*____________________________________* 🌍WATA DUNIYA🌍 LABARI/RUBUTAWA KHADIJA S.SAMINU ('YAR GATAN MAMA) MARUBUCIYAR..... 👇🏻 RAYUWAR MU! A WANI GIDA RANA DUBU MAGANIN KAR AYI(Kar a soma) And now.... ⚔️WATA DUNIYA⚔️ *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ GODIYA Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga sarkin sarakuna lillahil wahidul ƙahhar!Wanda bai haifaba ba'a haifeshiba,mai jiya mai yau mai yanzu da anjima.Muna godiya agareka wadda bamui mata iyakaba ya mahaliccin aljanu da mutane,sama da ƙasa dama komai da komai. JINJINA✊🏻 Jinjina taban girma agareku masoyana,har kullum ina alfahari daku da yabon da kukeyimin,fatana Allah yabarmu tare yashiga lamuranmu ameen. GATANA ♥♥♥ Gatana MUHAMMADUR RASULILLAHI dukkan wata alaƙa idan ba takaba shirme ce! Hasara ce! Taɓewa ce! bata ƙarko,ƙaunarka itace aikinmu asonka aka haifemu muka girma,dominka muke rayuwa kuma dominka zamu koma gamai kowa mai komai,har kullum fatana kasoni kasoni kasoni Muhammadur' rasulullahi kashiga lamurana kabiyamin buƙatuna kadaɗamin ƙaunarka nida duk wanda yace ameen, sallallahu alaihi wasallama. GABATARWA!!! Wannan labari ƙagaggen labari ne,banyishi dan wasuba,nayishi dan Girman Allah dan mutane masoya addinin musulunci da musulmai,ban yarda wata ko wani su juyamin littafiba yin hakan base nafaɗaba,idan anga kuskure ina roƙon asanarmin domin nagyara insha Allahu.Nagode DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI. ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ SHAFI NA 1&2. ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ ✍🏻.... A fusace sarki ZALIMUZ-ZAMAN yajuyo da rinannun idanuwansa ga gimbiya ZALMAT cikin ɓacin rai da ƙunar zuci yace...... "Ki saurareni da kunnen basira kiji abinda zan faɗamiki dakyau,sanin kanki ne bana wasa bana alfarma ga dukkan wanda nagane cewa shi maƙiyinane,ba ruwana da alaƙata dashi inhar zaishiga gonata nikuma zansa fatanya nadatse kansa domin bani nakawo shiba! Da wace hujja za ki amfani ki sanar dani dalilinki na barin MUSLIM araye"?. ZALMAT ce ta ɗago da kanta sannan ta sauke idanunta afuskar sarki ZALIMUZ-ZAMAN wanda tari ne ta cukuikuye ta tattare kamar jiƙaƙƙen tsumma saboda ɓacin rai,kallon farko datayi masa taga zallar masifar dake fitowa daga ƙwayar idonsa,sunkuyar da kanta tayi akaro naba adadi kafin tasake duƙƙad da kanta ƙasa tace..... "Yakai wannan sarki mai dogon zamani,inamai sake baka haƙuri tare da baka baki akan kayi haƙuri bisa tseratar da maƙiyinka da nayi,banyi haka danna tozartakaba ya BABANA! Nayi hakane domin nacanzawa maƙiyanka tinani akanka sannan nashiga jikinsu yadda nan gaba ɗaukar fansa akansu bazai bamu wahalaba. Ya kai wannan sarki mai dogon zamani! Inaso kabani dama nan da wasu ƴan kwanaki ƙalilan inaso nakoma cikin maƙiyanka kuma maƙiya addininmu namusu ɓadda kama nacisu da yaƙi" "ZALMAT!!! Kidawo da hankalinki jikinki kinutsu kisan me bakinki yake furtawa akan ma'abota addinin MUSULUNCI!! " ZALMAT ta sake duban mahaifinta Sarki ZALIMUZ-ZAMAN sannan tace.... "Yakai BABANA! Ina sane da ƙiyayyar dake tsakaninka da waɗancan ƙananun mayaƙan,idona bai rufeba yakai BABANA! Burina akullum mune zamui nasara akansu basu zasui nasara akanmuba,kabani wannan damar domin na yiwa kaina na yiwa akwatin sihirinka alƙawarin sena kawoma kawunan maƙiyanka ka yi dariya ka tofamusu yawun ƙasƙanci sannan ka ajjesu a wukaƙantaccen waje wanda mutanenka zasu dinga kallonsu kaima kana kallo kana alfahari dani". ZALIMUZ-ZAMAN ya kalli ƴar tasa ZALMAT cike da so daƙaunarta cikin shauƙi da jindaɗin kalamanta yace... "Yake Ƴata! Inamai tabbatar miki na amince da buƙatarki kije kifara shirin tafiya garin DEENUL-ISLAM!. To amma banji kinyimin maganar ɗauko TAKOBIN KOGON ƊAUKAKA ba,shin ko kin manta ne"?. "Ban manta da itaba yakai BABANA,ina sane da ita domin ma itace tafarko acikin lissafina" "To yanzu idan kintafi DEENUL-ISLAM! waye zaidinga baki kariya kenan"?, "Akwai buƙatar kahaɗani da jajurtattun mugayen aljanun daka mallaka yakai Babana,sannan kabani wani ɓangare daga TASKAR SIHIRINKA saboda kare kaina alokacin da wata musiba ta afko inda nake azaune" "Ina alfahari dake Ƴata ZALMAT! Har kullum kece ke ƙoƙari akan maƙiyana,bisa wannan gudummuwa da kike bani,nayi alƙawarin baki kujerata aduk sanda kika kawomin kawunan sarakuna guda uku,sannan kika danƙamin TAKOBIN KOGON ƊAUKAKA ahannuna,awannan lokaci nikuma zansauka daga kan wannan kujera tawa nabaki domin kema kigudanar da mulkinki kiyaƙi MUSULMAI" ZALMAT ce ta ɗago da saurin gaske tare da kallonshi cikin rawar baki take faɗin.... "Kawunan waɗanne sarakuna kakeso nakawo maka ya Baba na? Sannan a'ina ne zansamo wannan takobin da kake faɗa? Kuma zuwa nan da wane lokaci kake buƙatar nacika waɗannan aiyuka daka bani"? ZALIMUZ-ZAMAN ne ya karkace ya bushe da wata mahaukaciyar dariya wadda seda ilahirin ɗakin ya amsa ,ya daɗe yana ƙyaƙyatawa kafin ya gimtse bakinsa ya kalleta yace..... "Yake Ƴata! Ban ƙayyademiki lokacin da zaki kawominba,saboda nasan yadda dukansu suke da mummunan hatsari wanda duk wanda ya shigesa baya iya fita koda kuwa zai mallaki gaba ɗaya dodannin tsafin dake faɗin wannan duniya. Kema nabaki wannan aikine domin na jarrabaki sannan nabar tarihi cewa ƳATA ZALMAT tayi abinda dubun dubatar sarakuna suka kasa,ciki kuwa harda ni kaina... Kawunan sarakuna Uku dana ce kikawomin ba kowaɗanne sarakuna bane illa!! SARAUNIYA SINIYYA!,SARKI KAMALUD DEEN! da SARAUNIYA ZULFA.Waɗannan sarakunan uku duka suna mabanbantan waje kuma kowannensu yana da ƙarfin mulki da mayaƙa sannan kuma guda biyu daga cikinsu suna ɗauke da Addinin musulunci, bazan cika burikana na duniya ba senaga kawunansu agabana. Sannan wajan da zaki samo wannan TAKOBI ba ko'ina bane illa 🌎WATA DUNIYA 🌎" SARKI ZALIMUZ-ZAMAN yana kawowa nan azancensa ya miƙe tare da shigewa yabar ZALMAT azaune. Tinani ne yashiga zarya cikin ƙwaƙwalwarta lokaci guda taji gabanta yana tsananta faɗuwa,"Ni yanzu ZALMAT ta'ina zanfara kenan acikin waɗannan ayyuka da suka riskeni yanzu? 🌎🌎🌎🌎🌎🌎DEENUL-ISLAM! Cike da jarumta MUSLIM yake sanyawa SARAUNIYA SINIYYA magani aguraren dataji raunuka sanda suke yaƙin ceton rai tare da rundunar SARKI ZALIMUZ-ZAMAN,babu abinda Sarauniya SINIYYA take iyawa banda ambaton Ubangijin talikai,bayan sunɗau wasu lokuta ne ta buƙaci MUSLIM yabata ruwa tasha.Cikin sadaukarwa yatashi ya kalli gabas,yamma,kudu da arewa yaga bai hangi ta inda zaisama mata ruwan dazata shaba gashi se wahalalliyar shaƙuwa ce take sarƙe mata numfashi.Tajigata ainun dan daƙyar take iya buɗe idanunta wanda suma suke mata zugi kamar anzuba mata barkono.MUSLIM ne yana tsaka da roƙon ALLAH ya hanyi wani siririn kogo wanda yake da tabbacin jaririma bazai iya shiga cikinsa ba balle kuma shi ƙarfaffan namiji maiji da ƙwanji,ruwane kawai yake kwarara tacikin siririn kogon dan yana iya hango yadda ruwa ke zuba kamar da bakin ƙwarya.Wani daɗine ya ratsashi sanda sukai ido biyu da ruwan,cikin ƙarfin hali yasake jan ƙafarsa wadda takemasa zugi da raɗaɗi sakamakon ciwukan da sukai mata ƙawanya. Yana isa daf da bakin kogon ya hangi wata narkekiyar macijiya sai azababben sheƙi da walwali takeyi tana ƙoƙarin tura kanta jikin wannan siririyar ƙofar kogon.Caccaka kanta takeyi iya ƙarfinta tana samarwa kanta hanya inda cikin ƙanƙanin lokaci batare da MUSLIM ya ankaraba yanemi macijiyar yarasa bayan tayiwa kanta hanya ta wuce inda zata,cikin ikon Allah ya hangi ruwan yanata kwaranyowa tacikin wannan hanyar yana fitowa harya yiwa kansa hanya yana gudu kamar ana hankaɗoshi. ALLAHU AKHBAR!✊🏻Kalmar data fito daga bakin MUSLIM kenan inda ya yunƙura cikin sauri yayi inda zai sadashi da ruwan domin yad'iba yakaiwa SARAUNIYA SINIYYA tasha. Isarsa inda ruwan yake keda wuya ya..........⚔️. Kaɗan daga cikin ⚔️🌍WATA DUNIYA 🌍⚔️kenan ina fatan zakuyi haƙurin bibiyata sannan ku sambaɗamin ruwan comment wanda zaibani k'warin gwiwar cigaba dakawo muku shi akan lokaci nagode. ⚔️⚔️⚔️⚔️⚔️ Domin gyara sharhi ko bada shawara atuntuɓeni ta wannan layin👇🏻 07047530638🌍⚔️ Allahumma Salli ala Muhammadir'rasulullah..!!!Sallallahu alaihi wasallama💖 ƳAR GATAN MAMA✍🏻. ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ LABARI/RUBUTAWA KHADIJA S.SAMINU (ƳAR GATAN MAMA) Marubuciyar...... A WANI GIDA RAYUWAR MU! MAGANIN KAR AYI! nd now...... ⚔️WATA DUNIYA⚔️ ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ SHAFI NA 3&4 ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ Isarsa inda ruwan yake keda wuya yasaka maɗebinsa tare da kanfato ruwan yatafi da sauri domin yakaiwa SARAUNIYA SINIYYA,yana zuwa yatarar da ita kwance inda yabarta babu alamunma akwai numfashi atare da ita. Cike da karaya yake shafamata ruwan afuskarta yana addu'ar Allah yasa tatashi.Ya ɗauki tsawon lokaci ahaka da ita batare data farfaɗoba Dan haka ya shiga zullumi yana tinanin yadda suka tsinci kansu shida Sarauniya SINIYYA kwatsam ya hangi wata guguwa mai ƴarfin gaske ta tawo ya saitin inda suke,bai ankaraba segani yayi ta taddasu inda ƙasa tashige masa idanu lokaci guda yarufe idon tare da ambaton Ubangijin talikai yana neman yayi musu taimakonsa. Dajin gaba ɗaya ya hargitse bishiyo sek'ara sukeyi inda halittun dajin kegudu suna iface-iface saboda yadda guguwar ke ƙoƙarin raba bishiyun da mazauninsu,sunɗau tsawon daƙik'u ahaka kafin daga bisani guguwar taɗauke tamkar bata taɓa faruwa ba.MUSLIM ne yakai dubansa ga gefen hagunsa inda yakejin wani wuci mai shiga jiki yana ta shi awajan,hankalinsane ya tashi sa'ilin da yayi tozali da wani jibgegen Aljani me matuƙar muni da ban tsoro na tashin hankali. Duk wasu nau'o'i na muni wannan jibgegen Aljanin yahaɗasu,baƙik'k'irinne mai azabar muni yadda idan ka kalli cikin idanunsa sekaji inama -inama saboda yadda kanka zai sara sakamakon ganin munin wannan mushrikin Aljani. Kallon inda MUSLIM yake tsugunne Aljanin yayi tare da bushewa da wata mahaukaciyar dariya wadda seda ilahirin dajin ya amsa inda wannan dariyar ta tsorata halittun dake cikin dajin...... Dariya yake ba ƙaƙƙautawa inda fuskarsa ke wani cakuɗewa tana cukuikuyewa yanda ba wanda zaizo yakalleshi awannan halin saboda muni,idan kuma mutum yayi nasarar kallon wannan Aljanin to tabbas bazai yadda yasake ba saboda yadda mara imanin Aljanin ke wangale bakinsa dake ɗauke da wasu jajayen haƙora zaro-zaro kamar takubba. Duk wannan abubuwa dasuke faruwa basu sa SARAUNIYA SINIYYA ta farkaba daga dogon suman da tayi. Ba tare da MUSLIM ya luraba wannan gibgegen Aljanin mai bantsoro ya bayyana agabanshi sekace anjefoshi,kallon MUSLIM yayi sosai kafin yaɗaga takobinsa sama cikin zafin nama yayo kan MUSLIM da ita. Tana daf da isowa jikin MUSLIM kenan ya daka wani wawan tsalle yaigefe guda takobin ta sauka awani waje daban.... Cike da ɓacin rai wannan jibgegen Aljanin yasake ɗaga takobinsa tare da kurma ihuu! yayo kan MUSLIM.Takobin tayi nasarar zuwa inda MUSLIM yake domin bata sauka ko'inaba se acinyarsa. Cike da murnar samun nasara Aljanin yasake ɗaga takobinsa sama domin yasake daɓawa MUSLIM akaro na biyu,wata mahaukaciyar mulmulalliyar guguwa ce tataso wadda tai silar faɗuwar takobin daga hannunsa yana tangal-tangal tare da kare idanuwansa. MUSLIM ne yai ƙarfin halin ɗago kansa domin yaga wane gagarumin abune yadakatar da mutuwarsa adaidai wannan lokaci? Idanunsane sukayi tozali da Gimbiya ZULMAT ɗiyar sarki ZALIMUZ-ZAMAN tsaye afarfajiyar sararin samaniya ɗauke da wata sharɓeɓiyar takobi wadda tsininta ya tokare zuwa ƙasa inda MUSLIM da SARAUNIYA SINIYYA suke idanunta sunrine sunyi jajir kamar gauta saboda tsananin ɓacin rai. Wata iriyar girgiza dajin yakeyi kamar ana juyashi,yayinda wasu daga cikin bishiyun dajin suke barin mazauninsu su faɗi ƙasa,ba komai ya haddasa wannan bala'inba illah wani wahalallen ihu da Gimbiya ZULMAT dakeyi tana saukowa izuwa dandanyar ƙasa tana mai ɗaga takobinta sama da nufin ta sauketa akan wannan Hatsabibin Aljani mai matuƙar muni da bantsoro. Cikin zafin nama ya kaucewa sarannata ta hanyar ɓacemata tanemeshi ta rasa,tana huci tare da sauke numfashi awale tasaki takobin nata tare da sakin jiki ta zauna adandanyar k'asa tana kallon yadda MUSLIM yake yatsina fuska yana kallon raunin cinyarsa da alama ba ƙaramin ciwo Aljanin yajimasaba. Kallonsa ta sakeyi akaro naba adadi kafin ta yunk'ura ta tashi taje inda yake tsakanin zama da kwanciya ta kalleshi tare dayimasa sannu,baiko kalleta ba ballantana tasa ran zai amsamata,hakanne yasa tabar inda yake takoma inda SARAUNIYA SINIYYA ke kwance kamar matacciya tacigaba da sakamata magani araunukan jikinta. Taɗau lokaci ahaka kafin daga bisani ta taso tadawo wajan MUSLIM ɗauke da magungunan shima tahau sanyamasa batare data nemi izini awajansa ba.Yanajin yadda azaba take ratsa ilahirin jikinsa sanda take sakamasa maganin amma dake namijin mazaje ne bai nunamata afuskaba balle ta fahimci ya zafin ciwon yake,sai da ta tabbata tagama sanya masa maganin sannan tatashi taɗaukomai tulun ruwan sha ta miƙamai,kamar bazai karɓa ba kuma seya tsinci kansa da karɓa harda yimata godiya sannan yakai bakinsa. Gefe guda takoma ta zauna tare da tsunduma cikin tinani mai nisan gaske. Batare dasuka duka sunluraba suka hangi wata jibgegiyar.......... ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ Domin gyara sharhi ko bada shawara atuntuɓeni ta wannan kayin👇🏻 07047530638. Allahumma Salli ala Muhammadur'rasulullah❤️SAW 💖 ƳAR GATAN MAMA✍🏻. ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ LABARI/RUBUTAWA KHADIJA S.SAMINU (ƳAR GATAN MAMA) Marubuciyar...... A WANI GIDA RAYUWAR MU! MAGANIN KAR AYI! nd now...... ⚔️WATA DUNIYA⚔️ ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ SHAFI NA 5&6 ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ Batare dasu duka sun luraba suka hangi wata jibgegiyar damusa wadda girmanta ya zarce tinani,tsoro ne yakama MUSLIM saboda kallon yanayin dayake ciki na rashin ƙwarin jiki ga kuma saran dake cinyarsa bazai bari yayi wani yunƙuri dazai kare SARAUNIYA SINIYYA ba.ZULMAT ce ta miƙe tsaye da wani mugun sauri tare da nufar inda damusar da tawo. Kallon kallo akafara tsakanin damusa da GIMBIYA ZULMAT kowannensu na neman ran ɗan uwansa. Batare da ZULMAT ta kula ba damusar nan tadaka tsalle da nufin ta sauka akan GIMBIYA ZULMAT,cikin zafin nama ZULMATA ta kauce mata wanda hakan ya dalilin faɗuwar damusar ak'asa ragwaf...... Faɗa sukeyi sosai tsakaninta da wannan damusa ba ƙak'k'autawa,tashi sama GIMBIYA ZULMAT takeyi tana dirowa tare dakai sara suka ga wannan damusa,k'arar da ZULMAT keyi yaisanadiyyar farkawar SARAUNIYA SINIYYA daga dogon suman da tayi,idanunta fes ta saukesu akan Zulmat dake ta faɗa da Damusa. Sake buɗe idanunta tayi sosai saboda mamakine yakamata ganin GIMBIYA ZULMAT na faɗa da damusa a inda suke amma batai yunk'urin kashe suba. A'iya saninta ZULMAT babbar mak'iya Addinin Musulunci ce ita da mahaifinta,"to amma me yasa take ƙok'arin karemu bayan bata tare damu"?,"menene dalilinta nayin hakan"?. SARAUNIYA SINIYYA ce kewa kanta waɗannan tambayoyi dukda tasan batada mai bata amsoshinsu. Mamakintane ya ninku sanda taga Damusar nan nawani shu'umin tsalle tana dira kan Gimbiya ZULMAT yayinda ita kuma tafara kasa kare kanta,sunɗau wasu ƴan daƙik'u ahaka kafin Gimbiya ZULMAT tasamu nasara cakawa wannan DAMUSA mashi agefen idanunta guda ɗaya. Wani razanannen ihu Damusar tayi wanda saida ya haddasawa dajin girgiza gaba ɗaya, ihu Damusar taci gaba dayi tana zagaye inda sukaifaɗa da ZULMAT,bazato babu tsammani sukaga Damusar tayi wata girgiza ta koma wani murtukeken Aljani mai bantsoro wanda atake yazube awajan saboda jigata. ZULMAT ce takai dubanta gareshi tare da kecewa da wata muguwar dariya ganin tayi nasara akansa.Matsawa tayi inda SARAUNIYA SINIYYA take zaune tana yimata sannu tare da ɗaukar tulun ruwa ta miƙamata domin tasha,batai musu ba ta amsa fuskarta lulluɓe da wani yalwataccen murmushi mai ƙayatarwa. Kai ruwan bakinta tayi bayan tace... "Bismillah!" Tasha mai yawa kamar bazata barshi ba sannan tayiwa ZULMAT umarni data miƙawa MUSLIM yasha,baiyi musu ba ganin SARAUNIYA tasha yasa shima yasha yaƙoshi. Bayan sunɗau wasu mintuna ahaka ne Gimbiya ZULMAT ta kalli SARAUNIYA SINIYYA tare da faɗin....... ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Tinda SARKI ZALIMUZ-ZAMAN ya tashi yashiga turakarsa yakasa zaune yakasa tsaye saboda yadda ƙwaƙwalwarsa take neman hargitsewa da tinani,ganin zai wahalar da kansa yanzu ne yasa yaɗau tulun giya yahau sha babu ƙaƙƙautawa ,saida yayi mankas sannan ya ajje tare da bajewa saboda yanaso yasamu hutu kafin yatashi yaɗora daga inda yatsaya. Bayan yatashi ne yakoma inda kayan tsaface-tsafacensa suke yahau dube-dube akan ayyukan daya bawa ƴarsa ZULMAT domin yanason yasan tsakaninsu da mak'iyansu waye zaiyi nasara.Buga ƙasa yakeyi yana maimaitawa lokaci guda yana kallon madubin tsafinsa tare da karanto wasu ɗalatsiman tsafi masu wahalar ganewa. Ya haɗa gumi sosai kamar wanda aka tsamoshi daga cikinruwa saboda ruɗanin daya shiga sanda yaga......... ⚔️🌍⚔️🌍⚔️DEENUL ISLAM. MUSLIMAT ce tashigo turakar SARAUNIYA SINIYYA domin neman izini bisa shawarar dasuka yanke tsakaninta da MUSLIM akan tafiya ɗakko ⚔️TAKOBIN KOGON ƊAUKAKA⚔️ta iske basu dawo ba tunfitar dasukayi sa'ilin tana can tana bawa jakadiya sak'o. Neman waje tayi ta zauna tare da............ ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ "Sarauniya ina mai neman afuwarku bisa abubuwa marasa daɗi dasuka faru tsakaninmu yaƙin daya gabata,sannan inamai neman alfarmarku daku zauna tare dani bima'ana inason nashiga cikinku saboda wani dalili" ZULMAT ce take faɗin wannan magana idanunta nakan SARAUNIYA SINIYYA tanason ta gane ainayin abinda ke ran sarauniyar. Gyaran murya Sarauniya tayi tare da gyara zamanta sannan tasake duban ZULMAT tace...... "Shin wane dalili ne yasa kikeson kishiga jikinmu kizauna damu?, Kuma yabatun mahaifinki da saninsa zaki zauna tare da..........✍🏻 ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Domin gyara sharhi ko bada shawara atuntuɓeni ta wannan layiin👇🏻 07047530638. ƳAR GATAN MAMA✍🏻. ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ LABARI/RUBUTAWA KHADIJA S.SAMINU (ƳAR GATAN MAMA) Marubuciyar...... A WANI GIDA RAYUWAR MU! MAGANIN KAR AYI! nd now...... ⚔️WATA DUNIYA⚔️ ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ SHAFI NA 7&8. ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ "Shin wane dalili ne yasa kikeson kishiga jikinmu kizauna tare damu?,kuma yabatun mahaifinki da saninsa zaki zauna tare da mu?". "Yake wannan Sarauniya mai dogon zamani,inamai tabbatar miki da cewa,zancen gaskiya mahifina ZALIMUZ-ZAMAN bashi da masaniya dangane da komowata cikinku da zama,sedai yana sane da taimakon MUSLIM danayi sa'ilin da ake gudanar da yak'in daya gabata,haƙiƙanin gaskiya ran mahaifina yaɓaci sosai,hakan yasa yake tinanin nima maƙiyarsa ce kamar ku tinda har zan iya taimakonku alokacin da kuke buƙata,komawata gareshi keda wuya ya fatattakeni yatozartani gaban jama'ar gari ya umarci afita dani domin ayanzu baida maƙiyar data kaini" ZULMAT na zuwa nan azancenta tasa gefen hannunta tare da goge ruwan hawayen daya wanke mata fuska sannan taci gaba da faɗin...... "Yake wannan Shugaba mai adalci inason kiyimin adalci kizauna dani da zuciya ɗaya saboda ayanzu bani da wani abin dogaro idan ba ke da mutanenki ba,nazaɓi nadawo nazauna tare daku ne saboda nasan kuɗin bazakuƙi karɓata ba sannan....." Katseta Sarauniya tayi ta hanyar faɗin..... "Babu komai! Zan zauna tare dake kizama tamkar ɗana MUSLIM awajena,amma akwai sharaɗi guda ɗaya" "Wane sharaɗi ne ya Shugabata" Zulmat ta faɗa bakinta na rawa.... "a'a karki damu kanki,bawani abune mai wahala ba,inason nasanar miki cewa mu ma'abota addinin musulunci ne kuma kema yazame miki dole matuk'ar da gaske kikeson zama damu ki karb'eshiii" Sarauniya na zuwa nan azancenta ta tashi tafara haɗa kayansu na matafiya domin so take suɗau hanya zuwa gida. Haka kuwa akayi suka hau dokunansu sannan sukaɗauki hanyar zuwa DEENUL-ISLAM wanda shi ne ainihin garinsu. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ "Gyara kintsi dakyau! Gyara kintsi dakyau!! Allah yaja da ran SARKI KAMALUD-DEEN mai dogon zamani mai gaskiya da ruƙon amana,uwa uba mai son talakawa mai kishin addininsa wato MUSULUNCI" Sarki ne yayi gyaran murya tare da faɗin..... "Uumm! Barka dai,muna godiya da wannan yabo da akaimana.Amma me akeso afaɗamana haka dawurwuri?" Waziri ne ya gyaran zamansa sannan yamaida kansa ƙasa yace..... "Allah yaja zamaninka,daman wani bawan Allah ne ya iso wannan gari mai albarka sannan ya buk'aci akawoshi wajanka" "Shin anbashi masauki mai kyau? Anbashi abincin dazaici yasha?" "Allah yaja zamaninka babu abinda ba'ayi masa ba,yanzu haka ya kimtsa kai kaɗai yake son gani" "Tom babu damuwa,ashigo mana dashi ciki" Bayan SARKI KAMALUD DEEN yabada umarni ne akatafi ashigo da baƙon daya sauka agarin...... Basu ɗauki wani lokaci ne segasu sunshigo dashi izuwa turakar sarki. Wani dattijon mutum ne tsoho tukuf wanda shekarunsa sunkai kimanin shekara casa'in da haihuwa,domin kuwa tsufan nasa yakai tsufa daƙyar yake buɗar baki yayi magana,bayan antaimakamasa ya zauna ne yadubi sarki tare da faɗin...... "Allah yaja zamaninka! Inamaka fatan alkairi tare da fatan na same ku lafiya" Sarki ne ya dubeshi duba na tsanaki sannan yace..... " Amm! Sannu dai baba,mungode da fatan alkairin dakayi mana,amma zamuso muji daga ina kazo garemu kuma mene kake tafe dashi"? Dattijon ne ya gyara zama tare da faɗin..... "Allah yaja zamaninka sarki mai dogon zamani,da farkodai ni sunana NUJBEER ƊAN NAJABURU anhaifeni aƙasar NILDIHAL nataso acikinta,bantaɓa aureba kuma bantaɓa shiga wani gari domin wani daliliba sai wannan garin naka,ni na kasance ina ɗauke da wani babban matsayi acikin manyan bokayen garin NILDIHAL. Sanin kanku ne a al'adarmu duk farkon shekara da ƙarshen shekara akwai wasu al'amura da suke faruwa damu masu kyau ko marasa kyau,ni NUJBEER ƊAN NAJABURU duk shekara ni ne farkon wanda ke fara ganowa ƙasarmu abinda zaifaru sannan ni ne wanda keyin aiki domin maganin wannan matsalar. Naƙware nayi shura a aikina,nayi fice na gagara ako'ina nafaɗin wannan duniya tamu,babu wani burin duniya nawa dabai cika ba sai guda ɗaya,wannan burin cikarsa shi ne zaicike dukkan wani matsayi danake nema afaɗin duniya" Dattijon yaɗago da kansa ya kalli sarki KAMALUD-DEEN ya nisa sannan yacigaba da cewa..... "Allah yaja zamaninka yakai wannan sarki mai dogon zamani.Wannan buri nawa bawani buri bane se buri guda ɗaya wato burina na ɗaukar TAKOBIN KOGON WATA DUNIYA wanda ake yimai laƙabi da KOGON MAI RABO,wannan kogo yana da mummunan hatsarin gaske wanda musifun dasuke cikinshi sunfi ƙarfin tsaface-tsafacenmu baki ɗaya matsafan wannan duniya. A'iya binciken dana ɗauki shekaru inayi nagane cewa tsafina da duk wani abu danake tak'ama dashi bazai bari na iya shiga wannan wajeba sedai taimakon abin bautarku,madubin tsafina yanunamin cewa kai kaɗai kaine wanda zanhaɗa kai nashiga wannan KOGO kuma naɗauki wannan TAKOBII" Koda NUJBEER ƊAN NAJABURU yazo nan azancensa,seyai shiruu! ya ƙurawa SARKI KAMALUD-DEEN idanu yanaso yagane ainihin abinda ke ƙunce afuskarsa. Sarki yaja dogon numfashi tare da kallon NUJBEER ƊAN NAJABURU yanamai jinjina kansa tare dayin shiru na wasu ƴan dak'iƙu sannan yai gyaran murya yace...... "Umm! Yakai wannan tsoho ma'abocin shekaru da dogon tarihi,munji duka bayananka kuma mungamsu dasu,sedai bamu yanke musu hukunciba ahalin yanzu munason ka koma masaukinka zamu nemaka" Cike da k'warin gwiwa NUJBEER ƊAN NAJABURU ya amsa tare da bin wani bafade sukanufi inda akabashi amatsayin masaukinsa.... ⚔️🌍⚔️🌍⚔ Domin gyara sharhi ko bada shawara atuntuɓeni ta wannan layin👇🏻 07047530638. MORE COMMENT MORE TYPING⚔️⚔️ ƳAR GATAN MAMA✍🏻. ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ LABARI/RUBUTAWA KHADIJA S.SAMINU (ƳAR GATAN MAMA) Marubuciyar...... A WANI GIDA RAYUWAR MU! MAGANIN KAR AYI! nd now...... ⚔️WATA DUNIYA⚔️ ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* NA SADAUKAR DA WANNAN LABARIN GABA ƊAYANSHI GAREKI MAHAIFIYATA ABAR ALFAHARINA HJY.ƘURAINABU IDRIS YARO YAHYA,ALLAH YAJA DA RAI AMEEN😍😘💞💞 ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ SHAFI NA 9&10 ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Haka kuwa akayi sukaɗauki hanyar DEENUL-ISLAM wanda shine ainihin garinsu. Koda suka isa masaurauta yamma takawo jiki sosai domin daf ake da sallar magriba.Mutanen garin kowa sai barka da zuwa yake musu tare da miƙo gaisuwa ga SARAUNIYA SINIYYA da MUSLIM dakuma baƙuwar dasuka gansu tare wato GIMBIYA ZULMAT duk da awajan wasu daga mutanen garin ba baƙuwar fuska bace awajansu kasancewar ba inda ZULMAT bata shiga yaƙi domin kare addininsu na iyaye da kakanni. Mayaƙan garin kallonsu kawai sukeyi cike da mamakin meyakawo ZULMAT masarautar su. Basu tsinke da lamarinba saida sukaga sun sakko daga dawakansu sunnufi cikin masarauta. Nan Sarauniya tayi umarni da akawowa GIMBIYA ZULMAT kayan ƙwalam da maƙulashe,haka kuwa akayi cikin ƙanƙanin lokaci aka cika gaban GIMBIYA ZULMAT da kayanci da sha iri-iri,batare da ɓata lokaci ba tahaucin wanda zata iya sannan tabar wanda zata bari. Jim kaɗan aka kirayi sallar magriba inda kowa yatafi domin ya gabatar da ita banda GIMBIYA ZULMAT.Bayan SARAUNIYA SINIYYA ta gabatar da sallah ne tasa ashigo mata da GIMBIYA ZULMAT domin tanason suyi magana ta fahimta da ita. "Ina maiyiki sannu tare da fatan kinji daɗin kalar tarbar da mutane na sukayi miki" Sarauniya ke faɗin wannan magana sanda Zulmat tazauna agefenta bayan isowarta. "Yake wannan Sarauniya mai ɗumbin tarihi,haƙik'a nayi farin ciki mara misaltuwa da kalar tarbar dana samu awannan masarauta,kuma najinjina karramawa irintaki da mutanen da suke tare dake yake. Yake wannan sarauniya! Inamai sanar dake cewa naga alamun mamaki sun bayyana ƙarara afuskar mutanenki sanda idanuwansu sukayi tozali dani,ina tsoron kada su sakaki kikoreni daga wannan gari,domin nasan keɗin kinabin maganar mabiyanki aduk sanda suka kawo miki shawara kinabinta.....ina tsoron kada subaki shawarar dazata saka kice bazaku zauna tare danib......." Katseta Sarauniya tayi ta hanyar faɗin.... "Ki kwantar da hankalinki yake baƙuwata,inamai tabbatar miki babu wani wanda ya isa ya umarceni da korarki awannan garin gaba ɗaya,namiki alƙawarin zama tare damu duk rintsi duk wuya matuƙar zakibi dokokin da zamu gindaya miki kuma zaki rayu kamar yadda muke rayuwa,sannan kuma zakiyi abu guda ɗaya,inamai tabbatarmiki da zarar kinbi dokokinmu bamai rabamu harsai idan kece kika buƙaci hakan" "Waɗanne sharaɗai ne yake shugabata"? "Bawasu sharuɗai bane masu yawa,abu nafarko dai inamai farin cikin sanardake cewa....ALLAH shine mahaliccin dukkan komai kuma shikaɗai akeyiwa bauta,gareshi mukazo gareshi zamu koma,shikaɗai ne mahalicci shiya halicci mutum da aljan sama da ƙasa dama komai da komai. Sharaɗi na biyu kuma kiyimin alƙawarin zaki zauna damu da zuciya ɗaya,sannan bazaki haɗa kai da wasu afarmakemuba,idan kika saɓa alƙawari zamu yaƙeki" Nisawa ZULMAT tayi sannan ta jefi Sarauniya da tambaya kamar haka.... "Shin wane abune guda ɗaya da kikafaɗa acikin sharuɗanki wanda ayanzu banji kin maimaita dashi ba"? "Yake baƙuwata! Ba wani abu bane guda ɗayan dana manta banfaɗa ba sai.....Inamai umartarki daki zauna damu bisa gaskiya da amana,kada kicutar dako sauro dake rayuwa awannan gari balle wani bawa dayake cikinsa" "Na yadda da duka sharaɗanki yake shugabata,sai dai guda ɗaya wanda sainayi tinani akansa.Sannan inamai neman alfarma guda ɗaya awajanki" Sarauniya SINIYYA ta kalli Gimbiya ZULMAT duba na tsanaki sannan ta kada baki tace..... "Shin wane sharaɗi ne baki yarda dashiba acikin sharaɗaina? Wace alfarma kike nema awajena"? ZULMAT ta gyara zamanta sannan tadubi SARAUNIYA SINIYYA tace....... "Sharaɗi ɗaya da banyarda dashi ba shi ne:Bazan musulunta ba kuma bazanyi rayuwa kamar yadda kuke yiba.Alfarmar danake nema kuma itace:Inason acanzamin masauki amaidani cikin mutane yanda kaɗaici bazai dame niba" Nisawa Sarauniya tayi tare da tsayawa takalli Zulmat tsayin wasu daƙiƙu sannan tace...... "Hmm! Yake jarumar baƙuwata,inamai farin cikin sanar dake abinda baki sani ba,inason kisa aranki shi ADDININ MUSULUNCI ba addini ne na takurawaba ba'ayiwa mutum tilas akansa harsai yaji aransa yanason shigarsa,dan haka ni bazan tilastamiki kishiga addininmu ba harsai idan ke dakanki kikai ra'ayi zanfi kowa jindaɗin hakan. Alfarmar da kika nema awajena kuma zanyimiki ita,zansa ashiga dake ɓangare-ɓangare dake kizaɓi inda kikeson zama da kanki,inafatan hakan yayi miki?" "Godiya nake yake wannan sarauniya mai tarin alkairai,bisa ga kyautatawar dakikamin naji inason zama tare dake har ƙarshen rayuwata sai dai inatsoron abu guda ɗaya wato babana,nasan idan SARKI ZALIMUZ-ZAMAN hankalinsa yakoma jikinsa zaibuƙaci dana koma mahaifata domin ayanzuma nasan bak'in ciki da ɓacin raine yasa ya koreni,ni kuma naɗaukarwa kaina alƙawarin yadda yatozartani sena tozartashi bazan sake masa biyayya ba kuma sena......" "Bana sanar dake abinda Allah maɗaukakin sarki yace ba yake wannan jarumar baƙuwa tamu?" MUSLIM ne yafaɗa yana riƙe da hannunshi inda yajingina jikin ƙofar dayake yana kallon SARAUNIYA SINIYYA da ZULMAT. Juyowa sukayi atare suna kallonsa sanda yake ƙarasa shigowa cikin turakar Sarauniya,bayansa MUSLIMAT ce hannunta ɗauke da kayan marmari. Murmushine ya bayyana kan fuskar ZULMAT sanda taga MUSLIM,sake dubansa tayi tare dacewa...... Bayan sunyiwa kansu mazauni ne MUSLIM ya fuskanci ZULMAT tare da cewa.... "Bismillahir'rahmanir'rahim! Allah maɗaukakin sarki yace: "Yanzu bakwa ganin idan kuka juya baya dagabin Allah zakuyi ɓarna abayan ƙasa ku yanke zumuncinku? waɗannan sune waɗanda Allah ya la'ancesu ya mayar dasu kurame ya makantar da idanunsu" (surat Muhammad:22,23), Waɗannan da suke warware alƙawarin Allah bayan anƙullashi,suke yanke abinda Allah yayi umarni da a sadar dashi kuma suke yin ɓarna abayan ƙasa,waɗannan la'ana ta tabbata garesu kuma mummunar makoma tasu ce" (Al'ra'ad :25) Ubangijinka ya hukunta cewa kada kubautawa kowa sai shi,kuma yayi umarni da a kyautatawa iyaye,idan ya kasance ɗaya daga cikinsu ko su duka biyun suntsufa alhali kana (raye)to kada ka gwalesu,kada ka kyare su,ka faɗamusu magana mai taushi,ka ƙasƙantar dakai garesu kariƴayin addu'a da cewa Allah kajiƙan su kamar yadda suka reneni ina ƙarami" Shiru yayi yatsaya yana kallon ZULMAT ganin yadda ta tsareshi da ido ko ƙiftawa batayi yace da ita.... "Kallon fa?" Wani ƙayataccen murmushi ta sakarmai tare da gyara zama sannan tace..... "Natsaya kallonka ne saboda yadda nake ganin wani kyawu yana sake fitowa daga cikin fuskarka lokacin da kakeyimin bayani,inajin wani farin ciki yana lulluɓeni sanda zazzaƙar muryarka take bayanin,sedai har yanzu ban fahimci inda ka dosa ba,dan haka cigaba" GIMBIYA ZULMAT tagama maganar tana kashewa MUSLIM idanu. SARAUNIYA SINIYYA ce takai dubanta inda MUSLIMAT ke zaune tahaɗe rai tayi kicin-kicin alamun kishin Muslim sun bayyana ƙarara akan fuskarta. Murmushi MUSLIM yayi jin abinda ZULMAT tace dukda cikin ransa kalamanta basu wani yimai daɗiba kasancewar bashi kaɗaine wajanba amma yayi murmushi sannan yace..... "Daga Abu Musa Mugira ɗan Shu'ubatu Allah ya yarda dashi daga Annabi (S.A.W)yace:"Lallai Allah ta'ala ya haramta muku saɓawa iyaye,da rowa da neman karɓar dukiyar mutane ta hanyar gadar zare,da binne ƴaƴa mata,kuma ya haramta muku yaɗa jita-jita da yawan roƙon mutane da ɓarnatar da dukiya", (bukhari da muslim ne suka ruwaito) Sannan......." "Wai kai bazaka faɗi komai ba se kada asaɓawa iyaye ne? suma fa iyayen suna abinda baidaceba kasani,inba hakaba yaza'ai babana ya kore ni daga mahaifata?bayan banyimai wani laifi ba? sannan kace bazan ɗauki fansa akansa ba" ZULMAT takatse shi da faɗin hakan. Gaba ɗayansu suka juyo suka kalleta jin tambayar da tayi.MUSLIMAT ce tai karaf tace.......... ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Domin gyara sharhi ko bada shawara atuntuɓeni ta wannan layin......🙌🏻🙌🏻 07047530638 MORE COMMENT MORE TYPING. ƳAR GATAN MAMA✍🏻. ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ LABARI/RUBUTAWA KHADIJA S.SAMINU (ƳAR GATAN MAMA) Marubuciyar...... A WANI GIDA RAYUWAR MU! MAGANIN KAR AYI! nd now...... ⚔️WATA DUNIYA⚔️ ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* NA SADAUKAR DA WANNAN LABARIN GABA ƊAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA ALLAH YAJA DA RAI YAƘARA LAFIYA AMEEN. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ SHAFI NA 11&12 ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Na sadaukar da wannan shafin baki ɗayanshi gareki AUNTY SAILUBA Allah yabar ƙauna😘😘Son So fisabilillahi😍😍. Comment ɗinki nasani nishaɗi😘😘⚔️⚔️⚔️. ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ Gaba ɗayansu suka juyo atare suna kallonta jin tambayar da tayi.MUSLIMAT ce tai karaf ta kalleta tare cemata...... "Shin bakiji bayanin da akayimiki game da girman iyaye bane kike wannan kalami akan mahaifinki?ko kuma har yanzu baki gane bane ba" Murmushi GIMBIYA ZULMAT tayi mai sauti wanda saida fararen hak'oranta suka bayyana kana ta kauda kai daga kallon MUSLIMAT tamaida kallonta ga SARAUNIYA SINIYYA tace ..... "Yake shugabata! Alfarmar canzamin masauki da kikace zakiyi ɗazu inamai tabbatar miki dana samu masaukin da nakeson zama" Kallonta SARAUNIYA SINIYYA tayi tare da maidata mata murmushi mai sauti sannan tace..... "Ina ne masaukin naki ya baƙuwata?" "Inda JARUMI MUSLIM yake da zama nan ne masaukin naw....." "A'uzu billahi minash'shaiɗanir'rajeem! Kin saɓa lamba,domin baki faɗi abinda zai yuwuba sam! Inaso tun wuri kijanye ƙudurinki akan MUSLIM domin zuciyarsa bashi da gurbin da zai ajjeki acikinta,zuciyarsa tawa ce ni ɗaya babu wajan ajjek....... " MUSLIMAT ce tsaye kan ZULMAT tariƙe ƙugu tana haki kamar wadda tai tseren doki. Wata sassanyar ajiyar zuciya ZULMAT ta sauke yayinda ƙasan zuciyarta ke ayyana mata wasu abubuwa game da MUSLIM dama ita kanta MUSLIMAT ɗin,ƙasa ta sake yi da kanta tare dasa hannunta tana jujjuya zoben azurfar dake maƙale aɗan yatsanta. SARAUNIYA SINIYYA kam cike da ɓacin rai takalli MUSLIMAT tare da faɗin....... "Ashe daman baki da hankali? Meyasa bazaki magana cikin tausasawa ba? Kifita daga nan kibamu guri bamason mukuma jin wata magana daga bakinki....... ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Cike da ƙwarin gwiwa NUJBEER ƊAN NAJABURU ya amsa tare da bin wani bafade suka nufi inda aka bashi amatsayin masaukinsa. Bayan tafiyarsa SARKI KAMALUD-DEEN yai shiru inda ƙwak'walwarsa tashiga kaikawo game da lamarin wannan tsoho,a haka dai zaman fada nayau yatashi jiki asanyaye domin shi lamarin tsohon yafirgita shi,kallon waziri sarki yayi tare da faɗin..... "Umm! Shikuwa wannan bawan Allah awaɗannan shekarun nasa mai yake jira inba mutuwarsa ba?" Waziri ne yayi gyaran murya tare da gyara zamansa tukunna yasadda kansa ƙasa yace.... "Allah yaja zamaninka! Duba da cewa wannan bawan Allah kafiri ne,kuma yatafi da rayuwarsa gaba ɗaya wajan neman duniya,kaga kuwa dan yanzu yace yanason zuwa ɗaukar wannan TAKOBI ba abin mamaki bane ba Allah ya temake ka" Koda sarki yaji haka sai yayi shiru sannan yace..."Allah yasa mu dace" da "Ameen" Waziri ya amsa tukunna yayiwa sarki sallama shima. Haka rayuwa taci gaba da tafiya awannan gari na SARKI KAMALUD-DEEN suna tare da tsoho NUJBEER ƊAN NAJABURU suna jiran sabon wata yakama inda awannan lokacinne zasu tafi WATA DUNIYA domin su jarraba sa'arsu ta ɗaukar TAKOBIN KOGON WATA DUNIYA wato TAKOBIN ƊAUKAKA. Wannan kenan...... ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Koda MUSLIMAT tafito ɓangarensu tawuce zuciyarta na tafasa kamar ta tsaga ƙirjinta tafito dan baƙin cikin abinda akai mata,yauce rana ta farko da Sarauniya ta taɓa haɗe mata fuska tare da korarta daga turakarta,yauce rana tafarko dataji tanajin haushin MUSLIM har cikin zuciyarta,yauce rana ta farko dataji baƙin cikin dabata taɓajin irinshiba domin kuwa yaune ta tabbatar da tana da kishi kamar sauran mata,'yama za'ai sarauniya takawo wata ƙasurgumar kafira sannan ta kusantata da Muslim?'tambayar da tayiwa kanta kenan batare da tanasa ran akwai mai bata amsaba.Haka daren yau ya ƙare mata cike da saƙe-saƙe akan lamarin ZULMAT domin gani takeyi soyayyace tsakanin MUSLIM da kuma ZULMAT ɗin. Bayan fitarta kuwa aɓangaren su sarauniya,sarauniya lallaɓa gimbiya zulmat tayi akan tayi haƙuri tazauna aɓangarenta zataimata duk abinda take buk'ata. Ankai ruwa rana kafin ta yarda,domin tirjewa tayi ita lallai da Muslim takeson rayuwa awannan garin domin ta fuskanci shi kaɗaine yake iya tausasa harshensa idan zaiyi magana,saɓanin yadda kowa yake yi agadare.Saida Muslim yasa baki tukunna tayadda ta zauna anan. Wannan kenan..... ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Sarki ZALIMUZ-ZAMAN ya haɗa gumi sosai kamar wanda aka tsamoshi daga cikin ruwa saboda ruɗanin daya shiga sanda yadda ƴarsa ZULMAT na yaƙi tana kare maƙiyansa. Cikin ɓacin rai da ƙunar zuci yai fatali da kayan tsafinnasa yafito domin ganawa da mutanen dake son ganinsa..... Bai sake tsinkewa da lamarin ZULMAT ba saida yazauna yana dube-dubensa,nan ya hangi yadda ZULMAT tasaki jiki tazauna cikin maƙiyansa suna yimata wasu zantuka(magana akan musulunci) daban wanda seda yaji kamar yakashe kansa dan bak'in ciki.Baiyi wata -wata ba yajuya madubin tsafinsa tare da rufe idonsa yana karanto wasu ɗalatsiman tsafi masu wahalar rik'ewa. Gimbiya ZULMAT tana tsaye gefen tagar ɗakin da akabata amatsayin masaukinta wanda shike kusa da turakar Sarauniya SINIYYA taji masarrafar sarrafa sautinta wato kunnenta na amsa amon kiran da mahaifinta SARKI ZALIMUZ-ZAMAN yake mata,sake gyara tsayuwarta tayi sosai nan ta tabbatar da gaske nemanta yake yi,ko ba'a faɗamata ba tasan hankalinsa atashe yake domin tana da tabbacin yaga duk abinda yake faruwa da ita.Rufe idonta tayi tare da ɗaga ƙafarta tagama shigowa cikin ɗakin,gadan -gadan tanufi bangon ɗakin kafin ƙiftawar ido segata agaban sarki ZALIMUZ-ZAMAN...... "Cikin girmamawa da neman afuwa gareka babana mai mulkin kafiran wannan nahiya tamu" Gimbiya ZULMAT ta faɗa tanamai sadda kanta ƙasa lokacin data buɗi ido taganta agaban sarki zalimuz-zam.Cikin matsananciyar damuwa da ɓacin rai sarki zalimuz-zaman yaɗago yadubeta da rinannun idanunsa wanda launukansu yakoma zuwa jajaye kana yace...... "Inamai tinatar dake da kakkausar murya cewa....Bana amince da komawarki cikinsu domin idan kinga abu zai cutar dasu ki temake suba,a'ah! Na yadda da zuwanki ne saboda inason kisamu sauk'i wajan ɗaukomin TAKOBIn nan,domin allon tsafina ya tabbatarmin da MUSULMAI ne kaɗai zasu iya ɗaukar wannan TAKOBI,ke kuma zaki shiga cikinsu ne domin idan sunɗauka ki yak'esu da k'arfin tsafina da naki ki karɓota ki kawomin ita,ta hakanne zaki samu damar mallakar wannan masarauta kamar yadda nai miki alk'awari amma kinje kintsaya kina sakarci da rashin...." "Cikin neman afuwa da tausasawa nake son nayima bayani yakai babana! Shin wane sarki ne ko sarauniya dake faɗin wannan duniya zaibaka tsoro? Kaine fa kake da mugayen matsafa da hatsabiban Aljannu wanda idan kayi niyya zaka iya sakawa suk'arar maka da kowa dake wannan duniya,shin mene kuma zaisa kadinga kokwanto? Kai ne ka mallaki tsofaffin gumaku wanda idan kaso atsafinka saika dawo dasu sababbi yanzu,shin wane mai mulkine zaija dakai? Ya babana! Inamai farin cikin sanar dakai cewa....Lallai burinka zai cika matuk'ar ina numfashi adoron ƙasa bazaka faɗi ba,koda kuwa kafaɗi bazakasha ƙasaba yakai babana! Abu guda ne nakeson sani,shin yaushene za'afita domin zuwa WATA DUNIYA 🌍domin inason nasani kar lokacin yayi asamu wata matsala" Nisawa sarki ZALIMUZ-ZAMAN yayi tare da samun waje ya zauna dan se yanzu ne yasamu nutsuwa jin yadda ƴartasa take kambama girmanshi tanasashi nishaɗi sannan yace...... "Hhhhh! Ina alfahari dake ZULMAT,domin kin ɗakko wayo da dabarata dakuma mugunta irin tawa,ke inama tinanin ke kinfini iya tsara komai dan haka nabar komai ahannunki. Batun ɗaukar TAKOBI kuma sabon wata mai kamawa ne,yau muna ashirin ga wata aƙa'idar tafiya WATA DUNIYA🌍zaku shigeta ne ɗaya ga watan dazai kam ......... ⚔️🌍⚔️🌍⚔️🌍⚔️🌍 Inajin comment ɗinku masu comment na ⚔️WATA DUNIYA⚔️marasa comment kuma ina sane daku wallahi zanyi abinda yadace🥺. Allah yasa mugama da duniya lafiya😘💃🏻💞💞 Domin yabo sharhi ko bada shawara atuntuɓeni ta wannan layin.....👇🏻 07047530638💞💞. ƳAR GATAN MAMA✍🏻. ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ LABARI/RUBUTAWA KHADIJA S.SAMINU (ƳAR GATAN MAMA) Marubuciyar...... A WANI GIDA RAYUWAR MU! MAGANIN KAR AYI! nd now...... ⚔️WATA DUNIYA⚔️ ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ SHAFI NA 13&14 ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ 🔥WANNAN LABARI ƘIRƘIRARREN LABARI NE,MALLAKINA NE,BAN YARDA WANI KO WATA YAJUYAMIN LABARI BA TAKOWACE SIGA.🔥 🔥🔥ALLAH YASAKAMA IYAYENMU DA MAFIFICIN ALKAIRI YASADASU DA RAHAMA DUNIYA DA LAHIRA YA HAƊASU DA ANNABIN RAHAMA AMAFARKINSU KO AFARKE,WANDA IYAYENSU SUKA RIGAMU GIDAN GASKIYA ALLAH YAJIƘANSU YASA CAN TAFIMUSU NAN YA KYAUTATA NAMU ZUWAN🔥🔥 🔥🔥🔥YAU MUNWAYI GARI MUNTSINCEMU ASABUWAR SHEKARA😭😭ALLAH MUNROK'EKA DAN ISARKA DAN KAƊAITAKAR SARAUTARKA ALLAH KA YAFEMANA KURA-KURAN DA MUKA AIKATA WANDA MUKA SANI DA WANDA BAMU SANIBA NA SHEKARAR DATA GABATA KASA MUYI AIKI NA GARI ASABUWAR DATA FARA DAGA YAU,ALLAH KASA MUCIKA DA KALMAR LA'ILAHA ILLALLAHU MUHAMMADUR'RASULILLAHI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA😭🔥🔥🔥 🔥🔥🔥ALLAH YADDA NAFARA RUBUTA WANNAN LABARI LAFIYA ALLAH KASA NAGAMASHI LAFIYA,ALLAH KASA NA RUBUTA ABINDA ZAI AMFANENI YA AMFANI AL'UMMATA,ALLAH IDAN HAR ARUBUTUNA ZAN RUBUTA ABINDA ZAI ƁATAR DA AL'UMMAR ANNABINKA ALLAH KA KARYA BAKIN ALƘALAMINA NA KASA,ALLAH KARKA BANI DAMA KO IKON RUBUTA ABINDA BA DAI-DAI BA NIDA DUKKAN WANI MARUBUCI DAKE FAƊIN WANNAN DUNIYA,ALHAMDULILLAHI 🔥🔥🔥 ZALIMUZ-ZAMAN ya kece da wata mahaukaciyar dariya wadda seda ɗakin ya girgiza sannan yace da ita........ "Hhhh! Ina alfahari dake ZULMAT,domin kin ɗakko wayo da dabarata da kuma mugunta irin tawa,ke inama tinanin ke kinfini iya tsara komai dan haka nabar komai ahannunki. Batun ɗaukar TAKOBI kuma sabon wata mai kamawa ne,yau muna ashirin ga wata,aƙa'idar tafiya 🌍WATA DUNIYA🌍zaku shigeta ne ɗaya ga watan dazai kama" Gyara zama ZULMAT tayi tukunna tayi gyaran murya tasake duban babannata tace..... "Yakai babana! Inaso kasanar dani koda kaɗan daga cikin haɗarin dake cikin wannan kogo da za'a ɗauki TAKOBIn acikinsa" "Bamai faɗuwa bane!! Nace miki bamai faɗuwa bane haɗarin dake cikin wannan kogon,a'iya binciken dana ɗauki shekaru inayi naga tarin musibu kala daban-daban acikinsa wanda tsafin matsafin basa iyawa dashi,kuma bincike ya tabbatar da MUSULMAI ne zasu ɗauketa,sannan wajan ɗaukarta dolene seka ambaci sunan abin bautarsu tukunna zaka ɗauka" "Cikin zaƙuwa da son jin wannan sirri ya babana! Ina mai buk'atar ƙarin haske awannan bayanin naka,shin koda ba musulmi ba idan yakira sunan abin bautar musulmai zai iya ɗaukar wannan takobin?" "Hhhhh! Yaro yarone,haka batun yake yake kyakkyawar ɗiyata mai fikira da kaifin basira,ya tabbata koda ba musulmi bane mutum indai har ya isa inda wannan TAKOBI take sannan yakira sunan abin bautar musulmi da girmamawa to babu makawa zai ɗauketa,to amma abinda na fahimta anan yake ƴata! Na fuskanci waɗanda suka saka wannan sharaɗin sun sakashi ne saboda sui sanadin karya alk'awarin damukayi tsakaninmu da iyayenmu na cewa bazamu bar addininsu ba har ƙarshen rayuwar mu,tinda inhar zamuje ɗaukar abu mu nemi temakon abin bautarsu kenan watarana ma zamu yadda dashi kenan?" ZULMAT tayi murmushi mai sauti sannan tace.... "Inamai farin cikin sanar dakai cewa:Zanyi iya bakin k'oƙarina akan naga nakawoma wannan TAKOBI kota halin ƙaƙa,sannan inason ka kwantar da hankalinka ka kauda kai daga dukkan abinda zaka ga nayi kozakaji nace,komai kaga nayi nayishine domin kai,sannan inaso kasani bazasu taɓa yarda dani ba har se na nunamusu zan iya komai akansu sannan na nuna musu soyayya hakanne zaisa su yadda dani,zanyi duk me yuwuwa domin cikar burinka yakai babana" Tagama maganar tare da ajje hannunta akan wani tudu da suke zaune agabansa.Sarki zalimuz-zaman shima yaɗora hannunsa akan nata tare da jinjina mata kai alamar yayi mata alk'awari. Murmushi tayimai sannan tadoshi bangon ɗakin batare da ɓata lokaci ba se buɗe ido tayi awannan ɗakin da akabata amatsayin masaukinta.Bata tsaya yin komai ba tahaye makeken gadon dake ɗakin tare da kwantawa tana maida numfashi sannan ta tsunduma duniyar tinani ahaka bacci yai gaba da ita. Koda gari ya waye kowa yana ta sabgarsa inda Sarauniya tasa aka kaiwa ZULMAT kayan ci dana sha kala daban-daban,bayan taci tasha ne tagama shiryawa sannan tafito domin zuwa wajan sarauniyar,lokacin data iso inda sarauniya take MUSLIM yana gefenta suna gaisawa inda MUSLIMAT ke zaune itama tana jawa sarauniya yatsun ƙafarta. "Ina fatan kintashi lafiya ya shugabata" Abinda ZULMAT tafaɗa kenan sanda ta ida ƙarasowa inda suke gaba ɗayansu. Faɗaɗa murmushinta sarauniya tayi tare d agyarawa daga kishingiɗen da take sannan ta miƙawa ZULMAT hannunta na dama tace..... "Rabon ubangiji ya tabbata agareki ya jarumar baƙuwata!" Bamusu tabata hannunta tare dayimata murmushi sedai bata bata amsaba.SARAUNIYA SINIYYA taji daɗin yadda taga ZULMAT dan haka tanuna mata kusa da ita tare da mata alamun ta zauna. Bata musaba ta zauna agefen sarauniyar sannan tadubi MUSLIM tana wani ƙayataccen murmushi mai kwantar da hankalin masoya tace....... "Nayi farin cikin ganinka lafiya cikin kyakkyawar kama yakai wannan jarumi ma'abocin kyakkyawar mu'amala" Saida MUSLIM yasaci kallon MUSLIMAT yaga yadda tahaɗe rai sannan ya saisaita fuskarsa ya kalli ZULMAT yace..... "Lafiya nake,yaya kwanan baƙunta" "Aini banyi zama kamar yadda baƙi suke zama ba,domin baƙi suna zamane aɗarare basa sakewa,basa samun sakin fuska daga iyayen gidansu,ana ajjesu awajen da ba'a shigarsa harsai irinsu sunzo ake karkaɗe ƙurar cikinsa abasu su zauna,amma ni anbani muhalli wanda yake abin ƙawatawa da birgewa,nikam wannan wane irin karamci ne?" MUSLIMAT ce tayi murmushi tare da duban ZULMAT tace..... "Inamai neman afuwarki bisa rashin fahimtar data shiga tsakaninmu jiya,sannan inamai farin cikin sanar dake cewa: Aishi baƙo mutumne wanda ya kamata akarramashi abashi kulawa da duk wani abin buk'ata harsai yaji inama karya bar wannan guri daya zauna" Murmushi zulmat tayi mata sannan tace.... "Hmm! Wato kudai nafuskanci har rige-rigen aikata alkairi kukeyi ko? naga kuduka kuna ƙoƙarin kyautatamin kuma kun ciyar dani daga abubuwa masu daɗi" MUSLIMAT ce tayi murmushi sannan tace.... "Bana sanar dake wani abuba yake jarumar baƙuwarmu mai sanyin halaye?" "Ina sauraronki gwanayen iya zance" Tabata amsa tana murmushi. "Allah maɗaukakin sarki yace:"Ba za ku kai ga matakin ƙarshe na aikin alheri ba har sai kun ciyar daga abinda kukeso" (ali'imran),sannan yasake cewa:"Yaku waɗanda kuka bada gaskiya ku ciyar daga nagartattun abubuwan da kuka samu kuma daga abinda muka fitar muku daga cikin ƙasa,kada ku ɗauki abinda bashi da amfani daga dukiyoyinku(kuyi sadaƙa dashi)"(baƙara ),wato dai ana nufin kada kayi sadaƙa da abinda yake bashi da kyau sai dai kayi da kyakkyawa.Faɗin ubangiji kenan to ta yaya kike tinanin zamu sauke ki awaje mara kyau sannan mubaki abu mara kyau? dole indai muna aiki da abinda muka karanta daga abinda Allah ya saukar mana(ALƘUR'ANI)mu baki abinda mukeso domin kasancewa munji daga majiya mai k'arfi cewa'imanin ɗayanku ba zai cikaba har sai yasowa ɗan uwansa abinda zaisowa kansa' Ina fatan kingane" MUSLIM ne yatari numfashin MUSLIMAT tare da cewa"Haka kuma Allah maɗaukakin sarki yace:"Wanda duk ya aikata wani aiki na alheri dai dai da ƙwayar zarra zai ganshi" (zilzilah)haka kuma yasake cewa:"Wanda duk yayi aiki na gari don kansa"(ALJASIYAH). Kinga kuwa wannan kyautatawa da mukai miki kanmu muka yiwa domin ya tabbata duk wanda yayi wani aiki nagari kansa yayiwa,hakanan kuma hanyoyin aikin alheri suna da yawa" GIMBIYA ZULMAT ta kallesu ɗaya bayan ɗaya sannan tayi murmushi ta dubi SARAUNIYA SINIYYA tace...... "Kinyi dace da ƴaƴa nagari masu yiwa baƙi magana mai daɗi,sedai ke yau bakice dani komai ba". Kallonta sarauniya tayi sannan tagyara zamanta tace....... ⚔️🌍⚔️🌍⚔️🌍 Domin gyara yabo sharhi ko bada shawara atuntuɓeni ta wannan layin👇🏻 07047530638. 'YAR GATAN MAMA✍🏻. ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ LABARI/RUBUTAWA KHADIJA S.SAMINU (ƳAR GATAN MAMA) Marubuciyar...... A WANI GIDA RAYUWAR MU! MAGANIN KAR AYI! nd now...... ⚔️WATA DUNIYA⚔️ ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA,ALLAH YAK'ARA MIKI LAFIYA DA TSAWON KWANA🥰💞💞. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ SHAFI NA 15&16. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ ......Kallonta SARAUNIYA SINIYYA tayi sannan tagyara zama tace.... "Tom ni sedai naimiki cigaban maganar MUSLIMAT idan kinaso,inba hakaba banda abin cewa" "Kome zaki faɗa inaso ya shugabata! Domin inajin daɗin yadda kika zauna dani haka kike hira dani babu tsangwama babu wani abinƙi sai kyautatawa" Murmushi sarauniya tayi sannan tace... "Daga Anas Allah ya yarda da shi ya ce: Abu Talhatu Allah ya yarda dashi ya kasance shine mafi ansar na madina dukiya ta dabino(yawan dukiya)Kuma dukiyar da yafiso daga dukiyoyin nasa itace BAIRAHA'U (wato lambunsa),wanda ya kasance yana kallon masallaci,kuma Manzon Allah (SAW)ya kasance yana shiga lambun yasha daga ruwansa mai daɗi. Anas yace: Lokacin da wannan aya ta sauka wato"Ba za ku kai ga matakin ƙarshe na kyakykyawan aiki ba sai kun ciyar daga abinda kukeso" Sai Abu TALHA ya tawo wajen Manzon Allah (SAW)yace: Ya rasulillahi Allah ya saukar maka da aya da tace:"Ba za ku kai ƙarshe na aikin alheri ba harsai kun ciyar daga abinda kuke so",Ni kuma daga cikin abinda na mallaka nafi son lambuna mai suna BAIRAHA'U.Saboda haka na sanyashi sadaƙa saboda Allah maɗaukakin sarki inamai ƙaunar ladan abin daga Allah maɗaukaki.Dan haka ka sanyashi inda Allah ya shiryar da kai,sai manzon Allah(SAW)yace:Madalla,wannan dukiya ce mai matuƙar daraja,wannan dukiya ce mai daraja.kuma naji zancenk..." "Inada tambaya gareki yake wannan sarauniya mai girma da daraja,idan na fahimta mutumin dukiyar tasa ya ɗauka ya bayar saboda jin abinda abin bautarku yace? hakanne yasa kuma kuke kyauta da abubuwan da kukeso? to kuma lambun nasa ya aka rabashi ga al'umma bayan ya bayar da ita?" SARAUNIYA SINIYYA tayi ƙayataccen murmushi zuciyarta tanajin daɗin yadda GIMBIYA ZULMAT tasaki jiki tanajin zantukansu kuma alamu sun nuna zata iya musulunta tinda har take sauraron abinda Allah ya saukar musu....... Saida tagama tinaninta tana sakin murmushi ajejjere sannan ta dubi gimbiya ZULMAT tace.... "Kamar yadda kikaji ya bayar da BAIRAHA'U(wato lambunsa)saboda jin abinda Allah maɗaukakin sarki yace,to amma bayan Annabi (SAW)yagama yabamasa sai yace dashi:"Kuma naji abinda kace,amma ina ganin yafi kyau ka sanyashi ga makusantanka" Sai yace"Haka zanyi ya Rasulillahi" Sai Abu TALHATU ya raba wannan dukiya tsakanin ƴan uwansa da ƴaƴan baffansa.(Bukhari da muslim ne suka ruwaifo shi). Kamar dai yadda kika gani muna koyine da kyawawan ayyuka kuma muna girmama baƙo. Baga al'umma aka fitar dashi aka raba ba,an rabashine ga makusantansa domin ya tabbata cewa karka fitar da abinda ka mallaka har sai kafara bawa makusantanka,idan kabasu ne sun wadata,saika bayar ga jama'a domin suma su samu" GIMBIYA ZULMAT ta kishingiɗa gefen MUSLIM sannan tayi murmushi tace..... "Lallai bazan bar wannan gida mai tarin karamci ba harsai bayan raina,domin kallon wannan ɗan naki MUSLIM kaɗai yana sanyani nishaɗi,gashi kema kina yimin zantuka wanda suke sanyawa naji farin ciki sai dai ina tsoron abu guda" MUSLIMAT tai karaf tatari numfashin ZULMAT tare da faɗin.... "Ina fatan dai bason MUSLIM ne ya kamaki ba? Domin kuwa tun muna ƙanana akabashi ni nice wadda zai aura idan muna da numfashi,kuma wane abune wanda kike tsoro?" Wani matsiyacin murmushi ZULMAT ta saki tare da busar da iska ta bakinta ta lumshe dara-daran idanunta sannan ta buɗesu fes akan MUSLIMAT takashe mata ɗaya sannan tace..... "Hhhh! Banda abinki wace macece zatayi tozali da kyakkyawan namiji kamar MUSLIM bataji tana sha'awar ya kasance abokin rayuwarta ba? Hakan yasa tun lokacin da idona ya sark'e da nasa naji inason nasake ganinsa,shiyasa da mahaifina ZALIMUZ-ZAMAN yayi umarni da akasheshi ni kuma na tseratar dashi saboda inaso nadinga ciyar da idanuwana duk lokacin da suka buk'aci hakan, abu guda da nake tsoro yakasu gida biyu:gida na farko shi ne BABANA ZALIMUZ-ZAMAN,gida na biyu kuma shi ne abinda zai rabani da MUSLIM annurin rai..." Wani tari ne bazato yasark'e MUSLIMAT wanda seda MUSLIM yamiƙo mata gorar ruwa tasha inda ruwan nazuwa maƙogaronta taji wani ɗaci mara misaltuwa wanda hakan yai sanadiyar furzar da ruwan ya sauka akan fuskar ZULMAT....... ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Duk wani shiri da NUJBEER ƊAN NAJABURU zaiyi na tafiya 🌍WATA DUNIYA🌍yagamashi jira yake kawai sabon wata yakama domin yau saura kwana tara kenan alissafinsa,kullum yakan shiga wajan sarki KAMALUD-DEEN domin yaji ina suka kwana azancen tafiyar..... Wannan kenan. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Koda gimbiya ZULMAT tafita daga turakar ZALIMUZ-ZAMAN zama yayi dirshan adandaryar ƙasa sannan yaɗaga kansa sama yasa hannunsa ɗaya aƙasa tare da dukan wajan.Dukan wajan keda wuya sega ƙasar wajan ta tsage tarabe zuwa gida biyu,batare da ɓata lokaci ba ZALIMUZ-ZAMAN yashige ciki inda ƙasar takoma yadda take tahaɗe tazama guda ɗaya. Koda yashiga ciki........ ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Domin gyara,sharhi ko bada shawara a tuntuɓeni ta wannan layin...👇🏻 07047530638. MORE COMMENT MORE TYPING. SANARWA🥳🥳🥳 ⚔️WATA DUNIYA⚔️HAR YANZUFA BAMU SHIGA WATA DUNIYAR BA,MUJE ZUWA AMMA SAI KUNYI HAƘURI DANI DAN ALLAH.SANNAN DAN ALLAH INA BUƘATAR ADDU'ARKU GAREKI"ALLAH KA AZURTA BAIWARKA KHADEEJAH DA LAFIYA MADAUWAMIYA KABATA IKON AMFANI DA LAFIYAR DAN ARZIK'IN MASOYINKA"ABINDA ZAKUCE KENAN,DAN GIRMAN ALLAH.NAGODE😍🥰💞💞. ƳAR GATAN MAMA✍🏻. NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA,ALLAH YASHIGA LAMURANKI BABATA🥳🥳. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ SHAFI NA 17&18. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Koda yashiga ciki bai sauka ko'inaba sai kan wani mulmulallen hamshaƙin wani dutse mai azabar kyau da ɗaukar ido wanda idan kayi tozali dashi saika ɗan kanne idonka saboda yadda yake barazanar kashe idanun,yana da girman gaske wanda girmansa zaikai girman ɗaki guda,gefen dutsen wasu gumaka ne masu matuƙar muni da baƙi na tashin hankali.Zamansa kan dutsen keda wuya wajan yayi wata girgiza tare da juyawa sama ya koma ƙasa,lokaci guda wata guguwa tashigo wajan mai azabar k'arfi,manya-manyan halittun aljanu ne suka fara tittiɓowa takowa ce hanya dake wajan. "Sai kai sarki mai nisan zamani,ka gagara ka cika ka bunƙasa ka take duk wanda ba masoyinka ba,shin wace buƙata ce dakai haka daka buk'ci ganinmu da gaggawa? Sauraronka muke yakai wannan sarki mamallakin aljannu da bokayen dake faɗin wannan duniya!!" Wani daga cikin aljanun yafaɗa da muryarsa mai rikitarwa da sanya tsoro azuciyar mutane.ZALIMUZ-ZAMAN ya kece da wata mahaukaciyar dariya wanda saida yaɗauki daƙik'a hamsin yanayi tukunna yagimtse bakinsa ya murtuke fuskarsa kamar wanda yaga mala'ikan mutuwa yace......... "Hhhh! Ina Alfahari da ƙarfin ikon danake dashi dakuma ɗiyata ZULMAT wadda zuciyarta take ataurare,tana da zafi da kuma tsauri akan ƙudurinta.A....Awannan lokaci inason sanar daku cewa ƴata zulmat ta tafi garin DEENUL-ISLAM domin haɗa kai da maƙiyanmu maƙiya addininmu domin ta shiga jikinsu ta ɗaukomin ⚔️TAKOBIN WATA DUNIYA⚔️wato takobin ɗaukaka,sanin kanku ne abinciken da manyan matsafan wannan duniya tamu sukayi sungano cewa farkon wata makullin ƙofar wata duniya ke buɗewa kuma awannan lokacin ne mai buƙatar wani abu daga cikinta yake shiga domin shigar ƙudurinsa,kuma sanin kankune kwana goma sha biyar za'ayi acikin duniyar afito,domin makullin ƙofar zai rufene idan wata yara ba! Shin wane taimako zakubawa zulmat domin tazama itace wadda zata ɗauki wannan takobin?" Babban cikinsu wanda ya bayyana amatsayin wani gwoggwon biri baƙiƙk'irin mai azababben muni da ban ƙyanƙyami ne ya buɗe mummunan bakinsa tare da gyatsine fuskarsa taƙara muni ninki huɗun wanda yake dashi da ya kece da wata sheɗaniyar dariya wadda seda ilahirin wajan ya haɗe jikinsa yayi baƙiƙk'irin tare da sanyawa sauran aljanun dake wajan suka saki wani azababben ihu tare da haɗa baki wajan faɗin..... "DUJAALA!!!" ALjanin da aka kira da DUJAALA! Ya tsagaita da dariyar da yakeyi sannan ya dubi ZALIMUZ-ZAMAN da razananniyar murya yace........ "Bamusan lokacin da kazama me gajeren tinani kamar sauran mutane ba,sanin kanka ne kai mutum ne amma ba kamar sauran mutane ba,ya...ya za'ai kabar yarinyarka ta shiga cikin mutanen da ba addininmu ɗaya da ita ba?Bayan kasan mutanen nan suna ɗauke da wani shu'umin tsafi wanda mu kafatanin kafirai bamu dashi yanda idan ɗaya daga cikinmu ya shiga cikinsu sai sunyimai abinda mawuyacine ya kuɓuta se sun jashi ya karya alƙawarin dake tsaninsa da iyaye da kakanni..... ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Wani tari ne bazato ya sarƙe MUSLIMAT wanda seda MUSLIM yamiƙo mata gorar ruwa tasha inda ruwan na zuwa maƙogaronta taji wani ɗaci mara misaltuwa wanda hakan yai sanadiyar furzar da ruwan,koda ruwan yafito bai sauka ko'inaba sai fuskar gimbiya ZULMAT. A mamakance ZULMAT take dubanta sanda tafurzo mata ruwan domin ita tahaƙik'ance azuciyarta da gangan MUSLIMAT tazuba mata afuska babu wata ƙwarewa da tayi,afusace ta kalleta da niyar nuna mata kuskurenta na ɓatamata fuska ta tsinkayi muryar SARAUNIYYA SINIYYA tana nacewa...... "Nikam kuyimin hak'uri zanshiga daga ciki domin gabatar da sallar walha" GIMBIYA ZULMAT tadawo da hankalinta ga sarauniya tace.... "Nasha ziyartar garuruwan musulmai kuma naga suna sallali biyar ne arana daga wannan lokaci zuwa wannan lokaci amma banga sunayi a irin wannan lokacin da kikace zakiyiba!Shin ko su sunrage watane daga wanda aka saukar muku" Murmushi sarauniya tayi sannan ta numfasa tabata amsa kamar haka..... "Hmm! Hakane zancenki kyakkyawar bak'uwata,haƙiƙa ubangiji mamallakin kowa da komai ya saukarmana da salloli guda biyar ne ta hanyar Annabinsa,kuma wannan guda biyar ɗin sune sallolin farillah wanda suke wajibi akan dukkan wani musulmi saidai munayin nafilfili alokuta mabanbanta domin cike inda baicikaba afarillarmu kasancewar ba wanda yakeyin dai-dai sai Annabin Allah maɗaukakin sarki.Yazo daga Abu Zarri Allah ya yarda dashi cewa Manzon Allah (SAW)Yace:Idan kuka wayi gari kowace gaɓa daga ɗayanku akwai sadaƙa daga gareta.Domin kowane tasbihi sadaƙa ne,kowace hamdala sadaƙa ce,kowace hailala sadaƙa ce,kowace faɗar ALLAHU AKHBAR sadaƙa ce,yin umarni da kyakkyawan aiki sadak'a ne,hani ga mummunan aiki sadaƙa ne.Amma yin raka'a biyu da walha zai iya tsayawa amaimakon wannan.(Muslim ne ya ruwaitoshi). To kinji yadda zancen yake hakan yasa nakeso nayi raka'a biyu yanzu domin nasamu wannan ladan" "Yayi kyau,nikam me yasa idan zakui zancen kuke tsarashi fiye da yadda mukeyin namu" "Saboda mu mun kasance muna faɗine daga abinda Allah maɗaukakin sarki yafaɗa,shi kuma zancen Ubangiji mai girma da buwaya atsare yake babu gyara acikinshi". GIMBIYA ZULMAT ta numfasa tare da gyara zamanta tukunna tace.... "Tom shiga kiyi sallar inyaso nima zanshiga daga ciki kafin kidawo" Shiga SARAUNIYYA SINIYYA tayi inda ZULMAT ta tashi tanufi masaukinta dake daura da ɗakin sarauniyar tabar MUSLIM da MUSLIMAT azaune. "Me yasa kake sakarwa wannan kafirar fuska hartake cewa tana sonka baka ɗauki wani mataki ba? Shin ko kaima ka kamu da sontane bamu sani ba? Meyasa! Meyasa!!" MUSLIMAT ta faɗa cikin mabayyanin ɓacin rai jikinta har rawa yake inda idanunta suka kaɗa sukayi jawur se wura hanci takeyi. "Allah yaƙara miki lafiya jarumar masoyiyata! Banda abinki me ZULMAT take dashi wanda baki dashi da zaisa na sota? Shin kodai kinfara tantama game da sonda nake miki?amatsayinki na macen da tasan kanta bazaki iya kishi da ZULMAT bane?" MUSLIM ya bata amsa fuskarsa ɗauke da murmushi tare da kashe mata ido ɗaya.Kallonsa tayi tare da wurga masa wata narkekiyar harara wadda saida ya tintsire da dariya sannan tace.... "Dole ka kalleni kayi dariya tinda kana shirin cin amanata saboda wata ƙasurgumar kafira wadda bata da makoma,da kake cewa meta fini aikai bakaga hakanba tinda ina kallon yadda kake yimata wani kallon ɗaukar hankali,ada bana kokwanton sonda kakeyimin amma yanzu inaji ajikina kashirya yaudarata tinda idonka yahau kan farar mace maraba da cuta,hmm! Gaka gata nan kaje nabarka da ita jahilcima ya isheka!!" MUSLIMAT ta faɗa cikin ƙololuwar ɓacin rai ta tashi tabarshi awajan tana sakin wani kuka mai cin rai.Koda tafice ta barshi awajan dafe kai yayi tare da tashi shima yanufi ɓangarensa. Koda ZULMAT tashiga sashenta bangon ɗakin ta shige inda ta bayyana aturakar mahaifinta sarki ZALIMUZ-ZAMAN........ 👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻 DAN ALLAH INA ROƘON ALFARMA GAREKI IDAN KINGA SAƘONA"ALLAH KABAWA KHADEEJAH CIKAKKIYAR LAFIYA MAI ƊOREWA KABATA IKON AMFANI DA LAFIYAR DAN ARZIƘIN ANNABINKA"ABINDA ZAKUCE KENAN DAN GIRMAN ALLAH NAGODE🤝🏻🥰💞💞. MORE COMMENT MORW TYPING. DOMIN GYARA,SHARHI KO BADA SHAWARA ATUNTUƁENI TA WANNAN LAYIN....👇🏻 07047530638. ƳAR GATAN MAMA✍🏻. NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN BAKI ƊAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA,ALLAH YAƘARA MIKI LAFIYA DA TSAWON KWANA MAI AMFANI AMEEN.MUCH LUV🥰🥰. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ SHAFI NA 19&20. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ 🥰🥰GUDALIYAR BABANTA GUDALIYAR YARGATA WANNAN SHAFIN NAKI NE KIYI YADDA KIKESO DASHI NAGODE.SON SO FISABILILLAHI🥰🥰💞💞. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Koda ZULMAT tashiga sashenta bangon ɗakin tashige inda ta bayyana turakar mahaifinta sarki ZALIMUZ-ZAMAN,koda ta ganta aciki saita shiga duban mahaifinnata bata ganshiba,ko'ina na ɓangaren ta duba amma babushi babu dalilinsa. Koda taga zata wahala seta nufi inda kayayyakin tsaface-tsafacensa suke domin ta duba taga inda yashiga.Dube-duben ƙasa ta fara inda taga zata ɓata lokacinta dan haka kawai ta kunna wutar tsafinsa tare da zaman dirshan aƙasa tana ɗiban wani ruwa me kalar shuɗi tana watsawa acikin wutar,watsawa takeyi inda idonta yake arufe bakinta yana karanto wasu ɗalatsiman tsafi masu wahalar riƙewa acikin abinda take cewa baka fahimtar komai se inda take faɗin"YUSH-SHIBAYIL AMNASH,YUSH-SHIBAYIL AMNASH"Kalmar da tafi maimaitawa kenan inda cikin daƙik'a ɗari uku da saba'in sega hoton ZALIMUZ-ZAMAN ya bayyana shida gungun Aljanun da suke tare aƙarƙashin ƙasar ɗakinnasa.Sake kallon ALJANI DUUJALA tayi tare da zare ido jin kalaman da yake faɗawa mahaifinta akan shigarta garin musulmai yanaso ya wargaza mata shirinta gaba ɗaya.Sake ɗiban ruwannan tayi tare da watsawa akan wutar take wajan da take zaune yadare inda ta bayyana gaban SARKI ZALIMUZ-ZAMAN. Dubanta takai ga sarki ZALIMUZ-ZAMAN tare da sunkuyar da kanta wanda hakan yayi dai-dai da rufe bakin ALJANI DUUJALA!! "Ina yima barka da wannan lokaci ya sarki mai cikakken iko da jarumta!Sannan inayiwa kafatanin baƙinka barka da zuwa tare da fatan suna lafiya" GIMBIYA ZULMAT ta faɗa kanta aƙsa yayin da ƙasan zuciyarta fal yacika da tsoron yadda zasu kwashe da mahaifinnata. Ɗagowa sarkin yayi ya kalleta sannan yamata umarni data dawo kusa dashi ta zauna kana yace..... "Marhaba nake da zuwanki jarumar ƴata,yanzu nake shaidawa aljanun danake da iko dasu tafiyarku garin DEENUL-ISLAM tare da faɗamusu dalilin tafiyar taki,sai dai sunƙaramin tsoro akan wanda nake dashi game da yuwuwar musuluntarki idan kikaci gaba da zama acikinsu domin kuwa an... " Katse shi gimbiya zulmat tayi ta hanyar faɗin..... "Ka gafarceni ya babana! Inamai tabbatar maka babu wani wanda ya isa yasa na karya alƙwarin dake tsakanina dakai,akafirci aka haifeni ashi na girma kuma ashine zancigaba da rayuwa,shin mene ne zaisa tsoro yadinga shiga zuciyarka bayan kana da tabbas akaina ya babana" DUUJALA Yayi wata girgiza kana yatari numfashinta da faɗin....... "Ke yarinya ce mai ƙaramin tinani,mutanennan suna da wani shu'umin sihiri wanda idan ka haure kwana bakwai atare dasu seka shiga addininsu koda kwa ba kaso seka shiga ta hanyar sihirinsu,domin kuwa zasu cikama zuciya da sonsu ta hanyar kyautatawa tare dayima zantuka cikin salama yadda zakaji bakason barin cikinsu,inajimiki tsoron cin amanar iyaye da kakanninki ta hanyar fita daga addininsu da zummar shiga addinin MUSULUNCII" "Inaso kasani yakai DUUJALA! Cewa ni ba matsoraciya bace sannan ba raguwa bace kuma ba mara wayau baceba,na je na raɓesune saboda buƙatar mahaifina kuma ko yanzu mahaifina ya janye ƙudurinsa akan TAKOBIN WATA DUNIYA ni kuma zandawo garin haihuwata nazauna domin ni bazan taɓa yin wani abu bada umarnin mahaifina ba" "Na yarda na amince dake yake ƴata abar alfaharina,nabaki dama akaro na biyu kikoma cikinsu domin kwanaki suna cigaba da matsowa na buɗewar ƙofar WATA DUNIYA,sedai banji kinyimin magana akan yadda kukayi dasu ba" "Ka gafarceni yakai babana! Ina mai tabbatar maka cewa su waɗannan mutanen abin duniya da dukiya basa gabansu,sedai naji suna maganar zasuje wani domin wani abu ko JIHADA ko JIHADI nadai manta asalin sunansa,naji suna maganar zasui shiri akwanakinnan domin tafiya yinshi,kuma naji sunce garin yana daf da WATA DUNIYA kaga da yuwuwar su shiga suma domin ɗaukar TAKOBIN,nima zanyi amfani da wannan damar domin nabisu,yayin da muka ɗaukone zansare kan sarauniyar kamar yadda ka umarceni na kawoshi gareka ya babana" "Meyasa baki tambayesu shin zasu shiga WATA DUNIYA domin ɗaukar takobinba" ALJANI DUUJALA yatari numfashinta da wannan tambayar...... "Saboda matuƙar na fito da abinda yakaini fili garesu zasu fuskanci makirci ne ya kaini kuma bazasu bari burina yacika ba,hakan danai shiyasa suka saki jiki dani batare dasun kawo komai ba". ZALIMUZ-ZAMAN ya numfasa tare da cewa.... "Har yanzu inatsoron kyautatawarsu gareki tasa kishiga addininsu" "Bazan shigaba ya babana! Domin na tambayesu game da addininsu sunce bazasu takuraminba harsai naji inason shiga da kaina,kuma sanin kankune babu ranar dazata fito naji araina inason shiga addininsu". Hakadai sukaita musayar zance atsakaninsu kafin aƙarshe kaifin harshe irinna zulmat tare da dagewa akan alƙawarinta yasa suka rabu da ita.Su ALJANI DUUJALA suma suka kama gabansu bayan yarjejeniyar zasu dinga zagawa domin ganin abinda zulmat takeyi agarin da kuma bata kariya saboda kar wani abu yasame ta. Bayan tafiyarsu ne itama takoma garinsu Muslim tare da komawa ɗakinta kamar bataje ko'ina ba. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Yau saura kwana takwas kenan alissafin NUJBEER ƊAN NAJABURU na sauran kwanakin tafiya WATA DUNIYA,yauma kamar kullum yaje wajan sarki inda ya zauna sukayi hira.Sarki KAMALUD-DEEN ne ya dubi NUJBEER ƊAN NAJABURU fuskarsa ɗauke da murmushi yace....... "Inamai farin cikin ganinka cikin k'oshin lafiya yakai wannan tsoho mai dogon tarihi,nikam da bazan b'ata maka raiba dana yimaka wata tambaya" "Tambayeni kanka tsaye,domin babu shamaki tsakaninmu kasancewar ka mutuntani baka nunamin girman kai kamar sauran sarakuna ba" Sarki ne yayi murmushin jin daɗi kana yace.... MORE COMMENT MORE TYPING. 👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻 DAN ALLAH INA NEMAN WATA ALFARMA AGAREKU,ALFARMAR ITACE"ALLAH KABAWA BAIWARKA KHADEEJAH CIKAKKIYAR LAFIYA MADAWWAMIYA,ALLAH KABATA IKON AMFANI DA LAFIYA DAN SON DA KAKEWA ANNABINKA MUHAMMADU SAW"ABINDA ZAKU CE KENAN DAN GIRMAN ALLAH.NAGODE ALLAH YABADA IKO AMEEN👏🏻. DOMIN GYARA,SHARHI KO BADA SHAWARA ATUNTUƁENI TA WANNAN LAYIN....👇🏻 07047530638. ƳAR GATAN MAMA✍🏻. 🌍WATA DUNIYA🌍 LABARI/RUBUTAWA KHADIJA S.SAMINU ('YAR GATAN MAMA) MARUBIYAR....👇🏻 RAYUWAR MU! A WANI GIDA MAGANIN KAR AYI..! RANA DUBU nd now👇🏻 ⚔️WATA DUNIYA⚔️ LABARIN DA AKA GINA SHI AKAN SOYAYYAR ADDININ MUSULUNCI DA MUSULMAI DA K'IYAYYAR KAFIRCI DA KAFIRAI.AKWAI CIN AMANA,SOYAYYA,K'IYAYYA,YARDA,SADAUKARWA D SAURANSU. INA ROK'ON ALLAH YADA'DA MANA KISHIN MUSULUNCI AMIN💞💞 *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA ALLAH YAJA DA RANKI YAK'ARA MIKI LAFIYA🥰🥰. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ SHAFI NA 21&22 ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Sarki KAMALUD-DEEN ne yayi murmushin jin daɗi kana yace....... "Yakai wannan tsoho mai tarin shekaru ma'abocin hikima da basira inason jin wani abu daga rayuwarka idan bazan matsa maka ba" "Hhhhh! Ai wannan abu ne mai sauƙi,zanbaka tarihina amma ba yauba kasancewar yau inada muhimmin abu agabana,kuma ni awannan lokaci banda muradi sai kwanaki su cika mutafi ɗaukar takobi wanda shi ne cikar buri na,zanbaka amma se munje WATA DUNIYA" Koda yafita yakoma masaukinsa haka sarki yaita tinani akansa tare da jinjinawa girman taurin kai irinna NUJBEER ƊAN NAJABURU ahaka shima ya shiga turakarsa. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Koda MUSLIM yashiga turakarsa neman waje yayi ya yada haƙarƙarinsa domin ji yakeyi duk jikinsa babu ƙwari tamkar ankwance wasu notika ajikinsa saboda kalaman MUSLIMAT,tabbas yanason MUSLIMAT kuma ita yake da burin ya aura,amma ya zaiyi da soyayyar da ZULMAT take yi masa? ya tambayi kansa,ya lura da duka zuciyarta take ƙaunarshi tinda harta kasa ɓoyewa agaban kowa,kuma ya daɗe da sanin haka saboda yasha gani a ƙwayar idonta aduk sanda suka haɗu afilin daga,yana kyautata zaton silar sonsa kaɗai zai iya sawa ta rabauta da shiga addinin MUSULUNCI,idan kuwa hakane zai bata dukkan wata kulawa domin ya temaketa tasamu rabo shima yasamu addininsa yasamu ƙaruwa,zai jure kowane ɓacin rai dazai fuskanta awajan MUSLIMAT,zaiyi komai zaiyi amfani da soyayyar da ZULMAT takeyimasa domin ya jata yazuwa addinin MUSULUNCI.Haka yaita wannan tinanin ahaka wani nannauyan bacci ya ɗaukeshi. Koda ZULMAT ta zauna ita kaɗai tinani ne yacika zuciyarta kan yadda zata cika alƙwarin mahaifinta inda gefe guda kuma take tinanin abinda zai rabata da MUSLIM dan ayanzu ji take soyayyarsa ta mamaye zuciyarta,sonsa yarigada yagama shiga lungu da saƙo na zuciyarta,ko yaya ta rufe ido zanen fuskarsa take gani,idan ta kwanta bacci babu abinda takeyi se mafarkin yana nuna mata wata soyayya tare da kalamai masu wuyar mantawa. Wani tinani tayi aranta wanda hakan yasa cikin hanzari ta fito daga ɗakin tanufi waje.Fitarta keda wuya ta haɗu da wata kuyanga wadda ta tawo hannunta ɗauke da wani kwando me kyau ancikashi da dangin tufa inibi dabino da sauransu. "Barkanki dai wannan baiwa" Abinda tace da baiwar kenan wanda hakan yai sanadiyar tsayawarta ta juyo tana duban zulmat yayinda ta amsa da cewa....... "Barkanki dai " "Ina fatan banɓatamiki lokaci ba,sannan ina neman wata alfarma wajanki idan bazaki damu ba" "Wacce alfarma ce wannan kike nema awajena ya shugaba ta" "Inaso ki nunamin ɓangaren da zai sadani da ɓangaren MUSLIM" "Wannan ba abin damuwa bane ya shugabata! Yanzu hakama can zani domin nakaimai wannan kayan marmarin" Murmushi Zulmat tayi tare da karɓar kwandon tace zata kaimasa inda itakuma baiwa mesuna HUMAIRA'U ta juya ɓangarensu. Tafiya take da mamakin wannan baƙuwa mai tsabar kyau da kwarjini wadda ta tsaida ita,bata ganin gabanta saboda yadda mamakin yalulata duniyar tinani har tayi wani ɓangaren banasu ba. "Haba HUMAIRA'U yazaki tawo kanki asama kibigeni haka batare da saninkiba?" Babu zato Humaira'u taji wannan zancen yadira amasarrafar sarrafa satinta,ɗagowa tayi cikin hanzari ta dubi mai maganar tare dakai dubanta ƙasa inda matar take kallo. "Ya ra'ufu ya rahimu! Nikam yau naga ta kaina,tayaya naimiki wannan aika-aikar?" Humaira'u tafaɗa tana duban matar,hannunta aka saboda yadda abin ya kiɗimata,ba wani abu baneba illa ɓarin kayan abinci datayiwa matar.Wani haɗaɗɗen biski ne da miyar taushe wadda taji gyaɗa anshanana mata man shanu ƙamshi ya karaɗe ilahirin wajan,shine sanda ta tawo tana tinani sukayi tawo mugama tazubar mata su ak'asa.Tsinkayar muryar matar tayi tana tambayarta da faɗin.... "Tayaya zansan meya sameki tinda kintawo gaba-kaɗi kina duban wata bakya kallon gabanki? Ke kam ma mekike tinani haka dan Allah awannan lokacin,shin kodai wani abune yafaru awannan masauratar bamu sani ba?" Ta ida magana tana tsugunnawa domin takwashe burabuskon sama-sama domin dayawa yahaɗu da ƙasa,bata da zaɓin daya wuce itama tasunkuya ta tayata danhaka itama ta tayata suka kwashe danma an auna arziƙi miyar akwai ragowa da yawa domin sanda mazubin miyar yatashi faɗuwa ba kifewa yayiba zama yayi adandanyar ƙasa wanda hakan yai sanadiyar miyar tayi tsalle tafito daga ciki,mazubin biskinne yakife inda gabaɗayanshi yazube awajan,haka suka kwashe wanda zai kwasu tukunna Humaira'u ta dubeta da cewa...... "Hmm! FANTA yau ni naga abinda nagani,wata zankaɗeɗiyar matashiyar budurwa nagani wadda aƙalla shekarunta zasui ashirin da bakwai wato na haihuwa,duk inda ake neman kyau to wannan yarinya tana da madararsa,wato idan kika kalli idanunta zaki gansu dara-dara cikinsu farare karrr! Tana da cikar fuska domin datayimin murmushi bakiga yadda kundu-kukinta suka tashiba kamar fanke inda ƙasansu kuma gefen bakinta suka lotsa(dimples)ke abindai sekin gani,ke nifa bazan iya fasaltamiki kyan wannan halitta ba domin ubangiji yazuba baiwar kyau atare da ita,kuma wani ƙarin abinma a......" "Kinga Humaira'u kimin yadda zangane wai awane ɓangare kika ganta" "Ashsha! Ke kinji irinta,bakwa tsayawa kuci ribar zance in anayi,aɓangaren sarauniya na ganta tana neman ɓangaren yarima Muslim nikuma zankai masa kayan marmari ke intak'aicemiki magana karɓar kwandonma tayi ta tafi ɓangaren nasa,ni wallahi hankalina ya gaza kwanciya kar wani mummunan abin yafaru tsakaninsu kinsan kyawawan mata da janye hankalin maza kuma ma......." "Kedai JAKADIYA da wuya kigama faɗar labari baki sako sharri acikinsaba,inbanda abinki yarima Muslim ɗin dayake da tsoron Allah zaki danganta da haka?To ai wannan da kikegani ba ƙaramar kai bace domin itace GIMBIYA ZULMAT ƴar sarki ZALIMUZ-ZAMAN dake garin SILDAN kuma yau kimanin kwanakinta shida awannan masarauta domin ya riskeni anyi zaman fada anan sarauniya take shedawa jama'arta tayi bak'uwa kuma itace baƙuwar,tazone saboda mahaifinta ZALIMUZ-ZAMAN yayi mata korar kare daga garinsa yac..... JAKADIYA HUMAIRA'U ta riƙe haɓa tare juyawa ta kalli gabas,yamma kudu da arewa sannan tagyara tsayuwarta tace.... "Allahu akhbar! Allah sarkin buwaya,wato aduniya indai kana neman wani abu seka sameshi matuƙar ka miƙa lamuranka gareshi.Na yadda da haka,kinga yanzu dana tawo hankalina atashe yake, kawai sonake nasamu wanda zanfaɗawa mu shiga bincike muji daga ina tafito? ashe kece zaki buɗamin inda aka rufemini,ni dake kinsan kwana biyu banida lafiya danko tafiyar da sarauniya tayi ba dani akaiba shiyasa bansan meke faruwaba amma yanzu gaki.To metayiwa sarkin ya koreta? Kuma me tazo tayi anan,ita sarauniyar ta yadda da ita,anya ba wani abune ya kawotaba ta laƙe da haka?" "Ke illarki seki jerawa mutum tambaya kamar akurkuku,yo da ke akasa aɓangaren tuhuma ba'asan me zaki ba yadda kike jeron tambaya sekace nakashe yarima" JAKADIYA HUMAIRA'U ta karkace baki tare da haɗe rai tace.... "Kinga FANTA sauri nake zanshiga mugana da sarauniya,inbazaki faɗanba nasan nayi". Kallonta FANTA tayi sheƙek'e tare da gyara tsayuwa tace..... "Atafiyar dasu sarauniya sukayi domin ɗaukaka kalmar ALLAH shine fa suka haɗu dasu mayaƙan SILDAN suka yaƙesu aka kashemana mutane da dama,ƙarshedai ita ɗiyar tasa ta dakatar da yak'in tare da temakonsu ta tseratar dasu,kuma naji daga majiya mai ƙarfi cewar son yarima takeyi shiyasa ta temakesu,tojin haka da mahaifinta yayi shine fa ya koreta dan taji haushi, ita kuma seta dawo nan domin tarama abinda yayi mata.Kuma kingama idan darabo ta silar haka ta musulunta kinsan ance so yana canza mutum" Gwalalo ido jakadiya tayi tare da jinjina kai ta dubi Fanta tace.... DAN ALLAH INA NEMAN ALFARMA AWAJANKU MASU KARATU,DAN ALLAH KU ROƘAMIN LAFIYA DA CEWA"ALLAH KA AZURTA BAIWARKA KHADEEJAH DA CIKAKKIYAR LAFIYA SANNAN KABATA IKON AMFANI DA LAFIYAR DAN ARZIƘIN MASOYINKA MUHAMMADU SAW"ABINDA ZAKUCE KENAN DAN ALLAH,ALLAH YABIYAWA KOWA BUƘATUNSHI AMEEN NAGODE🥰🥰💞💞. MORE COMMENT MORE TYPING....... DOMIN GYARA,SHARHI KO BADA SHAWARA ATUNTUƁENI TA WANNAN LAYIN....👇🏻 07047530638🌍. ƳAR GATAN MAMA✍🏻. 🌍WATA DUNIYA🌍 LABARI/RUBUTAWA KHADIJA S.SAMINU ('YAR GATAN MAMA) MARUBIYAR....👇🏻 RAYUWAR MU! A WANI GIDA MAGANIN KAR AYI..! RANA DUBU nd now👇🏻 ⚔️WATA DUNIYA⚔️ LABARIN DA AKA GINA SHI AKAN SOYAYYAR ADDININ MUSULUNCI DA MUSULMAI DA K'IYAYYAR KAFIRCI DA KAFIRAI.AKWAI CIN AMANA,SOYAYYA,K'IYAYYA,YARDA,SADAUKARWA D SAURANSU. INA ROK'ON ALLAH YADA'DA MANA KISHIN MUSULUNCI AMIN💞💞 *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYANSHI GA MAHAIFIYARA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA,ALLAH YA SAKAMIKI DA ALKAIRINSA AMEEN🥰🥰💞💞. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ SHAFI 23&24 ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Gwalalo ido jakadiya tayi tare da jinjina kai tadubi Fanta tace..... "Lallai wannan ake kira cakwakiya,ashe abinda ke faruwa kenan kum..." Katseta Fanta tayi ta hanyar cewa..... "Kingani tafiyata kar abincina yayi sanyi garin samawa gulma wajan zama" Tafaɗa tare da ɗaukar kayan abincinta tai gaba tabar Jakadiya riƙe dabaki.Itama bata da zaɓin daya wuce tatafi harkar gabanta dan haka ta wuce tai hanyar sashen SARAUNIYA SINIYYA!!.... ****** Koda GIMBIYA ZULMAT ta isa ɓangaren YARIMA MUSLIM tsayawa tayi abakin ƙofa tare dayin shiru talula duniyar tinani....... "Shin koya zai tarbeni idan naƙarasa? Ina sonsa! Ina ƙaunarsa!! Zan iya komai akansa ciki kuwa harda kashe kaina idan ya buƙaci hakan daga gare ni,zan iya kashe duk wani wanda yace zaiyi tarayya dani cikin soyayyarsa,itama MUSLIMAT na barta araye ne saboda tarigani faɗawa cikin soyayyarsa kuma na bata nan da wani lokaci idan abinnata yayi nisa ma'ana taci gaba da nuna ƙaunarsa agabana!Zan aikata inda kakannina da mahaifiyata suka tafi kuma baazata dawo ba, YUSH-SHIBAYIL AMNASH-YUSH-SHIBAYIL AMNASH Katemakeni akan soyayyata kasa yasoni sonda ko mahaifiyarsa bai yiwa irinshi ba,YUSH-SHIBAYIL AMNASH-YUSH-SHIBAYIL AMNASH karka watsamin ƙasa a idona.... " Shiru tayi kuma na tsayin daƙiƙa saba'in da uku kafin ta buɗe baki ta furta afili tace....... "Ya abin bautar MUSULMAI kasa bawanka yasoni ka tallafawa soyayyata!!" Gama faɗin haka keda wuya ta tura ƙofar dazata sadata da inda MUSLIM yake,seda taratsa faluka har uku kowanne ya ƙawatu da kayan ado na alfarma sannan takai jikin wata ƙofa wadda samanta aka rubuta 'TURAKAR YARIMA MUSLIM' ganin haka ya tabbatar mata nan ne inda take nema dan haka ta tura ƙofar tare da tsayawa ta kasa shiga. MUSLIM daga inda yake zaune akan sallayar daya idar da salatid-dhuha hannunsa ɗauke da alƙur'ani mai girma yaɗago da kansa ya sauke kyawawan idanunsa akanta wanda suke rikitata ta mance komai aduk sanda tayi tozali dasu,kallonta yakeyi batare daya buɗe baki yayi maganaba sai tinanin dayakeyi aransa mene ne ya hanata ƙarasa shigowa? cigaba da kallonta yayi harseda tafara tinanin to kodai baiji daɗin shigowarta babu neman izini ba? Hakan data tina yasa tayi saurin juyawa tare da neman waje afalon dake kusa da ɗakinnasa ta zauna domin ta jirashi koda kwa zaiɗauki lokaci bai fitoba tasa aranta bazata tashiba kuma bazata takuramasa ba tinda taga shima kundinsu ne wanda abin bautarsu ya saukar musu yake karantawa,saboda suma aduk lokacin da suke duba kundin tsaface-tsafacensu basajin daɗi idan wani abu yagifta batare dasun isa inda sukeson kaiwa ba. Ganin ta juya yasa MUSLIM cikin hanzari ya ajje ƙur'anin hannunsa tare da biyo bayanta.Tana tsaka da tinani ƙamshin tirarensa dake sanyamata kasala ya bayyana mata masoyinta kuma muradinta ya iso inda take dan haka batare da jinkiri ba taɗago kanta ta sauke idanunta afuskarshi........ ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Koda MUSLIMAT ta isa ɓangarenta mukulli tasaka ta kulle sashen nata tare da shigewa can ƙuryar ɗakin tahaye ƙarshen gado ta haɗa kai da gwiwa tahau rusa kuka iya ƙarfinta. Tin tanayi sauti yana fita har seda muryarta ta dishe tadena fidda sauti saboda tsabar kukan datai wanda da hawaye yana ƙarewa tabbas yau se nata ya ƙare.Kamar an tsikareta haka ta tashi daga kan gadon ta isa bakin kwabarta tare da buɗewa tashiga watsi da duk kayan da suke ciki wanda aƙarshe can ƙasan kayanta ta ɗauko wani kundi na tarin hotuna. Cikin hanzari ta buɗe ta shiga fiddoda hotunan mabanbantan mutane tare da ƙaremusu kallo tana k'ara sautin kukanta,bata tsayaba harseda takawo kan wani hoto dake ɗauke da jabun MUSLIM,SARAUNIYA SINIYYA da wasu mata guda biyu dakuma wasu maza guda biyu da kuma ita kanta MUSLIMAT ɗin..... Kallon hoton takeyi tana sakin wani kuka mai cin rai tare da toshe bakinta da gefen zanin dake jikinta,ajje hoton tayi ta ɗauki wani daban wanda hotontane itada Muslim suna yiwa juna murmushi,tashi tayi takoma inda tafara zama tare da duƙunk'une jikinta ta takure kanta tana sauke ajiyar zuciya ajejjere tana cigaba da kallon hoton wasu siraran hawaye na zirarowa ta gefen idanunta.Ahaka ta wanzu tsawon awanni kafin batai auneba wani nannauyan bacci yayi awon gaba da ita. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Koda JAKADIYA HUMAIRA'U ta isa b'angaren sarauniya bata tarar da kowa ba se wata amintacciyar sarauniya mai suna SHATU tana niyyar fitowa ita kuma zata shiga. "Barka dai Jakadiya,yana ganki haka afirgice incedai ko lafiya?" "Ahaf! Kaga ƴar halak inakwa nemanki,amma bara nafuto tukunna nadawo gareki" Jakadiya ta faɗa tare da sa kai turakar sarauniyar,bayan ta nemi izinin shiga anbata ne tazauna ta sunkuyar da kai tare da cewa. "Amincin Allah ya tabbata agareki ya adalar shugaba mai mulkar mutanen wannan masarauta" "Tare dake Jakadiya,mungode" "Allah yaja zamaninki! Daman wata jita-jita naji game da baƙuwarki.Allah ya temake ki kozan iya jin gaskiyar lamari daga bakinki?Allah ya temake ki ko'ina na wannan masarauta zancenta akeyi tare da yaɗa jita-jitar cewa wai son yarima takeyi hakan yasa tazo domin ta kawomasa ziyar...." Ɗaga mata hannu sarauniya tayi tare da faɗin....... "Munji zancenki kuma....kamar yadda kika faɗa ba musulma bace ba,sannan akwai wani dalilidai bayan soyayyar yarima amma ki rabu da jita-jita zaifi domin duk waɗanda suka kamata susan dalilin zamana da ita nafaɗamusu sun sani". "Yanzu ranki ya daɗe kina nufin zaki bata auren yarima kenan?Sannan ita Muslimat ta yadda ta rabu da yariman? "Duka su biyun inada cikakken iko dasu,dan haka zan iya bawa Muslimat umarni akan ta barwa Zulmat MUSLIM ta aura domin da soyayyar da take masa kaɗai zamu iya janta yazuwa addininmu na musulunci..." Sarauniya nagama wannan maganar taɗan lumshe idonta tsawon daƙik'a hamsin tukunna ta buɗe.Ganin haka ya tabbatarwa Jakadiya Humaira'u sarauniyar ta ƙosa da maganar dan haka tayi mata sallama ta tafi...... ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Koda MUSLIM ya fito ya tarar da ZULMAT zaune tazuba uban tagumi tana........ 👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻 DAN ALLAH INA NEMAN ALFARMA AWAJANKU"ALLAH KABAWA BAIWARKA KHADEEJAH CIKAKKIYAR LAFIYA KABATA IKON AMFANI DA LAFAIYAR"ABINDA ZAKUCE KENAN DAN ALLAH ,NAGODE. MORE COMMENT MORE TYPING. DOMIN GYARA,SHARHI KO BADA SHAWARA ATUNTUƁENI TA WANNAN LAYIN.. .07047530638. ƳAR GATAN MAMA✍🏻. ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ LABARI/RUBUTAWA KHADIJA S.SAMINU (ƳAR GATAN MAMA) Marubuciyar...... A WANI GIDA RAYUWAR MU! MAGANIN KAR AYI! nd now...... ⚔️WATA DUNIYA⚔️ ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.ƘURAINABU IDRIS YARO YAHYA ALLAH YACI GABA DA ƘARFAFA LAMURANKI AMEEN😍💞💞. ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ HASSANA IYAYI(Mmn Masoyi) Allah yak'aramk lafiya da basira yatsareki yabar zumunci🥰🤗Wannan shafin naki ne kiyi yadda kikeso dashi🤗🥰. ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ SHAFI NA 25&26 Koda MUSLIM ya fito ya tarar da ZULMAT zaune tazuba uban tagumi tana tinani wanda bazaka iya ganewa saboda yadda take yi da fuskarta da idonta da bakinta zai tabbatarma da tinanin nata akan abu mai muhimmanci ne kuma tanajin daɗin haka..... Sanda ya ratso yazo daf da ita yaga ayadda ta ɗago da kanta ta zuba idanunta acikin nasa ko ƙiftawa batayi,wani murmushi takeyi ajejjere ba ƙaƙk'autawa.Yunƙurawa tayi daga inda take zaune da niyyar ta durƙusa masa ya dakatar da ita da faɗin.... "Banyiwa soyayya adalci ba idan har na bari kika zuba gwiwoyinki aƙasa da nufin roƙon soyayyata,ni ya kamata na durƙusamiki domin ko yaushe afagen SO namiji ke nema gun mace kuma ita yake lallaɓawa domin samun soyayyarsa agunta!Namiji shi ne bawa agun mace domin shike mata hidima har se yasaka tausayinsa acikin ƙoƙon ranta to asannane zaiyi nasarar samun soyayya agareta,domin daga sanda mace tafara tausayin namiji to da alama gaba kaɗan zata faɗa soyayyarsa.Hmm! Sedai kash!! ni anrigada anyimin matar da zan aura awannan masarauta dan haka ne nake faɗamiki tausasan kalamai naban hak'uri da lallashi saboda naga alamu sun nuna kamar kina shirin fara son...... Cikin kuka mai haɗe da sheshshek'a ZULMAT ta tare MUSLIM da cewa.... "Dakata!! Ka sauraramin da wannan mayaudaran kalaman naka masu tarwatsa nutsuwa da hankalina,daman tsawon lokacin dana ɗauka ina ɗawainiya da soyayyarka baka fuskanci mai nake nufi ba? Kana nufin kacemin daman amahaukaciya ka ɗaukeni? Kana nufin bazaka sharemin hawaye ba sai dai nazama na rasa komai nawa kenan? Na rasa mahaifiyata,na rabu da mahaifina da mahaifata,sannan aƙarshe na rabu da SOYAYYATA!!?.....Bazai yuwuba MUSLIM,tinda nakejin sunanka bantaɓa furtashi ba saboda girmamawar da nake maka,amma yau kanaso kasakamin dafin da bazan warke ba,me nayiwa rayuwa haka takeson wora ni ta inda saina gwanmace mutuwataaa!!" Ai tana zuwa nan azancenta wani jiri ya ɗebeta ta tafi da baya zata faɗi inda cikin rashin sa'a tafaɗi adandaryar ƙasa yayin da hannunta yabugu da glass ɗin dake ajje atsakiyar falon. Razani firgici da tsantsar tashin hankali ne suka dirarwa MUSLIM cikin daƙiƙu goma sha biyar wanda hakan ya haddasamai bugun zuciya mai tsananin gaske, wanda lokaci ɗaya yaji wata irin nadamar abinda yayi mata ya lulluɓeshi saima duk ya tsani ya kansa,cikin jarumta ya durƙusa ya tallafo kanta tare da runtse idonsa dan yadda yakeji acikin ransa abin bazai faɗuba.Hankalinsa ne yakuma tashi sanda yai tozali da jinin dake zuba ahannunta,sam bai lura da bigewarta da glashing ba sai yanzu"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!" Ya furta afili tare da tashi da sauri yai umarni da asamo likita ya dubata. Kafin kace me tini zancen suman ZULMAT ya mamaye ko'ina na cikin masarautar domin gulma yau take ranarta wannan haɗu da wancan waccan haɗu wancan tini zance yaje inda mai zancen baijeba,hankalin SARAUNIYYA SINIYYA yayi mugun tashi saboda yadda lamarin ZULMAT yai tsamari,tin da hantsi ZULMAT tafaɗi gashi yanzu gari yarufe rana ta nufi maɓoyarta amma bata farfaɗoba,anbada tabbacin farfaɗowarta kowane lokaci amma har yanzu bata farfaɗoba Sarauniya se kaiwa take tana komowa saboda tashin hankali da ɓacin rai daya lulluɓeta jin abinda yafaru yai sanadiyyar faruwar hakan.ZULMAT ba ita ta farfaɗoba harse bayan isha'i Sarauniya ta tsinkayi muryarta data dishe tana maganar cikin harharɗewar magana tana cewa..... "Soyayya bata yimin adalci ba,da ace zata yimin adalci da bata kamu da son wanda mahaifina yafi tsana arayuwarsa ba,ni ce wadda mahaifina yafiso amma hakan baisani na fifitashi akan SOYAYYATA ba!Na fifita wanda ba addinina ɗaya dashi ba ashe shirme nakeyi bansa niba? meyasa zaka yimin haka?meyasa bazakaji tausayi na ba?me yasa!Me yasa!!" Da hanzari SARAUNIYA SINIYYA ta juyo ta fuskance ta fuskarta ɗauke da alhini da kuma nuna ɓacin ran da take ciki amma hakan bai hana agane farin cikin farkawar ZULMAT ɗinba akan fuskarta,dai-dai fuskarta ta sunkuyo daga inda take tsaye hannunta sak'ale a bayanta ta furta "Alhamdulillah! Gimbiya Sannu da jiki,muna fatan bakyajin komai yanzu ajikinki?" Rinannun idanuwanta ZULMAT ta ɗago ta sauke su kan fuskar SARAUNIYA SINIYYA wasu siraran tagwayen hawaye masu zafi suna biyo gefen fuskarta, bakinta na rawa ta kuma duban sarauniyar sannan tace.... "Ashe bazaki iya sakawa ɗanki yasoni ba?ashe bazaki ji tausayi na ba?ashe maganganun da kukeyi basa aiki akanku se iya kanmu kafirai?ashe bazai soni ba,kifaɗamin mena rasa ajikina da namiji bazai soni ba?mena rasa!! Yau kodai ya furtamin yana sona ko kuma nacakawa kaina wuk'a naje inda mahaifiyata da kakannina suka tafi domin bazan bari nacigaba da rayuwa ba sena kashe kai....." ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ MUSLIMAT ba ita ta farka ba harseda wata yunwa ta matsawa cikinta kasancewar ko karin kumallo bata yiba yau saboda ɓacin rai,sallah ta gabatar sannan tukunna taɗauki kayan marmari dake lufude cikin kwando a ajje tahau ci baji ba gani,bata samu nutsuwaba har seda taji tayi nak ba masaka tsinke sannan takoma gefe tazuba tagumi tana nazari. "Agaskiya bana jin ko ZULMAT zata musulunta silar samun soyayyar MUSLIM zan barmata shi,domin kuwa nima ina sonshi fiye da yadda nakeson kaina,rashinsa arayuwata zai zama dai-dai da rasa rayuwata nikuma bazan yi gangancin rusawa kaina farin ciki ba koda kuwa hakan zai silar barina wannan masarautar..." ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Yau saura kwana uku alissafin NUJBEER ƊAN NAJABURU na tafiya WATA DUNIYA dan haka kowane shiri da zaiyi ya gamashi domin kuwa ya shiryawa wannan tafiyar fiye da yadda bawa nagari yakewa kansa tanadi wajan ambaton Lillahil'wahidil'ƙahhar.... ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ ALJANI DUUJALA!bayan tafiyarsu DUNIYARSU suna isa yatara kafatanin aljanun dake ƙarƙashin ikonsa tare dayimusu bayani kamar haka..... "Inamai jinjinawa UBANGIJINMU SHALBAYN bisa sa'a dayake bamu adukkan ƙudurinmu na fili dana boye.JINJINA GA SHALBAYN!JINJINA GA SHALBAYN!!" Nan gungun aljanun dake wajan suka ruɗe tare da haɗa baki cikin girmamawa wajan faɗin... "JINJINA GA SHALBAYN!JINJINA GA SHALBAYN!!JINJINA GA SHALBAYN!!!" Wata mahaukaciyar dariya ALJANI DUUJALA yahau ɓaɓɓakawa wadda yaɗauki tsawon daƙiƙa sittin da ɗaya da rabi yanayi sannan ya gimtse bakinsa yace....... "Ina alfahari da kasancewarku ƙarƙashin ikona sannan inamai umartarku da ku bani aron hankulanku saboda muyi magana akan abinda yataramu" Wani ALJANI mai bayyanannen muni ya karkace baki tare da maimaita abinda shugabannasu yace cikin wata iriyar murya mai sanya firgici......... 👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻 DAN ALLAH INA NEMAN ALFARMARKU"ALLAH KABAWA KHADEEJAH LAFIYA MAI ƊOREWA DAN ƘARFIN IKONKA"ABINDA ZAKUCE KENAN DAN ALLAH.NAGODE🥰😍 MORE COMMENT MORE TYPING. DOMIN GYARA,SHARHI KO BADA SHAWARA ATUNTUƁENI TA WANNAN LAYIN👇🏻 07047530638. ƳAR GATAN MAMA✍🏻. ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ LABARI/RUBUTAWA KHADIJA S.SAMINU (ƳAR GATAN MAMA) Marubuciyar...... A WANI GIDA RAYUWAR MU! MAGANIN KAR AYI! nd now...... ⚔️WATA DUNIYA⚔️ ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.ƘURAINABU IDRIS YARO YAHYA ALLAH YAJA DA RAI YAƘARA LAFIYA. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ SHAFI NA 27&28 ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Wani ALJANI mai bayyanannen muni ya karkace baki tare da maimaita abinda shugabansu yace cikin wata iriyar murya mai sanya firgici azuciyar mai imani,shugabannasune bayan Aljanin yagama bayaninsa yamiƙe daga ƙasaitacciyar kujerar dayake kana yace... "Yaku tattarin ALJANUN DUUJALA! Ina son muyi magana ne akan sarki ZALIMUZ-ZAMAN amma kafin nace komai inason nasan suwaye zasu iya zuwa garin DEENUL-ISLAM suyi duk mai yuwuwa domin ganin GIMBIYA ZULMAT bata musulunta ba?sannan inaso nasanar daku cewa alƙawarin dana ɗaukarwa ZALIMUZ-ZAMAN na temakamasa yasamu TAKOBI bazan cika shiba" Ajejjere suke kallonsa tare da jinjina lamarin dayazo musu dashi,ɗaya daga cikin aljanunne ya kalleshi tare dacewa.... "Kaine jiya kaine yau kaikake da isa da iko damu dan haka muna sauraronka yadda kace haka za'ayi...!" Aljani DUUJALA!Ya karkace baki ya shek'e da wata razananniyar dariya kana yace.... "Sannunka GUNZAIL naji daɗin wannan magana taka dan haka nakeso naji tabakin Aljani AR'TIYAN domin banason daga baya wani yace zai kawo wata shawara wadda baazan ɗauketa ba saboda lokacin da aka kawota bakin alƙalami ya rigada ya bushe...." Aljani AR'TIYAN! ya ɓaɓɓake da wata mahaukaciyar dariya kana ya gimtse bakinsa yace...... "Wanene yake da cikakken iko acikin aljanun wannan duniya idan ba kaiba?yadda kafaɗa shi ne dai-dai ya shugabanmu,dan haka sedai nace wannan shawara taka itace dai-dai domin ni daman da aka faɗamin ZALIMUZ-ZAMAN yanaso ya mallaki wannan TAKOBI dazai mallake mutane da Aljanun dake faɗin wannan duniya ni daman ban aminta ba domin sam bazan yadda muzana aƙarƙashin ikonsa ba" Wani ɗan dunƙulen aljani dake gefe ya karkace baki yace...... "Oh! Daman ai shugabane yake dankwafar damu idan munyi niyyar ganin bayan sarki ZALIMUZ-ZAMAN,amma yaza'ai ace mutum yana mulkarmu mu Aljannu inba sakaci irin namu ba?ai kawai mu nunamai soyayya mu shiga jikinshi muyi yadda ƴarsa zata yiwa mutane" Wata dariya Aljani AR'TIYAN!Yake ƙyaƙyatawa saboda jin abinda Aljani DUƘUFUL!yace....Aljani DUUJALA!ya dubesu yace.... "To naji daɗin hakan da kuka yanke da kanku,dan haka kowa yasan me yakeyi mudage muɗauko TAKOBIn nan daga baya saimu zaɓi guda acikinmu yazama shike mulkarmu baki ɗaya,inamai umartarku wasu su shirya su tafi DEENUL-ISLAM domin gano mai GIMBIYA ZULMAT take ciki,iya masifa karku barta ta karɓi addininsu. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ A mamakance SARAUNIYA SINIYYA tajuyo takai dubanta ga GIMBIYA ZULMAT jin kalaman da ke fitowa daga bakinta...... Babu shiri tayi umarni da aka kiramata MUSLIM da MUSLIMAT domin ta nuna ikonta akansu baki ɗaya..... 👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻 DAN ALLAH INA NEMAN ALFARMA"ALLAH KAƘARAWA KHDEEJAH LAFIYA KA TSARKAKE MATA ZUCIYARTA TA DAUWAMA AHAKA"DAN ALLAH ABINDA ZAKUCE KENAN NAGODE. MORE COMMENT MORE TYPING..... DOMIN GYARA,SHARHI KO BADA SHAWARA ATUNTUƁENI TA WANNAN LAYIN.....07047530638. ƳAR GATAN MAMA✍🏻. ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ LABARI/RUBUTAWA KHADIJA S.SAMINU (ƳAR GATAN MAMA) Marubuciyar...... A WANI GIDA RAYUWAR MU! MAGANIN KAR AYI! nd now...... ⚔️WATA DUNIYA⚔️ ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABAƊAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.ƘURAINABU IDRIS YARO YAHYA ALLAH YAƘARAMATA LAFIYA AMEEN. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ SHAFI NA 29&30. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ ❤️❤️❤️❤️❤️❤️ UMMUNAH💖🙌🏻🙌🏻 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️ Idan kaji ana cewa jinjina ɗaya kenan🤗Ni wannan jinjinawar tawa ba guda ɗaya bace agareki Ummun@h🙌🏻Ke ce wadda koyaushe kike ƙaramin ƙarfin gwiwa abisa duk lamuran da zan dn haka ina matuƙar godiya tare d addu'ar Allah yatsareki d ke da zuri'arki dn arzik'in Annabi da Alƙur'ani👏🏻Allah yashiga dukkan lamuranki,kinfi ƙarfin abaki kyautar page dn dukama littafin mallakinkine saidai fatan nasara.Hayaty son so fisabilillahi❤️💖😍💞💞. ❤️❤️❤️❤️❤️❤️ Ummun@hhh💖🙌🏻 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️ ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ Babu ɓata lokaci tayi umarni da a kiramata MUSLIM da MUSLIMAT danta nuna ƙarfin ikonta akansu.Bayan tafiyar ne ta juyo da dubanta ga GIMBIYA ZULMAT fuskarta tamkar hadari dan yadda ta haɗeta baazaka ce ta taɓa dariyaba tace.... "Ashe daman ke bakya da wayo har haka? me zaisa ki lalata rayuwarki kiƙarar da ita saboda wani ɗa namiji?shin dama kinzo duniya dominshi ne da zaki kashe kanki saboda shi,shin dama soyayyarki ce ta kawoki wannan garin namu ba abinda kikace mana b...." Saurin dakatar da ita ZULMAT tayi ta hanyar ɗaga mata hannu tare da fashewa da kuka tace..... "Yake wannan Sarauniya mai ƙarfin iko! Duka waɗannan tambayoyi da kikayimin amsarsu haka ne domin tunda nake atsayin rayuwata bantaɓa neman wani abu na rasaba sai yau,sarakuna da ƴaƴan sarakuna bansan adadin waɗanda sukanemi aurena ba amma nace ba wanda nakeso nace ni bama zanyi aurenba,kwatsam naga MUSLIM na kamu da sonsa kuma na ajje izzata da isata na furta ina sonsa amma shi ya....." Maganar ce ta maƙale amaƙoshinta sakamakon shigowar su MUSLIM inda suke,sarauniya ta sake ɓata rai ganin bataga MUSLIMAT ba dan haka ta dubi FANTA tare da cemata.... "Shin ina MUSLIMAT take nace kisanar inason ganinta?" "Allah yaja zamaninki!Munje tare da ni da YARIMA amma bata buɗe ɗakinba kuma mun ƙwanƙwasa cikin girmamawa sedai muna tunanin kota samu wutawa ne?" Umarni ta sake badawa akan asake komawa abugamata akiramata ita yanzunnan amma yanzunma haka sukaje suka dawo batare da MUSLIMAT ta buɗe ba.Ran Sarauniya yakai ƙololuwa wajan ɓaci dan haka ta taka da kanta suka mara mata baya domin kiran MUSLIMAT ɗin da kanta. Fitarta keda wuya ZULMAT ta tsige ƙarin ruwan dake maƙale ahannunta tare da zabura taduro daga gadon ta durƙusa tasa gwiwoyinta aƙsa tare da haɗa hannunta alamar roƙo idanunta nacigaba da zub da hawaye tace da muslim..... "MOSLIM" A mamakance MUSLIM ya juyo ya kalleta tare ɗan rage tsayinsa akanta ya tsuguna saitin inda take suna fuskantar juna jin ayadda ta ambaci sunansa,kallon juna sukeyi kafin daga bisani tasake cewa..... "Shin dama haka so yake baya yiwa mai yinsa adalci ko kuma mune bama yiwa masoyanmu adalci?nasan mahaifiyarka mai adalci ce,ina kyautata zaton zatace kazaɓane tsakanin NI ko MUSLIMAT,ina haɗaka da YUSH-SHIBAYIL AMNAS....." Bata ƙarasaba kuma saitayi saurin toshe bakinta saboda tuna abinda takeson cewa dn haka da saurinta tagoge ruwan hawayen daya cikamata fuska tace.... "MOSLIM!! Kayi haƙuri nasaba da faɗin hakanne domin sunan Ubangijinmune amma ka gafarceni bazan sake faɗinsaba matuƙar ina cikin wannan gari naku,kasani SOn da nake maka zai iya sakani komai kuma komai kyansa ko muninsa gareni ko ga wani na.MOSLIM!!Ina gamaka da girman abin bautarku kasoni koda dai-dai da zarra ni hakanma ya ishe ni,idan kuma bazaka soni ba kasanar dani domin na kashe kaina dan hakan shizai zama mafita agareni" Ta k'arasa faɗa tanamai toshe bakinta saboda yadda wani kuka mai ƙarfin gaske ya ƙwacemata ba tare data shirya masa ba. Tunda MUSLIM ya sauke idansa akanta har kawo yanzu bai saukesuba saboda yadda yakejin zuciyarsa na bugawa da ƙarfin gaske yanajin babu daɗi kukan da takeyi agabansa tana neman temakonsa,sunkuyar da kansa yayi tare da ɗagowa ya kalleta yace da ita..... "Shin zaki iya sanar dani wane irin SO kikeyimin?" "Ina yima SO irin na matar da bata taɓa haihuwaba tsawon shekaru,kwatsam seta samu ciki ta haifi yaro ko yarinya,sannan tinda ta haifi wannan cikin bata sake samun wani ba dan haka ta ɗauki son duniya ta ɗorashi akan wannan abinda ta haifa,to inamai tabbatar maka da inamaka SO wanda yafi wannan domin ni nawa son da nakema bansan silar farawarshiba kuma bansan danme nake sonka ba nidai kawai na tsinci kaina asoyayyarka kuma zan iya komai saboda soyayyarkaa" Jinjina kai yasakeyi tare da kallon cikin k'wayar idanunta sannan yasake cewa...... "Kince zaki iya komai saboda SOna to idan nace ki kashe kanki zaki iya?" Cikin hanzari yaga ta mik'e da sauri tanufi can lokon gadon data kwanta ta tsugunna tare dasaka hannu cikin wani k'aton kwando wanda aka shaƙeshi da kayan marmari ta ɗauko wata sharɓeɓiyar wuk'a da aka saka acikin kwandon tare da zare murfinta ta saita maƙogaronta da ita......... "Koba komai zanyi alfahari da wannan rana da wannan lokaci dazan kashe kaina kuma marubuta zasu dinga rubuta labarin SOYAYYATA domin tasha ban-ban data sauran masoya,sai dai SOYAYYATA tasamu naƙasu daga ɓangaren masoyina,kuma naso ace kaine zaka kasheni da hannunka yadda bazanji zafin yankan dazakai yayin kasheni ba sai dai naji daɗi kasancewar soyayyace tasa zaka kasheni ba ƙiyayya ba,ina sonka!ina sonka!!ina sonka mosleem!!!" Tana faɗin haka ta sake saita wuƙar tare da rintse idanunta,zata burmata kenan Muslim yabuɗe iya k'ololuwar muryarsa tare da sufa ya dira kusa da ita ganin tana daf da aikata abinda ta faɗa ya hankaɗata kan gadon dake kusa da ita......... ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ SARKI KAMALUD-DEEN yana zaune cikin shigarsa ta alfarma anata fadanci kwatsam sarkin zance yace..... "Allah ya temake ka! Tun ɗazu wasu bafulatanai guda biyu suka iso kusa da wannan fada kuma da alama kai suke son gani" "Tom madalla!Sarkin zance meyasa baka sanar mana tunda wuri ba saida suka gaji da jiranmu?" "Allah yaja zamaninka!Ayimin afuwa ajizanci ne irin naɗan adam na manta ne ranka shi daɗe" Nan take sarkin yayi umarni da ashigo dasu fada domin aji meke tafe dasu.Hakan kuwa akayi bayan sun kwashi gaisuwa sunzauna ne aka Umarci ɗaya daga cikin manyan garin wanda asalinsa bafulatani ne aka umarceshi daya tambayesu meke tafe dasu.......... 🙌🏻🙌🏻🙌🏻🙌🏻anzo wajanfa mutane na🤗🤗ko yaya za'a ƙarke da ZULMAT da MUSLMAT da MUSLIM⁉️ Muna daf da tafiya ⚔️WATA DUNIYA⚔️🌍dan haka kowa yai shirin tafiya nidai nagama nawa.Dan Allah kudinga min uzuri sbd yanayin posting ɗin nawa👏🏻. 👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻 DAN ALLAH INA NEMAN ALFARMARKU"ALLAH KABAWA KHADEEJAH LAFIYA MAI ƊOREWA DAN ƘARFIN IKONKA"ABINDA ZAKUCE KENAN DAN ALLAH.NAGODE🥰😍 MORE COMMENT MORE TYPING. DOMIN GYARA,SHARHI KO BADA SHAWARA ATUNTUƁENI TA WANNAN LAYIN👇🏻 07047530638. ƳAR GATAN MAMA✍🏻. ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ LABARI/RUBUTAWA KHADIJA S.SAMINU (ƳAR GATAN MAMA) Marubuciyar...... A WANI GIDA RAYUWAR MU! MAGANIN KAR AYI! nd now...... ⚔️WATA DUNIYA⚔️ ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.ƘURAINABU IDRIS YARO YAHYA ALLAH YAJA DA RAI YAƳARA LAFIYA AMEEN. ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ SHAFI NA 31&32. ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ Bayan ya tambayesu ne nafarkon ya matso inda aka umarceshi tare da fuskantar sarki yanamai sunkui da kansa yace..... "Allah yuttin zamanma ardujo min emijodi eh wuttudo gelle ma amma emi lei undalma ehlamuma,Allah rene amma emi shoggumarle bel eh na i eh bali miwadi shoggu eh goddo hadiyan shede an moyi mocyamide mohokkitata yande hanjun wadi bimi dun tetanayan halal an" Bayan ya gama bayaninsa ne aka buƙaci ɗayan shima yafaɗi ƙarar daya kawo dan haka nan da nan ya matso tare da cewa..... "Allah yuttin zamanma ardujo emider lamorde de e de fulbe riskube mihokki goddo cymade amma bo mosalake mohokkitatayande mo cyamide" Bayan sungama bayaninsune sarki yabuƴaci wannan bafulatanin dakejin HAUSA daya fassara musu domin su san kalar hukuncin dazasu yankewa maganar tasu. Jin haka shikuma ya gyara zamansa cikin ladabi yace..... "Allah ya temakeka! Na farko yace 'Allah yaja zamaninka!Ni na kasance ina agefen wannan gari naka amma ina ƙarƴashin kulawar wannan masaurata taka.Allah yaja zamaninka! Na kasance ina cinikayyar dabbobi da shanu,dan haka munyi ciniki da wani amma ya hanani kuɗina sannan yace ma yacinye bazai biyaba shiyasa nakeson aƙwatar min haƙƙina'.Shikuma na biyun yace'Allah yaja zamaninka!Ina daga cikin bafulatanan wannan masaurata masu arziƙin shanu,nabawa wani mutumi rance na kuɗaɗe masu yawa amma ya hanani ya cinyemin kuɗina'.Wannan shi ne abinda suka faɗa Allah yaja zamaninka,amma ni aganina duk kusan abu ɗayane yake damunsu" Nan sarki yayi gyaran murya tare da faɗin..... "Amm! Ka tambayar mana su shin suna da shaida?" Cikin bin umarni ya kalli na farkon tare da cemasa...... "A wodi shaidujoba?" Nan bafulatanin ya kalleshi tare da sunkuyar dakai yace......Bashi da shaida. Sarki da kansa ya gyara zama tukunna yace dasu..... Ayanzu baku da shaida ko hujjar da zatasa akama waɗanda suka riƴemuku kuɗi saboda faɗin Allah acikin alƙur'ani maigirma yana cewa' Ya ku waɗanda suka bada gaskiya! idan kukayi mu'amala ta bashi (ko sautu ko rance)izuwa ajali abin ambato,to,ku rubuta shi(don ujiyewa ga jayayya)marubuci yayi adalci(acikin rubutun ,kada yayi daɗi acikin dukiya da ajali ko ragi)kada marubuci yaƴi rubuta irin yadda Allah ya sanar da shi ya rubuta,(don abinda aka rubuta shi ne ke tabbata)wanda haƙƙi ka kansa yabada shifta,(yayi furuci da abinda yake kansa)yaji tsoron Allah Ubangijinsa (acikin shiftar) kada ya tauye komai (daga abinda ake binsa),idan wanda haƙƴin nan yake kansa ya kasance wawa(almubazzari,ko rarrauna ga barin shifta saboda ƙanƴanta ko girma ko bashi da ikon yin shifta saboda bebantaka ko rashin sanin yare) to, waliyinsa ya bada shifta,(mahaifinsa,ko wani wasiyinsa ko kuma mai tafinta,ya bada shiftar da adalci,ku kafa shaidu guda biyu) akan wannan bashin daga mazajenku balagaggu musulmai ƴaƴa ye,ku musulmi idan shaidun nan basu kasance mazaje biyu ba,to mutum guda da mace biyu su shaida,daga waɗanda kuka yarda dasu na daga shaidu(saboda addininsu da adalcinsu,amfanin mata biyu a shaida)saboda in ɗaya ta mance (shaidar)to ɗaya wacce bata manta ba ta tinawa ɗaya wadda ta manta,kada shaidu suƙi idan an kirawo su(izuwa ɗaukat shaida ko bada ita)kada ku ƙosa daga rubuta haƙƙin da ku kaƙi shaida akansa,(saboda yawan abukuwa)k'ank'ane ne haƙƙin ko mai yawa,izuwa ajalinsa.Wannan rubutawa shi yafi adalci nan ga Allah,(saboda abinda aka haddace ba kasafai yake zama ba)shi ne yafi dai-dai ga shaida,(don shi ne maganin mantuwa)shi ne kuma yafi kusa izuwa ba za'ayi kokonto (acikin gwargwadon haƙƙi ko ajali ba)sai ko idan tazama ciniki mahalarciya(ta yau da kullum)ku ke ma'amala da ita a tsakaninku,(wacce baku rubuta wani ajali ba),to ba laifi a gareku in baku rubuta ba,ku shaidar idan kunyi ma'amala ta ciniki (saboda shine yafi ije saɓani),kada a cuci marubuci (da a kallafa masa ya rubuta abinda bai kamata a kallafa masa ya rubuta ba,)kada a cuci shaida (da akallafa masa ya shaidar da abinda bai kamata ya shaidar ba).To idan kuka aikata (abinda aka haneku ga barinsa,)to wannan (aikatawan nan)fasiƙanci ne a gareku,(watau tawaye ne ga Allah,)kuji tsoron Allah (acikin amru da nahyu).Allah yana sanar daku (masalahohin al'amarinku.Allah masani ne da komai'......Wannan shi ne faɗin ubangii akan bashi da mu'amalar yau da kullum da bada shaida da ladaban ma'amaloli da gargaɗi acikin tsare gaskiya acikin kowace ma'amalar ciniki ko waninsa,da bayanin shiryar da bayi izuwa maslahohin duniyar su ,domin duniya gonar lahira ce.Gyaran lahira bazai yuwuba saida gyaran duniya,saboda haka Allah yayi bayanin gyaran duniya da wannan aya wacce itace mafi tsawon ayoyin alƙur'ani mai girma". Cikin hikima wannan bafulatanin yayi musu bayani inda aƙarshe dai ɗaya ya dubeshi kana yace..... "Allah walle miyardake eh lamuma mi anditi eh yerdaki jomirawo inifu itata goddun seto mitefi jomirawo" Da haka sarki yasa anemo waɗanda suka cinyemusu kuɗin ba'asamosu ba dan haka sarki yasa akayimusu alkairi mai yawa sannan suka tafi.Jin daɗin hakan kuwa suna komawa segasu sundawo da kirdirmo da man shanu kiriga guda sunkawo kyauta ga sarki.Yau da haka zaman fada yaƙare inda suka gaisa da NUJBEER ƊAN NAJABURU ya jaddadamasa cewar yaufa saura kwana biyu sui tafiyar nan dan haka yasake shiri fitar yammaci zasuyi. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Koda su DUUJALA!! da GIMBIYA ZULMAT suka tafi tunani kawai yakeyi yanda zaiyi idan ya mallaki TAKOBIN WATA DUNIYA⚔️⚔️⚔️domin yana hango yadda zaidinga sare kawunan sarakunan MUSULMAI sannan ya mallaki garuruwa da mutanen cikinsa,yasan ƴarsa ZULMAT da son sarauta dan haka yamata alƙawarin zaibata idan ta kawomasa TAKOBIn amma azuciyarsa zancen yasha ban-ban domin kafin takawomasa zaiyimata abinda koyace tahau kujerar baazata iya hawaba,idan kuma tahau zaiyi sihirin da inhar ta doshi kujerar sedai taji wucin wuta yana tunkarota yadda bazata iya ƙarasawa ba sedai dole ta barshi akai ita tagama aikinta kenan domin kuwa bayajin zai iya barin mulkinnan alhali idonsa ya garau,dan yarigada yasan lokacin mutuwarsa akwai nisa dan haka dole ya shaƙata...... ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ 👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻 DAN ALLAH INA NEMAN ALFARMARKU"ALLAH KABAWA KHADEEJAH LAFIYA MAI ƊOREWA DAN ƘARFIN IKONKA"ABINDA ZAKUCE KENAN DAN ALLAH.NAGODE🥰😍 MORE COMMENT MORE TYPING. DOMIN GYARA,SHARHI KO BADA SHAWARA ATUNTUƁENI TA WANNAN LAYIN👇🏻 07047530638. ƳAR GATAN ƁMAMA✍🏻. ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ LABARI/RUBUTAWA KHADIJA S.SAMINU (ƳAR GATAN MAMA) Marubuciyar...... A WANI GIDA RAYUWAR MU! MAGANIN KAR AYI! nd now...... WATA DUNIYA🌍 ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.ƘURAINABU IDRIS YARO YAHYA ARZAI.ALLAH YAJA DA RANKI YAƳARAMK LAFIYA AMEEN. ⚔️🌍🌍🌍⚔️ SHAFI NA 33&34. ⚔️🌍🌍🌍⚔️ Haka ZALIMUZ-ZAMAN yagama nazarinsa kaf kafin daga bisani yaishiri domin shiga fada. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Koda SARAUNIYA SINIYYA ta isa ɓangaren MUSLIMAT seda sukakai ruwa rana kafin ta buɗemusu ƙofa saboda sanya kuka tayi batare data faɗi dalilin kukannata ba,koda Sarauniya taga tafito juyowa kawai tayi batare data yimata magana ba wanda hakan ya tilastawa MUSLIMAT biyosu batare data dena kukanba,koda sarauniya ta isa daf da shiga inda su ZULMAT da MUSLIM suke zuwanta keda wuya sega MUSLIMAT inda isowarsu yayi dai-dai da da ƙarajin muslim yana faɗin...... "Kada ki kashe kanki ZULMAT saboda soyayyata,na yarda zan..."Se kuma sukaji yayi shiru wanda hakan ya tabbatar musu babu lafiya dan haka sukashiga da saurinsu domin ganewa kansu abinda ke faruwa. Isarsu keda wuya suka hangi ZULMAT akan gadon da MUSLIM ya hankaɗata faɗuwarta yayi dai-dai da shigar wuƙar ta wuda dantsen hannunta inda cikin rashin sa'a wuƙar tashiga jikinta sosai jini sai malala yake yi. Gaba ɗayansu babu wanda hankalinsa bai tashiba har ita mai gayya mai aikin MUSLIMAT seda ta girgiza duk da acikin zuciyarta tana ayyana dama ZULMAT ɗin ta mutu koda soyayyarta ta tsira. cikin ruɗani MUSLIM ya riƴeta yana kuka lokacin dayaga hannunta na zubda jini amma ahaka take ƙoƙarin ta ɗaga wuƴar tasokawa cikinta tare da cewa"ZULMAT ki tausayawa mahaifinki,ki tuno mahaifiyarki ki tausayawa masoyanki karki kashe kanki saboda ni domin ni...." "Domin kai me?" MUSLIMAT tai maza ta tari numfashinsa da faɗin hakan. "Domin ni ayanzu zan iya yadda da soyayyarta ko yanzu matuƙar nima zata yimin ɗaya" Cikin gigita da zancen da ZULMAT taji MUSLIM na furtawa tasakar masa wuƙar hannunta tare da motsa leɓanta wanda yake jajir irin na kyawawan indiyannan tasaki murmushin ƙarfin hali tare da cewa.... "Menene abu ɗayan da zanyima ka karɓi soyayyata?" "Ki karɓi addininmu na musulunci ki gasgata Allah ɗaya ne bashi da abokin tarayya,nikuma inhar kikabar addinin iyayenki da kakanninki nayimiki alƙawarin baki soyayyata tare da baki kowace dama akaina dama kowace buƙata da zakizomin da ita nikuma zan amince" ZULMAT ta runtse idonta tare da sunkuyawa takama zancen zuci. "Inada tabbacin addininsu yafi namu komai da komai kuma shi ne addinin gaskiya ba namu ba,to amma yazanyi da mahaifina?Mtsww!To ai shima jikina yana bani munafuntata yakeyi dan haka nima zanje masa ahakan,amma dai inajin tsoro,kai to wanema tsoro zanji tunda yayimin alƙawarin bani soyayyarsa kuma nasan shi bazai yaudare niba,hakan na nufin yarabu da MUSLIMAT kenan?" Tana isowa nan atunaninta tai maza ta ɗago da fararen idanuwanta masu tsananin kyau ta saukesu akan SARAUNIYA da MUSLIMAT sannan tadawo da kallonta ga MUSLIM tace.... "Abaya nayi tunanin wannan ranar zata zomin wato ranar da zan shiga addinin musulunci,amma daga baya sena lura shiɗin hatsari ne agareni dan haka na fidda rai daga gareshi har nafara tunanin kodai nima banda rabo acikinshi kamar mahaifina?" Cikin matsanancin mamaki su duka suka ɗago suka kalleta jin tace daman tanason shiga addinin musulunci tare da son jin wane daliline ya canza mata ra'ayi taji ta dena son shigarshi.Sake ɗagowa tayi ta kallesu tare da sakarmusu wani ƙayataccen murmushi wanda yasake fito da zallar kyawun da take da shi. Kallon-kallo sukeyi tsakaninsu anrasa mai bakin magana dan haka ZULMAT ta dubesu tafara magana kamar haka........ ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ 👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻 DAN ALLAH INA NEMAN ALFARMARKU"ALLAH KABAWA KHADEEJAH LAFIYA MAI ƊOREWA DAN ƘARFIN IKONKA"ABINDA ZAKUCE KENAN DAN ALLAH.NAGODE🥰😍 MORE COMMENT MORE TYPING. DOMIN GYARA,SHARHI KO BADA SHAWARA ATUNTUƁENI TA WANNAN LAYIN👇🏻 07047530638. ƳAR GATAN MAMA✍🏻. ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ LABARI/RUBUTAWA KHADIJA S.SAMINU (ƳAR GATAN MAMA) Marubuciyar...... A WANI GIDA RAYUWAR MU! MAGANIN KAR AYI! nd now...... WATA DUNIYA🌍 ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA MAHAIFIYATA HJY.