Daga kafadu zee tadanyi tana cewa "just going through abubbuwan damukayi a class" "wow, that's Good, wane level kike?" tafada tana maida mata littafin "100level" inji zee tana jawo littafin Dan Wara idanu Aysha tayi "wow, kice kina cikin sabbin zuwan school dinnan kenan" Kada kai zee tayi tana murmushi "ok you better be really ready don akwai aiki agabanku sosai" Dariya zee tayi tace "yes ma'am" Dariya suka sakeyi atare "shekaranjiya naba Umminmu labarin ki, she's so happy itama, tace na miqa miki saqon godiyarta" Zuciyarta tadanyi skipping beat, mahaifiyar Deen fa kenan. Sai tadan daga gira daya "Godiyar me?" "Bracelet dina dakika ganomin" Yar Dariya zee tayi tace "haba don gano Bracelet kawai?" "agareki ne kawai amma gareni babban abu kikayimun don I can give anything to get back my Bracelet" Dan Wara idanu zee tayi "is it that important?" Kada kai Aysha tayi "fiyeda tunaninki, its something very special" tafada tana shafa Bracelet din dake maqale da hannunta "really? Tell me about it" inji zee cikin zaquwa Dan murmushi Aysha tayi sannan tace "never mind, what matters shine an ganoshi" Zainab Bataji dadi ba Amma bata nuna ba, wataqila tafara zaqewa ne, ya kamata tabi ahankali karta lallatama kanta aiki, be kamata ta fiye shishigi ba, duka yaushe suka fara magana ma da zata so jin wani abu gameda ita, she really needs to be careful kar ta fita kan Aysha Da wannan tunanin ta dauki burger da ba'a fasa ba Cikin wadanda tasiya ta tura gaban Aysha cikin friendly smile tace "bismillah" Girgiza kai Aysha tayi tana cewa alhamdullilah Dan 6ata rai zee tayi tace "why?" Dariya Aysha tadanyi ganin yadda ta 6ata fuska tace "am not a fan of burger, baya min dadi" Kada kai kawai tayi bata qara matsa mata ba ta maida kanta akan littafin gabanta Itama Aysha saita fiddo wani Littafi daga jakkarta tana cewa "nima bari naduba wasu sums, suna bani wuya, na rasa yadda zanyi dasu, I hate calculations" Dagowa zee tayi daga littafin ta ta kalleta tana mata Dariya tace "really? Is it that hard?" "very hard, ni dama ba fan din calculations bane, I hate it, Dakyar nake coping a class" tafada cikin yanayin mita Cikin karambani da neman gindin zama zee tasa hannu ta dauki takardar tana cewa "mugani, maybe I can help" Wani kallo Aysha tayi mata sai kuma ta fashe da Dariya tana cewa "really? Kinsan wane level nake? 300level. Tayaya 100 level student zai koyar da 300level?" Wani murmushi ya kufcewa zee ganin abinda ke cikin littafin Aysha din Tasan calculations dinnan, sunyishi back then in Nigeria Hakan yasa ta dago ta kalli Aysha tace "well, let's see" Wata takardar zee ta fiddo ta ajiye sannan ta tambayi Aysha ina ne kebata matsala Cikin son qureta Aysha ta nunamata wani question tana son ganin ta ina zata fara Ahankali zee ta kwafe question din cikin takardar data fiddo sannan ta kauda Littatafan Aysha Agefe sannan tafara solving din question din tana explaining cikin qwarewa. Tunda tafara Aysha ta kafe takardar da idanu tana kallon yadda take solving question din cikin qwarewa kamar wata expert mathematician Saida tagama sannan ta dago ta kalleta tace "Are you clear now?" Daukar takardar Aysha tayi tana kallo cikin mammaki don dama question din data sani ne ta gwada mata don ganin ko zata iya saigashi tayi solving dinshi expertly "wow! Tayaya kikayi Hakan?" tafada tana bin takardar da kallon mammaki Murmushi kawai zee tayi batace komai ba "ya ilahi! Wlh kinyi shi daidai, but how come kika iya solving sum din 300level while you're just in 100 level?" Murmushi zee tasake yi "you know, mathematics is all about calculations and using of formular(s), akwai wadanda muddin zasusan formular din abu to zasu iya solving dinshi ko an koyamusu ko ba'a koyamusu ba, what you need to know about mathematics is how to use formulars and steps you should take" tafada tana copying magangganun Deen back then Tafi Aysha tafara impressively "wow, am impressed, ashe ina tareda mathematician" Wara idanu zee tayi tana Dariya "No! Nima duka me na iya?" Murmushi Aysha tayi tace "Allah kin iya, tunda har kika iya solving wannan question din, haka shima yayana yake tun yana qarami allah yabashi qwalwa, lokacin yana secondary school shike topping kowa a mathematics, har takai seniors dinshi ma na zuwa yayi musu solving, nima shi kemin don dai yanzu ma bayanan shiyasa nake shan wahala" Dan Wara idanu zee tayi "wow, kinada yaya?" "yes, inada yaya daya sunanshi yaya mussadiq, he's a mathematician too amma Koda yaushe he's busy beda lokacin nunamani wani lokacin sainayi Dakyar nake samun ya gwadamin, to yanzu yamayi tafiya, am left all alone with my problems" tafada tana 6ata fuska Dariya zee tayi mata cikin zuciyarta kuma tana jindadin jin cewa mussadiq yayi tafiya, yes! Seems yatafi yabata space don tayi bincikenta hankali kwance "amma yanzu tunda gaki ai shikenan" inji Aysha cikin jindadi Dan Wara idanu zee tayi tace "nima fa ba sosai na iyaba, just the little my brain could take" "yes, atleast your brain could take something, nifa? Yanzu let's solve another one" inji Aysha tana maido littafinta gabansu tana sake matsowa kusada zee Gwada mata wani question din tayi wanda shima zee ta iya shi, nan take suka hau solving dinshi shima Wasa wasa Saida sukayi solving question biyar duk masu matuqar wuya a zaman dasukayi, sosai karatun da zee keyi da Deen yayimata rana yau don sosai tayi impressing din Aysha kuma ta burgeta A bangaren Aysha kau jitayi kamar ta goya zee don dadi Dama tun shekaranjiya da zee ta maido mata Bracelet dinta taji ta kwanta mata arai, gashi tanada wani stylish way of life dataji ya burgeta plus suna mai girma dake gareta wato sunan dear mahaifiyarsu, tun a lokacin taji tayimata Washegarin ranar data maido mata Bracelet dinta ta nemeta don haka kawai taji tana son qara ganinta kota sake mata Godiya amma bata ganta ba kuma gashi batasan department dinta ba, haka ba don taso ba ta haqura Sai gashi yau batareda tayi tsanmmani ba tasake haduwa daita anan Haka kawai taji tanajin kanta very free around her abinda bata saba yi ba don ko qawaye batadasu sai wadanda za'a hadu a gaisa kawai Amma lokaci guda taji tanason qulla abota da wannan kyakyawar cool lady din mai burgewa Bata ida burgeta ba Saida tayi realizing baiwarta na iya lissafi Lissafi na matuqar ba Aysha wuya don dama can bata sonshi Saidai course din datake yi dole Saidashi shiyasa take matuqar wahala Kasancewar tana ganin subject din a matsayin subject mai matuqar wahala Hakan yasa duk wanda ya iyashi yakuma qware akai yake matuqar burgeta don gani take their brain is so special Hakan yasa Zainab ta ida tafiya daita, takuma ji ajikinta tayi qawa, ko babu komai zata dinga qaruwa ta wannan fannin daita Suna ahaka har lokacin shiga next lecture dinsu zee yayi Haka ta tashi ba don sun gaji da karatun ba tayi mata sallama Tambayarta Aysha tayi yaushe zata fito tace mata 2:30pm kuma daga nan gida zata tunda last lecture ne Hakan na nufin bazasu sake haduwa ba don lokacin dazata fito ita tana class "here" Aysha ta miqa mata wayarta Amsa zee tayi tana kallon wayar saikuma ta dago ta kalleta da alamun tambaya "Your digits please, so that gobe basai nasha wahalar nemanki ba kuma zamu dinga Gaisawa idan muna gida" Murmushi zee tayi, ko ba'a fadaba tasan tarkonta ya kama, Aysha na sonta da abota Loda mata numberta tayi acikin wayar sannan tabata Amsa tayi tayi flashing dinta saigashi kiran yashigo "save it please, zan kiraki anjima inji ko kin isa gida lfy" Murmushi zee tayi mata tace "ok, thanks, bari natafi kar lokaci ya wuce" "ok bye" "bye" Da haka ta fito daga library din zuciyarta fess. Gashi tasamu shiga awajen Aysha ga tasamu information din mussadiq bayanan, very big opportunity. Fatanta dai allah yabata ikon kammala komai kafin dawowarshi... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:41 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *064* *ONE-SIDED LOVE* "Hmm Aymaan kenan, ni aganina riqe kashi a ciki baya maganin yunwa, 6oye abinda ke zuciyarka is not a Good idea, aganina fidda abinda ke zuciyarka zaifi kabarshi yana weighing dinka down" inji Ahmad yana kallon Aymaan dake zaune kan office kujerarshi mai jujjuyawa ya maida kanshi can baya yana kallon ceiling Ahankali ya dago daga jinginen dayake ya zauna dakyau yana fuskantar Ahmad "Ahmad kenan, karka manta anason duk abinda zakayi ka lura da lokacin daya kamata kayishi kakuma lura da moment din daya cancanci yin abin, am waiting for the right time, dude" "waiting? Har yaushe zaka cigaba da jira? You want it then reveal it, karka manta abari ya huce shike kawo rabon wani" "kaima kuma karka manta rabon mutum baya ta6a wuceshi, idan rabota ce zan mallaketa Ahmad Nima kaina inason rabuwa da wannan nauyin dake kan qirjina, nafika son furta abinda ke raina don ni yake hanawa sukuni dare da tana ba kai ba But not now, haryanzu zuciyarta batayi healing ba, banaso na dagula mata lissafi Nasamu kwanan nan tana dan walwala, tana farinciki, banason abinda zai zo yasake dagula mata shi" Ajiyar zuciya Ahmad yayi yace "kai komai sai kace farinciki farinciki, what if farincikin nata baya nufin naka farincikin fa?" "then saina haqura da nawa ita tasamu saboda farincikinta on it own yana sani farinciki" Furzar da iska Ahmad yayi sannan ya qara matsowa jikin table din gabanshi yace "Aymaan kana sonta ko baka sonta?" Dan murmushi Aymaan yayi ya koma jikin kujera ya jingina "meyasa kake tambayar da kasan amsarta?" "Don't answer my question with a question dude!" inji Ahmad a dan fusace Murmushi Aymaan yasakeyi sannan ya sake Dagowa daga jingina da kujerar dayayi ya matso jikin table din daya raba tsakiyar su "yes, I love her. With all my heart, all. Tun lokacin dana fara ganinta nafara jin wani abu a zuciyata gameda ita Lokacin da Ummy tabani labarin ta kuma sainaji tausayinta yasamu matsugunni a zuciyata Sainaji inajin pain dinta a zuciyata, sainaji kamar ni akayiwa abinda akayi mata, kamar na dauke mata abinda takeji a zuciyarta na maido tawa Saikuma naji duk duniya babu abinda nakeso kamar walwalarta da farincikinta, every single smile of her means alot to me and also every single drop of her tears means to me too. I love her so much, so very much" yafada emotionally "why then baxaka gayamata ba Aymaan? Kafison kayita Ajiyar abin a zuciyarka har abin yazama maka something else? Look at you Aymaan, you're no more yourself" Murmushi Aymaan yasake yi "zai wuce, komai zai daidaita" "when? Yanzu fa haka kai kadai ke haukanka, ita batasan ma kanayi ba, tell me yaushe zai wuce?" "Ahmad its not as easy as you think, Zainab's heart is already injured and still yet to heal, why zan kuma zan qara dagula mata lissafi?" "yaushe zatayi healing? Haryanzu fa tana sonshi, it's first love we're talking about Aymaan, bakasan first love ba ko? Jiranta tayi healing kamar jiran gawon shanu ne, heal her with your love" Kallo Aymaan ya kafe Ahmad dashi na wani lokaci sannan yace "yes, nima inason yin haka amma nakasa" "why?" Shiru Aymaan yaqara yi yana kafe desk din gabanshi da kallo "maybe am scared" "scared? Scared of what?" Ajiyar zuciya Aymaan yayi yace "baxaka gane ba, wani abin da ka fadeshi kaji amsar da zai bugar maka zuciya gwara kabarshi a zuciyar ka jure duk illar da zaiyi ma zuciyarka. Yes inason na fadamata amma ina tsoron amsar dazata bani, baki yasan abinda zai furta besan abinda za'a mayar mashi ba. Zan jira, zan jira har sai naga perfect time din daya kamata na furta mata feeling dina Zan cigaba da supporting wish dinta harta cimma burinta, wataqila Hakan zaisa nayi earning soyayyarta..." ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ Kamar yadda Aysha tace sai gashi ta kira zee can marece likis Lokacin suna tareda batool a daki Basu dade suna gaisawa ba sukayi sallama akan sai sun hadu gobe idan allah ya kaisu Sosai Batool da zee sukayi ta murna akan nasarar dasuka samu suka kuma zauna suna qara planning abubbuwan daya kamata suyi nan gaba A 6angaren Aysha kau Koda taje gida ranar da labarin zee ta tusa umminsu gaba tanata bata labarin ta da yanayin turancinta don slang din turancinsu ba daya bane Hakan yasa yanayin na zee ke burgeta ga uwa uba maths data iya Agaban Ummin ma takira zee suka gaisa tana mata fatan takoma gida lafiya Basu dade kan wayar na sukayi sallama Haka kawai itama umminsu Aysha taji yarinyar ta kwanta mata arai itama dukda ko ganinta bata ta6a yi ba Haka dai Aysha ta kwana da doqin wayewar gari don sake haduwa da new friend dinta Ahankali ahankali abota tashiga tsakanin zee da Aysha irin sosai dinnan Koda yaushe suna tare inhar ba class daya daga cikinsu yake ba Sosai yarda da shaquwa tashiga tsakaninsu inda ta Hakan duk zee tasan tarihin rayuwarsu Saidai kamar yadda Ahmad yasamo information din Hakan itama tasamu, bata samu abinda takeso ba don da alamu ma ita kanta Ayshar batasan meye silar 6acewar Deen ba, abinda tasani kawai shine ya rasu Sosai Hakan yaqara dagulawa zee lissafi, tarasa yadda zata 6illowa lamarin Bata saniba ko dagaske Aysha din batasan komai akai bane koko tasani kawai it's their secret shiyasa bata fadamata ba Abu na biyu data fuskanta gameda Aysha shine tana soyayya, soyayya mai matuqar wahala Da farko kafin tasan komai tana lurada kullum idan suna tare wani na bugowa Aysha waya Idan tazaro wayar taga shine sai alamun tsoro ya bayyana a fuskarta, saita daga kiran cikin rawar jiki tana magana cikin kame kame Kuma duk sadda suka gama waya sai taga wani expression marar dadi a fuskarta Da farko tayi tunanin da Mussadiq ne suke wayar don dama taga alamun ba mutunci ba ya isheshi sai daga baya ta fuskanci ashe saurayi ne Soyayya take da saurayin datake matuqar tsoro kuma abin daure kai aciki shine tana sonshi sosai amma kuma tana tsoronshi don ko waya ya kirata sai taita jawo addu'o'i kafin ta daga Abin na matuqar daure wa zee kai don ita tunda take bata ta6a ganin irin haka ba Amma sai tayi ignoring tayi kamar batasan me take ciki ba don batason shishiginta ya cika yawa don haryanzu she's not done with her mission don tasa a ranta ko tayaya ne saita samu information akan mutuwa ko 6acewar Deen Tun zee na kauda kai akan Hakan har wata rana tayimata magana "Aysha, wai meke tsakaninki da wanda kuke waya ne? Abin da daure kai, kullum idan yabugo sai inga kinshiga fargaba" Ajiyar zuciya Aysha ta sauke sannan tace "Saurayi na ne ummie" "saurayinki? Saurayinki kike tsoro?" Dan murmushi tayi "ba tsoronshi ba nake, masifarshi ce banaso" "masifa yake miki?" "kusan Hakan, he like complaining alot, komai sai yayi complaining, dana complaining da wanda bekai ayi complaining ba, wlh har tsoron ganin kiranshi ya shigo wayata nake" ta qarashe tana dafe goshinta "complaining? Wani abu kike masa da bayaso?" "not at all, kawai shidai akwai shi da neman dalili dik yadda zakayi kaffa kaffa akan karkayi wani laifi bazaka tsira ba, gashi beda hqr ga kishi Yanzu jiya don ya kirani ban daga da wuri ba ya hau fushi, kira uku yaimin nikuma lokacin ina wajen Umminmu wayata kuma nabarta daki Shine fa daga baya danagani na kirashi, yama tsaya ya saurari uzuri na yaqi yahau yimin masifa daga baya ma ya katse kiran, nayi ta bugawa yaqi dagawa daga baya ma ya kashe wayar, jiya ko barcin kirki banyi ba, kwana nayi ina tura mashi load and loads of messages din ban haquri amma haryanzu yaqi saurarena, kinga yanzu na kira yashiga naci sa'a ya daga amma still be sauka ba" ta qarashe maganar cikin damuwa Tunda tafara maganar zee ke kallonta cikin mammaki, meye Hakan? Dama akwai irin wannan soyayyar? "ban gane yaqi sauka ba, laifin me kikayi masa? Daga ya kira baki daga ba? Ko babu dalili kinada right din qin daga wayar shi bare da dalili" "hmm, baki sanshi bane, ya wuce duk tunaninki abu kadan ke fusatashi" "so?" zee tafada cikin qunar rai "don abu kadan yake fusatashi sai yace zai sauke kwandon bala'i akanki? Kefa budurwarshi ce ba mata ko baiwa ba" Ganin kamar zee ta fusata yasata dafa kafadarta tana cewa "haba ummie, bafa yadda kike tunani bane, ni nasan duk soyayyar dayake yimin ce tajawo Hakan, shifa idan ya kirani ban daga da wuri ba sai yayi tunanin ko ina tareda wani ne ballantana yaji line busy, ranar mai rabamu sai allah. Tsananin sona yasamashi tsananin kishina shiyasa beson yaji koda labarine wai anganni da wani bare kallo ko magana tashiga tsakaninmu dashi. He's the jealous type don ko wani wuri natafi be saniba sai yaita kawo zargi a ranshi" "what? Kuma shine kike kiran haka da so? Idan babu zancen igiya meya kawo igiya? Definitely yana yin abinda yake zarginki dashi kenan" Cikin rashin fahimta Aysha tace "ban gane ba" "idan har zai dinga zargin kina tareda wani ko zaki yaudareshi to Definitely shima yaudararki yake shiyasa shima yake ganin kamar yaudararshi kike" Shiru Aysha tadanyi saikuma ta girgiza tana murmushi "A'a ummie, kece dai baki fahimceshi ba, idan kinga irin haka to namiji na tsananin kishinki ne kuma soyayya ke kawo kishi" "idan haka ne shima sai ya dinga gayamiki me yake ciki da kuma ina da ina zaya tunda kema kina sonshi ai kuma kina kishinshi. Wannan ai be dace ba a matsayinki na budurwarshi yana zarginki yana miki wadannan abubbuwan inaga kunyi aure?" "idan mukayi aure wadannan abubbuwan duk tarihi zasu zama, kinga hankalinshi zai kwanta tunda ya riga ya mallakeni" "bazai daina ba Aysha, śaboda shi mutum mai yawan zargi kome zakayi komin taka tsantsanka saiyaji zarginki a zuciyarshi ko yaya ne, kuma irinsu sai kiga basu cika Gaskiya ba shiyasa suke ganin kowa marar gaskiya" "kibar cewa haka Ummie, ni nasan Umar nakuma yarda da soyayyar dayake min, insha allah da munyi aure komai zai wuce" "Hmm, banga alama ba Aysha, mutumin dayake miki masifa kamar 'yarshi kafin ya mallakeki Kiyi tunanin me zai dinga yi nan gaba idan ya mallakekin, Gaskiya wannan ba mijin aure bane" "ummie kibar fadin haka, ke bakisan soyayya bane shiyasa" tafada convincingly Dan murmushin takaici zee tayi "wannan ba soyayya bace Aysha, wannan wahala ce, Umar ko mema sunanshi ba sonki ba yake" "you know what? Mubar maganar nan don Allah, bazaki ta6a ganewa ba, wanda be ta6a soyayya ba bazai gane yadda take ba, so Mubar maganar watarana idan kika fara zaki gane abinda nake nufi" Shiru zee tayi tana kallonta ganin tama raina mata hankali, wai batasan soyayya ba, lallai ma. Kyaleta tayi kawai ta fita harkar soyayyarta Saidai kullum da 6acin ran abinda ke faruwa a wannan wahallaliyar soyayyar take kwana Abin ma gaba gaba yakeyi don kusan Koda yaushe saiya saiya 6ata mata rai, abin dai gwanin haushi wani sa'in zee Saitaji kamar taita marin Aysha don takaici Kwata2 bata iya ganin laifin Umar duk abinda zaiyi mata, gata very timid daya fara yimata masifa sai tayi shiru ko wani lokacin ma taita hawaye Sosai Hakan ke qonama zee rai musanmman idan taga kwata2 Aysha takasa daukan haske akan cewa abinda Umar keyimata ba soyayya bane, soyayya tariga ta rufe mata idanu gani take duk abubbuwan dayake mata duk cikin so ne (wannan labarin ya faru a real life, I just feel like sakoshi a labarin nan ne, akwai masu irin wannan wahallaliyar soyayyar, yar uwa duk mai treating dinki irin Umar ba masoyinki bane Duk wanda zai kira wayar ki kiji faduwar gaba ko tsoro maimakon kiji sanyi a ranki to ba masoyinki bane Duk wanda magana mai dadi bata shiga tsakaninku a matsayinku na masoya sai akasin haka to baya sonki. Ki taimakawa rayuwarki ki rabu dashi, karki yaudari kanki akan idan kukayi aure zai chanza ko zaki iya chanzashi Aure yasha banban da hangen da Mafi yawan yanmata ke mashi, wata rayuwa ce mai zurfi wanda bazaka santa ba saika shige ta Masu qaunar juna da nuna tsantsar kulawa da juna kamar zasu hadiye juna ya suka qare bare ire irensu Aysha da Umar. Wanda Hakan tafaru daita nacan yanzu tana regretting, a lokacin an nunamata Gaskiya an gwadamata amma so ya rufe mata ido taqi ganewa gashi yanzu tana ganewa in a hard way Duk namijin da baya regarding feelings dinki baya kuma gudun 6acin ranki tun kina gidanku to ba mijin aure bane yar uwa, ki roqi allah ya chanza miki da Mafi alhairi, idan kina sonshi dayawa ki roqi allah ya sassauta miki don wlh wahala zakisha, Allah yasa mu dace🤲🏻) Tun zee na jin takaicin Aysha har tafara bata tausayi don ta lura soyayya ke dawainiya daita, so ya riga ya rufe mata ido bata ganewa Hakan yasa tafara Binta da lallami tana qoqarin fahimtar daita don harga allah tanajin Aysha har can qarshen zuciyarta, tana jinta kamar yar uwarta ta jini amma ina? Wanda yayi nisa bayajin kira Wani irin makahon so take yima Umar wanda fuskantar Hakan dayayi yasa yake mata abinda yaga dama don yasan babu abinda zata iya saboda tana tsananin sonshi (wannan ma na daya daga cikin illolin nunama namiji so dayawa, bawai karki nuna mashi soyayya ba A'a karki nunamishi irin zurfin da kikayi acikinta, Kiyi saisa saisa karki bari ya fahimci yayi miki mugun kamu don idan soyayyar mace ta fito fili harta dara ta namiji to soyayyar zata zama very boring to him, zaki ficemashi a kai dukda kau shima yana sonki din, haka maza suke, da alamu ma sunfi son masu garasu sosai, maza mutanen mu😆) Watarana suna zaune as usual suna labari cikin nishadi kira yashigo wayar Aysha Ganin yadda ta waro idanunta cikin tashin hankali kawai yaba zee amsar wake kiranta Kauda kai tayi gefe tana jin ranta na 6aci Tana jin sadda Aysha ta daga wayar tayi sallama cikin low calm voice har wata nutsuwa ta musanmman takeyi idan suna waya Batasan me suke cewa ba don da larabci suke magana har tagama wayar. Tayi mammakin gama wayarsu da wuri don ba Haka yasaba ba, suna dan dadewa suna waya kamar abin arziqi nan kau shegen masifarshi yake zazzagemata ta waya Jin Aysha ta kamo hannunta yasata dagowa ta kalleshi Ganinta tayi Duk a burkuce yanayin tsoro a tattare daita Hakan yasata cewa "meya faru ne?" Hadiye wasu yawu Aysha tayi sannan tace "Ummie, wai cewa yayi nafito gashi can harabar school, am scared, bansan dame yazo ba, muryarshi doesn't sound good" Tsayawa zee tayi tana kallonta, wai saurayi yakawo mata ziyara take haka kamar wanda zata inda za'a yankata Rufe Littatafan gabanta zee tayi sannan ta miqe tsaye "muje" tafada tana kallonta "ina?" inji Aysha tana kallonta itama fuskarta pale with fargaba "rakaki zanyi" tabata Amsa Sauke wata nannauyar Ajiyar zuciya Aysha tayi sannan itama Saurin tashi ta dauki jakkarta ta Rataya tace "muje" Tana lura da yadda Aysha ke sauri a tafiyarta har tana dan hardewa da alamun kila batason su jima basu isa Wurin ba yaji haushin sun shanyashi Yitayi kamar bata gane nufinta ba ta cigaba da normal tafiyarta, sai jitayi tana son ganin wanda beautiful rich mace kamar Aysha keyiwa rawar qafa haka Daga nesa suka hangeshi zaune bisa booth din arniyar motarshi da alamu shima dan masu shi ne kamar dai Aysha Har suka qarasa wajen tana kallon bayanshi don baya yabasu Sallamar Aysha ce yasashi Dagowa daga danne dannen dayake a waya ya juyo garesu Kallo daya zakayimashi kasan shima balarabe ne don the same skin colour gareshi da Aysha Saidai baida kyau sosai, farinne kawai saikuma kyan fatarshi wanda da alamu harda hutun dayake ciki yabata gudunmawar glowing Dama da murtukaken fuskarshi ya juyo amma ganin zee yasa yadanyi jimm yana kallonta cikin yanayin rashin fahimta sannan ya kalli Aysha cikin son qarin bayani Cikin fara'a Aysha tafara gabatar da zee da itama ta Hade rai cikin larabci sannan ta juyo ta kalli zee tace "Ummie meet Umar, my love" Jitayi kamar ta kwadeta don haushi ganin yadda take wani rawar kafa wajen introducing din amma saita daure ta dago kai ta kalli wanda aka kira Umar na 2secs sannan ta kauda kai tana dan ta6e baki tayimashi sallama Kamar bazai amsaba shima saiya amsa sama sama sannan ya maida hankalinshi kan Aysha kamar dama jira yake yafara yimata magana da larabci cikin fada fada Tsayawa zee tayi tana kallon ikon allah don yamaqi tsayawa yaba Aysha din dake son yin magana damar yin maganar data fara saiya katseta yanayi yana watsa hannuwa kamar wani ubanta Hakan ba qaramin 6ata ran zee yayi ba dukda batasan me suke magana akai ba Amma ko don ita datake baquwa acikinsu kuma baquwar budurwar shi yaci ace yaji kunyar masifeta a gabanta Hakan yasata taka mashi burki a fusace "Hey mr man! Meye haka? Zaka tusa mutane gaba kana masu ihu?" tafada cikin harshen turanci rai a 6ace Dakatawa yayi ya tsaya yana kallonta kamar a mammakince sai shima a harshen turanci yace "Me kika ce?" "cewa nayi meyasa zaka tisa mutane a gaba da ihu? Waye diyarka anan, Is this also in your manners of speech" Riqo hannunta zee taji anyi ta juyo taga Aysha ce idanunta fall hawaye Haushi yaqara kamata ta fizge hannunta daga riqonta tana cewa "dalla kyaleni, waye diyarshi? Waya haifa anan dazai tisamu agaba da ihu?!" "who are you?" yafada yana jin zuciyarshi na qara 6aci "kai ka cancanci wannan Tambayar, waye kai daxaka tisamu gaba da haushi!" "Ummie!" inji Aysha da dan qarfi hawayenta na gangarowa Matsawa baya tayi ganin tana niyyar riqomata hannu cikin 6acin rai tana cewa "dalla karki ta6ani, kai waye dazaka tisata gaba kana mata masifa kamar ubanta? Haihuwarta kayi? Ko baiwarka ce? Zaka kwaso jiki kazo har school kasameta kacimata mutunci, did you even have conscience?" Afusace yajuya kan Aysha yafara magana cikin larabci Katseshi zee tayi da "look, ba ita tayimaka ba ni nayi maka, ni zaka kalla kayiwa magana da yaren dazan gane ba ita ba!" Juyowar yayi ya kalleta cikin turanci shima yace "kinsan ko meke tsakaninmu zaki shiga tsakaninmu? Kinsan ko wanene ni?" "waye kai banda wanda besan darajar mace ba, wanda be darajja soyayyar da akemishi, babu abinda ke tsakaninka daita sai mugunta kuma baka cancanci soyayyarta ba!" "Zainab!" inji Aysha saikuma ta fashe da kuka Cikin tsananin 6acin rai Umar yake nuna kanshi da yatsa "ni.. Ni kike cewa haka?" "eh kai, sai me?" Juyawa yayi ya kalli Aysha dake kuka har lokacin yace "infact, it's over!" Ya juya Afusace zai bar wajen "Umar!" Aysha tafada da qarfi tana yunqurin Binshi Riqo hannunta zee tayi tana cewa "let him go Aysha, so what?" Fizge hannunta Aysha tayi daga riqonta itama a fusace tana cewa "leave me alone!" Sannan tajuya ta nufi Umar dahar yashiga mota ya rufo kofar Kwankwasa glass din gefen shi Aysha take tana cewa ya bude mata cikin kuka amma ko kallonta beyi ba ya tada motar yaja da qarfi ba don zee ta fizgo Aysha ba da saiya bigeta "Umar!!" tasake kiran sunanshi tana kallon motarshi data nufi gate aguje Binshi tasoyi sai taji takasa yin gaba saboda an riqeta Juyowa tayi taga zee ce riqe da ita Hakan yasa ta fizge jikinta daga riqonta "take your hands off me!" Qara matsowa zee tayi tana qoqarin yimata magana saita daga mata hannu "stay away From me!" Saita juya ta nufi hanyar fita daga school din itama Binta da kallo zee tayi tana jin zuciyarta na suya And on her very eyes her only link to Deen's problem is gone... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:41 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *065* *THE GIRL* Iya dagulewa ran zee ya dagule, tsayawa tayi tana kallon hanyar da Aysha tabi ta fita cikin dacin rai Juyowa tayi taga har few mutane sundan taru suna kallon abinda yafaru Janye idanunta tayi daga kansu ta wuce cikin school din feeling very bitter Har aka tashi daga school din ranar ran zee na a dagule gashi bata qara ganin ko wulgin Aysha ba a school din Drivern da Aymaan ya samomata yazo wanda shi ke maidota gida don mostly Aymaan dama ke kawota school din Shiga motar tayi suka bar school din cike da dacin rai. **** "wow, this is crazy! Kodai asiri yayi mata?" inji batool tana kallon zee da haryanzu fuskarta ke a dagule "ba asiri bane, kawai tsantsar soyayya ce, tana sonshi ne over" "kutt... Wallahi ba'ayi namijin dazai juyani tun ina gidanmu ba, wannan ai idan tashiga gidanshi tashiga uku, tun yanzu yana mata iko kamar ubanta ina ga tashiga gidan nashi yasan ya mallaketa?" "abinda nake gwadamata kenan taqi fahimta, you have to see yadda yakeyi mata, ko babu komai ai kasancewata a wajen yakamata ya ragamata amma kinga yadda yake mata? Not minding who and who is watching?" "irinsu ne zakiga ko bayan auren ne basajin komai su duzgata agaban mutane, sai kiga mutunci ya zube hatta abokanshi ma sunsan batada wata daraja awajen shi" Ajiyar zuciya zee kawai tayi batace komai ba Tunani take ace misali Deen ne Hakan, Deen ne keyimata Hakan, zata iya jurewa, kai da kamar wuya, duk son datake mashi bazata iya jurar wulaqanci daga wajenshi ba Saidai son ya kasheta "yanzu meye mafita? Gashi kince ta tafi cikin fushi, idan tayi deciding ta rabu dake fa? Ya kenan?" Shiru zee tayi bata amsa ba sai kafe waje daya datayi da idanu "kema da kin kyaleta kawai, gashi yanzu Hakan na neman ta6a friendship dinku wanda wargazewar abotarku daidai yake da wargazewar shirinmu, gashi dama bamu samu abinda mukeso ba har yanzu" "ni ba damuwa ta wargazewar abotar mu ba, damuwata halin dazata tsinci kanta aciki, yanzu da nan gaba Batool, yes nafara abota da Aysha saboda wani dalili nawa na kaina amma yanzu ina jinta a raina fiyeda yadda ya kamata na jita Bana regretting abinda nayi don shine daidai Koda abotar tamu zata watse bazan damuba kamar yadda zan damu idan Aysha tayi ending up da Umar a matsayin miji Kwata2 they dont make a match Aisha is very cool, kamar Deen. Batada hayaniya, very jovial and timid. While Umar masiffafene na gidan gaba gashi he doesn't have regard to her feelings, yanzu yana mata Haka yana mata masifa kamar zai rufeta da duka wa keda tabbacin idan sukayi aure bazai dinga dukanta ba? Kwata2 Aysha ba match din Umar bane" Ajiyar zuciya batool tayi tace "to ya zakiyi? Idan allah ya qaddara shine mijinta fa? Ya zakiyi? Ya zatayi?" "insha allah bashi bane ba ma, insha allah mijinta na nan tafe, very nice and kind person wanda zai sata farinciki akoda yaushe, insha allah..." Har dare Aysha na maqale a ran zee, tunani takeyi ko a wanne hali take ciki yanzu Qila ma tana can tanata kiran wayar shi baya dagawa kokuma tana mashi text upon text kamar yadda tace tana mashi idan suka 6ata Wayarta tajawo tashiga number Aysha din tashiga rubuta mata short text message _*wani lokacin abinda zuciya keso baya zama alhairi ga mutum.. Wani sa'in you have to let go what your heart crave for saboda ba alhairi bane a gareta*_ _*No guy is worth your tears and when you find one that is, he won’t make you cry*_ _*ki roqi allah yayimiki za6i na alhairi, karki roqeshi akan lallai sai za6inki zai mallaka miki*_ Turamata tayi sannan ta tura wayarta qarqashin pillow ta kwanta ta lumshe idanunta trying to catch some sleep Ta jima tana saqa da warwara sannan barcin yayi nasarar dauketa. Washegari haka zee taje school da yaqinin ganin Aysha suyi magana Saidai har suka tashi daga school din bataga ko mai kama daita ba, takira number ta ma bata shiga, haka ta haqura tana jin ranta babu dadi Wasa wasa Saida sukayi kwana uku basu hadu da juna ba tun zee na damuwa tana kiran wayarta da bata shiga always harta haqura ta qyaleta kawai A cikon kwana biyar da yin abin watarana zee na zaune cikin class tana duba wani Littafi taji an dafata a kafada Ga mammakinta tana Dagowa sai idanunta sukaci karo da Aysha Tsayawa tayi tana Binta da kallon mammaki don bata ta6a expecting itace ba Harara Aysha ta gallamata sannan tace "Wurin zaman ma baza'a bani ba?" Dan murmushi zee tayi saita matsamata cikin tsokana tana cewa "Wata sabon gani, yan yaji an dawo" Hararar wasa Aysha tayimata tana zama tace "kuda kukaqi zuwa biko" Dariya zee tayi tace "biko na nawa, a school dinnan babu inda ban shiga ba da sunan nemanki, shikenan daga samun dan misunderstanding kinyi cutting off dani ko wayarki bana samu" Murmushi Aysha tayi tace "ba Haka bane, dubeni kiga, bakiga na chanza ba?" Sai a lokacin zee ta tsaya ta kalleta dakyau sai taga tadan rame tayi pale "ya sallam, meya sameki? Naga kamar kin rame" Murmushi Aysha tayi tace "ba kama bane, na rame. Yanzu haka ma da sauqi. Tun ranar da muka rabu nake rashin lfy" Wara idanu zee tayi saikuma tayi alamun fuskar tausayi "meya sameki? Kuma shine ko Kiyi informing dina?" Murmushi Aysha tadan sakeyi sannan tace "ni tun washegarin ranar ban qara sanin inda wayata ba take sai jiya, tayaya zanyi informing dinki to?" "to meya sameki?" Murmushi kawai Aysha tayi Dan Wara idanu zee tayi tace "badai saboda abinda yafaru ba?" Dan murmushi tasakeyi tace "it doesn't worth it, right?" "tell me its not because of it" inji zee tana kallonta Wani murmushin taqara yi sannan tace "sadly, it is" Shiru zee tayi tana kallonta not knowing what to say "Zainab, in gayamaki wani abu?" Kada mata kai tayi still looking at her "tunda nake ban ta6a yarda da wata ba ko inji mutum ya mugun kwantamin kamar ke ba, saina dinga jin kamar na dade da sanin ki, sai na dinga jin kamar akwai wani bond daya hadamu tare da daddewa tunma kafin haduwarmu" Shiru zee tayi still looking at her batareda tace komai ba "shiyasa naji bana iya rabuwa dake dukda abinda kika yimin yakai na rabu dake din don da wata ce I won't have anything to do with her anymore, a dalilin abinda kikayi nayi rashin lafiyar kwana uku" Zee dai har lokacin bata ce komai ba kuma bata daina kallonta ba "Zainab kowa da irin jarabtar da allah yayimishi, ni tawa kenan. Kowa sai yace Umar baya sona while ni nasan yana sona Everyone was against soyayyarmu, yayana, ummie na dukda dai bata nunawa fili but itama batason relationship dinmu and now you. Hakan yaci ace na haqura ko? Amma nakasa, I love Umar fiyeda tunanin kowa, nima bansan yaya akayi ba kawai I know I can't live without him kuma na gasgata Hakan a kwanan nan Can you believe don Umar yace it's over na kwanta rashin lafiya harda qarin ruwa? Wannan yaci ya nuna muku ba laifina bane, it's my heart's" "Aysha, nasani. It's hard to forget someone you love musanmman first love Nima I was once in your shoe, infact am still there Amma mine is totally different From yours Nawa yana sona, a zuciya akuma aikace Yana gudun 6acin raina, yana son farincikina, baya iya fushi dani, baya iya hurting feelings dina amma naki fa? Ke kanki kinsan wannan abinda kukeyi ba soyayya bace, ke kanki kinsan ke kadai ke sonshi shi baya sonki" "yana sona ummie, nina sani, kawai baya gwadawa ne" "to meye amfanin soyayyar da ba'a gwadawa? Haka zakuyi ta yafiya Aysha, bazaki ta6a sanin dadin soyayya ba idan kuka cigaba da tafiya a Hakan, kuma juma'a mai kyau tun daga laraba ake ganeta, your marriage life depends on your love foundation" Kada kai Aysha tayi sannan tace "ki tayani da addu'a, naga message dinki na rannan and I decided zanyi yadda kikace, zan dinga addu'a allah ya za6amin mafi alhairi ko Umar ne ko bashi ba sa6anin da danake addu'ar allah ya mallakamin shi" "Good, idan ma bashi bane ki roqi allah ya sassauta ko ya ciremaki sonshi gabadaya daga zuciyarki, komai mai yuwuwane a wajen allah, sai kiga abin yazama tarihi" Kada kai Aysha tayi tana murmushi "thanks, zanyi Hakan insha allah, nima bada son raina nake wasu abubbuwan ba Amma insha allah zan dage da addu'a, kema ki tayani" Itama zee saita kadamata kai "insha allah, ukhtie" Murmushi sukayi atare Buga tagumi Aysha tayi da hannu daya "bani labari" "labari? Labarin me?" inji zee "labarin soyayyarki, daji zaiyi dadi naji kince he loves you so much beson ganin 6acin ranki" Dan murmushi mai ciwo zee tayi ta maida hankalinta kan littafin gabanta Dauke littafin Aysha tayi tace "saifa kin gayamin, I love hearing love stories musanmman wanda akwai kulawa sosai aciki, tell me, waye very Lucky guy daya samu mallake zuciyarki" Dariya zee tayi tace "hmm is he really Lucky?" "sosai ma, keta daban ce nasan shima nasan na daban ne, special people always spiced up" Dariya zee tayi afili a zuciyarta kuma tana cewa 'yeah, he's special kamar yadda kowa na ahalinshi yake including you' "inaji" inji Aysha tana qara buga tagumi "to ni ta ina zan fara?" "ki fara kota ina ne" tabata Amsa "ok, bari nafara ta ranar damuka fara haduwa" Gyara zama Aysha tayi cikin son jin labari fuskarta beaming with smile "Ranar wata juma'a ce...." Nan tashiga bata labarin soyayyarsu da Deen. Komai ta gayamata babu abinda ta rage mata har takawo daidai ranar introduction dinsu saita tsaida labarin iya nan "wow! So so romantic! Mutumin harya shiga raina, very cool guy dama ana samun irinsu a duniya?" "why not? Gaki? Komai naku na hallaya iri daya, you're also cool kamar shi, inajin shi kika biyo" inji zee Dariya Aysha tayi tace "ta yaya xa'ayi na biyoshi? Mutumin dabamu hada komai dashi ba? Honestly speaking soyayyarku ta burgeni, dama mune Hakan" Murmushi kawai zee tayi mata "yanzu ankusa engaging din naku?" Girgiza kai zee tayi ahankali "ba'ayi ba? Wait ma, meyasa yanzu kike Dubai shikuma yana Nigeria?" "Destiny" tafada ahankali tana kallon Aysha Jikin Aysha ya danyi sanyi ganin yanayin datayi maganar "bangane ba, where is he?" "I don’t know either" tafada tana jin komai na dawomata sabo "I don’t get you" inji Aysha cikin rashin fahimta "he's.. Gone" tafada cikin murya mai sanyi "on our introduction day... Ya tafi.. Wai maybe forever wai maybe not, Hakan ya rubuta a takardar daya bar min" "Zainab are you crying?" inji Aysha ahankali "nasaba, I do that everyday" tafada tana tsane fuskarta "ina yatafi? Meyasa ya tafi?" "I don’t know" tafada tana kallonta trying to control her emotion "tell me, gayamin komai" Shiru zee tadanyi sannan tace "Ranar na wayi gari da matsanancin farinciki, I can't believe ranar family din Deen zasu zo suga nawa kuma mainly akan maganarmu, wannan tunanin nasani shiga shauqi marar misaltuwa Ranar nayi wanka na zauna ina cancada kwalliyata ina humming best waqa ta ina tunanin izuwa lokacin suna can suna tattaunawa akanmu, kwatsam sai aka bubbugo kofata mummy tashigo rai a jagule..." Nan tashiga bata kingin labarin da bata bata ba daga qin zuwan mutanen Deen har zirga zirgar da akayi tayi gidansu ana taddawa rufe, har zuwan ta da kanta, har bata wasiqarshi daya ajiye mata da akayi har collapsing datayi lokacin data gama karanta ta har farkawarta bayan kwanaki biyar, har rayuwar quncin data cigaba dayi daga lokacin har zuwan qanwar daddynta Nigeria da shawarar tahowa daita nan datayi har kawo yanzu (Saidai ta 6oyemata gano asalin Deen dasukayi dakuma dalilinta na zuwa school dinnan datayi) Sosai labarin zee ya ta6a Aysha sai gashi itama tana hawayen "why? Meyasa ya tafi?" tafada cikin hawaye "I don’t know" itama zee ta bata amsa cikin hawaye "yanzu dama kina cikin wannan yanayin? Bakiyi kama da mai wata matsala ba" "yes, ba lallai bane nayi kama dame matsala ba physically amma idan kika ga zuciyata you'll cry for me, its still broken" "sorry" Aysha tafada cikin tausayawa Kada kai zee tayi batace komai ba sai tsane hawayenta data cigaba dayi "kowa da irin qaddararshi, wataqila kema ba alhairi ne ba agunki" "wataqila.." inji zee itama "kinada pics dinshi? Inason ganinshi" Gabanta yafadi, wai meyasa duk wanda taba labarin shi sai yace yana son ganinshi? Lallai akau ganinshi agareta bamai yiwuwa bane, not now. "banida, duk na gogesu, babu abinda zanyi dasu kuma, hotonshi na cikin zuciyata ya isheni" Kada kai tayi tace "hakane, amma karki dora mashi laifi ummie, karki tsaneshi, allah kadai yasan dalilin tafiyarshi, don’t judge him please" Murmushi kawai zee tayi sai tace "I won't, dafarko naso yin Hakan amma daga baya da nasan wasu abubbuwa gameda shi sai nafara tunanin qila it's not his fault din" "Me kika sani gameda shi?" inji Aysha Murmushi zee tayi tace lakaci hancin Aysha cikin wasa "zan gayamaki.. But not now, muje mu nemo wani abu dazamu sama cikinmu, am hungry" tafada tana shafa cikinta Murmushi Aysha tayi tana tashi tsaye "muje, nima kina fadin haka naji nima cikina yayi min warning alarm" Dariya sukayi atare suka fita daga class din suna tafe suna fira cikin annushuwa Daga ranar suka sake qullewa kamar da kai harma fiyeda da don sau da dama Aysha na bugowa ta hada zee da umminsu su gaisa, ranar farko da zee ta gaisa da Umminsu Saida taci kuka kamar zata shide Ba mahaifiyarta bace amma taji wani iri sosai a zuciyarta kamar itace din bata ta6a jin muryar mahaifiyarta ba shekara da shekaru, muryar Ummin sak muryar Deen, very cool. Aysha tasha tambayarta yaushe zatazo gidansu amma Saidai tayita yimata kwana kwana kullum da excuse din dazata bata harta haqura ta qyaleta A bangaren soyayyar Aysha da Umar kau bata qara sanin yaya suke ciki ba don Aysha tabar waya dashi a gabanta, takuma bar bata labarinshi amma tasan confirm suna tare. Watarana zee na zaune library da Aysha suna fira littatafai a gabanta da alamu ma karatu sukeyi suka zarce firar. Wayar Aysha tayi beeping Dauka tayi ta duba sai gani zee tayi fuskarta ta washe Yar qarar murna tayi sannan ta jefa wayar cikin jakka ta miqe tsaye "hey, meya faru?" inji zee "zomuje zaki gani, I have a very huge suprise for you" tafada tana damqo hannunta Tashi zee tayi tana bin Aysha dake janta "wait, littatafanmu fa" Sai a lokacin itama ta tuna, saurin tattarasu tayi ta jefa a jakka taqara Kamo hannunta "muje" "wai ina zaki kaini? Inji dai ba siyar dani zakiyi ba" inji zee cikin Dariya tana bin Aysha dake janta har lokacin "eh mana, siyar dake zanyi kowama ya huta" Aysha tabata Amsa tana cigaba da janta Dariya zee tayi tace "ko duniyar nan aka tara basu sayena yarinya" "kima godewa allah idan kika samu aka tayaki Riyadh 100" Aysha tabata Amsa suna nufar harabar school din "kutt... Nafi qarfin haka yarinya kema kin sani" "ok just wait and see, zakisha mammaki" Cigaba da jan hannunta tayi suna tafe suna fira suna Dariya har suka qaraso parking space din "Akhie!!!" Aysha tafada da qarfi cikin yar muryarta tasaki hannun zee data ja burki babu shiri tanufeshi da sauri Juyowa yayi daga basu bayan dayayi yana waya daidai lokacin da Aysha ta fado ajikinshi Cak komai nata ya tsaya dasukayi ido hudu dashi kamar yadda shima a 6angaren shi komai nashi ya tsaya Cak a sanadin ido hudun dasukayi da wanda be ta6a tsanmmanin gani ba _the girl_... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:41 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *066* *THE GIRL 2* Jitayi kamar Kaffafuwanta na narkewa ahankali, sotake ta juya da sauri tabar wajen amma kaffafunta sunqi bata hadin kai "Akhie, ashe dagaske zakazo? Banyi tunanin dagaske kake ba da kace zakazo, am very happy wlh" inji Aysha cikin tsananin jindadi Ganin kamar hankalinshi ma ba akanta ba yake yasa ta juya tana kallon inda yake kallo Dan buda idanu tayi saikuma tayi Dariya "Akhie, gatanan, itace wanda naketa baka labari, my bestie... Ummie meet my brother" Kasa cewa komai zee tayi saima sauke idanunta datayi aqasa jin yadda nashi ke yawo akanta Dukda idanuwan nashi toshe suke da shade as usual "oho? Wannan ce bestie din taki da kike bani labari?" inji Mussadiq yana daga gira daya sama "eh yaya, itace" inji Aysha cikin jindadi "wow, tanan kenan ta 6illo, taga wancan hanyar babu riba shine ta biyo tanan" inji Mussadiq yana mata wani kallo Zee da gabanta keta faduwa ta dago ta kalleshi, tama rasa abinda zatayi ko zatace "I don’t get you Akhie" inji Aysha cikin rashin fahimta "ita ai ta gane.. So miss spy tanan kika 6illo kuma?" yafada yana maida akalar Tambayar ga zee Kasa cewa komai tayi still sai kallonshi datake tanason lalubo abinda zata fada amma it seems kwalwarta ma ta daina aiki na wucen gadi "Yaya wai yaya kake wasu magangganune da bama fahimta?" "kece bakya fahimta my dear little sis, ita karr take. Dafarko kinzo min a suffar almajira kinzo kinamin kuka kina min yaren da bana ganewa a tunaninki am so dumb da zan fada tarkonki, da Hakan beyiwu ba sai kika chanza dabara kika biyoni wancan supermarket din kina min la6el, shima da kika ga babu riba sai kika biyo ta innocent sister dita ko?" Tunda yafara magana zee ke girgiza kanta hankali tashe Saidai still bakinta yakasa buduwa bare tayi qoqarin kare kanta Cire shade din idanunshi yayi ya matso dab da ita "for the last time who are you?" yafada cikin low but dangerous voice Matsawa baya zee tayi tana kallonshi shima a idanu jikinta na rawa "I said who are you!" Yafada da tsawa tsawa "Akhie?" inji Aysha datayi saurin shiga tsakiyarsu "meye haka yaya? Dama ka santa ne?" "ita zaki tambaya, wai Aysha why are you too dumb, I warned you akan yin abokai, didn't I?" yafada a fusace "you do, amma nima ai bana abokai, wannan kadai ce.." "shut up kafin na wankeki da mari! Cewa nayi never make a friend bance Kiyi ko daya ba, saboda I knew you're too dumb to know who your enemies are" "yaya wannan fa babu ruwanta, bama yar qasar nan bace, she's From Nigeria, sunan Umminmu gareta, itace ta tsintar min Bracelet dina, da ita muke maths lesson har nake gane wasu abubbuwan, she's very nice kuma she's there for me akan komai" "oh? Kema sunan Ummin tace maki sunanta?" Saikuma ya nufi zee daketa raba idanu Tundazu a fusace "who are you?!" Yafada yana Kamo wrist din hannunta Fara qoqarin kwacewa tayi amma takasa "of all lies dakikeyi babu wanda yafi 6ata min rai kamar liqama kanki pure sunan mahaifiyarmu dakikeyi don kisamu shiga awajen mu, who the hell are you?!" "let go of my hand!" zee tafada tana qwace hannunta Dakyar daga riqonshi, idanunta har sun duri ruwa "yar Nigeria? Dama Nigeria is full of corrupt people, Saidai albishirinki, acan ne zakayi abu kaci bulus ba anan ba! Anan din ma ba irina ake ta6awa ba atafi scot-free! Da alama wadanda ke turoki sunsan ko ni wanene kece baki sani ba shiyasa su suka kasa zuwa wajena Saidai su turoki, amma kema zan tabbatar kinsan ko ni wanene!" "ni babu wanda ya turoni, nafada maka Hakan can baya, yanzu ma na fadi Hakan kuma ko gobe muka sake haduwa Hakan zan fadamaka!" "ni kike ma tsawa?!" Yafada yana charging towards her Aysha tayi saurin shigewa tsakiyarsu again Dayake ruwa ruwa ce itama har idanunta sun duri ruwa "Akhie wai meye haka? Ummie dama kinsanshi ne?" tafada tana maida akalar tambayar ga zee Girgiza kai tayi sai kuma ta shiga Kada kai, duk ta rude "look Aysha, n.. Na ta6a ganinshi a wani supermarket, I.. I mistook him for someone, nayi tunanin wani ne dana sani shiyasa nayi mashi magana.." "a lokacin idanuwan ki sun daina aiki ne? Koko kwalwarki tasamu matsala ne dahar zanyi miki kama da wani, Hakan yasa har kika zube a qasa kika kama kaffafuna?" Runtse idanunta tayi gam tanajin zuciyarta na wani irin zafi kamar ana gasamata ita a oven Wasu zafaffan hawaye suka silalo ta qasan ruffafun idanunta "Are you crying? Save that crocodile tears, kibari sai kin ganki behind bars sannan" yafada yana watsamata wani mugun glare Bude idanunta tayi akanshi dasukayi jajur sannan ahankali cikin qunar rai tace "yes, a lokacin na zube a qasa nakuma kama kaffafunka but had it been nasan kaine ko kallo bazaka isheni ba" Daga cikakkiyar girarshi daya yayi cikin yimata kallon raini hankali "really? To kinsa wanene da? Kuma dukda kin gane bani bane din kika biyoni wancan supermarket din kika yimin la6el, can you also explain that?" Izuwa lokacin zuciyar zee ta harzuqa matuqa, ita macece da bata qaunar wulaqanci ko yaya ne gashi ta lura wannan gayen ya matuqar qwarewa a wannan fannin "speak!" Yafada da qarfi yana yi kamar zai qara matsowa inda take cikin barazana Kallonshi tayi cikin fushi tace "you know what? Go to hell! I owe no one any explanation! Idan guntun qwalwarka tabaka kai nake bibiya so be it!" "what! Ni kike cewa I should go to hell?!" Yafada cikin tsananin 6acin rai don fuskarshi tafara ja ja ja ja din 6acin rai "Akhie please... Ummie Kiyi shiru please" inji Aysha da duk suka rudata Batayi shirun ba sai cewa da tayi "Go to hell nace? That's not what I mean, I mean go to hell and burn to ashes!" "what!" Yasake fada cikin qurewar 6acin rai "albasa batayi halin ruwa ba! Kai ke kama dashi ba shike kama dakai ba, kuma kamar ta fuskace don shi yanada pure heart ba kamar naka black coal heart ba!" Saurin Runtse idanu tayi ganin ya daga hannu zai kawo mata mari Itama Aysha ganin Hakan yasa tadanyi qara ta Runtse idanunta gamm Shiru sukaji Hakan yasa suka shiga bude idanun ahankali har suka budesu tarr a kansu Mussadiq ne tsaye Hannunshi maqale a iske wanda ya daga da niyyar kashe zee da mari Kallon wanda ya riqe hannun a iska sukayi wanda shima mussadiq yake kallo idanunshi na chanza launi "yaya Aymaan!" zee tafada cikin kuka tana rugawa bayanshi ta kama dayan hannunshi dayake free ta kifa kanta akan kafadarshi tana kuka mai cin rai Yarfar da hannunshi Aymaan yayi yana Binshi da wani kallon tsana da kishi "kasan wake daga hannu akan mace da niyyar duka? DABBA!" Yafada cikin tsananin 6acin rai Shima Mussadiq kallonshi yake cikin tsananin 6acin rai wanda har kana ganin yadda broad chest dinshi ke sama ke qasa ta spotless white shirt dinshi "Did you just call me an animal? Did you just insult me?!" ya tambaya yana kallonshi eye-in-eye "I don’t insult people, I just describe them" inji Aymaan shima yana kallonshi cikin ido "you brat!" inji mussadiq yana tunkaroshi mugun hasale "who do you think you are?!" Yafada yana kai mashi blow Saidai this time around Aymaan was too quick wajen tarewa "karka soma, wancan karon kaci bulus saboda wadannan kartin banzan dake zagaye dakai, yanzu kuma your empty brain yakamata ya sanar dakai kai kadai ne" Fizge hannunshi yayi a fusace yasa hannu ya tura qirjinshi wanda Hakan yasa yadanyi baya Shima rai a 6ace ya nufoshi shima ya tura qirjinshi da qarfi wanda Hakan yasa shima yin baya Saurin riqo hannunshi Aysha tayi tana kiran sunanshi itama zee ta riqo hannun Aymaan dake niyyar tunkararshi again "please Aymaan mutafi, ka kyaleshi" tafada tana qara qanqame hannunshi ganin yadda yake qoqarin kwacewa Itama Aysha kama hannun mussadiq dake son zuwa wajen Aymaan tayi ta qanqame idanunta taff hawaye tana cewa "Akhie ka kyaleshi, don Allah" A daidai nan wasu mutane hudu cikin mufti suka iso wajen I.D card din dasuka nunama su Aymaan yasa suka gane jami'an tsaro ne Hankalin zee yasake tashi "you're under arrest" inji daya daga cikinsu yana kallon Aymaan Fizge hannunshi yayi daga riqon zee a fusace yace "saboda me? Me nayi?" "idan munje station zakaji dalili, a shawararce zaifi kyau kayi shiru ka Adana duk abinda zakace har saimunje station don duk abinda kace yanzu will be use against you in the station" Hankali a tashe zee tace "sir, ba laifinshi bane, you guys should listen" "sorry ma'am, aikinmu mukeyi" Sannan suka maida kallonsu akan Aymaan da yakejin wani abu mai wuyan wucewa ya tokaremashi wuya "shall we?" suka fada suna nuna mashi hanya Hannu yasa a aljihunshi ya zaro I.D card dinshi shima yace "Dr Aymaan, gynaecologist a As-shifa'u specialist hospital. Zan biyoku amma a motata" "No.." Sukaji ance a bayansu Juyawa sukayi sukaga mussadiq ne da haryanzu fuskarshi ke jajur Zuwa yayi gaban Aymaan yana kallonshi eye-in-eye "bazaka tafi a motarka ba, su zakabi" "nafison idan ina magana da masu hankali kar mai empty kwalwa yayi min trespassing, na tsani shiga muhallin daba na mutum ba" inji Aymaan shima yana kallon cikin idonshi "zan nuna maka, zan nuna maka ni cikkaken marar hankalinne.. Arrest him!" Yafada authoritively Zee ce ta matso gaba "kaga, dani kakeda case bada shi ba, idanma arresting dinne ni za'ayi arresting" "in that case... A hada da ita" yafada yana maida shade dinshi a idanu sannan ya juya "Akhie!" inji Aysha cikin tashin hankali amma ko tsayawa beyi ba bare ya kalleta "let's go please" inji daya daga cikin jami'an yana nuna musu hanya Juyawa sukayi babu musu suka shiga binsu suna a tsakiyar su "ummie!" inji Aysha dake kuka sosai saikuma ta ruga wajen mussadiq daya shiga motarshi Saurin kama murfin motar tayi "Akhie please ka tsaidasu, gasucan zasu tafi da..." Kallon daya watsamata yasata kasa cigaba da maganar sai rufe bakinta datayi da taffukan hannu tana cigaba da hawaye "get in" yafada in a low but angry voice Bata motsa ba sai kukan data cigaba dayi "I Said get in!!" Yafada cikin qaraji wanda yayi mugun firgitata Batasan sadda ta zagaya ba ta bude dayan murfin tashiga ta zauna tana sobbing "ki yimin shiru kafin na karkaryaki!" Babu shiri tayi tsitt sai hawayen dasuka kasa tsaiduwa A fusace ya tada motar yaja a 360 Ta glass din gaba Aysha ta hangi su zee na shiga motar dasu jami'an sukazo daita Fitt sukazo suka wucesu sanadiyar gudun da sukeyi suka fice daga makarantar Itama motar dasu zee ke ciki ta maramasu baya suma suka fice daga makarantar Aysha ta baya take Juyawa tana kallon motar dasu zee suke ciki, suna kaiwa wani junction sai taga Motarsu zee ta kama wata hanya daban da wanda suke akai sun wuce Juyowa tayi ido taff hawaye da niyyar yima mussadiq magana Saidai yanayin fuskarshi yasa takasa cewa komai sai hadiye yawun datayi ta koma ta lafe a kujera tana matsar hawaye Basu dade ba suka shigo unguwarsu kasancewar ba qaramin gudu yake falfalawa ba akan titin don Hakan na daya daga cikin dalilin da yasa ummie bata barin yayi tuqi da kanshi dole saita hadashi da mai tuqashi don kwata2 be iya tafiya ahankali, on normal days dayake cikin Good mood ma ya aka kaya bare yanzu da ranshi ke a 6ace Kallo daya zaka yima unguwarsu kasan ta shahararrun masu kudi ne don ko street din wajen ka kalla shikadai saiya baka amsa A kofar wani tangamemen gate mussadiq ya taka burki wanda Saida sukayi gaba ba don seatbelt dake jikinsu ba da sai sun daki gaban motar Horn ya danna mai irin mugun tsawon nan don tunda ya danne be daga hannu ba har Saida aka wage tangamemen gate din don ko ba'a fadama securities din ba sunsan shine don dama sun haddace salonshi Dagudu wasu securities din suka nufo motar da har lokacin bata shiga ba dukda anriga da an bude gate din Juyowa yayi ya kalli Aysha dataci kukanta ta qoshi sannan cikin Hade fuska yace "ukhrujj!" Dan kallonshi tayi sai tadan share hawayenta da bayan hannu ta sa hannu ta bude kofar tafita Wining glass din wajenshi yayi Hakan yasa securities din qara matsowa suna kwasan gaisuwa "karku bari tasake fita!" Yafada cikin bada umarni Cikin sarawa suke amsawa da angama Be qara sauraronsu ba yafara dage glass din Daya daga cikin securities din yayi qarfin halin cewa "erm.. Yalla6ai ko nashigo na tuqaqa naga kamar ka gaji" Ko kallo be isheshi ba ya ida dage glass din yayi reverse da qarfi yaci taya sannan ya wuce da mugun gudu Duk bin motar securities din sukayi da kallo cikin zullumi don tabbas sunga ranshi a 6ace yake kuma tuqi a gareshi a wannan yanayin ba abu mai kyau bane, haka suka juya suka shige cikin gidan suma don dama Aysha tana sauka tashige gidan Dagudu tabarsu nan. Maimakon akaisu police station sai aka kaisu headquarter ta c.i.d bisa umarnin Sir mussadiq Saida aka amshe wayoyinsu sannan aka shiga dasu wani daki mai kama da office Saidai it's empty dai wani dogon desk da kujeru dake kewaye dashi Dafarko cewa akayi su zauna aka tafi aka barsu nan, zee banda hawaye babu abinda takeyi, shikau Aymaan kawai zama yayi ya jingina da kujera yayi folding hannayenshi a qirji yana karkada kafaffu shikadai yasan abinda yakeji a zuciyarshi ga sniffing da zee keyi akai akai dake qara dagula mashi lissafi, gashi yakasa rarrashinta don bayajin ko magana yana iya yi a wannan lokacin Suna ahakan wasu ma'aikata biyu suka shigo suma cikin kayan gida suka zauna a kujerun dake facing dinsu Gyaran murya daya daga cikinsu yayi sannan yace "zamu iya sanin sunanka?" yafada yana kallon Aymaan da ko kallo mutumin be isheshi ba "magana muke" mutumin yaqara fada I.D card dinshi na dazu yasake Ciro wa ya turamashi a gabanshi Dauka mutumin yayi ya duba suka kalli juna da dayan mutumin sannan mutumin ya maida kallonshi kan zee "kefa? Zamu iya sanin sunanki?" Qara sniffing tayi sannan tace "Zainab" "to malama Zainab da mallam Aymaan kunsan akan me ake tuhumarku?" Shiru sukayi "akan spying, mai girma sir mussadiq yana zarginku da bibiyarshi wanda yana alaqanta Hakan da leqen asiri ko mugun nufi da aka saba yiwa manyan yan kasuwa irinshi, me zakuce gameda Hakan?" Nan ma shiru "munaji" inji dayan mutumin Aymaan ne ya kallesu for the first time tunda suka shigo Kamar bazaiyi magana ba sai ya motsa baki Dakyar yace "zakuyi magana da lawyer na" Kallon juna mutanen biyu sukayi sai suka sake kallonshi "munsan da lawyern naka ai, yanzu kai muke tambaya tunda ku abin ya shafa ba lawyern ba" inji dayan, kana iya jiyo 6acin rai kadan a muryar "zakuyi magana da lawyer na, that's it" yasake fada firmly batareda ya kallesu ba Kallon juna suka sakeyi, ba don sir mussadiq yace kar ata6asu da babu abinda zai hana daya daga cikinsu fallamashi mari, babu abinda yafi basu haushi kamar yadda yake masu magana a gadarance Kada kai na farkon yayi sannan ya kalli dayan cikin harshen larabci yace mashi sutafi sai suka tashi suka fita daga wajen suka qara barinsu alone *AYSHA* Dagudu tashiga cikin qaton gidan, harabar gidan ba dai girma ba gashi qasan shimfide yake da kwalta ga flowers of different types shufke a gefe gefen titin Tayi tafiya mai nisa koko ince gudu mai nisa kafin ta isa maid entrance din gidan Saida kofar tayi scanning face dinta sannan ta bude tashige ciki "Ummie!" tafada cikin daga murya tana shiga makeken falon daya qawatu da kayan alatu ga tattausan carpet da duk takawa daya zakaji kamar zaka nutse aciki don taushi da laushi Sama tanufa tafara hawa stairs din da shima kanshi abin kallo ne da gudu Kasancewar stairs din mai lanqwasar maciji ne Saida ta dauki lokaci kafin ta qarasa saman Wani qaton falon taqara cin karo dashi shima mai mugun kyau ta wuceshi sannan tashiga passage din dazai sadata da dakin Ummie Koda ta qarasa kofar dakin ummie banda haki babu abinda takeyi don tasha gudu ba qarya Bubbuga kofar dakin tahau yi da qarfi qarfi Can aka bude kofar wata maid ta bayyana Russunawa tayi tana gaidata Saidai har tayi gaba tashige cikin dakin Wata mata dattijuwa na hanga zaune bisa tattausan carpet gefe kuma irin pillow dinnan ne masu kyau zagayayyu irin wanda akafi gani mostly a gidajen sarauta ta kishingida akai, plate a gabanta cike da yankakkun fruits wanda take dauka da daddaya tana ci "Ummie!" Aysha ta qara kiran sunanta tana nufota Saurin dagowa matar tayi ta kalli saitin Ayshar _Tsarki ya tabbata ga ubangiji mai hallitu_ (abinda nafada kenan a raina don sak fuskar Deen nake kallo a gabana, kawai banbancin shine wannan mace ce kuma tadan manyanta) Qarasowa zee tayi ta fada jikin Ummie taqara Fashewa da wani sabon kukan "subhanallilah! Ya bunatie, meya faru?" tafada a rude tana tashi daga kishingiden datake Cigaba da kukanta Aysha tayi tana qara qanqame Ummin A rude Ummie ta cigaba da Tambayar Aysha meya faru cikin harshen larabci hankalinta duk ya tashi, tuni maids din dakin suka shiga sulalewa daya bayan daya suna fita Dakyar Aysha ta samu ta tsagaita kukanta, cikin larabci tashiga cewa "Ummie, yaya ne" "yaya? Meya faru dashi?" ta tambaya hankali tashe Girgiza kai Aysha tayi tace "kawai daga zuwa saiyasa aka kama bestie ta da ita da yayanta akaje aka kulle" tafada cikin kuka "aka kulle? Bangane ba" "Ummie, wannan qawar tawa danake baki labarinta? Itace yau yaya yazo school don ya ganta don kodayaushe cikin matsa mashi nakeyi yazo ya ganta shine yau yazo amma daga zuwa sai suka kama fada wai spy ce tana spying dinshi ne wai don ya ganta wasu wuraren kafin nan, shine ita tace ba spy bace shine yaji haushi zai mareta sai yayanta yazo From nowhere ya tare sai fadan yakoma kanshi sai yasa aka kamasu aka kulle" Tunda tafara maganar ummie bata fahimci ko kalma daya nata ba din a dunqule take bata labarin Hakan yasata zama so confused "look Aysha, ki nutsu. Ki fadamin komai cikin kwanciyar hankali yadda zan gane" Kada kai Aysha tayi tana share hawayenta da bayan hannu "to ina jinki yanzu, wace qawarki kike cewa?" "wannan wanda nake baki ku gaisa?mai sunanki" Kada kai ummie tayi cikin gamsuwa "eh nagane, takwarata? To meya faru?" Cikin nutsuwa Aysha tashiga bata labarin abinda yafaru From A-z Ajiyar zuciya ummie ta sauke tana dan dafe kai "ya sallam, yanzu shikenan duk wanda ya ra6eka yazama abokin gabanka? Wannan wane irin hali ne ga bunnaya?" tafada cikin rashin jin dadin abinda yafaru Qara share hawayenta Aysha tayi tace "ummie nayi qoqarin fahimtar dashi itama tayi qoqarin fahimtar dashi amma yaqi ya saurari ko daya daga cikinmu, ita batama san shine Mussadiq al-hassan ba, batasan status dinmu ba don ban ta6a gayamata ba kawai nadai bata labarin mu ne in a simple way bance nice qanwar mussadiq al-hassan mai companies din Nurul-haqq ba, tayaya to zatayi mashi leqen asiri mutumin da batama sani ba, ni babu abinda yafi dagamin hankali kamar idan na tuna yanzu haka suna can kulle" tafada cikin kuka "kiramin shi a waya, wannan abin nashi yafara wuce gona da iri, shikenan kowa saiya dora mashi alamar zargi? Soyake ya hana kowa mu'amalla da kowa kamar yadda ya hana kanshi? Kiramin shi" "ummie kinsan bazai daga ba, ki kirashi da wayarki zaifi saurin dagawa" "miqo min ita gatacan bisa cushion, wai ina ma yake shi?" Aysha data tashi da sauri zata dauko ta amsa da "ya dai ajiye ni yatafi" "badai gudu yake ba kamar yadda yasaba, ya tafi da driver?" "bana tunanin Hakan, can dai shikadai yazo" Amsar wayar ummie tayi daga hannunta tayi dialing din number ta kara a kunne Ringing daya biyu aka daga Daga can 6angaren sukaji muryar mussadiq yana cewa "Aslm alaiki ya ummie" Dan Hade fuska ummie tayi wanda yayi mugun yimata kyau kamar dai yadda Deen keyi "wslm, ina kake?" "ina wani aiki ne ummie" "wane aiki? Aikin kama mutane da basuji ba basu gani ba?" "Ummie waya..." "kazo kasameni gida yanzu yanzunnan, fatan kajini" tafada in warning Cikin amsar umarni yace "to Ummie" Katse kiran ummie tayi sannan ta cigaba da kwantar ma autar tata hankali akan ta kwantar da hankalinta komai zai warware Sai gashi ko minti tallatin ba'ayi ba ya iso gidan "bunnaya, me kake so kazama ne? Shikenan kowa ma abokin gabarka ne? Shikenan kowa ma bazai ra6eka ko ya ra6i wani naka ba? Wannan wane irin aqida ne?" "ummie mutane ba abin yarda bane, maqiyi bazai fito da pasta manne da goshi na rubutun shi maqiyinka ne, kowa na iya zama maqiyinka" "kai shikenan baka kyautatawa kanka zato? Kalleka.. Bakada aboki ko daya saboda rashin yarda, yan uwanka ma baka zuminci dasu yadda ya kamata, kowa.. Kana iya yiwa kowa kallon maqiyi. A dalilin Hakan yasa baka bayyana kanka, anfi sanin sunanka fiyeda kai kanka, yan tsiraru kawai suka sanka, kana iya zuwa wuri kayi hidimarka kafita ba'asan dakai ba Amma dukda Hakan zargin kowa kake, anya wannan hanyar daka dauko mai 6ullewa ce?" Shiru yayi "Nan gaba waya sani qila har muma zargin mu zaka dinga yi, a dalilin wannan halin naka ko budurwa baka ta6a yi ba, ga yanmata nan masu sonka a cikin families dama abokan arziqi amma kai bama ta aure kake ba, mussadiq nima inason ganin jikana, inason ganin jininka dana Aysha kafin na mutu dukda ita mutuwa bata ga babba bata ga yaro saita dauki yaro tabar tsoho amma ai ko babu komai anfi sama babban ran fara tafiyar, mussadiq Koda banga 'ya'yanku ba zanso ganin auren ku" Jikin mussadiq yayi sanyi, dama haka yake kuma ummie tasan lagonshi data ambaci mutuwa sai komai nashi ya sure, ya tsani ummie takira ma kanta mutuwa sai yaji kamar da gaske din tafiya zatayi ta barshi kamar yadda mahaifinsu da dan uwanshi sukayi Dagowa yayi ya kalli ummie "ummie kibar fadin haka don Allah" "to ai Gaskiya ce bunnaya, kowanne mai rai saiya dandani mutuwa, kuma ita wannan yarinyar ni kaina na santa don muna Gaisawa da ita ta waya, da ba alhairi bace ba agareku da naji Hakan a jikina, tun magana ta daita ta farko ta kwanta mun, be kamata kome yazo kanka ka yanke hukunci dashi ba" "ummie sau uku kenan nake haduwa daita..." Nan ya fayyace musu yadda duk haduwarsu ta kasance "bunnaya, akwai coincidence, bayan Hakan wata haduwar ta allah ce kuma alhairi ce, ta yiwu allah keta hadaku wataqila yanada wata manufa akanku amma kayi bincike, abinda ya kamata kayi kenan tun farko bawai kaita zargi ba" "nafara, yanzu haka school din nakoma nasa an daukomin file dinta, muna tsaka da Hakan kuka kirani" "yauwa, bincike ya kamata kayi saika kamata dumu2 da hujjoji sannan zaka yanke hukunci bawai ka yanke hukunci akan zargi ba Yanzu kasa a sallamesu ka kuma basu haquri inyaso sai ka cigaba da binciken ka akansu Insha allah babu wani mugu dazai ra6eku, kodayaushe kuna cikin addu'o'ina dare da rana, kuma zaku cigaba da kasancewa cikin addu'o'ina, insha allah babu mugun dazai ra6eku" Kada kai mussadiq yayi cikin gamsuwa Cigaba dayi musu nasiha tayi mai ratsa jiki kamar yadda tasaba yimasu sannan ta sallami mussadiq akan yaje yasa asake su. *** A can gidansu Aymaan kau hankalinsu duk ba a kwance ba, driver yaje daukar zee Saidai batanan, duk inda ake saka ran ganinta a fadin makarantar ba'a ganta ba Ga shima Aymaan wayarshi bata shiga kamar dai ta zee Kuma sun kira Ahmad sun sanar dashi yaje asibitin ance shima ya dade da fita Haka dai Ahmad yaita yawon nemansu musanmman ma zee da ba koina tasani ba a garin, ga numbobinsu basa shiga Hakan yaqara dagula masu lissafi. *AYMAAN/ZEE* Suna zaune Jigum Tundazu abin duniya ya ishesu musanmman zee take jinta a matuqar takure She can't believe wai yau ita aka rufe a custody dukda ba irin wannan rufewar bace ta wulaqanci Tunda nan Wajene mai tsafta ga fili ga fresh air don akwai fankoki masu bada iska sosai aciki ga abinci mai kyau da aka basu Tundazu wanda haryanzu babu wanda ya kalleshi gashi babu duka babu zagi don tunda mutanen nan suka fita banda wanda yakawo musu abinci babu wanda yaqara Shigowa Saidai kullewa kullewa ce Koda a cikin gidan aljannar duniya aka kulleka, dole wannan right of movement din da aka tauyemaka ya dameka A 6angaren Aymaan kau abin yafi 6ata mashi rai, shi ba kulleshi din ba yafi 6ata mashi rai wanda yasa aka kulleshi dinne Gani yake bekai wannan matsayin ba, gani yake qasqanci ne Hakan mutum kamar mussadiq yasa a tsareshi dukda kau yasan ya isa yasa ayimashi fiyeda Hakan ma kuma ayi din babu yadda ya iya Amma ya rasa meyasa tun haduwarsu ta farko yaji baya son gayen, yana jin haushinshi fiyeda tunani shiyasa yake ganin tsareshi da akayi ta dalilin shi ba qaramin qasqanci bane a gareshi Suna ahaka sukaji ana bude kofa Babu wanda ya dago acikinsu bare ya kalli mai shigowar "kuna iya fitowa" inji wanda yashigo din Dagowa sukayi atare suka kalli mutumin sai kuma suka kalli juna da alamun tambaya "you're free, zaku iya fitowa" Wata nannauyar Ajiyar zuciya zee ta sauke tana jin sanyi a zuciyarta shikuma Aymaan yadan ta6e baki alamun ko ajikinshi Atare suka tashi suka fito Ce masu yayi su biyo bayanshi sukayi yadda yace harya kaisu wani office daban Ce masu yayi su shiga suka shiga shikuma yafito ya rufo kofar yayi tafiyarshi A tsaye yake jikin window yana kallon waje ta window din hannayenshi zube a aljihunshi Wani qululun baqinciki ya sake tokare Aymaan, da yasan shi zasu gani a office dinnan da babu abinda zai sashi Shigowa Ahankali mussadiq ya juyo yana kallonsu still hannayenshi zube a aljihu Shiru ya ratsa dakin na wasu daqiqu babu mai uhm bare uhm uhm Can saiya tako ya dawo kusada wani table din office din yadan jingina dashi yana dora hannu daya akan desk din "seems yau ma is a Lucky day for you guys, Saidai rana 99 na 6arawo rana daya kuma na meshi, ku tafi amma idan kere na yawo zabo na yawo zasu hadu Saidai ku kuji haduwarmu ta gama don it gonna be worst" Atare suka ta6e baki kamar hadin baki Aymaan na shirin magana zee ta rigashi "a juri zuwa rafi dai, kuma am assuring you wannan tsaremu dakasa akayi na few hours saikayi regretting dinshi, saiyasa watarana ka kasa hada idanu damu Mutum darajja gareshi kowanne mutum da baiwar da allah yabashi wanda sai an taqa zai gane Hakan Kayi amfani da matsayinka ka tsaremu, to kajira ranar da kai kanka kunyar kanka zaisa ka kasa daga idanu ka kallemu straight in the eyes kamar yadda kayi yanzu A lokacin zaka gane arziqi is nothing don arziqin besa kasamu abinda wadanda ka wulaqanta suka samo maka ba, a lokacin zaka gane kowama da ranarsa kuma gamewar bazata amfaneka da komai ba don it's like crying over a split milk" Aymaan ne yadanyi murmushi "haba lil sis, meyasa kike 6ata yawun bakinki har haka? Magana ta hankali mai hankali ake yimawa don shi zaifi ganewa, it's better Kiyi saving din yawunki mai daraja for something more valuable" Takowa mussadiq yayi gabansu ya tsaya yace "kamar yadda nafada dazu, you guys are very Lucky, shiyasa har kukeda damar maida yadda akayi yanzu, amma ku guji ranar da Luck din xaibar side dinku cos you'll regret it. Kuna iya tafiya tun kafin Luck din ya fece yabarku tun yanzu" "kai kalmar Lucky ta cancanta don albarkacin wani kakeci da nasa akowanne daqiqa ka dinga tuna ni cikin qunar rai amma unfortunately bazan iya ba saboda darajar shi dama mai daraja akecin darajar shi" inji zee "out.. Kun isheni da hayaniya and this is not market, so out!" Yafada yana nuna kofa "ko baka fadaba, amma ka tuna zuru batacin zuru" inji Aymaan sai ya kama hannun zee suka juya suka fita daga office din suna maido mashi kofar da qarfi Bïñ kofar yayi da kallo sannan ya sauke Ajiyar zuciya yakoma ya zauna bisa kujerar Wurin mai jujjuyawa yafara jujjuyawa _the girl_ Meyasa presence din yarinyar kesashi jin wani iri, absence dinta ke dada jefashi wani hali Meyasa yakasa mancewa da ita tun haduwarsu ta farko Meyasa yakasa mance fuskarta tun a gani na farko? Shi ba mutum bane mai yawan maida kai ga kammanin wani musanmman mace amma sai gashi ita tun a ganin farko kwalwarshi tayi capturing face dinta A haduwa ta farko bayan ya warwatsa mata kudade ajiki yayi tafiyarshi yaji wani yanayi marar dadi kamar yasa ajuya ya koma wajenta A haduwarsu na biyu ma bayan yatafi yabarsu da cashier gab da zasu sha kwana ya juyo yana kallonta Daga nesa suna barin wajen, nan ma Wannan feeling din yaji kamar ya tsaidata kamar yakoma wajenta Yanzu ma basu ida fita ba yaji kamar ya dakatar da ita inda Koda dakatar da itan yayi besan me zaice mata ba Menene Hakan to? Meye ma'anar Hakan?... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:41 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *067* *THE UNVEIL* Fitowa sukayi harabar wajen suka nufi hanyar gate Aymaan kanshi na kan wayarshi da aka maido masu abinsu dazasu fita yana kunnata Babu dadewa ta kunnu yashiga contact ya lalubo number Ahmad yayi dialing Ringing daya biyu aka daga "ya sallam Aymaan ina ka shiga? Na nemeka kamar zan zauce.." abinda Ahmad yafara dashi kenan yama manta da sallamar "hmm, ai gashi yanzu kajini ko? Kana ina?" "ganinan nadawo gidanku daga yawon nemanku, kasan kau zee ta 6ata?" Dan murmushi Aymaan yayi ya dan kalli zee dake kallonshi shima saita Janye nata idanun "gamunan tare, kazo ka dauke mu" Jin sallalamin su ummy da ihun murnar batool yasa yadan Janye wayar daga kunnenshi kadan "dagaske? Amma kai dan air ne, ina kuka shiga munata neman ku harda hadawa da police station?" "kazo c.i.d headquarter ka daukemu" be jira amsarshi ba ya katse kiran Sake kallon zee yayi yaga bashi take kallo ba Amma ta kare goshinta da hannunta saboda hasken rana Juyawa yayi yaga wasu kujeru qasan wani tent saiya kalli zee yace "muje can mu zauna mu jirashi" Kallonshi tayi kamar zatayi magana saikuma tafasa suka wuce inda yace din suka zauna Shiru wajen ya dauka na wani lokaci Can zee tadan muskuta wanda Hakan yasa Aymaan Dagowa yana kallonta Batareda tabari sun hada idanu ba ta fara cewa "Am sorry.." Shiru yayi yana kallonta Hakan yasa ta dago idanunta itama ta kalleshi "for what?" ya tambaya yana kallonta cikin ido Sauke nata idanun tayi sannan ahankali tace "I caused it all, duk ni naja komai" Murmushi yayi mai kyau yace "bake ya kamata kibada haquri ba.. Nine. Am sorry nakasa hanaki zama a tsare for some hours" Dagowa tayi tasake kallonshi cikin wani yanayi sai ta girgiza kai "nice najamana, naja maka tsarewa na wani lokaci" Murmushi yayi ya kalli gate daga inda yake zaune "I can do more than that... For you." ya qarashe yana maido kallonshi akanta "kawai baqincikina shine kasa kareki danayi daga zaman tsarewar, dani kadai ne ko shekara nawa zanyi bazan damu ba Amma the thought of ke a tsare shiyafi komai dagula min rai... Am sorry" Sunkuyar dakai kawai tayi batace komai ba sai wasa data cigaba dayi da zoben hannunta Shima be sake cewa komai ba sai maida hankali dayayi yana hango gate ta inda suke zaune Babu dadewa motar Ahmad ta iso wajen Ajiyar zuciya Aymaan ya sauke "ya iso... Muje" yafada yana tashi tsaye Itama Dagowa tayi ta hango motar sannan ta tashi tabi Aymaan daya fara tafiya Har Ahmad ya fito saiya hangosu Hakan yasashi tsayawa Kofar baya Aymaan ya budewa zee ta shiga ya rufo sannan ya bude ta kusada driver yashiga shima Ahmad ya shiga suka rurrufo kofar, tada motar Ahmad yayi yaja suka bar wajen. Tafiya sukeyi ahankali cikin normal speed babu mai cewa komai Can Ahmad ya juyo ya kalli Aymaan da idanunshi ke kan titi "Aymaan, wai meya faru ne? Meya kawoku wancan Wurin?" yafada yana maida kallonshi a titin "muje gida sannan" Aymaan ya amsa a taqaice Ajiyar zuciya Ahmad yayi ya cigaba da tuqinshi Zee na Jinsu amma batace komai ba sai kallon waje datake ta window din motar Koda suka isa gida duk su dama ake jira, nan take akayi musu caa akan meya faru, ina sukaje Saida suka zauna sannan Aymaan yafada masu komai daga inda yaje school din da niyyar daukota har hangosu dayayi a parking space din kamar suna hayaniya da mutumin har Qarasowarshi wajen da yadda fadan yakoma kanshi Sai aka maida akalar Tambayar ga zee akan me ya hadasu Nan zee ta gayamasu yadda komai yafaru takuma gayamasu haduwarsu da mussadiq din a supermarket lokacin da suka fita da batool siyo jakka Saidai ta 6oyemasu cewa la6el tayimashi ta dinga binshi abaya, kawai cewa tayi tayi 6atan hanya ne sai suka hade dashi shikuma sai yace shi take bibiya Kowa mammaki ya cika shi da kuma jimami akan abinda yafaru, cikin masu mammakin harda Ahmad da abin yafi kowa kadashi, lallai ba qaramin tsallake rijiya da baya sukayi ba Mussadiq? Mussadiq al-hassan yasa akamasu kuma ya sakesu da wuri haka? Nan su Abbu suka yanke shawarar fidda zee daga makarantar saboda tsaro tunda zuwa makarantar na neman zama barazana agareta, kawai gwara a maida ta school dinsu batool tunda ba'ayi nisa a semester din ba qila a kar6eta Sosai Batool taji dadin Hakan don Hakan na nufin tare zasu dinga zuwa school kenan kuma zasu dinga yini tare Cikin wadanda sukaji dadin Hakan harda Aymaan don shima abinda ke ranshi kenan kawai sun rigashi furtawa ne kuma yaji dadin da bashi ya furta din ba A 6angaren zee kau ba taji dadin haka ba sam, Saidai bata nuna ba, that means tabar makarantar annur kenan? Tabar Aysha? *** Kwance take idanunta akan cieling din dakin tana kallon design dinshi wanda a zahiri bashi take kallo ba tayi nisa ne a tunaninta "zee nasan bakiji dadin hukuncin dasu ummy suka yanke ba Amma that's the best solution, tunda mutumin nan ya dora ayar tambaya akanki bazai barki ba, zaita bibiyar ki ne har saikin fada tarkonshi so maganin kar ayi kar asoma gwara kibar musu school din" Ajiyar zuciya zee ta sauke still idanunta akan ceiling din "ni ba barin school dinne matsala ta ba, rushewar hanyar cikar mission dina yafi damuna, gashi na shaqu da Aysha, zanyi kewarta" "hakane amma abinda zaki duba anan shine wannan hukuncin is for your own Good, Ahmad yana yawan bani labarin how dangerous that guy is, yana iya yin komai kuma yaci bulus don yanada both matsayi da kudi da connections, ja dashi ba qaramin kasada bane, batun mission dinki kuma allah zai kawo mana mafita ta hanyar da bama zato kawai mu cigaba da addu'a" Qara sauke Ajiyar zuciya zee tayi tace "to allah yasa Hakan shiyafi alhairi" "Amin summa amin" batool ta amsa Wayar zee ce tayi Ring Tashi tayi ahankali zaune sannan ta jawo wayar dake kusada ita kan bedside locker Dan Wara idanu tayi ganin sunan dake yawo a screen din Ganin Hakan yasa batool cewa "waye?" "Aysha" zee ta amsa tana picking call din "bestie" inji zee cikin fara'a Wani irin wawan Ajiyar zuciya zee taji Aysha ta sauke sannan cikin murya Kamar zatayi kuka tace "ummie na" "na'am sahibatie" "wayyo ummie na, nayi tunanin bazaki daga kirana ba Tundazu nake son kira amma fargaba ta hanani" Murmushi zee tayi tace "inqi dagawa kuma mezai hanani dagawa?" "komai ma ummie, am sorry, am very very sorry for what happen dazu, da nasan abinda zai faru kenan da ban fara gayyatarshi ba" Murmushi zee tasake yi "Don't be, misunderstanding ne kawai" "wlh bakiji yadda naji ba a lokacin, laifi na ma ne, nasan halin yaya sarai amma banyi tunanin abin zakai Hakan ba da ko sunanki bazan ta6a ambata mashi ba" "kinga babu komai, kibar damun kanki, komai ya wuce insha allah" inji zee "nagode qwarai ummie da fahimtarki, fatan dai komai lafiya, ba'ayi muku komai ba ko?" "babu abinda akayimana, komai lfy lau" "yayanki fa? Shima is ok ko?" "kowa lfy lau, na gayamaki babu abinda sukayimana" "masha allah, naji dadin jin Hakan... Ga ummie ku gaisa" Wara idanu zee tayi saita kalli batool da itama ta Wara nata idanun don wayar a handsfree take duk tana sauraron su "Assalamu alaiki habibty" muryar Ummie mai cike da kwarjini ta daki dodon kunnenta Hadiye wasu yawu tayi sannan cikin nutsuwa itama ta amsa sallamar ta dora da gaisheta, duk maganar dasuke a harshen turanci suke yinta "lfy lau habibty, ya gida ya mutanen gida" "alhamdullilah, ummie" inji zee cikin nutsuwa "masha allah, ina mai baku haquri akan abinda yafaru tsakanin ku da hussain, Gaskiya banji dadi ba kwata2, abin ya 6ata min rai sosai kuma zan dauki mataki akai kuyi hqr kinji" "haba ummie komai ya wuce insha allah, dama rashin fahimta ce kawai" "babu wata rashin fahimta, haka yake. Narasa inda yasamo wannan baqar aqidar, shikenan mutum beda yarda kona misqala zarratin? Ai dazu Saida nayi mashi fada sosai nakuma ya sakeku kuma saina dauki mataki akai" Murmushi zee tayi cikin jin qaunar matar, da wata ce ko ajikinta bare har tayi tunanin kira ta bada haquri "babu komai ummie, allah yaqara lafiya" "Amin, ina Ummin naki?" "tana dakinta" "kai mata mu gaisa don Allah" "to ummie, hold on" tafada tana tashi tsaye ta nufi kofa batool ma ta sauko daga gadon ta maramata baya A daki suka iske Ummu batool tafito daga bayi da alamu ma wanka tayi Kaimata wayar tayi Daga gira Ummu batool tayi alamun waye, cikin rada zee tace mata umminsu Aysha ne Kara wayar Ummu batool tayi a kunne tayi sallama ummie ta amsa ta dayan bangaren Gaisawa suka farayi cikin mutunci sannan ummie tayi introducing kanta takuma shiga bata hqr akan abinda yafaru Cikin fara'a Ummu batool ke nuna babu komai ai komai ya wuce insha allah Sundan jima suna wayar sannan sukayi sallama ummie ta maido ma zee wayarta Koda ta maida a kunne sai taji muryar Aysha Nan take gayamata gobe insha allah zatazo Da farko zee taso hanata zuwa amma saita nace akan saitazo Hakan sukayi sallama bayan tace zee ta turo mata address dinsu Kallon Ummu batool zee tayi tana Tambayar ta tura mata din Cewa tayi ta tura mata din tunda zuminci zatazo babu komai taga alamun suna da kirki sosai kuma kamar basuda matsala Da Hakan ta turama Aysha address din suka koma dakinsu da ita da batool suna cigaba da firar kirkin ummie da Aysha Sai gashi washegarin kamar yadda tace zatazo tazo din bayan sallar la'asar Sosai zee tayi murnar ganinta kuma akayimata tarbar mutunci Sosai suka gaisa da Ummu batool sannan suka wuce daita sama dakinsu zee Batool tunda taga Aysha taji itama ta kwanta mata a rai lokaci guda don ko ba'afada ba kallo daya zakayi mata kasan tanada nutsuwa sosai Anan zee tayi introducing din batool agareta suka kuma gaisa cikin mutuntawa sannan zee tafito ta sauko qasa don samarwa qawar tata abin ta6awa. Lokacin da ta dawo saita tarar firarsu ma sukeyi abunsu saita ajiye masu abin data kawo tana musu bismillah Tare duk suka sauko qasa kan dan carpet din data shinfida masu suka shiga cin abincin suna fira "uhmm, abincin nan yayi dadi, daga ji nasan ummie na ta girka" inji Aysha tana lumshe idanunta alamun abincin na kaimata karo "to ni na dafa, wannan dakike ganinta babu abinda ta iya sai a girka ta shaqe plate taci, duk abincin dazaki shigo gidan nan kici ko agaba ne ni na girka shi" inji batool Dariya duk sukayi "kai nidai ban yarda ba, ummie ta tafi kama da wanda ta girka abincin nan" Dariya suka sakeyi batool tace "wato har kammani ke akwai kenan na wanda ya girka abinci?" "qwarai kuwa, da kin kalli abincin kika kalli wanda ya girka sai kiga sunyi matching" Dariya suka sake sawa Haka sukaita firarsu har suka gama cin abincin aka kauda abubbuwan dasuka 6ata suka koma kan gado aka shiga fira "ummie, wlh jiya dake na kwana arai, tsabar yadda nasa abin a raina sai gashi harda su mafarki wai yaya yaqara sawa an kamaki" Dariya sukayi "kincika sa abu arai wlh" inji zee tana Dariya Itama dariyar tayi tace "wlh, ai haka nake. Gashi dama halin yayan nawa nasani, haka yake bayada yarda kona diss, haka yake tun yana qaramin shi. Can you believe ko aboki qwara daya baya dashi? Ummie tace yafara wannan halin ne tun bayan rasuwar dan uwanshi" Dan Wara idanu zee da batool sukayi cikin hadin baki sukace "tun rasuwar dan uwanshi?" Murmushi Aysha tadanyi "ummie, ban gayamaki mu asalin wayeba, na baki tarihina just briefly batareda na fadamaki wasu abubbuwa ba Kinsan ko waye yaya na? Kinsan companies din nurul haqq masu rassa daban daban?" Batool tayi saurin amsawa "waye besan nurul haqq ba? Saidai idan ba a dubai yake ba, itama kanta zee datazo jiya jiyan nan tasan wasu wuraren, sis wannan park din damukaje ranan? To shima na nurul haqq ne" tafada tana kallon zee Zee data dauki hasken abinda batool ke nufi saita Kada kai cikin mammaki tace "natuna, koba wannan mai girman ba? Mai Hade da zoo" "shi... Na yayana ne" inji Aysha Duk Wara idanu sukayi sosai cikin mammaki dukda sunsan komai pretending ne kawai "yayana ne mammalakin duk wani company na nurul haqq, mussadiq al-hassan" "ya sallam! Kina nufin ke qanwar mai wadannan wuraren ce?" inji batool cikin kaduwa, yadda take acting din yayi mugun hawa kamar dama yau tafara sani Murmushi Aysha tayi tace "eh, duk wadannan wuraren mallakin yaya mussadiq ne, Saidai baya bayyana identity dinshi kamar yadda muma yake hanamu bayyana namu duk don maqiya wai. Yanada saurin zargi da rashin yarda shiyasa shi kanshi idan ba saninshi kayi ba baka gane babban dan kasuwa ne kuma shi keda wadannan wuraren. Na ta6a baki labarin cewa twins ne ko?" tafada tana kallon zee dake kallonta Tundazu babu kyaftawa Kada kai zee tayi saurin yi "eh kika ce dayan ya rasu ko?" Kada kai itama Aysha tayi "eh haka nace amma a zahirin Gaskiya ba mutuwa yayi ba" Ji zee tayi kamar an kwada mata guduma akai "b..be mutu ba?" tafada cikin rawar murya itakau batool tama kasa cewa komai sai kallon Ayshar datakeyi "to ya mutun za'ace amma ba mutuwar allah da annabi ba.. Ina nufin kasheshi akayi" Wannan karon tashin hankalin zee qarara yafito a fuskarta "kasheshi akai? Waya kasheshi?" Da Aysha mai lura ce data lura da yadda zee ta tashi hankalinta fiyeda yadda ya kamata data dora ayar tambaya akan Hakan "eh, saceshi akayi daga baya aka kasheshi" "innallilahi waina ilaihi rajiun" zee da batool suka fada atare hankalinsu a tashe "nima ummie ke bani labari don a lokacin ko haihuwata ba'ayi ba akwai dai qaramin cikina wanda ba'ama san dashi ba. Mujaheed shine Hassan mussadiq kuma Hussaini, yan biyu ne masu tsananin kama da juna don ummie ma kanta takan kasa banbancesu wani lokacin Saida suka dan fara girma aka fara samun signs da ake banbancesu dashi Nafarko shine dimple dinsu. Mujaheed nada dimple a tsakiyar gemu kamar dai nawa don ance shi na biyo while mussadiq nashi a kumatun haggu yake Na biyu kuma yanayin qiriniyarsu. Mussadiq yafi Mujaheed qiriniya nesa ba kusa ba don Saida mussadiq yariga mujaheed fara rarrafe harma tafiya ma Kamar ummie ke cewa mujaheed yanada sanyi sosai sa6anin mussadiq dake da qiriniya don Mafi yawancin lokuta inda ta ajiye mujaheed nan zatazo ta dauke shi shikau mussadiq daka ajiye shi zai qara gaba yaje yaita 6ana Haka ma yara basa qwarar mussadiq don shi ba'a sashi kuka Saidai yasa Yayinda shikuma mujaheed babu ruwanshi sai yara suyita bugunshi baya ramawa Saidai kuma mujaheed yafi mussadiq juriya da haquri don da wuya yayi kuka don cewa tayi ko rashin lafiya yake baya irin rigimar da mussadiq keyi Idan shine bashi da lafiya, Saidai shirunshi da sanyinshi suqara yawa, ko cikin yara yashiga masu qiriniya suna qwararshi baya kuka duk abinda zasuyi mashi idan kaga yayi kuka to abin yakai qurewa Shiyasa ko a soyayyar dasuke masu ta mujaheed tafi don shi bayan soyayya harda tausayi don yaro mai sanyi dama yafi soyuwa a zuqatan iyaye ko don tausayawa yanayinshi Abin yafaru ne ranar washegarin wata babbar sallah, lokacin suna saudiya don dama can ne asalinmu daga baya muka dawo nan Kamar yadda al'adar wannan ahalin take dik washegarin sallah walau babba ko qarama ana haduwa a babban family house dinmu inda anan kowa da kowa na dangi, qwansu da kwarkwatan su saisun hallarta harda wadanda ba garin suke ba Ana haduwa agidan don taya murnar sallah da sada zuminci To suma haka suka shirya ranar tunda safe Abbanmu yakai ummie da twins dinta Lokacin Abbanmu dan kasuwa ne wanda yayi suna sosai a madina a harkar kasuwancinshi kuma a lokacin shima ana iya sashi a sahun masu kudin family dinmu Kamar yadda ummie ta gayamin tace tunda sukaje gidan Hassan wato mujaheed ya liqemata duk inda yayi yana maqale gashi ranar sanyinshi yaqara yawa fiyeda yadda yake da Sai tayi tunanin ko bayada lafiya ne dukda jikinshi babu zafi Saita sa6eshi ta goyashi ta cigaba da aikinta dashi a baya Haka taita yawo dashi abaya har bayan zuhr don Koda zatayi sallah ma Saidai ta ajiye shi kusada ita yana kallonta har tagama sannan ya rarrafo yadawo kusada ita ya sake lafewa ajikinta Ganin wannan lauye lauyen nashi yafara yawa yasa tasa aka siyomashi maganin ciwon kai don aganinta qila bejin dadi ne Tabashi yasha ta maida shi baya ta goya har yayi barci ma Be farka ba sai wajajen la'asar, tabashi abinci yaci sannan cikin gwarancinshi ya nuna wa ummie zaije wajen mussadiq da tunda suka shigo gidan yake cikin yara suna wasa Sawa tayi akaishi wajensu din dukda bata cika son yana shiga yaraba saboda qwararshi da akeyi saikuma tayi tunanin ai gwara ya saba qila da haka da haka shima zai iya ramawa idan akayi mashi Nan ta cigaba da hidimarta cikin dangi anata kai kawo cikin annushuwa da nishadi Can wajajen bayan la'asar kadan aka fara jin hayaniya a tsakar gidan Tun suna ji sama sama har abin yafara yawa Hakan yasasu fitowa ciki harda ummie Abinda ummie tagani yayi matuqar girgizata don Saida jiri yakusan kadata ba don anyi saurin tareta ba Mussadiq tagani jina jina jikinshi duk ciwo ga kayanshi sunyi futu futu harda yagewa a wasu wuraren Da gudu suka nufeshi cikin tashin hankali don anason riqeshi amma sai fizge fizge yakeyi Da gudu ummie ta qarasa gabanshi ta jayoshi ajikinta tana kiran sunanshi cikin kuka Jin muryar ummie yasa yabar fizge fizgen saiya dago ya kalleta saikuma luuu yafada ajikinta asume. Kwatanta tashin hankalin da aka shiga a lokacin 6ata baki ne Nan take aka shiga kiran iyayen maza dasuka fita ta waya cikin qanqanin lokaci saigasu sun duro gidan ciki harda Abbanmu Lokacin gidan banda koke2 babu abinda akeyi Cikin gaggawa aka wuce dashi asibiti cikin masu zuwa harda Umminmu Nan take likitoci suka kar6eshi aka shiga bashi taimakon gaggawa Saida aka kusan awa sannan akasamu aka shawo kan mussadiq numfashinshi yadawo normal yakuma samu barci sanadiyar allurar barci da akayi mashi Sai a lokacin likitocin suka fito wajensu ummie da suka kasa tsaye suka kasa zaune nan suka kwantar masu da hankali akan komai ya daidaita yama samu barci Nan kowanne ya sauke Ajiyar zuciya na jindadin Hakan Saidai ashe zaune bata qareba Tafiyar su likitocin keda wuya sai ummie da sai a lokacin tasamu zama taqara zabura ta miqe tsaye kamar wanda aka tsikara Duk sai aka kalleta ana Tambayar lafiya 'mujaheed... Ina mujaheed?' Nan kowa ya tuna dashi don tashin hankali yasa anma manta dashi Tofa nan aiki sabo yafara don duk inda aka duba inda akasan za'a ganshi dama inda bazai iya shiga ba Amma babu shi Babu inda ba'a duba ba a fadin gidan lungu da saqo amma babu mujaheed babu alamunshi Nanfa hankali ya tashi ba ko kadan ba, tsakanin ummie da Abba aka rasa wanda yafi wani rikicewa Duk fadin unguwar dama wajenta babu inda ba'a duba ba Amma babu mujaheed Ummie har qaramin hauka saida tayi suma kau tayishi babu iyaka Wasa wasa har dare babu mujaheed Izuwa lokacin an yada cigiya gidajen t.v da radio amma shiru Daren ranar babu wanda ya runtsa a familynmu, ranar murna ta chanza lokaci guda zuwa ta baqinciki, abu goma da ashirin, ga mussadiq a asibiti ga mujaheed ya 6ata. Washegari ma dasa neman da akeyi akayi inda aka baza jami'an tsaro sosai wajen nemanshi Ummie a lokacin bata ganuwa don itama dole qarshe aka bata gado a lokacin ma aka san da cikina. Wasa wasa kwana daya yakoma biyu yakoma uku amma still babu mujaheed, Izuwa lokacin ummie da Abba sunzama abin tausayi ba kamar ummie don ita abin yafi ta6ata, babu abinda take Tunawa sai maqale mata dayaitayi tun safe, datasanin barinshi fitar datayi yafi cikin kwando Saidai komai muqaddari ne Daga allah, dole allah ya rubuta Hakan zai faru" Dakatawa tayi ta dago ta kalli su zee da izuwa lokacin fuskarsu sunyi sha6e2 da hawaye sai a lokacin itama taji dumi dumin nata a fuskarta Hakan yasa tasa bayan hannu ta sharesu dukda Hakan ba yana nufin wasu bazasu sake zubowa ba "A kwana na hudu aka bugo ma Abba waya da number da akayi hiding dinta. Yana ganinta jikinshi yabashi kiran yashafi mujaheed dinshi Hannu na rawa ya daga yana jin zuciyarshi kamar zata faso qirji Kamar yadda yayi tunani Hakan ne don wadanda suka sace mujaheed ne suka bugo suna buqatar kudin fansa inhar suna son a sakomasu dansu. Da farko Abba qin yarda yayi yace dole saiya ji muryar danshi yakuma tabbatar shine sannan Aikau sai suka bashi saiga muryar mujaheed radam yana kiran Abba da ummie cikin kuka Sosai hankalin Abba yayi mugun tashi nan take shima hawaye suka kawo mashi a idanu Nan take yashiga magiyar don Allah suyi hqr karsu cutar mashi da danshi zai basu duk abinda sukeso Jin Hakan yasa suka ce zasu sake shi amma sai sun bada kudin fansa Nan suka yankama Abba kudin dazai bayar na fitar hankali Abba yaso neman ragi amma firr suka qiya sukace ya za6a ko kudi ko mujaheed Nan kuma suka jamashi kunne akan karya saki yasako jami'an tsaro aciki don sakosu aciki daidai yake da mutuwar mujaheed, suka kuma ce zasu sake kira don gayamasu inda zasu kai kudin. Sosai hankalin ahalinmu yasake tashi Inda duk wanda yaji adadin kudin dasuka nema saiya girgiza Saidai Abba a shirye yake ya bada dukkan abinda ya mallaka don dawowar danshi Mafi soyuwa a gareshi A lokacin mussadiq ya dade da farfadowa Saidai wata irin rashin lafiya yake mai zafin gaske ga ciwukkanshi da basu ida warkewa ba kullum cikin kukan ina mujaheed yake abinci ma Dakyar yake ci. Ummie kuwa tafi kowa zama abin tausayi kodayaushe ciki kuka take duk tabi takoma kamar ba ita ba ga tashin hankali ga ciki. Wasu daga cikin family dinmu suka bada shawarar sanyo jami'an tsaro acikin case din amma firr Abba yaqi yarda don babu abinda zaisa yayi tempering da rayuwar danshi. Haka ya hada kudin nan cass family dinsu suma duk sun kawo gudunmawa aka hada kudadden ana jiran suqara bugowa don dole saisun bugo tunda da hidden number suka bugo wancan karon Sai bayan kwana biyu suka bugo suna Tambayar an hada kudin, baki na rawa Abba ya amsa da eh sai suka fadamashi inda xa'akai Roqonsu yashigayi cikin magiya kan suqara bashi mujaheed yaji Muryarshi Babu musu aka bashi 'Abba' mujaheed yafada cikin mugun sanyi 'Abba... Ummie' Kasa controlling kanshi Abba yayi Saida yayi hawaye 'mujaheed bunnaya, kana lafiya?' yafada cikin rawar murya 'Abba?' mujaheed yasake fada 'kayi hqr zaka dawo kaji? Abba zaizo ya daukeka' inji Abba hawaye na gudu sosai a kumatunshi 'muccadik' mujaheed yaqara fada cikin sanyin murya 'mussadiq nanan lfy, shima zaizo kaji? Kaji dana' Daga Hakan sai yaji muryar daya daga cikin 6arayin na cewa ya isa haka nan tunda sunyi maganar Nan yasake gayamasu inda zasu kai kudin da lokacin dazasu kai dakuma qara yimasu gargadi akan karsu sake su sako jami'an tsaro aciki idan ba Haka ba a bakin ran dansu. Nan aka shirya komai Abba da kanshi yaje bada kudin Kuma ya ajiyesu inda suka ce sannan yatafi Saidai shiru shiru basu bugo ba sukace ga inda zasuje su dauki yaron ba Tun suna jira har hankalinsu yafara tashi da jin yadda shirun yayi yawa Sai a kwana na biyu da bada kudin sannan aka bugamashi waya, a lokacin saura qiris ya zauce Nan aka gayamashi inda zaije ya dauki mujaheed cikin wata ash din mota, zasu bar motar a bude dayaje kawai ya bude ya fiddashi ya tafi dashi Cikin jindadi Abba yayi shirin tafiya, jikinshi har rawa yakeyi don har jiri jiri yakeji na neman dibanshi Dashi da Hussaininshi suka tafi dauko shi inda akace din Wuri ne da sai anfara fita daga gari ma, babu gidaje a wajen sai busassun ciyayi don lokacin rani ne Tun daga nesa suka hango motar ash colour din da akace gefen titi. Parking Abba yasa Hussaininshi yi tun kafin su qarasa suka fito da sauri suka nufi kofar Saidai suna kaiwa inda tsakaninsu da motar baya wuce taqi ashirin sukayi mugun ganin da basu ta6a irinshi ba Motar da akace masu mujaheed na ciki ta tashi da wuta🔥 a gaban idanunsu.."✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:42 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *068* *THE UNVEIL 2* _🙈ni yau ido rufe zanma yi typing saboda kunyar wasu nakeji 🙈🙈_ Toshe baki zee tayi idanunta awaje tana kallon Aysha da kuka yafara cin qarfinta "a..agaban idanunsu motar taita ci da wuta... Abbanmu ahakan yaso qarasawa ga motar amma Hussaininshi da tsirarun mutanen da wutar tajawo hankalinsu suka hanashi ta hanyar rirriqeshi. And..and before his very eyes, beloved son dinshi ya qone qurmus dashi da mot..." Kasa idawa tayi saboda kukan dayaci qarfinta. Kamar hadin baki da zee da batool suka rarrafa wajenta suka rungumeta suka hada kai waje guda suna kuka kamar ransu zai fita Sun dauki tsawon lokaci ahakan anrasa wanda zai rarrashi wani Can Aysha ta dago da jajjayen idanunta tana kallon su zee da har lokacin kukan sukeyi "ba acikin hayyacinshi ba aka maido Abbanmu gida, daga nan akayi asibiti dashi. Itama ummie najin abinda yafaru ta yanke jiki ta fadi, kan kace me jini ya 6allemata Itama kamar abba sai aka kwasheta sai asibiti. Kamar hadin baki shima mussadiq jikinshi ya rikice yashiga convulsing, numfashi ma Dakyar yake fizgoshi daga huhunshi. Iya tashin hankali wannan ahalin sun shigeshi a lokacin. Nima don Allah yayi zanzo duniyar shiyasa cikin ikon allah aka shawo kan bleeding din da ummie keyi Lokaci guda happy family dinmu ya tashi daga happy family zuwa akasinshi Abba tunda ya kwanta gadon asibiti be qara tashi ba Saida yayi wata daya a kwance sannan watarana yatafi cikin barcinshi. Yatafi yabi danshi yabar matarshi abar qaunarshi da cikin dake jikinta dakuma danshi da har lokacin beda cikkaken lafiya. Haka ummie tayi takabarshi, ga ciki ga ciwo don tun lokacin da ta yanke jiki ta fadi lokacin da aka dawomata da labarin mutuwar mujaheed ta hadu da ciwon hawan jini. Haka tayi takabarshi tagama ta cigaba da zama gidanmu tareda mussadiq da shima izuwa lokacin ya warware sosai Saidai kwata2 ya chanza daga mussadiq din da aka sani. Mussadiq mai qiriniya mai surutu yakoma so silent. Yana iya yini batareda ya furta ko kalma daya ba, ga wata rashin yarda da ya bijiro daita lokaci guda. Baya yarda wani ya ra6eshi ko kadan Duk yadda kau kake dashi. Ko baqi ummie tayi walau family dinmu ko wasu daban baya yarda yabar jikin ummie duk inda zata yana maqale daita. Idan baqin zasu shekara suna mashi magana ko kallo bazasu isheshi ba Idan kuma sukace zasu daukeshi da tsiya sai ya fasa ihu kamar wanda ake yankawa Hakan yasa duk masu qulafucin daukarshi suka haqura Saidai gani daga nesa wato ajikin ummie Da farko ummie tayi tunanin yarinta ne kuma qila harda abinda yagani ranar da abin yafaru tunda tana kyautata zaton kome yafaru a ranar mussadiq yagani tunda da alamu ma kamar shi kuftowa yayi Saidai a lokacin ko an tambayeshi bazai iya bada amsa ba don qarami ne sosai magana ma bata gama nuna a bakinshi ba Hakan yasa take yimashi addu'o'i sosai da rubutun sha duk na dangana wanda zai kuma taimaka mashi wajen manta abinda ya faru din Saidai abin yafara bata tsoro ne ganin harya fara girma bai bar wannan sabon halin nashi ba A lokacin baya zuwa ya lafe jikin ummie Saidai duk tsiyarka daga nesa nesa zaku gaisa dashi ya maida fuskar ya dinke tsaf idan zaka shekara yimashi magana bazai amsa ba A lokacin an haifeni sai ya kasance bayan ni da ummie babu wanda yake kuma yarda dashi. Anyi maganin anyi gwajin both physically and mentally amma result din ya nuna babu abinda ke damunshi, he's normal Saidai a kowacce rana abin nashi qara gaba gaba yakeyi Har takai ni kaina yafara hanani kula mutane, ko zuwa yayi ya ganni da yara muna wasa saiya fizgoni daga cikinsu ya hanasu zuwa wajena kuma gashi a lokacin mugun tsoronshi yara sukeyi saboda rashin warginshi shiyasa wani lokacin da sun ganshi sai su gudu ko susha Jinin jikinsu, lokacin fa bazai wuce shekaru goma sha biyu ba Saidai rashin warginshi yasa ko manya saisu kasa tsawatar mashi saboda kwarjinin dayake masu Wannan abin ba qaramin cima ummie tuwo a qwarya yake ba don da dama can haka yake da da sauqi amma sanin cewa daga baya ya bijiro da wannan halin yasa abin ke damunta sosai Ko shiryamu tayi muje gidajen danginmu baya zuwa Saidai yaita yawo dani mudawo gida, idan tagane Hakan saita tisa shi gaba da fada shikuma data fara sai yaita kuka kamar ranshi zai fita Tasha zaunar dashi ta tambayeshi meyasa yake abinda yakeyi ko wasu sukeson yimashi wani abu ne? Sai ya girgiza kai kawai yace 'ummie banason kowa sai ke da ukhtie' Haka rayuwa taita tafiya tun ummie nasa abin a rai harta fawwalawa allah komai ta cigaba da Binshi da addu'a Mussadiq ko a makaranta be ta6a yin aboki ba nima ya hanani yin qawa ko daya, kasancewar shi kadai ne yaya na kuma abin koyi na tunda mostly sai kiga a kowanne gida qarami yafi saurin koyi da wa ko yayanshi bisa ga yadda zasuyi koyi da iyaye saboda kusanci dake tsakaninsu, sai ya kasance nima bana Sakin jiki da mutane ko a family dinmu ne don ko ummie ta tilasta mana zuwa gidajen su bama shige masu, daga gaisuwa shikenan, gwara ni fuskata kodayaushe asake take kuma idan akayi min magana zan amsa asake shikau yaya a kodayaushe fuskarnan tashi na dinke tsaf ko magana akayi mashi cikin cin magani zai amsa. sai ya kasance bamuda wata qawa sai Umminmu Haka zamu zauna mu ukunmu muyita nishadi wanda mostly dama a lokacin ake ganin Dariyar yaya mussadiq Familynmu kau tun suna surutu wai ummie takasa controlling dinmu tasanya mana aqidar qin jininmu a zuciyarmu har suka gaji suka qyaleta suma suka yanke mu'amala daita suka bar aiko yaransu gidanmu wanda Hakan ba qaramin dadi yayi wa yaya ba Saidai dukda Hakan ummie bata fasa turamu zuminci gidajen su ba dukda ba wani kulamu suke ba idan munje ita acewarta ta fita haqqin zuminci Kawu Hussaini da iyalanshi ne kawai wanda basu juya mana baya Ba, kuma 'yayanshi na zuwa gidanmu shima kanshi yana zagayowa akai akai yana duba lafiyar mu kuma ko sau daya be ta6a nuna 6acin ranshi akan halayen mussadiq ba, yana matuqar haquri akan Hakan don shi mutum ne mai matuqar haquri da kawaici. Ahaka har yaya mussadiq yagama karatunshi ya mallaki hankalin kanshi to a lokacin Kawu hussain ya damqa mashi gadonmu dake hannunshi tun rasuwar Abbanmu Kasancewar fannin kasuwanci yaya mussadiq ya karanta saiya zuba kudadden a business yafara jujjuyasu A lokacin kawunnan mu da danginmu maza sunyo caa wajen bama mussadiq shawarar yadda zaiyi da kudin Saidai duk ya watsa masu qasa a idanu ta hanyar yin watsi da dukkanin shawarwarunsu yayi amfani da nashi Cikin ikon allah sai gashi allah yasama abin albarka kasuwancinshi yafara girma Nan kuma danginmu suka tuso ummie gaba da maganar aure, wai ya kamata mussadiq yayi aure tunda ya isa kuma ko a dangine yana iya za6ar wacce yakeso tunda akwai yanmata kala kala a dangin. Firr mussadiq yaqi yarda yana cewa shi yanzu ba aure ke agabanshi ba kuma Koda auren zaiyi sai wacce yakeso basai an kawo mashi tallar yanmatan dangi ba Wannan abin ba qaramin rikici yakawo a danginmu ba, nan kowa ya dora laifin akan Umminmu wai ita keson rabamu da dangin mahaifinmu, sosai abin ya damu Umminmu a lokacin takuma so fahimtar dasu akan bazata iya yiwa mussadiq dole ba akan ya auri wata ba amma sukaqi sauraronta saima suka dauki gaba da ita da muma gabadaya Ashe tun farkon rikicin yaya mussadiq ke tattara dukkanin harkokinshi yana maido su nan dubai Kwatsam watarana yazo ma ummie da maganar komawarmu dubai Da farko ummie qin yarda tayi tana cewa babu abinda zai fiddata daga saudiya Hakan kamar tabbatar da magangganun dangin Abbanmu ne na tanason rabamu da danginmu ne Dakyar mussadiq yashawo kan ummie inda Saida yabi gidajen dangin namu da daddaya yana fadamasu kasuwancinshi zai kaimu can ba wani abu ba kuma zamu ware lokaci muna zuwa saudiya ziyara Abin mammaki sai aka rasa wanda zai qalubalanceshi akan hakan, hayaniya da cecekucen da ummie tayi tunanin zasuyi sai taji tsit basuce komai ba Hakan yasa muka tattaro namu ya namu muka dawo nan dubai da zama Cikin ikon allah cikin qanqanin lokaci business din yaya ya ha6aka yayi albarka, budi yaita shigo mashi takoina, kowa na kwadayin samun share a company dinshi kasancewarshi jajirtacce a aikinshi ga riqon Gaskiya don yaya mussadiq ba duk rintsi baya cutar mutum kuma baya bari a cuceshi shiyasa bada kowa yake aiki ba saiya yarda dakai dakuma qwarewarka a aiki dakuma yanayin riqon amanarka Har lokacin dabi'arshi ta rashin yarda na nan, baya barin wani space komin qarantarshi wanda xa'a iya yaudararshi, yana yin komai nashi cikin taku shiyasa Koda yafara bude wurare irinsu parks, malls da makarantu be sanya sunanshi ko sunan daya daga cikinmu ba saiya za6i yasanya wani sunan daban wanda duk qwaqwar mai qwaqwa bazai san mai su ba sai idan dama can ya sanshi. Gwara gwara gidajen marayun dayake dasu wanda ya bude su da sunan Abbanmu da dan uwanshi mujaheed wanda yatara marayu aciki yana kula dasu da saran ladar Hakan allah yakaima su Abba har cikin qabarinsu. Danginmu na kawo mana ziyara jifa jifa muma muna zuwa qaranci sau biyu a shekara mostly qaramar sallah da babbar sallah. Tunda muka dawo nan qasar ban ta6a yin qawa ba sai akanki, bansan meyasa ba tun aganin farko naji kin kwanta min arai, naji kamar akwai wani connection tsakanina dake. Dan zaman da mukayi dake farko farkon abotarmu kuma yasa kika ida shiga zuciyata naji komai naki na burgeni, a lokacin na bawa Umminmu labarin ki kuma na hadaku a waya inda itama nan take kika kwanta mata takuma bani go ahead akan abotarmu A lokacin yayana bayanan yana switzerland business trip kamar yadda yasaba tafiye tafiyenshi na business Tun yana can nake bashi labarin ki, dafarko ya nuna 6acin ranshi akan Hakan yana cewa ba ya hanani yin abokai ba? Amma saiya haqura lokacin da ummie tayimashi magana tace itama tasanki ke mutuniyar kirki ce, babu yadda ya iya saiya kyaleni kawai amma yayi min gargadi akan na dinga kulawa Jiya kwanan shi biyu da dawowa kuma tunda yadawo nake addabarshi akan yazo ya ganki Saidai yace he's busy amma idan yasamu lokaci zaizo Shine fa kwatsam jiya muna zaune dake a library yayi min text akan gashi nan yazo ganin bestie din tawa dana addabeshi da batunta shiyasa kikaga na Kamo hannunki cikin jindadin wannan bazatar dayayi mana, ashe halinshi zai saida nan saniba" Ajiyar zuciya duk sukayi kowannensu idanu jajur a dalilin kukan dasuka sha na labarin mujaheed. "wataqila ba laifinshi bane shima... Tabbas mun ta6a haduwa dashi sau biyu kafin ranar Ranar farko yayi min kama da wani dana sani a Nigeria shiyasa naje na sameshi, am so desperate that banyi saurin gane bashi bane ba sai daga baya, daga bayan ma bayan yatafi. Haduwarmu ta biyu kuma a wani supermarket ne, nida batool munje siyayya sai bamu samu abinda mukaje nema ba kuma munga abin a magazine dinsu shiyasa ma mukazo shopping din Sai naje wajen cashier nayi complaining akan Hakan saiya bani haquri yakuma kira akace ya turoni na amsa sama wajen Manager To wajen zuwa office din Managern na 6ace Naita shige shigen hanyoyi amma nakasa gane hanya kuma narasa hanyar dazanibi nadawo inda nafito. To anan muka sake clashing dashi inda nan take yayi concluding Binshi nake, I was shocked and scared jin yana tuhumata da bibiyarshi, Dakyar nasamu su cashier sukazo suka ceceni a wajenshi To kinga after all these, ganina kwatsam a matsayin qawarki dolene ya tabbatar mashi da zarginshi, I know shiyasa yayi concluding akan tabbas ni yar leqen asirinshi ce bayan bemasan ita kanta kalmar spy din ba qaramin kadamun hanji yake ba idan aka ambaceta" Dariya duk sukayi "that's yaya mussadiq for you, komai saiya dora mashi ayar tambaya. Jiya ran ummie ya 6aci sosai dajin abinda ya aikata shiyasa nan take tasashi Sakinku" inji Aysha "Allah sarki, ai bayada laifi, duniyar ce ta zama abin tsoro, mutane ba abin yarda bane... Nikau sai naga kamar mussadiq baya rasa sanin wani abu gameda sace mujaheed, as in why lokaci daya zai chanza yabar yarda da mutane bayan da ba Haka yake ba?" inji batool "abinda yake daurewa kowa kai kenan, tabbas qila yaga wani abin wanda ya firgitashi amma kuma yakamata ya manta tunda lokacin da abin yafaru yanada qarancin shekaru tunda lokacin shekarun su uku uku da yan kai" "nikuma nafi zargin cikin familynku, anya babu wanda mussadiq ke zargi acikinsu duba da yadda be yarda dasu ba kwata2?" inji zee "hmm I don’t think so ummie saboda kamar yadda nafada dazu lokacin da abin yafaru yanada qarancin shekaru bazai iya recalling komai ba kuma da ace zai iya da nasan zai fadane right away, kawai ni nafi tunanin razanar abinda yafaru aranar ne taqi sakinshi haryanzu, a lokacin brain dinshi is so fragile wajen daukar irin wannan shock din shiyasa abin yayi affecting dinshi sosai ya zauna ajikinshi har girmanshi batareda shi kanshi yasan meyake damunshi, wataqila Hakan yasa mashi tsoron mutane da rashin yarda dasu har zuwa wannan lokacin don so da dama idan ummie ta tsareshi da Tambayar meyasa yake saurin zargin mutane kuma baya saurin yarda da mutum sai yace shima besaniba kawai yana ji ajikinshi kowa ma na iya zama maqiyinshi shiyasa yakasa yarda da kowa" Duk Kada kai sukayi cikin alhini, tabbas akwai lauje cikin nadi a wannan al'amarin, dagaske ne mussadiq besan komai ba kawai Hakan nan ne yake jin baya iya yarda da mutum ko yanada dalilin yin Hakan? Allah kadai yasan Gaskiya dashi mussadiq din Ajiyar zuciya batool ta sauke "to allah ya bashi mafita akan abinda ke damunshi, allah yajiqansu Abba" Da ameen duk suka amsa Saidai deep down batool da zee sunsan wannan addu'ar ta Abba ce kadai don mujaheed nanan da ranshi Cigaba da firarsu sukayi wanda duk ta deen ce, Aysha nabasu labarin yarintarshi wanda itama ummie ke bata su don sosai Aysha ke kaunar deen dukda bata zo ta tardashi ba, da kingata zaune da ummie to labarin deen suke har wani dadi takeji idan ummie na fadin abubbuwan data biyo nashi musanmman a hallaya sai tajita cikin shauqi na musanmman. Sai gab da magrib drivern gidansu Aysha yazo Saida suka rakata wajen ummu batool sukayi bankwana inda tabata kyautar turarruka takuma bata saqon gaisuwa ga umminsu sannan tacewa batool ta dauki rubber dambun naman datayimata dazu a kitchen idan sun sauka tabata, godiya sosai Aysha tayimata sannan suka fito Atare su ukun suka sauko qasa suna tafe suna fira cikin raha Wucewa batool tayi don yin yadda ummu batool tace sukuma suka nufi kofa. Wayar Aysha ce tayi ringing daidai sun kusa isa bakin kofar Dubawa tayi saikuma ta dago ta kalli zee Harara zee ta gallamata cikin wasa ta kauda kai don ko ba'a fadaba tasan wannan umar dinne Dan murmushi Aysha tayi sai kuma tayi saurin yin gaba don amsa kiran kafin ta tsinke Dayake sauri take kuma hankalinta na kan waya bata lura da bude kofar da aka rigata yiba tasa kai sai quuuum! Taji taci karo da abu Yar qara tasaki taja baya tana sosa goshinta cikin yanayin jin zafi "ya sallam! Are you ok?" Taji muryar zee dake qarasowa na fada a bayanta Daga kai tayi taga mai ya qumeta sai taganshi shima tsaye yana murza goshinshi cikin yanayin jin zafi Sanye yake da farar spotless shirt da baqin wando sai lapcoat dinshi rataye a kafada Dagowa yayi shima ya kalleta sai suka hada ido Ganin yadda ya 6ata fuska yana kallonta yasata Dan buda idanu tace "oh! Sorry" Bece komai ba Sai duqawa dayayi yana tsintar Wayar data fadi qasa Binshi da kallo tayi sai taga ashe Wayar hannunta ne ta fadi Kafin tayi wani abu harya miqe ya miqomata "oh, thanks.. So much" tafada tana amsar Wayar Kada kai yayi "always be careful kuma ki dinga kallon gabanki don next time bazaki sa'ar karo da abu mai taushi kamar goshina ba, sai abu mai mugun tauri kamar garuu" Dariya zee da batool data fito yanzu sukayi yayinda Aysha ta 6ata fuska "wayace maka goshin naka da taushi? Dafarko nayi tunanin da dutsin marmara(rock) naci karo" Wani kallo yayimata yace "koba dutsin marmara ba" ya cigaba da tafiyarshi "gayamashi dai ukhtie, kedai idan kika koma gida ki tabbatar ummie takaiki kinga mai duba qashin kai, kar ace wani wuri ya tsage baki sani ba" inji batool Dariya Aysha da zee sukasa yayinda aymaan ya dakata Daga tafiyarshi ya juyo ya kalleta sai kuma ya cije lip ya girgiza kai "kinci sa'a agajiye nake yanzu amma ki kiyayi haduwarmu" Dariya suka sake sawa shikuma ya cigaba da tafiyarshi ya nufi stairs "ammm... Akhie?" Jin Hakan yasashi dakatawa daga hawan stairs din dazai fara saiya juyo Fuska dauke da murmushi tadan qara matsowa gabanshi "erm.. Dama akan abinda yafaru jiyane... Am sorry on my behalf, my brother's and my mum. Am sorry about that and that won't happen again insha allah" Sai a lokacin yama shaidata, kamar wanda yagani tareda wannan marar mutuncin jiya Kallon zee yayi sai itama tadan tako tana cewa "Aysha... Sunanta Aysha, qanwar mussadiq, tazo bayar da haquri ne on his behalf" Sake maida kallonshi yayi akan Aysha da tadan sha jinin jikinta Ganin yadda yanayin fuskarshi ta chanza Dan ta6e baki yayi yace "oh? Thanks then" saiya juya ya cigaba da tafiyarshi harya haye sama Bataji dadin Hakan ba don sai taga kamar shi be haqura ba Zee ce tadan yi Dariya tace "Dayake yanzu yadawo kuma ya kwaso gajiya, don't worry Hakan yake idan yana gajiye" inji zee duk don Aysha taji Dama dama "saikace wani ya aikeshi ba" inji batool tana qarasowa itama Murmushi Aysha tayi tace "ai dole, aikin hospital akwai wahala" Da Hakan suka juya suka fita daga falon sukayi mata rakiya har mota. Shiga tayi gidan baya duk suka miqamata kayayyakinta sannan ta rufo kofar suka Shiga daga ma juna hannu "sai monday ko?" inji Aysha Murmushi zee tayi saita kadamata kai "to allah ya kaimu, zamuyi waya... Ukhtie sai munyi waya" ta maida akalar maganar ga batool Ansawa sukayi da to shikenan sannan suka cigaba da dagama juna hannu har suka fita daga gidan Juyowa sukayi xasu koma ciki "meyasa baki gayamata kinfita daga school din ba" "let her find out herself" zee ta amsa suna shigewa cikin gidan **** A satin zee zaman fita gida tayi don anacan ana mata cukucukun Shiga school dinsu batool Cikin satin aka gama komai saiya kasance monday mai zuwa xatafara zuwa school din, murna wajen batool ba'a magana A bangaren Aysha kuma ganin zee bata zuwa school ta addabeta da kira tana tambayar lafiya tabar zuwa school Daga baya dai zee tafito ta gayamata Gaskiya cewa an chanxa mata school ne Aysha bataji dadi ba kwata2 sai tayi tunanin ko dama basu huceba kawai pretending sukayi komai ya wuce Zee tace mata wlh komai ya wuce ita kanta batasan da barin makarantar ba sai daga baya kuma ai Hakan baxai shafi abotarsu ba tunda ga waya Haka dai sukayi sallama rai babu dadi musanmman zee datakejin duk bata kyautawa Aysha ba, amma ya ta iya? Sosai komai yafara dawowa normal, zee tafara zuwa school kuma babu laifi tana jin dadin school din dukda basu kamo kafar school dinsu Aysha a karatu ba Koda yaushe tare suke da batool sai idan dayansu na class kuma kullum tare suke zuwa suna dawowa a motar batool Koda kuwa mutum daya keda lecture ranar. A 6angaren aymaan kuwa Sosai hankalinshi ya kwanta da Hakan don shi dama hankalinshi be kwanta da wancan makarantar kawai amincewa yayi don babu yadda ya iya amma yanzu hankalinshi ya kwanta tunda kullum suna tare da batool. Yau wednesday. Tafe zee take tareda batool zasu nufi parking space don tafiya gida Suna tafe suna firarsu "nikuma wlh sai inga gwara mubari sai komai ya lafa sannan, kinga fa ga exam nan around the corner, yanzu lokacin karatu ne Sosai" inji batool "au sai yanzu za'ayi karatun sosai kenan. Matsalata da to irinku kenan bakwa fuskantar abu dawuri sai wuri ya fara qurewa, ni ko yanzu akace kule cass zance" inji zee tana juya idanu Kya6e baki batool tayi tana mata kallon sheqeqe "sannu, to waye yace miki shi be shirya ba? Nima ko yanzu akace min kule cass zance" "A'a wlh, akace miki kule yanzu zubawa aguje zakiyi kaffafu na ta6o qeya" "kutt.. Amma kin qoshi saura juice" inji batool tana kwafa Dariya zee tayi tace "juice dinma nariga na kora dash...." Kasa qarasa maganarta tayi, lokaci guda ta damqi hannun batool da qarfi Saurin kallonta batool tayi sai gani tayi wani wuri take kallo Hakan yasa itama kallon wajen Itama wara idanu tayi cikin tsantsar mammaki _Mussadiq?!_.... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:42 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *069* *RIVALRY* Zaune yake kan booth din wata danqareriyar baqar motar mai salqi Sanye yake cikin tsaddadun qanannun kaya farin wando da farar t-shirt mai guntun hannu wanda ya taimaka wajen bayyana damtsen hannunshi ya dora baqar guntuwar jacket akai Gyarariyar sumar kanshi tayi luff sai sheqin gyara datake Idanunshi dade da shade as usual kanshi a duqe yana dandanna faskekiyar wayar hannunshi Kallon juna zee da batool sukayi sai kuma suka maida kallonsu akanshi Tsayawa sukayi suna kallonshi, bawai don yamasu kyau ba ko wani abu sai don yanayin dayayi parking din motarshi da yadda yayi blocking Motarsu zee yadda bazata iya fita ba saiya janye tashi Qara kallon juna sukayi cikin rashin sanin abinyi gashi ko sau daya be dago ba da alamu ma besan da wanzuwarsu ba awajen Batool ce tayi qarfin halin qarasawa wajen mottocin sannan cikin sakin fuska tayimashi sallama Ahankali ya dago ya dora idanunshi dake cikin shade akanta Badon taga motsin la66anshi ba da bazata san ya amsa sallamar ba "amm... Excuse me, I think you have to adjust your car, you've blocked ours" tafada tana nuna nasu motar Kallon motar data nuna yayi saiya yatsuna fuska kamar yaga abin kyama ya maida hankalinshi akan wayarshi again Daga girarenta batool tayi cikin mammakin abinda yayi saita juyo ta kalli zee dake baya tana kallonsu with unreadable expression Sake maido kallonta tayi kanshi sannan a karo na biyu tasake mashi magana Saidai wannan karon cikin larabci "nace ka tare mana hanya, ka gyara parking motarka fita zamuyi da motar mu" Sake Dagowa yayi ya kalleta a yatsine cikin gadara kamar mai ciwon baki yace "Me kike buqata wai?" "motarmu nace, ka taremu ka gyara parking" tafada patiently Qara kallon motar yayi a yatsine sannan yace "kijira nayi abinda yakawoni nagama sannan" Kallon mammaki tashiga yimashi "mujira kagama abinda ya kawoka? How?" Karkatawa yayi ya zaro bundle din kudi ya ajiye daga qarshen booth din inda batool take "take and go" Yafada yana maida hankalinshi akan wayarshi "And what was that for??" yaji muryar da Tundazu ita yake son ji na fadin Hakan Sake Dagowa yayi ya kalleta, fuskar da kwadayin ganinta ya hanashi sukuni a yan kwanakinnan Zee ce data qaraso wajen itama tsaye Hannu daya riqeda kugu fuskarnan a tsuke Kallon up and down yayimata sannan yasake Karkatawa yasa hannu a aljihu ya zaro wani bundle din ya dora akan dayan ya sake maida hankalinshi akan abinda yakeyi Ran zee yasake 6aci "seems you're deaf, cewa tayi ka gyara motarka zata fidda tata" "shiyasa nabaku wannan kuje kusha coffee kafin nagama abinda nake na dauke" "waye anan yayi maka kama da mayunwacin coffee ko almajira?" "almajira? A ganina kowa anan yasan wacece" yafada yana mata wani kallo Wani abu yasake tsayamata a wuya "look, ko ka dauke wannan kwasgwamar motar ka ko mukira maka security yanzunnan" tafada cikin quluwa Besan lokacin da wani murmushi ya su6uce mashi ba wanda Hakan ya bayyana dimple dinshi na gefen haggu Ahankali ya zare shade din idanunshi ya zuba mata oily eyes dinshi da kallonsu ke tsundumata cikin wani yanayi "Go ahead mhiz" yafada ahankali gefen bakinshi dauke da smirk Afusace tajuya zata bar wajen batool tayi saurin Kamo hannunta itakuma ta fizge ta cigaba da tafiyarta Binta da kallo su biyu suke wani murmushin na qara kufcewa Mussadiq. Wai shi zatakai qara wajen security, lallai yarinyar nan get mind "please ka gyara motar ka mutafi mu bama neman rigima" inji batool Kallo daya yayimata ya dauke kanshi ya maida a wayarshi Hakan yasa tayi shiru ta tsaya Kallon ikon allah Lallai sai yau ta ida yarda da zancen zee na mutumin nan bayada mutunci ko diss Suna ahaka saiga zee ta taho biye da wani security a bayanta Sosai Hakan yaba mussadiq Dariya ganin yadda ta taho rai a Hade wani sololon security biyeda ita wai nan shi ta kiramawa Qarfin halinta ba qaramin Dariya yake bashi ba saiya fuske yayi kamar besan dasuba har suka qaraso "yauwa, gashi nan" inji zee tana nunashi Security din ya kalli gayen yace ""kai dagaske ne kayi blocking din Motarsu kuma kaqi kaucewa su fita?" yafada cikin cin serious Dagowa mussadiq yayi ya kalli security din da ya Hade fuskarnan alamun babu wasa Sa hannu yayi ahankali ya zare shade din idanunshi ya zuba mashi su sannan ahankali yace "Wani abu nakeyi, idan nagama zan Janye" Wani mugun kwarjini mussadiq yayima security din Hakan yasashi fara kame kame "am.. To..to ka kusan gamawa?" "eh" ya amsa a gajarce yana sake maida hankalinshi kan wayarshi Juyowa security din yayi ya kalli zee "to, ko kubari zuwa anjima idan kuka fito daga lectur..." "kamar yaya mubari sai anjima? Wane lecture zamu gama bayan wanda muka riga muka gama, yanzu gida zamu to. What the hell is he doing da dole saiya gama zai Janye mu wuce?" inji zee dakeji kamar tayi bindiga "to yanzu yaya kike son ayi bayan yace..." "kaga kyaleta, dauki wannan kayi tafiyarka komai zaiyi daidai" mussadiq ya katseshi da fadin Hakan yana turamashi kudadden daya Fiddo dasu Saurin dauka security din yayi yana washe baki yana zuba Godiya Yayinda ko kallonshi mussadiq be qara yiba Zuwa security din yayi ya wuce su zee dasuka saki baki Suna kallonshi batareda yako sake kallonsu ba Ran zee ya qara 6aci "you know what? Am a king everywhere I go, I was born to rule and my instructions are made just to be followed, don haka kowa zaki kira babu abinda zasu iyayi, I mean har shugaban makarantar nan, so is better kujira din harna tashi tafiya" Cikin huci zee tace "you're born to rule the morons not someone like me, am a Queen myself. I rule also and giving instructions is also my role, I'll never follow instructions From someone like you, never!" Fizgo hannun batool da Tundazu tazama yar kallo tayi suka nufi gate Dan murmushi mussadiq yayi yana Kada kai "we shall see" yafada under his breath Bata saki hannunta ba har Saida suka fita daga school din "meye haka to zee? Da kika fiddomu nan me zamuyi?" "cab zamu samu muhau yakaimu gida" "motar fa?" "ya cinye ya kora da ruwa" ta amsa still tana huci "hmm, zee kenan. Nifa banga abin tada jijiyar wuya anan ba, kinsan kowaye wannan mutumin basai an fadamaki ba, sai inga gwara mubishi ahankali ya bari mu Fiddo motar" "ke kije to kibishi ahankalin, ni allah yasani bazan iyaba. The guy is so rude, wai mema ya kawoshi nan?" "hmm who knows" "to nidai da naje yaimin wulaqancin da zanyi sati inajin ciwonshi gwara na haqura nahau cab" "to idan muka koma gida akace ina motar fa?" "Sai muce ta lallace ne tana school gobe zamuje da mechanic ya gyara" Kada kai batool tayi "to shikenan, amma gayen nan beda mutunci sam" "fadi 6ata baki, kwata2 halinshi yasha banban dasu, wani mummuna dashi" Dariya batool tayi "idan mummuna ne to shima Deen mummuna ne tunda kamar su daya" "whatever" inji zee tana juya idanu Haka suka tsaya suna jiran cab dazai kaisu gida Saidai duk wacce tazo wucewa idan suka tsaidata bata tsayawa bare ma akaiga a daidaita Wasa wasa suna nan tsaye har tsawon Mintuna talatin, ga Cab din na wucewa amma yadda kasan basa ganinsu don ko alamun tsayawa babu wacce tayi wajensu Abin mammaki kuma wasu cab din saisu wucesu suje su tsaya agaban wasu dasuma suke jiran abin hawan, sai gashi dik wadanda suka taddasu can sai tafiya suke Abin sosai yabasu mammaki don duk tsaidawar dasukema cab basa tsayawa yadda kasan they are invisible, ahaka har sukayi awa daya tsaye bakin titi. Izuwa lokacin duk sun gaji ga rana daketa kwalarsu Suna tsaye motarshi tafito daga makarantar tazo taja burki a gabansu Sauke glass din gefenshi yayi yana kallonsu fuskarshi dauke da smirk "na gayamaki, am a king, I rule. Tunda nace saina gama abinda nakeyi na tafi sannan zaku tafi, qaramar qwalwarki yakamata ta gayamaki Hakan za'ayi. Ko zaku shekara anan babu wanda zai tsaya bare yaji ina zaku ya kaiku. Yanzu kunada za6i biyu, Is either kuje ku dauki motar ku kutafi ko kuma kuje gida qasa, have a nice day" Yana kaiwa nan ya wana glass din motar sama ya ja motarshi yawuce yabarsu anan. Bin motar sukayi da kallo har tayi nisa "kutt... Wlh gayen nan kwahi yaimana" inji batool saikuma ta fashe da Dariya Wani qululun baqinciki ya tokarema zee wuya "kwahi? Aikau Saidai yau mukoma gida qasa, allah bazan shiga motar nan ba" inji zee cikin kunar rai tanajin kamar tayi kuka Wata Dariyar batool ta fashe daita tace "ana nan dai, ai two option yabada is either mutafi mu dauko motar ko mutafi a qasa, kinga idan ma kika tafi a qasan duk cikin option dinshi ne, gwara muyi fuska muje mu dauko motar kawai" Haushi zee taji yaqara qumeta "nikuma baxanyi ko daya daga ciki ba, bari kigani" tafada tana zaro wayarta daga cikin jakka Number Aymaan ta lalubo ta buga Saidai akace a kashe take, sake bugawa tayi nan ma haka "ki bugama Ahmad yazo ya daukemu number Aymaan bata shiga" Wayarta batool ta zaro don yin yadda tace din Saidai shima bata shiga Number Aysha zee ta lalubo tsabar dai tanason proving dinshi wrong Saidai itama tata bata shiga "omg! Wlh gayen nan dagaske yake, Ato tun wuri bari kiga muyi yadda yace" inji batool tana Dariya sosai wanda ita zee Dariyar ke qara tunzurata don ita bataga abin Dariya ba anan Anan batool tabarta tsaye tana ta lalube laluben numbobi tawuce cikin school din don dauko motar. Harta dauko tadawo zee nanan inda take tanata jaraba kira amma still basa shiga gashi taqi haqura Parking kusada ita tayi ta leqo tace "zee wlh kitaho mutafi, tunda yace Hakan Hakan za'ayi, bakisan kwahin yan biyu ba ko?" Ko kallonta zee bata yiba "haba sis kitaho mutafi kiyi hqr, ko babu komai in-law dinki ne, qila wasan qanen miji yafara yimaki tun yanzu" "batool, wlh tlh ki kiyayeni, tom" inji zee cikin quluwa Dariya batool ta fashe dashi tana rufe baki "to kiyi hqr nabari, yanzu dai don Allah kishigo mutafi" Saida batool taita roqonta tareda rarrashi sannan Dakyar ta yarda ta shigo motar sai kumburi take itakau batool banda qumshe Dariya babu abinda takeyi, taja motar suka halba titi suka dauki hanyar gida Ranar da 6acin ran abinda mussadiq yayimata ta kwana ga haushin batool dake mata Dariya every now and then Washegari Zee na zaune a aji tana ida wani rubutu kafin ta tashi ta fita wani student yazo wajenta yayimata sallama Dagowa tayi ta kalleshi ta amsa tana mashi kallo mai alamar tambaya "you're called in bio-chem lab" "bio-chem lab? Ni?" "eh, koba kece Zainab Farouq ba?" Kada kai tayi "eh nice" "to you're called" "ok thanks" Binshi da kallo tayi harya fita tana Tambayar kanta neman me akeyi mata to? Kasa ida abinda takeyi tayi ta tattarasu ta zuba cikin jakka ta tashi ta fita Direct laboratory din tanufa Kofar arufe take Hakan yasa ta bubbuga Izinin shigowar da aka bata yasata tura kofar tashiga ciki Qarasawa tayi ciki da sallama Saidai kingin sallamar sun maqale ne lokacin da sukayi ido hudu da juna Tsayawa tayi tana kallonshi cikin mammakin ganinshi anan sai kuma takama waigen lab din don ganin wanda yasa a kirata amma babu kowa ciki sai shi kadai "ni nasa akiraki" yafada yana dan ta6e baki Maido kallonta tayi akanshi tana jin wani qululun haushi na tasomata "sit, kin tsaya kina kallona da wadannan idanun, I don’t like them" _O'O! I don’t like them_ Maganarshi ta yanzu ta tunomata da maganar Deen Juyawa tayi zata koma ta inda tafito "ba cewa nayi kifita ba" "Sai kace? I did what I want at the time I want to" "kuma shine nasa kizo nan kika zo din?" "that's because bansan kaine ba and now that I know am doing the right thing" tafada tana nufar kofa Batasan ya akayi ba sai kawai taji ansha gabanta, it's so sudden har Saida tadan ja baya a tsorace "bakiyi abinda ya kawo ki ba zaki tafi? You must be joking" "look mallam get out of my way, meye zaka wani taremin hanya?" "saboda ban gama dake ba kike niyyar tafiya, kibari nabaki izinin yin Hakan tukkuna" "waxaka ba izini? You must be joking" Nufota yayi cikin majestical takunshi yana matsowa daf daita "Did I look like a comedian to you?" Dan takawa baya tayi ganin kusancin na neman yin yawa tana kallonshi shima ya tako, with every takunta baya shikuma takushi ne towards her "wai meye Hakan ne? Get out of my way" tafada tana kallonshi gabanta na dan faduwa "banyi abinda yasa nakiraki ba" "meyasa ka kirani din? I thought kace nabar bibiyarka yanzu cikin ni dakai wake bibiyar wani?" "ke lokacin dakika bibiyeni na hanaki Hakan?, nima yanzu its my turn so is better ki saurareni ko in saki saurarona don dole" Yanayin dayayi maganar yana qara matsowa gabanta yasata danjin tsoro "naji dakata... Ina Jinka, Menene?" tafada cikin quluwa "sit first" "sauri nake, basai na zauna ba, fadi abinda zaka fadi naqara gaba" "tun jiya ya kamata kisan duk abinda nace ba'a yimin gardama, ki zauna konasaki zaman kwana uku batareda kin iya ko yunqurin tashi ba" Besan sadda murmushi ya kufce mashi ba ganin tayi saurin neman wuri ta zauna tun kafin ma ya ida "Good for you" yafada yana qara murmushin shi na gefen baki "kaga inada abinyi, Menene?" inji zee dake jin kamar taita ihu, gashi sotake ta tashi amma tsoro takeji yace zai zaunar daita takasa tashi na kwana uku, kenan kwahi zai sake yimata? Haye dogon desk dake gefe yayi ya zauna sannan ya kalleta yace "magana zamuyi" Shiru tayi batace komai ba kuma bata kalleshi ba "meyasa kikabar Annur?" "saboda naga dama" ta amsa a qulle "wannan ba amsa bace, I repeat meyasa kika bar Annur?" "bansaniba, look mallam inada abubbuwan yi dayawa, danasan kaine tun farko baxakaga qeyata anan ba" "da kinsani kikace, idan kinji ance danasani to abin yariga yafaru babu yadda aka iya akai don haka kiyi shiru kibani amsata" yafada commandingly "kai kasani a school din Da zakazo ka tsareni kana tambayata meyasa nafita, nina shiga saboda ina ra'ayin Hakan kuma nafito a lokacin danake so" "Ko ya fiddaki ba" "waye?" "kin fini sani. tell me, meye hadinki dashi?" "shi wa?" ta tambaya tana mashi wani kallon haushi "wannan mahaukacin dake binki akoina waiting for opportunity don nuna gwaninta, bayan duk kuri ne" yafada yana yatsina fuska "oh? Kana nufin wanda yasan darajar mace kuma yake kishin ganin anci zarafinta?" "A'a, ina nufin wanda burinshi yasamu dama koyaya ne na nuna gwanintarshi ta bogi ga mace" "kuma saigashi gwanintar tashi ta bogin ta qayyatar don sau dubu yafi mai daga hannu da niyyar dukan mace" Dan murmushi yayi sannan ahankali ya zare shade din idanunshi "waya koyamiki baqar magana?" "idan ka gama zan tafi inada abubbuwan yi" tafada tana kauda kai gefe "riqeqi nayi dama? Kawai dai kisani da kin tashi batareda nagama ba tau zaki kasance a tsaye har gobe warhaka or better still kiyita tafiya har gobe warhaka" Jitayi ranta ya qara 6aci "Me kake nufi da Hakan? Kwahi zakayimin?" tafada a fusace Wannan karon he can't help but chuckle "kwahi? Meye Hakan?" "kafini sani, cemaka akayi don jiya kayi min shizaisa naji tsoron ka?!" Yanzu ma murmushi ya kufce mashi mai sauti wanda Hakan yaqara lo6ar da dimple dinshi "kinga, am here for something different gashi kina samu muna wata maganar daban, you're wasting my precious time" Kasa magana tayi saboda haushi, wai ita kema 6atamashi lokaci "nasan shi ya fiddaki a school din saboda wani banzan dalilinshi na kareki, abinda besaniba shine am limitless, ina keta duk inda naga dama a lokacin da naga dama, the guy is so full of himself bayan babu abinda yasani sai hauka, maybe shiyasa tun farkon haduwata dashi naji beyimin ba, it's better ki bashi shawara tunda kunfi kusa akan yasan dawa dawa zaija da don sahun giwa ya take na raqumi, yayi kadan yaja dani, daga mashi kafa nake and I don’t think zan cigaba da daga mashi Ita" Dakatawa yayi yaji ko xatace wani abu saiyaga batada niyyar cewa komai don bama shi take kallo ba Hakan yasashi cigaba "secondly, maganar dakika fadamin ranar a office is still stocked in my brain, bansan ma'anarta ba Amma I bet you zan sani, zan gano Saidai ina baki shawarar don’t try to play cunny plays with me don am a turtle itself, slow but cunny. Kifita daga harkata for your own Good" Qara Dakatawa yayi yaji me zatace Saidai still tayi mashi shiru Hakan yasa yasan maidashi fool tayi wanda dama best answer dinshi shine shiru, Saidai Hakan be dameshi ba tunda dai taji duk abinda yace kuma dama ba wadannan magangganun kadai suka kawoshi ba harda wani dalili nashi daban so be damu ba. Tashi yayi tsaye yana maida shade din hannunshi a idanu "fatan kin fahimci dukkan magangganuna kuma zakiyi amfani dasu.. For your own Good... Have a wonderful day" Yana kaiwa nan ya juya yabar lab din in his usual majestical steps Ajiyar zuciya zee ta sauke, lallai mutumin nan ya cika dan rainin hankali, ita duk acikin magangganunshi babu wanda tayi mata ma'ana "mtcheew, aikin banza kawai" tafada tana miqewa tsaye itama ta fita daga lab din Daga ranar kuma bata sake ganin ko mai kama dashi ba a school din. Everything keep going smoothly har kwatsam watarana ta tashi da text din Aysha a wayarta *_Am sick, ki tayani da addu'a, I don’t know if I can survive it_* Sosai hankalin zee ya tashi lokacin dataga text din. Sukan kwana biyu yanzu basuyi waya ba don sun rage waya ba kamar da ba kuma zee na kyautata zaton har lokacin fushi take saboda tabar Annur don tun a lokacin tadan ja baya kadan da ita, suna yin waya amma not very often kamar da Babu 6ata lokaci ta kira number tata Saidai bata shiga Hakan yasa hankalinta qara tashi Koda tagayama batool saita bata shawarar su gwadawa ummie suji ya zatace Koda suka gwadawa ummie itama ummie ta nuna damuwar ta akai sosai sai tace ya kamata suje su dubota Jin Hakan yasa zee qwalalo idanu Da farko taso qin yarda amma sai Ummu batool ta nunamata muhinmmancin yin Hakan kuma bayan Hakan Aysha nada kirki sosai ta yaba da hankalinta kuma tunda har ta iya yimata text tana a halin ciwo be kamata tayi watsi daita ba Da Hakan zee ta yarda da zuwan amma deep down a tsorace take, babu wanda take fargabar haduwa daita kamar ummie don ko muryarta taji ta waya sai tajita wani iri bare ace taganta a zahiri. Ahakan suka yanke shawarar gobe insha allah zasuje don dama zee tasan address dinsu don Aysha ta dade da bata complimentary card dinta. Washegari daya kama saturday suka shirya wajajen bayan la'asar suka fita suka hau cab don motar batool tasamu matsala tana wajen gyara ga Aymaan tunda safe yafita don kwanan nan he's always busy. Cab suka tsaida suna fadamashi unguwar dazasu yace su shigo don unguwar sannaniyar unguwa ce a garin. Shiga sukayi sannan yaja motar suka shilla Tunda suka shigo unguwar suke kalle kalle ta window, unguwar is so silent ga street din very smooth ga gidaje masu shegen kyau sunata wucewa Ahaka har sukaji Motarsu ta tsaya Kallon kofar tangamemen gidan dasuka tsaya sukayi sannan suka kalli juna Batool ce tafara bude murfin kofar tafita sannan itama zee ta fito Tsayawa sukayi kallon kofar gidan cikin shagaltuwa Saida mai cab yayi masu horn sannan suka tuna basu sallameshi ba Zee ce ta zuge jakkarta ta sallameshi sannan ta dawo wajen batool suna cigaba da kallon tangamemen gate din gidan Su tunaninsu ma ta ina zasu fara bubbuga gate din Qarasawa sukayi bakin qaramar kofar dake maqale da gate din batool tashiga kwankwasawa Basu dade suna kwankwasawa ba aka bude wani dan taga dake daga saman qaramar kofar gate din ana leqosu "yes? Kusu wanene?" inji mai leqen Kasancewar da larabci yayi magana batool ce ta amsa "mu qawayen Aysha ce, munzo ganinta fatan nan ne gidansu" Shiru yayi yana kallonsu, can yace "bari nakira na sanar, suwaye za'ace?" "kace da Zainab da batool ne" Be sake amsawa ba ya maida Wurin ya rufe Kallon juna sukayi "kaji manya" inji batool tana chuckling Dan ta6e baki zee tayi batace komai ba Suna ahaka sukaji alamun za'a bude kofar Hakan yasa suka maida hankali kanta Kofar gabadaya aka bude yanzu mutumin dazu yasake bayyana "bismillah, kushigo ciki" Batool ce tayi gaba zee na biye daita suka shiga gidan Dan Wara idanu sukayi ganin tafkeken qayattacen gidan dasuka tsinci kansu aciki "muje" inji wani daban mai irin shigar wanda ya bude masu gate Binshi sukayi abaya suna taka shinfidaddiyar kwalta din wajen suna bin silent street din wajen da kallo da yadda aka qawata koina da furrani. Sun danyi tafiya sannan suka qarasa main entrance din Door bell mutumin daya rakosu ya danna, can bayan some seconds aka bude kofar wata maid ta bayyana Sannu da zuwa tayimasu sannan ta kauce tayimasu iso ciki Yanzu ma batool ce tafara shiga zee na bayanta gabanta banda faduwa babu abinda yakeyi. Wow! Kowanne yayi gasping a zuciyarshi ganin irin haduwa da tsaruwar da falon yayi. Fadar irin qayatuwar da falon yayi 6ata baki ne Saidai mai karatu ya hasaso ma kanshi Iso maid din tayimasu tana wucewa Wurin stairs Cigaba da binta sukayi suna yi suna yan kalle kalle a falon Hawan stairs din suka shiga yi wanda shima kanshi abin kallo ne suka cigaba da bin maid din har suka isa sama Wani falon suka sake iskewa sama wanda tsakaninshi dana qasa sun rasa wane yafi kyau, abu daya kawai suka sani, wancan na qasan yafi girma. Cikin girmamawa maid din ta nuna masu wajen zama duk suka yima kansu matsugguni a kan dakkakun kujerun falon Kan kace me? Har anfara cika masu gabansu da kayan motsa baki sannan aka tafi aka barsu bayan angayamasu suyi making kansu comfortable Kasa ta6a ko daya daga cikin abubbuwan da aka ajiyemusu agaba sukayi sai kalle kallen dasuka cigaba dayi suna jinjina dukiyar da aka narkar wajen qera wannan qerarren gidan Ahaka sukaji sallamar ummie cikin cool muryarta, muryar data sanya gaban zee faduwa Amsawa duk sukayi suna Dagowa. Gaban zee yasake yankewa ya fadi Wasu irin emotions ne suka shiga building up a zuciyarta still idanunta akan matar da take Deen sak ajikinta Harta qaraso ta zauna idanunta na kanta Gani tayi tana magana fuskarta dauke da murmushi amma batasan me tace ba, hankalinta yayi nisa Mintsinin da batool tayimata ya maido ta daga duniyar kallon ummie data tafi Sai a lokacin taga ashe batool ta zamo qasa tana gaidata Hakan yasa itama zamowa qasa tana gaidata cikin rawar murya Amsawa ummie tayi tana cewa su tashi su koma kan kujera amma sukaqi Zee najin batool na Tambayarta ya jikin Aysha itakuma tana amsa mata da sauki sosai tana ma daki Duk maganar dasukeyi zee kanta na qasa tana battling da hawayen dake son kwacemata "wacece takwarata acikin ku?" inji ummie cikin fara'a Batool ta nuna zee cikin murmushi "Zainab.." Dagowa zee tayi ahankali tasake kallonta Miqomata hannu ummie tayi alamun tazo Kamar wanda aka ingiza sai gani tayi ta rarrafa wajenta da sauri ta riqe hannun nata ta damqesu ta dora fuskarta akai hawayen datake riqewa suka 6allemata Sosai Hakan yaba ummie mammaki don harda sheshekarta To meya sata kuka? Ko tunani take jikin Aysha yayi tsanani? Tambayar da ummie tayiwa kanta kenan Hakan yasata dago fuskarta tana share mata hawayenta fuskarta dauke da murmushi "karki damu diyata, ai Ayshar ma jikin yayi sauqi, kibar kuka" Wasu sabbin hawayen suka sake gangaromata Wannan wane marar imani ne? Wane mai qonnaniyar zuciya ne ya raba uwa da danta na tsayin shekaru batareda kowannensu yasan da wanzuwar dayan ba? Wane marar imani yayi Hakan? Jitayi ta tadota tsaye tana cewa sutaho takaisu su ganta don ita harga allah tayi tunanin ciwon Aysha din takema kuka Tare suka jera suka tafi har suka isa bakin kofar dakin Aysha Kwankwasawa ummie tayi sannan ta Murda handle din kofar tashiga hannunta jaye dana Zainab A zaune Aysha take kofin shayi a hannunta da alamu shi take sha, ga hannun daure da cannular da alamun Saida akayi mata qarin wani abu ajikinta Sosai Aysha ta wara idanu ganin su zee don bata ta6a zaton zatazo ba Da sauri ta ajiye cup din hannunta ta Wara mata hannu zee tayi sauri ta qaraso itama suka rungume juna cikin shauqi suna Fashewa da kuka atare, kowanne da ma'anar kukan shi Zee kukan da bata ida ba na dazu ne itakuma Aysha nata na daban ne. "Ummie, na rabu dashi... Narabu da Umar.. Finally na rabu dashi" inji Aysha cikin kuka Jin Hakan yasa zee Saurin dagota tana kallonta da mammaki "kin rabu dashi?" inji zee cikin mammaki Kada kai Aysha tayi hawaye nasake gangaromata "eh, nima na gano Gaskiya ummie, Umar baya sona, Finally zuciyata ta yarda da Hakan. Ni kadai nake hauka na, Finally na gane Gaskiyar dakike son ganar dani, and I decided to let him go, Narabu dashi har abada Koda Hakan na nufin rasa rayuwata" "bazaki rasa rayuwarki ba Aysha, ba akan wannan mutumin ba.. Don be cancanci Hakan ba, be cancanci Koda digon hawayenki ba, insha allah zakiyi farinciki without him, you'll move on zaki samu wanda nan gaba zaki waiwaya rayuwarki tabaya dashi kiyi murmushi kice gwamma da akayi" Sake rungumeta Aysha tayi gam tanajin sauqin abinda takeji a zuciyarta a sanadin magangganun zee. Murmushi ummie tayi sannan tajuya tabar dakin tana qara jin qaunar Zainab har cikin zuciyarta Batool ce ta qaraso wajensu itama ta zauna ta kamo hannun Aysha Hakan yasa ta dago ta kalleta "kiyi hqr Aysha, wani abin muna sonshi ne amma ba alhairi bane a garemu, wanda allah ya taqaitama wahala sune suke gane Hakan da wuri, Kiyi hqr kiyita addu'ar allah yasa Hakan shiyafi alhairi kuma ya za6a miki Mafi alhairi" Haka sukaita bata shawarwaru da kwantar mata da hankali Sai gashi taji sauqin zuciyarta sosai sanadin qarfin gwiwar dasukayita bata Sai gashi daga baya ummie tashigo ta iske suna fira cikin nishadi Aysha harda Dariya Sosai abin yabata mammaki, yarinyar da yau kwana uku kenan ko magana batayi sai hawaye Dadi sosai ummie taji tafita tasa aka aika musu da abinci Tare suka ci suna fira wanda Hakan ba qaramin taimaka ma Aysha yayi wajen rage nauyin zuciyarta. Ganin magrib takusa yasa suka fara haramar tafiya Duk yadda Aysha taso qara tsaidasu qiyawa sukayi don Saida ummie dama ta bige musu warning kan karsuyi dare. Tare suka fito da Aysha falon saman suna tafe suna Dariyar firarsu Qamshin turaren da zee taji yasata dagowa ta kallo falon idanunshi suka gauraya Zaune yake gaban ummie aqasa yana dan mammatsa mata qafa Saurin Janye idanunta tayi akanshi suna ida Qarasowa falon Ganinsu yasa ummie fara washe baki "tafiya zakuyi tun yanzu?" inji ummie "wlh kau ummie, ance karmuyi dare ne" inji batool "Gaskiya kam, Hakan yayi sosai ai mun gode qwarai, zuwanku ya samar da abinda kwana uku kenan muketa fama bamu samu ba, Allah yasaka da alhairi, allah yayimaku albarka" Cikin jindadin addu'arta suka shiga amsawa da amin Kallon mussadiq da kanshi ke qasa haryanzu yana cigaba da tausa kafarta ummie tayi tace "kaga qawayen Aysha ko? Suna zuwa ta warware" Dagowa yayi yaimasu kallon seconds 2 yace "oh? Mungode" "takwara wannan shine yayan Aysha, mussadiq" Murmushi zee tayi sannan ta dan kalleshi "Good evening" tafada tana dauke kai "evening" ya amsa a taqaice batareda ya kalleta ba "Good evening yaya" inji batool Dagowa yayi ya kalleta sannan itama ya amsa a taqaice ya cigaba da abinda yakeyi "bunnaya, ka tashi hakanan kaje ka saukesu gida kaga dare yafara" inji ummie Atare duk suka kallo ummie cikin dan Wara idanu "na kaisu? Basuzo da mota ba?" "bazuso daita ba, ko?" ta maida akalar Tambayar kan zee "eh.. Amma ai zamu samu cab, babu damuwa" tafada hoping bazata matsa masu yakaisu din ba, she dont want to have any thing to do with him again "samun abin hawa anan unguwar ba qaramin wahala bane don basu cika Shigowa ba kuma idan kukace sai kunfita daga unguwar dare zakuyi, kubari yakaiku kawai, ai dama shima fita zaiyi yanzu" "ummie.. Driver yakaisu mana. Ni inada urgent meeting dazanyi yanzu" "nasan da Drivern nace ka kaisu ai, idan baxaka kaisu ba kafito ka fadamin sai nasan abunyi" Sunkuyar da kanshi yayi don yasan haushi taji sai yace "to ummie" Dan hararar shi tayi sannan ta maida kallonta kan su zee tana cewa "yauwa 'yayana kubari yakaiku kunji? Ina zuwa" Daga haka ta tashi ta nufi dakinta Shima tashi mussadiq yayi bayan wucewarta yanufi hanyar fita yana cewa "Don't waste my time" Binshi da kallo sukayi sannan batool da zee suka kalli juna sai zee taga kumshe Dariya ma take Hakan yaqara quleta saita dauke kai cikeda haushi Ummie ce tasake fitowa riqeda yar shopping bag a hannunta tabasu Dakyar tasasu amsa suna mata Godiya sannan suka rakosu har qasa har inda mussadiq ke jiransu cikin mota Batool ce tayi saurin wucewa ta bude back seat tashiga leaving zee da only option din Shiga front seat Badon taso ba ta bude kofar gaban ahankali tashiga itama Daga masu hannu ummie da Aysha suka shiga yi suna masu fatan tsari suma suna maida masu martani ta hanyar daga musu hannu Saida ummie taja mashi kunne akan gudu a titi sannan yaja motar suka bar gidan. Tunda suka hau kwalta babu mai cewa komai sai motar tayi tsitt kamar babu mutane ciki Dukda ummie tayi mashi gargadin gudu da mota Saida yayi dukda shi nan ba gudu yake ba Sosai, Saidai su zee a tsorace suke da speed din motar musanmman batool Saidai babu wanda yayi mashi magana allah allah kawai suke sukai gida ya saukesu Abin mammaki sai gashi batareda sun mashi kwatance ba yabi dasu hanya tiryan tiryan har cikin unguwarsu kuma har kofar gidansu Abin yabasu mammaki sosai don basu ta6a sanin yasan gidan ba. Lokacin har duhu duhun magrib yafara A kofar gidan yaja ya tsaya da motar daidai itama motar Aymaan tana danno kai opposite dinsu Hango motar yasa gaban zee faduwa tayi saurin fara qoqarin bude kofar Saidai tajita gamm alamun a kulle take Juyowa tayi ta kalli mussadiq a fusace daidai lokacin da Aymaan ya dallo hasken motarshi saitinsu Saurin Juyawa tayi tana kallon Aymaan ta cikin motarshi wanda yayi mutuwar zaune yana kallonsu suma... ✍️ Ummin fasihu 🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:42 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *070* *RIVALRY* Komai na Aymaan ne ya tsaya lokacin da idanunshi suka hango mashi su Ahankali ya Runtse idanunshi yasake budesu hoping zaiga wani abin daban amma still sune. Zainab da wannan marar mutuncin a mota, a qarqashin rufin mota daya. Wani abu da besan ko Menene ba yazo ya tokare mashi qirji wanda Hakan yasa yaji numfashinshi na bashi wuya Wurin fizgowa. A bangaren su zee ma mutuwar zaune both ita da batool dake baya sukayi suna kallonshi Zuciyarta ce tashiga racing sosai ganin yadda ya kafesu da idanu babu ko kyaftawa fuskarshi expressionless Saurin sake kai hannu tayi Wurin lock din tana qoqarin budewa Saidai still gamm yake Hakan yasa tajuyo akan mussadiq dayayi balancing a fusace "mallam meye haka wai? Ka budewa mutane kofa" Dan kallonta yayi sai yayi murmushi yace "saboda me?" "saboda zan fita, am suffocating" tafada tana dan satar kallon Aymaan hoping zai iya jiyo abinda suke cewa kar yayi musu wata fassarar "motata ce, lock dinane ba yanzu naga damar budewa ba, ai bani nace ku liqemun akan dole saina kawoku ba" "muma cemaka akayi don son ranmu muka biyoka? Saboda ummie ta fadi Hakan kawai yasa muka biyoka if not ko kallo kasan baka ishemu ba" "then sai kuyi hqr dani kokuma better still ku 6alle murfin kofar kufita" Hakan yaqara harzuqa zee Saidai kafin tasake magana taji alamun tashin mota Hakan yasa ta waiga taga motar Aymaan ne tazo tawuce gate tayi horn Ba'a dade ba aka bude mashi kofa ya danna kan motar ciki yashige. Maida idanun zee tayi ta lumshe cikin wani yanayi Yayinda shikuma mussadiq yadanyi murmushin gefen baki Qarar cire lock taji wanda ke nufin ya bude kenan "out" yafada yana hada rai Jin sautin bude kofa sukaji abaya batool ta fita "Are you deaf?" mussadiq yaqara fada Sotake tajuyo ta gaggayamashi magangganu amma qululun daya tokaremata qirji ya hana Hakan yasa kawai tasa hannu ta bude murfin motar tafita tabar mashi ita abude tawuce Binta da kallo yayi harta shige don batool dama tana sauka taqara gaba don itama ta tsorata da yanayin Aymaan Bude kofar nashi side din yayi shima yafito daga motar riqeda ledar da ummie tabasu wanda 6acin rai yasa zee mance ta Gate din gidan yanufa inda maigadi ke qoqarin rufe qaramar kofar gate din Miqamashi ledar yayi mai gadin ya amsa fuskarshi dauke da alamun tambaya "na yanmatan dasuka shigo ne" Yana gama fadin Hakan ya juya ya nufi motarshi yashige ya tadata yajanyeta yabar kofar gidan yana jin wani nishadi a zuciyarshi Zee data kusan kaiwa kofar main entrance taji kamar maigadi na qwalamata kira Hakan yasa ta dakata daga tafiyarta tajuyo tana kallonshi harya qaraso Ledar hannunshi ya miqo mata yana cewa gashi inji wanda ya saukesu Kallon ledar tayi taga wanda ummie tabasu ne, kamar karta amsa taji amma sai kuma ta amsa tayimashi Godiya sannan ta juyo da niyyar tafiya Wani irin bugawa zuciyarta tasakeyi lokacin da sukayi ido hudu da Aymaan dake tsaye bakin kofa yana kallonta Jitayi kamar ta saki ledar don rikicewa don sosai kallon dayake binta dashi ya rikitata Ahankali ya dauke idanunshi akanta ya cigaba da warware hannun longsleeve din shirt dinshi wanda ya nannade wajen alwalla sannan yazo ya ra6ata ya wuce. Sake tamke idanunta tayi cikin wani yanayi tanajin yadda zuciyarta ke bugawa har lokacin Innallilahi, what's all these? Ta dade sosai anan din batareda ta iya sake motsawa ba sai kuma tunanin kar yadawo ya taddata wajen yasa ta cira kafarta Dakyar ta wuce ciki Tana shiga daki batool na fitowa daga bayi Tsayawa sukayi suna kallon juna Can batool ta qaraso ciki tana cewa "Sai yanzu yabarki kika taho?" Ajiyar zuciya zee ta sauke ta qaraso batareda ta amsa ba ta zauna gefen gado "ya akayi kuma?" inji batool "batool, yaya Aymaan fa ya ganmu" tafada tana kallonta "nagani nima, am scared like hell, tunda nasamu nashigo ban ganshi ba na hauro sama da gudu, wlh haryanzu gabana faduwa yake" inji batool "hmm naki mai sauqi ne batool, yanzu muka Hade dashi aqasa.. Kai damn this guy!" tafada tana dafe kai "Menene kuma?" inji batool tana kallonta "ashe mance ledar da ummie tabamu nayi a motar don 6acin rai, shine yazo yaba maigadi yakawo min, daidai na amsa ina juyowa muka sake ido hudu da yaya Aymaan kuma na tabbata yaji lokacin da maigadi ke cewa gashi inji wannan mutumin" Wara idanu batool tayi "what if yayi tunanin shiya baki?" "abinda nake gudu kenan, dama tun farko banso zuwa gidan nan ba yanzu ga irinta, yanzu da wane ido zan sake kallonshi? Mutumin dayasa aka tsaremu dani dashi few weeks ago yagani taredani a mota harda saqon leda, kai" tafada cikin takaici "Gaskiya kam abin beyi ba yanzu yaya zamuyi?" inji batool Saurin juyowa zee tayi tana facing dinta "don Allah idan yadawo kije ki fadamashi duk abinda yafaru, ki gayamashi muma bada son ranmu muka shiga motar ba, I just can't bear it idan ya cigaba da yimin wannan kallon" Wara idanu batool tayi "wa? Ni? Ca6 bakisan yaya Aymaan ba, Kodan kinga Koda yaushe yana washe baki? To wlh idan bude miki dayan shafinshi bayada kyau, ko giyar wake nasha bazan fara tunkararshi ba yanzu don qaramin aikinshi ne ya hurgadoni waje" Sake dafe kai zee tayi, ita ba komai tafi jiba sai kar ya yimata wata fassarar kar girmanta dayake gani ya zube" "amma karki damu, ta inda aka hau tanan za'a sauka kawai ummy zamu gayamawa ta gayamashi, nasan zai fahimta" inji batool Dagowa tayi ta kalleshi "dagaske?" "sosai ma, zata fahimtar dashi" Dukda Hakan ba taji dadi ba, kawai tuna irin kallon dayayi mata dazu takeyi ranta na qara jagulewa Ranar kasa fitowa ayi dinner da ita tayi Duk kuwa yadda batool tayi tayi daita ta fito Kawai jitake bazata iya sake hada ido da Aymaan ba, kunyarshi takeji sosai. Kamar yadda batool tace ma zee Hakan akayi, Ummu batool suka samu sukayi ma bayanin komai harda ganinsu da mussadiq da Aymaan yayi suka kuma roqeta ta sanar dashi Dariya Kawai ummy tayi tace shikenan zata gayamashi Basu saniba ko ta gayamashi din don Aymaan beyi musu maganar ba kwata2, tun zee na noqe noqenta harta ware itama don wanda takeyi don shi bema damuba harkar gabanshi kawai yake kuma ko a fuska be ta6a nunamasu ba Saima cigaba da mu'amalantarsu dayayi kamar yadda yasaba. Saidai a bangaren Aymaan abin na nan a ranshi tun lokacin daya faru. Shi kanshi be iya musalta yadda yaji ranar da yaga zee agaban mota tareda wani, wanin ma mussadiq Dakyar ya iya shiga da motarshi yayi parking yafito ya wuce cikin gida yana jin kamar zuciyarshi zatayi exploding at any moment Babu tunanin da zuciyarshi bata kawo mashi ba akan ganinsu dayah Be ta6a sanin yanada kishi har haka ba sai ranar Dakyar yasamu yayi alwalla yafito don lokacin sai kiraye kirayen sallar magrib akeyi Saukowa yayi daga stairs din ahankali still yana jin yadda zuciyarshi tayi mashi jingim Saidai me? Yana bude kofa yasakai zai fito yaga maigadi yana bata shopping bag wai gashi abata inji wannan gayen Ga mammakinshi kuma saita amsa tana Godiya Jiyayi kamar an makamashi guduma akai a lokacin Jiyayi kamar zuciyarshi zata fashe a lokacin Cikin qarfin hali yazo ya ra6ata ya wuce batareda yasake kallonta ba yana jin kamar akan gajimare yake tafiya ba qasa ba Be dawo ba sai bayan isha'i, kuma Koda ya haye sama yashige dakinshi Be qara saukowa ba don baya buqatar sake ganinta a lokacin don shikadai yasan yadda zuciyarshi ke mashi Washegari ne bayan yadawo daga aiki ummy ta iskeshi har daki inda anan ta gayamashi duk abinda yafaru Yaji dadi jin zarginshi be tabbata ba Amma dukda Hakan abin bebar yimashi zafi ba, duk lokacin daya tuna Da image din zee da mussadiq agaban mota sai ranshi ya 6aci, he can't help but notice yadda sukayi matching dajuna sosai. *BAYAN KWANA UKU* Tafe suke suna hira jefi jefi kowanne da littafi kare a goshin shi saboda ranar da ake qwalawa "kai wlh garinnan badai zafi ba, ina ganin weather din Nigeria is harsh ashe tanan tafi?" inji zee "hmm kema kya gani shiyasa idan zafi yashigo har wani baqi na musanmman kakeyi, fararen sukoma baqaqe baqaqen kuma su qara extra runewa" inji batool "Ca6 amma kuna qoqari, yanzu idan azumi yazo fa ya zakuyi?" "ji wata tambaya, daga azumin zamuyi saboda ana zafi? Dole muyi ko muci ubanmu" Dariya zee tayi tace "wa zaici ubanku?" "Yana can yana jira da sanda, gwara ka taimaki kanka duk wuya kayi" inji batool "hmm Gaskiya bana jin ina iya azumi a qasar nan, kutt! Yanzu fa zafin yafara Shigowa ina ga cikin azumi lokacin ana tsakiyar zafi?" "aikau wlh babu inda zaki, sai kin dandana kema, kutt! Aikau wlh karma kifara, azumi sai kin yishi anan kiji ingayamiki" "Sai ki hanani tafiya to idan kina iyawa" inji zee tana Harararta "tsaf ko, allah ya kaimu lokacin kiga ikon allah" Da haka suka qarasa food canteen din school din suka shiga Akwai yan mutane ciki inda Mafi yawanci abin sakawa aciki yazo nema wasu kuma fekewa sukayi ma hot ranar waje A cikin wajen akwai tebura da kujerun zama Kowanne table zagaye yake da kujeru uku. Batool ce ta nufi wani table dake daga gefe taje taja daya daga cikin kujerun dake zagaye dashi ta zauna Yayinda itakuma zee tawuce siyomasu abinda sukeso Ruwa da drinks masu sanyi ta siyo masu tareda peanuts Dawowa tayi ta iske batool na waya "ok ganinan, nima yanzu nashigo canteen, ok ganinan zuwa" Zama zee tayi "keda wa?" "nida farhana, wai inzo anfara submitting wannan assignment din" "amma saimun gama sannan ko?" inji zee "Sai mun gama me? Dole naje nabada yanzu ga lecturern ba mutunci ya isheshi ba" tafada tana tashi tsaye "to yanzu zaki dawo ko?" "eh mana, kawai badawa zanyi indawo" tafada tana wucewa Maida hankalinta tayi kan abubbuwan gabanta ta bude ruwa ta zuba a dan kofin robar da ake siyarwa tareda ruwan, ta zuba aciki takai baki tafara sipping tana lumshe idanu jin sanyin ruwan na ratsa mata bushashen maqoshinta. Bata ajiye kofin ba Saida taga bayan ruwan sannan ta sauke cup din tana Ajiyar zuciya Jitayi kamar ana kallonta Hakan yasata bude idanunta dake lumshe tunda tafara shan ruwan Jada baya tayi babu shiri cikin tsoro a sanadin abinda idanunta sukaci karo dashi Razanar datayi yasa kingin ruwan da basu ida wucewa ba kwareta tashiga tari babu kakkautawa Dago idanunshi dake cikin spec sa6anin shade daya saba qwamawa yayi ya kalleta Ganin dagaske take tarin yasashi saukar da qafar dayayi crossing yana kallonta "hey, are you ok?" Cigaba da tarin tayi hannunta dade da baki idanunta har sunyi ja Hakan yasashi saurin sake daukar kofin gabanta ya zuba wasu ruwan yakai mata saitin baki Kasancewar a lokacin babu abinda take buqata kamar abinda zai tsayar mata da tarin yasa babu musu itama ta matso jikin table din daya raba tsakiyarsu ya kafamata kofin a baki tashiga shan ruwan Saida tadan sha dayawa sannan ta kauda kai Hakan yasashi shima Janye kofin daga bakinta Ahankali take sauke numfashin tarin datayi Hanki fari qall taga ya miqo mata, batace komai ba ta amsa tashiga goge gefe da gefen bakinta daya 6aci da ruwa Tana cikin gogewa kamar ance ta kalli bakin kofar Shigowa Wurin, sai idanunta sukayi mata mummunan gani. Dammm qirjinta ya buga lokacin ta hangi Aymaan tareda batool tsaye bakin kofar sun kafamata idanu Batasan lokacin da ta saki hanki din hannunta ba Cikin tsananin kidima Ganin yanayinta dakuma kafe waje guda da idon dayayi yasa shima mussadiq kallon inda nan shima idanunshi suka gano mashi Aymaan da haryanzu ke tsaye kamar statue a inda yake idanunshi sunyi wani irin mugun kadawa Dan daga girarenshi mussadiq yayi ya ta6e baki sannan yakoma yasake balancing a kujera Ahankali Aymaan yashiga Takowa wajensu still idanunshi akansu babu ko kyaftawa Zee jitayi kamar tajita ta 6ace daga wajen, sosai yanayin Aymaan ya razanata don tunda tasanshi bata ta6a ganinshi cikin irin wannan yanayin ba. Qarasowa wajen yayi ahankali shima yaja dayar kujerar data rage ya zauna Sauke idanunta zee tayi tana jin yadda jikinta ke rawa innerly Jawo peanuts din gaban zee yayi batareda ya kalleta ba ya bude seal din yashiga dauka da daddaya yana sakawa a baki yana tauna ahankali . Wurin ne yayi shiru, very tensed ga zee data kasa Dagowa har lokacin Yayinda mussadiq ko ajikinshi danna wayarshi ma yake hankali kwance Can ya dago daga danna wayar dayake ya kalli zee directly wanda idanunta ke a qasa har lokacin "so what did you say baby? Wancan din yayi miki ko a chanza wani?" Dagowa zee tayi a mammakince tana kallon mussadiq dake kallonta shima Baby? Wacece baby? "bakice komai ba dear" yafada softly yana mata wani kallon qasan ido irinna masu jin barci Cikin tsananin mammaki take kallonshi sai kuma ta kalli Aymaan dake taunar peanuts din bakinshi Shima mussadiq kallon Aymaan din yayi saiya daga gira data "oh! Nagane.. Nagane. Shikenan zamuyi waya, I'll take my leave yafada yana maida wayarshi a aljihu ignoring kallon shock din da zee ke mashi yafara qoqarin tashi "ina zaka bayan baka gama ba?" inji Aymaan batareda ya kalleshi ba Dakatawa mussadiq yayi daga tashin dayayi niyyar yi don dama abinda yake so kenan, ya tanka Maida kallonshi Aymaan yayi akan zee da har lokacin takasa ko motsi "ki bashi amsar shi mana _*baby*" yafada yana kallonta, kallon dake dada Kada yan cikin ta Girgiza kai tafara tana qoqarin lalubo voice dinta dataji tarasa nan take mussadiq ya katse ta "karka damu, maganar tsakanina da ita ne, zamu qarashe a waya" Dagowa Aymaan yayi a karo na farko tunda ya zauna ya kalleshi straight in the eye "who are you? How dare you?" yafada in a low dangerous voice Murmushin gefen baki mussadiq yayi yace "wanne kake son na amsa daga ciki?" "kanada wani irin qarfin hali, an ta6a fadamaka Hakan?" inji Aymaan yana kallonshi eye-in-eye Qara Sakin shegen smirk dinshi yayi "kanada abin ban Dariya, an ta6a fadamaka Hakan?" yafada shima yana kallonshi eye-in-eye Murmushin dayafi kama dana takaici Aymaan yayi yace "A'a, amma ba abin mammaki bane idan ka fadi Hakan don abinda zaiba mahaukaci Dariya ba lallai bane yaba kingin normal people ba" "Careful now, don’t let your brains go to your head?" Katse shi Aymaan yayi da " Brains aren’t everything. In fact, in your case they’re nothing" Dan murmushi mussadiq yayi yace "you know what? Nasha wannan tunanin, I don’t know what makes you so stupid, but it really works" " I’d explain it to you, but your brain would explode" inji Aymaan Sunkuyowa mussadiq yayi gaban Aymaan wanda Hakan yaqara basu kusanci "you know what? Anyone who told you to be yourself simply couldn't have given you worse advice.. So be yourself" ya miqe tsaye Shima miqewa Aymaan yayi "I do heed to advice, but if I Said advice.. I mean advice given By a sane being" "sane or insane.. I don’t care, all I know is am advising you to stop sticking your nose into my business.. For your own Good" Zai wuce Aymaan ya sha gabanshi "and where did you think you're going? Am not done with you yet" inji Aymaan da kallo daya zakamashi kasan bala'i ke cin zuciyarshi "yaya Aymaan..." batool data qaraso Tundazu tafara fadi Saidai kallon daya watsa mata yasata kasa idawa Maida kallonshi yayi akan mussadiq dake kallonshi sheqeqe "ba'a taka ko baki bakin gonata, meya kaika ra6arta?" inji Aymaan yana kallon mussadiq da bloodshot eyes dinshi, kallo daya zakamashi kasan baya cikin hayyacinshi, fushi ya fiddashi daga hayyacinshi kamar yadda yasaba yima masu haquri da aka kai bango Yar Dariya mussadiq yayi "yaushe ka chanza sana'a? Koma yaushe ne am sorry to say anci baya Sosai, From Likita to manomi" "abin bazai ida baka mammaki ba sai na chanza daga manomin zuwa mafed'i" "Yaya Aymaan, don Allah ka saurareni.. Please" inji zee da duk take a tsorace da yanayin kowannensu Be kalleta ba ya cigaba da cewa "answer me, wani tsautsayi yasaka ra6ar gonata?!" Yafada cikin qaraji "yaya Aymaan please.. Look kallonmu akeyi" inji batool cikin tsananin tsoro "ra6a? To ka jira, nan bada dadewa ba zan shige cikinta tsamo tsam.." Naushin da Aymaan yakai mashi ya katse shi yayi saurin tarewa da hannu Girgiza mashi kai mussadiq yashiga yi yana murmushi "karka soma.." Bangajeshi Aymaan yayi da dukkan qarfinshi wanda Hakan yasa yayi taga taga zaya fadi sai kuma yaci nasarar tsaida kanshi Dagowa yayi ya kalleshi a fusace "alright.. You'll get it" Nufoshi yayi shima Aymaan ya Nufoshi suka cakumi juna Kan kace me fada ya kaure aka shiga musayar blows🤜🏻🤛🏻 Wajen ne ya rikice don dama tunda suka fara hankalin kowa yadawo kansu. Bugun juna sukeyi with all their strength kowanne na qoqarin huce haushin dan uwanshi daya dade danqare a zuciyarshi Sosai jikin zee ke rawa, hannayenta rufe da baki hawaye na rige rigen gangarowa a fuskarta. Dakyar mazan food canteen din suka samu suka 6an6aresu daga jikin juna kowannensu da irin ciwon dayaji a wajen dan uwanshi Aymaan dayafi zuciya aka shiga qoqarin fitar dashi daga canteen din yana fizgewa yana zagin mussadiq da shima ake riqe dashi cikin canteen din Dakyar aka samu aka fiddashi daga canteen din su zee na biye dashi suna hawaye Fizgewa yayi daga riqonsu a fusace yana dakamasu tsawa akan su sakeshi Sakinshi sukayi suna son ganin ko komawa zaiyi saiya juya ya nufi motarshi hannunshi daya dafe da kai Saurin maramashi baya zee tayi "yaya.. Yaya Aymaan please listen to me" Ko kallonta beyi ba ya cigaba da tafiyarshi harya kai Wurin motarshi ya bude kofar Riqe kofar itama tayi cikin kuka "Aymaan ka saurareni mana.. You're going nowhere in this condition!" Juyowa yayi ya kalleta da rinnanun idanunshi "as if you care " yafada ahankali " whatever yaya, just listen, I..." Katseta yayi ta hanyar daga mata hannu sannan kuma ya Hade taffukanshi waje guda 👏 "spare me that.. Please" Ya ida bude kofar yashige "Akhie.." batool tafara Jawo murfin kofar yayi ya rufe da qarfi sannan yaja motar da mugun qarfi yabar wajen Bïñ motar sukayi da kallo devastated. *** Tunda ya hau titi yake tsula wani uban gudu kamar mai gasar tsere, babu ruwanshi da bin dokokin hanya kawai kutsawa yake yana driving yadda yaga dama Saida yayi nisa sosai sannan yasamu wuri ya gangara gefen titi yayi parking ya dora kanshi bisa sterring yana sauke numfashi ahankali Ya dade ahakan sannan ya dago kanshi ya jingina da kujerar bayanshi Tunawa yayi da yadda komai yafaru. Hanya ce ta biyo dashi hanyar school dinsu, sai yaji babu abinda yakeson gani kamar ita saiya yanke shawarar shiga school din Yana parking a inda ake parking yafito ya shiga makarantar Harya fara shawarar ta ina zai fara nemansu sai kamar wasa ya hango batool tana ta sauri Sunanta yakira da qarfi Hakan yasa ta tsaya tajuyo ta kalleshi Wara idanunta tayi saita Nufoshi shima ya nufeta suka Hade a hanya "ina zaki?" injishi "Wani assignment zanyi sauri nabada" "ina Zainab?" "Tana food canteen, tarema muke assignment kawai zan bada nakoma" "ok muje na rakaki sai Mukuma canteen din" Tare suka je department din nasu tayi submitting sannan suka juyo suka dawo suka kama hanyar canteen din Qarasawa bakin kofar wajen sukayi suka shiga Idanunshi ne ya sauka a kansu suka yimashi mugun gani Wannan marar mutuncin ne ya sunkuyo yana bata ruwa abaki tana sha Saida tagama sha sannan ya ciro hanki yabata tana goge bakinta dashi Mutuwar tsaye yayi Yayinda yaji komai na kwance mashi, zuciyarshi ta tasomishi har wuya yanajin kamar zata biyo ta baki ta fito waje and daga nan yayi loosing control har duk abinda yafaru yafaru Haryanzu kuma be daina jin radadin da zuciyarshi ke mashi ba Lumshe idanunshi yayi yafara ambaton allah a zuciyarshi har yasamu tadan yimashi sauki Bude rinnanun idanunshi yayi yana furzar da huci sannan ya sunkuya ya dauki gorar ruwa wanda yasaba ajiyewa a gaban mota ya 6alle murfin ya kafa kai dukda ba wani sanyi garesu ba ya ida tuttula sauran a kanshi sannan ya qara Sakin nannauyan Ajiyar zuciya Lalubo wayarshi yayi cikin aljihu ya Fiddota Number Ahmad yashiga nema Saidai kafin ya ganota kira ya shigo wayar *Ahmad* yaga yana yawo a screen din wayar Wani numfashin yasake saukewa sannan ya daga kiran ya kara a kunne "kana ina?" inji Ahmad ta cikin wayar "ina nan" Aymaan ya amsa a taqaice "to kayi maza kazo Aymaan I have a huge surprise for you please" "Menene?" inji Aymaan moody "kawai kazo please, its urgent, ina office idan kuma baxaka iya zuwa ba ka fadamin inda kake zanzo" Jin seriousness din Muryarshi yasashi fara wondering meke faruwa "ok, ganinan" yafada yana katse kiranshi Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya sake tada motar yahau kan titi yaja wannan karon cikin normal speed A parking space yayima motarshi matsugguni sannan ya fito daga cikinta ya rufe Kallon harabar kamfanin su Ahmad din yayi sannan ya sake furzar da huci yafara tafiya yanufi ciki not minding yadda kayan jikinshi sukayi squeesing sukayi kaca kaca ga ruwan daya sheqawa kanshi dazu a mota, yadai koma gashinan dai kamar sabon kamu Direct elevator yashiga ya danna floor din da office din Ahmad yake, cikin qanqanin lokaci ya isa wajen Fitowa yayi daga cikin elevator din ya wuce office dinshi Direct Kwankwasawa biyu yayi aka bashi izinin Shigowa Murda handle din yayi ya tura kofar yashiga Dagowa Ahmad yayi daga laptop din gabanshi, Ganin Aymaan ne yasashi saurin tashi tsaye yana cewa "omg! Tun dazu sai yanzu ka iso?" Sai kuma ya lura da yanayin Aymaan da shigarshi "Are you ok? Meya samu kayan ka? And your face, ya naga duk bruises?" Zama Aymaan yayi a opposite dinshi ya harde hannayenshi a qirji "inajinka" yafada a taqaice "meya sameka wai Aymaan?" "idan bakada abin fada zan tafi" inji Aymaan yana eyeing dinshi "A'a nikau keda abin fada, bari kagani" yafada shima yana zama har wani kyarma yakeyi Wurin zaman "inada wani mugun surprise for you" yafada yana kallon Aymaan "uhun?" inji Aymaan yana kallonshi "bari na faro maka daga farko Kaga valentine is approaching, kowa yanzu shirye shiryen abubbuwan da zaiyi ya burge masoyiyarshi yake, shine nima nafara tunanin me ya kamata nayi na burge *B-baby* na" Tunda yafara magana Aymaan ke Binshi da wani matsiyacin kallon haushi Be lura ba hakan yasashi cigaba da cewa "saina fara tunanin me ya kamata nayi saina yanke shawarar hada sunana da nata inyi creating video dinsu insamu waqa mai dadi ta soyayya inyi amfani daita..." "Are you crazy? Wannan ne banzan surprise din daka dameni nazo nagani?" inji Aymaan a fusace "Kash! Matsalata dakai rashin haquri" "gudawa ne ni" inji Aymaan a qule "koma dai Menene kabari nakai aya mana, na yarda idan nakai aya babu abinda yayi making sense aciki kayimin dik abinda kaga dama" Shiru Aymaan yayi be tanka ba hakan yasa ya cigaba da cewa "Hakan yasa na yanke shawarar nemo mana waqa mai dadi wanda zata hau da love mood din kuma inason tazamo ta hausa mai ratsa zuciya Shine na dauki laptop nahau website nafara browsing waqoqin hausa na soyayya masu tashe. Nasamu guda goma duk na kunnasu nafara sauraronsu daya bayan daya harna saurari duka. Acikinsu daya tafi kwanta min kuma tahau da abinda nakeson hada mana Sunanta *kalmar so* Saboda dadinta na saurareta yafi sau goma, sai daga baya naji inason ganin video din waqar sai nayi downloading din videon. Bari ka gani" yafada yana sungumo laptop din ya zagayo wajen Aymaan dake kallonshi Tundazu cike da takaici Jawo wata kujera yayi ya zauna kusada shi ya shiga lalubo waqar cikin sauri Dan Tsaki Aymaan yaja ya kauda kai yana jin wama yasashi zuwa tun farko gashi yana qara mashi akan abinda yakeji a zuciyarshi Kida yaji yafara tashi acikin laptop din alamun harya kunna sannan aka fara waqar _kalmar so tana nufin abinda zuciya tasoo_ _amma anawa 6angaren rai ne da rayuwa_ _so ne lagwan mutane biyu inda shaquwa_ _mai kama dan Adam da aljan da deguwa_ _Domin mu gane so, sai mun qara nutsuwa_ _don dole dole so shike kaimu koguwa_ Juyowa Aymaan yayi ahankali don kallon videon don waqar ta shigeshi shima dukda he's not in the mood, amma waqar ta ta6ashi a zuciya Wani wawan jada baya yayi da kujerar lokacin dayaci karo da abinda ke kan screen din laptop din Tashi yayi tsaye yana kallon screen din idanu awaje kamar zasu fado _so sam beda tausayiii_ _so sam beda tausayii_ _inyai ta6argaza amsar saita bada nayi_ _ba tsoro yake ba shima_ _sannan be gudun husuma_ _zai iya tada yan Adam duk tsaye don yanada girma_ Qara jada baya Aymaan yayi yana kallon fuskar kan screen din Fuskar da be dade dagani ba yanzu Fuskar da ya nannausa yan Mintuna dasuka wuce Mutumin da dazu dazun nan aka 6an6areshi Dakyar daga jikinshi _mussadiq?_ Girgiza kai yayi Mussadiq bayajin hausa, ko zo na yankaka da hausa bayaji _Deen?_ Kanshi ne yayi wani mugun sarawa har Saida yayi saurin dafewa Kallon smiling face din mutumin dake cikin screen din yayi yana cigaba da waqar guitar a rataye a wuyanshi yana kadawa Baki na rawa yace _*"DEEN"*_✍️ alhamdullilah! 💃💃 Anan zan dakatar da Deen mutafi hutun ramadan 💃💃 inda zamu cigaba insha allah bayan sallah idan allah yakai ranmu Masu Deen! Deen!! To Deen is back!!! Yadawo da wani salo mai ban mammaki, ya dawo muku da bazata kala kala, kudai ku biyoni zuwa bayan sallah muji yadda chakwakiyar zata kaya. Qaqa qara qaqa! Ga Aymaan ga mussadiq, ga kuma Deen ya fado From nowhere. Yanzu wasan zai fara, ku kasance da Ashaaaaanty dinku Domin jin yadda xa'a qarqare chakwakiyar nan Allah kabamu ikon yin ibadunmu lafiya, Allah kasadamu da alhairan wannan watan mai albarka (amin summa amin) Ina mai neman gafarar duk wanda na 6atamawa da sani na ko bada sanina ba, nima na yafewa kowa. Ma'asallam! Sai mun hadu bayan sallah 😘😘😘 Ummin fasihu 🧚🏻‍♀️🧚🏻‍♀️🧚🏻‍♀️🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:42 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *071* *THE MUSICIAN🎼* *barkanmu da dawowa daga hutun azumi, fatan kowa yayi ibadunshi cikin qoshin lafiya, allah yasa dukkanin ibadunmu kar6a66u ne, yakuma maimaita mana🤲🏻* Qara qurawa gayen kan laptop din idanu Aymaan yayi zuciyarshi na bugu sosai Tabbas inhar wannan gayen ba mussadiq bane to tabbas DEEN ne Tashi Ahmad yayi shima ya qaraso inda Aymaan ke tsaye haryanzu kamar statue "kaima kaga abinda nagani ko?" inji ahmad sai alokacin aymaan ya iya motsawa ta hanyar juyowa ya kalleshi saidai yakasa cewa komai don yawun bakinshi ma sun kafe gabadaya dakyar ya kalato wasu bussasun yawu ya hadiye sannan yace "who is this?" Dan buda idanu ahmad yayi "haryanzu tambaya kake?" girgiza kai aymaan yafara "karka cemin wannan shine...Deen" "masu irin wannan fuskar biyu ne duk fadin duniyarnan Mussadiq da Deen. kenan wannan is either Mussadiq ko Deen, kuma ni dakai munsan wannan ba mussadiq bane" "but.. this can't just be, how... I mean yaushe Deen yaxama mawaqi?" inji aymaan confused "watanni biyar dasuka gabata" Ahmad yabashi amsa cikin rashin fahimta aymaan yace "wata biyar? ban ganeba" Ajiyar zuciya Ahmad ya sauke sannan ya gwadamashi kujera yace "mufara zama tukun" Dan jimm aymaan yayi kamar bazai zauna din ba saikuma yaja kujerar ya zauna yana jin yadda zuciyarshi tayimashi jingim shima Ahmad jan kujera yayi ya maidota kusadashi ya zauna ya dago ya kalli aymaan dake kallonshi shima "nima nashiga rudani fiyeda yadda kashiga lokacin danayi tozali da wannan fuskar. abun kamar al'mara, kallo daya nayimashi kwanyata ta burkuce, fuskar Sir Mussadiq sak nake gani a screen din saidai yaren dayake sam ba nashi bane, hakan yasa wani abu ya gifta kwalwata. domin kore tantama ta sai na jawo laptop din hannu na rawa nashiga searching din sunanshi and this appear..." sake jawo laptop din Ahmad yayi ya juyota gabanshi yashiga danne2, shidai aymaan kallonshi Kawai yakeyi bece komaiba har yagama ya sake juyomashi laptop din gabanshi janye idanunshi aymaan yayi daga kanshi yamaida kan laptop din. kafe sunan dake qasan hoton mai fuskar Mussadiq din yayi nawasu daqiqu sannan ahankali ya bude baki yace" *BALARABE?*" "yes, balarabe. wannan sunan yasameshi ne a wajen abokanshi da fans dinshi wanda hakan yayi sanaddiyar 6acewar ainahin sunanshi, don dayawa basusan real name dinshi ba, sunfi saninshi da wannan sabon sunan wato *BALARABE*. Bari kaga full name dinshi..." yafada yana scrolling laptop din *KAMALDEEN MUHAMMAD a.k.a BALARABE* Abinda ya bayyana kenan a screen din kafe sunan aymaan yayi da idanunshi babu ko kyaftawa cigaba da scrolling Ahmad yayi yana karanto mashi content din kamar haka "KAMALDEEN MUHAMMAD,also known as BALARABE shahararren mawaqi ne mai zamani wanda yayi fice a fagen waqoqin nanaye wanda duk suka ta'alaqa ne akan soyayya. BALARABE yayi fice kuma yayi suna a wannan harkar cikin dan qanqanin lokaci da baigaza wattani biyar ba, abinda ba'a ta6a samu ba a record din wani mawaqi ba. Abin mammakin bewuce yadda wannan mawaqin yasamu kar6uwa tun awaqarshi tafarko mai taken *KECE* Waqar datayi nasarar bayyanashi ga duniya inda har takaishi ga matsayin dayake ayanzu. BALARABE yasamu nasarar xama fittace ba iya Arewa ko Nigeria kadai ba hatta wasu qasashen na qetare sunsan da zamanshi A kuma binciken da akayi BALARABE yana daya daga cikin sannanun Celebrities na Arewa inda yakeda tarin mabiya a shafukanshi na sada zumunta.." Dan dakatawa Ahmad yayi daga karatun dayakeyi yawaigo yakalli aymaan dake bin karatun shima tundazu. "Bari kaga nashiga shafinshi na Instagram" shiga yayi din sannan yaqara karkato da fuskar laptop din gun aymaan wanda haryanzu besake furta komaiba Gasping Ahmad yayi "kalla.. over 4million followers! OMG! wlh mutuminnan is famous.. ji pics dinshi... see likes.. kalli millions of comments! cewa akayi idan yayi posting abu koda ordinary picture dinshi ne baya samun likes qasa da million kalli shows dinshi, duk jiya nayi downloading dinsu..." Kunna mashi daya daga cikin videos din shows din yayi Deen ne tsaye cikin wasu tsaddadun fararen qanannun kaya, wuyanshi rataye da guitar yana kadawa ahankali Abinda zaifi daukar hankalinka a wajen shine tarin mutanen wajen, yadda kasan tururuwa sai ihu suke da whistling yayinda shikuma ke rero waqarshi cikin cool voice dinshi cikeda nutsuwa kafeshi da idanu Aymaan yayi yana kallon kamillaliyar fuskarnan tashi ma'abociyar fara'a, dakuma yadda dimple dinshi ke lo6awa gwanin sha'awa waqa yake cikeda qwarewa yayinda sautin waqar ba iya kunne take shiga ba direct cikin zuciya take wucewa tana wanzar da shauqi acikinta. lumshe idanu Aymaan yayi ahankali yana sauke numfashi ahankali Ganin hakan yasa Ahmad dannama vidiyon pause ya kalleshi "ya kagani? Deen is Back!" yafada cikin jindadi bude idanunshi Aymaan yayi ahankali ya kalleshi "And what's good about that?" inji Aymaan yana mashi wani kallo Dan wara idanu Ahmad yayi "kamar yaya what's good about that? watanni nawa muna nemanshi? yanzu mun sameshi kana fadin haka?" Maida kanshi aymaan yayi ya jinginar da kujera yasake maida idanu ya lumshe sannan ya bude "eh, haka nace. what's good about ganinshi? dubi fuskarshi, yayi kama da mai wata damuwa? nace yayi kama da mai wata damuwa!" ya qarashe maganar a fusace "haba aymaan..." "yayinda ya jefa wata a tasku, yayi sanaddiyar qauracewar farinciki a rayuwarta, shi yanacan cikin jindadi da walwala yana cin duniyarshi da tsinke! how cruel?" ya katse Ahmad cikin zafin rai "Aymaan, karka yanke hukunci akan abinda baka.." "karna yanke hukunci akan abinda ban sani ba? gayamin meye ban sani ba. akan wannan mutumin rayuwar mutane da dama suka dagule ciki harda tawa! ya yaudari diyar mutane wanda tasoshi da dukkan zuciyarta ta kuma kafe kai da fata akan sai shi batareda tayi la'akari cewa shi ba kowa bane! taso bijirewa mahaifinta duk don shi! qarshe me yayi? bad'a mata qasa yayi a idanu ya tafi ya barta lokacin datafi buqatarshi hakan dayayi ya chanza komai a zuciyarta? ya ta6a soyayyar datake mashi? A'a saima qara haukacewa datayi akanshi inda ta dauki dukkan lamuranshi tayi uwa maqar6iya inda kullum da tunanin yadda zata inganta rayuwarshi take kwana take tashi, batada buri sai ganin rayuwarshi ta dawo daidai kamar ta kowa, ta sadaukar da abubbuwa da dama kuma tana kan sadaukarwa duk saboda shi, duk saboda wannan butulun da yanzu nasan ko sunanta baya iya tunawa" yadda yake maganar Kawai ta isa kagane ranshi a matuqar 6ace yake don har jijiyoyin wuyanshi tashi sukeyi don masifa, he can't believe mutumin dasuke hauka akanshi yana can hankalinshi kwance bayada wata damuwa "haba Aymaan, meyasa zaka yanke hukunci akan abinda bakada tabbaci akai? dama ana judging book by it's cover ne? don kaga mutum yafito daidai hakan na nufin har cikinshi daidai yake? yayinda wasu murmushi kezama ado agaresu wasu malullu6i ne, mallulu6i na lullu6e ainahin halin dasuke aciki. Zainab was heartbroken and always in pain, hakan ya hanata murmushi ko dariya ko wasu harkokin na gabanta? wasu suna fara'a ne domin 6oye ainahin halin dasuke aciki, wasu suna murmushi ne don sunga kowa nayi bawai don hakan na zuwa daga can qasan zuciya ba. yadda zee ke kwana tana tashi dashi arai shima hakan take a wajenshi Zainab na maqale a zuciyar Deen kuma zan gwadamaka hujja" Yana kaiwa nan yasake jawo laptop din yayi yan danne2nshi sannan ya juyoma Aymaan yana cewa "wannan wata firace da akayi dashi a gidan wani television ko wata daya ba'ayi ba" danna play botton yayi wanda hakan yaba vidiyon damar farawa Deen ne zaune kan kujera yana facing presenter din gidan t.v din sanye yake cikin wata dakkakiyar sky blue shadda wacce tayi mugun hawanshi takuma qara fiddo mashi qwarjininshi da haiba kanshi babu hula sai lallausan gashinshi dayayi trimming dake kwance luff luff gwanin sha'awa yaqara haske da kyau ga cute lips dinshi dasukaqara yin pink fiyeda da kallon presenter din yakeyi dake yimashi tambaya fuskarshi asake "Mallam balarabe zaka iya gabatar ma masu saurare kanka?" murmushi Deen yadanyi sannan yace "insha allah, sunana KAMALDEEN MUHAMMAD amma anfi sanina da BALARABE yayinda wasu kuma ke kirana Deen" "masha allah, Mallam balarabe zamuso sanin yadda akayi kasamu wannan sunan na BALARABE, koko dama kai balaraben ne Don ana yada jita jitan qila ka hada jini da larabawa duba da yadda kayo ruwansu" murmushi Deen yayi "ban hada komai da larabawa ba kamar yadda ake hassashe, ni cikkaken bahaushe ne, sunan BALARABE kuma na sameshi ne awajen abokai na, nickname ne Kuma sai yabini" yafada cikin cool voice dinshi "masha allah, to Mallam balarabe meye yaja ra'ayinka har kafara wannan harka ta waqa?" inji presenter din "eh to, dafarko nafara waqa ne ba don nasan inada talent din ba, Kawai ina yine don yaxama Abin debemin kewa duk lokacin da nakejina so boring, sai daga baya aka fahimtar dani talent dina akan waqa sannan aka kwadaitamin bayyana wannan talent din nawa ta hanyar shiga harkar waqar" "masha allah, yanzu tun lokacin daka fara waqa zuwa yanzu aqalla kayi guda nawa? kana iya qayyadesu" dan murmushi deen yayi "waqoqin danayi kuma suka fito adadinsu 27 yayinda akwai wadanda nake aiki akai kuma suna gab da fitowa suma insha allah" "to masha allah, mallam balarabe zaka iya fadamana nasarorin daka samu sanaddiyar waqa?" "Alhamdullilah, babu abinda zance a wannan ga6ar sai godiya ga Allah (s.w.t) don nasarori kam na samesu sosai a wannan harkar ta waqa, ciki harda famousity, a sanaddiyar waqa sunana ya zaga wuraren da qila har inmutu bazanje wajen ba, takuma sa ansan dani Kuma nima nasan mutanen da ban ta6a mafarkin zan sansu su sanni ba bayan hakan kuma tazama garkuwa gareni inda take a.matsayin sana'a agareni wanda nake samun rufin asiri sosai acikinta, Alhamdullilah" "to Mallam balarabe qalubale fa? kasan duk nasara tana tareda qalubale, wadanne irin qalubale ka fuskanta a wannan harkar ta waqa?" kada kai Deen yayi "gaskiya ne, kowanne nasara yana tattare da qalubale. gaskiya qalubalen dana fuskanta bawata mai yawa bace, a lokacin da nayanke shawarar fara waqa nakuma tuntu6i kakata akan hakan taso hanani don a ganinta babu Abinda yake cikin harkar sai tarin shiririta da shirme amma da taimakon uban gidana muka samu muka shawo kanta har ta amince takuma sanyamana albarka akai wanda inada tabbaci albarkar ke bibbiyarmu haryanzu" ya qarashe murmushi a fuskarshi shima presenter din murmushi yayi "ka ambaci ubangida, zaka iya fadamana waye ubangidanka ko jagoranka wato role model dinka a wannan harkar?" jimm Deen yadanyi saikuma yadanyi slight murmushi "eh... inada role models biyu... da wanda da taimakonshi nashiga wannan harkar sai wadda tasani nayi realising talent dina.." saikuma yayi shiru staring in space Ganin hakan yasa presenter dan muskutawa sannan yace "wacce tasaka realizing talent dinka? wacece?" nanma shiru yadanyi still staring blankly at space saikuma yayi wani guntun murmushi yana sauke idanunshi qasa Ahankali yaqara dagowa ya kalli presenter din still murmushin bebar fuskarshi ba "wata ce... wata" yafada ahankali yana kallon fuskar presenter din saidai a zahiri ba fuskarshi yake gani ba,.wata fuskar yake gani daban "Idan aka ambaci kalmar *waqa*.. ita ke fara zuwa raina. Idan nashiga studio da niyyar yin waqa inajin presence dinta ajikina, dana lumshe idanu na don nafara ita nake gani tana min rad'ar waqar daxanyi nikuma nashiga binta ahankali. itace dalilin komai na career dina, itace dalilin nasarata a duniya, itace dalilin zuwana matsayin danake aciki yanzu, itace nasarata. *waqa tana zuwa ne daga zuciya, duk waqar datazo directly daga zuciya zakaga tafi wadda za'a zauna a tsara* wannan kallaman nata sune sukeyin guiding dina a kodayaushe" "dafarko na dauki hakan kamar abu marar yiwuwa yayinda nasha qoqarin qirqirarta da abinda yake a zuciyata amma daga baya sai nayi realizing gaskiyar maganarta lokacin da nake rero abinda ke zuciyata batareda sanina ba. Duk waqar dazanyi tana zuwa ne daga can qasan zuciyata kuma kowacce is reffering to her..." dan murmushi yasake yi absentmindedly sannan in a whisper yace "my role model" shiru ya ratsa wajen na wasu daqiqu, can presenter din yace "to Mallam balarabe, zaka iya fadamana ko wacece wannan role model din taka? dakuma matsayinta a wajen ka" Nan ma saida yadanyi shiru sannan yadanyi guntun murmushi "she's an angel, angel of light and beauty, duk inda ta gifta tana barin walwalin haskenta awajen, hasken daxai cigaba da haskaka wadanda tabari awajen. she's innocent, straightforward, mean, honest, stylish and fun to be with. tanada baiwar da duk inda taje komin qanqantar zamanta awajen sai tabar memories, sweet brainsticking memories" presenter din dake enjoying moment din cikin doqi yace "wacece agareka? girlfriend?" dagowa Deen yayi yakalleshi na wani lokaci wanda expression din fuskarshi yasa murnar presenter din fara komawa ciki sauke idanunshi yayi a qasa sannan ya girgiza kai "A'a..." sai kuma yayi shiru can kuma ya dago yaqara kallon presenter din "Actually.. a halin yanzu kowanne na rayuwa ne a wata duniyar tashi daban... and... mun haramta ga juna.. ta haramta gareni" sauke kanshi yaqara yi qasa yana lumshe oily eyes dinshi shiru wajen ya dauka, shi kanshi presenter din jikinshi yayi sanyi be daddara ba yasake cewa "ta haramta agareka kamar yaya?" Ajiyar zuciya Deen ya sauke sannan ya dago yakalli presenter din yana murmushin qarfin hali "I'll be glad Idan mukayi dropping wannan topic din, it's something personal, I dont want to discuss it" yafada politely jin hakan yasa shima,presenter din dropping topic,din ya cigaba da yimashi wasu tambayoyin daban. Ajiyar zuciya Aymaan ya sauke ya maida kanshi ya jinginar da kujera tareda lumshe Hazel eyes dinshi jiyake kamar kanshi zai rabe gida biyu ga wani abu dake tasomashi a qasan zuciya mai dacin gaske shima Ahmad bece komaiba sai kallonshi dayake yana jiran jin me zaice kuma Jan kujerar dayake akai Aymaan yayi baya sannan ya miqe tsaye binshi dakallo Ahmad yayi ga mammakinshi sai gani yayi ya juya ya nufi kofa sakin baki Ahmad yayi yana kallonshi har yakai bakin kofa sannan cikin qarfin hali ya kira sunanshi dakatawa Aymaan yayi daidai lokacin daya kai hannu kan handle batareda ya juyoba tashi tsaye Ahmad yayi "ya zaka tafi just like that?" batareda ya juyo ba yace "what again? akwai wani abu bayan wannan ne?" qara wara idanu ahmad yayi cikin mammaki "bangane ba, aren't we suppose to discuss about this?" sai a sannan Aymaan yajuyo "discuss about what? there is nothing to discuss about" "amma..." "baka jishi ba? he said sun haramta da juna, ni wanene dazan halarta haram?" Aymaan ya katseshi da hakan kasa cewa komai Ahmad yayi sai bin Aymaan dayake da kallo baki sake juyawa Aymaan yayi ya murda kofar ya bude yafita tareda maidota da qarfi leaving Aymaan still standing mouth agape Besan yadda ya fito a daga company din ba saidai.Kawai yaganshi a jikin motarshi yana kiciniyar budeta ya dade yana kiciniyar budeta kafin ya gane ashe ba makullin motar bane yake amfani dashi lalubo makullin motar yayi sannan ya bude ya shiga yarufo murfin kai key din yayi jikin motar yana son kunnata saidai yakasa daidaita key din da inda ake zurashi saboda rawar da hannunshi yake ganin hakan yasashi sakin key din kawai ya hada kanshi da sterring yana sauke numfashi ahankali kanshi sarawa yake, mugun sara, jiyake kamar ya cireshi ya jefar ko zai huta why? meyasa abbubuwa suka taru suka cakudemashi yau? meyasa abubbuwan dayake kasa jura ke faruwa dashi yau first is Mussadiq, yanzu kuma Deen? meyasa sai yanzu Deen zai bayyana? meyasa ya bayyana tun yanzu? bude rinnanun idanunshi yayi ahankali kenan dama duk wannan abin da ake bayaso Deen ya bayyana? yayi tunanin zaifi kowa farinciki Idan Deen ya bayyana tunda hakan na nufin farincikin zee itama amma sai yaga sa6anin haka, Abinda yakeji kwata2.beyi kama da farinciki ba, mutumin da suka dade suna nema ya bayyana amma baya murna. so strange! ya dade cikin motar ahakan kafin yasamu yadan dawo normal, atleast yasan zai iya lalla6awa yakai kanshi gida wayarshi dake gaban motar ya dauka ya Kunna missed calls yagani rututu, daga ummy, abbu, batool da... qurawa sunanta dake rubuce a screen din wayar idanu yayi itace tafi qarancin kira acikinsu amma itace kiranta yafi tasiri agareshi Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ajiye wayar batareda ya.maida kowa cikinsu kira ba, ya duqa ya dauki key din daya saki daxu ya zura a keypoint din ya tada motar ya jata ahankali yabar company din.....✍? *manage please, nima managing nayi nayimuku post din, keep praying for me, heart you all💗* Ummin fasihu🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:42 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *072* *THE MUSICIAN 2* Qarar bude kofa taji amma hakan besata dagowa ba ko janye ido daga inda ta kafe da kallo ba ahankali batool ta qaraso wajenta ta zauna gefenta tana kallonta shiru yadan ratsa dakin kafin batool ta sauke Ajiyar zuciya "zee.." bata motsa ba kuma bata juyo ta kalleta ba "zee ya kamata kisaki ranki hakanan, all is well insha allah" tafada cikin son kwantar mata da hankali shiru dakin yasake dauka kamar baxata ce komai ba can kuma tace "meyasa?... meyasa wadannan abubbuwan ke faruwa dani?" kasa amsawa batool tayi sai kallonta datake emotionally "daga wannan sai wannan? when will I have peace of mind?" tafada wasu hawayen na kawo mata jawota batool tayi ta rungumeta ta gefe tana dan jijjiga kafadarta alamun rarrashi "Zainab, all will be well insha allah" "when? yaushe komai din zai daidaita? am fed up, nagaji" tafada hawaye na gangaromata a kumatu "yanzu ina Aymaan, ni dake munsan yanayin daya bar school daxu kuma gashi haryanzu be dawo gida ba and baya picking calls, allah kadai yasan halin dayake ciki kuma kowanne hali yake ciki nice sila" "shhhh... kibar fadin haka, insha allah yana nan lfy lau kuma zai dawo, kibar dorama kanki laifi da damuwa" shiru zee tayi tana sauraronta, wani iri take ji a zuciyarta, komai baya mata dadi. tunda take da Aymaan bata ta6a ganinshi a irin yanayin data ganshi yau ba gabadaya ya burkuce kamar ba gentle Aymaan data sani ba, ya burkuce ya koma wani daban kuma duk itace sila and she don't blame him, dole ya fusata a yanayin daya gansu ganinsu fa yayi yana bata ruwa a baki, mutumin da yasha attempting marinta yana tare mata har takai da an tsareshi na wani lokaci wanda hakan ba qaramin cin fuska bane agareshi duba da matsayinshi da reputation dinshi amma shi zai gani yana bata ruwa abaki dole koma waye hakan yafaru dashi yaji zafin abun da farko ya ganta a motarshi yanzu kuma yaganta taredashi yana bata ruwa looking more like lovers, Idan ya yarda wancan karon bada son ranta tashiga motarshi ba yanzu fa? ai ba dura ya iske yana mata ba. wani irin haushin Mussadiq taji tana ji, bata ida tabbatar da Mussadiq is soo annoying ba sai yau, tarasa dalilin dayasa tun farkon haduwarsu dashi suke samun matsala dashi, kwata2 rayuwar dasukayi da Deen beyi kama data Mussadiq ba ko kadan, rayuwar dasukayi da Deen is opposite data Mussadiq don duk lokacin dasuka hadu basa rabuwa ta dadi kuma tarasa dalili Jin tsayuwar motar awaje yasata dan qame jikinta waje daya kamar yadda batool itama tayi kallon juna sukayi sannan suka tashi atare suka nufi window inda suke iya hangen harabar gidan tanan ganin motar Aymaan na parking yasa suka wara idanu suka kalli juna cikin murna "he's back!" tare suka nufi kofa da sauri har suna rige2 fitowa sukayi suka fara saukowa saman stairs din cikin sauri cak zee ta tsaya tsakiyar benen takasa qarasa sauka saboda tozalin datayi dashi tsayawa tayi tana kallonshi kamar yau tafara ganinshi ya koma kamar bashi ba, Aymaan data sani tsaftsaf always looking neat and tidy shine tsaye agabanta cikin squeezed and dirty shirt harda yaga awasu wuraren ga fuskarshi duk bruises daya samu wajen fadan dasukayi dazu, he looked more like a thug ganinshi a wannan yanayin yasata kasa qarasawa sai tsayawa datayi tana kallonshi "Akhie!" inji batool tana fadawa jikinshi hannu yasa ya taro bayanta batareda ya janye idanunshi akan zee daya fara kallo tun shigowarshi *she's an angel, angel of light and beauty* tunawa yayi da kalaman Deen *duk inda ta gifta tana barin walwalin haskenta awajen,hasken dazai cigaba da haskaka wadanda tabari awajen* How true his words are "Aymaan..." muryar ummy ta katseshi janye idanunshi yayi daga kan zee ya maida kan ummy data qaraso itama gabanshi Dan murmushi yasakarmata yana kallon worried face dinta "Aymaan ina kashiga? anata kiran wayarka baka picking shima Ahmad ba'a samunshi, yanzu haka Abbu yafita nemanka" tafada tana kallonshi dry murmushi yasake qirqira yana sakin batool sannan yamatso gaban ummy yariqo hannunta "kuyi hqr, ina tareda Ahmad ne kuma nabar wayata a mota" ganin ummy na bin jikinshi da kallo yasa shima kallon jikinshi ganin abinda ummy ke kallo yasashi dan murmushi yace "ummy Bari nashiga nadan watsa" kada mashi kai ummy Kawai tayi tana kallonshi juyawa yayi ya nufo stairs din su ummy na binshi da kallo tunda yataho bugun zuciyarta ya qara gudu, cigaba da kallonshi tayi zuciyarta na cigaba da bugawa tana kallon yadda yake qara kusantota sotake ta bar wajen amma takasa ko motsawa kamar yadda takasa janye idanunta akanshi shikuma a nashi bangaren ba ita yake kallo ba, idanunshi na qasa harya fara taka stairs din ahankali yake taka stairs din harya qaraso inda take tsaye ahankali ya dago hazel idanunshi ya kalleta hada idanu sukayi wanda hakan yasa Zainab saurin janye nata idanun ta saukesu qasa zuciyarta na cigaba da bugawa ahankali taji wucewarshi ta gefenta ya cigaba da haura stairs hawaye ne suka taru a idanunta dake kallon qasa tana jin wani sense of guilt a qasan zuciyarta saida taji qarar rufewar kofar dakinshi sannan itama tajuya tayi saman da sauri ta bude kofarsu tashige Ajiyar zuciya ummy da batool dake kallonsu tundazu sukayi, ummy tajuya tana lalubo number abbu don sanardashi dawowar Aymaan itakuma batool tabi zee sama. 