ƘURAINABU IDRIS YARO YAHYA AIZAI.ALLAH YA DAFAMK YA BARMU TARE AMEEN. ⚔️🌍🌍🌍⚔️ SHAFI NA 35&36. ⚔️🌍🌍🌍⚔️ AUNTY HUMAIRA FILLO INAMK FATAN ALKAIRI TARE DA FATAN HAIHUWAR YAN BAKWAI😎KISAMU KIYIMIN TAKWARA🥰🥰😂😂Allah yabar zumunci nabaki wannan shafin kiyi yadda kikeso dashi🙌🏻🙌🏻✨✨. ⚔️⚔️⚔️ "Wata rana mahaifina SARKI ZALIMUZ-ZAMAN sun ziyarci wani ƙauye dake cikin garin KANWA me suna ALBAS domin neman wani YANKI wanda duk matsafin daya mallakeshi to afaɗin duniyar nan babu wani shu'umin da zai kadashi koda kuwa yana aiki da kafatanin aljaun dake faɗin wannan duniya. Wannan YANKI idan kasameshi zaka tawo dashi gidanka sannan zaka haƙa wani rami acikin turakarka ka binneshi yadda ko ruwan sama baazai iya fito dashi ba.To da zarar ka mallakeshi zaka samu ƙarin matsayi acikin matsafan dake wannan duniya tamu kuma zaka mallaki ƙananun Aljannu da shuwagabanninsu,zasu zama aƙarƙashin ikonka domin baazasuyi wani abu batare da umarninka ba.Alokacin da suka isa wannan ƙauye na ALBAS an gwafza yaƴi mai matuƙar firgitarwa wanda cikinsu ba wanda bai fidda raiba ciki kuwa harda mahaifina,bayan wahalar da sukasha wadda baazata faɗuba aƙarshe mahaifina yasamu nasarar mallakar wannan YANKI da temakon mahaifiyata mai suna LUSH-SHIFAH ta temakeshi matuƙa wajan ganin yasamu wannan yanki saboda wani temako daya yimata sanda ya shigo garin. LUSH-SHIFAH ƴace ga SAIBUL-LIDAH wanda ya daɗe da barin duniya sanadin wani yaƴi da sukaje basu samu nasaraba se gawarwakinsu aka tsinta duk da hakama ba'aga wasuba,tun bayan mutuwar SAIBUL-LIDAH mariƙiyar LUSH-SHIFAH take gallaza mata itace komai na gidannan duk wahalarsa haka zatayisa koda zai silar kwanciyarta rashin lafiya,to asanda su ZALIMUZ-ZAMAN suka isa garinsu se ya haɗu LUSH-SHIFAH da tulun ruwa akanta inda hannunta kuma yake ɗauke da karare wanda duk safiya itake zuwa tasamosu dasu ne za'a girka abinci suci,kuma duk ranar da bata da lafiya bata samu damar ɗebowaba to tabbas wannan rana babu mai bata abinci awannan gida.Koda yaganta yadda take tafiya daƙyar se hakan ya tabbatar masa da cewa awahale take saboda duk alamunta sun nuna hakan tana tafiya tana hutawa kamar wadda ƙwai ya fashewa aciki. Koda ZALIMUZ-ZAMAN ya tozali da ita seyaji yakamu da matsananciyar soyayyarta wadda tausayinta da yaji yai sanadiyar hakan agareshi,saukowa yayi daga kan raƙuminsa ya karɓi kararen hannunta yaɗorasu bisa raƙuminsa yatemaka mata harzuwa gida,suna tafe suna taɗi har suka iso inda yakejin kamar karsu rabu saboda yadda yakejin daɗin muryarta kasancewar akwaita dazaƙin murya sekace sarewa.LUSH-SHIFAH akwai matsanancin kyau me ɗaukar ido sannan fara ce tas! kamar atsaga jini yafito haka take,ga zireren hancinta kamar antsaida kara saboda tsayuwarsa,bakinta ɗan ƙarami ga leɓɓan jajir dasu sekace na jarirai sa'ilin da haƙwaranta suke jere farare karr! gwanin ban sha'awa idan tana motsa bakin tana magana dan haka ta tafi da imaninsa.Ba ramammiya bace ba haka kuma bata da muguwar ƙiba intaƙaicemuku irin matannan ne tsaka-tsaki domin LUSH-SHIFAH ta haɗa komai na kyau sedau cikas ɗinta ɗaya RASHIN GATA!.Koda LUSH-SHIFAH taji abinda yakawo shi garinsu setayi shiru tana tunani kafin daga bisani tace masa yatafi amma idan gari yayi duwu yadawo zata bashi saƙo. Koda ta shiga kallon banza da hantara ta shashi ƙarshema aka raba abincinta biyu aka bata rabi tare da watsawa akuyoyi rabin akace saboda tafita ta tsaya da ɗan cirani ba'asan daga inda yafito ba,babu yadda ta iya haka taci zuciyarta babu daɗi inda kuma wani gefe na zuciyarta ke tunanin yadda zata bawa ZALIMUZ-ZAMAN sirrin da inhar ya yishi zai samu wannan YANKI dayazo nema. Haka kuwa akayi dare nayi segashi yadawo zauren gidansu inda yaɗebi ƴasa yaita watsawa jikin wani langa-langa kamar yadda tacemasa yayi idan ya iso donta hakanne zata gane isowarshi,koda taji haka tai maza ta fito hannunta ɗauke da wata ƴaramar akwatu me azababben kyau famiƙa masa. "To ni yanzu yazanyi da wannan abu da kika bani?" "Wannan sune makaman da zasu temakama wajan cirar wannan YANKI domin wannan tanadin mahaifina ne,ya tanadin waɗann abubuwa daf da tafiyarsa ta ajali kuma yasha wahala wajan samosu,kayi gaggawar barin wajannan tunkafin aganka kaje kayi amfani da tsafin da kake dashi kagane komai,idan kagane kafito da duku-duku tunkafin zakara yayi cara ka doshin kogon da zaka ciri wannan yanki inamai tabbatar maka kaine zaka cireshi indai kayi yadda nafaɗama" Yaji daɗin matuƴa dan haka ya buɗe baki da niyyar yimata godiya kwatsam yaji tana ihu tana cemai yatafi,baimusu ba yatafin saboda tozali da wani mutum daya fito daga cikin gidan yahau jibgarta kamar bazai barta ba,ya tausaya mata sosai dan haka ya ƴuduri aniyar bazaibar wannan gari ba seya aureta kodan yarabata da rayuwar gidansu wadda yakejin dashi ya tsinci kansa aciki da tini yadaɗe da guduwa saboda bayason wahala da aikin wahala. Kamar yadda ta umarceshi haka yayi inda yasamu nasara bayan baƙar wuyar dayasha.Anyi ɗebi ba daɗi kafin subashi auren LUSH-SHIFAH saboda basason tayi auren yanzu saboda koba komai zata wuta da wani abin amma dake lokacinta yayi badan son ransuba suka bashi ita saboda sun ganshi cikin koɗaɗɗun tufafi azatonsu matsiyaci ne,haka tai sallama da kowa ana zunɗenta ta auri matsiyaci domin basusan wane ne ZALIMUZ-ZAMAN ba. Zama sukeyi cike da so da ƙaunar junansu domin babu wani gurbi dabai cikeba cikin zuƙatansu,basu wani daɗeba LUSH-SHIFAH tasamu ciki na,murna agun mahaifina abin ba'a magana domin kyaututtuka masu girma yake bawa duk waɗanda sukazo yimasa barka da samun rabona.Sanda ta haifeni ya raɗamin sunan yayarsa wato ZULMAT. Duk wani so da kulawa iyayena sunbani domin kowa so yake ya nunawa ɗan uwansa yafini ƙaunata,kwatsam tafiya ta tasowa mahaifina zaije ya yaƙi wani garin musulmai,to tafiyar zata ɗaukeshi lokaci mai tsawo dan haka yatafi da ni da mahaifiyata wanda awannan tafiyar ne mahaifiyata ta samu tashiga addinin musulunci batare da mahaifina yasani ba!Koda suka dawo tana cigaba da addininta dai-dai saninta akansa domin tashiga binciken litattafai iri-iri ahaka ta iya komai na musulmai bada saninsaba hartakai ga tana koyamin wasu abubuwan aɓoye duk da lokacin ina da yarinta. Wata rana da bazan taɓa mantawa da itaba arayuwata mahaifiyata ta ɓoye acikin ɗakinta tana sallah nikuma ina mata gadin ƙofar da ni da wata amintacciyarta ASIYA wadda itama ta samu tashiga addininku silar mahaifiyata,haka mukeyi duk lokacin da ɗayanmu zai sallah sai mutum biyu su tsare hanyoyin shigowa gudun kar wani yagani yasanar da mahaifina.Ni ce wadda nake saitin ɗakin nata cikin tsautsayi naga mangwaro ya faɗo natafi domin ɗaukarshi inda cikin rashin sa'a mahaifina yashiga ɗakin ya taddata tana sallarta hankalinta kwance,takaici da ƙunar zuci suka ziyarci mahaifina lokacin daya fuskanci wannan sallartata bata ɗan koyo bace alamu sun nuna tadaɗe tanayin abarta aɓoye wanda hakan yatabbatar masa da tadaɗe tana munafuntarsa mebi ma akwai wata manufa aranta tanason ta cutar dashi nan gaba ta cishi da yaƴi. Cikin hanzari ya koma turakarsa tare da ɗauko sharɓeɓiyar takobinsa yanufi ɓangaren mahaifiyata,isowarsa keda wuya na iso ina haki tare da sakin wani irin kuka wanda abaya banyadda mutum na kuka kamar ransa zai fita ba sai a wannan lokacin,kuka nake ina roƙon mahaifina akan kada yakashe mahaifiyata amma sam yaƙi saurarata inda........ ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Nagode sosai da jimirin bibiyata da kukeyi🙋🏻‍♀️🙋🏻‍♀️🙋🏻‍♀️✨💞💞. 👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻 DAN ALLAH INA NEMAN ALFARMARKU"ALLAH KABAWA KHADEEJAH LAFIYA MAI ƊOREWA DAN ƘARFIN IKONKA"ABINDA ZAKUCE KENAN DAN ALLAH.NAGODE🥰😍 MORE COMMENT MORE TYPING. DOMIN GYARA,SHARHI KO BADA SHAWARA ATUNTUƁENI TA WANNAN LAYIN👇🏻 07047530638. ƳAR GATAN MAMA✍🏻. ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ LABARI/RUBUTAWA KHADIJA S.SAMINU (ƳAR GATAN MAMA) Marubuciyar...... A WANI GIDA RAYUWAR MU! MAGANIN KAR AYI! nd now...... WATA DUNIYA🌍 ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYANSHI GA MAHAIFIYATA ABAR ALFAHARINA HJY.ƘURAINABU IDREES YARO YAHYA.ALLAH YAJA DA RAI AMEEN. ⚔️🌍🌍🌍⚔️ SHAFI NA 37&38. ⚔️🌍🌍🌍⚔️ Allah Kashiga lamuranmu dan arziƙin masoyinka💖MUHAMMADUR'RASULULLAHI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA💖. 💖💖💖💖💖💖💖💖 YA MUHAMMAD✨✨ 💖💖💖💖💖💖💖💖 YA RASULULLAH✨✨ 💖💖💖💖💖💖💖💖 Ina ƙaunarka ya Rasulullahi banda wata buƙata awajan Ubangijinka bayan soyayyarka,ya Nabiyullahi ka roƙamini ƙaunarka🤲🏻🙌🏻✨✨✨ 💖💖💖💖💖💖💖💖. Kuka nake ina roƴon mahaifina kada ya kashe mahaifiyata amma sam yaƴi saurarata inda aƙarshe yajawoni jikinsa tare da saka hannunsa laya tsakanin wuyana yaɗaga ɗayan hannun nasa tare da faɗin sunan abin bautarmu da ƴarfin gaske ya sarewa mahaifiyata kai....." Kuka ne yaci ƙarfin ZULMAT inda tacigaba da yin abinta jikinta na tsuma kamar ana kaɗa mata gangi,tausayinta ne yabi ya lulluɓesu baki ɗayansu amma banda MUSLIMAT saboda gani takeyi Zulmat duk tana yin hakanne saboda ta samu soyayyar MUSLIM. Sarauniya da kanta tabata ruwa tasha sannan taci gaba da cewa..... "Koda yasare mata kai saiya cikani ya maida dubansa ga ASIYA data duƙa gaban mahaifiyata tana kuka mai taɓa zuciya tare da addu'o'i wanda ni bansan su ba tana jifan mahaifina da munanan kalamai kamar su"azzalumi maci amana,kafirin banza da wofi kaje Allah zaibi mata haƴƴinta insha Allahu bazaka mutuba sai kaga sakamakon abinda kayiwa ZAINAB(YUSH-SHIFAH)wanda shi ne sunan data buƴaci asanya mata sanda ta karɓi addinin musulunci.Koda ZALIMUZ-ZAMAN yaji kalamanta se itama yasa takobin hannunsa yasauke kanta kusa dana mahaifiyata sannan yajuya yai ficewarsa.Fitarsa yayi dai-dai da tsugewar ruwan sama me azababben ƙarfi ga wata guguwa wadda take barazanar ɗaga muhallanmu ta watsar,walƙiya akeyi hasken yana shigowa inda nake zaune da gawarwaki tamkar aciki ake walƙiyar saboda hasken dake mamaye gawarwakin,kukan danasha na wannan rashi da nayi shi nr kuka na farko da nasan nayi nakuma kasa mantawa dashi se kuma kukan yau wanda soyayyarka ta sanyani. Tirƙashi!!!😰Ashe duk wannan rashin imani da mahaifina ya gwadawa mahaifiyata akan idona bai ishe shiba,domin kuwa bai bari anfita dasu garin musulmai anyi musu sallah ba,kuma bai bari anhaɗa wuta anƙonasu ba seya saka su awani gu inda yake gudanar da tsaface-tsafacensa ahaka dai bansan ya gawarsu ta ƙare ba.Kewar mahaifiyata ta isheni tare da tunanin rayuwata nan gaba,ahaka na girma cikin tsoron musulunci wanda mahaifina yake sanyamin akoyaushe. Yakan zauna ya maida hankali wajan faɗamin illolin shiga musulunci wanda tun bana yadda har na dawo ina tsoronsa tuƴuru,akwai lokacin da muka taɓa fita yaƙi muka haɗu daku har kake yimin tayin addininku ida baka manta ba da farko naso na karɓa saboda kalmomi da kake faɗamin masu daɗin sauraro amma daba baya sena tuna yadda mahaifina ya kashemin mahaifiya saboda musulunci,amma ayanzu a shrye nake dako mene ne zaifaru dani yafaru inhar zansamu soyayyarka kuma bazaka haɗa soyayyata data wata ba! Ko wacece kuwa awannan DUNIYA!!" Kallon kallo aka shiga yi tsakanin MUSLIM,SARAUNIYA SINIYYA da kuma MUSLIMAT saboda jin abinda ZULMAT tace..... SARAUNIYA SINIYYA ta sunkuyar da kanta ƙasa tare da sakin wani murmushi mai haɗe da jin daɗi dakuma baƙin ciki.Jin daɗin nata shi ne ZULMAT zata karɓi addinin gaskiya wato musulunci tabar kafirci sannan zata tayasu yaƙar kafirai masu bijirewa wato ma'abota girman kai,baƙin cikinta kuma shi ne yadda MUSLIMAT takasa fahimtar gwaggwaɓan ladan dazata samu idan ta sadaukar da soyayyar da takeyiwa MUSLIM to amma ko taƙi ko taso dole tabarwa ZULMAT tinda ayadda abu yafito fili ZULMAT tafita son MUSLIM tinda har zata iya barin addininta da danginta akansa,tashi tayi gaba ɗaya daga inda take tare da komowa inda ZULMAT take zaune takamo hannuwanta ta sakasu cikin nata sannan tafara mata magana kamar haka..... "Nikam alabarin da kika bamu naji kince mahaifiyarki na sallah mahaifinki ya kasheta,shin ita batai yunƙurin cetar kanta ba?" "Yake wannan Sarauniya mai adalci! Inamai tabbatar miki mahaifiyata batai yunƙurin ceton kanta ba alokacin sema cigaba dayin sallarta da tayi,lokacin da ta ɗago tana shirin ta sunkuya mahaifina ya sauke kanta ƙasa..." Shiru tayi tare da sunkuyar da kanta ƙasa wasu zafafan hawaye suka samu hanyar gangarowa daga idanuwanta suka fara rige-rigen sauka ahannunta dake ajje kan cinyarta,taɗauki lokaci ahaka sannan ta ɗago da kanta fuskar nan tayi jajir idanunta ya kaɗa kamar babu fari acikinsa tace..... "Ya Shugabata! Ina so ayanzu base anjima ba kisadani da wanda zai shigar dani wannan addinin naku na musulun...." Batakai ƙarshe ba wata mahaukaciyar guguwa mai ƙarfin gaske wacce take haɗe da ƙananun duwatsu ta fara buga ƙofofin dake inda suke kana taratso ta iso inda suke........... ⚔️⚔️⚔️⚔️⚔️ TOFA KUDAI KUBIYONI DOMIN SAURA ƘIRI MUTAFI IZUWA WATA DUNIYA MAI CIKE DA WAHALHALU,SHIN KOWAYE ZAICI NASARA ACIKINSU❔✨💞💞. 👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻 DAN ALLAH INA NEMAN ALFARMARKU"ALLAH KABAWA KHADEEJAH LAFIYA MAI ƊOREWA DAN ƘARFIN IKONKA"ABINDA ZAKUCE KENAN DAN ALLAH.NAGODE🥰😍 MORE COMMENT MORE TYPING. DOMIN GYARA,SHARHI KO BADA SHAWARA ATUNTUƁENI TA WANNAN LAYIN👇🏻 07047530638. ƳAR GATAN MAMA✍🏻. ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ LABARI/RUBUTAWA KHADIJA S.SAMINU (ƳAR GATAN MAMA) Marubuciyar...... A WANI GIDA RAYUWAR MU! MAGANIN KAR AYI! nd now...... WATA DUNIYA🌍 ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYANSHI GA MAHAIFIYATA ABAR ALFAHARINA,ALLAH YAƘARAMIKI LAFIYA AMEEN. ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ SHAFI NA 39&40. ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ Kowa ƙoƴari yakeyi ya kare idanunsa saboda yadda guguwar take shigowa kai sekace iya zallar ƙasa da duwatsune suke shigowa babu iska. Guguwar nan ba ita ta tsayaba har tsawon daƙiƴa dubu ɗaya da ashirin da biyu da rabi sannan ta lafa yayinda su dukansu sun cure guri guda.Ga mamakinsu se sukaga wasu ƙananun baƙaƙen tsuntsaye sun kewaye ɗakin yayin da wasunsu suka yiwa kansu mazauni ajikin ƙofar shigowa babu abinda kakeji se kukansu wanda yake fita mara daɗin sauraro....... Girgiza sukayi atare sannan suka buɗe bakunansu lokaci guda sega wuta tafito wadda babu makawa idan ta sauka jikin mutum seta ƙonashi. Cikin ƙarfin hali da tsananin ɓacin rai GIMBIYA ZULMAT tamiƙe tsaye tare da ɗaga hannunta sama ta sunkuyar da kanta tare da buɗe baki tawura wata iska sannan tasake ɗaga ɗayan hannunnata sama take sega wani mulmulen haske ya bayyana cikin daƙiƙu goma sha uku ta fuskanci wutar da tsuntsayen nan suka turomusu take wutar ta koma ga tsuntsayen suka hau ci da wuta suna iface-iface ahaka seda suka ƙone ƙurmus se tokarsu ke zuba ƙasa. Ajiyar zuciya ta sauke sa'ilin da taga tokarsu tana zuba alamun tagama dasu,juyowa tayi ta kalli su MUSLIM wanda kawai kallonta sukeyi tare da neman ƙarin bayani daga gareta,fuskantar hakan datayi yasa tahaɗe fuska kaɗan tarage murmushin da take masa kana ta tafi gadan-gadan bangon ɗakin cikin ƙiftawar ido bangon yatsage ta shige cikinsa..... "Shin ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ LABARI/RUBUTAWA KHADIJA S.SAMINU (ƳAR GATAN MAMA) Marubuciyar...... A WANI GIDA RAYUWAR MU! MAGANIN KAR AYI! nd now...... WATA DUNIYA🌍 ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.ƘURAINABU IDRIS YARO YAHYA ARZAI ALLAH YAƳARA LAFIYA AMEEN. SISINAH✨DAGA NAN HAR NA ƳARE NABAR MIKI SHAFUNAN NAN KIYI YADDA KIKESO DASHI✨💖💞💞. ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ SHAFI NA 41&42. ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ Kallonta ZULMAT tayi batare da tace komai ba ta koma masaukinta zuciyarta cike da tunani kala daban-daban. Tunani ne yabi ya addabeta ta rasa aduniya yanzu mene keyi mata daɗi,to yanzu meya kamata tayi kenan,haka dai tana saƙawa da warwarewa har dare ya raba batare data rintsaba saboda yau jitakeyi sam bazata iya bacci ba,daga sashenta tana juyo haniniyar dawakai da motsi mabanbanta saboda dare ya raba ana shirin fitowa.Bata ankaraba taji alamar aba taɓa ƙararrawa,tashi tayi domin taga wanda aka turo kiranta. "Fata na akullum ki samu ki rabauta da addinin gaskiya" Muslim ta gani jingine aƙofar ɗakin nata ya nannaɗe hannuwansa aƙirjinsa yana kallonta fuskarsa ɗauke da wani yalwataccen murmushi, ƙuramasa ido tayi bata ko ƙyaftawa saboda yadda taga daga rabuwarsu zuwa yanzu kamar sake zubamai wani kyan akayi daban bayan nasa.Sun ɗauki aƙalla mintuna goma sha biyar atsaye batare data buɗe baki tayimai magana ba,ganin haka yasa yasake ɗaga leɓensa na sama sannan yace....... "Alamu sun nuna baki bacci ba,ina fatan dai lafiya ko?" Firgigit tayi tare da ɗan sunkuyar da kanta saboda lokaci ɗaya taji wata kunya ta lulluɓeta,ɗan mutsutstsuka idanuntw tayi sannan tace.... "Babu komai,nayi bacci kaine ka tashe ni" Sake dubanta yayi kana yace..... "Yanzu ne zamu ɗauki hanya ina fatan ashirye kike?" Da "to" ta amsa masa sannan takoma cikin ɗakin inda babu daɗewa tafito da ƙaramar akwatinta wadda tace bazata iya tafiya babu ita ba. Gaban MUSLIMAT ne yayi mummunar faɗuwa sanda taga harda ZULMAT za'a tafi "Wato harda kafira zamu tafi kenan? to taje tayi mai,wannan ai sedai ta kafurtar da musulmi badai ta musuluntar da kafiri ba,yazama dole nayi maganin rashin kunyar kafirar nan..." Haka taita zantukan zucinta ranta aɓace danji takeyi kamar taje ta shaƴe Zulmat ta huta. Sarauniya cikin shigarta ta alfarma ta fito sannan ta tsaya sukayi addu'o'in samun nasara sannan suka nufi WATA DUNIYA🌍⚔️. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ NUJBEER ƊAN NAJABURU shi ne farkon wanda yafara fitowa domin tafiyar,daya fuskanci duk basu shirya bane yaɗau abin busa yahau busa cikin sulusainin daren da kowa ke sharar bacci masu gwaggwaɓan rabo kuma na tsayuwa domin neman biyan buƴatunsu.Busawa yake yi ba ƙaƙƙautawa sekace maroƙin da yaje fada,cikin wani irin salo yake busar inda iska take aikin ɗaukar sautin nasa tana ratsa makwancin mutanen garin taje kunnunwansu.Hakan da yayi yasaka mutane mamakin kodai wani abune ke faruwa haka basu sani ba? kafin kace me! tini wajen yacika da al'umma kamar filin idi,mayaƴan garin kowa yaɗauki makaminsa domin zatonsu gagarumin tashin hankali ne ya iso musu wanda basu shiryawa ba. Cirko-Cirko mutane sukayi suna kallonsa tare da yin zantuka marasa fita sosai wato dai ƙunƙuni.Faɗi suke ba daban tsufansa ba da se sun ladaftar da shi.Ba jimawa Sarki Kamalud-deen yafito da tawagarsa inda shima yasaɓi jakarsa suka nufi barin masaurautar,ai se sannan jama'a suka fuskanci dalilinsa na cikamusu kunnuwa da busa amma duk da haka wasu basubar Allah wadai ba,ahaka dai suka ɗauki hanya domin shiga ⚔️WATA DUNIYA🌍. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Tunda suka fara tafiya basu tsaya ba seda suka iso wani katafaran daji wanda ya banbanta da na nahiyarsu me cike da ababen tsoratarwa,ahalin da suke ciki rana ce amma ayadda idanunsu ke gani zaka ce dare ne ya tsala ba rana ba,wani irin sanyi ne mai shiga cikin ƙashi ke ratsa ilahirin jukkunansu yana sakasu makyarkyata. So suke su yada zango amma kuma zuciyarsu tafi yarda dasu cigaba da tafiya dan sun ƙagu subar wannan baƙin dajin su shiga wani kosaji daɗin tafiyar........ Sunyi tafiya wadda zata ɗebi awanni biyar dan lokacin suna da yaƴinin magriba tayi,dan haka ne suka yada zango domin suyi sallah suyi buƴatunsu kafin su san abinyi awannan dajin.Wani Kogo suka hanga can gabansu cikinsa akwai haske tamkar ba acikin yake ba dan haka........... 👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻 DAN ALLAH INA NEMAN ALFARMARKU"ALLAH KABAWA KHADEEJAH LAFIYA MAI ƊOREWA DAN ƘARFIN IKONKA"ABINDA ZAKUCE KENAN DAN ALLAH.NAGODE🥰😍 MORE COMMENT MORE TYPING. DOMIN GYARA,SHARHI KO BADA SHAWARA ATUNTUƁENI TA WANNAN LAYIN👇🏻 07047530638. ƳAR GATAN MAMA✍🏻. ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ LABARI/RUBUTAWA KHADIJA S.SAMINU (ƳAR GATAN MAMA) Marubuciyar...... A WANI GIDA RAYUWAR MU! MAGANIN KAR AYI! nd now...... WATA DUNIYA🌍 ⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️ *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.ƘURAINABU IDRIS YARO YAHYA ALLAH YABAKI TSAWON RAI MAI AMFANI DA LAFIYA MAI ƊOREWA AMEEN. OUM MUS'AB✨HABIBTY💖💖💖✨Allah yabar ƙauna ya ƙarfafi alƙalaminki tawajena✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ SHAFI NA 43&44. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Kallon-kallo suka shigayi tsakaninsu sannan suka yanke shawarar shiga wannan kogo domin su huta sannan su sake ɗaukar hanyar sui gaba. Sarauniya ta sakko daga kan dokinta sannan tayi tattaki kana tabasu umarnin kowa ya sauka domin shiga wannan kogon. Wata ƙaramar ƙara tasaki wadda tabi iska tashiga kunnuwansu batare data sani ba,sake sako ƙafar tata tayi da niyyar ta sakko nan tasakejin kamar tasoke da tsinin takobi wanda hakan yasa tasaki ƙarar mai amo yadda kowa ya fuskanci daga indaƴarar tafito.Muslim ne yayi saurin dawowa da baya domin yaga meke faruwa da ita,yana kallon inda ƙafarta take yaga jini yana zuba kamar anwuda ƴafartata..... "Me ya sameki haka baki magana da wuri ba?" Ya faɗa tare da riƴe ƙafartata yana kallon yadda ta runtse idanunta da alama tanajin zafin yadda jinin ke fita aƴafarta,ran Muslimat ne ya ɓaci taji kamar taje ta shaƴe Zulmat dan gani take yi duk abinda Zulmat keyi tana yine danta muzguna mata. Sarauniya kam batasan meke faruwa ba dan tuni sunshige cikin wannan kogo ita da tawagarta,sunyi maɗaukakin mamaki ganin yadda kogon yake da girman gaske kamar ba'a cikin wannan baƙin dajin yake ba.Girmansa yafi ƴarfin tunaninsu domin kuwa wannan kogo aƙaramin ƙiyasi zai iya ɗaukar mutane dubu biyar zuwa sama batare daya girgizaba,yana da wani irin haske na ban mamaki sedai hasken baya kashe idanu,idan kaɗaga kanka ka kalli saman kogon zakaga dutsen kamar an ɓuɓɓulashi saboda wasu wuda-wuda dake saman kuma duk wasu alamu sun nuna daga wannan wudar ne hasken ke fitowa,dubansu suka kai can wani loko acikin kogon inda batare da sunyi zatoba sukaga ƙunshi-ƴunshin kaya mabanbanta da akwatuna wanda hakan ya tabbatar musu koba yanzu ba mutane ko wasu halittun sun zauna acikinsa. ⚔️Koda Muslim yaji bata bashi amsaba seya temaka mata ta sauko ƙasa tukunna yafara ƙoƙarin saka mata magani wajan da taji cuwon.Haniniyar dawakai ne suka cikamusu kunnuwa tare da wata irin guguwa wadda take tasowa daga kudu dasu,cikin gaggawa suka fara ƙoƴarin shigewa cikin wannan kogo inda aka saka mayaƙa abakin kogon domin tsaronsu. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Tunda su NUJBEER ƊAN NAJABURU suka ɗauki hanya basu tsaya ko'ina ba se katafaren garin ILBAS wanda dagashi tafiyar kwana shida ce zata kaisu 🌍WATA DUNIYA🌍 Saukarsu keda wuya suka hau shirye-shiryen yadda zasui da tantance waɗanda zasu shiga WATA DUNIYAR acikinsu. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Mayaƴan kowa yaɗaga takobinsa domin jin da gaske mutane ne zasu iso inda suke,dawakai aƙalla sunkai tamanin ne suka dannakai ɗauke da mutane akansu hannayen kowannensu ɗauke da itace yanacin wuta,saurin mayar da takubbansu sukayi domin sun lura waɗannan mutanen ba wannan ne karon farko na shigowarsu dajin ba saboda itacen da suka gansu dashi yasa suka gane hakan. Batare da faɗa ko wani mugun abuba suka sauko daga kan dawakansu sukayi cirko-cirko inda cikin daƴiƴu saɓa'in sega wani ƙayataccen doki ya ratso daga cikin na bayansa ya iso sahun gaba ɗauke da wata haɗaɗɗiyar farar mace mai tsananin kyau da kwajini ko'ina na jikinta anƴawatashi da kayan ado masu ɗaukar ido.Yana isowa yai wata girgiza segashi cikin ƙiftawar ido dokin ya ɓace yakoma wata sihirtacciyar kujera ta gold matar na zaune akanta ƙafarta ɗaya kan ɗaya tana kallon mayaƴan sarauniya Siniyya. Kafin kace me tuni an sanar dasu Sarauniya Siniyya cewa ga mazauna wannan kogo sun dawo,babu musu ta umarci mutanenta dasu fito subawa masu wajan gunsu,ɗaya daga cikin tawagarta ne yace.... "Allah yaja zamaninki! Me zaisa mufita bayan ba ginawa sukayi yazama nasu ba✍🏻 👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻 DAN ALLAH INA NEMAN ALFARMARKU"ALLAH KABAWA KHADEEJAH LAFIYA MAI ƊOREWA DAN ƘARFIN IKONKA"ABINDA ZAKUCE KENAN DAN ALLAH.NAGODE🥰😍 MORE COMMENT MORE TYPING. DOMIN GYARA,SHARHI KO BADA SHAWARA ATUNTUƁENI TA WANNAN LAYIN👇🏻 07047530638. ƳAR GATAN MAMA✍🏻. NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA 'DAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA ARZAI ALLAH YAJA DA RAI AMEE. 💖💖Mmn Masoyi (HASSANA IYAYI MMN NOOR) Har ko yaushe bazan gaji dayimiki addu'ar Allah yasakamiki da alkairi ba,Allah y biyamiki dukkan buk'atunki ameen💖💖 ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ SHAFI NA 45&46. ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ "Allah yaja zamaninki! Me zaisa mufita bayan ba ginawa sukayi yazama nasu ba?" Kallon Bawan dake magana SARAUNIYA SINIYYA tayi dakyau sannan tace mass... "Lokacin da muka tsinci kanmu awannan daji mai cike da ikon Allah bamu sakawa ranmu zamu samu mafaka ba,sannan bayan shigowarmu munci Karo da k'unshi-k'unshi na kaya Wanda suka tabbatar mana akwai wad'anda suka rigamu zama awannan waje. Shin idan muka cigaba da zama bamu fitaba yaya sunanmu awajansu? Kana ganin zasu rabu damu ne?,sanin kanku ne idan muka zauna bamui musu adalci ba,me guri yazo dan haka abashi wajansa" Tana kaiwa nan azancenta tasakai aka kareta tukunna tafice domin bawa masu wajan wajansu.Fitarta ke da wuya ta hangi Matar da ke zaune kan k'asaitacciyar kujerarnan tana ta karkad'a k'afa da k'arewa kowa kallo rai ahad'e kamar wadda akawa laifi nashirin d'aukar mataki.Inda take Sarauniya ta dosa tare da mik'a Mata hannu tai Mata sallama,itama babu musu ta mik'amata hannun saidai bata cemata komai sek'in sakin hannun da tayi,kowa ya tsaya yana kallon yadda ta rik'e hannun Sarauniyar. Sarauniya ce ta d'ago da kanta ta kalli matar jin yadda hannunta ke zugi da rad'ad'i kamar taji ciwo Ana barbad'amata gishiri,wani shu'umin murmushi tagani kwance afuskar Matar da alama ita cikin farin ciki take,yunk'urawa tayi domin ta janye hannunta amma hakan yak'i yuwuwa,idanunta takai kan hannuwannasu domin meke faruwa.... YA ALLAH!!! Abinda SARAUNIYA SINIYYA ta iya furtawa kenan sands idanunta yagane mata yadda hannunta ya daddare duk yayi jajur jini yafara samun hanya.Sake d'ago kanta tayi suka had'a ido da Matar inda Matar ta kashe Mata ido d'aya tare da sakar Mata wani shu'umin murmushi tace.... "Wace ce ke dahar kika shiga sasena?" "Me wace ce da baza'a Shiga sasenki ba? Ki saketa tunkafin kiga wace ce it an" GIMBIYA ZULMAT ce ta mayar Mata da martani cikin kakkausar murya me cike da gargad'i. Ran Matar ne yakai k'ololuwa wajan b'aci dan haka cikin zafin nama ta furzar da iskar dake bakinta sannan ta sanya hannunta ta hankad'a Sarauniya gefenta inda Sarauniyar takifa k'asa tana kiran sunan Allah. YARIMA MUSLIM ne cikin zafin nama ya tawo da guru daga inda yake tsaye domin zuwa ga Sarauniyar... Cikin matsanancin b'acin rai Matar tayi wata girgiza Wanda cikin dak'ik'ar da batafi biyu da rabi ba Yarima Muslim yajishi ad'ad'd'aure kuma anti sama dashi.Cikin tashin hankali tawagar Sarauniya dama sarauniyar suke kallon Matar wadda ta rikid'e tazama rabinta mutum rabinta macijiya. "Kiyi gaggawar saukeshi tun kafin kisan koni wace ce,ki rabu dasu ko kum.." "Ko kuma me!!?" Matar ta tambayi Gimbiya Zulmat tana zazzare idanu kamar taiwa sarki k'arya. "Ko kuma kigane ke k'aramar hatsabibiya ce,sannan.." Ai bata gama maganarta ba Matar ta bud'e bakinta tare da wuro mutsu wuta mai azababben zafi....✍🏻 👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻 DAN ALLAH INA NEMAN ALFARMARKU"ALLAH KABAWA KHADEEJAH LAFIYA MAI 'DOREWA DAN K'ARFIN IKONKA" ABINDA ZAKU CE KENAN DAN ALLAH.NAGODE🥰😍 MORE COMMENT MORE TYPING✍🏻 'YAR GATAN MAMA✍🏻 NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA 'DAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA ARZAI ALLAH YA JIK'AN MAGABATANKI YAYI MUSU RAHAMA AMEEN. 🌍'YAN WATA DUNIYA FANS🌍NA BAKU SHAFINNAN KYAUTA💖 ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ SHAFI NA 51&52. ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ "Yana daga cikin hatsabibancinta ko da mutuwa kikai akamiki amfani da ita sai kin dawo ya rayuwarki kamar ba abinda ya faru da ke,hakama idan ciwo kikaji da zarar kika karata ajikin ciwon cikin k'ank'anin lokaci zai koma fiye da baya,domin zaki samu lafiya ta ke ba tare da b'ata lokaci ba,sannan...." Tana zuwa dai-dai nan azancenta tai hanzarin mik'ewa tare da zuwa inda MUSLIMAT take yashe ta karamata ita ajikinta,cikin k'ank'anin lokacin tahau tari tare da yin wani amai na dafin saran da MACIJIn yayi Mata.Haka ta ringa binsu sannu-sannu tana karamusu suna tashi Wanda se a k'arshe ta nufi inda SARAUNIYA DA MUSLIM suke,cikinsu tahau tunanin wa zata Fara sanyawa ne? ' Tabbas idan nafara sanya masa za'ace saboda ina k'aunar sa ne,kuma mutanen wajennan zasu tabbatar da son zuciyar da nake d'auke da shi' tuna haka yasa da sauri ta nufi kan sarauniya ta sanya Mata ajikinta ta ke Sega hasken Takobin ya mamaye ilahirin jikinta cikin k'ank'anin lokaci itama tahau aman tare da mai da kanta k'asa tana maida numfashi,ganin haka yasa GIMBIYA ZULMAT ta Ciro mazubin dake sak'ale a wuyanta d'auke da ruwa ta mik'awa Sarauniyar ta karb'a Tasha. Mamaki yabi ya cika zuciyar MUSLIMAT ganin d'awainiyar da ZULMAT take ta yi dasu,abin ya k'ayatar da ita sai dai rashin kula inda MUSLIM yake ya dameta dan haka ta dubi ZULMAT tare da cewa..... "Hmm! Ko ba komai dole a yabamiki bisa namijin k'ok'arin da kikayi akanmu awannan lokacin,sedai zuciyata ta kasa aminta da ke har yanzun domin ina ganin tsantsar munafunci da son zuciya acikin idanunki,nikam ban aminta da keba kuma ban aminta da son da kikeyiwa YARIMA ba tunda har kika iya barin wani abu ya cutar dashi ke kuma kika tseratar da rayuwarki" A fusace Gimbiya ZULMAT ta juyo da dubanta ga MUSLIMAT ta tsaya ta kalleta tsawon dak'ik'u bakwai da rabi sannan ta sakar Mata wani shu'umin murmushi mai sauti Wanda har seda hak'waranta suka bayyana tsantsar kyawunta ya sake fitowa sannan tace.... "Hhhh!!! Bara kiji wani Abu, 'Wata rana munfita yak'i tare da mahaifi na,kusan ranar anci mu da yak'i domin kuwa d'ai-d'aiku ajama'armu suka tsira,koda komai ya lafa...Mahaifina ya shiga k'ok'arin ceton ran jama'arsa,seda ya tabbatar da ya gama dasu tukunna ya tunkari inda nake, koda aka tambayeshi dalilin hakan se yace da jama'arsa" Na bar d'iya ta ne ak'arshe saboda na bata kulawar da ban bawa wani ba awannan waje,domin Ku duka temakon gaggawa nabaku,ita kuma bazan iya bata k'ank'anin lokaci ba sabida ita ce RAYUWATA!!! Da ita nafara dubawa afarko inamai tabbatar muku sunanku matattu domjn koda naga ta farfad'o Zan shagalta da kallonta ne sonta na ninkuwa azuciyata" Koda mutanen sukaji haka se kowa yakama bakjnsa har muka is a gida. To ananma haka ne Nafi sonsa fiye da komai nawa ciki harda numfashi na...Sannan ni nasan bazai mutu yanzu ba se ya cikamin alk'awarirrikan da ya yimini,sannan" "Sannan ya kashe ki,ya rage kafirci da kafirai irinki?" ....... ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ ALJANI DUUJALA! Ya had'a tattarin Aljanun tare Fara magana kamar haka.... "Sanin kanku ne Abin bauta HUZNAZ shi ne yake bamu sa'a adukkan shirinmu da mukeyi,kuma jna tabbacin yanzuma shi zai bamu ita awannan waje da muka zo,inason duk Ku cire tsoron da ke ranku Ku kashe duk wani bil'adama matuk'ar yazo ne saboda yad'ebi dukiya da wannan Takobi...Mene ra'ayinku?" Wani Aljani mai sanyin hali da sanyin d'abi'u dake amsa sunan ASH yabud'e baki yace.... "Ya Shugabanmu! Raina ya cika da tsoro game da lamarin d'aukar wannan takobi,sanin kanmu ne bazamu iya d'aukarta ba se mun kasance cikin musulmai,to Yaya kenan zamuyi idan ubangijin musulunci ya bawa mabiyansa wannan sa'ar muje mushiga uk.." Bai k'arasa maganarsa ba wani Aljani d'an tumurmuri yai tsalle tare da fad'in.... "Akwai dabara" Dukansu suka juyo gareshi danjin wace dabara ce haka... "Dabarar ita ce,mu tafi wajan wani sarki mai bin UBANGIJIN MUSULUNCI saimu ce mass munaso mu biyashi ya shigar damu,da zarar munshiga saimu cakud'a dash my d'akko bayan komai ya kammala saimu komowa addininmu na iyaye da kakanni ya kuke gani?" Cike da jin dad'in shawarar tasa suka had'a baki tare da sakin wani razanannan ihu mai firgitarwa,bayan ihun ya lafa ne ALJANI ASH ya dubesu tare da cewa...... ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ SARKI KAMALUD-DEEN ya yanke shawara tare da umartar Tsoho NUJBEER 'DAN NAJABURU ya karb'i addinin ISLAMA kafin su shiga wata duniyar..... 👏🏻👏🏻👏🏻ALLAH KAJIK'AN MAGABATANMU KAYI MUSU RAHAMA,ALLAH IDAN TAMU TAZO KASA MUCIKA DA KALMAR 'LA'ILAHA ILLALLAHU MUHAMMADUR-RASULULLAHI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA,ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMADIN WASALLAM💖 More comments more typing✍🏻. Domin gyara sharhi ko bad a shawara atuntub'eni ta 07047530638. 'YAR GATAN MAMA✍🏻 *____________________________________* ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ LABARI/RUBUTAWA KHADIJA S.SAMINU ('YAR GATAN MAMA) MARUBUCIYAR 👇🏻 RAYUWAR MU! A WANI GIDA MAGANIN KAR AYI (Kar a soma) RANA DUBU (Ta b'arawo...) And now.... ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA 'DAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA ALLAH YAJA DA RAI YA BADA RABO MAI AMFANI AMEEN❤️ ❤️❤️❤️K'awata kuma Yayata ta amana(AYSHERCOOL) Allah ya k'ara lafiya yasa kankarar zunubai ne,Allah y k'ara basira da hazak'a ameen❤️❤️❤️ ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ SHAFI NA 53&54 ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ .......✍🏻 Koda BOKA NUJBEER 'DAN NAJABURU yaji wannan Batu na Sarki sai ya kalleshi fuskarsa d'auke da dariya sannan yace.... "Yanzu Kai banda abinka inakai ina fad'amin wannan kalma haka mai zafin gaske? Zafin Kalmar nan ya kusa ya k'ona ni,tunda sauran k'arfina akemin tayi amma lokacinma duk Wanda yamin tayin daga wannan maganar baya sake wata Dan a take nake ganin bayansa,kaima na rabu dakaine saboda buri na yana tattare da Kai" Koda yagama wannan said yabar gaban Sarki tare da komawa can nesa dasu ya zauna ya tsunduma tunani. WAIWAYE..... NUJBEER 'DAN NAJABURU gawurtaccen matsafi ne Wanda yayi suna sunan da duk Wanda yazo azamaninsa saiya sanshi saboda hatsabibancinsa,yasha gwagwarmaya tsakanin mabiya addininsa da mabiya addinin musulunci,bai tab'a fad'uwa ba kasancewar ya mallaki duk wani abinda zai taimakamai tsakaninsa da wani mahaluk'i dake doron duniya,ya kashe bil'adama yanda ko shi kansa bai isa ya k'iyasta adadin ran da ya kashe ba,ba wani buri ne dashi ayanzu haka ba illa burin d'aukar Takobin wata duniya wadda bincikensa ya tabbatar masa idan ya d'auketa to tabbas ko shed'an la'ananne se ya sarawa shed'ancinsa domin shi zai zama yana mulkar dukan wash masuji da tak'adaranci da tsafi afad'in duniyar nan,sannan bincikensa ya tabbatarmai akwai wani kogo acikin WATA DUNIYA Wanda ake kiranshi KOGON HATSABIBAI acikin wannan kogo akwai wata rijiya mai baki arba'in da d'aya,rijiya ta kowacce acikin akwai babban sirri da take d'auke dashi,rijiya ta bakwai tana d'auke da wani shud'in ruwa Wanda matuk'ar ka d'ebeshi ka wanke tundaga tsakar kanka had yatsa! To tabbas zaka dawo sabon mutum ma'ana yaro,idan ka dawo yaro zaka sake wanke jikinka dashi yadda zaka zama saurayi,idan kuma harka maimaita akaro na uku to babu makawa zaka koma tsoho fiye da yadda kake ayanzu wannan k'uduri yananan azuciyar NUJBEER 'DAN NAJABURU yana son yadawo k'arami ya k'ara dire hatsabibancinsa adoron k'asa. Wannan kenan... Koda NUJBEER 'DAN NAJABURU ya tashi sai sarki ya shiga dogon nazari akansa tare da mamakin girman Kai irin nashi,ahaka dai har lokaci ya k'ure suna tunani. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Bayan ALJANI ASH ya gyara zamansa akan dutse ne yai gyaran murya sanann yace... "Shin kun manta Ubangijin Musulunci ance yana ji yana ganin komai? Bakwa tunanin yajimu yazo ya wargaza mana shirinmu? Da-dai wata shawarar ba wannan ba" "Ka jika da wata magana kamar ba jarumi ba,wa..wa yace maka Ubangijin Musulunci yana jinmu yana ganinmu,ka duba kogonnan da kyau ka gani baabu wata k'ofa da wani zai lab'e ya jimu ko ya ganmu dan haka tsoro yafita aranka,Kai idanma baka yadda ba bara na mama misali...Lokacin iyayenmu da kakanni ina waje suke samu suyi sirri su had'a kalolin makircinsu kuma burinsu ya cika,idan har yana jinsu ya Hana burinsu cika mana" Bayan ALJANI DUUJALA ya gama wannan maganar haka sauran aljanun sukaita kawo hujjoji mababanta domain Aljani Ash ya yadda su canzamai tunani,tun yana musawa dai harya yadda sabida sarkin yawa yafi sarkin k'arfi. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ "Sannan ya kashe ki, ya rage kafirci da kafirai irinki?" Wani mugun kallo Gimbiya Zulmat ta watsamata sannan ta sunkuyar da manta k'asa idanunta sunyi jajur saboda b'acin rai jikinta yahau rawa kamar mazari,yunk'urawa tayi cikin zafin nama Wanda seda hantar cikin Muslimat ta kad'a saboda yadda ta razana da ganinta..... Domin gyara sharhi,ko bad a shawara 07047530638. 'YAR GATAN MAMA✍🏻. *____________________________________* ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ LABARI/RUBUTAWA KHADIJA S.SAMINU ('YAR GATAN MAMA) MARUBUCIYAR 👇🏻 RAYUWAR MU! A WANI GIDA MAGANIN KAR AYI (Kar a soma) RANA DUBU (Ta b'arawo...) And now.... ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA ARZAI. ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ SHAFI NA 55&56 ⚔️🌍⚔️🌍⚔️ Jikinta ne yahau rawa inda k'irjinta ke dukan dubu-dubu saboda tunanin me GIMBIYA ZULMAT zata yi Mata,ga mamakinta se gani tayi tazo ta wuceta taje kan YARIMA MUSLIM tana bashi kulawar da bata bawa kowa awajanba,duk inda zata tab'a ajikinsa se tayi kamar tayi kuka saboda ji takeyi tamkar ciwon ajikinta yake,ta bawa kowa mamaki barin MUSLIMAT da tayi bata kulata ba,kowa tunaninsa ya bashi zuwa zatayi taimata abinda bazata manta ba amma se suka ga sab'anin haka.SARAUNIYA SINIYYA tunda ta dawo cikin hayyacinta se tayi sujjada ga ubangijinta tana mai yi masa godiya bisa tseratar da su da yayi ta silar baiwarsa ZULMAT ta jima tana rok'awa Zulmat samun gwaggwab'an rabo wato rabon shiga musulunci,dukkan abinda ke faruwa akan I donta ya faru sedai ta sawa ranta bazata sakewa MUSLIMAT magana akan ta rage abinda takewa ZULMAT ba tunda ai kishi ba hauka bane ba. WAIWAYE..DEENUL-ISLAM✊🏻 A wani gari mai sun a DEENUL-ISLAM✊🏻 Anyi wani sarki Mai cikakken k'arfin mulki ya shahara matuk'a da gaske wajan gudanar da gaskiya acikin mulkinsa,yana da tsantsar tsoron Allah da k'ok'arin kamanta adalci atsakanin mabiyansa,hakan yasa jama'ar garin suke matuk'ar sonsa saboda yadda bashi da son zuciya ko kad'an a al'amuransa.SARKI ABDALLAH! Yana da Mata guda biyu GIMBIYA SUWAIBATU da GIMBIYA MAIMUNATU. GIMBIYA SUWAIBATU ita ce matarsa ta lalle wadda al'ada ta zab'a masa ita amatsayin abokiyar rayuwa,ita kuma MAIMUNATU se bayan ya zama Sarki ne aka tilastamai se ya k'ara aure kasancewar sarki baya zama da mace d'aya. Allah ya bawa SARKI ABDALLAH son haihuwa Dan 'ya'yan 'yan uwansa kamar nasa ya d'auke su yana ji dasu yanda bazaka iya tantance nasa ne kona waninsa ba.Ubangiji sarkin hikima da iyawa,da ya tashi sai bai azurta GIMBIYA SUWAIBATU da haihuwa ba tsawon shekara goma sha d'aya lokacin GIMBIYA MAIMUNATU tana da shekara d'aya agidan SARKI ABDALLAH! Kuma cikin ikon Allah se gata da ciki ,bayan ciki ya cika watanninsa ya isa haihuwa Maimunatu ta haifi d'anta namiji mai kama da Sarki Abdallah sak Murna da farin ciki ba kalar Wanda Maimunatu batayi ba haka ma Suwaibatu tayi murna iya iyawarta tabada gudummuwa sosai awannan haihuwa. Lokacin da ta haihu Sarki bayanan sunyi wata tafiya se dawowa yayi ya tarar da abin farin ciki ya same su,yayi farin ciki sosai sedai bai nuna yadda ya kamata ba agaban mutane hands hakan yai sanadiyar sanyawa Gimbiya Maimuatu jin wani Abu azuciyarta har danginta suka zugata suka cemata duk shirin Suwaibatu ne saboda bata da k'wan da zata kalla shiyasa ta shiga ta fita ta hanashi farin ciki saboda ba haka taso ba. Wannan hud'ubar ta samu mazauni mai girman gaske azuciyar Maimunatu Wanda hakan ya jawo ta Dena yadda d'anta yadena zuwa hannun Suwaibatu koda kwa gata-gata ne saita hanata ko tace yunwa yake ji ko makamancin haka.Wannan Abu da MAIMUNATU ke yiwa SUWAIBATU yafara damun SARKI ABDALLAH saboda ko agabansa yana ganin yadda take hanata d'aukar MUJAHEED(sunan Yarima) gashi yaron jininsu ya had'u da GIMBIYA SUWAIBATU da ya ganta ya ringa wangale baki kenan ta d'aukeshi amma Maimunatu ta Hana.Abin duniya yabi ya ishi GIMBIYA SUWAIBATU kullum kuka da rok'on Allah ya bata haihuwa ko itama ta kalla taji dad'i. Allah maji rok'on bawansa kwatsam MUJAHEED na da shekara biyu da Rabi Sega GIMBIYA SUWAIBATU da juna biyu,zo kuga murna da farin ciki gun Sarki da duk wani masoyinsu,kowa yayi farin ciki da samun wannan ciki na GIMBIYA SUWAIBATU ciki harda wad'anda basason ta haihu abaya seda sukayi farin ciki saboda suna so suga yadda Maimunatu zatayi Dan tunda ta haihu ta samu lasisin hulak'anta Wanda ranta keso saboda gani take itace magajiyar wannan masaurata bayan ran Sarki tunda SUWAIBATU juya ce🥵 Tarairaya da tattali SUWAIBATU ta shashi wajan Sarki da Mahifiyar Sarki wato FULANI saboda akwai kyakkyawar alak'a tsakaninsu SUWAIBATU bata yards ta hulak'anta FULANI ba ganinta take kamar mahaifiyarta sab'anin MAIMUNATU da bata kallon kowa da gashi. Sannu-Sannu bata Hana zuwa sedai adad'e ba'a zona,lokacin baya k'arya dankwa cikin GIMBIYA SUWAIBATU ya isa haihuwa ko yau ko gobe amma ji kake shiru gashi ciki harya shiga wata na sha d'aya yana son fita amma haihuwa shiru sedai cikin yayi girman gaske Dan ko tashi yanzu ya gagareta,ganin haka yasa FULANI tasa aka kwashi GIMBIYA SUWAIBATU ta koma b'angarenta dan gani takeyi ba wata baiwa da zata iya kula da ita sai ita da kanta. Wata goma sha d'aya da kwana goma dai-dai GIMBIYA SUWAIBATU ta tashi cikin dare da wani azababben ciwon ciki Wanda yai barazanar tafiya da rayuwarta,taci matuk'ar wahala wadda bazata fad'u ba kafin Allah ya bata nasarar haihuwar yara biyu kyawawa MACE da NAMIJI..... ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMADUR'RASULULLAH💖 More comments More Typing. Domin gyara sharhi ko shawara 07047530638. 'YAR GATAN MAMA✍🏻 *____________________________________* ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ LABARI/RUBUTAWA KHADIJA S.SAMINU ('YAR GATAN MAMA) MARUBUCIYAR 👇🏻 RAYUWAR MU! A WANI GIDA MAGANIN KAR AYI (Kar a soma) RANA DUBU (Ta b'arawo...) And now.... ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA ARZAI.ALLAH YA SAKA MIKI DA ALKAIRI AMIN. .....KA FA'DI ALKAIRI KO KAYI SHIRU..... ......DAI DAN WANI KARKATACCEN WANI..... .....ABINCIN WANI GUBAR WANI..... ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ SHAFI NA 57&58 ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ Bayan GIMBIYA SUWAIBATU ta haifi yarannan biyu bata kuma sanin inda kanta yake ba har tsawon kwana uku bata d'auki yarannan ahannunta ba dan haka yaran suna k'ark'ashin kulawar FULANI mahaifiyar Sarki ABDALLAH.Acikin rana ta hud'u da haihuwarta ne aka fara ganin haske game da rashin lafiyar tata,d'aya bayan d'aya FULANI ta dinga d'ora Mata Yaran da ko suna Sarki yak'i sakamusu yace sai sunan da ta zab'a,ganin yadda tak'i sakewa da yaran yasa FULANI ta fita domin ta fuskanci har yanzudai SUWAIBATU tana nan da kunya yadda ake buk'ata sab'anin MAIMUNATU wadda da kanta ta d'auki MUJAHEED ta mik'awa Fulanin. GIMBIYA SUWAIBATU kamar jira take yi nan tahau rungumar yaran tana sumbatarsu had'e da sanya kuka Wanda ko ba'a fad'aba ansan na farin ciki ne,tun Sarki na kallonta har ya dakatar da ita da fad'in... "Haba ke kuwa Uwar biyu kukan ya isa haka mama,kodai kina tuna yadda aka dinga miki rowar yaro ne?, kiyi farin ciki Ubangijinki ya wanke miki bak'in ciki ya baki biyu mace da namiji babu ta inda kika samu tawaya,nikam ki dena kuka haka matar amana dan ni yanzu haka Zan iya kyautar yarannan idan zasu dinga sakamin ke kuka...Kinsan fa ina k'aunarki kamar nay..." Dariya ce ta k'wace Mata jin maganarsa sannan ta bud'i baki tace... "Nasan kana sona kana k'aunata kuma nima ta b'angarena hakan ne,sedai Zan rok'eka wata alfarma" Jinjina Mata Kai yayi alamun yana sauraronta dn haka taci gaba da fad'in.... "Ina neman alfarmarka ko bayan raina dan Allah kada ka fifita yarannan da MUJAHEED d'an wajan MAIMUNATU kayi adalci atsakaninsu domin dukansu d'aya ne awajanka sannan..." Katseta yayi ransa ad'an had'e kana ya jefeta da.... "Bazan iyaba...Idan nace Zan iya nayiwa kaina k'arya kema kinsani, na dad'e ina neman haihuwa daga gareki,har na samu bandena rok'on nasamu gudan jini na daga gareki ba seda na samu zaki fad'an kalar son da zan yiwa yara na? Ko kusa ma banson irin wannan maganar kowanne zai zauna amatsayinsa.Sannan maganar mutuwa ran kowa ahannun Allah yake dan haka kidena wannan maganar,wane suna kika zab'awa Yarima da Sarauniyar namu?" Dukda bataji dad'in maganar tasa ba haka ta lullub'awa fuskarta murmushi mai d'aukar hankali sannan tace... "Macen inaso asanyamin sunan Babata,duk da ina tantama akan sunan inatsoron Karna kasa tsawatar Mata idan tayi laifi,shi kuma asanya masa MUSLIM Ina rok'on Allah ya dawwamar dashi acikin musulmai yasa yazama mai kare musulmai,ko bayan raina kafad'a masa wasiyyata" Ta fad'a tana had'a hannunta alamar rok'o.Jikin SARKI ABDALLAH ne yayi sanyi jin yadda duk magana saita ambaci mutuwa dan haka sai ya karb'i yaran yai musu hud'uba sannan ya ajjesu ya matso kusa da ita ya rungumeta yana lallashinta dan ya fuskanci zafin ciwon data tashi ne ya Sanya Mata haka,suna ahaka shima wasu siraran hawaye suka zuba agadon bayanta Wanda suka fito a idanunsa batare da ya sani ba. Yarinya taci sunan FULANI wato HUSNIYYA inda ake kiranta da SINIYYA shi kuma MUSLIM.Anti shagalin suna Wanda ba'a tab'a irinshi ba a fad'in garin dama masu mak'otaka dashi taron ya samu halartar many an mutane inda yara suka tashi da many an kyaututtuka na bajinta da ban girma,anyi komai ya k'ayatar da mutane kad'e-kad'e da bushe-bushe babu kalar da ba'aiba marok'a sunci abinda sukaci awannan shagali domin Sarki yayi b'arin dukiya kamar baya sonta.Wannan kenan... FULANI tana matuk'ar k'aunar takwararta SINIYYA jinta take har ranta dan haka kusan awajanta take rayuwa dan seta buk'aci babarta sannan take maidata. Bayan GIMBIYA SUWAIBATU tayi kwana arba'in da haihuwa da kwana uku kwatsam ta tashi da wani matsanancin ciwon ciki Wanda yad'aga hankalin mutanen masarautar baki d'aya.Kwana d'aya tayi da ciwon nan tace ga garinku man...... Domin gyara sharhi ko bada shawara 07047530638. 'YAR GATAN MAMA✍🏻 *____________________________________* ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ LABARI/RUBUTAWA KHADIJA S.SAMINU ('YAR GATAN MAMA) MARUBUCIYAR 👇🏻 RAYUWAR MU! A WANI GIDA MAGANIN KAR AYI (Kar a soma) RANA DUBU (Ta b'arawo...) And now.... ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA 'DAYA GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA ARZAI,ALLAH YAJA DA RAI😍. .....Kowa yayi da kyau,zaiga da kyau..... ......Sharri d'an aike ne duk daran dad'ewa zai dawo maka daga inda ka aike shi.... .....Mu aikata alkairi ko badan kawunanmu ba don zuriyarmu,domin du Daren dad'ewa wannan alkairin namu zai zama abin ado ga Iyayenmu, 'yan uwanmu da 'ya'yan da zamu aifa yanzu ko nan baba...Ba iya nan alkairin zai tsaya ba,,,sai ya bimu har gidanmu na gaskiya inda babu makawa sai munje.... ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ SHAFI NA 59&60. ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ Kwana d'aya tayi tana wannan azababben ciwon cikin tace ga garinku nan... 'Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un' Wannan mutuwa ta GIMBIYA SUWAIBATU ta kad'a ilahirin jama'ar masauratar DEENUL-ISLAM dama kewayenta,dan kafin kace me tuni zancen mutuwarta ya zaga ko'ina yaje har indama ita kanta bata jeba. FULANI ta rud'e kuka kawai takeyi dan ita kanta ta kasa dauriyar da zata lallashi Mai Martaba ta bashi baki.Sarki ABDALLAH kuwa yana can baisan inda kansa yake ba dan ya suma har wad'anda ke tare dashi basusan adadi ba,kasancewar mutuwar tata bayan magriba ne akace abarwa safiya idan an idar da sallar asubahi asallaci gawarta.Cikin dare surutai Sarki ya ringayi har baisan me yake fad'aba danshi ayanzu ji yakeyi tamkar ba'a tab'a yimasa mutuwa ba aduniya sai yau,ya shiga matsanancin rud'ani ayau dan gizo GIMBIYA SUWAIBATU ta ringa yi masa gata tazo gabanshi tana fad'in " Zo kusa Dani mijina ina tare da Kai" Babu zato kawai sedai kawai aganshi ya rungume gawar yana dariya had'e da kuka harsai an rabashi da ita yake gane ashe ba gaske bane sai kansa ya kuma sarawa kamar zai fashe. Tun farkon dare FULANI tayi iya k'ok'arinta wajan saita nutsuwarta tare da godewa Ubangiji bisa wannan sak'on dad'i da ya iso musu dashi na d'aukar GIMBIYA SUWAIBATU,ta hana kowa zuwa inda yaran suke ciki harda GIMBIYA MAIMUNATU dake gurshek'an kuka Wanda FULANI tace na tsantsar munafunci ne,bayan ta Fara bawa yaran kulawar da ta dace ne ta umarci SARKI ABDALLAH da ya yiwa matar tasa wanka amma taga hakan bazai yuwuba saboda bashi da nutsuwa ita kuma bazata bari abarta haka batare da anyi mata sutura ba dan haka ta Kira mutum biyu daga makusantanta da kuma wata amintacciyar baiwarta wadda girma ya kamata ta buk'aci akawo komai da za'a buk'ata domin suyi Mata sutura. Bayan sun d'orata akan wani tudu d'aya daga cikinsu mai suna MARYAMU ta zauna ta fallafeta yayin da ita kuma FULANI tazama ita ke wanketa HANSATU na zubo ruwa yayinda BAIWAR FULANI ke nad'e ruwan daga wajan.Sun fara da Bismillah da kabbara sannan suka yimata Sarki da alwala kamar yadda akeyi sannan suka samu sabulu mai k'amshi suka wanketa da shi,saida suka wanketa sau uku (MAARA)sannan suka had'a tsarkakken ruwa suka saka ganyen magarya da d'an kafur suka d'auraye ta,bayan sun gama suka shimfid'eta akan doguwar sallaya mai kyau sannan suka d'akko auduga Fara kar suka toshe duk wata k'ofa dake jikinta Kama daga Gabanta,hancinta,idonta,kunnenta....Sannan suka d'auko likkafani shima fari kar burin duk wani mumini suka sakamasa turare me d'an karan k'amshi sannan suka saka Mata kamar yadda mukeyi bayan anrufe ko ina na jikinta ne aka saka mad'auri tunda k'afarta aka nannad'eta dashi tazama cikakkiyar Gaea sannan aka zuba yashi akan faranti aka d'ora akan cikinta gudun kumburin ciki😭😭(Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Allahumma arzuk'ni bish-shahadati indal-mauti...Allah kasa mu cika da kyau da imani kayi mana suttura duniya da lahira.Allah ka ciremana dirtyn dake cikin zuciyoyinmu ka ciremana hassada da k'yashi da magance mana cin naman juna kasa mu zauna d kowa lafiya.....Allahu akhbar Allah kayiwa dukkanin Wanda ya shaida da LA'ILAHA ILLALLAHU MUHAMMADUR'RASULULLAHI SALLALLAHU ALAIHI WASALAMA Rahama ka yalwata k'abarinsa dan arzik'jn masoyinka MUHAMMADU!!!).Bayan komai ya kammala ne wasu daga makusantanta suka shigo suka kwana tare da ita. Kamar yadda aka fad'a kuwa akayi bayan an idar da sallah aka sallaceta,gazkiya GIMBIYA SUWAIBATU ta samu al'ummar Annabi SAW fiye da tunanin mai tunani,acikin masauratar akwai wani b'angare da Sarki ya ware domin shi da zuriyarsa ananne aka sakata ad'aya daga cikinsu Wanda yake agefen dama dana Sarki idan Ilahu yayi kiransa yabar wasiyya nan za'a sakashi. Anyi komai cike da jimami har kowa ya watse akabar masarauta da 'yan cikinta,yara FULANI ta yanke shawarar d'akko wata daga danginta wadda take zaune agida dalilin rasuwar mijinta,haka kuwa akayi ta dawo masarauta da zama domin shayar da 'yan biyu Wanda so da k'aunarsu ya manage zuk'ata da dama. Tunda Allah ya d'auki ran GIMBIYA SUWAIBATU SARKI ABDALLAH ya d'auki son duniya ya d'ora akan yarannan,ji yake dasu dan ko k'uda bayason ya tab'asu, duk kwa Wanda ya nuna yana sonsu se Sarki yayimasa alkairin da har ya mutu bazai manta shiba,hakan da Sarki yake nunawa agaban kowa yasa GIMBIYA MAIMUNATU tad'au tsanar duniya ta d'orata akan marayun yaran da basu jiba basu gani ba,dan tun sanda FULANI tace bata yarda ta shayar dasu ba tasan akwai munafurcin da aka shirya. BAYAN SHEKARA GOMA SHA BIYAR... HUSNIYYA DA MUSLIM sun girma sosai kyawawa gwanin birgewa yara masu tarbiya da ganin girman mutane,tunda suka taso basu San babu ba ko bak'in cikin rayuwa wannan dalilin yasa basu fuskanci wani Abu ta fuskar maraici ba,kasancewar Sarki da FULANI sun fifitasu fiye da kowa amasarautar dan shi MUJAHEED babarsa ta riga da ta sakamai tsanar 'yan uwansa tare da girman Kai Wanda hakan yasa ko bayi idan sunganshi ala dole sukeyimai kirari sab'anin yadda sukeyiwa 'yan biyu kyautar Allah..... Allah kasa mu cika da kyau da imani ameen. Domin gyara sharhi ko bad a shawara 07047530638. 'YAR GATAN MAMA✍🏻 *____________________________________* ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ LABARI/RUBUTAWA KHADIJA S.SAMINU ('YAR GATAN MAMA) MARUBUCIYAR 👇🏻 RAYUWAR MU! A WANI GIDA MAGANIN KAR AYI (Kar a soma) RANA DUBU (Ta b'arawo...) And now.... ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA 'DAYA GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA ARZAI ALLAH YAJA DA RAI. K'awata Rahmatullah Allah amincin ubangiji ya tabbata agareki,ina mik'o gaisuwa mai suna gaisuwa😍😍 Allah mai iko da buwaya,na gama zancen mutuwa jiya yay se gashi muntashi da rasuwar wata yarinya alayinmu mai shekaru uku wadda k'yanda amai da gudawa sukayi silar mutuwarta,ina ta'aziyya ga k'awata Aminatuwa da 'yan gidansu baki d'aya Allah yayi Mata Rahama yasa ta huta,ita kuma aunty Hajja Allah yabata hak'urin rashinta ameen. ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ SHAFI NA 61&62 ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ MUJAHEED babarsa ta riga da ta sakamai tsanar 'yan uwansa tare da girman Kai Wanda hakan yasa ko bayi idan sun Gandhi ala dole sukeyimai kirari sab'anin yadda sukeyiwa 'yan biyu kyautar Allah.GIMBIYA MAIMUNATU ta rigada ta cusamasa son sarauta tare da kitsa masa HUSNIYYA(SINIYYA)da MUSLIM sune abokan adawarsa dan haka yasa jikinsa daga garesu,sannan yayi hankali da wannan tsohuwar dan bata k'aunarta bata k'aunar d'anta ya gaji sarauta,da Takawa ne kad'ai ta yadda yayi kusanci bayan ita acikin masarautar dan haka yazama baya girmama kowa agidan dan tunaninsa ya Fara komawa kan sarauta baki d'aya,idan yaga mutanen masarauta kallon k'ask'anci yake musu saboda tunanin da yakeyi nan gaba kad'an Sarki zai shek'a ya hau karaga ya taka kowa duk su zama a k'ark'ashinsa⚔️ Ahakadai rayuwa taci gaba da gudana SARKI ABDALLAH ya fifita 'yan biyu fiye da komai kuma su yake mallakawa komai nasa hakama FULANI duk garin Allah akwai abinda zata mallakawa Siniyya ko Muslim,awata ranar asabar FULANI ta buk'aci ganin Sarki da iyalinsa baki d'aya ita kanta FULANIN da GIMBIYA MAIMUNATU da amayarsa SARAUNIYA SAUDATU da wani mashahurin Sarki yabasa bayan mutuwar GIMBIYA SUWAIBATU saikuma yaran suma da kuma wad'anda keda alhaki n sanin komai amasarautar.Kowa ya hallara amma banda Maimunatu dan haka Fulani tasa akirata,koda tazo bata kalli kowa da mutunci ba ta samu ta zauna bayan ta gaida Fulani sama-sama.Fulani ce tayi gyaran murya tare da kishingid'a tafara fad'in... "Da farko dai zanfara da ta'aziyyar d'iyata Suwaiba wadda bazan tab'a mantawa da ita ba,muna fatan Allah yakai haske k'abarinta yasa ta dawwama ashugabar matan gidannan har acan gidan aljanna. Tabbas wannnan mata 'yar halak ce kuma zuciyarta tsarkakakkiya ce domin har a lokacin da take gangarar mutuwa wasiyyarta akan kada Mai Martaba yai banbanci tsakanin 'ya'yansa ne,to amma kowa yasan hakan bazai yuwu ba duba da rik'on maraya damai uwa araye bazai zama d'aya ba,to amma ke naki d'an rayuwar da ya keyi har gwanda ace marayane Wanda bashi da mafad'i,kinbi kin kanainaye rayuwar yaro da son zuciya da rashin ganin girman mutane,na miki magana ni da ke ba d'aya ba ba biyu ba,shima nasakashi yamiki magana basau d'aya ba amma naga alamun bazaki gyara ba,kinbi kinsa yaro yanajin Izza da jin shi wani ne saboda yana sa rai da mulkar al'umma... To Bari kuji baki d'ayanku ina magana ne cikin bada umarni ba neman shawara ba,ina so kuma ina umartarka da idan zakayi murabus ko bayan raina inason kabawa jikana MUSLIM kujerar da kake Kai...Idan kuma baya da muradi ko wani al'amari daban to lallai abawa HUSNIYYA sarautar wannan masarauta,ko da bana numfashi aba d'aya daga cikinsu sai dai idan basa raye sunbi salihar mahaifiyarsu to abawa d'an wajan Maimunatu sannan asanya salihan bayi su kewayeshi saboda mahaifiyarsa zata sakashi yayi shugabanci cikin zalinci sa son zuciya" Kowa na wajan kasa motsawa yayi saboda abin yafi k'arfinsu bayan haka kuma ba Wanda ya isa yaja da maganar FULANI ciki kuwa harda SARKI ABDALLAH da kansa.Gyaran murya Sarkin yayi tare fad'in.... "Allah yaja zamaninki! Kamar yadda kika fad'a haka ne,mun dad'e muna mamakin wannan hali Nata saidai babu yadda zamuyi,kowa da irin rayuwarsa.Wannan umarni da kika bamu muma mundad'e da irinshi acikin ranmu kuma muna da niyyar barin wasiyya akan hakan,amma tunda kinfad'a shikenan hakan za'ayi " GIMBIYA MAIMUNATU ce ta cika tayi fam dan haka tamik'e azuciye ko gabanta bata gani zata fita Fulani ta dakatar da ita da fad'in... "Idan ke kika kawo kanki kifita idan kuma kiraki akai ki zauna" "To ai naga anyi hakane dan a tozarta ni a hulak'antani ni da d'ana dan haka banga amfanin zamana ba,su kuma suyi sarautar mugani" Tana gama fad'in haka ta fice kamar ta kifa dan bak'in cjki tana d'aukarwa kanta alk'awarin indai tana raye se d'anta yayi sarautarnan inba hakaba suduka su rasa. Bayan fitarta dukda b'atawa mutane rai da tayi hakan be d'ad'a FULANI da k'asa ba dan daman tasan arina kuma tasan yau ta rama cin kashi da rashin ladabin da ta d'auki shekaru tana yimata,haka kowa ya watse inda ita kuma can ta shiga fafutukar raba Sarki da matayun yaransa dama FULANIN kanta..... Domin gyara sharhi ko bada shawara ...07047530638. 