💖💖💖💖💖💖💖💖💖 *ABUJA, NIGERIA🇳🇬* Tafiya take tana dan bin harabar wajen da kallo. mutanen dake harabar wajen basuda yawa, don yan tsirarun mutane ne jifa jifa awajen cigaba tayi da tafiyarta tana scanning wajen kamar mai neman wani "ranki shi dade!" taji wata familiar murya namata magana a bayanta tsayawa tayi daga tafiyar datake sannan ta juyo ahankali qarasowa saurayin yayi wajenta yana washe baki ganin hakan yasata itama murmusawa "ranki ya dade, kune yau a ma'aikatar mu?" inji saurayin bayan ya qaraso "aikaudai Mallam Habeeb, ya aiki?" tafada tana gyara zaman sidebag dinta "Alhamdullilah, gashinan munata fama, ya zafi2 ya school?" "Alhamdullilah, daga can ma nake nayi tunanin dropping nan nayi checking abokinka, meya samu wayarshi?" "bata shiga?" "baya dagawa dai" "ayyah, yana cikin studio ne, nasan yanzu haka silent take" kada kai tayi tana dan ta6e baki "nima nayi tunanin hakan" "muje, nasan yanzu ma yakusan gamawa" inji saurayin "ok, muje" tare suka jero suna tafe suna dan labari jifa jifa har suka shige wani building wani passage suka bi suna cigaba da firarsu Idan suka hadu da wasu a hanya su gaisa har suka qaraso inda zasu tun kafin su shiga tafara jin cool voice dinshi na tashi in a cool rymth lumshe idanunta tayi ta bude ahankali sannan tashiga ta kofar da Habeeb ya budemata akwai mutane a studio din as usual amma basuda yawa, kowa hankalinshi da imaninshi ya tattara ya koma akanshi don dayawa basusan da shigowarsu Habeeb ba daga idanu tayi ta kalleshi tacikin glass din dayake ciki kanshi sanye da headphones sai mic dake girke a gabanshi mai dauke da abin tace murya jitayi zuciyarta na melting lokacin data sauke idanunta akan fuskarshi, fuskar da duk duniya bataga mai kyawunta ba, fuskar da ke narkar da zuciyarta daga kallo daya _Duba kigaa yadda sonki yayi dani.. dukda nasan kina sane_ _ki kalli cikin idanuwanaaa.. nasan xasu zayyane_ _wannan al'ajab na sone da qauna.. baki na kiranki neee_ _dana fada kiji_ _kibani agaji_ _indaina rangaji_ _kidanyi tsokaci_ _kibani ma'aji_ _ba zancen na gaji_ _ki kauda fuu da ji_ _a so baya ji_ _labarin zuciya_ _ni zaki tambaya_ _Abinda nakaji_ _ya zarce duniyaa_ _Idan na waiwaya_ _koko na sunkuya_ _amsar guda nakeji.._ _kinzaman habibiya_... Kafe pink moving lips dinshi tayi da idanunta tana jin yadda sautin muryar tashi ke sinking har qasan zuciyarta ahankali ta janye idanunta daga kan bakinshi tafara yawo dasu a fuskarshi idanunshi a lumshe suke wanda hakan yaba zarazaran lashes dinshi damar hadewa, tarasa yaushe yafi kyau, Idan idanunshi na a lumshe ko Idan suna a bude. kallon cikkakun girarenshi tayi ganin yadda suke motsawa ahankali, gangaro da idanun nata tayi kan pointed nose dinshi daya dace da fuskarshi, ahankali tasake maida idanun kan bakinshi dake motsawa haryanzu. lumshe idanu tasakeyi ta bude tanajin wani abu na tasowa daga qasan zuciyarta anya a duniya akwai wanda zai so gayen nan kamar yadda take sonshi? she doubt it, ajikinta tana jin duk wani mai son Deen to saidai yabi bayanta don soyayyar datake mashi batada iyaka Deen on the other hand besan tana yi ba, yayi nisa, nisa daga wannan duniyar tamu, yana wata.duniyar daban, wanda yasaba shiga duk lokacin dayake waqa idanunshi na alumshe amma yana gani clearly saidai ba abinda wadanda kecikin studio din ke gani yake gani ba he has wander into his dreamland kamar yadda yasaba acikin lumssasun idanunshi wani beautiful scene yake gani fuskar da kullum ke zuwa mashi tana mashi gizo dare da rana, fuskar da sai idan yana ganinta yake iya rairo abinda ke zuciyarshi, fuskar da tazame mashi kamar abincin dayake ci ko iskar dayake shaqa _ya za'ai na burge wacce nakeso da qauna? ya za'ai?_ _kalamaina sun kadan ta fahimceni sannan... ba hanya_ _kalamaina sun kadan ta fahimceni sannan ba hanya!!_ _inaso tasoni ne ba guruu babu laya_ _babu dad'i babu qarya.. ni banison riya_ _badon kwalliyaba kuma badon dukiya ba_ _badon zantuka ba kullum taimun maraba_ _ina sonki.. ina sonki.. inaa sonki_ _ina sonki so na gaskiya ba yaudara ba_ _ina sonki.. ina sonki.. ina sonki ni.._ _ina sonki so na gaskiya ba yaudara ba_ _ina sonki so na gaskiya ba yaudara baaaaa_ ihu studio din ya dauka da tafi wasu harda fito. sosai mutanen cikin studio din ke nuna jindadinsu afili sai kirari suke mashi bude lumsassun idanunshi yayi ahankali yana bin mutanen cikin studio din da kallo murmushi a fuskarshi ahaka oily idanunshi suka sauka a kanta inda take tsaye tayi crossing hannayenta a qirji itama tana kallonshi kafe juna da kallo sukayi na wani lokaci sannan ahankali deen ya sakarmata kyakyawan murmushinshi jitayi wani farinciki ya mamaye zuciyarta nan take, ahankali itama ta sakarmashi nata murmushin mai kyau. *** "ya school?" yafada cikin cool voice dinshi "Alhamdullilah, ya naka aikin?" ta tambaya itama suna cigaba da tafiya side by side "Alhamdullilah also, yasu mamy?" "su mamy na nan lfy lau, tace ka kyauta daka maidasu gefe guda" Dan murmushi yayi yana cusa yatsunshi cikin saisayayen sumarshi wadda bata kai ta da cika ba "hmmm ba haka bane" yafada cikin murmushi "to yane? kwata2 ka daina zuwa, ganinka yanzu sai an cika form, aita kiran wayarka ma ba'a samu" she complained "am sorry, I've been busy ne a kwanakinnan amma zanzo, kiba mamy hqr" Dan wara idanu tayi tace "A'a, kabari duk ranar dakaje kabata, ni babu ruwana" murmushi kawai yayi bece komai ba ganin hakan yasa itama bata qara cewa komai ba suka cigaba da tafiya silently, tafiya gefe da gefe taredashi ba qaramin dadi yake mata ba musanmman Idan ta lura da yadda ake binsu da kallo inda mostly mata ne ke kallon nasu kowanne fuska dauke da kishi don sun lura Deen baya kula kowacce mace sai ita hakan yasa basasonta ko kadan. parking space suka isa Deen yashiga waige2 "ina motarki?" Dan daga kafadu tayi "tadan samu matsala tana wajen mechanic" "to da me kikazo?" "adaidaita, yanzu ma dashi zan koma" "amma kinsan adaidaita na wuya a arear nan ko?" Dan 6ata fuska tayi "I'll wait, no p" Ajiyar zuciya ya sauke "ina zuwa" yana fadin hakan ya juya Dan murmushi tayi seems tarkonta ya danu, dama da gangan tasa drivernta dropping dinta tace yatafi kawai ko minti biyu ba'ayi ba wata blue din mota ta qaraso wajenta ta tsaya Deen ke ciki "get in, let me drop you" yafada bayan ya sauke glasses din qasa Dan sunkuyowa tayi tana kallonshi "aren't you busy? kabarshi kawai xan samu adaidaita" bece komai ba sai matsowa dayayi ya bude mata kofar Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ida bude murfin tashiga ta maido ta rufe tada motar yayi sannan yajata suka fita daga wajen. Tafiya suke babu mai cewa komai acikinsu sai qira'ar Qur'an dake tashi cikin motar Deen hankalinshi na kan titi yana driving at normal speed while itakuma tana lafe a kujerar mai zaman banza tana shaqar qamshinshi daya hadu da sanyin a.c din motar yabada wani sanyayar yanayi. Babu jimawa suka isa kofar gidansu, batasan sun iso ba saida taji tsayuwar motar, sai.taga sunyi saurin zuwa, bata gaji da shaqar qamshinshi ba "here we are" inji Deen tashi tayi zaune sosai "Bazaka shiga ba?" Dan wara oily eyes dinshi yayi "zan dai shigo soon insha allah" "hmm to saina gayamata" tafada tana qoqarin fita "me zaki gayamata?" yafada yana kallonta "kazo amma you choose to turn around and go back" "bazaki fadamata nazo ba" yafada fuskarshi da slight murmushi "saina fada" tafada tana ida fita "I dare you" yafada daringly fuskarshi da slight murmushi kada kai tayi tana kwafa "zaka gani kau" tafada tana rufo mashi kofar motar dagama juna hannu sukayi sannan tajuya tanufi tangamemen gate din gidansu shikuma yaja motarshi yaqara gaba. *10:15pm* "Shikenan Kaka, allah yakaimu goben lfy" yafada ahankali murmushi Kaka tayi ta shafa mashi kai "Amin kyakyawana, yanzu kaje ka kwanta dare yayi nima barci nakeji" "to Kaka, saida safe" "Allah ya tashemu lfy, karka manta kayi alwalla kuma kayi addu'a" kada kai yayi cikin murmushi sannan ya tashi ya kashemata fitilun dakin yabarmata na bedlamp kadai sannan yayimata sallama yafita. ahankali yake takawa kasancewar dare yayi hakan yasa anajin faint sautin takunshi, ahaka harya isa dakinshi. dakin is so big and neat, yasha kayan furnitures na zamani ga haske takoina. direct gefen makeken gadonshi that is neatly spread ya nufa yafara rage kayan jikinshi jefa wadanda yacire yayi a wani dogon bin inda dama yake saka kayanshi masu datti kafin laundrier yazo ya dauke washegari toilet yashige don freshen up. ya dade sosai a toilet din sannan yafito daure da towel a kugu sai wani a hannunshi yana tsane jikinshi chanzawa yayi cikin kayan barci farare sannan ya shinfida sallaya ya gabatar da shafa'i da witr sannan ya rufe da addu'o'i nade sallayar yayi ya maida ma'ajinta sannan ya miqe tsaye. maimakon ya nufi gadonshi ya kwanta saiya nufi wani side din na daki ahankali ya bude wata qofa wanda ta sadashi da balcony din gidan stepping yayi cikin balcony din yana kallon waje yana feeling yadda iskan daren ke kadawa koina yayi shiru sai kukan tsintsaye da zaka dinga jiyowa daga nesa dana qanannun qwari garin yayi duhu sai hasken wata dake haskawa faintly ahankali ya zura hannayenshi cikin aljihunnan wandonshi yana bin wurin da kallo yaushe zaibar jinshi so empty? yaushe wawakeken gurbin dake zuciyarshi zai cike? yaushe duhu zai yaye? yaushe haske zai qara ziyartar rayuwarshi? yaushe farinciki zai sake ziyartar rayuwarshi? yaushe? ahankali ya daga kanshi ya kalli sama yana hango wata daya fara disashewa alamun soyake shima yashige cikin gajimare bin yan mitsi mitsin taurarin dake saman yayi da kallo trying to count them amma sunyi yawa daya fara saiya 6ata a lissafin. haqura yayi ya sauke idanunshi qasa yana qara observing din garin hasken watan dake dan haska garin sai qara disashewa yake hakan yasa garin ke qara duhu, duhun da ga wasu na dan qanqanin lokaci ne don da gari ya waye zasuga haske, amma agareshi ba haka abin yake ba, koda gari ya waye wa kowa baxai waye mashi ba ya dade cikin duhu kuma besan iya lokacin daxai sake dauka acikinshi ba. maybe forever maybe not...✍? Ummin fasihu🧚🏻‍♀?*🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *072* *THE MUSICIAN 2* Qarar bude kofa taji amma hakan besata dagowa ba ko janye ido daga inda ta kafe da kallo ba ahankali batool ta qaraso wajenta ta zauna gefenta tana kallonta shiru yadan ratsa dakin kafin batool ta sauke Ajiyar zuciya "zee.." bata motsa ba kuma bata juyo ta kalleta ba "zee ya kamata kisaki ranki hakanan, all is well insha allah" tafada cikin son kwantar mata da hankali shiru dakin yasake dauka kamar baxata ce komai ba can kuma tace "meyasa?... meyasa wadannan abubbuwan ke faruwa dani?" kasa amsawa batool tayi sai kallonta datake emotionally "daga wannan sai wannan? when will I have peace of mind?" tafada wasu hawayen na kawo mata jawota batool tayi ta rungumeta ta gefe tana dan jijjiga kafadarta alamun rarrashi "Zainab, all will be well insha allah" "when? yaushe komai din zai daidaita? am fed up, nagaji" tafada hawaye na gangaromata a kumatu "yanzu ina Aymaan, ni dake munsan yanayin daya bar school daxu kuma gashi haryanzu be dawo gida ba and baya picking calls, allah kadai yasan halin dayake ciki kuma kowanne hali yake ciki nice sila" "shhhh... kibar fadin haka, insha allah yana nan lfy lau kuma zai dawo, kibar dorama kanki laifi da damuwa" shiru zee tayi tana sauraronta, wani iri take ji a zuciyarta, komai baya mata dadi. tunda take da Aymaan bata ta6a ganinshi a irin yanayin data ganshi yau ba gabadaya ya burkuce kamar ba gentle Aymaan data sani ba, ya burkuce ya koma wani daban kuma duk itace sila and she don't blame him, dole ya fusata a yanayin daya gansu ganinsu fa yayi yana bata ruwa a baki, mutumin da yasha attempting marinta yana tare mata har takai da an tsareshi na wani lokaci wanda hakan ba qaramin cin fuska bane agareshi duba da matsayinshi da reputation dinshi amma shi zai gani yana bata ruwa abaki dole koma waye hakan yafaru dashi yaji zafin abun da farko ya ganta a motarshi yanzu kuma yaganta taredashi yana bata ruwa looking more like lovers, Idan ya yarda wancan karon bada son ranta tashiga motarshi ba yanzu fa? ai ba dura ya iske yana mata ba. wani irin haushin Mussadiq taji tana ji, bata ida tabbatar da Mussadiq is soo annoying ba sai yau, tarasa dalilin dayasa tun farkon haduwarsu dashi suke samun matsala dashi, kwata2 rayuwar dasukayi da Deen beyi kama data Mussadiq ba ko kadan, rayuwar dasukayi da Deen is opposite data Mussadiq don duk lokacin dasuka hadu basa rabuwa ta dadi kuma tarasa dalili Jin tsayuwar motar awaje yasata dan qame jikinta waje daya kamar yadda batool itama tayi kallon juna sukayi sannan suka tashi atare suka nufi window inda suke iya hangen harabar gidan tanan ganin motar Aymaan na parking yasa suka wara idanu suka kalli juna cikin murna "he's back!" tare suka nufi kofa da sauri har suna rige2 fitowa sukayi suka fara saukowa saman stairs din cikin sauri cak zee ta tsaya tsakiyar benen takasa qarasa sauka saboda tozalin datayi dashi tsayawa tayi tana kallonshi kamar yau tafara ganinshi ya koma kamar bashi ba, Aymaan data sani tsaftsaf always looking neat and tidy shine tsaye agabanta cikin squeezed and dirty shirt harda yaga awasu wuraren ga fuskarshi duk bruises daya samu wajen fadan dasukayi dazu, he looked more like a thug ganinshi a wannan yanayin yasata kasa qarasawa sai tsayawa datayi tana kallonshi "Akhie!" inji batool tana fadawa jikinshi hannu yasa ya taro bayanta batareda ya janye idanunshi akan zee daya fara kallo tun shigowarshi *she's an angel, angel of light and beauty* tunawa yayi da kalaman Deen *duk inda ta gifta tana barin walwalin haskenta awajen,hasken dazai cigaba da haskaka wadanda tabari awajen* How true his words are "Aymaan..." muryar ummy ta katseshi janye idanunshi yayi daga kan zee ya maida kan ummy data qaraso itama gabanshi Dan murmushi yasakarmata yana kallon worried face dinta "Aymaan ina kashiga? anata kiran wayarka baka picking shima Ahmad ba'a samunshi, yanzu haka Abbu yafita nemanka" tafada tana kallonshi dry murmushi yasake qirqira yana sakin batool sannan yamatso gaban ummy yariqo hannunta "kuyi hqr, ina tareda Ahmad ne kuma nabar wayata a mota" ganin ummy na bin jikinshi da kallo yasa shima kallon jikinshi ganin abinda ummy ke kallo yasashi dan murmushi yace "ummy Bari nashiga nadan watsa" kada mashi kai ummy Kawai tayi tana kallonshi juyawa yayi ya nufo stairs din su ummy na binshi da kallo tunda yataho bugun zuciyarta ya qara gudu, cigaba da kallonshi tayi zuciyarta na cigaba da bugawa tana kallon yadda yake qara kusantota sotake ta bar wajen amma takasa ko motsawa kamar yadda takasa janye idanunta akanshi shikuma a nashi bangaren ba ita yake kallo ba, idanunshi na qasa harya fara taka stairs din ahankali yake taka stairs din harya qaraso inda take tsaye ahankali ya dago hazel idanunshi ya kalleta hada idanu sukayi wanda hakan yasa Zainab saurin janye nata idanun ta saukesu qasa zuciyarta na cigaba da bugawa ahankali taji wucewarshi ta gefenta ya cigaba da haura stairs hawaye ne suka taru a idanunta dake kallon qasa tana jin wani sense of guilt a qasan zuciyarta saida taji qarar rufewar kofar dakinshi sannan itama tajuya tayi saman da sauri ta bude kofarsu tashige Ajiyar zuciya ummy da batool dake kallonsu tundazu sukayi, ummy tajuya tana lalubo number abbu don sanardashi dawowar Aymaan itakuma batool tabi zee sama. 💖💖💖💖💖💖💖💖💖 *ABUJA, NIGERIA🇳🇬* Tafiya take tana dan bin harabar wajen da kallo. mutanen dake harabar wajen basuda yawa, don yan tsirarun mutane ne jifa jifa awajen cigaba tayi da tafiyarta tana scanning wajen kamar mai neman wani "ranki shi dade!" taji wata familiar murya namata magana a bayanta tsayawa tayi daga tafiyar datake sannan ta juyo ahankali qarasowa saurayin yayi wajenta yana washe baki ganin hakan yasata itama murmusawa "ranki ya dade, kune yau a ma'aikatar mu?" inji saurayin bayan ya qaraso "aikaudai Mallam Habeeb, ya aiki?" tafada tana gyara zaman sidebag dinta "Alhamdullilah, gashinan munata fama, ya zafi2 ya school?" "Alhamdullilah, daga can ma nake nayi tunanin dropping nan nayi checking abokinka, meya samu wayarshi?" "bata shiga?" "baya dagawa dai" "ayyah, yana cikin studio ne, nasan yanzu haka silent take" kada kai tayi tana dan ta6e baki "nima nayi tunanin hakan" "muje, nasan yanzu ma yakusan gamawa" inji saurayin "ok, muje" tare suka jero suna tafe suna dan labari jifa jifa har suka shige wani building wani passage suka bi suna cigaba da firarsu Idan suka hadu da wasu a hanya su gaisa har suka qaraso inda zasu tun kafin su shiga tafara jin cool voice dinshi na tashi in a cool rymth lumshe idanunta tayi ta bude ahankali sannan tashiga ta kofar da Habeeb ya budemata akwai mutane a studio din as usual amma basuda yawa, kowa hankalinshi da imaninshi ya tattara ya koma akanshi don dayawa basusan da shigowarsu Habeeb ba daga idanu tayi ta kalleshi tacikin glass din dayake ciki kanshi sanye da headphones sai mic dake girke a gabanshi mai dauke da abin tace murya jitayi zuciyarta na melting lokacin data sauke idanunta akan fuskarshi, fuskar da duk duniya bataga mai kyawunta ba, fuskar da ke narkar da zuciyarta daga kallo daya _Duba kigaa yadda sonki yayi dani.. dukda nasan kina sane_ _ki kalli cikin idanuwanaaa.. nasan xasu zayyane_ _wannan al'ajab na sone da qauna.. baki na kiranki neee_ _dana fada kiji_ _kibani agaji_ _indaina rangaji_ _kidanyi tsokaci_ _kibani ma'aji_ _ba zancen na gaji_ _ki kauda fuu da ji_ _a so baya ji_ _labarin zuciya_ _ni zaki tambaya_ _Abinda nakaji_ _ya zarce duniyaa_ _Idan na waiwaya_ _koko na sunkuya_ _amsar guda nakeji.._ _kinzaman habibiya_... Kafe pink moving lips dinshi tayi da idanunta tana jin yadda sautin muryar tashi ke sinking har qasan zuciyarta ahankali ta janye idanunta daga kan bakinshi tafara yawo dasu a fuskarshi idanunshi a lumshe suke wanda hakan yaba zarazaran lashes dinshi damar hadewa, tarasa yaushe yafi kyau, Idan idanunshi na a lumshe ko Idan suna a bude. kallon cikkakun girarenshi tayi ganin yadda suke motsawa ahankali, gangaro da idanun nata tayi kan pointed nose dinshi daya dace da fuskarshi, ahankali tasake maida idanun kan bakinshi dake motsawa haryanzu. lumshe idanu tasakeyi ta bude tanajin wani abu na tasowa daga qasan zuciyarta anya a duniya akwai wanda zai so gayen nan kamar yadda take sonshi? she doubt it, ajikinta tana jin duk wani mai son Deen to saidai yabi bayanta don soyayyar datake mashi batada iyaka Deen on the other hand besan tana yi ba, yayi nisa, nisa daga wannan duniyar tamu, yana wata.duniyar daban, wanda yasaba shiga duk lokacin dayake waqa idanunshi na alumshe amma yana gani clearly saidai ba abinda wadanda kecikin studio din ke gani yake gani ba he has wander into his dreamland kamar yadda yasaba acikin lumssasun idanunshi wani beautiful scene yake gani fuskar da kullum ke zuwa mashi tana mashi gizo dare da rana, fuskar da sai idan yana ganinta yake iya rairo abinda ke zuciyarshi, fuskar da tazame mashi kamar abincin dayake ci ko iskar dayake shaqa _ya za'ai na burge wacce nakeso da qauna? ya za'ai?_ _kalamaina sun kadan ta fahimceni sannan... ba hanya_ _kalamaina sun kadan ta fahimceni sannan ba hanya!!_ _inaso tasoni ne ba guruu babu laya_ _babu dad'i babu qarya.. ni banison riya_ _badon kwalliyaba kuma badon dukiya ba_ _badon zantuka ba kullum taimun maraba_ _ina sonki.. ina sonki.. inaa sonki_ _ina sonki so na gaskiya ba yaudara ba_ _ina sonki.. ina sonki.. ina sonki ni.._ _ina sonki so na gaskiya ba yaudara ba_ _ina sonki so na gaskiya ba yaudara baaaaa_ ihu studio din ya dauka da tafi wasu harda fito. sosai mutanen cikin studio din ke nuna jindadinsu afili sai kirari suke mashi bude lumsassun idanunshi yayi ahankali yana bin mutanen cikin studio din da kallo murmushi a fuskarshi ahaka oily idanunshi suka sauka a kanta inda take tsaye tayi crossing hannayenta a qirji itama tana kallonshi kafe juna da kallo sukayi na wani lokaci sannan ahankali deen ya sakarmata kyakyawan murmushinshi jitayi wani farinciki ya mamaye zuciyarta nan take, ahankali itama ta sakarmashi nata murmushin mai kyau. *** "ya school?" yafada cikin cool voice dinshi "Alhamdullilah, ya naka aikin?" ta tambaya itama suna cigaba da tafiya side by side "Alhamdullilah also, yasu mamy?" "su mamy na nan lfy lau, tace ka kyauta daka maidasu gefe guda" Dan murmushi yayi yana cusa yatsunshi cikin saisayayen sumarshi wadda bata kai ta da cika ba "hmmm ba haka bane" yafada cikin murmushi "to yane? kwata2 ka daina zuwa, ganinka yanzu sai an cika form, aita kiran wayarka ma ba'a samu" she complained "am sorry, I've been busy ne a kwanakinnan amma zanzo, kiba mamy hqr" Dan wara idanu tayi tace "A'a, kabari duk ranar dakaje kabata, ni babu ruwana" murmushi kawai yayi bece komai ba ganin hakan yasa itama bata qara cewa komai ba suka cigaba da tafiya silently, tafiya gefe da gefe taredashi ba qaramin dadi yake mata ba musanmman Idan ta lura da yadda ake binsu da kallo inda mostly mata ne ke kallon nasu kowanne fuska dauke da kishi don sun lura Deen baya kula kowacce mace sai ita hakan yasa basasonta ko kadan. parking space suka isa Deen yashiga waige2 "ina motarki?" Dan daga kafadu tayi "tadan samu matsala tana wajen mechanic" "to da me kikazo?" "adaidaita, yanzu ma dashi zan koma" "amma kinsan adaidaita na wuya a arear nan ko?" Dan 6ata fuska tayi "I'll wait, no p" Ajiyar zuciya ya sauke "ina zuwa" yana fadin hakan ya juya Dan murmushi tayi seems tarkonta ya danu, dama da gangan tasa drivernta dropping dinta tace yatafi kawai ko minti biyu ba'ayi ba wata blue din mota ta qaraso wajenta ta tsaya Deen ke ciki "get in, let me drop you" yafada bayan ya sauke glasses din qasa Dan sunkuyowa tayi tana kallonshi "aren't you busy? kabarshi kawai xan samu adaidaita" bece komai ba sai matsowa dayayi ya bude mata kofar Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ida bude murfin tashiga ta maido ta rufe tada motar yayi sannan yajata suka fita daga wajen. Tafiya suke babu mai cewa komai acikinsu sai qira'ar Qur'an dake tashi cikin motar Deen hankalinshi na kan titi yana driving at normal speed while itakuma tana lafe a kujerar mai zaman banza tana shaqar qamshinshi daya hadu da sanyin a.c din motar yabada wani sanyayar yanayi. Babu jimawa suka isa kofar gidansu, batasan sun iso ba saida taji tsayuwar motar, sai.taga sunyi saurin zuwa, bata gaji da shaqar qamshinshi ba "here we are" inji Deen tashi tayi zaune sosai "Bazaka shiga ba?" Dan wara oily eyes dinshi yayi "zan dai shigo soon insha allah" "hmm to saina gayamata" tafada tana qoqarin fita "me zaki gayamata?" yafada yana kallonta "kazo amma you choose to turn around and go back" "bazaki fadamata nazo ba" yafada fuskarshi da slight murmushi "saina fada" tafada tana ida fita "I dare you" yafada daringly fuskarshi da slight murmushi kada kai tayi tana kwafa "zaka gani kau" tafada tana rufo mashi kofar motar dagama juna hannu sukayi sannan tajuya tanufi tangamemen gate din gidansu shikuma yaja motarshi yaqara gaba. *10:15pm* "Shikenan Kaka, allah yakaimu goben lfy" yafada ahankali murmushi Kaka tayi ta shafa mashi kai "Amin kyakyawana, yanzu kaje ka kwanta dare yayi nima barci nakeji" "to Kaka, saida safe" "Allah ya tashemu lfy, karka manta kayi alwalla kuma kayi addu'a" kada kai yayi cikin murmushi sannan ya tashi ya kashemata fitilun dakin yabarmata na bedlamp kadai sannan yayimata sallama yafita. ahankali yake takawa kasancewar dare yayi hakan yasa anajin faint sautin takunshi, ahaka harya isa dakinshi. dakin is so big and neat, yasha kayan furnitures na zamani ga haske takoina. direct gefen makeken gadonshi that is neatly spread ya nufa yafara rage kayan jikinshi jefa wadanda yacire yayi a wani dogon bin inda dama yake saka kayanshi masu datti kafin laundrier yazo ya dauke washegari toilet yashige don freshen up. ya dade sosai a toilet din sannan yafito daure da towel a kugu sai wani a hannunshi yana tsane jikinshi chanzawa yayi cikin kayan barci farare sannan ya shinfida sallaya ya gabatar da shafa'i da witr sannan ya rufe da addu'o'i nade sallayar yayi ya maida ma'ajinta sannan ya miqe tsaye. maimakon ya nufi gadonshi ya kwanta saiya nufi wani side din na daki ahankali ya bude wata qofa wanda ta sadashi da balcony din gidan stepping yayi cikin balcony din yana kallon waje yana feeling yadda iskan daren ke kadawa koina yayi shiru sai kukan tsintsaye da zaka dinga jiyowa daga nesa dana qanannun qwari garin yayi duhu sai hasken wata dake haskawa faintly ahankali ya zura hannayenshi cikin aljihunnan wandonshi yana bin wurin da kallo yaushe zaibar jinshi so empty? yaushe wawakeken gurbin dake zuciyarshi zai cike? yaushe duhu zai yaye? yaushe haske zai qara ziyartar rayuwarshi? yaushe farinciki zai sake ziyartar rayuwarshi? yaushe? ahankali ya daga kanshi ya kalli sama yana hango wata daya fara disashewa alamun soyake shima yashige cikin gajimare bin yan mitsi mitsin taurarin dake saman yayi da kallo trying to count them amma sunyi yawa daya fara saiya 6ata a lissafin. haqura yayi ya sauke idanunshi qasa yana qara observing din garin hasken watan dake dan haska garin sai qara disashewa yake hakan yasa garin ke qara duhu, duhun da ga wasu na dan qanqanin lokaci ne don da gari ya waye zasuga haske, amma agareshi ba haka abin yake ba, koda gari ya waye wa kowa baxai waye mashi ba ya dade cikin duhu kuma besan iya lokacin daxai sake dauka acikinshi ba. maybe forever maybe not...✍? Ummin fasihu🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:43 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *073* *THE HARD DECISION* *Aslm fans, ya kuke😊 sorry for jina shiru kwana biyu, bear with me bear with me, insha allah andawo kenan🥰, masu kira da masu cigiya dama masu sakamu addu'a duk ina Godiya, Godiya marar adadi. Allah yabar zumunci Amin🤲🏻* Ringing din da wayarta keyi akaro na uku yasata jan dogon tsaki tareda jawo wayar afusace shin me kiran baya ganewa ne? tunda taqi dagawa tun farko ya kamata ya gane batason takura ya kyaleta hakanan. da niyyarta da kashe wayar amma ganin unknown number yasata dakatawa. ba wai rashin sanin mai kiran yasata dakatawa ba sai,yadda taga number, very special number da kallo daya zaka mata ka haddaceta katsewa kiran yayi cigaba da riqe wayar tayi,taga ko za'a qara kira amma shiru hakan yasa ta juyazata maida wayar inda ta daukota kafin ta gama ajiye wayar wayar tasake daukar ruri hakan yasa tafasa ajiyewar tasake dagota number ce dai, wannan ko maye ne sai haka saida kiran yakusan tsinkewa sannan ta daga takara a kunne batareda tace komai ba can ma shiru akayi ba'a ce komai Dan yamutse fuskarta tayi ta dago wayar taduba taga kiran na counting to meyasa ba'a magana? maidawa tayi a kunne again taji shiru hakan yasa taji ranta ya 6aci sai kawai ta tsinke kiran tana jan tsaki ko seconds biyar ba'a qara ba wani kiran yasake shigowa na number qin dagawa tayi kuma hakan besa aka fasa qara kira ba a kira na uku ta daga a fusace ta kara a kunne da niyyar zazzagawa koma waye bala'i kwanannan she's not in a.good mood, abu kadan ke fusatata amma seems basa ganewa most especially wannan annoying caller din bude baki tayi da niyyar fara masifa saidai kafin tafara aka katseta da "How dare you?" cikin wata muryar da kanaji kasan mammalakinta a wuya yake sakin baki tayi in confusion, waye wannan? the voice... "I said how dare you! ni nakiraki awaya ki tsinke? kinsan koni waye!" yafada cikin tsawa2 da alamu hakan ba qaramin 6ata mashi rai yayi ba wani murmushin takaici yazo mata, hmmm dama takawo hakan, the annoying fringe won't just leave her alone cikin son qara quleshi tace "and who are you?" cije lower lip dinshi yayi daga dayan 6angaren, yadda tayi maganar cikin izgili ba qaramin qara qonamashi rai yayi ba "just don't let me show you the real me baby, I bet you you'll be sorry" yafada tsakankanin haqora "really?" tafada in a mockery sound sai tadanyi dariya sannan tace "well am sorry bana daga wayar zarraru, lokacina qayyadadene kuma ina amfani dashi ne wajen yin abu mai amfani, zarraru number doctor ya kamata su kira. zasu fi gane yarensu. have a nice day" saita fara qoqarin cire wayar daga kunnenta don tsinke kiran amma annoying muryarshi tasake katseta "KARKI SOMA! karki fara tunanin katsemin waya or else.." sai kuma taji shiru jitayi fargaba tadan ziyarci zuciyarta "or else?" ta tambaya cikin dakewa "you'll be sorry" yafada cikin low but dangerous voice taji d'arr a yanayin yadda yayi maganar, mexeyi mata? kwahi? dama ana kwahi ta waya? wane irin kwahi zaiyi mata, wadannan tunanin sunsata jin fargaba don tasan yana iya yin komai don ba mutunci gareshi ba. amma Idan taqi katse kiran me hakan ke nufi? hakan hanya ce ta nunamashi cewa tsoronshi takeji, wanda hakan ke nufin qarin raini akan wanda yayi mata, no way! "then.. make me be" tafada daringly sannan batareda tabashi damar maida numfashi ba ta katse kiran tamayi blocking number gabadaya Tilla wayar tayi gefen gado cikin fushi da fargaba "do your worst!" tafada cikin son kawar da fargabar tunanin abinda zaiyi mata, no matter what bazata gwadamashi tana tsoronshi ba, that's it. A bangarenshi kau sakin baki yayi yakuma kasa sauke wayar daga kunnenshi he can't believe ta katse mashi kira a karo nabiyu, shi? Mussadiq Al-hassan? shine yau ake katsewa kira? bayan hakan kuma takirashi zarrare? sauke wayar yayi ahankali yana kallon numberta, number daya sato a wayar qanwarshi, duk don yaji ya take yakuma ji ko wannan mahaukacin dan uwan nata beyi something stupid ba amma ji Abinda tayi mashi, na farko taqi daga kiran harya jeramata uku abinda be ta6a ba sannan bayan ta daga ta katse mashi kira, abinda duk duniya ya tsana, qarin gishiri a ciwo ta kirashi zararre. lallai ma! qara maida lower lip dinshi yayi ciki yana tauna ahankali he'll make her be sorry that's a promise! A bangaren zee kau komawa tayi ta jingina da frame din gado zuciyarta babu dadi, sosai damuwa ta mamaye zuciyarta. yau kwana biyu kenan da faruwar wannan al'amarin sai taga kamar Aymaan avoiding dinta yake kwata2 baya bari su hadu Idan ma sun hadun baya bari ko magana ta hadasu zaya bar wajen wasa wasa har sukayi kwana biyar ahakan, ko kwakwarar magana daya bata shiga tsakaninsu ba, koda yana zaune awuri datazo wajen zai wayance ya kara waya a kunne ya tashi yabar wajen hakan ba qaramin dagulawa zee lissafi yake ba, duk jikinta yayi sanyi tana jinta so guilty. duk yadda takeso magana ta hadasu koda gaisuwace yaqi bata damar hakan, don kwata2 ya toshe duk hanyar dazasu mu'amallanci juna ya sauya mata daga Aymaan din data sani zuwa wani Aymaan din daban. *** Zaune yake yana kallon yadda Aymaan ke attending wata patient yana mata bayanai. yafi minti goma yana mata bayanin sannan ya rubuta mata magungguna ya bata takardar yana fada mata ranar dazata sake dawowa for checkup. Godiya sosai matar wanda da alamu taji dadin ganawarta da Dr Aymaan din tayi sannan ta tashi tafita shikuma yajawo wani file gabanshi yana yan rubuce rubuce Ajiyar zuciya Ahmad ya sauke sannan yace "wani lokacin kamar mutum y rufeka da duka don takaici" Dan murmushi ne ya kufcema Aymaan saidai bece komai ba "yanzu da zuwana patients nawa kayi attending agabana? ka shanyani kamar kayan wanki, tsabar bana gabanka dukda patients din sun qare Bazaka saurareni ba?" sai a lokacin Aymaan ya dago ya kalleshi sannan ya dan ta6e baki "I thought zuwa kayi ka kalli yadda ake attending patients" "dole kace haka tunda ni ai nataso nazo wajenka, dole kayimin wulaqanci son ranka tunda ni nakawo kaina" inji Ahmad yana fuming fuska murmushi kawai aymaan yayi bece komai ba saima cigaba da aikin gabanshi dayayi "to maganar dai da bakaso ne, maganar dakaita avoiding dina akanta itace takawoni, Aymaan kabani mammaki, ban ta6a tunanin zaka sare a daidai wannan stage din ba, ban ta6a tsanmmanin haka agareka ba" Aymaan be dago daga Abinda yake ba ya kalleshi amma hakan bazai hana mutum hango yadda mood din fuskarshi ta chanza ba "Aymaan, Idan mutum zaiyi taimako yayi da zuciya daya haka Idan bazaiyi ba yaqiyi da zuciya daya" sai a lokacin Aymaan ya dago daga rubutun dayake ya kalli Ahmad, ya tsaida idanunshi akanshi na wani lokaci kafin yace "me kake nufi?" "kafini sanin Abinda nake nufi Aymaan, da gaske ne so sone amma sonkai yafi, saidai inason kasani duk inda akasa sonkai gaba ana aikata kuskure,kuskuren dake jawo tarin danasani" Aymaan da ranshi yafara 6aci yace "go straight to the point Mallam, I hate kwana kwana" "Batun Deen nake maka, zancen dakake qoqarin watsarwa saboda son kanka" ran aymaan yasake 6aci "then? meye nayi na sonkai aciki? are you trying to blame me for everything? koko ka kuramce lokacin dayace sun haramta ga juna?" yafada cikin 6acin rai "ba maganar hallarci ko haramcin dake tsakaninshi da zee ke gabanmu ba, hallalci dake tsakaninshi da iyayenshi da danginshi shine gabanmu, haba Aymaan? you've been helping tunfarko, ka sadaukar da abubbuwa dayawa tun daga farkon wannan abin, ka jajirce kayi tsayin daka akan wannan al'amarin, sai yanzu da komai yazo gangara zaka cire hannunka akai, haba aymaan, you need to think twice" kallonshi Aymaan keyi tunda yafara maganar harya kai aya, saiya sauke Ajiyar zuciya "yanzu me kake tuhumana dashi? kana tuhumana ne akan rashin bayyanarshi ga iyayenshi ne ko me?" "ina tuhumarka ne akan qin taimakawa d'an uwanka musulmi saboda wani dalili naka na daban, Aymaan ka ta6a tambayar kanka meyasa warwarewar komai ke biyowa ta wajenka? kaine silar sanin asalin Deen, kaine silar warwarewar cunkussashen matsala dake cunkushe shekara da shekaru, ain't you proud of that? Aymaan nasan kana son Zainab kuma duk abubbuwannan dakakeyi kanayi ne don tsoron rasata, kana gudun kar bayyanar Deen tazama rugujewar mafarkinka nason mallakar zee saidai karka manta matar mutum kabarinsa, babu mai auren matar wani, Idan zee matarkace babu wanda ya isa ya aureta saikai haka zalika Idan ba matarka bace duk dubararka duk wayonka baxaka ta6a mallakarta ba" Dan murmushin takaici Aymaan yayi "wannan fatanka ne agareni ko?" girgiza kai Ahmad yayi yana Dan murmushi "meyasa zanmaka wannan fatan? Aymaan ni kaina zanfi kowa jindadi Idan ka mallaki Zainab, saidai mu musulmaine, munada imani kuma imanin mutum bazai ta6a cikaba sai ya yarda da qaddara walau mai kyau ko akasinta. Idan Zainab matarkace zaka aureta aymaan Idan Kuma ba ita bace ka roqi Allah ya musanya maka da mafi alhairi, Aymaan ba dukkan Abinda bawa keso yake zaman mashi alhairi ba, kullum Abinda akeso da bawa shine ya roqama kanshi Abinda yafi alhairi ta hakan kawai zai cigaba da ganin haske a rayuwarshi bayan haka ya kamata ka tausayawa Deen, Aymaan kata6a saka kanka a matsayinshi ko sau daya? mutuminnan na rayuwarshi ne acikin duhu, haryanzu lalube yake don shi kanshi besan koshi waye ba. ace kanada iyaye kanada dangi amma baka ta6a saninsu ba? ace kanada uwa amma baka ta6a sanin dadinta ba? ko dan wannan yaci ace ka tausayamashi ka taimaka mashi, bakasan dalilin dayasa kafi kowa shiga case dinnan ba, bakasan dalilin dayasa kodayaushe kaine sanadin warwarar wannan matsalar, bakasan inda zaka tsinci sakammakon wannan taimakon naka ba" qara matsawa jikin table din daya raba tsakaninsu Ahmad yayi ya kamo hannun Aymaan dake kallonshi tundazu da hannu bibbiyu yace "Aymaan I know this is a very hard decision for you amma ka kalli abin da idon basira, kayi tunani akai, ka kwatanta misalta kanka dashi sannan ka yanke abinda kake ganin yafi dacewa, kayi tunani Aymaan" *** kashe motar yayi sannan yacire seatbelt din dake jikinshi ya bude kofar motar yafito ahankali Dan lumshe oily eyes dinshi yayi yana dan qanqantar dasu sanadin rays din rana daya dallemashi fuska rufe kofar yayi sannan yadanna mata remote sannan yajuya yafara takawa cikin tafiyarshi mai cikeda nutsuwa mutanen dake harabar wajen keta gaisheshi inda matan kowacce ke gaisheshi cikeda kicihi da iyayi shidai iyakarshi slight murmushi kawai ahaka harya shiga cikin building din. Da manager dinshi suka cikaro shima yana shirin fitowa washe fuska Habeeb yayi yana qarasowa "Dan halaq kai nafito nema dama, kayi baqi" "baqi? suna ina?" inji Deen yana cigaba da tafiya "suna reception suna jira.. kuma da alamu manya ne sosai don kallo daya zakamasu kagane da alamu dai akwai babban kamu" ya qarashe cikin rad'a yana kashe mashi ido daya Dan harararshi Deen yayi bece komai ba sai cigaba da tafiyarshi dayake duk inda suka iske mutane sai an gaidasu musanmman Deen da suke bama wani extra girmamawa ahakan suka qarasa reception din inda baqin nashi ke zaune suna jiranshi su biyun idanu suka zubamashi kamar zasu hadiyeshi ko kyaftawa basason yi yayinda Deen ya qaraso gabansu da friendly face dinshi sallama yayi musu wanda saida sukaji saukarta.har qasan zuciyarsu cikeda sanabe suka amsa suna wani kwanainaya duk wai don su burgeshi "kune baqin namu?" ya tambaya still wearing the friendly face daya daga cikinsu datasha matsasun qanannun kaya ta.langwa6e kai tace "eh, tundazu muna nan muna jira duk mun gaji da zama" "ayyah,afuwan. ai yanzu jira yaqare.. shall we?" yafada yana nunamasu alamun su biyoshi cikin jindadin yadda yasake musu suka tashi yayi gaba suka bishi abaya har suka isa office dinshi office din dan madaidaici ne saidai it's very neat and tidy saida ya nunamasu wurin zama suka zauna sannan shima yawuce kujerarshi ya zauna yana facing dinsu, ana haka shima manager dinshi yashigo shima riqeda dan tray mai dauke da two table water da glass cups ya ajiye.gaban yanmatan shima fuskarshi awashe saiya koma gefen Deen ya tsaya "yeah, how may I help you miss(s)" inji Deen yana maida hankalinshi akansu fuska asake duk blushing sukayi suna jin kansu untop don samun kansu gaban wannan shahararren mutumin yana basu full attention ba qaramin fasa masu kai yake ba cikin karya murya wadda tayi magana dazu tace "ni sunana halimatu amma anacemin hally baby diya ga minister of finance wannan kuma qawatace jamcy diyar comissioner of education, dama ba komai ya kawomu ba illa munaso kayimana waqa ne na birthday kasancewar insha allah next week Friday qawata jamcy keyin birthday, zamuso kayimata waqa inso samune ka hallarta kayimana show" ta qarashe tana wani jujjuya idanu kada kai Deen yayi sannan ya maida kallonshi ga wadda takira jamcy din wadda itama ta tsuke cikin English wears anci makeup sai qyalli ake, Dan murmushi yayi mata yace "congratulations and happy birthday in advance" wani dadi yaqara qumesu hakan yasa tayi murmushi broadly itama cikin narke murya tace "thanks so much" "saidai am very sorry domin bazan samu damar yimuku aikin nan ba kasancewar ranar dakuke magana baninan inada aiki aranar a kebbi state, I sincerely apologize for this" yafada cikin nuna rashin jindadin yadda baxai samu yimasu aikin ba suma kallo daya zaka masu kasan murnarsu takoma ciki "kanada aiki ranar?" inji hally cikin rashin jindadi "yes, zanje wani daurin aurene nayimasu waqa a dinner, sunriga sunyi schedule din ranar tun watan daya gabata, am very sorry" yafada apologizingly "but.. yanzu babu yadda za'ayi kayi cancelling wancan schedule din? zan biya koma nawa ne" inji jamcy murmushi Deen yadanyi "am sorry miss, amma baxan iya cancelling schedule dinba, it's almost a month dasuka kama ranar sai yanzu kawai one week da bikin na chanza magana? kema kinsan hakan beyi daidai ba, hakan karya alqawarine and a promise is a debt, nasan ku kanku baxakuso nayi hakanba, your conscience will bother you too I know" shiru sukayi saidai kwata2 ba haka sukaso ba "to yanzu Mr balarabe ya kake ganin za'ayi? please karka cemin hakan bazai yiwuba, nariga nagama sanar da dukkan friends dina kai xakazo ranar, please do something" yadda take shagwa6ewa sai.kayi tunanin wata yar shekara uku ce sai wani mar mar take da idanu ga wani langwa6e wuya datake tana 6ata fuska kamar zatayi kuka Ajiyar zuciya Deen daduk ya qagara sutafi yayi yadan cije lower pink lip dinshi cikin naxari can yace "gaskiya nima banji dadiba, Am sorry for the dissapointment, gashi duk ranakunnan dazasu zo I'll be busy, da wuya asamu ranar da zan kasance free, saboda irin hakan yasa masu son aiki kezuwa dawuri sosai don kama rana da lokaci saboda irin wannan dissapointment din, amma... babu komai zanyi qoqari nayi squeezing time nasamu ko waqar ce kadai nayimuku kinga koda banzoba nidin dai nayi waqar" hakan yadan yimasu dadi "oh! we're very grateful, da babu gwara babu dadi, ko?" inji hally tana kallon jamcy kada kai jamcy tayi still fuska a kwa6e tace "hakane mungode, dukda naso kaidin kazo amma still duk lokacin dakake less busy kazo don kaima ka tayani murna, ga i.v din dakuma complimentary card dina, number na naciki, feel free to come anytime youre less busy" tafada tana doramashi cards din asaman table din murmushi yayi ya dauki cards din yace "oh.. thanks so much, insha allah xanzo duk.lokacin danake less busy, Habeeb.." Habeeb dake tsaye yana sauraronsu tundazu yadan sunkuyo yana cewa "yes sir" "take their names, Idan kuma akwai sunayen datakeso asaka a waqar kayi listing dinsu" "ok Sir" inji Habeeb yana dawowa kusada yanmatan don yin yadda yace cikin qanqanin lokaci suka gama komai suka kumayi ciniki sannan suka fara shirin Tafiya turamashi faskekiyar wayarta jamcy tayi agabanshi kallon wayar yayi saikuma yadago ya kalleta kashe mashi ido daya tayi cikin salo tace "your digits..please" tafada tana wani narke murya Dan murmushi yayi zaiyi magana tayi saurin katseshi da "pleeease" tana narke fuska dauke idanunshi yayi daga kanta yana ta6e baki cikin zuciyarshi don wannan ba karo na farko bane da mata ke mashi irin wannan shirmen ba babu musu yadauki wayar yashiga lodamata phone number dinshi daya saba ba ire irensu wanda ko sau daya baya picking call dinsu sannan ya turamata agabanta cikin jindadi ta dauki wayar tayi dialing number sai gashi daya daga cikin wayoyinshi tafara Ringing "save it, zamu dinga gaisawa" tafada cikin lullumshe idanu "alright, insha allah" yafada yana kada kai nan tazaro kudin aikin dasukayi ciniki ta dora a table suma, Habeeb ya dauka ya qilga yaga suncika sannan suka tashi suna bankwana inda sai ranar daren birthday din zasu dawo su amshi aikinsu. bankwana suka sakeyi kamar basuson tafiya sannan suka wuce Habeeb na take musu baya don rakasu waje Ajiyar zuciya Deen ya sauke bayan fitarsu sannan yakoma jikin kujera yadan kishingida guntun tsaki yaja, shifa shiyasa beson aikin mata, ya lura duk yawancinsu ba hankali ya ishesu ba, kullum burinsu su burgeshi shikau haryanzu yakasa ganin wacce ta burgeshi koda daidai da kwayar zarra ce, he found them so annoying and suffocating yana haka aka sake bude kofar office din dagowa yayi ya kalli kofar yaga ashe Habeeb ne sai washe baki yake bebi takanshi ba yajawo wata takarda yana dubawa "yayi mai farinjini! gaskiya aiki a matsayin manager dinka ba qaramin alhairi bane agareni, kai allah yaqara nisan kwana" Habeeb ya qarashe yana fifitama Deen yana dari biyar biyar miqaqqu dake hannunshi ta6e baki Deen yayi ya maida hankalinshi kan Abinda yakeyi don kobe tambaya ba yasan kudin menene hannunshi "ai dama ina ganinsu nasan fa yau kakata ta yanke saqa, da ganinsu kaga 'ya'yan manya, wannan mai kamada zabuwar tabani wai na shigar daita, wahallaliya" ya qarashe yana fashewa da dariya harda xama kan kujera qara ta6e baki Deen yayi don yasaba da hakan, hakan yasha faruwa, yanmata suyita tulama malohon kudi wai a sunan kamun kafa shi yarasa meke damun qwalwar wasu matan "gaskiya aikinnan akwai samu, bayan albashi ga allowances wajen yanmata, kai allah dai yaja zamani ai balarabe nidakai mutu karaba takalmin kaza, donma kacika kwafsawa? da kana bada hadin kai da nafi haka samu, narasa sadda zaka waye?" "zakaci ubanka ne Idan na koreka daga aikin kwata2, now get out" inji Deen yana hade cikkakun girarenshi yar dariya Habeeb yayi yace "haba oga, ai bama za'ayi haka ba. insha muna jone kodayaushe babu mai rabamu sokake nakoma wajen oga Audu mai sallamar #500 arana? ga aiki ga wahala amma anyi gudun tsiya kasamu #500 arana? nan kau hmmm abin ba'acewa komai dai" "aikau ka kusan komawa wajenshi tunda naga alamun ba nutsuwa zakayi ba" "haba balarabe, wace nutsuwa bayan wannan danayi? ai duk wanda yaganni yanzu yasan na nutsu, haba ai da da da yanzu ba daya ba wlh. Don ma kanamin black stomach, kwata2 baka bani hadin kai. ni narasa wane irin.mutum ne kai da kwata2 baka wayewa. ji yadda mata ke binka kana.gudunsu, a xamaninnan wlh mata inba mahaukatan kudi suka ganka dasu basu binka kaiko mata ba kudinka ba sukeso kai sukeso, wasu ma suna iya 6atar da ko nawane akanka amma kai ko ajikinka, mtcheew allah dai na ragewa aya zaginta, wlh danine kai? hmmm" ya qarashe yana.kada kai yana cije lower lip dinshi yar dariya Deen yayi yana cewa "Dan Air.. dakaine ni mezakayi" "hmmm ai fadi ma 6atawa, ace ni mata ke rubibi haka ai ina? zanyi zamanina yadda ya kamata inci duniyata da picking stick, ai ina ganin nima dai waqarnan zan koya nafara qila adace nima azo ana rubibi na, ca6! da kaga abu, tsala tsalan yanmata zan dinga sawa a vidiyoyina ba irin naka ba da babu wani armashi ko qayatarwa, saidai.kayima mutane tsaye gandadar kana waqa ko irin yanmatan nan da akesawa a vidiyo baka sawa kuma ahaka ake rubibin kallon vidiyon,mtcheew. Don qauyanci ko amshi bakaso mace tayi maka, kafiso kayima kanka komai, haba abin ko armashi babu, wlh koyaya kasanyo mace ciki abin saiya fi armashi amma kai baka ganewa babu inda kafi afki sai share yanmata, wai kaga mata tsala tsala suna binshi amma batasu yake ba kamar wani marar lafiya, gaskiya ya kamata ka binciki kanka wlh, kar ace bakada lafiya ne baka saniba ni duk duniya babu wacce na ta6a ganin ka kula ko kake kulawa sai ko *Lailah*, ita kadai naga kuna dan shiri daita, itama kuma nasan saboda babanta shiyasa kake kulata har kuka dan shaqu don nasan da babanta ba ubangidanka bane itama ba kulata ba zakayi...." barin sauraronshi Deen yayi ya cigaba da Abinda yakeyi don yasan halin Habeeb, Idan yafara zuba yadda kasan ru6a66iyar radio hakan yasa wani lokacin yake bude kwandon shara ya jefashi ya rufe ya cigaba da harkar gabanshi shi yanzu soyayya ma bata burgeshi, kai ba soyayya bama matan gabadaya basa burgeshi, so dayane yariga ya daukeshi dungurungum yaba wata, wacce duk duniya ita kadai ke iya burgeshi, saidai kash! tayimashi nisa, nisan da ko hangenta bazai iya yiba...✍? Ummin fasihu🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:43 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *074* *THE HARD DECISION 2* Horn biyu yayi sannan yaga alamun gate din yafara motsi alamun za'a bude komawa yayi ya jinginar da kanshi da kujerar ya lumshe gajiyyayun idanunshi yana jin lokacin da aka wangale gate din amma ko motsawa beyiba, can yaji ana kwankwasa glass din motar ahankali ya bude idanun nashi dasukayi ciki ya kalli mai kwankwasar sannan ahankali yasauke glass din motar cikin girmamawa da fara'a maigadin yafara yimashi sannu dazuwa Dan murmushi kawai yayi mashi yana daga mashi hannu, ganin hakan yasa maigadin yasan yau ba lau ganin ya sake tada motar yasa maigadin dan jada baya yabi motar da kallo harta shige cikin gidan sannan shima yashiga cikin zuciyarshi yanajin babu dadi ganinshi a wannan yanayin dabe saba ganinshi ba. Parking yayi a parking space sannan yakashe motar saidai maimakon yabude kofa yafita saiya maida kanshi ya dora akan sterring tareda sake lumshe idanunshi this is the toughest time of his life, komai ya jagule mashi, kanshi ya dauki chaji yarasa ma wane tunani ya kamata yayi, he was feeling very very exhausted, komai ya daina tafiya mashi daidai. ya dade sosai a wannan yanayin sannan can yasamu ya dago yasa hannu ya bude kofar cikin mutuwar jiki yafito. jawo briefcase dinshi da lapcoat dinshi yayi sannan ya rufe kofar hannu yasa yadan sassauta necktie din wuyanshi sannan yafara takawa ahankali cikin mutuwar jiki yanufi cikin gida. Jin alamun za'a bude kofar datayi yasata saurin waigawa daga kallon datake ta kalli kofar dama ba kallon take ba don idanunta kawai ke kan t.v din amma hankalinta kwata2 baya akai qurawa kofar idanu tayi har ta ida budewa mai shigowarya shigo wani Ajiyar zuciya da batasan dashiba tayi tana jin dan relief a zuciyarta cigaba da binshi da kallo tayi tana kallon yadda yake komai akasalance gani tayi ya maida kofar ya rufe sannan yajuyo yanufi hanyar wucewa sama yana qara sassauta daurin necktie din dake damunshi ganin kamar bema lura daita a falon ba yasata miqewa tsaye tana kallon yadda yake tafiyar tashi cikin jan kafa, kallo daya zakamashi kasan amatuqar gajiye yake kuma yana buqatar hutu saidai batajin tana iya kyaleshi don tundazu take nan xaune duk don taga dawowarshi tagaji da sharetan dayake, tagaji da nuna halin ko in kula dayake nuna mata, tanaso su shirya, tanaso su koma kamar da dukda dama can bawai tasake irin sosai dinnan dashi bane bare ace tayi missing company dinshi, kawai dai sotake tabashi hqr takuma tabatarda baya riqe daita arai ko babu komai hakan zai bata sallamar zuciya "Akhie?.." tafada daidai lokacin daxai fara taka stairs cak ya tsaya daga yunqurin hawan stairs din dayayi fara kamar wanda aka tsaida da remote ganin ya tsaya kuma be juyoba yasata fara takowa ahankali wajenshi tana jujjuya magangannu a zuciyarta tana son gano wacce kalma zayafi dacewa tayi amfani daita saita tazarar tsakaninsu yarage kadan sannan ta tsaya tana kallon bayanshi dake kallonta haryanzu Dan qaqalo murmushi tayi tana dan wasa da yatsunta nervously tace "Akhie kadawo? sannu da dawowa" "yauwa" taji ya amsa mata ataqaice sannan yafara taka stairs din zai wuce ganin hakan yasata saurin sake dakatar dashi da cewa "Akhie, inason muyi magana please" be dakata daga tafiyar dayake ba yace "later, yanzu am tired" "nasani, amma maganar bamai tsayi bace please ka saurareni" tasake fada itama tana haurowa saman ganin yafara yimata nisa, tasan Idan tabari yatafi ita dasake sashi a ido sai Allah yayi dakatawa yayi daga tafiyar amma bai jiyoba hakan yasa zee tasake matsowa kusa.tana cewa "please, koda 2mins ne" Ajiyar zuciya aymaan ya sauke ahankali sannan yajuyo ahankali ya fuskanceta ya zubamata Hazel idanunshi sauke idanunta tayi tana cigaba da fidgeting yatsunta tama rasa ta ina zata fara jin shirun zaiyi yawa yasa Aymaan cewa "2mins dinfa na Tafiya" dago large eyes dinta tayi ta kalleshi idanun na kyallin ruwan hawayen dasuka fara taruwa aciki kallonshi tayi taga shima kallonta yake babu ko kyaftawa ahankali tasake sauke idanun sannan cikin sanyayar murya tace "kayi haquri.." "Don Allah.." tasake fada tana dagowa tana sake kallonshi shima kallonta yake bece komai ba kuma bayada alamun cewa komai din hakan yasa tasake sauke idanunta qasa hawayen dake maqale a idanun suka digo qasa "Am so sorry... I... nasan komai zanfada maka bazan ta6a iya wanke kaina agurinka ba, am sorry, kayi hqr kadaina fushi dani... am so sorry" ta qarashe muryarta na breaking saboda kukan dake shirin kufcemata saurin rufe fuskarta tayi da taffukan hannayenta tana kukan marar sauti Lumshe idanu Aymaan yayi ya bude cikin wani yanayi yana jin ranshi na qara dagulewa kallonta a wannan yanayin ba qaramin sake burkita mashi lissafi yayi ba yayinda yakejin sheshekarta har cikin zuciyarshi "shhhh... wayace ina fushi dake? ni ba fushi nake dake ba Zainab" yafada cikin tattausar murya dagowa fuskarta datayi.sha6e2 da hawaye tayi daga cikin taffukanta ta kalleshi tace "ba wani, ni nasan fushi kake dani, babu ruwanka dani, you no longer speak to me, ko kallona bakayi, Idan nazo wuri saika tashi, Idan nayimaka magana baka amasawa, you're totally ignoring me" tafada cikin shesheka murmushi ya kufcemashi ganin yadda take magana cikin shesheka kamar wata qaramar yarinya, ahankali yashafa saisayayar sumarshi sannan yace "ayyah, am sorry. ni ba ignoring dinki nake ba kawai am busy ne a kwanakinnan amma am sorry Idan hakan ya 6atamiki rai" dago wet eyes dinta tayi ta kalleshi tanajin wani sanyi sanyi a zuciyarta, girgiza kai tayi tace "ni zance maka sorry, nice nayimaka laifi amma wlh ba yadda kayi tunani bane, ni bansani ba, bansan shine ba.. bama shiri ma kwata2 dashi, shine keta zuwa school din yana tarana.. and kodayaushe saimunyi fada dashi.. ranar ma bansan yadda akayi yazo wajen ba, Kawai saidai naga..." "shhhh..." Aymaan ya dakatar daita daga bayanin datake son yimashi murmushi yayi yana kallon cute fuskarta, Dan matsowa yayi kusada ita yana kallon fuskarta still fuskarshi dauke da murmushi yace "I know Zainab, no need to explain. Actually ni banji haushinki ba saboda nasan koke wacece, I know yayi hakan ne don inji haushi.. kuma naji. shiyasa nayi taking out haushin akanshi, so kibar damun kanki unnecessary kinji? nasan babu komai atsakaninku, koda akwai banida hurumin dakatar dake ko hanaki, don haka kibar damuwa kinji" kada kai tayi tanajin kamar anyi lifting dutsi mai nauyi daga kan qirjinta "kanada hurumi akan haka Akhie, kanada hurumi akan komai saboda kai yayana ne, kafini sanin what's best for me, kafini sanin Abinda zai cutar dani kuma ka isa kasani abu nayi ka hanani kuma na hanu" murmushi sosai Aymaan yayi yana jin sanyi na ratsa cunkussashiyar zuciyarshi sanadin kalamanta "hakane, nagode qanwata. sorry for making you cry, now wipe those.tears kar wancan.uwar gulmar tafito taganki haka taga wallenki" murmushi ya kufcemata ta sauke kanta tana goge fuskarta da bayan hannu akunyace tanajin dadin yadda yayi maganar yanzu cikin barkwanci kamar yadda yasaba, kobabu komai hakan sign ne na ya daina fushi daita "good, yanzu Bari natafi, your 2mins yazama almost 10mins, Bari natafi karna fadi don nafara ganin double double" sake murmushi tayi kawai batace komai ba hakan yasa yajuya kawai yashiga qarasa.haurawa saman binshi da kallo tayi harya ida haurawa saman sannan ta danyi ihun murna qasa qasa sannan tajuyo tasauko daga stairs din takoma falon tanajin wani irin dadi a zuciyarta, atleast tasan sun shirya dashi kuma zaibar riqeta a zuciya, hakan yasa taji zuciyarta tayi wasai tanajin wani dadi a zuciyarta. **** Dagowa tayi daga kallon wayar hannunta datake ta juyo ta kalli Lailah dake kwance rigingine dan qaramin pillow rungume a qirjinta idanunta a lumshe "kai gaskiya bestie, dole ma ki rikice akan wannan gayen, ya hadu over, soo masha allah" injita murmushi kawai Lailah tayi batareda ta bude idanun ba gyara zama budurwar tayi tace "gaskiya zakuyi making perfect match Idan har kuka jone, just look at him so handsome and geogous" "hey! watch out, banfa cika son ana yabamin taurarona ba, karki ja labari ya chanza yazunnan" inji Lailah tana dan hade face dariya budurwar tafashe dashi sannan cikin sigar tsokana tace "iyee? su kishi manya. yo labarin ya chanza mana. ke nifa inajin nakusa chanzawa daga supporter zuwa rival, muddin na cigaba da kallon wannan fuskar tsab zaki hangoni cikin yan takararki" tashi Lailah tayi kamar wadda aka mitsina ta kwace wayar hannun budurwar tana cewa "to narabaki dasake kallonshi Idan kuma kika qara ko bayan idanuna ne ban yafeba" dariya tasakeyi tana riqe ha6a "Idan baki yafeba sai akace mai zai sameni?" "tsab zaki watse don tsab zan dagamiki nono bari ganin ina washe miki 36" inji Lailah tana komawa tasake kwanciya dariya sosai budurwar tasake yi sannan tace "sannu uwata, aikau dole na kiyaye inba sonake na watse ba, kika dagamin nono aina kade" "har ganyenki kau" Lailah dake danne dannenta a wayar tabata amsa tasowa budurwar tayi daga kan stool din datake tadawo saman gadon itama kusada Lailah ta zauna "Babe gaskiya mutumin nan yayi akowane siga, ina baki qwarin gwiwar kicigaba da jajircewa wajen winning heart dinshi, wlh Idan kika mallaki balarabe kin more" sauke wayar datake dannawa tayi ta kalleta sannan ta tashi zaune itama tana facing yarinyar "Meenah, Abinda kike fada is easy wajen fada amma da matuqar wuya wajen aikatawa. tun lokacin dana fara dora idanuna akan balarabe yagama da zuciyata, tun ranar daya fara zuwa gidannan nakamu da mahaukacin soyayyarshi. ada inajin ana love at first sight, this and that duk bana daukar hakan serious saida hakan yafaru akaina, Meenah I love this guy, fiyeda tunaninki, fiyeda tunanina ma" "then fight for your love Lailah, kinada komai, komai da kowacce mace zatayi taqama dashi. kinada kyau Lailah, Idan kinso kina iya contesting gasar kyau kuma ki cinye saboda allah yayimiki baiwar kyau both facial da na diri, gaki diyar maishi babu Abinda kika nema kikarasa ga ilimi both Islamic and western ga wayewa, kin mallaki komai Lailah don haka wannan ma zaki mallakeshi insha allah" Dan murmushi Lailah tayi tadan kada kai "hakane, amma kinsan ita soyayya babu ruwanta da Abinda da Abinda ka mallaka, sai kiga ke mai taqamar kin mallaki komai kinanan zaune wata dako kamo kafarki batayi ba tazo tayimiki zarra, misali ni yanzu.. na mallaki komai amma nakasa mallakar zuciyarshi, yayinda nikuma tawa zuciyar ke begenshi shi tashi wata take bege" "Lailah, kar wannan ya sanyayar miki gwiwa, wancan ex dinshi ce, kinsan meye ex? short time din EXPIRE kenan" Dan murmushi Lailah tayi tace "expire.. amma ba agunshi ba, nidake munsan yadda haryanzu zuciyarshi ke bugawa daita acikinta, Meenah haryanzu balarabe yana sonta.. har gobe. And.. wannan shiyafi komai yimin ciwo. kinsan zafin ka dinga kallon wanda kake bege yana begen wani? kinsan zafin kafada soyayyar wanda kakeda tabbacin bakama gabanshi sam?" "Lailah kibar cewa bakya gabanshi, ke kanki kinsan kina gaban balarabe, ko babu komai yana treating dinki with respect yana kuma kulaki" komawa Lailah tayi ta jingina da frame din gado tana dan murmushi mai ciwo tace "yana treating dina da respect? dama waye balarabe baya treating da respect? kema kinsan wulaqanci ba halinsa bane ba, haka yakewa kowa" "ba kowa ba, kema kinsan baya kula mata dik yadda zasu shigemashi, he always try to avoid them in a polite way though" "wayasani ko nima yana qoqarin avoiding dinane? wayasani ko yana kulani ne don dole? ni nasan nike cusa kaina agareshi, be damu daniba" "Lailah..." "kinga Meenah nagane, nagane bakyason gwiyaguna su sare ne shiyasa kike encouraging dina haka, amma a fidda sonkai Meenah kema kinsan nikeson balarabe not the other way round. Da farko nazaci abin zaizomin da matuqar sauqi, ganin simpliness dinshi da yadda yakeda sauqin sha'ani can kuma ganin nafara gaining attention dinshi saina fara jindadi ina tunanin shima ya fara sona ne duba da yadda yake treating dina yana kuma kulani, ashe nice ban fahimci abin ba, ashe yana treating dinane yadda yake treating kowa, Idan ma akwai banbanci Dan kadan ne kuma shima saboda alaqar dake tsakaninshi da abbana ne. kwatsam nagano ashe duk Abinda nake tunani duk imagination dinane, banice gabanshi ba, yanada wadda yakeso, wacce tariga ta mamaye mashi zuciya. ada Idan ina sauraron waqarshi sai naita ganin qila duk kalamanshi dayakeyi ni yakemawa ashe ba haka bane, ashe yana expressing kanshi ne ga wata, wata can" ta qarashe tana girgiza kai ahankali tana iya qoqari wajen controlling emotion dinta tarasa dalilin dayasa duk lokacin data tuna da akwai wata wadda wanda take so ke haukar sonta takejin zafi, zafi marar misaltuwa a.zuciyarta" dafata Meenah tayi a kafada tace "kar hakan ya sanyayar miki gwiwa Lailah, bakisan dalilin dayasa Allah yarabashi da wancan din ba, bakisan dalilin da Allah ya hadaku ba, wataqila dama they didn't deserve each other, wataqila dama kece perfect match dinshi, maybe he's the ONE and you're also the ONE. wataqila qaddara ce ta rabasu da wancan don ke ta hadaku" Ajiyar zuciya Lailah ta sauke ahankali tace "I hope so, Meenah Idan narasa balarabe..." "bazaki rasashi ba insha Allah, kisamu wannan yaqinin kikuma dage da addu'a dakuma qoqarin mantar dashi wancan ki kafa taki rumfar a zuciyarshi" "it's not easy..." "it is insha Allah, it will be.,kawai kidage da du'a, I'll help too" kallonta Lailah tayi tadanyi murmushi "thanks Meenah, thanks for always been there for me" murmushi itama Meenah tayi tana dan bige kafadarta tace "shut up, what are amminai for? insha Allah saimun 6arar da gwamnatinta, sai munkoma mune da mulkin!" dariya Lailah tayi ganin yanayin datayi maganar tana jin wani qwarin gwiwa itama a qasan zuciyarta. *** kwance yake kan neatly spread gadonshi, yayi matashin kai da pillow yana kallon sama, sanye yake da singlet sai short nicker, dakin yayi shiru babu Abinda kake ji sai qarar a.c da aka qure adakin. *_bakasan dalilin dayasa kafi kowa shiga case dinnanba_* *_bakasan dalilin dayasa kodayaushe kaine sanadin warwarar wannan matsalar ba_* *_bakasan inda zaka tsinci sakammakon wannan taimakon naka ba_* lumshe idanunshi Aymaan yayi yana dafe goshinshi da hannu daya *_kaine silar sanin asalin Deen, kaine silar warwarewar cunkussashen matsalar dake cunkushe shekara da shekaru, aint you proud of that?_* *_I know this is a very hard decision for you Aymaan amma ka kwatanta misalta kanka dashi sannan ka yanke abinda kake ganin yafi dacewa_* bude idanun yayi ahankali ya zubama p.o.p din dakin ya qureshi da kallo kallo daya zakamashi kagane yana cikin tsantsar damuwa, yarasa tunanin dazaiyi yarasa me zai yanke. ga qoshi ga kwanan yunwa. bayyanar Deen zai samo abin farinciki ga kowa amma baya tunanin harda shi. yayinda bayyanarshi xaizama hanyar warwarewar matsalolin wasu shi zai zama silar toshewar nashi. what should he do? what decision should he make? ya zaiyi? Ummin fasihu🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:43 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *075* Tunda zee da Aymaan suka shirya zee hankalinta yasake kwantawa don sosai shariyarshi ya hanata nutsuwa don tana matuqar girmamashi kuma yanada qima sosai a idanunta, baxataso abinda zai lallata kyakyawar alaqar dake tsakaninsu ba. tuni ta cigaba da harkokin gabanta lafiya lau takuma dauki tunanin duk abubbuwan dasuka faru ta watsar gefe ta cigaba da harkokinta. kasancewa exam is at the corner yasa ta maida hankalinta sosai a karatunta dukda dai bawai exam din ya matso kusa sosai dinnan bane. yanzu tafi zama library a duk lokacin da batada lecture kasancewa batool ba gwanar zaman library bace yasa kusan kodayaushe ita kadai ke tafiyarta library din tayi karatu sai Idan zasu gida ko Idan zasu shiga cafteria suke haduwa. Yau ma kamar kullum tana zaune a kusurwar library din inda nan ta maida mazauninta duk lokacin da tazo library din littatafai ne gabanta sai pen a hannunta tana rubuce rubuce sosai hankalinta yatafi akan abinda takeyi har ya kasance batasan abinda ke wakana ba a kewayenta. tadade tana jin wani qamshi qamshi wanda kamar ta saba jinshi saidai bata maida hankali akai ba don sosai kanta ya dauki zafi da abinda take ko qwaqwaran motsi batason yi. ahankali wani siririn zufa ya gangaro daga gefen kanta ya silalo gefen fuskarta Ajiyar zuciya ta sauke ahankali tana dan dakatawa da rubutun datake ajiye pen din hannunta tayi da niyyar dauko hanki a jakka don share zufar saidai kafin tayi hakan taga an miqomata wani hanki fari qall babu musu ta amsa tafara tsane gumin dashi can kamar wadda aka tsayar da remote ta qame qamm kasa cigaba da tsane gumin tayi haka kuma takasa dagowa bugun zuciyarta ne yafara qaruwa yayinda kwakwalwarta tafara lissafa mata Abinda ke faruwa ta dan dade a wannan position din kamar wanda aka dasa kafin can tafara dago idanunta cikin qarfin hali bisa kyakyawar fuskarshi ta sauke idanunta wanda hakan yayi daidai da faduwar gabanta ahankali tadan jabaya tana kallonshi a bit shocked and surprised a bangarenshi kau zaune yake kan kujerar dake facing dinta yayi balancing yayi crossing kaffafunshi as usual idanunshi toshe suke cikin black shade fuskarnan atamke hankalinshi na kan wayar hannunshi dayake daddanawa hankali kwance ahankali zee ta hadiye yawu still zuciyarta na racing rabonta dashi tun ranar dasukayi fada da aymaan a canteen, sai gani tayi kamar an sauyashi ne don yaqara mata wani qwarjini bisa wanda yakedashi tunawa tayi da qarshen haduwarsu ta waya hakan Kuma yaqara mata gudun bugun zuciyarta, tasan yauma baxasu wanye lafiya ba qoqarin daidaita yanayin fuskarta tayi tana cin serious itama sannan ta jefa hankin hannunta a dan waste basket din dake gefen kujerarta. daukar pen din data ajiye tayi ta maida hankalinta akan littatafan gabanta tana qoqarin ida daidaita nutsuwarta cigaba da pretending din yin aikin gabanta tayi saidai samm bawani gane abinda takeyi take ba hankalinta duk yana kanshi tana jiran jin mezai biyo baya ahankali tadan wurga idanunta a fakaice tana duba library din sai taga almost kowa yafita saura mutum daya kawai dake daga farko farkon library din sake maida idanunta tayi kan littatafan gabanta tana saqe saqen abinda ya kamata tayi, ta tashi ne? kota bari taga ikon Allah? batason tabashi slight chance din dazai gane tana tsoronshi don hakan bazai taimaka ba kwata2 saima damar dazai bashi na cigaba da takura mata saidai dukda hakan tana fargaba don ta lura samm mutumin nan bayada mutunci ko digo, ita abinda yafi daure mata kai ma shine dalilin dayasa yake bibiyarta, meyasa bazai sakarmata mara ba hakanan? a lokacin,da ita ke bibiyarshi shike bayaso amma yanzu data fita harkarshi shi yanzu ya bude nashi shafin na takuramata. me ya kamata tayi don getting rid of him daga rayuwarta? meya kamata tayi? koko takai qararshi wajen school authority? tunawa tayi da kallamanshi na rannan dayace ko shugaban school din be isa ya hanashi ba, shin hakan gaskiya ne? koko kawai cika bakine kawai? motsin dataji daga gaban library din ya katsemata guntun tunaninta kallon wajen tayi taga wannan saurayin dayayi saura ne ke shirin fita daga library din Dan bude idanunta tayi tana kallonshi harya ida ficewarshi daga library din ahankali ta sauke idanunta ta maida kan littafin gabanta zuciyarta fall saqe saqe, ahankali tasake dagowa tadan saci kallonshi qasa qasa sai taga haryanzu hankalinshi nakan wayar hannunshi shawara tafara yi da zuciyarta kan meya kamata tayi ita kadai dashi a wannan quiet wurin beyi making sense ba, Idan yayimata wani abin fa? wait.. Idan wani yashigo ya taddasu haka fa? Idan batool tashigo fa? Idan akasake coincidence tashigo tareda Aymaan fa? gabanta taji yafadi sanaddiyar wannan tunanin dayaxo mata. no, bazata sake bari irin abinda yafaru abaya yasake faruwa ba, no way! dagowa tayi sai gani tayi wannan karon wayarce kare a kunnenshi yana magana qasa qasa cikin larabci cikin gadara kamar wanda akaiwa dole. ganin hakan yasata yanke shawarar yin amfani da wannan damar wajen fecewa rurrufe littatafan tashigayi da sauri ta cuccusasu a jakka sannan ta miqe tana gyara nadin veil dinta rataye jakkar tayi tazo ta giftashi zata wuce cakk ta tsaya lokacin dataji an cafki tsintsiyar hannunta wara manyan idanunta tayi saboda yadda abin yazo mata so sudden saurin Juyowa tayi tana fizge hannun nata da qarfi tana kallonshi da manyan idanunta dake ware haryanzu ko motsawa beyiba bare ya juyo yadda kasan bashi ya riqo hannun nata ba sai cigaba ma dayayi da wayarshi hankali kwance motsi bakinta yafarayi kamar zatayi magana saidai tama rasa abinda zatace hakan yasata qara juyawa da sauri zata wuce qara kamo tsintsiyar hannunta taji anyi, sake Juyowa tayi ta kalleshi in shock sai gani tayi wannan karon shima ita yake kallo cikkakiyar trimmed girarshi daya ya dagamata ahankali in a naughty way kafin tayi wani tunanin taji an fizgota da qarfi and the next thing data gani shine fuskarshi daff da tata wanda tazarar dake tsakanin tsinin hancinta da nashi befi 1 inch ba 💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖 qara kallon kanta tayi a mirror din a karo na babu adadi, sotake taga inda beyiba cikin kwalliyarta ta gyara. ita kanta tasan qarshen kyau tayishi saidai tarasa meyasa takejin kamar haryanzu beyiba, tundazu take gaban mirror din tana kwalliyar amma haryanzu takasa gamsuwa da ita. ahankali ta buga tagumi tana kallon kanta cikin mirror din tarasa yaushe tazama haka, wai yau ita ke tsaye gaban mirror for almost an hour don kawai ta burge wani, just to impress wanda batajin zaima tsaya kallonta bare ya tantance irin kwalliyar tata she can't believe itace wannan dai classic Lailah din wadda maza basa gabanta, wadda ta dauki soyayya shirme har take kallon duk wanda yazo wajenta dasunan soyayyar mashirmanci, yanzu itace tsundum tayi nitso cikin kogin soyayyar, soyayyar ma mai wahalar wa. Tunawa tayi da ranar data fara ganinshi wanda baxata ta6a mantawa ba don ranar na maqale a qwalwarta tana iya tunawa very vividly tunawa tayi da lokacin data fara ganinshi a kofar main entrance dinsu lokacin tadawo daga school tunawa tayi da yadda taganshi jingine da daya daga pillar wajen yana dan daddana qaramar wayarshi tunawa tayi da yadda ya dago oily idanunshi ya saukesu cikin nata wanda tundaga eye contact dinnan komai nata ya chanza, rayuwarta ta sauya ta chanza daga Lailahrta tada takoma wata sabuwar Lailah din daga kallo daya komai nata ya chanza, labarin rayuwarta ya sauya takoma wannan lailahr, Lailah datasha banban da wancan. shigowar wata qaramar yarinya tana tsallen murna ya katseta daga guntun tunaninta tajuyo tana kallonta qarasowa yarinyar tayi wajenta cikin tsallen murna tana kalkadama Lailah ledojin chocolates din hannunta ko bata tambaya ba tasan inda ta samosu amma still tace "tofa? kekuma daga ina haka? who gave you chocolates?" cikin washe baki yarinyar tace "uncle mana kuma harda Icecream ma babba mami tace naba Jamila tasamin a fridge" Dan wara idanu Lailah tayi tace "wow! yanzu ina uncle din?" "yana falo tareda mami, mami tace kizo ku gaisa" tafada tana qoqarin bude daya daga cikin pack din chocolates din shiru Lailah tayi tana sauraron yadda bugun zuciyarta ya chanza, dukda dama tasan da zuwanshi kuma tundaxu shi take jira don tun jiya dataji abbanta na waya dashi akan yau zaizo takasa nutsuwa tanata jin kamar tajawo lokacin amma gashi yanzu yazo din amma kuma tanajin kamar bazata iya zuwa dinba dukda yadda zuciyarta ke kwadayin ganinshi din. Ajiyar zuciya ta sauke tasake kallon kanta a mirror din, sanin cewa Idan ta cigaba da lagudar fuskar tana iya 6ata kwalliyar ma takoma wani abin daban hakan yasa ta miqe tsaye tana gyara rolling din veil dinta ta dauki turare taqara dan fesawa sannan ta kwashi wayoyinta tanufi hanyar fita tana qoqarin ganin ta saita bugun zuciyarta *** qara wara manyan idanunta tayi in outmost shock zuciyarta na mugun bugu kusanci sosai ke tsakaninsu don hannayenta data dafa qirjinshi dasu ya hana jikinsu hadewa waje daya huramata iskar bakinshi mai qamshin mint yayi yana qara daga mata gira daya "da ina zaki?" yafada cikin muryar rad'a qoqarin tashi tafarayi tanajin yadda inner jikinta ke rawa hanata tashin yayi ta hanyar zagaya hannunshi ta bayanta ya ruqota wanda hakan ba qaramin jan lantarkin jikinta yayi ba agigice zee tace "innalillahi, wh..what are you doing" tafada tana qoqarin tashi again "am showing you how crazy I am, you called me psycho, don't you?" yafada still cikin rad'a yana kusanto fuskarshi ga tata jabaya tayi tana qara tareshi da taffukan hannayenta dake kan qirjinshi "m..mussadiq stop, wai meye haka? a..are you in your right sense?" tafada cikin rawar murya zuciyarta kamar zata faso qirjinta tafito "no.. ni zarrare ne, koba haka kikace ba?" "Mussadiq.." "kince number Dr ya kamata na nema don mu gana shine nazo kibani" "Mussadiq zanmaka ihu, I swear" tafada muryarta na rawa, sosai tsoro ya bayyana a fuskarta wani guntun murmushi ya su6ucemashi sannan yaqara matso da fuskarshi dab da tata "hakan ma zaifi qayyatarwa, azo aganmu ahaka" yafada still cikin rad'a qamshin bakinshi sai shigarmata hanci yake saboda kusancinsu hankalin zee ne yaqara tashi, iya rudewa ta rude, ga yadda tunanin wani yazo yagansu ahakan yaqara hautsinamata yan ciki dama haka Mussadiq yake, she know he's crazy amma batasan Abin nashi yakai har hakaba "Mussadiq let me go.. this is wrong, you know it" tafada cikin muryarta data kasa daidaitawa tunda take bata ta6a samun irin wannan kusancin da namiji ba dukda ba bisashi tafado ba saidai suna daff sosai don taffukan hannunta data tare qirjinshi dasu ya hanata ida fadawa kanshi wanda shine kadai contact din jikinta da nashi sai kuma hannunshi dayasa ya tareta abaya don hanata tashi ganin beda niyyar yin yadda tace din yasata dan rintse idanunta ta bude sannan cikin ahankali tace "please.." nanma shiru yayi sai kallo daya kafe fuskarta dashi "you're not my muhharam Mussadiq, this is totally wrong, please let me go" tasake fada tanajin kamar ta fizge kanta saidai tasan any slight struggle zaisa taqare ajikinshi abinda Kuma bataso kenan "sai kin maimaita Abinda kika fada ranar" "Mussadiq.." "nine zarrare ko?" saurin girgiza kai tayi "ni kika katsewa kira?" "no, I.." "maimaita Abinda kika fada aqarshe, mema kikace?" "m..mussadiq wannan duk ya wuce.. I... kabarni natashi tukkuna please" "yadda zaki gudu ko? answer me, ni kika katsewa kira? kinsan hakan meyake nufi agareni?" tunda yafara magana take girgiza kai, ita kadai tasan yadda takeji qara matso da fuskarshi daff tata yayi yana cewa "speak, are you a lizard?" qara girgiza kai tayi tana maida kanta baya "m..mussadiq..." "yes?" "stop moving closer.. please" "why?" yasake fada still moving closer "al..alright, am.. am sorry" tafadi kalmar datasan ita kadai zata ceceta ganin still bebar matso fuskar ba yasata sake cewa "am sorry, ba gashi nafadi ba? please stop" "you're sorry for what?" yafada still moving closer "sorry for hanging up your call" "and?" "and.. and for calling you a psycho" tafada tana qara jabaya "and?" "and.. and for... for daring you" "and?" Dan squeezing fuskarta tayi cikin rashin fahimta "I.. I think that's all" "really? you thought so?" yafada yana daga gira daya "am sorry for everything then, please let me go, this is totally wrong" tafada kamar zatayi kuka shiru yayi yana sake kafeta da idanunshi dake lullu6e cikin glass din idonshi itama sai samun kanta tayi da kafeshi da idanu kamar yau tafara ganinshi sun dan jima ahakan idanunsu kafe da juna motsa baki Mussadiq yayi zaiyi magana saidai kafin yayi zee ta rigasa "Deen.." tafada ahankali cikin murya mai kama da rad'a kallonta ya cigaba dayi bece komai ba hawaye yaga sun taru a idanunta data kafeshi dasu babu kyaftawa ahankali suka zubo suka gangaro kumatunta mammaki ne ya kamashi ganin hawayen nata sunqi tsayawa sai gangarowa suke daga cikin idanunta dasuka fara chanza launi hakan yasa ahankali ya janye hannunshi daya tareta dashi abaya saidai bata motsaba bare ta tashi din tana nan a yadda take still wet idanunta kafe dashi jiyayi duk badadi don saiyayi tunanin shine silar hawayen nata "are you ok?" yafada yana kai hannunshi fuskarta ya sharce hawayen kumatun damarta da yatsa firgigit tayi lokacin da taji contact din yatsar a fuskarta sai kuma tayi saurin kallonshi kamar wadda ta farka daga barci sai kuma tayi saurin tashi tsaye shima tashin yayi yana kallon yadda take share hawayen fuskarta da bayan hannunta saurin duqawa tayi ta dauki jakkarta data fadi tun lokacin daya fizgota ta rataya idanunta aqasa "Z... Ummie" ya kirata yana kallonta bata kalleshi ba tazo zata wuce still kanta aqasa shan gabanta yayi, ganin hakan yasa ta chanza hanya nan ma ya tare yana kallonta yanason suhada ido amma taqi dago fuskarta "Ummie..." "get out of my way please" ta katseshi cikin muryarta dake rawa sosai "but why..." kasa qarasawa yayi saboda dagowa datayi ta kalleshi da idanunta dasuka qarasa rinewa daidai kuma lokacin wani hawayen ya digo cigaba da kallonshi tayi da idanun nata batareda ta iya fadin abinda takeson fadi ba jikin Mussadiq ne yayi sanyi, tabbas ya hango wani abu cikin idanunta mai wuyar fassaruwa kuma kallo daya yaimata yagane she's emotionally hurted ahankali ya kauce mata daga hanya still yana kallonta bata jira komai ba tawuce dasauri tanufi kofa juyawa yayi yana binta da kallo yana cire shade din idanunshi a lokaci guda harta fice daga library din. dasauri tafito daga library din ta juya tabi wata hanya cikin gudu gudu sauri sauri bata tsaya ba saida takai wani quiet wuri inda babu mutane dagudu ta qarasa gindin wata bishiya ta durqushe wajen kukan datake riqewa tundaxu ya kufcemata ta toshe bakinta da taffukan hannayenta tacigaba dayi da dukkanin zuciyarta ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ tun daga nesa data hangoshi zuciyarta tasake sauya bugu ahankali shauqi yafara mamaye zuciyarta harya tsuma dukkanin jikinta ahankali ta cigaba da saukowa daga stairs din idanunta akanshi zaune yake kan daya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun falon sanye yake cikin wata dakkakiyar dark brown shadda wadda tafiddo farar fatarsh sosai kanshi na sanye da hula zanna bukar wadda ta shiga da shaddar hannunshi sanye da tsaddadiyar agogon fata brown kaffafunshi kuma sanye suke da baqaqen socks. zaune yake a kujerar dake facing kujerar mami fuskarshi dauke da qayyataccen murmushinnan nashi mai bayyana beauty point dinshi agabanshi akwai Dan qaramin table na glass dake cikeda drinks da kayan ciye ciye wanda da alama ko ta6asu beyiba. shagala tayi da kallonshi harta qaraso falon batasaniba saida muryar mami ta katseta daga lulawar datayi duniyar kallonshi "kinga baqon August ko?" inji mami tana nuna Deen dake murmushi murmushi Lailah tayi tace "lallai kam mami, nima yanzu Afrah taje take gayamin, maraba da baqin August" dagowa Deen yayi ya kalleta yadan hade girarenshi sai kuma ya sauke kanshi qasa murmushi still a fuskarshi "shiyasa garin yau ya lumshe kamar za'ayi ruwa ashe dai da dalili" inji mami cikin tsokana "aikaudai mami, but are you sure nan yazo direct? tayiwu fa 6atan hanya yayi don ni ban yarda wannan ziyarar tamuce ba" inji Lailah data zauna kujerar kusada ta mami qara dagowa Deen da duk kunya ta hanashi saqat yayi ya kalli Lailah again da expression din 'ke ko?' a fuskarshi, itakuma tayi murmushi tana dan juya idanunta "lallai kau, babu mammaki. to Mallam balarabe anya ziyarar nan tamuce koko dai gaskiya Lailah ke fada?" hannu yakai yana dan shafa sumar kanshi cikin jin kunya yace "mami Lailah kawai sotake ta hadamu" "babu ruwana mami, ki tambayeshi yaushe rabonshi da gidannan" inji Lailah "ina ruwanki to? ai nasan ayyukane sukayi mashi yawa shiyasa amma ai kowa yasan son mai son zumunci ne" inji mami cikin kare Deen kallon juna Lailah da Deen sukayi Deen yayi wani murmushin gefen baki Dan 6ata fuska Lailah tayi tace "kai mami shine zaki bani gula?" dariya mami tayi "ai gani nayi kina neman yima dana sharri ne" "d'an da bama wani jidake yake ba?" inji Lailah yana kumburi "babu komai, ai tsakanin uwa da d'a sai Allah, babu mai shiga tsakaninmu" qara kumbura fuska Lailah tayi tana kauda kai tace "aike dama bakyason laifinshi" yar dariya mami tayi tace "ai baya laifi" saikuma ta fuskanceshi "ya aiki? komai lfy ko?" Deen da murmushi yaqi barin fuskarshi yace "Alhamdullilah mami, komai na tafiya daidai" "masha Allah, Allah ya taimaka ya cigaba da budawa" "Amin ya Allah mami" ya amsa cikin girmamawa "ya wajensu Kaka? kwana biyu haduwa tayi wuya" "suna lfy, tacema a gaidaku" "muna amsawa, insha allah zan shigo wajenta ma kwanannan" "to allah ya amince mami" duk hirar dasuke idanun Lailah na kanshi tana cikeda burgewa tana jin kamar ta hadiyeshi don so miqewa mami tayi tana cewa "ina zuwa bari nadubo wancan sarkin 6anar, yanzu haka tanacan tanayi dama Idan kaji shiru babu wulginta to gwara ka bincika" murmushi kawai Deen yayi "ayimin magana Idan katashi tafiya" "to insha Allah, a sauko lfy" ahaka mami tatafi tabarsu su biyu a falon sadda kai Lailah tayi tafara wasa da yatsunta nervously dama Idan suna wuri daya su biyu kadai haka takeji, duk saitaji ta takura jin shiru yasa tadan dago ta saci kallonshi sai taga hankalinshi ma nakan wayar hannunshi sauke idanun tayi tanadan murmushi sannan taqara dagowa tace "bakasha komai ba yaya" dagowa yayi daga kan wayar ya kalleta sai kuma ya kalli kayan gabanshi yace "hmmm nasha ruwa ai, wannan tullin kayan ina zani dasu? am full" tasan gaskiya yake fada don Deen baya yima abinci kawaici Idan yanaso ci yake "ok, ya aikin? hope yanzu ayyuka sundan lafa" tafada cikin son janshi da fira don tasan Idan tayi shiru saidai suyi zaman kurame don ta,lura kamar he's not good at fira, shirunshi yafi surutunshi "Alhamdullilah, da sauqi gaskiya sosai. pressure din yarage" "to Allah ya taimaka, more more grace to your elbow" murmushi yayi yace "Amin Amin, kefa? ya school?" "school Alhamdullilah, munata fama ga exam nata gabatowa" "to Allah yabada sa'a, adai cigaba da dagewa" "insha Allah yaya" haka suka cigaba da firarsu sama sama har suna haka abba yashigo. sosai abba yaji dadin ganinshi dukda dama yasan da zuwanshi, cikin girmamawa Deen ya gaidashi yana amsar handshake din da abba yake miqomashi a kunyace inda sabo yaci ace Deen yasaba da hakan don hakan nacikin al'adar abba miqama mutum hannu suyi musabaha duk banbancin shekarunsu kau abba irin mutanen nan ne masu faran faran ga raha da dariya nan ya zauna suka shiga labari wanda duk yashafi aikin Deen a yanayin dasuke firar zaka hango tsantsar qaunar da abba keyima Deen shikuma Deen zaka hango tsantsar girmamawa da biyyaya dayakema abban. can kuma suka tashi abba da Deen suka fita waje suka bar Lailah a falon parking space suka nufa inda Abba yanunama Deen sabuwar motarshi daya saya kwana uku daya wuce wadda ke lullu6e cikin rigar motar da taimakon Deen suka yaye lullu6in motar. danqareriyar motace yar yayi mai mugun kyau, sosai Deen yayima Abba allah yasanya alhairi sannan yashiga duba mashi lafiyar motar kamar yadda Abba ya buqata don ganin ko tanada wani fault daya kamata agyara kafin afara hawanta Lailah ce ta tashi daga inda take zaune taqarasa jikin Windows din falon tadan yaye labulen wajen tana leqensu Deen ne tagani gaban motar ya dage murfin gabanta ya sunkuya yana dubata tattare hannuwan rigarshi dayayi yaba farar fatar hannunshi bayyana mai cikeda kwanttatun gargasa lumshe idanu tayi ahankali tasake budewa akanshi, tarasa meyasa komai Deen yayi saiyayi mugun yimashi kyau. cigaba da kallonsu tayi har yagama yan gyare gyaren dayake, Abba ya zagaya yashiga motar Deen na gaban motar still harya tadata shikuma yaqara sunkuyawa yana duba engine motar sun dan dade ahakan kafin abban yafito bayan yakashe motar shikuma Deen ya maida murfin gaban motar ya rufe alamun sungama Abinda sukeyi sake lullu6e motar sukayi sannan sukazo suka wuce suka kama hanyar part din abban. Ajiyar zuciya Lailah tasauke tana sakin labulen, sosai take tausayama kanta na fadawa son maso wanin datayi, fatanta dai Allah yabata mafita akan wannan matsalar tata yakuma sassauta mata. sai bayan sallar isha'i Abba da Deen suka sake shigowa main house din don Deen yayi bankwana dasu mami. basu dade ba suka fita da Abba da Deen da Afrah data liqemashi suka rakashi har wajen motarshi ko anan ma sundan qara dadewa suna fira sannan Deen yashiga motar bayan sunyi sallama ya tada motar yajata. bin motar da kallo Lailah dake leqensu ta windown dakinta tayi harta fice. sauke wata nannauyar Ajiyar zuciya tayi sannan tasaki labulen takoma ta jingina da bango tana Lumshe idanunta. 💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚 Tun bayan rabuwar zee da Mussadiq bata qara walwala ba, haka ta qarasa ranar cikin qunci da rashin kuzari sosai batool ta damu da hakan kuma tambayar duniyarnan tayimata akan meke damunta amma taqi gayamata saidai tace mata babu komai dole ta haqura ta kyaleta saidai tasan akwai abinda ke damunta kuma tafi alaqanta hakan da qila mikin soyayyarta ne yatashi don dama haka take wasu lokacin, duk yadda takeson 6oye damuwarta tayi pretending she's ok wani lokacin kasawa, wani lokacin kawai sai kaga mood dinta yachanza takoma very depressed. murda handle din kofar akayi tawaje aka turo kofar batool ce tashigo dakin ta tsaya daga bakin kofar tana kallon zee haryanzu zaune take inda tabarta rungume da pillow ta kafe wuri guda da ido Ajiyar zuciya batool ta sauke sannan ta qarasa shigowa cikin tana sakin murmushi cikin son wartsakar daita fadawa tayi kan gadon itama gefen zee tana dariya wanda hakan yadawo da zee daga duniyar tunanin data shiga tajuyo tana kallonta "albishirinki" inji batool happily dauke kanta xee tayi daga kallonta don kwata2 bata cikin mood din wasa, kamar bazatayi magana ba can kuma tace "goro" murmushi batool tayi tace "to yarinya Akhie tafiya zaiyi, guess where?" Dan kallonta zee tayi saikuma tasake kauda kai, da batool tasan yadda batason ko magana ce dabatazo tana takura mata ba amma sanin wacece batool din yasata sanin amsamata din kawai shine kwanciyar hankalinta "where?" ta tambaya tana dan yatsine fuska cikin qosawa "Nigeria!" batool tabata amsa cikin murna saurin juyowa Zainab tayi ta kalli batool din "Nigeria?.."✍? Ummin fasihu🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:43 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *076* *THE TRIP* "Are you serious?" inji zee tana kallon batool cikin mammaki "wlh yanzu naji suna labarin da ummy, gobe ma zasu tafi zasubi flight din 12noon" shiru zee tayi tana kallonta, kawai saita tsinci kanta dajin wani irin kewar kasar tata. bata ta6a tunanin zatayi missing Nigeria nan kusa ba amma yanzu dataji wannan zancen saitaji tayi missing dinta sosai, tayi missing qasarta da mutanen ciki, jitayi dama daita za'ayi tafiyar amma kuma anya zuwan bazai famamata tsohon mikinta na zuciya ba? kodayake anan dinma ba tsira tayiba, tagudo nan don mance past dinta tayi moving on amma seems it's not easy don kullum past dinta cikin hunting dinta yake kauda kanta tayi daga kallon batool din tace "me zaije yi acan to?" "asalin tafiyar batashi bace, Ahmad wani business trip zaikaishi can shine shima yace zayaje don yarabu dazuwa gashi dama kwanannan he's less busy" "kenan tareda Ahmad zasu tafi?" "yeah... did you want to go too?" inji batool tana quramata idanu wani kallo zee tayi mata sai ta kauda kai "never!" tafada tana hade fuska murmushi batool tayi "nayi tunanin kina kewan can ne" "banayi" tabata amsa tana komawa ta jingina da frame din gadon murmushi tasake yi tace "A'a dole kiyi missing Nigeria, gida gidane ko don mahaifanki dake can" "ai yanzun ma kamar tare muke don kullum muna waya kuma Idan naso ganinsu ma zan gansu ta video call so bana wani missing dinta" murmushi kawai batool tayi bata qara cewa komai ba saidai talura da yadda mood din zee yaqara chanzawa wanda ta tabbata harda zancen tafiyar tasake dagulamata mood din A daren ranar barci rabi da rabi zee tayi, sosai tunanin tafiyarsu Aymaan ya tsayamata arai yakuma tadomata tsumin kewar qasarta da mutanen cikinta. washegari sukuku ta tashi, jiki babu kwari tahau daily chores dinsu da shirin makaranta. suna zaune a dining suna breakfast Aymaan ya sauko daga sama shima yayi joining dinsu. gaidashi batool da zee sukayi ya amsa cikin kulawa da barkwanci kamar yadda yasaba sannan shima ya gaida ummy batool ce tayi serving dinshi sannan ta koma ta zauna tacigaba dacin abincinta jawo abincin yayi gabanshi yafara ci saidai rabin hankalinshi nakan zee daketa tsakurar abincin sama sama Dan murmushi yayi sannan yadauki mug din shayinshi dake tururi yadan kur6a ya ajiye yasake kallon zee "ke yar Nigeria, hope kinsan yau zankaiwa qasarku ziyara?" dagowa zee tayi ta kalleshi sai tadanyi murmushi "hmmm jiya nakejin labari, Allah ya tsare hanya" Dan daga gira daya yayi yace "hakama zakice? nayi tunanin liqewa zakiyi kice kema kina zuwa" Dan ta6e baki tayi tace "saidai nace Allah yakiyaye hanya" dariya batool tayi tace "hmmm haka zakice ai, yarinya tazo qasar turai taji dadi ta manta da qauyenshi" taqara fashewa da dariya Aymaan na tayata "kekau kullum tana cin dajaja🍗ta larabawa tana shan ni'imttaciyar weather mu ba dole ta manta ba?" inji Aymaan kumbura fuska zee tayi tana makamasu wani kallo "wane ni'imttaciyar weather? ai wlh Nigeria tafi nan weather mai ni'ima. kuda nan da rana tsabar zafi kamar ana gasa mutum a oven? a qasarnan Idan kayi walwala da zirga zirga cikin kwanciyar hankali to darene, ahakan kuma kukeda weather mai kyau?" tafada tana harararsu "ahaka kuma kike qara haske kina fresh, dakike can kauyen naku ko rabin kyan yanzu baki kaiba dukda ni'imttaciyar weather taku" inji batool "wake haske? ai kuma kunsan nafi kyau danake qasarmu, anan banda tsabar rana da zafi me akeyi, badon ina kaffa kaffa da kaina ba da yanzu nazama duna qila sai an haska da touchlight za'a dinga ganin fuskata dakyau" dariya duk sukayi harda ummy dake aikin sauraronsu "aimu ranarmu fari takesawa ba baqi ba ko kin ta6a ganin balarabe baqi? koma akwaisu yan kadanne, mafi yawancinmu fararene" inji Aymaan "Allah mai iko, yanzu nan kuma jinku kuke ku larabawa ne ko?" inji ummy da sai yanzu tasa baki dariya zee tayi "karfin hali kenan, dadai ba'a san asalin balbela ba" kumbura fuska batool tayi tace "yo Idan ba larabawa bane ba su wanene?" "ato, tayani tambaya" inji Aymaan "cikkakun larabawa nemu" inji batool "fararen ma kuwa" Aymaan yabata amsa dariya sosai zee keyi don sosai suka bata dariya "A'a gwarama kayi shiru da bakinka Aymaan, Idan ana maganar farare kabar zazzaqewa don.kunya zakasha" inji ummy dake taya zee dariya Dan 6ata rai Aymaan yayi yace "to ni ba farin bane? wai batool ni ba fari bane?" Dan kallonshi batool tayi saikuma tafashe da dariya "wlh tlh Akhie kai baqine" ta qarashe tana saurin miqewa daga kan kujerarta don dama kusadashi take sakin bakinshi Aymaan yayi yana kallonta itakuma takoma bayansu ummy dake dariya tana dariyar itama "kutt... nizakiba kunya muna team daya? lallai kin qoshi" yafada yana kwafa ya sake daukar mug din shayinshi "yo ai gaskiya ne Akhie, kasan ni bana qarya" inji batool tana dariya kada kai kawai Aymaan yayi bece mata komai ba ya cigaba dacin abincinshi kujerar kusada ummy batool taja ta zauna taqi komawa kusadashi suka cigaba da breakfast din nasu cikin walwala, wannan karon murmushi kwance a fuskar zee dakejin duk wata damuwarta data tashi daita ta yaye ganin hakan yasa Aymaan Dan murmusawa don dama burinshi kenan, kullum burinshi farincikinta, ya tsani ya ganta cikin damuwa ko yayane. ahaka suka gama breakfast din su zee suka tashi don wucewa school "ukhtie baki gayamin tsarabar dazanyi miki ba Idan zan dawo" inji aymaan yana kallon zee kafin zee tayi magana batool tayi saurin ca6ewa da "ka siyamin komai nacan dangin maqulashe na gargajiya irinsu magarya, goruba, taura, jawuwa, jan madam, kanya..." "wa ake tambaya wake bada amsa? kinji na ambaci sunanki ne?" Aymaan ya katseta yana mata kallon up & down kumbura fuska tayi tana kallon ummy "nida kika kira baqi nikuma kikeso nayimiki tsaraba?lallai bakida hankali" yafada yana binta da mugun kallo qara kumbura fuska tayi kamar zatayi kuka "yauwa ukhtie inajinki" ya maida hankalinshi kan zee dake qumshe dariyarta "nidai babu komai yaya, kawai fatana Allah yakaiku lafiya ya maidoku lafiya akuma gaidamun su mummy sosai ace nayi kewarsu sosai" "kenan bakison tsarabar komai?" girgiza kai tayi kawai "to ni Idan nayimiki don karan kaina fa?" murmushi zee tayi "it ok, xanji dadi sosai" murmushi shima aymaan yayi yadan kauda kai saikuma yasake kallonta "to Shikenan, zan miki tsaraba, wadda bazaki ta6a mantawa ba" Dan daga gira daya tayi "dagaske?" kadamata kai yayi alamun eh "shukran so much" kada mata kai kawai yayi ya kauda kai yacigaba da cin abincinshi dabe cinye ba juyawa zee tayi tayima ummy sallama sannan tasake yima Aymaan bankwana tanufi kofa batool daketa kumbure kumburenta itama tayima ummy sallama sannan ta kalli Aymaan da hankalinshi kekan abincinshi tace "to nima Akhie Allah yakiyaye yakaiku lfy amma karka manta harda atamfofi irin nacan da shaddoji da kayan kad'i irinsu kuka, ku6ewa, ya6do, daddawa..." duqewa tayi saboda jifanta dayayi da spoon din hannunshi tana dariya "wlh yarinyar nan ta rainani nizakiba sautun daddawa da kuka?" gwalo tayimashi sannan tanufi kofa tana cigaba dayimashi dariya suka fice itada zee. binsu da kallo Aymaan da ummy din sukayi harsuka fice daga falon sannan kowanne ya janye idanunshi yana sauke Ajiyar zuciya ummy ce tadago takalli Aymaan tace "kana ganin komai zaitafi smoothly?" qurawa plate din gabanshi idanu aymaan yayi sannan yadan sauke Ajiyar zuciya sannan yadago yakalli Ummin "insha Allah ummy, just pray for us" "to Allah yabada sa'a yakuma taimaka" "Amin ya rabb" haka suka cigaba da karinsu suna labari jefi jefi duk akan tafiyar. sai wajajen 11am Ahmad yaduro gidan cikin shirinshi na tafiya saida suka gaisa da ummy sannan ya haura sama dakin Aymaan sai wajajen 11:30am suka sauko kowanne cikin shirin tafiya kowanne goye da jakkar goyawa wanda ke daukeda duk abubbuwansu na amfani. saida sukayi bankwana sosai da ummy tayimusu addu'o'in tsari sannan suka bar gidan cikin motar da Ahmad yazo daita wanda drivern gidansu ke jansu. lokacin dasuka isa airport din saura mintuna shabiyar jirginsu yatashi nan suka shiga yin duk wani tantancewar daya kamata suyi kafin lokacin tashin jirgin. cikin qanqanin lokaci suka gama all neccesary things dazasuyi suka bi ayarin passengers masu shiga jirgi suma suka shiga suka zazzauna a seats dinsu dake.kusada juna. cikin qanqanin lokaci aka fara sanarwar tashin jirgin nan kowa duk ya daddaura belt din cikin few minutes jirgin ya daga ya lula sararin samaniya *** Wunin ranar a school cikin walwala zee tayishi, bata yarda ko kadan taba tunani damar yin tasiri a zuciyarta ba. yau bataje library ba kamar yadda tasaba saboda gudun sake haduwa da Mussadiq dukda tasan ba qaramin aikinshi bane ba yabiyota har class din dayake Idan yaga dama. sai bayan asr sannan suka fito daga school din da ita da batool suka nufi motarsu suka shiga suka fice daga school din. fitarsu keda wuya shima yaba drivernshi umarnin sutafi, drivern yataka motar yaja suma suka fice daga school din. 💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙 sai da marece liss jirginsu Aymaan ya sauka a babban filin jirgin sama na babbar birnin tarrayar Nigeria wato Abuja. cikin qanqanin lokaci suka fito suka gama clearing din komai sannan suka kamo hanya suka nufi hanyar fita daga airport din ganin ba'a dade da gama magrib ba yasasu fara tsayawa a massalacin dasuka fara cin karo dashi sukayi sallah sannan suka fito neman abin hawa. basu wani jimaba suka samu adaidaita sahu suka hau suna gayamashi hotel din daxai kaisu tafiyar mintuna shabiyar sukayi suka isa hotel din suka sauko suka biya mai adaidaitan haqqinshi sannan suka shige cikin hotel din. cikin qanqanin lokaci suka kama daki suka biya sannan aka rakasu dakin a lokacin har wasu massalattan sunfara sallar isha'i hakan yasasu sake fitowa sukaje sukayi sallar tasu a massalacin hotel din sai bayan sun dawo sun nutsu har sunci abinci sannan suka doddora sabbin layyukansu dasuka siya. nan Ahmad yajawo laptop yafara aikin gabanshi shikuma Aymaan ya shigewarshi toilet. sai bayan awa daya aka turomusu sms na zasu iya amfani da layyukansu nan take suka fara ma mutanen Dubai domin sanardasu isowarsu Nigeria lfy sun dade suna waya dasu inda saida suka farayi da iyayen Ahmad sannan suka kirasu ummy suma daga nan suka maida akalar kiran wajensu Daddy(mahaifan zee) dake katsina don sanardasu isarsu don suma sunsan da tafiyar don dasun gama Abinda yakawosu zasu biya ta katsina din kafin sukoma Dubai suma sundan jima suna gaisawa dasu sannan sukayi sallama. daga haka Aymaan yawuce yayi shirin kwanciya yayi kwanciyarshi yabar Ahmad nan daya cigaba da aikin dake gabanshi. yana jin lokacin daya kira abokin aikinshi nanan Abuja din suna tattaunawa akan abinda yakawosu dakuma fitarsu ta gobe. maida idanunshi Aymaan yayi ya rufe kamar mai barci amma ba barcin yakeba, banda saqe saqe babu abinda ke kai komo a kwalwarshi. ahakan har Ahmad yagama duk abinda yake shima yazo ya kwanta ya dade sosai idonshi biyu kafin yasamu can cikin dare barci ya sadado shima ya daukeshi. *WASHEGARI* Sai bayan sallar zuhr suka fita daga hotel din. dama abokin aikin Ahmad ne yazo daukarsu don haka gabadayansu suka nufi motar da mutumin yazo daita duk sanye suke cikin qannanun kaya sunyi kyau sosai mussanman aymaan dayayi shigar all white wanda yayi mugun yimashi kyau sosai saidai fuskarnan tashi babu wannan walwalar da fara'ar da aka saba ganinta dashi. kallo daya zakamashi kasan cewa yau baya cikin good mood kwata2 ko a motama Ahmad da usman (abokin aikinshi) kawai ke labarinsu shikau hankalinshi nakan wayar hannunshi dayake daddanawa tunda suka shiga motar sunyi tafiyar kusan mintuna 30 sannan suka iso inda zasu. jin tsayuwar motar yasa Aymaan sanin sun iso duk fiffitowa sukayi banda Aymaan da saida ya mula yasha iska sannan ya bude kofar 6angarenshi yafito. Ahmad tun jiya yake lura da take takenshi dakuma yadda yake wani shashan qamshi amma be kulashi ba don yasan abinda ke damunshi kuma yasan qiris yake jira ya burkuce musu shiyasa yake taka tsantsan yana lalla6awa harsuyi abinda ya kawosu sutafi. maida kofar aymaan yayi ya rufe bayan yafito sannan yafara bin harabar wurin dasuke da kallo wurin babban industry ne ya hadu daidai misali don koina is neat and well trimmed. akwai mutane jefi jefi a harabar wasu tsaye wasu kuma na kaiwa da kawowa. waya usman yazaro yayi kira, bayan yagama yajuyo kansu Ahmad yace suje. gaba yayi suma suka maramashi baya har suka shiga cikin building din. suna tafe Ahmad da usman na magana yayinda Aymaan dake bayansu yayi tsit sai bin wurare yake da kallo cikin nazari. Ahaka har suka qaraso reception din. anan suka hadu da managern wajen wanda yayi musu tarba mai kyau wanda da alamu akwai sannaya a tsakaninshi da usman anan usman ya gabatar mashi da Ahmad da Aymaan suka gaisa inda har lokacin babu walwala tareda Aymaan. iso managern yayi musu zuwa wani qayyataccen waiting room yakuma sa aka kawomasu abu mai sanyi sannan ya sanardasu sudanyi haquri ogan na studio yanzu amma insha Allah yakusan fitowa. da hakan yafito yabarsu wajen don jiran isowar ogan. tunda suka zauna Aymaan ya jingina da jikin kujera ya rungume hannayenshi a qirji ya sauke idanunshi qasa. ko kallon kayan drinks din gabansu beyi ba bare yayi marmarin ta6a daya daga ciki kawai dai zaune yake yana kalkada kaffafunshi yana saqe saqen da shikadai yasansu. sunyi 20mins ahakan sannan suka farajin alamun ana tunkaro dakin dasuke su Ahmad daketa labarinsu daya shafi business tuni suka nutsu suka maida dukkan hankalinsu ga kofar shigowa wajen yayinda Aymaan ko motsawa beyiba daga position dayake ba. qarar budewar kofar yaji sannan yaji sallamar manager din daya kawosu nan din, can saiya sake jin sallamar cikin wata very cool calm voice. bugun zuciyarshi ce tafara sauya salo lokacin da wannan muryar ta dira kunnuwanshi. su Ahmad ne suka samu damar amsa sallamar yayinda shikuma ahankali yafara dago idanunshi daga qasan dasuke kallo cikin two pair of oily eyes dinshi ya saukesu wanda yaqara yin daidai da motsawar zuciya...