'YAR GATAN MAMA✍🏻 *____________________________________* ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ LABARI/RUBUTAWA KHADIJA S.SAMINU ('YAR GATAN MAMA) MARUBUCIYAR 👇🏻 RAYUWAR MU! A WANI GIDA MAGANIN KAR AYI (Kar a soma) RANA DUBU (Ta b'arawo...) And now.... ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA 'DAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA ARZAI ALLAH YA SAKA MIKI DA MAFIFICIN ALKAIRINSA AMIN. ......Ina fatan alkairi gareki AUNTY MUMMY Allah ya sanya alkairi yasa anyi kenan ya had'a kanku keda abokiyar zamanki.Allah ya rabaku da 'yan shige da fice yakawo k'azantar d'aki amin...... .....So ya shigeni,,,,ye,,, ye,,, ye,,, So ya shigeni...k'auna kabani....Na rasa ta yadda zanyima bayani,,,Dan Sanka ya rigada ya tab'ani,,,ko da yaushe in kana kulani,,,zuciyata bata samun rauni,,,Azuciyata Kai giniii...da hannu bazai rushe shiba... ....Kalamai dad'ad'a Dan Kai nake,,, soyayya zanfad'a dakai nake,,, me kuma zanbid'a idan dakai?,,,wuya bazana shaba na tsallake,,,gidanka zanyiwa rufi,,,nakama hannunka mu tafi azuciyata Kai kafi,,,idanu bazai iya ganeshi ba hahh.... ....Da sanyin safiya idan natashi,muryarka nafiso naji afarko,,,katashi lafiya Sam bani fashi sanin hakan shizai sakamini k'arkko,,,ya kake ciki,shi na binciki,inji me kaci,nima shi zana ci,,far in cikinka nawanehehe hawayenka bazana so bahahh,,,so ya shigeni yeyeye k'auna ka bani😉🥱😴🤭🤐 Na rufe bakina karsu jini nawad'a shauk'in wak'ar fasihin mawak'inmu Umar M Shareef💗 ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ SHAFI NA 63&64 ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ Babu abinda GIMBIYA MAIMUNATU batayi ba akan taga burinta ya cika amma Allah bai bata nasaraba kullum se karb'ar mata mak'udan kud'ad'e akeyi akan burinta zai cika amma har yanzu jikake shiru.Ak'alla tayi shekara biyu zuwa uku tana k'ok'ari akan buk'atarta ta biya amma bata biya yadda take so ba sedai Sarki da Fulani sund'anja baya da 'yan sunfara Jan Mujaheed ajiki sedai abin nad'an lokaci ne lokaci kad'an sekaga sunrabu dashi idan ta bankamusu turare se su jashi ajiki su watsar da su,abinfa yafara damun 'yan biyu dukda su da mutanen masarautar sunfara fahimtar abin bana lafiya bane ba ammadai kowa ya Kama bakinsa yayi shiru. Bayan wasu shekaru da basu wuce uku ba kawai sai aka gayyaci Sarki zuwa wani taro acan wani gari dake nesa dasu ,dan haka Sarki ya wakilta YARIMA MUJAHEED yaje amatsayinsa hakan ba k'aramin dad'i yaiwa Gimbiya da Mujaheed ba dan haka cike izza yace MUSLIM ya rakashi,ko da sukaje ahanyar dawowarsu babu ciwo ba farmaki ajali ya dirarwa YARIMA MUJAHEED! Tashin hankali iya tashin hankali MUSLIM ya shigeshi shi da bayin da sukayi tafiyar,ko da sukazo da labarin mutuwarsa sai GIMBIYA MAIMUNATU ta birkice lallai Muslim ne ya kasheshi saboda yaga zai gashi sarauta,tijara ba kalar wadda batayi ba tare da ik'irarin suma duk sai sunbishi bamai hawa kujerar acikinsu.Ko da ya mutu sai asirin yasaki Mai martaba da Fulani suka dawo hayyacinsu suka rungumi yaransu 'yan biyu kyautar Allah,wata biyu da rasuwar wata ranar talata kawai aka wayi gari da tsintar gawar YARIMA MUSLIM scan k'ofar baya dake masarautar,rud'ani da firgici ya shiga zuk'atan mutane Sarki kuwa fita yayi daga hayyacinsa inda Fulani tunda abin yazo kunnenta ta fad'i shikenan bata sake magana ba sedai bi da idanu kawai sedai hawaye na zirara daga idanunta,ita kenan ta saka SINIYYA agaba ta rik'eta kamar k'aramar yarinya taita zirarar da hawaye gashi tanason magana amma ba damar hakan. Sarki ya shiga damuwa halinda Fulani ta tsinci kanta aciki Wanda hakan yasanya yazama wani iri,shekar Fulani d'aya tana halin ciwo tace ga garinku nan wannan mutuwa ta tab'a Sarki matuk'a da gaske Wanda bayan yafara dawowa cikin hankalinsa ne batare da yayi shawara da kowa ba ya shirts bikin nad'a HUSNIYYA domin cika wasiyyar mahaifiyarsa,dukda hakan ya kawo tsaiku wajan jama'a masu cewa mace bazata mulkesu ba amma Sarki yayi kunnen Uwar shegu dasu har komai ya kammala.GIMBIYA MAIMUNATU ba k'aramin hauka tayi ba Wanda k'arshe jini ya ringa fita ta hanci da bakinta yayi ajalinta. SARAUNIYA SINIYYA Tasha gwagwarmaya arayuwarta gaba d'aya sai dai tayi dace da dangin miji nagari masu k'aunarta Dan k'anwar mijinta mai suna AISHATU wadda ake Kira da MIMI tasu tazo d'aya sunason juna matuk'a da gaske Dan haka komai bazaka iya fassara alak'arsu ba idan kagani.Lokacin tunbayan auren sarauniya haihuwarta d'aya ta maida sunan d'an uwanta,Muslim Nada shekara Tara da rabi aduniya aunty Mimi ta haifi inda Muslim ya dage lallai irin sunanshi za'asakamata,haka kuwa akayi aka sanyamata suna MUSLIMAT inda kaso biyu da rabi na rainon Muslimat agun Sarauniya ne sabida shak'uwar dake tsakanin yaran Muslim baya rabuwa da ita saidai bacci yarabasu,muslimat nada shekara uku cif aduniya auntyMimi tazuba ta zuba maganin b'era acikin wani mazubi nufinta yasha muslimat ta d'aukabatare dakowa yasaniba ta zubamusu a lemo Dana murna zasu sha Sarauniya ta aiko d'aukarta lemon da bata shaba kenan se su anty Mimi ne sukasha inda se d'ebesu akayi baki d'ayansu,daga wannan lokaci Sarauniyat taci gaba da ruk'on Muslimat tare da koma cemata amaryar Muslim.... Bayan wani lokaci sunyi hankali sunfara soyayyarsu mai cike da zumud'i gwanin birgewa,soyayya suke kamar su cinye juna.Allah yayi Muslim da son musulunci da kishinsa kamar mahaifiyarsa Dan hakat yana yawan tafiya domin yad'a kalmar LA'ILAHA ILLALLAHU MUHAMMADUR'RASULULLAHI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA...... Astagfirullah...... Domin gyara sharhi ko bada shawara 07047530638 'YAR GATAN MAMA✍🏻 *____________________________________* ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ LABARI/RUBUTAWA KHADIJA S.SAMINU ('YAR GATAN MAMA) MARUBUCIYAR 👇🏻 RAYUWAR MU! A WANI GIDA MAGANIN KAR AYI (Kar a soma) RANA DUBU (Ta b'arawo...) And now.... ⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️ *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA 'DAYANSHI GA MAHAIFIYATA HAJIYA K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA ARZAI ALLAH YAJA DA RAI. 💞💞💞Zab'in raina..ba watta bayan ke kinsani, zamuyi aure ki zamma mata nikwa nazan miji💞💞💞 💖Soyayyace azuciyata ke d'aya na sakka💖 💖Ke kika dace nabai sadakina mu shige d'aga💖 💖Nak'I na kauce akanki ko Sara ko sassak'a💖 💖Ni na amince abani inbada komai na mallaka💖 💕Kinhana k'unci,,,, 💕Kinsaka barci ,,,, Gareni kinhana ciwon zuciya🖤🖤🖤 💖Nayi mafarki dani dakai munzam mata miji💖 💖Domin sadaki komai kace inyima bajan aji💖 💖Kazama Sarki nazama baiwa gareka babu ji💖 💖So na da zak'i ka d'and'anamin aharshena naji💖 💕Bashi da d'aci,,, 💕Nafiye naci,,, Akanka ance bani da zuciya 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻🤐 ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ SHAFI NA 65&66 ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ Sunyi nisa basaji basa gani game da soyayyarsu domin soyayya ce ta gaskiya wadda babu algus acikinta wato soyayyar tun yarinta,anriga anyimusu alk'awarin aure to kuma gashi yanzu ZULMAT ta shigo rayuwarsu batare dasun shiryawa hakanba to yanzu kenan Yaya za'ayi da wannan lamari? Shin zai rabu da d'aya ne ko kuma zai auresu duka? Tana zuwa nan atunanin da takeyi taji GIMBIYA ZULMAT akusa da ita tanamata magana akan ta kimtsa zasubar wannan daji ayanzu.Babu musu aka kare Sarauniya ta tashi sannan sukahau dawakansu sukaci gaba da tafiya. ****** Tunda suka isa wani kogo ajigace ta girgice ta dawo suffarta ta mutane kana tahau feshin wuta ta bakinta idanunta yayi jajur kamar garwashin wuta.... "Lallai yau antab'oni a inda ba'asan ni wacece ba dan haka ya zama wajibi nad'auki fans at a agun wad'annan k'ananun halittun Dan bazan tab'a yafewa abinda suka yimin ba" Kasancewar duk sauran macizan suma awahale suke yasa basu wani fuskanceta ba sedai zuwa nan da wani lokaci tukunna. ****** Koda sukabar wannan bak'in dajin mai matuk'ar duhu da sanyawa mutum tsoro sai suka shiga wani daji Wanda yake da hasken da ko allura kayar zaka ganta agun,wasu dogayen bishiyun dabino ne Wanda iya lissafinka bazaka iya lissafa suba sune suke ajere reras awannan dajin ta jikinsu akebi awuce ahakadai dak'yar suka samu suka wuce wannan daji batare da wani Abu ya same suba. Sund'auki tsawon lokaci suna tafiya daga wannan waje su shiga wannan waje haka suka ringayi had suka iso inda sukeson isowa wato WATA DUNIYA...... TO FA MUN ISO YANZU NE ZAMU SHIGETA DOMIN JI DA GANIN MENE DA MENE ACIKITA SANNAN MUGA WANDA ZAIYI NASARAR 'DAUKAR WANNAN TAKOBI,KUDAI KU BIYO NI KHADEEJAH CE DAI TAKU NAGODE. domain gyara sharhi ko bad a ko bad a shawara. 07047530648 'YAR GATAN MAMA✍🏻 NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA 'DAYA GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS ARZAI ALLAH YAJA DA RAI AMEEN. 💖Rabin jikina gata💖 💖Da hannu na nunata💖 💖Duk Wanda yak-kushe ta💖 💖Dani dashi fam-fam-fam💖 💖Idanu basu ganinta,bare hannu ya tab'ata,,,.......k'aunarki bani bari sam💖 💕Ka zama bango,,, 💕Jikinka nan zanzo injingina,,, 💕Nai maka ungo,,, 💕Ko yaushe kazo garen ba tambaya💖 ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ SHAFI NA 67&68 ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ Wata iriyar k'ofa ce mai masifar kyau wadda aka k'erata da zallar azurfa da lu'u-lu'u duk Wanda yayi tozali da ita se ya tsaya ya sake kallonta saboda yadda take d'aukar idanu,wata nahiya ce mai matuk'ar girma na ban mamaki Wanda girmanta yaci ahad'e garuruwa biyar zuwa acikin garuruwanmu sai a iya had'e kano,Kaduna, Niger,dama wasu cikin garuruwanmu ak'iyasi,kana saka k'afarka zakajita kan dutsunan wuta k'ananu Wanda suke malale aduniyarrr... Maimakon kasami garuruwa ko unguwanni acikin duniyar,sedai ka hangi wasu k'ofofi manya masu bala'in kyau da tsayi guda biyu,magabata sunsha bada labarin yadda wannan duniya take da kuma yadda abubuwan arzik'i mabanbata suke ciki,koda rundunoninsu suka iso farfajiyar duniyar kowa tsayawa yayi shida jama'arsa yana tunanin wacce k'ofa zasu shiga daga ciki domin cikar burikansu? NUJBEER 'DAN NAJABURU ne ya gyara tsayuwarsa jikin kakkaurar sandarsa tare da bud'e idonsa sosai yana kallon wannan k'ofofi guda biyu tare da lumshe idonsa sanda ya fuskanci k'ofar da zasu Shiga... SARAUNIYA SINIYYA ce ta buk'aci da abata ruwa domin tayi alwala tayi sallah tare da umartar jama'arta suma kowa yayi dansuyi nafila raka'a biyu domin samun nasara awannan yak'i da suka fito yi.Ko da rundunar SARKI KAMALUD-DEEN suka ga haka se suma suka d'aura alwalar tare da shigewa gaba suka jasu sallah... Bayan sun idar da sallah ne sukayi addu'o'i sannan SARKI KAMALUD-DEEN ya Fara bayani kamar haka.... Da temakon Ubangijinmu mukeson shiga wannan DUNIYA mai tarin al'ajabai domin d'aukaka kalmarsa,muna Neman d'aukinsa daya bamu nasara akan wannan niyya tamu,sanin kanku ne wannan DUNIYA dad'ad'd'iya ce mai shud'ad'd'en tarihi Wanda magabatan magabatanmu da Dana suka kasa ganin bayan Mak'iya Allah n cikinta,wad'annan halittu sun kasance mak'iya Ubangijinmu kuma mak'iya addininmu suna zaune awannan DUNIYA mai tarin tarihi da tarin dukiya,suna da manyan gumakai Wanda suke bautawa Wanda suka sassak'asu da gwala-gwalai da zinare da lu'u-lu'u, dukiyar da ke cikinta ba Wanda yasan adadinta ciki hardasu Kansu Wanda suke tare da ita,akwai wata TAKOBIN 'DAUKAKA wadda suka ginata zallar zinari fari da lu'u-lu'u da jauhari,kyawunta ya b'aci dan fad'ama b'ata baki ne,manyan matsafan cikinsu ne suka had'a k'arfi da k'arfe domin Samar da ita,tana yi musu amfani mabanbanta domin idan suka fito sukashigo duniyarmu suna amfani da ita tundaga farkon garin da suka shigo ta hanyar bud'eta daga cikin kufinta su cakata ak'asar wannan gari,to da zarar sun cakata tashiga k'asar garin to se ilahirin mutanen garin sun koma addininsu na kafirci tare da komawa k'asansu su mulkesu ko da kuwa basa so,manyan musulmai sunsha yanke shawara akan wannan takobi amma hak'ansu baya cimma ruwa ake ganunsu.Musulmai muna burin mallakar wannan Takobi ne saboda idan tadawo hannunmu shikenan mun karya alkadarin wad'annan hatsabiban kafirai kuma da ita ne zamu samu galaba akansu.Kafirai suna son mallakar tane saboda suma su sumulki ma'abota addinin musulunci. Akundin tarihi da muka karanta muji cewar... 'YAR GATAN MAMA ✍🏻 NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA 'DAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA ARZAI ALLAH YAJA DA RAI AMIN. NAFI SON BEGEN MUHAMMADU HAR A K'ARSHEN RAYUWATA. 💖💖💖💖💖💖💖 Yau bayani ke gare ni,,, Gashi zanwak'e Ku jini,, Ko da ba ilimi gareni ba.. Son MUHAMMADU❤️yayi kanta 💖💖💖💖💖💖💖💖 Can a birnin zuciyata,,, Sonka shi ne tanadinta,, Zuciyata ta aminta,,,,, Son ka gama mamayeta 💖💖💖💖💖💖💖💖 Jibrilu yazo gareka,,, Sai yace maka ankira ka,, Zakaje gun rabbananka.. Musd'afa ka samu gata 💖💖💖💖💖💖💖💖 ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ SHAFI NA 69&70 ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ A littafan tarihin wannan duniya duk munkaranta hakan hakanne yasa ilahirin masadautun da muke dasu muka had'e kanmu domin jiran wannan rana muzo muma mugwada tamu sa'ar muna rok'on Ubangiji ya bamu nasara. K'ofa ta biyu suka tunkara wadda tun kafin su isa gareta ta bud'e da matuk'ar sauri yadda seda suka kare idanuwansu saboda wata iska mai k'arfin gaske data fito daga cikin k'ofar... YARIMA MUSLIM ne ya zare takobinsa tare da sanya k'afarsa bayan yayi Bismillah ya d'aga murya sosai tare da d'aga hannunsa sama yace "Allahu akhbar!"yasa Kai ciki inda mazaje suka goya masa baya. Acan waje kuwa GIMBIYA ZULMAT ce ta tari SARAUNIYA SINIYYA akan abata Kalmar shahada tanason shiga addininsu kafin su shiga,lokacin da su ALJANI DUUJALA suka ji haka daga inda rundunarsu take sun so zuwa su hanata amma sai sukai tunanin kodai itama irin tasu zatayi suka hanata,batare da b'ata lokaci ba aka lak'anawa GIMBIYA ZULMAT Kalmar shahada tazama cikakkiyar musulma kamar kowa ta dawo sabuwa dal babu wani datti atare da ita,yayin da aka fad'amata sunaye se tace babu sunan da take so se sunan da aka fad'amata GIMBIYA AMINATU..! Farin cikin mutanen wajen baya fad'uwa domin kowa jinsa yake cikin farin ciki saboda ZULMAT tana da shiga rai ga kuma uwa kyanta da idan kana tareda Ita bakason rabuwa jizakai ta mugun shiga ranka (Kamar yadda nima k'aunarta ta mamaye ni🤪) sai bayan komai ya kammala ne suka rankaya suka takewa mazan baya. Koda su YARIMA MUSLIM suka shiga tunkafin suje ko'ina suka ga gwarazany mayak'a ajeren ajikint wani dog on bango Wanda kowannensu hannunsa d'auke da Takobi ya zareta yana tsaye kamar sassak'ashi akai agun ba tsayuwa yayi ba.Ko da suka gama shigewa tas se k'ofar ta maida kanta ta rufe yayinda rufewarta keda wuya wad'annan mayak'an da yawansu zaikai kimanin dubu uku da d'ari biyar sukayo kansu bakunansu d'auke da mad'aukakin ihu mai razanarwa kowanne yanason d'aukar ran Wanda ya riska... Suma cike da jarumta da yak'ini suka d'aga takubbansu tare da d'aga murya kowa yana "ALLAHU AKHBAR! ALLAHU AKHBAR!!" Cikin k'ananun dak'ik'u suka cure waje guda suka fara rafka yak'i naban mamaki... Sun d'auki wajan awanni bakwai sunayi kafin su sami nasarar gamawa da wad'annan mayak'an sukayi gaba. Basu yi wani mad'aukakin nisa ba suka Fara jiyo wani irin gurnani Wanda kafin suyi wani tunani suka ga wasu manyan halittu agabansu masu matuk'ar muni da ban tsoro ta ke... 'YAR GATAN MAMA✍🏻 NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA MAHAIFIYAYA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA ARZAI ALLAH YA K'ARA LAFIYA DA RABO MAI AMFANI AMIN. ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ SHAFI NA 71&72 ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ Ta ke suka rankayo baki d'ayansu Wanda yawansu zaikai kimanin dubu biyar da d'oriya,wasu irin manyan halittu ne bak'ak'e masu matuk'ar muni Wanda daga kallo d'aya bazakai muradin sake wani ba,suna da tsayi da k'iba dan k'irar samudawa garesu,hak'waransu zak'o-zak'o masu mugun tsini,idanunsu d'ai-d'ai atsakar goshi masu girma jajaye gwanin ban tsoro,k'afafun kofato garesu idan ka kallesu dai duka babu kyan gani sedai kawai nace'astagfirullah' saboda yadda na fad'esuma abin babu dad'i ko kad'an,tsalle suke yi suna wani irin gurnani mai rikitarwa da tsoratarwa don har barazanar toshe dodon kunnuwansu yake yi. Babu abinda kake iya ji se ihun wad'annan halittu da kuma mazaje da Jaruman mataye wad'anda ashirye suke su bada rayukansu ga ADDININ MUSULUNCI..! Sara suka had'e da yanke-yanke shi kad'ai sukeyiwa junansu inda wad'annan halittun suke had'awa da wani siddabaru domin b'acewa suke yayinda d'aya cikin jaruman suka kawo musu Sara da suka sedai su nemesu su rasa.Cikin ikon Ubangiji haka suke wannan artabu tare da rud'ewa jikake suna "ALLAHU AKHBAR! ALLAHU AKHBAR!!" Fad'uwar kafirai kawai kakeji k'asa babu k'ak'k'autawa. Sun d'auki tsawon lokaci kafin su gama da wad'annan mugayen halittun,da yawa cikinsu sun sami raunuka amma ahaka suka dage domin cigaba da tafiya. Tsawon dak'ik'a d'ari Tara da sittin da uku suna tafiya batare da wata Matsala ba kawai suka Fara hango wata mulmulalliyar guguwa tana yowa sama tana k'asa tare da tawowa inda suke da gudun gaske.... Cike da k'arfin zuciya da jarumta suka had'a baki suka cigaba da kabbara cikin d'aga murya tare da d'iba da azababben gudu suka tunkari guguwar... Isarsu gareta ke da wuya suka nemeta suka rasa.Inda sunayin gaba kad'an wucin wuta ya addabesu domin ji sukeyi kamar zasu k'one saboda azababben wucin wutar,koda suka isa inda wutar keci wuta ce bata wasa ba Dan se ahad'a Mayan gidajen zamaninmu saba'in kafin kagano iyakar inda wutar ta tsaya.Kabbara suke yi suna Kiran Ubangiji babu gazawa take wannan wutar tayi sama kamar anjefata inda sunakai dubansu wajen zuka ga wajan yazama wani wawakeken rafi cike da ruwa kamar kasa hannu ka d'ebo sedai babu hanyar wuce wa.... 'YAR GATAN MAMA✍🏻 NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA ARZAI ALLAH YABADA TSAWON RAYUWA MAI AMFANI AMIN. ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ SHAFI NA 73&74 ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ Wannan shi ake Kira ga samu ga rashi,ko wannensu ya tsaya yana tunani tare da rok'on Ubangijin sammai da k'assai da ya dafamusu ya kawo musu d'auki daga sharrin dake wannan DUNIYA.SARAUNIYA SINIYYA da dokinta ke kusa-kusa da wajen ta d'aga sharb'eb'iyar takobinta tare da jansa ta d'aga murya tare da girmama Ubangijinta Wanda yafi kowa ta danna cikin ruwan ba tare da jin komai ba,ganin haka yasa GIMBIYA ZULMAT take Mata baya inda suma suka rufa musu baya bakunansu suna fad'in "ALLAHU AKHBAR! ALLAHU AKHBAR!!" Haka suka rud'e suna fad'i ba k'ak'k'autawa.Ga mamakin wasunsu koda suka shiga se suka jisu kan dandanyar k'asa inda kuma wasunsu hakan ba bak'on abu bane awajansu dan sunsan kad'anne daga makircin mak'iya Ubangiji,wasu kalolin halittun ruwa ne suka dinga firfitowa yadda suke da yawa kai bama zaka fara tunanin sanin adadinsu ba,duk wasu dabarun yak'i yi sukeyi amma halittun k'ara tuttub'owa suke yi suna sake wani irin yawa inda suka fara karaya ganin yadda mutanensu suka fara zubewa k'asa wasu mugayen raunuka wasu kuma matattu. Ba k'aramin lokaci suka d'aukaba kafin Ubangiji yabasu nasarar gamawa da wannan halittun agajiye suka yi gaba. Ko da suka yi gaban basu tsinci Kansu ako'ina ba se wani waje wanda aka masa wani irin gini mai hawa-hawa wanda hawansa idan kad'aga kai baka isa ka gano k'arshenshi ba dan tsayin nasa ya wuce afad'eshi, wasu tagogine ajikin ginin k'anana-k'anana abin har ya b'aci dan idan agininmu ne na nan abin zai zama asaka bulo d'aya atsallake d'aya haka wajan yake kaidai kawai sedai ka kalla.Haka suka cigaba da kutsawa ciki suna cigaba da ambaton UBANGIJIN MUSULUNCI babu gajiyawa atare da su ko kad'an,sunyi tafiya mai suna tafiya,yayin da suka Kai rabin ginin kawai suka fara jiyo haniniyar dawakai tako'ina kamar kunnuwansu zasu fashe,kalle-kalle suke yi amma basu ga ta inda ake tunkaro suba kawai sai jin harbi sukayi da mashi kamar ruwa sakinsa kawai ake tako'ina,cikin jarumta da kuma k'warewa afannin sanin kalolin makirci NUJBEER 'DAN NAJABURU ya bud'e tafukan hannayensa tare da rufe idonsa take kafin k'iftawar ido wasu kibbai da masu masu azababben yawa suka hau fitowa ta hannun nasa suna isa wajan wad'ancan cikin k'ank'anin lokaci wad'anda suka turoma suka koma can garesu inda suka b'arar da su baki d'ayansu. Kabbara dandazon MUSULMAI suka d'auka tare da cigaba da tafiya,batare da sun ankaraba wasu k'ananun aljanu masu had'arin gaske suka dinga fitowa ta tagogin jikin wannan ginin,ko wace taga seda aljanu d'ari suka fito daga cikinta, k'ananun kawuna garezu inda suke da k'aramin jiki se kuma jikinsu shima k'arami yayinda wasu k'ayoyi ke shimfishe ajikinnasu se kuma harsensu dogo tsininsa kamar mashi kaifinsa kamar takobi,tunkarosu sukayi da azababben gudu yayinda cikin ikon UBANGIJIN MUSULUNCI kafin su iso inda suke sukadinga zubewa ak'asa shirif-shirif matattu. Hamdala suka yi tare da godewa UBANGIJIN MUSULUNCI bisa d'aukin da yake ta kawo musu batare da ya bari sun fad'i ba.... ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMADUR'RASULULLAHI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA💖 'YAR GATAN MAMA. NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA 'DAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA ARZAI ALLAH YAJA DA RAI YAJIK'AN MAGABATA AMIN. ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ SHAFI NA 75&76 ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ Sunsha matuk'ar wahala wadda tasa duk suka fara canza kamanni dan yanzu ya zamana da k'yar suke cigaba da tafiyar,babu komai a ran mafiya yawansu banda tsoron me ze je yazo domin inda suka shiga ayanzu dole tsoro ya shiga zuk'atansu dan wani irin kogo ne mai azababben duhu na masifa ga wasu irin sautinka da suke tashi a cikinshi ba tare da sunga me fidda sautikanba,kowannen su hannunsa d'auke da itacen wuta yana haska gabansa,ba abinda sukejin k'afafunsu na takawa se k'asusuwa mabanbanta Wanda suka kasa gane na mutane ne ko kuma a'a? Wata iriyar azababbiyar iska ce mai matuk'ar k'arfin gaske ta taso daga cikin kogon tayo Kansu. Kabbara suka had'a baki suka sake yi wadda daman can ita ce d'auke abakunan nasu, kamar k'iftawar ido haka iskar ta d'auke sedai ta samu nasarar zubar da mutane da yawa dan ta zubda mutune sama da ashirin yayin da sauran da suka rage suka tsaya akan k'afafunsu ta k'yar sannan suka cigaba da tafiya... Suna yin gaba kad'an suka ga hanyar ta rabe biyu hagu da dama inda saitin inda suke ya had'e jikinsa Kai bazaka tab'a cewa hanya ceba,kallon kallo suka Fara yi tsakaninsu kowa na tararrabin hanyar da zaibi ta kaishi ga asalin inda yake son zuwa dan kowa ya tabbatar da wajan ya koma haka ne domin ajuyar musu da hankali su kasa gane ainahin inda zasu bi,tsakaninsu kawai suka yanke shawarar subi hanyar da ke dama da su wadda take bak'ik'k'irin baka gano komai acikinta se azababben bak'i na tashin hankali. Had'a baki suka yi tare da d'aga takubbansu suka ruga da azababben gudu izuwa wannan duwun,k'ara suka Fara ji me had'e da kuka had'e da shasshek'a ana fad'in " Ku temake ni bayin Allah zasu cutar dani...Allah ka kawon d'aukink" Ai kawai se maganar ta katse suka sake jin ihu had'e da k'arar da tafi ta baya,basu tsaya ba suka ci gaba da tafiya suna kiran UBANGIJIN MUSULUNCI! Wani waje suka iso Wanda yake da d'an haske dan kana iya ganin gabanka da bayanka,babu zato bare tsammani kawai suka hangi wani matashi Wanda shekarunsa zasui talatin da biyar zuwa da shida sanye da kayan bayi irinna jikin bayin masauratar SARKI KAMALUD-DEEN yana kwance ak'asa jini na zuba daga sassan jikinsa jikinsa d'aure da kakkaurar igiya an mammatse shi da ita dagani yana cikin azaba se fad'i yake yi " 'Yan uwana kuzo Ku temaka mini ku kwance ni kada na rasa rainaaa"_Wasu daga cikin bayin da ke sanye da irin kayan jikinsa suka yi kansa inda sauran suka ci gaba da tafiyarsu zuciyarsu banda ambaton UBANGIJIN MUSULUNCI babu abinda take yi. Ko da suka isa inda wannnan mutumin yake yana ta kukansa duk yabi ya basu tausayi matuk'a gaya, suna zuwa jikinsa domin suyi dabara su kwance shi kawai basu zata ba suka dinga jin wata mahaukaciyar dariya wadda ta ke barazanar toshe kunnuwansu yayin da k'asar wajan ta dare biyu suka shige cikinta inda shi kuma mutumin da suka je temako yazama wata murtukekiyar halitta ya had'iyesu baki d'ayansu. Ko da suka ci gaba da tafiya basu tsinci Kansu a ko'ina ba se gaban wani DUTSE me mugun girma da tsayi Wanda suka yi imanin cikinsu babu wani Wanda zai iya hawansa ko makamancin haka, YARIMA MUSLIM ne ya d'aga takobinsa me azababben tsayi tare da cakawa ajikin dutsen.... Ga mamakinsu base suka ga ya b'ace ba kamar dama babu shi awajan⚔️ ⚔️⚔️⚔️⚔️Wani haske suka Fara hangowa daga nesa dasu can saman wani d'an k'aramin mulmulallen DUTSE ⚔️⚔️⚔️⚔️ ⚔️⚔️⚔️⚔️TAKOBIn ce akansa tana cikin murfinta Wanda jikin murfin nata ke d'auke da zinare da lu'u-lu'u,matsawa wajan suke yi a hankali yayin da idonsu ya sauka kan mulmulallen dutsen wanda ya kasance zallar GOLD me azababben kyau haskensa ya haske wajan... Kowa ya zo inda yake son zuwa amma ya ja ya tsaya ya kasa taka k'afarsa ya k'arasa gaban dutsen kamar wanda yake gano mutuwarsa awajan. NUJBEER 'DAN NAJABURU da ya gama galabaita yaja k'afarsa da k'yar tare da kallon sauran mutanen suke tare ya kuma rik'e Takobinsa da kyau sannan ya tunkari inda TAKOBI n ta ke domin so yake ya d'auka kafin kowa ya dawo daga duniyar tunanin da ya shiga,nishad'i ne ya Kama shi yayin da zuciyarsa ta cika da far in ciki ganin babu abinda ya sa me shi ya isa jikin Gold d'in tare da fad'in sunan UBANGIJIN MUSULUNCI a rarrabe jikinsa na rawa ya d'ora hannunsa jikin dutsen da niyyar ya d'auki Takobin kawai batare da ya Lura ba tuni wasu macizai sun zagayeta sun fiddo harsunansu waje yayin da kafin yayi yunk'uri wata iska mai k'arfin gaske ta d'ebeshi ta watsar da shi can gefe daban. Duk abinda ya faru akan idonsu Sarauniya dan haka kowa ya sake tsayawa yayin da tsoronsu ya ninka na da... ⚔️YARIMA MUSLIM ne ya d'aga Takobinsa tare da rugawa wajan da azababben gudu inda GIMBIYA ZULMAT ta mara masa baya⚔️ Ko da isarsa wajan Macizan sun nunku sunfi na baya yawa, cikin jarumta ya d'agata tare da sare kan wasu daga macizan,inda sake d'agawar da zaiyi ya ga Takobin ta rabe biyu.GIMBIYA ZULMAT ce ta dira gabansa tana wani irin wuci tare da mik'awa Yarima Takobin hannunta ita kuma tana d'aga hannunta se ga wannan makirar Takobin ta bayyana ahannun nata tana ta shek'i da d'aukar idanu, tana zuwa hannunta ta saita ta inda Macizan suke wanda ga mamakinta sunk'ara yawa kamar wasu gero saboda yadda suka cakud'e waje d'aya suka lullub'e Takobin.Tana saita su da ita wani haske ya fito daga cikinta ya sauka Kansu wanda ta ke suka Fara zubowa k'asa babu k'wari... Matsawa ta ke yi gabansu suma suna matsawa yayin da wasu tuni sungudu wasu kuma lokacinsu ya riske su... Isarta jikin Gold d'in ke da wuya ta saka hannunta jikin Takobi tare da rufe idonta tace "ALLAHU AKHBAR..!" Ga mamakin su se suka ga ta Ciro TAKOBIN 'DAUKAKA! Tsayawa tayi akan k'afafunta sosai hawaye na bin idanunta jikinta na rawa kamar mazari yayin da kukanta yafara k'arfi idanunta sunyi jawur... 'Dago dara-daran idanuwanta tayi tare da sauke su kan YARIMA MUSLIM ta nemo jarumta ta sakar masa wani lallausan murmushi tare da d'aga hannunta da TAKOBIN 'DAUKAKA ta ke kai ta mik'a masa tare da girgiza masa kai alamun tabbatarwa, kallonta yayi sosai da sosai tare da d'an had'e mata rai kad'an... Fuskar da tayi bazai karb'a ba yasa ta saka hannunta d'aya tare da ruk'o hannunsa d'aya ta d'ora masa ita sannan ita kuma ta juya ta koma inda su Sarauniya suke. Motsin NUJBEER 'DAN NAJABURU suka ji daga bayansu,ko da suka juya se suka ganshi jikin wata rijiya hannunsa d'auke da guga ya d'ebo wani shud'in ruwa acikinta,kafin su ankara suka ga yad'aga ruwan ya zubashi ajikinsa tundaga tsakar kansa.Mamakine ya cikasu ganin ya dawo d'an k'aramin yaro me azababben kyawu...... Allah ka tsarkake mana zuciyoyinmu ka barmu ahanyarka da'iman.Allah bamu nufi kowa da sharri ba Allah ka lalata shirin duk wanda ya shiryamana mugunta karka bashi sa'a akanmu ya Allahu amin. 