✍? Ummin fasihu🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:43 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *077* Kafeshi yayi da kallo shima Deen din ya tsinci kanshi da tsareshi da nashi idanun. "bismillah, gasunan tundaxu suke zaman jiranka" maganar Habeeb ta dawo da Deen daga duniyar kallon Aymaan janye idanunshi yayi akanshi ya kalli kingin mutanen dakin yana sakarmasu kyakyawan murmushinshi yana ida qarasowa dakin. Ahmad tunda ya dora idanunshi shima akan Deen yayi suman zaune, be ta6a sanin kammanin nasu yakai hakaba, ba don yasani ba da yana iya rantsewa cewa wannan Mussadiq ne. "barkanku da warhaka, sorry for keeping you waiting" yafada calmly cikin friendly tone yana miqamusu hannu don suyi musabaha da usman dake farko suka fara musabahar sai Ahmad dayayi iya bakin qoqarinshi wajen daidaita nutsuwarshi yana murmushin yaqe sannan ya miqama Aymaan da har lokacin idanunshi bebar fuskar Deen ba ganin be amshi hannun ba saima kallonshi daya tsaya yanayi yasa shima Deen cigaba da kallonshi trying to read his expression don shima tun kallon farko dayayiwa mutumin yakejin kamar akwai wani abu attatare dashi. harya fara fidda rai da zai amshi hannun yafara shawarar saukewa Aymaan ya dago nashi hannun yabashi sukayi musabahar wanda ko second daya basuyi ba kowanne ya janye nashi hannun iso Deen yayi musu akan sutaso sutafi office dinshi yadda zasu tattauna dakyau. duk miqewa sukayi yayi gaba batareda ya qara kallon gefen aymaan da ko motsawa daga zaunen dayake beyiba yayi hanyar fita daga dakin. Ahmad ne ya dafa kafadar Aymaan ganin beda alamun tashi din dagowa Aymaan yayi yana kallon Ahmad da wani irin expression a idanunshi, fuskar roqo Ahmad yayimashi yana mashi nuni daya taso please. dakyar yasamu yataso din yana cije lip dinshi na qasa. suma hanyar fita sukayi Don kingin harsun fita. basuyi wata doguwar Tafiya ba suka qarasa office din Deen din duk yimasu iso managern yayi ya gwagwadamasu wurin zama duk suka zauna a kujerun dake facing table din daya raba tsakaninsu da Deen dake zaune yana facing dinsu ta dayan 6angaren. tunda Aymaan ya zauna yayi crossing kaffafunshi ya sauke kanshi qasa yana danne2 a waya be qara dagowa ba a bangaren su Deen kuma gaisawa suka sakeyi dasu Ahmad sosai sannan Habeeb yafara magana "wannan shine wanda nacema zaizo yau dashi da abokanshi, sunanshi usman ya rako abokanshi ne akan wani aiki amma gashi nan ai, waqa abakin mai ita tafi dadi" duk murmushi sukayi sannan usman ya amsa da "hakane Mallam Habeeb, ni sunana usman mahmud wadannan abokainane kuma yan uwana da Ahmad da Aymaan, su yan Nigeria ne amma suna zaune ne a Dubai yanzu hakan ma aiki ne yakawosu nan din, wannan Ahmad din shi yayimin magana tun kafin suzo akan zasu shigo 9ja kuma xaiso haduwa da shahararren mawaqinnan balarabe don fan dinka ne sosai dukda yanacan amma yana yinka kuma yana sauraron waqoqinka sosai, kasan shahara babu abinda bata kawowa, kai kananan zaune waje daya amma bakasan iyakar inda ka zaga ba. ganin yadda yake kwadayin ganinka yasa nikuma nace insha allah zanyi qoqari na hadaku... to Mallam Ahmad yau dai gaka ga balarabe face-to-face" yaqarashe yana kallon Ahmad daketa murmushi tunda yafara maganar "aikaudai Dan uwa, yau gani ga wanda nadade ina mafarkin gani a zahiri. gaskiya naji dadi sosai don I never thought ganinka will be this easy for me, ban ta6a tunanin zanganka anan kusa ba koda daga nesa ne bare ace har nasamu damar magana dakai, gaskiya am very happy today and ina farincikin gayamaka cewa.muna yinka sosai, more more basira insha Allah" Deen dake murmushi sosai yace "Thanks so much bro, am glad and happy I can statify your expectations without my knowledge, Allah praise be to Allah dayabani damar gamsar daku da guntun baiwar dayabani, allah yasaka da alhairi yakuma cigaba dabani ikon cigaba da gamsardaku da aikina" "Amin ya allah, ai Mr balarabe sunanka yayi trending inda kwata2 baka tunani kuma bakomai yaja hakan ba sai irin yadda kake captivating zuciyar mutane da salon waqarka, ga sanya nutsuwa ga sanya shauqi don duk daskarewar zuciyar mutum dayaji waqarka saita motsa wlh, allah dai yaqara basira yasa afi haka" inji usman "Amin amin, Allah yaqara daukaka yaqara zaqin murya da kaifin kwalwa.." tashin da Aymaan yayi yasa Ahmad Dan yin shiru wayace kare a kunnenshi hannu daya a aljihu "hello..." daga haka yawuce hanyar kofar office din yafice Duk binshi da kallo sukayi harda Deen harya ida ficewa daga office din maido dubansu sukayi kan Deen da haryanzu idanunshi nakan kofar office din yar dariya Ahmad yayi yace "workaholic kenan, haka yake kodayaushe cikin aiki mutum kamar agogo" duk dariya sukayi banda Deen dayayi murmushi kawai "yes as I was saying Idan babu damuwa nima zanso adan yimin waqa ace yau gani da waqar actor na kuma ni akaiwa, gaskiya I'll be very happy Idan akayi granting wannan wish din nawa" murmushi Deen yayi yace "babu damuwa insha allah, hakan bazai gagara ba saidai wane iri kakeso? just waqar koko harda performing?" dan wara idanu ahmad yayi "wow performing? sounds nice. wane procedure akebi to Idan mutum nason ayimashi performing din?" "gaskiya Idan performing ne ana sanarwane dawuri misali a month to the date yadda za'a riga akamamaka ranar" "hakan yayi, insha Allah zamu dawo don performing din very soon amma yanzu kasancewar zuwa mukayi kuma ba dadewa zamuyi ba inajin waqar kadai ta wadatar" "alright to wace iri kakeso?" "waqar mahaifiya, umma ta nakeso ka waqe" yafada yana washe baki duk murmushi mai sauti sukayi "masha Allah, Shikenan insha allah yanzu Habeeb kar6i bayyanan komai da komai, yaushe kukeson waqar?" "eto, kaga bawani dadewa zamuyi anan dinba kawai wani aiki ne yakawomu zamuyi mu juya, insha allah jibi mukeson juyawa Idan Allah yakaimu" "alright, jibi da yaushe zaku tafi?" "jirgin marece zamubi insha Allah" "to kuna iya dawowa jibin dasafe insha Allah everything will be ready" cikin jindadi Ahmad yace "kai masha allah, mungode kwarai allah ya qara daukaka" da Amin ya amsa yana murmushi sannan Habeeb yashiga yin abinda Deen din yasashi. cikin qanqanin lokaci suka gama clearing komai suka dan qara ta6a fira cikin raha da barkwanci inda anan saida Ahmad yayi ya dauki hoton Deen shikadai sannan kuma yabada akayimusu taredashi. lokacin da zasu tafi har waje saida Deen da Habeeb suka rakosu saboda dan sabo daya shiga tsakaninsu adan wannan lokacin suna tafe suna fira. tundaga nesa suka hango Aymaan zaune kan wani benci dake karkashin wata bishiya dake parking space din kanshi sadde yana latse latsenshi a waya. har suka qaraso dan nesa da wajen be dagoba don bema nuna alamun yasan dasuba dukda tun fitowarsu yagansu tsayawa sukayi adan nesa da wurin sukayi bankwana cikin aminci sannan Deen ya juya batareda shima ya kalli gefen da Aymaan yakeba yatafi Habeeb na takemashi baya. saida sukaga wucewarsu sannan suka nufi inda Aymaan yake "haba aymaan, meye hakan dakayi? you just walk out without even excusing yourself, hakan dakayi is not proper" inji Ahmad dagowa yayi ya makamashi wani kallo sannan ya tashi yana pocketing wayarshi "kunga muje, abinda yasa kuka iskeni anan ma don babu car key a hannuna ne" yafada yana wucesu "aida kabi adaidaita tunda garin ba baqonka bane bare ka 6ace" Ahmad yabashi amsa "I thought as much saidai earliness dinku na minti biyar ya hana hakan, dakun qara minti biyar aciki da yadda kace din za'ayi" Aymaan yabashi amsa Ahmad zai sake magana usman yadan dafa kafadarshi yana murmushi sannan yajuya wajen Aymaan dake qoqarin chanza akalar tafiyarshi daga motar zuwa hanyar waje yace "kyaleshi dude, muje please wani lokacin sai ya dinga abu gadaiyanan" da hakan yabude motar ya budewa Aymaan din dake cika yana batsewa backseat din. kamar karya shiga saikuma yashiga don bazaiso qara saida halinba mussanmman ga usman dayake baqo awajenshi sannan suma duk suka shiga gidan gaba usman ya tada motar suka fice daga industry din *** yauma sai wajajen bayan asr suka fito daga school din suna tafe suna firarsu suka nufi parking space inda sukayi parking din motarsu tundaga nesa suka hangeshi zaune bisa booth din danqareriyar motarshi baqa sanye yake cikin shigar suit dinshi as usual saidai babu coat din sama acikinshi sai farar spotless shirt da guntuwar jacket dinta dake sama. idanunshi sanye da shade as usual ya sunkuyar dakai yana danne danne a wayar hannunshi. kallon juna batool da zee sukayi sannan suka sake kallonshi don yau ma kamar kwanaki parking yayi yadda yaga dama don yauma yaga taremusu motarsu dole saiya janye tashi sannan zasu samu damar fiddo tasu. rolling idanu zee tayi cikin qosawa, meyasa wannan mutumin baxai fita rayuwarsu ba hakanan? "ai shikenan, sai kije ki fiddomana motar" tafada ma batool tana juyar da kai gefe guda "wa? ai wannan aikinki ne tunda naga kunfi kusa" batool tabata amsa "ai shikenan saimu nemi abin hawa mutafi don yau babu wanda zai 6atamin rai abanza" inji zee tana juyawa zata nufi hanyar gate yar dariya batool tayi tace "good idea, ashe kema yanzu kingane fada da aljani babu riba" tafada tana binta harara zee ta gallamata ta gefen ido suka cigaba da tafiyarsu batareda sunqara bi takan parking space din ba "Ummie!!" sukaji an kwalamasu kira daga bayansu "Ummie! sis batool!" atare suka juyo saikuma suka wara idanunsu atare "Aysha!!" sukayi exclaiming atare sannan suma suka nufeta cikin sauri da murna a tsakiyar hanya suka hadu su ukun suka rungume juna suna tsuwar murna saida suka gama haukarsu sannan suka saki juna suna dariya "yau kece a school dinmu?" inji zee tana riqe ha6a harara Aysha ta gallamata tace "aike kin manta da mutane ko kiran mutane bakiyi yanzu bare akaiga kin nemi ganinsu" dariya zee tayi tace "haba daughter, wlh kina raina" "banga alama ba ai, yanzu ma badon na takurama Akhie yakawoniba da haka za'aita Tafiya" "ai haka take wannan matar batason zumunci ko kadan" inj batool "ai harda ke, kema yaushe rabon da ki kirani?" inji Aysha tana harararta itama gwalo zee tayima batool data turo baki tana cewa "hhh yarinya wayace ana shiga tsakanin uwa da 'ya?" "yasu Ummie? ya school?" inji zee tana kallon Aysha "school babu dadi, haryanzu nakasa sabawa da rashinki" tafada tana Dan kwa6e fuska itama zee kwa6e fuska tayi tace "ayyah same here" "bawani same here keda baki damu da mutane ba?" "haba Ayush dita? nina isa" Aysha zatayi magana wayarta tayi Ringing zaro wayar tayi taduba saikuma tajuya takalli saitin parking space suma bin inda tabi da kallo sukayi sukaga Mussadiq ne wanda haryanzu ko dagowa beyiba daga danne dannen dayake Juyowa Aysha tayi ta kallesu tace "bari kuga natafi, yaya yafara min warning dama dakyar nasamu yakawoni don saida Ummie ma tasa baki, naji dadin ganinku sosai" "muma haka dear, ki gaidamin Ummie insha allah muma zamu shigo" inji zee Dan harararta tayi tace "kamar gaske" dariya sukayi zee tace "allah dagaske" "to Allah yasa, a gaidamin kowa da kowa please" "insha Allah saimunyi waya" Juyawa tayi dasauri tanufi motar don har Mussadiq duro daga booth din motar. wucewa yayi gefen driver ya bude ya shige itakuma Aysha ta zagaya dagudu bude dayan 6angaren tayi itama tashiga wanda yayi daidai da tashin motar ganin hakan yasa zee kauda kai daga kallon wajen tana kallon gefe zuwa motar tayi ta wucesu aguje tana barmasu qura bin motar sukayi da kallo harta fice daga school din suka ta6e baki atare "Dan wahala" inji batool "na bugawa a news" zee ta amsa Juyawa sukayi suka koma parking space din suka shiga motarsu suma suka fice daga school din. *** Aymaan qarasa wunin ranar yayi yana hidindimunshi shikadai duk yadda Ahmad yaso yasaki ranshi qiyawa yayi dole ya qyaleshi yasan meke damunshi kuma beyi mammakin yadda yayi reacting ba don koshine hakan zaiyi kwata2 Deen yazomusu a yadda basuyi tunani ba, ganinshi a zahiri yafi jinshi don kama kawai suke da Mussadiq amma Aura dinsu yasha banban duk yadda yake ganin Mussadiq da qwarjini Deen yafishi, yafishi komai kama daga qwarjini, haiba da wata iriyar baiwa tashiga rai farat daya. a kallo daya yagane dalilin dayasa zee ta haukace a soyayyarshi don he worth being crazy for. kwanansu biyu agarin a cikon na uku wato ranar dazasu tafi suka koma industry din saidai wannan karon Aymaan be bisuba daga Ahmad sai usman. anan suka tadda har an kammala masu aikinsu kamar yadda aka alqawartamusu kuma aikin yayimusu sosai har hakan yasa Ahmad yakasa 6oye farincikinshi. anan Ahmad kecemashi insha Allah zaiso yayimusu performing watarana shikuma Deen yace Allah yakaisu lokacin saida Ahmad duk yatura latest waqoqinshi da videos dinshi sannan sukayi bankwana suka tafi. Qarfe 5:30pm taimasu a airport inda zasu hau jirgin katsina wanda zai tashi 6:00pm cikin qanqanin lokaci suka gama komai suka shiga jirgin 6 dot jirgin yadaga zuwa garin katsina ta dikko dakin kara *KATSINA* Lokacin da suka sauka a filin jirgin sama dake katsina har duhu yafara don ba'a dade da gama sallar magrib ba. lokacin har drivern da daddy yaturo don daukarsu ya dade da isowa. basusha wahala ba wajen ganin juna nan ya tayasu zuba kayansu a booth suka shiga motar yaja suka fice daga airport din. Tarba sosai Mummy da Daddy sukayi musu don rasa inda zasu sasu sukayi don murna. saida suka fita sukayo sallah tareda Daddy sannan suka dawo cikin qanqanin lokaci aka cikamasu gaba da girke girke kala kala. nan suka zauna suna kwasan girkin suna firar yaushe gamo Mummy nama Aymaan tsiya akan Allah yayi yau shine a 9ja. saida suka gama cin abincin sannan sukasa aka kaisu part dinsu da aka riga aka gyareshi tsaff sai zuba qamshi yake. dayake duk agajiye suke cikin qanqanin lokaci sukayi shirin barci kowanne yabi lafiyar gado. *WASHEGARI* Yau takama Saturday weekend shiyasa Daddy befita ba hakan yabashi damar zama dasu Aymaan sosai suna firar dabasu idaba ajiya. suna cikin haka Mummy itama tazo tayi joining dinsu suka cigaba da firarsu gwanin sha'awa. acikin firar ne aka kama topic din zee inda aka zarce zuwa rabuwarsu da Deen wanda yayi sanaddiyar barinta qasar. Daddy ne kebada labarin yana fadin yadda tunfarko yaqi yarda da soyayyarsu saboda irin haka amma suka nace da ita da Mummy harya haqura sai gashi Abinda yake gudu yafaru Aymaan ne ya gyara zama yana kallon Daddy yace "to amma Daddy kai aganinka meyasa yatafi din? wannan tafiyar tashi kwatsam batareda wata hujja ba akwai alamun tambaya, gashi ance shima yana sonta" Mummy ce tace "nima haryanzu abinda ke dauremin kai kenan, dole akwai dalili wanda shine duk bamusaniba" "wane dalili kuke nema bayan wanda yanuna na bayasonta? wayasani ko dama yaudararta yake ba ita yakeso ba dukiyarta yakeso shiyasa dayaga alamun bazaici ribaba ya yanke shawarar rabuwa daita don yaga a take takena bazan ta6a bari ya cutar da shalele ba" jinjina kai Ahmad da Aymaan sukayi cikin nazari can Ahmad yace "amma ni aganina Idan saboda yaudararta kawai yake baya sonta yana iya fitomata a mutum yace bayayi su rabu basai abin yakai ga barin gari ba, kufa duba kugani ace kawai don yasan bazaiyi nasara ba wurin yaudararta yaci kudinta saiya tattara yabar gari? yabar mazauninshi yabar karatunshi? yadda naji ance wai yana level na qarshe a school anya hakan yakai dalilin dazaisa yayi watsi da shekarun daya 6ata yana karatu saboda wannan dalilin? gaskiya akwai wani abin bayan wannan" Mummy tace "nima abinda nake tunani kenan, ace ka 6ata tsawon shekaru da tsabar kudade bayan ba wani hali ke garesu ba ace yabar karatun saboda dalilin da baikai yakawo ba?" "To ku aganinku mezaija hakan?" inji Daddy yana rungume hannu a qirji "ba kunce sai ranar introduction yabar garin ba? anya dalilin bayada alaqa da introduction din?" "how?" inji Mummy "meyasa saida maganar introduction tatashi sannan yagudu? ko baya sonta din yana iya Bari ayi introduction din tunda introduction din ba daurin aure bane kosa biki? then meyasa akan hakan kawai zai yanke wannan hukuncin?" shiru dakin duk ya dauka kowa da alamun yayi zurfi a tunani "waye mahaifinshi?" Aymaan ya jefo masu tambayar daga sama "cewa akayi daga mahaifinshi har mahaifiyarshi rasuwa sukayi tun yana qarami" inji Mummy "waye mahaifinshi yasha banban da mahaifinshi na raye ko amace? koda mahaifinshi ya mutu ai yakamata asan kowaye shi ko, meye sunanshi? waye danginshi kuma ina yake zaune kafin ya rasu din hakama mahaifiyarshi" "to nidai duk lokacin dana tambaya haka Zainab kecemin don itama Idan ta tambayeshi haka yake fadamata wai shi kanshi besansu ba kawai wannan kakar tashi ya bude ido yasani, kaga da sunzo introduction din daduk ansan wadannan abubbuwan" "good, yanzu munfara kamo bakin zaren dalilin dayasa yagudu din, tayiwu akwai Abinda suke 6oyewa gameda asalinshi ne ko kuma bayada wadanda zasu zone kwata2" duk kada kai sukayi cikin gamsuwa Daddy yace "no wonder, koda mukaje gidansu bayan tafiyarsu babu wanda yasan kowa nasu, wani neighbour dinsu ma cewa yayi tunda suka dawo unguwar almost 12years babu wani Dan uwa nasu daya ta6a zuwa wajensu" inji Daddy "good, wannan yayi daidai da dalilin barinsu garin wato rashin asali, yanzu tambayar anan shine waye DEEN?" inji Ahmad shiru dakin yayi Mummy da Daddy sai kada kai suke cikin mammakin wannan al'amari, tunda suke basu ta6a kawoma ransu wannan tunanin ba "no wonder, shiyasa tunfarko naji hadin beyimin ba ashe bayada asali? kinga irinta ko maimuna? har abada duk Abinda babba ya hango qaramin kome zai hau bazai hangoshi ba, kinga irinta ko?" inji Daddy itadai Mummy batace komai ba sai tunane tunanen datake Deen bashida asali? anya? haka kawai taji bata yarda cewa Deen beda asali ba, beyi kama da marar asali ba. "Allah ma ya taimaka nakawo shawarar yin introduction din da ahaka za'a tafi yaita yaudararmu bayan beda asali daga qarshe yayimana abinda yai niyya ya gudu don yasan bashida kowa bare ayi tracing dinshi" haka Daddy yaita banbamin fada shikadai yana qara aibata Deen yana qara dorawa Mummy laifi data goyi bayanshi a lokacin itadai mummy batace komai ba sai tagumi data buga tayi shiru abubbuwa da dama na kai kawo a kwalwalwarta suma Aymaan da Ahmad basuce komai ba sai kallon daddyn suke har saida ya gaji don kanshi yayi shiru. sai a sannan Aymaan ya kalli Ahmad yayimishi ido akan ya fiddo. wayarshi Ahmad yafiddo yadanyi yan shafe shafenshi sannan yajuyo da screen din saitin Daddy yace "Daddy kasan wannan?" amsar wayar Daddy yayi yana qurawa wayar ido saikuma ya wara idanu yace "ai shine wannan, kalli kobashi bane?" yafada yana gwadawa Mummy itama wara idanu tayi don hoton Deen ne jikin screen din zaune cikin shigar suit sai baqin glass a idanunshi yadan sunkuyar dakai yana rubutu kan wata takarda "shine wlh, ina kuka sanshi?" inji Mummy "shine wa Mummy?" inji Ahmad "kamal mana, tabbas wannan kamal ne" "to wannan fa?" inji Ahmad din yana miqomasu wata wayar daban atare suka leqa wayar nan ma the same person suka gani saidai wannan yana sanye ne cikin manyan kaya na hausawa ga kuma murmushi a fuskarshi sa6anin wancan "wannan ai duk hotunan mutum daya ne, ina kuka samu wadannan pics din?" inji Daddy "Daddy a matsayinka na businessman wanda ke harkoki na qasa dana waje nasan kasan wani Dan kasuwa mai suna Mussadiq Al-hassan ko?" "Mussadiq Al-hassan?" "Eh the young multi-millionaire na qasar Dubai mai companies din NURUL-HAQQ masu rassa qasashe daban daban?" "oh, wai Sir Mussadiq Al-hassan? waneDan kasuwa ne besanshi ba duk fadin duniyarnan? nasanshi sosai" "kenan ka ta6a ganinshi? kasan kammaninshi?" "A'a gaskiya bansan kammaninshi ba don he's always hideous, kasan manyan yan kasuwa sunansu yafi fuskarsu sanuwa don most of them basu cika bayyana kansu ba, ban ta6a ganinshi ba amma ina fatan watarana naganshi din don inada burin haduwa dashi koda badon muyi business ba Kawai don naganshi nima nasa hakan a record dina...amma meya kawo wannan zancen muna wani Batun daban?" inji Daddy Dan murmushi Ahmad yayi yace "saboda wannan shine Mussadiq Al-hassan" yafada yana nuna wayar hannun daddyn kallon wayar daddy yayi saikuma ya kalleshi "bangane ba" shine Aymaan be qara cewa komai ba sai rungume hannu dayayi a qirji yana binsu da ido "ina nufin wannan shine the famous Sir Mussadiq Al-hassan dakake burin ganin" qara kallon hoton hannunshi yayi in confusion "Mussadiq Al-hassan kuma? wannan ai Deen ne" "A'a, ga Deen can hannun Mummy" yafada yana nuna wayar hannun Mummy kallon wayar hannun Mummy din sukayi saikuma suka kalli juna Mummy ce tayi magana wannan karon "kamar yaya? wannan ai duk mutum dayane" "A'a wadannan mutane biyu ne living in their different world, wannan shine Mussadiq Al-hassan wanda ahalin yanzu yana can Dubai..wannan kuma Kamaldeen Muhammad wanda maganar damuke yanzu yana nan Nigeria a garin Abuja" "bangane me kakeson cewa ba, kana nufin wadannan hotunan ba mutum daya bane?" inji Daddy very confused "yes, mutane biyu ne Daddy" ""but how on earth mutane biyu zasuyi kammanni guda? saidai ko..ko.." kasa idawa Daddy yayi lokacin da wani tunani ya gifta kwalwarshi "saidai.. ko twins ne?" Mummy ta qarasawa Daddy maganarshi cikin rawar baki Dan murmushi Ahmad yayi "yes, ta hakan kawai za'a samu irin haka mummy" cikin rawar baki Daddy yace "kenan..kenan Deen twin ne" "yes Daddy, Deen twin ne, twin din the famous Sir Mussadiq Al-hassan"...✍? Ummin fasihu🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:43 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *078* Tsitt falon ya dauka sai kallon kallon da ake bakin Mummy da Daddy sunqirufuwa don mammaki. can Daddy yayi qarfin halin fizgo muryarshi datayi qaura na wucen gadi "I..still dont get you, kayimana bayyani yadda yakamata. what are you trying to say?" Ajiyar zuciya Ahmad ya sauke yadan gyara zama sannan yace "maganar gaskiya dole kuma abin ya rudaku don muma saida muka shiga rudani a farkon bayyanar wannan al'amari. Bayan rabuwar Deen da Zainab kun turota tabiyo ummy Dubai don tasamu tayi moving on ta manta da past dinta amma mutum na nashi Allah na nashi, maimakon past din yawuce sai yacigaba daga inda ya tsaya. dafarko zee tafara recovering daga past dinta saidai ba'a kai koina ba ya dawo mata alokacin da ta hadu dawani Deen din acan..." Tiryan tiryan Ahmad yashiga basu labarin abubbuwan dasuka faru tundaga haduwar zee da Mussadiq Al-hassan na farko a park zuwa haduwarsu nabiyu a supermarket ya gangaro zuwa lokacin da suka gane masu fuskar Deen din biyu ne zuwa lokacin dasuka samo information akan Mussadiq Al-hassan har suka gane su yan biyu ne, ya gangaro zuwa admitting din zee da akayi school din Aysha Al-hassan don samun information akan 6acewar Deen zuwa yadda Aysha ta warwaremasu yadda Deen din ya 6ace, ya kuma gangaro zuwa bayyanar Deen din wanda yanzu haka shahararren mawaqi ne anan Nigeria, yakuma gayamasu dalilin wannan tafiyar tasu wanda sunyita ne don su hadu da Deen dinne face-to-face ya gangaro da labarin har zuwa yanzu dasuke zaune. shiru falon ya dauka bayan qarewar wannan rikittacen labarin dayayi kama da tatsuniya daga Mummy har Daddy babu wanda ya iya motsin kirki don haryanzu shock din labarin begama sakinsu ba. Ahmad ya cigaba dacewa "kuyi hqr bamu sanardaku tun farkon faruwar al'amarin ne don kar hankalinku yatashi a lokacin kuma alokacin bamu ida tabbatar da komai ba. yanzu haka munzo Nigeria ne don muyi confirming koshi dinne mukuma san inda yake zaune kuma munada burin sadashi da iyayenshi da yan uwanshi insha Allah" Mummy batasan sadda tayi bursting in tears ba "innalillahi waina ilaihi rajiun, wannan wane irin rashin imanine? wane irin rashin tausayine zaisa araba mutum da danginshi tun yana qarami a nisantasu a kawoshi wata uwa duniya? kai Dan Adam abin tsoro ne" tafada tana hawaye sosai shidai Daddy yakasa cewa komai saidai shima kallo daya zakayi mashi kasan abin ya ta6ashi sosai. "to meyasa kuka baroshi acan? meyasa baku taho dashi ba kuka maidashi wajen dangin nashi?" inji mummyn still hawaye a idanunta Dan murmushi Ahmad yayi "ai Mummy its not that easy, tayaya kawai zamu tunkareshi da wannan maganar off hand? kallon mahaukata ma zai mana, kawai ahankali zamubi komai. maimakon mutsaya yimusu bayani kawai hadasu ya kamata mufara yi sai bayanin ya biyo baya" "ta yaya to zaku hadasun?" inj Mummy "shine muke shawara son yi, hadasu abune mai wuya saboda ba a wuri daya suke ba, dole saidai daya ya tadda daya, ko na Nigeria ya tadda na Dubai din ko na Dubai din yazo Nigeria, amma tayaya? shine babban abinda kecimana tuwo a qwarya" hanki Mummy tasa tashare fuskarta tana qara jin abin a ranta sannan ta dago ta kallesu "Zainab tasan da bayyanar Deen din?" kallon juna Ahmad da Aymaan dayazama kamar baya wajen saboda rashin maganarshi sukayi sannan Ahmad ya maida kallonshi ga Mummyn "A'a, dama somuke muyi confirming sannan mu sanar daita" shiru falon yasake dauka kowa da abinda ke kai komo a zuciyarshi dagowa Daddy yayi for the first time tun bayan bada labarin Ahmad "yaushe zaku koma Dubai?" "gobe insha Allah" tashi tsaye Daddy yayi "kubari sai jibi yadda muma zamu samu damar hada visar mu" duk dagowa sukayi suna kallonshi "yes, muma zamuje Dubai din, tare zamu koma" yana kaiwa nan yawuce binshi da kallo sukayi harya wuce, sosai farinciki yakama Mummy don dama can tana burin zuwa Dubai din bare yanzu da wannan abin yafaru, she can't wait taga wannan mai kama da Deen din. Washegari shirye shiryen tafiyarsu suka yini sunayi inda Mummy keta shiko Daddy baka gane yanayinshi don gadai yanan, sosai Mummy ta lura da restlessness dinshi don ko jiya daddare taji yadda yaketa juyi yakasa barci. saida suka shirya komai tsaff aranar ya kasance wayewar gari kawai suke jira suyita tafiya. Washegari Qarfe 1 tayimusu a airport kasancewar jirgin Qarfe 2 zasubi. saida suka gama clearing din komai sukayi sallar zuhr sannan suka shiga jirgin. cikin Dan qanqanin lokacin aka gama duk abinda ya kamata jirgi ya daga sai Dubai✈️✈️✈️ **** Yau ma kamar kingin yan kwanakinnan ganinshi sukayi zaune bisa booth din motarshi. yawan zuwanshi a school din yaja mutane dayawa sanin dashi. kullum Idan sunfito zasu tafi gida saisun ganshi a parking space bisa booth din motarshi yana danne dannen waya saidai tun ranar dayazo da Aysha beqara taremusu mota ba hasalima nesa da motarsu yake parking yanzu. haka zasuzo sushige motar tasu sufice batareda yako dago ba bare ya kalli gefensu kuma suna fita daga school din shima zai diro daga booth din shima yashige motar yabar school din. zirga zirganshi a school din yasa yasamu tarin crushes batareda yasaniba don dayazo yanmata zasu fara parade agabanshi suna kai komo saidai shi ko sau daya be ta6a lura da hakan ba shidai kawai dayayi abinda yakawoshi yake ficewa. yauma ko gefenshi bata kallaba ta zagaya passenger seat tabude tashiga itakuma batool tashiga mazaunin driver don haryanzu zee bata iya mota ba. tada motar tayi tajata suka fice daga school din. suna fita school din tasa speed sosai har suka iso wata corner ta yanka suka shiga ciki dagowa zee tayi ta kalleta cikin ayar tambaya "meye haka?" "shii.." inji batool tana tsaida motar sannan tafito ta xagaya ta budewa zee daketa binta da kallo har lokacin. fitowa zee tayi babu musu batool taja hannunta suka koma farkon corner suka la6e suna leqen waje "wai meye haka ne?" inji zee again "shiii kibari idanunki su gayamaki, ki cigaba da kallon gate din school amsarki na can" inji batool tana qara leqawa itama zee leqawa tayi don ganin Abinda batool din keson tagani daidai nan motar Mussadiq tafito daga school din ta halba kan titi. saurin maido zee dake leqe haryanzu batool tayi suka maqale a garu har motar tazo tawuce dagudun tsiya Ajiyar zuciya batool ta sauke tana dafe zuciyarta "mtcheew, wai menene to? ni banga komai ba" inji zee "bakiga komai ba? bakiga motarshi datazo tawuce ba?" "motar wa?" "Mussadiq mana, dummy" tabata amsa tana wucewa wurin motar tasu "so? meye a wucewar motar?" inji zee tana dan wara hannuwa "gwadamaki nayi saboda ke Mussadiq kezuwa tunda gashi kingani muna fitowa ya fito" inji batool data bude kofar mazauninta tsaki zee taja tana qarasowa itama "shiyasa zaki wani tsaidamu anan? mtcheew wlh wani lokacin Idan kikayi abu kamar aita jibgarki" dariya batool tayi tace "ato, Idan nagayamaki ba yarda zakiyi ba shiyasa na gwadamaki, to wlh is better kinyi warning dinshi yabar zuwa don alamu sun nuna zuwan nan nashi zai iya jawo carryover din mutane dayawa, wlh saikinga yadda yanmata ke crushing akanshi, class dinmu dakinga group of yanmata maganarshi akeyi, yawani zo ya janye hankalin yanmata daga karatu bayan ga exam nata gabatowa da wannan cunkussashiyar fuskarshi" tsaki zee dahar tashiga motar tasake ja tace "nidai don Allah muje, kinwani tsaida mutane akan unnecessary thing bayan kinji tundaxu nakecewa yunwa nakeji, mtcheew nima dai zuciya zanyi na iya motarnnan hakanan" dariya batool tayi tace "dadai yafi don nima na gaji da janki kiwani tilewa mutane babu amfani" harararta zee kawai tayi bata tanka mata ba itakuma ta tada motar suka fito daga corner suka halba titi suma. 🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍 Lokacin dasuka dawo gida sai suka tadda ummy nata aiki kamar mai shirin taryar baqi hakan yasa suka tambayeta tabasu amsa cewa su Aymaan ne ke kan hanya nan da nan batool ta turo baki gaba "ya haka? bakya murna da dawowarsu ne?" inji ummy "dama nasan kinfi sonshi akaina, kawai don yatafi na yan kwanaki ji yadda kike shirye shirye kamar zakiyi tarban wasu sarakuna, dakuma nice nasan bazakiyi wannan zumudin ba" tafada tana qara huro kumatu kallon up & down ummy tayimata tace "yo ke dama zumudin dawowar me zanyi miki bayan tafiyar taki hutune agareni da jan maganarki, dalla kauce min ahanya jare" tafada tana wucewa qara 6ata fuska batool tayi tajuyo ta kalli zee gwalo zee tayimata tana gwalemata idanu sannan tayi hanyar sama tana dariya tana jinta tafashe da kukan shagwa6a tayi wucewarta tana murmushi kaya tafara ragewa tashige toilet ta watsa saboda zafin da akeyi sannan tafito tunanin dawowarsu Aymaan kawai takeyi, tunda suka tafi sau daya sukayi waya lokacin data kirashi tayimashi ya hanya a washegarin tafiyarsu daga ranar basu qara waya ba sai taji kamar bata kyautaba takamata taqara kiranshi ko sau daya ne daga kafadu kawai tayi don aikin gama ya gama tunda harsun taho ma kaya ta chanza tana tunanin wane tsaraba yayi mata, yace zaimata tsarabar dabazata manta ba, to meye shi? nan ma daga kafadu tayi koma menene ai zata.gani Idan sun iso. saida tagama shiryawar sannan tafito daga dakin tayi joining ummy a kitchen itama tayi mammakin ganin girke girken data tadda tanayi, lallai ummy naji da Aymaan, wadannan duk na tarbonshi ne? saida tafara zuba abincin ranarta taja kujera agefe ta zauna tana ci tana taya ummy da fira, saida tagama sannan itama tazo tayi joining Ummin suka cigaba da shirya girkin tana cewa dole batool tayi kishi wannan irin gara da ake shiryawa Aymaan? murmushi kawai ummy tayi batace komai ba don batason zee tasan da zuwansu Daddy tafison abin yazomata as surprise. Sai wajajen magrib suka gama dukkan shirye shiryen nasu suka gyagyara koina gida yaqara extra kyalli, harda batool aka kama wajen aikin bayan tagama kumbure kumburenta saidai every now and then saitayi complaining akan irin uban shirin da akeyi na tarbon Aymaan din. saida suka gama komai sannan suka haura sama don lokacin har anfara kiraye kirayen sallah sai wajajen 8 Abbu yafita da mota don zuwa taryarsu a airport, tun a lokacin batool tafara kokwanto anya Aymaan dinne kadai don bataga dalilin dazaisa Abbu yaje tarbonshi ba a airport kamar wani baqo, shiru tayi kawai ta cigaba da zuba ido tana jiran dawowarsu. suna falo suna kallo suna fira motar Abbu tadawo, ummy ce farkon miqewa kamar wadda aka tsikara tayi waje tana lale lale marhabin nan take suma su zee suka tashi suka takemata baya don ganin kwam lokacin dasuka fito har motar tayi parking mutanen ciki sunfara fitowa kamar a mafarki zee ta hango Mummy tafito daga motar wara manyan idanunta tayi cikin tsananin mammaki tana bude baki lokacin dataga shima Daddy ya zagayo daga dayan 6aren motar wani irin ihu tasaki sannan taruga dagudu saitinsu direct Daddy tanufa tana zuwa ta qaleshi ta maqalqaleshi tana cigaba da ihun murnarta. dariya sosai kowa nawajen keyi ganin yadda take ihu tana tsalle tsalle kamar yar yarinya raba jikinsu tayi taqara kallon Daddy kamar mai son tantance eh shi dinne saikuma taqara rungumeshi tana cigaba da ihun murna tana kiran sunanshi sosai farinciki ya mamaye zuciyar Daddy da bakinshi yaqi rufuwa, ganin diyar tashi yake kamar ba ita ba taqara mashi girma kodon sun jima basu hadu bane? hango Mummy datayi tareda ummy yasata sakin Daddy taruga wajenta itama ta rungumeta tana kiran sunanta cikin tsananin murna murmushi kawai Mummy tayi tana Dan shafa bayanta don ba qarya itama tayi missing dinta sosai suna ahaka batool tazo ta ture zee daga jikin Mummy tana cewa "dalla ya isa hakanan, kinwani bi kin maqalqaleta saikace mummyn takice ke kadai" tafada itama tana rungume mummyn harararta zee tayi takoma wajen Daddy "Daddy shine baka gayamin zakuzo ba?" murmushi Daddy yayi "ai gashi yanzu kinganmu daga sama ko?" "i miss you soo much Daddy!" "miss you more shalele" "to ya isa hakanan, mushiga ciki, sun kwaso gajiya zaku qaramasu wata gajiyar" inji ummy gabadaya suka dunguma suka nufi ciki Zainab still a maqale jikin Daddy binsu da kallo Aymaan da babu wanda yayi ta tashi yayi saiya girgiza kai yanufi booth yafara sauko kayan ciki muryar batool ce ta katseshi daga abinda yakeyi "oyoyo Akhie! ashe harda kai aka dawo? wlh nama manta dakai akayi tafiyar sai yanzu dana hangoka" wata lafiyayyar harara ya makamata ya cigaba da fiddo kayan "da fatan dai kayomin tsarabobi na don ina ganinka naji babu Abinda nake kwadayi kamar goruba" daukar jakka daya yayi ya rataya yajawo dayan trolley din yanufota juyawa tayi saurin yi tanufi cikin gidan dagudu don tasan Idan ya kamata saita gane kurenta a tsaitsaye a falo batool ta taddasu hakan yasa ta qaraso da sauri jim kadan saiga Aymaan shima yashigo bude baki ummy tayi sannan tace "Allah sarki, wlh na manta dakai" 6ata fuska Aymaan yayi yaqaraso dakin yana cewa "ai dama nasan ba'aji dani" dariya duk sukayi daidai lokacin zee ta dago suka hada ido da Aymaan wani kyakyawan murmushi tasakar mashi wanda yakusan melting zuciyarshi, hakanan tayi hasashen qila wannan shine tsarabar dayace zaiyi mata wato ya kawomata su Daddy shima mayarmata martanin murmushinta yayi yana jin wani sanyin farinciki na ratsa zuciyarshi sannan yayi hanyar sama yana cewa "to nidai na haye kafin gajiya ta kadani" Jin hakan yasa Abbu cewa suma su Mummy arakasu masaukinsu su Dan huta kafin sufito cin abinci su zee suka rakasu har masaukin nasu dayasha gyara sai qamshi yake badon zee tasoba suka juyo suka barsu don sudanyi freshning up basu dade ba suka sake dawowa main falo din inda suka dunguma gabadaya sukayi dining inda aka baje kolin girke girken da akayimusu kowa yashiga kwasa fira ce sosai ta 6arke a tsakanin wadannan families din biyu, hira suke cikin raha da barkwanci, zee haryanzu tana maqale kusada daddynta murmushi yaqi barin fuskarta shima aymaan sosai ake firar dashi don nan take fara'arshi da surutunshi yadawo kamar bashine yakoma wani dunkum ba a Nigeria sun raba dare sosai atare suna maida yadda akayi saida sukaga barci yafara cin qarfinsu sannan suka haqura kowa yaje ya kwanta. *WASHEGARI* Ranar fashin school sukayi sukaqi zuwa sai sukayi qaryar basuda lecture ranar Haka sukayi zamansu suna aikin bude tsarabobin dasu Mummy sukayi musu suna hira cikin nishadi Mummy kau dik inda zee ta gifta saita bita da kallocikin sha'awa don taga zee taqara hankali sosai kamar ba itaba ga kuma tausayinta datakeji a qasan zuciyarta don sosai taji dadin yadda ta taimakama Deen batareda tayi la'akari da Abinda yayi mata ba, that's shows tanada good heart. sai bayan asr Ahmad shima yaduro gidan. dama jiya tun a airport suka rabu shi yawuce gida kasancewar dare yayi lokacin kuma dama yayimusu alqawarin zai dawo yau don akwai zaman da Daddy keso suyi ayau din. bayan sun gama gaigaisawa cikin mutunci shima ya zauna aka dasa firar daga inda ta tsaya. can Daddy yayi gyaran murya wanda ya tattaro hankalin kowa zuwa wajenshi suka zubamashi ido cikin son jin mai zaice "to Alhamdullilah, muna godewa Allah daya hadamu cikin aminci da qoshin lfy muna kuma roqonshi ya cigaba da wanzarda farinciki da hadin kai atsakaninmu" "wannan zaman namu yanada.dalili koko ince zuwanmu qasarnan ma gabadaya, wasu acikinku sunsan dalilin wasu kuma basu saniba ammazasu sani very soon inshaAllah. amma dafarko zanfara nuna jinjina da yabawa ga jajircewar wadannan samarin biyu wajen qoqarinsu na aikin qwarai dasuka sanyo gaba, haqiqa kun cancanci yabo akan jarumta da nargartattun halaye naku kuma muna fatan Allah yabiyaku yasaka maku da alhairinsa" duk da Amin aka ansa wasu kuma kamar irinsu zee da batool basusan inda zancen yadosa ba haryanzu "Aymaan da Ahmad sunje Nigeria akan wani aiki, aikin da babu mai iya biyansu sai Allah, kuma muna fatan Allah yabamu nasara yakawo mamu warwarewar wannan al'amari. sunyi mana bayani, bayanin da nasan kowa anan yasanshi kuma mun gamsu hakan yasama muma muka shirya mukazo nan don ida warware matsalar dukda badamu aka faraba" zee dai kallon Daddy take very confused don haryanzu takasa gane inda ya dosa kamar ance ta dago kai sai sukayi ido hudu da Aymaan dake kallonta tundazu wani guntun murmushi yaimata kawai ya dauke kai "ga wadanda suka sani dakuma wadanda basu saniba ina farincikin sanardaku bayyanar KAMALDEEN MUHAMMAD wato DEEN" wani irin bugawa zuciyar zee tayi har saida ta dafe saitin zuciyar tana miqewa tsaye batareda tasaniba gasping batool tayi tana wara idanu kamar zasu fado cikin tsananin shock murmushi Daddy yayi yana kallon zee dake tsaye haryanzu hannunta a saitin zuciyarta idanunta a ware tana kallonshi "yes daughter, Deen is back. Deen yadawo, yana Nigeria. can su Aymaan sukaje kuma sun ganshi sunyi magana dashi" girgiza kai zee take unbelievabling tanajin komai a mafarki tanason yin magana amma takasa "eh Zainab, Deen ya bayyana, munsan inda yake. yana Abuja yazama mawaqi, munso mugayamaki tunda wuri amma muka yanke shawarar fara confirming.komai sannan, Deen ya bayyana, na ganshi Aymaan ma ya ganshi, munyi magana dashi" cigaba da girgiza kai zee tayi don sam zee bata yarda ba, dole wani suka gani, wani mai kamadashi kokuma Mussadiq, yes qila Mussadiq suka gani sukayi tunanin Deen ne "m..mussadiq ne" tafada cikin wata murya mai rawa sosai "A'a Zainab, ba Mussadiq bane, Deen ne. look.. duba dakanki kigani" yafada yana fiddo wata laptop yabude duk zubamashi idanu sukayi in curiosity harya gama yan danne dannenshi ya juyomasu ya ajiye akan stool din kusadashi yayinda image din laptop din yafito tarr kowa na falon nagani waqa ce ta video da sajenshi tafara tozali kasancewar gefen fuskarshi akafara haskowa bugun zuciyarta ne ya ninku lokacin da aka hasko pink lips dinshi wadanda bazata ta6a qin ganesu ba daidai lokacin lips din suka fara motsawa cikin salon waqa _karki barni.. sahibata_ _karki qini... ki fahimta_ _sai dakee... zani huta_ _zuciyata ga kece ta lalla6o_ _ta amince ki maidata yar dako_ _kinga qaunarki taimun riqon la6o_ _wani reshe ya kama ya jijjigo_ zee batasan sadda takoma kan kujerar data tashi ba jagwab lokacin datayi tozali da full face din Deen din. _kingani ban iyawa da So haka_ _magani zaki ban don na waraka_ _kinga ya maidani wani sa d'aka_ _yafi qarfina sai yaita ha66aka_ _tunda nabaki raina da zuciyaa!_ _me kikeso nayimiki zan iyaa!_ _yau dake gobe na shaida tunjiyaa_ _kinga nazam kamar marar lafiyaa_ _zuciyata ❤️ tanaimun bugun tara💗_ _gashi nikuma naqi na haqura_ _dukda nasha wuya bani daddara_ _kai bala'i na So🤍 nada takura😭_ _wai ina kika jene masoyiyaa!_ _nayi nemanki naqara tambaya!!_ _har wadansu sunaimini dariya😔_ _ni bazan daina sonki ba kinjiya_ _dukda yasani ban jiyo Dan kira_ _tallafa min kissamini lafiya🙏🏻😭_ (sai dake ? hamisu breaker) Ummin fasihu🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:43 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *079* *wannan page din nakine takwara, nagode da ziyarar jiya fatan kun koma gida lafiya🥰* Rufe baki batool tayi da hannunta dake dan 6ari idanunta cikeda kwalla, she's shocked Idan akwai kalmar datafi shock ma tayishi. she can't believe Deen ne wannan, she can't believe Deen is back! dauke idanunta tayi daga screen din laptop din takalli saitin zee haryanzu zaune take inda take motionless, idanunta dasuka sauya launi kafe a screen din babu ko kyaftawa haka suka cigaba da kallo har waqar taqare kowa Juyowa yayi yana kallon zee don ganin reaction dinta amma haryanzu tana a yadda take yadda kasan statue "munfara ganinshi ne ta media, mawaqine sosai wanda ke zamani. yana xaune a Abuja kuma acan yake gudanar da rayuwarshi, wannan tafiyar ma damukayi duk don muganshi ne kuma muga inda yake yadda komai zaizo mana da sauqi" inji Ahmad yana kallon zee Aymaan kau hannunshi ne rungume a qirji ya sadda kai qasa bakama ganin fuskarshi bare kasan halin dayake ciki. kuka ne ya kufcema batool tayi saurin rungume zee dake gefenta tanayi ahankali "Zee Deen is back"tafada cikin rawar murya tana qara qanqame zee dahar yanzu batayi motsiba ganin batace komai ba yasa batool dan sakinta ta dago ta kalleta ganin still idanunta na saitin laptop saita sa hannu tajuyo fuskar saitinta "kinji zee, Deen is back, say something. abun farinciki ne right? abun farinciki ne" inji batool tana hawaye sosai kallonta zee kawai keyi batace komai ba sai gangarowa da hawayen dake maqale a idanunta sukayi ahankali tasa hannu ta janye hannayen batool daga riqon datayiwa fuskarta ta miqe ahankali kowa dagowa yayi yana kallonta harda Aymaan da shima idanunshi sun chanza launi sosai ahankali tafara takawa ta wuce ta nufi stairs ahankali Aymaan daya lura da yanayin tafiyarta ya miqe idanunshi akanta takai bakin stairs ta daga kafa kenan zata fara taka stairs din wani wawan jiri ya dibeta tayi baya baya Aymaan da dama kamar yasan da hakan yayi wuff cikin zafin nama ya qarasa kafin takai qasa ya tarota tafado jikinshi har yana durqushewa akan gwiwa daya farr farr idanunta keyi kamar mai qoqarin budesu yayinda sukuma suke rufewa kafe fuskarta Aymaan yayi na kallo yana jin yadda jijjiyoyin kanshi ke tashi rudu rudu "Zainab.." yafada ahankali kamar a rad'a "Deen..." itama tafada ahankali daidai lokacin da idanunta suka ida rufewa ruff tsayawa yayi yana kallon fuskarta kawai batareda ya iya ko motsawaba kingin yan dakin ne suka qaraso wajen a gigice kowa na kiran sunanta. dagudu batool tadawo hannunta riqeda bottle water ummy ta amsa aka bude murfin aka shashafamata ruwan a fuska amma shiru qara yayyafamata sukayi nanma ko motsi batayi ba ganin hakan yasa Aymaan dake jin kanshi kamar zai rabe gida biyu don sara yunqurawa ya tashi daita a hannunshi hanyar fita falo yanufa hakan yasa Ahmad saurin ficewa yanufi parking space. kafin Aymaan ya isa harya bude mashi back seat Aymaan ya sunkuya ya sakata ciki sannan ya nufi gaban motar yana barma su ummy kofar bayan bude don su shiga. ummy da Mummy ne suka shiga bayan while Aymaan da Ahmad ke gaba sukuma Daddy suka hau dayar motar tareda batool daketa qoqarin dakatar da hawayenta cikin qanqanin lokaci suka fice daga gidan suka nufi hospital din da Aymaan ke aiki. babu 6ata lokaci aka kar6eta aka kuma shiga bata taimakon gaggawa Aymaan baya cikin likitocin dake dubata don suna kaita dakin da aka kwantar daita yafice daga asibitin su ummy sune suka zauna waje jugum kowa abin duniya ya dameshi ba'a dade ba akafara kiraye kirayen sallar magrib hakan yasa duk mazan suka wuce massalaci suka bar matan anan. dawowarsu daga massalacin yayi daidai da fitowar likitocin daga dakin da aka kwantar da zee saurin qarasawa sukayi suna tambayar yadda ake ciki ataqaice suka amsamasu yanzu komai yayi daidai amma zasuso ganin mahaifanta personally a office Abbu da Daddy suka bisu suka wuce office din. bayani marar dadi likitocin suka basu na hawan jinin zee daya qara tashi ya hau sosai sunkuma sanar dasu damuwa tayimata yawa har abin na neman ta6amata zuciya shawarwari suka basu na yadda yakamata su bar barinta tana shiga damuwa domin hakan ba qaramin illa bane agareta yanzu sannan sukace zasu daurata akan magani wanda zai taimaka mata sosai akan halin datake ciki. sosai jikinsu yayi sanyi sunajin badadi sosai Abbu ne yayi qarfin halin tambayarsu halin datake ciki yanzu sukace yanzu sun shawo kan komai don yanzu haka barci take sanaddiyar allurai da akayimata. sosai suka qara yimasu bayanai akan ciwon zee din da shawarwaru sannan suka shaidamusu mutum daya kawai za'abari yayi jinyarta kingin saidai sukoma gida. Tare da likitocin suka sake fitowa daga office din suka nufa ward din da aka kwantar da zee din gabadaya a kwance suka taddata tana sauke numfashin barci ahankali hannunta daure da drip babu wanda be tausayamata ba a wannan halin don she looks so pale kamar wadda tayi wata tana jinya. basu dade ba aciki suka fito waje inda anan suka hau shawarar wadda za'a bari wajenta tunda sunce mutum daya suke buqata. daga qarshe dai ummy aka bari daita kingin duk suka fito zasu gida batool sai 6atarai take don ita da so samune ta zauna. haka suka bar asibitin cikin nauyin zuciya da jimami kowanne tausayinta danqare a zuciyarshi. koda suka isa gida kowa shigewa yayi part dinshi kasancewar dare yayi hakan yasa kowa shigewa sashenshi with heavy heart. batool na zaune bisa sallaya bayan tagama sallolinta wayatafara Ringing waigawa tayi taga wayar zee dake kan mirror ke Ringing din tashi tayi ta dauka da niyyar kasheta amma ganin mai kiran yasata dakatawa kallon wayar ta cigaba dayi tana shawarar ta daga ne koko ganin zata tsinke yasata saurin dagawa ta kara a kunne "Aslm Ummie na" inji Aysha daga dayan bangaren "wslm Ayush" inji batool cikin son daidaita yanayinta "laa sis batool, ya kike" "lfy lau, ya kike yasu Ummie?" "duk lfy, ina mutuniyar?" Dan shiru batool tayi saikuma tace "oh tayi barci" "barci yanzu? this is just to 9" "ai... qila agajiye takene shiyasa" tafada adan daburce don dama batool bata iya qarya ba Dan shiru Aysha tayi can tace "this is not true, gayamin meke faruwa? ina Ummie?" "ai...ai gaskiya nake.." "no sis batool kada muyi haka dake, kifadamin gaskiya please, tsakaninki da Allah ina Ummie?" rolling idanu batool tayi, batajin tana iyayin qarya kuma bayan ta hadata da Allah Ajiyar zuciya ta sauke "tana hospital" "what!!" "erm... look da sauki sosai kawai dan zazza6ine bawani abu ba" "innalillahi waina ilaihi rajiun, wane hospital? meya sameta?" tafada hankali tashe "zazza6ine kawai kuma nace miki dasauqi" "wane hospital take?" "A-shifa'u hospital amma nama san gobe za'a sallame... hello? hello?" ina har an katse kiran sauke wayar tayi daga kunnenta tana sauke Ajiyar zuciya ahankali. *** ahankali ya murda handle din kofar ya turo ahankali batareda tayi qara ba sannan yashigo shima hango ummy yayi saman dayan gadon wanda dama na masu jinya ne tana barci ida qarasowa yayi dakin idanunshi akanta har saida yazo gabb da gadonta kafe fuskarta datayi fayau yayi da idanunshi dasukayi ciki ciki ya dade sosai ahakan kafin ya motsa yabar wajen yanufi yar locker kusada gadonta ya dauki file din dake kai ya bude yashiga going through dinshi saida yagama sannan ya maida ya ajiye ya gyaramata tafiyar ruwan drip din sannan yajuya yafice daga dakin as quietly as he entered *WASHEGARI* Da wuri mutanen gidansu batool suka bar gidan suka nufi hospital don dama jinsu suke kamar akan qaya, saida suka hadama yan asibitin breakfast sannan suka fito suka hade dasu Daddy suka kamo hanya. lokacin dasuka isa har lokacin zee bata farka ba amma likitocin sun tabbatar musu komai is normal kawai alluran ne basu gama sakinta ba. haka suka zauna don ana barin zama a ward din suna fira wanda duk ta Deen ce da zee. suna ahakan har wajajen 11am lokacin harda su Daddy cikin ward din aka kwankwaso kofa izinin shigowa sukabada don sunyi tunanin Ahmad ne ko Aymaan dukda Aymaan din be dade da fita ba murda kofar akayi aka turo Dan wara idanu batool tayi ganin mai shigowar Aysha ce sanye cikin milk abaya tayi irin shigarsu ta larabawa saidai fuskarnan dauke take da alamar damuwa mammaki ne yakama batool don ita tama manta dawata wayar dasukayi daita jiya mammaki be ida kasheta ba saida Aysha tashigo na bayanta ya bayyana sakin baki tayi cikin tsananin mammaki bama ita kadai ba harda dukkan mutanen dakin zuciyar Daddy da Mummy sukayi wata iriyar faduwa lokacin da idanunsu sukayi tozali dashi sanye yake cikin simple qanannun kaya sa6anin suit da aka saba ganinshi dasu saidai wannan baqin tabarau din nashi na gado nanan maqale da idanunshi kowa na dakin idanunshi nakanshi yayinda shikuma idanunshi ke kanta ya kafeta dasu babu kyaftawa. gaisuwar Aysha ta dawo dasu daga duniyar kallon Mussadiq duk suka maido hankalinsu kanta yan dakin suka shiga amsa gaisuwar tata banda Mummy data kafe Aysha itama da kallo tana ganin wasu qanannun qanannun kammaninsu da Deen kama daga coolness din muryarta da dimple dinta na tsakiyar gemu mai lotsawa koda magana take. kasa janye idanu Mummy tayi akanta tanajin zuciyarta na melting ahankali cikin shauqi, tabbas wadannan jinin Deen ne ko makaho tashafa saiya gane. cikin damuwa Aysha tawuce gefen zee dake kwance takama hannunta ahankali tana tambayarsu yamai jiki asanyaye kamar mai shirin kuka cikin sigar kwantar da hankali su ummy ke amsamata cewa da sauqi sosai yanzu ma barci take. shiru Aysha tayi tana kallon fuskar zee kamar zatayi kuka don ganinta a wannan condition din ba qaramin ta6ata yayi ba. ahankali shima Mussadiq dake bakin kofa har lokacin qarasowa dakin idanunshi dake lullu6e da tabarau akan sleeping zee Daddy har wani dauke numfashi yayi saboda Juyowa dayayi ya kalleshi cikin alamun girmamawa yadan russunar dakai yace "good morning" ataqaice dafarko kasa amsawa Daddy yayi saboda rikicewa saikuma yasamu ya fizgo muryarshi dakyar yace "y..yes, g..good morning" be qara bi takanshi ba yawuce wajenda su ummy ke zaune suma yashiga gaidasu cikin turancinshi mai slant din Arab ganin hakan yasa Daddy saurin juyawa daga dakin ya bude kofa yafita duk arikice. amsawa su ummy da Mummy data kasa janye idanu akanshi sukayi, gani take kamar batun wannan na gabansu ba Deen bane ba qaryane don itadai idanunta Deen yake gwadamata tambayarsu yayi jikin mai jiki suka amsamashi cikin fara'a daga nan yaja bakinshi yayi shiru. batool ce ta dago tadan saci kallonshi sannan ta gaidashi beko kalli gefenta ba ya amsa ahankali ya cigaba da tsayuwarshi yana kallon zee dake barcinta ahankali "Aysha meet Mummy, maman zee" inji batool tana nuna Mummy tare suka kalli Mummy da Aysha da Mussadiq wara idanu Aysha tayi cikin mammaki "really?" kada mata kai batool tayi hakan yasa Aysha wucewa wajen Mummy dasauri tayimata side hug cikin jindadi tana dariya wani farinciki ya kama Mummy itama tanata murmushi suka shiga sabuwar gaisawa Aysha na tambayarta ya Nigeria kuma yaushe sukaxo Mummy na amsa mata. ummy ce tadago ta kalli Mussadiq dake tsaye daga nesa dasu kamar wani saqago cikin larabci tace mashi "ko ka iya cire drip kunga yaqare gashi basu shigo ba" kallonta yayi saikuma yakalli drip din sannan ahankali ya qarasa wajen batareda yace komai ba duk binshi da kallo sukayi harya qaraso yafara cire drip din daga cannula din hannun zee yana cikin hakan idanun zee suka fara motsi arufen dasuke shidai Mussadiq belura ba don hankalinshi nakan Abinda yakeyi ahankali tafara bude idanunta dake ganin biji biji harsuka ida budewa tangaram again wannan fuskar ita taqara yin arba dashi kafe gefen fuskar tashi tayi da ido babu ko kyaftawa harya gama yajuyo shima ya kalleta suka hada ido. Shima kasa dauke idanunshi yayi akanta suka kafe juna da idanu na wani lokaci tunawa dayayi akwai mutane a dakin yasashi saurin janye idanunshi daga kanta yajuya zai wuce caraff yaji an cafko hannunshi wanda hakan yasashi tsaya cak daga tafiyarshi Dan shiru yayi sai kuma yafara Juyowa ahankali harya ida Juyowa ya sauke idanunshi cikin nata dake qyallin hawaye tsayawa yayi yana kallonta kawai batareda ya iya amsar hannunshi daga nata ba. "Deen..." tafada in whisper...✍? *kuyi hqr, haryanzu jikin sai a slow, acigaba dasani a du'a🙏🏻* Ummin fasihu🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:43 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *080* ahankali yasa hannu yaxare glasses din idanunshi yana kafeta da oily eyes kamar wadda idanun suka tunama wani abu saitafara releasing hannun nashi ahankali still idanunsu acikin najuna dukkan mutanen dakin idanunsu na kansu not moving "waye shi?" yafada ahankali idanunshi anata kowa wara idanu yayi yana kallonshi in outmost shock "who is Deen?" yaqara tambaya yana kallon tsakiyar idanunta bazai manta ba farkon haduwarshi daita Abinda takirashi kenan, wancan haduwar tasu a library ma ta kirashi da hakan and know? waye mai wannan sunan? meyasa Idan ta ambaci sunan saitayi hawaye? su ummy ko kallonsu suke hankali a mugun tashe kowa yakasa motsi "tell me, who the hell is he!" yafada da Dan qarfi idanunshi na dan sauya launi "hey Mr, incase ka manta this is hospital ba filin kasuwanciba" Juyowa duk sukayi suna kallon Aymaan dake tsaye bakin kofar ward din hannunshi zube a aljihu wani qololon baqinciki ya tsayawa Mussadiq awuya daga ganinshi hakan yasashi jan guntun tsaki yajuya ya cigaba da kallon zee data maida idanunta ta lumshe "Ummie..." "muna buqatar kowa yafita don zamu dubata" yaqara jin muryar Aymaan na katseshi da hakan su ummy dai kasa cewa komai sukayi sai binsu da kallo dasuke da daddaya ignoring dinshi Mussadiq yayi ya cigaba da kallon zee "are you ok?" "wannan likitan ta zai iya gane hakan wanda hakan zai yiwuwu ne Idan kuka bashi wuri ya dubata, don't ask her if she's ok cos you can only get the answer from her doctor.. that is Me" inji Aymaan yana qarasowa gaban gadon shima Juyowa Mussadiq yayi yana kallonshi in the eye sternfully shima Aymaan na maida martanin irin kallon yadda kasan zakaru biyu masu shirin afkawa juna kingin mutanen dakin kallonsu kawai suke sunkasa cewa komai kowa da Abinda ke jeka kadawo a zuciyarshi Mummy ce tayi qarfin halin tankawa ta hanyar cewa "it ok, Bari mufita dama tunda ta tashi kamata yayi adubata, batool, daughter kutaso mukoma waje" tafada reffering to Aysha da batool kamar jira sukayi duk sai suka tashi harda ummy sukayi waje har lokacin da Aymaan da Mussadiq basu Bar jifan juna da mugun kallon dasukeyi ba can ahankali Mussadiq ya maida shade dinshi yana cije lower lip dinshi sannan shima yajuya yafice daga ward din kamar zai tashi sama da kallo Aymaan da zee suka bishi harya fita. Dan tsaki Aymaan yaja sannan yajuyo ya kalli zee, sauke idanunta zee tayi kawai batareda tace komai ba qarasowa gefen gadon yayi yana kallonta "ya jikin?" yafada yana zura hannu daya a aljihu idanunshi kanta kadamashi kai kawai tayi batareda tace komai ba shima batareda yasake cewa komai ba yashiga dubata saida yagama sannan yadanja baya yana sauke abin kunnenshi qasa ya dauki file dinta ya ciro pen yafara rubutu "I hope kinsan condition din heart dinki" dagowa tayi takalleshi taga hankalinshi ma na kan rubutun dayake "Idan ta cigaba da samun attack irin wannan am sorry to say komai na iya faruwa... ciki harda bugawarta" sauke idanunta tayi batace komai ba "the heart is the strongest organ of the body and at the same time the most fragile organ, ya danganta da yanayin datake ciki at the particular time, saidai akowanne yanayi take yakamata mai ita yasan cewa it's the most important organ that without it no other organcan perform it's function" daidai nan yadago ya kalleta yaga itama shi take kallo "without out heart there will be no life, tana bugawane tareda rayuwa, tana tsayawa rayuwa ma zata tsaya.. cak kamar tsayuwar agogo" still idanunsu nacikin najuna "mutuwa abuce data zama dole, mutuwa ta sanaddiyar bugawar zuciya is very normal don mutuwa daya ce amma silolinta nada yawa kuma bugawar zuciya na daya daga cikinsu Don haka don zuciyar mutum tabuga yamutu abune da bazai zama na alhini ba... saidai Idan zuciyar tabuga a dalilin Abinda be cancanci bugawar zuciyar ba ko akan wanda be cancanta ba.. za'a kira hakan ne bada tsautsayi ba saidai ganganci" kallonshi take sosai lokaci guda kuma hawaye suka fara taruwa a large eyes dinta "zaya mutu ne akan wanda be cancanci hakan ba yabar wadanda suka cancanci hakan, wadanda kullum burinsu farincikinshi, walwala da nishadi. wadanda suke iya sadaukar da komai akanshi tunkafin yazo duniya har yashigo duniyar har wannan lokacin dayake qoqarin wancakalar da rayuwarshi akan wani abin daban.. har abada" "zaya tafi yabarsu suna baqinciki, baqincikin da wanda yatafi dominshi bazaiyi rabin rabinshi ba saboda shi bashida asara ko yanada ita yar kadan ce batakai ta wadannan mutanen ba... kuma ba kowa bane wadannan mutanen face IYAYE" "Iyayenka ne zasu iya xama dakai akowane irin yanayi, suyi sharing kowane feeling dakai, farinciki? baqinciki? qunci? damuwa? komai. kuma duk lalacewarka bazasu ta6a rabuwa dakaiba duk wahalar dakake basu bazasu ta6a yin watsi dakai ba.. duk runtsi" "wadannan mutanen?.. su ya kamata mutum yafara sawa agabanshi, yafara duba wane hali zasu shiga Idan har ya aikata wani abin bawai mu rufe zuciyarmu ba mu makance qarshe muzo muyi Abinda zaiyi hurting our beloved ones na har abada" Dan shiru yayi yana kallon yadda hawayenta yaqi tsayawa Dan murmushi yayi yana sauke idanunshi kan file din dake kan locker haryanzu "hawaye... wani lokacin rahamane domin yana gangarowane tareda kaso mafi yawa na damuwa amma Idan yayi yawa harya rikida yakoma jini yana zama babban illa.. ga zuciya da gangar jiki gabadaya" sake dora pen yayi kan file din yasake yan rubuce rubuce sannan ya maida yarufe dagowa yayi batareda yasake kallonta ba yace "za'a doraki akan magani, please endeavor to take them at the right time ko don beloved ones dake damuwa da damuwarki" yana kaiwa nan yajuya yanufi kofa. binshi da kallo tayi da rinnanun idanunta harya fice fashewa tayi da wani kuka mai tsuma zuciya tajawo pillon kusada ita ta cusa fuskarta aciki tana cigaba dayi. *** A bangaren Mussadiq kuwa yana fitowa beko kalli kowa ba yanufi hanyar fita daga wajen. sosai ranshi ke a 6ace don ba qaramin qonamashi rai Abinda Aymaan yayimashi yayi ba. harshi zai mashi taqama da matsayinshi? harshi zai koro waje don kawai taqamarshi shi likita? a stairs suka kusa cin karo da Daddy dake tareda Abbu suma sun karyo kwana saurin sake dauke numfashi Daddy yayi ganin kamar ya kalloshi ya kauda kai har Mussadiq da 6acin rai bemasa yawani tantancesu ba yayi wucewarshi sauke numfashi yayi nannauya yana bin bayanshi da kallo sannan yajuyo gun Abbu dake kallonshi "lafiya daiko?" inji Abbu "lfy... kawai Idan nadora idanuna akanshi.. sainaga kamar Deen ne" inji Daddy yana qara bin inda Mussadiq yabi da kallo murmushi Abbu yayi yace "ai ikon Allahn kenan, wani abin saisun hadu su biyun ankasa tantancesu, Allah dai ya nunamana ranar" "Amin" inji Daddy sannan suka wuce saman Direct parking space din asibitin Mussadiq yanufa ya nufi motarshi ya bude yashige ya maido ya rufe yadda yake abubbuwa da qarfi zaisa kagane har lokacin afusace yake saida yashiga motar sannan yatuna ashe tare suke da Aysha dogon tsaki yaja sannan yazaro wayarshi ya lalubo numberta yayi dialing Ringing biyu aka daga cikin larabci yafara yimata bala'i kamar zai jawota ta wayar ya daka (nidai bansan meyake cewa ba🙁) can ya katse kiran yana sake jan wani tsakin yakoma jikin kujerar motar ya rungume hannayenshi a qirji Idan akwai wanda kebashi haushi duniya to saidai yabiyo bayan Aymaan, yarasa dalilin da tun a haduwarsu nafarko yaji bemashi ba, he just hate him for no reason. *Deen?* waye Deen? meyasa zee ke yawan ambatar wannan sunan? meyasa take kuka duk lokacin datake ambatar sunan? dole yagano kowaye? dole yagano dalilin kukanta akodayaushe akanshi. rungume hannayenshi yayi yana saqa da warwara shikadai. sauke wayar tayi daga kunnenta jiki asanyaye sannan ta kalli su Mummy "erm... I think I have to go" tafada asanyaye "tun yanzu?" inji batool tana matsowa kusada ita ahankali ta kada kai cikin damuwa "Akhie ne... yace nafito.. qila akwai inda zashi" tafada asanyaye murmushi Mummy tayimata tace "ayyah, ai mungode qwarai ma. kiyi sauri to karku tsaidashi, batool ki rakata" da to batool ta amsa tana gyara mayafinta ajiye ledar hannunta Aysha tayi tace "Allah ya sawwaqe, insha Allah zan dawo" "to mungode qwarai ki gaida Ummie qwarai kinji?" inji ummy cikin kulawa kada kai tayi tana murmushi sannan suka juya tareda batool suka wuce Tafiya suke basu cewa komai saidai batool ta lura kamar Aysha tana cikin damuwa "yadai?" inji batool tana kallonta Dan murmushi kawai Aysha tayi batace komai ba "karfa kidamu, insha Allah taji sauqi, trust her she's strong, danasan hakan zaki damu da ban gayamaki ba tunfarko" murmushi Aysha tayi tace "I want to see her before I leave, kinga fa tafarka yakamata naganta kafin natafi" Dan shiru batool tayi kamar mai tunani sai can tace "in that case muje mugani nasan yaya bazai hanaba iyaka yayimana warning yace karmuyi hayaniya" cikin jindadi Aysha tace "yes! let's go please" ida qarasawa bakin ward din zee din sukayi, saboda zumudi Aysha ce agaba murda handle din tayi tatura tasawo kai daidai lokacin da shima yasawo nashi sai jikake quuum! sun qume. saurin jabaya tayi tana dafe goshi cikin jin zafi kamar yadda shima yayi alokaci daya suka dago suka kalli juna "ya sallam! sannu, bigewa kukayi?" inji batool data qaraso wajen ahankali yanayin Aymaan ya chanza lokacin daya gane ko wacece Aysha saiya hade rai yana qarasa fitowa yajawo kofar Aysha data lura da sudden chanjin fuskar saitayi tunanin ko laifinta ne dasuka qumen hakan yasata cewa "sorry" "same" ya amsa sama sama batareda yasake kallonta ba ganin zai wuce yasa batool saurin cewa "amm.. yaya wai da ganin zee zatayi kafin tatafi, tafiya zatayi" Dan Juyowa yayi yadan kallesu sannan yace "saidai wani lokacin amma yanzu ba'a yarda wani yashiga ba" daga hakan yajuya yawuce suka bishi da kallo cikin rashin jindadi batool takalli Aysha "sorry" Dan murmushi Aysha tayi tace "babu komai ai zan dawo, muje Akhie najira" Juyawa sukayi suka nufi hanyar ficewa daga asibitin lokacin dasuka isa parking space Mussadiq yakusan bindiga, tun daga nesa yake jifansu dawani mugun kallo ganin hakan yasa batool dakatawa tun kafin su qarasa sukayi bankwana qarasawa Aysha tayi ta zagaya tashige motar yaja kamar dama shigowarta yake jira suka fice a tamanin ta6e baki batool tayi tajuya itama tanufi cikin gida...✍? *ya hqr dani🙁 adai cigaba da wanke hannu ana tayamu du'ai wlh aljannun typing dina sunfara kawo gardama😆 anemo masu ruqiya🤣🤣* Ummin fasihu🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:44 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *081* Inda su mummy suke aymaan yanufa ya taddasu zazzaune hardasu daddy dabasu dade da isa wajen ba duk dagowa sukayi daga firar dasuke suna kallonshi shikuma yaqaraso yana murmushi "likita bokan turai, fatan dai diyar tawa tana lfy" inji abbu murmushi yasakeyi "eh komai normal, yanzu abinda xataci za'a samarmata taci saitasha magani" masha allah duk suka fada cikin jindadi daddy yadora da "sannu da qoqari d'ana, allah yayi albarka wa rayuwa" duk da amin suka amsa banda aymaan dayayi murmushi Kawai "to yanzu muna iya shiga ko? dazu kawani koromu waje ko yar kararnan babu" inji ummy tana harararshi dariya duk sukayi daddy yace "ato ai gwara hakan idan kuna ciki ba lallai bane kubari yayi aikinshi yadda ya kamata ba" shidai murmushi aymaan yayi bece komai ba tashi duk sukayi zasu wuce ward din daidai nan batool data dawo daga rakiyar aysha tayi joining dinsu "ina zaku mummy?" "wajen zainab, we can see her now" kallon aymaan tayi cikin mammaki, ba yanzu yace ba'a buqatar kowa cikiba? mugun kallon daya watsamata yasata kauda kai tana dan turo baki sannan tajuya tabisu mummy da har sun wuce Jin alamun za'a bude kofar yasa zee saurin share fuskarta ta maida idanunta ta rufe Jin muryoyinsu mummy adakin yasata bude idanun dasukayi ja tana kallonsu harsuka qaraso wajenta duk sannu suka shiga yimata kowa namata kallon tausayi kowanne damuwa qarara a fuskarshi ahankali take kada masu kai tana dan murmushi cikin dan qanqanin lokaci aka hadamata kakkauran shayi aka bata don tasha babu musu ta amsa tana sha tana kallon yadda kowa ke qoqarin kyautata mata don sata farinciki *sune zasu iya zama dakai akowane irin yanayi, suyi sharing kowane feeling dakai, farinciki? baqinciki? qunci? damuwa? komai.* maganar aymaan tadazu tadawo mata a kwalwa *wadannan mutanen?.. su ya kamata mutum yafara sawa agaba, yafara duba wane hali zasu shiga idan ya aikata wani abin bawai mu rufe zuciyarmu ba mu makance qarshe muzo muyi abinda zaiyi hurting our beloved ones na har abada* Dan lumshe idanu tayi tasake budesu. tabbas aymaan yayi gaskiya, meyasa kullum takeyin abinda daga qarshe beloved ones dinta ke finta shan wahala? meyasa kodayaushe take saka beloved ones dinta cikin damuwa? meyasa take sakasu a wahala bayan wanda takeyi donshi bemasan tanayi ba? imagine? he's a musician, famous musician while ita tananan tanason kashe kanta awofi tunawa tayi tun bayan barowarta Nigeria wanda yanzu almost 1year ne babu wani abin kirkin data ta6uka illa 6ata lokacinta, tunaninta da tsaddadun hawayenta ga wanda qila yanzu bayama iya recalling sunanta ita tananan tana hauka akanshi tana 6ata lokacinta akanshi while shi yanacan yayi moving on harya zama wani abin acan how foolish is she? jitayi ma ta tsani komai ma, ta tsani asibitin ma, idan ta tuna saboda shi take kwance akan gadon datake akai saitaji wani baqinciki yaqara mamaye zuciyarta maganinta akabata ta kar6a ta shanye sannan takoma jikin pillon da aka taramata abaya ta jingina "are you ok now ko kina buqatar wani abin?" inji ummy cikin kulawa kallon ummy zee tayi saita kada kai sannan ahankali tace "inaso mukoma gida" duk kallonta sukayi "mukoma gida? why? keda bakida lfy?" inji abbu Dan murmushi da iya fatar le6e ya tsaya tayi tace "naji sauqi ai, Kuma banason scent din hospital dinne yana tadamin zuciya" taqarashe zancen tana yatsine fuska "ikon allah, to ai sai abari likitocin suzo muji ta bakinsu tunda suke bada sallamar idan sunga lafiya lau ana iya sallamarki saisu bada, zaman asibiti dama sai don dole bayada wani dadi" inji ummy daidai nan aka bubbugo kofar ward din saida akabada izinin shigowa sannan aka murdo kofar saiga Ahmad yashigo tareda ummanshi da aymaan cikin yin sallama cikin fara'a mutanen dakin suka amsa sallamar sunama umman Ahmad maraba umman Ahmad mai yawan fara'a ta qarasa ciki suka shiga gaisawa cikin fara'a da girmama juna tana tambayar jikin mai jiki batool tunda umma tashigo takasa sakewa Kuma akunyace ta gaidata ta amsa warmly cikin kulawa daga haka ba'a qarajin bakinta ba zee ma cikin girmamawa ta gaida umman wadda ta amsa cikin kulawa tana tambayarta ya jiki ta amsa da dasauqi itakuma umman tashiga kwararamata addu'o'in samun afuwa gaisawa sukayi da Ahmad shima yana tambayarta yajiki shima ta amsa da da sauqi fira ce ta kaure adakin atsakanin ahalin cikin fara'a da nishadi Inda manyan ke firarsu sukuma qananun na sauraronsu daga bayama Ahmad da aymaan suka fice daga ward din sai wajajen 12 noon suka sake dawowa dakin Inda anan su ummy sukayima aymaan zancen sallamar da zee tace tanaso qara dubata yayi sannan yace za'a sallameta bayan zuhr don taji sauqi sosai Kuma zata ida warwarewa muddin zata cigaba dashan maganinta on time umman Ahmad na taredasu har lokacin sallamar aka sallamesu suka fito tare Inda Ahmad yawuce da ummanshi gida suma aymaan sukayo gida suma. Acikin kwanakin dasuka biyo baya zee tayi iyakar bakin qoqarinta naganin taragewa kanta damuwa kodayaushe cikin making kanta busy take don kar ma tabama tarin tunannikan dake qunshe aranta damar tasiri azuciyarta. kodayaushe cikin walwala take Kuma cikin mutane don bata yarda ta kadaice ko yaya ne. sosai take fighting da zuciyarta wajen ganin ta yakice tunaninshi kwata2 daga zuciyarta A bangarensu ummy kau wannan sabon halin na zee sosai yabasu mammaki don zee ta tashi daga zee din dasuka sani tana neman komawa her real lively zee Abinda yafi dauremusu kai shine watsi da maganar Deen datayi don tun ranarda aka gwadamata shi bata sake tada maganarshi ba Kuma dataji alamun za'a dauko topic dinshi zata tashi tsam tabar wajen. abin nabasu mammaki sosai don ga yadda abaya tanuna son bayyanar deen basuyi tunanin xata shashantar da maganar ba dawuri haka. ganin bata ko qaunar atada maganarshi don kosun tada barin wajen take yasa suka bar tadamata zancen nashi suka koma can atsakaninsu suna cigaba da qulla plan dinsu na yadda zasu hada Deen da ainahin ahalinshi. *2 WEEKS LATER* "Kaka kinyi shiru" yafada yana kallonta da oily eyes dinshi Ajiyar zuciya ta sauke sannan tadago ta kalleshi "kyakyawana me zance?" "Kaka kifadi Abinda ke ranki, kinsan koma menene kika fada ya zauna ni Kawai izininki nake nema idan kuma baki bani ba zan haqura" "kyakyawana, bawai hanaka nakesonyi ba, kasan yadda banason kanayin nesa dani koyayane, kodayaushe nafison najika kusadani" "nima Kaka, kullum burina mu kasance atare amma kema kinsan yanayin aikina yanzu, tafiye2 naciki don hakan na daya daga alamomin nasarar aikin" "amma baka ganin wannan yasha banban da dukkan tafiye tafiyen dakake? kamal bafa garin zaka bari ba, qasar zaka bari gabadaya. wakasani acan? tayiwu masu satan mutane nema sukeson yaudararka da sunan aiki" Deen kasa dakatar da dariyar data kufcemashi yayi hakan yasashi darawa ganin hakan yasa Kaka Dan hade rai "au, wato dariya ma nabaka" "to Kaka saceni fa kikace za'ayi, kamar wani toy?" "koma dai menene, ai baka girmi sacewa ba indai wurin wadannan marassa imanin yan kidnafin ne? yo su ina ruwansu da yaro da babba? ai sunma fison babba" murmushi Deen yayi "Kaka anan Nigeria ke akwai kidnappers nikuma barin qasar zanyi gabadaya, Kuma wannan tafiyar ba daka zan tafi ba, Alhaji Bashir yasan komai akan tafiyar nan Kuma yabada goyon baya Kuma beyi hakan ba saida yayi bincike sosai sannan kuma shi ainahin wanda zanje wurinshi nasanshi, Dan Nigeria ne amma acan yake dazama shida iyayenshi wadanda sai daga baya nasan cewa ashe sunsan juna da Alhaji Bashir don mahaifin yaron tsohon abokin Alhaji Bashir ne tun yarinta" "shi mahaifin yaron ne abokin Alhaji Bashir?" inji Kaka "eh, nima sai daga baya Alhajin ke gayamin bayan namashi magana yasa an bincika, Kuma yaron yanada kirki sosai dukda sau biyu muka ta6a haduwa dashi lokacin sunzo Nigeria harnayi ma mahaifiyarshi waqa kuma dukda yakoma can din zumuncinmu be yanke ba don kodayaushe muna ta6o juna via media" buga tagumi Kaka Kawai tayi tana kallonshi batace komai ba, tarasa dalilin dayasa kwata2 tafiyarnan bata kwanta mata arai ba "amma Kaka idan bakyason tafiyar babu komai saina fasa nabasu hqr dama bawai amsa nabasu ba tsayayya" "A'a niba wai tafiyar ce banaso ba Kawai tunanin kewarka dazanyi nake" "Kaka kwana uku Kawai zanyi fa, kuma zamu dinga waya ga Lailah ma nan nasan zata dinga zuwa tana debemiki kewa tunda dama tasaba zuwa bare yanzu datasan bananan" "hakane.. to allah yasa hakan shiyafi alhairi. ai tunda Alhaji ya yarda nasan baza'a samu matsala ba insha allah amma fa ka kula kuma dakaga Abinda beyimaka ba kajuyo gida" murmushi Deen yayi cikin jindadi "insha allah Kaka, babu Abinda zai faru sai alhairi insha allah" "allah ya yarda, dakai da habibun zaku?" "eh dashi zamu insha allah" "to allah ya tabbatar da alhairi" inji Kaka "amin summa amin kakata" yafada yana Dan jawo kaffafunta data miqar saman tutu yana Dan tattausa mata suna cigaba da firarsu wanda yashafi tafiyar tashi A daren ranar Deen yaba Ahmad tsayyayar amsa akan samun hallartar taron daya gayyaceshi don yayi musu performing. sosai Ahmad yayi farinciki yakuma bayyanama Deen irin farincikin daya shiga abin haryaso yayi yawa Nan suka tattauna sosai akan Abinda yashafi tafiyar Inda firr Deen yaqi yarda da zancen Ahmad na ya sauka gidansu ya nace akan shidai zaiyi lodging a hotel babu yadda Ahmad ya iya haka ya haqura suka cigaba da tattaunawar. Shirye shiryen tafiyar Deen yashiga yi Inda da taimakon Alhaji Bashir wato mahaifin Lailah akayi musu visa dashi da manager kuma abokinshi Habeeb cikin qanqanin lokaci komai nasu na tafiya ya kammala ya kasance ranar kawai ake jira A bangaren Kaka har lokacin bawai tafiyar ta kwanta mata bane kawai dai hakanan take pretending kamar ta yarda amma deep down batason tafiyar jitake kamar idan yatafi ya tafi kenan, sau dayawa saitaji kamar tacemashi afasa tafiyar amma ganin kamar shi yanason tafiyar yasa take hqr badon taso ba. Acikin wadanda basason tafiyar harda Lailah, tasan zatayi kewarshi sosai dukda koda yananan ba kullum take sanyashi a ido ba amma the thought of zai tafi wata qasar yanasa jin wani iri, kamar zatayi loosing dinshi ko wani abu makamancin haka. ahaka dai akaita rarrafawa har ranar daren dazasuyi tafiyar ranar da daddare kasa isashen barci Kaka tayi, juyi kawai taitayi har gari yawaye. washegari kuma duk tayi wani iri har hakan ya daga hankalin Deen tambayar duniyar nan yayimata akan meke damunta amma taqi sanardashi, ganin hakan yasa da farko cewa zaiyi cancelling din tafiyar indai tafiyar ce bataso don bazai iya tafiya against her wish ba dafarko tayi tunanin dawasa yake fadin hakan amma ganin ya tubure akan yafasa yasata komawa lalla6ashi don lokacin har 10am gashi 12pm jirginsu zai tashi ganin yaqi yarda din yasa Kaka yima Alhaji Bashir waya Inda ta zayyanemashi komai babu shiri shima alhajin ya iso gidan Inda anan suka hadu dakyar suka shawo kanshi ya yarda da tafiyar don shima a lokacin zuciyarshi tafara bashi akwai wani baqon al'amari dake shirin faruwa dashi Har airport suka rakasu Inda nan ma da taimakon Alhaji sukayi settling komai don yafisu sanin takan komai awajen tunda daga Deen din har Habeeb wannan ne fitarsu qasar waje nafarko. cikin qanqanin lokaci akafara sanarwa Inda ake buqatar passengers sufara boarding jirgin Sosai jikin Kaka yayi lakwas lokacin dasuke bankwana amma ganin yadda Deen ke kallonta keenly yasa taqi bayyana hakan don shima da alamu asanyayen yake addu'o'in tsari suka yimasu sosai sannan sukayi sallama Deen namasu alqawarin dasun sauka zai chanza layi yakirasu ahaka suka rabu Inda suka wuce sukabi ayarin passengers dake boarding jirgin wasu hawaye ne suka zoma Kaka lokacin da Deen ya 6acemata yayinda wani feeling na emptiness ya mamaye zuciyarta a bangaren su Deen kau shigewa jirgin sukayi Inda duk suka nemi seat number dinsu suka zauna. shiru Deen yayi ya jinginar da kanshi jikin kujerar dayake akai yana sauraron 6a66atun Habeeb dayaqi qarewa haka kawai yakejin wani feeling azuciyarshi wanda bazai iya pointing finger akai ba ahaka akafara sanar da tashin jirgi and in few minutes jirgin ya tashi ya lula sararin samaniya✈️ Ummin Fasihu🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:44 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *081* *jiya nasha kira😆 am sorry naso nayimuku jiya amma page dinne banason gutsira muku, Ku ma nasan zakufi son long page, to yaudai ga long page💃🏻* Qarfe 8:00pm daidai jirginsu Deen yayi landing a babban filin jirgin sama na babban birnin Abu dhabi fara saukowa passengers din jirgin sukayi aciki hardasu Deen dasukayi matuqar gajiya due to the long journey kasancewar darene yasa koina yake tarr da haske yadda kasan ba dare ba gashi sai hada hada akeyi gwanin sha'awa saida suka gama clearing din komai suka amshi luggages dinsu sannan suka fito suna tafe suna qarewa wajen kallo Acikin zuciyarsu suna yaba kyau da tsarin qasar. basu sha wahala ba suka samu cab wanda zata kaisu hotel din da Ahmad yariga ya kamamasu tunkafin zuwansu suka shige suka kama hanya A gaban qayyataccen hotel din aka saukesu suka shiga bayan sun sallami mai cab din basu sha wahalar locating masaukinsu ba don dama Ahmad yariga yayi settling komai kuma yaturomasu information about komai don haka Kawai zuwa sukayi aka tantancesu sannan aka rakasu dakinsu. kasancewar agajiye suke sosai yasasu yin wanka Kawai suka rama sallolin da'ake binsu sannan kowanne yabi lafiyar gado. *WASHEGARI* Tunda safe Deen yafita ya chanzo masu layi don babu Abinda yakeson ji a lokacin kamar muryar kakarshi he missed her so much don jiyake kamar yayi wata daya baya tareda ita ne setting komai yayi sannan ya zauna zaman jiran lokacin da aka dibarma SIM din kafin yafara aiki to whine away time saiya ciro laptop dinshi yafara yan dube dube aciki, duk Abinda yakeyi habeeb nacan nade kan gado don shi dama tun bayan sallar asuba yakoma ya kwanta bemasan lokacin da Deen yafita nemo layi ba. yana zaune yana aikinshi a laptop yana sipping tea dayasa aka kawomashi wayarshi tayi beeping ajiye mug din hannunshi yayi ya dauki wayar yaduba, gani yayi sms ne na companyn SIM card din alamun yana iya amfani dashi yanzu gyara zama yayi yafara saka number wayar Kaka cikin zumudi yanajin wani dadi a zuciyarshi. ko kwakwarar ringing biyu batayiba aka daga kiran kamar dama ita akejira "kyakyawana?.." yaji muryar Kaka daga dayan bangaren wani sanyi yaji ya ratsa zuciyarshi lokacin da muryarta ta doki kunnenshi hakan yasashi sakin kyakyawan murmushinshi "Kaka ta" "kyakyawana, kasan tun yaushe nake jiran kiranka? meyasa baka kirani ba sai yanzu?" yaji tafada muryarta.na dan breaking "Kaka sai yanzu layin yafara aiki, nima naqosa nakiraki naji muryarki, nayi kewarki" "nima kyakyawana, ni sai yanzu nake danasanin barinka yin tafiyar nan. ina kewanka sosai ga mafarkai da naitayi jiya... yanzu dai yaushe zaka dawo?" tafada cikin muryarda kanaji kasan tana cikin damuwa sosai "mafarkai? mafarkan me Kaka?" "babu komai, insha allah alhairi ne. yanzu dai yaushe zaku dawo?" murmushi Deen yayi "Kaka duka yaushe mukazo? jiya fa mukazo" "nidai na qagara kadawo ne" "zamu dawo kaka insha allah, kinga saima fa gobe ake taron, yau dai zamu hadu da mutumin muyi shirye shiryen daya kamata, gobe muje muyi masa aikinsa jibi mu juyo insha allah" Ajiyar zuciya Kaka tasauke ahankali sannan tace "to allah ya yarda ya bada sa'a yakuma maidoku lfy" "amin kakata, kinga bamu gaisa bama ko? fatan jiya kinyi barci lfy kinkuma tashi lfy" "hmm ai jiya barci rabi da rabi nayi, kwata2 gidan babu dadi idan babu kai aciki" "nikuma jiya barci harda minshari, dakyar nasamu sallar asuba ma" yafada cikin sigar tsokana "ja'iri, dama nasan bawani sona kake ba, wato ni inanan nakasa barcin kirki saboda kai kaikuma kana can kana barcinka hankali kwance" dariya Deen yayi "to Kaka me yafi raina, wai kinga qaton dakin damuke kuwa? ga a.c ai dole na shari barci na" yafada cikin dariya cikin son lighting up mood din Kaka "ah lallai, gwara kau kashari barcinka.. ina habeebun ko batare kuke ba?" dagowa Deen yayi yakalli habeeb dake nade cikin bargo har lokacin yadan ta6e baki yace "gayacan nade yanata sharar barci" "barcin lafiya yanzu Qarfe tara koko ku nan dare ne?" "A'a, to mu nan Qarfe goma ma, Kawai lallaci ne tunda muka dawo sallar asuba yabaje ko motsi bayayi" "to kodai a.cn nasu na daban ne shiyasa idan mutum ya kwanta beson tashi? kaima fa cewa kayi saida ka makara da asuba" dariya Deen yayi cikin tsokana yace "yo dama tayaya zaki hada a.c din turai dana Nigeria? sanyinshi ma na dabanne har wani feshi feshi ruwa masu qamshi yake" "A.cn?!!" inji Kaka tana kwalalo idanu dariyar da Deen yafashe daita ne yasata gane ashe shaqiyanci Kawai yake mata "zakaci qaniyarka ne, badai ka maidani kakarka ba?" tafada tana kwafa "to dama mecece?" yafada cikin dariya ahaka suka shiririce sunata kwasar fira yadda kasan ba kudinsu suke qonewa ba saida suka jima suna wayar sannan sukayi sallama kowanne farinciki fall zuciyarshi yana gama wayar da Kaka yakira Alhaji Bashir Inda shima ya sanardashi isarsu suma sundan dade suna waya sannan sukayi sallama daga shi sai ya juya akalar kiran zuwa ga Ahmad ya sanarda Ahmad isowarsu tun jiya anan Ahmad kecewa yana kan hanya ma don shima tun jiya yake baza idanun ganin kiranshi shiru, Jin hakan yasa Deen cewa to saiya shigo din sukayi sallama ya katse kiran sake kallon Inda habeeb yake kwance yayi ya girgiza kai yamiqe yanufi gadon yaye bargon dayayi rufa dashi Deen yayi wanda hakan yasashi bude idanu babu shiri "kasan allah? zan fita nayimaka booking flight kakoma Nigeria tunda barci yakawoka nan din" inji Deen yana hade cikkakun giranshi murza idanu habeeb yashigayi yana qoqarin tashi zaune "wannan ne kuma bazai yiwuba, idan kaga nabar qasarnan saina gama zagaye koina lungu da saqo nacikinta sannan, ca6! inzo qasar waje jiya inkoma yau? wasama kenan" sakin bargon Deen yayi yana kwafa yanufi toilet yana cewa "wasa kake gani, zaka gane ne" da haka yashige toilet don freshen up. Babu jimawa Ahmad ya qaraso, direct dakinsu yanufo don dama shi ya kamamasu dakin, lokacin har sunyi wanka duk sun shirya cikin farinciki Ahmad ya tarbesu yanamasu sannu dazuwa yadda Ahmad yanuna farincikin zuwansu har mammaki yaba Deen don shidai yana mammakin irin wannan soyayyar da wannan gayen kemashi. anan suka zauna suka shiga tattaunawa akan event din gobe sosai suka baje suna fira don daga Ahmad har habeeb ba'asan gwani ba a surutu gwara gwara ma Deen din don ko rabin d'iminsu bayadashi saida sukaji anfara kiraye kirayen sallar zuhr sannan dik suka tashi suka fita masjid din hotel din sukayi sallah suka dawo anan Ahmad yayi suggesting idan sunaso saiya dan zaga dasu gari to whine time away da Deen yace A'a amma da habeeb yanace akan don allah sutafi din ya haqura ba don yasoba don shi becika son saurin shishigewa mutum ba yafison ya tsaya matsayinshi shiryawa sukayi suka chanza kaya sannan suka fito amotar da Ahmad yashigo daita suka shiga Inda Ahmad ne ke tuqin, suka fice daga hotel din. *** A bangaren zee kau tafara adapting da wannan sabon halin nata data tsiro dashi yanzu batada wani buri daya wuce ta tsaida hankalinta waje guda itama tayi wani abin kirki koda guda ne ta dade tana 6atama kanta lokaci batareda tasani ba yanzu batason wasting any single second abanza Kuma ita sai yanzu dawowarta Dubai kebata haushi, akan wani banzan dalili tabar qasarta ta nisanci iyayenta takuma datse karatunta idan tatuna da bata baro Nigeria ba da wannan shekarar zatayi graduating saitaji wani baqinciki ya mamaye zuciyarta akanshi tabar makarantarta lokacin da takusan gamawa kuma anan din ma saboda shi taita canje canjen school while shi yanacan yana gina rayuwarshi hankali kwance, idan ta tuna hakan ba qaramin zafi takeji a zuciyarta ba shiyasa yanzu ta zage damtse bata barin komai yayi distracting dinta komai qanqantarshi, sotake itama tazama wani abu, she want to made it also, she want to move on. hakan yasa yanzu ta tattara hankalinta kacokam ta maida ga karatunta, bata wasa dashi ko kadan, ta maida dukkan attention dinta akai shiyasa wani lokacin bata cika sanin Abinda ke wakana a gidan ba. yau ma kamar kullum tana zaune cikin dakinsu a tsakiyar gadonsu littatafai takoina tana aiki tsabar yadda hankalinta ya dauku ko sanin shigowar batool batayiba sai jitayi an fige pen din hannunta saurin dagowa tayi adan tsorace, ganin batool ce sai tadanyi tsaki tana girgiza kai hayewa kan gadon batool tayi tana cewa "bookworm, ke shikenan idan kika samu littafi bakyaji bakya gani, dama haka kikeda tsoron exams? is better kiragewa kanki don munan bamada tsaurin exams kamar can qasarku dazakiyita abu guda kamar cin qwan makafi" harararta zee tayi "wake tsoron exams?" "ke mana, tunda exam ya gabato kinwani addabi kanki da karatu kullum abu daya ko gajiya babu, gwara ki sassautawa.kanki don kanki bursting zaiyi abanza ingayamaki" ta6e baki zee tayi tace "to naji bani pen dina Kuma ni ba don exams nake karatu ba don exams be ta6a tsoratani,ba saboda akodayaushe ashirye nake ba kamar kuba dakuke bari sai yazo gab sannan kuyita tsalle tsalle" ta qarashe tana fige pen dinta daga hannunta taduqa tana cigaba da rubutunta ta6e baki tayi tace "kyaji dashi... wai kinsan wani abu?" batareda ta kalleta ba ta girgiza kai "dazu mukayi waya da habiby" tafada tana farr da idanunta mere baki zeetayi tace "iyee? shagali" "yacemin he's very busy yau don yanzu haka yana tareda wani babban baqo ne" inji batool tana kallon zee dake sauraronta absent-mindedly "allah sarki" inji zee tana cigaba da Abinda take "Kuma kinsan wani abu?" batool tasake tambaya rolling idanu zee tayi cikin qosawa sannan tadago ta kalleta "don allah don annabi batool spare me, wai bakiga abinda nake ba ne? don allah ki kyaleni hakanan sai distracting dina kike da labarai marassa ma'ana" tafada cikin qosawa riqe ha6a batool tayi tana kallonta harta gama sannan ta kada kai Kawai ta miqe batareda tace mata komai ba tafice daga dakin fuuu binta da kallo zee tayi tadanyi shiru na wani lokaci saikuma ta daga kafadu tajuya ta maida hankalinta akan abinda takeyi *** sunyi yawo sosai agarin Inda Ahmad ya shiga dasu wurare daban daban qayattatu na garin. sosai sukaji dadin wannan fitar don sun kashe kwarkwatan idanunsu ba dan kadan ba daga qarshe saida Ahmad yabiya dasu gidansu Inda sukaje suka gaida su umma sosai sukayi musu tarba na musanmman don harda baban Ahmad suka tadda gidan anan suka qarashe wunin sai gab da magrib sannan suka kamo hanyar hotel din wannan yar fitar dasukayi ba qaramin sabo yajawo ba tsakanin gayun uku don lokacin dasuka dawo ma sun dade suna fira kafin Ahmad yatafi akan sai goben idan sun hade wajen event din Bayan tafiyar Ahmad Deen yasake bude laptop dinshi yana qara shiri na aikinsu na gobe sosai mutuncin ahalin Ahmad ya burgeshi shiyasa shima yaji yanason yimasu aiki na burgewa haka yakusan raba dare yana aiki Inda habeeb uban rakad'i tun yana damunshi da 6a66atunshi na santin zaga garin dasukayi har barci yaci qarfinshi ya bugas yabarshi anan shima saida barcin yafara cin qarfinshi sannan ya haqura ya kwanta zuciyarshi cikeda tunanin event din na gobe *WASHEGARI* Kasancewar yau Saturday yasa bayan sallar asuba duk komawa barci sukayi musanmman zee data kusan raba dare jiya tana karatu don da asuba ma dakyar batool ta iya tadata tayi sallah takoma tasake bin lafiyar gado ahankali tafara motsi da idanunta dake arufe saboda hasken rays din rana dayayi reflecting fuskarta Dan yamutsa fuskar tayi tana yin juyi agadon tana lallube involuntaryly Jin bata ta6o komai ba yasata qara miqa hannu tana lallubawa nan ma wayam hakan yasata fara bude idanunta dabasu gaji da barcin ba ahankali waiwaigawa tayi taga dagaske ita kadai din ce adakin hakan yasata miqewa zaune tana miqa agajiye ahankali take bin dakin dake wani qamshin dadi da kallo ganin yadda yake fess fess tana wondering yaushe aka gyarashi, kardai ace ranan barci tayi sosai duba yar qaramar agogon dake kan bedside locker tayi taga duka Qarfe tara ne da yan mintuna Kuma a irin wannan ranakun na weekend suna kaiwa har 10 kwance lallai yau batool yan aikin ke bisa kai tunda harta tashi dawuri haka hardasu gyaran daki. sauko qaffafunta tayi daga kan gadon tana qara miqar da gajiyayyun ga6o6in jikinta sannan ta tashi tawuce hanyar toilet brush tafarayi sannan tayi wanka sannan tafito cikin bathing robe Dan dakatawa tayi daga bakin qofar toilet din ganin gadon data tashi tabari ayamutse yakoma tsaff tsaff kamar ba'a ta6a kwanciya akai ba gawani qamshi da dakin yaqara dauka da mammaki tabi koina na dakin da kallo taga bakowa hakan yasata ida qarasowa dakin walking slowly to waya shigo yagyara gadon daga shigarta wanka? tambayar datayiwa kanta kenan ganin Babu mai bata amsa yasata wucewa closet dinsu tazaro wata light silky gown kalar yellow ta shirya acikinta a gurguje sannan tadan shafa roll on mai sanyin qamshi tazura takalmin soso ta bude kofar tafice ahankali take saukowa a stairs din tana qarewa gidan kallo saboda wani extra kyallin dayake gidan yasaba zama cikin gyara da qamshi amma nayau yasha banban dana kullum don sosai gidan yaqara daukan extra kyalli ga wani qamshi dayake na musanmman Babu abinda yafi bata mammaki irin extra silent da gidan ya dauka yadda kasan babu kowa adakin "batool?.." tafada tana qarasowa cikin falon tana waige2 "batool!" tasake kiranta tana yin hanyar kitchen saidai sauke idanunta datayi a dining area yasata jan burki daga tafiyar datake Dan wara idanunta tayi tana tana kallon yadda aka qawata dining area din wurin sai bada different colours of dim lights yake "wow!" tafada ahankali tana yin wajen tundaga nesa ta hangi dining table din wanda da alamu abubbuwan ciye ciye aka jejjera akai saidai bata iya hango ko meye saboda rufeshi da akayi da white spotless sheet qarasawa tayi bakin table din tana kallonshi kafin ahankali tasa hannu ta yaye farin qyallen nasama "HURRAY!!!" taji wajen ya dauki ihu nan take wanda hakan yasa harta tsorata saurin waigawa tayi nan taga dukkan ahalin gidan ne duk sun fito from nowhere suna tafi suna waqar _Happy birthday to you_ _Happy birthday to you_ _Happy birthday.._ _Happy birthday_ _Happy birthday to you!!_ Hangame baki zee tayi in outmost shock wait.. wai dama yau ne birthday dinta? Nan take wajen yadauki kidan ryhmth din waqar Happy birthday mai dadin gaske su ummy na bin waqar "ya sallam!" zee tafada cikin wani irin shauqi taruga wajensu ta rungumesu gamm tana tsallen murna dariyar farinciki wajen ya dauka raba jikinta tayi dasu tana kallonsu "tayaya kukasan yau ne birthday dina? ni kaina na manta" tafada cikin tsananin farinciki "mu ai bamu manta ba" inji daddy da sai alokacin ma ta lura dashi wara idanu tayi taruga wajenshi "daddy! yaushe kadawo?" tafada tana rungumeshi "jiya" yabata amsa "shine ban saniba?" "it's a surprise!" sakin daddyn tayi tanufi ummy ma ta rungume kai da gani dadin ne yaimata yawa "kai amma kun shammaceni, this is the best surprise ever! thank you" tafada cikin murna bakinta yaqi rufuwa don farinciki "you deserve it dear, Happy birthday" inji abbu yana miqamata wani dan box dake lullu6e da ledar gifts irin.mai qyallin nan "wow! thank you abbu" tafada cikin jindadi tana amsar box din "Happy birthday sweet daughter" inji ummy itama tana bata wrapped gift dinta "ohh! thanks so much sweet ummy" tafada tana rungume ummy kafin ta amsa "Happy birthday shalele" inji daddy yana miqamata guntun box shima wrapped cikin ledar gift Dan ihun murna tayi sannan ta amsa "thank you daddy" "Happy birthday ukhtie, wullnp" inji aymaan shima yana bata nashi gift din dake cikin dan madaidaicin flat box "wow! shukran akhie" tafada tana amsa cikin murna "Happy birthday rude sis" inji batool tana miqamata wani siririn abu nannade a ledar gift "thank you silly girl.. meye wannan abin kamar kara?" tafada tana jujjuyashi ahannu kashe mata ido daya batool tayi tace "karki damu, zakiji dadinshi sosai saboda nasan duk sai.kinfi jindadin gift dina.bisaga na kowa" harararta zee Kawai tayi ta ajiyeshi shima Inda duk ta ajiye kingin gift din Nan duk kallo yakoma kan mummy ganin hakan yasa mummy kauda kai "mummy kefa? ina gift dina?" tafada ashagwa6e wata harara mummy ta gallamata hakan yasa ta tur6une fuska tana turo baki "dama nasaba baki birthday gift ne? wannan sai wadanda sukaji zasu iya" dariya duk yan dakin suka dauka ummy tajawo zee jikinta tace "kyaleta daughter ai dadin abun kinada iyaye dayawa" "aikaudai, gasunan tili tili duk masu sonki" inji abbu itadai mummy ta6e baki Kawai tayi batace komai ba "To yanzu yaushe za'a fara cin abincin? nidai cikina yafara kiran ciroma" inji batool tana yatsine fuska aymaan dake kusada ita yayi kamar zai tandaremata qeya tayi saurin duqewa "ffo Kawai" yafada yana harararta "A'a da gaskiyarta, daughter taho muje mufara mu nima dai dauriya Kawai nake" inji mummy tana kamo hannun batool dariya wajen yasake dauka suma suka bisu dining din dayake shaqe da kayan ciye ciye kala2 "wow! dik yaushe kukayi wannan?" inji zee tana zama tana qarewa table din kallo "kina can kina wannan barcin asarar mana, to don ma kisani nima ga nawa birthday din saikin ramamin yarinya don ba akyauta nayi miki wahalar yau ba" inji batool wani kallon uku saura kwabo zee tayi mata ta watsar addu'a suka farayi sannan akace birthday girl zata fara ta6a abincin kafin kowa yaci tsayawa zee tayi tana qarewa abubbuwan kan table din kallo sannan tayi murmushi ta miqa hannunta ga wani plate dake cikeda favorite snack dinta wato burger tana cewa "zanfara da gift din mummy" dariya duk mutanen wajen sukayi don dagaske mummyn ce tayi burger din Kuma tayishi exactly yadda takesonshi gutsira tayi tafara tauna ahankali tana lumshe idanu saikuma ta bude ta kalli mummy "thank you sweetest mummy!" yadda tayi maganar yasa mutanen wajen qara sa dariya itakau mummy murmushi Kawai tayi tana girgiza kai bismillah akayi kowa yafara cin Abinda yakeso a table din sosai zee takejin dadin moment din, rabon da taji irin farincikin datakeji ayau harta manta tunda take bata ta6a celebrating birthday dayasata farinciki kamar na wannan dama ita bawani celebrating birthday dinta takeyi sosai ba, yawanci duk tareda tsoffin qawayenta (sumy) take celebrating dinshi Inda zata kwashesu sutafi outing Inda zasuje susamu wani grand restaurant suci su qoshi sukuma yi shopping wanda duk ita zata biya saikuma daddy da duk ranar birthday dinta saiya bata wani abu a matsayin gift itakau mummy ba'a ma maganarta don bawani shiri sukeba alokacin bare akaiga maganar gift rabonta da celebrating birthday shekara biyu kenan don wancan har yaxo ya wuce batasaniba don alokacin suke cikin chakwakiyar su master lokacin Deen na kwance asibiti sai wannan wanda busy yasa tama manta shaff dawani birthday don da basuyimata bama da sai daga baya zata tuna tayi mammaki Kuma taji dadin wannan bazatan sosai don tunda take bata ta6a birthday mai armashin wannan ba firace ta kaure a dining din suna fira mai cikeda barkwanci da tsokana ga dan kidan dake tashi har lokacin ta bayan fage sosai kasancewarta cikin wannan Happy family din yaqara sanyayamata rai tana Jin kamar su dawwama ahaka "wow! gaskiya bazan gaji da godemuku ba.,you guys made my day. wannan birthday din is the best birthday of my life, I heart you millions times" tafada farinciki fall zuciyarta "wani abin ma sai anjima" inji batool saikuma tayi saurin toshe baki alamun tayi su6ul da baka ganin duk mutanen wajen,sun harari batool yasata sanin tabbas akwai Abinda suke 6oyewa "anjima? wayyo allah me Kuma zai faru anjima? karku kasheni da dadi" tafada tana dan tsalle a kujerarta kamar wata qaramar yarinya "mtcheew mai bakin parrot beyi ba" inji aymaan yana gallama batool harara sannan ya maida kanshi kan abincinshi "nidai don allah ku gayamin, pleeease" inji zee tana marairaicewa "dont mind them daughter, Kawai yar qaramar liyafa zamuyi na birthday dinki anjima, that's all" inji ummy "really? amma ai meyasa? wannan ma ya wadatar" inji zee don itafa dama can tara mutane ana celebrating birthday becika burgeta ba tafison tayishi in a small way "bawai wani taro bane, Kawai iya mune zamu dan zauna muyi celebrating in a small way kingane ai, a garden ma za'ayi, Kawai daga mu sai mu" ummy tabata amsa "Kuma munason yin hakane don yazama memory da kowa zai riqe koda watarana bama tare irin hakan mu dinga tunawa munajin dadi" inji abbu kada kai zee tayi cikin gamsuwa tace "allah yakaimu, can't wait" cigaba dacin abincin sukayi, itadai batool bata qara cewa komai ba don karta sake wani su6utar bakin ahaka suka gama karyawar cikin jindadi saida suka sake dadewa a zaune suna fira kafin afara watsewa zee da batool sukayi clearing table din komai yakoma daidai sannan da taimakon batool zee ta kwashi gifts dinta suka haye sama cikin zumudin budewa suga abubbuwan dake ciki...✍? *banso datse page dinnan ba amma ya na iya? 🤦🏻‍♀? banason rushing dinshi don haka kuyi hqr _reunion_ sai next page insha allah* Ummin Fasihu🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:44 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *083* *last page nayi mistake wurin numbering, 82 ne instead of 81* Akan gado suka baje gifts din suka shiga budewa da daddaya kwalin Abbu mai dan girma suka fara budewa nan sukaci karo dawata tsadaddiyar Abaya kalar sky blue mai hula irin ta alkyabba tasha stones masu walainiya atakoina na jikinta sai daga gefe takalmine kalar kayan masu shegen kyau da yar guntuwar purse wani ihu suka saki atare cikin tsananin murna suna qanqame juna fadin farincikin dasuke 6ata lokaci da baki ne sakin juna sukayi batool tazaro rigar tana dagata sama don su ganta dakyau "OMG! wayoo allah na, zee don girman allah kibani idan baki baniba zan mutu" inji batool tana rungume rigar qaqam ajikinta fizge rigar zee tayi tana cewa "allah yajiqanki ya gafartamiki, idan kin mutu zanyi volunteering gero musha gumba" "muguwa, kede wlh mutuncinki qalilan ne" inji batool tana harararta gwalo Kawai zee tayimata tana maida rigar carefully cikin kwalin ta rufe ta maida gefe sannan suka dauko gift nagaba dan madaidaicin box din ummy suka bude Inda anan sukaci karo da tsadaddun yan kunnenshi da sarqa da bangles dinsu duk iri daya sai daukar ido suke nan ma ihun murna sukayi suna santin kyawun jewelry din gift din daddy shine nagaba Inda anan sukaci karo da wata faskekiyar waya ta yayi mai daukar ido anan ma ihun suka saka kamar qanannun yara suna tsallen murna next sai gift din aymaan dake cikin flat box ahankali suke yage ledar da akayi wrapping kwalin dashi har suka raba kwalin da ledar Jan kwali sukaci karo dashi mai dan fadi daga murfin kwalin sukayi nan take abubbuwan ciki suka bayyana wara idanu duk sukayi bakinsu na forming 'O' shape suna kallon kayan cikin kwalin speechless Acikin kwalin wani dan kwali ne mai shape din heart dauke da qananun qananun candies of various colours suma masu shape din heart, Kasancewar abin da aka rufe kwalin transparent ne yasa suke iya hango mouth-watering candies din dake ciki agefe kuma wata yar kwalbar turare ce wadda kallo daya zakamata kasan tsaddadiyace sai dan birthday card mai design din red roses ajiki. sun dade suna kallon abubbuwan batareda sun iya cewa komai ba batool ce tafara iya magantuwa "wow! wow!! wow!!" tafada kamar wata jiniyar mota tana bude transparent covering din candies din ahankali ta dauko guda daya aciki takai bakinta ta gutsira tafara tauna tana yin luum da idanu "wayyo ummy na, wlh tunda nake ban ta6acin candy mai dadin wannan ba, don allah ci kiji" inji batool tana kaima zee da haryanzu takasa magana candy din abaki ahankali itama zee da duk jikinta yayi sanyi ta gutsira tafara tauna tana jin yadda gardin candy din ya gaurayemata baki "how was that?" inji batool cikin zumudi ganin batayi magana ba kuma har lokacin bata bar kallon candies dinba yasa batool kallonta murnarta na dan komawa ciki "zee lfy?" tafada ahankali tana kallonta sai a lokacin zee tajuyo ta kalleta itama Dan kirkirar murmushi zee tayi wanda iyakarshi fatar baki "am.. am ok, Kawai gift dinne yayi mugun burgeni" tafada tana daukar card din tana jujjuyawa azahiri ba gaskiya bane Abinda tace ba don ganin wadannan candies dinne suka sata a wannan yanayin sai suka tunomata da candies dinsu na ranar Valentine wanda da ita da Deen sukaci suna celebrating soyayyarsu, sak wadannan irin wadancan ne banbancin kawai colour don na wancan na chocolate ne wannan kuma kaloline daban daban kowanne kuma da taste dinshi Bude card din tayi Inda anan taci karo da yar farar linkakkiyar takarda wanda ke tsakiyar card din cirota tayi ta warwareta tafara karantawa *_To a Special Princess_* _*Today marks a Special day to a Special person*_ _*Happy birthday to the cutest and unique being i've ever came across*_ _*may this day mark the beginning of your indefinite happiness and joy*_ *_may allah continue to brighten the way for you and may your unique smile stayed plastered to your face forever (Ameen)_* *_Enjoy your day PRINCESS👸🏻_* saida tagama karantawa sannan talura ashe tare suke karantawa da batool don tunda tabude itama ta leqo kanta tana karantawa itama "woow! ashe haka akhie iya tsara kalamai! mugani.." inji batool tana neman amsar takardar daga hannun zee 6oye takardar zee tayi abayanta tana harararta dukda yadda takejin zuciyarta na rawa rawa "yo saboda me? amebo you better face your business" tafada tana ninke takardar saidai har lokacin zuciyarta batabar rawa ba dukda rubutun aymaan gajere ne ba qaramin tasiri yayi a zuciyarta ba wani tunani yakeson bijiromata a zuciya amma takama iyakar bakin qoqarinta don kaudashi don bata fatan hakan ta kasance ko a mafarki domin kawar da tunanin saita janyo gift din batool wanda duk ciki shine qaraminsu "nidai wannan abu bansan ko meyeba, abu kamar icce kamar kara" tafada tana qoqarin warwarewa dariya batool tafashe dashi tace "kedai duba, am telling you babu gift din dazakiji dadinshi irin nawa" "ahakan? to allah yasa" ida warwarewa tayi nan Abinda batayi expecting ba ya bayyana qara fashewa da wata yar iskar dariya batool tayi ganin yadda zee tasaki baki tana kallon gift din ba komai bane illa pen saidai pen din nada kyau kuma jikinshi transparent ne Inda taciki tana iya hango yar takardar da batool ta cusa ciki ajikin takardar tarubuta *_Happy birthday bookworm_* "kutt.. amma kinyi mugun raina min hankali, dama wannan ne gift din?" cikin dariya sosai batool tace "ai naga kamar zakifi jindadin gift dina bisaga na kowa yadda kwana biyun nan kika maqalewa littafi" jifanta zee tayi da pillow tana cewa "silly girl" atare suka tattare kayayyakin suka adana banda candies din wanda batool tabude ciki sai zaqa take zama sukayi suna cigaba da firarsu suna cikin haka wayar zee tayi beeping dauka tayi taduba saitaga birthday message ne daga Aysha Dan wara idanu tayi tace "waya gayama Aysha?" daga yatsa batool tayi kamar irin tana cikin aji dinnan makamata pillow zee tayi tace "waya aikeki?" dariya batool tayi tana sosa Inda ta bugamata pillon tace "har sai an aikeni? kema kinsan tasake taji labari daga baya cewa kinyi birthday ba'a gayamata ba kaina zata huce, ya akayi lokacin da aka sallameki asibiti ba'a gayamata ba har taje ta iske wayam? ba nan tazo tahauni da masifa ba kema harda tayata?" "mtcheew, kede kikasani mai bakin parrot Kawai" "eh din, don haka kima shirya nasan tana nan tafe anjima wurin taron nan" sakin baki zee tayi tana kallonta "gayamata kikayi?" juya idanu batool tayi "sosai ma, tun yaushe nakai mata i.v? kece fa bakisan da wannan abin ba sai yau, kinacan kun daura aure da littafi dama ya za'ayi kisani? to na gayyaceta bama ita kadai ba harda yayanta" kwalalo idanu zee tayi "Mussadiq?!!" "yes? wlh harda shi saidai yakawo mana kwafsi wai bayanan yana wani business trip tun last week injita" inji batool tana ta6e baki alamun ko ajikinta sakin baki zee tayi tana kallon batool lallai batool batada hankali, tarasa wanda zata gayyatomata sai wannan mutumin? bayan tasan yadda basa shiri dashi ga gabar dasukeyi da aymaan? to waima meye alaqarsu dazata wani gayyaceshi? haka Kawai saita gayyaceshi bayan tasan bawani maganar arziqi sukeyi ba? Tunawa tayi da karonsu na qarshe a school lokacin ba'a dade da sallamarta ba a wannan kwanciyar datayi asibiti a lokacin ta quduri aniyar tattara komai daya shafi Deen ta watsar don sotake tayi moving on for real saidai har lokacin Mussadiq bebar bibiyarta ba a school abin nashi harya kai duk Inda tayi saita ganshi hatta sabon wurin data chanza tana ke6ewa don tayi karatu saidai abinda yafi daure mata kai shine duk lokacin data ganshi baya nuna yama san da ita awurin don ko kallon banza bata isheshi ba bare na arziqi, yi yake kamar besan da wanzuwarta ba awajen hartayi Abinda zatayi tabar wajen tasha hasashen kodai ba.ita din yake bibiya ba hakan kesata chanza wurin zama kodayaushe Kuma sai taga duk Inda taje saiyaje hakan yasata tabbatar da eh ita din yake bibiya ganin hakan yasata yanke shawarar samunshi tayi warning dinshi yafita harkarta don ahalin yanzu bata buqatar taqara hada wani abu da Abinda yashafi Deen don shi dinma sotake ta gogeshi a kwalwarta ta huta hakanan hakan yasa watarana taje tasameshi yana zauna daga nesa da Inda take as usual nan tacemashi yabar bibiyarta hakanan kota hadashi da hukumar makarantar don bataga dalilin daxai dinga bibiyarta ba haka Kawai a ranar ta tabbatar da Mussadiq dan air ne na gaske don gabadaya saiya juye abun kanta ya nuna ita har wacece dazai bibiyeta kuma mema zaisa ya bibiyeta ko taga yazo wajenta ne ko yayimata magana cikin shaqiyanci yace Kawai sotake tayi making kanta noticeable ne awajenshi amma shi samm ko sanin da ita bayayi yadda ya juyar da maganar yana mata shaqiyanci shiyafi 6atamata rai gashi ya iya gayama mutum magana yadda zakaji kamar kaita kurma ihu saida sukayima juna tass sannan tawuce tabarshi yana mata dariyar shaqiyanci wanda ke qara qonamata zuciya, sai taji wama yace tunfarko taje tasameshi gashi ya 6atamata rai a banza tun daga lokacin bata qara kulashi ba kuma shima be fasa bibiyarta ba saidai ko kallo baya isanta don itama ta quduri aniyar watsar dashi tayi pretending batasan dashi ba kullum tana ganinshi amma bata kulashi saikuma taga daga baya tabar ganinshi kusan kwana hudu kenan, ashe tafiya yayi? kenan da yana nan din haka zata gayyaceshi? wannan ai zubar da mutunci ne girgiza kai tayi sannan ta miqe tsaye tana kallon batool on a serious note tace "batool mu ajiye batun wasa, karki qara yimin haka, idan ina abuna karki qara sakoman wannan mutumin aciki" "to amma..." "nadai gayamaki" zee ta katseta sannan tanufi hanyar toilet tashige tana maido qofar da qarfi ta6e baki batool tayi tadaga kafadu ta cigaba da cin candy dinta hankali kwance *** Dago kai aymaan yasake yi ya kalli Ahmad dake kai kawo a dakin looking very restless saiya mere baki yasake maida hankalinshi akan wayar hannunshi "what should we do now?" inji Ahmad dabe bar safa da marwan ba har lokacin qara ta6e baki aymaan yayi batareda ya Dago daga danne dannen dayakeyi ba dakatawa daga zirga zirgan Ahmad yayi ya kallo aymaan "wato kai ko ajikinka, mutane,nacikin damuwa kai kawani harde kana danne danne ko a kwalar rigarka ko?" yafada a little angry qara ta6e baki aymaan yayi yana dagowa ya kalleshi "su mutanen su sukaso sa kansu a damuwar, ni banga abin damuwa ba anan" "dama tayaya za'ayi kagani? ni ai nagama lura bawai son wannan al'amarin ba kake Kawai kana following ne shiyasa ko ajikinka" "to da fa? kaima kasan dalilin dayasa haryanzu nake cikin case dinnan, Kawai don nacikama zee burinta na sadashi da ahalinshi Kawai yasa kaga ina biye ba don hakan ba..." saiya daga kafadu tsaki Ahmad yaja Kawai yajuya yabar kallonshi "yanzu haka za'ayi abinnan Babu Mussadiq? ni nafison sufara haduwa dashi haduwa zaifi tsari wlh" ta6e baki yayi yace "saikaje can Australia din kasameshi kataho dashi yadda abin zaifi tsari" sake juyowa Ahmad yayi ya gallamashi wata muguwar harara hakan yasa aymaan murmusawa kwafa Ahmad yayi yajuya "kaga wannan duk fa ba abin 6acin bane, idan shi Mussadiq din bayanan ai qanwarshi nanan, banaji batool tace zatazo ba?" "dukda hakan, idan Mussadiq yazo komai zaifi armashi" "hmm koba armashi ba, wataqila ma gwara da bayanan don wannan mahaukacin Babu Abinda ke kanshi sai hauka, banda hauka me zaizo yaiwa mutane?" "ai dama kai ba sonshi ba kake" "ni ai naga yana sona, Kawai.ku manta dashi kuyi proceeding plan dinku, wayasani ma ko hakan zaifi" Ajiyar zuciya Ahmad yayi saidai still fuskarshi na nuna alamun rashin jindadi furzar da huci yayi sannan yace "ok, bari na lalubo Deen din" daga kafadu Kawai aymaan yayi yacigaba da danne dannenshi shikuma Ahmad yazaro waya zai lalubo Deen din *** Kamar yadda batool tayi hasashe tun bayan asr Aysha ta diro gidan sosai sukayi murnar ganin juna nan suka rungume juna suna murna bayan sungama suka baje adakinsu batool suna fira Inda anan itama Aysha din tabata birthday gift din data kawomata Inda xee tanuna jindadinta sosai takuma yimata godiya adakin sukayi zamansu sunata firarsu Inda acan waje Kuma ake decorating garden din daza'ayi dan taron daza'ayi anjima. *8:00pm* Ahankali take nada mata veil din cikin qwarewa irin nadinsu na larabawa saida tagama sannan tadauko turaren dake kan mirror din (aymaan's gift) tashiga feffesamata shi ajiki, nan take dakin yadauki wani qamshi mai sanyin dadi "wow! gaskiya turarenan yayi, I love the scent" inji Aysha tana ida gyagyaramata Inda beyiba murmushi Kawai zee tayi kaucewa Aysha tayi yadda zee zata samu damar ganin kanta a jikin mirron "now, here you go" Aysha tafada tana murmushi dagowa zee tayi ta kalli kanta ajikin qaton madubin nan take tawara idanu tana kallon kanta without blinking dariya Aysha tayi ganin yadda zee ke kallon kanta ta mirror Babu ko kyaftawa sai tace "to ya?" cikin wara idanu zee tace "wai.. dagaske nice anan?" dariya Aysha tasakeyi tana xagayawa bayanta ta dafa kafadunta ta sunkuyo yadda zasu dinga kallon kansu ta mirror tace "ga zahiri?" "wow! this is...amazing! tayaya kikayi transforming dina haka?" inji zee cikin murna "bani nayi transforming dinki ba, dama ke kyakyawace gakuma kyawawan kaya dole ki chanza... now time for selfie" inji Aysha tana zaro wayarta sukayi posing ta daukesu daidai nan aka bude kofa batool tashigo "wai wannan wane irin shiriritane? kunsan lokaci yayi amma kuntsaya kuna..." maqalewa a iska kingin maganarta tayi datayi tozali da zee wara idanu tayi cikin mammaki tana kallon zee baki bude "who is this?" inji batool idanunta still akan zee harararta zee tayi ta kauda kai tana murmushi "wow! wow! wow!!" tafada tana qarasowa wajensu itadai Aysha banda murmushi Babu Abinda takeyi "zankad'aziya kenan, wai zee kin ganki kuwa?" tafada tana bin koina na jikin zee da kallo fari zee tayi da idanu tana tsuke baki "ya nakoma?" "kai aradu dafarko nakasa.ganeki, kinga wai yadda rigar tayi maki? kai dole mukashe selfie, tashi tashi" tafada tana zaro wayarta Nan fa suka samu abin yi sukaita daukar kansu selfie dukkansu suna styles kala2 ahaka har aka sake bude kofar "wai wannan shirun na lafiya ne? kufa kadai ake jira" inji ummy data leqo idanunta ne suka sauka kan zee "kai kai kai masha allah, diyar tawa takoma haka?" inji ummy tana qarasa shigowa dakin murmushin kunya zee tayi "kai masha allah, gaskiya kinyi kyau daughter, allah yayi albarka yaqaro shekaru lodi lodi masu albarka" duk da amin suka amsa harda Aysha Kasancewar duk da turanci suke maganar "yanzu kuyi sauri inajin ai kungama ko? ku kadai ake jira" "eh mungama ummy" inji Aysha "to mutafi, kowa ya hallara ku kadai ake jira" "ummy baqin sun iso" inji batool cikin zumudin "idan kika kin gani" inji mummy tana doroma zee hular Abayar bisa kai wanda keda jela jelar zarruruwa wadanda suka dan karemata fuska kama hannunta ummy tayi sukayi waje su Aysha na maramasu baya koina tarr yake da haske dukda Kasancewar dare ne, daukar hanyar garden din sukayi suna tafe Aysha na gyarama zee rigarta dake dan jan qasa abaya Garden din shima tarr yake da haske dake haskowa daga both kwayaye masu haske da masu kaloli anyi decorating garden din gwanin sha'awa ga fararen plastic kujerun da mutanen da aka gayyata duk suka zazzauna akai daga gaban mutanen Kuma wata royal blue kujera ce mai kyau sosai sai dan qaramin glass table daga gabanta wanda ke dauke da dan madaidaicin cake dake dauke da burning candles masu kaloli akai. mutanen wajen basuda wani yawa daga su Abbu sai su mummy sai su aymaan da Ahmad dakuma iyayen Ahmad din Ahankali suka qaraso garden din suna tafe fuskokinsu dauke da murmushi sosai kallo yadawo kan zee wadda taxama kamar tauraruwa acikinsu Ahankali take tafiya hannunta cikin na ummy dake janta fuskarta dauke da murmushi dukda bata ganin mutanen wajen sosai saboda baza bazan hularta dasuka dan karemata gani taga alamun mutanen dai nada dan yawa sautin 'masha allah' keta tashi daga bakunan mutanen wajen cikin yaba irin kyawun datayi wanda hakan kesata murmushin kunya tana qara sinne kai acan na hango aymaan dake sanye cikin wani danyen tsaddaden yadi kalar madara yaci gayunshi Inda yayi shigar milk and brown tun lokacin dasuka shigo garden din idanunshi ke kanta ya kafeta dasu babu kyaftawa dukda baduka fuskar tata yake gani ba yana hango karan hancinta da guntun bakinta dake shining saboda lipgloss datasa, yana ganin yadda yake curving beautifully idan tana murmushi da kallo yarakasu har ummy ta qarasa daita wajen da aka tanada mata don zama koda suka isa wajen bata zauna ba sai qarasowa da mutanen wajen sukayi wajenta suka fara gaisawa akunyace zee keta gaidasu don duk saitaji kanta yayi girma ganin itace centre of attraction din wajen aymaan dai yakasa ko kyafta idanu akanta duk motsinta saiyabishi da Hazel eyes dinshi jiyayi an zungureshi hakan yasashi waigowa yana dawowa daga duniyar kallonta "kallatu ance mutaso mu yanka cake" inji Ahmad cikin tsokana harararshi aymaan yayi sannan ya tashi suka qarasa wajen mutanen daduk sun koma gaban wajen ana shirin yanka cake din hada idanu Aysha tayi da aymaan yawani hade rai tareda kauda kai binshi da kallo tayi saikuma ta ta6e baki itama ta kauda kai waqar birthday suka shiga yimata suna tafi sannan da taimakon mutanen wajen ta yanka cake din tafi wajen yadauka sosai ana dariyar farinciki anan zee tashiga ciyar da makusantanta suna ramawa suma ciro wani guntun tayi tanufi bakin Aysha dake kusada ita tanata murmushi cikin murmushi Aysha ta bude bakinta tasaka mata nan ma aka dau tafi itama Aysha guntun ta dauke ta bata tana lakuta mata sauran akumatu dariya duk aka dauka ganin Abinda tayi kamar ance Aysha tadago sai suka qara hada idanu da aymaan wani mugun kallo ta jefeshi dashi ta kauda kai Dan buda idanu aymaan yayi yana kallonta saikuma ya kauda kai yana kwafa acikin zuciyarshi bayan sungama kowa yakoma mazauninshi ya zauna Inda akabar zee kadai gaban wajen zaune a maxauninta anan ne Ahmad daya ari aikin m.c yafara gabatar da mawaqin dazai danyi entertaining dinsu be ambaci suna ba Kawai dai gabatarwa yayi mashi yakuma buqaci atafa mashi tafi din kau aka dauka wanda yayi daidai da shigowar mawaqin filin sanye yake cikin wani ratsatsen suit fari Inda yayi shigar mai combination din fari da jaa farin wando sai jar shirt yadora coat fari asama, wuyanshi sanye da jan necktie guntu, kaffafunshi sanye da fararen half cover, yar saisayyayar sumar kanshi sai shining take abayanshi kuma managern shine kuma mai sakarmashi kida shima cikin shigar suit saidai nashi baqaqe ne da wannan kyakyawan murmushin yaqarasa shigowa wajen yana kallon mutanen wajen dake tafamashi kowa idanunshi akanshi ahankali yadanyi bowing alamun godiya still murmushi afuskarshi habeeb kau tuni yanufi wurin setting dinsu Inda zai dinga sakarmasu kida musabaha Deen yayi da Ahmad dake gaban stage din sai washe baki yake mic din hannunshi Ahmad yabashi ya amsa yana godiya sannan yajuyo yana kallon audience din tun shigowarshi bugun zuciyoyin mutane biyu suka chanza, zee da Aysha Aysha binshi Kawai takeyi da kallo cikin mammaki da bugawan zuciya mammaki take yaushe yayanta yadawo daga tafiyar harya zo nan din, saidai kuma sai take ganin kamar bashi ba duba da wasu dabi'u dayakeyi wanda kamar banashi ba, ga sumarshi yar kadan sa6anin ta yayanta dakeda yawa kuma a kwance luff zee kau bata ganshi ba don yana daga can gefe ne kuma yana facing mutane saidai zuciyarta wani irin bugu take kamar zata faso qirjinta, sosai takejinta awani yanayin da bazata iya musaltashi ahankali Deen yayi gyaran murya sannan cikin harshen turanci ya gaida mutanen wajen yakuma gabatar da kanshi ta hanyar amfani dasunan da akafi sani dashi wato *Balarabe* sannan yatayasu murnar wannan taron dasuke na zagayowar ranar haihuwar diyarsu yana kuma yin fatan allah ya maimaita Tunda yafara magana zee taqame a kujerar datake zaune kwalwarta ke birgita mata cikin kai tana jin kamar bamaa duniyar ba take wannan muryar... waye mai wannan muryar? ahankali Deen yayima habeeb alamun suje zuwa, nan take habeeb yashiga aikinshi Inda ya sakarmasu wani cool kida mai dadin gaske lumshe idanunshi Deen cikin son daidaita nutsuwarshi daya rasa Inda ta fece tun shigowarshi wannan wurin yanemi duk wata nutsuwarshi yarasa, Abinda besaba faruwa dashi ba yasaba hallarta taron daya linka wannan jama'a linki ba linki amma beta6a tsintar kanshi a irin wannan yanayin ba sai wannan karon, meyasa? Ajiyar zuciya yasauke ahankali yana iyakar bakin qoqarinshi wurin cooling down humming yafarayi cikin cool voice dinshi yana lumshe idanunshi ahankali yafara rero waqar birthday dayayi composing saboda taron sosai waqar ke tafiya cikin wata iriyar salo mai narka zuciya tsit wajen ya dauka kowa hankalinshi akanshi suna sauraron yadda yake rairo baitukan waqar cikin qwarewa da salo na daban kasa ko kyafta idanu Aysha tayi akan Deen, kallonshi Kawai take kamar tana kallon wani hallita daban yaushe akhie yazama mawaqi? Tunda yafara waqar zee tarasa awane duniyar take ciki, komai ya burkuce mata, zuciyarta, kwalwarta, ruhinta suka shiga harmutsawa takasa gane takaimaiman Abinda ke faruwa akewayenta Kawai Abinda take iya ji shine wannan muryar Deen kau a bangarenshi shima bugawar da zuciyarshi keyi yafara affecting waqarshi don sai sarqewa yakeyi akai akai duk iyakar bakin qoqarinshi naganin ya daidaita nutsuwarshi abin ya faskara, jiyake kamar zuciyarshi zata tsinke saboda gudu habeeb dake gefe yana playing piano yana lura da yanayin Deen dukda bakowa zaiyi saurin fahimtar uneasiness din nashi ba amma shi yagane don yasan Deen yasan yadda yake aikinshi, dole akwai Abinda yake damunshi dukda Deen nadan kallon gefen zee saidai baya wani tsayawa kallonta don shi kanshi ba Acikin nutsuwa yake ba bare har yatsaya kallon wani abin aymaan duk Abinda ake idanunshi nakan zee yana lura da halin data shiga ahankali yaga tamiqe tsaye daga kujerarta tana kallon Deen daya juya mata baya shima Deen sai akayi daidaitoni ya juyo side dinta cikin waqar yana ambaton birthday girl sauke idanunshi yayi kanta tana atsaye tana kallonshi shima wani irin bugu zuciyoyinsu sukayi lokaci guda dukda basu tantance juna ba don zee bata hangenshi sosai saboda hular kanta shima bega fuskarta ba sosai saboda boye rabin fuskar da hular tayi ahankali ya cigaba da waqar yana kallonta zuciyarshi na lugude _Happy Happy birthday... to... you..._ yaqarashe baitin da daddaya lokacin da zee tasa hannu tazame hular kanta tafada baya cak numfashin su biyu ya dauke na wucin gadi kallon juna suke kamar idanunsu zasu fado Babu mai iya kwakwarar motsi acikinsu tsit wajen ya dauka kowa idanunshi akansu jikin Deen ne yafara rawa yadago hannu yana nuna zee da yatsarshi dake rawa lips dinshi ma na rawa as well "Z... Zainab?.." yafada cikin wata iriyar murya ko motsi zee batayi ba Kuma ko kyaftawa idanunta dake kanshi basayi ahankali yafara kusantota still yana nunata jikinshi na rawa har lokacin "Zainab.." ahankali kowa yafara tashi daga saman seat dinshi kowanne idanunshi akansu harda habeeb shima da besan meke faruwa ba ahankali zee tafara takawa tanayin baya baya ganin yana kusantota kallo daya zakayiwa su biyun kasan babu wanda kecikin hayyacinshi "Zainab.. stop, please" yafada ganin tana qara nisantarshi "stop!" yafada yana nufota da sauri kamar mahaukaci saurin juyawa tayi kamar wanda abin tsoro yabiyo tana tattare rigarta tayi hanyar barin garden "No! Zainab!" inji Deen yana maramata baya "Balarabe!" inji habeeb yana takema Deen baya shima ------ saukowa yayi daga cikin motar ya maida kofar yarufe hannu yasa ya gyara red guntun necktie dinshi sannan ya zagayo ta dayar 6aren motar bude back seat yayi yadan zira jikinshi ciki can saigashi yafito riqeda abu ahannunshi maida kofar yayi yarufe yama kulle motar gabadaya sannan yajuyo dago abin hannunshi yayi yana kallo qaton bunch of flowers ne mai glass vase daga qasa wajen mariqinshi misalta kyawun flowern 6ata bakine saidai masu karatu suyi hasashe da kansu saidai kallo daya xakayi mata kasan tsaddadiyace ta qarshe murmushinshi na gefen baki ya su6ucemashi lokacin dayakai hancinshi jikin flower din ya sinsina qara riqeta yayi dakyau sannan yafara takawa cikin takunshi ta qasaita ya nufi Inda yake kyautata zaton nan ake taron tafe yake yana saqe saqen yadda zata kaya tsakaninsu don yasan akwai chakwakiya agaba yana cikin saqe saqenshi yaji kamar hayaniya na kusantoshi dagowa yayi wanda yayi daidai da bangajeshi da akayi baya baya yayi cikin ikon allah kuma yasamu ya tsayar da kanshi saurin juyawa yayi yabi figure din daya wuce dagudu da kallo dukda wulgin mutum Kawai yagani amma yagane itace juyowa yayi yaga meya biyota saidai kafin yayi hakan yaji anqara bangajeshi again wanda hakan yayi sanadiyar su6ucewar flowern hannunshi ta fadi aqasa jikake tassss! tayi qarar fashewa cikin zafin nama ya damqi gefen rigar wanda ya bangajeshin ya maidoshi baya daqarfi daga yunqurin yin gaba dayakeyi dagowa sukayi atare suka kalli juna lokaci guda oily eyes dinsu na sarqewa ana juna....✍? *please masu kirana ina typing kuna maidomin aiki baya, koyaya nadaga kafin nagama wayar Abinda narubuta ya fece shiyasa ma bana dagawa, please ku dinga yin haquri tunda ku ma kunsan inamuku iya qoqarina* Ummin Fasihu🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:44 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *084* *THE REUNION* wani irin jada baya su biyun sukayi kamar wadanda aka tura da force mai qarfi alokaci daya suka sake wara oily eyes dinsu akan juna suna kallon juna kamar suna ganin wata hallita daban ne ba mutum ba wani irin rawa inner part dinsu ya dauka zuciyoyinsu na wata iriyar halbawa kamar zata faso qirjinsu habeeb ne yafara qarasowa wajen saidai babu shiri yaja wani irin mugun burki lokacin dayayi tozali da Deen guda biyu suna kallon juna dauke numfashinshi yayi yana wani irin kwalalo idanu waje kamar zasu fado daga socket dinsu daidai nan kingin jama'ar suka qaraso wajen Inda suma sukaci karo da the same scene suma anan suka taka burki suna kallonsu kowanne speechless wani irin gasping Aysha tayi mai sauti tana yin baya baya aymaan dake bayanta yayi saurin tarota daga faduwar datayi niyyar yi tafado jikinshi "Hey.." inji aymaan yana kallon yadda take farfar da idanu mummy ce data lura dasu tayi saurin qarasowa wajensu itama takama Aysha din da kejin kanta na juyamata ganin hakan yasa itama umman Ahmad matsowa sai aymaan ya sakarmasu ita ahankali Mussadiq yaqara jabaya still idanunshi dasuka fara sauya launi akan Deen, komai na jikinshi rawa yake ga jijjiyoyin kanshi dasuka fito rad'o rad'o cikin kidima da fitar hayyaci yasa hannu yazaro wata qaramar pistol from nowhere ya nuna Deen da haryanzu yakasa motsi daita yadda jikinshi ke rawa haka hannunshi dake riqeda bindigar keyi don saima yitake kamar zata silale dukda iyakar qoqarin dayakeyi na riqeta sosai "w..who are you?" yafada cikin wata iriyar murya dake rawa sosai duk buda idanu mutanen wajen sukayi suna kallonsu cikin kidima "speak or I shoot!" inji Mussadiq cikin qaraji jikinshi na rawa sosai yana qara nuna Deen da bindigar, kallo daya zakamashi kasan baya cikin hayyacinshi don ko cewa akayi ya danna kunamar bindigar baya iyawa saboda rawan da ilahirin jikinshi keyi shikau har lokacin Deen kasa ko kwakwarar motsi yayi Kawai yana tsaye ne yana kallonshi kamar gunki rolling idanu aymaan yayi cikin zuciyarshi yana cewa 'ai dama nace wannan mutumin mahaukaci ne' "mu..Mussadiq" "speak!" Mussadiq ya katse Ahmad daya fara magana "Mussadiq calm down.." "go away!" yafada yana maida akalar bindigar kan Ahmad "listen son.." "who are you? kusu wanene!" yaqara fada yana pointing dinsu duka yana jabaya, sosai alamun gigita ta bayyana ajikinshi ahankali bindigar ta su6uce a hannunshi dake karkarwa ya cigaba da kallon Deen yana haki "calm down son.. calm down, this is your twin.. Mujaheed" inji Abbu dake qoqarin calming dinshi down dago rinnanun idanunshi yayi ya kalli abbu "yes, Mujaheed.. your lost brother" "No.." inji Mussadiq cikin muryar mai kama da rad'a "yes.." "he's dead" yaqara fada "he's alive" "No" "calm down" "No.. No!" yafada yana dafe kai "Mussadiq.." inji Abbu again yana qoqarin kusantoshi "No, don't come closer.. don't" yafada yana jada baya duk tsayawa sukayi suna kallonshi saurin juyawa yayi cikin sassarfa zai bar wajen sai gani sukayi timm yafadi aqasa gasping mutanen wajen sukayi sukayi saurin nufarshi dagoshi sukayi sukaga kamar ma baya motsi "aymaan quick kawo mota" inji Abbu juyawa aymaan da be motsa daga Inda yakeba tundazu yayi yanufi parking space Ahmad kuma yanufi Deen dahar lokacin baya motsi kamar wanda aka dasa "Deen" yafada yana ta6a kafadarshi saidai beko dago bayan bare ya kalleshi, idanunshi nanan kyar akan Mussadiq habeeb ma yana daga baya kusan shima suman tsayen yayi don yakasa motsawa daga Inda yake saidai ya kalli wannan ya kalli wannan atsakanin Deen da Mussadiq aymaan ne ya qaraso da motar wajen yafito da taimakonshi aka daga Mussadiq aka sakashi abayan mota tareda Aysha da itama tuni tasuma aymaan yashiga front seat dashi da Abbu yayinda Ahmad yaja hannun Deen suka nufi motarshi shima yasakashi a front seat habeeb yayi saurin binsu yashiga backseat shikuma Ahmad yazagaya mazaunin driver ganin hakan yasa su kingin suka shiga wata motar Inda akabar ummy datace zata tsaya tareda zee agidan ajere motocin suka fita daga gidan suka halba titi *** dagudu zee tayi hanyar stairs tana hayewa da bibbiyu bibbiyu ba don allah ya tsareba data sha qasa yadda rigar keta tadeta tana kawo mata tirjiya a gudun nata bata ja burki akoina ba sai dakinsu Inda tashiga ta maido kofar tarufe ta danna sakata sannan tanufi toilet dagudu shima tabude tashige tarufo harda murza makulli. komawa tayi ta jingina da kofar tana maida numfashin gudun datayi _Deen_ _Deen dinta tagani_ _Deen dinta_ hannu bibbiyu tasa ta toshe bakinta dasu tareda silalewa qasan tiles wani irin kuka yazo mata mai tsuma zuciya tashigayi hannunta toshe da baki dukkan ilahirin jikinta na gab gab kuka take da dukkanin zuciyarta jikinta na rawa sosai, she can't believe yau idanuwanta Deen suka gani, Deen dinta, her timid, silly boyfriend. wanda ta yanke qauna dasake sakashi a ido. zuciyarta takasa yarda, kwakwalwarta takasa dauka. bugun kofar dataji ne yasata dan tsagaitawa daga kukan datake kofar dakin ake bubbugawa ana kiran sunanta data saurara saitaji muryar ummy ce sosai take bubbuga kofar tana kiranta tazo ta bude maida kanta zee tayi jikin kofar ta lumshe idanu wasu hawaye nasake gangaro mata tanajin ummy nata haukan bubbuga kofar da kiran sunanta amma takasa koda motsi ne bare ta iya tashi ta budemata *** tsaye yake yana kallon Mussadiq dake kwance bisa gado ta glass kofar dakin a gefe guda kuma yana sauraron Dr dakemusu bayyanin cewa yanzu komai normal dama shock ne kuma lokacin dazai farka zai sakeshi komai zai koma daidai haka ya tsaya yana kallon photocopy dinshi dake kwance ko kyaftawa babu kwakwalwarshi ta hargitse ta yamitse yarasa wane tunani ma zaiyi "Balarabe" muryar habeeb tadawo dashi daga duniyar kallon Mussadiq dagowa yayi ya kalleshi saikuma ya maida kallonshi akan mutanen wajen yana binsu da kallo one after the other mutane biyu Kawai ya iya shaidawa acikinsu, daddy da mummy yarasa meke faruwa, meyasa yake gane gane, wane irin mafarki ne wannan harmutsatse? dafarko yaga Zainab, macen da yasan qila harya mutu bazai qara ganinta ba yazo kuma yaga wani mai irin kammaninshi sak yadda kasan kanshi yake kallo a madubi yanzu kuma mummy da daddy wadanda shidai a Nigeria yasansu, to meke faruwa ne? wannan wane irin birkittacen mafarki ne mai dogon zango? yaushe zai farka? yakamata mafarkinnan yaqare hakanan tunkafin kwalwarshi tayi bursting suma shi suke kallo cikin tausayawa halin dayake aciki don kallo daya zaka mashi kasan tsabar taurin rai ne Kawai yakeyi mammaki ma suke yadda shi ya iya jurewa be suma ba, idanma sumar ne aishi ya cancanci yayita tunda shi kwata2 besan komai ba, everything just came at sudden ne, besan yanada yan uwa ba, besan shi twin bane, besan yanada iyaye bayan wadanda yasan sun rasu ba sa6anin su Mussadiq dasuka san dashi maida kallonshi akan habeeb dake kallonshi yasan mafarki be dakatuwa harsai yaqare amma bazai iya dauka ba kuma soyake ya farka ko ya bar wannan page din na mafarkin ahankali ya matsa kusada habeeb yakama hannunshi yariqe gamm yana kallonshi "habeeb ka fiddani daga nan, ka kaini wajen kaka" shike maganar amma saiyaji kamar bashi ke motsa bakin ba, ganin komai yake amafarki shiru habeeb yayi yana kallonshi yama rasa Abinda zaice mashi "habeeb wani irin mafarki nakeyi, don allah ka tasheni ko ka fiddani daga nan" tasake fada yana Jin kanshi soo empty wani irin tausayinshi ya tsirgama mutanen wajen suna kallonshi cikeda tausayawa "nima mafarkin nake Balarabe, wai ka rabe gida biyu" inji habeeb cikin yin qasa da murya, kallo daya zakamasu kasan they're totally confused "nima, nima naganni agabana, gani tsaye gakuma wani nidin agabana, kuma.. kuma naga Zainab.. Zainab dita, mubar nan habeeb... kwalwata zata fashe" "Kamal" muryar mummy ta katseshi juyowa sukayi suna kallonta babu ko kyaftawa harta qaraso gabansu idanunta sun duri ruwa sosai tausayinshi ke tsuma zuciyarta "Kamal ba mafarki ba kake, this is real"tafada tenderly kallonta yakeyi Babu ko kyaftawa "mummy?" yafada ahankali kamar maison jingina dagaske ita dince kada mashi kai tayi hawayenta na gangarowa "eh son, mummy ce. mummyn Zainab. it's real...taho taho ka zauna" tafada tana jan hannunshi tanufi kujera binta yashigayi kamar rakumi da akala har ta zaunar dashi sai binta da ido yake "Kamal this is real, ba mafarki bane, nice.. mummyn Zainab, wancan kuma daddy, ka tuna? kuma dagaske kaga Zainab kuma dagaske ku biyu ne masu irin kammaninka, kai tagwaye ne" kafeta yayi Kawai da idanunshi yana kallonta confused "iyayenka basu rasu ba, mahaifinka ne Kawai yarasu amma mahaifiyarka nanan, tana nan da ranta, wancan kuma twin dinka ne, kaine Hassan shine Hussain, bayanshi kuma kanada qanwa Aysha duk suna nan Dubai ne, kaima saceka akayi tun kana qarami aka kaika Nigeria amma kai ba dan Nigeria bane, kai Balarabe ne, Dan saudia, mahaifinka mutumin saudiya ne mahaifiyarka kuma yar misra, Kaka ba kakarka bace bakada alaqa daita, ga danginka nan suna nan, saceka akayi.." kuka ne yaci qarfin mummy tashigayi da dukkanin zuciyarta bama ita kadai ba babu wanda babu kwalla a idanunshi idan ka cire Deen daketa kallon bakin mummy tunda tafara magana cikin kuka mummy tace "Deen ba sunanka Kamaldeen ba sunanka Mujaheed.. Mujaheed Al-hassan shikuma twin dinka Mussadiq Al-hassan, kai Balarabe cikkaken Balarabe ne Kamal" batool datakasa jurewa ta rungume umman Ahmad dake kusada ita batareda tasani ba ta cigaba da rusa kukanta kamar ranta zai fita "eh Deen, kai asalinka Balaraben saudiya ne, duk acan mahaifanka suke, acan aka haifeka dakai da Dan uwanka Mussadiq saidai shekararka uku aka saceka aka kasheka ashe baka mutu ba, qila Kawai wucewa dakai akayi aka nuna an kasheka saigashi ankaika Nigeria. mahaifinka yarasu amma mahaifiyarka nanan tana cikin garin nan yanzu haka" inji Abbu shima cikin kwantar da murya bin Abbu shima Deen yake da ido Kawai becewa komai Kawai kallon motsin bakinshi yakeyi "daga baya muka gane hakan, wannan dalilin yasa muka quduri aniyar hadaka da danginka, shine ma dalilin zuwanmu Nigeria lokacin daka fara ganinmu, babu wani aikin daya kaimu, kai ka kaimu Deen kuma bawai saboda aiki yasa muka gayyatoka nan ba mun gayyatoka ne don hadaka da ahalinka da bakasan dasu ba" inji Ahmad da shima idanunshi suka rine aymaan sai kallon Deen yake shima da jajjayen idanunshi yakasa cewa komai saida Deen yagama sauraronsu tsab sannan ya maida kallonshi kan mummy da har lokacin hawayen idanunta sukaqi tsayawa "Kaka..." yafada ahankali kamar mai rad'a "ku kaini wajen Kaka don allah" yafada yana kallonsu cikin wani yanayi hawayen mutanen yakasa tsayawa ganin yadda yake magana so confused kamar dan shekara biyun daya 6ata tsakiyar hanya yana gantali Abbu zaiyi magana aymaan ya katseshi "No Abbu.. zaku fasamashi kwalwa, don't stress his brain futher, yana buqatar hutu, idan kuka takura za'a samu matsala" saikuma ya kalli Deen "kanason zuwa wajen Kaka?" saurin kadamashi kai Deen yayi kamar qaramin yaro "taso to, taso nakaika" yafada yana miqamashi hannu Dan tsayawa yayi yana kallonshi saikuma ya miqamashi hannu ya tadashi aymaan yayi gaba jaye da hannunshi suka fice daga wajen wani kukan batool taqara rushewa dashi, bama ita kadai ba harda sauran matan dakin, mazan nema masu dan tauri taurin rai iyakarsu hawaye kowa jikinshi yayi sanyi lakwas jikin daddy yafi nakowa yin sanyi, ganin Deen a irin wannan yanayin ba qaramin sanyayamashi jiki yayi ba, yarasa Inda zai tsoma ranshi yaji sanyi habeeb dai haryanzu bece komai ba saidai alamu sun nuna shi ya gamsu da bayyanansu don they make sense to him don shima yadade yana zargin Deen ba bahaushe bane, komai nashi sak na larabawa dukda hasken fatarshi ba irin fauu dinnan bane irin na kajin jikin kajin turawa amma dai daka ganshi kaga ruwan Arab haka suka zauna jigum har aymaan yadawo duk dagowa sukayi suka kalleshi "anyi mishi allurar barci to settle his brain" Abinda Kawai ya iya fadamasu kenan duk Ajiyar zuciya suka sauke kowa najin zuciyarshi da ruhinshi badadi daga baya ne suka yanke shawarar yakamata wasu sukoma gida wajensu ummy Abbu da umman Ahmad da abban Ahmad suka tafi sukabar mummy, daddy, batool data maqale sai aymaan da Ahmad suka kwana a asibitin. 💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜 ahankali yafara bude idanunshi dasukayi mashi mugun nauyi dafarko biji biji yafara gani kafin daga baya ganinshi yafara yin clear ahankali yake bin dakin da kallo cikin son tuna inane wajen shikadai ne kwance adakin, ganin yanayin dakin yasashi gane a asibiti yake ahankali yakai hannu yadafa kanshi dake mishi ciwo ahaka yasamu ya lalla6a yamiqe zaune cigaba da bin dakin yake da kallo cikin son tuno Abinda yafaru ahankali abubbuwan dasuka faru jiya suka shiga dawomashi tiryan2 shiru yayi confused, abin tambaya anan shine dukkan wadannan abubbuwan mafarkine ko dagaske yafaru, idan mafarkine meya kawoshi asibiti harya kwanta? yana cikin wannan saqe saqen aka bude kofa aka shigo dagowa yayi ya kalli kofar sai suka hada idanu da mummy wani sanyayyan murmushi ta sakarmashi tana qarasowa ciki nan kingin mutanen suka ida shigowa da daddaya yake binsu da kallo yaga duk mutanen jiya ne, kenan hakan na nufin ba mafarki ba yake? "sannu.. ya jikin?" inji mummy tana masa murmushi tenderly shima murmushinshi yayimata asanyaye sannan ahankali yace "alhamdulillah" aymaan ne yashigo Ahmad biye dashi sai habeeb abayansu duk da idanu yabisu yana tuna every bit of conversation dinsu na jiya saurin qarasowa wajenshi habeeb yayi cikin murnar ganin ya farka "Balarabe" yafada yana kallonshi Dan murmushi Deen yayimashi shima yana kallonshi "ya jikin?" ya tambaya "alhamdulillah" ya amsa mashi shima asanyaye qarasowa aymaan yayi wajenshi shima "sannu..akwai Abinda ke damunka ko kemaka ciwo" ahankali ya girgiza kai "No, just a slight headache" "sannu.. zai daina insha allah..mummy adan bashi wani abu" inji aymaan da to mummy ta amsa nan da tashiga hadamashi tea duk shi suke kallo kamar t.v harta gama hadawa tabashi amsa yayi yana godiya sannan yafara sha yasha sosai sannan ya ajiye, nan ya buqaci yin sallah habeeb ya rakashi bakin toilet yayi alwala yafito sannan yahau sallayar da har an shimfidamashi ya rama sallar asuba don lokacin har gari yawaye don takwas ma tawuce duk fita sukayi lokacin dazaiyi sallar yarage saura habeeb Kawai da Ahmad yana nan zaune ya idar da sallar aka bude kofar atare duk suka dago suka kalli kofar don ganin mai shigowa Aysha ce tsaye abakin kofar batool abayanta hada idanu sukayi da Deen dake kan sallaya har lokacin kafe juna sukayi da idanu yayinda bugun zuciyoyinsu ya tsananta ahankali hawaye suka taru a kumburrarun idanun Aysha tana kallon yayan nata dasu shima dai Deen kallonta Kawai yakeyi yana Jin wani feeling na alaqa mai qarfi gameda ita a zuciya da gangan jikinshi "come in Aysha, come in and say hi to your brother" inji Ahmad dake kallonsu dagowa tayi ta kalli Ahmad saikuma tasake kallon Deen dashima ita yake kallo har lokacin dafa mata kafada batool tayi cikin qarfafa gwiwa hakan yasa Aysha fara takawa kamar wadda kwai ya fashemawa aciki ta nufi Inda Deen yake tana kallonshi saida ta qaraso gabanshi ta tsaya suna kallon juna saikuma tayi qasa ta durqusa cikin daidaita tsayinsu tana kallonshi still sake kafe juna da idanu sukayi na wani lokaci ahankali Deen yasakarmata guntun murmushi bin dimple din tsakiyar gemunshi Aysha tayi da kallo babu kyaftawa "what's your name?" yafada ahankali dagowa tayi tana kallon eyeball dinshi "A..Aysha" tafada cikin rawar murya hawayen idanunta na gangarowa "meyasa kike kuka?" ya tambayeta da harshen turanci saurin goge hawayen tayi tana girgiza kai "n..na daina" tafada cikin muryarta dake a disashe murmushi yayi shima idanunshi na chanza launi miqomata hannu yayi kallon hannun tayi saikuma ta dago hannunta ahankali tasaka acikin nashi ya riqe gamm wani feeling na jini na yawo ajikinsu "dagaske ke qanwata ce?" ya tambaya ahankali yana kallonta wasu hawayen suka gangaromata tana kadamashi kai dasauri "dagaske ni twin ne kuma... kuma inada Mama?" fadawa jikinshi tayi cikin kasa jurewa tafashe da kuka mai ta6a zuciya "eh yaya.. kanada Mama..mai sonka, tana sonka sosai yaya..muma muna sonka yaya.. bamu ta6a mantaka ba daidai da second daya ba tun tafiyarka, meyasa katafi kabarmu?.. meyasa kabarmu da kewarka yaya? karka qara tafiya yaya.. karka qara barinmu.. muna sonka yaya" kuka take sosai koina na ilahirin jikinta banda rawa babu Abinda takeyi, ta qanqameshi sai sheshekar kuka takeyi ahankali Deen yasa hannu ya zagayo bayanta ya rungumeta shima batareda ya iya cewa komai ba sai sauraron bugun zuciyoyinsu abin haryanzu bebar yimashi kama da mafarki ba, wai shikeda family, shikeda qanwa, shikeda mahaifiya lumshe idanu yayi yana sauraron sautin kukan Aysha yana Jin yadda kukan ke ta6amashi zuciya ahankali yaqara bude baki yace "stop crying.. please" kamar cewa yayi taqara saita qara rushewa da kuka tana qara cusa fuskarta a qirjinshi Ajiyar zuciya ya sauke sannan yabude jajjayen idanunshi ahankali "am here now, I promise bazan sake tafiya ba" ya tsinci kanshi da fadin haka qara fashewa da kuka Aysha tayi tana qara qanqameshi kamar zata shige jikinshi shima qara rungumeta yayi zuciyarshi na melting babu wanda zuciyarshi bata motsa ba don masu saurin kuka irinsu batool harsun bude shafi kamar ance yadago sai suka hada idanu da Mussadiq dake tsaye bakin kofa yana kallonsu kafe juna da kallo sukayi kamar sunsamu t.v shima Mussadiq idanunshi sunyi jajur sun dan kumbura harda lips dinshi yanzu babu coat ajikinshi sai t-shirt din ciki kamar dai Deen ahankali Deen yadaga Aysha daga jikinshi idanunshi still akan Mussadiq komawa gefe Aysha tayi tana kallon yayyen nata biyu tana hawaye cigaba da kallon juna sukeyi babu mai ko kyaftawa ahankali Deen ya dago hannunshi ya miqoma Mussadiq binshi da kallo Mussadiq ya cigaba dayi batareda ya motsa ba kowa na dakin shi yake kallo yaga me zaiyi Deen be sauke hannunshi ba kuma be janye idanunshi daga kanshi ba ahankali Mussadiq yashiga takowa yana tunkaro Deen harya qaraso gabanshi kallon hannun da Deen ke miqomashi yayi yana tuna kalamansu daddy *Mujaheed be mutu ba, yana raye kuma yadawo gareku* maida kallonshi yayi akan fuskar Deen yana kallo sannan ahankali kamar wanda ake controlling da remote yadago hannunshi ya dora akan na Deen wani irin electric feeling ya tsirgamasu gabadaya ilahirin jikinsu zubewa Mussadiq yayi on his knees the next minute sai gani mutanen dakin sukayi sun qanqame juna cikin wata iriyar wawiyar runguma "Mujaheed.." Mussadiq yafada cikin wata iriyar murya kamar ba tashi ba "Mussadiq.." inji Deen shima cikin rawar murya wasu hawaye masu zafin gaske suka gangaromasu alokaci daya suna qara qanqame juna "Mujaheed..😭" "Mussadiq😭"...✍? Ummin Fasihu🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:44 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *085* *THE REUNION* sun jima ahakan rungume dajuna kamar zasu shige jikin juna, feeling dasukeji yana tasomasu daga zuciya zuwa ilahirin jikinsu is unexplainable ahankali suka raba jikinsu dana juna suka hade goshinsu waje guda kowanne na mayar da numfashi dago wet eyes dinsu sukayi atare suna kallon juna batareda sun iya cewa komai ba "I thought you're gone..forever" inji Mussadiq cikin muryar rad'a daidai wasu hawayen naqara gangarowa daga idanunshi kasa cewa komai Deen yayi sai hannu daya daga yayi cupping fuskarshi "the memory is still fresh Mujaheed.. nakasa mantawa..lokacin..,lokacin dasuka sakaka amota suka tafi, nan kadai nake iya riqewa.. nasan ya isa na manta saboda dadewa da shudewar shekaru.. amma nakasa.. nakasa kullum sai wannan scene din yazomin a mafarki.. kullum sainayi mafarkinka da yadda aka rabamu..." in between kuka Mussadiq ke wannan maganar "ashe zaka dawo? ashe zanqara ganinka?.. kasan yadda rabuwarmu tayi affecting dina? kasan yadda rayuwata ta chanza bayan tafiyarka?" shidai Deen kallon yadda yake kuka sosai yake shima hawayenshi naqin tsayawa, besan meyake magana akai ba don shi betuna komai ba amma kalamanshi ba qaramin ta6amashi zuciya suke ba bare yadda yaga yana kuka sosai kukan da kallo daya zakayimashi kasan daga qasan zuciya yake tahowa shima Mussadiq grabbing fuskar Deen yayi "ina kashiga all these years? meyasa katafi kabarmu? karka qara wannan gangancin kaji? if you do I'll kill you" yafada yana riqe fuskar Deen sosai murmushi suka saki atare suka sake rungume juna "I won't, I promise" inji Deen yana qara rungume Mussadiq Aysha dake gefe itama ta rarrafo wajensu ta rungumo bayansu atare suka dago suka kalleta da wet eyes dinsu sai suka sakarmata murmushi suka sake rungume juna su ukun suka hade kansu waje guda kowa na dakin share hawayen farinciki yake kowa murmushi a fuskarshi mai nuna farinciki dasuke ta ya wadannan bayin allahn sun dade ahakan sannan suka saki juna kowanne murmushi afuskarshi sai a lokacin suka lurada yadda mutanen dakin suka qara yawa don harda su mummy adakin da kallo duk suka bisu suna kallon yadda suke masu murmushi kowanne farincikinshi yakasa 6oyuwa suma murmushin suka maida masu atare fuskarsu na nuna how grateful they are kafin wani yayi magana acikinsu wani Dr yashigo dakin riqeda waya sallama yayi sannan yace "wannan wayar tunjiya ake kiranta, a dayan dakin muka tsinceta" duk kallon wayar sukayi "akhie, your phone" inji Aysha Jin hakan yasa Mussadiq miqa hannunshi Dr din yabashi, saida yayimashi alamun thank you da ido sannan ya maida hankalinshi akan wayar, lokacin harta tsinke wani murmushi yayi sannan yadago yakalli Deen dake kallonshi "it's ummie" yafada yana nunamashi screen din wayar gaban Deen yafadi saidai bece komai ba sai cigaba da binshi da kallo dayayi ganin yana re-dialing number handsfree yasa shiyasa kowa na dakin kejin sautin ringing din alamun tashiga bugu uku tayi aka daga cikin wata kamillaliyar murya mai sirki da yanayin damuwa akayi sallama ta dayan bangaren gaban Deen yasake yankewa lokacin da muryar tadaki kunnenshi sai kallon wayar yakeyi kamar yana hango mai maganar ta cikinta amsa sallamar Mussadiq yayi cikin wata murya mai cikeda annushuwa yana gaidata da harshen larabci bema ida gaisuwarba ta katseshi itama cikin harshen larabci da "Mussadiq ina kake? dama kabaro Australia? nayita kiran numberka tacan bana samu, yaushe kadawo? kuma kasan jiya Aysha bata dawo ba? gidan wannan qawar tata taje birthday dinta tun yamma amma haryanzu bata dawoba gashi wayarta bata shiga, ina cikin damuwa sosai Mussadiq gashi kaima naita kiranka baka dagawa" tun sadda tafara magana Mussadiq keta murmushi yana kallon yanayin fuskar Deen dayayi kasaqe yana sauraron yaren da ummie keyi, yasan larabci ne amma besan metake cewa ba don bayaji kwata2 sai dan wanda ba'a rasaba wanda suke dan tsinta a islamiyya kallon wayar Kawai yakeyi yabata dukkan hankalinshi yana sauraron muryar da akecewa ta uwarshi ce dafa kafadarshi Mussadiq yayi still yana murmushi sannan ya amsa ma ummie "ummie muna tare daita" yafada yana kallon Aysha dake sauraronsu itama "kuna tare? yaushe kadawo harkuka hade?" inji ummie adayan 6angaren a mammakince "jiya.. karki damu gamunan zamu taho yanzu and guess what" yafada yana kallon Deen "what" inji ummie "zamu tahomaki da wani Abinda bazaki ta6a mantawa ba" yafada yana kallon Deen yana murmushi "menene abin?" inji ummie "sai munzo Kawai, gamunan" daga haka saiya katse kiran dagowa yayi ya kalli Deen daya maidashi t.v tundazu murmushi yayi mashi "are you ready to see your ummie?" yafada yana mashi murmushi gaban Deen ne yaqara faduwa "I..don't know" yafada ahankali murmushi duka yan dakin sukayi "c'mon akhie, just calm down, we'll be there for you and you'll like her I assure you" inji Aysha kada kai Kawai Deen yayi saidai he's very nervous zaije ganin wata kuma wai mahaifiyarshi, shida ya girma da tunanin baida mahaifa amma yanzu wai mahaifiyarshi zaije gani, wannan tunanin nasashi Jin wani iri. tashi Mussadiq yayi yaqarasa gabansu Abbu yana murmushin da ke nuna tsantsar godiya da hallarcin dasukayi masu cikin turanci yafara magana "bansan ta ina xanfara ba amma inaso kusani ko za'a tara dukkan kalaman duniyar nan babu wadda zatayi daidai da bayyana maku irin godiyar damuke muku, allah kadai zai iya sakamaku Abinda kukayi mana" duk murmushi sukayi abbu yace "mu godewa allah son, allah shine yanufi hakan zai faru, allah shine abin godiya" dik kada kai kingin sukayi atare kuma suka furta alhamdulillah cikin tsantsar nuna godiyarsu ga allah subhanahu wata'ala "zamuje gida, inaso kubiyomu don allah" inji Mussadiq din yadda yazage yana magana cikin Kasa dakai da fara'a zai baka mammaki kamar ba wannan proud Mussadiq dinba mai ego "eh to, bazamu ce A'a ba saidai ba dukkanmu zamuje ba, as you can see anan ma bamuda yawa don su daddy sun koma gida dazu saboda wata yar matsalar data taso, so muma munason zuwa can ne amma aymaan da Ahmad suna iya binku, muma lalurace zata hana hakan" inji Abbu basuji dadin hakan ba amma basuce komai ba "Ahmad ina aymaan?" "yana office I guess" inji Ahmad "to kayimashi magana kace yabiku injini" "to shikenan Abbu" "abbu don allah batool tabimu? pleeease?" inji Aysha cikin marairaicewa kallonta Abbu yayi saikuma ya kalli batool itama ta shagwa6e fuska "alright then" inji Abbu dadi sukaji wanda hakan.ya bayyana a fuskarsu "yanzu bari mu mutafi" da addu'ar tsari suka bisu suka fice suka bar daga Deen sai Mussadiq, Aysha, batool, Ahmad da habeeb anan Ahmad yafita don nemo aymaan shikuma Mussadiq yafiddo wayarshi yayi kira a office dinshi yasameshi tareda Abbu yanayin dayaga fuskar aymaan yasa yasan maganar me Abbu kemashi "kajini ko?" "to Abbu" inji aymaan fuskarshi na bayyana rashin jindadin shi "to saikun dawo mu muntafi" inji Abbu yana yin hanyar fita da addu'ar tsari suka bishi harya fita sannan Ahmad yajuyo kan aymaan da ranshi ke a6ace "meye fa'idar binsu din?" inji aymaan afusace "su suka buqaci hakan" "su wa?" "Mussadiq" "mtcheew, idan mukaje me xamuyi musu? ni wlh banason irin wannan tunda anyi mai wuyar ba shikenan ba?" ta6e baki Ahmad yayi yace "wannan Abbu ya kamata ka fadamawa mallam, saida yatafi sannan zakaita.tada jijiyoyin wuya, wannan ai ihu bayan hari ne" wata uwar harara aymaan ya makamashi yakoma ya zauna cikeda takaici dariya Ahmad yayi yace "saika shirya don't keep us waiting" yana kaiwa nan yafice tsaki aymaan yaja cikeda takaici, sosai yaji haushin binsu dazaiyi don shi yanzu haka shirin tafiya gida yake don ganin wane hali zee take don tun jiya take ranshi daita ya kwana gashi ankawo mashi kwafsi shi bega dalilin binsu ba, is not as if basusan hanyar gida bane, kwata2 bega amfanin binsu ba. haka yaita dacin rai shikadai a office din yanajin kamar yayi bindiga acan ward dinsu Deen kuwa Deen keta kallon Mussadiq daketa waya yana bada order daban daban azahiri kallon Mussadiq yake amma a badini hankalinshi ma ba akanshi yake ba, tunaninshi yayi nisa daga duniyar dasuke ciki jiyayi anja hannunshi hakan yasashi dawowa daga duniyar tunanin daya lula yakalli mai kama mashi hannu yaga Aysha ce tana mashi wannan cool murmushin nata irin nashi shima murmushin ya maida mata yana damqe hannunta itama sukayi interlocking yatsunsu ko mintuna shabiyar basu qaraba ordern da Mussadiq yabada suka iso sabbin qannanun kaya ne kala biyu iri daya kala daya ya dauka yaba Deen daya don shima ya chanza don duk kayan jikinsu sunyi squeezing cikin dan qanqanin lokaci suka chanza suka fito sakin baki mutanen dakin sukayi lokacin dasukayi arba dasu biyun ganin yadda suka fito a ainahin identical twins din komai nasu daya baka ta6a banbancewa, Abinda ma yasa yan dakin suka iya babancesu shine sumar kansu Inda na Mussadiq yafi na Deen yawa, baya ga wannan Babu wani banbanci. cikin qanqanin lokaci suka gama shirinsu sukayi shirin tafiya bayan wani Dr ya rubuta masu sallama. atare duk suka fito Inda saida Ahmad yayi excusing kanshi don zuwa tahowa da aymaan. saida aymaan ya6atama Ahmad rai da shiririta kafin yafito suma suka nufi parking space din wata shegiyar danqareriyar mota qirar Lamborghini suka gani awajen Inda ganin habeeb agabanta yasasu sanin aciki zasu dafarko aymaan yaso qin binsu cikin motar yace zai biyo bayansu Acikin tashi amma daga baya ya haqura saboda yadda Ahmad yaita lalla6ashi duk sunyi wannan abin ne kafin su qarasa wajen motar koda suka isa exchanging pleasantries sukayi tsakanin juna babu yabo babu fallasa suka shishiga motar Inda ta kwashesu duka saboda girmanta koda wasa aymaan be kalli gefen Mussadiq ba kamar yadda shima hakan take a 6angarenshi saima dai Aysha da idanunsu ke yawan hadewa Inda da hakan yafaru kowa zaiyi saurin kawar dakai haka sukayi wannan tafiyar in silent for fifteen minutes kafin su isa unguwarsu Mussadiq. tun a farko farkon unguwar zaka fahimci kashigo unguwar manyan mutane sakamakon manya manyan gidajen dasuketa wutowa ahaka har motar ta tsaya a bakin wani tangamemen gate basuyi one minute da tsayuwa ba aka wangale musu qaton gate din motar ta danna kai ciki. tafiya sosai sukayi yadda kasan ba gidan suka shigo ba sannan motar ta tsaya. guards ne takoina suka rurrugo suka tsaya agaban motar acikinsu wani yabude musu kofar duk suka dare suna basu hanya don saukowa da daddaya suka fara saukowa daga motar har suka gama fitowa sosai mammaki ya bayyana afuskokin guards din lokacin dasukayi arba da Mussadiq da Deen sai kallonsu suke dasun kalli wannan saisu kalli wannan saidai babu damar magana "welcome home akhie" inji Aysha tana ma Deen daketa bin harabar gidan murmushi Jin kalmar 'HOME' yasa Deen jin wani iri a zuciyarshi ga yadda bugun zuciyarshi ke qara tsananta at every passing minute "shall we?" inji Mussadiq yana kama hannun Deen daidai entrance aka kawosu so basai sunsha wahalar yin wannan uwar tafiyar ba don daga gate zuwa ainahin gidan akwai tafiya sosai hakan yasa nan da nan suka isa bakin kofar shiga doorbell Mussadiq ya danna sau biyu sannan yaqara juyowa yana kallon Deen da kejin wani uneasiness ajikinshi ga wasu gumin dasuka fara tsatsafomashi a saman goshi, tunda yake beta6a shiga halin nervousness irin na yau ba murmushin qarfafa gwiwa Mussadiq yayi mashi yana dan bugun shoulder dinshi daidai nan aka bude kofar. ganin Mussadiq yasa maid din data bude kofar saurin jabaya tana russunawa cikin girmamawa tana musu sannu dazuwa shigewa yayi still riqeda hannun Deen suka shiga qayyataccen falon daya bayan daya kingin ma suka shiga Inda aymaan ne qarshen shigowa duk sannu dazuwa maid din dake cikin uniform takemusu cikin girmamawa har suka gama shigowa sannan tayi saurin qarasowa falon tana nunamasu wurin zama duk suka zazzauna and within a twinkle of an eye anfara shigomasu da kayan ciye ana diddirewa Aysha taso yin sama dagudu tun shigowarsu amma Mussadiq ya hanata saidai ya tabbatar kowa ya zazzauna sannan yayi excusing kanshi ya haye sama domin iske ummie can. tun bayan tafiyar ummie falon yadauki shiru, Deen dai a zaune yake amma baya cikin nutsuwarshi kwata2 don ko a yanayin yadda yaketa gyara zama zaka gane hakan zuciyarshi bugu take kamar ganga jiyake kamar zai mutu saboda nervousness ahankali yaturahannayenshi biyu tsakiyar cinyoyinshi dake amiqe ta takure yana kallon qasa sunkusa mintuna biyar ahakan kafin sufara Jin tafiya natahowa daga saman stairs bugun zuciyar Deen yaqara speed nan take gumi suka fara tsatsafomashi takoina be dago ba amma yana jin yadda sautin tafiyar keqara kusanto falon ga faint voices dayakeji suna tunkarosu duk daga kai mutanen falon dasuka qagara suga ummie sukayi banda Deen suna kallon su ummie dasuke saukowa daga stairs din kallo daya wadanda basu ta6a ganinta ba sai yau sukayi mata suka san cewa tabbas itace ummie, ko mahaukaci ya laluba zai tabbatar saboda mugun kammanin dake tsakaninsu kamar tayi kaki tundaga nesa tafara sakamasu murmushi tana saukowa Mussadiq abayanta dukda bata shaida kowa ba acikinsu hakan be hanata tarbarsu da fafadan murmushinta ba har suka ida saukowa stairs din cikin larabci tafara musu lale marhaban cikin sanyayyar muryarta datadan manyanta tunda muryarta ta daki dodon kunnen Deen kanshi yaqara kwancewa, inner jikinshi yafara rawa ahankali qara cusa hannayenshi yayi tsakankanin kaffafunshi yana matsesu cikin rikicewa. ida qarasowa cikin dakin sukayi Inda Mussadiq yayiwa ummie masauki a kujerar dake facing dinsu cikin larabci tashiga sake yimasu sannu dazuwa fuskarta fall fara'a sosai tayimasu kwarjini hakan yasa duk suka sunkuyar dakai suna murmushi dan rad'a Mussadiq yayimata akunne hakan yasata yin Dan dariya sannan cikin harshen turanci tasake yimasu sannu dazuwa tana tambayarsu sun iso lfy? duk amsa mata suka shigayi cikin girmamawa suna gaidata daya bayan daya tana amsawa tana kallonsu idanunta ne ya sauka kan Deen da har lokacin kanshi ke akasa ya makure wuri guda kamar maijin sanyi Dan tsiramashi ido tayi sannan takalli Mussadiq dake kusada ita cikin tsokana a harshen turanci don Mussadiq ya gayamata akwai wadanda basajin larabci tace "shikuma wancan d'an nawa fa? tsoron mutane yake?" yar dariya duk sukayi sai Mussadiq yace "da alama" shidai Deen bedago ba saima lumshe idanun dayayi yana sauraron bugun zuciyarshi "d'ana? wai dagaske tsoron.mutane kake?" inji ummie tana kallonshi keenly tana lura da yanayi da dama dake kamanceceniya dana wani wanda tasani haka Kawai taji itama zuciyarta na halbawa tun lokacin data dora idanu akanshi soyake ya dago amma yakasa, tsoro yakeji yakuma rasa na menene "ummie da alamu dai tsoronki yakeji" inji Mussadiq yana murmushi "ni?" inji ummie a mammakince "ga alama nan" yafada yana kallon Deen fuskarshi fall murmushi sake kallon Deen da ina part dinshi kerawa sosai tace "d'ana dago ka kalleni kaji?" zuciyarshi ce tabada damm! lokacin dayaji ta kirashi da d'anta ahankali yashiga dago kanshi kamar mai tsoro cikin bin umarninta harya ida dagowa idanunsu ne suka sarqe dana juna wanda yayi daidai da bugawar zuciyarsu alokaci guda kafe juna sukayi da idanu Inda Deen ke kallon fuskar mahaifiyarshi for the first time in his life yayinda ummie afarko kallonshi take blankly kamar wanda hankalinta yagudu na wucin gadi saikuma ahankali tadawo daidai ahankali idanunta suka shiga warawa akanshi kamar kuma wanda aka tsikara tayi saurin juyowa ta kalli Mussadiq da har lokacin ke kusada ita maida kallonta tayi akan Deen dahar lokacin kallonta yake babu kyaftawa atsorace saikuma taqara kallon Mussadiq qara kallon Deen tayi dasauri sannan taqara kallon Mussadiq kamar wata zarrariya ahankali tafara qoqarin tashi jikinta na rawa, ganin hakan yasa Aysha saurin qarasawa wajen tana riqota juyowa tayi atsorace ta kalli Aysha din saikuma taqara kallon Deen ta kalli Mussadiq "Aysha.. idanuna gane gane sukemin, gani nayi yayanki yakoma biyu" tafada cikin rawar murya tana qoqarin tashi qoqarin maidata zaune Aysha tashiga yi tana cewa "ki kwantar da hankalinki ummie..." "yayanki biyu fa nake gani, ko idanuna sunfara lallacewa ne? kalla kigani ga wani can ga wani nan" tafada tana qara binsu da kallo kamar ta66a6iya "eh ummie su biyu ne, nima nagani" wani irin wara idanu ummie tayi "kema kingani? kinga su biyun" kada kai Aysha tayi tana qoqarin danne hawayenta "eh ummie, aidama su biyu ne, dama su biyu kika haifa" shiru ummie tayi tana kallonta saikuma tace "eh subiyu na haifa amma ai yanzu daya ke akwai, wancan ya... ya..." saikuma takasa idawa sai juyawa datayi tana kallon Deen dake kallonta har lokacin zuciyarta na wata iriyar bugawa kusada ita Mussadiq yazo ya duqa "beyi komai ba ummie, beyi komai ba... gashi nan yadawo gareki" kallon Mussadiq tayi shock all over her face kada mata kai yayi "yes ummie, Mujaheed dinmu beyi komai ba, gashinan yadawo, gashinan agabanki, yadawo garemu" girgiza kai ummie tashigayi unbelievable jikinta na rawa sosai "No" tafada unbelievable "yes ummie Mujaheed is alive"...✍? *I can't go futher, kuyi manage please banajin well🤒* Ummin Fasihu🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:44 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *086* girgiza kai ummie tashigayi cikin rashin yarda, tayaya za'ace Mujaheed na raye bayan an tabbatar agaban idanun mutane ya qone cikin mota "he was kidnapped ummie not killed, dama nasan Dan uwana bazai mutu hakanan ba, nasha ji ajikina akwai wani sashe na jikina a wani wuri, nasha jina incomplete, ashe shine kuma gashi cikin yarda allah yadawo, yadawo garemu ummie dawowa ta har abada" duk wannan maganar da Mussadiq keyi idanunshi nakan Deen dake kallon ummie still itama ummie idanunta na kanshi tana Jin wani irin feeling mai qarfi na yawo a ilahirin jikinta tashi Mussadiq yayi yaqarasa wajen Deen dake makure waje guda har lokacin yariqo hannunshi ya tadoshi tsaye sannan yanufo ummie duk da kallo mutanen falon sukabisu dashi harsuka qarasa wajenta jan Deen Mussadiq yayi qasa ya kasance sun duqa agaban mahaifiyar tasu "Mujaheed ga ummie, ummie ga Mujaheed, rabonku da juna shekaru ashirin da uku kenan amma na tabbata koda bayan shekaru dubu ne kuka hadu bazaku kasa gane juna ba" hawaye sosai kezuba a idanun ummie data kafe Deen dasu shima Deen hawayen yakeyi involuntary yana bin fuskarta da kallo hannu ummie tadaga ahankali tadora afuskarshi kamar mai tsoro, ahankali tashiga tatta6a fuskar "Mujaheed?" tafada tana cigaba da tatta6a fuskarshi "ummie.." Deen shima yafada ahankali "Mujaheed" "ummie na" "Mujaheed na!" tafada daqarfi tana jawoshi ajikinta lokaci daya cikin fashewa dawani matsanancin kuka wani irin warmness yaji lokacin data sakashi ajikinta, warmness din dabazai iya misaltawa ba yasha samun warmness ajikin Kaka idan ta rungumeshi amma wannan na daban ne don sai jiyayi kamar yanarke su cigaba daxama ahakan saboda wani unexplainable sense of comfort dayakeji a jikinta dama wannan ake kira da mother embrace? kuka sosai ummie keyi tana magana at the same time cikin larabci, tariqeshi gagam kamar zata sakashi ajikinta shima dai jiyake kamar yashige cikin jikin natan ne don shima gagam ya rungumeta bayajin Abinda take cewa amma ga duk kalma daya dazatayi saiya amsa da kalmar 'ummie na' kuka suke sosai su biyun kowanne uncontrollable ahakan wani irin tari ya sarqe ummie tashigayi babu kakkautawa Jin hakan yasa Deen raba jikinsu yadago yana kallonta sai yaga she's coughing blood, tana tari jini nafita abakinta arude ya riqota ahannunshi jikinshi na rawa sosai "ummie! no..No, ummie No!" yafada cikin ihun kuka yana dan jijjigata da gudu kingin yan dakin suka qaraso wajensu cikin tashin hankali "ummie kar kiyimin haka please! please stop am scared!" yafada cikin kuka sosai yana mannata ajikinshi not minding yadda jinin ya 6atamashi kaya har lokacin tarin ummie keyi amma a mugun galabaice Mussadiq kau tuni yatashi arude yakoma gefe yafara qoqarin lalubo number family Dr dinsu aymaan ne yaqaraso gaban Deen yana qoqarin amsar ummie ahannunshi amma Deen ya matsa baya yana qara qanqameta "No! go away!... ummie na" yafada cikin fitar hayyaci yana qara qanqame ummie din "calm down ok? she's gonna be ok, kabari nadubata" inji aymaan ahankali "No!" Deen yaqara fada cikin kuka sosai gani yake kamar sake rabasu za'ayi "idan baka bari nadubata ba zamu iya rasata, ka duba kagani she's in a very critical situation, tama suma zamu iya rasata" sai a lokacin Deen yafara dawowa hankalinshi saidai be saketan ba sai maida numfashin dayakeyi "kabari a dubata before it's late, kun dade ba atare ba nasan yanzu bazakaso kuyi rabuwar har abada ba" inji aymaan again cikin persuading voice maganar aymaan tashigeshi hakan yasa yafara nutsuwa qara matsowa aymaan yayi kusada ita yana neman kama ummie din "kawota na kaita saman kujera" maimakon yabashi din saiya qara qanqameta yafara qoqarin tashi daita "easy" inji aymaan yana dan tarosu ganin zasu fadi da taimakonshi Deen yakaita kan dagowar kujerar ya kwantar saidai yaqi matsawa ko inch daga kusada ita saima bake wajen dayayi "alright, kadan matsa nadubata" yafada gently ahankali Deen ya matsa din amma hannunshi na riqe da nata gamm kamar wanda za'a kwacemawa babu 6ata lokaci aymaan yafara dubata ruwa da tissue yafara buqata dagudu Aysha dake tsaye tareda batool sunci kuka sun godewa allah taruga ta dauko tabashi amsa yayi yafara bata ba ummie taimakon gaggawa cikin qwarewa Mussadiq daketa safa da marwa shima tsayawa yayi yana kallon aymaan don har lokacin Dr din daya kirawo be isoba cikin qwarewa aymaan yashiga ceto rayuwar ummie 🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍 zaune take takafe waje da kallo ta glass window dake kusada ita kofin shayi ke hannunta wanda tuni yahuce ma don tunda aka bata kur6a biyu tayimashi takuma fita babinshi idanunta na kafe akan window daya kasance glass ne don ana iya hango waje tarr ta wajen kallo daya zakayi mata kasan bata awannan duniyar tamu kwata2 bude kofar dakin akayi ahankali aka shigo Inda ta barta nan tazo ta sake taddata girgiza kai Kawai tayi sannan tanufeta zee batama san da shigowarta ba saida taji an dafata saurin dagowa tayi daga duniyar tunanin data lula ganin ummy ce yasa tadanyi murmushi tana kai kofin shayin da har yayi sanyi baki murmushin itama ummy tayi mata taja kujera ta kawo kusada ita ta zauna "daughter" takirata ahankali dagowa zee tasake yi ta kalleta "haryanzu baki shanye shayin ba?" qara kai kofin zee tayi abaki ta kur6a dukda rashin dadin dayake mata gashi yayi sanyi "gashinan ina sha ummy" murmushi ummy tayi "ai yama huce ko? mugani kinasonshi ahakan ko ahada wani mai zafin?" saurin bata zee tayi cikin marairaice fuska tace "ni nama qoshi ummy kalla kigani nasha dayawa" kallon shayin da ba'asha ko kwata ba tayi tayi murmushi tace "to shikenan yanzu tashi ki chanza daddy na qasa yana jiranki kutafi yawo" nan take fuskarta tayi brightening "dagaske?" tafada cikin zumudi "dagaske, maza yi sauri kar yaita jira" da sauri ta tashi cikin jindadi dama tagaji da wannan zaman loneliness din tasan koyaya suka fita koda kaso kadan ne zai rage daga cikin damuwarta wucewa bathroom din dakin tayi ummy tabita da ido cikeda tausayawa saikuma tadan girgiza kai sannan ta tashi tafita riqeda kofin shayin zee din *** Ahankali tafara bude idanunta dasuka yimata nauyi da farko biji biji tafara gani sai ahankali ahankali ganinta yafara dawowa akan fuskarshi tafara sauke idanunta yana kallonta itama affectionately lumshe idanu tayi akanshi tasake budewa and he's still there hakan ya tabbatar mata ba mafarki bane kamar yadda tayi tunani "ummie na" yafada ahankali yana qara damqe hannunta dake cikin nashi idanunta ne suka fara qyallin hawayen dasuka fara taruwa a kwarin idanunta girgiza mata kai yayi yana kai hannunta dake hannunshi saitin bakinshi ya sumbata yace "don't ummie, you're sick, please no more tears.. am here" ahankali takai hannun nata tashafi gefen fuskarshi daidai nan hawayen suka gangaro dora nashi hannun yayi saman nata dake bisa kumatunshi yasa dayan hannun yana share mata hawayen "ina katafi kabarmu?" tafada in tears "bazan qara barinku ba" ya amsa mata riqo fuskarshi tayi "karka qara nisantarmu kaji? karmu sake haka dakai" "har abada ummie.. har abada" rungumeshi tayi cikin shauqin qaunar d'an nata mafi soyuwa a zuciyarta shima rungumeta yayi yanajin kamar su dawwama ahakan ahankali Aysha ma ta matso tayi joining dinsu ganin hakan yasa shima Mussadiq qarasawa suka rungume juna dukkansu in a big family hug kowa na dakin murmushi ne afuskarshi na farinciki da taya murna na wannan family reunion din saida komai ya lafa sannan su aymaan suka nemi tafiya anan ummie taso riqesu wai ba yanzu ba su tsaya suci abinci inyaso idan sun tashi tafiya saisu tafi tare don sotake suje suyima su Abbu godiya don they own them much cikin girmamawa sukayi turning request dinta down Inda suka nuna gwara dai su tafin kuma ai batada lafiya tafiya bazata yiwuba agareta yanzu ba don taso ba tabari suka tafi Inda tasa aka kaisu bayan goma ta arziqi data hadosu dashi wanda saida tayimasu tilas sannan suka amsa bayan tafiyar su aymaan ummie tasa aka kirawo dukkan ma'aikatan gidan Inda anan tayi musu introducing Deen amatsayin d'ayan d'anta kuma twin din Mussadiq sosai ma'aikatan sukayi mashi maraba cikin girmamawa a qasan zuciyarsu kuma suna mammaki to ina yashiga tuntuni don sudai basu ta6a ganinshi ba ko sanin dashi anan ummie tabada order ashirya abinci Inda nan take tasa akayo hiring kuku wadda ta iya abincin Africans agefe kuma kaya sosai tasa aka fitar domin yin sadaka ga mabuqata amatsayin nuna godiya ga allah daya bayyana mata d'anta da farko taso sanarda yan saudiya saidai Mussadiq ya hana yace ai zasuje subari Kawai sai sunje shidai Deen dan kallo yazama shida habeeb da aka barsu tare suna kallon irin rawar kafar da akeyimasu kowa burinshi ya faranta mashi. Daga baya wani haddaden part aka kaisu don suyi wanka su shirya Inda part din ma abin kallo ne don ya qayattu iya qayatuwa har lokacin Deen bebar Jin komai kamar a mafarki ba, Kawai gani yakeyi soon za'a tasheshi ya farka yaga komai mafarki ne koda suka gama shiryawa sukayi Acikin wasu tsaddadun kaya wanda tuni akayi musu order su saida suka shirya tsaf sannan suka dawo main falo din Inda anan akayi leading dinsu zuwa dining area wanda izuwa lokacin shake yake kalolin abinci daban daban akusada ita ummie tasashi zama tashiga serving dinshi da kanta, kallo daya zaka mata kasan tana cikin tsananin farinciki shikau Deen maidata t.v Kawai yayi dama gashi akwai asirin kallo ya iya kafe abu da kallo babu ko gajiya duk Abinda tanuna mashi akan yanaso zai kada mata kai Kawai idanunshi akanta, kwata2 baya qaunar Abinda zai janye mashi hankali daga kallon wannan kamillaliyar fuskar tata itama ta lura da kallon dayake mata saidai bata damuba don tasan ba laifinshi bane koda yayi fiyeda hakan don itama tana iya kwana tana kallonshi batareda gajiyawa ba da kanta ta dinga feeding dinshi Inda shikuma yabuda ciki yana amsa Aysha tashiga tsokanarshi wai daga zuwanshi ya kwacemata matsayin autanci dariya duk sukayi ummie na cemata sai hqr don ita yanzu tabar yayenta kuma hira sosai ta kaure atsakaninsu cikin yaren turanci Inda shima habeeb,ba'a barshi abaya ba don 'A' ne a surutu daga bayama komawa yayi basu labarin Nigeria Inda kowa ya kasa kunne suna sauraronshi shikuma yana cigaba da zuba kamar Radio a bangaren Deen kau baya cewa komai sai amsar abincin da ummie ke feeding dinshi yana kallonta affectionately kamar wanda aka hallita don haka hakan wadannan ahalin suka kasance cikin farincikin da basu ta6a Kasancewa ba. *** ahankali take dibar Icecream din da dan qaramin cokalin Icecream din tana kaiwa baki sosai taji dadin wannan fitar don ta ragemata kaso kadan daga cikin damuwarta cigaba dashan Icecream din tayi gefe guda kuma tana sauraron hirar daddy dayake mata duk don yasata nishadi bata cewa komai sai aikin sauraro Kawai saikuma idan akayi abin dariya tadan murmusa daga jiya zuwa yau duk ta chanza, yar jarumtar datakeyi a yan kwanakinnan duk ta fece, she looks so sad dukda yadda take qoqarin 6oyewa tun tana sauraron daddy har hankalinta yabar wajenshi kallon titi take ta front glass yayinda hankalinta yayi nisa da Inda suke lura da daddy yayi cewa hankalinta sam baya taredashi yasashi dan sakin Ajiyar zuciya shima kallo daya zakamashi kasan he's very disturbed as well ahankali ya dora hannunshi guda bisa hannunta dake kan cinyarta wanda hakan yasata juyowa ta kalleshi ganin yana kallonta keenly yasata sakarmashi dry murmushi sannan taqara kai spoon din Icecream din abaki tanasha tace "inajinka daddy" "bakya jina shalele, tunanin me kikeyi?" Dan buda idanu tayi saikuma ta girgiza kai tana qara murmushi "inafa Ji daddy, babu tunanin danake" murmushi daddy yayi yace "tunaninshi kikeyi?" juyowa tayi ta kalleshi saikuma ta kauda kai "wa?" "Deen" yabata amsa yana kallonta qara kauda kai tayi tana hadiye abu mai d'aci "A'a, me zaisa nayi tunaninshi?" "you still love him right?" inji daddy yana maida idanunshi kan titi shiru zee tayi tana Jin yadda kalmar 'LOVE' din tayi tasiri a zuciyarta "No.." tafada ahankali "na tsani soyayya" taqara fada cikin tone dayake bayyana iya gaskiyarta "meyasa? saboda Deen yatafi yabarki? what if... what if ba laifinshi bane?" yafada yana qara kallonta kauda kai tasake yi tana qoqarin maida hawayen dasuke neman tararmata "I don't care daddy, Kawai na tsani soyayya ne daduk wanda zaimin, ko kalmarta banason jin an ambata akusadani" "shalele, Deen..." "daddy please, dakasan yadda maganar nan ke affecting dina da ka daina, banason wata magana datayi alaqa dashi ko soyayya, am fed up, nagaji" yanayin datayi maganar yasa daddy sauke Ajiyar zuciya cikeda tausayinta yasan a halin datake ciki be kamata ya dinga tadamata irin wannan maganar ba, amma ya zaiyi? sosai yakejin guiltiness a zuciyarshi, sosai abin ke damunshi, soyake ya furta koshima zaiji sallamar ruhi. kingin tafiyar sun qarasata ne in silent babu wanda yasake cewa komai har suka iso gida saidai zuqatan kowannensu cike take da saqe saqe daban daban. koda suka qaraso gida su aymaan sunriga da sun iso tuni afalo suka taddasu suna firar Abinda yafaru acan gidansu Mussadiq din zee tunda tashigo suka dan gaisa da mutanen falon tayi sama Kawai abinta don sosai mood dinta ya chanza dalilin maganar da daddy ya tadomata aymaan da shima yana falon binta Kawai yayi da kallo harta haye saman yanajin badadi sosai a zuciyarshi. a daren ranar batool ta tisa zee agaba tana bata labarin yadda haduwar Deen da family dinshi ya kasance babu abunda yafi tsayawa batool kamar yadda taga wannan uban yan girman kan ke kuka kamar yaro don sai nanatawa takeyi tana cewa wlh bata ta6a tunanin ko kowa zaiyi kuka Mussadiq zaiyi ba gwara gwara Deen don shi yanada dakiya babu laifi don weakness dinshi be bayyana ba sosai saida suka hade da ummie. itadai zee aikinta sauraro Kawai don duk surutun da takeyi idanunta a lumshe suke bata cemata ci kanki ba saidai hankalinta na kanta tana sauraronta ga mammakinta kuma tana jin dadin labarin don har jitake dama tana wurin komai yafaru ko babu komai tayi farincikin haduwar Deen da ahalinshi wanda hakan babban burine nata data dade tanason cikashi, dukda babu wata alaqa atsakaninsu yanzu kuma har abada babu alaqar dazata qara shiga tsakaninsu tana tayashi murna, tana taya shi da familyn nashi murnan sake saduwa, tana kuma yimasu fatan alhairi. *10:00pm* zaune suke a wani dan balcony su biyu suna fira kowanne da mug din shayi ahannunshi sanye Deen yake da fararen kayan barci dasukayi mugun haskashi while Mussadiq daga shi sai baqin trouser da farar singlet habeeb kau tuni yabi lafiyar gado don dama shi baya wasa da barci gashi jiya a asibiti ba wani barcin kirki yayi ba hakan yaba su Deen damar samun lokacin fira sosai Inda duk yawancin rabi da kwatan firar Mussadiq keyi Deen kuma yafi yin aikin saurare. Dan shiru sukayi kowanne na kur6ar tea dinshi ahankali kallon Deen Mussadiq yayi yaga he was staring into space da alamu hankalinshi yatafi Dan murmusawa yayi sannan yace "a coin for your thought" kallonshi Deen yayi sai yadanyi murmushi "ba tunani nake ba" "really?" inji Mussadiq yana dariya "yadda kake kafe waje daya da kallo kana sauke Ajiyar zuciya akai akai zaka cemin ba tunani ba kake? tell me, meke saka cikin damuwa bayan gamu?" inji Mussadiq seriously murmushi Deen yasakeyi "babu komai.. I think I'm exhausted" murmushin gefen baki Mussadiq yayi yace "sure, you're exhausted, tunaninta ai ya isa yayi exhausting dinka" kallonshi Deen yayi cikin rashin fahimta "wa?" kashe mashi ido daya yayi yace "kafini sani ai, ummie mana" "ummie?" "yes...I mean your Zainab" Dan wara idanu Deen yayi saikuma ya kauda kai "no, that's not true" "yes, it is. tundazu ai kallonka Kawai nake nasan me kake ciki ai" saikuma yadaga kafadu "anyway banga laifinka ba ai,she worth it, she worth more.,Zainab macece mai kyakyawar zuciya" Deen dake kallonshi yace "kasanta ko kaima?" murmushi Mussadiq yayi "sosai ma, abokiyar fada ta ce amma yanzu nasan idan nahadu da ita dakyar kunya zata bari na iya kallonta" yaqarashe yana qara sipping tea dinshi "abokiyar fada as how?" inji Deen murmushi Mussadiq yasakeyi "tun farkon haduwarmu har zuwa yanzu da fada muke rabuwa.. dafarko fadan gaske ne don alokacin I don't like her don ni gani nake ma batada gaskiya amma daga baya fadan saiyazo yanamin dadi hartakai dakaina nake tsokanota don haka Kawai sainaji ina missing tsiwarta" murmushi yasakeyi "dafarko na dauka bibiyata take da sharri hakan yasa nayi mata rashin mutunci karo da dama ashe da alhairi take bibiyata" Deen dayayi kasaqe yana sauraronshi ya gyara zama yace "tell me, kabani labarin komai please" murmushi Mussadiq yayi yaqara kur6ar shayinshi sannan yace "mun fara haduwa ne awani supermarket Inda naje don haduwa da wani colleague dina...." from A-Z Mussadiq yabashi labarinsu da fadan dasukeyi, aqarshe ya ida da "saiyanzu nagane magangganunta na ranar danasa aka tsaresu kuma maganarta nakan hanya, zaiyi wuya na iya hada idanu daita after all these" shiru Deen yayi cikin sanyin jiki yana Jin babu dadi sosai, sanin cewa duk shine silan wulaqancin da Mussadiq yayimata yasashi jin babu dadi sosai har hakan ya bayyana a fuskarshi "am sorry, nasan bazakaji dadi ba, nima yanzu haka nakeji, jinake kamar na,maido hannun agogo baya nayi deleting wuraren" inji Mussadiq in a serious tone Ajiyar zuciya Deen yayi yace "babu komai Mussadiq, ai rashin sanine, kuma rashin sani akace yafi dare duhu. Kawai inajin babu dadi ne Mussadiq. i've caused her pain upon pain, na cutatamata fiyeda tunanina... nasan bazata ta6a yafemin ba domin ban cancanci yafiyarba" "amma Mujaheed meke tsakaninku daita? farkon haduwarmu daita da sunanka takirani *DEEN* sannan akwai lokuta da dama idan muna tare saita quramin idanu sai takirani da sunanka tana hawaye, dukda su abbu sunyimin bayani briefly Inda suka nuna tasanka basu fadamin alaqarku ba Kawai nunamin sukayi tasanka acan takuma zonan taganni shiyasa suka nemi hadamu" shiru Deen yadanyi sannan ya dan hadiye yawu mai d'aci sannan yace "she's my.. ex girlfriend" wara idanu sosai Mussadiq yayi yana kallonshi "as in?" yafada yana kallonshi cikin mammaki kada mashi kai Deen yayi "mu masoya ne.. ada. she's my first love" shiru Mussadiq yayi shocked for a moment sannan yace "and then? yanzu fa? ya akayi kuka rabu?" ahankali Deen ya lumshe idanu ya bude, kaida ganinshi kasan yanajin ciwon abin "yaudararta nayi" yafada ahankali sake wara idanu Mussadiq yayi "what?" "yes, I betrayed her trust.. na yaudareta na gujeta alokacin da tagama sakankancewa tabani ragamar zuciyarta, am a bad man ko? ofcourse nasan am a bad man, tun a wancan lokacin" "to amma meyasa? dama baka sonta?" inji Mussadiq confused shiru Deen yayi saikuma yayi saikuma yace "har yanzu my heart beats for her and it will continue... forever" shiru shima Mussadiq yayi yana kallonshi sannan yasake cewa "tell me, kabani labarinku from A-Z please" "labarinmu bayada dadi Mussadiq, farkon keda dadi amma qarshen yafi mad'aci d'aci" "dukda hakan kabani Mujaheed, inason sanin komai please" Ajiyar zuciya Deen ya sauke sannan ya ajiye mug din hannunshi yatashi ahankali yataka zuwa bakin balcony din yana kallon harabar gidan dake fayau da haske ga securities takoina "munfara haduwa ne a ranar wata juma'a, ina sauri zan tafi class daukar wani lecture...." and kamar yadda Mussadiq ya buqata tiryan2 yabashi labarin soyyayarsu from A-Z lokacin daya gama bashi labarin sosai jikin Mussadiq yayi lakwas don dafarko ma he's speechless shikau Deen tsohon mikinshi ne yafamo don tuni zuciyarshi tashiga zugi da radadi idanunshi sun kada sosai "to amma meyasa katafi all of the sudden Mujaheed?" Dan murmushi Deen yayi yace "qaddara Mussadiq... qaddarata" "Kuma nayi regreting tunkafin nayi nisa, na azabtu kuma ina kan azabtuwa Mussadiq Kuma zan cigaba da azabtuwa har qarshen rayuwata.. I deserve it anyway" "amma meyasa dakayi regreting baka dawo ba Mujaheed? meyasa kaza6i kayita zama kana cutuwa kana kuma cutar daita" inji Mussadiq "nadawo Mussadiq,nadawo... amma a qurarren lokaci don lokacin tariga tayimin nisan dabazan iya ko hangenta ba" "kamar yaya? lokacin tadawo nan Dubai?" "nima bansani ba, amma da ace lokacin nasan Kawai dawowa tayi nan zan iyayin,komai domin nabiyota, saidai kamar yadda nagayamaka tayimin nisa, nisan nisan da ko muna wuri daya baxan iya mallakarta ba" kallonshi Mussadiq keyi confused "bangane ba? bazaka iya mallakarta ba kamar yaya?" sai a lokacin Deen yajuyo ya fuskanceshi yace "eh mana, batayi aure ba? tayaya zan bibiyi matar aure" wara idanu Mussadiq yayi yana kallonshi "aure? wacece tayi aure?" "Zainab mana, tun bayan nayi breaking heart dinta tayi auren huce takaici which I don't blame her, kai dama bakasan tanada aure ba?" wani irin kallo Mussadiq keyima Deen in confusion, aure? waye yayi auren? badai zee ba "tayaya kasan tayi aure? waye yafada maka?" inji Mussadiq confused "wanda bazaimin qarya ba akanta kuma nagani da idona" "waye bazai maka qarya ba?" "her Daddy"....