'YAR GATAN MAMA✍🏻 NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA ARZAI ALLAH YA K'ARA MA IYAYENMU LAFIYA AMIN. ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ SHAFI NA 77&78 ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ Mamakinsu ya kuma k'aruwa sanda ya sake d'aga ruwan ya kuma zubashi tun daga tsakar kansa har k'afafunsa,ai baikai ga sauke hannunsa ba ya dawo babban mutum me kimanin shekaru sittuna au saba'una🤪'tabd'ijam shi da yakeson zama saurayi me ji da rayuwa hakamadai ai ana jika' Ai da gama wannan tunanin suka ga ya sake d'aga gugar yana murmushi ya juye duka ruwan akansa batare da yayi ragowa ba,,,,,,,,,WARRR,,,,,,,,,Hhhh! Ai kawai maimakon yadawo matashi se ya zama wata mummunar halitta shi ba biri ba shi ba mutum ba,ta ke ya lek'a kansa cikin rijiyar inda ba b'ata lokaci yayi tozali da suffar da ya koma batare da wani nazari ba ya tak'ark'are ya saki wani razanannen ihu mai firgiyarwa wanda se da ya tsoratar dasu gaba d'ayansu,wani irin kuka yake yi mai had'e da gunji gwanin ban tsoro yana safa da marwa daga nan ya shek'a da gudu yayi can... Halin da ya fara shiga ne yakuma sanya musu wani azababben tsoro suka rink'ayin baya-baya kamar masu tsoron mayen da ke jin yunwa,,,,WARRR,,,,,,wasu kalolin k'uraje ne sukahau fitowa daga ko wane sashi na jikinsa inda sukadinga fidda wani irin ruwa mai tsutsotsi manya mabada k'yank'yami ta ke wasu macizai sirara suka hau fiddowa takowace b'ula dake wajan tare da tawowa inda yake, ai da ganin haka bai wata-wata ba ya arta da wani irin gudu kamar ya kai kamar ya fad'i haka ya k'arasa gaban d'aya rijiyoyin ya fad'a cikinta yayin da su Sarauniya suka ji babu dad'i amma babu damar taimakonsa tunda shi yakai kansa. ....... Koda ta dawo inda su Sarauniya suke se ta tsaya tana kallonsu murmushi d'auke afuskarta yayin da idanuwanta basu bar zubda hawaye ba,duk da sun so sanin me ya sakata kukan haka suka k'yaleta saboda babu damar wata tambaya ahalin da suke ciki. Sake rik'e Takobin yayi sosai a hannunsa ransa cike da mamakin GIMBIYA AMINATU da atunaninsa itama buk'atar Takobin ce ta kawota'to amma me yasa ta bashi?' Ya tambayi kansa bayan babu mai bashi amsa sai ita kanta ita kuma ya fuskanci yanzu tana cikin damuwa domin ko ba'a fad'amaka ba fuskarta ta nuna hakan dan haka kawai yaci gaba da kad'aita UBANGIJIN MUSULUNCI tare da biyo bayansu domin su koma can inda suka baro ragowar jama'arsu Wanda sunsan zuwa yanzu sunacan suna tunanin angama da su ne. Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Kalmar da dandazon Musulmai suka rud'e suna fad'a kenan saboda hangosu da suka yi nesa da su suna tawowa garesu... Farin ciki yau ya mamaye zuk'atan Musulman domin yau sunsamu sunga bayan zaluncin da ke WATA DUNIYA domin wannan Takobin ita ce suke k'arar da duk wata rundunar Musulmai da ita to yanzu kuma gata ta dawo hannun Musulmai kaga shikenan zalunci yazo k'arshe. SARKI KAMALUD-DEEN ne ya tashi fuskarsa d'auke da mad'aukakin murmushi ya je ya rungume YARIMA MUSLIM yana musu barka da arzik'i.SARAUNIYA SINIYYA bayan ta samu waje ta zauna MUSLIMAT ta iso inda suke tare da yi musu ban gajiya yayin da k'asan zuciyarta ke cike da k'unci jin GIMBIYA AMINATU(ZULMAT)ce ta samu nasarar d'aukar Takobin sannan ta bawa MUSLIM ita duk takaici nema ya kamata dan ji takeyi kamar taje ta shak'e Aminatu ko ta tsira soyayyarta ma ta tsira! Wani mugun kallo ta wurgawa Aminatu asirrance ba tare da kowa ya gani ba sedai ita wadda tayiwan daman idonta akanta yake dan haka kawai GIMBIYA AMINATU ta lumshe idonta tare da yi mata wani k'ayataccen murmushi Wanda seda gaban MUSLIMAT d'in yai mummunar fad'uwa dan ta yi imanin da YARIMA Aminatun taiwa wannan malalacin murmushin ba abinda zai hana ta shiga ranshi dan dole se hankalinsa ya kwanta, hakan yasa ta sake had'e rai tare da sunkuyar da kanta gudun karwani ya fuskanci me sukeyi batare data sani ba ashe duk abinda suke yi akan idon SARAUNIYA SINIYYA suke yinsa,,,,,,,WARRR,,,,. *****Sun d'auki tsawon kwana ashirin da d'aya awata duniyar saboda suna yiwa mutanensu da basu mutu ba magani,yau ne suke shirye-shiryen komawa garuruwansu domin angama duk wata tattaunawa da za'ayi akan Inda za'abar wannan TAKOBI an yanke abarwa Yariman ahannunsa domin antabbatar da shima dukiya bata gabansa,zuwa wannan lokacin GIMBIYA AMINATU ta yi dogon nazari akan soyayyar ta da Yarima ta yanke cewar ta rabu da shi ta rok'i Ubangijin Musulunci daya bata Wanda ya fishi dan haka ta yanke bazata koma garinsu ba saboda bataso tazama silar b'acin zumuncinsu shi da Muslimat danta lura da gaske bazata barmata shi ba. Bayan ta mik'e ne agabansu tai musu sallama kamar yadda addini ya tanadar sannan ta fara magana kamar haka... "Ina mai farin cikin zama tare da Ku dan gashi dalilin hakan na had'u da babban rabo na rabauta da addinin musulunci nasamu babban rabo rabon da zanyi farin ciki ace Mahifina ZALIMUZ-ZAMAN shi ma ya samu, ko ba komai zanyi alfahari Ni da Mahifiyata da Mahaifina munkoma ga mahaliccinmu muna masu yarda da shi. Sai dai kash! Inaji ajikina mahaifina bazai tab'a shiga Musulunci ba saboda yadda ya d'auki rayuwarsa, na gode miki dake da jama'arki yake adalar Shugaba domin kin kyautatamini azaman da nayi tare da ke,tabbas ked'in ta dabance kuma naji dad'in yadda kikai k'ok'ari akan d'anki ya soni Wanda sonsa shi ya zamemin silar samun dukkan rabo asalin zuwa na garin DEENUL-ISLAM da sanin mahaifina ZALIMUZ-ZAMAN shi ya turoni domin na shiga jikinku Ku yarda dani sannan nabiyoku yazuwa Wannan DUNIYAR domin bincikensa ya nuna masa rundunar kice zatai nasarar d'aukar takobi, na yarda da duk abinda yace amma k'asan zuciyata ba abinda yaturoni zan aikata ba dan inajin soyayyar Yarima har raina" Haka dai tabasu duk labarin yadda sukai da zancen sare kan sarakunan da ya cemata, da zancen fansar ran mahaifiyarta da taso d'auka sannan ta d'ora da fad'in... "Amma a yanzu na fuskanci mahaifiyata baiwa ce ubangiji yayi Mata kuma shi zaibi Mata hak'k'inta ita da baiwarta da ya kashe saboda son zuciyarsa. Sannan inamai baki hak'uri yake wannan Sarauniya mai adalci akan rabuwa daku da zanyi ayanzu, bazan koma garinmu SILDAN ba sedai zanshiga k'asashen musulmai domin d'aukaka Kalmar ALLAH! Kamar yadda na d'aukaka ta kakannina a baya,badan raina naso ba Zan rabu daku sedan farin cikin Wanda nazo dominshi shi da nasoyiyarshi dan na fuskanci zafin so bazanyi rashin adalci gareta wajan k'wace Mata farin cikinta ba abinda nayi miki abayama ina neman yafiyarki dan girman Allah!" Ta fad'a idonta akan Muslimat hannunta ahad'e alamar rok'o yayin da idanunta ke zirarar da hawaye. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Abinda leb'en SARAUNIYA SINIYYA ke maimaitawa kenan saboda yadda taji maganar GIMBIYA AMINATU daga ba zato ba tsammani ji take yi bazata iya rabuwa da Aminatu ad'an sabon da suka yi da ita ,tana tsaka da tunanin ta tsinkayi muryar MUSLIMAT cikin rauni tana fad'in... "Ki gafarce ni yake kyakkyawar bak'uwarmu ma'abociyar hak'uri da kyawawan d'abi'u,tabbas na cutar da ke da kalamai marasa dad'i tare da mugun kallo bayan ke baki tab'a kallo na se cikin sigar salama! A zamana dake na aikata babban zunubi Wanda nakejin tsoro kada ubangiji yak'iyin yafiya agareni bazanso zama SHADDADU 'DAN A'DU ba daya dad'e yana sab'on ubangiji yana bashi dama amma ak'arshe taurin Kai da son zuciya ya hanashi zuwa ga alkairin da ke kiransa harseda ya halaka kum.." Katseta Aminatu tayi ta hanyar tambayarta wane ne SHADDADU 'DAN A'DU? Nan taja hannunta suka sauna sannan tafara da fad'in... "K'ISSAR IRAMA ZATUL IMAD..! Wannan k'issar ita ce ta Shaddadu d'an A'du tafara daga. 'Allah ta'ala ya fad'a acikin alk'ur'ani cewa,"Ba ka ga ni bane yadda Ubangijinka ya aikata da A'DAWA da Irama zatul Imad,Wanda ba'a halicci wani gari a duniya kamarsa ba?" ~~~~~Alhamdulillahi nakusa gama wata duniya Ubangijin Musulunci ina godiya a gareka~~~~~ 'YAR GATAN MAMA✍🏻 NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA ALLAH YA K'ARA MIKI LAFIYA DA ARZIK'I MAI AMFANI🙌🏻💞💞 END.......✍🏻🙌🏻💞💞. ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ SHAFI NA 79&80 ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ K'ISSAR IRAMA ZATUL IMAD....🙌🏻💞💞 Taci gaba da fad'in... " Safiyanu ya ruwaito daga Mansur d'an Abiwa'il ya ce,"Wani mai suna Abdullahi d'an kulabata,ya fita Neman rak'uminsa da ya b'ata. To yana cikin yawo a daji cikin Sahara a k'asar ADON,sai yai kicib'is da wani birni mai ganuwa da benaye da gine-gine masu tsawo.Yayin da ya kusa da garin sai ya zaci zai sami wani agun amma sai baiga wani mai shiga ko mai fita agunba. Saboda haka sai ya sauka daga kan Taguwarsa ya d'aureta ya rataya takobinsa ya shiga ta k'ofar ganuwar.Yana shiga sai yaga wasu k'ofofi manya guda biyu,bai tab'a ganin irinsu a duniya ba,wajan tsawo da firma. Sai yaga itacen da akai k'ofar dashi na turaren Udu ne,an lullub'eshi da yak'utu yalo da ja,hasken su ya game ko'ina. Yayin da yaga ba kowa sai mamaki ya kamashi,ya bud'e k'ofar garin ya shiga sai yaga wasu irin benaye da aka gina su da Zubarjadi ya Yak'utu,an lullub'e su Lu'u-lu-u,sannan a kowane bene akwai d'akuna da aka gina su da zinare da azurfa da Yak'utu da Zubarjadi. Yayin da yaga haka kuma baiga kowa agurin ba sai tsoro ya Kama shi.Sannan sai ya dubi layukan da suke cikin garin,sai yaga a kowane layi ga bishiyoyi nan sunyi 'ya'ya a k'ark'ashinsu ga k'oramu nan tana gudana suna d'aukar ido saboda tsananin kyau da haske.Sai ya ce "Lallai wannan ita ce Aljannar da Allah ya siffata wa bayinsa a duniya.Na gode wa Allah da ya shigar dani Aljanna." Sannan sai wannan mutumin ya d'ebi duk abinda zai iya d'auka na daga zinare da azurfa da lu'u-lu'u da yak'utu da mirjani acikin wannan gari,sannan ya fito ya hawo taguwarsa yai ta tafiya har ya iso k'asar YAMAN ya sanar da mutane inda yaje da abinda yagani.Ya said a wasu daga cikin kayan da ya samo,bayan sun canza Kama saboda tsawon zamani. Sai labarin wannan mutum ya yad'u har ya Kai kunnan KHALIFA SAYYADINA MU'AWIYA d'an ABU SUFYANU,da khalifa yaji wannan Batu sai ya aikawa magajin garin Sana'a yace azo masa da wannan mutumin. Bayan da aka zo dashi Sayyadina Mu'awiya ya keb'e da shi ya tambayeshi abinda ya gani a tafiyar da yayi.Mutuminnan ya gayamasa duk abinda ya gani awannan birni da yanayin garin da kamanninsa.Sai sayyadina Mu'awiya bai gaskata labarin ba saboda girman abinda yaji,yacew bana zaton wannan labari naka gaskiya ne.Sai mutumin yace,to ai inada irin kayan da na d'ebo a garin, yace "Mene ne?" Yace "Lu'u-lu'u ne da almiski da za'far." Yace " Kawo mu gani." Da ya bashi ya sinsina sai yace baiji K'amshin almiskin ba,sai yasa a dandak'ashi,da aka dakashi sai K'amshi ya game wajan wajan,sannan sai khaifa gaskatashi. Daganan sai khalifa yace "Ya za'ai is an sunan wannan garin da tarihinsa da ya Gina shi? Ni dai nasan babu wani mutum da akaba shi irinw abinda akaba ANNABI SULAIMANU(AS),kuma ko shi bai gina irin wannan birnin ba." Sai wasu daga cikin waziran khalifasuka ce "AI yanzu babu Wanda zaka tambaya a sami cikakken labarin wannan gari a wajansa,sai Ka'abul Ahbari,kasa a kirashi ka sa mutumin ya b'uya ta yadda idan shi Ka'abun yana bada labarin ya zama yanajin abinda yake fad'a,domin irin wannan gari a irin wannan kamanni labudda zai kasance yana da wani labari me zaman kansa." Sai Sayyadina Mu'awiya (Allah ya k'aramasa yards) ya aika aka Kira Ka'abul Ahbari. Yayin da yazo Khalifa ya tambayeshi yace,"Ya Aba Ishak'a na Kira ka ne akan wani al'amari da nake fatan kana da masaniya akansa,Ka'abu yace, ya Sarkin Muminai,ka dace da Wanda zai baka labari tambayi abinda kaso." Sai yace,"Ka bamu labari akwai wani gari aduniyan man Wanda aka gina shi da Zinari da Azurfa,ginshik'ansa kuma na Zubarjadi da Yak'utu?Sannan ga k'oramu suna gudana k'ark'ashin bishiyoyi? Sai Ka'abu yace," Na rantse da Wanda raina yake cikin ikonsa,na zaci babu Wanda zai tambayeni wannan gari,amma yanzu Zan baka labari ya Sarkin muminai game da wannan birni da Wanda ya ginashi." ****Amma shi wannan gari kamar yadda labari ya risk I sarkin muminai,Wanda ya ginashi shi ne Shaddadu d'an A'du,shi kuma garin sunansa Irama zatul Imad, Wanda ba'a tab'a gina wani birni a duniya tamkarsa ba,Sai Mu'awiya yace,"To bamu labarinsa ya Aba Ishak'a." Sai Ka'abi yace,"Sunan Wanda ya Gina garin SHADDADU 'DAN A'DU, 'DAN IWASA , 'DAN IRAMA, 'DAN SAM, 'DAN ANNABI NUHU(AS) Shi Shaddad ance mutum ne me yawan 'ya'ya,ance 'ya'yansa sunkai dubu hud'u.Ya auri Mata dubu, ya rayu tsawon shekara dubu. Yayin da A'du ya mutu yabar 'ya'ya guda uku sune Shaddadu da Shadidu,da Irama,amma Shaddad shine babba saboda haka shi ya gaji sarauta,yayin da lamarinsa yai k'arfi yaci Sarakuna da yak'i ya mallake k'asashensu har mulkinsa ya game duniya baki d'aya.Gabas da yamma kudu da Arewa. Ance, mutane hud'u ne suka mulki duniya gabadayanta,biyu muminai biyu kafirai,muminan su ne Annabi Sulaimanu da Zulk'arnaini (AS) Kafiran sune,Shaddadu da Namaruzu d'an kan'ana. An ruwaito cewa,shi shaddadu mutumne me yawan karanta littattafai wad'anda aka saukar ga Annabawan da suka gabata, saboda haka duk lokacin da yaga siffar Aljanna a duniya. Saboda haka saiya tara waziransa ance yana da wazirai dubu,yace yanaso su Tara masa injiniyoyi da k'wararrun magina,na gabashin k'asa da yammanta. Yayin da suka tara su,sai ya umarcesu da su yawaita abayan k'asa su gano wurin da ya dace me kyan k'asa da k'oramu da bishiyoyi yanaso zai gina Aljanna awajan.Wad'annan masana suka shigat duniya sukaita yawo harsuka sami wani wuri a k'asar YAMEN Wanda zai dace da wannan buk'ata ta sarki.Saboda haka sai Sarki ya tura jnjiniyoyin man guda dubu a k'ark'ashin kowane d'ayansu akwai guda dubu, sukaje suka Tsara yadda za'agina garin,suka zanata asuffar murabba'a,farsakhi arba'in daga kowanne b'angare. Yayin da suka gama tsarawa da fidda harsashi, sai suka sanar dashi.Saboda haka sai Sarki Shaddad yace was Waziransa,shin wai baku San cewa ni ne nake mulkar duniya gaba d'ayanta ba? Suka ce k'warai kuwa Kaine,yace to inaso lallai kuje Ku taro gaba d'ayan zinare da azurfa da yak'utu da zubarjadi da almiski da za'afaran,da sauran dukkanin kayan ado na duniya baki d'aya." Suka ce"An gama" Sukaje suka Tara na k'asashensu sannan suka tura na sauran k'asashe aka tattaro gaba d'aya har Wanda suke hannun mutane,jama'a suka koma suna cikiniki da fatu memakon dirhami. Bayan da aka gamatara wad'annan a'loli sai maginan suka rik'a yin bulo da zinare da azurfa suka rik'a yin ginin dashi har suka katangance gaba d'aya garin. Bayan da aka gama sai kuma suka rik'a gina benaye da gidaje da d'akuna shima na zinare da azurfa, suna musu diraku na zubarjadi Kore da yak'utu ja,suka sa wad'annan gidajen da benayen suna fuskantar bishiyoyi wad'anda aka lullub'esu da yak'utu da lu'u-lu'u,sannan ga k'oramu nan suna gudana ak'ark'ashin benayen. Maginan nan suka k'awata garin nan da kayan ado iri-iri,Wanda duniya bata tab'a ganin irinsu ba.An ce tsawon shekarun da sukai suna gina wannan birni shi ne shekara d'ari uku. Bayan da suka kammala ginin sai suka sanar da sarki,shi kuma sai ya umarci duk Sarakunansa da waziransa da sukai shinfid'u na alfarma da dukkan kayan alatu na amfanin yau da kullum. An ce sai da suka shekara goma suna safarar kaya zuwa garin. Ka'abu ya ce, yayin da suka gama kai wad'annan kayayyaki suka sanar da Sarki,sai ya zab'i wazirai daga cikin makusantansa ya ce,su shirya tarewa zuwa IRAMA ZATUL IMAD. An ce sai da suka shekara ishirin suna shirye-shiryen tarewa agarin. Sannan sai Sarki Shaddadu ya tashi da shi da wad'anda ya zab'a da matansa da kuyanginsa,sai da ya rage tsakaninsa da shiga birnin tafiyar yini da kwana sai Allah ya turo masa Mala'ika ya ce da shi. "Idan ka furta cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah,Zan barka ka shiga garin,in ko baka yarda ba,Zan d'auki ranka yanzunnan." Da Shaddadu yaji haka,sai yai girman kai ya kafirce.Nan ta ke Mala'ika yai musu tsawa suka mace baki d'aya. Babu Wanda ya isa garin a cikinsu. Ka'abu ya ce "Wannan shi ne labarin IRAMA ZATUL IMAD ya sarkin muminai. Amma akwai wani mutum d'aya da zai shiga garin a wannan zamanin naka,har ma yazo ya ba da labarin abinda ya gani,zai shiga daji yana Neman Rak'uminsa da ya b'ace. Daga nan Allah zai nuna masa garin har ya shiga.Amma kafin shi da bayanshi ba wanda zai sake shiga. Allah shi ne mafi sani. MUSLIMAT ta sake rik'e hannun GIMBIYA AMINATU da kyau ta share hawayenta sannan ta ce " Kinji k'arshen K'ISSAR IRAMA ZATUL IMAD! Kinji yadda Ubangiji ya dinga bawa Sarki SHADDADU 'DAN A'DU damammaki yana yadda yaso.Ubangiji bai gajiya ba yasake turowa amasa tayin shiga musulunci amma son zuciya da girman kai suka hanashi. Tunda kikazo garinmu kika ce kinason masoyina naji na tsaneki na dinga cuzgunamiki abaya da ace nabar miki shi da zai zama ta silata zaki shiga ADDININ MUSULUNCI! Amma dake rashin rabo nima yana bibiyata haka na k'ek'ashe k'asa nak'i amincewa buk'atarki na dinga jifanki da munanan kalamai Kafira 'yar kafirai kaico na...Na manta ba ke kika haifo kanki akafirci ba haifoki akai kuma nima da Ubangiji ya so se ya sakoni acikin kafiran dan shi ne mahaliccin kowa da komai,nayi bak'in ciki da baki shiga addininmu ta silata ba,amma bazan yadda na k'ara kuskuren danai ba wajan rabaki da YARIMA MUSLIM domin ni kaina nayi imanin kinfini son sa. Na riga da na tabbatar da soyayyar da kikemasa ta gaskiya ce,kafin asamu Wanda ke yiwa wani irinshi za'a kwana a tashi ana dubawa ba'a samu ba,dan ni kaina na sani bazan iya rabuwa da rayuwata ba saboda soyayyar da nake masa,ke kuwa naga iya fiye da haka dan haka nake miki albishir da ki yarda dani ki yarda yanzu da zuciya d'aya nake tare da ke,a yanzu inajinki kamar 'yar uwata ta jini,sannan inamai baki hak'urin abinda na miki a baya,kuma inayi miki albishir da na barmiki YARIMA MUSLIM kuyi aure Ku zauna tare nikuma kuyimin addu'ar samun nagari kamar shi ko Wanda ya fishi... Koda ta gama maganar tashi tayi daga jikin GIMBIYA AMINATU tare da komawa can gefe ta zauna ta sunkui da kanta tana wasa da zoben azurfar hannunta.Bayan tashinta Gimbiya Aminatu kasa motsawa tayi se baki data bud'e dan wani mad'aukakin mamaki ne ya cikata tun sanda MUSLIMAT ta fara yi mata maganar... Wani irin farin cikine mara misaltuwa ya shiga ratsa ilahirin magudanar jinin jikinta,ji tayi tazama wata sakayau kamar yau tazo duniya dan murna bata shiryaba kawai taji wasu tagwayen hawaye suna zubowa daga idanunta,zuciyarta ce ta bata kamar bata yiwa Muslimat adalci ba idan tayi Mata haka dan haka itama ta mik'e tsaye tare da cire rigar k'arfen jikinta ta ajjeta gefe dan ta fara damunta tukunna ta fara takawa ahankali domin zuwa inda Muslimat ta zauna ta nutsu kamar me d'aukar darasi... Idanuwa ne suka tsinci Kansu akanta suna kallonta,dan sanda ta tawo seda ilahirin wad'anda ke wajen suka kalleta tare da jinjinawa sarkin da yayi mata kyakkyawar sura.GIMBIYA AMINATU (ZULMAT) tana da kyawu madararsa domin duk irin yadda ake fad'ar kyawun mahaifiyarta LUSH-SHIFAH ta fita sau uku,tana da kyan d'aukar hankali yanda ko sarki ne ke kan doki yai tozali da ita se yaji inama Fulani ce🙌🏻lol... Sanda taje ta tsugunna gabanta idonta na zubda hawaye,memakon ta fad'amata batai mata adalci ba idan ta rabata da masoyinta?ai kawai seta rungumeta tana k'ara sakin kuka tare da fad'in... "Nikam kin gamamin komai nagode miki har bansan me zan ce ba,kema Ubangijin musulunci ya mallaka miki wani kamar shi dannasan ba namijin da ya fishi" "Allah ya ga zuciyarta ya bata nagartacce kuma adalin namiji mai ji da mulki,ya ajje girma da iko yace shi yanason abashi auren GIMBIYA MUSLIMAT!" Sarkin zancen SARKI KAMALUD-DEEN ke wannan maganar yayin da idanun kowa ya koma kansa. Agurguje.....😁 Farin ciki ya shiga zukatansu dajin wannan abin arzik'i dan haka suka tafi da shirin nan da lokaci k'alilan za'asha shagalin biki harnasu MUSLIM. A hanyar komawarsu ne suka had'u da ALJANI ASH! inda ya taresu yana kuka yana basu labarin yadda ubangiji ya halakar da rundunar ALJANI DUUJALA! a k'ok'arinsu na hana su gimbiyar d'aukar TAKOBI,nan yake fad'a musu watay runduna ta MACIZAI sunzo domin suma su halakar da su se Allah y halakar da su da wuta inda duk suka Kama da wuta suka zama toka,shima ya tsirane saboda sanda sukaje basajar musulunci shi da gaske ya karb'a shiyasa baibisu d'aukar TAKOBI n ba. GIMBIYA AMINATU tayi mamaki tare da jinjinawa UBANGIJIN MUSULUNCI sannan ta rubuta TAKADDAR GAYYATA IZUWA ADDININ MUSULINCI YA KAIWA BABANTA ZALIMUZ-ZAMAN!... ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ Ko da tagama masa bayani se ya juya ya d'auki hanyar garin SILDAN cikin k'iftawar ido ya isa garin har cikin turakar SARKI ZALIMUZ-ZAMAN... ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ Su ma basu wani d'auki lokaci ba suka isa garin DEENUL-ISLAM inda farin ciki ya cika zuk'atan mutanensu kowa ka gani fuskarsa shar dashi ya wage baki kamar gonar auduga😁 Bayan shigar kowa b'angarensa ai tuni zancen musuluntar GIMBIYA AMINATU da aurenta da YARIMA MUSLIM da zancen auren MUSLIMAT da SARKI KAMALUD-DEEN ya bi ya karad'e kunnwan jama'ar masarautar sukaita k'ananun maganganu Hardai SARAUNIYA SINIYYA bayan ta huta ta sanar da kanta inda suke murna wasu kuma dai ta ciki na ciki kawai. ...Ko da isarsa garin se ya tarar da mayak'ansu duk a shirye shi kad'ai ake jiran fitowarsa ba abinda kakeji se haniniyar dawakai,ganin haka ya tabbatar masa da ya samu labarin duk abinda ya faru kenan,dan haka kawai ya sake komawa suffarsa ta wani farin tsuntsu mai tsananin kyawu ya rik'e takardar da bakinsa ya k'arasa turakar da ita,bai sake ba seda yaje dai-dai fuskar S.ZLMZ-ZMN sannan ya saketa inda shi kuma tundaga tawowarta ya tsaya cak yasan sak'o ne aka turomasa.Hannunsa ya d'aga ya dakatar da ALJANI ASH! da ke shirin fita tare da sa shi yadawo suffarsa yadda zai iya ganinshi... "Bud'e miniii" Ya fad'a da mad'aukakiyar muryarsa mai firgitarwa.Babu musu shikuma ya bud'e tare da karanta masa sannan ya sakamasa ita afuska yaji K'amshin tilon 'yarsa ZULMAT yaga rubutunta,amma ga mamakinsa se yaga ta saka AMINATOU💞Bawai baisan ta musulunta bane a'a sanin da yayi nema yasa ze fita da kansa domin yak'arta ya rabata da doron duniyar baki d'aya,Ashe shi tunaninsa gajere ne ita tuni ta rik'a har zata iya aikomasa da sak'on banza da wofi?( Allah k rabamu da rashin rabo amin).Ai yana gama tunani ya kalli Aljanin tare da wuramasa iskar bakinsa a ta ke ya sank'ame awajan. ...Ko da GIMBIYA AMINATU taji sak'onta shiru se ta tabbatar da lallai babu sa'a mahaifinta yana nan rashin rabo na d'awainiya da shi,kuma tana da tabbacin yanzu haka idan bata rigashi ba shi zaizo yaga bayanta harma al'ummar da basuji ba basu gani ba,hakan yasa cikin k'ank'anin lokaci tai shirin yak'i tare da fitowa a shiryenta sai kawai ganinta sukayi kana ta fad'amusu shirinta,babu yadda suka iya haka suka shirya amma babu SARAUNIYA SINIYYA dan rabuwa sukayi da ita saboda tana fama da mura. Shi kuwa ZALIMUZ-ZAMAN tunda ya zauna a inda yake yaketa faman tunanin yadda zaiyi yayiwa 'yarsa Zulmat kisan hulak'ancin da se duniya ta fad'eshi ta kuma danshi baisan wata Aminatu ba Zulmat kad'ai ya sani,tunani yake d'aurawa kafin yakai k'arshe se ya warware ahaka seda ya kwana uku curr ba tare da kuma yace wa mayak'ansa su koma sai ya shirya ba suma haka sukai kwanakin akan dawakai dan duk Wanda ya sauna yasan makomarsa gun shugaban nasu. A wannan hali Babbar rundunar gwarazan musulman ta iso cikin garin SILDAN yayin da mayak'an cikinta sukayi yunk'urin afka musu amma GIMBIYA AMINATU wadda suka sani da ZULMAT ta ratso ta dawo gaba yayin da sukai tozali da ita se kowa ya yada makaminsa ba tare da ya shiryama hakan ba. Gaban SARKI ZALIMUZ-ZAMAN ne yayi wata mummunar fad'uwa yayin da kansa ya sara jikinsa ya hau rawa alokaci guda wanda hakan ya matuk'ar bashi mamaki, "To me hakan yake nufi kenan?Tsoron 'yarsa yake ji ko kuma yau tsoron musulunci ne ya shige shi? Kai bazai yuwu ba" Ya fad'a yana gama mik'ewa tsaye tare da fitowa cikin shirin yak'i... "Wayyo,me yake faruwa dani ne haka yau? Banga haka amadubin tsafi na ba kuma me yasa hakan ke shirin faruwa da ni,tabbas idan dai-dai idanu na nake gani yau k'arshe na ne yazo amma idan sunsan wata basu san wata ba ina k'arasawa zansare kan maciyiyar amana kamar yadda na sare na uwarta itama naje na tsaface ta shikenan su sauran hatsabibancinsu mai sauk'i ne" Yana zuwa nan a tunaninsa yaja linzamin dokinsa yad'aga ya tunkare su da matsanancin gudu.Ko da ganin haka ta ke GIMBIYA AMINATU itama ta zaburo ta tunkaroshi cikin zafin nama da zafin zuciya tana kabbara da iyakacin muryarta inda suma sauran abinda ke bakunansu kenan ji kake "ALLAHU AKHBAR!" sunan Ubangijin musulunci ya karad'e kunnuwan mak'iya inda cikin nasara kuma sai zubda kafirai akeyi yayinda wasunsuma duk sunfara karaya dan duk alamu sun nuna yau musulman ne ke da nasara basu ba dan haka jikkunansu sunyi sanyi wasuma suka fara b'oyewa saboda tsira da rayuwa dan sunga halin da mai gayya mai aiki yake ciki... Can kuwa wajan Gimbiya Aminatu da Sarki Zalimuz-zaman yak'i suke gwafzawa kowa yana Neman ran d'an uwansa cikinsu ba Wanda yake saurarawa wani,kana kallon idanuwansu zaka ga zallar wutar k'iyayya na ci kamar ta k'ona gari ba kawunansu ba. ⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️ Sun d'auki tsawon lokaci suna yak'i tsakaninsu yayin da ak'arshe UBANGIJIN MUSULUNCI ya bawa MUSULMAI nasarar k'arar da mafi yawan kafiran inda ak'arshe ragowar rundunar SARKI ZALIMUZ-ZAMAN suka amshi gaskiya lokacin da suka zubda makamansu sanadin ganin GIMBIYA AMINATU ta sare kansa ya fad'i k'asa suka hangi tutarsu ma ak'asa yayin da suka ga tutar musulmai da kuma dandazon musulmai.Kuka Gimbiya Aminatu take rafkawa har numfashinta na sark'ewa sabida azabar da takeji acikin zuciyarta mahaifinta ya komawa mahaliccinsa ame babban laifi ga uwa uba girman kai da tsantsar zalunci,Idan ba Kalmar Allah ba mai zaisa ta kashe mahaifinta?sedai yanzu zatai alfahari da cewar ta kawo k'arshen zaluncinsa kuma tayi sanadiyar musuluntar mutanensu masu azababben yawa.Bayan komai ya lafa ne musulunci ya kafu agarin sannan suka koma garin DEENUL-ISLAM aka ci gaba da shirye-shiryen bikinsu. ⚔️⚔️⚔️⚔️ Rana bata k'arya sedai uwar d'iya taji kunya,anyi shagali iya shagali bikinsu ya k'ayatar ya samu halartar manyan sarakunan duniya dama Wanda ba Sarki ba inda k'arshe aka d'auki GIMBIYA MUSLIMAT akai masarautar SARKI KAMALUD-DEEN da ita yayin da GIMBIYA AMINATU akai garin SILDAN da ita kasancewar YARIMA MUSLIM shi aka nad'a ya zama Sarki yake mulkar mutanen tsohon azzulumin Sarki acikin adalci da gaskiya. Anyi komai komai ya k'are inda akabar masoya suke shan soyayyarsu Suna zaune cikin soyayya da k'aunar juna uwa uba mutunta juna da Kuma Gaskiya. Kowa yana alfahari da wannan had'in bama kamar SARAUNIYYA SINIYYA da kullum se ta godema mahaliccinta bisa wannan baiwa da Yayi musu baki d'aya. ⚔️⚔️⚔️⚔️ Bayan shekara biyu GIMBIYA AMINATU ta haifo santalelen d'anta namiji Wanda aka saka masa YARIMA ABDALLAH! yaro yanashan gata iya gata dan mutanen gari ma sunaji da yaron kasancewar yaron shiru-shiru ba shi da wata hayaniya kullum idan mahaifansa SARKI MUSLIM DA GIMBIYA AMINATU suka kalleshi se sunce ALHAMDULILLAHI🥰💞💞 ALHAMDULILLAHI ANAN NA KAWO K'ARSHEN WANNAN LABARIN NAWA MAI TAKEN⚔️WATA DUNIYA ...INA ROK'ON UBANGIJIN ABINDA NAYI DAI-DAI YASA NA 'DORE AKAN HAKA WANDA NAYI BA DAI-DAI BA YASA NA GYARA DAN ALFARMAR SHUGABA SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA. DAN ALLAH INA ROK'ON ADDU'ARKU GARE NI "ALLAH KA BAWA BAIWARKA KHADIJA LAFIYA MAI 'DOREWA KA BATA IKON BI DA LAFIYAR TA HANYARKA" NIDA DUK MUSULMI,ABINDA ZAKU CE KENAN NAGODE. DOMIN GYARA SHARHI KO BADA SHAWARA KU TUNTUB'ENI AWANNAN LAYIN...07047530638. Allahumma salli ala Muhammadur'rasulullahi sallallahualaihhi wasallama. 'YAR GATAN MAMA✍🏻