✍? Ummin Fasihu🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:44 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *087* "her dad? but... when? I mean yaushe tayi auren kuma waye mijinta?" inji confused Mussadiq "tayaya za'ayi insani Mussadiq? all I know shine tayi aure don har i.v card dinta saida nagani da idanuna" inji Deen shiru Mussadiq yayi still confused, dama Zainab matar aure ce? towaye mijin? wani tunani yazo mashi arai, dasauri ya kawar dashi ina? impossible! sake kallon Deen yayi yace "yaushe daddyn nata yagayamaka hakan?" "three weeks bayan tafiyata?" "ina kuka hadu?" "nine nadawo... nakasa jurewa ne... nakasa walwala kuma na nemi dukkan farincikina narasa, alokacin nagani rayuwa batareda itaba is meaningless shiyasa na yanke shawarar dawowa nayi facing koma menene but... it's too late" kallonshi Mussadiq yake tunda yafara magana haryakai aya, Dan shiru yayi kamar mai tunani saikuma yace "dakaje saiyace maka tayi aure?" "eh, haka yacemin kuma yabani evidence kuma ya tabbatar min cewa a lokacin ma bata qasar sun fice honeymoon daita da angonta" "i.v kadai be isa shaida ba Deen" "har hoton bikin saida nagani Mussadiq, tunda kaga na yarda hujjar dayabani takai na yarda din ne" kan Mussadiq yaqara kullewa, kenan dagaske aure yakawo zee nan? "nakasa yarda" inji Mussadiq Dan murmushi Deen yayi mai ciwo yace "nima haka, dafarko nakasa yarda amma daga baya dole na haqura na rungumi qaddarata" "amma be kamata tayi aure ba Kawai don kayi breaking heart dinta, there will never be smoke without fire, ya kamata tayi tunanin dole ne akwai dalilinka nayin hakan... wait, tell me. meye dalilinka na barinta at the first place?" inji Mussadiq yana kallonshi murmushi Deen yayi ya kauda kai Kawai juyo dashi Mussadiq yayi ta hanyar dan dakar kafadarshi "Hey magana fa nake maka" yafada yana mashi wani kallo "baka cemin kanada saurin fushi ba? meye abin fushi anan?" "look ka amsamin tambayata kana qara kuleni" inji Mussadiq da kanshi yadau zafi sosai "meyasa kabarta bayan kana sonta? bayan nasan idan itace kome zai faru bazatayi hakan ba duba da yadda ta jajirce akan soyyayarku dukda rashin amincewar mahaifinta" "saboda ni banida wannan jajircewar? am a coward" shiru Mussadiq yayi yana kallonshi Dan budamashi idanu Deen yayi yace "yes, dafarko naso sarewa a soyayyarta saboda tunanin status dinmu ba daya ba, ita mai kudi ni talaka ina ganin kamar hakan bazai yiwuba... maimakon na gwada sa'ata nagani saina yanke shawarar sarewa wanda ba don da taimakonta ba da soyyayarmu bazata ma samu asali ba na biyu kuma naso sarewa.lokacin da na fahimci kwata2 daddy baya ra'ayina.. maimakon nayi fighting for our love sai naso haqura.. still ba don qarfafa gwiwarta ba agareni da alokacin soyyayarmu ta datse and lastly daga qarshe bayan duk gwagwarmayar damukasha kokuma nace datasha I still back down... wanda hakan ke nuna ni lusari ne... coward" shiru Mussadiq yayi Kawai yana kallonshi yakasa cewa komai janye idanunshi Deen yayi daga kanshi yana kallon harabar gidan absent-mindely "am weak Mussadiq... inada rauni takoina, wannan shike qwarata" sake kallon Mussadiq yayi da dan murmushi a fuskarshi "be kamata na kasance haka ba ko a matsayina na namiji?" "meye rauninka na qarshe? meye dalilinka na qarshe?" inji Mussadiq yana kallonshi in the eyeball kauda kai Deen yayi Kawai bece komai ba "nafarko kanada hujja Mujaheed, abu ne mai wuya mai kudi da talaka suyi soyyaya, yana faruwa but it's rare musanmman da macen itace mai kudin nabiyu kuma mahaifinta bayaso, wannan ma hujja ce don aure batareda yarda daya daga iyaye ba babbar matsala ce, konine ina iya sarewa a wannan ga6ar to amma na qarshen fa? meye dalili? bayan kasamu,amincewar yarinyar da iyayenta har suka baka damar turowa, meye dalilinka na janyewa har ka za6i ka datse karatunka mai matuqar muhinmmanci daka samu dakyar? meye dalili?" inji Mussadiq yana kallonshi sosai kallonshi shima Deen yayi for some seconds da idanunshi dasuka chanza launi sannan ya kauda kai yana kallon gabanshi "Kaka.." yafada ahankali cikin rashin fahimta Mussadiq yace "mene?" "my grandmum" yafada ta yadda zai gane Dan shiru Mussadiq yayi kamar mai tunani saikuma ya kalleshi "wannan matar? wanda ta saceka?" wani kallo Deen yayimashi "babu wanda yasaceni, karka sake fadamata haka, kakata ce, my grandmum" Ajiyar zuciya Mussadiq yayi yana rolling idanu sannan yace "to naji, ita kakar taka ita tasaka guduwa?" "eh" inji Deen ataqaice "akan wane dalili?" "saboda ta isa" inji Deen yana daukar hanyar barin balcony din don kwata2 firar ta ficemashi arai "to amma..." "am tired and sleepy Mussadiq, mubar firarnan please. good night" yana kaiwa nan yashige yabar Mussadiq nan tsaye cikin saqe saqen zuci. a daren ranar kasa barci Deen yayi don sosai wannan firar tasu tafama mashi tsohon mikin zuciyarshi, haka ya kwana yana juyi shima Mussadiq be iya barcin kirki ba don shima sosai abin ya tsayamashi arai sai hada magangganunsu yakeyi yana rarrabasu cikin son samoma kanshi amsoshin tambayoyinshi. *WASHEGARI* suku suku Deen yar tashi, dafarko yaso manta a Inda suke sai daga baya yatuna. har lokacin jikinshi da zuciyarshi asanyaye suke, yanayin komai ne cikin sanyi gashi dama yanada sanyi sai sanyin nashi yaqaru. atare sukayi breakfast da dukkan family din Inda har lokacin ummie ke nan nan dashi don ko alokacin ita tayi feeding dinshi ganin tadamu sosai da suku sukunshi yasashi yin qarfin hali wajen dan gyagijewa yana pretending komai lau Mussadiq kau duk motsinshi idanunshi nakanshi yana kuma lura da yanayinshi, ahakan har suka gama suka koma sama Deen ne gaban mirror yana bottoning din boturan rigarshi besan shigowar Mussadiq ba sai Jin muryarshi yayi daga sama "kakarka tasa kun gudune saboda batada wanda zata nuna kokuma tasa suje wannan introduction din amatsayin yan uwanka kuma tana tsoron don kar ta silar hakan asirinta ya tonu na cewa batada wata alaqa dakai ta jini, right?" dakatar da Abinda yakeyi Deen yayi ya daga kai yana kallon Mussadiq dake jingine da kofa hannayenshi harde a qirji ta mirror din gabanshi tashi Mussadiq yayi daga kofar yashiga tunkaro Deen "hakan yasata sakaku guduwa Inda ba'asankuba bare asirinta yatonu... shikuma daddy saboda haushin yaudarar dakayiwa diyarshi yasashi yimaka qaryar tayi aure don nesantar dakai ga ita har abada" sai a lokacin Deen yajuyo ya fuskanceshi "mene? tayaya kasan qarya yayi?" inji Deen yana kallonshi "to da me kake tunani? cikin sauqi zaisake baka ita bayan ka gudu ka 6ata damarka tafarko? plus dama abin be kwanta mashi ba tunfarko tunda tunfarko yayi zargin zaka yaudareta, guduwarka kuma ta tabbatar da hakan so dole yanemi hanyar rabaka daita na har abada kota halin qaqa" shiru Deen yayi for sometimes sannan yace "to meye tabbacinka akan batayi aure ba?" "Aysha" "Aysha?" "eh... ita qawarta ce sosai, naje nasameta na tambayeta tace gaskiya batada aure dukda bansani ba ko itace,bata bayyana mata hakan ba don abotar tasu ma asalinta shirine, qila dagasken batada auren kokuma tanadashi bata dai bayyana mata bane" hope din da Deen yafara samu da farko farkon maganar Mussadiq yakoma ciki jin Abinda yafada daga qarshe yes it's possible ace tanada auren bata dai bari Aysha tasani bane, amma idan dagaske batadashi fa? wani irin yanayi Deen yashiga, ada yasare kwata2 akan Deen amma wannan dan hope din da Mussadiq yabashi yasa yanajin wani irin yaqini na tasomashi from nowhere "ka shirya zamu gidansu" muryar Mussadiq ta katse mashi tunaninshi "gidansu wa?" inji Deen yana dagowa "zee din mana" Mussadiq yabashi amsa yana nufar bathroom "mezamuyi acan din?" inji Deen again zuciyarshi na bugawa "wannan ne bansani ba" yafada yana fadawa toilet din bin rufaffiyar qofar Deen yayi da kallo batareda ya iya motsawa daga Inda yake ba kuma. *** Tunda ta tashi yau tagama duk Abinda takeyi ta koma ta nade akan gado yau Monday Kuma sunada lectures amma haka Kawai taji bata iya zuwa school din don tasan kotaje babu Abinda zata dauka ganin hakan yasa itama batool yin zamanta don jitayi bata iya zuwa itakadai yanzu haka tana qasa tareda su ummy don bata iya wannan zaman saman irinna zee wajajen bayan la'asar su ummie suka duro gidan dafarko sunso zuwa dasafe amma sanin cewa ba lallai bane su iske mazajen gidan ba yasa suka daga tafiyar zuwa marece alokacin daga mummy da ummy sai batool ke falon zaune suna fira, su Abbu da daddy na part din Abbu, aymaan kuma bedawo daga asibiti ba suna zaune afalo suna fira sukaji qarar doorbell batool ce ta tashi taje domin dubo waye bude kofar tayi nan taci karo da fuskokin dabatayi tsanmmaniba wara idanu tayi cikin mammaki tana cewa "ummie! sannunku dazuwa.. ku shigo" tafada cikin murna tana kaucewa don basu damar shigowa ummie dake murmushi tace "fara dai gayama masu gidan abamu izini tukunna" dasauri batool tajuya takoma falon ta sanardasu mummy suma sunyi mammaki nan suka cemata tashigo dasu kowacce na qoqarin yafa mayafinta da sallama ummie dake gaba tashigo Aysha abayanta rungume juna sukayi da batool da Aysha cikin murnar ganin juna ganin su Mussadiq na qoqarin shigowa yasa batool dan nutsuwa kallonsu tayi, su biyun sanye da kaya iri daya baka ko iya banbancesu itama batool ta sumar kansu ta iya gane Deen aciki kallo daya tayimashi tasan he's so nervous dubada yadda beson ko dago kai habeeb ne ke bayansu wanda shima sanye yake cikin qananun kayanshi masu kyau gabadaya ta gaidasu tana jan Aysha gefe don subasu wurin wucewa amsawa sukayi saidai har lokacin Deen be dago ba ahaka suka shige falon ganin hakan yasa suma shigowa Aysha nama batool rad'an ina zee itama tana bata amsa acikin rad'a cewa tana sama. koda suka shigo falon sai suka iske duk sun zazzauna anata gaisawa hakan yasasu suma qarasowa suka zauna Aysha tashiga gaidasu ummy. saida batool ta gaida ummie tasake gaidasu Deen sannan ta tashi tayi kitchen domin kawomasu abin motsa baki Akan stool din kowacce kujera ta ajiye musu sannan takoma ta zauna kusada Aysha cikin mutuntawa sosai da fara'a su ummy ke gaisawa Inda suma su Mussadiq suka gaishesu cikin girmamawa shidai Deen duk Abinda akeyi yakasa sakin jiki kwata2 don ko dagowa beson yi, sosai yakejinshi atakure musanmman idan yanajin muryar mummy tunanin cewa zee na cikin gidan nan ya hanashi sukuni ko kadan. ummy takira Abbu Inda take sanardashi zuwan baqin nasu ba'a jima ba kau saigasu Abbu da daddy suma sun shigo falon. nan aka shiga sabuwar gaisuwa cikin farinciki da walwala suma yan samarin suka shiga gaidasu cikin girmamawa sukuma suna amsawa cikin kulawa suna masu barka dasake saduwa duk wannan abin da akeyi har lokacin Deen yakasa dagowa yayinda shikuma daddy yakasa janye idanunshi akanshi kwata2 anan ummie tashiga yimasu godiya sosai akan Kasancewarsu silar sake haduwarsu da Mujaheed dasuka dade da fidda rai dashi anan tashiga basu labarin yadda rabuwarsu ta kasance cikin hawaye da yadda hakan yayi silar mahaifinsu kuma mijinta kowa saida ya tausaya mata don sosai labarin ya ta6asu dukda sun sanshi dama godiya taita yimusu har abin yaso yin yawa tana nuna tsantsar godiyarta agaresu hawaye a fuskarta dakyar suka samu tayi shiru sunata rarrashinta da yimata,nuni da ta godewa allah donshi ya tsara komai a yadda yafaru dinnan suma ba wayonsu bane ko dabararsu anan Kuma aka shiga fira wanda duk ta Kaka ce kowanne nakawo ra'ayinshi akanta Inda suka kasa tsayar da matsaya akan ko ita ta saceshi din kokuma tanada alaqa da 6acewarshi anan aka buqaci Deen yabasu labarin iya zamansu daita dukda halin dayake ciki na uneasiness haka yabasu labarin rayuwarshi tun tasowarshi daya bude idanu yasan Kaka babu komai a labarin sai tsantsar kulawa da qauna da Kaka keyimashi nan kansu yaqara kullewa suka rasa a wane matsayi zasusa Kaka dole idan sunason wannan chakwakiyar ta warware su samo Kaka don ita kadai zata iya warware masu wannan sarqaqiyar nan suka shiga shawarar yadda zasu samu Kaka dafarko akace sukoma Nigeria suje su isketa amma firr ummie taqi yarda tace bazata ta6a barin Deen yaqara nesa daita ba saidai sutafi tare haka sukaita shawarwari har daga baya suka samu mafita Inda Deen yabasu tabbacin Kaka zatazo nan Dubai dakanta dasuka tambayi tayaya sai yace abar komai a hannunshi yasan yadda zaiyi. ahaka suka cigaba da tattaunawar har zuwa wani lokaci anan ummie tashiga tambayar ina zee nan akace tana sama, sai ummy tasa su batool suje sutaho daita halan batasan da zuwansu bane. tunda aka ambaci sunan zee Deen yaqara rasa yar nutsuwarshi bugun zuciyarshi ce ta sauya yayinda wani feeling mai tsuma jiki ya mamayeshi sauke kanshi yayi qasa ya cigaba da sauraron firar dasu ummie keyi sama sama yayinda duk hankalinshi da nutsuwarshi suka tattara sukayi hanyar dayaga su batool sukayi, dukda ba kallon wajen yake ba amma gabadaya hankalinshi na wajen. ahankali bugun zuciyarshi tafara sauyawa tana yin doubling ahankali yashiga murza taffukan hannunshi together kamar mai son yin maganin sanyin nan sosai tsigar jikinshi ke tashi yanajin kamar ya dago amma yakasa dagowar ahakan ya tsinkayi muryar da kunnuwanshi suka jima suna bege da marari, muryar da sai yanzu yasan iya adadin kewar dayaimata "Ummie" yaji tafada cikin zazzaqar muryar da har yanzu beji mai irinta ba cigaba dazuwa mashi muryar tayi cikin gaisawar dasuke da ummie kasa riqe kanshi yayi daga qin dagowa ahankali yafara dago oily eyes din nashi kamar wanda ake controlling da remote daidai nan itama ta kallo wajen kamar tasani caraff oily eyes dinshi ya sarqe da nata large pure white eyes din...✍? *ga post din dare😆 nasan wasu harsun fidda rai🙁* Ummin Fasihu🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:44 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *088* Qirjinsu yabada damm lokacin da idanun nasu suka gauraya dajuna ko seconds biyu batayi ba tana kallonshi ta janye idanunta ta maidasu akan ummie dake mata magana murmushi tayi tadan sunkuyar dakai Jin yadda ummie keta mata godiya itama cikin murmushi zee kecewa babu komai ai allah shine abin godiya kasa janye idanu Deen yayi akan zee, gani yake kamar mafarkan daya sabayine kamar ba dagaske ita yake gani ba komai nata nanan her geogous smile, her melodious voice, her breathtaking beauty sanye take cikin wata doguwar hijab harqasa milk colour, fuskarta babu makeup sosai amma she looks so cute ahankali yakejin yadda zuciyarshi ke melting in emotions ga yadda zuciyarshi ke bugu sosai linkin yadda takeyi ada A bangaren Mussadiq ma ita yake kallo dan murmushi na forming agefen bakinshi wanda duk kwakwarka baka iya gane yanayi saishi dakeyin abinshi yadda zee ta basar ta hanyar avoiding qara kallon gefensu yabashi dariya, irin wannan dabi'un nata na Jin kai da class yasa tunfarko tafara burgeshi ahankali yayi gyaran murya sannan yace "hyy good afternoon" ko bata juyo ba ta gane mai muryar kuma tasan daita yake amma saitayi kamar bata saniba don saima kallon Aysha tayi cikin murmushi tana mata magana "yaya namiki magana ummie" inji Aysha tana nuna Mussadiq da qarfi tayi maganar so kowa yaji hakan yasa zee juyawa ta kalli saitin data nuna maimakon idanunta sufada akan Mussadiq din saisuka sake sauka Acikin na Deen da haryanzu ita yake kallo saurin sake janye idanun tayi tana jin yadda zuciyarta taqara bugawa da qarfi "hmm hyy" tafada ahankali batareda taqara kallon gefensu ba "thanks so much for your effort, words can't express our gratitude to you, jazakillah biljannah" inji Mussadiq yana kallonta "amin, thanks too" ta amsa batareda tasake kallon gefensu ba saikuma ta tashi tsaye kamar wadda ke kan allura ta riqo hannun Aysha "let's go upstairs" tafada tana janta "gulma zakuje yi ko?" inji ummy cikin tsokana dariya Kawai sukayi suka tashi su ukun sukayi hanyar sama suka haye. ta qasan ido Deen yabisu da kallo harsuka haye saman wani sad feeling yaji ya mamaye zuciyarshi ahankali ya lumshe idanunshi ya bude yana jin wani daci daci a maqoshinshi sama sama ya cigaba da sauraron firar su ummie jiyake kamar yatashi yafita ko yadanji sauqin Abinda yakeji a zuciyarshi idan yashaqi iskar waje kamar Mussadiq yasan meke ranshi sai ji Deen yayi yana excusing kansu akan cewa zasu dan fita waje jin sun amince yasa Deen saurin miqewa kamar dama akan qaya yake sauran ma suka miqe suka fice wajen atare wajen qarafunan da aka qawata entrance din yanufa yana dafawa yayi inhaling iskar dake kad'awa mai sanyi sannan yafesar qarasowa Mussadiq da habeeb dake bayanshi sukayi suma shiru wajen ya dauka yayinda Deen yakafe harabar wajen da kallo da idanunshi dasuka sauya launi abun da matuqar ciwo ace kuna under roof daya da wadda kake matuqar so da bege amma ko kalma daya takasa shiga tsakaninku ga yadda yaga tanayi ma kamar batama ganeshi ba don ko kallon kirki batayi mashi ba, she looks so okay and calm kamar ma ganinshin be tunamata da komai ba kodai dagasken tayi aure ta manta dashi? tayiwu nan din gidansu mijinta ne, tayiwu Abbu da ummy iyayen mijinta ne, then waye mijin? daidai nan sukaji anyi horn abakin gate atare duk suka kalli saitin gate din daidai lokacin da shima maigadi yaruga don zuwa budewa cigaba da kallon wajen sukayi har aka bude gate din wata ash colour mota ta danno kai tashigo ciki direct parking space tanufa tayi parking kauda kai Mussadiq yayi yana dan ta6e baki don ko ba'a fada ba yasan ko waye bude kofar akayi a bangaren driver aka fito sannan aka maida aka rufe da kallo Deen yabi aymaan daya zagayo ta dayan side din motar ya bude backseat ya fiddo briefcase dinshi maida kofar yayi yarufe ya kulle motar sannan yajuyo hannunshi daya riqeda briefcase dayan kuma rataye da farar lapcoat dinshi hada idanu sukayi da Deen dake kallonshi har lokacin Dan dakatawa aymaan yayi da tafiyar don beyi expecting ganinsu ba saikuma ya cigaba da tahowa yana janye idanunshi daga na Deen Deen dai cigaba da kallonshi yayi har ya qaraso, babu irin tunanin dabaizo mashi ba arai akan aymaan ganin ya kusan qarasowa yasashi dan janye idanu shima yana dan lumshesu yana Jin yadda zuciyarshi kemashi wani irin zafi da sallama aymaan ya qaraso wajen yana Dan kallonsu atare duk suka amsa suna dagowa suna kallonshi banda Mussadiq daya juyar dakai ma dukda shima ya amsa sallamar "likita bokan turai" inji habeeb cikin washe baki murmushi aymaan yayi yace "kune agidan namu?" "eh wlh barka da dawowa" inji habeeb yana Bashi hannu musabaha sukayi aymaan na amsawa da barka dai shima Deen danne zuciyarshi yayi yadanyi forming murmushi yabashi hannu "welcome" yafada ahankali "welcome too" aymaan yafada sunayin musabahan "why are you here?" inji aymaan batareda yako kalli gefen Mussadiq ba bare su gaisa "yanzu muka fito ai" inji Deen kafin susake magana sukaji muryoyin su ummy zasu fito duk atare suka juya daidai lokacin dasu ummie suka fito harda su zee suna fira cikin wasa da dariya "A'a Dr, andawo?" inji ummie don ta shaidashi murmushi yasaki sannan yadan matso yana gaidata cikin girmamawa amsawa tayi cikin kulawa tana tambayarshi ya aiki da alhamdulillah ya amsa yana tambayarta ya qarfin jiki amsa mashi tayi da da sauqi sosai ko bega alama ba cikin dariya yace eh yaga alamu ma ba alama bama kadai duk dariya sukayi banda Deen da Mussadiq da abin bewani basu dariya ba shidai Deen sai kallon aymaan yake akaikaice yakasa janye idanu akanshi Kasancewar idanunshi na akanshi yasa yaga lokacin da aymaan ya dagawa zee gira daya itakuma tayi murmushi shyly tana kauda kai shima murmushin yayi yana binta da wani kallo sauke idanunshi Deen daga kansu yana jin zuciyarshi na yin jingim, jiyake kamar an doramashi qaton dutse akai itadai Aysha bata ma yarda suka hada idanu da aymaan ba don sai kauda kai takeyi tunda talura da yadda yake wani shasha mata qamshi yana hade haden rai idan yaganta ta yanke shawarar fita sabgarshi itama sallama ummie tashiga yimasu bayan ta amshi address dinsu Ahmad akan suma zataje hargida tayimasu godiya, dama kuma already sunyi exchanging number akan zasu dinga kiran juna akai akai akan maganar Kaka har wajen motarsu suka rakasu Inda anan ummie tasa su Mussadiq suka fiffidomasu kayan dasuka zomasu dasu dafarko sunso qin amsa suna cewa yayi yawa gashi dama sun hado su aymaan da tilin kaya jiya nacewar da ummie tayi yasa akan dole suka amsa suna masu godiya sosai Nan sukayi sallama cikin aminci da fara'a kamar wadanda suka dade dasanin juna itadai zee tuni takoma ciki don tunda suka tsaya jayayya akan kaya ta silale ta fece suna nan har motar tasu ta tashi maigadi yabude masu gate suka fice da taimakon su aymaan suka kwashi kayan dasu ummie suka kawo suma suka koma ciki *** cigaba da kai kawo yake waya kare a kunnenshi, kallo daya zakamashi kasan cewa yana cikin damuwa sosai don sosai hakan ya bayyana a fuskarshi haryanzu amsa daya ake bashi, lambobin dayake kira kwata2 basa shiga Ajiyar zuciya ya sauke yana sauke wayar daga kunnenshi sannan yajuyo ya kalleta tana nan Inda take buga uban tagumi, idanunta harsun gaji da zubar da hawaye "innalillahi waina ilaihi rajiun.. meke faruwa ne haka? wlh haryanzu babu wayar kodaya acikinsu datake shiga" inji Alhaji Bashir cikin tsantsar damuwa "innalillahi waina ilaihi rajiun, allahuma arjini fi musibati, wannan wane irin abu ne? kuma harda number abokin naka dayaje wajenshi din bata shiga?" inji mami dake zaune kusada Kaka cikin damuwa "wlh harda ita, I don't know what's going on. dukkansu nambobinsu bata shiga" inji Alhaji cikin damuwa qara fashewa da kuka Kaka tayi cikin dakussashiyar muryarta wadda tagaji da kuka "dama saida raina yabani, saida naji banason tafiyar nan saida naji ajikina tafiyar nan ba alhairi bace, yanzu gashi ta tabbata innalillahi waina ilaihi rajiun, yanzu ina zansakaina ni ma'u? ya zanyi da rayuwata? wlh bazan iya rayuwa babu kyakyawana akusadani ba, wlh mutuwa zanyi" saikuma tafashe da matsanancin kuka Lailah dake kusada ita da damqe hannunta itama tana hawaye tun shekaran jiya wancan suke cikin tashin hankali kwata2 number Deen dana habeeb sunbar shiga gashi shekaran jiya yakamata sudawo amma haryanzu shiru babu su babu alamunsu ga numbersu bata shiga jawo Kaka mami tayi ajikinta tashiga bata baki tana kwantar mata da hankali amma yadda kasan qara zugata takeyi "banida kowa saishi, shima beda kowa saini. tunda ya bude idanu duniya ni kadai yasani nashi, bayan ni besan kowa ba bayada hayaniya, babu ruwanshi da kowa meyasa ake bibiyarshi da sharri? dama ni ban yarda da wannan abokin nashi dayace zaima aiki ba, aiki ace harsai kabar qasarka kaje Inda bakasan uban kowa ba? ai daji ba alhairi bane gashi beda lafiya, akasi kadan za'a samu ciwonshi na namonia (pneumonia) yatashi kuma idan yatashi dakyar yake sha kamar bazaiyi rai ba haka yakeyi abu goma da ashirin duk suntaru sun hau kanshi ya akeson yayi da rayuwarshi? yanzu haka muggai ne azzalumai sunsa yafito yazo qasarsu Inda babu yadda zaiyi dasu, yanzu yazanyi idan wani abu yasamu Kamal? yazanyi da rayuwata?" duk cikin kuka sosai take wannan xancen, tsabar kukan datasha muryarta ma bata fita sosai don tun shekaran jiya take abu guda ko abinci bata iyaci saboda tashin hankali "kiyi hqr Kaka insha allah babu Abinda zai faru dasu, ki kyautata masu zato na tabbata wani akasi akasamu qila amma insha allah zasu dawo cikin qoshin lafiya Kuma karki manta baban yaron abokinane, tsohon abokinane damukayi primary da secondary dashi daga baya kuma aka rarrabu insha allah mundin yana taredashi babu Abinda zai faru dashi na cutarwa" inji Alhaji cikin son kwantar mata da hankali "tsohon abokinka? tsohon aboki fa kace, waya san meya zama bayan rabuwarku? Kawai daga kunyi firamari da sakandiri atare shikenan saika yarda dashi kusani tura jikana wajenshi? wayasan meya zama bayan rabuwarku? ai muggayen mutane.sai daga baya suke zama mugaye bawai la'akari za'ayi da yarintarsu ba" "yanzu dai insha allah daga nan zuwa gobe xan tabbatar nasamo mana information.ko yaya ne akansu, don allah ki.kwantar da hankalinki Kaka, jifa yadda kika koma ko abinci fa bakya ci sai aikin kuka. Balarabe yanzu babu Abinda yafi buqata wanda yafi addu'a, ki kwantar da hankalinki Kaka" inji Alhajin cikin rarrashi "kiyi hqr Kaka mu cigaba da kyautata musu zato.insha allah zasu dawo garemu cikin qoshin lafiya, mu cigaba dayimasu addu'a insha allah zasu dawo garemu cikin aminci" inji mami haka dai suka taru sunata rarrashin Kaka da kwantar mata da hankali Lailah kau na gefe itama damuwa ce rubuce koina a fuskarta, bata jin tana iya jurewa idan wani abu yasamu Balaraben ta, fatanta allah ya kareshi aduk Inda yake ya maido masu shi lafiya. *** Washegari su ummie sukaje gidansu Ahmad Inda su shigar dare ma sukayi musu don saida suka ma kirasu saboda dama sun amshi contact dinsu awajen su abbu sosai su iyayen Ahmad sukaji dadin zuwan nasu Inda anan sukayiwa juna tarbar mutunci godiya sosai ummie tashiga yimusu suma tana samasu albarka musanmman ma Ahmad sosai suma suka nuna babu komai ai d'a nakowa ne suna kuma tayasu murnar sake saduwa Ahmad kau fita dasu Deen yayi waje Inda suka samu wani tent sukayi zamansu suna fira abin mammaki saigashi tasu tayi saurin zuwa daya da Mussadiq don nan da nan suka jiki da juna kan kace me sunyi nisa a firarsu wanda mostly ta Abinda yashafi aikinsu ne wato Business shidai Deen becika sakamasu baki ba don mostly besan akan me suke magana akai ba daga baya ma tashi yayi ya koma gefe ya tsaya yana bin harabar gidan da kallo yana feeling daddadan iskan dare dake kadawa gabadaya daga jiya zuwa yau duk ya chanza yakoma kamar bashi ba sosai damuwa ta bayyana a tattare dashi dukda iya bakin qoqarin dayakeyi na 6oyewa yakasa mantawa da image din Zainab, zuciyarshi taqi bashi sukuni dukda yana tunanin da aure akanta kuma auren wannan likitan yasan indai har tanada auren what he's doing was wrong don it's very wrong kadinga tunanin matar wani saidai yarasa dalilin dayasa yakasa tankwara zuciyarshi akan haka don with every passing minute tunaninta qara addabarshi yake soyyayarta kuma qara qaruwa takeyi hakan yasa duk yabi ya susuce yarasa Abinda kemashi dadi ahakan har lokacin tafiyarsu tayi suka kamo hanyar gida a hanya ummie taita tambayarshi meke damunshi don duk yadda yake qoqarin 6oye damuwarshi musanmman ma agabanta saida tagane yana cikin damuwa murmushi Kawai yakeyi yace babu komai yagaji ne Kawai haka ummie ta kyaleshi ba don ta yarda gajiyar bace saidai bata takura mashi ba suna isa gida ta kadasu part dinsu wai suje su kwanta tunda duk agajiye suke musanmman ma Deen din koda suka shiga part din nasu duk shirin barci sukayi kowa yanemi lafiyar gado ya kwanta bayan sun.kashe wuta Deen dai dama ba barci yakeji ba don haka kwance yake Kawai staring to dark space ya dade sosai ahakan don dare yayi ma sosai don koina yayi tsit, kamar.daga sama yaji muryar Mussadiq nacewa "she's not married" shiru ya ratsa dakin nawani lokacin kafin wutar bedside lamp yakawo sanadiyar kunnawa da Deen yayi "bakayi barci ba?" inji Deen yana kallon side din Mussadiq Kasancewar kowa dama da bed dinshi sai alokacin Mussadiq yajuyo daga juyamashi bayan dayayi "kaima ai bakayi ba" yabashi amsa "me kace yanzu?" inji Deen "nace batayi aure ba" Mussadiq yabashi amsa shiru Deen yayi yakura mashi ido for sometimes sannan yace "tayaya akayi kasani?" "Ahmad ya gayamin, she's not married amma she will be soon idan kayi sake" yafada yana gyara kwanciyarshi shiru Deen yasakeyi na wani lokaci dagaske batada aure? kenan he still has another chance? amma meyasa yace zatayi soon idan yayi sake? "meyasa kace hakan?" inji Deen "saboda akwai masu harinta" Mussadiq yabashi amsa "masu harinta? su waye?" inji Deen yana kallonshi beson ko dauke ido akanshi "kai yanzu baka gane wannan annoying likitan sonta yake ba?" "ni dafarko nayi tunanin shine mijin nata ai" kya6e baki Mussadiq yayi "Zaidai zama idan kayi sake, sonta yake na dade dasanin hakan kuma he can do anything to win her heart don haka kanada babban aiki agabanka" shiru Deen yayi yana tunani yes it's possible ace aymaan son zee yake, bazai manta da kallon dayayi mata ba rannan, the look is something else, gashi the guy is perfect atakoina, ga kyau ga ilimi ga gayu he can easily win any girl's heart saiya tsinci kanshi da comparing kanshi dashi da me da me yafishi? shima aymaan din dame dame yafishi saidai beyi nisa a comparison dinba zuciyarshi ta tuna mashi da matsayinshi awajen zee yanzu zee yanzu ba kallon wancan Deen din nata take mashi ba, yasan kallon mayaudari take mashi, maqaryaci maci amana tunawa yayi da yadda tanuna halin ko in kula dashi ranar nan yitayi ma kamar batasan da wanzuwarshi ba awajen wataqila ma ta tsaneshi ko ganinshi batason yi, gashi shikanshi kunyarta yakeyi, tayaya ma zai iya sake tunkararta? me zaice mata? dawane ido zai kalleta "kayi shiru" inji Mussadiq jin shirun yayi yawa "Mussadiq banajin inada wata dama kuma, banajin zee zata sake saurarata bare tasake bani wata dama, tunkararta da niyyar sake samun yardarta is just a lost battle, bazanci nasara ba" Dan dagowa Mussadiq yayi yana kallon Deen a mammakince "wait.. wai kana nufin harka sare kafinma ka gwada sa'arka?" girgiza kai Deen yayi "meye amfanin gwada sa'ar da kasan baxakayi nasara ba? nasan zee bazata ta6a qara yarda dani ba, nasan yanzu haka ma ta tsaneni" shiru Mussadiq yayi yana kallonshi har lokacin da unknown expression a fuskarshi can yadan saki murmushi yakoma ya kwanta yana cewa "good... kace yanzu nadawo cikin game din kenan" kallonshi Deen yayi "kamar yaya kadawo game?" murmushi Mussadiq yayi "dama ina cikin game din ai, bayyanarka dakuma jin cewa kaima kana ciki yaso sani janyewa amma yanzu no need, am still in" kallonshi Deen yake cikin rashin fahimta can yace "meaning?" juyowa Mussadiq yayi yadda zasu fuskanci juna sosai yace "meaning ina sonta and zan cigaba da trying wajen winning heart dinta" wara manyan oily eyes dinshi Deen yayi "what?"...✍? Ummin Fasihu🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:45 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *089* Dan murmushi Mussadiq yayi ganin irin kallon da Deen kemashi "yes, you know what? Abinda bakasaniba shine a rayuwar nan idan bakayi kau ban wuri akeyi, idan kai kana iya wasa da opportunity dinka wasu irina baxasu iya bada even the slighest chance wajen su6ucewar damarsu ba, what you don't know is kafin zuwanka nafara developing feelings akanta, banace inamata mahaukacin so ba irin wanda bazan iya rabuwa daita ba ko idan narasata zan shiga wani hali, I just like her, attitude dinta na burgeni sosai and idan so samune zanso mallakarta amma zuwanka dakuma jin labarinku yasani jin cewa babu wanda ya cancanceta sama dakai and na yanke shawarar barmaka ita amma tunda you can't do it ina tunanin gwara nadawo cikin game din don bazan iya haqura wannan Dr din yasameta ba just like that" yana kaiwa nan yajuya ya gyara kwanciyarshi yarufe entire jikinshi da bargo kasa dauke idanu Deen yayi akanshi still cigaba yayi da kallonshi yanajin yadda zuciyarshi tayi wani irin jingim wait, is Mussadiq serious? this is crazy! kenan yana nufin yana iya soyayya da wadda yakeso? saiya tsinci kanshi da kishin Mussadiq fiyeda aymaan sai jiyayi yana iya haqura da zee yabarwa aymaan amma badai Mussadiq ba maimakon firar dasukayi yasashi jin sauqin Abinda yake damunshi sai abin yaqara worsen daren ranar be runtsa ba yadda yaga rana haka yaga dare. Washegari Deen yatashi yarasa Abinda kemashi dadi aduniyar nan da zancensu da Mussadiq ya kwana kuma haryanzu zancen yaqi sakinshi shidai gani yake kamar wasa yakeyi, ai da kunya ma yaso wadda yakeso saidai kuma bega alamun da wasa Mussadiq yake ba, what if dagaske yake? ga mammakinshi sai yaji yafi kishin Kasancewar zee da Mussadiq bisa ga aymaan ina? bazai yiwuba, bazai ta6a barin hakan ya yiwuba. Mussadiq kau hankali kwance yake hidindimun gabanshi yana lura da Deen amma yayi kamar besan yana yiba yayinda deep down yake mashi dariya lallai mutum ga kishi ga tsoro, zai koyamashi hankali ne ahaka akayi kwana biyu cikin kwanaki biyun nan Deen ba qaramin shiga damuwa yayi ba he so much crave to see Zainab don wani lokacin saiyaji kamar yayi tsuntsuwa yaganshi agabanta yaga fuskarta koda na second daya ne sosai kewanta da begenta ke nuqurqusarshi agefe guda kuma haryanzu hankalinshi yaqi kwanciya adalilin maganar dasukayi da Mussadiq cikin kwanaki biyun nan babu wanda yasake tada ma Dan uwanshi maganar amma Deen yakasa sukuni don harwani sanyama Mussadiq ido yayi yana studying movement dinshi A bangare guda kuma kewar Kaka ke addabarshi, he missed her so very much, yanaso yaji muryarta koda sau dayane amma ya haqura yaqi kiranta ko bude wayarshi don gani yake it's not yet time. sosai shaquwa da sabo yashiga tsakanin Deen da sabon family dinshi don kowa jidashi yakeyi most especially ummie don ko motsi yayi saita tambayi akwai damuwa? yadda ummie take nuna tsantsar damuwarta da qaunarta akanshi yasa yake iya qoqarinshi wajen 6oyemata halin dayake ciki na damuwa Aysha ma sosai jininsu ya hadu da Deen don sunfi shiri ma dashi busaga Mussadiq she's very fond of him don muddin tana nan to kodayaushe suna tare tana mashi fira kokuma kagansu tana koya mashi larabci shima he's very fond with her don kusan dabi'unsu daya daita habeeb kau anzama dan gida, shi yana waya da mutanenshi na 9ja dukda baya yawan barin wayar akunne gudun kiran Alhaji Bashir shi sosai qasar tayimashi don kusan kodayaushe saiyasa Mussadiq ya hadashi da driver ya dan yawata dashi yaga gari ko kadan qasar bata isheshi ba bare yaji yagaji da zamanta, he's living happily Acikin familyn Deen din. fitowa Deen yayi yana dan strolling yana qarewa gidan kallo haryanzu mammakin irin girman gidan yake don yadda kasan unguwa guda ce tsari da kyawun gidan baya misaltuwa don shi tunda yake beta6a gani ko yataka gida mai irin kyawunshi ba ahankali yake tafiya hannayenshi zube a aljihu sosai Deen yaqara chanzawa cikin yan kwanakinnan, yaqara wani irin kyau da fresh ga kwarjininshi daya sake fitowa sosai. habeeb bayanan as usual, yafita yawon zaga gari dinshi shikuma Mussadiq yana garden yana wasu yan ayyuka a laptop, Aysha kuma tana school. gajiya dayayi dazama shikadai yasashi fitowa shima don yadan sha iska yana tafe ma'aikatan gidan na gaidashi yana amsamasu da dan murmushi harya qaraso garden din garden din ya hadu ga trimmed grass carpet tun daga farkon garden din har qarshe ga wani dan swimming pool daga can kusurwar garden din mai kyan gaske ga shufke shufken kayan itatuwa daya qara qawata garden din yakuma bada shades ga garden din wani iska mai sanyin dadi ke kadawa a garden din, garden din is very quiet sai dan kukan tsuntsaye da akeji akai akai ahankali yanufi Inda Mussadiq yake zaune ya duqufa akan aikin gabanshi Mussadiq besan da shigowarshi ba garden din ba saida yaji motsi akusada shi dagowa yayi daidai lokacin da Deen kejan kujerar dake facing dinshi ya zauna murmushi Mussadiq yayi mashi shima ya maida mashi martani "sannu workaholic" qara murmusawa Mussadiq yayi yace "yauwa ai kaima ka kusan zama hakan, lokacin kadan yarage yanzu haka chanza komai nakeyi yadda zai dawo da sunanmu mu biyu" kalloshi Deen yayi "ban gane ba" "yes, lokaci yayi da zamuyi running komai mu biyu" inji Mussadiq wani kallo Deen yayi mashi "cemaka akayi na iya business? karma kasoma don banada ra'ayin business kwata2" "hmm ai aikin gama ya gama mallam, nufinka ni,zan cigaba da running komai bayan gaka? impossible" "look seriously nifa banida ra'ayin business sam, is better ka cigaba da running abinka yadda kafara don ni bama shi na karanta ba" "me ka karanta?" "engineering" "wow! still ba'a makara ba ai sai ka karanci business din ai shima" "A'a bana ra'ayinshi kwata2 ne, koda xanyi wani abu to engineering zan cigaba dayi" "wane irin engineering ka karanta?" "constructional engineering amma yanzu mechanical engineering nakeso nasake karanta nayi zurfi akai" "why?" "saboda nadan fara aikin mechanic ne kwanakin baya and I love it, zanso na cigaba" "yaushe kayi aikin mechanic?" "bayan rabuwarmu da zee" shiru Mussadiq yayi saikuma yadan kada kai "not bad but still komai saiya koma da sunanmu mu biyu afterall dukiyar ai batawa bace ni kadai tamuce all, aikina Kawai juyamana ita" "nidai A'a, continue the way it is please, karka chanza komai" Dan ta6e baki Kawai Mussadiq yayi ya cigaba da Abinda yakeyi besake tanka mashi ba shiru yadan ratsa wajen "kenan ka iya gyaran motoci?" Mussadiq yayi breaking silent din murmushi Deen yayi "ko kanada wadda za'a gyara maka ne?" murmushi shima Mussadiq yayi "yanzu kam babu amma za'a samu soon, amma you're talented kuma kace da kana carpentry?" kada kai Kawai Deen yayi bece komai ba "wow! ga carpentry ga mechanic ga singing, duk kai kadai?" murmushi Kawai Deen yayi "wane kafiso ciki?" shiru Deen yadanyi can yace "gaskiya mechanic" "why?" "hakanan Kawai aikin gives me joy" Dan shiru Mussadiq yayi cikin tunani sai yace "what of ka koma school ka karanci mechanical engineering din kaga saika bude wani forum kafara displaying dinshi, waya sani ko nan gaba kama dinka qirqirar motocin dakanka?" dan wara idanu Deen yayi "really?" "yes, wannan aikin is very talented something, kaga tunda.kace it gives you joy allah kadai yasan Abinda zaka iya creating if you put it to work" "wow Ka kawo shawara, Kawai haka za'ayi" inji Deen cikin jindadi "but waqarka fa?" "nifa inayin waqa don nishadi ne, banma ta6a tunanin zanci abinci daita ba" dariya Mussadiq yayi "ikon allah kenan ai, amma twinnie kanada basirori wlh, idan babu wannan akwai wannan idan babu wannan akwai wannan duk Inda tafadi shaa nikau daga business sai business, dull me" murmushi Deen yayi yace "business din ma,ai aikin qwalwa ce da basira, babu aikin datafi chaza qwalwa da kai kamar business, you're talented too" murmushi Kawai Mussadiq yayi ya cigaba da danne dannenshi "ya kamata nafara zazzagawa dakai companies.dinmu" inji Mussadiq hankalinshi akan screen din laptop din dan ta6e baki Deen yayi don wannan bashi ne damuwarshi ba asali ma Abinda yakawoshi wajenshi daban shiru wajen yadauka nawani lokaci kafin Deen yace "kaje wajenta?" tsaida Abinda yakeyi Mussadiq yayi for a moment sannan ya dago ya kalleshi cikin rashin fahimta kauda kai Deen yayi, he know he sound stupid amma yakasa jurewa ne "wa?" "kafini sani ai" inji Deen yana harararshi Dan murmushi Mussadiq yayi "tayaya za'ayi insani baka gayamin ba" "gidansu zee" yafada yana kauda kai sake yin Murmushi yayi yana maida hankalinshi akan system "oh! mezai hana? ai da zafi zafi ake dukan qarfe kuma abari ya huce shike kawo rabon wani, ko jiya naje, yauma xanje" wani mugun kallo Deen ke binshi dashi tunda yafara harya kai aya "to karka qara zuwa" yafada yana hade cikkakun girarenshi "saboda?" "saboda she's mine ok? karka qara zuwa kaji na gayamaka" yafada yana fuming don dagaske ranshi ya 6aci dariya Mussadiq ya fashe daita "yaushe tazama taka?" ya tambaya cikin shaqiyanci "dama can tawace kuma a tawan zata cigaba da Kasancewa, so back off!" yafada yana eyeing dinshi "to? kaida ke tsoron tunkararta? cewa fa kayi baka iya facing dinta" "babu ruwanka, that was then amma yanzu I'll fight, I'll fight everyone akanta including you" yafada yana watsamashi harara dariya Mussadiq yasake fashewa daita harda tafi "wow! wayaga fighter, tofa duk wannan courage din daga ina? rannan fa kace kayi backing off" "yanzu kuma nace am IN😬" yafada tsakankanin haqora cikin dariya Mussadiq yace "Alright Alright, aini banida matsala da hakan, ina iya backing off ai idan ka matsa saidai fa zan dora ne idan naga kana neman gazawa" harararshi Kawai Deen yayi ya kauda kai chuckling Mussadiq yayi ya cigaba da aikinshi cikin zuciyarshi yana cewa 'baban kishi' shiru wajen yadan sake dauka sannan deen yace "inane unguwarsu? inason zuwa gidansu" "wajen zee din zaka ko wani daban?" "Ina ruwanka?" inji Deen yana eyeing dinshi😠 dariya Mussadiq yayi yace "ok ok da alamu dai awuya kake, Kawai shawara nakeson baka ne, idan wajenta zaka kaje school dinsu instead zakafi samun damar yimata magana amma idan gidan kaje ba lallai bane kasamu ganinta bama" shiru Deen dake huci haryanzu yayi can yace "really?" "sure" "to inane school din?" "zan kaika" *** Fitowa sukayi daga cafeteria din suna tafe suna fira suna dariya both of them sanye suke cikin abaya saidai kowacce da kalar tata hannayen kowacce rungume da books dayan kuma riqe da yar polythene nylon dake dauke da abubbuwan dasuka siyo a cafeteria din tafiya suke suna fira kamar sauran daliban dake wucewa jefi jefi kamar daga sama sukaji ance "Zainab..." cak zee ta tsaya daga tafiyar datake zuciyarta na bugawa lokaci guda batool ce tajuya saitaga Deen yana takowa wajensu kafin tayi komai taji zee dabata juyo ba ta damqi hannunta tafara janta zasu wuce "Zainab.. Zainab please wait" yafada yana binsu da sauri ganin suna wucewa cigaba dajan batool dake biye daita tayi bata tsaya din ba saima qarama tafiyarta sauri datayi ganin hakan yasa shima qara pace dukda be iya sauri ba harya samu yasha gabansu "Z...Zainab, please listen" yafada yana dan sauke numfashin saurin dayayi wani kallo ta watsa mashi wanda yasa gabanshi faduwa hakan yasashi saurin sauke nashi idanun juyawa tayi zatabi wata hanyar yayi saurin qara shan gabanta "Zainab please" yasake fada pleadingly "wai mallam lafiyarka kuwa?!" tafada atsawace tana jifanshi dawani kallo Dan jabaya yayi sanadiyar ihun datayi mashi don sosai tsawar tashigeshi (ya tsani tsawa remember?) "lafiya zaka zo kana tarewa mutane gaba, who are you?" tafada afusace "kiyi hqr please, am sorry idan kinji haushi" tsaki taja tazo zata wuce don sosai jikinta ke rawa innerly sake tareta Deen yayi "please kibani 5mins muyi magana idan babu damuwa..." "akwai damuwa, banida lokacin 6atawa" tafada bluntly "please Zainab, atleast listen to me, nasan ayanzu babu Abinda kikafi tsanar gani kamar fuskata..." "then meyasa kake gwadamin ita bayan kasan haka" tafada a masifance shiru Deen yayi yama rasa abinda zai sake cewa "Ka matsar mana ahanya mallam zamu wuce" "please Zainab, ki saurareni, kibani dama nayi explaining kaina" yafada cikin magiya "did you owe anyone any explanation?" "yes, I owe you zee, please let me explain" "na yafe explanation din, I don't know you and I don't wanna see ever again" taja hannun batool daqarfi suka wuce "Zainab! Zainab!..." tana jin yadda yake qwala mata kira amma bata juyoba saima saurin datakeyi batool dai na biyeda ita tanayi tana waigen Deen harya 6acemasu wani empty class zee tajasu suka shiga saita saki hannun batool tawuce ta zauna kan wata chair tadafe goshinta binta da kallo batool tayi nawani lokaci sannan ta qaraso wajenta "haba zee, what have you done? dubi yadda kikayima mutuminnan" wani kallo zee tadago tana mata "me nayimashi?" "wannan abin dakikayi mashi wulaqancine be kamata..." "Hey look mallama spare me that ok? babu ruwanki ok? wannan abin be shafeki ba in any way so stick your nose out of my business" tafada cikin fushi idanunta na durar qwalla sakin baki batool tayi tana kallonta saikuma ta kada kai tajuya tafice daga classroom din sake dafe goshi zee tayi dayan hannun kuma ta dafe saitin zuciyarta dashi tana sauke Ajiyar zuciya ahankali lumshe idanunta tayi tana cigaba da sauke numfashi ahankali. Deen ya dade a Inda suka barshi tsaye daga baya ne daya gaji da tsayuwar yajuya yakoma ta Inda yafito tun daga nesa Mussadiq ya hangoshi, Dan murmushi yayi ganin yanayin yadda yake tafiya kamar wanda kwai yafashemawa aciki qarasowa Deen yayi yasa hannu yabude motar yashiga ya zauna kusada Mussadiq dayasha shade dinshi a ido yana sauke Ajiyar zuciya "harka dawo?" inji Mussadiq kadamashi kai Kawai ya iya yi don sosai jikinshi yaqara sanyaya "are you ok?" inji Mussadiq again yana kallonshi furzar da huci yayi sannan yace "yeah" "to ya? mutafi ne?" shiru Deen yadanyi "No katafi, idan natashi dawowa zan kiraka saika turo ko driver kokuma kagayamin yadda zancewa mai cab saiya kawoni" "first option din yayi zan turo driver" inji Mussadiq bude kofar Deen yayi zai fita saiyaji Mussadiq yace "3:00pm suke tashi yau" juyowa Deen yayi ya kalleshi "akwai masjid ai anan ko?" "eh akwai akwai signboards daxaiyi directing dinka" "ok thanks"inji Deen yana rufo kofar "bye saika dawo" inji Mussadiq yana wining glasses din motar yana tsaye motar ta fice daga school din Ajiyar zuciya ya sauke dama yasan this is going to be tough amma ya quduri aniyar jajircewa, wannan karon bazaiyi wasa da any slight chance dinshi ba, yayi determine cewa zaiyi fighting for his love no matter what....✍? Ummin Fasihu🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:45 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *090* Ajiyar zuciya Deen ya sauke sannan yajuya yakoma cikin school din wani tent yasamu yayi zamanshi aciki ya harde hannayenshi a qirji ya zubama harabar school din ido haka Deen yaita zama har lokacin zuhr yayi tashi yayi yafito daga tent din yafara dube duben Inda zaigano hanyar masjid kamar yadda Mussadiq yafada akwai signboards masu directing mutum duk Inda yake son zuwa a school din da taimakon signboards din yagano hanyar masjid din yawuce ciki bayan sallar ne yafito yana tafe yana kalle kallen mutanen dake zirga2 amma harya koma wurin tent din bega mai kama daita ba komawa mazauninshi yayi ya zauna yasake harde hannayenshi a qirji yana cigaba da jiran tsanmmani Tunda Qarfe uku ta buga yaketa baza idanun ganin ta Inda zee zata 6illo mutane da dama dasuka gama lectures din ranar sai fita suke yayinda wasu sai lokacin ma suke gyara zaman tsayawa school din Kasancewar sunada kingin lectures din gaba tun yana hange hangenshi daga zaune harya kai ga ya tashi yafito daga tent din yana bin masu wucewa da kallo qara kai duba yayi ga wristwatch dinshi saiyaga har uku da rabi hakan yasashi fara tunanin kodai suntafi batareda ya lura ba harya fara fidda tsanmmani da ganinta can kamar ance ya waiga sai yaganta tafe da ita da batool wani irin nannauyan numfashi yasauke yana murmushin jindadi beyi wata wata ba yanufesu fuskarshi still dauke da murmushi Tundaga nesa batool ta hango Deen tafe yana sakin cool murmushinshi Dan satar kallon zee tayi dake gefenta saitaga fuskarnan nata amugun tsuke take wanda hakan ya tabbatar mata cewa itama ta ganshi dan ta6e baki batool tayi ta kauda kai daidai nan Deen ya qaraso "Aslm alaikum" yafada still smiling batool kadai ce ta amsa itakau zee ko kallon gefenshi batayi ba taqara gaba ganin hakan yasa itama batool binta maramasu baya yayi "erm... Zainab" yakira sunanta amma ko nuna alamun taji batayi ba "Zainab please listen to me, please" cigaba da tafiyarta tayi yadda kasan he's invisible "Zainab please ki saurareni, just this once please" yafada yana cigaba da binsu haka yaita binsu yana mata magana amma yadda kasan batasan da wanzuwarshi ba har suka qarasa motarsu bude seat dinta tayi tashiga tarufo tana danna lock "Zainab please" yafada yana leqota da glass din motar dake rufe saidai ana iya hangenta Kasancewar ba tinted bane ko kallonshi batayi ba saima wayarta data zaro tana daddanawa haka ya sunkuyo yana mata magana wanda batama iya ji Kasancewar glass din asama yake batool dake kallon komai ta bude mazaunin driver ta shiga itama tana Jin duk badadi ganin yadda zee ke ignoring dinshi tadan tsaya taga kozai janye daga jikin motar amma taga beda niyya hakan yasata tada motar sannan tayimashi horn ahankali yatashi daga jikin motar yana kallon zee dake kallon wayarta har lokacin cikin damuwa matsawa baya yayi don ba motar space and yanaji yana gani motar ta tashi ta wuceshi da kallo yabita harta fice daga school din gabadaya Ajiyar zuciya ya sauke yana jin zuciyarshi cikin qunci yasan dama ba lallai bane zee ta saurareshi ba, ya riga ya tafka kuskuren dazai dade yana danasani, he deserve this and more tunda shi yaja komai, duk Abinda yafaru shine sila yanzun ma saida yagaji da tsayuwa sannan yawuce wurin tent din daya zauna dazu yaciro waya don kiran Mussadiq. ------ shiru motar ta dauka kamar babu kowa ciki tunda suka kamo hanya babu wanda yace uffan acikinsu can batool ta sauke Ajiyar zuciya tadan saci kallon zee dake kallon waje ta window sannan tasake maida kallonta ga titi "gaskiya Zainab Abinda kika yima gayen nan baki kyauta ba" inji batool banza zee tayi ta kyaleta "ko babu komai shi musulmi ne, yayi miki sallama kobazaki yimashi magana ba,atleast answer the salaam amma yayimiki,sallama ko kallonshi bakiyi ba" Ajiyar zuciya zee tayi tana rolling idanunta "wai batool meye damuwanki ne? ina ruwanki dana amsa sallamarshi ko ban amsa ba? what if na amsa acikin zuciyata? please batool kibar shiga wannan maganar idan ba sokike mu sa6a ba" "Zainab ni gaskiya nake fadamiki, kome mutumin nan yayi miki be kamata kiyimashi wulaqanci ba, agaban fa mutane kikayi ignoring dinshi yana binki yana begging dinki amma ko kallo, haba?" "ni nace ya tareni agaban mutane? duk Abinda nayimashi shiyaja, he even have guts dahar zai tareni, mema zai gayamin idan na saurareshi?" "ki saurareshi tukunna mana, bakisan me yazo dashi ba, bakisan me zaice maki ba" "kuma banason sani ok? please and please kifita harkata akan wannan batun batool, banason musamu misunderstanding akan hakan" Ajiyar zuciya batool ta sauke ta cigaba da tuqinta batareda tasake tankawa zee ba itama zee maida hankalinta tayi akan window ahaka har suka isa gida. Washegari ma kamar jiya tana fitowa daga class bayan daukar wani lecture sai cin karo tayi dashi daga dan nesa da class dinsu dauke kai tayi kamar bata ganshi ba tanufi hanyar fita daga wajen binta shima yashiga yi yana mata magana da magiyar ta saurareshi not minding who and who is watching kamar jiya ko kulashi batayi ba ta cigaba da tafiya tama rasa inda zata nufa daga qarshe tayi hanyar class dinsu batool luckily anata suna ajin ana jiran lecturer yashigo hakan yasa itama fadawa class din tawuce wurin zaman batool ta xauna kusada ita "kekuma fa? daga ina?" Ajiyar zuciya zee tadan sauke "class" ta amsa ataqaice "to dakika shigo nan bakiga lecture zamuyi ba" "babu damuwa, I'll take part too" batool zatayi magana lecturer yashigo hakan yasa suka nutsu lecture din ya daukesu almost an hour kafin sugama Inda duk Abinda akeyi hankalin zee ba wajen yake ba yayi nisa bayan lecturer yafita students suma suka fara fita tattare books dinta batool tayi tajuyo ta kalli zee taga hankalinta ma baya kusa kwata2 girgiza kafadarta tayi wanda hakan yasata yin firgigit ta kalleta "lafiyar ki kuwa? tunanin me kike?" Ajiyar zuciya zee tasauke sannan tahau waige waigen class din "wai har angama lecture din?" "A'a ke za'a jira, nidai tashi am hungry nasama ma cikina wani abu" inji batool tana miqewa tashi itama tayi aqasan zuciyarta tana fatan karsu ga Deen idan sunfita kallon agogonta tayi awa daya kenan tasan yagaji yatafi ma da wannan tunanin tafita saidai me tana fita ta hangoshi qarqashin wata bishiya dake daga opposite din class din jingine ya zubama kofar ido ganinta yasashi miqewa daga jinginar da yayi yana sakarmata murmushi saurin kauda kai tayi ta sake rungume books dinta tawani hada rai tazo tawuce nufota yayi hakan yasa tayi hanyar fita wajen da sauri "Zainab... wait" yafada yana binta shima da Dan sauri binsu da kallo batool tayi harsuka fita daga wajen sannan ta girgiza kai itama tafito tayi hanyar cafteria cigaba da bin zee Deen yayi yana mata magana amma ko kallonshi batayi ba tarasa Inda zata dosa kuma don zai iya binta duk Inda taje gashi suda wani lecture sai nan da 30mins data gaji da bin dayake mata saita juyo afusace tana makamashi wani mugun kallo ganin hakan yasa shima dakatawa yana kallonta "meye damuwanka danine? wai who are you ma?" tafada afusace "Zainab..." "tambayarka nayi waye kai?" "Kamal ne.. Kamal dinki" wani kallo tayimashi "Kamal din wa? as far as am concern banta6a sanin mai irin sunan nan ba" "Zainab nasan kina tsananin fushi dani amma don allah ki saurareni even if sau daya ne please... nasan nasaki a qunci dayawa..." "qunci? dawa dawa kasa a qunci? look at me up and down nayimaka kama damai wata damuwa?" rasa Abinda zaice yayi don kwata2 she's not helping matters "Zainab..." "am Happy bakaga haka ba? ko bakaga alama ba? banada wata damuwa daidai da qwayar zarra, quncin me kake magana akai to?" "Zainab..." "look sunana yafita daga bakinka don ba'ayishi don kazo kana cikamun kunnena dashi ba, as far as am concern I don't know you, ban ta6a ganinka ba so please kabar bina kamar wadda kabaiwa Ajiyar kidney dinka, I have nothing to do with you ok? spare me please" tana kaiwa nan ta juya "Zainab! Zainab!!" ina harta wuce furzar da zazzafan huci yayi yana riqe waist dinshi "this is serious" yafada ahankali Ataqaice haka Deen yaita bibiyar zee a school cikin son ganin ta tausaya ko sau dayane ta saurareshi amma a banza don kwata2 qara botsarewa takeyi every passing minute wani lokacin haka zaita binta yana mata magana taqi tankamashi yadda kasan da gini yake wani lokacin kuma tafada mashi baqa saidai duk Abinda take mashi baya sarewa haka yake lallashin zuciyarshi yana cigaba da binta yana baiwa kanshi kwarin gwiwar cewa watarana zata saurareshi kullum haka zaizo ya wuni a school din yana binta batareda gajiyawa ba kwata2 baya damuwa da irin wulaqancin da zee kemashi don yasan he deserve it tunda shine sila wannan karon yayi determine bazai sareba kamar yadda yasaba abaya, he's determine to show zee how far he can fight for her love batool dai abin bayamata dadi kwata2 ita Deen bala'in tausayi yake bata musanmman idan taga yabiyo zee tana ignoring dinshi akwai lokacin da taje tasameshi tace mashi ya kyaleta tunda bata saurararshi yabata space atleast qila tasauko amma saiyace mata karta damu shi Abinda takemashi baya damunshi cos he know he deserve it haka dai ta kyalesu dole ta zubamasu ido Mussadiq ma a 6angarenshi yana sane da duk Abinda ke faruwa saidai ya kyaleshi yana son gani how far he can go and he was amazed as how Deen yaqiyin ko gexau daga qudurinshi na shawo kan zee Deen fa yakoma zee's chewing gum, duk Inda tayi yana biye saidai idan tana a class tun tana mashi masifa harta kyaleshi takoma bata tankamashi ko shekara zaiyi yana zuba sosai wannan taurin kan na Deen yabata mammaki tasanshi very timid da saurin sarewa but this time around labarin na neman chanzawa abubbuwan datake mashi ya isa ya haqura ya kyaleta koda itace autar mata amma ita gani tayima ko ajikinshi kamar ma bashi take mawa ba haryanzu taqi bashi damar explaining kanshi shima kuma haryanzu beda niyyar haqura wani lokacin cikin mutane zaita binta babu Abinda ya dameshi saidai ita taitajin kamar ta nutse tagaji, tagaji sosai da wannan nacin na Deen hakan yasa watarana daya biyota yana mata magana tayi wata hanya binta yayi yana cigaba dayimata magana har sukaxo wani wuri da babu mutane juyowa tayi tana kallonshi hannaye riqeda kugu hakan yasa shima tsayawa yana kallonta shiru yabiyo bayan haka suna kallon kallo "gayamin me kakeso, mezanyi maka kabar bina kamar snail and it's shell?" ta tambaya a qule murmushi keson kufcema Deen amma yayi saurin hadiyewa "inason ki saurareni ne please" "ok ina sauraronka meya faru?" tafada cikin qosawa rasa ta ina zaifara yayi "you have 2mins" tafada tana kallonshi "Zainab it's about Abinda yafaru atsakaninmu ne, Don allah kiyi hqr ki gafarceni, nasan ban cancanci yafiyarki ba amma Don allah ki yafemin..." "na yafemaka, shikenan?" ta katseshi da hakan Dan buda idanunshi yayi "d..dagaske?" "dagaske, yanzu zan iya tafiya?" cikin jindadin yafiyar datayi mashi yace "oh thank you, nagode nagode sosai Zainab" "it ok, now I'll get.going karka qara bibiyata kuma" tafada zata wuce saurin tare gabanta yayi yace "No please Zainab" "meye kuma?!" tafada afusace "O'O! please don't shout" yafada pleadingly harara ta gallamashi jin ya ambaci sararshi "Zainab I know Abinda zance yana iya 6ata miki rai amma kiyi hqr, please mukoma kamar da please, Zainab I still love you, wlh haryanzu my heart beats for you please.." "how dare you?" tafada ahankali idanuwanta na kadawa shiru yayi ganin reaction dinta "how dare you say that to me?" "Zainab am sorry but.. that's the pure truth, I love you Zainab, ban ta6a daina sonki ba kullum soyayyarki banda qara hauhawa babu Abinda takeyi a zuciyata" "qarfin halinka ashe yawuce yadda na musalta?" tafada tana kallonshi sosai kamar da mammaki "kiyi hqr zee, amma this is the truth... I love you... I still love you, I never stop loving you and I'll never stop" Dan murmushi zee tayi "wane irin love kake magana akai don ya kasu kashi kashi" "true love zee, inamaki soyayya ta gaskiya" "soyayya ta gaskiya, irin wanda kesa agudu abar heart breaking letter?" lumshe idanu Deen yayi zuciyarshi na zafi "Zainab..." "ko irin wanda kesa a karya alqawari?" "Zainab kiyi hqr" "ni tambayarka nayi bacewa nayi kabani haquri ba" tafada hawaye na taruwa a idanunta "wacce daga ciki kake nufi?" "Zainab... nasan na yaudareki nakuma ci amanarki amma..." saikuma yarasa Abinda zaice "yes? amma me?" tafada tana kallonshi hawayen idanunta na barazanar zuba to her greatest surprise saitaga yafara yin qasa before she knew it yana kan knees dinshi wara idanu tayi tareda kyafkyaftasu akanshi "amma kiyi hqr zee, kiyi hqr... banida hujjar dazan kare kaina kona wanke kaina illa nabaki hqr" "Deen meye haka kakeyi?" tafada tana dan jabaya "kiyi hqr zee" "ka tashi" tafada hawayenta nazubowa "No zee, I can lay for you ma, nidai Kawai ki yafemin" ganin zaiyi laying din yasata cikin tsawa tace "stop!" ganin be saurareta yasata qarasowa gabanshi dasauri itama ta zube a gwiwowinta tana tareshi "I said stop!" tafada tana turashi baya "nacemaka kayimin kneeling ko kayimin laying ne?" tafada cikin kuka "I don't know what to do again Zainab" yafada idanunshi na kadawa sosai "ni nace kaimin wani abu? you always make me cry, Ka qware wajen sani kuka, kanajin dadi kaga ina kuka ko?" tafada cikin kuka sosai girgiza kai Deen yayi yana matsowa kusada ita "A'a wlh, Zainab aduk duniya,babu Abinda na tsana sama da kukanki, I hate seeing you cry" "amma kuma kake sani? duk wadancan daka sakani be isheka ba saika qara sani?" tafada cikin kuka sosai dama qiris take jira "Zainab kiyi hqr, please forgive me, bansan yadda akayi nima nake saki kuka ba, I swear it's again my wish" "against your wish? katafi kabarni Deen, shima against your wish ne?" sunkuyar dakanshi yayi daidai da digar hawayenshi "nasoka da dukkan zuciyata Deen, nabaka amana na yarda dakai na damqamaka amanar zuciyata as a whole amma kai mekayi? you broke it into pieces and throw it back at me!" runtse idanunshi Deen yayi gam zuciyarshi na mugun zafi "katafi kabarni Deen alokacin danafi buqatarka, ka kunyatani, you betrayed my trust for you!" "am..sorry" yafada cikin rawar murya sosai "katafi without even looking back for once, katafi kabarni without caring wane hali zan shiga... sau daya ko,sau daya,baka ta6a waiwayena ba" rufe fuskarshi Deen yayi da taffukanshi zuciyarshi na wani irin zafi "kuma shine yanzu zakace kana sona kuma? are you this cruel?" tafada tana kallonshi da jajjayen wet eyes dinshi ahankali Deen ya janye taffukanshi daga fuskarshi datayi ja ga hawaye a cheeks dinshi "Zainab nasan nasaki a qunci da baqinciki, nasan nayi breaking heart dinki amma wlh bada son raina bane nayi hakan kuma nima na azabtu don tun bayan rabuwarmu dake ban qara farinciki ba.." "shiyasa har kayi moving on harka zama wani a duniya? while nikuma inanan nakasa gaba nakasa baya" Dan lumshe idanu Deen yayi yabude yace "Zainab duk Abinda nazama aduniya kece sila, kece silar sanina a duniyar nan da'akayi" "katafi kabarni Deen batareda tunanin kadawo kaga halin daka barni,acikiba ko sau daya" "Zainab nadawo, wlh nadawo... nakasa jure zama babu ke wlh adaddafe nayi three weeks nadawo amma...amma aka tareni da mummunan labarin daya girgiza zuciyata akace min wai...wai kinyi aure kinbar qasar" dagowa zee tayi tana kallonshi da rinnanun idanunta "ni?" tafada ahankali "eh zee, fadin halin dana shiga aciki a lokacin baxai misaltuba, kusan haukacewa nayi, zee nayi kuka, nayi nadama nayi danasani kuma ina kanyi, wlh tun bayan rabuwarmu basake farinciki ba rayuwata bata sake tafiya daidai ba" shiru Kawai Zainab tayi tana kallon yadda yake magana yana hawaye kallo daya zakamashi kasan da dukkan gaskiyarshi yake magana "Zainab ki saurareni yau zan fadamiki komai, zan fadamiki silar komai" shiru zee tayi tana kallonshi nawani lokaci sannan tace "ina sauraronka"....✍? *naso mugama Deen kafin babban sallah amma allah be yarda ba, anyimana haihuwa najiki sosai so baxan dinga samun damar posting ba don haka anan zan tsaya harsai bayan sallah idan allah yakai ranmu, allah yanunamana wucewarta lafiya🤲🏻* Ummin Fasihu🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:45 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *091* *Barka da sallah to you all, fatan anyi sallah cikin qoshin lfy, allah ya maimaita mana🤲🏻* "it all started ranar damuke waya dake daddy dinki yayi banging in naji komai.. naji duk fadan da daddy yayimiki da kalamanshi akan soyayyarmu..." _*FLASHBACK*_ _"wato ke bakyajin magana ko? duk abinda nake gayamaki ta kunnen dama yake shiga yafita ta haggu ko? dama bakida hankali bansaniba?"_ _"ina nunamiki hanya kina rufe ido! kinje kina biyewa wancan dan iskan yaron ya huremaki kunne ya bushe maki idanu bakya ganin kowa da mutunci ko? eh!!"_ _"kullum kinacan banda qara liqemashi babu abinda kikeyi ko? and itama good for nothing uwarki babu abinda takeyi sai goyon bayanki ko?"_ cikin kuka sosai yajiyo muryar zee nacewa _"don allah daddy kayi hqr wlh ina sonsh..."_ cikin ihu sosai yaji daddy ya katseta da _"will you shut that your dirty mouth up! are you stupid! ina yimaki magana kina min zancen banza zancen wofi?!"_ _"harni zaki fadawa soyayya? ni zaki fadawa kina sonshi! soyayyar banza soyayyar wofi! soyayyar dakike mashi yakai wacce nakemaki koko soyayyar dayake miki takai wacce nakemaki? wato ni kuka maida shashasha ashe? ni inacan ina haukana ku kunacan kuna abinda kukaga dama babu abinda ya dameku.. am disappointed in you Zainab, very disappointed"_ kitt... Deen ya katse kiran don jiyayi bazai iya cigaba da saurare ba sosai jikinshi yayi sanyi musanmman idan yatuno sautin kukan zee dayake jiyowa qasa qasa tashi yayi daga kishingiden dayake kan katifarshi ya zauna ya jingina da bango sosai zuciyarshi ta quntata ga wani d'aci d'acin dayakeji a maqoshinshi haka ya zauna shiru na wani lokaci ya kafe wuri guda da ido besan iya lokacin daya dauka ba ahakan sai jiyayi haske ya dallomashi fuska sanadin yaye labulen dakinshi da akayi dagowa yayi ya kalli kofar yaga kakace "wai kyakyawana kwana biyun nan meke 6oyeka a daki? saikazo kashige kayi shiru kamar wata amaryar qauye, badai bakajin dadi bane kake 6oyemin?" inji kaka tana qarasowa gyara zamanshi yayi yana kokarin gyara yanayin fuskarshi "A'a kaka Kawai nagaji ne shiyasa nashigo nadan kwanta" "Ka kwanta? kwanciyar lafiya yanzu bayan la'asar? maza tashi to kaje can shagon Abba ka qaromana barkono don naga wancan be isa kaga zaka dan warware ma idan kadanyi tafiya amma idan ka kwanta yanzu ai kasan abinda zaka jawowa kanka" tafada tana kwance ha6ar zanenta "to" ya fada yana qoqarin tashi kudin tabashi tana fadamashi abubbuwan dazai siyo sannan tarakoshi har tsakar gida saida taga fitarshi sannan takoma ahankali yake tafiya a layin nasu hannayenshi zube a aljihunshi kanshi asunkuye idan ka kalleshi saikayi tunanin tafiyar qasaita yakeyi yayinda kwata2 ba haka bane damuwar dake ranshi ma ta isheshi shagon Abba din yaje inda ya iske jira sosai hakan yasa yanemi wuri a dan bencin dake waje ya zauna don jiran jama'ar su rage harde hannayenshi yayi a qirji ya kafe waje guda da ido ya lula duniyar tunani besan adadin lokacin daya dauka ba ahakan sai jiyayi an dan girgizamashi kafada saurin dagowa yayi ya kalli mai girgizamashi kafadar sai yaga ashe Abban ne "yadai kyakyawan kaka? kaxo ka zauna nan shiru tundazu sai magana nakemaka bakaji, halan dai ba magana kaje ka janyowa kaka ba" inji Abba cikin tsokana don shima tsarar Deen ne don ko zai girmeshi baxai bashi shekaru masu yawa ba murmushi Kawai Deen yayi yace "siyayya nazoyi naga shagon acike shiyasa nace bari najira" "waya gayamaka ana komawa gefe azauna ajira shago yarage? sai kaga wadanda suka zo daga bayanka ma,sun rigaka tafiya, irin haka ai magana zakayi saina baka ma batareda kajira ba tunda duk yarane masu sayayyar amma kazo ka zauna anan salan kaja kaka taji shiru tafito ta tattaro yan unguwa zuwa shagona nemanka" ya qarashe cikin tsokana murmushi Deen yasakeyi sannan yace "barkono zaka bani da maggi" "na nawa?" inji Abba yana,komawa shagon da yanzu babu kowa ciki Deen na biye dashi saida Deen yagama siyayyarshi tsaf sannan yabiya yajuyo yakamo hanyar gida daga nesa ya hangi wata dalleliyar mota kofar gidansu ahankali yake tafiya idanunshi akan motar yana wondering ta wanene be gama zancen zucinshi ba yaga anfito daga gidansu gabanshi ne yafadi lokacin da sukayi ido hudu da daddy wani matsiyacin kallo daddyn ya jefeshi dashi sannan yayi gaba fuuu mutumin dake taredashi na maramashi baya yana yi yana waigen Deen dayayi tsaye yakasa qarasowa wannan motar yaga sun nufa sun bubbude kofoffin gidan gaba sun shiga sannan aka tada motar suka bar wajen atsiyace bin motar Deen yayi da kallo harta bar layin gabanshi ne yacigaba da faduwa meya kawo daddy gidansu? tunawa yayi da magangganunshi na dazu dayaji ta waya hakan yasa zuciyarshi taqara tsinkewa koma me yakawoshi ya tabbata ba alhairi bane duba da matsiyacin kallon daya jefeshi dashi ahankali kamar marar lakka yaja qafaffunshi yanufi kofar gidan nasu cikin fargabar abinda zai tarar aciki da sallama yashiga ciki amma shiru hakan yasashi ida qarasawa cikin gidan inda ya hango kaka zaune kan sabuwar tabarmarta ta buga tagumi kanta a sunkuye ahankali yasakeyin sallama yana qarasowa yana kallon kakar tashi wadda harlokacin bata dagoba bare ta amsa sallamar tashi saida ya qara kusantota sannan ya lura da dami damin kudadden dake gabanta yan dari biyar biyar sunkai wajen wrapper biyar hakan yasashi dan wara idanu yana kallonsu shima "kaka?" yafada yana qarasowa "kaka meye wadannan?" yafada yana kallon kudadden sai a lokacin kaka tadago ta kalleshi "idanuwanka sunfara ciwone? kudaddene, kudadden daka siyar da mutuncinmu akai" kallon rashin fahimta Deen yayimata "bangane ba kaka" "tayaya za'ayi kagane Kamal? tayaya? bayan baka dauki maganata abakin komai ba baka yarda da,hangen danake maka ba" tafada cikin qunar zuciya "kaka..." "Tunfarko saida nagayamaka yarinyarnan ba sa'arka bace, tafi qarfinka amma ka nunamin kafini sanin abinda duniya keciki, to gashinan... gashinan ubanta yazo har gida ya taddani har nan yayimin wankin babban bargo babu abinda ya manta be gayaminba, ga Kuma kudi nan ya ajiye yace akyalemashi yarshi yariga yayimata miji, yanzu Kamal abinda zakamin kenan? ina zaman zamana? ina rayuwata cikin rufin asiri da kwanciyar hankali zakaje kasiyomin tashin hankali da kudinka? da mutunci na da komai wadannan mutanen sukazo sukayimin tass suka zubemin wadannan tsinnanun kudadden niga matsiyaciya? yayi maka kyau" ta qarashe tana miqewa tsaye tana share hawayenta tunda tafara yaji kamar an zaremashi dukkanin lakka ajiki yakasa koda kwakwarar motsi nuna kudadden kaka tayi cikin muryar kuka tace "gasunan ka kwashesu don dama kai suka kawomawa, sunce dama abinda kakeso,kenan ba diyarsu ba Kuma idan basu isheka ba kayi magana su qaromaka don suna iya baka ko nawa ne don ka kyalemasu diyarsu" tana kaiwa nan tajuya tashige daki tarufo tana hawaye kasa ko kwakwarar motsi Deen yayi awajen sosai zuciyarshi taqara dagulewa yarasa abinda kemashi dadi yana nan tsaye aka fara kiraye kirayen magrib cikin mutuwar jiki yajuya yanufi kitchen dinsu ya ajiye siyayyar dayayi sannan yafito yawuce wajen bokitan ruwansu batareda yako kalli gefen kudadden dake kan tabarma har lokacin ciccika butocinsu yayi daruwa yayi alwalla sannan yadawo kofar dakin kaka turawa yayi yaji gamm hakan yasashi sanin rufewa rtayi daga ciki cikin kwantar da murya yace "kaka don allah kiyi hqr kitaso kiyi alwalla lokacin sallah yayi" banza tayi dashi ta kyale "kinji kaka?" nanma shiru jiyayi an kabbara sallah hakan yasashi cewa "kaka zantafi masallaci don allah kifito kiyi alwallar ga ruwan can nazuba" banza tayi nan ma ta kyaleshi hakan yasashi juyawa Kawai yatafi zuciyarshi a quntacce koda yadawo daga sallar sai yaga alamun tafito tayi alwalla din don butarta ma babu ruwa hakan yasashi sake nufar kofarta saidai har lokacin a kulle take haka yatsaya yayta bubbuga yana bata haquri akan tabude amma tayi banza dashi har lokacin isha'i tayi dole ya haqura yaje ya chanzo alwalla yasake fita sallah koda yadawo ma,bata budeba haka yasha bubbugarshi yagaji ya haqura yaje ya kwashe kudadden dasu daddy suka bari zuciyarshi na quna yashiga dakinshi daidai nan yaji wayarshi dake gefen katifa na ringing saida yafara adana kudadden sannan yazo ya dauki wayar yaduba lokacin harta tsinke ganin sunan zee yayi Kuma har 3missed calls sauke ajiyar zuciya yayi sannan yakashe wayar gabadaya ya ajiyeta ranar sosai kaka tayi fushi dashi don qin bude dakinta tayi tana jinshi yana didimarshi shikadai a tsakar gidan taqi fitowa shi yayi tatar qullin koko ranar ya daka barkonon duk tana jinshi taqi fitowa dukda yadda takejin kamar tafito ta tayashi din don tasan dole aikin yayimashi yawa aranar dai haka kowannensu ya kwanta rai babu dadi Washegari tunda yadawo daga sallar asuba yashiga kiciniyar dora koko saida yafara hura wuta ya dora ruwa sannan yaje yafara surfen waken qosai kaka na daki tana jinshi amma bata fito ba don har lokacin tana cikeda baqincikin abinda su daddy sukazo sukayimata jiya tana jinshi harya gama yazo bakin dakinta ya kwankwasa shiru tayi batace komai ba saiya sake kwankwasawa yace "ina kwana kaka" nan ma shiru yasan tana jinshi hakan yasashi cewa "kaka zantafi kai markade" nan ma shiru hakan yasashi tashi zai juya yaji muryarta qasa qasa tana cewa "kasa rigar sanyinka" kallon kofar yayi yadanyi murmushi sannan yace "to kaka" komawa yayi daki yasanyo rigar sanyin dukda bawani iska akeyiba yadawo yasake mata sallama sannan yatafi be dade ba sosai yadawo da markaden lokacin har gari yafara haske ganin kaka agaban murhu tana hura wutar kosai yasashi jindadi sosai zuwa yayi ya ajiye markaden yazo zai tayata hura wutar saita tashi tabar mashi murhun fuska atamke tawuce tadauki markaden be damuba ya cigaba da hura wutar itakuma tashiga hada kullin kosan haka sukaita aiki ba uhm ba uhm uhm kamar kurame da taimakon Deen suka sheqa kokon lokacin har yan saye sunfara shigowa ahaka suka shiga sallaman customers dinsu inda kaka ke gaban kaskon qosai shikuma Deen ke sallaman masu saye zuwa 10 saura sungama tsaff sun gyara gidan, har lokacin kaka taqi sakarmashi fuska ahaka suma sukayi kalaci sukayi wanka ganin Deen beda niyyar shiryawa yatafi school yasata kallonshi fuska adaure tace "Makarantar fa?" "kaka yau bazani ba" "dalili?" turo baki yayi "nidai bazan iya fita kina fushi daniba" harara ta gallamashi "zakaje ka shirya ka wuce koko?" qara narkewa yayi yace "kaka wlh konaje bazan iya komai ba, don allah kiyi hqr kibar fushi dani" "ni fushi nace inayi dakai? Kawai kaje kaitayi tunda nidai baka ganina da mutunci kaje kayi duk abinda kakeso, babu ruwana" "haba kaka, wlh bakiji yadda nakejiba idan kina fadin haka, duk duniya wa nakedashi bayan ke? ke kadai zaki sani nayi ki hanani nabari don allah kibar fadin haka" yafada kamar zaiyi kuka "Kuma shine nace ka rabu daita kaqiya? duk abinda nake gudanmana kenan ai, don yimin yarinyarnan tayimin don alamu sun nuna tanada hankali amma ai ba anan take ba, yanayinmu dasu ba daya bane kuma bazai ta6a zama daya ba, mu dasu mabanbantan mutanene masu mabanbantan rayuwa wanda hadawarmu abune mai matuqar wuya" "kiyi hqr kaka, wlh nima bansan abin yakai haka ba amma insha allah zan kiyaye" kauda kai Kawai tayi batace komai ba "kinji don allah kaka?" yafada cikin marairaicewa "to indai kanason mu shirya dakai kafita harkar wannan yarinyar, iyayenta ba mutanen arziqi bane ka kyalemasu diyarsu suyita kaya allah zai baka wacce tafita, kadai jini ko?" "to kaka" "bawai to a iya fatar baki Kawai, a aikace nakeso don ko a Makaranta ban yarda ku haduba" "to kaka, insha allah hakan za'ayi" inji Deen in,affirmation dukda yasan wannan abun abune mai matuqar wahala "kudaddensu fa ya kayi dasu?" inji kaka "na adana, zan maidamasu kayansu" "dadai yafi" inji kaka tana ta6e baki "yanzu katashi kashirya kawuce Makarantar don bawai bari zanyi kayi qalula ba" murmushi Kawai Deen yayi yatashi yashige dakinshi tabishi da kallo cikeda qauna da tausayawa Ranar dayaje school be ganta ba Kuma yasan hakan be rasa nasaba da daddy don yasan tsaff ya hanata zuwa kodon karsu hadu haka ya yini a school din ranar cikin rashin kuzari, babu abinda yake mararin ji kamar muryarta, idan yatuna da sautin kukanta najiya saiyaji ranshi yaqara dagulewa gashi ya manta wayarshi agida da babu abinda zai hanashi kiranta yasan yayima kaka alqawarin fita harkarta amma shi kanshi yasan abune marar yiwuwa bazai iya rabuwa da zee ba, bazai iya datse soyayyarsu ba don rabuwa daita daidai yake da rabuwa da farincikinshi gabadaya haka yawuni a school din ranar batareda ya iya ta6uka komai ba har lokacin tafiya gida yayi yakoma gida rai duk badadi koda yadawo gida da doqinshi yafada dakinshi don daukar wayarshi yakirata saidai yaga wayam be ganta ba neman duniyar nan yayimata be ga ko abu mai kama daita ba yana cikin haka ne kaka tashigo ta taddashi yana bincike bincikenshi hakan yasata hade rai tace "wai meye haka kawani burkita daki kamar dakin mahaukata?" yana dan yarfe gumin dayayi na neman dayake yace "kaka wayata nake nema wlh, naduba koina,ban ganta ba" "wayar allurace dazata 6ace harka burkita daki haka don nemanta? to tana wajena" dagowa yayi ya kalleta yaga tawani qara hade rai tana kallonshi "tana wajenki?" "eh" tabashi amsa kai tsaye "to.. amfani kike daita?" "A'a Kawai daga yanzu nahanaka riqeta tunda ba dole bane riqe wayar" tafada tana cika tana batsewa "amma.. meyasa" yafada ahankali "shine nace saboda ba dole bace, aidai duk cikin masu kiranka nice mai muhinmmanci ko? to zan haqura koma menene saimun hadu sai nafadamaka amma yanzu dai bakai ba waya" shiru Deen yayi rai babu dadi "menene kawani sunkuyar dakai kamar wanda akayiwa rasuwa?" ahankali ya girgiza kai "A'a babu komai" "to maza muje kaci abinci yau abinda kafiso nayimaka" tafada tana mashi murmushi don lightening dinshi "to" yafada Kawai yayi hanyar waje rai babu dadi a tabarmar dake waje ya zauna ya jinginar da kanshi yanajin zuciyarshi na d'aci ahaka kaka takawo mashi abincin ta tusashi gaba tana bashi abaki tana mashi fira duk don farantamashi shidai amsan abincin Kawai yake yana tauna yana hadiyewa badon dadi ba don gabadaya bemada appetite sosai zuciyarshi ta dagule, yasan saboda zee kaka tadauke wayar wanda hakan ke nufin bazai qarajin muryarta ba saidai wani bangaren zuciyarshi ta tausheshi kan yayi hqr idan tahanashi waya daita ai bazata hanashi haduwa daita a school ba hakan yasashi jin dan sauki sauki yadan saki ranshi yana jin kamar yajawo gobe don doqin ganin zee Washegari tunda wuri yaje school din dukda bayada lecture ko daya haka yabuga safkon zuwa duk don yaganta saidai shiru haka yaita gararanba cikin school din amma babu zee babu alamunta shine har bayan la'asar school din amma ko mai kama daita be ganiba class dinsu kuwa yaje sau babu adadi amma babu ita, dole daga baya yaja qafaffunshi yabar school din rai adagule wasa wasa saida sukayi sati batareda sun haduba ko sunyi waya izuwa lokacin yagane tabar zuwa school ne don kullum haka zaije yaci zamanshi a school amma babu ita babu alamunta ga kaka har lokacin taqi bashi wayarshi yakuma nema adakinta beganiba don ba qaramin 6oyo tayimata ba cikin satin nan guda duk ya chanza kamar bashi ba, kallo daya zakamashi kasan yana cikin tsananin damuwa kaka ma na lure da yanayinshi dukda qoqarin 6oyemata dayakeyi saidai babu yadda ta iya don ita aganinta hakan yafi gwara yarabu daita tun wuri kafin komai ya lallace, haka yasa taita iyakar qoqarinta wajen ganin tana yayemashi damuwa ta hanyar yimashi abubbuwan datasan yanaso saidai ko kadan hakan be taimakama yanayinshi ba don zuciyarshi tariga tayi nisa, batajin kira. Ana haka watarana Deen yadawo daga school ya tadda gidan a kulle ganin hakan yasashi wucewa gidan maqocinsu Mallam Nasiru don mafi yawanci idan zata fita nan take barin makulli yaro yasa yashiga ya tambayomashi ko an bar makulli can saiga matar Mallam Nasirun tafito dakanta tabashi makullin tace ai haihuwa kaka taje amsa qasan layinsu batama dade da tafiya ba amsar makullin yayi yaimata godiya sannan yawuce yabude gida yashiga direct dakinshi yashiga ya ajiye littatafanshi sannan yafada kan yar katifarshi shiru yayi ya qurawa ceiling idanu can kamar wanda aka tsikara yamiqe zaune yana zare zaren idanu sai kuma yamiqe dasauri yafita yanufi dakin kaka. bincike yafarayi adakin yana duba every possible place da kaka zata 6oyemashi waya haka yaita bincike yana yi yana kallon kofa harwani hada zufa yakeyi, can dakyar yaganota can qasan kwallarta ta daddaneta da kaya ajiyar zuciya ya sauke yana fiddota qara kallon kofar yayi sannan yasamu wuri ya zauna gefen gadonta yana kunna wayar don akashe take cikin sa'a kau takama dukda battery dinta yayi low sosai shiga yayi call log yaga number ta ce asama don dama itace tayi kiran qarshe qurawa number ido yayi nawani lokaci sannan yakai hannu da niyyar dannamata kira saidai kafin yayi hakan kiranta yashigo tsayawa yayi yana kallon kiran yakasa dagawa harta katse can saiga wani kiran lumshe idanu yayi yanajin sanyi a zuciyarshi, dama yasani duk inda take tana cikin damuwa kamar shi kuma tana missing dinshi itama akira na uku ya daga yakara a kunne shiru yaji ba'ace komai ba hakan yasashi cewa "Zainab.." nan ma shiru "hello Zainab?" nanma shiru "Zainab is this you? please say something" yafada cikin damuwa "Deen..." yaji tafada cikin rawar murya saikuma sheshekar kukanta yabiyo baya "Zainab are you crying? please kibari kinji kar zuciyata tabuga, am ok kinji?" yafada yanajin kamar shima yayi kukan "Deen ina kashiga? nakusan mutuwa saboda fargaba, meya samu wayarka?" yaji tasake fada cikin kuka "am ok zee, babu abinda yasameta Kawai babu charge ne" yafada cikin son kwantar mata da hankali "no Deen you are not ok, gayamin meya faru? me daddy yayimaka?" tafada cikin kuka "babu komai Zainab, babu abinda yayimin. I love you and I'll never back off, no.matter w..." fittt... yaji anfige wayar hakan yasashi juyowa arazane wara idanu yayi cikin faduwar gaba ganin kaka tsaye agabanshi da wayar hannunta zaiyi magana yaga takara wayar a kunne yaci ta cigaba dacewa "eh yana jinki, Mallama mekuma kike nema da jikana? mekuma yasaki nemanshi?" shiru tayi saikuma tace "eh nice, kaka ce nagodema allah dayasa kika gane hakan, meye kuma kike nemanshi bayan abinda kukaimashi eh?" tafada amasifance "to ahir dinki wlh, karki qara kiran yarona wlh don shima yariga yagama dake, dama ai qarfin haline irin nashi banda haka ai ke ba kalar matar dazai aura bace" "kaka.." inji Deen daya sandare atsaye tunda tafara "menene? menene kake hanani magana? kabari nayimata wonin kina jina? wlh kifita harkar jikana kina jina ko? muba,kowan kowa,bane,bamuda wadanda zasu tsayamana idan kika jefamu a chakwakiya. muna zaman zamanmu ne cikin rufin asiri da wadatar zuciya, muna zamanmu cikin farinciki don allah karki tarwatsa mana shi.don allah ki kyalemin yaro kije kema allah yahadaki da daidai ku masu kudi muma haka mungode daduk dawainiyar dakukayi mana da qaunar dakuka gwadamana amma don allah karki sake nemanmu, ba don muba don allah" daga haka ta katse wayar kitt tayi jifa daita kan gadonta juyowa tayi afusace tana kallon Deen dake kallonta shima kamar wanda ruwa ya cinye ga idanunshi sunyi jajir nunashi tayi da yatsa "wato bakajin magana ta ko? ban isa nasaka kayi ba ko kuma ban isa na hanakaba ko? to shikenan ga wayar nan kadau abinka amma kasani kasake ka qara kiranta ko takiraka ka daga ban yafe ba kuma ban yafe ba idan kaje kuka hadu bare harka bude baki kayimata magana, kai ko ita tazo wajenka tayimaka magana ka amsa ban yafeba, shashasha Kawai!" daga haka ta juya ta hankada labule tafice daga dakin afusace binta da kallo yayi harta fice sannan yazame yazauna bisa gadonta ya dafe kanshi dake mugun saramashi da hannu bibbiyu....✍? Ummin fasihu🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:45 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *092* Aranar Deen kasa walwala yayi kwata2, tunaninshi bewuce wane hali zee zata shiga ba bayan wayar dasukayi, haka Kawai yakejin duk inda take ba lfy. haka ya qarashe wunin cikin tsananin damuwa a bangaren kaka kau shareshi tayi dukda lura da halin dayake ciki datayi saidai batajin tana iya barin wannan al'amarin yacigaba da tafiya ahakan don tunfarkon kawo zancen zee taji abin be kwanta mata ba don bata qaunar abinda zai tarwatsa dan farincikinsu har yakai ga tonuwar babban sirrinta na shekara da shekaru a daren ranar kasa barcin kirki yayi, washegari kuma tunda wuri yafice school ko yadanji sauqin abinda yakeji dukda yanzu school din yabar yimashi dadi saboda rashin zee acikinta sosai yakejin kewarta kamar sunyi shekaru basu hadu ba ranar haka ya yini a school din batareda yama fahimci lectures din daya dauka ba bedawo gida ba sai bayan asr inda yauma kamar rannan ya tadda wata galleliyar mota a kofar gidansu tsayawa yayi yana kallon motar abubbuwa da dama na kai kawo a zuciyarshi can sai yanufi hanyar shiga gidan zuciyarshi fall saqe saqe da sallama yashiga yana bin mutanen tsakar gidan da kallo kamar yaddasuma suka dago suna kallonshi kaka ce zaune kan tabarma tana facing daddy da wannan mutumin dasuka zo tare rannan amsa sallama duk sukayi suna kallonshi hakan yasashi qarasawa yana karantar yanayin fuskokinsu gani yayi su daddy suna mashi kallon dayasha banban dana rannan don har murmushi yaga kamar daddyn namashi itakau kaka fuskarta babu yabo babu fallasa qarasawa yayi gabansu ya russuna ya gaidasu cikin girmamawa suma suka amsa cikin kulawa ganin zai tashi yasa daddy cewa "A'a d'ana zauna ai dama maganar takace" babu musu ya zauna yana satar kallon kaka dataqi kallonshi tundazu wanda ke tare da daddy yace "nasan kana mammakin meya dawo damu yau don nasan kaji labarin abinda yakawomu rannan ko?" shiru Deen yayi kanshi aqasa hakan yasashi cigaba dacewa "munzo bada hqr ne akan abinda yafaru rannan, agaskiya muma mun gane abinda mukayi samm be kyautu ba, munyi nazari munga sam bamu kyauta ba shiyasa mukazo baku hqr don muma ba ason ranmu mukayi hakan ba. kunsan dai yadda duniyar ta lallace yanzu, masu gaskiya yan qalillan ne, yanzu a duniya saika rasa wanda zaka yarda dashi don gur6atattun suke 6ata nagarin shiyasa duk ake tsoron tsoro abinda yasa daddy be yarda da zancenku ba kenan don yawanci mutane basuda gaskiya saisu nuna suna sonka don allah while a zuciyarsu ba haka bane. ba,komai alhaji ke gudu ba sai yaudara shiyasa Tunfarko beyi na'am da zancenku ba don Zainab itace diyarshi daya tilo bazaiso abinda zai cutar daita ba shiyasa Tunfarko yaqi amincewa amma yanzu yagano gaskiya, ya bincika yaga dagaske bazaka yaudareta ba shiyasa yajawoni muka sake dawowa don mubaku hqr akan abinda yafaru wancan karon, kuyi hqr sharrin zuciya ne kuma insha allah tunda yanzu ansamu fahimtar juna hakan bazai sake faruwa ba, don allah d'ana katayamu ba Baaba haquri" tunda suka fara magana kan Deen naqasa yana sauraronsu bece komai ba harsuka kai aya daddy ya dora da "hakane son dik abinda yafada hakane, insha allah,yanzu komai ya daidaita tunda ansamu fahimtar juna, idanuna yaso yarufe nayi abinda zaijawo tarin danasani nan gaba amma alhamdulillah tunda yanzu komai ya daidaita nakuma fuskanci soyayyar gaskiya kukewa juna, fatanmu anan dai allah yasa kun huce yakuma sa hakan yafi alhairi" nan ma kasa cewa komai Deen yayi don besan me zaice ba, ba zato yaji muryar kaka nacewa "amin amin, shikenan komai yawuce allah ya kyauta gaba" dagowa Deen yayi ya kalli kaka with surprise saiyaga har lokacin taqi kallon 6arinshi hakan yasashi sunkuyar dakai yanajin wani sanyi na ratsa qasan zuciyarshi, kenan kaka ta yarda daddy ma ya yarda, this is unbelievable! cikin jindadi suma su daddy suka shiga amsawa da amin nan suka sanardasu Deen halinda zee keciki cewar yanzu haka tana kwance asibiti sosai hankalin Deen yatashi dajin wannan labarin har hakan ya bayyana a fuskarshi nan suka nemi alfarmar Deen yabisu asibitin qila zuwan nashi ya taimakama yanayinta Deen yayi tunanin kaka zata hana sai gani yayi ta amince da hakan hakan yasa yashiga farinciki sosai saidai saida suka maidamasu kudaddensu wanda suka kawo rannan wanda dafarko su daddy sunso qin amsa amma ganin sun nace yasa suka amsa badon sunso ba babu 6ata lokaci Deen ya kimtsa suka wuce taredasu daddy asibitin da aka kwantar daita anan sukaje asibitin har komai yakoma daidai har takai ga tasamu sauqi an sallameta har daga baya daddy ya bijiro da maganar Introduction (all in book 1) Sosai batun Introduction din yaba deen mammaki don beyi expecting hakan ba a lokacin a tunaninshi sai sungama school sannan za'a fara maganar amma sadda zee tayimashi bayanin wai so ake atsaida maganar ne kawai bawai auren za'ayi ba yasa hankalinshi yadan kwanta don soyake ya kasance kafin lokacin koyaya ne yasamu abinda zai iya riqe kanshi da zee lokacin da zancen Introduction din ya iso ga kaka duk saita rasa kwanciyar hankali dukda bata nunawa Deen komai ba amma deep down abin na cinta nan take ta gano manufar su daddy akan wannan Introduction din dasuka qirqira wanda bata raba dayan biyu suna sane sukayi hakan dama wannan zuwan nasu da amincewarsu lokaci daya bawai shiganta yayi ba, tasan duk yadda za'ayi akwai maqalqashiya gameda hakan jin batun Introduction din ya tabbatar da zarginta yakuma darsa fargabar tonuwar sirrinta data dade tana rufewa sosai kaka tashiga damuwa komai ya kwance mata, kullum da tunani take kwana take tashi bata fatan sirrinta ya fallasa a wannan lokacin, bata fatan abinda zai maidamata hannun agogo baya duk halin datake ciki bata bari Deen yasani ba don batason kwata2 yasan da damuwarta yayinda a gefe guda tashiga nemama kanta mafita akan wannan hargitsatsen al'amarin dake shirin tunkarota A bangaren Deen kau besan kaka nayi ba, shi duniya cema tadawo mashi sabuwa inda suke shan soyayyarsu da zee kamar zasu hadiyewa juna, kodayaushe suna maqale awaya don har lokacin batayi resuming school ba don bata,ida warwarewa ba lokacin Introduction sai qara matsowa yake inda Deen kejin kamar yajawo ranar don doqi dukda bawai auren za'a daura ba bakuma saka rana za'ayi ba hakan besashi doqin ranar ba don gani yake wannan Introduction din sharen fage ne na mallakar zee tunda koba komai za'a tsaida magana ne akansu yadda koma wani yazo daga baya yana sonta akwai maganarshi akanta sosai cikin yan kwanakinnan Deen yadage da buga buga duk don yasamu yatara kudin daza'akai Introduction din hakan yasa shima yabar zuwa school din akan da anyi Introduction din saisuyi resuming school din gabadaya dashi da zee besan ya tsarin abin yakeba amma yasan ba'a zuwa hannu biyu neman aure wannan busyn daya shiga yasa beda lokacin lurada halin da kaka tashiga ciki *TWO DAYS TO THE INTRODUCTION* Zaune kaka take tsakar gida kan tabarma ta miqe kaffafunta ta hardesu tana kalkadawa ahankali kallo daya zakamata kasan cewa she's very disturbed kafe hanyar shigowa gidan tayi da ido kamar mai jiran 6illowar wani yayinda saqe saqe da dama keta kai kawo a kwanyarta da sallama Deen yashigo gidan wanda hakan yayi daidai da saukewar naunauyan ajiyar zuciya daga kaka murmushi yasakar mata lokacin daya hangota yaqaraso ciki hannunshi riqeda yar baqar leda cigaba da kallonshi kaka tayi batareda ya motsa ba harya qaraso ya zauna gefenta yana washh yana yatsine fuska alamun gajiya "wlh kaka nagaji, jikina ciwo" yafada yana qara yatsine.fuska jin shiru yasa yadago ya kalleta yaga itama shi take kallo "kaka?" yafada ahankali yana kallonta hakan yasata kauda kai wadda hakan yaba kwallar idanunta damar digowa ganin digar hawayen yasa hankalin Deen tashi nan take yanemi gajiyar tashi yarasa "subhanllilah, kaka menene? meya faru" yafada yana kamo hannunta zai juyo fuskarta don tabbatar da abinda yagani amma taqi bari "kaka don allah menene?" yafada yana qara qoqarin leqa fuskarta fizge hannunta dake cikin nashi tayi tarufe fuskarta da tafukkan hannu tareda fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya gaban Deen yayi mummunan faduwa ganin dagaske kuka take hakan yasashi saurin rarrafowa gabanta ya kama hannayenta zai janye daga fuskarta amma taqi bari "innalillahi, kaka wai meya faru? don allah kiyi magana" yafada cikin tashin hankali qin maganar tayi saima qara volume din kukanta datayi wanda hakan ba qaramin daga hankalin Deen yayi ba don jiyayi kamar shima yasa kukan "kaka don girman allah ki gayamin meke faruwa, don allah kiyi shiru ki gayamin, don allah" yafada kamar zaiyi kuka don har idanunshi sunfara chanza launi nan ma batace komai ba sai kukan data cigaba dayi wanda yakeji har cikin ranshi "kaka don allah ki gayamin, don allah kibar kukan nan zuciyata zata buga" yafada muryarshi na dan rawa rawa sai a lokacin tadago ta kalleshi fuska sha6e sha6e da hawaye "Kamal nima zuciyata zata buga, zasu rabamu, xan rasa raina. zamu rabu na har abada" "innalillahi waina ilahi rajiun, rabuwa kuma? haba kaka meyasa kike fadin wannan mummunan kalmar? don allah kibar fadin haka" "Kamal kaine komai nawa, baxan iya rayuwa babu kai ba baxan juri nisa dakai ba, mutuwa zanyi" taqarashe cikin fashewa da kuka sosai hawayene suka taru a idanunshi shima "kaka don allah kibar fadin haka, babu wanda zai rabamu, nima bazan iya rayuwa babu ke ba..." "to idan hakane mu gudu Kamal.. mubar nan wajen, mubar garinnan don allah" ta katseshi dasauri kamar zautatta tsayawa Deen yayi yana kallonta for a moment kafin yace "mugudu? kamar ya mugudu?" "mubar nan Kamal, nidai hankalina be kwanta da nan ba kuma, ina tsoron kar arabamu ina tsoro Kamal" tafada cikin yanayin tsoron "wazai rabamu kaka? waye zai rabamu" inji Deen in confusion "nidai mubar nan Kawai... tashi kagani, taso" tafada tana miqewa tsaye tana jan hannun Deen da kanshi yayi mugun kullewa tashi shima yayi tajashi har dakinta yana biye daita suka shiga "kagani? na tattara komai tafiya Kawai yarage, Kawai mutafi don allah" tsayawa yayi yana bin jakunkunan kayansu dake tsakiyar dakin da kallo Speechless, yama rasa meke faruwa "da daddare saimu tafi Kawai yadda babu wanda zai ganmu ko?" inji kaka da hawayenta yaqi tsayawa ga jikinta har lokacin rawa rawa yakeyi dakyar Deen ya iya tattaro yawun bakinshi ya hadiye.sannan yace "kaka.. wai meke faruwa ne? ina zamu?" "koina ma,.Kawai muyi nisa danan" "amma akan wane dalili kaka? Kawai saimu bar gari haka Kawai? haka Kawai saimu gudu mubar gari kamar 6arayi" yafada totally confused "Kamal, bazaka ganeba amma ni nasan abinda na hango, wlh inaji ajikina idan muka cigaba dazama anan sai an rabamu, inajin hakan ajikina" tafada wasu hawayen nasake saukomata "wazai rabamu kaka?" "nima bansaniba Kawai mubar nan" "amma kaka shikenan saimu bar gari? ina zamuje? wa mukedashi? wani wurin garemu bayan nan?" "Kamal zamu samu wurin zuwa, nan ma ai sdaga wani wuri mukazo kuma muka samu nan din har muka zauna mukayi tsawon shekarunnan, mutafi insha allah zamu samu wurin zuwa allah na taredamu" "amma kaka karatuna fa? bama wannan ba kin manta jibi za'aje tsayar da maganarmu da Zainab? duk ahakan zamu bar gari?" inji Deen dake cikin confusion sosai, kwata2 magangganun kaka doesnt make sense to him "duk ina sane da hakan Kamal, duk wadannan basuda muhinmmanci yanzu" "basuda muhinmmanci?" ya tambaya cikin tsananin mammaki "eh Kamal, abinda yafi muhinmmanci shine mucigaba da rayuwa da juna..atare" shiru Deen yayi yana kallonta kamar yau yafara ganinta saikuma ya girgiza kai yakama kafadun kaka da hannun bibbiyu ya zaunar daita gefen gadonta "kaka meya faru? don allah ki gayamin meye silar dukkan wadannan abubbuwan" "babu komai Kawai sonake mubar garinnan, hankalina be kwanta da zama anan ba kuma" "meyasa hankalinki be kwanta da zamanmu anan ba din?" "Kawai hakanan, Kawai mutafi" tsayawa yayi again yana kallonta kamar yau yafara ganinta "intafi inbar karatuna bayan befi shekara ba zan qarqare gabadaya?" "wanda kayi allah yasamashi albarka, dama meye amfanin karatun don dai mutum ya iya rubuta da karantawa ne bayan hakan ko ka gama aibakada tabbacin cin abinci dashi tunda mutane nawa suke gararanba atiti da kwalinsu aiki ya gagaresu, idan mukaje inda mukaje saika samu aikin hannu mu cigaba da rufawa juna asiri" sake sakin baki Deen yayi yana kallonta cikin tsantsar mammakin abinda take cewa can kuma yace "maganata da Zainab fa?" tsaki taja "itama sai a haqura, aiba ita kadai ce mace aduniya ba ko?" cikin tsananin mammaki yace "a haqura?" "eh, allah zai hadaka da wacce ta fita" "haba kaka? jibi fa za'a tura..." "babu inda za'a tura, kai nifa dama can bason abinnan nakeba shima munafikin uban nata baso yakeba, na me zanbari a tarwatsamin farinciki a banxa a wofi? kama cire wannan maganar aranka don yanzu kam babu ita" jin magangganunta yayi kamar saukar guduma atsakiyar kanshi kallonta Kawai yake totally Speechless "kayi shiru kana kallona" tafada ganin kallon yayi yawa "amma dai,wasa kike ko kaka?" tsuke fuska tayi "alamun wasan kagani a fuskata" "to kaka idan ba wasa ba meye zamu kira wannan to?" "kai yayi maka kama dawasa amma babu ko alamun wasa a magana ta, batunka da wannan yarinyar babu shi!" "meyasa?" yafada ahankali yana kallon kaka da idanunshi dasuka kada sosai "saboda nace babu shi don haka kama manta da batwwannan yarinyar don ba alhairi bace agaremu" sosai zuciyar Deen take zafi jiyake kamar ana gasamashi ita "amma kaka kinsan inason Zainab ko?" yafada yana kallonta da idanunshi dasukayi jajir "zaka daina sonta ne ahankali" ahankali yashiga girgiza kai "kaka baxan ta6a daina sonta ba, babu ranar dazan daina sonta, kada allah ya gwadamin ranar kaka" "Kamal ni kake fadawa haka?" "kiyi hqr kaka, amma Zainab itace komai tawa, itace farincikina itace komai tawa bazan iya rabuwa daita ba" hawayene suka saukomata "itace komai taka Kamal, wato tafini matsayi agurunka?" girgiza kai yayi yace "ko daya kaka, kowanne da matsayinshi aguna kaka, bazata ta6a finki matsayi ba amma kamar yadda ban iya rayuwa babu ke haka itama bani iya rayuwa babu ita" kuka sosai kaka ta fashe dashi "ni kake fadawa bazaka iya rayuwa babu itaba Kamal? duka yaushe kasanta? kenan tafini muhinmmanci agurunka" "kaka ba haka bane, nina rasa dalilin dayasa baki sonta bayan ita tana sonki" yafada kamar zaiyi kuka "ni ba itace banisoba, bani daison munafikin babanta ya cutar damu ne" "me babanta zaiyi mana? yafa amince da maganarmu kuma harnan yaxo yabaki hqr akan abubbuwan dayayi amma dukda haka bazaki sama abin albarka ba? ni yanzu meye hujjata ta janye wannan maganar? mahaifinta ya yarda har yasa aturo to menene kuma ya rage?" "munafikine mahaifin nata, Kawai yanuna ya yarda ne amma hakan bekai zuciyarshi ba, turowan ma dayace ayi duk na manufa ne" tafada cikin kuka sosai "manufar me kaka? meye manufarshi akai?" "yasan bamuda kowa kamal shiyasa yace aturo, soyake ya titsiyemu" "meye don bamuda kowa? ai ba daga sama muka fadoba, saimu fadamasu komai gameda mu, kuma koda bamuda kowa wadanda zasu tsayamana bazasu gagaremu ba, ga Mallam Nasiru da sauran mutanen arziqin unguwarnan nasan zasu tsayamana" murmushin takaici kaka tayi "hmmm yaro yarone, bazaka gane komai ba Kamal, bazaka gane ba" "meye bazan ganeba kaka? kifadamin babu abinda bazan ganeba, idan akwai wani abu bayan wannan ki gayamin" "nidai nace babu maganarka da wannan yarinyar kuma gari dolene mubarshi, kaji na gayamaka" tafada tana daure fuska don tasan duk abinda zatace mashi bazai ganeba Tashi Deen yayi tsaye yana kallonta "kiyi hqr kaka amma baxan iya ba, baxan iya barin Zainab ba, ina sonta" daga haka yajuya yabar dakin binshi da kallo tayi baki sake harya fice daga dakin tunda suke bata ta6a sashi abu yaqiya ba sai yau fashewa tasakeyi dawani kukan mai tsuma zuciya cikin rasa abinyi kuma....✍? *manage please* Ummin fasihu🧚🏻‍♀? 8/2/21, 9:45 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *093* Tunda Deen yake beta6a shiga halin damuwa da confusion irin ranar ba koda yafita ma rasa inda zaya yayi Kawai saiyaita yawo batareda yasan inda zaya ba sosai damuwa tayimashi katutu arai, yarasa meya samu kaka data burkucemashi lokaci daya ta bijiro da wannan buqatar tata marar yiwuwa nan take yamanta dawani batun shirye shiryen Introduction, damuwa ta maye gurbin doqin dayakeyi aranar sai bayan isha'i yashigo gidan yana addu'ar allah yasa kaka tadawo hayyacinta tabar wancan maganar marar ma'ana saidai me? yana zuwa yatarar da wani tashin hankalin inda kaka ta tsaya akan bakanta na barin garin, qarshe ma tace idan shi bazai bita ba ita zata tafi ita kadai duk yadda allah yayi daita daidai ne sosai Deen yashiga tashin hankali ganin dagaske fa kaka take babu roqon da baiyi mata ba da magiya harda kukanshi amma firr kaka taqiya, takoma kamar wata zautatta bataji bata gani ganin dagaske tafiyar zatayi tabarshi yasashi shima amincewa da binta din don baxai iya rayuwa batareda itaba, itace yabudi ido yasani duk duniyar nan bayada kamarta, itace uwarshi itace ubanshi itace komai nashi xai iya rayuwa batareda zee ba dukda rayuwar bamai dadi ba don rasata yana daidai da rasa farincikinshi amma bazai iya rayuwa batareda kaka ba, bama zai iya misalta rayuwa batareda ita ba. haka ya amince ba don yasoba amma ya roqeta akan tabari sai gobe sai sutafi din kamar bazata yarda ba saikuma ta amince akan gobe tafiya babu fashi ko dashi ko babu shi tafiyarta zatayi ranar yadda Deen yaga rana haka yaga dare ganin komai yake kamar a mafarki, jiyake dama mafarki ne da babu wanda zaikaishi murna a duniyar nan kwata2 he never saw these coming, abin yaxomashi ne Kawai daga sama, yakasa yarda cewa zaiyi nisa da zee, nisa na har abada, yakasa ma imagine din hakan aranshi Kawai gani abin yake kamar a mafarki Washegari ko kofar gida be leqa ba, yana cikin daki idan kuma yafito to lokacin sallah ne yayi saiyayi alwalla yakoma dakin yayi abinshi abinci ma kasa ci yayi haka kaka ke kawo abinta tana daukewa itama kakar kallo daya zakamata kasan she's down sosai, she looks so pale and disturbed, komai na duniya bayayi mata dadi ganin Deen a halin dayake ciki baqaramin qara dagulamata lissafi yake ba saidai takasa yin komai akai, takasa koda consoling dinshi haka suka qarashe wuninsu agidan cikin wani irin yanayi marar dadi wanda basu ta6ayin irinshi ba tunda suke don kowa na qunqume a dakinshi babu mai fitowa saida dalili, magana ma kanta bata hadasuba sosai kowa nafama da zuciyarshi sai a lokacin isha'i Deen yafita daga gidan yaje masallaci don yin sallah sai bayan sunfito yahadu da wani dan unguwar nasu mai suna Salman wanda yakasance kamar aboki ne gareshi yabashi wani envelope tareda cemashi wata zatazo sunanta Zainab don allah idan tazo yabata saqon nada muhinmmanci tsokanarshi Salman yashigayi akan saqon menene, badai na soyayya bace shidai dan murmushi kawai yayi yayimashi sallama akan zaishiga gida don samm he's not in the mood for any joke koda yakoma gidan awaje ya tadda kaka tabuga tagumi very worried be tankamata ba yashige dakinshi don shima kanshi nashi damuwar ta isheshi kaya komawa dakin yayi ya raku6e wuri guda staring at space har lokacin yakasa yarda da abinda yake faruwa, he can't imagine wane hali zee zata shiga idan taji labarin tafiyarshi hakan yasashi lalubo wayarshi dake kashe tun jiya ya lalubo numberta ya bugamata jin muryarta yasa wasu emotional feelings tasomashi, she sound so innocent and cool nan take saiyaji tausayinta ya mamayemashi zuciya bata cancanci abinda yake shirin yimata ba, bata cancanci yayi breaking heart dinta ba bayan tasoshi da dukkanin zuciyarta, tasoshi a yadda yake batareda tayi la'akari da tarin difference dake tsakaninsu ba nan take yaji wani irin guiltiness a zuciyarshi, ya zaiyi? ya zaiyi da rayuwarshi? haka sukayi wayar yana iyakar bakin qoqarinshi wajen controlling muryarshi don wayar yake yana hawaye, tunanin cewa qila muryarta yakeji na qarshe yasa yakasa tsaida hawayenshi itama taso tagane kamar ba daidai yake ba don taji a yanayin muryarshi kamar he's not ok ganin hakan yasa yaimata qaryar mura yake. kalaman dayake mata amfani dasu da ace mai saurin ganewa ce data gane ba lafiya amma dayake bata kawo hakan aranta ba yasa batabi takansu ba sosai wannan innocence din nata kuma ba qaramin qara tsuma zuciyarshi yayi ba har hakan yasa daga baya yakasa cigaba da wayar daita sukayi sallama akan beda charge bayan gama wayar ya kasheta gabadaya ya zare sim card din ya karya yana hawaye sosai sannan yatashi ya tattara important stuffs dinshi ciki harda takardunshi, sannan ya dauko wannan band din da zee tabashi ranar Valentine wanda tun ranar ya adanashi cikin wani box yafiddoshi ya daura a hannu komawa yayi kan katifarshi ya takure waje guda staring into space idanunshi jawur. saida dare yayi sosai kafa dik ta dauke sannan suka fito daga gidan daga su sai kayansu wanda kecikin madaidaiciyar ghana must go sai qatuwar jakar goyo dake goye abayan Deen kulle gidan sukayi da katon kwado sannan suka nufi hanyar barin layin tafiya suke babu mai cewa kowa komai don duk yau maganar dasuka yiwa juna qididdigagga ce babu dadewa suka isa titi don dama basuda nisa da titi basu tsaya ba suka cigaba da tafiya gefen titin dake kwal don motoci ma sai jefi jefi suke wucewa saboda yadda dare yayi sunyi tafiya sosai kafin susamu wata adaidaita data tsaya gabansu don jin ko tafiya ce kaka ce tayima mai adaidaitan magana cewa tasha zasu saida yaqaremasu kallo sannan yafadamasu kudin dazasu bada kaka bata musaba tace suje dukda yasa kudi dayawa itadai burinta subar unguwar kwata2 ita tafara shiga sannan aka saka ghana must go din atsakiya inda akesa kaffafu sannan Deen da saikayi zaton kurmane saboda rashin maganarshi yashiga yana rufo yar kofar adaidaitan babu 6ata lokaci mai adaidaitan yaja sukabar wajen tafiyarsu zuwa tashar sunyishi ne silently don babu mai cewa komai cikinsu sosai halin da Deen keciki ke damun kaka amma batasan mezata yimashi ba, batada kalmar dazata fadamashi dazaisashi jin sanyi hakan yasa tayi shiru tana hoping cewa komai zai wuce very fast insha allah harga allah itama tasan wannan decision din yayi tsauri sosai musanmman ma ga Deen amma ya ta iya? hakan take ganin yafi musu alhairi don aganinta gwara wannan tashin hankalin da wanda take hangomasu nan gaba tafiyar 30mins yakaisu tashar inda sa6anin koina wajen akwai mutane sosai ga fitilu takoina yadda kasan ba tsakar dare bane biyan mai adaidaitan sukayi suka sauka da loads dinsu ciki suka shiga inda yawanci duk travellers ne dazasu kwana a tashar da drivers din motoci qarasawa ciki sukayi Deen biyeda kaka dake agaba yana sauraron yadda take tambayar inane wasu daga motocin zasu tafi shidai haryanzu ko uffan bece ba sai binta dayake everywhere she go har daga qarshe tasamo masu motar dazasu shiga wacce zata Abuja itama ta za6eta ne don taga takusan cika kuma zatayi saurin dagawa kayansu aka sakamasu a baya sannan suka kama seat suka shiga suka zauna saboda yadda iskan daren ke kadawa sosai akwai few mutane ma acikin motar inda wasu ma barci suke wasu kuma idanunsu biyu, cikinsu kaka ta tambayi wani time akace mata yanxu uku da rabi na dare hakan yasata sauke ajiyar zuciya takoma ta jingina jikin kujerar dagowa tayi ta kalli Deen dake zaune silently yana kallon yatsun hannunshi saitaji yayi mugun bata tausayi ahankali ta kama hannunshi tadan matsa tana kallonshi be dagoba bare ya kalleta sai cigaba da kallon hannayen nasu dayayi "kayi hqr Kamal... insha allah hakan shiyafi alhairi" tafada ahankali tana kallonshi da idanunta dasuka duri ruwa dan murmushi yayi wanda dagani kasan na qarfin haline Kawai ya kadamata kai batareda ya kalleta ba "yanxu gayamin meke damunka? kana buqatar wani abu?" tafada tana kallonshi cikin kulawa "inajin sanyi" yafada ahankali kallonshi tayi cikin tausayawa sai tajawoshi jikinta yadora kanshi a cinyarta tashiga shafa mashi kai "sannu, ai gari yakusan wayewa harda sanyin dare" tafada tana gyaramashi hular sanyin kanshi yadda zai rufemashi kunnuwa sosai don dama shigar sanyi yayi saboda yanayinshi ahankali Deen ya lumshe idanunshi yana sauraron bugun zuciyarshi dake bugawa abnormally ahaka har asuba tayi duk fitowa sukayi sukai sallah sannan suka koma cikin motar da gab take da cika don saura mutane biyu cikin qanqanin lokaci ta ida cika aka shishiga motar akayi duk abinda ya kamata sannan driver yahau ya tada motar yaja suka fice daga tashar Tunda Deen yake beta6a long and boring tafiya ba irin wannan tunda motar tafara tafiya ya maida kanshi ga window yana kallon waje yanajin cewa wai yau shi zaibar garinsu Katsina bawai bari na dawowa ba A'a na har abada dukda shekaru sunja sosai amma yana iya tuna lokacin da suka shigota sama sama, lokacin yanada shekaru goma aduniya tunawa yayi da fadi tashin dasukayi tayi da kaka kafin susamu wurin zama inda yazaman masu gida kusan na tsawon shekaru sha takwas dukda yasan Katsina ba garinsu bane amma hakan be hanashi jin kamar yana barin bane don duk cikin garurruwan dasuka zauna babu wanda sukafi dadewa suka kuma yi rayuwa comfortably kamarta gashi yayi achieving abubbuwa dadama acikinta marassa goguwa a memory lokacin dasuka fita kofar Welcome to Katsina wani feeling na emptiness ya ziyarci zuciyarshi shikenan, shikenan yatafi, yatafi yabar abubbuwa masu matuqar muhinmmanci a rayuwarshi batareda sanin lokacin sake waiwayarsu ba sai jiyayi kamar zuciyarshi tayi dropping daidai kofar yabarta abaya yayinda yanzu gangar jikin kecikin motar ana tafiya daita ahankali ya lumshe idanunshi, imagining yafarayi me zee keyi adaidai wannan lokacin wataqila tanacan cikin farincikin kasancewar yau zai turo magabatanshi, wataqila takirashi, wataqila sunacan sunata shirye shiryen Introduction din ya Zainab zataji? ya zataji idan dagabaya tagane abinda yayi, ya zataji idan tagano he yayi betraying trust dinta _*please don't leave me, no matter what*_ muryar zee tadawo mashi _*never... I will never*_ yasake tuna amsar dayabata lokacin sake maida idanunshi yayi ya lumshe yanajin wani irin zazza6i na tasomashi yasan shi da farinciki kuma har abada, yasan wannan new chapter din daya bude na rayuwarshi is the worst chapter lokacin dasuka tsaya sallar zuhr jikin Deen yayi ringis da zazza6i sosai hankalin kaka yatashi ganin hakan ahaka yayi qarfin halin saukowa shima cikin motar da niyyar yin alwalla yayi sallar saidai inda ya tsugunna yana alwallar yahau kwarara amai sosai hankalin kaka yaqara tashi duk ta gigice tana kuka ganin yadda yake zazzaga aman kamar zai amayar da yan cikinshi gabadaya da taimakon wasu daga mutanen motar yasamu ya tsaftace jikinshi ya daura alwalla yadawo wata yar rumfa dake wajen inda duk nan pasinjojin sukayi sallah sosai mutanen suka tausaya mashi don kallo daya zakamashi kasan yana jin jiki sosai adaddafe yayi sallar lokacin har ansiyomashi maganin masassara a wani dan chemist dake wajen kaka kuma ta siyamashi fura inda tabashi yasha kafin yasha maganin ko rabin furar besha ba yashiga kwara wani aman kamar zai zazzago yan cikinshi sosai kaka takuma rudewa, kuka take bilhaqi da gaskiya cikin tashin hankali tana ataimaka mata karya mutu shikadai gareshi sosai mutanen wajen suke bakin qoqarinsu wajen taimakawa don sosai Deen kejin jiki, yayi laqwas ga wani irin zafi da jikinshi yadauka kasancewar a inda suka tsaya qauye ne yasa babu wani clinic kusa gashi dan chemist dinma irin dan shagonnan ne da ake saide2 bawani abu suka saniba gameda lfy Kawai suna saida irin paracetamol ko maganin ciwon jiki saboda ire iren pasinjojin dakan tsaya a wajen idan suna buqata ganin halin da Deen keciki yasa mutanen wajen ba kaka shawarar gaskiya idan suka cigaba da tafiyar nan ahaka jikin Deen ida rikicewa zaiyi Kawai susamu cab dazai shiga cikin gari dake kusa takaishi clinic ko babban chemist inda za'a dubashi abashi right meditation hakan kau akayi, nan aka saukomasu kayansu dayake wurin kamar yar karamar tasha ce nan da nan suka samu mota Golf mai shiga cikin gari ahaka suka shiga kaka nata dauke hawaye babu 6ata lokaci motar tasu ta tashi tafita daga tashar tafiyar awa daya sukayi suka qaraso cikin gari inda drivern yakaisu wata yar qaramar clinic ta gwamnati lokacin Deen ko bude idanu be iyawa sosai tareda drivern suka shiga ciki ganin yadda Deen kejin jiki ga kaka tsohuwace bata iya handling komai ita kadai hakan yasa yatsaya ya taimaka wajen yin zirga zirgan komai har suka samu nasarar ganin likita anan aka dubashi aka rubuta mashi magungunnan daya kamata drivern nanan har saida yaga ansiyo magani inda dakyar suka samu Deen yasashi bayan yasha wani dan shayin da aka siyomashi wajen clinic din sannan yatafi yabarsu anan yakama gabanshi shima kasancewar basuda wurin zuwa yasa suka tsaya cikin asibitin don ga halin da Deen keciki tafiya bata yiwuwa agaresu ataqaice dai cikin asibitin suka kwana, Washegari kuma suka sake daukar hanya ba don ya warware ba amma da dan sauqi ataqaice dai sai wajajen 3pm suka isa garin Abuja a wurwurce har wani ramar dole kowannensu yayi suna isa Abuja suka qara danganawa da asibiti don a lokacin sosai jikin Deen yasake rikicewa wannan karon ganin yanayin da Deen keciki yasa aka basu gado saida sukayi kwana uku a asibitin kafin yadanji sauqi aka sallamesu a lokacin duk sun kashe yan kudaddensu wadanda suka rage basu wani taka kara suka karya ba gashi basuda mazauni dama acikin kwanakinnan asibitin ne yazama kamar gida agaresu duk kaka takoma wani iri ta fiffige saboda damuwa, bata ta6a kawowa haka tafiyar zata juyemasu ba gani take komai zaizo masu smoothly kasancewar lokacin dasuka fito sunada enough kudinsu wanda zasuyi tafiyar harsuzo susamu haya sukama inda zasu zauna amma wannan rashin lafiyar ta Deen dukta cinye kudin wajen hidindimun magungunna dana abinci ganin halin da kaka tashiga na zullumin inda zasu koma lokacin da aka rubuta musu sallama yasa Deen dahar lokacin bawai ya warke garau bane ya dauki jakar dayayi parking important stuffs dinshi yazaro wayarshi wanda zee tabashi anan yace ma kaka bari yaje ya siyar susamu ko kudin kama daki daya ne dafarko kaka taso hanashi saboda batason yashiga gantsareriyar ranar da akeyi ya maidoma kanshi ciwo baya amma kuma saita haqura sanin cewa basuda wani option tunda ita ba iya zuwa zatayi ba ahakan Deen yafita inda da tambaya yasamu shagon siyar da wayoyi yashiga don siyarda ita jin tayin wulaqancin da akamashi a shagon farko yasashi fitowa yanufi wani inda nan ma kanwar ja ce sosai abun yabashi mammaki ganin yadda suke mashi siyen wulaqanci bayan wayar babbace kuma mai tsada kamar ya haqura da siyar da wayar amma ganin itakadai ce hope dinsu yasashi hqra inda yasamu ya saidata wani shago wanda yafi sauran siyenta da kudi anan ya tambayi mai shagon inda zaisamu gida haya ko daki daya ne cikin sa'a saigashi mutumin ya hadashi dawani dilali da dama irin aikinsu kenan hadashi yayi da dilalin inda dilalin yatafi dashi ya nunnuna mashi gidajen dakeda vacant na hiring aciki Deen ya za6i daya inda yakama masu daki daya inda dakyar yasamu mai gidan ya yarda zai amshi kudin wata shidda daga baya sucika mashi sauran gidan dakuna uku ne sai kitchen da bayi akwai wasu occupant din aciki inda duk magidanta ne da iyalansu kowa da daki daya inda dakin da Deen yakama shine na qarshe saida yabiya kudin hayan aka bashi makullin dakin sannan yafito yatari adaidaita don komawa asibitin alokacin har jiyake kamar kanshi zai rabe gida biyu saboda sarawa haka dai yaita daurewa har suka iso asibitin ya sauka yabiya mai adaidaitan yashiga ciki A reception ya tadda kaka don lokacin har an maye gurbinshi dawani patient a gadonshi hakanyasa dole tadawo reception din ta zauna tana ganinshi tayi saurin miqewa tsaye don dama tundazu kamar a qaya take baxa idanu Kawai take taga ta inda zai 6illo tararshi tayi tanamashi sannu don he looks so weak qarfin hali Kawai yakeyi anan yafada mata yasamo masu mazauni amma daki daya albarka taita shimashi tana jeramashi sannu tana tambayar yanzu me yakeji cewa yayi babu komai Kawai ta tashi sutafi anan suka tattara yan kayansu suka fito daga asibitin suka tari adaidaita yafada mashi inda zaikaisu unguwar unguwar talakawa ce don ga yanayin unguwar Kawai zaka gane hakan har kofar gidan adaidaitan ta saukesu suka sassauke kayansu suka biya sannan suka shiga a lokacin har anfara kiraye kirayen la'asar saida suka gaigaisa da occupant din gidan sannan suka qarasa dakinsu anan Deen yake tambayarta yayi? hakan yasa tayi murmushi tana cewa yayi sosai allah yayi mashi albarka da amin ta amsa sannan yace bari yaje yadawo bejira cewarta ba yasake fita inda da kingin kudin hannunshi yayimasu sayayyar yan kayan daxasu buqata kama daga tabarma, bokiti, buta, yan plate biyu da cups sai tsintsiya kingin kudin kuma yasiyomasu kayan abinci wanda zasu dan fara dashi sosai farinciki ya lullu6e kaka lokacin daya dawo da kayayyakin hakan yasa taita samashi albarka tare suka tsaftace dakin suka shinfida tabarmar suka kuma ajiye kayansu da kingin kayayyakin da Deen yasiyo a wani Corner na dakin sosai dakin yayi fili don bawasu kayan kirki aciki sai a lokacin dik suka samu damar yin sallar la'asar din sannan kaka ta jiqamasu garin kwaki cikin wanda Deen yasiyo cikin kayan abincin suka sha Deen yasha maganinshi yakoma ya kwanta dukda babu kyau kwanciyar marece amma haka kaka ta kyaleshi don tasan yagaji sosai cos he looked so exhausted haka Deen yaita kwanciya idanunshi alumshe dukda ba barci yake ba tunanin zee Kawai ne dankare a zuciyarshi, yasan izuwa yanzu tagano komai kuma tasan ya yaudareta, yasan yanzu tana cikin wani hali don yaudara agun wanda kabama dukkan yarda ba qaramin ciwo gareshi ba haka yaita kwance har wajajen magrib sannan yafito yayi alwallar magrib inda ya tadda kaka waje suna dan fira da matan gidan alwallar yayi yafita inda bedawo ba sai bayan isha'i yana dawowa yashige ya kwanta ya rufa da qaton bargonsu yana rawar d'ari sanadiyar sanyin dayakeji nakaimashi har cikin qashi kan kace me har wani zazza6in yasake lullu6eshi inda kaka tashiga kuladashi cikin tsananin tausayawa jikan nata ataqaice dai haka Deen yaita fama cikin kwanakin dasuka biyo baya, yau lafiya gobe sauqi sosai rayuwa tayimusu wuya, ga ciwo ga babu kudi haka sukaita fama inda dan abincin da Deen ya siyamasu yaketa qasa every passing day ganin hakan yasa Deen fara fita nema ganin kwanciyar bayi bace haka yake fita ya yini waje yana yan buga buga qarshe yadawo da abinda be taka kara ya karya ba abu ya hademashi goma da ishirin, ga ciwon dayake tsaitsaiye ga fita nema ga tarin damuwa dake danqare a zuciyarshi gashi kaka bawata sana'a take ba bare itama ta taimaka don sana'a saida jari sukau ahalin yanzu ta cinsu ma Kawai suke, gashi rayuwa tafi tsada a Abuja bisa ga Katsina haka sukaita rarrakawa Deen yana iyakar kokarinshi na ganin basu rasa ciba ko yayane ahaka yasamu wani qaton shago a kasuwa na lemuna kala kala inda anan yake zuwa yatayasu safko carton cartons din juices ko ruwa daga manyan trailoli dake kawowa zuwa cikin shagon shima dakyar yasamu aikin ashagon kasancewar akwai masu irin aikin sosai awajen haka zasuyita zirga zirgan jigilar kayan daga motocin zuwa qaton store din shagon wasu masu barrow cikinsu kuma har dako sukema masu zuwa saye a shagon kasancewar shagon babban shagone yasa kodayaushe cikin busy yake, kodayaushe cikin sauke kaya da siyarwa suke hakan yasa masu dakon wajen ke jigatuwa sosai musanmman ma ire iren su Deen dabasuda barrow saidai a tittilamasu akai farko farkon fara aikin a shagon ba qaramar wahala Deen yasha ba don yana jigatuwa sosai at the end of the day inda kullum saiya kwana da zazza6i da ciwon jiki saboda wahala daga baya yaji ashe hayar barrow akeyi wanda hakan yasashi shima fara quma safko yaje don amsar hayar barrow inda hakan yadan sauqaqa mashi wahala haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda Deen ya cigaba da aiki wannan shagon inda yake samu ba laifi don ci da sha lafiya lau yake dauke masu harda yan buqatun yau da kullum saidai fa kullum lafiyarshi bawata cikkaka bace don da ana sabo da ciwo daya saba dashi saboda har lokacin bawata cikkakiyar lafiya gareshi ba Kawai qarfin haline irin nashi cikin sati biyu Deen ya chanza kamar bashi ba, ya rame ya rage haske, gashi yaqaro sanyi bisa wanda yake dashi kallo daya zakamashi idan kasanshi sosai kasan akwai abinda kecimashi zuciya, bayada walwala ko kadan, rayuwa ta daina yimashi dadi sosai kaka ke tausaya mashi don wani lokacin har kuka take 6oyewa tayi don sosai ta hango tarin damuwar da Deen keciki kwata2 farinciki yayi qaura a rayuwarshi Kawai rayuwa yakeyi badon yanajin dadinta ba haka ranaku sukaita wucewa tun Deen na iya controlling emotions dinshi harya kai gejin dayakejin be iya haqura, he missed zee so very much don idan akwai abinda idanuwanshi sukafi kwaidatuwa da gani a lokacin zee ce ganin yakasa cigaba da daurewa yasashi fara tara kudi secretly acikin kudin dayake samu don zuwa ganinta be damu da abinda zatayi mashi ba ko korar kare zata mashi kotasa a kulleshi wannan ba damuwarshi bane, damuwarshi Kawai yaganta yasata a idanunshi koda na seconds biyu ne ko zaiji sauqin abinda yakeji a zuciyarshi haka yatara kudinshi watarana tunda safe yafita azuwan zashi aiki ya zarce tasha inda anan direct yayi boarding motar Katsina...✍? *🤦🏻‍♀️wannan flashback yaqi qarewa ni ashaanty* *na yarda aski idan yaxo gaban goshi yafi zafi, I want to end it but it's not ending😩😩* Ummin fasihu🤧🤧 8/3/21, 8:01 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *084* *masu complain ba'a posting kullum kuyi hqr, am trying my best, da danakeyi a kullum dama yabada hakan yanzu dakukaga sa6anin hakan yakamata kuyimin uzuri, dama kebada komai* Sai wajajen 5pm motarsu Deen tashiga garin Katsina, garin da yaga ya chanza mashi daga yin yan kwanaki ba acikinshi ba saukowa yayi daga cikin motar kamar yadda kingin pasinjojin keyi yana sake bin wajen da kallo shaqar iska yayi ya fesar yanajin wani irin feeling a zuciyarshi marar misaltuwa ahankali yafara tafiya yana dan waiwaigawa don samun abin hawa ba jimawa wata adaidaita tazo ta paka gabanshi mai adaidaitan na tambayar tafiya ce amsamashi Deen yayi da eh sannan yafada mashi inda zashi fadamashi kudin dazai biya mai adaidaitan yayi shikuma Deen yashiga batareda yasake cewa komai ba tafiyar kusan mintuna shabiyar sukayi kafin adaidaitan taja ta tsaya alamun an iso ta cikin adaidaitan Deen yajuyo yana kallon tangamemen gate din gidansu zee kasancewar a opposite din gidan adaidaitan tayi parking kafe kofar gidan yayi da kallo bugun zuciyarshi na qaruwa "ko ba nan bane?" inji mai adaidaitan jin shiru yaqi sauka sai a lokacin Deen ya janye idanunshi daga kallon gidan yajuyo ya kalleshi yace "eh nan ne" saukowa yayi daga adaidaitan sannan yazura hannu a aljihu don fiddomashi kudinshi daidai nan wata baqar motar tashigo layin ciro kudin Deen yayi ya sallami mai adaidaitan daidai motar ta tsaya kofar gidansu zee jin an danna horn yasashi dan juyowa daga mai adaidaitan dake bashi chanji gabanshi ne yafadi ganin mota a qofar gidan amsar chanji yayi sannan yajuyo sosai yana kallon motar da baya iya hango mutanen ciki saboda duhun glass dinta zuciyarshi ce tashiga racing yana wondering waye acikin motar bude gate din gidan akayi amma maimakon motar tashiga saitacigaba da tsayuwa a wajen kafe motar Deen yayi da ido daga dayan bangaren yana ji ajikinshi cewa shima kallonshi naciki keyi _was it Zainab?_ tambayar da zuciyarshi tayimashi kenan wannan tunanin yasa bugun zuciyarshi qara qaruwa ahankali yaga anbude seat din driver hakan yasashi kafe wajen da ido don ganin mai fitowa bala yaga yafito daga ciki yana kallonshi kamar idanuwan zasuyi magana shima Deen kallonshi yake batareda ya motsa inda yake ba gani yayi bala yanufi baya da sauri yabude mazaunin bayan binshi da ido Deen yayi yana kallon ta inda naciki zai fito sosai zuciyarshi ke wani irin bugu, yau dai gashi a kofar gidansu zee wanda wannan shine zuwanshi gidansu na farko sosai zuciyarshi tabashi zee ce bayan motar ganin bala agaba hakan yasa bugun zuciyarshi qin daidaita, burinshi tafito yaganta ko yaji salama na cikine yafito ahankali tun baya hangenshi sosai saboda bala daya kareshi harya bayyana agareshi sosai daddy ne tsaye staring keenly at Deen kamar yadda shima Deen din ke kallonshi ji Deen yayi kamar an sagemashi gwiwa, tsabar sanyin da jikinshi yayi jiyake kamar kaffafunshi bazu iya daukarshi kallo daddy ke binshi dashi na tsagwaron mammaki don hakan yanuna qarara a fuskarshi hakan yasa Deen sauke idanunshi qasa yanajin wani irin kunyar daddy ta lullu6eshi "Kamaldeen?" daddy yafada cikin mammaki wanda hakan yasa Deen dagowa yasake kallon daddy "Deen.. is that you?" daddy yaqara cewa yana,binshi da kallo saurin kada kai Deen yayi saikuma ya tsallako cikin sauri yana zuwa ya tsugunna yana gaida daddy idanunshi aqasa "me kakeyi anan?" inji,daddy batareda ya amsa gaisuwarshi ba dagowa Deen yayi ya kalleshi saikuma yafara motsi da baki amma maganar taqi fitowa "kaga Mallam tashi kabude baki kayimin magana, meya kawoka gidana uhm?" yafada cikin fada fada tashi Deen yayi yanajin kamar ya nitse ya huta "d..daddy..." "am not your daddy, tambayarka nayi kuma amsa,kadai nake buqata awajenka" daddy ya katseshi da hakan "meya kawoka gidana?" yasake tambayar meanly "daddy kuyi hqr...please, am so sorr..." "haryanzu baka bani amsata ba" daddy yaqara katseshi "na..nazo nabaku hqr ne..." "haqurin me? wani abu yafaru?" inji daddy yanamashi kallon raini Deen dakejin kamar zuciyarshi zata katse don tsalle ya hadiye yawu dakyar sannan yace "daddy kuyi hqr don allah, nima bada son raina komai yafaru ba" "kanajina? kayi maza kabar kofar gidannan kafin kafara regretting zuwanka" inji daddy meanly "please daddy don allah" yafada pleadingly "nace kabar nan" inji daddy tsugunnawa Deen zaiyi yana cewa "please dadd..." "nace kabar nan!!" daddy ya katseshi atsawace wanda hakan ya hanashi ida kaiwa qasa saima jada bayan dayayi jin tsawar har tsakiyar kwalwarshi "you have guts dama zaka,kwaso kaffafunka kazomin kofar gida? who do you think you are? to wlh kabarmin kofar gida tunkafin nayimaka abinda zaisaka danasanin sanina" "daddy don allah kayi haquri" "bakaji ba kenan?" saiya fiddo waya yafara shafe shafe "don allah daddy kayi hqr, nasan ban kyauta ba nasan bamu nuna hallarci ba, kuyi hqr ku gafarcemu amma wlh bada son raina hakan yafaru ba wlh inason Zainab.. komai yafaru ne bisa qaddara" dakatawa da shafe shafen da yake daddy yayi yayimashi wani kallo "wannan kalmar tafita daga bakinka mayaudarin banza, wane irin so kake mata dahar zaka gujeta alokacin datafi buqatarta, you broke her heart and you still have the guts to say you love her? how dare you?" "daddy wlh qaddara ce, I love her so very much Kawai..." "you never loved her.. baka ta6a sonta ba, yaudararta dama kakeyi kuma ni tuni nasan da hakan, itace dai,batasan da hakan ba har saida kanuna true colour dinka... well wannan kuma kai yashafa yanzu don daughter ta tariga tayi moving on, ta cikwikwiye babinka ta yar a dustbin yanzu haka,tayimaka nisan da ko hangenta bazakayi ba don haka kariqe haqurinka kabarmin kofar gida kafin na sassa6amaka" tunda yafara magana Deen ke sauke ajiyar zuciya ahankali, jin magangganunshi yake kamar ana watsamashi garwashi, dakyar ya iya bude baki yace "I know daddy.. I know nariga na 6ata damana, nayi ruining chance dina kuma ba lallai bane nasake samun wata ba amma don allah kuyi hqr ku yafemin duk abinda yafaru asanadina" ta6e baki daddy yayi yace "babu abinda yafaru ma sai alhairi, so no need of neman yafiya don munan jimukai ma gwamma da akayi" rintse idanu Deen yayi cikin jin zafin abinda daddy yafada, zuciyarshi zafi take mashi kamar a oven "you can go now" inji daddy cikin rashin damuwa da halin daya shiga ahankali Deen yabude idanunshi dasukayi jajur ya kalli daddy sannan cikin rawar murya yace "I'll go daddy, amma don allah kabari naga Zainab please" wani kallo daddy yayimashi "kaga Zainab kayimata me?" "please daddy.. don allah kabari naganta please" yafada pleadingly muryarshi na rawa sosai idanunshi jajur "don kasake huremata kunne? to bazaka ganta ba, now get going" "don allah daddy.. ba huremata kunne zanyi ba, hqr itama zanbata akan halin dana jefata" "wane hali ka jefata? babu halin daka jefata don kamar yadda nafada dazu wannan abin jimukai gwamma da akai so no need to bother yourself" "daddy don allah kabarni naganta please...please" yafada yana dafe saitin zuciyarshi saiga hawaye "bazaka ganta ba nace, bakaji abinda nace ba? nace,tayimaka nisa nisan da ko hangenta bazakayi ba so karka qara 6atamin lokaci get lost!" tsugunnawa Deen dake hawaye sosai yayi don duk dauriyarshi yakasa riqesu "don girman allah daddy kabari naganta, don allah. idan ban ganta ba zan iya mutuwa please" "to allah yajiqanka don idan hakane mutuwa tazama ma dole don Zainab batanan ko tananan bazan bari kaganta ba don kallon fuskarkama na iya tadomata wani ciwon, so go Zainab batanan, bata garinnan, bata qasarnan koma tananan babu abinda zatayi maka saboda she belongs to someone else now, kotananan bakada hurumin ganinta because she's now someone's wife...she's married" dagowa yayi ya kalleshi saikuma yadanyi murmushi yana girgiza kai "daddy I understand bakason komai yasake hadamu da zee, I know abinda kakeyi shine abinda kowanne mahaifi da akayima abu irin wanda nayimaka zaiyi, nasan bakason naganta ne don karna huremata kunne or something like that, please daddy koda agabanka ne ka kirata please hqr Kawai zanbata na nemi yafiyarta" dan murmushin takaici daddy "wato ga maqaryaci ko? you think kowa maqaryaci ne kamar kai? believe it or not Zainab is someone else wife dama cemaka akayi tarasa manemane data nace sai kai? mtcheew bala muje" yafada yana qoqarin komawa cikin motar saikuma yasake juyowa kan Deen dake kallonshi still kamar statue yana qoqarin fassara me daddy kecewa "for the last time kabarmin kofar gidana for your own good amma" yana kaiwa nan yashige motar dama bala yashiga suka shiga ciki leaving Deen standing like a tree kasa gane me daddy ke nufi yayi, jiyayi kamar wani yare yayimashi dabaya fahimta Zainab? Zainab is married? haba impossible Kawai daddy beson yaganta ne shiyasa yace hakan amma babu yadda za'ayi ace Zainab tayi aure da wannan tunanin Deen yadanji zuciyarshi tayi sanyi qara daga kai yayi ya kalli gate din gidan dakeda tsayi sosai yana tunanin behind this gate akwai muradin ranshi aciki, baxai iya tafiya ba dukda warning dinda daddy yayimashi, he has come this far don Kawai yaganta kozaiji sauqin abinda zuciyarshi kemashi so duk yadda za'ayi duk tsawon lokacin dazai jira saiya jira don baxai zo abanza ba haka yakoma gefe yasamu dakali ya zauna yana kallon gate din kamar za'a iya budemashi at any moment haka yaita zama under the scorching sun yana jiran tsanmmani ga wata iriyar yunwa dake kwakularshi don dik yau beci wani abin kirki ba yana lura da yadda every now and then maigadi ke dan bude qaramin kofar gate din ya leqoshi saikuma yakoma bece komai ba bekuma tashi ba saima hoping dayake allah yasa daddy yaji tausayinshi ya yarda yaga zee din ahaka yana zaune marece yayi sosai don har rana tafara alamun faduwa wata mota ta qaraso kofar gidan dagowa yayi yana bin motar da kallo batareda ya motsq daga inda yake ba wasu maza biyu cikin shigar shirt and trouser suka sauko daga motar suka nufoshi har lokacin be motsa ba har suka qaraso wajenshi suna bin juna da kallo batareda sunce mashi komai ba daya daga cikinsu yakara wayar hannunshi kunne yana cigaba da kallon Deen "eh alhaji.. gashi nan mun iso... eh mun taddashi.. ok to shikenan" saiya katse wayar sannan yaqara fuskantarshi "young man meyasa kakeson proving stubborn? mai gidan nan ya buqaci kabarmashi kofar gida amma you stubbornly remain there, did you know what you're getting yourself into?" inji mutumin Deen dai bece komai ba sai cigaba da kallonshi dayake daga zaune dayan yazaro ID card yanuna mashi yace "mu yan sanda ne alhaji yakiramu nan ne don muyi getting rid of you from his house, so for your own good katashi katafi batareda mun tilastaka ba" sai a lokacin Deen ya bude baki ahankali yace "zan tafi, amma please kubari naganta... saboda naganta Kawai nataho daga inda nake mai nisa,.I promised idan naganta zan tafi koda bazaku bari nayimata magana ba" "bakaji yace tayi aure ba? she's married kuma batama qasar kwata2 bare kaganta so is better you leave" inji nafarkon "tana ciki sir, I know tana ciki Kawai bayaso naganta ne..." daidai nan aka bude qaramar qofar gate daddy yafito wanda kallo daya zakamashi kasan ranshi a matuqar 6ace yake "meye kuke jira haka baku tafi dashi ba? eh?" "alhaji abinda muke niyyar yi kenan, muna qoqarin fahimtar dashi yarinyar bata gidan ne" inji daya daga cikin yansandan "harsai kun fahimtar dashi? wazai maka qarya anan? wayai maka kama da qaramin mutum anan? who did you think you are da Zainab bazata auri wani ba bayan kai? gani kake don tanasonka bazata iya rayuwa,babu kai ba? inma haka kake gani you're totally wrong, she proved you wrong tunda gashi tayi exactly abinda kake ganin bazata iya ba, tayi moving on tayi aure tana abroad living happily, nobody needs you now so disappear" Deen dake hawaye tunda daddy yafara magana ya girgiza kai ahankali "daddy I know I hurt you guys and you're trying to hurt me back too, daddy ko iya nan ka tsaya naji kwatankwaci ko fin abinda nasaku ji, don allah ka sassautamin hakanan, kayi hqr kabari naganta nasan tana nan, Zainab bazata auri wani ba.. kada allah yasa hakan yafaru" sakin baki daddy yayi yana kallonshi tunda yafara saikuma ya kada kai yace "saidai atari gaba don hakan yariga yafaru, Zainab saidai wata ba 'yata ba don tayimaka nisa and if you think am lying ga wadannan..." yafada yana watsamashi wasu yan cards "check and see, fatan hakan zaibaka amsar ka" bin cards din qasan Deen yayi da kallo saikuma ya tsugunna yayi picking dinsu yatashi yana dubasu kanshi yayi wani mummunan sarawa lokacin dayayi arba da invitation cards wanda sunan zee ke rubuce 6aro 6aro ajiki amatsayin bride under it kuma sunan namiji ne wanda tashin hankali besa ya iya riqewa ba "yanzu ai zaka yarda ko tunda kagani da idonka, Zainab is married..happily don haka ka kama gabanka allah ya hadaka da rabonka" "impossible.." Deen yafada in whisper yana cigaba kallon cards din hannunshi da gajiyayyun idanunshi "but it is, it's possible don gashi ma kagani.. please officers send him away banason ganinshi anywhere near here" sakin cards din Deen yayi yanufo daddy dasauri "no.. daddy please don't do this to me, please" yafada da muryarshi datafi kama da rad'a yana nufo daddy saidai kafin ya iso officers din sun tareshi ganin zai turesu yawuce yasa suka rirrikeshi "ku sakeni! get your hands off me!" yafada cikin daga murya yana fizgewa da qarfi saidai sun riqeshi gamm "don't do this to me daddy... please" yasake fada cikin very cracked voice "kubarmin kofar gida dashi" inji daddy da ko kadan halin da Deen keciki be ta6ashi ba illa wani farinciki da satisfaction dayakeji na ya ramama zee abinda yayi mata "NO.. Zainab! Zainab!! Zainab please come out am here!!" yafada cikin daga murya sosai yana qoqarin wucewa gate din gidan amma mutanen sun rirrikeshi "take him away" inji daddy "don't do this to me..." yafada qirjinshi na heaving haka suka janye Deen dake maimaita 'don't do this to me' cikin muryarshi dake fita dakyar suka sashi a motarsu qarama ba irinta yan sanda ba maimakon ya cigaba da struggling kamar yadda suka zata saigani sukayi ya kife fuskarshi akan.front seat yadafe saitin zuciyarshi da hannu bibbiyu yana sauke numfashi masu nauyi hakan yasa dayan dan sandan saurin zagayawa yashiga mazaunin driver dayan kuma na taredashi abaya riqeda bindiga suka ja motar suka wuce ajiyar zuciya daddy ya sauke bayan tafiyarsu sannan yajuya yakoma ciki yana fatan yatafi kenan don idan yadawo he won't take it likely with him saida yaqara bigema su bala da masu gadi warning cewa kada maganar dawowar Deen yasake yayi leak har yaje kunnen mummy sannan yawuce ciki don dama dalilin dayasa bebi da hayaniya ba kenan don beson yajawo hankalin mummy tasan meke faruwa don tsaf zata ruguzamashi shiri a bangaren Deen kau tunda yakifa kanshi a tafukkan hannunshi be dagoba har suka iso idan suka ja suka tsaya bubbude kofoffin sukayi suka fita sannan mutumin baya ya fiddoshi ya watsar gefen titi "go away for your own good, idan kasake komawa we'll make sure you rot in jail" inji dayan sternly komawa sukayi cikin motar suka ja suka barshi nan kasa koda motsi yayi a inda yake yashe azaune, misalta abinda zuciyarshi ke going through lokacin abune mai matuqar wuya jiyake he's world is turning upside down sai lokacin yasan ashe kuka ma rahama ne don kasayi yayi sai ajiyar zuciya dayake saukewa kawai, tsakanin zuciyarshi da maqoshinshi yarasa wane yafimashi yaji yajin ciwo har akayi magrib akayi isha'i yana nan zaune inda suka barshi gefen titi yakasa ko motsawa hannayenshi still dafe dake zuciyarshi dayakejin tanamashi wani bala'in zafi daga baya ne yasamu yatashi dakyar yafara tafiya,cikin jan qafaffu tafiya yake batareda sanin inda zashi ba *** A bangaren kaka kau tunda marece take jiran dawowar Deen amma shiru wasa wasa har magrib tayi har akayi isha'i shiru hakan yasa hankalinta ida tashi babu shiri tafito daga gidan don nemanshi ita da daya daga cikin mazan gidan nasu sosai hankalinta yatashi dukda kwantar mata da hankali da mutumin keyi, gashi babu waya a hannun Deen bare akira aji abinda yafi dagamasu hankali shine sanin dasukayi kasuwar dayake aikin ana rufeta ne shidda da rabin marece kuma daga nan beda wurin zuwa sai gida don saima yadawo yake sake fita sallar magrib ganin lallashin da mutanen gidan keyima kaka da kwantar mata da hankalin beyi yasa suka fito din tareda wannan mutumin don cigitawa don suna zaman mutunci sosai da sabbin maqoftansu gidansu wani saurayi dake qasan layinsu sukaje wanda shima yana zuwa aiki akasuwa saidai ba aikinsu daya da Deen ba cikin sa'a suka taddashi be dade da dawowa sallar isha'i ba anan suka tareshi suka gaisa sannan suka tambayeshi don allah ko duk yau yaga Deen akasuwa amsamasu yayi da shidai gaskiya duk yau bega Deen ba kuma ba laifi ya bibbi ta shagonsu nan suka sake tambayarshi ko yasan wani daga cikin wadanda suke aiki a shagonsu Deen saida yadanyi tunani sannan yace eh yasan wani amma ba nan unguwar yake ba nan suka roqeshi yakaisu ko yaimasu kwatance saiyace to bari yashiga gida yafito saiya rakasu haka kau akayi babu dadewa saurayin yafito suka hau abin hawa sukaje unguwar dukda bawani nisa ke akwai ba cikin sa'a suka iske wanda sukaje nema a rumfar wani mai shayi saurayin daya kawosu yaje yakirashi suka dawo wajensu kaka suka gaisa sannan suka tambayeshi yaga Deen yau amsamasu yayi cewa gaskiya duk yau besa Deen a ido ba don bemazo aiki ba don har jajenshi saida akayi awurin kasancewar basu saba ganin yayi fashin zuwa aiki ba nanfa hankalin kaka yaqara dugunzuma, kan kace me harta fara kuka tana cewa ina Deen zai shiga cikin garinnan da duka duka ko wata basuyiba acikinshi? ina zata fara nemanshi? ataqaice dai haka suka koma gida cikin damuwa suka gayawa mutanen gidan nan suma hankalinsu yatashi, duk inda suke tunanin zasu ganshi sunje amma shiru babu shi qarshe dai nearest police station sukaje suka bada report din 6atanshi inda akayi musu alqawarin bincikashi sannan suka koma gida ranar yadda kaka taga rana haka taga dare kuka kau tun tanayi har muryarta yabar fita Washegari ma haka suka tashi da heavy heart, mutanen gidan dayake sunada kirki sosai su sukaita tausar kaka da har wani hiri hiri tayi saboda tashin hankali ranar ma haka suka dasa neman Deen amma shiru har police station din suka koma suma ba labari haka suka wuni cikin jimami mutane nadan shigowa sunama kaka jaje, daga baya ma har sanarwa sukakai gidan radio da taimakon su mazajen gidan sai wajajen isha'i kowa na waje an zazzauna kan tabarma matan gidan sunsa kaka atsakiya sunata qoqari wajen kwantar mata da hankali sukaji sallamar wasu maza daga bakin kofa amsawa duk sukayi suna bada izinin shigowa wasu maza suka shigo suna cewa ga wannan yaron da ake nema can waje asume kafin kowa yatashi kaka ta tashi don tunkafin su ida maganar tayi zumbur tamiqe tanufi waje agigice mutanen na maramata baya daga qarshen dakalin kofar gidan nasu tahangi tarin mutane hakan yasa tanufi wajen tana kuka sosai ratsa mutanen tayitayi harta qaraso gaban wurin inda taga Deen kwance daya daga cikin mazajen gidan na shafamashi ruwa a fuska agigice kaka tazube gabanshi tajawoshi ajikinshi tana rusa kuka kamar ranta zai fita ganin dik shafa ruwan da akayimashi be farkaba yasa mazajen wajen shawarar akaishi asibiti Kawai haka kau akayi cikin qanqanin lokaci aka samu abin hawa suka saka Deen da har lokacin ke unconscious aciki sai kaka da daya daga cikin mazajen gidan hayansu suka kama hanyar asibiti suna isa babu 6ata lokaci aka amshesu saboda ganin yanayin dasuka kawo Deen, nan da nan aka hau bashi taimakon gaggawa tun kaka na kuka har hawayen idanun suka kafe haka sukaita jira waje cikin tashin hankali suna jiran tsanmmani saida likitoci sukafi awa akanshi sannan suka fito inda suka nemi ganin iyayen yaron kaka da mutumin sukabi likitan har office dinshi inda anan yake gayamasu halin da Deen yake ciki cewa jininshi yahau sosai ga ciwon zuciya dake barazanar kamashi sosai hankalin su kaka yasake tashi inda ganin hakan ne yasa likitan kwantar masu da hankali cewa insha komai zaiyi daidai sannan ya rubuta masu magungunna da injections dasuke buqata haka suka fito daga office din likitan kaka still takasa daina kuka gani take kamar zata rasa Deen ne lokacin har dayan mijin matan gidan hayansu yaqaraso shima inda da taimakonsu aka siya duk abubbuwan da aka buqata don kaka bawani kudi gareta ba anan kaka ta kwana tareda Deen wanda da alamu allurar barci sukayi mashi, fuskarshi tayi fayau tafada sosai gwanin tausayi be farka ba sai Washegari wajajen taran safe yana tozali da fuskar kaka da tunda yabude ido tayi wajenshi tana kiran sunanshi yafashe da kukan daya kasayi tun a Katsina kuka yake sosai yana fadin yarasa zee shikenan yarasa zee har abada ganin yadda yake kukan yasa hankalin kaka sake tashi babu shiri tayi waje don kiran likita koda suka dawo ma kukan suka tadda yanayi yana shikenan yarasa zee, dakyar Dr yashawo kanshi yaqara yimashi wani allurar barcin wanda yasashi komawa to slumber nan take sosai kaka tadinga kuka tana kallon Deen daya dawo abin tausayi duk saitaji wani feeling na guiltiness zuciyarta tayimata mugun nauyi sanin cewa kowanne hali Deen yashiga itace sila lokacin da Deen yasake farkawa beyi kuka ba wannan karon saidai kallo daya zakamashi kasan he's really in pain he looks so sad and down and that day mark the beginning of his sorrowful life kwanansu biyar aka sallamesu saidai kwata2 Deen ya chanza yakoma kamar bashi ba he's no more the cool and happy Deen, farinciki yayi qaura a rayuwarshi Kawai rayuwa yakeyi batareda yasan dadinta ba baya murmushi, shirunshi ya ninka nada yakoma wani iri gashinan dai baya fita saida dalili wanda mostly zuwa masjid ne ko shiga toilet amma daga ba haka ba kodayaushe yana qunqume cikin daki kamar matar kulle wannan sabon sauyin na Deen ba qaramin sake dagulama kaka lissafi yayiba, wani irin tausayinshi takeji tana kuma rashin kyautawarta na hukuncin data yanke tunfarko, tasan ko mai yafaru itace sila hakan yasa takejin guiltiness sosai kaka fara jaraba sana'a tayi da yan kudin hannunta don tunda Deen yadawo beqara fita da sunan zuwa kasuwa ba gashi komai nasu qasa yakeyi hakan yasa kaka tattara yan kudinta tafara sana'ar toya fanke dasafe cikin ikon allah saigashi allah yasama abin albarka don kaka koyaya tayi abu dasunan sana'a sai allah ya albarkaci abin ya buda mata tun tanayi mutanen cikin gidan kawai na siye har yan waje suma suka gane suna shigowa saye cikin ikon allah saigashi suna samu suna rufawa kansu asiri da sana'ar saida Deen yafi wata a yanayin dayake ciki sannan yafara dan samuwa da taimakon addu'o'i da kaka ke sashi aciki kullum dakuma rubutun dangana datake bashi yaji sauqin abinda yakeji yakuma yi deciding yayi moving on dukda abu ne mai matuqar wuya agareshi yakasa mantawa da memories din rayuwarshi da zee abaya, jiyake da ana tariya daya tariyo rayuwarshi ta baya sun dawwama acikinta amma hakan be yiwuwa ganin wahala da fadi tashin da kaka kemasu itakadai don rufama kansu asiri yasa Deen yake shawarar cigaba da fita nema don he can't watch her struggling all alone ranar daya shirya zaya koma kasuwa farinciki awurin kaka baya misaltuwa don jitake kamar taita rawa don murnar yaronta yafara dawowa haka taita samashi albarka ta rakashi har waje tana qara godewa allah azuciyarta tana addu'ar allah yasa qarshen wahalar kenan, sosai tayini cikin farinciki don tasan koba komai dan fitan nan dazai dinga yi zai taimaka wajen ragemashi damuwarshi sosai sosai co-workers dinshi na kasuwan sukayi murnar dawowarshi don babu laifi sundan saba dashi kuma duk sunji abinda yasameshi hakan yasa sukaita mashi ya qarfin jiki yana amsamusu da faint smile dinshi dayanzu yazama shade to his sorrowful state babu 6ata lokaci yakoma aikinshi kamar da saidai kwata2 yanzu bayajin dadin aikin kamar farko kawai yiyake maganin zaman banza amma har a zuciyarshi aikin bemashi ba bawai don ba'a samu ba Kawai dai yafison yayi wani aikin daya kasance dole akwai experience yakasance aikin hannu daxaka koya ka iya ba wannan da qarfi Kawai yake buqata ba yana son aikin dake buqatar basira kamar dai wancan na capentary dayakeyi a Katsina hakan yasashi fara neman workshop workshop na capentary don komawa irin aikinshi nada amma duk inda yaje babu vacancy haka ya cigaba da aikin dakonshi a gefe yana neman aikin capentary amma tsit kakeji watarana yazo wucewa zaitafi kasuwa yabi tawata gareji daya saba bi idan zai tafi kasuwa, saiya tsinci kanshi da tsayawa ya qurawa wurin ido yana kallon kanikawan dake buge.bugen karafuna haka Kawai yaji aikin nasu yashiga ranshi farat daya hakan yasa ya qarasa wajen yana kallon mutanen wajen sallama yayima mutanen wajen wanda hakan ya maido hankalinsu akanshi amsamashi sukayi suna binshi da kallo hakan yasashi dan sakarmasu murmushi "erm...dan allah ina ogan garejin nan? nima garejin nakeson fara zuwa idan akwai vacancy, inason fara irin aikinku ne" kallon juna mutanen da duk samarine sukayi sai daya yace "kutt... wlh nayi tunanin balarabe ne dafarko, nan jira kawai nake yafara cemana *Hal anta majnunun*" dariya kingin suka kwashe daita sannan daya yace "majnunu fa mahaukacine Dogo, kodai anyi asarar kudin laraba ne" daya yace "Yo ai dama mahaukacinne, dama kajen haquri yayi da beyi magana ba dasai balaraben ya tambayeshi koshi majnunun ne don akallo daya akegane hakan" "kai wlh qaryane don ubanka, dani dakai wayafi ruwan mahaukata?" inji nafarkon haka suka cigaba da caftar mai cikeda ban dariya sukama manta da Deen dake tsaye yana kallonsu ganin hakan yafara shawarar koya tafine? saikuma yace bari dai yasake masu magana hakan yasashi sake cewa "don allah.. yana nan ne ogan?" sai a lokacin suka sake dagowa "eh to yanzu dai bayanan amma ko yananan dakyar zai daukeka muma kanmu complain yake munyi yawa" inji wani "sannu.. ina ruwanka da yanke hukunci akaran kanka,kabari yaga ogan mana yagayamashi idan ma munmashi yawan, bansan iyayi... kai balarabe kaje kadawo anjima idan yadawo saika sameshi" inji dayan "to da yaushe kenan?" inji Deen dake kallonsu "anjima kadan bayan azahar kadawo nasan yana nan",inji saurayin "to amma kai karasa aikin daya burgeka sai kanikanci kana fari tass dinka? ca6 wlh da nikeda farinka babu abinda zaisani kanikanci wlh saidai aikin office" inji Dogo "kaji marar kishin kai yana kushemana sana'a to wlh kamar kayi a kunnen oga" "yo ai gaskiya ne, kanikanci banda kwalliya da baqin mai me ake aciki, dubeni fa da haske na nazo garejin nan amma yanzu nazama dawanau" dariya suka fashe daita "a gidan ubanwa kaxo da haske? dama a dunan ka kazo sai uban qasusuwa banda ma rashin godiyar allah ai kaima kasan kamori kanikanci tunda gashinan kayi 6ul6ul dakau banda uban kai me kake dashi?" "tubarkallah bismillah" inji mutumin da akema tsiya din Deen be tsaya qarasa jin caftar su ba yawuce yana addu'ar allah yasa ogan ya daukeshi aikin don haka Kawai yaji aikin yashiga ranshi lokaci daya da wannan tunanin ya qarasa wajen aikinshi inda yashiga yin aikinshi yana fitowa daga sallar zuhr yawuce direct garejin yana addu'ar allah yasa ya tadda ogan cikin sa'a kau ya taddashi inda yaga mutumin magidanci ne don zaikai irin shekara arba'in dawani Abu dinnan saida suka gaisa sannan ya gabatar mashi da buqatarshi nason fara zuwa garejin da farko kamar baxai yarda ba don acewarshi yara sunmashi yawa saikuma yace yaje yadawo gobe idan allah yakaisu zai duba godiya Deen yayimashi sannan yatafi cikeda saran samun aikin Washegari kau tunda wuri yaje don harwani doqin zuwa yakeyi inda anan ogan yace ya daukeshi aikin yakuma gayamashi sharuddan garejin tareda gabatar mashi da sauran yaran garejin su biyar Dogo, Sule, Habeeb, Nura da Yusuf yakuma gayamashi a matsayinshi na junior dole yabi wadanda ya tadda koda ya girmeshi don yanzu shine junior dinsu kwata2 kuma akwai banbanci a sallama don anayine according to seniority duk Deen ya amince da hakan sannan ogan yace yana iya tsayawa yau din kokuma yaje yabari sai gobe yafara zuwa cewa Deen yayi zaifara yau din hakan yasa ogan ya hadashi da daya daga cikin yaran (Habeeb) akan yatafi dashi cikinsu ranar Deen yaqara sanin yadda yan garejin suke don shaqiyai ne na gidan gaba zolaya babu wanda besha ba wurinsu inda suka rad'amashi balarabe da qarfi da yaji don babu wanda ya tsaya bi takan sunanshi kawai sun rad'a mashi nasu wato balarabe ranar saidai yazama dan aike, dauko wancan spanner miqo wancan haka sukaita aikenshi idan be ganeba suyimashi bayani, at the end of the day aka sallamesu inda nashi sallamar duk yafi na sauran qanqanta be damuba ya amsa yai tahowarshi gida yanajin dadi don sosai yaji dadin yininshi daya a garejin don mutanen garejin badai ban dariya ba, suna aiki suna shaqiyancinsu hakan yasa koyaya kaje zauna wajen saisun saka nishadi saida yakoma gida yagayama kaka sabon aikin dayasamu yakuma bata sallamarshi kaka bataji dadi ba don sallamar batakai abinda yake samu a kasuwa ba gashi tana ganin aikin aikin qarfi ne zaifi na kasuwar wahala amma ganin yadda Deen yanuna yanason aikin yasa bata hanashi ba saima fatan alhairi datayi mashi to daga wannan lokacin Deen yazama bakanike shima yazamana kullum yana gareji Atashin farko Deen yayi popular a garejin, bayada surutu ko kadan saidai rashin kyashi dinshi yasa yaran garejin ke sonshi sosai don saidai kaji ana balarabe miqo kaza, balarabe yi kaza kuma nan take zaiyi yana haddace me akeyi dayake yana son aikin sosai hakan yasa yake saurin dauke komai batareda anyimashi maimaici ba, ga tambaya don duk abinda yashige mashi baya jinkirtawa wajen tambaya kaifin kwalwarshi da karsashinshi a aiki yasa cikin qanqanin lokaci yayi suna a garejin inda ogansu keji dashi sosai saboda tsantsar biyayyarshi da kaifin kwalwarshi duk cikin yan garejin Deen yafi sabawa da Habeeb don jininsu yafi haduwa dukda Habeeb nada surutu sosai sa6anin Deen shaquwarsu yasa Deen fara kwana shagon da Habeeb ke kwana kasancewar unguwarsu daya kullum tare suke zuwa gareji sukoma tare lokacin kwanciya kuma su hade a shago, wannan yasa abotarsu taqara qarfi sosai cikin yan watanni Deen yayi suna a garejin na ban mammaki, sosai customomi keson aikinshi don dayawa saisuka dawo idan sun kawo aiki basusan kowa ya ta6amasu mota sai Deen gaskiyarshi da rashin ha'inci irin na wasu daga cikin yaran garejin yasa customomi sukafi sonshi ga uwa uba sanyinshi da biyayyarshi dake matuqar burge mutane sosai hakan yasa nan da nan ya kwacema sauran customomi inda duk cikin yaran garejin yafi kowa customers dukda shine junior dinsu gashi ogansu ya yarda dashi sosai yana kuma yawan dorashi akan abubbuwa da dama saboda yarda dayayi dashi kasancewar ogan ba a iya kanikanci Kawai ya tsaya ba harda kasuwanci irin nasu na yan gwangwani daga baya ma saima ya miqa kusan ragamar kasuwancin hannun Deen don saiya zama kamar wani assistant dinshi don duk cikin yaran garejin babu mai makullin shagon kasuwancin ogan sai Deen wannan cigaban daya samu sosai saiya tsonewa wasu daga yaran garejin ido musanmman wadanda ke ganin sundade sosai a garejin tayaya wannan daga zuwanshi a dinga fifitashi akansu a matsayinshi na junior dinsu hakan yasa suka fara yimashi hassada suna ganin be cancanci matsayin dayake akai ba tun suna iya 6oye hassadar dasuke mashi harsuka kasa don dagabaya qarara suka fito suna nunamashi qiyayya, Habeeb ne Kawai mai kaunarshi tsakani da allah dayake hassada ga mai rabo taki take zama hakan yasa kodayaushe Deen cigaba Kawai yake samu takoina wanda hakan yasa yan garejin hada kai don qullamashi sharrin daxai dusashe tauraruwarshi ranar ranace da Deen bazai ta6a mantawa ba inda aka nemi wasu kayan engine akarasa a shagon wanda kudinsu ba dan kadan bane abin ya tadawa kowa na garejin hankali musanmman Deen don bayan ogansu shikadai keda key din shagon hakan yasa kullum shine qarshen tafiya gida tun ana daukar 6atan kayan wasa har akaga dagaske sun 6ata din inda babu wata wata aka dora ayar tambaya akan Deen dayake ogan irin mutanen nan ne dabasu yarda da qaddara ba ko asara nan take ya manta da tsantsar amanar Deen da gaskiyarshi yahau tuhumarshi acewarshi dole yasan wani abu gameda 6atan kayan nanfa hayaniya ta tashi ogan ya murje ido akan sai Deen yabiyashi kayanshi sosai hankalin Deen yatashi don tunda yake ba'a ta6a yimashi qazafi irin haka ba, duk yadda yaso wanke kanshi qin yarda dashi ogan yayi inda sauran yan garejin keta qara zugashi akan karya yarda mutane biyu Kawai suka goyi bayan Deen da Habeeb dawani maqocinsu a garejin mai saida tayoyi ganin hakan yasa Deen cewa zai biya amma allah yasani bashi yadauka ba, be ta6a sata ba kuma insha allah bazai ta6a yiba haka yadawo gida zuciya a quntacce yaba kaka labari inda itama ta tayashi jimami sosai tana tayashi jin zafin qazafin da akayimashi haka Deen ya tattaro yan kudaddenshi dayake tarawa kaka tacikamashi yabiya ogan daga ranar kuma ya daina zuwa garejin sosai rayuwa tasake juyema Deen inda yasake komawa halin qunci na da dama wannan aikin dayakeyi ke dan debemashi kewa hakan yasa yanzu yaqara komawa gidan jiya na halin damuwa komawa yayi tsohon shagonsu na kasuwa ya cigaba da aikin dako badon yanason aikin ba saidon baison zama hakanan sosai yayi missing gareji da kanikanci don yanason aikin sosai saboda aikin ma kanshi nasashi nishadi na musanmman har lokacin alaqarsu da Habeeb nanan don dafarko shima Habeeb yaso barin garejin Deen ya hanashi hakan yasa anytime he's free yake leqo Deen acikin kasuwa haka rayuwa ta cigaba da kasancewa har watarana Deen a hanyarshi tadawowa daga kasuwa lokacin har magrib takusa yagamu dawani mutum yana fama da motarshi harya wuce saikuma yadawo ya qarasa wajen mutumin yana mishi sallama amsawa mutumin yayi yana dagowa yana kalleshi hakan yasa Deen cewa "motar taqi tashi ne?" kamar wanda dama ke akan qaya yace "eh wlh dan saurayi, kaganta nan narasa meke damunta gashi sauri nake zani wani wuri gashi duk garejijika sun kulle na rasa yadda zanyi" yafada da alamun damuwa a fuskarshi "bari mugani..." inji Deen yana sunkuyawa gaban motar yana dubawa haka kawai yaji kwadayin kanikancin na tasomashi, rabonshi da ta6a mota da niyyar gyara tun lokacin dayabar garejinsu mutumin dai tsayawa yayi yana kallon Deen don kwata2 bemashi kamada bakanike ba, hakan yasashi tsayawa kallon ikon allah saida Deen yadan dauki lokaci a sunkuye sannan yacema mutumin yashiga motar ya tada yaji hakan kau mutumin yayi yashiga yatada Deen ya sake sunkuyawa yana gyaran cikin qanqanin lokaci motar ta tashi sosai farinciki ya lullu6e mutumin wanda hakan yakasa 6oyuwa a fuskarshi hakan yasa yafito yanata mashi godiya yana tambayar dama shi bakanike ne? murmushi kawai Deen yayi bece komai ba kudi mutumin yabashi amma firr Deen yaqi amsa, dik yadda mutumin yaso ya amsa qiyawa Deen yayi hakan yasashi haqura nan mutumin ya tambayeshi inane garejinsu, kamar Deen zaice bayada gareji saikuma yayi mashi kwatancen tsohuwar garejinsu kawai godiya mutumin yasake mashi suka rabu Bayan kwana biyu mutumin yaje garejin da Deen yaimashi kwatance don sosai Deen ya kwanta mashi yakuma shiga ranshi farat daya gakuma tunda yake bada gyaran mota ba'a ta6a yimashi gyaran dayaji dadinshi ba irin wannan saidai koda yaje bega Deen ba yakuma tambaya inda yana musu kwatancenshi suka gane Deen ne abinne yasosama yaran garejin rai don tun barin Deen garejin ba ranar banza da baza'a zo nemanshi ba, wasu ma har barin kawo aiki sukayi garejin hakan yasasu cewa su basu sanshi ba qila ba daidai yaimashi kwatancen ba daidai nan Habeeb yazo wurin jin abinda ake tattaunawa yasashi yin caraff yace kodai balarabe yake nema dasauri mutumin ya kadamashi kai yace eh yana kama da balarabe caraff daya daga cikin yaran garejin yace inda balarabe ne toya andade da korarshi daga garejin saboda sace sacen dayakeyi ran Habeeb ya6aci da kalamanshi nan yashiga maidamashi cewa saidai insune 6arayin amma Deen ba 6arawo bane kuma zakaran da allah yanufa dacara ko ana muzuru ana shawo saiyayi sannan yajuyo kan mutumin yace aiki ya kawo ko balaraben yake nema? mutumin daketa kallonsu tundazu yace balaraben yake nema hakan yasa Habeeb yace yataho yakaishi wajenshi sosai hakan ya 6ata ran yaran garejin don ba haka sukaso ba, dukda sun raba Deen da garejin sunkasa rabashi da masoyanshi don hatta ogansu shima yanzu danasanin abinda yafaru yakeyi don barin Deen garejin nashi ba qaramin cibaya yajamashi ba Cikin motar mutumin suka tafi neman Deen inda akan hanya Habeeb ke labartama mutumin duk abinda yafaru da barin Deen din garejin hakan yasa Alhajin tausayawa Deen yakuma ji yaqara shiga ranshi fiyeda da koda suka isa shagon basu iske Deen ba don acewar co-workers dinsu be dade da tafiya gidaba don wani lokacin yana komawa gida cin abincin rana Alhajin be gajiba yace suje gidan nasu shidai yanason ganinshi babu musu Habeeb yakaishi har gidan nasu inda anan suka hade da Deen da fitowarshi kenan da niyyar komawa kasuwar sosai Alhajin yaji dadin ganin Deen nan suka gaisa cikeda mutuntawa inda saida Alhajin ya tunama Deen inda suka fara haduwa don shi harya manta nan Alhajin ya buqaci zai dinga kiranshi duk lokacin dayakeda gyara yazo yayimashi babu musu Deen ya amince mutumin yabashi card dinshi mai dauke da address dinshi da number waya shima Deen yabashi number wayarshi haka kau akayi don duk lokacin da Alhaji Shamsu kamar yadda sunanshi yake ya buqaci gyaran mota zai latso Deen yazo yayimashi wani lokacin har hanya yakemashi yayima wasu don sosai yakeson aikin Deen saboda qwarewarshi shima Deen sosai yakejin dadin aikin Alhajin don mutumin akwai sanin darajar mutane, dukda shi mai kudine amma hakan besa ya qyamaceshi ba, yana nunamashi qauna sosai ahaka ne suka hadu da diyar Alhajin mai suna Lailah agidan Alhajin wanda tun a farkon haduwarsu ta afka soyayyarshi kuma haryanzu tana sonshi batareda yama san tanayi ba don shi banda gaisuwar mutunci babu abinda ke hadasu daita Alhaji Shamsu yanada mata daya sai 'ya'ya shidda duk mata, hudu daga cikinsu duk sunyi aure sai Lailah dake karatunta haryanzu sai yar qanwarta kuma autarsu Afrah Alhaji bayada d'a namiji kodaya kuma tunda yake beta6a jin qaunar mutum kamar yadda yakejin yadda yakeji gameda Deen ba hakan yasa ya daukeshi kamar danshi yana nunamashi qauna ta tsakani da allah ana haka watarana yabashi aiki inda yayimashi text din address din inda zaije yasamu motar don lallacewa tayi ahanya yabarta yahau wata yadawo sashi yayi yafara aikin gashinan zuwa haka kau akayi inda Deen yaje wajen yafara aikin motar can yana tsaka da aikin tunanin zee yafadomashi kamar yads tunaninta ke yawan kawomashi ziyara akodayaushe dukda yasan yanzu zee tayimashi nisa hakan besa yadaina tunaninta ba akodayaushe cikin tunaninta da begenta yakeyi fuskarta tayimashi gizo a idanunshi smiling like an angel hakan yasashi shima sakin guntun murmushi ahankali _old good memories of you.._ _never want to fade in my brain_ _you're stick to my brain like a magnetic glue_ _never wanting to shift for a bit_ _an angel.._ _the angel... that I never saw someone like her that exist_ _an angel..._ _the angel that will always never exist_ cikin cool voice dinshi yacigaba da waqar wanda anan take yake composing dinta dama yanzu haka yake, haka kawai yana zaune shikadai saiya fara waqa wanda mostly tana zuwa ne duk lokacin dayayi nisa cikin tunanin zee dinshi shikanshi besanin sadda yake farawa saidai yaji kawai yanayi kuma waqar nazuwa ne from the bottom of his heart don abinda yakejine yake furtawa directly a sigar waqar haka yaitayi yana aikinshi yana waqarshi, dayayi wannan yayi wannan, wasu da hausa wasu da turanci nan da nan yagama aikin ko harda waqar datayi making dinshi busy yasa yaga saurin aikin oho? yana gamawa ya maida gaban motar yarufe yadago yana share gumi tozali da Alhaji dayayi agabanshi yasashi dakatar da abinda yakeyi yana dan wara idanu "Alhaji yaushe kazo?" yafada da mammaki "tun lokacin daka fara waqarka" yabashi amsa kunyace takama Deen hakan yasashi sunkuyar dakai yana sosa gefen wuya "ashe ka iya waqa? gaskiya tunda nake banta6a jin muryar datayi captivating dina irin wannan ba" kunya Deen yaqaraji hakan yasashi cewa "to ko ka gwada motar kotayi?" murmushi Alhajin yayi yashiga motar yatada yajita tayi daidai hakan yasashi fitowa yana cewa tayi sosai murmushi Kawai Deen yayi Alhaji yasake cewa "kanada ra'ayin yin waqa? yadda naji muryarka dinnan awaqa nasan baqaramin mawaqi za'ayi anan ba" sunkuyar dakai Deen yaqara yi cikin jin kunya don dayasan Alhaji na wajen babu ma abinda zaisashi yi don yanajin kunyarshi sosai "kayi shiru?" "Alhaji bafa wani iyawa nayi ba" "wani ba iyawa kayi ba? wai kajika kuwa? gaskiya zan kwadaitamaka jaraba waqar muji don gaskiya inaji ajikina voice dinka zai mayar dakai wani, idan kanada ra'ayi kayimin magana zan tsayamaka insha allah, ai waqa ma babbar sana'a ce kuma baiwace babba, kayi tunani Akai" da to kawai Deen ya amsa badan yadauki maganar serious ba cemashi yayi yakai motar gida shi yanzu wani wurin zashi sannan yashige motar yawuce tun Deen na daukar maganar Alhaji wasa harya ga dagaske fa yakeyi don kodayaushe cikin yimashi maganar Alhajin yake tun yana zillewa beso haryaji shima sha'awar gwadawa din inda a gwajin farko ya burge mutane dayawa ahankali ahankali da taimakon Alhaji dakuma qarfafa gwiwarshi Deen yacigaba da waqar inda ahankali waqoqinshi suka fara samun kar6uwa acikin al'umma kan kace me? cikin ikon allah cikin qanqanin lokaci Deen yayi fice yakuma yi suna acikin mawaqan zamani sosai Alhaji yayi farinciki da hakan yakuma ginamashi studio inda zai dinga gudanar da harkar waqarshi sosai waqar ta kar6eshi don cikin qanqanin lokaci yayi suna yana kuma samu sosai acikinta wanda hakan yajawo chanjin rayuwa agaresu har suka mallaki gidan kansu ahaka ya nemi Habeeb abokinshi qwallin qwal yamaidoshi wajenshi yazama manager dinshi inda suke gudanar da harkar waqar tare ahankali Deen ya chanza daga poor timid guy zuwa rich handsome guy wanda harda kyawunshi ke qara mashi farinjinin jama'a yakuma zama abinda yazama yanzu....✍? Ummin fasihu🧚🏻‍♀? 8/5/21, 8:17 AM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *095* "duk abinda nazama na zama hakan ne ta dalilinki Zainab, am sorry for going away just like that, nayi danasanin tafiya nabarki, nayi danasanin rashin tsayawa kai da kafa wa soyayyarmu, natafi nabarki batareda tunanin ya zakiji bayan kingane na gujeki, I should have stay.. I should have tell you komai alokacin qila mu iya shawo kan matsalar atare, saigashi sanadin stupidity dina nayi wata irin rayuwa marar armashi kwata2, I guess that's what I deserve... and the amazing thing is yadda kikayi connecting dina da wadanda kwata2 banma san dasuba duk tsawon rayuwata... namaki sharri kinsakamin da alhairi, be kamata na iya hada idanu dake ba, bansan ta ina zanfara ba, bansan da wadanne kalamai zanyi amfani dasu ba wajen godemiki, all I know is samin masu golden heart irinki a duniyar nan zaiyi matuqar wuya" lumshe idanunta dasuka gaji da zubda hawaye zee tayi tasake budesu ahankali jikinta duk yayi sanyi dajin labarin Deen, he went through alot hakan yasa taji wani irin tausayinshi ya lullu6eta, mutum da gatanshi da family dinshi amma yasha wahalar duniya bata tunanin tunda mussadiq yake yasan wani abu wai aikin qarfi, kallo daya zakamashi kasan cewa shi real ajebo ne, besan komai ba sai hutu, yana nan cikin hutu da jindadi while twin dinshi nacan yanashan wahalar duniya, such is life "Zainab please forgive me, let's forget our past and start afresh.. ina sonki Zainab son da bazan iya misaltawa ba, ada naji kamar na hqra dake jin cewa ke matar wanice amma yanzu bazan iya ba... ki hukuntani takowace hanya amma banda ta hanyar juyamin baya..idan kikayi hakan zan zauce... zan mutu ...please" yaqarashe ahankali yana kallonta in the eye da oily eyes dinshi dake jiqe sanadin hawayen dayayi itama shi take kallo takasa janye idanu akanshi ganin yadda yawani marairaice mata komai nada ne yashiga flowing back a qwalwarta, tunawa tayi da farkon haduwarsu, tunawa tayi da yadda dafarko basa shiri takuma tuna yadda akayi suka shirya sosai memories din ke flooding qwalwarta inda take tuno rayuwar dasukayi a school inda suka zama kamar wasu besties, tunawa tayi da incident dinsu master da yadda yakusan rasa rayuwarshi akanta, tunawa tayi da soyayyarsu, yadda yake treating dinta like a queen, beson 6acin ranta ko kadan, yadda yake nunamata tsantsar so da qauna... "Zainab please give me another chance...kisake bani dama na nunamiki yadda nakesonki a zuciyata, kisake bani dama na nunamiki haryanzu wutar qaunarki na ruruwa a zuciyata, bata ta6a mutuwa ba kuma baxata ta6a mutuwa ba har abada... please kisake bani wata damar" yafada softly but romanticly "Zainab!.." atare suka dago daga Deen har Zainab din suka kalli saitin inda aka aka kirata Aymaan ne suka gani daga dan nesa dasu yana kallonshi shima fuskarshi expressionless "Akhie?" zee tafada ahankali tana tashi tsaye don daman har lokacin a kneeling position suke sai a lokacin tama lura da yadda marece yayi sosai, mammaki yakamata don ita harta manta dama cikin school suke ahankali Aymaan yafara takowa yana kusantosu hakan yasa shima Deen miqewa yana kallonshi batareda wani yanayi yanuna a fuskarshi ba saida ya qaraso gabansu sannan ya dakata idanunshi akan Deen dashima nashi ke kanshi saiya dan sakarmashi guntun murmushi yabashi hannu "aslm alaika" amsar hannun Deen yayi shima yana danyin murmushin da iyakarshi lips "wa'alaika sallam warahmatullah" daga haka kowa yajanye hannunshi Aymaan ya maida kallonshi kan zee "mutafi if you're through" yafada yana kallonta sauke idanunta tayi daga kallonshi saboda wani kwarjini dayaimata batace komai ba tazo tawuce tayi gaba Deen yabita da kallo ahankali ya maida kallonshi kan Aymaan dake kallonshi haryanzu dan murmushi Aymaan yasake yimashi sannan ahankali yace "bansaniba ko awajenku it's proper amma anan kokuma ince a musulunce bedace namiji yatare mace daba muharramarshi ba ahanya harya tsaidata tsawon lokaci haka, the proper way shine zuwa gidansu yanemi izinin magabatanta kafin yayi hakan... fatan za'a gyara" daga haka shima yajuya yabi bayan zee dahar tayi nisa binshi da kallo Deen yayi cikin tafarfasar zuciya idan yace be 6atamashi rai ba yayi qarya, he just appear from nowhere ya 6atamashi moment kuma har yanada gut din fadamashi baqar magana? furzar da huci yayi ahankali yakai hannunshi akan sumarshi yana scratching dinta *** tafiya suke babu mai cewa kowa komai, motar tawani dauki shiru kamar babu kowa ciki Aymaan hankalinshi nakan tuqinshi itakuma idanunta nakan kwalta bata yarda ta janyesu akai ba tafiya yake slowly don kwata2 motar bata gudu don gani zee take qila da aqafa take dasai tafi motar sauri saidai batace komai ba don ko hada ido bata yarda sunyiba don wani iri takeji sosai, jitake kamar ta 6ace daga motar ta huta, hakanan takejin rashin jindadin taddasu dayayi da Deen akuma yanayin daya taddasu, sosai takejin wani iri akan hakan, shi wonder me tunaninshi zaibashi akan hakan jitake taqara su isa gida tafita daga motar saboda yadda takejin kanta amatuqar takure amma saiwani tafiya yake slowly kamar snail ahankali taga ya gangara gefen titi hakan yasata dagowa tana kallon inda suka shiga akaro nafarko tunda suka taho tajuyo ta kalleshi lokacin yana neman wurin parking sake kallon wajen tayi sannan tasake juyowa ta kalleshi daidai shima yajuyo ya kalleta murmushi yasakarmata hakan yasata janye idanunta kanshi Kawai takasa cewa komai "want some ice cream?" yafada ahankali cikin romantic voice dagowa tayi ta kalleshi saikuma tayi saurin kauda kai ganin irin kallon dayake mata namasu jin barci girgiza kai tayi alamun A'a murmushi Kawai yayi bece komai ba ya bude motar yafito ya zagayo ya budemata dagowa tayi ta kalleshi "get down dear" yafada ahankali qara girgiza mashi kai tayi tace "banason ice cream..." "get down kona fiddoki dakaina" ya katseta da hakan tsayawa tayi tana kallonshi kamar da mammaki sai gani tayi ya sunkuyo kamar zai daukota hakan yasata saurin yin baya tana cewa "wait.. zan..zan fito" tafada tana zaro large eyes dinta wani qayattacen murmushi yasaki yaja baya yana cewa "better" ahankali ta sauko tana sissine kai cikin kunya murmushi Kawai yasakeyi yarufe kofar sannan ya nunamata hanya alamun suje babu musu tafara tafiya suka nufi Icecream joint din "which flavour kikeso?" inji Aymaan yana zaro wallet dinshi "vanilla" ta amsa ahankali juyawa yayi kan attendant din yayi mashi bayanin abunda sukeso babu 6ata lokaci akayimusu packaging din Icecream din da snacks acikin yar babba babbar leda aka basu Aymaan ya amsa yabiya sannan suka juya motarsu suka koma suka shiga Aymaan ya tada motar sukabar wajen yanzu ma a slow speed suke tafiya motar tayi shiru ahankali Aymaan ya waigo yadan kalli zee dake wasa da yatsunta ledar siyayyarsu akan cinyarta maida kallonshi yayi kan titi yadanyi murmushi "you still love him right?" ta tsinci muryarshi da fadin hakan dagowa tayi ta kalleshi saikuma ta janyesu dasauri ganin shima yajuyo xai kalleta "hmmm, am sorry na katsemuku moment dinku nasan I shouldnt interrupt you guys, sorry" yafada yana flashing dinta da murmushi girgiza kai zee tayi dasauri tace "ba yadda kayi tunani bane" "koma dai yayane be kamata kidinga ke6ewa da namiji daba muharraminki ba, batool fa saidai takoma gida ita kadai wai ta nemeki bata ganki ba gashi anata kiran wayarki bakya picking... Zainab you're matured enough dazaki banbance daidai da akasinsa, bawai cewa nake karki kulashi ba ko karku ke6e kuyi magana ba but do that in a proper way... Makaranta fa yabiyoki yakuma jaki inda babu mutane, mezamu kira wannan?" zee da tunda yafara magana takejin zuciyarta na bugawa sosai tadago ta kalleshi da idanunta dasuka fara durar ruwa "it's.. it's not what you think" tafada ahankali "waya gayamiki am thinking of something? am thinking of nothing Zainab.. I trust you kuma nasan hakan ba laifinki bane.. abinda Kawai nakeso na fahimtar dake shine try to do things in proper ways ok? ina baki shawara ne amatsayina na dan uwanki kuma yaya agareki, wannan dadewar dakikayi da dawowar da batool tayi babu ke bakisan iya tashin hankalin dazai iya jefamu aciki ba.. mu family dinki ne... we care about every slight thing about you... aduk abinda zakiyi kifara sa family dinki agaba kafin wani abin... shawara ce amma" ya qarashe da murmushi a fuskarshi saidai deepdown shikadai yasan abinda yakeji ganinsu dayayi tareda Deen ba qaramin dokarmashi zuciya yayi ba kuma haryanzu zuciyarshi bata bar hucin zafi ba Kawai daurewa yake yana iyakar qoqarinshi wajen controlling kanshi zee da jikinta yayi sanyi sosai da magangganunshi ta sauke idanunta qasa ahankali "am sorry" tafada ahankali murmushi yasakeyi "don't be, Kawai dai ki kiyaye" "insha allah" ta amsa asanyaye murmushi yasakeyi "now fiddo Icecream dinki kisha kar yayi melting" "zansha idan muka isa gida" "no kisha yanzu, idan ba hakan ba zan maki wata fassarar" kallonshi tayi, kamar zatayi magana saikuma tafasa ta bude ledar ta fiddo daya daga cikin robobin Icecream din ta bude tasa dan spoon din ta diba takai baki saita dago idanunta suka hada ido murmushi yayi mata itama tadan maida mashi tana sauke idanun qasa babu wanda yaqara magana acikinsu harsuka qarasa gida parking yayi a parking space sannan suka fito atare atare suka shiga cikin gidan zee agaba Aymaan abaya murda handle din kofar tayi tashiga da sallama hannunta riqeda da ledar snacks din ummie da batool dake falon suka dago suna amsa sallamar qarasowa zee tayi cikin falon tana dan murmushi azuciyarta tana tunanin mezata gayawa ummie idan tace ina ta tsaya "A'a? harkun dawo? kungama practical din" inji ummie tana kallon zee "p..practical?" "eh sungama.. koda najema gab da zasu gamane don ko 10mins banyiba dazuwa suka fito" inji Aymaan dashima yashigo dakin kallon Aymaan tayi suka hada ido ya kauda kai "ayyah, sannu" inji ummie tana maida hankalinta kan t.v tana cigaba da kallon program din datake kallo "bari nahau sama" inji Aymaan yana wucewa zee tabishi da kallo qasa qasa "inyee meye wannan din?" taji muryar batool data taso tadawo kusada ita nacewa hakan tana fizge ledar hannunta hade rai zee tayi tfara qoqarin amsa hakan yasa batool miqewa tayi hanyar sama miqewa itama tayi tabita tana saita bata ledarta murmushi Kawai ummie tayi tana girgiza kai tacigaba da kallonta asama kau bayan sungama guje2nsu suka zube agado kowa na maida numfashi batool ce tajuyo tana kallon zee dake kallon sama har lokacin tana maida numfashi "ina kika tsaya ne zee? babu inda ban nemeki ba amma banganki ba kuma inata kiran numberki bakya picking" juyowa itama zee tayi tana kallonta shiru tadanyi sannan tace "wane practical,ummie ke magana akai?" harara batool ta gallamata "na tambayeki kina amsamin tambaya da tambaya?" ajiyar zuciya zee tayi tamaida kallonta sama tace "ina tareda Deen ne" "Deen?" batool tafada cikin mammaki "yes" "kamar yaya kuna tareda Deen? doing what? yaushe ma kika fara saurararshi?" inji batool tana kallonta sosai qara sauke wata ajiyar zuciyar tayi sannan tace "yau... yau na tsaya na saurareshi, he told me everything" tafada batareda tabar kallon sama dakin ba "what did he told you?" "labarin da tsayi" zee ta amsa "to amma yafada.miki dalilin tafiyarshi?" "yes... kaka tasa suka gudu saboda gudun kar asirinta yatonu cewar batada wata alaqa da Deen, taji ajikinta sirrinta zai bayyana shiyasa ta yanke wannan hukuncin shikuma Deen bayada option dole yabita saboda tayi threaten zata tafi ita kadai lokacin dayaso kawomata gardama, shikuma baya iya rabuwa daita kasancewar itace komai nashi, ita kadai,yabude ido yagani a duniya amatsayin danginshi shiyasa yabita suka gudun" shiru batool tayi tunda tafara maganar harta kai aya "that makes sense amma duk wayonta gashi sirrin ya bayyana, waya gayamata anama allah wayau?" inji batool ajiyar zuciya zee tasake saukewa sannan ahankali tace "kuma... kuma wai ashe yadawo 3weeks bayan tafiyarshi, can you imagine wai daddy saiya cemashi nayi aure yakuma yimishi koran kare? banta6a tunanin daddy zaiyi haka ba" "daddyn yayi hakan?" inji batool cikin mammaki "yes.. nima nayi mammaki sosai, meyasa daddy zaiyi hakan? koda yayi hakan ne don yarama ai bekamata yace nayi aure ba, tunda harya dawo dakanshi ai yakamata ya tsaya ya saurareshi idan ma hukunci zai yanke mashi saiya yanke mashi wanda bekai wannan tsauri ba don wannan ba Deen kadai yayimawa ba harda ni, 3weeks da tafiyarshi lokacin ina cikin halin desperation, imagine da lokacin yasanar dani dawowarshi da bansha duk wahalar danasha ba" ajiyar zuciya batool ta sauke "gaskiya kamar daddy be kyauta ba amma saidai bamusan dalilin dayasa yayi hakan ba.. anyway komai yawuce ai gashi yadawo kamar ba'ayi ba" lumshe ido Kawai zee tayi batace komai ba "yanzu wane matsayi yake agareki" bude idanu tayi tajuyo tadan kalleta "kamar ya?" "ina nufin ya matsayin soyayyarku?" "wai he want another chance" "zaki bashi?" shiru tadanyi saikuma tace "I don't know" shiru yadan ratsa dakin kafin can zee tasake katse shirun da "wane practical ummie ke magana akai dazu?" dan ta6e baki batool tayi tace "well, wannan duk shirin Akhie ne, lokaci daya muka dawo dashi ganin nikadai nadawo babu ke yasashi tambayata nagayamashi komai saiyace to bari yakoma school din yaduboki wai idan nashigo aka tambayeki ince kin tsaya wani practical ne ganin zaki dade yasa kikace intaho zaki kira yaya Aymaan yadawo dake..shikenan saiya juya ko shigowa beyiba yakoma school din" shiru zee dake kallonta tunda tafara magana tayi saikuma ta sauke ajiyar zuciya ta maida idanunta ta lumshe tunani kala kala na kai kawo a kwalwarta *** tsaye yake agaban balcony inda yazama favorite wurinshi yana kallon harabar gidan dake tarr da haske kamar ba dare ba mussadiq ne yashigo wajen waya kare a kunnenshi ya qaraso wurin kujeru yaja guda ya zauna yana cigaba da wayarshi yana kallon bayan Deen saida yagama wayar sannan yadanyi murmushi yana ajiye wayar kan table "eh gaskiya ka afka dayawa..love is suffering someone here" yafada cikin sigar tsokana Deen beko juyoba bare ya tanka mashi "you know what yakamata karage tunani, don taqi sauraronka saika tsangwami kanka haka? dama nasan wannan stubborn girl din bazata saukoba so easily, kabi komai ahankali komai zai warware" juyowa Deen yayi ya 6allamashi harara "karka qara kiranta stubborn" yar dariya mussadiq yayi yace "but she is.. wannan yarinyar? uhmm nikadai nasan halinta" "baka kaini sanin halinta ba Mallam" ta6e baki mussadiq yayi "whatever Kawai dai nidai shawara zanbaka karage saka kanka damuwa don taqi sauraronka" "waya gayamaka taqi saurarona? ta saurareni nakuma gayamata komai" "wow, yaushe?" qarasowa Deen yayi wajenshi shima yazauna kan kujera daya "yau, I told her everything" "wow, sai tace me?" "bata kaiga magana ba wannan gayen yazo?" "who?" "wannan doctor din" yatsine fuska mussadiq yayi saikuma yata6e baki "that annoying fringe" "kabar cemashi hakan" "why? I don't like him from the beginning" "amma yanada kirki" "hmmm koba kirki ba" "seriously mussadiq yakamata kabar gaba dashi saboda mutumin kirki ne, harda shifa wajen taimaka mana mukayi re-uniting ga yadda yakula da ummy lokacin datayi collapsing, the man has a good heart" ta6e baki mussadiq yayi ya cigaba da danne dannenshi Kawai "saidai nalura kamar yanason zee" "fidda kamar, sonta yakeyi kuma shi taqama yake cousin dinta ne shiyasa yake wani jijji dakai yana nuna isa akanta, abinda yafi 6atamin rai gameda shi kenan" inji mussadiq ajiyar zuciya Deen ya sauke yace "koma menene nata zee tawace.. insha allah, insha allah zee matata ce" "allah yasa" "amin ya rabb" "kunyi waya da master din naka?" inji mussadiq "yes.. munyi magana nagayamashi komai though briefly, nasan very soon zasu duro Dubai" "kace nakusan ganin your so called kaka" inji mussadiq yana dan ta6e baki wani kallo deen yayimashi "kardai kafadi wani abu akan kakata" "to mai kaka" mussadiq yafada yana ta6e baki sannan yamaida hankalinshi kan wayar hannunshi shikuma Deen ya jingina da kujera ya harde hannayenshi a qirji yana kallon sararin samaniya....✍? Ummin fasihu🧚🏻‍♀? 8/7/21, 4:46 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *096* *NIGERIA* Sosai Alhaji Shamsu ke mammakin wannan al'amari kiran wayar Deen ba qaramin sashi a rud'ani yayi ba, ga wasu magangganu daya gayamashi masu birkita kwalwa dukda sama sama Deen yabashi labarin kasancewar labarin bana waya bane amma yagane abinda Deen keson gayamashi idan ba kunnuwanshi suka ji ba daidaiba yana nufin yahadu dawasu dayake ikirarin familynshi ne tayaya hakan zaya faru bayan tunfarko yabashi labarinshi inda yacemashi bayada sai kaka kuma shi bahaushe ne, ya kwatsam kuma zaice yahadu dawasu kuma family dinshi ne? kuma bama a qasarnan ba a Dubai? sosai kan Alhajin ya kulle yakasa samun amsoshin tambayoyin daketa kai kawo a kwalwarshi kenan Deen nacikin qoshin lafiya duk kwanakinnan? fadin tashin hankalin dasuka shiga a yan kwanakinnan 6ata bakine don kowa hankalinshi atashe yake dajin su Deen shiru musanmman kaka dahar wata rama tayi saboda tashin hankali da damuwa tunawa yayi da maganar Deen nacewa don allah yasama musu visa sutaho harda kaka Dubai akwai qullallen al'amarin da dole kaka zata iya warwarewa dama kuma Alhajin yayi niyyar zuwa Dubai din duk saboda jinshi shiru da akayi don harya gama komai na tafiyarshi inda zaibi jirgin dazai tashi jibi tattaunawarsu da Deen yasashi fara cuku cukun nema masu kakan visa suma inda tafiyar zata hada dashi da hajiya da kaka sai subar su Lailah da Afrah gidan qanin Alhajin koda labari yaje ga Lailah na tafiyar tasu saita burkuce ta dinga kuka ita don allah aje daita sosai ta tada hankalinta akan hakan don dama bayan kaka babu wanda yakaita shiga damuwar rashin Deen don kusan kodayaushe cikin kuka take duk tayi fayau daita don damuwa izuwa yanzu su mamy duksun gano son Deen take hakan yasa take basu tausayi ganin cewa idan ba'a tafi daita dinba zata qara shiga damuwa yasa Alhajin hadawa daita a tafiyar gashi dama anci sa'a suna cikin hutun Makaranta nan da nan Alhajin yayi cuku cukun tafiyarsu inda adaren ranar tafiyar yagama settling komai inda Washegari zasubi jirgin qarfe goman safe mai zuwa Dubai ranar ko barcin kirki kaka kasayi tayi, dukda Alhajin be gayamata sunyi magana da Deen ba don ita gani take Alhajin ya yarda ne sutafi nemanshi tare don tunfarko dama tanace zata bishi Alhajin ne be yarda ba haka takusan kwanan zaune zuciyarta fall addu'ar bayyanar Deen, danasanin barinshi wannan tafiyar kau tayishi yafi cikin kwando Washegari tunda safe suka fara shirye shiryen tafiya don jirgin nasu dawuri zai tashi qarfe tara tayimasu cikin airport inda cikin qanqanin lokaci suka gama settling komai qarfe goma nayi dota jirginsu ya lula sararin samaniya yadauki hanyar dubai *** ahankali Aymaan ke jujjuya dan qaramin puzzle box din hannunshi yana arranging din puzzle din, daya kumayi arranging dinsu sai yayi scattering dinsu saikuma yasake arranging dinsu dagowa Ahmad yayi karo na ba adadi ya kalleshi saikuma yadan girgiza kai "Aymaan" dan dakatar da abinda yakeyi yayi batareda ya dago ya kalleshi ba kuma bece komai ba gyara zama Ahmad yayi yana kallonshi sosai "Aymaan wai meke damunka ne kwanannan? yaushe muka fara 6oyewa juna damuwar juna? Aymaan you're not ok these days kuma you don't want to share your problem with anyone, aganinka barin damuwa aranka shine mafita?" yafada yana kallon Aymaan daya cigaba da jujjuya abin hannunshi kamar badashi yake ba ganin beda niyyar amsa mashi kuma baxai amsa mashin ba yasa ya yunkura yaqwace puzzle box din daga hannunshi yana cewa "am talking to you idiot!" komawa jikin cushion din Kawai Aymaan yayi ya lumshe ido yana sauke nannauyan numfashi "Aymaan... listen Aymaan barin kashi aciki baya maganin yunwa, kana cikin damuwa why not kayi sharing dinta dani? ko babu komai zakaji sauqi na kayi sharing din damuwarka dawani kuma ina iya samamana shawara dazata taimaka, ba haka muke dakai ba kaima kasani we're like brothers muna sharing damuwarmu mukuma zauna mu samama kanmu mafita atare, banajin dadin ganinka a wannan yanayin kwata2" yafada cikin kwantar da murya yana kallon Aymaan da har lokacin idanunshi ke a lumshe "Ka gayamin damuwarka please, I can help" "you can't help" Aymaan yafada ahankali still idanunshi a lumshe "meyasa? just tell me, we can't say" inji Ahmad sai a lokacin Aymaan yabude idanunshi wadanda suka kada sosai ya kalli Ahmad "you can't Ahmad, baxaka iya taimakamin ahalin danake ciki ba, I... am broken" yaqarashe cikin raunin murya ganin hakan yasa Ahmad saurin dawowa kusadashi yana kama hannunshi daya "meyasa nafara son abinda tunfarko ba nawa bane? why? meyasa nafara son wacce bazata ta6a mayarmin da so ba? why?" "Aymaan..." "kasan ciwon dake tattare dason wanda baya sonka kuma baxai ta6a sonka ba? kasan zafin dake tattare da ganin wanda kakeso yana son wani? ni haka tawa qaddarar so zatazomin? ada soyayya stuffs duk shirme na daukesu ina ganin Kawai rashin aikin yine amma jibeni yanzu.. crying over love while wacce nakeyi domin ta ma batasan inayi ba, what did i do to deserve this Ahmad? meye narasa na d'a namiji da xaisa bazata soni ba nima? meye Deen yafini? me Deen yafini dashi? meyasa ko sau dayane bazata waiwayeni ba? at least tanuna tasan inayi, tanuna tasan dani, what did I do to deserve all these pain?" sosai hankalin Ahmad yatashi ganin yadda Aymaan ke hawaye sosai, kana kallonshi zakasan he's really in pain "Aymaan please... kabar kukan nan haba kamar ba namiji ba" "tears are not sign of weakness, but of courage. hiding your emotions is self destructive and will never allow you to heal... haka Zainab ta ta6a gayamin kuma yanzu nagane hakan, babu abinda kecikin maganarta sai gaskiya, my heart is hurting ahmad, it's hurting terribly" yafada wasu hawayen nasake saukomashi Ahmad da jikinshi yayi sanyi sosai yajawo Aymaan jikinshi cikin sigar rarrashi yana cewa "Aymaan ba kome mutum keso yake zama alhairi agareshi, wani abin kanasonshi amma ba alhairi bane agareka shiyasa allah ke hanaka, allah shine mafi sanin daidai kuma ya tsara komai na rayuwarmu da dadewa, kayi hqr Aymaan kadage da addu'a, idan zee ce mafi alhairi agareka allah ya karkato da hankalinta kanka idan ba ita bace allah yaxa6a maka mafi alhairi, ka daina ganin laifin Deen ko zee, kadage da addu'a Kawai, wani baya ta6a auran matar wani" haka Ahmad yayita kwantarma Aymaan hankali da kalaman rarrashi harsaida Aymaan yaji sassaucin zugin da zuciyarshi kemashi *** A babban filin jirgin garin Abu dhabi jirginsu yasauka inda cikin qanqanin lokaci pasinjojin jirgin suka shiga saukowa daga jirgin can na hango su Alhaji Shamsu cikin masu saukowa tareda su kaka suna saukowa suma cikin qanqanin lokaci suka sauko sukayi clearing komai suka amshi kayansu dukda damuwar dasuke ciki hakan be hanasu ganin haduwar qasar ba wacce tahada jinsin mutane qabilu daban daban ahankali suke takawa suna nufar hanyar barin airport din dake dauke da mutane sosai sai kai komo suke kaka sai bin mutane masu wucewa take da kallo kamar don ganin ko zataga mai fuskar Deen, duk tawani yi yaushi kamar ba itama fitowa sukayi daga entrance din airport din inda adaidai lokacin idanun Lailah suka sauka akanshi still tayi da numfashinta tana sake wara ido tana kallonshi sannan tasake kyafkyafta idanunta cikin son gasgata abinda tagani hannun kaka dake gefenta ta damqe cikin sauri tana cewa "gashi can kaka, ga yaya balaraben can kalla kigani!" tafada da qarfi tana nuna Deen din dake tsaye jikin budaddiyar kofar motarshi yana kallonsu tacikin baqin shade din idanunshi bata tsaya bi takan kaka data sandare atsaye ba tayi wurinshi aguje tana kwala kiran sunanshi cikin kuka tana zuwa batayi wata wata ba tafada jikinshi tana kuka sosai qamewa yayi a tsayen dayake don ita kanta Lailah saida taji sanda ya dauke numfashi don be ta6a expecting hakan ba, hakan yasa itama saurin dawowa hayyacinta ta sakeshi tana dan ja baya "y..yaya, am sorry amma nakasa yarda kaine" tafada muryarta nadan rawa saikuma tajuya ta kalli su Abba dake can tsaye basu qaraso ba sannan tajuyo ta kalli Deen dahar lokacin beyi motsi ba "yaya kalli kaka.. ga kaka can, tareda ita mukazo.. kullum saitayi kuka saboda rashinka zoka gani" tafada tana jan hannunshi suka qarasa gabansu kaka Deen nabinta kamar sakarai "kaka ga yaya! kingani ko dama nace yana lafiya" tafada cikin tsananin murna batama lura da tashin hankalin dake fuskokinsu Abba ba "kaka..." taji anfada ahankali cikin raunin murya juyawa Lailah tayi ta kalli Deen din kusada ita don tabbas muryarshi taji amma kamar ba daga kusada ita ba gashi Deen din akusada ita yake kallon Deen din da Kamar bashi yayi maganar ba tayi kafin tace komai taji ansake cewa "kakata" still tayi jin muryar abayanta gakuma Deen agabanta da baiko motsa bakinshi ba wara idanu tayi gabanta na faduwa hakan yasa mussadiq dake gabanta dan sakin murmushinnan nashi nagefen baki yana kallonta tacikin glass din idanunshi saurin juyawa tayi daidai lokacin da Deen na ainahin ya rungume kaka dake tsaye kamar an dasata yana qara kiran sunanta yanajin wani irin kewarta na tasomashi daga qasan zuciya kamar sunyi shekaru basu hadu ba sosai Lailah ta girgiza ganin Deen biyu agabanta, bama ita kadai ba kowama na wajen saida ya girgiza don ko Alhajin Deen be gayamashi batun twin dinshi ba hakan yasa duk sukayi still kamar wanda aka dasa suna binsu da kallo inshock sunma kasa magana Habeeb dake tareda su Deen murmushi Kawai yakeyi don yasan za'a rina, that's the same shock he recieve lokacin dayaga Deen da mussadiq at the same time "kaka nayi kewarki.. nayi kewarki kakata" inji Deen yana cupping fuskar kaka data qurawa mussadiq din bayan Deen idanubabu kyaftawa "ky..kyakyawana.. k..kalli bayanka, nashiga uku.. kalli bayanka" tafada cikin rawar murya tana riqe hannayen Deen dake fuskarta gamm idanunta har lokacin akan mussadiq juyawa deen yayi yakalli mussadiq saikuma yajuyo ya kalli kaka yana murmushi "eh nagani kaka" "w...wani ne mai kama dakai" tafada har lokacin muryarta na rawa "eh kaka dan uwana ne" yafada ahankali yana murmushi "d..dan uwanka?" "kaka muje gida muzauna saina fadamaku komai.. karki damu kinji?" itadai batace komai ba sai riqe hannunshi datayi gamm tana kallon mussadiq kamar a tsorace, jikinta sai rawa rawa.yake sai a lokacin yajuya kansu Abba da Habeeb ke gefensu yanata murmushi ya tsugunna yana gaidasu suka amsa suna kallonshi saikuma su kalli mussadiq wanda hakan yasa shima mussadiq qarasowa ya cire glass din idanunshi yana yimasu sallama duk amsawa sukayi dakyar suna kallonshi don dukkansu arude suke they can't understand what's going on ganin dai haryanzu kamar suna cikin shock yasa Deen yimasu iso zuwa mota wanda girmanta yasa zata iya kwashesu tsaf duk wucewa sukayi wurin motar Habeeb na budemasu duk suka shiga "Lailah come and get in" inji Deen ganin taqi motsawa a inda take saida ta kalli Deen sannan ta kalli mussadiq daya daga gira daya yana mata wani kallon qasa qasa hakan yasata saurin kauda kai tawuce tanajin kamar zata harde kafaffu duk shishiga sukayi cikin motar inda mussadiq yashiga mazaunin driver yatada suka fice daga wajen ------ A gidansu mussadiq suka taka sauka tunda akafara tafiyar babu mai magana acikinsu kowa tunanin dake zuciyarshi ya isheshi jin motar ta tsaya ankuma bubbude kofofi yasa suka fara yunkurawa suna saukowa kowannensu sake wara idanu yayi yana kallon kantamemen gidan da aka kawosu sai bin koina da kallo suke cikin mammaki kansu na dad'a kullewa "Abba bismillah mushiga daga ciki" inji Deen da farinciki yakasa 6oyuwa a fuskarshi, he was just extra happy na ganin kaka ayau, jiyake kamar ya goyata don murna, he can't wait ya gwadama kaka umminshi datake yawan gayamashi tarasu kasancewar daidai entrance motar takawosu yasa basusha wahalar fallo hanya don ba laifi ko daga parking space akwai tafiya kafin azo entrance bisa jagorancin Deen da fuskarshi ke washe kamar gonar auduga suka shiga entrance din yabude masu kofar yashiga yana musu iso sudai binshi Kawai suke babu mai iya magana saboda yadda kansu yayi mugun qullewa wani katafaren qayattacen falo suka tsinci kansu aciki wanda tunda suke basu ta6a ganin mai irin haduwarshi ba daga can cikin falon suka hango wata mata fara qall mai mugun kama dasu Deen tayi shigarta cikin shigar larabawa daya qara fiddo kwarjininta da haiba "ummie! ummie! gasu Abba! ga kakata!" inji Deen cikin dan larabcin dayake ji yana jayeda hannun kaka da tunda taga ummie jikinta yadau rawa sosai ummie datun shigowarsu tamiqe ta karaso gabansu cikin murna da fara'a tana masu lale marhabin cikin harshen larabci Aysha kuma na wucewa wurin kaka da Deen ke riqeda hannunta har lokacin tana kallonta fuskarta fall murmushi iso ummie keta yimasutana cewa su zazzauna inda dakyar mutanen suka iya yin yadda tace don banda kallonta babu abinda sukeyi kamar sunsamu t.v kan kace me? maids sunfara kai kawo inda cikin qanqanin lokaci aka cikamasu gaba da abubbuwa iri iri babu wanda ya iya ta6a komai aciki dukkansu sai kallon ummie da Aysha daketa qara yimasu marhabin suke kansu na qara mugun kullewa Gaisawa suka farayi inda duk cikinsu Abba ne mai dan tauri taurin dayake amsawa lafiya lau, hajiya kaka kau jikinta banda rawa babu abinda yakeyi nan ummie take tambayarsu sunzo lafiya? duk suka amsa cikin qarfin halil banda kak da ha lokacin bata dawo nutsuwarta ba Aysha ummie ta kalla tace taje ta gwadama su mamy da kaka masaukinsu su huta sai tawuce da Lailah dakinta shikuma Deen yakaisu Abba suma masauki haka kau akayi, Deen yawuce dasu Abba Aysha tawuce dasu mamy da har lokacin zuciyarsu cinkushe take da tambayoyi kala kala adakin da Deen yakai Abba Abba yahau fadan wai duk meke faruwa ne, yazai kawosu wuri without any explanation yasa sukoma kamar wasu sakarkaru ganin kamar Abba yadan hau yasa Deen yashiga bashi haquri yana cewa ai zaiyi musu bayani "waye wancan matar balarabe? kaga yadda.kuke kama kuwa?" murmushi Deen yayi "Abba ummie na ce" "umminka? ba cewa kayi umminka da abbanka basa raye ba?" "nima haka nayi tunani amma a wannan tafiyar allah ya bayyana minsu, allah ya hadani da ainahin family dina" cikin mammaki sosai Abba yace "yanzu dagaske wannan ce ta haifeka? but how come? ya akayi kaka tace bakada iyaye? wacece kaka?" "wannan amsar kaka ce Kawai zata iya badata, itace Kawai zata warware mana komai" "hasbunallahu wani'imal waqeel, allah mai iko, wannan fa me kama dakai din?" murmushi Deen yayi "he's my twin brother" "you're a twin?" inji Abba cikin tsantsar mammaki murmushi Deen yayi yana kadamashi kai sosai Alhaji Shamsu yaita mammakin wannan al'amari inda abin yaqara kullemashi kai, miliyoyin tambayoyine ke kai kawo akanshi amma shima yasan babu mai bada amsarsu sai kaka ahaka Deen yafita yakoma bangaren da aka sauke su kaka inda yaje ya tadda kaka nata kuka kamar ranta zai fita su mamy suna zagayeta suna rarrashi amma taqi shiru cikin tashin hankali Deen ya qarasa wajensu yana tambayar kaka lafiya ganin Deen yasa kaka tashi tafada jikin Deen da qarfi ta rungumeshi qaqam kamar za'a kwacemata shi tacigaba da kuka sosai sosai Deen yarude jin irin kukan datakeyi hakan yasa yahau rarrashinta shima kamar zaiyi kukan "ka gafarceni Kamal, ka gafarceni" tafada cikin kuka sosai "kaka don allah kibar wannan kukan, don allah kibari" "dole nayi kuka Deen dolene nayi, na rabaka da kowa naka na tsawon shekaru, naita guje guje duk don kar arabamu dakai ashe dai zamu rabu din, nayimaka qaryar komai ma, nasa kayi tunanin bakada kowa gashi duk dubarata da wayau na yau sirrina ya tonu, Ka gafarceni Deen don allah" "kaka don allah kiyi shiru kibar fadin haka, ni haryanzu kece komai tawa kuma babu mai rabamu insha allah" "wlh nasan rabamu zasuyi Kamal, shikenan baxan qara ganinka ba, shikenan narasa Ka dama kai kadai nake gani naji dadi, kai kadai nake iya kira nawa, shikenan banida kowa kuma" haka kaka tadinga kuka tana surutai wanda dole tabaka tausayi gashi taqi sakin Deen don gani take rabasu za'ayi kowa na dakin saida jikinshi yayi sanyi Aysha kau dabatasan me suke cewa ba saboda hausar dasuke sai kallonsu take tana hawaye don sosai tsohuwar tabata tausayi dakyar Deen yasamu ya rarrashi kaka har tadan kwantar da hankalinta inda yasa Aysha ta hadamasu ruwan wanka sudanyi freshen up dakyar kaka tabar Deen yafita daga dakin mamy na cigaba da kwantar ma kaka hankali *RANAR WANKA....* Zaune suke a babban falon kowa idanunshi akan kaka dake hawaye har lokacin qarewa yan falon kallo nayi naga hardasu mummy da daddy da ummy da abbu agefe daya kuma babban Ahmad da ummanshi duk zazzaune akan kujerun falon aqasa kan carpet kuma zee ce Zaune jikin qafaffun ummy sai batool akusada ita sai Aysha sai Lailah adayan bangaren kuma Deen ne kusada kafar kaka dake kan kujera itama sai mussadiq kusadashi sai Habeeb sai Ahmad daga qarshe kuma Aymaan kowannensu kansu aqasa suna sauraron kaka da dakyar ta iya bude bakinta tafara magana....✍? Ummin fasihu🧚🏻‍♀? 8/10/21, 8:09 AM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *097* *WAIWAYE* "Asalin sunana Asma'u Mamman, ni marainiyace banida uwa banida uba don agidan marayu natashi na tsinci kaina a garin komasi dake qasar ghana. Acikin gidan marayu natashi kamar sauran yan uwana marayu damuke rayuwa a cikin gidan baza'a kira rayuwarmu da ingantacciyar rayuwa ba don gaskiya bama samun kulawa yadda ya kamata, abinci ma kanshi bama samun ingantacce saidai kame2 ga rashin ilimi daga na bokon har na arabi bama samu (gwara gwara na arabin tunda munsan wasu abubbuwan kamar yadda akeyin sallah da yan gajerun surori) ga rashin suturun kirki gidan marayun kasancewar anyi yawa sosai aciki yasa babu kulawa sosai gashi da dan tallafin da gomnati ke badawa duk wata aka dogara saidai idan allah ya taimakemu yajefo mana taimako daga ire iren mutane masu sadaka dasuke tunawa da yara marayu irinmu zama gidan marayunmu zama ne marar dadi don kowa burinshi allah ya rabashi da gidan ko ta hanyar adoption (daukar yara don rainonsu) kokuma aikatau don har taya wadanda xasu bar gidan murna mukeyi munaji dama mu Haka nataso nima kamar sauran yaran babu ilimin arabi ba na boko sai qwarewa a iya aikace aikace da rainon yara don yawanci marayun dasuka tasa suke komawa masu kula da qanannu qanannun cikinsu haka muka tashi cikin wata irin rayuwa marar alqibla, kullum a aiki da raino muke qarewa bamu fita daga gidan ko nan da wajen gidan, duk wanda kaga ta fita to ko ansamu masu daukarta ne ko tasamu aikin aikatau kokuma tayi aure don babu laifi akwai masu zuwa neman aurenmu agidan wani lokacin kuma marayu yan uwanmu maza ke auranmu haka natashi agidan kullum inama kaina fatan fita daga gidan watarana nima nasamu ingantacciyar rayuwa koyaya ne rayuwa awajen gidan na matuqar bani sha'awa musanmman idan ina ganin mutanen dakan shigo gidan marayun namu don daukarmu sai inji sunbani sha'awa ina kuma qara jin kwadayin son fita daga gidan inason jin yadda wajen yake saboda kwadayin son fita daga gidan yasa duk lokacin da akazo dauka har addu'a nake aza6eni nima, bandamu ba ko aikatau xanje inyi burina Kawai nafita daga gidan duk lokacin da akazo akayi dauka ba'a daukeni ba kwana nakeyi kuka bama ni kadai ba harda wasu acikinmu saboda yadda zaman gidan ya ishemu, burinmu Kawai mufita aganinmu rayuwarmu awaje saitafi tacikin gidan inganci ahaka harna girma naxama budurwa, ina shekara 20 wani mutum yazo neman aure na agidan da gudun tsiya na amince dashi batareda duba yanayin shekarunshi ba don babbane sosai don a haife ya haifeni gashi yanada mata biyu da 'ya'ya kusan goma sha ban damu da duk wannan ba alokacin na amince nan da nan aka daura aurenmu bayan anyi dan bincike dasukeyi na sanin mazaunin mutum da sana'arshi inda aka gano sana'arshi qera tukane na qasa da tulu dadai sauran kayan qerawa na qasa bayan daurin aurenmu aka damqani ahannun mijina daga ni sai yan kayana sai dan ihsani da manyan gidan suka hadamin wanda betaka kara ya karya ba nabi mijina bakina har kunne don tsabar murna muka bar gidan da tun haihuwata banta6a fitowa ba abin hawa muka hau dani da mijina har gidanshi wanda yakasance na qasa ne duk ya tsufa ya zaizaye gidan zagaye yake da yar gajeriyar katanga ta qasa inda idan kashiga ciki saika fara cinkaro da wani washeshen fili mai girma sosai inda daga nesa xaga hangi yan qanannu qanannun dakunnan dake gidan dakuna hudu ne gidan masu yan qanannun taga (window) daga can sama daki nafarko na maigidan ne sai biyu na kowanne matarshi daya kuma na yara inda na qarshen wanda da alamu saida akayimashi kwaskwarima saboda qamshin sabon shafen qasan dayakeyi nawane ni amarya babu kitchen gidan don a tsakar filin gidan suke girki sai makewayi dake daga can qarshen gidan. ahaka nashiga gidan ina kalle kalle inda yarane sosai tsakar gidan duk yan kuya kuya kusan duk kai daya kowa na,binmu da na mujiya, daga tagar dakunnan matan gidan kuma ina iya hango kawunnan mutane ana leqomu ahaka muka shiga dakina wanda yasha gyara ga tabarmi anbaza takoina sai dan tulu dake daga can kusurwar dakin ataqaice nan yazama dakina kuma ranar nazama cikkakiyar mace ta hanyar raya sunnar aure da mukayi da mijina da farko farkon zamana gidan komai na tafiya min lafiya lau don sosai.mijina kesona don yamafi fifitani akan kingin matan baya yarda inyi wahala don ko girkin gidan da sai andora qatuwar tukunya baya bari nayi kullum abinci na shi ke kawomin wanda duk yawanci kayan dadi ne hakan yaqara sani jindadin auren don ina samun kulawa sosai fiyeda wanda nake samu agidan marayunmu hakan yasa kan kace me nayi 6ul 6ul naqara kyau haka naita rayuwa mai dadi agidan mijina inda nalura kamar mijina bayason kingin matanshi saboda yadda baya shiga harkansu don becika shiga dakunnansu ba kuma maganar arziqi bata hadasu kullum sai fada ga yaranshi suma banga yana wani kula dasuba don suma rayuwarsu suke kara zube ina mammakin abubbuwan dake faruwa agidan dakuma yadda yake watsar da sauran iyalenshi saidai ganin ni bayamin haka yasa Kawai nashare na cigaba da more rayuwata acikin wata na hudu dayin aurenmu nasamu ciki inda sai anan nagane waye ainahin mijina tun lokacin dayaji batun cikina ya chanzamin kwata2 inda yafara tsiromin da wulaqanci iri iri inda tun bangane dalilin hakan ba harna gane ashe haihuwace bayaso lokacin nasha wahala sosai saboda cikin yazomin irin mai shegen laulayinnan ne gashi mijina yajuyamin baya abinci kanshi yabar bani sai alokacin nagane ashe matan gidan suke ciyar da kansu ma gashi matan gidan dama duk haushina sukeji saboda yadda mijinmu ke nuna kulawa agareni abaya hakan yasa alokacin babu mai tausayamin saima allah qara dasuke yimin da qannanun habaice habaice ahaka naita kashe yan kudadden hannuna a lokacin inasamu inci abinci don ko shekara zanyi banci abinci ba babu wanda zai damu da hakan agidan haka naita wahala ga laulayi ga rashin kula har na qulla wata biyu sai alokacin na yanke shawarar fara sana'a ganin idan nazauna hakanan yunwa zata kasheni ne abanza gashi duk na cinye yan kudaddena ahaka nafara aikin wankau dukda yadda banida lafiya haka nake daurewa nayi wanki don samun abinda zansaka aciki ahaka har cikina yayi wata biyar inda lokacin muka wayi gari mukaga ana tada daki daya a gidan cikin qanqanin lokaci aka gama ginin yaji shafen qasa kamar nawa inda sai anan nakejin labarin ashe aure zaiyi naji baqinciki sosai a lokacin don sai a lokacin nakejin ashe mutum ne shi daya saba da aure2 cikin sati biyu aka daura aurenshi dawata ta tare inda itama yakoma yimata duk abubbuwa na kyautata dayake yimin abaya ahaka naita rainon cikina nikadai yau fari gobe baqi inda har lokacin babu wani jituwa atsakaninmu da matan gidan don kowaharkar gabanta takeyi, kowa kanshi yasani da 'yayanshi ahaka naita rainon cikina da tun kafin na haifeshi allah ya dasamin qaunarshi sosai a zuciyata don koyaya nake cikin baqinciki na dan cikina ya motsa sainaji sauqi sauqi, kullum burina na haifeshi lafiya nima inga wanda zan kira nawa cikina na shiga wata takwas mijinmu ya6ata da amaryarshi kasancewar itama ta dauki ciki wulaqanci yafara mata itama kala kala hardamu ma yana cewa bamu iya komai ba sai haihuwa ahaka ya watsar daita itama tafara dandana abinda muke dandanawa ana hakan watarana yashigo dakina daya rabu dazuwa don har saida nayi mammakin ganinshi don rabonda yashigo dakina tun ina amarya ashe shigowar ma bata alhairi bace don yana shigowa babu cass bare ass ya sakeni saki irinna jahilci wato uku gabadaya yakuma ce na tattara nafitarmashi agida aure zai qara sosai naji ciwon abin sosai don abin nashi babu ko tausayawa, ga tsohon ciki ga saki sakin ma na wulaqanci ahaka nabaro gidan bayan kwana biyu saboda budemin wutar dayayi na nabarmashi gidanshi sanin babu inda zani don babu wanda nasani yasa ban zarce koina ba sai gidan marayunmu koda naje nafadama manyan wajen yadda komai yafaru sai Kawai suka bani hqr don dama sunsaba irin wannan case din don yawanci ana sako wadanda sukai aure sukuma dawo gidan marayun su cigaba da rayuwa haka nakoma cikin gidan da rayuwa har lokacin da allah ya saukeni na haihu lafiya inda na haifi d'a namiji saidai ko kwana beyiba yakoma sosai naji rashin d'ana don na kwallafa rai akanshi sosai kuma inasonshi sosai tunma kafin na haifeshi hakan yasa har ciwo saida na kwanta kafin daga baya na hqr na cigaba da rayuwata dukda har lokacin d'ana na maqale a zuciyata haka na cigaba da rayuwa a gidan har tsawon shekaru takwas inda ana tara nasamu wata tazo daukar yan aikatau aka hada dani matar munsanta sosai don tana yawan zuwa dibar yara agidan inda take rarrabawa aikatau kamar dai wata dillaliyace ta masu kudi mai kaimasu yan aiki kasancewar angaji dani a gidan yasa aka hada dani dukda na girma don lokacin shekaruna talatin aka samu akatafi dani don dama yawanci abinda yasa suke badamu aikatau don susamu sauqin yawanmu ne don bawani iya riqemu sukeyi ba nima dai naji dadin daukata da akayi agidan don nima nagaji da zaman gidan ahaka aka tafi damu inda aka rarrabamu wa masu kudi inda ni dawasu guda biyar ne za'a tura saudiya aikatau don matar har qasashe take tutturawa mutane yan aiki sosai naji dadi jin zanbar qasar gabadaya naje qasar da kullum nake burin ganinta koda a mafarki ne hakan yasa naita doqin tafiyar don har hangoni nakeyi acan ina shiga da fita da cud'anya cikin larabawa cikin qanqanin lokaci akayimana shirye shiryen tafiyar inda mukabi jirgin ruwa (6arauniyar hanya) har muka samu muka shiga qasar tunda nake ban ta6a ganin haddaden waje mai kyawun gaske irin na qasar. haka aka tafi damu munata zuba qauyanci har muka isa masaukinmu anan muka kwana Washegari kuma aka rarrabamu a gidajen dazamuyi aiki ni gidan wani attajiri aka kaini don kai koda ganin gidan kasan gidan masu dashi ne saboda haduwa, anan aka hadamu nida wadansu da suma aka kawo aikatau da matar gidan mai tsananin wulaqanci kwata2 mutan gidan basa qaunar baqar fata don afili suke nuna qyamarmu ahaka aka rarrabawa kowa aikinshi dakuma fadamana kudin albashinmu rayuwa agidan amatsayin yar aiki rayuwace ta wahala da qasqanci don kwata2 basa qaunarmu kamar ma ba kallon mutane suke mana ba don kuskure kadan idan kayi saika yabawa aya zaqinta ahaka muke wannan qasqanttaciyar rayuwar wanda saida na gwammaci zamana a qasarmu akanta don abin nasu ba iya kyama da hantara ya tsaya ba, abin haryakai harda cin mutuncinmu na 'ya mace inda mazajensu keyimana kallon dabbobin dazasu iya zuwa sujuye qazanttaciyar buqatarsu akai suyi tafiyarsu hakan dana gani yasa hankalina tashi ainun don abin abin tashin hankaline inda nan take nafara danasanin zuwana qasar haka naita lalla6awa kullum cikin roqon allah ya kareni daga sharrin mutanen don naga yadda sukeyima kingin yan uwana masu aiki inda suke maidasu kamar karuwansu idan kuma baki yarda ba a laqamaki wani sharrin da za'ayi miki hukuncin dazakiji inama tunfarko kin yarda da buqatunsu (hakan nafaruwa a real wlh, mutane yan Africa masu zuwa wasu qasashen don aikatau dadai sauransu ba qaramin tashin hankali suke fuskanta ba acan saboda tsananin qabilanci da ake nunawa acan inda yawanci ake maidasu sex machine don yawanci sunfison Africans don acewarsu sunfi satisfying dinsu, allah ya kyauta) ahaka nayi wata uku agidan ina kaff kaff dakaina ina addu'ar allah ya ku6utar dani saidai ba'a dauki lokaci ba wani d'an gidan yafara kawomun hari sosai hankalina yatashi da ganin hakan, hakan yasa naita kakaucemashi ina addu'ar allah ya ku6utar dani daga sharrinshi alokacin sosai zaman qasar ya gundureni don da nasan yadda za'ayi nagudu danayi gashi wacce takawomu tun ranar data kawomu bansake sata a idoba ahaka har watarana saurayin yaso raping dina lokacin babu kowa gidan don saida yayi yan dabarunshi na yadda zaisameni yaci karenshi babu babbaka ranar naga tashin hankali don da tsiya yaso afkamin saidai allah yabani ikon makeshi da vase din tangarau mai nauyi akai inda nan take ya silale yasume jini nabin kanshi ganin hakan yasa na rude don nasan shikenan tawa,ta qare don muddin akadawo aka taddamu haka shikenan nagama shaqar numfashi hakan yasani fitowa agigice don ni duk tunanina mutuwa yayi, cikin sa'a kau ban tadda mai gadi a gate ba hakan yasa na afka waje nafara gudu irin gudun fanfalaki burina Kawai intsira da rayuwata haka naita gudu shiga nan fita can batareda nasan inda na nufaba, kuka kau tun inayi harna kasa saboda muryata databar fita ahaka dare yayimin nasamu qarqashin wata gada na ra6a saboda yan kame dake kame da daddare na raku6e ina kyarmar sanyi ina addu'ar allah ya kawomin dauki ahaka har dare yayi sosai koina yadauki shiru, motoci nawucewa jefi jefi asaman gadar dana 6uya ahaka tun ban iya barci saboda sanyi da cizon sauro har wani barci marar dadi ya figeni can cikin barci naji motsi sama2 abinka da dama atsorace nake sainayi firgigit na tashi ina zare idanu ganin yadda hasken fitilu keta walainiya awajen yasani qara la6ewa ajikin bangon gadar ina toshe bakina don duk tunanina mutanen gidan danake aiki suka biyoni suna nemana kokuma yan kame daga saman gadar suke haskowa da fitilarsu mai mugun haske kamar masu neman wani abu nidai qamewa nayi wuri guda inata hawaye ina kyarma bayan kusan minti daya da haske hasken naji qarar abu tsindum sunjefo cikin ruwan gadar dake gudana yana tafiya atsorace nasake maqalewa ajikin bangon gadar ina qara toshe baki don atunanina su suka duro ciki can sainaga nabar ganin hasken can kuma naji tashin mota tasaman gadar aka tafi dukda antafi hakan besa na iya komawa barcin ba haka naita zaxzare ido cikin duhu ina kyarma saboda sanyin da akeyi gashi ina qarqashin gada ahaka har haske hasken alfijir yafara ketowa inda anan na yanke shawarar barin wajen don nagaji da cizon da,sauro keyimin hakan yasa na lalla6a ina qoqarin fita daga gadar kamar ance in kalli gabana saina hangi wani box mai dan girma daga nesa da inda nake kasancewar akwai tazara,da inda nake yasa nakasa hango ko menene sosai harzan wuce saina tuna da mutanen dasuka zo jiya suka jefo abu acikin gadar hakan yasa naji inason ganin koma menene ahankali nake bin gefe gefen gadar ina tattaka dutsinan ciki gudun karna afka cikin ruwan ahaka harna iso wurin kwalin daya jiqe jagab shima don dutsi ya tokareshi ne da,tuni yabi ruwa tsayawa nayi ina kallon kwalin cikin dan hasken safiya daya farayi ina saqe saqe zuciyata nabani qila sharace aciki suka jefar saidai kuma dukda hakan sainaji inason budewa inga me keciki ahankali nasa hannuna dake kyarma kyarmar sanyin danake ji nabude kwalin inda ganin abinda yake ciki yasa numfashina daukewa cakk na wucin gadi wani farin yaro nagani aciki hannayenshi da qafaffunshi a quqqule da igiyoyi bakinshi toshe da tsumma an daureshi tamau idanunshi alumshe babu alamun numfashi ko kadan attatare dashi....✍? *manage banida charge, qila gobe inyi* Ummin fasihu🧚🏻‍♀? 8/11/21, 2:03 AM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *cigaban 097* ja baya nayi amugun tsorace don ban ta6a tsanmmanin abinda zan gani kenan nan take jikina yahau rawa nafara yin baya baya hannu toshe da baki atsorace najuya nabar wajen dagudu ina bi ta duwatsun cikin ruwan harna samu na koma hanyar danabi nashigo qarqashin gadar nasamu nafita daga saman gadar na tsaya ina kallon kwalin danake hange daga nesa har lokacin zuciyata banda bugawa babu abinda takeyi sonike intafi amma kuma nakasa sai kallon kwalin nake batareda na iya motsawa daga inda nakeba kamar wanda aka jawo saina tsinci kaina da komawa cikin gadar kuma ina tafiya ahankali nasake nufar kwalin jiki na rawa nasake leqawa naga abinda nagani daxu yaro ne da bazai wuce shekaru uku ba, farine dukda ba irin tass dinnan ba na larabawa don nashi irin farin nanne mai jajaja, gashin kanshi ajiqe kamar yadda sauran jikinshi yake ya kwanto yarufe rabin fuskarshi nafi minti biyu atsaye ina kallonshi zuciyata na bugawa kafin cikin qarfin hali dasa hannu nadan ta6ashi ko motsawa beyiba hakan yasa naqara ta6ashi duk atsorace ganin be motsa ba yasa cikin qarfin halin na hau kekketa kwalin har ya ida fitowa fili sannan najuyoshi nasa hannu ina qunce mugun daurin da akayima bakinshi saida nasha wahala sannan na kwance na zazzaro tsummunan da aka cuccusamashi cikin baki ina kuka sosai don an daure mashi bakinne cikeda mugunta ga bakin da kumatunshi sunyi jajur alamun kwanciyar jini bayan nagama kunce bakin nakoma kan hannayenshi da qafaffunshi dake daddaure nahau quncewa, suma saida nashi wahala sosai kafin na samu kuncewa saikuma narasa abinda zanyi mashi daganan gashi gari yawaye don haske yayi sosai ganin hakan yasa nafara qoqarin daukarshi saidai yayimin nauyi sosai hakan yasa nadan kwantar dashi kan dutsin wajen nahau daddana mashi cikinshi daya dan yo sama akau saigashi ruwa sunshiga fitowa ta hanci ta baki, haka naita dannawa har suka daina fitowa saidai har lokacin ko motsawa beyiba hakan yasa na cije na cicci6eshi dukda lokacin yadan rage nauyi nasamu dakyar nadorashi abaya na don har inayi ina faduwa sannan nashiga takowa ahankali don barin cikin gadar dashi koda nafito rasa inda nanufa nayi gashi har lokacin ina tsoron kar ace yan gidan danake aiki nacan na nemana gashi nasan shima wannan yaron wadanda suka jefashi a gada sunyi hakan ne don son ganin bayanshi hakan na nufin daga ni har shi muna cikin hadari hakan yasa maimakon nayi titi nashiga cikin mutane saina yanki daji kawai batareda nasan inda muka nufaba burina Kawai na tseratar da rayuwarmu dukda har lokacin banida tabbacin ba gawace goye abaya na ba ahaka harna samu nayi nisa sosai harsaida naji ban iya tafiya sannan na haqura muka zube awajen ina sauke numfarfashi dagowa nayi ina kallon yaron wanda farat daya yashiga zuciyata ina jinshi fiyeda nakejin d'ana dana haifa yakoma bansan ko yana rayeba ko ya mutu don kwata2 baya motsi kuma natara yatsuna a hancinshi nidai banji yana numfashi ba kunnena nasa a saitin zuciyarshi ina sauraro ko zanji bugun zuciyarshi saidai shima shiru saida na dade ina sauraro sannan naji bugun zuciyar can qasa qasa sosai nayi murnar hakan don dafarko harna fara sadaqarwa dacewar yamutu tashi nayi ina kallonshi batareda nasan wani taimakon dazanyi mashi ba, nasan asibiti yakamata na nema na kaishi amma zuciyata taqi bani hadin kai don gani nake kaishi asibitin daidai yake da jefashi cikin hadarin daya fito don qilan hakan yazamo silar dazaisa mutanen dasuka so ganin bayanshi dafarko susake dawowa haka mukaita zama awurin cikin rashin sanin abinyi ga yunwa ga sanyi don daga ni har shi kayanmu ajiqe suke haka mukaita zama har rana tafara fitowa inda anan nasamu nacire mashi jiqaqiyar rigarshi ko yadanji sauqin sanyin haka natusashi gaba nabuga uban tagumi ina kallonshi batareda nasan abinda zanyi ba ahaka har rana ta take sosai ganin hakan yasa nasake miqewa na daukeshi nasake goyashi nacigaba da tafiya acikin dajin ranar naci baqar wahala don haka nawuni ina tafiya babu ci gwara gwara ruwa idan nahadu da matattarar ruwa ina dan kwalfa in jiqa maqoshina ahaka harna qarasa wani qauye qauye anan qarfina yaqare bansan ya akayi ba kawai sainaji lumm idanuna na rufewa dakansu kaina na juyamin nazube awajen dani da d'an dake bayana bansan iya adadin lokacin dana dauka ba asume saidai Kawai nafarka naganni cikin wani daki mai dan duhu duhu firgigit nayi na miqe zaune ina waige waige anan nagane kamar ma cikin bukka nike agarin waige waigena na hangi wannan yaron shima kwance daga dayan gefen dakin bansan sadda naqarasa wurin ba da rarrafe nayi saurin tattaroshi ajikina na rungume ga mammaki na sainaji yayi motsi yana yatsuna fuska saboda motsashi danayi saikuma yafara tari ahankali cikin wata iriyar dakussashiyar murya dabata fita sosai farinciki ne ya lullu6eni ganin ya motsa hakan yasani sake rungumeshi ina jin wani irin sonshi har qasan zuciyata sai kallon kyakyawar fuskarshi nakeyi babu ko kyaftawa kamar nasamu madubi ahaka wasu mutane suka shigo bukkar jin motsinsu yasani dawowa daga duniyar kallon yaron naja dabaya atsorace ina binsu da kallo kamar yadda suma sukemin suma larabawa ne saidai dagani yan qauye ne duba da yanayinsu mace ce da namiji duk sun manyanta sun tsaya daga bakin kofa sun zubamana idanu nima dai kallonsu nake amma atsorace sai qara rungume yaron jikina nakeyi qamm a qirjina yadda kasan za'a kwaceminshi kallon juna naga sunyi sunyi murmushi sannan suka qaraso ciki suna kallon yadda nake qara jabaya ina mannewa da jikin bukkar ganin yadda na tsorata yasa suka bar nufomu inda anan matar cikin murmushi don kwantar min da hankali tafara cemin na kwantar da hankalina babu abinda zasuyimin cikin larabci dukda banajin larabcin sosai amma nagane abinda take nufi saboda gwadawar datakeyi da hannu hakan yasa hankalina dan kwantawa miqomin hannu tayi akan nabata d'an nikuma saina qara matseshi jikina ina jada baya alamun ban badawa, murmushi sukayi sai mutumin cikin harshen larabci yake tambayata d'ana ne? dan zaman danayi agidan danake aiki yasani dan sanin wasu guntayen larabci hakan yasa nagane abinda yace min hakan yasa na kada kaina cikin sauri murmushi suka sakeyi nan suka hau nunamin baxasu cutar damuba taimaka mana zasuyi dakyar dai suka samu suka lalla6ani na yarda dasu nabasu shi suka mayar dashi shinfidarshi suka kwantar dashi inda anan naga sun cigaba dayimashi wani hayaqi wanda yaita sashi tari da shaqaqiyar muryarshi nidai ina gefe ina kallonsu harsuka gama yimashi duk maganin dasuke mashi suka kyaleshi yanata barcinshi abinci suka bani wanda kamar jira nake na amsa hannu narawa nashiga ci saboda tsananin yunwar da dama nakeji saida naci na qoshi sannan nadawo nutsuwata inda anan sukaso sanin wacece ni mekuma yakawomu qauyensu dayake duk bajin yaren juna muke ba yasa maganar kurame (demonstration) duk tafi yawa a maganarmu inda anan nake kwantantamasu cewa gudowa mukayi za'a kamamu mu ba yan qasar bane nakuma nuna masu sonike mubar qasar shiru sukayi suna kallona hakan yasa gabana cigaba da faduwa don duk a tunanina sungano yaron ba nawa bane don shi farine nikuma gaskiya baqa ce dukda ba irin qirin dinnan ba amma dai kwata2 bamuyi kama da yaron ba kuma gashi shi sak balarabe dukda jikinshi ba irin farinnan tass ba yake kamar na jikin kajin turawa amma farine irin mai jajaja wanda anasamun daidaikun masu irin fatar a Africa tambayata sukayi wacce qasa nake nace Ghana a Africa sai suka sake tambayata ina uban yaron cikin qwarin gwiwa nabasu amsar yamutu nima nan aikatau yakawoni saboda tsananin rayuwa saina tsinci kaina da gayamasu duk abinda yafaru a tsohon gidan danake aiki da silar gudowata, abu daya ne ban gayamasu ba shine yaron tsintarshi nayi sundade suna jujjuya maganata kamar dai basu yarda dani ba don saidai su kalli yaron su kalleni can sukace karna damu zasu taimaka min nakoma qasarmu can Africa amma sai yaron ya farfado tukunna yasamu lafiya ba haka nasoba amma babu yadda na iya haka na haqura ina addu'ar allah yarufamin asiri mubar qasar lafiya saida muka kwana uku agidan kafin yaron ya farka kuma abin mammaki yana farkawa yafara waige waige yana kiran ummie cikin muryar dabata fita munayin ido hudu dashi ya rarrafo wajena dasauri ya maqalqaleni sosai na sauke ajiyar zuciya ganin yadda yaron yayi don da yaqi yarda dani da qila mutanen sun zargeni duk yadda mutanen sukaso ta6ashi qiyawa yayi ya lafe ajikina yayi lamo kamar dagaske ni mamarshi ce ahaka muka qara kwanaki biyu inda na matsa ni sonike nakoma qasarmu don har lokacin hankalina be kwanta da zamanmu qasar ba izuwa lokacin sungama gamsuwa cewa d'ana ne saboda yadda yake liqemin kodayaushe yana maqale dani duk yadda sukaso muqara zama ko don jikinshi dabe ida warwarewa ba qiyawa nayi nace idan naje can zankaishi ayimashi magani ahaka suka haqura ranarda muka cika sati daya awurinsu namijin ya rakamu mukayi tafiya sosai bisa raqumma har mukazo wani qauye shima anan ya hadamu dawani wanda aikinsu fitarda mutanen qasar ta 6arauniyar hanya anan yabarmu bayan yadan bamu dan guzurin tafiya nikau naita godiya kamar zan ari baki anan aka hadamu da wasu mutanen dasuma qasar za'a fita dasu rabi da kwatansu duk yan Africa ne inda aka lodamu awani qaton jirgin ruwa cikin dare muka daga daren ranar ko rintsawa banyiba ina qanqame da KAMALDEEN kamar yadda nasamashi suna hankalina be kwanta ba saida naga mun qetare iyakar saudiya sai lokacin naji sanyi sanyi araina alokacin nakuma lura duk yawanci mutanen cikin jirgin yan Nigeria ne sannaniyar qasarnan datayi suna duk fadin Africa dama duniya bakidaya hakan yasa nima jin hankalina karkata acan ataqaice dai saida mukayi kwana uku muna tafiya sannan muka iso Nigeria aka jibgemu garin lagos lokacin jikin Kamal yaqara rikicewa saboda yanayin tafiyar tamu ga sanyin daya bibbigemu hakan yasa muna sauka na dangana da asibiti wanda dakyar dagano ta hanyar kwatance ganin mawuyacin halin dayake ciki yasa aka kar6eshi cikin gaggawa inda anan likitoci suka shiga bashi taimakon nikau nakasa zaune nakasa tsaye saboda yadda jinina ke kan akaifa jinake kamar zan rasashi ahaka likitocin suka fito daya daga ciki yanemi tattaunawa dani inda anan yake sanar dani yaron yakamu ne da ciwon nimonia (Pneumonia) saboda sanyin dayayi mashi mugun kamu (wannan ne Asalin ciwon Deen) sannan ya rubuta min abbubuwan dasuke buqata tareda magungunna koda naje wurin sayen sai akayi min lissafin kudadde masu yawa dukda ga lokacin bansan sunada yawaba don bansan kan kudin Nigeria ba sosai tambaya nayi inda xa'a chanzamin yan kudaddena dana taho dasu daga Nigeria aka nunamin naje na chanzo inda anan na fahimci ko rabin kudin maganin banidasu komawa nayi asibitin wurin likitan nayimashi bayani akan cewa kudaddena kenan ya taimaka ya dubamin shi banida komai bayansu cewa yayi babu abinda zai iya yimin indai ina buqatar lafiyar yarona inje inkawo abubbuwan dasuka buqata haka nasake fita hankalina amatuqar tashe gashi bansan kowaba bare na nufeshi ya taimakamin haka naita yawo inda daga qarshe nayi abinda banta6ayiba wato bara haka naita tare duk wanda nagamu dashi akan ya taimaka min inda qalilan ke saurarona har sudan bani wani abu wasu kau ko kallo ban ishesu ba ahaka nasamu nadan tattara yan kudadden nakoma wajen likitan nazube mashi su da wanda nasamo da wanda dama nake dasu nace yaduba yaga ko sun kai gani nayi yabi kudadden da kallo wanda hakan ya sanyaya jikina saikuma ya sa hannu yafara tattarasu ya hadesu ya kirga yana gama kirgawa yadanyi murmushi yana girgiza kai wanda hakan yaqara sanyaya min gwiwa don da alamu dai basu kai ba nurse yakira yabata wasu kudin banda nawa da takardar maganin yace taje tasiyo sannan yaturomin kudaddena yace na ajiye Kawai godiya naita yimashi harda kukana don da be taimaka min ba bansan inda zankuma je insamu taimako ba ahaka nurse din tadawo da abubbuwan daya aiketa saye nan da nan yatashi yafita yakoma inda aka kwantar da kyakyawana.." dan shiru tayi ta dago tana kallon mutanen dakin daduk suka maidata t.v, daidaiku ne babu hawaye a idanunsu kowa idanunshi yayi jajir jikinsu duk yayi sanyi kamar wadanda akayima shegen duka kallon Deen tayi da fuskarshi tayi jajir idanunshi sunyi jajir sungaji da zubda hawaye sai kallon kaka yake kamar yau yafara ganinta ahankali takamo hannunshi tariqe tareda matsewa anata tana dan murmushi sannan tacigaba dacewa "ataqaice dai saida muka kusan sati asibitin inda likitan duk ya daukemana komai nakula da lafiyar shi sai abinci Kawai nake siye da yan kudadden hannuna acikin wannan yan kwanakin Kamal yasamu sauki sosai ya warware inda wata shaquwa tashiga tsakaninmu, yadda yake liqemin sai kayi tunanin dama can yasanni ko mun hada wani abu dashi kuma ba haka yakema kowaba don nalura yanada qiwuya don ko likitan baya yarda dashi amma ni yadda kasan uwarshi. ahaka har aka bamu sallama inda likitan yaita gayamin abubbuwan daxan kiyaye saboda gudun tashin ciwonshi sannan yabamu kingin magungunnanshi yayimana fatan alhairi. sosai nagodewa mutumin da bazan ta6a mantawa da alhairinshi ba, ahaka nafito dashi abayana don nalura yanada bala'in son jiki gashi dama yanzu yake samun sauqi bazanso yayi tafiya ya wahala ba ahaka muka fito batareda munsan inda muka dosaba ga garin babu ruwan kowa da kowa, kowa harkar gabanshi yake karnaja xancen da tsayi, iya wahala mun wahala don saida mukayi kwana uku batareda masauki ba inda darana muke yawo ina dan yimana barar abinda zamuci idan dare yayi muzo tasha mukwana. sosai nagaji da barar danake don bara wata iriyar qasqanttaciyar sana'a ce wanda batada dadi kwata2, na gwammaci aikin wahala abiyani da yinta gashi kuma banaso na cigaba ahaka har kyakyawana yatashi ahaka shima don sosai naci buri akanshi naji inason koyaya ne yasamu rayuwa ingantacciya ahaka nafara neman abinyi inda daga baya nasamu aiki acikin tashar wajen wata bayerabiya mai saida abinci, dafarko wanke wanke nakemata da share share tana bani abinci safe da rana kafin daga baya yazamana har girkin nake tayata inda anan nadan koyamata wasu abincicikanmu na ghana wadanda suka samu kar6uwa sosai awajen customominta hakan yasa bayan abinci tafara biyana kudi wadanda nake adanasu don burina lokacin insamu inkama mana ko daki dayane mubar kwana tasha don kwata2 banason kwana tashar damukeyi don yawanci yan iska sunfi yawa aciki haka zasu kwana suna shaye shaye da bushe bushensu da kayan hayaqi nikuma banison kyakyawana yatashi cikin irin wannan environment din ahaka nasamu dakyar dahada kudin kama daki daya na rabin shekara muka koma can inda daganan muke zuwa aikin kullum nida kyakyawana wanda ke maqale dani duk inda nayi baya yarda da kowa saini sosai kyakyawana keda shiga ran mutane don mutane dayawa sunsanshi suna kuma sonshi don mutane sunsha bashi kyautar abubbuwa don yana matuqar burgesu saboda kyawunshi (kunsan yare dason kyawawa) ataqaice dai saida mukafi shekara agarin kafin na tattara muka bar garin muka koma garin minna inda anan nasa kyakyawana Makarantar primary da islamiya nikuma nakama sana'a ina kula damu nabaro lagos ne badon komai ba saidon dama ni garin beyimin ba, banaso kyakyawana yatashi acikinta bare yatashi da al'adunsu don sai ahankali hakan yasa ina tara isassun kudadden danaga zai ishemu natattaro muka barota sosai na jajirce akan ilimin kyakyawana, komai dazanyi duk saboda shi ne, nayi sana'o'i kala2 wadanda nikaina bansan iyakarsu ba nidai burina na inganta rayuwar kyakyawana wanda shikadai nake iya kira nawa kuma shikadai nake kallo inji dadi ataqaice dai munyi zaman garruruwa daban2 nayi sana'o'i daban daban dik don riqe kaina da kyakyawana wanda nake mashi kallon duniyata ina qaunar Kamal qaunar dabaxan iya misaltawa ba don da ata6amin shi gwara ni ata6ani sau dubu Kamal yataso yaro mai matuqar sanyi da rashin hayaniya, bayada hayaniya kwata2 ga tsantsar biyayya ga nagaba, gashi allah yabashi kwalwar daukar karatu don tun yana primary yake ciwo kyaututuka na hazaqar karatu both islamiya da boko hakan yake qara qarfafamin gwiwa wajen qara zagewa don tallafawa karatunshi shaquwar dake tsakanina da Kamal bata misaltuwa, nice komai nashi kamar yadda shine komai nawa, Kamal yakasance yarone mai tsananin tausayawa da jin qai, bayada qiwuya ko kadan don duk yawancin sana'o'i na tare dashi mukeyi yana matuqar taimakamin sosai ahaka harya girma yagama primary yakuma yi saukarshi tafarko inda alokacin ne muka sake tattarawa muka bar garin muka koma Katsina lokacin yanada shekaru goma sha biyu zan iya cewa duk tafiye tafiyanmu da zama garurruwan damukayi babu wanda naji dadinshi kamar na Katsina cikin ikon allah na tsayar da sana'a datayi matuqar amsata na saida Koko da qosai inda da ita muka samu muka,cigaba da rufama kanmu asiri anan nasamoma kyakyawana Makarantar secondary ta gomnati ya cigaba da zuwa inda anan ma yayi fice saboda hazaqarshi ahaka harya kammala yakuma fito da sakamako mai kyau inada burin kyakyawana yayi karatu mai zurfi kodan inganta rayuwarshi gashi nalura shima yanason karatun sosai hakan yasa naji inason ya cigaba da Makarantar gaba da secondary kasancewar babu kudin shiga Makarantar alokacin hakan,yasashi zaman gidan shekara daya inda anan maqocinmu wanda yazama kamar dan uwanmu yasama mashi wani shagon kafinta ya dinga zuwa, acikin shekara guda din nayita tari don babu laifi inasamu sosai da sana'ar nan,tawa ta Koko da qosai gashi Kamal shima yana dan samo wani abu andcan shagon nasu ahaka muka hada mukaita tarawa har shekara tazagayo muka samu yashiga Makarantar gaba da secondary din wanda dik shine burinmu zan iya cewa nafishi farinciki da fara zuwa Makarantar dayayi don harwani alfahari nakeji araina idan na kalleshi naga wannan yaron nawane rainonane. Deen yarone mai,matuqar sanyi hakan yasa wasu ke amfani da sanyinshi wajen cutardashi hakan yasa yake matuqar bani tausayi kuma nake tsayamashi tsayin daka bana kyale duk wanda ya ta6amin shi, kowama yasan irin yadda nakeji dashi kuma banison komai ya ta6ashi shiyasa ake shakkar yimashi wani abin don akanshi banajin nauyi ko kunyar kowa haka muka cigaba da rayuwa har zuwa lokacin da Zainab tashigo rayuwar Kamal..." cigaba tayi dabada labarin yadda akayi case din incident dinsu master inda anan tafara saninsu Zainab da yadda Deen ya kwanta asibiti harwani da zumuncin dasukayi da ahalin Zainab bayan lokacin saita gangaro kan soyayyarsu dakuma yadda soyayyar tasu bata kwanta mata ba tunfarko saboda dama tunfarko tahangomasu matsala a soyayyar nan ta gangaro kan yadda su daddy sukazo dashi da abokinshi Alhaji Abubakar(baban asaad) sukazo suka nuna rashin son dangantakar dake tsakanin Deen da zee dakuma cewa tajamashi kunne yafita harkar yarsu harzuwa lokacin dasuka dawo kuma dakansu daga baya suka bada haquri akan abinda sukayi suka kuma yarda da soyayyarsu wanda itama dole ta amince saboda yadda talura Deen nason zee din saikuma tagangaro zuwa maganar data tadamata hankali na batun Introduction dinsu wanda dafarko bata tashi hankalinta ba sai lokacin da wannan abokin daddyn yazo gidan shikadai lokacin Deen bayanan yana Makaranta yafadamata batun Introduction din yana kuma cewa dangin Deen suke buqatar gani najini don gaskiya bazasu wani yarda da bayada kowa ba sai ita don ba'a ta6a yin hakaba tunda ita kakarshi ce dole dai ace yanada dangi bayan ita babu yadda za'ace ita kadai ce danginshi saidai idan akwai wata qullaliya don haka su bazasu lamunci rainin wayau ba don bincike zasuyi na sosai da sosai bazasu aurama diyarsu marar asaliba tofa abinda yatashi hankalin kaka kenan alokacin komai ya dagulemata taga kamarma sunsan babu abinda tahada da Deen hankalinta yatashi sosai don saitaga kamarma sosuke su rabata da Deen din gabadaya hakan yasa alokacin ta tashi hankalinta ta burkuce ma Deen akan dole subar garin don saitaji garinma yaficemata akai gabadaya hakan shine dalilin barin garin nasu har suka koma Abuja nanma tabada labarin irin rayuwar tsukun dasuka shiga a Abujan kafin allah ya dafamasu suka hadu da Alhaji Shamsu wanda ta silarshi Deen yazama abinda yazama yanzu, ahaka harta gangaro kan wannan tafiyar dayayi dakuma yadda ranta be kwanta da tafiyar ba don jitayi ajikinta kamar zata rasashi ne ashe kaddarace ta kirashi.. kaddarar haduwa da ainahin ahalinshi...✍? *insha allah page 100 littafin zai qare, so start saying byebye to DEEN👐🏻* Ummin fasihu🧚🏻‍♀? 8/19/21, 6:39 PM - Buhainat😝: ahaka suke firar inda jefi jefi zee da Lailah kesamusu baki Aysha da batool nema masu surutun sallama sukaji anyimusu daga bayansu hakan ya katsesu daga firarsu duk suka dago suna amsawa "barka" yafada cikin murmushi suma martanin murmushin suka maida mashi suna amsawa banda zee da tunda tadago suka hada ido ta kauda kai "please kudan bani aronta for a few minutes..please" yafada yana nuna zee kallon juna batool da Aysha sukayi sukayi murmushi "oh.. sure" inji batool sai takama hannun Lailah tana cewa "kinga mukoma daga can sis" suka wuce sukabar daga zee sai Deen awajen qarasowa Deen yayi ya tsaya yana fuskantar zee dahar lokacin bata qara kallonshi ba harde hannayenshi yayi a qirji yana kallonta fuskarshi dauke da murmushi jin shirun yafara yawa yasa zee dagowa sai taganshi a yadda yake yawani kafeta da ido hade fuska tadanyi taqara kauda face ahankali cikin muryar rad'a taji yace "angry bird" dagowa tayi ta kalleshi dan budamata idanu yayi yace "yes, my cute angry bird" harararshi tayi Kawai tafara qoqarin ra6ashi tawuce "you know what?" ya dakatar daita da hakan tsayawa tayi batareda tajuyoba "banta6a ganin hallita mai kwatankwacin kyawunki ba aduk duniyar nan" qarasowa yayi gabanta yana kallonta "tell me.. what did you do to me?" dagowa tasake yi ta gallamashi harara ta kauda kai "zan wuce" tafada ciki ciki kaucewa yayi daga kan hanyar yana dan bowing "as you wish ma'am" kauda kai taqara yi cikin qoqarin 6oye murmushin dake neman su6ucemata tazo tasake ra6ashi tawuce "please kibani digits dinki idan babu damuwa" yafada daidai tawuceshi batareda tajuyo ba ko ta dakata daga tafiyarta tace "akwai damuwa" "ok please ki taimaka ki daga idan nabugo" yasake fada da d'an qarfi don tafara yimashi nisa banza tayi dashi ta cigaba da tafiyarta "i'll take your silent as yes" yaqara yafada yana kallonta dan murmushi Kawai zee tayi tana cigaba da tafiyarta, Deen won't change, her silly timid guy agefe kuma bayan su batool sunbasu wuri suka samu wani wurin suka koma suka tsaya suna fira suna cigaba da jiran fitowarsu abbu Lailah kasa concentrating tayi a firar tasu don hankalinta gabadaya yana gasu Deen data baro, she can't help but feel jealous, wani irin kishi taji tanaji ganin wanda take mugun crushing tsaye da wata duk yadda taso maida hankalinta akan firarsu batool kasawa tayi don banda satar kallon inda suke tsaye babu abinda takeyi ahaka har zee tabaro Deen tadawo wajensu inda hakan yayi daidai da fitowarsu abbu da kingin daga cikin gidan suna fira suna dariya anan hankalinsu yadawo kansu gabadaya wata sabuwar sallamar aka sakeyi tsakanin juna kafin su rakosu har wajen motocinsu zee zata nufi motarsu ummy Aymaan yabude mata kofar tashi motar yana cewa tashiga fuskarshi da murmushi dan maida mashi murmushin tayi taqaraso tashige motar batareda ta yarda tajuya takalli saitin inda takeji ana kallonta ba maida kofar Aymaan yayi yarufe yajuyo zai wuce suka kusan karo da Aysha data gama bankwana da batool data shiga bayan motarshi saurin jabaya Aysha tayi tana cewa "oh..sorry" rolling idanu Aymaan yadanyi yazo zai wuceta ciki ciki yace "clumsy gal" binshi da kallo tayi don tajishi harya zagaya seat dinshi kamar ance yadago sai suka hada ido don har lokacin shi take kallo kamar dama shi take jira yadago ya kalleta saita gallamashi mugun harara tareda murgudamashi baki sannan tajuya tawuce wajensu ummie dake dagama su ummy hannu dan murmushi yayi yana dan girgiza kai Kawai sannan yashige motar shishigewa motocin kowa yayi suka rurrufo sannan suka tada har lokacin ummie bata daina dagamasu hannu ba fuskarta dauke da murmushi shikau Deen yakasa dauke ido akan zee dake cikin motar Aymaan Ahaka motocin suka jera suka bar gidan anan kingin suka juya suka koma ciki dayake dare yayi sosai yasa Kawai su mamy dasu kaka suka wuce masaukinsu shima Alhaji haka inda Lailah zata kwana tareda Aysha duk sukayima juna bankwana suka shishige adaren ranar Lailah kasa barci tayi, jitayi komai ya dagulemata ganin Deen nason wata ba qaramin jagulemata lissafi yayiba hakan yasa ranar banda juye2 babu abinda takeyi don barcin yaqi zuwa a bangaren Aymaan ma haka, zuciyarshi takasa sukuni, yakasa hqr da tunanin zee dukda yanajin qamshi qamshin rabuwa daita, ganin barcin ya gagara yasashi miqewa daga baya yayo alwalla yafara nafilfilu inda daga qarshe yaita addu'ar za6in alhairi yana addu'ar allah ya sassautamashi soyayyar zee a zuciyarshi yakuma bashi haqurin da juriyar rabuwa daita idan batashi bace....✍? *manage🙏🏻* Ummin fasihu🧚🏻‍♀? *🙍🏻? 8/19/21, 6:43 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *099* *SEMI-FINAL* *TWO DAYS LATER* Acikin kwanaki biyunnan sosai su kaka dasu ummie suka zama kamar family zama suke yadda kasan sun dade dasanin juna don sosai zumunci yaqullu atsakaninsu wanda ga dukkan alamu zaiyi qarfi sosai don juma'a mai kyau tundaga laraba ake ganeta kaka tazama kamar wata kakarsu ta gaskiya don yanzu ba iya Deen ba hatta mussadiq da Aysha sunyi wani irin shaquwa da kaka, musanmman ma Aysha don tazama kamar wata kaka's pet kullum tana sashenta fira inda tadage wai tana koyon hausa awajen kaka mussadiq ma babu laifi yana yawan zuwa sashen kaka saidai be faye surutu ba Kawai dai zaije ne yayi zaune yana kallon firarsu da Aysha sannan yasha furar kaka wanda tunda tabashi yafara sha sau daya yaji duk duniya babu abinda yata6a yimashi dadi irin furar hakan yasa kullum yake lalla6owa yazo part din ya zauna baya fita saiyasha furar, itama kaka lura datayi da hakan yasa kodayaushe take tanadarmashi furar don ta lura masoyinta ne sosai abu nabiyu dake kaishi part din kaka kuma Lailah ce, yarinyar da tunda yafara dora idanunshi akanta a airport yakejinshi ba daidai ba haka Kawai yake samun kanshi dason tsareta yaita kallo batareda shima kanshi yasan amfanin kallon ba agareshi, Kawai dai burinshi kullum ya sameta ya kafamata wadannan idanun nashi yana kallo saidai ya lura yarinyar kamar bata magana don dafarko yayi tunanin she's the silent type sai daga baya daya tattara hankalinshi akanta yana studying dinta yagano damuwace ta maidata hakan don akodayaushe haka zaka ganta so moody bata magana saita kama, mostly yafi ganinta tana danne dannen wayarta with unknown expression a fuskarta yau ma kamar kullum part din kaka yashiga sanye yake da kayan gida don bedade da fitowa wanka ba bayan sundawo daga Yawon zagayen companies dinsu dayayi da Deen he's too tired shiyasa suna dawowa yashige toilet yayi freshen up sannan yafito ya shirya cikin qanannun kaya yafita yabar Deen dake jibge a kujera tunda suka dawo waya kare a kunnenshi yana magana qasa qasa sai zabga murmushi yake kamar wanda akewa wani babban albishir direct part din kaka yanufa don alokacin saiyaji babu abinda yakeso kamar furar kaka da sallama yashiga part din inda as usual ya iskesu a qayattacen falon nata daita da Aysha data daddage tana koyon hausa sai mamy daga gefe tana gyara wasu kaya don gobe zasu koma 9ja atare duk suka dago suna amsa sallamarshi ya qaraso cikin falon "sannu.. dai zuwa" Aysha tafada cikin yanayin hausarta data fara koya tana kallon mussadiq fuska washe harara ya gallamata yana zama kusada kaka cikin larabci yace "idan na wanka maki mari ko?" 6ata fuska Aysha tayi tana kallon kaka dariya Kawai kaka tayi tana cewa "kyaleshi kishi yake don kinfara iyawa shi be iyaba" dukda Aysha batasan me tace ba amma tasan rarrashi ne hakan yasa tadan tura baki tana sake komawa gefen kaka tana dan murmushi shima mussadiq murmushin yadanyi sannan yashiga gaidasu kaka da mamy suna amsawa cikin fara'a, kaka sai tsokanarshi takeyi shikau saidai ya sunkuyar dakai yana murmushi don besan me take cewa ba ba jimawa kaka ta tashi ta tafi wurin fridge din dakin tabude taciromashi furarshi data dama donshi tazo ta ajiye mashi nan take fuskarshi ta washe babu ko kunya yaqara jawo furar yabude yafara aikata don shi kanshi har mammakin yadda yakeson furar nan yake, gani yake da za'a bar bashi komai naci acigaba da bashi fura as abinci tsaff zai iya rayuwa yana shanta ita kadai haka yaita shan furarshi yana sauraron su kaka dasuka dasa darasinsu inda mamy ce yar fassara don idan Aysha tayi tambaya da turanci mamy ke fassarawa kaka itakuma saita bata amsa yana cikin sha yafara yawo da idanunshi a falon something is missing, akwai abinda babu a falon _Lailah_ dan dakatar da shan furar yayi yana tunani gobe su Lailah zasu bar Dubai sukoma Nigeria and har lokacin magana bata ta6a hadasu ba saiko gaisuwa sama sama irin hyy hello. ya lura idan yazo waje taganshi saita fara quramashi idanu kamar Maison tantance wani abu, daga bisani kuma saita janye idanunta akanshi baxata qara yarda ta kalleshi ba shima most time yanason yimata magana amma saiya fasa saboda yanayin damuwar dayake hangowa qarara afuskarta hakan yasa saiya zubamata idanu instead yaita kallo kamar t.v saida yasha fin rabi sannan yarufe kingin furar yatashi ya maida a fridge din dagowa kaka tayi ta kalleshi bayan yadawo yazauna tace "harka qoshi?" yanayin yadda tayimashi nuni yasashi gane metace hakan yasashi yin dan murmushi yana kada kai "na'am shukran laki, jazakillah" yafada ahankali murmushi itama kaka tayi sannan tajuya kan Aysha daketa maimaita wata kalmar hausa cikin son riqewa yadan qara zaman yan mintuna sannan yatashi yayi musu sallama yafita, he was wondering ina tashiga don a irin wannan lokacin batada wurin zama sai part din kaka main house din yashiga inda ya tarar babu kowa dama kuma ummie batanan hakan yasashi fita waje haka Kawai zuciyarshi tabashi yaje garden din gidan wanda hakan yasashi nufar wajen hannayenshi zube a aljihu yana takawa ahankali cikin tafiyarshi tundaga nesa ya hangota zaune kan kujera ta kafe waje guda da ido glass cup mai daukeda fresh milk ahannunta tsayawa yayi yana kallonta kamar mai karantar wani abu tattare daita sannan yafara takowa ya nufota saboda zurfin datayi a tunaninta yasa batasan sadda yazo wajen ba sai jitayi an zare glass cup din hannunta adan firgice ta juyo sai taganshi zaune a kujerar dake facing dinta yakai kofin abaki yana sipping ahankali quramashi idanu tayi kamar mai son tantance wani abu kamar yadda tasaba kullum insun hadu can saikuma ta janye idanunta ta maidasu qasa ajiye cup din yayi yana gyara zamanshi yace "yes bashi bane.. ba wanda kike tunani bane, mussadiq ne" yafada da turanci dagowa tayi ta kalleshi "muna kama sosai ko? kamar da saikin dauki mintuna kina kallona kafin ki iya tantance waye agabanki, aganina da dagaske abinda kike tunani hakane da bazaki dauki lokaci kafin ki iya tantancemu ba don a kallo daya zuciyarki zata baki ko waye agabanki" kallon rashin fahimta take mashi don duk takasa gane kan maganarshi "you're confused gal... so confused, you're confusing your brain and mind, yakamata kiyi realizing gaskiya izuwa yanzu" "gaskiya? as in?" inji Lailah tana kallonshi still confused komawa yayi ya jingina da kujerar yana kallonta qasa qasa yace "as in abinda kike tunani bashi bane, abinda kwalwarki ke tunani yasha banban da abinda zuciyarki ke tunani" yanayin yadda tayi da fuska yasashi sanin yasake kullemata kai hakan yasashi yin guntun murmushi yace "you think you love him? No, kisake bincikar zuciyarki" wannan karon kallonshi take sosai "what did you mean?" "I mean you two don't really deserve each other, there's someone who deserve you most, zuciyarki tagane hakan amma haryanzu kwalwarki takasa gane hakan" shiru tayi tana kallonshi nawani lokaci, wai akan me yake magana ne? badai akan Deen ba, idan ma akanshi ne tayaya yasani? shi kanshi Deen din bata tunanin yasan tana sonshi bare ya gayamashi "look, wani lokacin zuciyarmu tafi kwalwarmu saurin gano abu, so goes yours don haryanzu zuciyarki bata iya gane mere presence din wanda kwalwarki take ikirarin kinaso, meyasa akallo daya zuciyarki bazata baki cewa eh shidin ko bashi bane? meyasa saikin dauki lokaci kafin ki iya tantance hakan... because your heart doesnt really beats for him, you're decieving yourself ne Kawai" jitayi ranta ya6aci, who is he dazaiyi judging dinta haka? zuciyarshi ce ko tata? tayaya zai fita sanin abinda takeso? daukar wayarta dake kan table din tayi tafara qoqarin tashi don iya abinda zata iyayi kenan yanzu, tabarmashi wurin don taga alamun abin ma harda rainin wayau d'an murmushi mussadiq yayi yasake jingina da kujerar yana harde hannayenshi a qirjinshi yace "you might be angry but that's it, zuciyarki ba wa Deen take bugawa ba, idan ma tana bugamashi ada yanzu tadaina, da alamu tafiki hangen nesa saboda tuni ta hangomiki wanda yafi cancanta dake" tunda yafara maganar ta tsaya daga qoqarin tafiyar datake tana sauraronshi batareda tajuyo ba tashi shima yayi yatako har kusada ita "stop wasting your time on someone who's not even aware of your feelings maimakon hakan kiba wanda yafi cancanta dake dama, damar wanke dukkanin damuwar dake a zuciyarki.. mai kwadayin ganin murmushinki wanda kuma zai iya komai don dawwamar da murmushin akan fuskarki" daga hakan yazo ya ra6ata yawuce walking in his usual majestical steps binshi da kallo tayi daga inda take tsaye kamar mutum mutumi, takasa koda motsi don komai ya tsaya mata cakk sai magangganunshi dake mata kai komo a kwalwa. part din kaka yakoma inda nan ya tadda dukkan mutanen gidan harda Deen dashima izuwa lokacin ya chanza shiga da ummie da bata dade da dawowa ba fira suke gwanin sha'awa don dama haka sukeyi sutaru dakin kaka suyita fira zama yayi gefen Habeeb yana maida mashi martanin barka dayake mashi nan ya cigaba da sauraron firarsu wanda duk na komawar su Abba Nigeria ne don gobe zasuyi tafiyar tareda su daddy da mummy agogon hannunshi ya kalla sai yadago ya kalli Aysha dake kusada kaka da harshen turanci yace "Aysha anjima bayan isha'i kushirya keda Lailah nakaiku shopping" wara idanu Aysha tayi cikin murna "dagaske Akhie?" harararta yayi "dawasa" dariya mutanen falon sukayi ummie tace "wai nikam tana inane lailan? duk yau banganta ba" kafin kowa yayi magana mussadiq ya amsa da "tana garden" duk kallonshi sukayi harda Deen dake danna wayarshi saida yadago ya kalleshi tashi yayi yafara shirin fita not minding kallon da mutanen falon keyimashi yace "karku sani jira ok?" yafada reffering to Aysha sannan yafita kallon juna mutanen dakin sukayi saikuma sukayi murmushi sannan suka dora da firarsu kowanne da tunanin dake zuciyarshi BAYAN ISHA'I kallonshi yake harya gama shiryawarshi ya feffesa jikinshi da turarrukanshi sannan yajuyo suka hada ido daga gira daya yayi "what?" murmushi Deen yayi "babu komai Kawai am smelling something fishy ne" "to? akan me kenan?" tashi zaune Deen yayi sosai sannan yace "is there something you're hiding to me about Lailah?" wani kallo yayi mashi "as in?" "dazu kace tana garden, ya akayi kasan tana can?" "saboda tare muke acan" yafada yana dan ta6e baki wara idanu Deen yayi cikin murna "as I thought! kenan you two are dating! wow!" harararshi mussadiq yayi "ni nafada maka hakan?" "saika fada? wow amma natayaka murna don Lailah mace ce mai hankali sosai" "ina ruwanka ko mahaukaciya ce? bansan sa ido" yafada yana harararshi riqe baki Deen yayi yace "to? abin yar haka ce" "eh din, ka tsaya kasamu kaji da wancan mai taurin kan taka karka qara shiga sabgata banaso" yafada yana gallamashi hararar wasa nan da nan Deen ya hade fuska jin anta6omashi jewel dinshi "I've warned you times without number karka sake kushemin mata" kallon dage mussadiq yayimashi "da wa yabaka? ji qarfin hali, kama samu tafara kulaka" yafada yana mashi dariyar shaqiyanci "waya cemaka bata kulani? ina ruwanka ma.idan bata kulani? bana hanaka shiga sabgata daita ba?" inji Deen cikin hade girare "bakaso nashiga taka kashiga tawa?" "to karka qara shiga tawa nima babu ruwana da taka" "better" inji mussadiq yana kwama shade dinshi yafita yana dariya kwafa Kawai Deen yayi yakoma ya kwanta jawo wayarshi don dama jira Kawai yake yafita yabashi wuri yasamu yin wayarshi hankali kwance don dama Habeeb na can part din kaka cikin kwana biyunnan yafara samu zee na kulashi sama sama saboda nacin dayake mata kusan kodayaushe saiya kirata ga lots of romantic SMS dake turamata akai akai yanzu ba laifi relationship dinsu yafara farfadowa don abin ba yabo ba fallasa dukda bekai nada ba amma yana hango cewa zasu koma kamar da koma wucenan very soon a bangaren su mussadiq kuwa tare suka fice gidan dashi da Lailah da Aysha Lailah tayi mammakin jin zasu shopping din datayi, dafarko taso qi saida mamy ta tilasta mata sannan tashirya badon tasoba har lokacin kwalwarta a birkice take akan magangganun mussadiq, takasa kaudasu daga kwalwarta sai sake bitarsu take tanason fahimtar every single word dayace koda suka fito ta hangoshi a jikin motar saida gabanta yafadi don sosai yayi wani irin kyau cikin shigarshi ta larabawa sak hakan yasata sauke kanta qasa bata qara yarda ta kalleshi ba saboda yadda zuciyarta ta chanza bugu adalilin ganinshi back seat taso ta zauna amma Aysha tarigata hakan yasata bude front seat badon tasoba tashiga ta zauna ta maido kofar tarufe tunda tashigo daddaden qamshin turarenshi ya ziryarci hancinta wanda ya saukar mata da nutsuwa nan take komawa tayi jikin kujerarta ta lumshe ido ta cigaba da shaqar qamshin nashi, ahaka yaja motar suka bar gidan babban shopping mall yakaisu, dukda yanadasu dayawa hakan besa yaje daya daga cikin nashi ba don shi dama haka yake he hates attention don yasan idan yaje cikin nashi dole a dakatar da siye da siyarwa har saiya gama yatafi hakan yasa ko shopping din takama zaiyi bayayi cikin nashi dukda da wuya ma yafita shopping komai order yake badawa akawomashi har gida shopping sukayi sosai inda dafarko Aysha kadai keyi ganin hakan tayima Lailah dataqi daukar komai magana akan ta dauki abinda takeso mana batajin shopping din don ita dukma atakure take saboda komawa gefen da mussadiq yayi ya rungume hannu yazubamata ido talura mutumin nan ya iya kallo sosai babu ko irin basarwa dinnan don ko juyowa tayi takamashi yana kallonta baya janye ido ahaka tadan tsinci abubbuwa yan kadan ganin hakan yasa mussadiq qarasowa dakanshi yafara za6armata abubbuwan dasukayi mashi sosai mammaki ya kasheta ganin yadda yazage yana zazza6omata kaya yana lodamata a basket dinta hakan yasa tama kasa motsi a inda take Aysha kau dama tana ganin hakan tayi saurin wucewa da nata basket din zuwa wani bangaren tana murmushi kaya yake xa6armata masu mugun kyau kowanne hade da set din handbag da shoes dinsu har mammakin yadda,ya iya za6e take don ko ita albarka saida yagama lodamata iya son ranshi sannan yayi gaba binshi da kallo tayi batareda ta ko motsa ba shikau jin kamar bata biyoshi ba yasashi dakatawa ya juyo hada ido sukayi tayi saurin janye nata "c'mmon let's go" yafada yana kafeta da idanunshi kasa musa mashi tayi hakan yasa tafara takowa batareda ta taho da basket din ba ganin hakan yasashi dawowa ya jawo basket din yafara turawa sukayi bangaren turarruka nan ma cewa yayi ta za6a saita dauki biyu batareda tama tsaya tantancesu ba tajefa cikin basket din hakan yasashi girgiza kai sannan yadawo gaba yafara za6armata yana tilamata su ciki, itadai kasa cewa komai tayi sai kallon bayanshi datake, she was wondering wannan besan zafin kudi bane? don daukar kayan yake yadda kasan ba biya zaiyi ba ataqaice dai haka sukayi shopping din inda duk mussadiq yayimata, saida suka gama tsaff sannan suka wuce wurin cashier yabada a.t.m dinshi suka zare kudinsu daga nan kuma suka nufi Icecream joint inda yasiyo masu snacks da Icecream sannan suka juyo gida koda suka isa gida saida kowa yayi mammakin siyayyar daya yiwa Lailah,don sunyi over hakan yasa kowa qara gasgata tunaninshi akansu Lailah ma ranar kasa janye tunanin fitarsu tayi, kwata2 tunanin gayen yaqi barin kwalwarta don tadade batayi barci ba tanata juyi zuciyarta fall tunanin mussadiq sa6anin na Deen datakeyi kullum. WASHEGARI kasancewar jirgin qarfe shabiyu zasubi yasa suka isa airport din tun 11 da yan mintuna anan suka hade da family din zee ma dasuka rakosu daddy da mummy suma sosai hira ta 6arke atsakaninsu don wuri daya suka zauna suna jiran agama every necessary thing dayakamata kafin lokacin tashin jirgin yayi masu tafiyar acikinsu sune daddy, mummy, Abba, mamy, Habeeb da Lailah kaka kau ba yanzu ba don da ita za'a daga saudiya😜 iya manyan Kawai ke firarsu while su qannanun suna zaune shiru sai exchanging kallo dasuke tsakanin juna zee na zaune kusada Umminsu Aysha don tunda sukaxo ummie tajawota tazaunar daita kusada ita wanda hakan yasa takasa ko dago kai don sosai takejin kunyar ummie a inda take zaunen tana jin hasken idanunshi akanta amma taqi dagowa tana kuma jin yadda wayarta ke beeping kai da kai na shigowar saquna taqi dubawa don tasan ko ba'a fada shine a bangaren mussadiq ma ya tusa diyar mutane da kallo inda itama ta takura sosai da kallon qurillarshi a bangaren batool kau tana gefe suna chatting da Ahmad da baisamu zuwa rakiyar ba saboda wata tafiyar dayayi tun shekaran jiya, shagala datayi da chatting din taqi bin Aysha data tashi zataje siyen ruwa mai sanyi saboda qishin datakeji Aysha kadai tatafi tasiyo ruwanta bayan ta fadawasu ummie saida tagama siyayyarta tajuyo zata taho sukaci karo dawani gorar ruwan ta sun6ule tafadi "oh.. sorry" mutumin dasukayi karon yace yana sunkuyawa ya daukomata ruwan nata yatashi yana miqamata ganin Aymaan ne yasata dan buda ido saikuma tasa hannu ta kwace gorar adan masife tana harararshi "kuma ka iya kiran wani clumsy while you're clumsy yourself" tafada tana qara gallamashi harara tazo wucewa riko hannunta yayi wanda hakan yasata saurin juyowa tana zaro idanu "waye clumsy din?" yafada cikin hade "let go of my hand" tafada adan tsorace tana qoqarin kwace hannun "nine clumsy din?" yafada yana eyeing dinta batareda yasaki hannun ba 6ata fuska tayi kamar zatayi kuka har lokacin tana kicininyar kwace hannunta cikin rawar murya tace "ni..ni kasake min hannu" ganin dai da alamu kukan zatayi don har manyan idanunta sun duri ruwa yasa ya saketa yana cewa "kika qara bin hanyar danabi saina tsonemiki wadannan idanun" fashewa tayi da kuka tana saurin toshe bakinta sannan tabar wurin dasauri sakin baki yayi yabita da kallo donshi bega abin kuka ba anan, saida tayi nisa sosai sannan tajuyo ta gallamashi harara da wet idanunta ta murgudamashi baki sannan tajuya,tabar wurin dasauri kamar wadda aka biyo kasa daurewa yayi saida yasaki dariya marar sauti, lallai ashe dai wannan yarinyar matsoraciya ce? kwafa yayi Kawai yajuya ya qarasa wurin don siyen abinda zai siya don dama shima yabaro can ne don yin sayayya, izuwa yanzu yarage jin yadda yakeji towards zee wataqila allah ne ya qar6i addu'arshi don sosai wutar soyayyar zee tarage azuciyarshi kuma izuwa yanzu yagane cewa zee ta Deen ce kuma ya rage jin wannan zafin dayakeji duk lokacin daya gansu atare siyayyarshi yayi yakoma can wajensu inda sai shirye shiryen tafiya su daddy keyi don jirgin yakusan tashi tunda Aysha taga dawowarshi takoma bayan mussadiq don ya kareta don batason ma ganinshi kuma data dan leqo sai sun hada ido yayimata kallon zamu hadune saitayi saurin sake la6ewa abayan mussadiq shidai mussadiq besan sunayi ba hankalinshi nacan kan Lailah ahaka suka shiga bankwana inda zee kamar tayi kuka don sai jitayi tafara missing dinsu daddy tunma kafin sutafi ahaka suka tafi suna dagawa juna hannu cikin mixed feeling suna binsu da addu'ar safe journey Lailah duk yadda takejin idanun mussadiq akanta qin kallonshi tayi tajuya suka wuce saida takai daidai kofar dazata shiga sannan tajuyo idanunta suka fada cikin nashi murmushi ya sakarmata ahankali itakuma tayi saurin juyawa tashige. ahaka suna tsaye har jirgin nasu yadaga ya lula sama *AGURGUJE* kingin ranakun sunzo suntafi very fast inda su Deen keta shirye shiryen tafiyarsu zuwa saudiya sosai Deen ke doqin tafiyar don he can't wait yataka qasarshi ta haihuwa a bangaren soyayyarsu da zee kuwa kullum qara cigaba ake samu don da alamu zee tagaji dajan ajin tafara bada kai sosai suke shan soyayyarsu tawaya saidai idan yajene bata cika sakin jiki dashi sosai ba kamar dai da ranar daren tafiyar tasu sukaje gidansu Aymaan din don suyi bankwana inda suna zuwa Deen yasamu ya ke6e da zee a garden suna zance sukuma Aysha sukayi sama tareda batool sundan jima agidan kafin sufito zasu tafi inda su Aysha sukayi gaba ita da batool zasu fita suna gulmarsu zee wai suna can suna soyewa suga love birds abakin kofa sukaci karo da Aymaan da dawowarshi kenan daga asibiti inda ganinshi kamar daga sama yasa Aysha fasa qara takoma falon aguje da mammaki duk akabita da kallo harta qarasa wajen kaka ta la6e bayanta girgiza kai Aymaan yayi Kawai yashiga don qararta ma firgitashi tasoyi, yawuce yabar batool dake tsaye cikeda mammaki abakin kofar sadda yashiga ciki ya tadda anata tambayarta meye takema ihu ganinshi yasata qara la6ewa bayan kaka Kawai tana turo baki shidai bece komai ba yaqaraso yana gaidasu Ummie da murmushi anan yaji ashe gobe zasu wuce saudiya fatan sauka lafiya yayi masu sannan yawuce sama yana hararar Aysha dake la6e still abayan kaka ta gefen idanu har parking space suka rakosu suna masu fatan isa lafiya saida suka shiga motar suka ja suka tafi sannan suma suka juya ciki batool nata tsokanar zee *SAUDI ARABIA* lafiya lau suka sauka garin saudiya, fatherland din Deen inda yana taka qasar shima yaji eh wannan fatherland dinshi ne farincikin daya tsinci zuciyarshi aciki baya misaltuwa don ganin abin yake Kawai kamar amafarki twin din Abbansu Deen wato Al-hussain Kawai yasan da zuwansu kuma shi yaje tarbonsu a airport saidai ganin mussadiq biyu ba qaramin burkitamashi kwalwa yayiba don shima kwata2 besan da bayyanar Deen ba saida sukaje gida sannan sukayi mashi bayani dalla dalla inda fadin farincikin daya shiga ma 6ata lokaci ne sai godiya da kirari yake kwararawa allah mai yin yadda yaso maikuma maida abu marar yiwuwa abu mai yiwuwa kaka kau tasha godiya da addu'o'i awajenshi kamar ya ari baki haka suka kwana batareda sanin kowa a family dinba don Al-hussain yace kar agayawa kowa shida kanshi zai qirqiri family meeting gobe inda anan za'a bayyana Deen haka kau akayi don nan take aka sanar da gobe akwai family meeting wanda dama abune da akeyi duk in wani abu yataso Washegari a family meeting din inda babu wanda be hallara ba aka gabatar da Deen inda suka shigo shi da mussadiq cikin shiga iri daya fadin hautsinewar da wurin yayi 6ata lokaci ne don nan take wurin ya rude inda sai bayan Al-hussain ya gabatar da Deen amtsayin mujaheed daya 6ace awajen asiri yafara tonuwa inda matar Al-hussain ta tashi tana ihu tana bori wai qaryane mujaheed ya mutu saida aka tabbatar mata da hakan, wannan ba mujaheed bane mujaheed yamutu nan hankali yadawo kanta don sosai mutanen wajen suka cika da mammakin ganin yadda take ihu tana sambatu inda acikin sambatun ta tonawa kanta asiri asali dama matar Al-hussain bata qaunar Zainab matar al-hassan kwata2, wannan tsanar tasamo asaline tun lokacin dasuke amare kasancewar dama atare al-hassan da Al-hussain sukayi aure inda Zainab matar al-hassan tafi matar Al-hussain farinjini sosai danginsu Al-hussain sukafi sonta saboda saurin shiga ranta da kirkinta Duk abinda za'ayi itace kan gaba hakan yasa matar Al-hussain fara yimata hassada tana ganin duk ta saye soyayyar dangin mazajensu matar Al-hussain tariga Zainab haihuwa don saida tayi haihuwa biyu kafin Zainab ta haihu saidai ga haihuwar Zainab anfi murna yadda kasan ba'a ta6a haihuwar jika a dangin ba hakan yaqara tunzura matar Al-hussain abin be ida kasheta ba saida taga irin soyayyar da ake nunamasu mussadiq saboda wani irin jidasu akeyi a family din kamar su kadai ne jikoki kowa burinshi ya daukesu ga kyaututuka dasuke samu kota ina akai akai gashi kuma dama Al-hassan yafi Al-hussain wadata alokacin sai abin yataru yayimata yawa ganin bazata iya cigaba da qunsar baqincikin bane yasata Kawai shirya tagayyara family din Al-hassan din inda da zugar wata qawarta suka sa akayi kidnapping dinsu inda basu samu nasarar daukarsu su biyun ba don allah ya ku6uto da mussadiq sai sukayi garkuwa da mujaheed (Deen) duk tashin hankalin dasuka shiga alokacin matar Al-hussain jitake kamar ta taka rawa, sosai taji dadin ganin burinta na tarwatsa ahalin Al-hassan yafaru hakan yasa tama yanke shawarar salwantar da Deen a 6addashi daga doron qasa don su dawwama a baqinciki don sun lura sosai sukeson Deen saida tasa aka amshi kudadde dayawa wajen Al-hassan sannan tasa a qone Deen acikin motar da xasu sashi ciki agaban idon Al-Hassan hakan kau yafaru saidai abinda bata saniba shine alokacin jisukayi bazasu.iya qone Deen Acikin motar ba don he's way too innocent aganinsu be kamata yayi irin wannan mutuwarba hakan yasa Kawai suka jefashi aruwa aganinsu wannan mutuwar zatafi sauki tofa! sosai hankalin family din yatashi jin sambatun matar Al-hussain babu 6ata lokaci Al-hussain dayafi kowa rudewa alerting jami'an tsaro inda babu 6ata lokaci akazo akayi ramm daita aka wuce daita sosai family din suka shiga tashin hankali sai koke koke akeyi, shikanshi Al-hussain kasa tsaida hawayenshi yayi don sai alokacin komai kedawo mashi fresh, wannan wace iriyar matace yake zaune daita tsawon shekaru? sosai kowa ke mammakin abinda ta aikata don koda wasa batayi kama da wadda ke iya aikata rabin abinda ta aikata ba shima Deen sosai jikinshi ya mutu musanmman yadda yaga kowa nata rungumarshi ana kuka, kakarsu wato ainahin mamansu babansu babu wanda yakaita kuka tabi ta rungume Deen qamm kamar za'a kwace mata shi tanata sambatu cikin larabci saida hankali yadan kwanta sannan suka nemi jin yadda Deen ya bayyana inda anan akayi musu bayanin komai zokuga yadda akema kaka godiya kamar zasuyimata sujjada, addu'o'i kau aranar tashasu don acewarsu ba qaramin jihadi tayiba kuma sakamakonta na gun allah don dik abinda zasuyi mata bazasu iya biyanta ba...✍? Ummin fasihu🧚🏻‍♀? 8/19/21, 6:46 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *100* *FINAL🤸🏻‍♀?* Satinsu Deen biyu a saudiya inda acikin wannan sati biyun babu inda basu shiga ba domin zagayen dangi sai alokacin Deen yasan cewa ashe shi d'an dangi ne domin yanadasu ba adadi gashi sai nunamashi wani irin soyayya sukeyi suna jidashi suna riritashi kamar kwai idan yajuya yatuna da rayuwarshi tabaya yayi comparing dinshi data yanzu saiya godewa allah bisa ni'imomin dayayi mashi, abin har mammaki yake bashi wai shi da tun tasowarshi beda kowa beda wanda zai kalla ya kira nashi bayan kaka amma yanzu jibeshi xagaye tsamo tsamo cikin dangi dangin ma masu tsananin qaunarshi, dole ya godewa allah kaka ma abangarenta tasamu babban matsayi a wannan dangin don sosai suke qaunarta suke kuma girmamata, tuni suka qulle da ainahin kakarsu Deen suka xama kamar wasu aminnan juna a bangaren matar Al-hussain kau tanacan anmakata kotu da ita da qawarta dasukayi qulle qullensu tare bayan Al-hussain ya yanke igiya daya ta aurenshi dake kanta Satinsu biyu a saudiya suka daga zuwa misra garinsu ummie inda anan Deen yaqara ganin tsantsar qauna da tarairaya kowa soyake ya kasance taredashi kowa soyake yanuna yadda yake qaunarshi hakan yasashi zama kamar wani cele acikinsu Satinsu daya a qasar suka barota suka dawo Dubai inda dama Deen allah allah yake yadawo don sosai yayi missing *jewel* dinshi kamar yadda yasamata suna yanzu dukda kullum suna maqale awaya a bangaren zee ma sosai take missing baby boo din nata, rabonta dashi tun daren dazasu tafi saudiya gashi ba video call sukeyi ba bare su dinga ganin juna hakan yasa tayi wani irin missing dinshi, kullum idan suna waya saita dinga damunshi kan yaushe xai dawo saidai yace mata very soon insha allah relationship dinsu yanzu yayi improving sosai don har yana neman fin na da don sosai suke zuba soyayya mai tsayawa a qwalwa shaquwarsu tada tadawo tama ninka nada don wani lokacin ma idan suna jin yan shiriritarsu haka zasu dinga musayar kalaman soyayya ta sigar waqa atsakaninsu ta waya yanzu zee ita kanta tasan bazata gwadama Deen komai ba akan waqa don har mammaki yake bata idan yazaro mata wani baitin daya daga cikin dream dinta na neman tabbata don aduniya tanason waqa tana kuma dreaming tasamu wanda ra'ayinsu zaizo daya suyita tisa kansu agaba suna zubama juna baitika Yau tunda ta tashi takejin kanta cikin wani irin happy mood don Kawai tsintar kanta tayi dawani irin nishadi ayau din kowa ma na gidan ya shaida haka don qarara hakan ya bayyana a fuskarta da ayyukanta don tariga kowa nagidan tashi saidai suka tashi sukaga tama kusan gama aikace aikacen gidan haka tawuni cikin nishadi don abu kadan saita fashe da dariya dana dariya da wanda bana dariya ba har batool na tsokanarta kodai she needs psychiatric doctor ne? itadai Kawai saidai tayi dariya tace yau Kawai tana cikin nishadi ne without knowing why da daddare bayan isha'i suna zaune cikin dakinsu suna kallon wani series film cikin laptop din batool wayar zee tayi ringing ringing dinne yan dawo dasu daga duniyar kallon dasuka bada dukkan hankalinsu akai "mtcheew don allah shut that phone up tana distracting dina" inji batool idanunta akan laptop din batason ko janyesu daga kan screen din harararta zee tayi tasa hannu ta danna ma film din pause wanda hakan yasa batool tashi zaune azabure "haba meye haka?" tafada a little upset "saina gama wayar zamu cigaba" tafada tana jawo wayar dake gab da tsinkewa danna play batool tazo zatayi zee ta suri laptop din ta miqe tsaye tana mata gwalo itama miqewar tsaye tayi tafara kiciniyar kwace laptop din da zee ta6oye abayanta zee na zillewa tana dariya ahaka har kiran ya tsinke bata saniba wani yaqara shigowa dira zee tayi daga kan gadon still laptop din abayanta tana son rugama batool dake qoqarin kamota dago wayar hannunta tayi da niyyar kasheta ma gabadaya don taji dadin rigimar dasukeyi da batool don dama sun saba saidai number data gani na yawo akan screen din yasata yin still tana waro idanu batool dabata lura da yanayinta ba tasamu ta kwace laptop din tana dariya tana cewa "got yah!" "OMG!" inji zee tana kallon wayar idanu abude "meye?" inji batool tana matsowa bata amsa mata ba sai daga wayar datayi takara akunne ahankali sallamarshi dataji cikin cool voice dinshi ya ida tabbatar da zarginta, Deen is back! sauke wayar tayi saurin yi ta katse kiran sannan ta wawuro batool dake gabanta tawani irin rungumeta tana ihun murna "he's back! he's back! OMG!" saurin qwace kanta batool tayi tana cewa "wai meye haka? who is back?" cikin tsananin murna tace "my boo mana! kalla da number nan yakirani, wayyo! what a surprise!" tafada tana juyi tsaki Kawai batool taja takoma kan gadon tana bude laptop din saita kanta zee tayi kafin taqara daga kiran daya sake shigowa "hello?" taji anfada daga dayan bangaren "hello... is this for real?" tafada ahankali cikin yanayin mammaki sautin murmushinshi tajiyo sannan yace "kifito and see for yourself" "infito ina?" tafada tana dan wara idanu yar dariya yayi sannan yace "waje, ganinan a parking space kizo kiyimin iso" "are.. you serious?" yar dariya Kawai yayi yace "saikin zo" daga haka ya,katse kiran dungule hannayenta tayi tana ihun murna sannan tayi wani juyi tafada kan batool dake kallon ta "wai meye haka?" inji batool tana tureta daga jikinta "wai yana waje, what a huge surprise!" tafada cikin tsananin murna harararta batool tayi tace "ji gulma, kamar irin batasan dazuwanshi ba dinnan. ashe ba banza ba duk wunin yau baki yaqi rufuwa ashe kinsan abinda kika taka" "ji banza, wlh bansan da zuwanshi ba" ta6e baki batool tayi tana maida hankalinta akan laptop din gabanta tana cewa "saikiyi" dunguremata qeya zee tayi tana cewa "banza joy killer Kawai" ta tashi tanufi closet dinsu tabude cikin qanqanin lokaci tashirya cikin wata baqar abaya ta yafa gyallenta in a simple way tadan gyara fuskarta sannan ta feshe jikinta da turare zuwa tayi taqara dungure ma batool kai tana cewa natafi sannan tajuya tawuce dasauri kwafa batool data dago tana kallonta tayi sannan ta maida hankalinta kan abinda takeyi fitowa tayi daga falon sannan tafara takowa ahankali ta entrance din tanufi parking space hoping badai tsokanarta yakeyi ba bezo ba wata baquwar ash colour motar data gani pake a parking space din yasata jin wani irin sanyi na ratsa zuciyarta ahankali take takawa tana nufar wajen inda ko rabin kaiwa batayi ba aka bude murfin kofar daga bangaren driver yafito tsayawa tayi daga tafiyar datake tana kallonshi yana zagayowa dayan side din motar bata ta6a sanin har haka tayi missing dinshi ba sai yanzu, jitake kamar sun shekara basu hadu ba gashi yawani chanza yaqara yin fresh dashi shima bangaren Deen hakan take don shima sosai yaji yayi kewarta kuma ta chanza mashi sosai cikin dan lokacin dasukayi basuga juna ba ahankali ya sakarmata wannan cool murmushin nashi itama saita tsinci kanta da mayar mashi da martani ahankali yashiga takowa zuwa ina take tsaye hakan yasa ta cigaba da kallonshi abubbuwa dayawa nakai kawo azuciyarta komai nashi na daban ne hatta tafiyarshi, komai nashi cikin nutsuwa yakeyi, kai she love this guy! saida yaqaraso gabanta ya tsaya yana dan bada tazara atsakaninsu kallonta yakeyi da oily eyes dinshi fuskarshi dauke da murmushi, kasa cigaba da jurar kallon tayi hakan yasata sauke nata idanun qasa tana d'an murmushi "wow! you're welcome, dama yau zaka dawo baka fadamin ba? kai amma am very happy and surprise altogether, I missed you so much" inji Deen yana kallonta dagowa tayi ta kalleshi tana dan daga gira shima daga gira daya yayi yace "koba haka kikeda niyyar cewa ba?" harararshi tayi "to ba haka nayi niyyar cewa ba, besides fushi ma nake dakai, ashe yau zaku dawo amma shine baka gayamin ba kuma har waya munyi dasafe?" yar dariya yayi yace "it's a surprise, yanzu da kika ganin kamar daga sama ba kinfi jindadi ba?" kauda kai tayi tace "ni banwani jindadi ba" "ai bake zaki fadi jindadinki ko rashin jindadinki ba, fuskarki zata bayyana kuma tariga ta tonamiki asiri" harararshi tasakeyi sannan tajuya "muje" "to ranki shi dade" murmushi Kawai tayi suka jera atare suka nufi cikin gida zee tafara shiga falon sannan tayima Deen iso shima yashigo ciki bayan ya cire takalminshi saura baqaqen socks akafarshi bakinshi dauke da sallama falon babu kowa sai qamshin dake tashi afalon nunamashi wurin zama tayi ya qaraso ya zauna ahankali ita kuma tawuce kitchen ba dadewa tadawo da dan tray mai dauke da ruwa da drinks tazo ta ajiye akan stool din dake kusada kujerarshi dagowa tayi ta kalleshi saitaga shima ita yake kallo ya sakarmata murmushi kauda kai tayi itama tana murmushin tace "bari nakira ummy" "nabari" yafada yana kallonta juyawa tayi tawuce sama tanajin idanunshi kanta saida tahaye sama sannan ya daina kallon stairs din sannan yakoma ya jingina da kujera yana murmushi kai da ganinshi kasan yana cikin farinciki sosai ba'a jima ba yaji motsin saukowarsu hakan yasashi dagowa yaga ummy agaba zee biyeda ita cikin murmushin kunya ya miqe tsaye ya dan sinne kai har suka qaraso falon "A'a? maraba da mutanen saudiya, saukar yaushe?" tafada tana qarasawa ta xauna russunawa Deen yayi yana gaisheta cikin sinnar dakai amsawa tayi cikin kulawa tana cewa ya zauna maimakon yakoma ya zauna kan kujerar daya taso saiya zauna nan qasan carpet din "A'a? ka koma sama mana" inji ummy "A'a nanma yayi ummy" yafada akunyace "to ya hanya? ya mutanen saudiyan?" "alhamdulillah ummy duk suna gaidaku" "muna amsawa, yasu kaka?" "kaka na gida tana gaisheku itama" "muna amsawa, fatan kundawo lfy" "lfy qalau ummy" "to madallah... daughter kawomashi abinci kinji" dasauri yace "A'a alhamdulillah ummy" "to bari nahau sama, let me know idan zaitafi Zainab" "to ummy" Zainab dake tsaye bayan kujerar ummy tundazu ta amsa ummy ta tashi tawuce sama ajiyar zuciya Deen yasauke bayan hayewarta sannan yadago ya kalli zee dariya tadanyi "kamar na allah" tafada tana dariya dan wara idanu yayi "to da na wanene?" yafada yana tashi yakoma kan kujera itama dawowa tayi gaban kujerar da ummy ta tashi ta zauna "wow! I missed this girl so much, kinsan daga saukarmu wanka Kawai nayi na chanza nayonan? I just can't wait to set my eyes on you" murmushi zee tayi "miss you too" "A'a banga alama ba, naga nikadai ma ke doqi na" "haka dai kace" "hakane ma" "to ya hanya? hope kun iso lfy" "lfy lau wlh, hope munsameku lfy" "lfy lau, so how's saudi?" "alhamdulillah, duk lfy.. kinsan wani abu?" girgiza kai zee tayi "banta6a sanin haka mutum kejiba idan yana cikin family dinshi ba saida muke saudiya... wai nine tsamo tsamo cikin mutane kuma wai family dina, wlh ko amafarki banta6a hangowa kaina haka ba, jinike kamar ba gaske ba..I was just so overwhelmed.. banta6a sanin haka family keda dadi ba.. ranakuna a saudi da misra are one of my best moment ever" Zainab kasa daina murmushi tayi tunda yafara magana, kallo daya zakayimashi kasan he mean duk abinda yake cewa, sosai farinciki ke bayyane afuskarshi, sosai taji tana tayashi murna da hakan don wannan abin abin atayashi murna ne "congratulations, aidama family nada dadi bazaka gane hakan ba sai kana cikinsu, gaskiya ina tayaka murna, am very happy for you" murmushi Deen yayi sannan ya kalleta "and all these happened because of you, har duniya ta nade bazan ta6a mantawa da mutane biyu ba arayuwarta, dake da kaka. kun taka rawar gani arayuwata sosai kaka ta ku6utar dani takuma raineni cikeda so da qauna batareda tasan koni waye ba, takuma zamemun kowa alokacin dabanida kowa kekuma kinyi silar dawomin da komai dana rasa arayuwata, kindawomin da asalina kin dawomin da kowa nawa... tayaya za'ayi namanta daku Zainab?" sauke idanunta zee tayi tana murmushi don kallonta yake directly in the eye, maganarshi yasata jinta very emotional har tanajin kamar ta zubda mashi kwalla ahankali tace "you know.. komai muqaddari ne daga allah,allah yariga ya qaddara baxaka tashi cikin danginka ba yakuma qaddara xakayi rayuwa nesa dasu sannan ya qaddara cewa a irin wannan lokacin zaka dawo garesu, daga ni har kaka Kawai kamar tools ne na gudanar da abinda allah ya tsaramaka..allah yariga ya qaddara kaka ce silar raboka da danginka dakuma qasarka while nikuma ya qaddara nice silar hadaka dasu bayan shekaru masu yawa, so muma ba wayonmu bane Kawai hakan is destined don haka allah yakamata ka dinga godemawa domin ba qaramar ni'ima yayimaka ba, akwai mutane da dama irinka basu rayu dakowa nasuba kuma harsu koma ga allah,basu ta6a komawa ga nasu saidai ko a lahira saboda basuda rabon ganawa a duniyar kaiko kanada rabon sake ganawa da danginka aduniya, kanada rabon ganin mahaifiyarka wanda tun tashinka baka Santa ba, meyakai wannan? so ka cigaba da godewa allah domin ba qaramar ni'ima yayima ba" sosai magangganun zee suka sanyaya jikin Deen, hakane yanada rabon sake ganawa dasu ne shiyasa komai yafaru a yadda yafaru, da beda rabon ganawa dasu da qila be hadu da zee ba bare har ta silarta yasan asalinshi da ahaka zai qare rayuwarshi besan yanada mahaifiya ba a duniya, babu komai a maganar zee sai tsantsar gaskiya don yanada gashi dayake beda rabon haduwa da abbanshi saigashi shi bayanan, yatafi. qila shikuma sai acan, yana kuma fatan allah ya hada fuskokinsu a aljanna "alhamdulillah.. alhamdulillah rabbil a'alamin... alhamdulillah bi ni'imatika alayya" yafada ahankali saikuma yadago ya kalli zee da idanunshi dasuka kada sosai "marry me please... don allah kibari na mallakeki" wara idanu zee tayi saidai kafin tayi magana haryakai kan knees dinshi "please marry me" qara wara manyan idanunta tayi in shock "Deen.." "am proposing the second,time, will you marry me?" "Deen get up" "saikin amsa min" "Deen.." "I mean it" "ok..ok" tafada stana furzar da huci "YES" wani irin wara idanu Deen yayi "dagaske!" saiya tashi yadawo kan kujerar datake hakan yasata dan ja baya "dagaske?" "eh..eh" tafada tana qara jabaya "yaushe? gobe? jibi? inkoma ingayama ummie ta,turo gobe ayi komai?" tashi tayi tana kallonshi idanu aware "aturo ina? are you serious?" "anan mana, look barima natafi yanzunnan" yafada yana tashi saurin shan gabanshi tayi "ina zaka?" "wurin ummie mana dole nafadamata yau asan yadda za'ayi agama komai on time" "mene? are you alright? ina kata6a jin anyi hakan? Kawai daga cewa yes shikenan?" "to me zamu jira?" inji Deen kamar zaiyi kuka "bakaga karatu nake ba? saina gama ko ana tada wata magana" tsayawa yayi yana kallonta kamar wanda ake fadawa mugun abu "ka..me? Zainab sokike ki kasheni?" "na kasheka kamar yaya?" "Zainab bakiji abinda kikace ba? wai saikin gama karatu lokacin na sheqa kenan, haba wasane ma wannan" "kaike daukarshi wasa but am damn serious" tafada da iya gaskiyarta tsayawa yayi yana kallonta for some seconds saikuma yayi murmushi yace "to ai shikenan, we shall see.. ki yima ummie magana nizan tafi" "kamar ya we shall see? me kake nufi da hakan?" "time will tell, yanzu dai kiyiwa ummy magana bari nashigo muku da tsarabarku" yafada yana juyawa yafice daga falon fuskarshi dauke dawani murmushi dashi kadai yasan ma'anar kayanshi tadan jima bayan fitarshi atsaye cikin jujjuya maganar Deen sannan ta girgiza kai tahau sama don kiran ummy tareda ummy da batool suka dawo inda tundaga sama suke hango akwatinan biyun da Deen ya ajiye atsakar falon wara idanu duk sukayi suna ida saukowa ummy na tambayarshi wadannan kayan fa murmushi Kawai yayi yace "tsarabarku ce ummy, ayi hqr" mita ummy tafara akan kayan sunyi yawa daga baya kuma takoma godiya sai alokacin suka gaisa da batool itama tana mashi godiyar tsarabar anan sukayi sallama ummy taba zee ledar data sauko daita tace tabashi yaba kaka Deen yayi godiya yajuya yafita zee na bayanshi don yimashi rakiya saida suka isa parking space sannan yajuyo yana kallon zee itakuma ta miqamashi ledar da ummy tabata tana mashi godiyar tsarabar murmushi Kawai yayi daidai xaiyi magana mota tashigo gidan tsayawa sukayi suna kallon motar harta qaraso wajen parking din ta parka Aymaan da abbu ne suka fito daga motar sunyi mammakin ganin Deen sosai don basusan da dawowarsu ba har qasa ya tsugunna ya gaida abbu cikin girmamawa sannan sukayi musabaha da Aymaan nan suke tambayarshi saukar yaushe yace yau sudan dauki lokaci suna dan ta6a fira kafin suyi sallama su shige ciki bankwana suka sakeyi da zee sannan yashige motar yatada zee na nan tsaye haryaja yafice daga gidan sannan tajuya takoma ciki koda takoma ciki iskewa tayi duk suna falon sunata duba kayan da Deen yakawo akwatina biyune da qarami da babba, kallo daya zakayiwa kayan qaramun akwatin kasan na zee ne inda dayan kuma yayima kingin yan gidan sosai suke yaba kyawun kayan harda Aymaan wanda yanzu alhamdulillah bayajin komai gameda relationship din zee da Deen don sosai allah ya sassautamashi yakuma sa yayi facing din gaskiya cewa zee fa ta Deen ce. cikin ikon allah yarage jin yadda yakeji sosai akan zee don yanzu yama fara hasasowa kanshi wata, tunaninta ya addabeshi a yan kwanakinnan kullum bayada aiki sai tunaninta, saidai yasan abune dakamar wuya ta amince mashi but he'll try his best Bayan kwanaki uku da dawowarsu daga saudiya Deen da mussadiq suka daga zuwa Nigeria inda Deen zaije ne don waiwayar masana'antarshi shikuma mussadiq yajene da sunan rakiya amma abinda yakaishi daban agidan Deen suka sauka inda saida suka huta sosai sannan suka nufi gidansu Lailah bisa matsawar mussadiq sosai akayimasu tarbar mutunci inda ahalin sukayi matuqar farinciki da ziyarar tasu ta bazata ganin mussadiq da Lailah tayi aranar yaqara tabbatar mata da abubbuwan data dade tana hasashe tun bayan dawowarsu daga Dubai takasa nutsuwa, zuciyarta takasa samun sallama inda tunanin twin din Deen yabi yayi mata bake2 yayimata katutu azuciya kullum idan ta zauna kalamanshi Kawai kemata yawo a kwalwa, yanayin maganarshi, salonshi, komai nashi is different dukda kammaninsu daya da Deen saidai hallayarsu da yanayinsu ya banbanta, yayinda Deen keda sanyi sosai shi mussadiq talura is way too classic gashi kallo daya zakamashi ka iya jerashi a layin miskilai, haka Kawai takejin hallayar mussadiq yafi burgeta bisaga na Deen. koda ta sauko don su gaisa kasa looking directly at him tayi, abin mammaki saigashi maganarshi ta tabbata don yau akallo daya taganeshi dukda shigar da sukayi iri daya. fira sosai sukesha a tsakaninsu most especially Deen da Abba don mussadiq be cika magana sai shegen kallon daya kafe Lailah dashi babu ko kunyar su Abba ganin abin na neman yin yawa yasa Lailah excusing kanta ta haye sama donta lura mussadiq be iya takaittacen kallo ba saida zasu tafi sannan mamy takirata ta sauko don suyi bankwana inda anan suka d'an samu damar magana lokacin Deen da Abba are busy suna maganar aikin Deen dagowa tayi ta kalleshi taga ita din shima yake kallo, ahankali yasakar mata guntun murmushinshi itama d'an murmushin tayi ta sauke idanunta "your phone?" yafada yana miqamata hannunshi kallonshi tayi saikuma ta,miqamashi wayar hannunta amsa yayi yay dialing sabon layin dayayi na Nigeria kiran yashigo wayarshi sannan ya katse kiran ya maida mata "will call you later" yafada ahankali kada kai Kawai tayi daidai nan su Deen suka qaraso wajen sukayi bankwana suka tafi. kamar yadda yace din saigashi yakirata da daddare inda sukasha firarsu inda anan taqara sanin wasu daga cikin hallayenshi babu abinda yafi burgeta gamedashi kamar yanayin maganarshi, idan zaiyi magana adunqule yake yinta ko abaibai wanda dole saika nutsu sosai zaka gane ma'anarta. he just know how to deal with words. ga slang dinshi na Arab turanci yake mata amma da karin larabci saitaji turancin wani iri amma kuma ga mammakinta tamafison irin nashi din. sati daya sukayi a Nigeria inda cikin satin Deen yashiga busy sosai saboda aikin dasuka tararmashi yayinda shikuma mussadiq ya 6ata satin wajen yad'a manufarshi awajen Lailah Acikin satin ya bayyanama Lailah son dayake mata kuma yasamu kar6uwa don alokacin yariga yagama daita yatafi da imaninta a kwanansu na goma suka juyo Dubai lokacin hatta yan gidansu Lailah sunsan da soyayyar dake tsakaninta da mussadiq, Deen yafi kowa kowa farinciki da hakan don aganinshi sunyi mugun dacewa dajuna a bangaren Aymaan kuwa tunda yaga Deen agidansu lokacin dasuka dawo daga saudiya yafara neman hanyar yad'a manufarshi ga Aysha. at last ya tsaida wata shawarar dayaga ta hakan zaisamu kusanci daita nan yafara bibiyar Aysha a school dinsu yalura yarinyar is so timidshiyasa yake amfani da hakan wajen tsokanarta don sosai yake samun nishadi da hakan tun suna fada idan suka hadu har wata iriyar shaquwa tashiga tsakaninsu wadda cikin qanqanin lokaci ta rikide takoma soyayya anan Aysha tasan ainahin menene so saboda Aymaan ba baya ba afagen love da nuna kulawa sai alokacin taga ashe soyayyar datayi da umar abaya ba soyayya bace wahala ce don batasan haka soyayya keda dadiba sai akan Aymaan tofa atsakanin Deen da zee dakuma mussadiq da Lailah da Aymaan da Aysha sai narasa wadanda sukafi iya buga love, kowannensu ba daga baya ba don soyayyar kowanne abin burgewa ne Deen ne yafara yunqurowa a maganar tasu donfa shi dagaske yake bayada burin daya wuce na mallakar zee ganin hakan yasa mussadiq shima bijiro datashi maganar inda ummie taji kamar tazuba ruwa tasha don murna hakan yasa tayima yan uwanta da mutanen saudiya magana inda suma sukayi farinciki sosai da hakan babu 6ata lokaci suka fara shirye shiryen garzayowa Dubai domin qara maganar gaba kamar hadin baki adaidai lokacin shima Aymaan ya gabatarma su ummy maganarshi da Aysha sosai suma ahalin sukayi farinciki da za6inshi musanmman ma zee dataga mugun dacewarsu da Aysha don Aysha yarinyace dakowa zaiso hada jini daita abu kamar wasa cikin dan qanqanin lokaci mutanen su Deen suka garzaya wajensu abbu wanda daddy ya damqa komai ahannunshi don acewarshi shima ubanta ne inda anan sukaje neman auren zee inda nan aka tada maganar su Aymaan wanda hakan yayima kowa nawajen dadi, wato zasu bayar kuma za'a basu nan aka tsaida magana inda mutanen Deen suka nuna sunason ayi komai dawuri inda anan aka tsaida lokaci inda bayan wannan hutun nasu na wannan semester din za'asha biki sosai zee tashiga rudu lokacin dataji labari nan tafara kuka wai yayi kusa dayawa ita sotake tagama karatu batool kau mexatayimata banda dariyar qeta saigashi kwana biyu dasa ranar su Deen shima Ahmad yaturo magabatanshi akan maganarshi da batool inda shima qarshe aka jona danasu Deen da Aymaan, nanfa itama batool ta sire don kwata2 she didn't saw that coming saigashi zee ita takoma yima batool dariyar qeta asatin daya biyo baya kuma mutanen su Deen suka garzaya Nigeria don nemawa mussadiq Lailah inda shima.ataqaice aka jona danasu Deen ya kasance daurin aure hudu alokaci guda zokuga murna awadannan ahalin musanmman ahalin su Deen, ummie rasa inda zatasa ranta tayi don farinciki wai itace zata aurar da dukkan 'yayanta alokaci guda, wannan abin yakai abin farinciki suma ahalinsu batool ma hakan take dasu daddy, baxaka ma iya tantance wanda yafi wani farinciki ba. a bangaren su Lailah ma haka, sunyi farinciki sosai na hada zuri'a dazasuyi da ahalin su Deen gashi lokacin zaikama daidai lokacin da Lailah ke qarasa karatunta abindai ba'a cewa komai ahankali lokaci yaita tafiya inda ake shirye shirye takowane bangaren sosai kan amaren yadau zafi kasancewar ga jarabawa daketa gabatowa gakuma shirye shiryen biki haka sukaita fama har lokacin jarabawar yayi suka zana. alokacin saura duka yan satittika da bikin suna gama jarabawar kowacce tadawo gida basu qara zuwa school dinba aka hau yimasu gyare gyaren amare sosai iyayen amaren takowane bangaren suka zage wajen gyare 'ya'yansu wanda cikin qanqanin lokaci suka sauya suka fito a ainahin amaren biki na saura sati daya dangi suka fara bararowa takowane bangare gidansu batool sauran sati daya amma yadda kasan gobe ne bikin tuni su mummy suka iso Dubai don anan za'a daura auren both zee da batool biki saura kwana hudu su dangin su mummy suma suka fara durowa ciki harda aunty feenah wadda keda diya kyakyawa mai kama daita sosai tareda su cousins dinsu zee nanfa gida yaqara hargitsewa yakoma ainahin gidan biki abangaren su Deen ma hakan take don tuni gida yacika da larabawa kala2 tun biki saura kwana biyar gidan ya harmitse koda yaushe kaje banda tashin mandiri babu abinda kakeji biki saura kwana hudu duk aka kawo kayan lefe agidansu amare, kaya nagani nafada don fadin haduwar kayayyakin 6ata bakine itama Lailah Washegari aka tura nata lefen Nigeria kowa sai san barka akeyi bikin babu wata bidi'a daza'ayi illah dinner daxa'ayi ranar daurin auren haka ranakun sukaita wucewa kowa kanshi yadau xafi akan hidimar *RANA BATA QARYA...* Yau ranar juma'a takama ranar da kowa yake jira ranar da zata chanza labarin wasu auren mussadiq aka fara zuwa Nigeria aka dauro inda suka aka taho da amarya ta private jet akadawo Dubai dama sanin cewa most events anan Dubai za'a yishi yasa duk yawanci family dinsu Lailah sunriga sun iso Dubai din tun daren ranar suna isowa aka zarce massalacinda za'a daura kingin auren aka daura auren KAMALDEEN(MUJAHEED) da ZAINAB sai AYMAAN(ABUBAKAR) da AYSHA sai AHMAD da BATOOL(FATIMA) sosai garin Abu dhabi ya rude don babu wanda besan da wadannan daurin auren ba Deen tunda aka daura auren jinshi Kawai yakeyi kamar yana yawo kan iska komai sai yake mashi kama da mafarki, wai yau shine aka daura aurenshi da zee, yau zee tazama mallakinshi sujjudu shukur yayishi yafi a qilga fadin farincikin dayake ciki baya misaltuwa don shi kanshi baxai iya fasalta yadda yakeji ba abangaren kaka ma haka ana kawo mata labarin daurin auren tahau sujjadar godiya ga allah saikuma kuka, kuka takeyi kamar ranta zaifita, she can't believe yau ita keganin daurin auren Deen abinda tadade tana mafarki itama ummie saida ta tayata kukan don itama kasa riqe hawayen farincikin tayi itama jitake babu wanda yakaita farinciki aduniya aranar Washegari takama dinner inda wadda za'ayi da daddare daga nan kuma kowa ya dau matarshu yaqara gaba tunda safe kowanne gida ya hargitse da shirye shirye, kowanne gida babu matsaka tsinke shirye shiryen dinner sukeyi sosai sunason ya kasance one of the best dinner ever sai bayan isha'i sannan motoci sukaita zuwa daukar mutane zuwa dinner inda amaren motar angwayen kezuwa daukarsu idan kaga amaren lokacin idan ba farin saniba kayimusu bazakayi saurin ganesu ba sun chanza sunyi wani fresh sai glowing suke kowacce taci kwalliyarta acikin fararen wedding gown masu kyan gaske sukuma angwayen anci kwalabo Acikin baqaqen suit kowanne yayi wani irin breathtaking kyau fuskarsu sai glowing na angwanci sukeyi Deen kasa daina kallon zee yayi lokacin da aka shigo daita amota rabonshi da sata a ido tun lokacin dasuka gama exams suka rufe fita lokacin kusan saura sati uku ga bikin gani yayi kamar anchanzamashi itane kamar ba ita ba haka yatusata gaba da kallo harsuka isa wajen event din babu ko kyaftawa atare amaren da angwayen suka shiga hall din kowanne da amaryarshi agefenshi fadin haduwar dasukayi ma 6ata bakine don sun hadu over bayyanarsu yasa hall din kaurewa da tafi da whistle gawani waqa mai shegen dadi da aka saki ta background ahaka aka rakasu har zuwa maxauninsu sannan akafara event din taro yayi taro inda hall din ke dauke da manyan manyan mutane, businessmen, mawaqa yan uwan Deen dasukayi mashi kara, likitoci abokan Aymaan, fararen fata, baqaqe da larabawa dik an gwamutse a hall din anata chasu can nahango yan *DEEN FANS GROUP* tsamo tsamo cikin yan dinner, kowacce taci uban dauri sunsha ango sai bidiri akeyi iya qawatuwa dinner din ya qawatu inda aka gudanar dashi cikin salo mai matuqar burgewa basu suka tashi ba sai qarfe shadaya saura inda kowanne ango yadauki amaryarshi yayi gaba daita (dama kuma tunkafin sufito daga gidansu akayiwa kowacce nasiharta) a gida daya mussadiq da Deen zasu zauna don tare sukayi gini tun lokacin da akasa bikin saidai kowa da part dinshi, gidan dai awajene amtsayin gida daya amma aciki gidaje biyune komai iri daya kowanne danashi gidane daya hadu yakuma qawatu don fadin haduwarshi ma 6ata bakine anan kowa yashige da amaryarshi part dinshi inda daga nan nikuma naja bandararrun kafaffuwana najuyo gida don agajiye nake matuqa don baqaramin raqashewa mukayi ba nida yan Deen group a dinner. *TWO WEEKS LATER* sai alokacin daqara waiwayar amaren da angwayen inda kowanne gida naje abin gwanin sha'awa don kowannensu cin amarcinsu suke da picking stick gidan Deen ne qarshen zuwana inda na tadda zee a kitchen sanye cikin wasu hot English wears wadanda sukayi bala'in yimata kyau tana gaban cooker gas dinta tana soya musu egg omellete shikuma Deen na zaune daga bayanta kan wata kujera guitar ahannunshi yana kadawa cikin wani cool romantic tone, sanye yake cikin dogon baqin wando sai baqar singlet wanda suka fiddo farin complexion dinshi sosai zee da sautin guitar kemata dadi sosai sai kada kai take ahankali tana rausaya kugu tana humming ahankali tana cigaba da abinda takeyi dagowa daga kallon guitar dayakeyi Deen yayi ya kalli bayan zee ya quramata ido yana cigaba da kada guitar sannan yatashi ahankali yanufeta yana chanza salon kidan guitar din zuwa yayi ta bayanta gab daita sosai kafin tajuyo ya zagayo da hannunshi dake riqeda guitar ta gabanta daidai cikinta yacigaba da kadawa murmushi tayi tana cigaba da rolling kwai din ahankali ya sunkuyo da kanshi daidai wuyanta ya hura mata iska wanda hakan yasata dan shivering tana murmushi kai bakinshi yayi yadan ciji earlobe dinta sannan ahankali kamar arada cikin sigar waqa datayi daidai da sautin da guitarshi kebadawa yafara rairomata waqa ahankali kusada kunnenta jikinshi still manne daita *Deen*: _If I could do it all over_ _baby i'll do it different_ _maybe I wouldn't be here_ _in this..position_ murmushi zee tayi itama ta amsa *Zee*: _I found you then I lost you_ _looking back is torture_ _and it hurt to know that I let you go_ _you live right around the Corner_ Juyo daita yayi suna fuskantar juna fuskarsu dab dana juna hancinsu na gogar najuna suka cigaba da cewa *Deen & zee👩‍❤️‍?*: _And I could've had it all, could've had it all_ _true love❤️ I know I had it_ _true love❤️ it's so hard to find!!_ _true love❤️ If I could get it back_ _i'll never let it go this timeee💕_ *Deen*: _true love_ *zee*: _it's an inspiration🥰_ *Deen*: _true love_ *zee*: _it's was mine, all mine_ *Deen*: _true love_ *zee*: _yeah_ *Deen*: _I'll never let it go_ *zee*: _I'll never let it go.._ *Deen & zee*: _I'll never let it goooo💞💞💞💞💞💞_ hade bakinsu sukayi lokaci guda suka shiga bama juna hot French kiss kamar zasu cire le66en juna ganin hakan yasani saurin juyawa saikuma natuna da abinda take soyawa wanda da alamu ma sunmanta dashi nadawo nakashe gas din na wafci rabin kwan nayi waje ina cusawa abaki....✍? THE END💃🏻 alhamdulillah! alhamdulillah!! alhamdulillah rabbil a'alamin!!! allah na godemaka dakabani ikon gama novel dinnan lafiya, kurakuren dake cikinshi allah ka yafemin🤲🏻 ina yan amana? mutanen group dina masu haquri da uzuri🥰 ina miqa dunbin godiya ta agareku don kun nunamin qauna iya qauna, kunkuma yimin uzuri kunata bina da addu'o'i alokacin nake buqata yayinda wasu kuma suka kasayin hakan kullum sai complain yadda kasan biyanka albashi sukeyi. allah dai yabar qauna sweet sisters don qaunarku pure ce nima na shaida, allah yabar tare yakuma sake hadamu awani book din nagaba thanks soo much, Ashaanty heart you soo much💞💞💞💞💞